البقرة
Al-Baqara
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
الٓمٓ
Open ayah 2:1Alif Lam Mim.
ذَٰلِكَ ٱلۡكِتَٰبُ لَا رَيۡبَۛ فِيهِۛ هُدٗى لِّلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 2:2Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taƙawa.
ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Open ayah 2:3Waɗanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi.
وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ وَبِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ
Open ayah 2:4Waɗanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira.
أُوْلَٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدٗى مِّن رَّبِّهِمۡۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Open ayah 2:5Waɗannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma waɗannan su ne masu samun babban rabo. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da harufin <b>Alif </b> da <b>Lam </b> da <b>Mim </b> . Ban da ita wannan Sura da akwai surorin Alƙur\'ani da dama da Allah ya buɗe su da irin waɗannan haruffa. Da dama daga cikin malamai suna cewa, Allah ne kaɗai ya san abin da yake nufi da su. Wasu kuma sun yi ƙoƙarin bayyan ma’anonisu. Amma magana mafi inganci ita ce, Allah yana nuna mu\'ujizar Alƙurani ne ta hanyar ambaton waɗannan haruffa. Domin suna tabbatar wa larabawa cewa babu wanda zai iya kawo wani abu irin Alƙur\'ani, duk kuwa da cewa haruffansa su ne haruffan da suke magana da rubutu da su. Allah ya siffanta wannan Alƙur’ani da cewa, babu wani kokwanto a cikinsa, wato duk abin da ya ƙunsa tabbatace ne kuma gaskiya ne, don haka ne ya zama shiriya ga masu taƙawa, yana nuna musu gaskiya da bayyana musu hukunce-hukunce wanɗanda suka shafi aƙidunsu da ibadunsu da kuma mu’amalolinsu. An kira Alƙur\'ani da sunan Littafi duk kuwa da kasancewarsa a lokacin ba a tattara shi wuri guda ba; an yi haka ne domin a yi ishara zuwa ga cewa, nan gaba za a tattara shi wuri guda ya zama littafi wanda Musulmi a kowane lokaci za su riƙa karantawa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fayyace siffofin masu taƙawa waɗanda Alƙur’ani yake shiryar da su. Sun siffantu da siffofi guda biyar kamar haka: <b>Siffa ta farko </b>: Suna yin imani da gaibu. Gaibu shi ne duk abin da manzanni suka zo da shi, suka ba da labarinsa, kuma ido bai gan shi ba, wani tunani bai riske shi ba. Wannan ya haɗa da imani da ranar lahira da abin da ta ƙunsa na hisabi da mala’iku da labarin manzanni da littafan da Allah ya saukar gabanin zuwan Manzon Allah (ﷺ). Imani da gaibu shi ne yake bambance wa tsakanin mutum mumini da kafiri, saboda yana imani da duk wani abu da Allah ya ba da labarinsa ko Manzonsa ya faɗa ko da kuwa bai gano shi da hankalinsa ba. <b>Siffa ta biyu </b>: Suna tsayar da salla, wato suna yin ta kamar yadda shari’a ta koyar da su tare da kula da lokutanta da rukunanta da wajibanta da sharuɗɗanta. <b>Siffa ta uku </b>: Suna ciyar da abin da Allah ya arzuta su da shi. Sukan fitar da zakkar dukiyoyinsu, hakanan suna sadaka ta nafila da abin da Allah ya hore musu. <b>Siffa ta huɗu </b>: Su ne waɗanda suke yin imani da Alƙur’anin da Allah ya saukar wa Annabi Muhammadu (ﷺ) gaba ɗaya ba tare da ware wani ɓangare ko su riƙa karkatar da ma’anonin wani ɓangare nasa ba, kamar yadda ‘yan bidi’a suke yi ga wasu ayoyin waɗanda ba sa goyon bayan bidi’o’insu da aƙidunsu. Hakanan suna yin imani da dukkan littattafan da Allah ya saukar wa manzanni da annabawan da suka gabata, har da su kansu manzannin da annabawan. <b>Siffa ta biyar </b>: Su ne waɗanda suka tabbatar da zuwan ranar tashin alƙiyama da abubuwan da za ta zo da su na tayar da matattu da yi musu hisabi da saka wa mutanen ƙwarai da Aljanna; masu miyagun laifuffuka kuwa a saka musu da wutar Jahannama. An ware batun imani da ranar lahira duk kuwa da cewa ya shiga cikin batun imani da gaibu, saboda a zaburar da mutane ga ayyukan alheri a kuma tsoratar da su game da munanan ayyuka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗi sakamakon masu waɗannan siffofi da cewa, suna kan wata shiriya mai girma daga Allah mai yi musu tarbiya ta ƙwarai. Domin babu wata shiriya da ta kai siffantuwa da waɗannan siffofi. Don haka su ne waɗannan suke da babban rabo daga Allah, wato samun yardar Allah da gidan Aljanna ranar gobe alƙiyama.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ ءَأَنذَرۡتَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تُنذِرۡهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 2:6Lalle waɗanda suka kafirta, duk ɗaya ne a gare su, ka yi musu gargaɗi ko ba ka yi musu ba, ba za su yi imani ba.
خَتَمَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَعَلَىٰ سَمۡعِهِمۡۖ وَعَلَىٰٓ أَبۡصَٰرِهِمۡ غِشَٰوَةٞۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Open ayah 2:7Allah Ya toshe zukatansu da jinsu, kuma akwai wani lulluɓi a kan idanunsu, kuma suna da azaba mai girma. A nan Allah yana ba da labarin kafirai ne da irin taurin kansu wajen kafirce wa abin da Annabi (ﷺ) ya zo da shi na gaskiya. Allah ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, waɗannan kafirai sun kai matuƙa ga kafircinsu; yana da wuya wa’azinsa ya sa su saurare shi, har su yi imani, don haka kada kafircinsu ya dame shi. Domin Allah ya riga ya toshe musu zukatansu saboda zunubbansu, don haka imani ba zai sami hanyar shiga cikinsu ba. Kuma ya doɗe musu kunnuwansu saboda kafircinsu, don haka ba za su taɓa jin kiransa ba balle su amsa masa. Sannan akwai yanar da ta rufe musu idanuwansu ta yadda ba za su taɓa ganin gaskiya ba balle su yarda da ita. Saboda haka suka cancanci azaba mai girman gaske. Wannan yana nuna cewa, kafirci idan ya yi yawa a tare da bawa yakan toshe masa dukkan ƙofofin samun shiriya, duk kuwa yadda aka yi fama da shi ba zai taɓa karɓar gaskiya ba, don ba ya jin ta ba ya ganin ta kuma ba ya fahimtar ta saboda tsatsar zunubi da kafirci da suka lulluɓe shi.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَمَا هُم بِمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 2:8A cikin mutane kuma akwai waɗanda suke cewa: “Mun yi imani da Allah kuma mun yi imani da ranar lahira,” alhalin su ba muminai ne ba.
يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَمَا يَخۡدَعُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 2:9Suna ganin suna yaudarar Allah ne da waɗanda suka yi imani, amma kuwa ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu, kuma su ba sa jin hakan.
فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ فَزَادَهُمُ ٱللَّهُ مَرَضٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡذِبُونَ
Open ayah 2:10Akwai wata cuta (ta munafunci) a cikin zukatansu, sai Allah Ya ƙara musu wata cutar, kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi saboda ƙaryar da suke yi. Daga nan har zuwa aya ta 20 Allah (Mai tsarki da daukaka) yana mana bayanin munafuƙai ne tare da fallasa su da bankaɗo munanan siffofinsu don kowa ya gane su a kowane lokaci a kuma kowane yanayi. A lokacin da Annabi (ﷺ) yana zaune a Makka mutane kashi biyu ne: muminai sai kafirai. To amma bayan Musulmai sun yi hijira zuwa Madina, sai aka samu kashi na uku, su ne munafuƙai. Munafiki shi ne wanda yake bayyana Musulunci a bakinsa, amma yana ɓoye kafirci a zuciyarsa. Allah ya bayyana wasu siffofinsu a nan. Yana daga cikin siffofinsu suka riƙa bayyana imani da baki amma suna ɓoye kafirci a zukatansu, shi ya sa Allah ya ce: “Waɗannan ba muminai ne ba.” Kuma saboda wautarsu suna yin haka ne wai don a zatonsu suna yaudarar Allah ne tare da muminai, watau a tsammaninsu Allah bai san abin da suke ɓoyewa ba. Wannan ta sa idan yaƙi ya ɓarke tsakanin muminai da kafirai to su ba za a taɓa su ba, kuma ba za a taɓa dukiyarsu ba, sannan in an ci nasara a kan kafirai aka samo ganima, to tare da su za a raba. To amma ba su san cewa, kawunansu kaɗai suke yaudara ba, domin babu mai cutuwa da abin da suke yi sai su kaɗai. Allah ya ce, akwai cuta a zukatansu. Cutar kuwa ita ce ta shakka da ruɗani da munafunci, wannan ya sanya Allah ya ƙara musu wata cutar, domin duk sanda aka saukar da wata aya ga Annabi (ﷺ) to za su kafirce mata, sai cutar zukatansu ta ƙara hauhawa, haka za su yi ta rayuwa har mutuwarsu sannan su je su tarar da azaba mai raɗaɗi tana jiran su a lahira saboda ƙaryar da suke ƙirƙira da kuma ƙaryata Annabi (ﷺ) da suka riƙa yi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Alamar munafiƙi uku ce: Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya, kuma idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan kuma aka amince masa sai ya yi ha’inci.” [Bukhari #33 da Muslim #59].
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ قَالُوٓاْ إِنَّمَا نَحۡنُ مُصۡلِحُونَ
Open ayah 2:11Idan kuma aka ce musu: “Kada ku yi ɓarna a bayan ƙasa”, sai su ce: “Mu fa masu gyara ne kawai.”
أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡمُفۡسِدُونَ وَلَٰكِن لَّا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 2:12Saurara, lalle su su ne maɓarnata, amma ba sa jin hakan.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ ءَامِنُواْ كَمَآ ءَامَنَ ٱلنَّاسُ قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ كَمَآ ءَامَنَ ٱلسُّفَهَآءُۗ أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلسُّفَهَآءُ وَلَٰكِن لَّا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:13Idan kuma aka ce da su: “Ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani”, sai su ce: “Shin za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?” Saurara, lalle su ne wawayen, sai dai ba sanin (hakan). Har ila yau, Allah yana ƙara bayyana wani mugun halin na munafuƙai wanda shi ne, duk sa’adda sahabbai za su yi musu wa’azi su nuna musu kuskurensu, su neme su da su tuba zuwa ga Allah, sai su riƙa yi wa sahabban kallon wasu wawaye jahilai marasa hankali da har suka yarda suka bar garuruwansu da gidajensu da dukiyoyinsu suka yi hijira don wai su yi addinin Musulunci; sai su nuna su fa ba za su taɓa yin wauta irin wannan ba. Sai Allah ya mayar musu da martani da cewa, ai ko su ne tsantsar wawaye, tun da har suka guje wa abin da zai amfane su na imani da Allah suka rungumi abin da zai cutar da su saboda tsabar jahilci da wauta.
وَإِذَا لَقُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَوۡاْ إِلَىٰ شَيَٰطِينِهِمۡ قَالُوٓاْ إِنَّا مَعَكُمۡ إِنَّمَا نَحۡنُ مُسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 2:14Idan kuma suka haɗu da waɗanda suka yi imani sai su ce: “Mun yi imani.” To amma idan suka keɓanta da shaiɗanunsu (iyayen gidansu) sai su ce: “Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kwai izgili ne muke yi.”
ٱللَّهُ يَسۡتَهۡزِئُ بِهِمۡ وَيَمُدُّهُمۡ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ
Open ayah 2:15Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ɗimuwa. Wata muguwar sifa ta munafuƙai kuma har ila yau ita ce, yin fuska-biyu, wato idan sun shiga cikin muminai ko sun haɗu da su a hanya sai su riƙa nuna musu suna tare da su, su ma wai muminai ne. To amma da zarar sun koma ga manyan kafirai ko Yahudawa sai su nuna musu cewa, mu fa tare da ku muke, ku bar waɗancan muminai izgili kawai muke yi musu, amma zuciyarmu ba ta son su ko kaɗan. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa: Ai Allah ne yake yin izgili gare su, shi ya sa ya ƙyale su ba tare da ya ba wa muminai dama su gama da su ba, yake kuma ƙawata musu munanan ayyukansu, har ma suke zaton ko a kan gaskiya suke, ba su san cikin ɗimuwa da duhu suke rayuwa ba.
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلضَّلَٰلَةَ بِٱلۡهُدَىٰ فَمَا رَبِحَت تِّجَٰرَتُهُمۡ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ
Open ayah 2:16Waɗannan su ne suka musanya shiriya da ɓata, don haka kasuwancinsu bai yi riba ba, kuma ba su zamo shiryayyu ba. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana fito da haƙiƙanin matsayin munafuƙai, ta yadda suke nuna tsananin sha’awarsu da ƙaunarsu ga hanyar ɓata, suke ɗaukar ta a matsayin wata kadara mai daraja da za su iya kashe ko nawa ne don su mallake ta. Don haka suka amince su bayar da shiriya a matsayin kuɗin da za su fanshi wannan mummunar kadara (wato ɓata) da ita. Wannan shi ne haƙiƙanin kasuwancinsu a duniya; ashe kuwa wannan kasuwanci ne maras riba, kuma mai cike da hasara ta duniya da ta lahira.
مَثَلُهُمۡ كَمَثَلِ ٱلَّذِي ٱسۡتَوۡقَدَ نَارٗا فَلَمَّآ أَضَآءَتۡ مَا حَوۡلَهُۥ ذَهَبَ ٱللَّهُ بِنُورِهِمۡ وَتَرَكَهُمۡ فِي ظُلُمَٰتٖ لَّا يُبۡصِرُونَ
Open ayah 2:17Misalinsu kamar misalin wanda ya wahala har ya kunna wuta ne, yayin da ta haskaka abin da yake daura da shi, sai Allah Ya tafiyar da haskensu Ya bar su cikin duffai ba sa gani.
صُمُّۢ بُكۡمٌ عُمۡيٞ فَهُمۡ لَا يَرۡجِعُونَ
Open ayah 2:18Su kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka ba za su taɓa dawowa (kan gaskiya) ba. A nan ma Allah yana ƙara yi mana bayani ne a kan waɗannan munafuƙai, inda ya yi mana kwatance na zahiri domin mu fahimta da gaggawa; ya faɗa mana cewa, misalin halin da munafuƙai suka tsinci kansu a ciki kamar misalin wani mutum ne da yake tafiya ya samu kansa cikin matsanancin duhu, ga tsoro da ya mamaye shi ta ko’ina, sai ya yi ta fafutukar neman haske, ya wahala sosai har ya samo wuta wadda ta haskaka masa kewayansa, ya zamanto yana ganin komai da ke gabansa da bayansa, ya daina jin tsoron da yake ciki a farko, ya fara farin ciki, sai kwatsam hasken ya ɗauke, ga wuta na ci gabansa balbal, ga zafinta yana bugo shi, amma kuma babu haske sai dai duhu yana dukan duhu; ga duhun dare, ga duhun hadari, ga na ruwan sama, ga duhun rashin haske, ya samu kansa cikin duffai daban-daban ba ya ganin ko da tafin hannunsa. To haka sha’anin munafuƙai yake. Da farko suna rayuwa cikin duhun kafirci, sai Musulunci ya bayyana, sai suka ɗosani haskensa, suka sami kariya ta rayukansu da dukiyoyinsu. To amma da yake ba a kan gaskiya suka yi imani ba, sai hasken Musuluncin ya ɓace musu, yayin da suka mutu aka kai su ƙaburburansu, sai suka tsinci kansu cikin duhu na dukan duhu, ga duhun ƙabari, ga na kafirci, ga na munafunci, ga na saɓon Allah iri-iri, ga uwa-uba duhun wutar Jahannama. Tir da wannan makoma. Dalilin haka ya sa Allah ya ce da su, su kurame ne ba sa jin duk wata gaskiya ji na fahimta; bebaye ne ba sa iya faɗin gaskiya, sannan makafi ne ba sa ganin gaskiya su bi ta. Don haka ne ma babu yadda za a yi su dawo kan hanya.
أَوۡ كَصَيِّبٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فِيهِ ظُلُمَٰتٞ وَرَعۡدٞ وَبَرۡقٞ يَجۡعَلُونَ أَصَٰبِعَهُمۡ فِيٓ ءَاذَانِهِم مِّنَ ٱلصَّوَٰعِقِ حَذَرَ ٱلۡمَوۡتِۚ وَٱللَّهُ مُحِيطُۢ بِٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:19Ko kuma (misalinsu) kamar wani mamakon ruwan sama ne, wanda yake ɗauke da duffai da tsawa da walƙiya, har ta kai suna sanya \'yan yatsunsu cikin kunnuwansu don tsananin tsawarwaki saboda tsoron mutuwa. Allah Kuma Yana kewaye da kafirai (da iliminsa).
يَكَادُ ٱلۡبَرۡقُ يَخۡطَفُ أَبۡصَٰرَهُمۡۖ كُلَّمَآ أَضَآءَ لَهُم مَّشَوۡاْ فِيهِ وَإِذَآ أَظۡلَمَ عَلَيۡهِمۡ قَامُواْۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَذَهَبَ بِسَمۡعِهِمۡ وَأَبۡصَٰرِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 2:20Walƙiyar ta kusa ta fauce idanuwansu. Duk sa\'adda ta haska musu sai su ci gaba da tafiya cikin (haskenta); idan kuma ta rufe su da duhu sai su tsaya cak. Da kuwa Allah Ya ga dama da sai Ya tafiyar da jinsu da ganinsu. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai. </b>A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayar da misali na biyu game da munafuƙai. Ya misalta su da mutanen da suke tafiya cikin dare sai ruwan sama ya goce kamar da bakin ƙwarya, sannan ga duhu ya baibaye su ta ko’ina; duhun dare da na hadari da na ruwan sama, baya ga haka ga tsawarwaki da walƙiya. Duk sa’adda walƙiya ta haska sai su ɗan motsa gaba ɗaya daga inda suke. Idan kuma duhu ya rufe su sai su tsaya cak a inda suke. Sannan idan rugugin tsawa ya dame su sai su sanya yatsunsu cikin kunnuwansu saboda tsoron halaka. Sun manta cewa ilimin Allah da Ƙudurarsa suna zagaye da kafirai. To kamar haka su ma munafuƙai suke, suna rayuwa cikin duhu iri-iri, suna cikin damuwa, duk sa’adda Musulmai suka samu wata ɗaukaka da rinjaye sai su kawo kai don su sami ganima, amma duk lokacin da wasu ayoyi na Alƙur’ani suka sauka suna maganar azabar Allah (Mai tsarki da daukaka) da narkonsa ga munafuƙai sai su ji kamar asirinsu ne zai tonu. Ba su son sauraron ayoyin da suke bayanin wani umurnin Allah ko haninsa, don haka sai su riƙa toshe kunnuwansu da ‘yan yatsunsu. To sai Allah ya razanar da su da cewa, da ya ga dama da ya gusar musu da jinsu da ganinsu, su wayi gari dunɗum ba sa ganin komai ba sa jin komai sakamakon biris da gaskiya da suka yi. Domin kuwa Allah mai iko ne a kan komai.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Open ayah 2:21Ya ku mutane, ku bauta wa Ubangijinku Wanda Ya halicce ku, da waɗanda suka gabace ku, ko kwa yi taƙawa.
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فِرَٰشٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ فَلَا تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:22Shi ne Wanda Ya sanya muku ƙasa ta zama shimfiɗa kuma Ya sanya muku sama ta zama gini kuma Ya saukar da ruwa daga sama Ya fitar muku da arziƙi na \'ya\'yan itatuwa, don haka kada ku sanya wa Allah kishiyoyi alhalin kuna sane. Bayan da Allah ya gama maganar kashe-kashen mutane, wato muminai masu taƙawa da siffofinsu da kafirai da siffofinsu da munafuƙai da nasu siffofin, sai kuma ya dunƙule su gaba ɗaya ya kirawo su zuwa ga bauta masa shi kaɗai. Da ma bautar ita ce manufar halittarsu, kamar yadda ya faɗa a cikin Surat Az-Zariyati aya ta 56. Sannan ya kafa musu manya-manyan hujjoji guda huɗu: <b>Hujja ta farko </b> ita ce, shi ne wanda ya halicce su har da waɗanda suka gabace su, ya ba su ci da sha da buƙatunsu, don haka wanda ya yi halitta ai shi ne ya cancanci a bauta masa ba wani can daban ba. <b>Hujja ta biyu </b> ita ce, shi ne wanda ya shimfiɗa musu ƙasa wadda suke yawo a kanta, su yi gine-ginensu duk a kanta. Lalle wanda ya yi wannan ai shi kaɗai ya cancanta a bautawa ba wani ba can daban ba. <b>Hujja ta uku </b> ita ce, shi ne wanda ya ɗaukaka musu rufin samaniya, ya ƙawata shi da rana da wata da taurari, waɗanda suke amfanar su a rayuwarsu a bayan ƙasa. Wanda ya yi wannan aiki lalle shi ne ya cancanci bauta ba wani abu can daban ba. <b>Hujja ta huɗu </b> ita ce, shi ne ya sauko musu da ruwan sama daga girgije, wanda suke sha su da dabbobinsu, kuma ya shayar musu da gonakinsu suka sami amfanin gona da kayan marmari iri-iri da ganyayyaki daban-daban. Lalle mai wannan aiki shi ne wanda ya cancanci bauta ba wani can daban ba. Waɗannan ayoyi suna nuni ne ga Tauhidin Rububiyya wanda yake jagoranci zuwa ga fahimtar Tauhidin Uluhiyya, wato bautar Allah shi kaɗai ba tare da yi masa kishiya ba.
وَإِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّمَّا نَزَّلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا فَأۡتُواْ بِسُورَةٖ مِّن مِّثۡلِهِۦ وَٱدۡعُواْ شُهَدَآءَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 2:23Kuma idan kun kasance cikin kokwanto game da abin da Muka saukar wa bawanmu, to ku zo da kwatankwacin sura ɗaya kamarsa, kuma ku kirawo masu taimakonku ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya.
فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُواْ وَلَن تَفۡعَلُواْ فَٱتَّقُواْ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُۖ أُعِدَّتۡ لِلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:24To idan har ba ku aikata hakan ba, kuma ba za ku taɓa iyawa ba, to ku kiyayi wata wuta wadda mutane ne da duwatsu makamashinta; an kuwa tanade ta domin kafirai. </b>A waɗannan ayoyi Allah yana magana ne a kan gaskiyar annabcin Annabi (ﷺ) da gaskiyar Alƙur’anin da ya zo da shi. Allah ya kawo wata hujja ce mai ƙarfi wadda za ta kawo ƙarshen duk wani shaci-faɗin da kafirai suke yi game da Alƙur’ani. Allah ya bayyana cewa, shi fa Annabi (ﷺ), mutum ne kamarsu, yana magana da irin harshensu, kuma bai koyi wani ilimi na rubutu da karatu ba. To idan har shi ne ya ƙiriƙiri Alƙur’ani da kansa ba wahayi Allah ya yi masa ba kamar yadda suke da’awa, to su ma ai Larabawa ne irinsa, sai su kawo ko da sura ɗaya kamar ta Alƙur’ani wajen hikima da fasaha. Kuma suna iya gayyato duk wani wanda suke ganin zai taimaka musu don cim ma wannan buƙatar tasu. Idan kuwa har suka kasa yin hakan, kuma ba za su iya ɗin ba, to su yi maza su karɓi gaskiya don kare kansu daga azabar Allah wadda wuta ce ba irin wadda suka sani ba a nan duniya, domin ita wannan makamashin hura ta mutane ne masu laifuka da duwarwatsu, kuma an riga an yi tanadin ta musamman domin kafirai.
وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ كُلَّمَا رُزِقُواْ مِنۡهَا مِن ثَمَرَةٖ رِّزۡقٗا قَالُواْ هَٰذَا ٱلَّذِي رُزِقۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَأُتُواْ بِهِۦ مُتَشَٰبِهٗاۖ وَلَهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَهُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 2:25Kuma ka yi albishir ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai cewa suna da wasu gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Duk sa\'adda aka arzuta su da ’ya’yan itatuwa daga gare su sai su ce: “Wannan shi ne irin abin da aka arzuta mu da shi ɗazu.” An kawo musu shi yana mai kama da juna, kuma suna da wasu mata tsarkaka a cikinsu, kuma su masu zama ne a cikinsu dindindin. Bayan Allah ya ambaci sakamakon kafirci a ayar da ta gabata, sai kuma a nan ya ambaci sakamakon waɗanda suka yi imani, domin wannan shi ne tsarin salon Alƙur’ani wajen haɗa tsoratarwa da kwaɗaitarwa. Allah ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, ya yi albishir ga waɗanda suka yi imani da shi da abin da ya zo da shi na gaskiya, kuma suka aikata kyawawan ayyuka waɗanda suka nuna gaskiyar imaninsu, ya yi musu albishir da cewa, a lahira suna da wani sakamako na gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashin bishiyoyinsu da shuke-shukensu da ɗakunansu. Duk sa’adda aka kawo musu kayan marmari sai su zaci irin wanda aka taɓa kawo musu ne ba da daɗewa ba a Aljanna, saboda kamanninsu iri ɗaya ne, amma ba su san akwai banbanci ba wajen ɗanɗano. Sannan baya ga kayan marmari na Aljanna, har ila yau, suna da wasu mata na aure waɗanda suke tsarkaka ne daga duk wani abin ƙyama, kamar yadda suke da kyawawan halaye da ɗabi’u. Sannan wani abin kwantar da hankali gare su shi ne, za su dawwama a cikin wannan jin daɗi ba zai yanke musu ba har abada.
۞إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَسۡتَحۡيِۦٓ أَن يَضۡرِبَ مَثَلٗا مَّا بَعُوضَةٗ فَمَا فَوۡقَهَاۚ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فَيَعۡلَمُونَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡۖ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَيَقُولُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلٗاۘ يُضِلُّ بِهِۦ كَثِيرٗا وَيَهۡدِي بِهِۦ كَثِيرٗاۚ وَمَا يُضِلُّ بِهِۦٓ إِلَّا ٱلۡفَٰسِقِينَ
Open ayah 2:26Lalle Allah ba Ya jin kunyar buga kowanne irin misali komai ƙanƙantarsa, sauro da abin ya fi shi. To amma waɗanda suka yi imani suna sanin cewa, lalle shi (wannan misali) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Amma waɗanda suka kafirta sai su riƙa cewa: “Me Allah Yake nufi da wannan misalin?” Yana kuwa ɓatar da mutane da yawa da shi, kuma Ya shiryar da mutane da yawa da shi, kuma ba kowa Yake ɓatarwa da shi ba sai fasiƙai.
ٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهۡدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مِيثَٰقِهِۦ وَيَقۡطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 2:27Waɗanda suke warware alkawarin Allah bayan ƙulla shi, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi, kuma suke ɓarna a bayan ƙasa. Waɗannan su ne cikakkun hasararru. A waɗannan ayoyi kuma Allah yana sanar da cewa, ba ya jin kunyar bayar da wani misali da kowane abu na halittarsa komai ƙanƙantarsa kuwa, kamar sauro da abin da ya ɗara shi girma ko ƙanƙanta saboda hikimar da take cikin waɗannan misalan da fito da bayanai dalla-dalla don a gane. To yayin da Allah ya ba da irin waɗannan misalan masu sauraro sukan kasu gida biyu; kashi na farko su ne muminai masu yaƙinin cewa, wannan misali da Allah ya bayar gaskiya ne. Kashi na biyu kuma su ne kafirai, sai wannan misali ya ɗimautar da su har su nuna rashin yardarsu a kai, suna ganin don me Allah zai riƙa bayar da irin waɗannan misalan, sai su ƙara kafircewa a kan kafircinsu na farko. Sun kasa gane cewa, hikimar da ta sa Allah yake yin haka ita ce don ƙara bambancewa tsakanin mumini da kafiri. Don haka waɗannan misalan sukan zama sanadiyyar shiriyar muminai da dama, sannan kuma sukan zama sanadiyyar ɓacewar kafirai da dama. To amma fa ba wasu ne suke ɓacewa ta hanyar waɗannan misalan ba sai waɗanda suke kangare wa ɗa’ar Allah, waɗanda suke warware duk wani alƙawari da suka yi tsakaninsu da Allah, sannan suke yi wa shari’ar Allah karan-tsaye, kamar ƙin sadar da zumunci, sannan su yi ta yaɗa ɓarna ta kafirci da munafinci da zalunci a bayan ƙasa. To irin waɗannan halaye nasu su ne suka yi katutu a zukatansu har suka toshe musu zukata ya zamana ba su fahimtar duk wani misali da Allah zai bayar a Littafinsa.
كَيۡفَ تَكۡفُرُونَ بِٱللَّهِ وَكُنتُمۡ أَمۡوَٰتٗا فَأَحۡيَٰكُمۡۖ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 2:28Ta yaya kuke kafirce wa Allah alhalin a da kun kasance matattu, sannan Ya raya ku, sannan zai kuma mayar da ku matattu sannan Ya raya ku (a karo na biyu) sannan zuwa gare Shi ake mayar da ku?
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ لَكُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰٓ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَسَوَّىٰهُنَّ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖۚ وَهُوَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ
Open ayah 2:29Shi ne wanda Ya halitta muku abin da yake cikin ƙasa gaba ɗaya, sannan Ya nufi sama Ya daidaita su sammai bakwai, kuma Shi Masanin komai ne. A nan Allah yana nuna mamakin yadda waɗannan kafirai masu kafirce masa da kafirce wa shiriyar da ya aiko Manzonsa (ﷺ) da ita, tare da cewa, dalilai masu nuna girman Ƙudurarsa sun bayyana a sarari. Daga cikin irin waɗannan dalilai akwai cewa Allah ne ya kashe su sau biyu ya kuma raya su sau biyu. Kashewa ta farko, ita ce lokacin da babu su sannan ya samar da su; kashewa ta biyu, ita ce lokacin da yake karɓar rayukansu yayin mutuwarsu. Rayawa ta farko ita ce, halittarsu daga babu, sannan rayawa ta biyu ita ce, tayar da su daga ƙaburburansu bayan sun mutu. Su kansu kafirai za su tabbatar da hakan ranar gobe alƙiyama, kamar yadda ya zo a ‘Suratu Ghafir’ , aya ta 11. Sannan yana daga cikin manya-manyan dalilan cancantar a bauta wa Allah shi kaɗai, cewa ya halicci abin da yake cikin ƙasa gaba ɗaya domin amfanin ɗan’adam, sannan bayan ya gama halittar ƙasa ya nufi sama ya yi mata kyakkyawar halitta ya mayar da ita sammai bakwai. Kuma shi mai cikakken sani ne ga duk abin da ya halitta, kuma iliminsa ya game ko’ina.
وَإِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِنِّي جَاعِلٞ فِي ٱلۡأَرۡضِ خَلِيفَةٗۖ قَالُوٓاْ أَتَجۡعَلُ فِيهَا مَن يُفۡسِدُ فِيهَا وَيَسۡفِكُ ٱلدِّمَآءَ وَنَحۡنُ نُسَبِّحُ بِحَمۡدِكَ وَنُقَدِّسُ لَكَۖ قَالَ إِنِّيٓ أَعۡلَمُ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:30Kuma ka tuna sa\'adda Ubangijinka Ya ce da mala\'iku: “Lalle ni zan sanya wani halifa a bayan ƙasa.” Suka ce: “Yanzu za Ka sanya mata wanda zai yi ɓarna a cikinta kuma ya zubar da jini, alhali ga mu muna tasbihi tare da gode Maka, kuma muna tsarkake Ka?” (Allah) Ya ce: “Ni fa tabbas Na san abin da ku ba ku sani ba.”
وَعَلَّمَ ءَادَمَ ٱلۡأَسۡمَآءَ كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمۡ عَلَى ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ فَقَالَ أَنۢبِـُٔونِي بِأَسۡمَآءِ هَٰٓؤُلَآءِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 2:31Kuma sai (Allah) Ya koya wa Adamu dukkan sunaye (na abubuwa) sannan Ya kawo su gaban mala\'iku, sai Ya ce: “Ku faɗa min sunayen waɗannan abubuwan in kun zamanto masu gaskiya.”
قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ لَا عِلۡمَ لَنَآ إِلَّا مَا عَلَّمۡتَنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 2:32Sai suka ce: “Tsarki ya tabbata a gare Ka, ba mu da wani ilimi sai wanda Ka sanar da mu. Lalle Kai ne cikakken Masani, Mai hikima.”
قَالَ يَٰٓـَٔادَمُ أَنۢبِئۡهُم بِأَسۡمَآئِهِمۡۖ فَلَمَّآ أَنۢبَأَهُم بِأَسۡمَآئِهِمۡ قَالَ أَلَمۡ أَقُل لَّكُمۡ إِنِّيٓ أَعۡلَمُ غَيۡبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَأَعۡلَمُ مَا تُبۡدُونَ وَمَا كُنتُمۡ تَكۡتُمُونَ
Open ayah 2:33Ya ce: “Ya Adamu faɗa musu sunayensu.” Yayin da ya faɗa musu sunayensu, sai (Allah) Ya ce: “Ba Na faɗa muku cewa, lalle Ni ne Nake sane da gaibin sammai da ƙasa ba, kuma Nake sane da abin da kuke bayyanawa da kuma abin da kuke ɓoyewa ba?” Bayan da Allah ya gama maganar halittar ƙasa da abubuwan da ke cikinta, da halittar sammai da abubuwan da suka ƙunsa, sai ya shiga bayanin halittar ɗan’adam na farko, wato Annabi Adam (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Allah ya damƙa masa alhakin raya wannan ƙasar ta hanyar bin tsarin da ya haɗo shi da shi na shiriya, da kuma shimfiɗa adalci a bayan ƙasa da bauta masa shi kaɗai ba tare da haɗa shi da komai ba. Allah yana ba wa Annabinsa (ﷺ) labarin abin da ya faɗa wa mala’iku na cewa, zai halicci wata halitta da zai ajiye a bayan ƙasa, waɗanda wasunsu za su riƙa maye gurbin wasu, wato Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da zurriyarsa. Sai mala’ikun suka yi wa Allah tambayar neman sani, amma ba ta jayayya ba, suka ce: “Shin za ka ajiye waɗanda za su riƙa ɓarna a bayan ƙasa, suna kashe juna, alhali ga mu muna yi maka tasbihi da tsarkake ka a ko da yaushe? Me zai hana ka saka mu a madadinsu?” Sai Allah ya faɗa musu cewa, akwai abin da ba su sani ba na maslahar da ke tattare da sanya Adamu ya zama khalifa a bayan ƙasa. Daga nan sai Allah ya fara nuna wa mala’ikun wasu hikimomin da yake nufi game da halittar Annabi Adam (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai ya koyar da shi sunayen dukkanin abubuwa sannan ya nuna wa mala’iku su ya nemi su faɗa masa sunayensu idan har gaskiya suke a da’awar sun san abubuwa, kuma sun fi Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cancatar khalifanci a bayan ƙasa. To fa a nan take sai mala’iku suka tsarkake Ubangijinsu, kuma suka ƙara tabbatar da cewa, lalle su ba komai suka sani ba, Allah ne ya san komai kuma shi ne yake saka duk wani abu a mahallinsa da ya dace. To daga nan sai Allah ya umarci Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya faɗa musu sunayen waɗannen abubuwan. Yayin da ya faɗa musu sai suka fahimci fifikon da Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake da shi a kansu, kuma sai Allah ya ƙara tuna musu cewa, da man ai shi ne masanin gaibun da yake sama da wanda yake ƙasa, kuma ya san abin da suke bayyanawa da abin da suke ɓoyewa.
وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰ وَٱسۡتَكۡبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:34Kuma ka tuna lokacin da Muka ce wa mala\'iku: “Ku yi sujjada ga Adamu.” Sai duk suka yi sujjada, in ban da Iblis, sai shi ya ƙi, ya kuma yi girman kai, kuma ya tabbata cikin kafirai.
وَقُلۡنَا يَٰٓـَٔادَمُ ٱسۡكُنۡ أَنتَ وَزَوۡجُكَ ٱلۡجَنَّةَ وَكُلَا مِنۡهَا رَغَدًا حَيۡثُ شِئۡتُمَا وَلَا تَقۡرَبَا هَٰذِهِ ٱلشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 2:35Kuma Muka ce: “Ya kai Adamu, ka zauna gidan Aljanna kai da matarka, kuma ku ci (kayan marmarinta) cikin yalwa a duk inda kuka ga dama, kada kuma ku kuskura ku kusanci wannan bishiyar, sai ku kansance daga cikin azzalumai.”
فَأَزَلَّهُمَا ٱلشَّيۡطَٰنُ عَنۡهَا فَأَخۡرَجَهُمَا مِمَّا كَانَا فِيهِۖ وَقُلۡنَا ٱهۡبِطُواْ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ وَلَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُسۡتَقَرّٞ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ
Open ayah 2:36Sai Shaiɗan ya sa suka zame, sai ya fitar da su daga ni\'imar da suke ciki. Sai Muka ce: “Ku sauko ƙasa sashinku yana mai gaba da sashi; kuma kuna da mazauni a bayan ƙasa da wani jin daɗi zuwa wani ɗan lokaci.”
فَتَلَقَّىٰٓ ءَادَمُ مِن رَّبِّهِۦ كَلِمَٰتٖ فَتَابَ عَلَيۡهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 2:37Sai Adamu ya karɓi wasu kalmomi daga Ubangijinsa (na neman gafara), sai Ya yafe masa; lalle Shi ne Mai yawan karɓar tuba kuma Mai yawan jin ƙai.
قُلۡنَا ٱهۡبِطُواْ مِنۡهَا جَمِيعٗاۖ فَإِمَّا يَأۡتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدٗى فَمَن تَبِعَ هُدَايَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 2:38Muka ce: “Dukkanku ku sauko daga cikinta, sannan idan wata shiriyata ta zo muku, to waɗanda suka bi shiriyata, babu wani tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.
وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 2:39Kuma waɗanda suka kafirta suka kuma ƙaryata ayoyinmu, waɗannan su ne \'yan wuta, su masu dawwama ne a cikinta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da Manzonsa (ﷺ) cewa, ya umarci mala’iku da su faɗi su yi sujjada ga Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kuma nan take suka karɓa umarninsa suka faɗi suka yi masa sujjada, sai Iblis shi kaɗai ya nuna girman kai, ya bijire wa umarnin Allah ya ƙi yi wa Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sujjada. Sai Allah ya umarci Annabi Adamu da matarsa Hawwa’u da su shiga Aljanna su zauna a cikinta, ya yi musu izini da su ci komai na kayan marmari da ke cikinta a wadace, in ban da wata itaciya guda ɗaya wadda ya nuna musu ita ya ce, su nisance ta kada su ci ‘ya’yanta domin idan har suka ci to sun ƙetare iyakokin da ya gindaya musu. Sai Shaiɗan ya yaudare su ta hanyar yi musu waswasi ya sa suka ci ‘ya’yan wannan bishiyar, wanda a dalilin haka Allah ya fitar da su daga gidan Aljanna, ya umarce su da su dawo bayan ƙasa su zauna, wanda a nan ne ƙiyayya za ta bayyana a tsakaninsu, kuma nan ne wurin rayuwarsu, idan kuma sun mutu a cikinta ne za a binne su har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Bayan haka kuma sai Allah ya laƙanta wa Annabi Adamu wasu kalmomi da zai faɗa Allah ya yafe masa laifinsa, sai ya faɗa shi da matarsa, kuma Allah ya karɓi tubansu domin shi ne mai yafe wa muminai duk wani laifi da za su yi su nemi ya yafe musu. Daga nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Adamu da Hawwa’u da Iblis da su sauko daga gidan Aljanna gaba ɗaya, kuma ya faɗa musu cewa, idan wani abu na shiriya ya zo musu, littafi ne ko kuma wani manzo ne wanda zai nusar da su hanyar shiriya, idan har suka karɓe shi suka yi aiki da shi to za su samu cikakken zaman lafiya da farin ciki na har abada. Wanda kuwa ya bijire ya ƙi yarda da gaskiya ya ƙaryata ayoyin Allah, to wannan sakamakonsa gidan wuta ne, kuma zai zauna ciki har abada babu fita.
يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَوۡفُواْ بِعَهۡدِيٓ أُوفِ بِعَهۡدِكُمۡ وَإِيَّٰيَ فَٱرۡهَبُونِ
Open ayah 2:40Ya ku \'ya\'yan Isra\'ila, ku tuna ni\'imata da Na yi muku, kuma ku cika alƙawarina zan cika muku alkawarinku, kuma ku tsorace Ni Ni kaɗai.
وَءَامِنُواْ بِمَآ أَنزَلۡتُ مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُمۡ وَلَا تَكُونُوٓاْ أَوَّلَ كَافِرِۭ بِهِۦۖ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗا وَإِيَّٰيَ فَٱتَّقُونِ
Open ayah 2:41Kuma ku yi imani da abin da Na saukar yana mai gaskata abin da yake tare da ku (na wahayi), kada kuma ku zama farkon (jinsinku) da zai kafirce masa, kuma kada ku sayar da ayoyina da ɗan kuɗi kaɗan, kuma ku kiyaye dokokina.
وَلَا تَلۡبِسُواْ ٱلۡحَقَّ بِٱلۡبَٰطِلِ وَتَكۡتُمُواْ ٱلۡحَقَّ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:42Kada kuma ku gauraya gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓoye gaskiya, alhalin kuna sane.
وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱرۡكَعُواْ مَعَ ٱلرَّٰكِعِينَ
Open ayah 2:43Kuma ku tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku yi ruku\'i tare da masu ruku\'i.
۞أَتَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبِرِّ وَتَنسَوۡنَ أَنفُسَكُمۡ وَأَنتُمۡ تَتۡلُونَ ٱلۡكِتَٰبَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 2:44Shin yanzu kwa riƙa umartar mutane da ayyukan alheri ku kuma kuna mantawa da kawunanku, alhalin kuna karanta Littafi? Ashe ba za ku hankalta ba?
وَٱسۡتَعِينُواْ بِٱلصَّبۡرِ وَٱلصَّلَوٰةِۚ وَإِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلَّا عَلَى ٱلۡخَٰشِعِينَ
Open ayah 2:45Kuma ku nemi agaji ta hanyar haƙuri da kuma salla, kuma lalle ita (salla) babban abu ne sai dai ga masu ƙasƙantar da kai.
ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ رَبِّهِمۡ وَأَنَّهُمۡ إِلَيۡهِ رَٰجِعُونَ
Open ayah 2:46Waɗanda suka tabbatar da cewa, su masu haɗuwa ne da Ubangijinsu, kuma su zuwa gare Shi suke komawa. Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci asalin halittar ɗan’adam da kuma ƙiyayyar Shaiɗan a gare shi, ya kuma faɗa wa Annabi Adamu da zurriyarsa bayan ya saukar da su bayan ƙasa, ya ce kuma zai zo musu da shiriya wadda duk wanda ya bi ta to ya kuɓuta daga kowane irin tsoro da baƙin ciki. Sannan ya yi kashedi ga waɗanda za su saɓa wa wannan shiriyar da fuskantar wata azaba mai tsanani ta wutar Jahannama. To, a waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayani a kan Banu Isara’la ne waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen nuna wa annabawansu taurin kai da butulce wa ni’imar Allah mai yawa da ya yi musu. Banu Isra’ila su ne jikokin Annabi Yaƙuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). A nan Allah yana nuna musu ni’imar da ya yi musu, kuma yana umartar su da su zama masu cika alƙawari, idan sun yi hakan shi kuma zai ba su abin da ya alƙawarta musu na shiga Aljanna. Ya tunatar da su kan su ji tsoronsa shi kaɗai sannan ya umarce su da su gaskata Alƙur’ani ta hanyar imani da shi da aiki da abin da ya ƙunsa na shari’a, saboda yana ɗauke da irin abin da ya zo cikin littafin Attaura ta Annabi Musa wanda ya danganci Tauhidi, don haka ya gargaɗe su da kada su zama su ne na farko da za su kafirce wa wannan Alƙur’ani da wanda aka saukar wa Alƙur’anin shi ne Annabi Muhammadu (ﷺ). Har ila yau ya hana su musanya ayoyin Allah da wani abu na ƙyale-ƙyalen duniya wanda a wurin Allah ba a bakin komai yake ba, ta hanyar watsi da imani da Alƙur’ani da abin da Manzon Allah ya zo da shi da ɓoye gaskiya da take ta. Hakanan ya hana su cakuɗa ƙarya da gaskiya tare da ɓoye gaskiya, alhalin sun san irin illar da take cikin yin hakan. Kuma ya umarce su da tsayar da salla da rukunnanta da wajibanta, su bayar da zakkar dukiyarsu, sannan su tsayar da salla cikin jam’i tare da sauran muminai. Sannan Allah ya zarge su da abin da suke yi na umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, amma kuma su a karan kansu ba sa aiki da abin da suke yin umarni da shi, alhali ga shi suna karanta Attaura sun san abin da yake cikinta na hukunce-hukunce, wanda yin haka ya saɓa wa aikin mutane masu hankali. Daga bisani Allah ya umarce su da su nemi taimako ta hanyar tsayar da salla da haƙuri cikin duk al’amura, duk da cewa salla tana da nauyi ga wasu in ban da masu ƙasƙantar da kansu ga Allah waɗanda su ne suka tabbatar da cewa, akwai ranar gamuwarsu da Ubangijinsu wadda ita ce ranar alƙiyama.
يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَنِّي فَضَّلۡتُكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 2:47Ya ku \'ya\'yan Isra\'ila ku tuna ni\'imata da Na yi muku, kuma Ni Na fifita ku a kan sauran mutanen duniya.
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا يُؤۡخَذُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Open ayah 2:48Kuma ku kiyayi wata rana da babu wani (mai) rai da zai isar wa da wani (mai) rai komai a cikinta; kuma ba za a karɓi wani ceto daga gare shi ba, kuma ba za a karɓi wata fansa daga gare shi ba, kuma ba za a taimaka musu ba. </b>Daga nan har zuwa aya ta 61 Allah ya bayyana irin ni’imomi daban-daban da ya yi ta yi wa Banu Isra’ila, amma maimakon su yi masa godiya ta hanyar biyayya ga Manzonsa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai suka riƙa nuna butulci da kangare wa umarnin Allah da ƙin biyayya da girmamawa ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya kirawo su yana tuna musu irin ni’imominsa ga iyayensu wanda ko la’alla yin hakan zai sa musu godiyar Allah da shiga cikin addinin gaskiya na Musulunci. Ya kuma tuna musu yadda ya fifita su a kan sauran al’ummomi na zamaninsu ta hanyar aiko musu da manzanni daga cikinsu da saukar musu da littattafai, sannan ya tsoratar da su azabar lahira, ranar da kowa ta kansa yake, babu wani wanda zai iya magance wa ɗan’uwansa wata matsala a wannan rana, ko ya fanshi ɗan’uwansa kafiri ta hanyar ceto shi daga azabar Allah.
وَإِذۡ نَجَّيۡنَٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يُذَبِّحُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ
Open ayah 2:49Kuma ku tuna lokacin da Muka kuɓutar da ku daga jama\'ar Fir\'auna waɗanda suke ɗanɗana muku mummunar azaba, suna yanka \'ya\'yanku maza, kuma suna ƙyale \'ya\'yanku mata. A cikin wannan lamari akwai babbar jarraba daga Ubangijinku.
وَإِذۡ فَرَقۡنَا بِكُمُ ٱلۡبَحۡرَ فَأَنجَيۡنَٰكُمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ
Open ayah 2:50Kuma ku tuna lokacin da Muka raba muku kogi, sai Muka kuɓutar da ku, kuma Muka nutsar da jama\'ar Fir\'auna, alhalin kuna kallo. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tuna wa Banu Isra’ila irin yadda Fir’auna shi da magoya bayansa suka riƙa gana wa iyayensu azaba ta hanyar yanka ‘ya’yansu maza da ƙyale mata don su bautar da su a gidajensu, amma sai Allah ya kuɓutar da su daga wannan matsananciyar azaba. Wannan kuwa ba ƙaramar ni’ima ce gare su ba, don haka ya zama wajibi a kansu su yi wa Allah godiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambata musu wata ni’imar ta daban wadda ya yi musu lokacin da Fir’auna da rundunarsa suka biyo su don hallakar da su. Bayan sun iso gaɓar kogi sai Allah ya umarci Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya daki kogi da sandarsa, sai ko ya rabu gida biyu, suka ga hanya totar a gabansu suka bi suka ƙetare. Lokacin da Fir’auna ya iso shi da rundunarsa suka fara bi ta wannan hanyar sai Allah ya mayar da wannan kogi ya haɗe da su suka halaka gaba ɗaya, mutanen Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suna gani domin su huce haushin abin da ya faru gare su a baya.
وَإِذۡ وَٰعَدۡنَا مُوسَىٰٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗ ثُمَّ ٱتَّخَذۡتُمُ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَنتُمۡ ظَٰلِمُونَ
Open ayah 2:51Kuma ku tuna lokacin da Muka yi wa Musa wa\'adin (ganawa da shi) na kwana arba\'in, sannan ku kuma kuka kama bautar ɗan maraƙi a bayansa, alhalin kuna masu zaluntar kawunanku.
ثُمَّ عَفَوۡنَا عَنكُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 2:52Sannan sai Muka yi muku afuwa bayan haka, don ku yi godiya.
وَإِذۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡفُرۡقَانَ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Open ayah 2:53Kuma ku tuna lokacin da Muka ba wa Musa Littafin (Attaura) da abin da yake rarrabewa (tsakanin gaskiya da ƙarya) don ku shiriya.
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِنَّكُمۡ ظَلَمۡتُمۡ أَنفُسَكُم بِٱتِّخَاذِكُمُ ٱلۡعِجۡلَ فَتُوبُوٓاْ إِلَىٰ بَارِئِكُمۡ فَٱقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ عِندَ بَارِئِكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 2:54Kuma ku tuna lokacin da Musa ya cewa mutanensa: “Ya ku mutanena, lalle ku kun zalunci kawunanku ta hanyar mayar da ɗan maraƙi abin bauta, don haka ku tuba zuwa ga Mahaliccinku, kuma ku kashe kawunanku; wannan shi ne ya fi alheri a gare ku a wajen Mahaliccinku. Lalle shi Mai yawan karɓar tuba ne, Mai yawan jin ƙai.” Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tuna musu lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya je ganawa da shi ta tsawon kwana arba’in, su kuma Banu Isra’ila bayan tafiyarsa suka riƙa bauta wa ɗan maraƙi, suka zalunci kansu ta hanyar ɗaukar haƙƙin Allah na bauta su sanya wa ɗan maraƙi. Daga baya da suka tuba sai Allah ya yafe musu ko wataƙila sa yi godiya. Allah ya faɗi yadda tubar tasu za ta kasance yayin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kirawo su ya shaida musu cewa, sun fa zalunci kansu ta hanyar bautar ɗan maraƙi. Don haka dole ne su tuba; tubar kuwa ita ce, waɗanda ba su yi bautar ba daga cikinsu su kashe waɗanda suka yi, domin ta haka ne kaɗai Allah zai yafe musu laifinsu, don kasancewarsa mai karɓar tuba mai jin ƙai.
وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نُّؤۡمِنَ لَكَ حَتَّىٰ نَرَى ٱللَّهَ جَهۡرَةٗ فَأَخَذَتۡكُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ
Open ayah 2:55Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: “Ya Musa ba za mu yi imani da kai ba har sai mun ga Allah a sarari”, sai tsawa ta halaka ku, alhali kuma kuna kallo.
ثُمَّ بَعَثۡنَٰكُم مِّنۢ بَعۡدِ مَوۡتِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 2:56Sannan sai Muka tashe ku bayan mutuwarku, don ku yi godiya.
وَظَلَّلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡغَمَامَ وَأَنزَلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰۖ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 2:57Kuma Muka yi muku inuwa da girgije, kuma Muka saukar muku da mannu da (soyayyun) tsuntsayen salwa, ku ci daga daɗaɗan abin da Muka arzuta ku da shi; kuma ba su zalince Mu ba, sai dai kawunansu kaɗai suke zalunta. A nan har ila yau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tuna musu lokacin da suka faɗa wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, ba za su taɓa yarda da abin da ya zo musu da shi na gaskiya ba har sai ya nuna musu Allah a fili ɓaro-ɓaro sun gan shi. A dalilin haka Allah ya saukar musu da wata tsawa ta riƙa kashe su ɗaya bayan ɗaya suna kallo da idonsu. Sannan bayan duk sun mutu sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tayar da su don su gode masa a kan wannan ni’imar. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma har wa yau ya tuna musu ni’imar da ya yi musu lokacin da suke yawon ɗimuwa a cikin saharar Sina, ga tsananin zafin rana yana dukan su, sai Allah ya sauko musu da wani girgije ya riƙa yi musu inuwa, sannan ya saukar musu da Mannu da Salwa , watau darɓa da soyayyun tsuntsayen salwa, ya ce su riƙa cin wannan daddaɗan abinci. To amma duk da irin waɗannan ni’imomi bai sa sun natsu sun gode masa ba, sai ma ƙara butulce masa da suka riƙa yi. To amma wannan duk ba zai cutar da shi da komai ba; kawunansu kaɗai suke cutarwa.
وَإِذۡ قُلۡنَا ٱدۡخُلُواْ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةَ فَكُلُواْ مِنۡهَا حَيۡثُ شِئۡتُمۡ رَغَدٗا وَٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا وَقُولُواْ حِطَّةٞ نَّغۡفِرۡ لَكُمۡ خَطَٰيَٰكُمۡۚ وَسَنَزِيدُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 2:58Kuma ku tuna lokacin da Muka ce: “Ku shiga wannan alƙaryar ku ci daga (kayan marmarinta ta) inda kuka ga dama cikin yalwa, kuma ku shiga ƙofar garin a duƙe, kuma ku ce: “ (Allah Ka) kankare mana laifuffukanmu”, za Mu gafarta muku laifuffukanku. Kuma za Mu ƙara wa masu kyautatawa.
فَبَدَّلَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ قَوۡلًا غَيۡرَ ٱلَّذِي قِيلَ لَهُمۡ فَأَنزَلۡنَا عَلَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ رِجۡزٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ
Open ayah 2:59Sai waɗanda suka yi zalunci suka canza maganar da aka faɗa musu, sai Muka saukar da wata azaba daga sama a kan waɗanda suka yi zalunci saboda abin da suke aikatawa na fasiƙanci. A nan Allah yana ci gaba da tuna wa Banu Isra’ila lokacin da ya umarci kakanninsu da cewa, su shiga Baitul Maƙadisi, su ci irin arzikin da Allah ya aje a cikinta a wadace, kuma idan sun zo shiga ta ƙofar garin su sunkuyar da kansu su shiga a duƙe suna neman gafarar Allah. Ya yi musu alƙawarin cewa, idan har sun aikata hakan to zai gafarta musu zunubbansu sannan duk wani wanda ya kyautata aiki daga cikinsu zai ƙara masa falalarsa. To amma saboda kangarewarsu sai suka canza maganar da aka umarce su da ita, sai suka riƙa cewa: “Ƙwaya a cikin gashi.” Sannan kuma suka shiga garin suna jan gindi a ƙasa, a dalilin haka ne Allah ya saukar da azabarsa a kansu.
۞وَإِذِ ٱسۡتَسۡقَىٰ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ فَقُلۡنَا ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡحَجَرَۖ فَٱنفَجَرَتۡ مِنۡهُ ٱثۡنَتَا عَشۡرَةَ عَيۡنٗاۖ قَدۡ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٖ مَّشۡرَبَهُمۡۖ كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ مِن رِّزۡقِ ٱللَّهِ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ
Open ayah 2:60Kuma ka tuna lokacin da Musa ya roƙa wa mutanensa ruwan sha, sai Muka ce: “Ka bugi dutse da sandarka”, sai idanuwan marmaron ruwa goma sha biyu suka ɓuɓɓugo daga cikinsa. Haƙiƙa kowaɗanne mutane sun san mashayarsu. (Muka ce): “Ku ci kuma ku sha daga arzikin Allah, kuma kada ku yaɗa ɓarna a bayan ƙasa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tuna musu lokacin da suka nemi ruwan sha daga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yayin da suka tsinci kansu a saharar Sina, sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙi Allah ya shayar da su ruwa, sai Allah ya umarce shi da ya doki dutse da sandarsa, da ya aikata hakan, nan take kuwa Allah ya fitar musu da idanuwan marmaro na ruwa har guda sha biyu, wato adadin yawan ƙabilar Banu Isra’ila. Kowace ƙabila ta gane mashayarta. Sannan ya umarce su da su ci su sha daga abin da Allah ya arzuta su da shi, kuma kada su kuskura su yaɗa ɓarna a bayan ƙasa. Watau dai Allah ya hore musu ci da sha ba tare da wata wahala ba, kuma ya hore musu ruwan sha isasshe ba tare da wani tirmitsitsi ba.
وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نَّصۡبِرَ عَلَىٰ طَعَامٖ وَٰحِدٖ فَٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُخۡرِجۡ لَنَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۢ بَقۡلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَاۖ قَالَ أَتَسۡتَبۡدِلُونَ ٱلَّذِي هُوَ أَدۡنَىٰ بِٱلَّذِي هُوَ خَيۡرٌۚ ٱهۡبِطُواْ مِصۡرٗا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلۡتُمۡۗ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ وَٱلۡمَسۡكَنَةُ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ
Open ayah 2:61Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: “Ya Musa, ba za mu iya haƙuri a kan abinci iri ɗaya ba, don haka ka roƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana (wani abincin) daga abin da ƙasa take tsirarwa, daga mabunƙusanta da gurjinta da alkamarta da wakenta da albasarta.” Sai ya ce, “Yanzu kwa nemi musanya ƙasƙantaccen abu da wanda yake shi ne mafifici? To ku sauka kowane gari, domin za ku samu abin da kuka roƙa (a cikinsa).” Don haka sai aka sanya musu ƙasƙanci da talauci, kuma suka koma da fushin Allah. Hakan ya faru gare su ne saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haƙƙi ba. Hakan ya faru saboda saɓon da suka yi da kuma ta’addancin da suka riƙa yi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da tuna musu wata kangarar tasu da butulcewarsu ga ni’imar Allah yayin da suka nuna wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, su fa sun gaji da cin abinci iri ɗaya, (wato Mannu da Salwa ) wanda Allah yake ba su a kullum ba tare da sun sha wata wahala ba. Don haka suka nemi Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya roƙa musu Ubangijinsa don ya riƙa ba su irin abincin da ƙasa take fitarwa, irin su duma da alkama da albasa da wake da sauransu. A kan haka Annabi Musa ya zarge su da butulci da renuwa, yayin da suka fifita abinci mafi ƙasƙanci a kan mafificin abincin da ba inda za a same shi. Don haka ya ce musu, su je su shiga kowane gari za su sami duk abin da suke nema. To ganin yadda suka rena ni’imar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu, sai aka jarrabe su da ƙasƙanci da talauci wanda zai tilasa su su rusuna wa wasu suna neman taimako a wurinsu tun da sun rena ɗaukakar da Allah ya yi musu. Abu mafi muni ma da ya auka musu shi ne, fushin Allah da suka jawo wa kansu. Kuma Allah ya ce, ya yi musu haka ne saboda bijire wa ayoyinsa da suka yi ta yi, suna kashe annabawansa don sun faɗa musu gaskiya, kuma duk abin da ya kai su ga haka shi ne saɓon Allah da ƙetare iyakokin da suka riƙa yi.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلصَّٰبِـِٔينَ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 2:62Lalle waɗanda suka yi imani da Yahudawa da Nasara da Sabi\'awa, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira kuma ya yi aiki na ƙwarai, to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba. Hikimar kawo wannan ayar ana tsaka da bayanin laifuffukan Banu Isra’ila ita ce, don a nuna musu cewa, ƙofar tuba gare su a buɗe take matuƙar za su tuba su inganta imaninsu da ranar lahira su yi kyakkyawan aiki, to Allah zai ba su ladansu cikakke kuma babu wani tsoro a tare da su game da abin da za su je lahira su iske, kuma babu wani baƙin ciki da za su yi na abin da suka tafi suka bar shi a nan duniya. Waɗanda suka yi imani, a nan ana nufin al’ummar Annabi Muhammadu (ﷺ) wadda ta yi imani da shi, ta yi imani da dukkan littattafan Allah da manzanninsa. An ware su da wannan suna domin ƙarfin imaninsu da cikarsa. Yahudawa kuwa ana nufin mabiya Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka yi imani da shi, suka yi aiki da abin da aka saukar masa kafin a shafe aiki da addininsa, ko kuma kafin su gurɓata shi. Nasara kuma, ana nufin mabiya Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kafin a shafe addininsa ko kafin su jirkita shi. Sabi’awa kuwa wasu ƙungiyoyi ne, daga cikinsu akwai waɗanda suka kasance a kan aƙidar kaɗaita Allah da haramta duk wata alfasha da zalunci, duk da kasancewarsu ba bisa wani addini suke ba, to amma ba sa aikata kafirci. To duk wanda ya kyautata aiki daga cikin waɗannan al’ummomi da suka gabata, yana da kyakkyawan sakamako a wurin Allah, ba zai ɓata masa rayuwarsa ta lahira ba.
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ وَرَفَعۡنَا فَوۡقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱذۡكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Open ayah 2:63Kuma ku tuna lokacin da Muka ɗauki alƙawari mai ƙarfi daga gare ku, kuma Muka ɗaga dusten Ɗuri a kanku (Muka ce): “Ku karɓi abin da Muka ba ku da ƙarfi (Attaura), kuma ku tuna abin da yake cikinsa, don ku yi taƙawa.”
ثُمَّ تَوَلَّيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۖ فَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَكُنتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Open ayah 2:64Sannan bayan haka sai kuka juya da baya, to ba domin falalar Allah da rahamarsa a gare ku ba, lalle da kun kasance daga cikin asararru.
وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلَّذِينَ ٱعۡتَدَوۡاْ مِنكُمۡ فِي ٱلسَّبۡتِ فَقُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ
Open ayah 2:65Kuma haƙiƙa kun san waɗanda suka yi shisshigi daga cikinku game da ranar Assabar, sai Muka ce da su: “Ku zama birrai kuna ƙasƙantattu.”
فَجَعَلۡنَٰهَا نَكَٰلٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهَا وَمَا خَلۡفَهَا وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 2:66Sai Muka sanya ta (wannan uƙubar) ta zama izina ga al\'ummomin da suke zamanin faruwarta da kuma garuruwan da suke daura da su, kuma don ta zama wa\'azi ga masu taƙawa. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da tunatar da Banu Isra’ila alƙawarin da ya yi da su na cewa, za su yi imani da Manzansa (ﷺ); za su riƙe shari’arsa, kuma za su ƙanƙame Attaura da gaske, har ma sai da ya ɗaga dutsen Ɗuri a samansu don su karɓi wannan alƙawari da ya yi da su, su ci gaba da karanta Attaura suna aiki da abin da yake cikinta na ilmantarwa don su zama masu taƙawa. Amma kuma daga bisani sai suka warware wannan alƙawari, suka bijire masa. Ba don Allah ya nufe su da falalarsa, ya ba su damar tuba kuma ya karɓi tubarsu ba, to da sun wayi gari cikin halakakku a duniya da lahira. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da su labarin wasu kangararru daga cikinsu waɗanda suka kangare wa dokar Allah wadda ta hana su kamun kifi a duk ranar Assabar, ya neme su da su zauna gidajensu, amma sai suka bijire ma wannan dokar, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da su birai, ya ƙasƙanta su. Kuma Allah ya sanya wannan uƙuba da ya yi musu ta zama abin tsoratarwa kuma wa’azi da izina ga masu laifuka irin nasu, har ma da garuruwan da suke maƙotaka da su, hakanan kuma ta zama tunatarwa ga masu taƙawa.
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تَذۡبَحُواْ بَقَرَةٗۖ قَالُوٓاْ أَتَتَّخِذُنَا هُزُوٗاۖ قَالَ أَعُوذُ بِٱللَّهِ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ
Open ayah 2:67Kuma ku tuna lokacin da Musa ya ce wa mutanensa: “Allah Yana umartar ku da ku yanka saniya”, sai suka ce: “Yanzu ka riƙa yi mana izgili?” Sai ya ce: “Ina neman Allah Ya kiyaye ni da in zama cikin jahilai!”
قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ لَّا فَارِضٞ وَلَا بِكۡرٌ عَوَانُۢ بَيۡنَ ذَٰلِكَۖ فَٱفۡعَلُواْ مَا تُؤۡمَرُونَ
Open ayah 2:68Sai suka ce: “Ka roƙa mana Ubangijinka Ya yi mana bayanin yaya take?” Sai ya ce: “Lalle Shi yana cewa, lalle ita saniya ce, ba tsohuwa ba kuma ba budurwa ba, tana tsakatsakin haka.” Don haka ku aikata abin da ake umartar ku.
قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا لَوۡنُهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ صَفۡرَآءُ فَاقِعٞ لَّوۡنُهَا تَسُرُّ ٱلنَّٰظِرِينَ
Open ayah 2:69Sai suka ce: “Ka roƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana mene ne launinta?” Sai ya ce, “Lalle Shi yana cewa, lalle ita saniya ce mai launin fatsi-fatsi mai tsananin cizawa, tana faranta wa masu kallon ta rai.”
قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَ إِنَّ ٱلۡبَقَرَ تَشَٰبَهَ عَلَيۡنَا وَإِنَّآ إِن شَآءَ ٱللَّهُ لَمُهۡتَدُونَ
Open ayah 2:70Sai suka ce: “Ka roƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana yaya take, lalle shanu sun rikitar da mu, kuma lalle mu in Allah Ya so masu shiryuwa ne.”
قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ لَّا ذَلُولٞ تُثِيرُ ٱلۡأَرۡضَ وَلَا تَسۡقِي ٱلۡحَرۡثَ مُسَلَّمَةٞ لَّا شِيَةَ فِيهَاۚ قَالُواْ ٱلۡـَٰٔنَ جِئۡتَ بِٱلۡحَقِّۚ فَذَبَحُوهَا وَمَا كَادُواْ يَفۡعَلُونَ
Open ayah 2:71Ya ce: “Lalle Shi Yana cewa, ita saniya ce wadda ba horarriya ba ce da take noma kasa, kuma ba ta shayar da shuka; lafiyayya ce, babu dabbare-dabbare a jikinta”. Sai suka ce: “Yanzu ne ka zo da gaskiya”. Sai suka yanka ta, kamar dai ba za su aikata ba.
وَإِذۡ قَتَلۡتُمۡ نَفۡسٗا فَٱدَّٰرَٰءۡتُمۡ فِيهَاۖ وَٱللَّهُ مُخۡرِجٞ مَّا كُنتُمۡ تَكۡتُمُونَ
Open ayah 2:72Kuma ku tuna lokacin da kuka kashe wani mutum, kuma kuka riƙa tura wa juna (laifin kisan), Allah kuma Mai bayyanar da abin da kuka kasance kuna ɓoyewa ne.
فَقُلۡنَا ٱضۡرِبُوهُ بِبَعۡضِهَاۚ كَذَٰلِكَ يُحۡيِ ٱللَّهُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 2:73Sai Muka ce: “Ku doke shi (mataccen) da wani sashinta (saniyar).” Kamar haka ne Allah Yake raya matattu, Yake kuma nuna muku ayoyinsa don ku hankalta.
ثُمَّ قَسَتۡ قُلُوبُكُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ فَهِيَ كَٱلۡحِجَارَةِ أَوۡ أَشَدُّ قَسۡوَةٗۚ وَإِنَّ مِنَ ٱلۡحِجَارَةِ لَمَا يَتَفَجَّرُ مِنۡهُ ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ وَإِنَّ مِنۡهَا لَمَا يَشَّقَّقُ فَيَخۡرُجُ مِنۡهُ ٱلۡمَآءُۚ وَإِنَّ مِنۡهَا لَمَا يَهۡبِطُ مِنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:74Sannan sai zukatanku suka ƙeƙashe bayan haka, suka zama kamar dutse ko ma fiye da dutse ƙeƙashewa. Kuma lalle daga cikin duwatsu akwai waɗanda ƙoramu suke ɓuɓɓugowa daga cikinsu; akwai kuma waɗanda suke tsatssagewa ruwa ya fito daga cikinsu; akwai kuma waɗanda suke faɗowa saboda tsoron Allah. Allah ba marafkani ne ba game da abin da kuke aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Banu Isra’ila labarin iyayensu da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da suka neme shi da ya taimaka musu da binciken gano wani daga cikinsu da ya yi kisan kai, kuma ba su gane kowane ne shi ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa wahayi da ya umarce su da su yanka saniya, domin su doki wannan mamaci da wani ɓangare daga jikinta, sai ya dawo da ransa ya faɗa musu wanda ya kashe shi. To amma Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai bayyana musu wasu siffofi takamaimai na saniyar ba, domin yana nufin kowace iri suka yanka ta gamsar. To amma saboda tsaurin kansu da ta’annutinsu, sai suka ɗauki maganar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a matsayin izgili yake yi musu. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nemi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsare shi daga kasancewa cikin wawayen mutane masu yi wa mutane izgili. Duk da haka wannan bai sa Banu Isra’ila sun yanka saniyar ba, sai suka ci gaba da yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) tambayar ƙwaƙwa, suka ce ya roƙi Ubangijinsa ya faɗa musu wace irin saniya za su yanka? Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya faɗa musu cewa, Allah ya ce saniyar da za su yanka ba tsohuwa ba ce, kuma ba yarinya ba ce; saniya ce wadda take tsakatsaki, ba babba ba sosai, ba kuma ƙarama sosai ba. To duk da haka ba su wadatu sun tsaya iya nan ba, sai suka ƙara zaƙulo wata tambayar suka ce, Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tambayo musu Ubangijinsa launin saniyar da za su yanka. Annabi Musa ya ce, Allah ya faɗa masa cewa saniya ce mai rawayar launi tsantsa, kuma kyakkyawa wadda kyanta yake faranta wa duk wanda ya kalle ta rai. To maimakon Banu Isra’il su tsaya iya nan da tambayoyinsu na ƙwaƙwa, sai suka ci gaba da ce wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), su fa shanu sun rikita su, har sun kasa gano wacce ake so su yanka, don haka Annabi Musa ya sake neman Ubangijinsa da ya ƙara fayyace masa irin saniyar da yake nufi. To amma a wannan karo, sai suka ce insha Allahu za su gano saniyar da ake musu bayani. Daga nan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sake faɗa musu cewa, Allah ya faɗa masa cewa saniyar da ba a taɓa sa ta wani aiki ba na noma ko na ban ruwa ba, sannan kuma ba ta da wata naƙasa a tare da ita, kamar yadda kuma launin nata na rawaya ne tsantsa, ba tare da ya gauraya da wani launi ba. To fa sai a nan ne suka ce wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), yanzu suka ji ya zo da batu na gaskiya wajen tantance musu siffofin saniyar. Sai suka tafi neman ta, har suka samo ta suka yanka ta, abin da kamar ma ba za su iya yi ba. Wato sun yanka ta ba da son ransu ba. Ko kuma saboda irin yadda suka riƙa tambayar ƙwaƙwa, har sun kusa su ce ma sun fasa yanka saniyar. Domin da suna da sha’awar zartar da umarnin da Allah ya yi musu, da a karon farko sun zartar, to amma sai suka tsaya tambayoyi na rashin yarda, suka tsananta, sai su ma Allah ya tsananta musu. Daga nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su doki wannan mamaci da wani ɓangare na saniyar, sai suka yi hakan, Allah kuma ya sake raya shi, ya tashi ya faɗa musu sunan wanda ya kashe shi. Wannan abu da ya faru yana cikin dalilai da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Banu Isra’ila da sauran ‘yan’adam cewa, Allah zai iya sake tayar da matattu don yi musu hisabi a ranar gobe ƙiyama. Allah ya ce ya yi musu haka ne don su yi hankali, su bar aikata duk wani abu wanda zai cutar da su a wurin Allah. To amma maimakon su yi hankali su ƙara nutsuwa, sai zukatansu suka bushe, suka ƙeƙashe, suka zama masu tauri kamar dutse, ko ma fiye da dutse, domin dutse duk da taurinsa, ya fi zukatan Yahudawa laushi, domin a cikin duwatsu akwai waɗanda ruwa yake kwarara daga cikinsu, akwai kuma wanda yake tsagewa yana fitar da ruwa, akwai kuma wanda yake faɗowa ƙasa saboda tsoron Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙara tsoratar da su ta hanyar faɗa musu cewa yana sane da duk abin da suke kitsawa na saɓon Allah, kuma sai ya yi musu cikakkiyar sakayya a kan aikinsu.
۞أَفَتَطۡمَعُونَ أَن يُؤۡمِنُواْ لَكُمۡ وَقَدۡ كَانَ فَرِيقٞ مِّنۡهُمۡ يَسۡمَعُونَ كَلَٰمَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُحَرِّفُونَهُۥ مِنۢ بَعۡدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:75Yanzu (ku muminai) kwa sa ran su yi imani saboda ku, alhalin wata ƙungiya daga cikinsu suna sauraron maganar Allah sannan su jirkita ta bayan sun fahimce ta alhalin kuwa suna sane?
وَإِذَا لَقُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَا بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ قَالُوٓاْ أَتُحَدِّثُونَهُم بِمَا فَتَحَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ لِيُحَآجُّوكُم بِهِۦ عِندَ رَبِّكُمۡۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 2:76Kuma idan suka haɗu da waɗanda suka yi imani sai su ce: “Mun yi imani”, amma kuma idan sashinsu ya keɓance da sashi sai su ce: “Yanzu kwa riƙa faɗa musu abin da Allah Ya yi muku buɗi da shi don su kafa muku hujja da shi a wurin Ubangijinku? Shin ba za ku hankalta ba?”
أَوَلَا يَعۡلَمُونَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَ
Open ayah 2:77Shin ko ba su san Allah Yana sane da abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanawa ba?
وَمِنۡهُمۡ أُمِّيُّونَ لَا يَعۡلَمُونَ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّآ أَمَانِيَّ وَإِنۡ هُمۡ إِلَّا يَظُنُّونَ
Open ayah 2:78Kuma daga cikinsu akwai jahilai waɗanda ba su san Littafi ba sai burace-burace, kuma zato kawai suke yi.
فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ يَكۡتُبُونَ ٱلۡكِتَٰبَ بِأَيۡدِيهِمۡ ثُمَّ يَقُولُونَ هَٰذَا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ لِيَشۡتَرُواْ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلٗاۖ فَوَيۡلٞ لَّهُم مِّمَّا كَتَبَتۡ أَيۡدِيهِمۡ وَوَيۡلٞ لَّهُم مِّمَّا يَكۡسِبُونَ
Open ayah 2:79To tsananin azaba ya tabbata ga waɗanda suke rubuta littafi da hannayensu sannan su ce: “Wannan daga Allah yake”, don su musanya shi da wani ɗan kuɗi kaɗan. To tsananin azaba ya tabbata a gare su saboda abin da hannayensu suka rubuta, kuma tsananin azaba ya tabbata a gare su saboda abin da suka kasance suna tsuwurwuta.
وَقَالُواْ لَن تَمَسَّنَا ٱلنَّارُ إِلَّآ أَيَّامٗا مَّعۡدُودَةٗۚ قُلۡ أَتَّخَذۡتُمۡ عِندَ ٱللَّهِ عَهۡدٗا فَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ عَهۡدَهُۥٓۖ أَمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:80Kuma suka ce: “Wuta ba za ta shafe mu ba sai cikin wasu \'yan kwanaki ƙididdigaggu.” Ka ce: “Shin kun yi wani alƙawari ne da Allah, don haka Allah ba zai saɓa alƙawarinsa ba? Ko kuma kuna faɗar abin da ba ku da ilimi ne kuna jingina wa Allah?”
بَلَىٰۚ مَن كَسَبَ سَيِّئَةٗ وَأَحَٰطَتۡ بِهِۦ خَطِيٓـَٔتُهُۥ فَأُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 2:81E! Wanda duk ya aikata mummunan aiki kuma laifuffukansa suka kewaye shi, to waɗannan su ne ‘yan wuta, su masu dawwama ne a cikinta.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 2:82Waɗanda kuma suka yi imani kuma suka yi ayyuka na ƙwarai, to waɗannan \'yan Aljanna ne, kuma su masu dawwama ne a cikinta. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin yanayin da zukatan Banu Isra’ila suka zama, yadda suka taurare kamar duwatsu ko ma fiye da duwatsu, sai ya dawo kan muminai a waɗannan ayoyi yana faɗa musu cewa, su fitar da rai game da imanin waɗannan mutane, domin babu wata alama da ta nuna suna shirye da karɓar shiriya. Hasali ma malamansu ma waɗanda suke karanta musu Attaura da abin da yake cikinta na maganar Allah, suna canja ta, suna gurɓata ta, bayan kuwa sun fahimce ta, sai suka canza ma’anoninta zuwa wata ma’ana daban da za ta yi daidai da son ransu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗi mummunan hali na wasu Yahudawa, waɗanda suka yafa rigar munafinci a jikinsu. Wato duk lokacin da suka haɗu da Annabi (ﷺ) da sahabbansa, sai su ce: “Ai mu muminai ne”, amma idan sun koma cikin ‘yan uwansu Yahudu, sai sauran Yahudawan da ba su yafa rigar munafinci ba, su riƙa zargin waɗancan munafuƙan Yahudawan, suna ce musu: “Me ya sa za ku riƙa faɗa wa Musulmi abin da Allah ya sanar da mu a Attaura na siffofin Annabi ko labarin irin azabar da Allah ya saukar wa kakanninmu saboda kangararsu ko kuma abin da ya sanar da mu na cewa, akwai Annabin da zai bayyana mai siffofi iri kaza da kaza? Domin fa yin haka ai wata hujja ce kuke ba su da za su kafa mana ita gobe ƙiyama a gaban Allah cewa mun san gaskiya, kawai mun ƙi yin imani ne da gangan. Wannan abu da kuke yi rashin hankali ne.” Sai Allah ya ce, Yahudawa suna irin waɗannan maganganu da ‘yan uwansu a ɓoye, kamar ba su san Allah ya san duk abin da suke bayyanawa da abin da suke ɓoyewa ba, shi a wurinsa babu wani bambanci tsakanin abin da suke bayyanawa, da abin da suke ɓoyewa a zukatansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Yahudawa ba dukansu ne suke da ilimi ba; a cikinsu akwai ma waɗanda ba su iya ko rubutu da karatu ba, don haka ba ma sa iya karanta littafin Attaura; abin da kawai suka sani shi ne tatsuniyoyi da shaci-faɗi, kamar ganin da suke yi cewa babu wanda zai shiga Aljanna sai su, ko su ba za a sa su a wuta ba sai na ‘yan kwanaki kaɗan, da ire-iren waɗannan tatsuniyoyi marasa kan-gado. Allah ya ce babu komai na ilimi a tare da irin waɗannan Yahudawa in ban da zato da kame-kame. Kamar yadda ya faɗa a Suratun Nisa’i, aya ta 157. Sannan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani kason na Yahudawa, waɗanda su ne miyagun malamansu, waɗanda babu Allah a zukatansu sai neman abin duniya kawai, don haka sai su riƙa canza littafin Attaura, suna kuma rubuta wasu ƙarairayi da hannuwansu, amma sai su ce maganar Allah ce. To waɗannan miyagun malaman za su gamu da azaba mai tsanani saboda ƙaryar da suka riƙa yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka) domin su ci haram da ita, don haka sakamakonsu mai muni ne ƙwarai da gaske a lahira. Daga nan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci aƙidar da ta ja waɗannan miyagun malaman suka riƙa yi wa Allah ƙarya don su ci dukiyar mabiyansu, ta cewa, wai wuta a lahira ba za ta ci su ba sai cikin wasu ‘yan kwanaki kaɗan, daga nan sai a fitar da su, don haka ba su da wata babbar matsala a lahira komai suka aikata a nan duniya. Sai Allah ya umarci Annabi (ﷺ) da ya mayar musu da martani, ya tambaye su, ko suna da wata yarjejeniya da suka yi tsakaninsu da Allah (Mai tsarki da daukaka) a kan hakan, wadda za ta tabbatar da abin da suke da’awa? Idan suna da ita, to shi ke nan suna da hujja a hannunsu, domin Allah ba ya karya alƙawari. Idan kuwa babu wannan yarjejeniyar, to saboda me za su riƙa faɗar ƙarya suna jingina wa Allah? Sannan sai Allah ya ƙaryata waccan magana tasu ta cewa, su ba za a sanya su a wuta ba, sai na wanin ɗan taƙaitaccen lokaci, ya ce, ba haka ne ba, hukuncin Allah shi ne, duk wanda ya aikata laifi, kamar irin haɗa Allah da wani ko yi masa ƙarya, har zunubansa suka dabaibaye shi ta ko’ina, ya kuma mutu a kai bai tuba ba, to zai shiga wuta ne ya kuma zauna cikinta har abada babu fita. Su kuma waɗanda suka ba da gaskiya da Allah, suka yi kyawawan ayyuka, to waɗannan ‘yan Aljanna ne masu zama a cikinta har abada babu fita.
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ لَا تَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَانٗا وَذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَقُولُواْ لِلنَّاسِ حُسۡنٗا وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ ثُمَّ تَوَلَّيۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنكُمۡ وَأَنتُم مُّعۡرِضُونَ
Open ayah 2:83Kuma ka tuna lokacin da Muka ɗauki alƙwari daga Banu Isra\'ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riƙa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai \'yan kaɗan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa.
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ لَا تَسۡفِكُونَ دِمَآءَكُمۡ وَلَا تُخۡرِجُونَ أَنفُسَكُم مِّن دِيَٰرِكُمۡ ثُمَّ أَقۡرَرۡتُمۡ وَأَنتُمۡ تَشۡهَدُونَ
Open ayah 2:84Kuma ku tuna lokacin da muka ɗauki alƙawari da ku cewa, ba za ku zubar da jinanenku ba, kuma ba za ku fitar da junanku daga gidajenku ba, sannan kuka tabbatar da hakan, alhalin kuna masu shaida.
ثُمَّ أَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ تَقۡتُلُونَ أَنفُسَكُمۡ وَتُخۡرِجُونَ فَرِيقٗا مِّنكُم مِّن دِيَٰرِهِمۡ تَظَٰهَرُونَ عَلَيۡهِم بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَإِن يَأۡتُوكُمۡ أُسَٰرَىٰ تُفَٰدُوهُمۡ وَهُوَ مُحَرَّمٌ عَلَيۡكُمۡ إِخۡرَاجُهُمۡۚ أَفَتُؤۡمِنُونَ بِبَعۡضِ ٱلۡكِتَٰبِ وَتَكۡفُرُونَ بِبَعۡضٖۚ فَمَا جَزَآءُ مَن يَفۡعَلُ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ إِلَّا خِزۡيٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يُرَدُّونَ إِلَىٰٓ أَشَدِّ ٱلۡعَذَابِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:85Sannan sai ga ku, ku ɗin nan kuna kashe junanku, kuma kuna fitar da wata ƙungiya daga cikinku daga gidajensu, kuma kuna taimaka wa juna wajen cutar da su ta hanyar laifi da zalunci. Idan kuma sun zo muku suna kamammun yaƙi sai ku fanshe su, alhali fitar da su haramun ne a gare ku. Yanzu kwa riƙa yin imani da sashen Littafi kuma ku riƙa kafircewa da wani sashen? To ba komai ne sakamakon wanda yake aikata haka daga cikinku ba face wani wulaƙanci a rayuwar duniya, kuma ranar alƙiyama a mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba, kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da kuke aikatawa.
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا بِٱلۡأٓخِرَةِۖ فَلَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Open ayah 2:86Waɗannan su ne waɗanda suka musanya rayuwar duniya da ta lahira, kuma ba za a sassauta musu azaba ba, kuma ba za a taimaka musu ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tuna wa Banu Isra’ila wani ƙaƙƙarfan alƙawari da ya yi da su na cewa, kada su bauta wa kowa sai shi kaɗai, ba tare da sun yi shirka da komai ba, kuma su kyautata wa iyayensu ta duk hanyoyin kyautatawa, hakanan su taimaka wa marayu, wato yaran da suka rasa iyayensu maza kuma ba su balaga ba, mazansu da matansu. Sannan ya umarce su da su zamo masu faɗa wa mutane maganganu masu daɗi, wanda hakan ya ƙunshi yi musu nasiha da wa’azi ta hanyar da ta dace, ya ƙunshi yafiya da afuwa da sauransu. Kamar yadda ya umarce su da su tsayar da salla tare da kula da hukunce-hukuncenta, su kuma fitar da zakkar dukiyoyinsu su ba wa talakawa. To amma duk bayan wannan alƙawari mai ƙarfi da ya yi da su, sai ya zamana ‘yan kaɗan ne daga cikinsu suka cika wannan alƙawari. Bayan wancan alƙawarin, ya sake tuna musu wani alƙawarin na daban da ya yi da su, wanda shi ne ya hana su su riƙa kashe junansu ko kuma wasu daga cikinsu su riƙa korar wasu daga gidajensu haka kawai, ba tare da wani laifi ba, kuma suka amince da wannan alƙawari, suka ba da shaida a kansa, ba su musa ba ko kaɗan. To amma kuma sai ga shi daga baya sun zo suna faɗa da junansu, har suna kashe juna, wasu daga cikinsu suna korar ‘yan uwansu Yahudawa daga gidajensu ba gaira ba dalili, har ta kai ga suna taimaka wa wasu a kan cutar ‘yan uwansu, saboda tsabar aikata laifi da ta’addanci irin nasu. Wata sabuwar kuma ita ce, bayan wannan kashe-kashe da suke yi a junansu da korar junansu daga gidajensu, sai kuma ga shi idan wasu daga cikin ‘yan’uwansu Yahudawa sun faɗa hannayen abokan gabarsu a matsayin fursunonin yaƙi, sai kuma su zo suna fansar su da dukiyoyinsu, tare da cewa tun farko Allah ya hana su korar ‘yan’uwan nasu daga gidajensu, ya hana su su taimaka wa wasu maƙiyansa a kan yaƙar ‘yan’uwansu, amma ba su hanu daga aikata hakan ba. Shi ne a nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yake zargin su da irin wannan ɗanyen aikin nasu. Yaya za su ba da gaskiya da wani hukunci na Attaura, wanda shi ne fansar ‘yan’uwansu daga hannayen maƙiyansu, amma kuma su kafirce wa wasu hukunce-hukuncen, waɗanda su ne hana kashe-kashe a junansu da fitar da juna daga gidajensu?! Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗi sakamakon duk mai aikata irin waɗannan ayyuka da cewa, yana tare da taɓewa a nan duniya, kuma ranar lahira zai gamu da matsananciyar azaba, domin duk irin abin da suke aikatawa Allah yana sane da shi, babu abin da yake ɓuya a gare shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna mana irin waɗannan Yahudawa su ne waɗanda suka yi musanyar rayuwar duniya da ta lahira, a dalilin kafirce wa shari’ar Allah da suka yi, don haka ba za a taɓa sassauta musu azaba ba ranar gobe ƙiyama, kuma babu wani mai kawo musu ɗauki ya ƙwace su daga azabar Allah.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَقَفَّيۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ بِٱلرُّسُلِۖ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ أَفَكُلَّمَا جَآءَكُمۡ رَسُولُۢ بِمَا لَا تَهۡوَىٰٓ أَنفُسُكُمُ ٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡ فَفَرِيقٗا كَذَّبۡتُمۡ وَفَرِيقٗا تَقۡتُلُونَ
Open ayah 2:87Kuma haƙiƙa Mun ba wa Musa Littafi, kuma Muka biyo bayansa da manzanni, kuma Mun bai wa Isa ɗan Maryam hujjoji bayyananu, kuma Mun ƙarfafe shi da Ruhi mai tsarki. Ashe yanzu duk sa\'adda wani manzo ya zo muku da abin da zukatanku ba sa so, sai ku yi girman kai, don haka sai ku ƙaryata wasu, kuma ku kashe wasu?
وَقَالُواْ قُلُوبُنَا غُلۡفُۢۚ بَل لَّعَنَهُمُ ٱللَّهُ بِكُفۡرِهِمۡ فَقَلِيلٗا مَّا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 2:88Suka ce kuma: “Zukatanmu rufaffu ne.” A’a ba haka ba ne, Allah dai Ya la\'ane su ne saboda kafircinsu, don haka kaɗan ne waɗanda suke yin imani.
وَلَمَّا جَآءَهُمۡ كِتَٰبٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٞ لِّمَا مَعَهُمۡ وَكَانُواْ مِن قَبۡلُ يَسۡتَفۡتِحُونَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَمَّا جَآءَهُم مَّا عَرَفُواْ كَفَرُواْ بِهِۦۚ فَلَعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:89Yayin da kuma wani littafi ya zo musu daga Allah, yana mai gaskata abin da yake tare da su, alhali kuma a da sun kasance suna addu\'ar neman nasara a kan waɗanda suka kafirta (mushrikai). To yayin da abin da suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa. Don haka la\'anar Allah ta tabbata a kan kafirai.
بِئۡسَمَا ٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡ أَن يَكۡفُرُواْ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بَغۡيًا أَن يُنَزِّلَ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ فَبَآءُو بِغَضَبٍ عَلَىٰ غَضَبٖۚ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٞ مُّهِينٞ
Open ayah 2:90Tir da wannan abu da suka sayar da kawunansu da shi, wato suka kafirce wa abin da Allah Ya saukar, don hassadar cewa, (don me) Allah zai saukar da falalarsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, sai suka wayi gari da fushin Allah a kan wani fushin. Kuma azaba ta wulaƙanci ta tabbata ga kafirai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa mana cewa, ya ba wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) littafin Attaura, sannan a bayansa ya ci gaba da aiko wasu manzannin zuwa ga al’ummar Banu Isra’ila, waɗanda suka ci gaba da aiki da shari’ar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), har zuwa lokacin da ya aiko Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya kuma bayyana gaskiyarsa ta hanyar ba shi mu’ujizoji daban-daban, kamar tayar da matattu, da warkar da marasa lafiya da izinin Allah, hakanan ya ƙarfafa shi da Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya riƙa taimaka masa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna mana ƙyamar irin ta’annutin da Banu Isra’ila suka riƙa yi wa annabawan da ya aika musu. Wato duk sa’adda wasu manzanni suka zo musu da hukunce-hukuncen da suka saɓa wa soye-soyen zukatansu, sai su ji cewa waɗannan manzanni suna matsa musu ne, kuma sun rena musu wayo, don haka sai girman kansu ya ingiza su, sai su ƙaryata wasu daga cikin waɗannan manzannin, wasu kuma ma su kashe su. Sai kuma sai suka riƙa faɗar wata ƙaryar cewa, wai su abin da ya hana su su yi imani shi ne, zukatansu a rufe suke rif, don haka ba sa iya fahintar wani abu da manzanninsu suke faɗa musu. Sai Allah ya ƙaryata su, ya nuna abin da suke inkari ba haka yake ba; kafircinsu ne kawai ya jawo Allah ya la’ance su, ya nisantar da su daga rahmarsa, sakamakon abin da suka zaɓa na bijire wa koyarwar manzanninsu da annabawansu. Saboda haka sai ya kasance ‘yan kaɗan ne a cikinsu suka ba da gaskiya, ko kuma abin da suka yi imani da shi kaɗan ne ƙwarai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba mu labarin wani hali na Yahudawa tun kafin aiko Annabi Muhammad (ﷺ) shi ne yayin da suke a Madina, duk sa’adda wani faɗa ya ɓarke tsakaninsu da Larabawa mutanen Madina masu yin shirka, sukan ce musu: “Akwai wani Annabi da za a aiko nan ba da jimawa ba; idan ya bayyana za mu bi shi, mu haɗa ƙarfi da shi, mu yi muku irin kisan da aka yi wa Adawa da Samudawa.” Wato suna nufin kisan ƙare-dangi. Su Yahudawa a zatonsu Annabin zai bayyana ne daga cikinsu, sai kuma ya bayyana daga cikin Larabawa kuma Ƙuraishawa, abokan faɗansu. Yayin da Annabi Muhammad (ﷺ) ya zo da littafin Alƙur’ani, wanda yake gaskata abin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da sauran annabawa suka zo da shi na Tauhidi, kuma Banu Isra’ila suka gane shi ne Annabin da suke faɗar zai bayyana, suka kuma fahinci gaskiyar da ya zo da ita, to maimakon su yi imani kamar yadda suka kasance suna shelantawa, sai kawai suka kafirce masa, a dalilin haka sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya la’ance su, ya nisantar da su daga rahmarsa. Wannan kuma shi ne sakamakon kowane kafiri a duniya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da irin wannan mugun zaɓi da Yahudawa suka yi wa kawunansu, wato suka zaɓi su kafirce wa Annabin da suka san gaskiyarsa, suka zaɓar wa kawunansu shiga wutar Jahannama, ba don wani abu ba, sai don kawai tsabar hassada da ƙabilanci da suke yi wa Larabawa, wai don me Allah (Mai tsarki da daukaka) zai aiko da Annabi a cikinsu ba a cikin Banu Isra’ila ba, tare da cewa sun san shi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayar da falalarsa ne ga wanda ya ga dama daga cikin bayinsa babu mai iya hana shi. Wannan ne ya sa Yahudawa suka cancanci wani fushi daga Allah (Mai tsarki da daukaka) a kan fushin da suka cancanta a baya na laifukan da suka riƙa tabkawa. Don haka ne duk waɗanda za su bijire wa saƙon Annabi Muhammadu (ﷺ) a kowane zamani ne to suna da wata azaba mai wulaƙantarwa.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ ءَامِنُواْ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ نُؤۡمِنُ بِمَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا وَيَكۡفُرُونَ بِمَا وَرَآءَهُۥ وَهُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَهُمۡۗ قُلۡ فَلِمَ تَقۡتُلُونَ أَنۢبِيَآءَ ٱللَّهِ مِن قَبۡلُ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 2:91Idan aka ce da su: “Ku yi imani da abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “Mu muna yin imani ne da abin da aka saukar mana”. Kuma suna kafircewa da duk wani abu da ba shi ba, alhalin shi gaskiya ne, kuma mai gaskata abin da ke tare da su ne. To ka ce: “Me ya sa a da kuke kashe annabawan Allah idan kun kasance muminai?”
۞وَلَقَدۡ جَآءَكُم مُّوسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ ٱتَّخَذۡتُمُ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَنتُمۡ ظَٰلِمُونَ
Open ayah 2:92Haƙiƙa Musa ya zo muka da hujjoji bayyanannu, sannan kuka bauta wa ɗan maraƙi bayansa alhalin kuna azzalumai.
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ وَرَفَعۡنَا فَوۡقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱسۡمَعُواْۖ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَعَصَيۡنَا وَأُشۡرِبُواْ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡعِجۡلَ بِكُفۡرِهِمۡۚ قُلۡ بِئۡسَمَا يَأۡمُرُكُم بِهِۦٓ إِيمَٰنُكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 2:93Kuma ku tuna lokacin da Muka ɗauki alƙawari da ku, Muka kuma ɗaga dutsen Ɗuri a kanku, Muka ce: “Ku riƙi abin da muka ba ku da ƙarfi, kuma ku saurara”. Sai suka ce: “Mun ji kuma mun saɓa”. Kuma aka sanya musu tsananin son bautar ɗan maraƙi a zukatansu saboda kafircinsu. Ka ce: “Tir da abin da imaninku yake umartar ku da shi, idan har kun kasance muminai.” A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana yadda Banu Isra’ila suke iƙrarin cewa, su sun yi imani ne da Attaura kawai, kuma ta wadatar da su, ba sa buƙatar sai sun yi imani da Alƙur’ani. To shi ne a nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yake ƙaryata su, yana bayyana cewa, hatta ita ma Attaurar ba wani cikakken imani suka yi da ita ba. Duk da cewa shi Alƙur’ani Allah ya saukar da shi ne bayan Attaura, kuma yana gaskata abin da yake cikin Attaura na Tauhidi da rukunnan imani. Wannan magana tasu tubka da warwara ce, domin duk wanda ya ƙaryata Alƙur’ani, to ya ƙaryata sauran littattafan ma gaba ɗaya. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa Muhammad (ﷺ) da ya tambaye su, idan har da gaske suke sun yi imani da Attaura, me ya sa suke kashe annabawan Allah waɗanda su ma suna gaskata abin da yake cikinta? Kuma a cikin Attaura an haramta kashe kowane Annabi. A ƙarshe sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna a fili cewa, ƙarya suke yi, ba su yi imani da Attaurar ba, domin tun farko da Annabi Musa ya zo musu da hujjoji bayyanannu masu tabbatar da gaskiyar annabcinsa, sai suka koma suna bautar ɗan maraƙi lokacin da ya tafi ganawa da Ubangijinsa saboda ƙetare iyaka da zalunci. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tuna wa Banu Isra’ila labarin lokacin da ya ɗauki alƙawari mai ƙarfi a wurinsu, har ya ɗaga dutsen Ɗuri a samansu, kamar ya rufto ya faɗo musu, domin a tsorata su a kan dole su yi aiki da umarnin da aka ba su na cewa lalle su riƙe Attaura gamgam da himma da nashaɗi, kuma su saurari maganar Allah, sauraro na karɓa da miƙa wuya, amma sai suka amsa wa Allah (Mai tsarki da daukaka) da cewa, sun ji da kunnuwansu, amma kuma sun saɓa da ayyukansu. Son bautar ɗan maraƙi ya riga ya ratsa zukatansu, sun kwankwaɗe shi da gaske, kamar yadda mai jin ƙishirwa yake kwankwaɗar ruwa idan ya samu, har ya ratsa ko’ina a jikinsa. Bayanan da suka gabata sun tabbatar da cewa, imanin Yahudawa na jabu ne, tun da bai hana su kashe annabawan Allah ba, bai hana su bautar ɗan maraƙi ba, bai kuma hana su bijire wa umarnin Ubangijinsu ba. Don haka sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da wannan imani nasu, ya tabbatar da cewa, imani na ƙwarai shi yake sanya mai shi ya aikata alheri ya kuma kauce wa sharri.
قُلۡ إِن كَانَتۡ لَكُمُ ٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ عِندَ ٱللَّهِ خَالِصَةٗ مِّن دُونِ ٱلنَّاسِ فَتَمَنَّوُاْ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 2:94Ka ce: “Idan gidan lahira ya kasance keɓantacce a gare ku a wurin Allah ku kaɗai ban da sauran mutane, to ku yi burin mutuwa idan har ku masu gaskiya ne.”
وَلَن يَتَمَنَّوۡهُ أَبَدَۢا بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 2:95Ba za su taɓa burin mutuwa ba har abada, saboda abin da hannayensu suka aikata. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai.
وَلَتَجِدَنَّهُمۡ أَحۡرَصَ ٱلنَّاسِ عَلَىٰ حَيَوٰةٖ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْۚ يَوَدُّ أَحَدُهُمۡ لَوۡ يُعَمَّرُ أَلۡفَ سَنَةٖ وَمَا هُوَ بِمُزَحۡزِحِهِۦ مِنَ ٱلۡعَذَابِ أَن يُعَمَّرَۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:96Kuma za ka same su sun fi kowa kwaɗayin tsawon rai, fiye ma da waɗanda suka yi shirka. Kowane ɗayansu yana burin ina ma za a raya shi shekara dubu, kuma raya shi (shekar dubu) ba zai nensanta shi daga shiga wuta ba. Kuma Allah Mai ganin abin da suka kasance suna aikatawa ne. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, idan Yahudawan Madina suna da’awar cewa, don su kaɗai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanadi ni’imar gidan Aljanna a lahira, ban da sauran mutane, to ga wata hanya da za a bi a gane mai gaskiya, ita ce su haɗu su yi addu’ar tsinuwa, wato su roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya halaka maƙaryaci daga cikinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa, sam-sam Yahudawa ba za su taɓa karɓar wannan kira nasa ba, saboda suna sane da irin laifuffukan da suka tabka na kafirce wa Annabi da ɓoye gaskiya, kuma suna sane da cewa hanyar haɗuwa da mummunan sakamakon miyagun ayyukansu ita ce mutuwa; da zarar sun mutu, to sun faɗa cikin abin ƙi ke nan har abada. Wannan kaɗai ya isa ya hana su son mutuwa. To amma fa kada su manta da cewa, Allah yana sane da duk wani azzalimi mai keta dokarsa a bayan ƙasa, kuma komai daɗewa sai Allah ya damƙe shi ya nuna masa sakamakonsa. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ai babu wani jinsi na mutane da yake gudun mutuwa irin jinsin Bayahude, domin ya san abin da yake jiran sa a lahira na azaba, don haka za ka ga kowane ɗayansu yana son ya yi tsawon rai a duniya, ta yadda soyayyarsu da rayuwa a nan duniya, har ta zarce ta mushrikai waɗanda ma ba su yi imani da akwai ranar lahira ba, ballantana har su yarda da cewa akwai wani sakamako da zai biyo baya. Ai shi Bayahude burinsa shi ne ya rayu shekara dubu a duniya, to amma ya manata cewa, ko da an ba shi tsawon rai irin wannan, ba zai hana shi mutuwa ba, kuma da zarar ya mutu wuta ce makomarsa. Allah kuma yana ganin duk abin da suke aikatawa na miyagun ayyuka, ba abin da yake ɓuya a gare shi kuma zai yi musu sakayya a kansu ɗaya bayan ɗaya.
قُلۡ مَن كَانَ عَدُوّٗا لِّـجِبۡرِيلَ فَإِنَّهُۥ نَزَّلَهُۥ عَلَىٰ قَلۡبِكَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَهُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 2:97Ka ce: “Duk wanda ya kasance maƙiyi ne ga (Mala\'ika) Jibrilu, to lalle shi ne ya saukar da shi (Alƙur\'ani) a kan zuciyarka da izinin Allah yana mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma shiriya ne da bushara ga muminai.”
مَن كَانَ عَدُوّٗا لِّلَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَجِبۡرِيلَ وَمِيكَىٰلَ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَدُوّٞ لِّلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:98Duk wanda ya kasance maƙiyi ne ga Allah da mala\'ikunsa da manzanninsa da Jibrilu da Mika\'ilu, to lalle Allah maƙiyin kafirai ne.
وَلَقَدۡ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۖ وَمَا يَكۡفُرُ بِهَآ إِلَّا ٱلۡفَٰسِقُونَ
Open ayah 2:99Kuma haƙiƙa Mun saukar maka da ayoyi bayyanannu, babu kuma mai kafirce musu sai fasiƙai.
أَوَكُلَّمَا عَٰهَدُواْ عَهۡدٗا نَّبَذَهُۥ فَرِيقٞ مِّنۡهُمۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 2:100Yanzu ashe duk sa\'adda suka ƙulla wani alƙawari sai wani ɓangare daga cikinsu ya yi watsi da shi?! Bari! Yawancinsu ba sa yin imani.
وَلَمَّا جَآءَهُمۡ رَسُولٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٞ لِّمَا مَعَهُمۡ نَبَذَ فَرِيقٞ مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ كِتَٰبَ ٱللَّهِ وَرَآءَ ظُهُورِهِمۡ كَأَنَّهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:101Yayin da wani manzo daga Allah ya zo musu yana mai gaskata abin da yake tare da su (na Littafin Attaura), sai wani ɓangare daga cikinsu suka jefar da littafin Allah a bayansu kamar ba su san komai ba. Imamut Tirmizi [#3117] da Imamu Ahmad [#2483] sun ruwaito hadisi daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yahudawa sun zo wurin Manzon Allah (ﷺ) suka ce masa: “Ya Baban Alƙasim, mun zo ne mu yi maka tambaya a kan abubuwa guda biyar, idan ka ba mu amsarsu, to mun fahinci kai Annabi ne, kuma za mu bi ka. Sai Annabi (ﷺ) ya kafa musu shaida da Allah, kamar yadda Annabi Yakubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi da ‘ya’yansa, lokacin da suka ce: “Allah ne wakili bisa duk abin da za mu faɗa.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “To ku yi tambayoyinku.” Sai suka ce: “Ka faɗa mana mece ce alamar annabi?” Sai ya ce: “Alamarsa ita ce, idanuwansa za su yi barci, amma zuciyarsa ba za ta yi ba.” Sai suka ce: “To ka faɗa mana mene ne ya sa mace wani lokaci ta haifi ‘ya mace, wani lokaci kuma ta haifi ɗa namiji?” Sai ya ce, “Idan ruwan ‘ya mace ya rinjayi ruwan ɗa namiji, to sai ta haifi ‘ya mace, idan kuwa na mijin ne ya rinjayi na matar, sai ta haifi ɗa namiji.” Sai suka ce: “To faɗa mana, wane irin abinci ne Isra’ilu (Ya’aƙub) ya haramta wa kansa?” Sai ya ce: “Ya yi fama da cutar ciwon kwankwaso da ƙafafu (Sciatica ), bai samu wani magani da ya yi masa amfani ba, sai nonon abu kaza da abu kaza. (Imamu Ahmad ya ce wasu sun ce nonon raƙumi ne ya samu). Daga lokacin sai ya haramta wa kansa cin namansu.” Sai suka ce: “Ka yi gaskiya.” Sannan kuma suka ce: “To faɗa mana mene ne wannan tsawar da muke ji?” Sai ya ce:“Wannan mala’ika ne da Allah ya wakilta shi don ya kula da girgije, yana ɗauke da wani takobi na wuta a hannunsa, yana kora wannan girgije da shi har zuwa inda Allah ya umarce shi.” Sai suka ce: “To, shi kuma wannan ƙarar da ake ji ta mece ce?” Sai ya ce: “Muryarsa (Mala’ikan) ce.” Sai suka ce, “Ka yi gaskiya.” Sannan kuma suka ce masa: “To yanzu saura tambaya ɗaya ta rage, idan ka amsa mana ita, to za mu yi maka mubaya’a, domin babu wani annabi face yana da wani mala’ika da yake kawo masa labari. To ka faɗa mana kai wane ne mala’ikanka?” Sai ya ce: “Jibrilu ne (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).” Cikin mamaki, sai suka ce: “Jibrilu? Ai wannan shi ne wanda yake saukowa da yaƙi da kashe-kashe da azaba, ai wannan maƙiyinmu ne! Da dai ka ce mana mala’ika ne wanda yake saukar da rahama da tsaro da ruwan sama, da abin ya yi kyau.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi (watau aya ta 97-99).” [Hadisi ne mai kyau, ban da maganar tsawa da walƙiya]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce wa Annabinsa (ﷺ) ya faɗa wa waɗannan Yahudawa cewa, duk wanda yake gaba da Mala’ika Jibrilu, to ya sani cewa, shi Jibrilu yana saukar wa da Annabi Alƙur\'ani ne da umarnin Allah, ba a gaban kansa yake yi ba, don haka ba shi suke nuna wa ƙiyayya ba, Allah ne da ya aiko shi suke nuna wa ƙiyayya. Sannan kuma Alƙur\'ani da yake saukar masa, koyarwar cikinsa tana daidai da abin da ya zo a littattafan annabawan da suka gabace shi, kamar Attaura. Wannan kuwa babban dalili ne da yake nuna gaskiyarsa, sannan shi Alƙur’ani babbar bushara ce ga muminai ta irin abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanadar musu na ni’ima mai ɗorewa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa musu cewa, duk wanda yake ƙin Allah ko yake ƙin wani mala’ika, ko Mala’ika Jibrilu, ko Mala’ika Mika’ilu, ko yake gaba da wani manzo daga cikin manzannin Allah, to wannan kafiri ne, kuma Allah zai ɗauke shi a matsayin abokin gabarsa, domin Allah ba ya son kowane irin kafiri. Shi ya sa ya zo a hadisi ƙudusi inda Allah yake cewa: “Duk wanda ya yi gaba da wani masoyina, to lalle ina yi masa shelar yaƙi.” [Bukhari #6502]. Abdurrahman ɗan Abu Laila ya ruwaito cewa, wani Bayahude ya gamu da Sayyidina Umar (Allah ya kara masa yarda) sai ya ce masa: “Jibrilun nan da Annabinku yake ta faɗa fa maƙiyinmu ne.” Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya mayar masa da martani da cewa: “Wanda duk ya kasance maƙiyin Allah da mala’ikunsa da manzanninsa….(har zuwa ƙarshen ayar).” Ya ce: “Sai wannan ayar ta sauka.” [Duba Tafsirin Ibnu Abi Hatim Juzu’i na 1, shafi na182; da Fathul Bari na Ibnu Hajar Juzu’i na 8, shafi na16]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, ya saukar masa da ayoyi bayyanannu, masu nuna gaskiyar annabcinsa, babu wanda yake ja da su sai wanda ba mumini ba. Allah kuma ya faɗa masa cewa, Yahudawa wasu mutane ne marasa alƙawari; duk sa’adda suka ɗaukar wa Allah alƙawarin za su yi aiki da Attaura da abin da ta ƙunsa na shari’a, to sai an samu wasu daga cikinsu sun warware alƙawarin nan sun yi jifa da shi, ba komai ya jawo haka ba, sai domin yawancinsu ba masu imani ba ne, domin da suna da imani na gaskiya, to da sun kiyaye alƙawari, ba su karya shi ba. Daga cikin ire-iren karya alƙawarin da suka yi shi ne, lokacin da Allah ya aiko Annabinsa (ﷺ) ya zo kuma kamar yadda Allah ya siffanta musu shi a cikin littattafansu, kuma ya yi alƙawari da su a kan za su bi shi idan ya bayyana, to sai ga shi yanzu yawancinsu sun yi watsi da wannan alƙawarin, sun yi jifa da littafin Attaura can bayansu, kamar ba su taɓa sanin wani abu ba dangane da wannan Annabi da siffofinsa.
وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتۡلُواْ ٱلشَّيَٰطِينُ عَلَىٰ مُلۡكِ سُلَيۡمَٰنَۖ وَمَا كَفَرَ سُلَيۡمَٰنُ وَلَٰكِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحۡرَ وَمَآ أُنزِلَ عَلَى ٱلۡمَلَكَيۡنِ بِبَابِلَ هَٰرُوتَ وَمَٰرُوتَۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنۡ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحۡنُ فِتۡنَةٞ فَلَا تَكۡفُرۡۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنۡهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَزَوۡجِهِۦۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنۡ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡۚ وَلَقَدۡ عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشۡتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖۚ وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:102Sai suka bi abin da sheɗanu suke karantawa a (zamanin) mulkin Sulaimanu; kuma Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai sheɗanun su ne suka kafirta suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar wa mala\'iku biyu, Haruta da Maruta, a garin Babila. Kuma ba sa koya wa wani (tsafin) har sai sun faɗa masa cewa: “Mu fa jarraba ce, don haka kada ka kafirta”. Sai (mutane) suka riƙa koyo daga wajensu su biyu abin da suke raba tsakanin miji da matarsa da shi. Kuma ba za su iya cutar da wani da shi ba sai da izinin Allah. Sai su koyi abin da zai cutar da su kuma ba zai amfane su ba. Kuma haƙiƙa sun san cewa, tabbas duk wanda ya zaɓi (sihiri) ba shi da wani rabo a lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da kawunansu da shi, da a ce sun san (haƙiƙanin makomarsu).
وَلَوۡ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَمَثُوبَةٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ خَيۡرٞۚ لَّوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:103Da a ce su sun yi imani kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa da sakamakon (da za su samu) daga Allah shi ne mafi alheri, da a ce sun sani. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin halin da Yahudawa suka tsinci kansu a ciki, bayan sun yi watsi da littafin Allah da koyarwar annabawansu, sai suka rungumi koyarwar shaiɗanu a madadin haka, wanda sakamakon haka shi ne duk wanda ya bar koyarwar annabawa da ilimi mai amfani, to lalle a madadinsa sai ya rungumi wani ilimi marar kyau mai cutarwa. Don haka sai Yahudawa suka rungumi ilimin sihiri, kuma suka riƙa faɗar ƙaryar cewa, shi ne ilimin da Annabi Sulaiman yake amfani da shi wajen sarrafa mulkinsa, da shi ne ya mulki mutane da aljannu, har ma da dabbobi. Sai Allah ya ƙaryata su, ya wanke Annabi Sulaiman (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga aikata duk wani tsafi, shi kuma ba kafiri ne ba, aikata tsafi kuma kafirci ne. Don haka shaiɗanu ne suka kafirta ta hanyar fitowa suna koya wa mutane sihiri domin su ɓatar da su daga kan hanya. Hakanan Yahudawa suka rungumi sihirin da aka saukar wa wasu mala’iku su biyu, wato Harutu da Marutu a garin Babila da ke ƙasar Iraƙi, domin su zama jarraba ga mutane. Su kuma waɗannan mala’iku biyu ba sa yarda su koya wa wani sihirin, har sai sun yi masa nasiha da cewa: “Mu fa wata jarrabawa ce daga Allah, don haka kada ka yarda ka kafirta ta hanyar koyon wannan sihirin da aiki da shi.” To amma duk da wannan nasihar tasu, sai mutane suka riƙa koyon sihiri daga wajensu, suna aikata miyagun ayyuka da su, kamar na raba tsakanin ma’aurata biyu masu ƙaunar juna. Kuma su waɗannan matsafa ba su da ikon su cutar da wani da tsafinsu sai da izinin Allah da ganin damarsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Yahudawan nan da suka yi watsi da littafin Allah, suka kafirce wa Annabi (ﷺ) suka riƙi tsafi da matsafa bayan sun san cewa, sun yi wa kansu zaɓin tumun-dare ne, sun saki reshe ne sun kama ganye, domin kuwa ba su da wani rabo a lahira daga gidan Aljanna. To Allah ya yi tir da irin wannan zaɓi na banza da suka yi wa kansu; da kuma sun san yadda suka sayar da kawunansu da rabonsu na lahira a kan wani abu ƙanƙani wanda zai cutar da su duniya da lahira to da ba su aikata haka ba. Kuma da sun nutsu sun tsaya sun zaɓi imani da tsoron Allah maimakon tsafi, to da Allah ya saka musu da mafificin abin da suke nema a nan duniya na irin amfanin da suke hangowa a cikin koyon sihiri da aiki da shi.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقُولُواْ رَٰعِنَا وَقُولُواْ ٱنظُرۡنَا وَٱسۡمَعُواْۗ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 2:104Ya ku waɗanda suka yi imani kada ku ce, ra\'ina , (watau kula da mu), sai dai ku ce, dakata mana, kuma ku saurara. Kafirai kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi. Sahabban Annabi (ﷺ) sun kasance idan yana biya musu karatu sukan nemi ya ɗan dakata musu kaɗan domin su fahinci karatun sosai, to sai sukan yi amfani da kalmar ‘ra\'ina’ . A harshen Yahudawa kuma wannan kalmar tana kusa da wata kalma da take da ma’anar ‘daƙiƙi’, to sai su ma suka riƙa fakewa da wannan kalmar, suna zagin Annabi (ﷺ). Sai Allah ya saukar da wannan ayar, yana hana sahabbai amfani da wannan kalmar, a maimakonta ya ce su yi amfani da kalmar ‘unzurna’ wadda take nufin ‘dakata mana’. Kuma Allah ya umarce su da su saurari abin da Annabi (ﷺ) yake karantar da su sauraro na fahinta, kuma ya ba da labarin cewa kafirai masu gardama da ayoyin Allah, kamar Yahudawa da sauransu, suna da wata azaba mai raɗaɗi a lahira. Wannan ayar tana karantar da mu cewa, duk sa’adda muke amfani da wata kalma, ko wata magana, ya zamana maƙiya Musulunci suna yi mata muguwar fassara domin tana ɗauke da ma’ana mai harshen damo, to ya wajaba mu kauce mata, mu canza ta da wata kalmar da ba za a samu irin wannan matsalar tare da ita ba.
مَّا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَلَا ٱلۡمُشۡرِكِينَ أَن يُنَزَّلَ عَلَيۡكُم مِّنۡ خَيۡرٖ مِّن رَّبِّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَخۡتَصُّ بِرَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 2:105Waɗanda suka kafirta daga ma\'abota littafi da mushrikai ba sa ƙaunar a saukar muku da wani alheri daga Ubangjinku, sai dai Allah kuwa Yana keɓance wanda Ya ga dama da rahamarsa, Allah kuma Mai babbar falala ne. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗin halayen Yahudawa da Nasara har ma da mushrikai, na irin baƙin cikin da suke yi wa Annabi (ﷺ) da muminai, wai me zai sa Allah ya waro wani daga cikinsu ya ba shi annabta? To sai Allah ya mayar musu da martani cewa, yana keɓance wanda ya ga dama da rahmarsa ne, kamar ta annabci da manzanci da ilimi, don haka ne ya zaɓi Annabi (ﷺ) da annabci da manzanci, ya kuma saukar masa da Alƙur\'ani. Shi Allah (Mai tsarki da daukaka) falalarsa da rahmarsa masu yalwa ne masu girma.
۞مَا نَنسَخۡ مِنۡ ءَايَةٍ أَوۡ نُنسِهَا نَأۡتِ بِخَيۡرٖ مِّنۡهَآ أَوۡ مِثۡلِهَآۗ أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Open ayah 2:106Babu wata aya da za Mu shafe ko Mu mantar da kai ita, sai Mun kawo wadda ta fi ta alheri ko kwatankwacinta. Ashe ba ka san cewa, lalle Allah Mai iko ne a kan komai ba?
أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ
Open ayah 2:107Kuma ba ka sani ba cewa, lalle mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, kuma ba ku da wani majiɓinci ko wani mai taimako ba Allah ba? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da mayar da martani a kan wata ƙarya da Yahudawa suka fito da ita domin sukan Alƙur\'ani, ita ce ƙaryata cewa Allah idan ya ga dama yana canza wani hukunci na shari’a da ya saukar da wani daban wanda yake tattare da maslaha kamar na farkon, ko ma ya zamana mafi alheri. To shi ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake faɗa cewa, babu wani hukunci na wata aya da zai shafe, ya kawo wani sabo a madadinsa, ko kuma wata aya da Allah zai goge ta daga zuciyar Annabi (ﷺ) da sahabbansa (Allah ya kara masa yarda), ko kuma ya jinkirta saukar da ita, face sai ya saukar da wata ayar da ta fi wadda ya shafe, ta fuskar amfani da maslaha ga ɗan\'adam. Allah yana yin haka ne domin ya nuna cikar ikonsa a kan komai, domin kuwa matuƙar Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne mamallakin komai da ke sama da abin da yake ƙasa, kuma shi ne mai iko da su, yana sarrafa hukuncinsa a kan bayinsa yadda ya ga dama, to wajibi ne mu yarda da cikakken ikonsa a kan hukunci ga bayinsa yadda ya ga dama, ya halatta abin da ya ga dama, ko ya haramta, domin babu mai masa gyara a kan aikinsa, mu kuma bayinsa ne, ban da shi ba mu da wani wanda zai iya taimaka mana ya kare mu daga duk wani sharri.
أَمۡ تُرِيدُونَ أَن تَسۡـَٔلُواْ رَسُولَكُمۡ كَمَا سُئِلَ مُوسَىٰ مِن قَبۡلُۗ وَمَن يَتَبَدَّلِ ٱلۡكُفۡرَ بِٱلۡإِيمَٰنِ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ
Open ayah 2:108Ko kuma kuna nufin za ku tambayi Manzonku kamar yadda aka yi wa Musa tambaya a da? Kuma duk wanda ya canza imani da kafirci to haƙiƙa ya ɓace wa tsakiyar hanya. Daga nan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da yi mana bayani game da irin tambayoyin ƙure da wasu suka riƙa yi wa Manzon Allah (ﷺ), suna cewa idan har ya iya biya musu waɗannan buƙatu nasu, to a lokacin ne za su yi imani da shi. Kamar yadda Abdullah ɗan Abbas ya ce, Rafi’u ɗan Huraimilah da Wahabu ɗan Zaidu sun ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Ka hau sama ka zo mana da wani littafi a rubuce da za mu karanta, ko ka ɓulɓulo mana da ƙoramu, idan ka yi hakan, to za mu yarda da kai mu bi ka.” Sai Allah ya saukar da waɗannan ayoyi, yana jan kunnen muminai da kafirai da su guji irin waɗannan tambayoyi da buƙatu na ƙoƙarin ƙure Manzon Allah (ﷺ), ko nuna masa rashin gamsuwa da abin da ya zo da shi na shiriya, kamar yadda Yahudawan farko suka riƙa yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) irin waɗannan tamboyi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin tambayoyin ƙwaƙwa da Yahudawa suka yi ta yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a wannan Sura, aya ta 55 da 61 da 68-71 da Suratun Nisa’i , aya ta 133. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin waɗannan buƙatu da Ƙuraishawa suka riƙa bijiro wa Annabi (ﷺ) da su, domin su nuna gazawarsa, daga bisani su sami hujja a kan ƙaryata shi da suke yi, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Isra’i aya ta 89-93. To saboda irin waɗannan tambayoyi wasu daga cikinsu kafirci ne ƙarara, wasu kuma za su iya kaiwa ga kafirci, sai Allah ya yi gargaɗi a kan hakan da cewa, duk wanda ya musanya imaninsa da kafirci, to lalle wannan ya kauce wa hanyar Allah, ya kama hanyar halaka da taɓewa. Ayar ta nuna rashin halaccin tambayoyi marasa ma’ana a addini, ko na nuna rashin amincewa da wani umarni na Allah da Manzonsa, domin yin haka yana nuna rashin sallamawa ta gaba ɗaya ga Allah da Manzonsa (ﷺ). Hadisai na Annabi (ﷺ) sun zo da yawa masu nuna haramcin tambayar ƙwaƙwa, daga cikinsu akwai hadisin Sa’ad Ibn Abi Waƙƙas, ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce: “Musulmin da ya fi kowa laifi shi ne wanda ya yi tambaya a kan abin da ba a haramta ba, sai aka haramta shi saboda wannan tambayar tasa.” [Bukhari #7289, Muslim #2358]. Da kuma hadisin da Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya rawaito ya ce, Annabi (ﷺ) ya yi mana huɗuba a cikinta yake cewa: “Ya ku mutane, Allah ya wajabta muku aikin Hajji, don haka ku je Hajji.” Sai wani mutum ya yi tambaya: “A duk shekara ya Manzon Allah?” Annabi (ﷺ) ya yi shiru bai amsa masa ba, ya sake maimaitawa, Annabi bai amsa masa ba, har sau uku. Daga nan sai Annabi (ﷺ) ya ce, “Da na ce na’am, to da ya wajaba, kuma da ba za ku iya ba.” Sannan ya ce: “Ku ƙyale ni matuƙar na ƙyale ku, domin abin da ya ja waɗanda suka gabace ku suka halaka shi ne yawan tambayoyinsu da saɓa wa annabawansu. Don haka idan na umarce ku da wani abu, to ku aikata abin da za ku iya, idan kuwa na hana ku wani abu, to ku bar shi.” [Muslim #1373].
وَدَّ كَثِيرٞ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَوۡ يَرُدُّونَكُم مِّنۢ بَعۡدِ إِيمَٰنِكُمۡ كُفَّارًا حَسَدٗا مِّنۡ عِندِ أَنفُسِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلۡحَقُّۖ فَٱعۡفُواْ وَٱصۡفَحُواْ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 2:109Da yawa daga cikin ma\'abota littafi sun yi burin ina ma a ce su mayar da ku kafirai bayan imaninku, saboda hassada daga zukatansu, bayan kuma gaskiya ta bayyana a gare su. Don haka ku yi afuwa ku kawar da kai har sai Allah Ya zo da al\'amarinsa. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai.
وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Open ayah 2:110Kuma ku tsayar da salla ku kuma ba da zakka; kuma duk abin da kuka aikata na alheri domin kawunanku za ku same shi a wajen Allah. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba ne da bayyana miyagun ɗabi’u na Yahudawa da Nasara da irin hassadar da zukatansu suke ɗauke da ita dangane da shi Annabi (ﷺ) da kuma Musulmai, saboda ganin falalar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu ta aiko musu da Annabi daga cikinsu da saukar masa Alƙur\'ani mai cike da hikima da tsari. Wannan ya sa Yahudawa da Nasara suka riƙa fatan ina ma muminai za su yi ridda, su bar wannan addinin na Musulunci, duk a taru a zama ɗaya wajen kafirce wa Allah (Mai tsarki da daukaka) da Manzonsa (ﷺ) da littafinsa Alƙur\'ani. To sai Allah ya umarci muminai da su yi afuwa game da irin miyagun maganganun da suke fitowa daga bakunan maƙiyansu, su kawar da kai, domin suna yin haka ne da nufin su tunzura su har su kai ga ɗaukar wani mataki cikin fushi da ɓacin rai, wanda kuma yin hakan zai iya jawo rashin fahintar Musuluncin. Saboda haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya neme su da su kai zuciyarsu nesa, su yi watsi da duk wanda ya faɗa musu wata baƙar magana, su ƙyale shi har zuwa lokacin da umarnin Allah ko wani al’amarin zai zo, wato lokacin da za su nemi auka musu da yaƙi, su kuma Musulmi a umarce su da su tashi su kare addininsu da rayukansu, a nan ne Allah zai nuna musu fushinsa da azabarsa, kamar yadda ya faru ga Yahudawan Banun Nadhir da na Banu Ƙuraiza da Banu Ƙainuƙa’a, na kisa da korar da Annabi (ﷺ) ya yi musu daga Madina. Don haka muminai su ci gaba da addininsu kamar yadda Allah ya umarce su, su tsayar da salloli a lokutansu da kula da fitar da zakkar dukiyoyinsu domin taimaka wa mabuƙata, kuma kada su manta da alƙawarin da Allah ya yi musu na cewa, duk abin da suka yi na alheri, to ladansa yana nan a wurin Allah, ba zai tozarta ba, saboda Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ganin duk abin da suke aikatawa.
وَقَالُواْ لَن يَدۡخُلَ ٱلۡجَنَّةَ إِلَّا مَن كَانَ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ تِلۡكَ أَمَانِيُّهُمۡۗ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 2:111Kuma (Yahudawa da Nasara) suka ce: “Babu mai shiga Aljanna sai wanda ya kasance Bayahude ko Banasare”. Waɗannan burace-buracensu ne. Ka ce: “Ku kawo hujjarku idan kun kasance masu gaskiya”.
بَلَىٰۚ مَنۡ أَسۡلَمَ وَجۡهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ فَلَهُۥٓ أَجۡرُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 2:112E! Wanda ya miƙa fuskarsa ga Allah alhali yana mai kyautata aikinsa, to yana da ladansa a wajen Ubangijinsa, kuma babu tsoro a tare da su kuma ba za su yi baƙin ciki ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi mana bayanin irin ƙarairayi da cika baki na Yahudawa da Nasara da maganganu marasa kai, da babu hujja da dalili. Yahudawa sun riƙa cika baki suna cewa, wai in ban da Yahudu babu mai shiga Aljanna a ranar lahira; su ma Nasara ta ɓangarensu suka riƙa holoƙon cewa, su kaɗai ne ‘yan Aljanna. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haɗa su su duka ya mayar musu da martani iri ɗaya da cewa, duk waɗannan maganganu nasu burace-burace ne da ƙarairayi kawai, ba su da wata hujja da za su iya nunawa, idan kuwa ba haka ne ba, to su fito da hujjarsu su nuna idan su masu gaskiya ne. Maganar gaskiya dai ita ce, Musulmai su ne kaɗai ‘yan Aljanna, domin gidan Aljanna yana ga wanda ya miƙa kansa ga Allah shi kaɗai, ya yi aiki na ƙwarai ba tare da shirka ba, sannan ya bi shari’ar Annabi (ﷺ) sau-da-ƙafa. To wannan shi ne Musulmi, kuma yana da ladansa a wurin Allah a ranar lahira, wanda da ma shi ne gidan Aljanna. Don haka irin waɗannan mutane su ne waɗanda babu wani tsoro a tattare da su game da abin da za su tarar a lahira, kuma ba wani baƙin ciki tare da su dangane da abin da duk suka bari a nan duniya.
وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ لَيۡسَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ لَيۡسَتِ ٱلۡيَهُودُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَهُمۡ يَتۡلُونَ ٱلۡكِتَٰبَۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ مِثۡلَ قَوۡلِهِمۡۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 2:113Yahudawa suka ce: “Nasara ba a kan komai suke ba”, su ma Nasara suka ce: “Yahudawa ba a kan komai suke ba”, alhalin dukkansu suna karanta Littafi. Kamar haka ne waɗanda ba su da ilimi suka yi irin maganarsu. Kuma Allah zai yi hukunci a tsakaninsu ranar Alƙiyama a kan abin da suka kasance suna saɓani a cikinsa. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana surutan wofi na suka da Yahudawa da Nasara suke yi wa junansu, kowanne ɓangare yana nuna ɗan’uwansa a matsayin ɓatacce. Yahudawa sun kafirce wa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Attaura sun kuma ƙi yarda da gaskiyar da take wurin Nasara, su ma Nasara sun kafirce wa gaskiyar da take wurin Yahudawa, alhalin dukkansu suna karanta littattafan da ke hannunsu, waɗanda a cikinsu akwai abubuwan da suke ƙaryata iƙrarinsu. Injila ta ƙunshi gaskata Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), Attaura ma tana ɗauke da busharar bayyanar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ingancin annabcinsa, amma duk sun sa ƙafa sun shure waɗannan bayanai. Allah ya nuna irin waɗannan maganganu da suke yi, maganganu ne irin na jahilai marasa ilimi. To Allah zai yi hukunci a tsakaninsu, zai bayyana musu gaskiyar mai gaskiya, da kuma ƙaryar maƙaryaci a ranar alƙiyama, ranar da babu mai kuɓuta daga azabar Allah, sai wanda ya ba da gaskiya da duka annabawan Allah.
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن مَّنَعَ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ أَن يُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ وَسَعَىٰ فِي خَرَابِهَآۚ أُوْلَٰٓئِكَ مَا كَانَ لَهُمۡ أَن يَدۡخُلُوهَآ إِلَّا خَآئِفِينَۚ لَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Open ayah 2:114Wane ne mafi zalunci kamar wanda ya hana masallatan Allah a riƙa ambaton sunansa a cikinsu, ya yi ta ƙoƙari wajen rushe su? Waɗannan bai kamata su shige su ba sai a cikin halin tsoro. Za su gamu da wulaƙanci a duniya a lahira kuma suna da wata azaba mai girma.
وَلِلَّهِ ٱلۡمَشۡرِقُ وَٱلۡمَغۡرِبُۚ فَأَيۡنَمَا تُوَلُّواْ فَثَمَّ وَجۡهُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 2:115Gabas da yamma kuma na Allah ne. Duk inda aka fuskantar da ku to can ma alƙiblar Allah ce. Lalle Allah Mai yalwar falala ne, kuma Mai yawan sani. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wanda ya fi kowa zalunci da ta’addanci cikin masu laifi, watau shi ne wanda ya hana bayin Allah ambaton Allah da bauta masa a masallatan Allah, ya tashi tsaye wajen rusa masallatan da lalata su. To irin waɗannan azzalumai, Allah ya sanya uƙubarsu ita ce, kada a bar su su shiga masallatan sai cikin halin tsoro da fargaba, watau lokacin da Allah ya ba wa muminai iko da galaba a kansu. Ko kuma ana nufin Allah zai jefa tsoro da firgici a zuƙatansu yayin da suka zo shiga waɗannan masallatai don gudun azabar da Allah zai jefa musu, duk da haka kuma suna tare da ƙasƙanci da kunya ta nan duniya, da kuma azaba mai girma a lahira da take jiran su.
وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۖ بَل لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ كُلّٞ لَّهُۥ قَٰنِتُونَ
Open ayah 2:116Kuma suka ce: “Allah Yana da ɗa”. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Bari wannan magana! Duk abin da yake cikin sammai da ƙasa nasa ne, kuma dukkansu masu biyayya ne a gare Shi.
بَدِيعُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَإِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Open ayah 2:117Shi ne Wanda Ya ƙirƙiri halittar sammai da ƙasa; kuma idan zai zartar da wani al\'amari sai kawai Ya ce da shi: “Kasance”, sai ya kasance. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana mayar da martani ne ga masu cewa Allah yana da ɗa! Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani ta fuskoki guda shida: Fuska Ta Farko: Allah tsarkakakken Sarki ne, bai dace da a jingina masa ɗa ba, domin shi mawadaci ne da Zatinsa, kuma shi mai kamala ne; buƙatuwa zuwa ga ɗa kuma tana nuna gajiyawa ko tawaya, waɗannan siffofi ne da Allah ya tsarkaka daga gare su. Fuska Ta Biyu: Allah shi ne mamallakin sammai da ƙassai, da duk abin da suka ƙunsa, shi ne ya halicce su, kuma yake gudanar da ikonsa a cikinsu; dukkansu kuma bayinsa ne, shi kuma Ubangijinsu ne. Ɗa kuwa yana samuwa ne daga wasu abubuwa guda biyu waɗanda suka dace da juna. Watau ɗabi’a ta nuna cewa, ɗa wani ɓangare ne na mahaifinsa, to ashe ba zai zamo mahaluƙi ba ke nan ko kuma bawa ga Allah idan an ce shi wani sashe ne daga gare shi, kuma irinsa ne a kamanni. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ba shi da wani mai kama da shi, kuma babu mai tarayya da shi a cikin sifofinsa da ayyukansa da mulkinsa, don haka ya tsarkaka daga a jingina masa ɗa. Fuska Ta Uku: Gamewar mulkinsa ga ɗaukacin halitta ita ta tabbatar da wadatuwarsa ga samun ɗa. Fuska Ta Huɗu: Duk wani mahaluƙi, mai ɗa’a ne ga Allah (Mai tsarki da daukaka), mai miƙa wuya ne gare shi, har shi kansa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), mai saduda ne ya bi tsari na Mahaliccinsa a rayuwarsa, ya ƙi ko ya so, kamar yadda Allah ya bayyana a Suratul Isra’i , aya ta 44, da Suratur Ra’ad , aya ta 15. Fuska Ta Biyar: Wanda ya ƙirƙiri halittar sammai da ƙasa, ba tare da ya kwaikwaya daga wurin wani ba, duk da irin girmansu da manyan ayoyi da ke cikinsu. To yanzu wanda zai yi irin wannan gagarumin aiki, sai kuma a ce ya kasa yin wanda bai kai shi girma ba, kamar samar da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba tare da uba ba? To don me za su fitar da Annabi Isa daga cikin tsarin Ƙudurarsa, su mayar da shi abokin tarayya ga Allah, ko wani ɓangare nasa, har su kira shi ɗan Allah? Fuska Ta Shida: Allah (Mai tsarki da daukaka) yakan zartar da abin da duk ya yi nufin halittarsa ne da kalmar ‘kun’ , wato ‘kasance’, sai wannan abu ya kasance, ya samu kamar yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) yake son samar da shi. To ta wannan hanyar ne ya halicci Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Saboda haka duk wanda yake gudanar da aikinsa ta irin wannan hanyar, ba ya da buƙatar haihuwa, domin haihuwa hanya ce ta mahluƙi ajizi, Allah kuwa tsarkakakke ne daga wannan.
وَقَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ لَوۡلَا يُكَلِّمُنَا ٱللَّهُ أَوۡ تَأۡتِينَآ ءَايَةٞۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِم مِّثۡلَ قَوۡلِهِمۡۘ تَشَٰبَهَتۡ قُلُوبُهُمۡۗ قَدۡ بَيَّنَّا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يُوقِنُونَ
Open ayah 2:118Waɗanda ba su da ilimi kuma suka ce, “Me zai hana Allah Ya yi magana da mu ko kuma wata aya ta zo mana?” Kamar haka ne waɗanda suka gabace su suka faɗi irin wannan maganar tasu. Zukatansu sun yi kama da juna. Haƙiƙa mun yi bayanin ayoyi ga mutane masu sakankancewa.
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗاۖ وَلَا تُسۡـَٔلُ عَنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 2:119Lalle Mu Mun aiko ka da gaskiya, kana mai albishir kuma kana mai gargaɗi, ba kuma za a tambaye ka ba game da ‘yan wutar Jahima. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, mushrikan Larabawa, waɗanda ba su da ilimi irin na ma’abota littafi, suna ganin su suka fi cancanta Allah ya yi musu magana kai-tsaye, ba ta hanyar Annabi Muhammadu (Mai tsarki da daukaka) ba, don haka suna ganin babu buƙatar sai Allah ya aiko da wani Annabi na musamman, sai dai kawai ya yi magana da mutane kai-tsaye, ya faɗi umarninsa da haninsa. Wannan ba shakka jahilci ne wanda bai kamata a ce ma’abota littafi sun auka cikinsa ba, domin ko su sun yarda da aiko annabawa da manzanni. Hakanan kuma suka riƙa neman a zo musu da wata aya, duk da cewa, Annabi (ﷺ) ya zo da mu’ujizoji masu yawa, amma duk suka nuna ba su gamsu ba, suka ƙirƙiri wasu buƙatu suka ce sai Annabi (ﷺ) ya cika musu su sannan za su yi imani da shi. Duk kuma suna yin haka ne domin nuna taurin kansu da kangarewarsu, ba wai niyyarsu su yi imani ba, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Isra’i , aya ta 90-93. Allah (Mai tsarki da daukaka) har wa yau ya bayyana cewa, irin waɗannan buƙatu nasu na neman a kawo musu ayoyi irinsa ne al’ummomin da suka gabace su, kamar Yahudu da Nasara, suka riƙa gabatar wa da annabawansu, kamar yadda ya zo a Suratu An-Nisa’i , aya ta 159. Allah ya nuna mana cewa zukatan mushrikan Larabawa sun yi kama da zukatan Yahudu da Nasara wajen fito-na-fito da gaskiya da taurin kai da kangare wa annabawa, shi ne ya sa ayyukansu ma suka zama iri ɗaya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, ya fito da duk wasu ayoyi ko dalilai masu tabbatar da gaskiyar annabcin Annabi (ﷺ), ta yadda babu buƙatar sake wata tambaya a kai, sai dai wannan bayani da Allah yake yi, babu mai fa’idantuwa da shi sai mutane masu yaƙini a zukatansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da magana da Annabinsa (ﷺ), yana jaddada masa cewa, ya aiko shi ne da gaskiya, don haka aikowarsa gaskiya ce, abin da ya zo da shi ma gaskiya ne, kuma ya ɗora masa nauyin ya isar da saƙo na bushara ga duk wanda ya bi shi, ya isar da saƙo na gargaɗi ga duk wanda ya bijire masa cikin mutane da aljannu. Don haka babu wani laifi da za a kama shi da shi, don wasu sun ci gaba da zama cikin kafircinsu, sun ƙi yin imani da shi, bayan ya isar musu da saƙon gaskiya da aka aiko shi da shi. Waɗannan mutane ‘yan wuta ne, kuma masu dawwama ne a cikinta har abada.
وَلَن تَرۡضَىٰ عَنكَ ٱلۡيَهُودُ وَلَا ٱلنَّصَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمۡۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۗ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَ ٱلَّذِي جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ
Open ayah 2:120Yahudawa da Nasara ba za su taɓa yarda da kai ba har sai ka bi addininsu. Ka ce: “Shiriyar Allah lalle ita ce shiriya”. Idan har ka bi son zuciyarsu bayan abin da ya zo maka na gaskiya, to ba ka da wani majiɓinci ko mai taimakonka wajen Allah.
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَتۡلُونَهُۥ حَقَّ تِلَاوَتِهِۦٓ أُوْلَٰٓئِكَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 2:121Waɗanda Muka saukar musu da littafi suna karanta shi yadda ya cancanta a karanta shi, waɗannan su ne suke yin imani da shi. Kuma waɗanda suka kafirce masa to waɗannan su ne hasararru.
يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَنِّي فَضَّلۡتُكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 2:122Ya ku Banu Isra\'ila, ku tuna ni\'imar da Na yi muku, kuma lalle Ni Na fifita ku a kan talikai (na zamaninku).
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا تَنفَعُهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Open ayah 2:123Kuma ku kiyayi wani yini da wani rai ba zai isar wa da wani rai komai ba, kuma ba za a karɓi wata fansa daga gare shi ba, kuma ceto ba zai amfane shi ba, kuma su ba za a taimaka musu ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa ma’abota littafi ba za su taɓa yarda da shi ba, har sai ya bi addininsu, domin suna ganin su ne a kan gaskiya, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa irin martanin da ya kamata ya mayar musu, ya ce: “Shiriya ta gaskiya ita ce shiriyar Allah,” wadda ya zo da ita daga Ubangijinsa, watau addinin Musulunci. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da gargaɗin Annabinsa har ma da al’ummarsa, da kada su kuskura, ko da wasa su bi son zukatan ma’abota littafi, bayan Allah ya ɗaukaka su da falalar ilimi, wanda shi ne abin da aka yi wa Annabinsa (ﷺ) wahayi da shi na Alƙur’ani, mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya, yake bambancewa tsakanin ɓata da shiriya da tsakanin kafirci da imani. Kuma ya yi masa gargaɗi da cewa, idan har ya kuskura ya bi son zuciyarsu, to zai rasa mai jiɓintar lamarinsa ya janyo masa wani alheri, ko wanda zai taimaka masa ya kare shi daga wani sharri. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi duk wani ma’abocin littafi wanda ya rungumi Littafin Allah (Mai tsarki da daukaka), ya karanta shi, ya yi aiki da koyarwarsa bayan ya fahince shi, bai canza wani abu daga cikin ma’anoninsa ko ya gurɓata karantarwarsa ba, to wannan mumini ne na gaskiya, kuma imaninsa zai taimaka masa wajen ba da gaskiya da Annabi (ﷺ), domin zai ga yadda Littafinsa ya faɗi siffofin Annabi (ﷺ), kuma ya yi kira da a yi imani da shi duk sa’adda ya bayyana. To amma daga cikinsu, duk wanda ya kafirce wa Littafinsa, ta hanyar canza shi da jirkita ma’anonisa da kafirce wa Annabi (ﷺ), to masu irin waɗannan siffofi su ne hasararru duniya da lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Banu Isra’ila ni’imar da ya yi musu, wato wadda ya yi wa kakanninsu, ya fifita su a kan sauran al’ummomin zamaninsu, ya ba su sarauta, ya aiko musu da annabawa da yawa daga cikinsu. To wanda ya yi musu irin waɗannan ni’imomi, ai ya wajaba su gode masa ta hanyar shiga addininsa, da imani da Manzon da ya aiko. Daga ƙarshe Allah ya sake jan hankalinsu da su kiyayi gamuwarsu da azabar ranar lahira ta hanyar aiwatar da abin da ya wajaba a kansu, da barin abin da aka hana su, don su kare kansu daga azabar wannan yini, wanda babu wani mahaluƙi da zai iya taɓuka wa ɗan uwansa da komai, komai irin dangantakarsu, kuma komai ƙanƙantar wannan abu, kamar yadda babu wanda zai iya fansar wani a ranar daga azabar Allah, kuma babu wani kafiri da zai sami ceto a wannan ranar ko a kuɓutar da shi daga azabar Allah mai raɗaɗi.
۞وَإِذِ ٱبۡتَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ رَبُّهُۥ بِكَلِمَٰتٖ فَأَتَمَّهُنَّۖ قَالَ إِنِّي جَاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِمَامٗاۖ قَالَ وَمِن ذُرِّيَّتِيۖ قَالَ لَا يَنَالُ عَهۡدِي ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 2:124Kuma ka tuna lokacin da Ubangijin Ibrahimu Ya jarrabe shi da wasu kalmomi, sai ya cika su, sai ya ce: “Ni zan naɗa ka shugaba ga mutane”. Sai (Ibrahimu) ya ce: “Har da kuma zurriyata”; Sai (Allah) Ya ce: “Alƙawarina ba zai shafi azzalumai ba.”
وَإِذۡ جَعَلۡنَا ٱلۡبَيۡتَ مَثَابَةٗ لِّلنَّاسِ وَأَمۡنٗا وَٱتَّخِذُواْ مِن مَّقَامِ إِبۡرَٰهِـۧمَ مُصَلّٗىۖ وَعَهِدۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيۡتِيَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلۡعَٰكِفِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ
Open ayah 2:125Kuma ka tuna lokacin da Muka sanya wannan Ɗaki ya zama matattara ga mutane da kuma aminci; kuma ku mayar da Maƙamu Ibrahim wajen salla; kuma Muka yi umarni ga Ibrahim da Isma\'ila da cewa: “Ku tsarkake Ɗakina don masu ɗawafi da masu i\'itikafi da masu ruku\'u da sujjada”.
وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا بَلَدًا ءَامِنٗا وَٱرۡزُقۡ أَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ مَنۡ ءَامَنَ مِنۡهُم بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ قَالَ وَمَن كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُۥ قَلِيلٗا ثُمَّ أَضۡطَرُّهُۥٓ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلنَّارِۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 2:126Kuma ka tuna lokacin da Ibarhimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya wannan (wuri) ya zama gari mai aminci, kuma Ka arzuta mutanensa da kayan marmari, (amma) wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira daga cikinsu”. Sai (Allah) Ya ce: “Har ma wanda ya kafirta, zan jiyar da shi daɗi kaɗan, sannan in tilasa masa shiga azabar wuta, tir da wannan makoma.”
وَإِذۡ يَرۡفَعُ إِبۡرَٰهِـۧمُ ٱلۡقَوَاعِدَ مِنَ ٱلۡبَيۡتِ وَإِسۡمَٰعِيلُ رَبَّنَا تَقَبَّلۡ مِنَّآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 2:127Kuma ka tuna lokacin da Ibrahimu yake ɗaga harsashen ginin Ɗakin Ka\'aba tare da Isma\'ila, suna cewa: “Ya Ubangijinmu Ka karɓa mana; lalle Kai Mai ji ne Mai gani.”
رَبَّنَا وَٱجۡعَلۡنَا مُسۡلِمَيۡنِ لَكَ وَمِن ذُرِّيَّتِنَآ أُمَّةٗ مُّسۡلِمَةٗ لَّكَ وَأَرِنَا مَنَاسِكَنَا وَتُبۡ عَلَيۡنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 2:128“Ya Ubangijinmu, Ka sanya mu masu miƙa wuya gare Ka, kuma a cikin zurriyarmu ma (Ka samar) da wata al\'umma mai miƙa wuya gare Ka, kuma Ka nuna mana ayyaukan ibadarmu, kuma Ka karɓi tubanmu, lalle Kai Mai yawan karɓar tuba ne Mai jin ƙai.”
رَبَّنَا وَٱبۡعَثۡ فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِكَ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَيُزَكِّيهِمۡۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 2:129“Ya Ubangijinmu, Ka aiko da wani manzo daga cikinsu, da zai riƙa karanta musu ayoyinka, kuma yana koyar da su Littafi da hikima, kuma ya riƙa yi musu tarbiyya. Lalle kai Mabuwayi ne, Mai hikima.”
وَمَن يَرۡغَبُ عَن مِّلَّةِ إِبۡرَٰهِـۧمَ إِلَّا مَن سَفِهَ نَفۡسَهُۥۚ وَلَقَدِ ٱصۡطَفَيۡنَٰهُ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَإِنَّهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 2:130Babu kuma wanda zai ƙi addinin Ibrahimu sai wanda bai san ciwon kansa ba. Kuma haƙiƙa Mun zaɓe shi a duniya, kuma shi a lahira yana cikin mutanen ƙwarai.
إِذۡ قَالَ لَهُۥ رَبُّهُۥٓ أَسۡلِمۡۖ قَالَ أَسۡلَمۡتُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 2:131Ka tuna lokacin da Ubangjijinsa Ya ce masa: “Ka miƙa wuya”, sai ya ce: “Na miƙa wuya ga Ubangijin talikai.”
وَوَصَّىٰ بِهَآ إِبۡرَٰهِـۧمُ بَنِيهِ وَيَعۡقُوبُ يَٰبَنِيَّ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰ لَكُمُ ٱلدِّينَ فَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ
Open ayah 2:132Kuma Ibrahimu da Ya\'aƙubu suka yi wasiyya da wannan ga \'ya\'yansu cewa: “Ya \'ya\'yana, lalle Allah Ya zaɓa muku addini, don haka kada ku mutu face kuna Musulmi.”
أَمۡ كُنتُمۡ شُهَدَآءَ إِذۡ حَضَرَ يَعۡقُوبَ ٱلۡمَوۡتُ إِذۡ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعۡبُدُونَ مِنۢ بَعۡدِيۖ قَالُواْ نَعۡبُدُ إِلَٰهَكَ وَإِلَٰهَ ءَابَآئِكَ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ إِلَٰهٗا وَٰحِدٗا وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ
Open ayah 2:133Ko kuna nan ne lokacin da mutuwa ta zo wa Yaƙubu, lokacin da ya ce wa \'ya\'yansa: “Me za ku bauta wa a bayana?” Sai suka ce: “Za mu bauta wa abin bautarka kuma abin bautar iyayenka, Ibarhimu da Isma\'ila da Ishaƙa, abin bauta guda ɗaya, kuma mu gare Shi muke miƙa wuya.”
تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:134Waccan al\'umma ce da ta riga ta wuce; abin da ta aikata mallakarta ne, ku ma abin da kuka aikata naku ne, kuma ba za a tambaye ku ba game da abin da suka kasance suna aikatawa.” Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tuna wa Banu Isra’ila wasu daga cikin ni’imomin da ya yi musu a baya da irin yadda suka ƙalubalanci waɗannan ni’imomin ta hanyar butulci da kafirci da ƙaryata annabawa da ma kashe wasunsu, ya kuma bayyana irin cika baki da gadara da suka riƙa nunawa na cewa, su ne zaɓaɓɓu a wurin Allah, babu mai shiga Aljanna in ba su ba, da dai sauran ire-iren waɗannan maganganu nasu na soki-burutsu, sai Allah Ta’ala ya kawo wani ɓangare na tarihin Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), mahaifin Annabi Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Ishaƙa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kuma kakan Annabi Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), domin ya rushe abin da Yahudawa da Nasara da mushirikan Larabawa suke yaɗawa na alaƙarsa da gurɓataccen addinansu. Kuma ta ɓangare guda ya bayyana ƙaƙƙarfar alaƙarsa shi da ‘ya’yansa da addinin Musulunci da kuma Ɗakin Ka’aba wanda Allah ya umarce shi da ginawa don ya zama wata alama ce ta zahiri da kaɗaitar Allah da bauta, wato Tauhidi. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tuna wa Annabinsa (ﷺ) irin jarrabawar da ya yi wa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ta hanyoyi daban-daban, waɗanda suka shafi umarni da hani, da sauran hukunce-hukunce na shari’a da kuma wasu al’amura da ya jarrabe shi da su na rayuwa, kamar ƙiyayyar da mutanensa suka nuna masa, har suka yi yunƙurin ƙona shi ƙurmus da wuta da umarnin da Allah ya yi masa na ya yanka ɗansa Isma’il, ya kuma sallama wa wannan umarni, daga bisani sai Allah ya fanshe shi da wani abin yanka babba. Duk kuma ire-iren waɗannan jarrabobi da Allah ya yi masa, ya cinye su cib-cib. To daga nan sai Allah ya sanar da shi cewa, ya zaɓe shi ya zama Shugaba abin koyi ga mutane. Jin haka sai Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) da ya sanya wannan shugabancin na addini a cikin zurriyyarsa da za su zo bayansa. Sai Allah ya amsa masa da cewa, shugabanci na addini ba zai taɓa shiga hannun azzalumi ba, don haka ya janye wannan buƙata tashi. Allah kuwa ya cika wa Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wannan alƙawari, kamar yadda ya faɗa a cikin Suratul Hadid , aya ta 26. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tuna wa Annabi (ﷺ) irin ɗaukakar da ya yi wa Ɗakinsa mai alfarma na Makka, yadda ya kimsa soyayyarsa a cikin zukatan mutane, suna ta marmarin ziyarar sa babu ƙaƙƙautawa, ko sau nawa ɗayansu zai je ziyarar sa ba ya ginsar sa ko ya ƙosa da ganin sa. Bayan haka kuma ya mayar da shi wuri mai aminci ga rayukan jama’a da dukiyarsu, kai amincinsa ya kai har ga dabbobi da itatuwa, ta yadda ba a farauta a cikin haraminsa, kuma ba a cire itatuwan cikinsa, kamar yadda ya zo a hadisan Annabi (ﷺ). [Duba Bukhari #2129, da Muslim #1362]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da al’ummarsa da su riƙi wurin tsayawar Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zama wurin salla. Dalilin saukar wannan gaɓa ta ayar yana cikin Hadisin da Imamul Bukhari ya ruwaito daga Umar ɗan Khaɗɗab, yana cewa: “Na dace da (hukuncin) Ubangijina cikin abubuwa guda uku. Na ce, ina ma da a ce za mu mayar da wurin tsayuwar Annabi Ibrahim wajen salla, sai ko aka saukar da faɗar Allah: “Kuma ku mayar da Maƙamu Ibrahim wajen salla.” [Bukhari #412]. Don haka ya zamo sunnar mai yin ɗawafi, yayin da ya gama ɗawafinsa zagaye bakwai, ya je bayan Muƙamu Ibrahim ya yi salla raka’a biyu ya karanta Suratul Ikhlasi da Suratul Kafirun , kamar yadda Manzon Allah (ﷺ) ya yi. [Muslim #1218]. Wasu malaman tarihi sun fassara ma’anar Muƙamu Ibrahim da cewa, ana nufin wuraren da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tsaya lokacin aikin Hajji. Don haka a wannan ayar ana umartar Musulmi ne, mahajjata su yi koyi da shi wajen tsayuwa da ibada da addu’a a waɗannan wurare yayin aikin hajjinsu. Salla raka’a biyu bayan gama ɗawafi kuma ta shiga ciki. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa ya yi umarni mai ƙarfi ga Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da su tsabtace ɗakinsa daga shirka da kafirci da gumaka da ƙazanta, domin masu ɗawafi da masu zama cikinsa domin ibada, da masallata a cikinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta mana addu’a da ƙoƙon-barar da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya gabatar wa Ubangijinsa, yana neman da ya arzuta mazauna garin Makka da zaman lafiya na dindindin, sannan ya hore wa muminai daga cikinsu abin da za su ci. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa masa cewa, arziki a duniya Allah yana bayar da shi ga kowa ne, mumini da kafiri, bai taƙaita a kan muminai su kaɗai ba. To sai dai abin da Allah zai ba wa kafiri na arziki a nan duniya, komai yawansa ɗan kaɗan ne idan aka kwatanta shi da ni’imar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanadar wa masu imani a ranar lahira. Sannan shi kuma wanda ya kafirta, Allah zai jefa shi wutar Jahannama, wadda makoma ce mai munin gaske. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba wa Annabinsa (ﷺ) labarin lokacin da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka sanya harsashin ginin Ɗakin Ka’aba, don su ɗaga ta ta zama cikakken ɗaki, sanda suke ɗaga hannayensu suna addu’a Allah ya karɓa musu wannan aiki nasu, kuma Allah yana jin addu’arsu, kuma yana sane da aikinsu da kyakkyawar niyyarsu. Hakanan suka roƙe shi da ya sanya su su zama har ko da yaushe masu miƙa wuya ne da ƙasƙantar da kai gare shi da sallama wa umarninsa. Kuma suka roƙe shi da ya samar da wata al’umma mai miƙa wuya ga umarninsa a cikin zurriyyarsu. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karɓa duk waɗannan addu’o’i nasu gaba ɗaya. Hakanan cikin addu’o’insu sun roƙe shi ya bayyana musu wuraren ibadunsu, musamman ibadar Hajji, kuma ya datar da su ga tuba, sannan ya karɓi tuban nasu, domin shi ne mai karɓar tuba, mai rahama ga wanda ya so daga cikin bayinsa. Hakanan suka roƙe shi da ya aiko da wani Manzo daga cikin zurriyarsu Larabawa, wanda zai riƙa karanta musu Littafin Allah, yana koyar da su ilimin Alƙur’ani da Sunna, kuma yana yi musu tarbiyya ta zuci da ta halaye. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya karɓi wannan addu’a tasu, ya aiko da Annabi Muhammad (ﷺ) daga cikin ƙabilar Ƙuraishawa, gidan Banu Hashim, masu dangantaka da Annabi Isma’i (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ɗan Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Don haka ne Annabi (ﷺ) yake cewa: “Ni addu’ar Babana ne Ibrahim.” [Ahmad #2261]. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama magana a kan Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ɗansa Isma’ila, da yadda suka gina Ɗakin Allah, Ka’aba da umarnin Allah (Mai tsarki da daukaka), sai ya bayyana cewa, babu wanda zai ƙyamaci kasancewa ɗaya daga cikin mabiya addinin da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo da shi na kaɗaita Allah da bauta masa sai mutumin da yake wawa, wanda bai san ciwon kansa ba, domin Allah ya zaɓi Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya ba shi annabci da manzanci da shugabanci na addini, sannan kuma a lahira yana cikin ayarin mutanen kirki, masu samun babban rabo. Domin bayan Allah ya zaɓe shi a nan duniya, to ya umarce shi da ya miƙa wuya, ya sallama wa Ubangijinsa komai, kuma nan take ya amsa, ya miƙa wuyansa ga Ubangijin talikai, ya tsarkake addininsa gare shi shi kaɗai, ba tare da haɗa shi da komai ba. Haka kuma Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wasiyya da wannan umarni na Allah ga ‘ya’yansa cewa, su riƙi wannan addini, kada su yi wasa da shi har mutuwarsu ta zo musu suna kai, domin duk wanda ya rayu a kan abu, to zai mutu ne a kansa. Hakanan shi ma jikansa Yakubu ya yi wasiyya irin wannan ga ‘ya’yansa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya juyar da akalar tambaya zuwa ga Yahudawa masu ƙaryata Annabi Muhammadu (ﷺ) cewa, shin sun halarci lokacin da Annabi Yaƙubu kakansu mutuwa ta zo masa, ya tara ‘ya’yansa yana tambayar su, me za su bauta wa bayan mutuwarsa? Sai suka amsa masa da cewa, za su bauta wa abin bautarsa, kuma abin bautar iyayensa, waɗanda suka haɗa da kakansa Annabi Ibrahim, da baffansa Annabi Isma’il, da kuma babansa Annabi Ishaƙa. Dukkaninsu abin bautarsu ɗaya ne, wanda ya cancanci a bauta masa shi kaɗai ba tare da an haɗa shi da komai ba, shi ne Allah. Suka shelanta masa cewa, duk gaba ɗayansu sun miƙa wuya ne gare shi da ƙasƙantar da kai wajen bauta masa. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe wannan batu da kiran Yahudawa da Nasara cewa, su manta da maganar alfahari da iyayensu da kakanninsu. Kasancewarsu su zurriyarsu ne wannan kawai ba zai amfane su da komai ba a wurin Allah, domin su waɗancan al’umma ce da ta riga ta gabata, sakamakon ayyukansu su kaɗai zai shafa. Don haka su ma na zamanin Annabi (ﷺ) sai su tashi su nemi na kansu; abin da duk suka aikata a kansa ne za a yi musu tambayoyi da hisabi a ranar alƙiyama, ba za a tambaye su ayyukan iyayensu da kakanninsu ba.
وَقَالُواْ كُونُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰ تَهۡتَدُواْۗ قُلۡ بَلۡ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِـۧمَ حَنِيفٗاۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 2:135Suka ce: “Ku zama Yahudawa ko Nasara za ku shiriya”. Ka ce: “A\'a! Za mu bi addinin Ibrahimu ne wanda yake miƙe totar, kuma bai zamo daga cikin masu shirka ba.”
قُولُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَمَآ أُوتِيَ ٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ
Open ayah 2:136Ku ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana, da abin da aka saukar wa Ibrahimu da Isma\'ila da Ishaƙa da Yaƙubu da jikoki da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba annabawa duka daga Ubangijinsu, kuma ba ma nuna bambanci tsakanin wani daga cikinsu, kuma mu gare Shi muke miƙa wuya.”
فَإِنۡ ءَامَنُواْ بِمِثۡلِ مَآ ءَامَنتُم بِهِۦ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا هُمۡ فِي شِقَاقٖۖ فَسَيَكۡفِيكَهُمُ ٱللَّهُۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 2:137Don haka idan sun yi imani da irin abin da kuka yi imani da shi, to haƙiƙa sun shiriya, idan kuwa suka juya da baya, to haƙiƙa su suna cikin saɓani. To lalle Allah zai isar maka da su, kuma Shi Mai ji ne, Mai gani.
صِبۡغَةَ ٱللَّهِ وَمَنۡ أَحۡسَنُ مِنَ ٱللَّهِ صِبۡغَةٗۖ وَنَحۡنُ لَهُۥ عَٰبِدُونَ
Open ayah 2:138Rinin Allah, wane ne kuwa ya fi Allah kyan rini? Kuma mu masu bauta ne a gare Shi.
قُلۡ أَتُحَآجُّونَنَا فِي ٱللَّهِ وَهُوَ رَبُّنَا وَرَبُّكُمۡ وَلَنَآ أَعۡمَٰلُنَا وَلَكُمۡ أَعۡمَٰلُكُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُخۡلِصُونَ
Open ayah 2:139Ka ce, “Shin za ku yi jayayya da mu ne game da sha\'anin Allah, alhalin Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku? Kuma ayyukanmu namu ne, ayyukanku kuma naku ne, kuma mu masu tsarkake ayyuka ne gare Shi (Allah).
أَمۡ تَقُولُونَ إِنَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطَ كَانُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ قُلۡ ءَأَنتُمۡ أَعۡلَمُ أَمِ ٱللَّهُۗ وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَٰدَةً عِندَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:140Ko kuma kuna cewa ne, “Lalle Ibrahimu da Isma\'ila da Ishaƙa da Yaƙubu da jikoki sun kasance Yahudawa ne ko Nasara?” Ka ce: “Ku ne kuka fi sani ko kuma Allah?” Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya ɓoye shaidar da take wajensa daga Allah, kuma Allah ba rafkananne ne ba game da abin da suke aikatawa.
تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:141Waccan al\'umma ce da ta riga ta wuce, abin da ta aikata mallakarta ne, ku ma abin da kuka aikata naku ne, kuma ba za a tambaye ku game da abin da suka kasance suna aikatawa ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi mana bayanin ruɗuwa irin ta Yahudawa da Nasara ne game da wasu maganganunsu marasa kan gado da hujja. Wai kiran Annabi (ﷺ) da Musulmai suke yi cewa, su bar addininsu su zo su rungumi nasu shi ne shiriya. Yahudawa suka yi irin wannan kira zuwa ga addinin Yahudawa, Nasara ma suka yi irinsa zuwa ga Kiristanci. Sai Allah ya ce da Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, babu shiriya a cikin addininsu sam-sam; shiriya tana cikin addinin da Annabi Ibrahim ya zo da shi ne, wanda kuwa a cikinsa babu haɗa Allah da wani, sai kaɗaita Allah kawai wajen bauta. Don haka Annabi Ibrahim ba Bayahude ne ba, ba kuma Banasare ba ne, sannan ba mushiriki ba ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa muminai abin da kawai za su yi imani da shi shi ne, Kaɗaitakar Ubangijinsu Allah da kuma imani da duk abin da Allah ya aiko Annabinsa Muhammad (ﷺ) da shi. Haka kuma su yi imani da duk annabawan da ya aiko da littattafan da ya ba su, waɗanda ya bayyana musu sunayensu da ma waɗanda bai ambata musu komai na labarinsu ba. Su ba da gaskiya da su a dunƙule gaba ɗaya, ba tare da rarrabewa a tsakaninsu ba; saboda kafirce wa annabin Allah ɗaya daidai yake da kafirce wa dukkansu, kamar yadda ya ambata a Suratun Nisa’i , aya ta 150-151. Annabawan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambata a wannan ayar sun haɗa da: 1. Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), uban annabawa, wanda Allah ya saukar masa da wasu littattafai da ya ambata a Suratun Najmi , aya ta 36-37, da kuma Suratul A’ala , aya ta 19. 2. Annabi Isma’il, Allah bai sanar da mu komai dangane da littattafansa ba. 3. Annabi Ishaƙ da Annabi Ya’aƙuba. Su ma Allah bai sanar da mu abin da ya saukar musu ba. 4. Jikoki, su ne annabawan da suke cikin zurriyar Annabi Ya’aƙuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin Yahudu da Nasara cewa, idan su ma suka yi imani da irin abin da muminai suka yi imani da shi, to sun zama shiryayyu, idan kuwa har suka bijire, to ya kamata su muminai su fahinci cewa, waɗannan mutane jayayya kawai suke nema da adawa da su, ba gaskiya ba. Allah ya nuna wa Manzonsa (ﷺ) cewa, kada ya damu da adawarsu da makirce-makircensu, Allah zai tsaya masa, ya ba shi kariya, ya taimake shi a kansu, domin yana jin duk abin da suke faɗa a kansa, kuma yana sane da ƙulle-ƙullensu da suke shiryawa a ɓoye. Don haka sai Allah ya umarce su da lalle su lazimci addinin Allah wanda shi ne Musulunci, kuma da shi ne Allah ya rina su, ya fito da su cikin wata kyakkyawar kama mai ban sha’awa, kuma babu wanda ya fi Allah kyan rini. Don haka su zama masu ƙasƙantar da kai a gare shi masu bauta masa shi kaɗai. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya kira Yahudawa da Nasara waɗanda suke jayayya da muminai ba tare da gaskiya ba, ya faɗa musu cewa, yanzu ta yaya za su riƙa jayayya da muminai a kan sha’anin Tauhidi da miƙa wuya ga umarnin Allah, ko kuma a kan abin da Allah ya keɓanci Annabi (ﷺ) da shi tare da al’ummarsa, na fifita shi a kan sauran annabawa da fifita al’ummarsa a kan sauran al’ummomi? Da me suka dogara da shi na ganin su ne suka fi cancantar wannan matsayi, tare da cewa su duka Allah ne Ubangijinsu, kuma shi ne mai yin yadda ya ga dama. Kuma me zai sa su ya ba su, su kuma Musulmi ya hana su? Idan har shi ne yake ganin dama ya ba wa wanda yake so, to babu dalilin da zai sa su ce ba zai yi wa muminai baiwa ba, don su ma shi ne Ubangijinsu. Idan kuma ayyukansu ne suka sa Allah ya ba su abin da suke riyawa, to ai su ma muminai suna da nasu ayyukan waɗanda suka fi nasu kyau, domin su muminai suna tsarkake shi da bauta, saɓanin su da suke yin shirka. Idan kuwa haka ne, to su muminai su suka fi su cancantar wannan baiwar tasa. Daga nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ƙaryar da Yahudawa da Nasara suke yi na cewa, Annabi Ibrahim da ‘ya’yansa sun kasance a kan addinin Yahudanci ko Kiristanci, tare da cewa, waɗannan addinai ne da suka zo bayan shuɗewar waɗannan annabawa. To ta yaya kuma za a danganta su da waɗannan addinai biyu? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa (ﷺ) ya tambaye su: Shin su ne suka fi Allah sanin halin da manzannin suka kasance a kai? Babu shakka amsar ɗaya ce, Allah ne mafi sani. To idan haka ne, me ya sa suke ɓoye wannan shaidar, ba za su bayar da ita ba? Tabbas babu azzalumi kamar wanda zai ɓoye shaidar wajensa wadda daga Allah take. To irin waɗannan mutane su kwana da sanin cewa, Allah yana sane da duk abin da suke aikatawa, kuma zai yi musu sakayya a kai. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma a nan ya sake jaddada musu waccan magana da ya yi musu a baya cewa, su daina alfahari da iyayensu da kakanninsu da ayyukan da suka yi, wannan ba zai amfane su da komai ba, domin sakamakon waɗannan ayyuka za su taƙaita ne a kan masu su. Don haka su ma za a yi musu hisabi ne da sakamako a kan ayyukansu na alheri ko na sharri, ba za a tambaye su komai game da ayyukan iyayensu da kakanninsu ba.
۞سَيَقُولُ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَ ٱلنَّاسِ مَا وَلَّىٰهُمۡ عَن قِبۡلَتِهِمُ ٱلَّتِي كَانُواْ عَلَيۡهَاۚ قُل لِّلَّهِ ٱلۡمَشۡرِقُ وَٱلۡمَغۡرِبُۚ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 2:142Da sannu wawayen mutane za su ce: “Mene ne ya sa su juyawa su bar alƙibilar da a da suke a kanta?” Ka ce: “Gabas da yamma na Allah ne, Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.”
وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَٰكُمۡ أُمَّةٗ وَسَطٗا لِّتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِ وَيَكُونَ ٱلرَّسُولُ عَلَيۡكُمۡ شَهِيدٗاۗ وَمَا جَعَلۡنَا ٱلۡقِبۡلَةَ ٱلَّتِي كُنتَ عَلَيۡهَآ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يَتَّبِعُ ٱلرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِۚ وَإِن كَانَتۡ لَكَبِيرَةً إِلَّا عَلَى ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِيعَ إِيمَٰنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 2:143Kamar haka ne Muka sanya ku al\'umma tsaka-tsaki (zaɓaɓɓu) don ku zamo masu shaida ga mutane, kuma Manzo ya zamo mai shaida a gare ku. Kuma ba Mu sanya alƙiblar da ka kasance a kanta ba sai don Mu bayyana wanda yake biyayya ga Manzo da wanda zai ja da baya (ya bijire). Kuma lalle wannan babban lamari ne sai dai ga waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma Allah ba zai taɓa tozarta imaninku ba. Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai ga mutane.
قَدۡ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجۡهِكَ فِي ٱلسَّمَآءِۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبۡلَةٗ تَرۡضَىٰهَاۚ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَيَعۡلَمُونَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:144Haƙiƙa Mun ga jujjuyawar fuskarka zuwa sama, to lalle za Mu fuskantar da kai zuwa ga alƙibilar da za ka yarda da ita. Don haka ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma; ku ma (Musulmi) a duk inda kuke to ku juyar da fuskokinku wajajensa. Lalle kuma waɗanda aka ba su Littafi suna sane da cewa, lalle shi (wannan canji) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da suke aikatawa.
وَلَئِنۡ أَتَيۡتَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ بِكُلِّ ءَايَةٖ مَّا تَبِعُواْ قِبۡلَتَكَۚ وَمَآ أَنتَ بِتَابِعٖ قِبۡلَتَهُمۡۚ وَمَا بَعۡضُهُم بِتَابِعٖ قِبۡلَةَ بَعۡضٖۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ إِنَّكَ إِذٗا لَّمِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 2:145Lalle kuma da za ka kawo wa waɗanda aka ba su Littafi kowace irin hujja ba za su bi alƙibilarka ba; kuma kai ma ba mai bin alƙibilarsu ba ne; kuma sashinsu bai zama mai bin alƙibilar sashi ba. Kuma haƙiƙa idan har ka bi soye-soyen zukatansu bayan abin da ya zo maka na gaskiya, to lalle idan ka yi haka tabbas kana cikin azzalumai.
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمۡۖ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنۡهُمۡ لَيَكۡتُمُونَ ٱلۡحَقَّ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:146Waɗanda Muka ba su Littafi suna sane da shi (Manzon Allah) kamar yadda suke sane da \'ya\'yansu; kuma lalle wani ɓangare daga cikinsu tabbas suna ɓoye gaskiya alhalin suna sane.
ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ
Open ayah 2:147Gaskiya kam daga Ubangijinka take, don haka lalle kada ka zama daga cikin masu shakka.
وَلِكُلّٖ وِجۡهَةٌ هُوَ مُوَلِّيهَاۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ أَيۡنَ مَا تَكُونُواْ يَأۡتِ بِكُمُ ٱللَّهُ جَمِيعًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 2:148Kuma kowane ɓangare yana da inda ya sa gaba, don haka sai ku yi gaggawar cim ma alheri. A duk inda kuke Allah zai zo da ku gaba ɗaya. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai.
وَمِنۡ حَيۡثُ خَرَجۡتَ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۖ وَإِنَّهُۥ لَلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 2:149Ko ta ina ka fito, to ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma; kuma lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama gafalalle game da abin da kuke aikatawa ba.
وَمِنۡ حَيۡثُ خَرَجۡتَ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَيۡكُمۡ حُجَّةٌ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِي وَلِأُتِمَّ نِعۡمَتِي عَلَيۡكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Open ayah 2:150Kuma duk inda ka fita, to ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma. Ku ma duk inda kuke to ku juyar da fuskokinku wajajensa, don kada ya zama mutane suna da wata hujja a kanku, sai dai waɗanda suka yi zalunci daga cikinsu, don haka kada ku ji tsoron su, ku ji tsorona, kuma domin in cika muku ni\'imata, don ku shiriya. A waɗannan ayoyi, Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin batun canza alƙiblar Musulmi daga kallon Baitul Maƙdis zuwa fuskantar Ɗakin Ka’aba. Annabi (ﷺ) shi da sauran Musulmai sun kasance, yayin zamansu a Makka, suna fuskantar Baitul Maƙdis ne lokutan ibadarsu. Bayan sun yi hijira zuwa Madina da kimanin wata goma sha shida zuwa sha bakwai ma Baitul Maƙdis suke fuskanta. A daidai wannan lokaci kuma Annabi (ﷺ) yana ta addu’a, yana roƙon Allah, Allah ya canza masa alƙibla ta koma ana fuskantar Ka’aba. To sai ko Allah ya karɓi addu’arsa, ya umarce shi, tare da sauran Musulmai, da su fuskanci Ka’aba a lokutan sallolinsu. Allah ya riga ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, wawayen mutane cikin Yahudawa da Nasara, har ma da mushirikan Makka, za su sami wani abin magana yayin da za su ga Annabi (ﷺ) da sahabbansa sun canza alƙiblar sallarsu. Da farko mushirikai ne suka riƙa sukar Annabi (ﷺ) da cewa yana da’awar bin addinin Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), amma ba ya fuskantar Ka’aba, ɗakin da shi Annabi Ibrahim ne ya gina shi. Su kuma Yahudawa suka riƙa cika baki suna cewa, fuskantar alƙiblarsu da Annabi (ﷺ) yake yi, dalili ne mai nuna cewa addininsu shi ne gaskiya, don haka ba su da buƙatar shiga Musulunci. <b> </b>Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya canza wa Annabi (ﷺ) da sahabbansa alƙibla, sai kuma waɗannan mutane suka dawo suna sukan don me za su canza alƙiblarsu? To shi ne a nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗa musu cewa, gabas da yamma da abin da yake tsakaninsu duka mallakar Allah ne, shi ne yake yin yadda yake so da kayansa, don haka yana da damar ya ba da umarnin fuskantar ko’ina. Ai bin umarninsa shi ne muhimmi, ba inda za a fuskanta ba, don haka yana shiryar da wanda ya ga dama zuwa tafarkinsa madaidaici, kuma ya yi masa ɗa’a cikin dukkan umarninsa da haninsa. A dalilin dacen da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa wannan al’umma ta Annabi (ﷺ) ne, ya zaɓo su, ya mayar da su mafifita al’ummomi kuma adalai, domin su bayar da shaida ga annabawa da cewa, sun isar wa da al’ummominsu saƙon da Allah ya aiko su da shi. Sannan shi kansa Manzon Allah (ﷺ) ya zama shaida ga al’ummarsa a kan isar da saƙon Allah zuwa gare su, da kuma gaskiyar shaidarsu ga Annabawan Allah. Sannan Allah ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) hikimar canza musu alƙibla, ita ce don tantance wanda zai yi wa Annabi (ﷺ) biyayya da wanda zai yi ridda ya bar addininsa. Ba shakka lamarin wannan canji da aka samu babba ne; ba kowa ne zai iya rungumar sa da miƙa wuya ya sallama wa hukuncin Allah ba, sai wanda Allah ya so shi da shiriya. Yayin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Annabi (ﷺ) umarninsa na canza alƙibla zuwa Ka’aba, to wani mutum ya yi salla tare da Annabi (ﷺ), sannan ya fita sai ya wuce wasu mutanen Madina suna salla, amma suna fuskantar Baitul Maƙdis, sai ya faɗa musu sabon umarni da ya sauka, nan take kuwa suka juya suka fuskanci Ka’ana. [Bukhari #399 da Muslim #525]. Bayan saukar wannan umarni, sai wasu sahabbai suka riƙa tunanin makomar sallar ‘yan’uwansu da suka mutu suna fuskantar Baitul Maƙdis, shin ko Allah zai karɓi waɗannan salloli, ko kuma sun rushe? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwantar musu da hankali cewa, ba wanda zai tozarta wa ladan sallarsa da ya yi lokacin da ya fuskanci Baitul Maƙdis a baya, domin Allah mai girman rahama ne ga mutane. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sanar da Annabinsa (ﷺ) cewa, ya ga yadda yake ta ɗaga kansa sama yana addu’ar Allah ya canza masa alƙiblar, tare da sa ran cewa, a ko da wane lokacin Mala’ika zai sauko don sanar da shi biyan buƙatarsa, sannan Allah ya yi masa alƙawarin cewa, zai canza masa da alƙiblar da yake so. To shi ne daga bisani Allah ya umarce shi da ya fuskanci Ka’aba a sallarsa; su ma Musulmi a duk inda suke su fuskanci nahiyar wannan ɗakin. Yahudawa da Nasara ma sun karanta a cikin littattafansu cewa, wannan Annabin da zai zo zai riƙa fuskantar Ka’aba yayin salla, kuma sun san wannan gaskiya ce daga Ubangijinsu, Allah kuma yana sane da mutanen da suka san gaskiya, amma suka take ta, har ma suka riƙa sukan ta suna sane. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara sanar da Annabinsa (ﷺ) taurin kan Yahudawa da Nasara da yadda suka ƙanƙame wa ƙarya, suka ƙi barin ta. Kuma kowace irin hujja aka zo musu da ita, ba za su saki ƙaryar ba su kama gaskiya, domin ba sun ƙi bin ta ne domin sun jahilce ta ba, a’a, sun san gaskiya, sun karanta a littattafansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce shi ma Manzon Allah (ﷺ) ba mai bin tasu alƙiblar ba ne, kuma su kansu ma’abota littafi ba sa bin alƙiblar juna, Bayahude ba ya bin ta Banasare, shi ma Banasare ba ya bin ta Bayahude. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi Annabinsa (ﷺ) da kada ya bi soye-soyen zukatan ma’abota littafi, domin idan har ya aikata hakan, bayan ilimi da ya zo masa daga Allah, to zai tsinci kansa a cikin azzalumai. Da ma kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkake Annabinsa daga aikata wani abu irin wannan. Ko da yake Allah yana yin irin wannan jan kunne ne da sunan Annabinsa (ﷺ), amma yana nufin al’ummarsa, domin su fahinci girman lamarin, su kiyaye. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Annabinsa (ﷺ) cewa, Yahudu da Nasara sun san haƙiƙanin gaskiyar annabcinsa da gaskiyar abin da yake faɗa musu na maganar Allah, ciki har da batun canza alƙibla. Domin sun karanta siffofin Annabi (ﷺ) sarai a littattafansu da Allah ya saukar, kuma sun gane shi fiye da yadda suke gane ‘ya’yan cikinsu, amma saboda butulci, wasu daga cikinsu sai su riƙa ɓoye gaskiya alhalin sun san ta. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Annabi (ﷺ) tsantsar gaskiyar da ya zo da ita daga wajen Ubangijinsa, ita ta hana wani kokwanto ya shiga zuciyarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, kowaɗanne masu addini suna da inda suke fuskanta lokacin addininsu, ko dai da umarnin Allah suke yi ko kuma su ne suka ƙirƙirara wa kansu hakan ta hanyar bidi’a. Saboda haka sai ya umarci muminai da su riƙa yin takara da juna wajen aikin alheri, ya ƙarfafe su ta hanyar shaida musu cewa, duk inda suke mutuwa za ta riske su, kuma wajensa ne kaɗai makomarsu take gaba ɗaya ranar gobe ƙiyama, domin shi Allah babu abin da yake gagarar sa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Annabinsa (ﷺ) da ya mayar da Ka’aba alƙiblarsa a duk inda yake, domin wannan ita ce gaskiyar da babu sofanen shakka a cikinta, kuma Allah ba mai rafkana ba ne game da aikin bayinsa, yana sane da aikin kowa, kuma zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa. Har wa yau Allah ya sake nanata wa Annabinsa (ﷺ) umarnin ya fuskanci Ka’aba yayin sallarsa a duk inda yake, su ma muminai duk inda suke su fuskanci Ka’aba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo musu wannan canji ne don ya rushe hujjar Yahudawa da suke kafa wa Annabi (ﷺ) da Musulmai cewa, su daina sukan addininsu na Yahudanci, don ga shi su ma shi suke kwaikwaya, suna kallon alƙiblarsu idan suna ibada, kuma wai tun da har Musulmai sun yarda da alƙiblarsu, wannan ya nuna su ne a kan gaskiya, dole ne su zo su bi addininsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rushe wannan hujjar tasu daga tushenta. To yanzu babu wata hujja da ta rage, sai wata rarraunar hujja ta mushirikai masu cewa, tun da Annabi da sahabbai sun dawo suna fuskantar alƙiblarsu, to ya zama dole su zo su bi addininsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da kada su yi shayin waɗannan azzalumai, ko su ji tsoron rarraunar hujjarsu, su dai su ji tsoron sa shi kaɗai, domin shi ne wanda ya cancanta a ji tsoro. Daga nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara bayyana wata hikima ta samar da wannan canji na alƙibla, watau ya tabbatar wa muminai cewa, ya cika musu shari’o’in addininsu da kuma fatan su miƙa wuya ga umarnin Allah (Mai tsarki da daukaka) don su sami shiriyarsa.
كَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِيكُمۡ رَسُولٗا مِّنكُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِنَا وَيُزَكِّيكُمۡ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَيُعَلِّمُكُم مَّا لَمۡ تَكُونُواْ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:151Kamar yadda Muka aiko muku da wani manzo daga cikinku, yana karanta muku ayoyinmu, kuma yana tsarkake ku, kuma yana koyar da ku Littafi da Hikima, kuma yana koyar da ku abin da a da can ba ku sani ba.
فَٱذۡكُرُونِيٓ أَذۡكُرۡكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لِي وَلَا تَكۡفُرُونِ
Open ayah 2:152Don haka ku ambace Ni, Ni ma zan ambace ku, kuma ku gode Mini, kada kuma ku kafirce Mini.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱلصَّبۡرِ وَٱلصَّلَوٰةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 2:153Ya ku waɗanda suka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haƙuri da salla. Lalle Allah Yana tare da masu haƙuri.
وَلَا تَقُولُواْ لِمَن يُقۡتَلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتُۢۚ بَلۡ أَحۡيَآءٞ وَلَٰكِن لَّا تَشۡعُرُونَ
Open ayah 2:154Kada kuma ku ce wa waɗanda ake kashewa a kan hanyar Allah su matattu ne. A\'a, rayayyu ne, sai dai ku ne ba ku sani ba.
وَلَنَبۡلُوَنَّكُم بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلۡخَوۡفِ وَٱلۡجُوعِ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَنفُسِ وَٱلثَّمَرَٰتِۗ وَبَشِّرِ ٱلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 2:155Kuma lalle za Mu jarrabe ku da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiya da ta rayuka da ta \'ya\'yan itatuwa. Don haka ka yi albirshir ga masu haƙuri.
ٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةٞ قَالُوٓاْ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيۡهِ رَٰجِعُونَ
Open ayah 2:156(Su ne) waɗanda idan wata musiba ta same su sai su ce: “Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gare Shi muke komawa.”
أُوْلَٰٓئِكَ عَلَيۡهِمۡ صَلَوَٰتٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَرَحۡمَةٞۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُهۡتَدُونَ
Open ayah 2:157Waɗannan suna da yabo daga Ubangijinsu da rahma, kuma waɗannan su ne shiryayyu. Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci cewar, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ya canza wa muminai alƙiblarsu zuwa Ka’aba shi ne don ya cika musu ni’imarsa ta hanyar yi musu bayanin shari’un Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). To kamar irin haka ne ya yi musu wata ni’imar ta aiko da Annabi (ﷺ) a cikinsu, wanda sun san shi sarai, sun san nasabarsa da halayensa na ƙwarai, kuma ya aiko shi yana magana da harshensu na Larabci, yana karantar da su Alƙur’ani, yana yi musu kyakkyawar tarbiyya, ta hanyar koyar da su halaye na ƙwarai da hana su aikata laifuka da saɓon Allah. Ya karantar da su ma’anonin Alƙur’ani, tare da yaɗa sunnarsa a tsakaninsu, yana sanar da su abubuwa da yawa, waɗanda a da ba su san su ba, kamar labarun al’ummomin da suka gabata, da manzanninsu, da duk wani abu na ilimi wanda hankali kaɗai ba zai kai gare shi ba, sai ta hanyar wahayi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da ambaton sa, ambato na zuciya da na harshe da na gaɓoɓi, idan sun yi hakan, shi ma zai ambace su. Annabi (ﷺ) a wani Hadisi ƙudusi ya ce, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: “Ni ina nan a duk inda zaton bawana yake gare ni, ni ina tare da shi; idan ya ambace ni a ransa, ni ma zan ambace shi a raina; idan ya ambace ni a cikin wani taro, ni ma zan ambace shi a cikin taron da ya fi nasa alheri.” [Bukhari #7405 da Muslim #2675]. Hakanan Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Babu wasu mutanen da za su taru a wani ɗaki daga ɗakunan Allah, suna karanta littafin Allah, suna darasin sa a tsakaninsu, face sai nutsuwa ta sauka a kansu, rahama ta lulluɓe su, mala’iku sun zagaye su, kuma Allah ya ambace su a wajen waɗanda suke tare da shi.” [Muslim #2699]. Kamar yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su gode wa ni’imomin da ya yi musu masu yawa, kada su yi butulci. Kasancewar bawa ba ya rabuwa da ɗaya daga cikin halaye guda biyu, ko dai yana cikin ni’ima, to sai ya yi wa Allah godiya, ko kuma yana cikin musiba, to sai ya yi haƙuri, don haka sai Allah ya kira muminai, ya umarce su da yin haƙuri da tsayar da salla. Domin haƙuri da tsayar da salla, suna taimaka wa bawa wajen fuskantar duk wasu matsaloli na rayuwar duniya, domin wanda duk ya siffantu da su, to yana tare da Allah, cikin taimakonsa da agajinsa. Sannan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai su kira ‘yan’uwansu da aka kashe wajen ɗaukaka kalmar Allah da sunan ‘matattu’; a wurin Allah (Mai tsarki da daukaka) su ba matattu ba ne, a’a, rayayyu ne, suna can cikin jin daɗi na Aljanna, duk da cewa mutane ba su fahinci haka ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa bayinsa muminai cewa, zai jarrabe su da ɗan wani abu kaɗan na tsoro da zai jefa a cikin zukatansu ko yunwa da za ta kama su ko na asarar dukiyoyi da rayuka ko na ƙarancin abinci, to sai Allah ya umarci Annabinsa (ﷺ) da ya yi wa masu haƙuri albishir. Su ne waɗanda idan wani bala’i ya same su, sai su ce: “Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gare shi muke komawa.” Wato su bayin Allah ne masu miƙa wuya da sallamawa gare shi, kuma bayan mutuwarsu su tabbatar da wurinsa za su koma, inda zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa. To waɗannan masu haƙuri suna da yabo da martaba sha’aninsu daga Allah, kuma rahamar Allah Ubangijinsu za ta lulluɓe su ta ko’ina, kuma su ne waɗanda Allah ya yi musu gyaɗar dogo a nan duniya, suka dace da shiriyar Allah, suka bi ta. An karɓo daga Ummu Salama (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Na ji Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani Musulmi da wata musiba za ta same shi, sai ya faɗi abin da Allah ya umarce shi, ya ce: ‘Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu zuwa gare shi muke komawa, Allah ka ba ni lada a kan musibar nan tawa, kuma ka musanya min ita da mafi alheri.’ face sai Allah ya musanya masa da wadda ta fi ta alheri.” [Muslim #918].
۞إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلۡمَرۡوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِۖ فَمَنۡ حَجَّ ٱلۡبَيۡتَ أَوِ ٱعۡتَمَرَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِ أَن يَطَّوَّفَ بِهِمَاۚ وَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَإِنَّ ٱللَّهَ شَاكِرٌ عَلِيمٌ
Open ayah 2:158Lalle dutsen Safa da na Marwa suna cikin alamomin bautar Allah, don haka wanda ya je Hajji ga Ɗakin Allah ko ya je Umara, to babu wani laifi a gare shi ya yi ɗawafi tsakaninsu. Kuma wanda ya yi biyayya ta hanyar aikata alheri, to lalle Allah Mai godiya ne kuma Masani. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana a kan sa’ayi tsakanin Safa da Marwa. Safa da Marwa wasu duwatsu ne guda biyu a cikin garin Makka. Lokacin da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ajiye kuyangarsa Hajara a kwazazzabon Makka, ita da jaririnta Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), yayin da ruwansu na sha ya ƙare, Hajara ta ga ɗanta Isma’il yana ta kukan ƙishirwa, ga shi kuma ba ta da abin da za ta ba shi, sai ta tashi ta je ta hau kan dutsen Safa, ko za ta tsinkayo wani wanda zai taimake ta da ruwan sha, ba ta ga kowa ba. Ta gangaro ta nufi Marwa, nan ma ta hau, ba ta tsinkayo kowa ba. Ta yi haka har sau bakwai. Wannan shi ne dalilin yin sa’ayi guda bakwai a tsakaninsu yayin gudanar da aikin haji ko umara. A lokacin jahiliyya bayan Abdulmuttalib, kakan Annabi (ﷺ), ya sake haƙan rijiyar Zamzam bayan ƙafewarta, sai ya ɗauke wasu gumaka guda biyu waɗanda aka ajiye kusa da ita, ɗaya ana kiran sa Isaf, ɗayan kuma Na’ila; sai ya mayar da Isaf kan dutsen Safa, ya ɗora Na’ila a kan dutsen Marwa. Daga nan sai wasu ƙabilun Larabawa in sun zo Hajji a lokacin jahiliyya, sai su riƙa yin sa’ayi a tsakanin waɗannan duwatsu guda biyu, saboda gumakan da aka ɗora a kansu. To bayan zuwan Musulunci da aka shar’anta Hajji da umara, sai wasu daga cikin Musulmi suka riƙa jin nauyin ci gaba da yin sa’ayi a tsakanin waɗannan duwatsu guda biyu, sai Allah ya saukar da wannan ayar, yana faɗa musu cewa, su ma waɗannan duwatsu suna daga cikin alamomin bautar Allah, kuma masu dangantaka da tarihin Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ɗansa Annabi Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), don haka babu wani laifi don sun yi sa’ayi a duwatsun. Kuma duk wanda ya aikata farilla, sannan ya ƙara da taɗawwu’i, to shi ma Allah zai ƙara masa a ladansa domin Allah mai godiya ne, ba ya lalata aikin mutum na ƙwarai, kuma masani ne da yake sane da aikin bawansa na alheri, kuma zai ga sakamakonsa.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡتُمُونَ مَآ أَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلۡهُدَىٰ مِنۢ بَعۡدِ مَا بَيَّنَّٰهُ لِلنَّاسِ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أُوْلَٰٓئِكَ يَلۡعَنُهُمُ ٱللَّهُ وَيَلۡعَنُهُمُ ٱللَّٰعِنُونَ
Open ayah 2:159Lalle waɗanda suke ɓoye abin da Muka saukar na hujjoji da shiriya bayan Mun yi bayanin su ga mutane a cikin Littafi, to waɗannan su ne Allah Yake la\'antar su, kuma masu la\'anta su ma suke la\'antar su.
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيۡهِمۡ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 2:160Sai dai waɗanda suka tuba kuma suka gyara kuma suka bayyana, to waɗannan zan karɓi tubansu, kuma lalle Ni Mai karɓar tuba ne, Mai jin ƙai.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَمَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٌ أُوْلَٰٓئِكَ عَلَيۡهِمۡ لَعۡنَةُ ٱللَّهِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 2:161Lalle waɗanda suka kafirta kuma suka mutu suna kafirai, to waɗannan la\'anar Allah ta tabbata a kansu da ta mala\'iku da mutane gaba ɗaya.
خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ
Open ayah 2:162Suna masu dawwama a cikinta, ba za a sassauta masu azaba ba kuma ba za a saurara musu ba. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba ne da sukan malaman Yahudawa da Nasara, saboda suna ɓoye wa mutane abin da yake cikin Attaura da Linjila, na hujjoji bayyanannu game da gaskiyar annabcin Annabi (ﷺ). Wannan sukar ta haɗa da duk wani wanda yake aikata irin aikinsu na ɓoye gaskiya bayan ya san ta. Allah ya bayyana sakamakon masu irin wannan mummunar ɗabi’a da cewa, za su haɗu da la’anar Allah da ta mala’iku da ta muminai ko duk wata halitta ta Ubangiji. Babu mai kuɓuta daga wannan la’antar sai wanda ya tuba ya gyara laifinsa, ta hanyar bayyana wa mutane abin da ya ɓoye masu na gaskiya, to waɗannan su ne Allah zai karɓi tubansu, ya yafe musu laifinsu, saboda shi mai karɓar tuba ne, mai rahama ga bayinsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka kafirce masa, suka watsar da addinin da ya saukar na Musulunci, suka rayu a kan kafirci har mutuwa ta zo musu, Allah ya bayyana cewa, za su ci gaba da dawwama a cikin la’antar Allah da mala’iku da halittu gaba ɗaya, za kuma su zarce zuwa wutar Jahannanma a lahira, inda za su dawwama a cikinta har abada kuma babu ranar da za a sassauta musu azaba, ko a ɗan jinkirta musu ita.
وَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 2:163Kuma abin bautarku abin bauta ne Guda Ɗaya, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Shi ne Mai rahma, Mai jin ƙai.
إِنَّ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱلۡفُلۡكِ ٱلَّتِي تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِمَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن مَّآءٖ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٖ وَتَصۡرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ وَٱلسَّحَابِ ٱلۡمُسَخَّرِ بَيۡنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Open ayah 2:164Lalle a cikin halittar sammai da ƙasa da sassaɓawar dare da rana da jiragen ruwa da suke tafiya a kan ruwa da abin da yake amfanar mutane da kuma abin da Allah Ya saukar daga sama na ruwa, Ya rayar da ƙasa da shi bayan mutuwarta, Ya kuma yaɗa duk wata halitta mai tafiya a cikin (ƙasa) da jujjuyawar iska, da kuma girgije da aka hore shi tsakanin sama da ƙasa, lalle akwai ayoyi ga mutane masu hankali.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادٗا يُحِبُّونَهُمۡ كَحُبِّ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَشَدُّ حُبّٗا لِّلَّهِۗ وَلَوۡ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِذۡ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ أَنَّ ٱلۡقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعَذَابِ
Open ayah 2:165Kuma akwai wasu mutane waɗanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waɗanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waɗanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huɗu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani ƙarfi na Allah ne gaba ɗaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne.
إِذۡ تَبَرَّأَ ٱلَّذِينَ ٱتُّبِعُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُواْ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَ وَتَقَطَّعَتۡ بِهِمُ ٱلۡأَسۡبَابُ
Open ayah 2:166Lokacin da waɗanda aka yi wa biyayya (shugabanni) za su nisantar da kansu daga waɗanda suka yi musu biyayya (mabiya), kuma suka yi arba da azaba, kuma duk wasu alaƙoƙi da ke tsakaninsu suka yanke.
وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُواْ لَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَتَبَرَّأَ مِنۡهُمۡ كَمَا تَبَرَّءُواْ مِنَّاۗ كَذَٰلِكَ يُرِيهِمُ ٱللَّهُ أَعۡمَٰلَهُمۡ حَسَرَٰتٍ عَلَيۡهِمۡۖ وَمَا هُم بِخَٰرِجِينَ مِنَ ٱلنَّارِ
Open ayah 2:167Kuma waɗanda suka yi biyayya suka ce: “Ina ma dai muna da wata dama ta komawa (duniya) don mu ma mu nisantar da kanmu daga gare su, kamar yadda suka nisanta kansu daga gare mu?” Kamar haka ne Allah Yake nuna musu ayyukansu suka zama nadama a gare su, kuma su ba masu samun fita ne daga wuta ba. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da bayinsa cancantarsa su bauta masa shi kaɗai, ba tare da sun haɗa shi da komai ba, domin shi ne ya siffantu da siffofi na kamala, kamar yalwatacciyar rahamarsa ga kowa da komai da kuma keɓantacciyar rahamarsa ga muminai ranar gobe ƙiyama. Sannan ya lissafa musu kaɗan daga cikin manyan ayyukansa na Rububiyya, waɗanda suka ƙunshi ni’imomi masu girma ga halittunsa, waɗanda ko su kaɗai aka duba sun isa zama babbar hujja a kan cancantarsa da bauta shi kaɗai. Waɗannan ni’imomi da Allah ya ambata a nan, sun haɗa da halittar sammai da ƙasa da irin abubuwan mamaki masu girma da ya ajiye a cikinsu; da zuwan dare da rana a kullum cikin tsari guda ɗaya, ba tare da sun yanke ba, suna sauka da haske da duhu da zafi da sanyi da tsawo da gajarta; da kuma manyan jiragen ruwa masu keta teku daga ƙasa zuwa ƙasa danƙare maƙil da kayan amfanin mutane; da kuma ruwan sama da yake saukarwa, ya fitar da tsirrai da shi, ya raya ƙasa bayan ta bushe, sannan ya yaɗa dabbobi iri-iri a bayan ƙasa. Sannan yake sako iska daban-daban, wata mai kaɗawa da ƙarfi, wata a hankali, wata mai zafi, wata kuma mai sanyi, wata mai amfani, wata kuma mai cutarwa. Hakannan kuma yadda yake hore haɗuwar girgije tsakanin sama da ƙasa don masalahar bayinsa. Duk waɗannan ayyuka ya yi su ne domin su nuna wa bayinsa cikar Ƙudirarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai, da a ce mutane za su yi aiki da hankulan da ya ba su. To amma duk da irin waɗannan dalilai na zahiri, sai ga wasu mutane suna ɗaukan wasu halittu su daidaita su da Allah wajen bauta da soyayya, suna son su kamar yadda suke son Allah. Amma Allah ya tabbatar da cewa, waɗanda suka yi imani su ne suke son Allah fiye da yadda waɗannan mutane suke son kishiyoyin da suka yi wa Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya juyo da magana zuwa ga Annabi (ﷺ) cewa, ina ma da ya ga halin da waɗannan mutanen masu fifita son wanin Allah a kan son Allah, za su tsinci kansu a ciki, su ma ina ma a ce sun ga hakan, lokacin da za su yi ido huɗu da azabar Allah ranar alƙiyama, daga lokacin ne za su tabbatar da cewa, duk wani ƙarfi da wani iko na Allah ne shi kaɗai, kuma irin azabar da ya yi tanadi ga masu kafirce masa ko yin shirka da shi mai tsanani ce. A ranar kuma duk wasu shugabanni na ɓata za su nisantar da kansu daga mabiyansu, su ma mabiyan za su yi haka, domin dukkansu sun ga azabar Allah ƙuru-ƙuru, duk wata dangantaka tsakaninsu a rananr ta ƙare, babu sauran ƙauna da za ta wanzu a lokacin. A lokacin ne mabiya za su yi burin ina ma za su samu wata dama ta komawa duniya don su yi baram-baram da waɗannan shugabannin nasu na ɓata, kamar yadda suka yi musu a lahira bayan sun nuna musu matuƙar ƙauna da soyayya da ta kai matakin bauta a gare su ba Allah ba. Sai dai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya riga ya gama nuna musu taɓewar ayyukansu, kamar yadda ya nuna musu azaba, domin su cika da nadama da yin da-na-sani marar amfani, domin wuta ce makomarsu ta har abada, babu ranar fita.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ كُلُواْ مِمَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٌ
Open ayah 2:168Ya ku mutane, ku ci halal mai daɗi na abin da ke fitowa daga cikin ƙasa, kada kuma ku bi hanyoyin Shaiɗan, lalle shi maƙiyi ne mai bayyana ƙiyayya a gare ku.
إِنَّمَا يَأۡمُرُكُم بِٱلسُّوٓءِ وَٱلۡفَحۡشَآءِ وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:169Yana umartar ku ne kawai da saɓo da ayyakan assha da kuma faɗin abin da ba ku da ilimi game da shi ku jingina wa Allah.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَلۡ نَتَّبِعُ مَآ أَلۡفَيۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ءَابَآؤُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ شَيۡـٔٗا وَلَا يَهۡتَدُونَ
Open ayah 2:170Idan kuma aka ce musu: “Ku bi abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “A\'a, za dai mu bi abin da muka samu iyayenmu a kansa”. To, ko da iyayensu ba sa hankaltar komai, kuma ba sa shiryuwa?
وَمَثَلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ كَمَثَلِ ٱلَّذِي يَنۡعِقُ بِمَا لَا يَسۡمَعُ إِلَّا دُعَآءٗ وَنِدَآءٗۚ صُمُّۢ بُكۡمٌ عُمۡيٞ فَهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 2:171Misalin waɗanda suka kafirta kamar misalin wanda yake ɗaga sauti ne ga wanda ba ya jin (komai) sai kira da sowa. Kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka su ba sa hankalta.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لِلَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ
Open ayah 2:172Ya ku waɗanda suka yi imani, ku ci daga daɗaɗan abin da Muka arzuta ku (da shi), kuma ku yi godiya ga Allah in har kun kasance Shi kaɗai kuke bauta wa.
إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ بِهِۦ لِغَيۡرِ ٱللَّهِۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Open ayah 2:173(Allah) Ya haramta muku mushe ne kawai da jini da naman alade da abin da aka kira sunan wani ba Allah ba (lokacin yanka shi). Don haka duk wanda ya matsu, ba mai zalunci ba, kuma ba mai ƙetare iyaka ba, to babu laifi a kansa ya ci. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana kiran mutane gaba ɗaya, muminansu da kafiransu da cewa, su ci abin da ya arzuta su da shi na dabbobi da tsirrai da kayan marmari, matuƙar abin da za su ci ya cika sharuɗɗa guda biyu, wato ya zamanto abin da Allah ya halatta amfani da shi ne, sannan kuma ba mai cutarwa ne ba. Sannan ya hana su biyayya ga Shaiɗan wajen haramta abin da Allah ya halatta ko halatta abin da ya haramta, domin Shaiɗan babban maƙiyinsu ne, mai nuna adawarsa gare su a fili, ba zai taɓa son su da wani alheri ba, sai dai ya riƙa yi musu ingiza-mai-kantu-ruwa, ya sa su aikata munanan ayyuka da miyagun ɗabi’u, waɗanda suka kai matuƙa a muni; ba ma iya nan kaɗai zai tsaya ba, a’a, sai ya riƙa sa su suna yi wa Allah ƙarya, suna ƙirƙirar wasu dokoki na banza suna cewa daga Allah suke, watau dai su haramta, su kuma halatta, bisa son zuciya, ba da wani dalili ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, mushirikai sun kasance duk sa’adda aka nemi su zo su bi abin da ya zo daga Allah, su amince duk abin da za su halatta ko su haramta, ya tafi daidai da shari’ar Allah, sai ka samu amsarsu ɗaya ce, ba za su taɓa sakin abin da suka tashi suka gada daga iyaye da kakanni ba. Allah ya soki irin wannan makauniyar biyayyar da suke yi wa iyayensu, kuma a kan me za su riƙa koyi da waɗanda bai cancanta su yi koyi da su ba, saboda ba su yi aiki da hankalinsu ba wajen bin gaskiya, kuma ba su da wani ilimi wanda yake musu jagoranci a cikin rayuwarsu ta addini da ta duniya? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da misalin kafirai, waɗanda idan mai wa’azi ya zo musu, yana faɗa musu gaskiya, sam ba sa fahimtar komai daga abin da yake faɗa, ko da kuwa sun saurare shi. Misalinsu kamar makiyayi ne a tsakiyar dabbobinsa da yake ƙwala kira, suna dai jin sautinsa, amma ba sa gane ma’anar maganarsa, to hakanan waɗannan kafiran suke. Lokacin da suka bijire wa imani da Annabi (ﷺ) a karon farko, sai kafofin jinsu da ganinsu da fahintarsu duk suka doɗe, ba sa jin gaskiya su fahince ta, balle su karɓa, ba sa iya faɗar gaskiya, ba sa kuma ganin hanyar gaskiya balle su bi ta, a dalilin haka ba sa fahintar wani abu na gaskiya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su ci abin da yake tsattsarka ne, mai amfani, wanda Allah ya arzuta su da shi, kuma su tsaya su gode masa a kan ire-iren waɗannan ni’imomi da ya yi musu, godiya da zuciyoyinsu da harsunansu da gaɓoɓins. To idan har sun kasance masu biyayya ne da miƙa wuya da ƙanƙantar da kansu ga Allah, to za su yi aiki da wannan umarni da yake yi musu. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da cin halal mai daɗi, sai kuma ya lissafa musu wasu abubuwan da aka haramta musu ci. Allah ya haramta musu cin mushen dabbar da ta mutu, ba tare da an yanka ta ba yanka na shari’a da jinin da ya kwararo daga wata dabba da naman alade da abin da aka yanka shi da sunan wanin Allah, kamar dabbar da ake yanka wa gumaka da makamancinta. To amma a nan an yi togaciyar lokacin larura, mutum yana iya cin wani abu daga waɗannan da aka ambata gwargwadon larurarsa, to duk wanda ya yi haka to ba shi da wani laifi, Allah mai gafara ne tun da ya ɗauke masa zunubi, mai rahama ne yayin da ya yalwata wa bayinsa, bai takura musu ba.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡتُمُونَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَيَشۡتَرُونَ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلًا أُوْلَٰٓئِكَ مَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ إِلَّا ٱلنَّارَ وَلَا يُكَلِّمُهُمُ ٱللَّهُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَلَا يُزَكِّيهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Open ayah 2:174Lalle waɗanda suke ɓoye abin da Allah Ya saukar na Littafi, kuma suke musanya shi da ɗan kuɗi kaɗan, waɗannan babu abin da suke ci a cikkunansu sai wuta, kuma Allah ba zai yi musu magana ba ranar tashin alƙiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma lalle suna da wata azaba mai raɗaɗi.
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلضَّلَٰلَةَ بِٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡعَذَابَ بِٱلۡمَغۡفِرَةِۚ فَمَآ أَصۡبَرَهُمۡ عَلَى ٱلنَّارِ
Open ayah 2:175Waɗannan su ne waɗanda suka zaɓi ɓata a madadin shiriya da kuma azaba a madadin gafara. Don haka yi mamakin haƙurin (zamansu) a cikin wuta.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ نَزَّلَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِي ٱلۡكِتَٰبِ لَفِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ
Open ayah 2:176Wannan ya faru ne saboda lalle Allah Ya saukar da Littafinsa da gaskiya. Kuma lalle duk waɗanda suka yi saɓani dangane da Littafin, tabbas suna cikin saɓawa mai nisa. Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin cewa ya halatta duk wani abu mai daɗi da amfani ga mutane, ya kuma wajabta musu gode wa ni’imominsa, sai kuma ya kawo bayani a kan miyagun malamai masu ɓoye gaskiya, suna shar’anta wa mabiyansu shari’o’i waɗanda ba na Allah ba, kamar malaman Yahudawa da Nasara, waɗanda suka ɓoye gaskiyar annabcin Annabi (ﷺ) bayan sun karanta siffofinsa a Attaura da Linjila, suka riƙa wasa da hukunce-hukuncen Allah, su sassauta wasu, su canza wasu, domin kwaɗayin abin duniya ko samun matsayi, ba su san cewa, dukiyar da suke ci sakamakon canza hukuncin Allah, wuta ce suke ci a cikinsu, kuma ranar gamuwarsu da Allah, ba za su ji wata magana mai daɗi daga gare shi ba, ba zai tsarkake su daga zunubbansu ba; a madadin haka sai dai su haɗu da azaba mai raɗaɗin gaske. Waɗannan mutane masu ɓoye ilimi da irin aikinsu na canza hanyar shiriya da wata ɓatacciyar hanya, suna barin gafarar Allah ne, su ɗauki azabarsa. Allah ya nuna mamakinsa game da wannan ƙarfin hali nasu na aikata aikin da zai kai su ga faɗawa wutar Jahannama, yaya suka iya yin haƙuri a kan aikin da zai kai su ga shiga azaba mai tsanani?! Waɗannan miyagun malamai lalle sun cancanci azabar Allah saboda ɓoye gaskiya da suka riƙa yi. Domin Allah dai ya saukar da Littafinsa da gaskiya kuma ya bayyana ta a fili a cikinsa, ashe bai dace a ɓoye ta ba, domin ɓoye ta ya saɓa da manufar Allah wajen saukar da littafinsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suka ba da gaskiya da wani sashe na littafi, sannan suka kafirce wa wani sashi, suka ɓoye wani ɓangare na hukunce-hukuncensa, suka bayyana wani ɓangaren, to masu irin wannan ɗanyen aiki sun kauce wa hanyar gaskiya, sun yi nisa a cikin ɓata.
۞لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ وَءَاتَى ٱلۡمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ ذَوِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَٱلسَّآئِلِينَ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُوفُونَ بِعَهۡدِهِمۡ إِذَا عَٰهَدُواْۖ وَٱلصَّٰبِرِينَ فِي ٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَحِينَ ٱلۡبَأۡسِۗ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ
Open ayah 2:177Ba wai aikin ɗa\'a shi ne ku juyar da fuskokinku mahudar rana ko mafaɗarta ba ; sai dai aikin ɗa\'a shi ne, wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da mala\'iku da littattafai da annabawa, kuma ya bayar da dukiyarsa, alhalin yana son ta, ga dangi na kusa da marayu da mabuƙata da matafiyi da kuma masu roƙo (bisa larura) da \'yantar da bayi, sannan kuma ya tsayar da salla, kuma ya bayar da zakka, da kuma masu cika alƙawarinsu idan suka ƙulla alƙawari ; da masu haƙuri a cikin halin talauci da halin rashin lafiya da lokacin yaƙi. Waɗannan su ne waɗanda suka yi gaskiya, kuma waɗannan su ne masu taƙawa. Bayan canza Alƙibla daga Baitul Maƙdis zuwa fuskantar Ka’aba, sai kuma rigima ta ci gaba tsakanin Musulmi da abokan hamayyarsu Yahudawa, lokacin da su suke ganin sallar Musulmi babu ɗa’a ga Allah a cikinta, saboda sun daina fuskantar Baitul Maƙadis, alƙiblar annabawa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa, tsayawa a dubi wata nahiya gabas ko yamma lokacin yin ibada, ba shi ne kawai ɗa’a ga Allah ba, ballantana har Yahudawa su riƙa ganin Musulmi ba sa yin ɗa’a ga Ubangiji, don sun daina fuskantar alƙiblarsu. Ɗa’a ta gaskiya ga Allah ita ce yin imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da dukkan littattafan da Allah ya saukar wa annabawa da yin imani da dukkan annabawa da manzannin Allah, da kuma ba da kyautar dukiyarsa don Allah, tare da yana son abinsa, ya ba wa danginsa na kusa ko marayu ko mabuƙata ko matafiyin da guzurinsa ya yanke masa, ya taimaka masa da abin da zai mayar da shi garinsa da mai roƙo bisa larura, ko ya bayar da dukiyarsa don ‘yanta bayi da makamantansu. Hakanan kuma tsayar da salla kamar yadda ya kamata, da bayar da zakka ga masu ita, da cika alƙawari tsakanin bawa da Ubangijinsa ko tsakaninsa da ‘yan’uwansa duk suna cikin ayyukan ɗa’a. Haƙuri ma a lokacin talauci ko rashin lafiya ko lokacin yaƙi duka ayyuka ne na ɗa’a. Wato mutum ya danne damuwarsa, ba tare da raki ba. To duk wanda ya siffantu da waɗannan siffofi da aka ambata, shi ne mai taƙawa, ta hanyar aikata wajibi, da barin abin da aka hana aikatawa.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِي ٱلۡقَتۡلَىۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰۚ فَمَنۡ عُفِيَ لَهُۥ مِنۡ أَخِيهِ شَيۡءٞ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَآءٌ إِلَيۡهِ بِإِحۡسَٰنٖۗ ذَٰلِكَ تَخۡفِيفٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةٞۗ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 2:178Ya ku waɗanda suka yi imani, an wajabta muku ƙisasi dangane da waɗanda aka kashe; ɗa da ɗa, bawa da bawa, mace da mace. To duk wanda aka yafe masa ƙisasin ɗan uwansa, to sai ya bibiye shi ta hanyar da ta dace, shi kuma ya biya diyyar ta hanyar kyautatawa. Wannan (abin da aka ambata), sauƙi ne da rahama daga wajen Ubangijinku. Don haka duk wanda ya ƙetare iyaka bayan haka, to yana da azaba mai raɗaɗi.
وَلَكُمۡ فِي ٱلۡقِصَاصِ حَيَوٰةٞ يَٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Open ayah 2:179Kuma a cikin (hukuncin) ƙisasi akwai (tsare) rayuwa a gare ku, ya ku ma\'abota hankula, don ku samu taƙawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai hukuncin zartar da ƙisasi a kan wanda ya yi kisan ganganci, kuma ya yi umarni da daidaito wajen wannan ƙisasi, wato a kashe ɗa yayin da ya kashe ɗa. Haka hukuncin yake yayin da namiji ɗa ya kashe ‘ya mace ko bawa ya kashe bawa irinsa ko mace ta kashe mace irinta. Amma idan magadan wanda aka kashe suka yafe wa wanda ya yi kisan, to shi ke nan babu zancen ƙisasi, sai a bayar da diyya. To a irin wannan yanayi wajibi ne a kan shi wanda ya yi afuwa, kada ya riƙa goranta wa wanda ya yi wa afuwar ko ya riƙa jifan sa da wata baƙar magana, kuma kada ya ɗora masa nauyin da Allah bai ɗora masa ba. Shi kuma wanda aka yafe wa ya yi ƙoƙari ya biya diyyar da take kansa, ba tare da taurin bashi ba ko mummunar magana ga wanda ya yi yafiyar ba. Cikin irin waɗannan hukunce-hukuncen da Allah ya saukar na ƙisasi, da yin afuwa da biyan diyya, akwai sauƙaƙawar gaske ga bayinsa, da rahama da tausayi gare su. To amma duk wanda ya yi wani ta’addanci daga baya, kamar ɗan’uwan mamaci ya kashe wanda aka yi wa afuwa, ko shi wanda aka yi wa afuwa, ya sake maimaita laifin kisan kai, to babu shakka wanda duk ya yi haka yana da wata azaba mai raɗaɗin gaske. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci hikimar shar’anta yin ƙisasi da cewa, shi ne kare rayuwar al’umma. Domin duk wanda ya san irin wannan hukunci na ƙisasi yana jiran sa idan har ya yi sanadiyyar salwanta rayuwar ɗan’uwansa da ganganci, to babu shakka zai yi ƙoƙarin bijire wa zuciyarsa kan abin da za ta saƙa masa na aikin ta’addanci. Don haka wannan zai taimaka wajen rage yawan kashe-kashe ciki al’umma. Babu masu fahimtar irin wannan hikimar, sai masu hankula, waɗanda za su yi tunani da hankulansu domin fahintar hikimomin shari’a. Ba za a taɓa samun zaman lafiya ba, sai a ƙarƙashin bin dokokin Allah (Mai tsarki da daukaka).
كُتِبَ عَلَيۡكُمۡ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ إِن تَرَكَ خَيۡرًا ٱلۡوَصِيَّةُ لِلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَ بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 2:180An wajabta muku, idan alamun mutuwa suka zo wa ɗayanku, idan har ya bar wani alheri (dukiya), to ya yi wasiyya ga mahaifa biyu da dangi mafiya kusanci, ta hanyar da ta dace (a shari\'a). Haƙƙi ne tabbatacce a kan masu taƙawa.
فَمَنۢ بَدَّلَهُۥ بَعۡدَمَا سَمِعَهُۥ فَإِنَّمَآ إِثۡمُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يُبَدِّلُونَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 2:181To wanda ya canza shi (lamarin wasiyya) bayan ya ji shi, to lalle laifinsa yana kan waɗanda suka canza shi ne kawai. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
فَمَنۡ خَافَ مِن مُّوصٖ جَنَفًا أَوۡ إِثۡمٗا فَأَصۡلَحَ بَيۡنَهُمۡ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 2:182To duk wanda ya ji tsoron kaucewa bisa kuskure ko bisa zalunci daga mai yin wasiyya sai ya sasanta tsakaninsu (mai wasiyyar da waɗanda aka yi wa wasiyyar); to wannan babu laifi a kansa; lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyyana cewa, ya wajabta wa muminai idan ɗayansu ya ga alamun kusantowar mutuwa gare shi, kuma yana da dukiya, to ya yi wasiyya ga iyayensa da danginsa da wani kaso na wannan dukiyar tasa. Ya kuma yi wannan wasiyya yadda ya dace da adalci, ba tare da almubazzaranci ko rowa ba, ya yi la’akari da wanda ya fi kusanci da kuma wanda ya fi buƙata cikin waɗanda zai yi wa wasiyyar, sannan ba tare da ya cutar da magadansa ba. Allah ya nuna cewa, wannan al’amari kaƙƙi ne a kan duk masu taƙawa; masu kula da haƙƙoƙin wasu dake kansu. Wasu daga cikin malamai suna ganin ayar rabon gado ta cikin Suratun Nisa’i, aya ta 11 ta shafe hukuncin wannan ayar. Abu Umamatul Bahili (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana faɗa a huɗubarsa ta hajjin bankwana cewa: “Allah ya bai wa kowanne mai haƙƙi haƙƙinsa, don haka babu wasiyya ga mai cin gado”. [Abu Dawud#2870 da Tirmizi#2120]. Amma kuma wasu malaman suna ganin ba a shafe duk hukuncin ayar ba gaba ɗaya. Har yanzu tana nuna mahimmancin wasiyya ga makusanta waɗanda ba za su ci gadon wannan mamaci ba, to sai ya yi wasiyya da wani kaso daga cikin dukiyarsa bayan ya mutu, amma da sharaɗin kada kason ya wuce ɗaya bisa ukun dukiyar. To bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna girman sha’anin wasiyya da wajabcinta, sai kuma ya gargaɗi wanda zai canja ta daga yadda aka bar masa ita, Allah ya bayyana cewa, duk wanda ya canja wasiyya daga yadda ya ji ta daga bakin mai wasiyya, ta hanyar ya ƙara ko ya rage daga abin da mamaci ya bar masa, to haƙiƙa ya ɗaukar wa kansa wani babban laifi, kuma babu wani laifi da zai shafi mamacin da ya bar masa wasiyyar a kan haka. Allah mai ji ne kuma masani ne zai yi wa kowa sakayya gwargadon aikinsa mai kyau ko mummuna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin wanda ya lura da cewa mai barin wasiyyar ya tabka kusukure a cikin wasiyyarsa, ya bai wa wani, ya hana wanda ya fi cancanta komai, ko ya ba wa mawadaci marar buƙata a cikin dangi, ya hana talaka mai tsananin buƙata a cikinsu, to a nan sai mai kula da wasiyya ya shiga tsakani ya sasanta dangin mamacin ya gyara kuskuren dake ƙunshe cikin wannan wasiyyar, to bai yi laifin komai ba, sai ma ladan sulhu da za a ba shi. Allah mai gafara ne ga waɗanda suka tuba, mai rahama ne gare su.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Open ayah 2:183Ya ku waɗanda suka yi imani, an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suke gabaninku, don ku samu taƙawa.
أَيَّامٗا مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۚ وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُۥ فِدۡيَةٞ طَعَامُ مِسۡكِينٖۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَهُوَ خَيۡرٞ لَّهُۥۚ وَأَن تَصُومُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:184Waɗansu kwanaki ne ƙididdigaggu. To duk wanda ya kasance marar lafiya a cikinku ko a kan wata tafiya, to (idan ya sha azumi) sai ya rama a waɗansu kwanakin na daban. Kuma waɗanda za su yi azumi da wahala su ba da fansa ta ciyar da miskini; to duk wanda ya ƙara (a kan abincin miskini), to wannan alheri ni gare shi. Amma ku yi azumin shi ne ya fi muku alheri, in har kun kusance kuna sani.
شَهۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهۡرَ فَلۡيَصُمۡهُۖ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۗ يُرِيدُ ٱللَّهُ بِكُمُ ٱلۡيُسۡرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ ٱلۡعُسۡرَ وَلِتُكۡمِلُواْ ٱلۡعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 2:185Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alƙur\'ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane kuma ayoyi ne bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa (tsakanin ƙarya da gaskiya). Don haka duk wanda ya halarci wannan watan daga cikinku, to ya azumce shi, kuma wanda ya kasance marar lafiya ko a kan wata tafiya, to (idan ya sha azumi) sai ya rama a waɗansu kwanakin na daban. Allah Yana nufin sauƙi a gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani a gare ku, don ku cika adadin (kwanakin Ramadan), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da Ya yi, don ku yi godiya.
وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌۖ أُجِيبُ دَعۡوَةَ ٱلدَّاعِ إِذَا دَعَانِۖ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لِي وَلۡيُؤۡمِنُواْ بِي لَعَلَّهُمۡ يَرۡشُدُونَ
Open ayah 2:186Kuma idan bayina sun tambaye ka game da Ni, to Ni kusa Nake (da su), Ina amsa kiran mai kira idan ya kiraye Ni; to su amsa Mini nawa kiran, kuma su yi imani da Ni, don su shiryu.
أُحِلَّ لَكُمۡ لَيۡلَةَ ٱلصِّيَامِ ٱلرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَآئِكُمۡۚ هُنَّ لِبَاسٞ لَّكُمۡ وَأَنتُمۡ لِبَاسٞ لَّهُنَّۗ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَخۡتَانُونَ أَنفُسَكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡ وَعَفَا عَنكُمۡۖ فَٱلۡـَٰٔنَ بَٰشِرُوهُنَّ وَٱبۡتَغُواْ مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِۚ وَلَا تُبَٰشِرُوهُنَّ وَأَنتُمۡ عَٰكِفُونَ فِي ٱلۡمَسَٰجِدِۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَقۡرَبُوهَاۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Open ayah 2:187An halatta muku saduwa da matanku a daren azumi. Su sutura ne a gare ku, ku ma kuma sutura ne a gare su. Allah Ya san cewa ku lalle kun kasance kuna ha\'intar kawunanku, sai Ya karɓi tubanku kuma Ya yi muku afuwa; to a yanzu ku sadu da su (da daddare), kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku, kuma ku ci, kuma ku sha har farin zare ya bayyana a gare ku daga baƙin zare na alfijir (wato ketowar Alfijir), sannan kuma ku cika azumi zuwa dare, kuma kar ku sadu da su alhali kuna i\'itikafi a masallatai. Waɗannan iyakoki ne na Allah, kada ku kusance su. Kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinsa ga mutane, don su samu taƙawa. A waɗannan ayoyi, Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin yadda ya wajabta wa wannan al’umma ibadar azumi, kamar yadda ya wajabta wa al’ummomin da suka gabace ta, domin hikimar yin hakan shi ne samun taƙawa. Domin rahama ta Ubangiji da tausayawarsa ga bayinsa, bai umarce su da yin azumi na tsawon watanni ba, a’a, sai ya sanya shi tsawon ‘yan kwanaki ne kaɗan. Bayan haka kuma, sai ya yi rangwame ga marar lafiyar da ba zai iya yin azumi ba da matafiyi da yake neman sauƙi cikin tafiyarsa da cewa, za su iya ajiye azumi, daga baya su rama a wasu kwanakin daban. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin wanda yake yin azumi da kyar cikin matsananciyar wahala, zai iya ciyar da mabuƙaci ɗaya a madadin kowace rana. Amma idan ya ga dama don raɗin kansa, yana iya ciyar da fiye da mabuƙaci ɗaya, to yin haka aikin alheri ne. Wasu masana tafsiri suna cewa, wannan gaɓar a wannan ayar ta yi nuni ne a kan cewa, an ba wa mutumin da zai iya azumi zaɓi na ya yi azumin ko ya sha, ya ciyar a madadinsa, daga baya aka shafe wannan hukunci na bayar da zaɓi, aka wajabta wa duk wani mai ikon azumtar watan Ramadana a ayar dake biye da wannan. Amma wasu masana suna ganin ayar tana nan ba a shafe ta ba, kuma tana magana ne a kan waɗanda yin azumi yake ba su wahala matuƙa kamar tsoho da tsohuwa tukub ko marar lafiyan da aka fitar da ƙaunar warkewarsa, koma mace mai ciki ko mai shayarwa waɗanda suke jiye wa kansu ko ‘ya’yansu tsoro shiga mawuyacin hali idan sun yi azumi, to sai su sha azumin, su ciyar a madadinsa. Wannan fahimta ce ta wasu sahabbai da tabi’ai. [Duba Ibni Taimiyya, Sharhu Umdatul Fiƙh, 1:262-264]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babbar falalar watan Ramadan da cewa, ita ce saukar da Alƙur’ani a cikinsa, Littafin da ya ƙunshi shiriya da fayyacewa tsakanin ƙarya da gaskiya ga mutane. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin wajabcin azumtar wannan wata mai daraja ga duk wanda ya riski watan yana zaune a gari, ba matafiyi ba. Amma idan mutum ba shi da lafiya ko yana cikin halin tafiya, to yana iya ajiye azumi, ya rama a wasu kwanakin daban. Wannan sauƙi ne daga Allah ga bayinsa, domin shi Allah (Mai tsarki da daukaka) har ko da yaushe mai son sauƙaƙawa ne gare su, ba mai son tsanantawa ba, domin bayinsa su zamanto masu gode masa game da ni’imar shiriya da ya yi musu da nusantar da su ga falalar wannan ibada, tare da sauƙaƙe musu hukunce-hukuncenta. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya dawo da maganarsa zuwa ga Annabinsa (ﷺ) cewa, idan bayin Allah sun yi masa tambaya game da kusancin Allah gare su, to su sani cewa, Allah yana nan kusa da su, yana kuma amsa addu’ar duk wanda yake roƙon sa, don haka su abin da yake wajibi a kansu shi ne su amsa masa nasa kiran, su yi masa ɗa’a tare da miƙa wuya gare shi, da haka ne za su dace da gaskiya, sannan su sami cim ma buƙatunsu. A farkon lokacin da aka wajabta azumi, an haramta wa Musulmi bayan sun yi barci da daddare, sannan suka farka, su ci ko su sha ko su sadu da matansu. Sai bin wannan doka ta zama da wahala a wurin wasu, sai Allah ya sassauta musu ita da cewa, ya halatta musu saduwa da matansu a cikin daren Ramadan, kamar yadda ya halatta musu su ci su sha a cikinsa, har zuwa hudowar alfijir. Albara’u ɗan Azib (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Sahabban Annabi (ﷺ) sun kasance idan ɗayansu yana azumi, sai ya yi barci kafin ya yi buɗa baki, to ba shi da damar idan ya farka cikin dare ya ci ko ya sha wani abu, har sai kashe-gari bayan faɗuwar rana. Sai wata rana wani sahabi mutumin Madina, ana kiran sa Ƙaisu ɗan Sirma, yana azumi, da lokacin buɗa baki ya yi, ya zo gida ya tambayi matarsa, ko tana da abinci? Sai ta ce: ‘A’a, amma bari in je in nemo maka.’ To shi kuma ya yini yana aiki, ya gaji, sai barci ya ɗauke shi. Matar ta dawo yana barci, sai ta ce: ‘Ka shiga uku.’ Ya wayi gari, ya yini bai ci komai ba. Da rana ta take tsaka, sai kawai ya faɗi ya suma; sai aka je aka faɗa wa Annabi (ﷺ) abin da ya faru, sai wannan ayar ta sauka: ‘An halatta muku saduwa da matanku a daren azumi....’ Sahabbai suka yi farin ciki da haka sosai. Sannan kuma ɗaya ɓangaren ayar ya sauka tana cewa: ‘....kuma ku ci, kuma ku sha har farin zare ya bayyana na alfijir....’ Game da faɗar Allah cewa: “....Allah ya san cewa kun kasance kuna ha’intar kawukanku....”, Albara’u ɗan Azib yana cewa: “Yayin da aka wajabta azumtar watan Ramadan, sahabbai ba su da damar kusantar iyalansu a tsawon watan gaba ɗaya, sai ya zamanto wasu mazajen suna yin ha’inci, sai Allah ya saukar da aya mai cewa: “....Allah ya san cewa, lalle kun kasance kuna ha’intar kawukanku....” [Bukhari #4508]. Game da faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka): “....ku ci, ku sha har farin zare ya bayyana daga baƙin zare na alfijir....”, Sahlu bn Sa’ad (Allah ya kara masa yarda) yayin da ayar ta fara sauka, babu ambaton kalmar ‘alfijir’ a cikinta, sai ya zamanto duk lokacin da wani zai yi azumi, sai ya ɗaura farin zare da baƙin zare a ƙafafuwansa, sai ya yi ta ci, yana sha abinsa, har sai lokacin da zai iya tantace tsakaninsu, sai Allah ya saukar da ƙarin ‘na alfijir’, daga lokacin sai suka fahinci ashe ana nufin dare ne da yini. [Bukhari #1917, da Muslim #1091]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana masu i’itikafi saduwa da matansu lokacin da suke cikin ibadar i’itikafi a masallaci, yana mai ƙara bayyana musu cewa duk waɗannan abubuwan da ya hana mai yin azumi da mai i’itikafi aikatawa dokoki ne na Allah, kada su kuskura su keta su. To kamar yadda Allah ya yi cikakken bayani dangane da hukunce-hukuncen azumi, haka ne yake bayyana sauran hukunce-hukuncen shari’a a wannan Littafi nasa, da kuma a kan harshen Manzonsa (ﷺ), domin mutane su gane yadda ya kamata su yi wa Allah ɗa’a, wajen aikata wajibai, da guje wa abubuwan da aka haramta.
وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ وَتُدۡلُواْ بِهَآ إِلَى ٱلۡحُكَّامِ لِتَأۡكُلُواْ فَرِيقٗا مِّنۡ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ بِٱلۡإِثۡمِ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:188Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, haka kuma kada ku miƙa dukiyoyinku zuwa ga masu shari’a, don kawai ku ci wani ɓangare na dukiyar mutane ta hanyar saɓo, alhali kuna sane. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi gargaɗi ga mai da gangancin saɓa wa hukunce-hukuncen azumi, ya ce waɗannan iyakokin Allah ne kada wani ya kuskura ya kusance su balle ya ƙetare su, sai kuma ya biyo bayansu da bayanin wani hukunci na bai-ɗaya, wanda shi ne haramcin cin dukiyar mutane ba tare da wani haƙƙi ba. Wannan doka ce mai shiga cikin hukunce-hukunce da yawa. Sannan sai ya yi wani hani a keɓance, watau shi ne haramcin bayar da cin hanci ga alƙalai ko mahukunta don su bayar da damar cin dukiyar wani ba a kan gaskiya ba, kamar mutumin da ake bi bashi, mai kuɗin kuma ba shi da wata bayyananniyar sheda a kan wannan bashi, sai ya musanta bashin da ke kansa, alhalin ya san gaskiya ne, idan an je gaban alƙali sai ya ba da cin hanci domin ya danne wannan haƙƙi da ke kansa ya cinye dukiyar ɗan’uwansa ba bisa gaskiya ba, alhali yana sane.
۞يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَهِلَّةِۖ قُلۡ هِيَ مَوَٰقِيتُ لِلنَّاسِ وَٱلۡحَجِّۗ وَلَيۡسَ ٱلۡبِرُّ بِأَن تَأۡتُواْ ٱلۡبُيُوتَ مِن ظُهُورِهَا وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنِ ٱتَّقَىٰۗ وَأۡتُواْ ٱلۡبُيُوتَ مِنۡ أَبۡوَٰبِهَاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Open ayah 2:189Suna tambayar ka dangane da jirajiran wata. Ka ce: “Su lokuta ne (don amfani) ga mutane da (tantance lokacin) Hajji.\" Kuma ba ya daga cikin aikin ɗa\'a, ku zo wa gidaje ta bayansu, sai dai mai aikin ɗa\'a shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku shigo wa gidajen ta ƙofofinsu, kuma ku kiyaye dokokin Allah don ku rabauta.
وَقَٰتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ يُقَٰتِلُونَكُمۡ وَلَا تَعۡتَدُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ
Open ayah 2:190Kuma ku yaƙi waɗanda suke yaƙar ku don ku ɗaukaka kalmar Allah, kuma kada ku ƙetare iyaka. Lalle Allah ba Ya son masu ƙetare iyaka.
وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ ثَقِفۡتُمُوهُمۡ وَأَخۡرِجُوهُم مِّنۡ حَيۡثُ أَخۡرَجُوكُمۡۚ وَٱلۡفِتۡنَةُ أَشَدُّ مِنَ ٱلۡقَتۡلِۚ وَلَا تُقَٰتِلُوهُمۡ عِندَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ حَتَّىٰ يُقَٰتِلُوكُمۡ فِيهِۖ فَإِن قَٰتَلُوكُمۡ فَٱقۡتُلُوهُمۡۗ كَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:191Kuma ku yaƙe su duk inda kuka same su, kuma ku fitar da su ta inda suka fitar da ku; kuma fitina (ta kafirci) ita ce mafi tsanani fiye da kisa, kuma kada ku yaƙe su a wurin Masallaci mai alfarma, har sai idan sun yaƙe ku a cikinsa, idan har suka yaƙe ku, to ku ma ku yaƙe su. Kamar haka ne sakamakon kafirai yake.
فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 2:192Amma idan suka daina, to lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai jin ƙai.
وَقَٰتِلُوهُمۡ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتۡنَةٞ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ لِلَّهِۖ فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَلَا عُدۡوَٰنَ إِلَّا عَلَى ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 2:193Kuma ku yaƙe su har ya zamanto ba a sami wata fitina ba, kuma addini ya zamo na Allah ne. Idan suka daina, to babu sauran kai farmaki sai a kan azzalumai.
ٱلشَّهۡرُ ٱلۡحَرَامُ بِٱلشَّهۡرِ ٱلۡحَرَامِ وَٱلۡحُرُمَٰتُ قِصَاصٞۚ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَٱعۡتَدُواْ عَلَيۡهِ بِمِثۡلِ مَا ٱعۡتَدَىٰ عَلَيۡكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 2:194(Idan sun yaƙe ku a) wata mai alfarma, (ku ma ku yaƙe su a) wata mai alfarma, kuma a cikin abubuwa masu alfarma akwai ƙisasi. Don haka duk wanda ya yi muku ta\'addanci, to ku ma ku rama ta\'addancin gwargwadon yadda ya yi muku ta\'addanci; kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani lalle Allah Yana tare da masu taƙawa.
وَأَنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا تُلۡقُواْ بِأَيۡدِيكُمۡ إِلَى ٱلتَّهۡلُكَةِ وَأَحۡسِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 2:195Kuma ku ciyar da dukiyoyinku domin taimakon addinin Allah, kuma kada ku jefa kawunanku zuwa ga halaka, kuma ku kyautata; lalle Allah Yana son masu kyautatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin hikimar da ke cikin halittar jinjirin wata tun yana ƙarami har ya girma ya cika. Wasu sahabban Annabi (ﷺ) sun yi masa tambaya cewa, mene ne hikimar da take cikin yin hakan? Me ya sa kuma watanni aikinsu ba ya kama da na rana wajen fitowa gaba ɗaya bisa kamanni guda, sai dai su riƙa caccanzawa daga ƙanƙanta har su girma, sannan kuma su dawo suna raguwa har kuma su ɓuya? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ba su amsar cewa, Allah ya yi haka ne domin waɗannan watanni su zama lokutan gane al’amuran ibadunsu, kamar Hajji da azumi da idodi da kuma kiyaye lokutan al’amuransu na yau da kullum da yarjejeniya da za ta shigo tsakaninsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana a kan wata al’ada marar ma’ana ta Larabawa yayin fita zuwa aikin Hajji ko dawowa lokacin da mutum ya sanya ihrami sai ya haramta wa kansa shiga gidansa ta ƙofar gida. Idan ya buƙaci shiga to sai dai ya hauro ta bayan gidan. Suna yin haka ne kuma da sunan bautar Allah da neman lada a wurinsa. Wata rana wani mutumin Madina ya dawo daga Hajji sai ya shiga gidansa ta ƙofar gida, sai hakan ya zama abin magana a cikin jama’a, aka riƙa sukan wannan mutum, sai Allah ya saukar da wannan ayar, yana faɗa wa muminai cewa, wannan al’ada ta haurowa ta bayan gida, ba ita ce aikin alheri ba a wurin Allah (Mai tsarki da daukaka). Aikin alheri a wurinsa shi ne mutum ya kiyaye dokokinsa ta hanyar aikata umarninsa da barin haninsa. Don haka daga yanzu kowa ya dinga shiga gidansa ta ƙofar gidan ba ta baya ba. Kuma su lizimci taƙawa, domin da ita ne za su cim ma buƙatarsu ta samun rabauta a wurin Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su yaƙi duk kafirin da ya fito yana yaƙar su. Kuma su tsarkake niyyarsu da yi domin Allah kawai, don haka kada su kuskura su yi ta’addanci wajen mayar da martani a kan kafiran da suke yaƙar su. Wato kar su riƙa kashe musu mata da yara da tsofaffi da sauran waɗanda ba su shiga yaƙi da su ba; aikata hakan ta’addanci ne, Allah kuwa ba ya son ‘yan ta’adda masu zarce haƙƙinsu. Annabi (ﷺ) ya kasance idan ya shirya rundunar yaƙi yakan yi wasiyya ga shugaban wannan runduna da mayaƙansa ya ce musu: “Ku yi yaƙi da sunan Allah kuma don Allah, ku yaƙi wanda ya kafirce wa Allah, ku yi yaƙi, kada ku riƙa satar ganima, kuma kada ku riƙa yin yaudara kuma kada ku riƙa yin gunduwa-gunduwa da gawarwakin abokan faɗanku, kada kuma ku kashe yara. Idan kun haɗu da maƙiyanku mushrikai, to ku kirawo su zuwa ga abubuwa guda uku; kowane ɗaya daga cikin ukun suka amsa muku; to ku karɓa daga wajensu, ku fasa yaƙar su.” [Muslim #1731]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su yaƙi kafiran da suke yaƙar su a duk inda suka haɗu da su, sannan su ma muminai su kore su daga garuruwan da su kafiran suka kore su a baya. Shirkar da suke ciki ta fi kisansu girma a wurin Allah. Hakanan abin da kafirai suke yi wa muminai na hana su addininsu shi ma ya fi kisa muni a wurin Allah, domin zafin kisa taƙaitacce ne, amma zafin azabar kafirci mai ɗorewa ne har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai fara kai wa kafirai hari a masallaci mai alfarma na Makka; amma kuma idan kafiran su ne suka fara kawo musu hari a wannan wuri mai tsarki, to lalle muminai su mayar musu da martani, kuma suna iya kashe su a wannan wuri domin nuna musu sakamakon ta’addancinsu. Amma idan sun tuba sun musulunta sun bar yaƙar su to su sani cewa, Allah mai gafarta musu duk laifukansu da suka wuce, kuma zai yi musu rahama ya datar da su ga samun duk wani alheri na duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya maimaita umarnin yaƙar mushrikai har a kai ga murƙushe bautar wanin Allah gaba ɗaya, addini da bauta su zama na Allah ne shi kaɗai, muddun dai su mushrikan za su ci gaba da yaƙar su; to amma idan sun rabu da su sun daina yaƙar su, sun tuba zuwa ga Allah to wajibi ne kuma su muminai su daina yaƙar su, domin wanda ya cancanta a yaƙa shi ne azzalumi mai cutar da muminai da kafircinsa da shirkarsa. Sai kuma Allah ya bayyana hukuncin yaƙar kafirai ‘yan ta’adda a cikin wata mai alfarma yayin da su suka fara yaƙar muminai a cikinsa. Allah ya halatta wa muminai yaƙar su matuƙar sun yaƙe su a cikin wannan watan; kamar yadda suka keta alfarmar watanni masu alfarma, to a bi su da ɗaukar fansa ta hanyar keta musu irin waɗannan watannin masu alfarma a yaƙe su a cikinsu; wannan shi ne sakamako na adalci, wanda duk ya yi ma muminai ta’addanci to su mayar masa da martani gwargwadon irin ta’addancinsa. To amma sai Allah ya umarci muminai da su kiyaye dokokin Allah kada su yi ramuwa da abin da ya fi ta’addancin da aka yi musu muni. Su kiyaye dokokin Allah domin yin haka shi zai sa su zama tare da Allah, domin yana tare da duk wani mai bin umarninsa ya guji haninsa. Daga nan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni da ciyar da dukiya saboda shi don ɗaukaka addininsa, ya gargaɗi muminai da su guji jefa kansu cikin halaka ta hanayar barin umarninsa ko aikata abin da ya hana, kamar rowa da ƙin bayar da taimako wajen gina addinin Allah ko ba shi kariya daga maƙiyansa. Ya umarce su su zama masu kyautatawa a ko da yaushe tare da kowa domin Allah yana son mutane masu kyautatawa. An karɓo daga Abu Ayyuba Al-Ansari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mun kasance wata rana a birnin Rum, sai mayaƙan Rumawa masu yawa suka fito mana, sai mayaƙan Musulmi kwatankwacinsu ko fiye da su a yawa su ma suka fita taren su. Uƙba bn Amir yana jagorantar mutanen Misra, mutanen Madina kuwa Fadhalatu bn Ubaid ne yake jagorantar su. Sai wani Musulmi ya kutsa cikin rudunar Rumawa har sai da ya shiga tsakiyarsu, sai Musulmi suka riƙa yi masa hargowa suna cewa, yaya zai jefa kansa cikin halaka? Sai Abu Ayyuba Al-Ansari ya tashi ya ce: “Ya ku mutane, kuna yi wa wannan ayar irin wannan fassarar, alhalin wannan ayar a kanmu mu mutanen Madina ta sauka. Lokacin da Musulunci ya yi ƙarfi ya samu mataimaka da yawa, sai waɗansu daga cikinmu suka riƙa faɗa wa ‘yan’uwansu a ɓoye Annabi (ﷺ) bai sani ba, suna cewa: “Duk mun kashe dukiyoyinmu, ga shi yanzu Musulunci ya yi ƙarfi, kuma masu taimaka masa sun ƙara yawa, me zai hana mu yi zamanmu mu kula da farfaɗo da dukiyoyinmu da suka salwanta?! Sai Allah ya saukar da wannan ayar ga Annabinsa (ﷺ) domin mayar mana da martani a kan abin da muka faɗa wa juna, Allah ya ce: “Ku ciyar don Allah kada ku jefa kawunanku a cikin halaka.” Don haka abin da ake nufi da halaka a nan shi ne, barin fita yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah da zama a gida don kula da dukiya da gyaranta.” Wannan ta sa Abu Ayyuba Al-Ansari bai gushe ba yana fagen fama don ɗaukaka addinin Allah har ya rasu aka binne shi a ƙasar Rumawa.” [Tirmizi #2974, Nasa’i As-Sunan Al-Kubra #11029].
وَأَتِمُّواْ ٱلۡحَجَّ وَٱلۡعُمۡرَةَ لِلَّهِۚ فَإِنۡ أُحۡصِرۡتُمۡ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۖ وَلَا تَحۡلِقُواْ رُءُوسَكُمۡ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡهَدۡيُ مَحِلَّهُۥۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ بِهِۦٓ أَذٗى مِّن رَّأۡسِهِۦ فَفِدۡيَةٞ مِّن صِيَامٍ أَوۡ صَدَقَةٍ أَوۡ نُسُكٖۚ فَإِذَآ أَمِنتُمۡ فَمَن تَمَتَّعَ بِٱلۡعُمۡرَةِ إِلَى ٱلۡحَجِّ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۚ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖ فِي ٱلۡحَجِّ وَسَبۡعَةٍ إِذَا رَجَعۡتُمۡۗ تِلۡكَ عَشَرَةٞ كَامِلَةٞۗ ذَٰلِكَ لِمَن لَّمۡ يَكُنۡ أَهۡلُهُۥ حَاضِرِي ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Open ayah 2:196Kuma ku cika aikin Hajji da umara domin Allah. To idan an tsare ku, sai ku gabatar da abin da ya sawwaƙa na hadaya, kuma kada ku aske kawunanku har sai hadaya ta kai wurin yankanta. To wanda ya kasance a cikinku mara lafiya ko akwai wata cuta a kansa, (idan yayi aski) to sai ya yi fidiya ta (hanyar) yin azumi ko sadaƙa ko yanka. Idan kuwa kun amintu, to duk wanda ya yi tamattu\'i da yin umara tare da Hajji, to sai ya yanka abin da ya sawwaƙa na hadaya; amma wanda bai samu ba, sai ya yi azumin kwana uku a lokacin aikin Hajji, da kuma na kwana bakwai idan kun dawo gida. Waɗannan kwana goma ke nan cikakku. Wannan hukuncin yana ga wanda iyalinsa ba sa cikin hurumin Makka ne. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, ku sani cewa, lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne.
ٱلۡحَجُّ أَشۡهُرٞ مَّعۡلُومَٰتٞۚ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ ٱلۡحَجَّ فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِي ٱلۡحَجِّۗ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ يَعۡلَمۡهُ ٱللَّهُۗ وَتَزَوَّدُواْ فَإِنَّ خَيۡرَ ٱلزَّادِ ٱلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُونِ يَٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Open ayah 2:197(Lokacin) hajji wasu watanni ne sanannu. Don haka duk wanda ya wajabta wa kansa aikin Hajji cikin waɗannan (watanni), to babu maganar saduwa da mace, kuma babu fasiƙanci, kuma babu jayayya a cikin aikin Hajji. Kuma duk abin da kuka aikata na alheri, Allah Yana sane da shi. Kuma ku yi guzuri, amma mafificin guzuri shi ne taƙawa, kuma ku kiyaye dokokina ya ku ma\'abota hankula.
لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَبۡتَغُواْ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكُمۡۚ فَإِذَآ أَفَضۡتُم مِّنۡ عَرَفَٰتٖ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ عِندَ ٱلۡمَشۡعَرِ ٱلۡحَرَامِۖ وَٱذۡكُرُوهُ كَمَا هَدَىٰكُمۡ وَإِن كُنتُم مِّن قَبۡلِهِۦ لَمِنَ ٱلضَّآلِّينَ
Open ayah 2:198Babu wani laifi gare ku ku nemi falala daga Ubangijinku, don haka idan kun gangaro daga Arfa, to ku ambaci Allah a wurin (da ake kira) Mash\'arul Haraam , kuma ku ambace Shi kamar yadda Ya shiryar da ku, ko da yake a da tabbas kun kasance daga cikin ɓatattu.
ثُمَّ أَفِيضُواْ مِنۡ حَيۡثُ أَفَاضَ ٱلنَّاسُ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 2:199Sannan kuma sai ku gangaro ta inda mutane suka gangaro kuma ku nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.
فَإِذَا قَضَيۡتُم مَّنَٰسِكَكُمۡ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَذِكۡرِكُمۡ ءَابَآءَكُمۡ أَوۡ أَشَدَّ ذِكۡرٗاۗ فَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا وَمَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖ
Open ayah 2:200To idan kun gama ayyukanku na Hajji, to ku yi ta ambaton Allah kamar yadda kuke ambaton iyayenku, ko ambaton Allah ya fi yawa. To daga cikin mutane akwai wanda yake cewa: “Ya Ubangijimu, Ka ba mu (rabo) a nan duniya”, kuma a lahira ba shi da wani rabo.
وَمِنۡهُم مَّن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ حَسَنَةٗ وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ
Open ayah 2:201Kuma daga cikinsu akwai wanda yake cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu kyakkyawa a nan duniya, kuma Ka ba mu kyakkyawa a lahira, Ka kuma tsare mu daga azabar wuta.”
أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ نَصِيبٞ مِّمَّا كَسَبُواْۚ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
Open ayah 2:202Waɗannan suna da babban rabo na daga abin da suka aikata, kuma Allah Mai gaggawar hisabi ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin hukunce-hukuncen Hajji da umara a cikinsu, ya umarci waɗanda suka shiga haramin aikin Hajji ko umara da su cika aikinsu da rukunansa da wajibansa, kuma su yi shi don Allah ba don wani ba. Idan wani abu ko wasu suka hana su kaiwa ga Ɗakin Allah, kamar tsoro ko rashin lafiya ko wani dalili daban, to sai su yanka abin da Allah ya hore musu na raƙuma ko shanu ko tumaki. Kuma ya umarce su da kada su cire haraminsu idan wani abu ya tsare su har sai abin hadayarsu ya kai ga isa wurin da aka tsare su. Idan kuma ba wanda aka tsare ba ne to zai yanka hadayarsa ne a Haramin Makka. Idan na Hajji ne zai yanka shi ranar salla, wato goma ga Zulhijja. Wanda ya haɗu da rashin lafiya ko kwarkwata ta dame shi a kansa ya zama cikin buƙatar ya aske kansa, to yana iya askewa, to amma bayan ya aske zai yi azumin kwana uku, ko ya ciyar da miskini shida kowane cikinsu ya ba shi rabin mudu ko ya yanka akuya. Idan matsala ta kau ta rashin samun shiga garin Makka, maniyyata suka samu isa Ɗakin Allah to duk wani maniyyaci da ya ɗauko umara kaɗai ya gama ta kuma yana niyar zai shiga aikin Hajji, to wajibi ne zai yi hadaya da abin da Allah ya hore masa cikin raƙuma ko shanu ko ƙananan dabbobi. Hakanan hukuncin yake ga mutumin da ya yi hajjin Ƙirani , wato ya haɗa umara da Hajji a niyya ɗaya. Idan kuwa wani ba shi da ikon yin yanka na hadaya to sai ya yi azumin kwana uku a lokacin Hajji, sannan bayan ya gama aikin hajjinsa ya dawo garinsu sai ya yi azumin kwana bakwai. To wannan hukunci da aka ambata a nan ya shafi wanda ba mazaunin garin Makka ba ne, domin su ba su da hukuncin Hajji na Tamattu’i . Sannan sai Allah ya yi umarnin da yin taƙawa ta hanyar aikata abin da aka wajabta masa da kuma barin abin da aka hana shi, kuma ya tunatar da bayinsa cewa, su sani shi mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya saɓa masa, ya aikata abin da ya hana. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana watannin Hajji da cewa, watanni ne sanannu, watau watan Shawwal, Zulƙi’ida da Zulhijja. To duk wanda ya ƙulla niyyar Hajji a cikin waɗannan watanni, dole ne ya nisanci kusantar mata da maganganu na kwarkwasa, ya nisanci duk wani aikin saɓon Allah, wanda ya haɗa har da abubuwan da aka hana shi aikata su lokacin da yake cikin harami, da zagin Musulmi, ya kuma guji jayayya ba bisa gaskiya ba. Annabi (ﷺ) yana cewa: “Duk wanda ya yi Hajji don Allah, bai yi batsa ba, bai yi fasiƙanci ba, to zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” [Bukhari #1521, da Muslim #1350]. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya kwaɗaitar da su kan aikin alheri ya bayyana musu cewa, duk abin da bayinsa suka gabatar na alheri kaɗan ne ko mai yawa, to za su ga sakamakonsa a wurin Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci masu zuwa Hajji da su yi guzuri na abin da za su buƙata a wannan tafiyar tasu domin kada su je suna roƙon mutane abin hannunsu. To amma duk da haka sai Allah ya nuna musu cewa guzurin da ya fi kowane muhimmanci shi ne guzurin taƙawa domin ita ce abincin zukata, da ita ne ake samun jin daɗi na har abada. Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mutanen Yamen sun kasance suna zuwa aikin Hajji ba guzuri, sai su ce su masu dogaro ga Allah ne. amma idan sun iso garin Makka sai su riƙa roƙon mutane. Sai Allah ya saukar da faɗarsa: (kuma ku yi guzuri, amma mafificin guzuri shi ne taƙawa).” Sannan Allah ya umarci masu hankali da ita wannan taƙawar domin su ne suka san amfaninta da muhimmancinta fiye da kowa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin wasu daga cikin ayyukan Hajji. Allah ya bayyana wa mahajjata cewa, babu laifi don sun zo aikin Hajji sun yi wani abu na kasuwancinsu. Abdullah ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Akwai wasu kasuwanni da suke ci tun a lokacin jahiliyya a lokacin aikin Hajji watau kasuwar Ukaza da Majanna da kuma Zulmajaz. Lokacin da Musulunci ya zo sai Musulmi suka riƙa jin kamar laifi ne su ci gaba da cin waɗannan kasuwanni a lokutan aikin Hajji, sai Allah ya saukar da wannan ayar.” [Bukhari #2050]. Ya umarci mahajjata idan sun baro Arfa sun iso Muzdalifa su ambaci Allah a wurin. Wannan ambaton Allah da aka yi umarni da shi a nan ya ƙunshi har da salla da addu’a a wurin. Kuma su ambace shi, su tuna shiriyar da ya yi musu ta hanya madaidaiciya bayan a da sun kasance a cikin mabayyaniyar ɓata. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Ƙuraishawa waɗanda ba sa yin tsayuwar Arfa kamar yadda sauran ƙabilu suke tsayuwa, watau iyakarsu Muzdalifa sai su juyo. Sai Allah ya umarce su a nan cewa, su ma su je su tsaya a Arfa tare da sauran mutane sannan idan lokacin barin Arfa ya yi su shigo tare da sauran jama’a su taho Muzdalifa. Allah kuma ya umarci alhazai da su nemi gafarar Allah a kan zunubansu, domin shi Allah mai yin gafara ne ga duk wanda ya neme ta a wajensa mai rahama ne ga bayinsa muminai. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci alhazai da cewa, idan sun kammala ayyukan hajjinsu sun sauke harami, to su yawaita ambaton Allah (Mai tsarki da daukaka),kamar yadda suke ambaton iyayensu, kai su ambace shi fiye ma da yadda suke ambaton iyayensu. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci alhazai da yawan ambatonsa sai kuma ya umarce su da addu’a domin wannan lokaci ne da ya dace a karɓa addu’o’insu. Sannan Allah ya zargi wanda idan yana addu’a duniya kaɗai yake roƙa, ba shi da wani rabo a lahira. Sai kuma ya yabi muminai masu roƙon Allah ya ba su alherin duniya da na lahira, kuma ya kare su daga azabar wuta ta lahira. To irin waɗannan bayi na Allah su ne suke samun babban sakamako a kan aikinsu na Hajji da suka yi, sannan a lahira Allah ya datar da su samun alherin da suka roƙa. Allah mai gaggawa ne wajen lissafin ayyukan bayinsa kuma mai gaggawa ne wajen yi musu sakamako. Daga nan sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mahajjata da yin kabarbari a ranakun zaman Mina, wato “Ayyamut tashriƙ ”, waɗanda su ne ranar sha ɗaya da sha biyu da sha uku na watan Zulhijja. Waɗannan kabarbari sun haɗa har da kabbarar ranar sallar layya, sannan da sauran kabarbari a sauran kwanaki na lokuta daban-daban. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa babu laifi a kan mahajjaci ya bar Mina a rana ta goma sha biyu ko ya jinkirta fita har zuwa rana ta goma sha uku domin ya yi jifa a wannan ranar, duk mutum na da zaɓi a nan, matuƙar dai ya kiyaye dokokin Allah ya aikata abin da ya umarce shi da shi ya kauce wa abin da ya hana shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wasiyya ga bayinsa da taƙawa, kuma su tabbatar da cewa, za a taru a gabansa ranar gobe ƙiyama domin yi musu hisabi.
۞وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن تَعَجَّلَ فِي يَوۡمَيۡنِ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِ وَمَن تَأَخَّرَ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۖ لِمَنِ ٱتَّقَىٰۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
Open ayah 2:203Kuma ku ambaci Allah a cikin wasu kwanaki ƙididdigaggu. To duk wanda ya yi gaggawar (barin Mina) cikin kwana biyu, to babu laifi a gare shi; wanda kuwa ya yi jinkiri, to babu laifi a gare shi, (amma dukkansu) ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani cewa, zuwa gare Shi za a tattara ku.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُعۡجِبُكَ قَوۡلُهُۥ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيُشۡهِدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا فِي قَلۡبِهِۦ وَهُوَ أَلَدُّ ٱلۡخِصَامِ
Open ayah 2:204Kuma daga cikin mutane akwai wanda zancensa yake burge ka a rayuwar duniya, kuma yana shaidar da Allah ga abin da yake cikin zuciyarsa, alhali kuwa shi mai tsananin husuma ne.
وَإِذَا تَوَلَّىٰ سَعَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيُفۡسِدَ فِيهَا وَيُهۡلِكَ ٱلۡحَرۡثَ وَٱلنَّسۡلَۚ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلۡفَسَادَ
Open ayah 2:205Kuma idan ya juya baya, zai yi ta yawo a cikin ƙasa don ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya lalata amfanin gona da dabbobi. Allah kuwa ba ya son ɓarna.
وَإِذَا قِيلَ لَهُ ٱتَّقِ ٱللَّهَ أَخَذَتۡهُ ٱلۡعِزَّةُ بِٱلۡإِثۡمِۚ فَحَسۡبُهُۥ جَهَنَّمُۖ وَلَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ
Open ayah 2:206Idan kuma aka ce masa: “Ka kiyaye dokokin Allah” sai girman kai ya kama shi saboda saɓo. To Jahannama ta ishe shi (makwanci), kuma lalle tir da wannan makwanci.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشۡرِي نَفۡسَهُ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ رَءُوفُۢ بِٱلۡعِبَادِ
Open ayah 2:207Kuma daga cikin mutane akwai wanda yake sayar da kansa don neman yardar Allah. Allah kuwa Mai yawan tausayi ne ga bayi. A waɗannan ayoyi bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin halin muminai masu yawan ambaton Allah a ko da yaushe da kuma waɗanda babu Allah a cikin lamuransu sai duniya kaɗai, sai kuma Allah ya zo da bayanin wani rukuni na mutane waɗanda maganganunsu suke ba ka sha’awa saboda fasaharsu da yadda suke sarrafa zance, musamman cikin abin da ya shafi sha’anin duniya ban da na lahira, ko kuma idan suna magana a kan taimaka wa Musulunci da Musulmai da son Manzon Allah (ﷺ), sai ka ji kamar da gaske, sai dai magana ce kawai ta fatar baki ba ta je har zuci ba. Za ka ga ɗayansu ma wani lokaci kwalliyar maganar ma ita kaɗai ba ta ishe shi ba sai ya haɗa da ƙarfafa ta da cewa, ai Allah ma ya san abin da yake faɗa ɗin nan gaskiya ce, alhalin ya san shi maƙaryaci ne mai tsananin jayayya da husuma. Idan ya fita ya bar majalisin Annabi (ﷺ) sai ya fara nuna haƙiƙanin halayensa marasa kyau da muguwar aƙidar zuciyarsa ya yi ta ƙoƙari da kazar-kazar wajen yaɗa ɓarna a doron ƙasa, ta hanyar yaɗa kafirci da munafinci da zalunci da ayyukan ta’addanci kamar fashi da makami da tsorata bayin Allah da lalata shuke-shuke da kashe dabbobi da sauran abin da rayuwa ba za ta tafi ba sai da su. Idan ya samu ya ci nasara shi ke nan ya karya tsarin rayuwa gaba ɗaya ke nan; wannan kuma da ma shi ne burinsa. Kamar kuma yadda idan ya yaɗa ɓarna ta kafirci da saɓon Allah da zalunci a ƙasa hakan zai yi sanadiyyar Allah ya hana ruwan sama, sai a shiga fari shuka ta lalace, dabbobi ma su yi ta mutuwa. Wannan kuwa shi ne sakamakon irin aikinsa, domin Allah ba ya son ɓarna, don haka ba ya son maɓarnata ko da kuwa maganganunsu na ba wa mutane sha’awa. Mutum munafiki irin wannan duk lokacin da masu wa’azi suka yi masa wa’azi, suka neme shi da ya ji tsoron Allah, ya bar irin waɗannan miyagun laifuka da yake yi, to maimakon ya ji nasiharsu ya ɗauka, sai kawai ya kama nuna musu girman kai, laifinsa ya fi ƙarfinsa a madadin ya daina sai ma dai ya ƙara ci gaba, to irin wannan mutum ba wani sakamako da ya dace da shi sai wutar Jahannama, ita ce za a yi masa shimfiɗa da ita ranar alƙiyama. Tir da irin wannan shimfiɗa. A ɓangare guda kuma akwai wasu mutane waɗanda su kuma suna sayar da rayukansu ga Allah domin su sami yardarsa, Allah kuma mai tausayi ne ga bayinsa, masu irin wannan hali nagari, shi ya sa ya hore musu shiriyarsu da kimsa musu imani a zukatansu.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱدۡخُلُواْ فِي ٱلسِّلۡمِ كَآفَّةٗ وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Open ayah 2:208Ya ku waɗanda suka yi imani, ku shiga cikin addinin Musulunci gaba ɗaya, kuma kar ku bi hanyoyin Shaiɗan. Lalle shi maƙiyi ne a gare ku, mai bayyana (ƙiyayya).
فَإِن زَلَلۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡكُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Open ayah 2:209To idan kuka zame bayan hujjoji bayyanannu sun zo muku, to ku sani cewa, lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن يَأۡتِيَهُمُ ٱللَّهُ فِي ظُلَلٖ مِّنَ ٱلۡغَمَامِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Open ayah 2:210Shin ko akwai abin da suke jira ne, in ban da Allah Ya zo musu a cikin waɗansu inuwoyi na gizagizai da mala\'iku, sai a zartar da al\'amari? Kuma zuwa ga Allah ne ake mayar da al\'amura.
سَلۡ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ كَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُم مِّنۡ ءَايَةِۭ بَيِّنَةٖۗ وَمَن يُبَدِّلۡ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Open ayah 2:211Ka tambayi Banu Isra\'ila, sau nawa Muka ba su wata aya bayyananniya? Kuma duk wanda ya musanya ni\'imar Allah bayan ta zo masa, to lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne.
زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَيَسۡخَرُونَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۘ وَٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ وَٱللَّهُ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ
Open ayah 2:212An ƙawata wa kafirai rayuwar duniya, kuma suna yin izgili ga waɗanda suka yi imani. Waɗanda kuwa suka yi taƙawa su ne a samansu a ranar alƙiyama. Kuma Allah Yana arzurta wanda ya ga dama, ba tare da lissafi ba.
كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَمَا ٱخۡتَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۖ فَهَدَى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ مِنَ ٱلۡحَقِّ بِإِذۡنِهِۦۗ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٍ
Open ayah 2:213Mutane sun kasance al\'umma guda ɗaya, sai Allah Ya aiko da annabawa, suna masu albishir, kuma masu gargaɗi, kuma Ya saukar da littafi tare da su da gaskiya, don ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka yi saɓani a kansa. Kuma ba wasu ne suka yi saɓani a kansa ba sai waɗanda aka ba wa shi, bayan hujjoji bayyanannu sun zo musu, don zalunci a tsakaninsu; sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi imani ga abin da (mutane) suka yi saɓani cikinsa na gaskiya da izininsa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.
أَمۡ حَسِبۡتُمۡ أَن تَدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ وَلَمَّا يَأۡتِكُم مَّثَلُ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِكُمۖ مَّسَّتۡهُمُ ٱلۡبَأۡسَآءُ وَٱلضَّرَّآءُ وَزُلۡزِلُواْ حَتَّىٰ يَقُولَ ٱلرَّسُولُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ مَتَىٰ نَصۡرُ ٱللَّهِۗ أَلَآ إِنَّ نَصۡرَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ
Open ayah 2:214Shin kun yi tsammanin za ku shiga Aljanna ne, alhalin misalin irin abin da ya shafi waɗanda suka shuɗe gabaninku bai zo muku ba? Tsananin talauci da cuta sun shafe su; kuma an girgiza su sosai, har Manzo da waɗanda suka yi imani tare da shi suka riƙa cewa: “Yaushe ne nasarar Allah za ta zo?” Ku saurara, lalle nasarar Allah a kusa take. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffofin rukunai daban-daban na mutane, kama daga ‘yan duniya waɗanda babu abin da suka sa a gaba sai neman ta ido rufe zuwa ga munafuƙai masu nuna imani da ƙaunar Allah a baki, amma in sun koma gefe ban da ɓarna babu abin da suka sa a gaba, sai kuma muminai na gaskiya masu tsoron Allah da neman yardarsa. A waɗannan ayoyi kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo muminai gaba ɗaya yana umartar su da shiga Musulunci gaba ɗaya, wato su yi aiki da duk shari’un Musulunci. Yana yi musu gargaɗi kada su bi tafarkin Shaiɗan domin shi maƙiyansu ne na ɓoye da sarari, don haka yi masa biyayya yana nufin aukawarsu cikin halaka; idan suka kuskura har suka aikata ayyukan da suka saɓawa koyarwar Musulunci da gangan, to su sani cewa, babu wani abu da zai gagari Allah (Mai tsarki da daukaka) don haka shi mai iya hukunta su ne, domin ƙarfinsa ya fi na kowa da komai, wanda duk ya cancanci azaba Allah zai yi masa azabar da ta dace da shi domin ayyukansa gaba ɗaya suna tare da hikima, Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana inkarinsa ga waɗanda suka kauce wa hanyar gaskiya bayan sun ga hujjoji bayyanannu. Wannan abu da suka yi yana nuna kawai suna jiran lokacin halaka su ne ya zo, wato lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) zai zo ranar gobe ƙiyama tare da mala’iku, domin ya zartar musu hukunci na adalci, ya yi sakayya ga waɗanda suka kafirta a nan duniya; wannan kuwa ita ce halaka ta haƙiƙa. Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Allah zai tattara mutanen farko da na ƙarshe a ranar gobe ƙiyama har tsawon shekara arba’in idanuwansu bubbuɗe suna kallon sama, suna jiran a yanke musu hukunci, sai Allah ya sauko daga Al’arshi zuwa Kursiyyi cikin inuwoyi na girgije” [Dubi: Aɗɗabarani, Al-Mu’jamul Kabir #9763, Ad-Daraƙuɗuni, Ru’yatullahi #163, Ibn Nasr, Ta’azimu Ƙadris Salat #278]. Azzahabi da Ibnul Ƙayyim da Albani sun tabbatar da wannan hadisin [Dubi: Kitabul Arsh , Shafi na 76, Hadil Arwah , Shafi na 262, Sahihut-Targib #3591]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa (ﷺ) da ya tambayi Yahudawa game da abin da Allah ya ba su na hujjoji bayyanannu da mu’ujizozi masu yawa waɗanda suka tabbatar da gaskiyar annabawa da manzanni da Allah ya aiko musu, amma duk da haka sai suka riƙa ƙaryata wasu annabawan, suka riƙa kafirce musu suna juya wa waɗannan hujjoji da ayoyi baya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawarin narko da uƙuba ga duk wanda ya zaɓi kafirci a maimakon ni’imar Musulunci bayan ya zo masa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, an ƙawata ni’imomin duniya a idanuwan kafirai da zukatansu, sun kuma yarda da ita sun fifita ta a kan ni’imar lahira, suna kuma yi wa muminai izgili wai don ganin su ba su ɗauki ƙyale-ƙyalen duniya a bakin komai ba. Sun manta cewa, fifiko na haƙiƙa da ɗaukakar daraja ta gaskiya ita ce ta ranar lahira. Ai waɗanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari a nan duniya su za su zama a sama da duk wani kafiri, domin Allah zai ba su gidan Aljanna, ya ba su duk abin da suke sha’awa a cikinta, yayin da su kuma kafirai ‘yan ƙyale-ƙyale za su kasance a gidan wutar Jahannama cikin azaba marar ƙaƙƙautawa kuma ta har abada. Allah yana ba wa muminai falalarsa a Aljanna ba tare da lissafi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, mutane tun daga zamanin Annabi Adamu suke bautar Allah a kan addini guda ɗaya, shi ne Musulunci, haka suka rayu tsawon ƙarni goma a jere. Daga bisani sai saɓanin addini ya shigo su har ta kai sun koma bautar gumaka, daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko annabawansa suka riƙa hana mutane bautar wanin Allah, suna umartar su da bautar Allah shi kaɗai, suna yin albishir da ni’imar Aljanna ga duk wanda ya bi su, suna gargaɗi da wuta ga duk wanda ya saɓa musu. Na farkon waɗannan annabawa da Allah ya aika shi ne Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya saukar wa waɗannan annabawan da littattafai waɗanda suka ƙunshi labarai na gaskiya da dokoki na adalci don su yi hukunci da su a tsakanin mutanensu game da duk wani abu da suke jayayya a kansa, domin gaskiya ta bayyana a san ta, ƙarya ma ta fito a gane ta, a gane daidai a gane kuskure; daga nan hujjar Allah ta tsayu a kan bayinsa. To amma duk da cewa littattafan da Allah ya saukar, ya saukar da su ne don kan jama’a ya haɗu a kan aiki da gaskiyar da suka ƙunsa, to sai ga shi wasu sun saɓa wa muradin Ubangiji, suka sassaɓa a kan littattafan su kansu, wasu suka yarda da su suka yi imani da gaskiyar da take cikinsu, da yawa kuma suka ƙi yarda, suka ma ƙaryata gaskiyar da ta zo cikinsu, bayan dukansu sun samu hujjoji masu yanke shakku a kan ingancinsu. Kuma babban abin da ya jawo musu wannan saɓani shi ne samun wasunsu suna zaluntar wasu; to sai Allah ya shiryar da muminai zuwa ga bin miƙaƙƙiyar hanya, ya datar da su suka rungumi gaskiya suka riƙe ta ƙam-ƙam. Haka Allah yake shiryar da duk wanda ya ga dama cikin bayinsa ya nuna masa gaskiya ya ba shi ikon bin ta. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin irin yadda al’ummomin baya suka sassaɓa wa annabawansu, suka saki gaskiya suka kama ƙarya, ya kuma shiryar da muminai bin tafarki madaidici, to sai kuma ya bayyana musu cewa, bin wannan hanya miƙaƙƙiya yana tattare da wasu wahalhalu da jarraba iri-iri, don haka al’amarin yana buƙatar haƙuri da juriya. Allah ya faɗa wa muminai cewa, kada su yi tsammanin cewa, wannan hanya mai sauƙi ce, a’a cike take da matsaloli da wahalhalu iri-iri. Al’ummomin da suka gabata sun ɗanɗani tsananin talauci da rashi da cututtuka iri-iri; maƙiyansu suka tayar musu da hankali matuƙa gaya, har sai da lamarin ya kai manzannin da muminai suna tambayar juna: Yaushe ne taimakon Allah zai zo, domin su samu su fita daga wahalhalun da suke ciki? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, nasarar Allah tana nan tafe kusa ba daɗewa, domin ko mene ne ya yi tsanani to sauƙi yana nan tare da shi, kamar yadda Allah ya ambata a Suratus Sharhi , aya ta 5-6.
يَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَۖ قُلۡ مَآ أَنفَقۡتُم مِّنۡ خَيۡرٖ فَلِلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٞ
Open ayah 2:215Suna tambayar ka, me za su ciyar ne? Ka ce: “Duk abin da za ku ciyar na alheri, to ga mahaifa da dangi mafiya kusanci da marayu da miskinai da matafiyi. Kuma duk abin da kuka aikata na alheri, to lalle Allah Yana sane da shi.”
كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ وَهُوَ كُرۡهٞ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰٓ أَن تَكۡرَهُواْ شَيۡـٔٗا وَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰٓ أَن تُحِبُّواْ شَيۡـٔٗا وَهُوَ شَرّٞ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:216An wajabta muku yaƙi (ku muminai), ga shi kuwa kuna ƙin sa, kuma zai iya yiwuwa ku ƙi wani abu alhalin shi alheri ne a gare ku, kuma zai iya yiwuwa ku so wani abu alhalin shi sharri ne a gare ku. Kuma Allah Shi yake da sani, ku ba ku sani ba.
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلشَّهۡرِ ٱلۡحَرَامِ قِتَالٖ فِيهِۖ قُلۡ قِتَالٞ فِيهِ كَبِيرٞۚ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَكُفۡرُۢ بِهِۦ وَٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَإِخۡرَاجُ أَهۡلِهِۦ مِنۡهُ أَكۡبَرُ عِندَ ٱللَّهِۚ وَٱلۡفِتۡنَةُ أَكۡبَرُ مِنَ ٱلۡقَتۡلِۗ وَلَا يَزَالُونَ يُقَٰتِلُونَكُمۡ حَتَّىٰ يَرُدُّوكُمۡ عَن دِينِكُمۡ إِنِ ٱسۡتَطَٰعُواْۚ وَمَن يَرۡتَدِدۡ مِنكُمۡ عَن دِينِهِۦ فَيَمُتۡ وَهُوَ كَافِرٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 2:217Suna tambayar ka game da wata mai alfarma, yin yaƙi a cikinsa. Ka ce: “Yaƙi a cikinsa, babban laifi ne, amma hana (mutane) bin tafarkin Allah da kafirce masa da kuma (hana mutane shiga) Masallaci mai alfarma da fitar da mutanensa daga gare shi, su ne mafi girman laifi a wajen Allah. Kuma (laifin) fitina ya fi na kisa girma.” Kuma (kafirai) ba za su gushe ba suna yaƙar ku, har sai sun raba ku da addininku, idan da za su sami dama. Kuma duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, kuma ya mutu yana kafiri, to waɗannan ayyukansu sun lalace a duniya da lahira, kuma waɗannan su ne ma\'abota wuta, suna masu dawwama a cikinta.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أُوْلَٰٓئِكَ يَرۡجُونَ رَحۡمَتَ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 2:218Lalle waɗanda suka yi imani da kuma waɗanda suka yi hijira, kuma suka yi jihadi don Allah, waɗannan su ne suke fatan rahamar Allah; Allah kuwa Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.
۞يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡخَمۡرِ وَٱلۡمَيۡسِرِۖ قُلۡ فِيهِمَآ إِثۡمٞ كَبِيرٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَإِثۡمُهُمَآ أَكۡبَرُ مِن نَّفۡعِهِمَاۗ وَيَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَۖ قُلِ ٱلۡعَفۡوَۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 2:219Suna tambayar ka game da giya da caca. Ka ce: “A cikin lamarinsu akwai zunubi mai girma da kuma waɗansu amfanunnuka ga mutane. Amma zunubinsu ya fi amfaninsu girma” Kuma suna tambayar ka, me za su ciyar? Ka ce: “Abin da ya daɗu a kan buƙatunku.” Kamar haka ne Allah Yake muku bayanin ayoyi don ku yi tunani.
فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۗ وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡيَتَٰمَىٰۖ قُلۡ إِصۡلَاحٞ لَّهُمۡ خَيۡرٞۖ وَإِن تُخَالِطُوهُمۡ فَإِخۡوَٰنُكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ ٱلۡمُفۡسِدَ مِنَ ٱلۡمُصۡلِحِۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَعۡنَتَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 2:220Game da lamarin duniya da lahira. Kuma suna tambayar ka game da marayu. Ka ce : “Inganta musu dukiyarsu shi ne mafi alheri, kuma in kuka haɗa cimakarku da tasu, to ai \'yan’uwanku ne. Amma fa Allah Ya san mai son yin ɓarna daga wanda yake son yin gyara. Kuma da Allah Ya ga dama da Ya ƙuntata muku. Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Musulmin farko (sahabbai) suka riƙa yin tambayoyi game da sha’anin addininsu da rayuwarsu domin su dace da aƙidarsu ta Musulunci. Kamar yadda ayoyin suka yi bayanin wasu tambayoyi da suka riƙa tasowa saboda surutai da soke-soke na Yahudawa da munafuƙai da mushrikai a kan wasu al’amura, wannan ya sa Musulmi suka riƙa yin tambayoyi a kai domin su sami yaƙini game da waɗannan al’amura. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, sahabbansa suna yi masa tambaya game da abin da za su ciyar, mene ne shi? Kuma ya ya gwargwadon yawansa? Kuma ta yaya za su fitar da shi? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya amsa musu cewa, abin da duk za su ciyar ba a ƙayyade shi da wani jinsin dukiya ko wani gwargwado na musamman ba; duk abin da Allah ya hore wa mutum yana iya sadaka da shi, kaɗan ne ko mai yawa. Amma kuma waɗanda ya fi cancanta ya fara da su su ne waɗanda suka fi kusanci da shi, wato iyalansa sannan sauran danginsa gwargwadon kusancin kowane, sannan waɗanda suka fi buƙata cikin al’umma, kamar marayu sannan mabuƙata waɗanda ba su da abin da zai riƙe su, sannan matafiyi wanda guzurinsa ya ƙare, a taimaka masa da abin da zai maida shi garinsu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk abin da za su yi na kyautatawa ko na alheri to ba zai ɓoyu ba a wajen Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sane da shi kuma zai yi sakayya gwaggwaɓa a kansa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin farlanta wa bayinsa muminai fita yaƙi, duk da cewa ya san ba sa son hakan, saboda abin da yaƙi ya gada na salwantar rayuka da dukiya da lafiya da abin da yake tattare da shi na tsoro da fargaba. To amma idan an dubi abin ta wani ɓangare akwai alheri mai yawa a cikinsa, domin yana tare da murƙushe abokan gaba da samun nasara a kansu ko mutuwar shahada ga wanda Allah ya ƙaddara mutuwarsa a yaƙin, da kare addini da mutunci da ƙasa da koyar da maƙiya darasi, da sauran al’amura na maslaha waɗanda sun zarce zama ba tare da fita yaƙin ba. Haka kuma duk inda ayyukan alheri suke suna tattare da abin da zukata ba sa so, to amma alherin cikinsu mai yawa ne. Hakanan ayyukan sharri suna tattare da abin da zukata ke ƙauna, amma sharrinsu mai yawa ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ne kawai ya san abin da zai amfanar da al’umma da kuma marar amfani gare su. Don haka sai su bi umarninsa su kuma yi aiki da shari’arsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, sahabbansa suna tambayar sa a kan hukuncin yaƙi a cikin watanni masu alfarma. Sai kuma ya faɗa masa amsar da zai ba su, da cewa, yaƙi a waɗannan watanni babban lamari ne, sai dai kuma abin da mushrikai suke yi na hana mutane shiga addinin Allah da kafirce wa Allah da hana muminai zuwa Ɗakin Allah mai alfarma da ke Makka da korar muminai da suke wannan gari na Makka; waɗannan ayyuka da suke yi sun fi yaƙi a watanni masu alfarma girman zunubi a wurin Allah. Duk waɗannan ayyuka na mushrikai fitina ce wadda ta fi tsananin muni a wurin Allah fiye da kisan da Musulmi suka yi a cikin wata mai alfarma. Dalilin saukar wannan aya kuwa shi ne, wata rana Annabi (ﷺ) ya aika da wata ƙaramar runduna ƙarƙashin jagorancin Abdullahi ɗan Jahshi, sai suka gamu da wani mushriki ana ce masa Ibnul Hadhrami, sai suka kashe shi, ba su san cewa a watan Rajab suke ba. Sai mushrikai suka riƙa faɗa wa Musulmai cewa: “Kun yi kisa a cikin wata mai alfarma”. Sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Suna tambayar ka game da wata mai alfarma, yin yaƙi a cikinsa.” Daga nan sai kuma wasu suka riƙa cewa: “Ko ba su da laifi, to amma kuma ba su da lada.” Sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Lalle waɗanda suka yi imani da kuma waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihadi don yaɗa kalmar Allah, waɗannan su ne suke fatar samun rahamar Allah; Allah kuwa mai yawan gafara ne mai yawan jin ƙai.” [An-Nasa’i, As-Sunan Al-Kubra #8803, Abu Ya’ala #1534, At-Tabarani #1670]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Musulmi irin mummunar ƙiyayyar kafirai a gare su saboda addininsu, kuma ba za su gushe ba suna yaƙar su ta hanyoyi daban-daban domin cim ma manufarsu wadda ita ce su raba su da addininsu su mayar da su kafirai irinsu idan har za su samu wannan damar. To amma har abada ba za su samu ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk Musulmin da ya yi ridda ya bar addininsa har ya mutu bai tuba ba, to duk ayyukan ibada da na alheri da ya taɓa yi sun rushe, ba wani aikin da zai samu ladansa a wurin Allah, kuma ya zama ɗan wuta mai dawwama a cikinta har abada. To amma waɗanda suka miƙa wuya ga gaskiya, suka yi imani, suka yi hijira daga garuruwansu don tsira da addininsu, sannan suka yaƙi maƙiya Allah don taimakon addininsu da ɗaukaka kalmar Allah (Mai tsarki da daukaka); to waɗannan su ne suke sa ran samun rahamar Allah da Karramawarsa, kuma lalle Allah zai girmama su ya ba su ladan da suke fatan su samu a wurinsa, saboda shi Allah mai yafe zunubbai ne, mai rahama ne ga bayinsa, yana musu gwaggwaɓar sakayya a kan ayyukansu, a duniya da lahira. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, sahabbansa suna tambayar sa hukuncin shan kayan sa maye da hukuncin caca; sai ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa, game da ta’ammuli da kayan maye da caca akwai ɓarna mai yawan gaske da laifuka masu girma; saboda abin da suke haifarwa a tsakanin jama’a na gaba da ƙiyayya da hana ambaton Allah da tsayar da salla. Sannan kuma ta gefe guda akwai amfani ga mutane masu ta’ammuli da su, kamar abin da giya take haifar wa da mashayinta na manta duk wata damuwarsa ta rayuwa ko dukiyar da masu caca suke samu ta hanyarta. Sai dai idan an kwatanta tsakanin amfaninsu da ɓarnar da suke haifarwa da irin zunuban da suke tattare da su babu shakka ɓarnar ta zarce amfanin nesa ba kusa ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, sahabbai suna yi masa tambaya game da abin da za su bayar sadaka daga cikin dukiyoyinsu, sai ya umarce shi da ya amsa musu da cewa, su ciyar da abin da ya yi saura a kan buƙatunsu na yau da gobe. Hakanan ya faɗa masa cewa, suna yi masa tambaya game da dukiyar marayu da take zama a hannuwansu, yaya ya kamata su mu’amalance ta don kada su faɗa cikin matsala. Sai ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa, babban abin buƙata dangane da dukiyar maraya shi ne kulawa da ita da haɓaka ta. To idan sun yi hakan ba tare da sun karɓi komai na lada daga wurinsu ba, wannan suna da lada mai girma a wurin Allah. Idan kuma sun ɗauki wani abu na ladan wahalarsu wajen juya dukiyar can, kamar su haɗa cimarsu tare da ta marayu ko su riƙa cirar wani abu daga ribar dukiyar gwargwadon wahalarsu, to wannan ma ya halatta, amma da sharaɗin kada su cuci marayun, domin su nan ‘yan’uwansu ne na addini, ɗan’uwa kuwa yana iya haɗa cimarsa da ta ɗan’uwansa babu wata damuwa ga yin haka. Amma duk da haka kada su manta da cewa, Allah yana nan yana sa ido a kan duk abin da suke yi; wanda duk yake da mummunan nufin lalata dukiyar maraya da cinye masa ita, Allah yana sane da shi, hakanan wanda yake da kyakkyawar niyyar taimaka wa maraya da gyara masa dukiyarsa shi ma Allah yana sane da shi, kuma zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa da niyyarsa. Wannan hukunci da wannan sauƙi daga Allah ne domin ya sauƙaƙa wa bayinsa ya kawar musu da duk wani abu da zai ƙuntata musu. Da Allah ya ga dama da sai ya jefa su cikin ƙunci da wahala domin Allah mabuwayi ne babu abin da zai gagare shi, amma kuma mai hikima ne yana sanya komai a muhallinsa da ya dace da shi. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Yayin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Kada ku kusanci dukiyar maraya sai ta hanyar da take mafi kyau”, da kuma faɗarsa: “Lalle waɗanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci….” sai duk wani mai maraya a ƙarƙashinsa ya koma gida, ya raba abincinsa da abin shansa da na maraya, idan ya ci abinci ya rage sai ya ajiye masa har sai ya cinye ko ya lalace. To wannan al’amari ya dami sahabbai, sai suka sanar da Annabi (ﷺ) halin da suke ciki, sai Allah ya saukar da wannan ayar: (kuma suna tambayar ka game da marayu. Ka ce: “Inganta musu dukiyarsu shi ne mafi alheri, kuma in kuka haɗa cimarku da tasu to ai ‘yan’uwanku ne.” Daga lokacin sai suka dinga haɗa abincinsu da abin shansu da nasu). [Abu Dawud #2871, da Ahmad #3002].
وَلَا تَنكِحُواْ ٱلۡمُشۡرِكَٰتِ حَتَّىٰ يُؤۡمِنَّۚ وَلَأَمَةٞ مُّؤۡمِنَةٌ خَيۡرٞ مِّن مُّشۡرِكَةٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَتۡكُمۡۗ وَلَا تُنكِحُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَتَّىٰ يُؤۡمِنُواْۚ وَلَعَبۡدٞ مُّؤۡمِنٌ خَيۡرٞ مِّن مُّشۡرِكٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَكُمۡۗ أُوْلَٰٓئِكَ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلنَّارِۖ وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱلۡجَنَّةِ وَٱلۡمَغۡفِرَةِ بِإِذۡنِهِۦۖ وَيُبَيِّنُ ءَايَٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 2:221Kuma kada ku auri mata mushirikai har sai sun yi imani, kuma lalle baiwa mumina ta fi \'ya mushirika alheri, ko da (mushirikar) ta burge ku. Kuma kada ku aurar wa mushirikai har sai sun yi imani; kuma lalle bawa mumini ya fi (ɗa) mushiriki alheri, ko da ya burge ku. Su waɗancan (kafirai), suna kira ne zuwa ga wuta, Allah kuwa Yana kira ne zuwa ga Aljanna da gafara da izininsa, kuma Yana bayyana ayoyinsa ga mutane don su wa\'azantu.
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡمَحِيضِۖ قُلۡ هُوَ أَذٗى فَٱعۡتَزِلُواْ ٱلنِّسَآءَ فِي ٱلۡمَحِيضِ وَلَا تَقۡرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطۡهُرۡنَۖ فَإِذَا تَطَهَّرۡنَ فَأۡتُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَكُمُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلتَّوَّٰبِينَ وَيُحِبُّ ٱلۡمُتَطَهِّرِينَ
Open ayah 2:222Kuma suna tambayar ka game da jinin haila. Ka ce: “Shi cuta ne, don haka ku ƙaurace wa mata a (kwanakin) haila, kuma kada ku kusance su har sai sun tsarkaka. To idan suka yi tsarki, sai ku zo musu ta inda Allah Ya umarce ku. Lalle Allah Yana son masu yawan tuba, kuma Yana son masu tsarki.”
نِسَآؤُكُمۡ حَرۡثٞ لَّكُمۡ فَأۡتُواْ حَرۡثَكُمۡ أَنَّىٰ شِئۡتُمۡۖ وَقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُم مُّلَٰقُوهُۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 2:223Matanku gonaki ne a gare ku, don haka ku zaike wa gonakinku ta inda kuka ga dama, kuma ku gabatar wa kawunanku (laduban da shari\'a ta tanadar muku). Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani cewa, lalle ku masu saduwa ne da Shi. Kuma ka yi albishir ga muminai.
وَلَا تَجۡعَلُواْ ٱللَّهَ عُرۡضَةٗ لِّأَيۡمَٰنِكُمۡ أَن تَبَرُّواْ وَتَتَّقُواْ وَتُصۡلِحُواْ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 2:224Kuma kada ku mayar da Allah Ya zamanto kariya ga rantse-rantsenku don su hana ku aiki na ɗa\'a ko na taƙawa ko na sulhu tsakanin mutane. Kuma Allah Mai ji ne, Masani. </b>Daga aya ta 221 har zuwa aya ta 242, wani kundi ne na tsarin zamantakewar iyali. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa wannan rukuni na rayuwar ɗan’adam muhimmancin gaske, domin ginuwarsa tana farawa ne daga gidan da ya fito. Samun mutum nagari, wanda ya san darajar rayuwarsa a bayan ƙasa da manufar halittarsa a duniya, shi ne abin da zai taimaka wajen samar da al’umma ta gari, wadda za ta raya ƙasa, ta kiyaye dokokin Allah a rayuwa. Don haka waɗannan ayoyi suka yi bayani a kan mas’alolin aure da zamantakewar aure da ila’i da saki da idda da ciyarwa da shayarwa da raino da sauran wasu al’umura masu alaƙa da hakan. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fara bayaninsa a kan hukuncin aure tsakanin mace mushrika da mumini, ko tsakanin mumina da mushriki. Allah ya hana irin wannan aure har sai idan sun musulunta. Kuma ɗa namiji mumini ya auri mace baiwa mumina, ya fi masa alheri da ya auri mace ‘ya mushrika, wadda ba ta kaɗaita Allah, ko da kuwa tana da wani abu tare da ita da zai ja hankalinsa, kamar tsalelen kyau ko asali na nasaba ko tarin dukiya. Hakanan su ma mata muminai kada iyayensu, ko waliyyansu, su kuskura su bayar da su aure ga waɗanda suke mushirikai, matuƙar ba su shiga addinin Musulunci ba. Su ba da su aure ga bayinsu muminai, ya fi alheri wurin Allah, fiye da su ba wa ‘ya’yan mushirikai ‘ya’yansu mata, ko da kuwa su ‘ya’yan mushrikan suna da abin da zai ja hankali, kamar kyau ko asali ko dukiya ko sarauta, saboda duk wanda ba Musulmi ne ba, zai ja wanda yake tare da shi ne zuwa son duniya fiye da lahira, ya jefa shi cikin ayyukan da za su kai shi ga shiga wuta. Shi kuma Allah yana kira ne zuwa ga Aljanna, ta hanyar koyar da bayinsa shari’arsa, wadda ta ƙunshi umarni da hani, waɗanda aiki da su ne zai kai mutum ga shiga Aljanna. Kamar yadda Allah yake kwaɗaitarwa a kan tuba da neman gafara da lizimtar ayyuka na ƙwarai, waɗanda za su zama kaffara ga zunubban bawa. Da haka ne Allah yake bayyana hujjojinsa da hukunce-hukuncensa da hikimominsa ga mutane, wala’alla hakan zai sa su tuna abin da suka manta na gaskiya, su ɗau izina, su wa’azantu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa cewa, muminai suna tambayar sa game da hukuncin mu’amalar aure tare da matansu yayin da suke jinin haila, shin za su ƙaurace musu ne gaba ɗaya ko za su kusance su ta hanyar saduwa? Sai Allah ya ce, ya faɗa musu cewa, shi jinin haila cuta ce, kuma ƙazanta ce, kada su sadu da matansu lokacin da suke al’adarsu ta haila, har sai jininsu ya ɗauke sun yi wanka, to a lokacin ne ya halatta su sadu da su ta inda Allah ya halatta musu saduwa da su, wato matancinsu. Allah ya yi bayanin wannan hukunci ne ga bayinsa saboda yana son masu tuba su tsarkake zukatansu daga laifuffuka, kuma masu tsarkake jikinsu daga duk wata najasa da wata ƙazanta. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yahudawa sun kasance idan mace a cikinsu tana haila, to ba sa cin abinci tare da ita, ba sa zama gida ɗaya da ita. Sai sahabban Annabi (ﷺ) suka yi tambaya a kan haka, sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Kuma suna tambayar ka game da jinin haila. Ka ce: ‘Shi cuta ne, don haka ku ƙaurace wa mata a kwanakin haila.’ Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa sahabbai: “Ku yi komai da su, amma ban da saduwa.” [Muslim #302]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sanar da bayinsa cewa, matansu gonakinsu ne, a cikin mahaifarsu suke saka ‘ya’yansu tun suna ɗigon maniyyi, har su girma a haife su a matsayin mutane da ikon Allah. Don haka ya halatta a gare su su sadu da matansu ta kowane ɓangare suka ga dama, matuƙar za su zo musu ta gabansu, wajen da shi ne muhallin shukar ‘ya’ya a mahaifa. Sannan Allah ya umarce su da su yi tanadin ayyukan alheri waɗanda za su amfane su a gidan lahira, kuma ya umarce su da su bi dokokinsa ta hanyar aiki da umarninsa da barin duk abin da ya hana, sannan su tabbatar su sakankance cewa, makomarsu zuwa ga Allah take. Sannan ya umarci Annabinsa da ya yi albishir ga muminai na sakamako mai girma da za su samu a wurin Allah. Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Yahudawa suna da’awar cewa, idan mutum ya tara da matarsa ta bayanta, wai za ta haifi ɗa mai harare-garke. Sai wannan aya ta sauka: “Matanku gonaki ne a gare ku, don haka ku je wa gonakinku ta inda kuka ga dama.” [Muslim #1435]. Abun Nadhr ya ce wa Nafi’u, bararren bawan Abdullahi ɗan Umar: “Ana ta faɗin cewa, kana cewa Ibn Umar ya ba da fatawar halaccin saduwa da mata ta duburarsu.” Sai Nafi’u ya ce: “Ƙarya suke mini, amma zan faɗa maka yadda abin yake. Ibn Umar ya karanta mini Alƙur’ani wata rana har ya zo ga faɗar Allah Ta’ala: “Matanku gonaki ne agare ku....” sai ya ce: “Nafi’u ka san labarin wannan ayar? Mu mutanen ƙabilar Ƙuraishawa mun kasance muna tarawa da matanmu ta hanyar goho, lokacin da muka zo Madina, muka auri matan Madina, sai muka nemi mu yi abin da muka saba yi da matanmu da su, sai suka ƙi yarda, kuma suka ɗauki abin da girma, domin su matan Madina mazajensu suna saduwa da su ne ta rigingine, sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Matanku gonaki ne a gare ku, don haka ku zaike wa gonakinku ta inda kuka ga dama.” [An-Nasa’i, As-Sunan Alkubra #8978, At-Tahawi, Sharhu Ma’anil Athar , #4067]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da kada su mayar da rantsuwa da Allah wani shamaki da za su fake da shi su ƙi aikata ayyukan alheri, kamar biyayya ga iyaye ko taimaka wa dangi da mabuƙata ko su yi rantsuwar da za ta hana su sulhu tsakanin mutane, kamar mutum ya rantse cewa, shi ba zai yi abu kaza ba na alheri, idan an zo an nemi da ya yi wannan abu sai ya ce ai ya riga ya rantse ba zai yi ba, don haka a ƙyale shi. Idan har hakan ta faru, to wannan kada ya hana shi aikata alheri, abin da zai yi shi ne, kawai ya karya wannan rantsuwar, ta hanyar aikata abin da ya ce ba zai aikata ba, sannan ya yi kaffarar rantsuwarsa. Allah yana jin kowa, ya san kuma niyyar kowa, mai kyau da marar kyau. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani mutum ya kai dare a wajen Annabi (ﷺ), da ya koma gida sai ya sami yaransa duk sun yi barci, sai matarsa ta kawo masa abinci, sai ya rantse da Allah ba zai ci ba, saboda yaran nasa, sannan daga baya ya canza ra’ayi ya ɗauki abincin ya ci. Da gari ya waye ya zo ya faɗa wa Annabi (ﷺ) abin da ya faru, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda duk ya yi rantsuwa, sannan ya ga abin da ya rantse a kansa waninsa ya fi shi alheri, to ya aikata wannan da ya fi shi alherin, ya yi kaffarar rantsuwarsa.” [Muslim #1650].
لَّا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا كَسَبَتۡ قُلُوبُكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ
Open ayah 2:225Allah ba zai kama ku da yasasshen zance a cikin rantse-rantsenku ba, sai dai zai kama ku da abin da zukatanku suka ƙudurce. Kuma Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan haƙuri. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin hukuncin rantsuwa; ya bayyana cewa, ba ya kama bayinsa a kan yasasshiyar rantsuwa da suke yi, irin wadda bakunansu suka saba yi cikin wasu al’amuransu, ba tare da suna nufin rantsuwar ita kanta ba. Ko kuma rantsuwar da mutum zai yi a kan wani abu da yake da ƙwaƙƙwaran zato haka yake, sai kuma daga baya ya bayyanar masa cewa ba haka abin yake ba. Allah ya ce ba zai kama bayinsa da laifin irin waɗannan rantse-rantse ba; sai dai zai kama su da duk wata rantsuwar da za su yi ta ƙarya. Amma ga wanda ya yi rantsuwar ba zai yi abu kaza ba, ko sai ya yi abu kaza, sannan ya karya rantsuwar, to zai yi kaffarar rantsuwa a nan duniya, idan kuwa bai yi ba, to zai gamu da uƙubar ranar lahira. Allah mai gafara ne, kuma mai haƙuri ne, ba ya gaggauta musu uƙuba saboda ƙarancin ladabinsu wajen yawan rantse-rantse da sunansa cikin al’amarinsu, kuma ba ya fushi da su a kan hakan.
لِّلَّذِينَ يُؤۡلُونَ مِن نِّسَآئِهِمۡ تَرَبُّصُ أَرۡبَعَةِ أَشۡهُرٖۖ فَإِن فَآءُو فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 2:226Waɗanda suke rantsuwar ba za su sadu da matansu ba, za a yi musu jinkiri na wata huɗu; to idan sun dawo, to lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.
وَإِنۡ عَزَمُواْ ٱلطَّلَٰقَ فَإِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 2:227Idan kuwa suka yi niyyar saki (a cikin zukatansu), to lalle Allah Mai ji ne, kuma Masani. </b>To bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin hukuncin rantsuwa a dunƙule, sai kuma ya zo da bayanin wata rantsuwa ta musamman da miji yake yi a kan matarsa, wadda ake kira ila’i , wato mutum ya rantse cewa ba zai kusanci matarsa ba; sai Allah ya bayyana hukuncinta da cewa, an ba shi wata huɗu ne, idan ya dawo ya ci gaba da hulɗar aure da matarsa kafin ƙarewar wannan wa’adi da aka ba shi, ko kuma daidai lokacin da watannin suka cika, to shi ke nan magana ta ƙare, sai su ci gaba da zaman aurensu. Allah mai gafara ne a gare shi a kan wannan lokacin da ya shafe ba tare da kusantar matarsa ba, sannan mai rahama ne gare shi, ta yadda ya bar masa aurensa, ba tare da ya ɗora masa kaffarar rantsuwa ba. Idan kuma har ya zamanto yana nufin saki ne da wannan rantswar, to ya yi gaggawar sakin wannan mata, ba tare da ya cutar da ita ba, ta hanyar watsi da ita har wani tsawon lokaci, domin Allah mai ji ne, yana jin sakin da zai yi mata, yana kuma sane da abin da ya ƙulla a zuciyarsa na niyyar sakin, babu abin da yake ɓuya gare shi (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) Ya yi rantsuwar ƙaurace wa matansa (wata ɗaya). A daidai lokacin kuma ya gurɗe a ƙafa, sai ya zauna a wani ɗakin benensa tsawon kwana ashirin da tara, sannan ya sauko. Sai matansa suka ce masa: \"Ya Manzo Allah, ka yi rantsuwar ƙauracer wa wata ɗaya ne\". Sai ya ce: \"Ai wata yakan zamanto kwana ashirin da tara.\" [Bukhari #1911].
وَٱلۡمُطَلَّقَٰتُ يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ ثَلَٰثَةَ قُرُوٓءٖۚ وَلَا يَحِلُّ لَهُنَّ أَن يَكۡتُمۡنَ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِيٓ أَرۡحَامِهِنَّ إِن كُنَّ يُؤۡمِنَّ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِي ذَٰلِكَ إِنۡ أَرَادُوٓاْ إِصۡلَٰحٗاۚ وَلَهُنَّ مِثۡلُ ٱلَّذِي عَلَيۡهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ وَلِلرِّجَالِ عَلَيۡهِنَّ دَرَجَةٞۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Open ayah 2:228Kuma mata waɗanda aka saki za su dakatar da kawunansu (tsawon) ƙur’i uku, kuma ba ya halatta a gare su su ɓoye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifarsu, in sun kasance suna yin imani da Allah da ranar ƙarshe; kuma mazajensu su suka fi cancantar dawo da su a cikin wancan lokaci in sun yi nufin sulhu; kuma su (mata) suna da haƙƙi kwatankwacin irin wanda yake kansu ta hanyar da aka sani, kuma mazaje suna da fifiko a kansu. Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima. </b>Wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin matan da mazajensu za su sake su bayan sun tare da su. Ya bayyana cewa, idan waɗannan mata masu yin jinin haila ne, kuma ba sa ɗauke da ciki, to yayin da aka sake su, kada su yi gaggawar yin wani auren; a’a, za su jira tsawon ƙuri uku. Ƙur’i kalama ce wadda a harshen Larabci tana nufin ‘haila’ tana kuma nufin ‘tsarki’, don haka malamai suka yi saɓani wajen tantance ma’anar ta wannan ayar; sai dai a ra’ayin manyan sahabbai daga cikinsu har da halifofin Annabi huɗu, da manyan tabi’ai da wasu daga cikin manyan malamai suna ganin ma’anar kalmar a wannan wuri shi ne ‘jinin haila’. Watau idan mutum ya saki matarsa, to iddar ta tana ƙare wa ne da ɗaukewar jinin al’adar ta ta uku bayan sakin. Kuma haramun ne a kansu su ɓoye batun hailarsu ko batun cikinsu, saboda ɓarnar da yin hakan zai haifar. Domin idan ta ɓoye hakan, wannan zai iya jawo jingina ɗa ba ga ubansa ba, wanda kuma wannan yana tattare da matsaloli masu tarin yawa da za su shafi yanke zumunci da gado da auratayya da sauransu. Hakanan ɓoye hailarta, ko ta ba da labarin cewa ta yi jini, alhalin ƙarya take, wannan zai haifar da hana mijinta haƙƙinsa na kome, da halatta aurenta ga wani mijin ba shi ba kafin lokacinsa ya yi; yin haka shi ma zai haifar da irin waccan ɓarna da aka ambata a baya. Ko kuma ta yi ƙaryar ba ta yi jini ba, domin ta ci gaba da karɓar kuɗin ciyarwa, alhali ba haƙƙinta ba ne, wataƙila mijinta ya dawo da ita bayan kuma iddarta ta riga ta ƙare, ya zamana suna zaman zina a tsakaninsu. To irin wannan aiki babu matar da za ta yi shi, sai wadda ba ta yi imani da Allah da ranar lahira ba. Kuma mazajensu su ne suke da haƙƙin dawo da su kafin gama wa’adin iddarsu, matuƙar suna son su ci gaba da zama na ƙauna da mutuntawa a tsakaninsu. Wannan hukunci ya taƙaita a kan matar da mijinta ya yi mata saki na ɗaya ne ko na biyu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi batun haƙƙin matayen aure a kan mazajensu da haƙƙin mazajensu a kansu, ya bayyana cewa, wajibi ne a kan kowanne ɓangare ya kiyaye haƙƙin ɗaya ɓangaren, kada wani ya zalunci wani, kuma maza suna da fifiko a kan matansu wajen girman haƙƙi da biyayya. Allah shi ne mai cikakken iko da buwaya, don haka yana iya yi wa duk wanda ya saɓa wa dokarsa horo, sannan mai hikima ne cikin duk hukunce-hukuncen da ya shar’anta wa bayinsa.
ٱلطَّلَٰقُ مَرَّتَانِۖ فَإِمۡسَاكُۢ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ تَسۡرِيحُۢ بِإِحۡسَٰنٖۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَأۡخُذُواْ مِمَّآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ شَيۡـًٔا إِلَّآ أَن يَخَافَآ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَا فِيمَا ٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَعۡتَدُوهَاۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 2:229Saki sau biyu ne (ɗaya bayan ɗaya), don haka ko dai ya riƙe ta ta hanyar da aka sani, ko kuma ya sake ta tare da kyautatawa. Kuma bai halatta gare ku ba ku karɓi wani abu daga cikin abin da kuka ba su, sai fa idan su (ma\'aurata) biyu sun ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba. To idan kuka ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba, to babu laifi a gare su game da abin da ta fanshi kanta da shi. Waɗannan iyakokin Allah ne, kada ku ƙetare su, kuma duk wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to waɗannan su ne azzalumai.
فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوۡجًا غَيۡرَهُۥۗ فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَآ أَن يَتَرَاجَعَآ إِن ظَنَّآ أَن يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۗ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:230To idan ya sake sakin ta, ba za ta halatta a gare shi ba bayan haka har sai ta auri wani mijin daban. To idan ya sake ta, to babu laifi gare su su koma, idan sun yi zaton cewa za su tsayar da dokokin Allah. Waɗannan dokokin Allah ne, Yake bayyana su ga mutanen da suke da sani. </b>Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, sakin da miji yake da haƙƙin kome, shi ne sakin farko da na biyu kawai, saɓanin yadda suke yi a zamanin jahiliyya, mutum ya yi ta sakin matarsa yana dawo da ita ba iyaka. Sai Allah ya yi wa tufkar hanci. Don haka idan mutum ya yi wa matarsa saki biyu, kuma ba ta gama iddarta ba, to yana da zaɓi ya dawo da ita su ci gaba da zaman gaskiya, ba cuta ba cutarwa, ko kuma ya ƙyale ta har ta gama iddarta, su rabu cikin mutunci, ba tare da ya cutar da ita ba. Idan sakin ya zaɓa, to bai halatta a gare shi ya karɓi wani abu da ya ba ta na sadaki ko waninsa ba. Sai dai idan akwai tsoro ta ɓangarensa, ko ta ɓangaren matar, cewa idan suka ci gaba da rayuwar aure, to wani daga cikinsu ba zai kula da haƙƙin abokin zamansa ba, to a wannan lokaci ya halatta ta mayar masa abin da ya ba ta domin su rabu. Babu laifi a kanta, idan ta yi hakan, shi ma ba ya da laifi idan ya karɓa. <b> </b> An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Matar Sabitu ɗan Ƙaisu (Allah ya kara masa yarda) ta zo wurin Annabi (ﷺ) ta ce: \"Ya Manzon Allah, ba na zargin Sabitu a addininsa da ɗabi\'unsa, sai dai ba zan iya zaman aure da shi ba.\" Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce mata: \"To za ki mayar masa da gonarsa da ya ba ki?\" Sai ta ce: \"E\". Sai ya ce wa Sabitu: \"Ka karɓi gonarka ku rabu\". [Bukhari#5273, 5274, 5276]. An karɓo daga Rabiyyi\' \'yar Mu\'awwiz ɗan Afra (Allah ya kara mata yarda) cewa, ta yi khul\'i tsakaninta da mijinta a zamanin Manzon Allah (ﷺ), sai Manzon Allah (ﷺ) ya umarce ta ta yi idda da haila ɗaya. [Tirmizi#1185, da Ibn Maja #2058]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk waɗannan hukunce-hukunce iyakokinsa ne, bai halatta muminai su tsallake su ba bayan ya bayyana su a gare su filla-filla, wanda duk ya tsallake wani hukunci daga waɗannan hukunce-hukunce, to babu shakka ya zama azzalumi na haƙiƙa, domin ya aikata abin da ya haramta a gare shi ya aikata. To idan kuma mutum ya yi wa matarsa saki na uku, to ta haramta a kansa, ba shi da damar yin kome, har sai ta auri wani mijin daban, kuma ya sadu da ita. To idan mijin na biyu ya sake ta, ta gama iddarta, babu laifi tsohon mijinta ya sake auren ta, bayan sun tabbatar cewa za su yi zaman aure tare da mutunta juna da kula da haƙƙin juna. Duk waɗannan hukunce-hukunce da suka gabata, Allah yana bayyana su ga masu ilimi, domin su ne za su fahince su, kuma su fahintar da wasu, da haka kowa sai ya amfana da su.
وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ سَرِّحُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖۚ وَلَا تُمۡسِكُوهُنَّ ضِرَارٗا لِّتَعۡتَدُواْۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ وَلَا تَتَّخِذُوٓاْ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ هُزُوٗاۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَمَآ أَنزَلَ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡحِكۡمَةِ يَعِظُكُم بِهِۦۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ
Open ayah 2:231Kuma idan kuka saki mata, sai wa’adin iddarsu ya kusa, (idan kuna son su) sai ku riƙe su ta hanyar da ta dace (a shari\'ance) ko kuma ku ƙyale su ta hanyar da ta dace (a shari\'ance); kuma kada ku riƙe su da nufin cutarwa don ku ƙetare iyakar (Ubangiji). Duk wanda ya aikata haka kuwa, to haƙiƙa ya zalunci kansa. Kuma kada ku mayar da ayoyin Allah abin izgili, kuma ku tuna ni\'imar Allah da Ya yi muku da abin da Ya saukar muku na Littafi da Hikima Yana yi muku wa\'azi da shi. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani lalle Allah Masanin komai ne. Haka kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara jawo hankalin maza cewa, idan sun saki matansu, har suka kusa kammala wa’adin iddarsu, to ko dai su dawo da su, idan za su kiyaye musu haƙƙinsu na aure, ko su ƙyale su su kammala wa’adin iddarsu, ba tare da sun cutar da su ba. Allah ya hana cutar da mata masu idda ta hanyar dawo da su yayin da suka kusa kammala iddarsu, da niyyar tsawaita musu iddarsu, ko kuma don kada su auri wasu mazajen, ko kuma don tursasa musu sai sun biya khul’i don su fanshi kawunansu; yin haka ta’addanci ne gare su, kuma wanda duk ya yi irin haka, to ya zalunci kansa, domin daga ƙarshe shi ne mai cutuwa ta hanyar zunubi da yake ɗaukar wa kansa, da kuma uƙubar Allah da yake jawo wa kansa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana ɗaukar abin da Allah ya saukar na hukuce-hukunce, abin yi wa izgili, ko wasa da shi, ya umarci bayinsa su tuna ni’imomin Allah da ya yi musu, waɗanda ba za su lissafu ba, daga cikinsu har da wahayin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Annabinsa (ﷺ), wanda ya haɗa da Alƙur’ani da sunnar Annabi (ﷺ), waɗanda da su ne Allah yake yi musu wa’azi da tunatarwa. Sannan Allah ya umarce su da su kiyaye dokokinsa ta hanyar aiwatar da umarninsa da guje wa haninsa, kuma su sani cewa ilimin Allah ya kewaye komai, babu wani abu da bai san da zamansa ba.
وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحۡنَ أَزۡوَٰجَهُنَّ إِذَا تَرَٰضَوۡاْ بَيۡنَهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ ذَٰلِكَ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ مِنكُمۡ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ ذَٰلِكُمۡ أَزۡكَىٰ لَكُمۡ وَأَطۡهَرُۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:232Kuma idan kun saki mata sai suka cika wa’adin iddarsu, to (ku waliyyai) kada ku hana su su auri mazajensu (na da) idan sun yi yarjejeniya a tsakaninsu ta hanyar da ta dace (a shari’a). Wannan (abin da aka ambata) shi ne wanda ake yin wa\'azi da shi ga wanda ya kasance daga cikinku, yana imani da Allah da ranar lahira. Wannan shi ne abin da ya fi alheri a gare ku kuma ya fi tsarki; kuma Allah Shi ne Yake da sani, ku ba ku sani ba. A wannan ayar kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana waliyyan matan da suka kammala iddarsu, su takura musu, su hana su sake auren mazajensu na da, waɗanda suka yi musu sakin kome, muddin sun yarda su koma su ci gaba da rayuwar aure a tsakakaninsu, tare da kiyaye wa juna haƙƙi da zaman mutunci. Wannan hani Allah yana yin sa ne kuma yana tsawatar da duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira. Kuma waliyyan matan su yi aiki da wannan doka, su bar hana mata sake auren mazajensu na da. Wannan shi ne ya fi musu alheri a wajen Allah, kuma shi ne abin da zai tsarkake musu zukatansu daga gaba da ƙiyayya, kamar yadda shi ne abin da zai tsare musu mutuncinsu da na ‘ya’yansu. Allah ne ya fi sanin abin da zai amfani bayinsa a duniya da lahira. Amma bayi ba su san a ina alherin yake ba, sai abin da Allah ya sanar da su, saboda haka ya wajaba su sallama wa Allah hukunce-hukuncensa, su yi biyayya gare shi ba ga soye-soyen zukatansu ba. An karɓo da Ma\'aƙil ɗan Yasar (Allah ya kara masa yarda) cewa, ya aurar da \'yar\'uwarsa ga wani mutum Musulmi a zamanin Annabi (ﷺ), suka zauna tare na wani ɗan lokaci sai ya yi mata saki ɗaya, bai kuma dawo da ita ba har ta ƙare iddarta. Sai daga baya ya dawo yana son ta ita ma kuma tana son sa, sai ya shiga cikin manema auren ta, sai Ma\'aƙil ya ce masa: \"Ya marar mutunci, na mutunta ka na aurar maka, amma sai ka wulaƙanta ta ka sake ta, to wallahi har abada ba za ta sake koma wa gidanka ba.\" Sai Allah ya san buƙatar mijinta gare ta da buƙatarta ta koma wa gidan mijinta, sai ya saukar da wannan ayar. [Bukhar i#5130, da Abu Dawud #2087, da Tirmizi #2981].
۞وَٱلۡوَٰلِدَٰتُ يُرۡضِعۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ حَوۡلَيۡنِ كَامِلَيۡنِۖ لِمَنۡ أَرَادَ أَن يُتِمَّ ٱلرَّضَاعَةَۚ وَعَلَى ٱلۡمَوۡلُودِ لَهُۥ رِزۡقُهُنَّ وَكِسۡوَتُهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ لَا تُكَلَّفُ نَفۡسٌ إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَا تُضَآرَّ وَٰلِدَةُۢ بِوَلَدِهَا وَلَا مَوۡلُودٞ لَّهُۥ بِوَلَدِهِۦۚ وَعَلَى ٱلۡوَارِثِ مِثۡلُ ذَٰلِكَۗ فَإِنۡ أَرَادَا فِصَالًا عَن تَرَاضٖ مِّنۡهُمَا وَتَشَاوُرٖ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَاۗ وَإِنۡ أَرَدتُّمۡ أَن تَسۡتَرۡضِعُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِذَا سَلَّمۡتُم مَّآ ءَاتَيۡتُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Open ayah 2:233Kuma iyaye mata za su shayar da \'ya\'yansu tsawon shekara biyu cikakku, ga wanda ya yi nufin ya cika wa\'adi na shayarwa. Kuma wajibi ne a kan wanda aka yi wa haihuwa ya ciyar da su (mata masu shayarwa) da yi musu tufafi ta hanyar da aka saba. Ba a ɗora wa wani rai sai abin da zai iya. Kar a cutar da uwa saboda ɗanta, haka kuma kar a cutar da uba saboda ɗansa. Kuma kwatankwacin irin wannan ya wajaba kan magajinsa. To idan su biyun sun yi nufin yaye bisa ga yarjejeniya da shawara da junansu, to babu laifi a kansu. Kuma idan kun yi nufin nema wa \'ya\'yanku mai shayarwa, to babu laifi a kanku idan kun bayar da abin da ya kamata ta yadda aka saba. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani cewa, lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. Bayan rabuwa ta tabbata tsakanin miji da mata, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaddara an samu haihuwa a tsakaninsu, to a nan Allah (Mai tsarki da daukaka) bai bar al’amarin yaron da aka samu tsakanin waɗannan ma’aurata su yi yadda suka ga dama ba, sai ya saukar da hukuncin shayarwa da bayanin nauyin da yake kan uwa da uba dangane da ɗansu da yake shan nono. Allah ya umarci iyaye mata da su shayar da ‘ya’yansu tsawon shekara biyu cur, idan har uwar da uban suna da buƙatar hakan, ko shi uban shi kaɗai, ko ita uwar ita kaɗai, waninsu ya buƙaci cika wa’adin shayarwa. To a yayin wannan shayarwa dole ne uba ya ɗauki nauyin ci da shan uwar da tufatar da ita gwargwadon yadda ya dace a al’adance, ba tare da almubazzaranci ba, kuma ba tare da ƙwauro ba. Allah ba ya ɗora wa mutum sai abin da zai iya ɗauka. Sannan ya bayyana cewa haramun ne ita uwa ta ƙi karɓar shayar da ɗanta ko ta nemi sai an biya ta fiye da ladanta domin kawai ta cutar da uban yaron. Kamar yadda Allah ya haramta wa uban yaro ya hana uwarsa ta shayar da shi, don kawai ya cutar da ita. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wajabta wa wanda yake da gadon yaron da ubansa ya rasu, irin abin da ya wajabta wa shi uban na ciyarwa da tufatarwa ga uwar yaron, ba tare da cutar da ita ba. Sannan Allah ya halatta wa iyayen yaro yaye ɗansu kafin cikar shekara biyu, bayan sun yi shawara a tsakaninsu, sun yarda da hakan, saboda wata maslaha da suka hango ta shi yaron. Hakanan Allah ya halatta wa iyaye maza su nemo wa ‘ya’yansu masu shayar da su, amma ba da nufin cutar da iyayen yaron ba, sai don wani dalili na daban. To idan ya yi haka babu laifi bayan ya biya jingar shayarwa ga ita mai shayarwa, ya biya ta haƙƙinta cib-cib, ba tare da ya rage mata komai ba. Sannan Allah ya yi umarni da a kiyaye dokokinsa ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi, da barin abin da ya hana, kuma bayinsa su san da cewa babu wani abu da yake ɓoye gare shi, yana ganin duk ayyukansu masu kyau da marasa kyau, kuma zai yi musu sakayya a kai.
وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَعَشۡرٗاۖ فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ
Open ayah 2:234Kuma waɗanda suka mutu daga cikinku, suka kuma bar mata na aure, (su matan) za su yi zaman jira na wata huɗu da kwana goma. To idan sun cika wa’adinsu, babu laifi a kanku (waliyyansu) cikin duk abin da suka aikata game da kawunansu ta hanyar da aka saba (a shari\'a). Kuma Allah Mai cikakken sani ne game da abin da kuke aikatawa. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da bayanin iddar takaba da cewa, idan mutum ya rasu, to wajibi ne a kan matarsa ta yi takabar mutuwarsa, wato ta zauna tsawon wata huɗu da kwana goma a gidan mijinta, ba tare da kwalliya ba, ko saka turare ko fita daga gida ba tare da wata larura ba. Wannan idan matar ba mai ciki ba ce. Idan tana da ciki, to takabarta za ta ƙare ne da zarar ta haihu. To idan har ta fita daga takaba, babu wani laifi a kan waliyyanta don sun bar ta ta yi ado ko ta fita daga gidanta, ko ta sa turare ko ta yi wani auren. Allah yana sane da duk wani abu da mutane suke aikatawa a fili ko a ɓoye kuma zai saka wa kowa gwargwadon yadda ya kiyaye dokokinsa. An karɓo daga Zainab \'yar Ka\'ab ɗan Ujra, ta ce: Furai\'a \'yar Malik ɗan Sinan, watau \'yar\'uwar Abu Sa\'id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ta ba ta labari cewa, ta je wurin Manzon Allah (ﷺ) tana tambayarsa cewa ko za ta iya komawa zuwa danginta Banu Khudra, domin mijinta ya fita neman bayinsa da suka tsere, har sai da ya cim masu a wani wuri mai suna Al-Ƙadum sai suka kashe shi a nan. Ga shi kuma mijinta bai bar ta a cikin gida mallakinsa ba bai kuma bar mata abinci ba? Sai Manzon Allah (ﷺ) ya faɗa mata cewa \"E, tana iya tafiya.\" Ta ce: Sai bayan na juya na tafi har na iso wajen Masallacin Annabi (ﷺ) sai ya sa aka kirawo ni, ya ce mini: \"Me ma kika ce?\" Sai na maimaita masa abin da na faɗa da farko na al\'amarin mijina. Sai ya ce: \"Ki zauna a gidanki har sai faralin idda ya cika wa\'adinsa\". Ta ce: Sai na yi idda a wannan gidan tsawon wata huɗu da kwana goma. Sai a zamani halifancin Usman (Allah ya kara masa yarda) ya aiko yana tambaya ta game da labarina, ni kuma na sanar da shi, sai ya karɓe shi ya yi hukunci da shi.\". [Tirmizi #1204, da Nasa\'i #3530, da Ibn Maja #2031, da Ahmad #27087, 27363, da Ibn Hibban #1331].
وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا عَرَّضۡتُم بِهِۦ مِنۡ خِطۡبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوۡ أَكۡنَنتُمۡ فِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ سَتَذۡكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُواْ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗاۚ وَلَا تَعۡزِمُواْ عُقۡدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡكِتَٰبُ أَجَلَهُۥۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ
Open ayah 2:235Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi wa mata jirwaye da shi na neman aurensu ko kuma kuka ɓoye a cikin zukatanku, Allah Ya san cewa ku za ku riƙa maganarsu, sai dai kar ku yi alƙawari da su (na aure) a asirce, sai dai in za ku faɗi zance wanda yake sananne a (shari\'a). Kuma kada ku ƙulla igiyar aure (da mata masu takaba) har sai faralin idda ya cika wa’adinsa. Kuma ku sani lalle Allah Ya san abin da yake cikin zukatanku, don haka ku kiyaye Shi. Kuma ku sani lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai haƙuri. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da bayanin hukuncin neman auren mai idda ko mai takaba, da kuma sauran bayanin hukunce-hukuncen saki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da mace take takaba ko take iddar saki uku, bai halatta ga wani manemi ya fito ƙarara ya bayyana neman aurensa gare ta ba, amma babu laifi ya yi mata jirwaye na neman aurenta. Hakanan babu laifi don ya ɓoye son aurenta a zuciyarsa kafin ta gama iddarta. Allah ya san za su riƙa maganar aurensu yayin da suke cikin idda a bayyane ko a ɓoye, don haka ya ɗauke musu laifin yi musu jirwaye da neman aurensu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haramta ɗaura auren mace tana cikin idda, har sai ta kammala wa’adin iddarta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi duk wanda ke da niyyar saɓa wa hukuncinsa, ya bayyana cewa ya san abin da suke ɓoyewa a zukatansu na kwaɗayin auren waɗannan mata masu idda, don haka su guji ɓoye wata aniya wadda ta ci karo da dokar Allah don gudun gamuwa da uƙubarsa, kuma su sani cewa, Allah mai gafarta wa bayinsa ne idan sun yi laifi sun tuba, mai haƙuri ne, ba ya gaggauto musu da azaba a lokacin da suka saɓa masa, don haka duk sa’adda suka saɓa masa, to su gaggauta tuba, su koma gare shi, zai gafarta musu.
لَّا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِن طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ مَا لَمۡ تَمَسُّوهُنَّ أَوۡ تَفۡرِضُواْ لَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى ٱلۡمُوسِعِ قَدَرُهُۥ وَعَلَى ٱلۡمُقۡتِرِ قَدَرُهُۥ مَتَٰعَۢا بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 2:236Babu laifi (sadaƙi) a kanku idan kun saki mata, matuƙar ba ku riga kun sadu da su ko kuma kun yanka musu sadaki sananne ba. Sai ku yi musu kyauta (ta kwantar da hankali); mai yalwa daidai yalwarsa; talaka ma daidai ƙarfinsa. (Wannan) wata kyauta ce (da za a bayar) ta hanyar da aka saba; haƙƙi ne a kan masu kyautatawa.
وَإِن طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدۡ فَرَضۡتُمۡ لَهُنَّ فَرِيضَةٗ فَنِصۡفُ مَا فَرَضۡتُمۡ إِلَّآ أَن يَعۡفُونَ أَوۡ يَعۡفُوَاْ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ عُقۡدَةُ ٱلنِّكَاحِۚ وَأَن تَعۡفُوٓاْ أَقۡرَبُ لِلتَّقۡوَىٰۚ وَلَا تَنسَوُاْ ٱلۡفَضۡلَ بَيۡنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ
Open ayah 2:237Idan kuwa kun sake su ne tun kafin ku sadu da su, alhalin kuma kun yanka musu sadaki, to sai (ku bayar) da rabin abin da kuka yanka, sai fa in su matan sun yi afuwa ko kuma wanda a hannunsa igiyar aure take ya yi afuwa; kuma ku yi afuwa shi ya fi kusa ga taƙawa. Kuma kada ku manta da kyautatawar da take tsakaninku. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. A waɗanan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin da ya danganci mutumin da zai auri mace, ya sake ta kafin ya sadu da ita, alhalin bai yanka mata sadaki ba. To a irin wannan yanayi, miji zai yi mata kyauta ta kwantar da hankali gwargwadon ƙarfinsa, da kuma yadda ya dace a shari’ance. Kuma yin wannan kyautar haƙƙi ne a kan duk wanda ya siffantu da siffar kyautatawa ga mutane. Idan kuma ya sake ta ne kafin ya tare da ita, alhalin an riga an yanka mata sadaki, to sai ya ba ta rabin sadakin da aka yanka mata, sai dai idan ta ce ta yafe masa ya riƙe sadakinsa duka, ko kuma shi ya yafe mata, ya bar mata duk sadakin gaba ɗayansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɗaitar da duk ma’auratan cewa, ɗaya ya yi wa ɗaya afuwa, ya bar masa, kuma yin hakan shi ne ya fi kusa da taƙawa. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara jan hankalin ma’auratan da kada su manta kyautatawar da take tsakaninsu. Miji na iya ba wa matarsa fiye da yadda ta cancanta na sadaki, hakanan ita ma matar tana iya yi wa mijinta rangwamen sadaki don tuna alherin da yake tsakaninsu, kuma Allah yana ganin duk ayyukan bayinsa, kuma duk irin aikin da mutum ya yi na alheri, to ba zai faɗi a banza ba, Allah zai yi masa sakayya da alherin da ya fi nasa.
حَٰفِظُواْ عَلَى ٱلصَّلَوَٰتِ وَٱلصَّلَوٰةِ ٱلۡوُسۡطَىٰ وَقُومُواْ لِلَّهِ قَٰنِتِينَ
Open ayah 2:238Ku kiyaye salloli da kuma salla mafificiya, kuma ku tsaya domin Allah kuna masu nutsuwa.
فَإِنۡ خِفۡتُمۡ فَرِجَالًا أَوۡ رُكۡبَانٗاۖ فَإِذَآ أَمِنتُمۡ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَمَا عَلَّمَكُم مَّا لَمۡ تَكُونُواْ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:239To idan kuna cikin halin tsoro, sai ku yi salla kuna tafe da ƙafafuwanku ko a kan ababan hawanku. To idan kun amintu, sai ku ambaci Allah kamar yadda Ya sanar da ku abin da ba ku kasance kun sani ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni da a kiyaye sallolin farilla gaba ɗayansu ta hanyar yin su a lokutansu da kula da rukunansu da sharuuɗansu, sannan ya ware sallar La’asar ita kaɗai, ya jaddada kula da ita. An karɓo daga Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: A ranar yaƙin gangami Manzon Allah (ﷺ) ya ce: \"Allah ya cika musu gidajensu da ƙaburburansu da wuta, sun shagaltar da mu ba mu yi salla mafificiya ba har rana ta faɗi.\" [Bukhari #2931]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: \"Duk wanda sallar la\'asar ta kuɓuce masa, to kamar ya yi asarar iyalansa ne da dukiyarsa.\" [Bukhari #552, da Muslim #626]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su tsaya a sallolinsu cikin nutsuwa ta zuciya da ta gaɓɓai, da barin wata maganar da ba ambaton Allah ba, ba kuma karatun Alƙur’ani ba. To bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci masallata da tsayawa a sallar cikin nutsuwa da barin duk wata magana wadda ba ta danganci ambaton Allah da karatun Alƙur’ani ba, sai ya yi togaciyar hukuncin salla a lokacin da ake tsakiyar yaƙi a filin daga, ko lokacin faruwar wani abun tsoro. A irin wannan lokaci ma dole Musulmi sai sun yi salla, ba a ɗauke musu ita ba, sai dai idan suna jin tsoron ba za su iya yin ta ba kamar yadda ake yin ta a halin kwanciyar hankali, to su dai sallace ta a kowane irin yanayi suke ciki, suna tafe ne a kan ƙafafuwansu ko kuma a kan abubuwan hawansu ko suna kallon alƙibla ko ba sa kallon ta, ko ta halin ƙaƙa suka gudanar da ita, ta wadatar. To amma duk sa’adda wancan tsoro ya kau, wajibi ne su dawo su tsayar da salla kamar yadda aka koyar da su da farko, su yi ta cikakkiya. Domin ilimin da Allah ya koyar da su da hukunce-hukuncen da ba su san su ba a da, wannan wata babbar ni’ima ce a gare su da ya wajaba su yi wa Allah godiya a kanta.
وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا وَصِيَّةٗ لِّأَزۡوَٰجِهِم مَّتَٰعًا إِلَى ٱلۡحَوۡلِ غَيۡرَ إِخۡرَاجٖۚ فَإِنۡ خَرَجۡنَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِي مَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ مِن مَّعۡرُوفٖۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 2:240Kuma waɗanda suke rasuwa daga cikinku suke barin matan aure, (to za su yi) wasiyya ga matansu cewa, a jiyar da su daɗi har zuwa shekara, ba tare da an fitar da su ba; to idan su suka fita da kansu, to babu laifi a kanku dangane da abin da suka aikata wa kansu na abin da yake sananne a shari’a. Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.
وَلِلۡمُطَلَّقَٰتِ مَتَٰعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 2:241Kuma matan da aka sake su suna da wata kyauta ta kwantar da hankali ta hanyar da aka saba, (wannan) haƙƙi ne a kan masu taƙawa.
كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 2:242Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ku hankalta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni da cewa, wajibi ne ga mazaje idan sun zo mutuwa, su bar wa magadansu wasiyyar cewa, matansu na aure su zauna a gidajen mazajen nasu masu rasuwa har tsawon shekara guda cikakkiya, sannan a kula da cinsu da shansu, ba tare da an fitar da su daga gidajen ba. Amma babu wani laifi a kan waliyyan mamaci, idan su matan suka fita daga gidajen bayan sun kammala takabarsu wata huɗu da kwana goma, suka yi kwalliya, suka sanya turare, suka nemi wani auren, da abin da ya yi kama da haka, wanda bai fita daga iyakokin shari’a da al’ada ba. Allah mabuwayi ne, babu mai iya hana shi yin uƙubarsa ga duk wanda ya saɓa wa umarninsa, ya aikata abin da ya hana, kuma mai hikima ne, duk wani hukunci da ya shar’anta cike yake da hikima da dacewa. Yawancin malamai na farko da na baya-baya suna ganin wannan aya an shafe hukuncinta da aya ta 234 wadda ta gabata, inda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wajabta wa matar da mijinta ya rasu ta yi masa takaba ta tsawon wata huɗu da kwana goma (idan kuma mai ciki ce, to za ta zauna tsawon lokacin da za ta haihu, da zarar ta haihu, to ta fita daga takaba). Waɗannan malamai sun ɗauki zamanta a gidan mijinta mai rasuwa tsawon shekara ɗaya, kamar yadda ya zo a wannan ayar zama ne na takaba, don haka suka ce, wannan hukunci an shafe shi da ayar da ta gabata wadda ta bayyana cewa, takabar miji wata huɗu ce da kwana goma kawai. Amma wasu daga cikin malamai na tabi’ai da wasu na baya-baya suna ganin ayar tana umarni ne ga mazaje idan sun zo mutuwa, to su yi wasiyya ga magadansu a kan su ƙale matansu su zauna a gidajensu tsawon shekara ɗaya, kada su fitar da su, sai idan su ne suka zaɓi su fita. Wannan kuwa ya kasance ne kafin Allah ya shar’anta rabon gado, a inda ya ambaci kason mace daga dukiyar mijinta. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wajabta wa maza su ba wa matan da suka saki wani abin tagomashi na dukiya ko tufafi gwargwadon yadda ya dace, ba tare da takurawa ba. Allah ya ƙarfafa hakan da cewa, wannan haƙƙi ne a kan masu taƙawa. To kamar yadda a baya Allah ya bayyana hukunce-hukuncen shari’arsa filla-filla, hakanan yake ci gaba da bayanin sauran ayoyin nasa da hukunce-hukuncensa dalla-dalla, don mutane su fahinta, su yi aiki da su.
۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَهُمۡ أُلُوفٌ حَذَرَ ٱلۡمَوۡتِ فَقَالَ لَهُمُ ٱللَّهُ مُوتُواْ ثُمَّ أَحۡيَٰهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ
Open ayah 2:243Shin ba ka ga waɗanda suka fita daga gidajensu ba su dubbai don tsoron mutuwa, sai Allah Ya ce da su: “Ku mutu”, sannan Ya raya su? Lalle Allah Ma’abocin falala ne ga mutane, sai dai yawancin mutane ba sa godiya.
وَقَٰتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 2:244Kuma ku yi yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah, kuma ku sani cewa, lalle Allah Mai ji ne, Masani.
مَّن ذَا ٱلَّذِي يُقۡرِضُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا فَيُضَٰعِفَهُۥ لَهُۥٓ أَضۡعَافٗا كَثِيرَةٗۚ وَٱللَّهُ يَقۡبِضُ وَيَبۡصُۜطُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 2:245Wane ne zai ba wa Allah kyakkyawan rance, sai Ya ninka masa shi ninki mai yawa? Kuma Allah ne Yake kame (dukiya), Yake kuma shimfiɗa ta, kuma zuwa gare Shi za a mayar da ku.
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰٓ إِذۡ قَالُواْ لِنَبِيّٖ لَّهُمُ ٱبۡعَثۡ لَنَا مَلِكٗا نُّقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ قَالَ هَلۡ عَسَيۡتُمۡ إِن كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ أَلَّا تُقَٰتِلُواْۖ قَالُواْ وَمَا لَنَآ أَلَّا نُقَٰتِلَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَدۡ أُخۡرِجۡنَا مِن دِيَٰرِنَا وَأَبۡنَآئِنَاۖ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ تَوَلَّوۡاْ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 2:246Shin ba ka ga wasu manyan mutane ba daga cikin Banu Isra’ila bayan (mutuwar) Musa yayin da suka faɗa wa Annabinsu: “Ka naɗa mana wani sarki, wanda za mu yi yaƙi (tare da shi) don ɗaukaka kalmar Allah?” Sai ya ce: “Shin ba kwa tsammanin idan an wajabta muku yaƙi, ba za ku yi yaƙin ba?” Sai suka ce: “Me zai sa ba za mu yi yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah ba, alhali kuwa an fitar da mu daga gidajenmu da ‘ya’yanmu?” To yayin da aka wajabta musu yaƙin sai suka juya baya sai ‘yan kaɗan daga cikinsu. Kuma Allah Masanin azzalumai ne.
وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ بَعَثَ لَكُمۡ طَالُوتَ مَلِكٗاۚ قَالُوٓاْ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ عَلَيۡنَا وَنَحۡنُ أَحَقُّ بِٱلۡمُلۡكِ مِنۡهُ وَلَمۡ يُؤۡتَ سَعَةٗ مِّنَ ٱلۡمَالِۚ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰهُ عَلَيۡكُمۡ وَزَادَهُۥ بَسۡطَةٗ فِي ٱلۡعِلۡمِ وَٱلۡجِسۡمِۖ وَٱللَّهُ يُؤۡتِي مُلۡكَهُۥ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 2:247Kuma Annabinsu ya ce da su: “Lalle haƙiƙa Allah Ya naɗa Ɗalutu ya zama Sarki gare ku.” Sai suka ce: “Ta yaya zai samu sarauta a kanmu, alhalin mun fi shi cancatar sarauta, kuma ba a ba shi yalwar dukiya ba?” Sai ya ce: “Lalle Allah Ya zaɓe shi a kanku, kuma Ya ƙare shi da yalwar ilimi da ta girman jiki, kuma Allah Yana bayar da mulkinsa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani.”
وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ءَايَةَ مُلۡكِهِۦٓ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلتَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَبَقِيَّةٞ مِّمَّا تَرَكَ ءَالُ مُوسَىٰ وَءَالُ هَٰرُونَ تَحۡمِلُهُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 2:248Sai Annabinsu ya ce da su: “Lalle alamar (cancantar) mulkinsa ita ce akwatin nan da zai zo muku wanda a cikinsa akwai nutsuwa daga Ubangijinku da kuma sauran abin da iyalin Musa suka bari da iyalin Haruna; mala’iku na ɗauke da shi. Lalle a cikin wannan tabbas akwai aya a gare ku, in kun kasance muminai.”
فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِٱلۡجُنُودِ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ مُبۡتَلِيكُم بِنَهَرٖ فَمَن شَرِبَ مِنۡهُ فَلَيۡسَ مِنِّي وَمَن لَّمۡ يَطۡعَمۡهُ فَإِنَّهُۥ مِنِّيٓ إِلَّا مَنِ ٱغۡتَرَفَ غُرۡفَةَۢ بِيَدِهِۦۚ فَشَرِبُواْ مِنۡهُ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ فَلَمَّا جَاوَزَهُۥ هُوَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ قَالُواْ لَا طَاقَةَ لَنَا ٱلۡيَوۡمَ بِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦۚ قَالَ ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ ٱللَّهِ كَم مِّن فِئَةٖ قَلِيلَةٍ غَلَبَتۡ فِئَةٗ كَثِيرَةَۢ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 2:249To yayin da Ɗalutu ya fita (bayan gari) da rundunarsa, sai ya ce: “Lalle Allah zai jarrabe ku da wata ƙorama, to duk wanda ya sha daga gare ta, to ba ya tare da ni, duk wanda kuwa bai sha ba, to wannan yana tare da ni, sai dai wanda ya kamfata sau ɗaya da (tafin) hannunsa.” Gaba ɗayansu sai suka sha daga cikinta sai ‘yan kaɗan daga cikinsu (su ne ba su sha ba). To yayin da ya ƙetare shi, shi da waɗanda suka yi imani tare da shi, sai suka ce: “A yau kam ba mu da iko wajen fuskantar Jalutu da rundunarsa.” Sai waɗanda suke da yaƙinin cewa za su haɗu da Allah suka ce: “Sau da yawa wata runduna ‘yan kaɗan takan yi rinjaye a kan wata runduna mai yawa da izinin Allah. Kuma Allah Yana tare da masu haƙuri.”
وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُواْ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:250Kuma yayin da suka yi fito-na-fito da Jalutu da rundunarsa, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka zubo mana haƙuri na musamman, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutane kafirai.”
فَهَزَمُوهُم بِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 2:251Sai suka murƙushe su da izinin Allah, kuma Dawudu ya kashe Jalutu, sai Allah Ya ba shi mulki da hikima, kuma Ya sanar da shi irin abin da Ya ga dama. Ba don yadda Allah Yake kare wani sashin mutane da wani sashi ba, to lalle da ƙasa ta lalace, sai dai kuma Allah Ma’abocin falala ne ga talikai.
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۚ وَإِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 2:252Waɗannan ayoyin Allah ne, Muna karanta maka su da gaskiya, kuma lalle kai tabbas kana cikin manzanni. A waɗannan ayoyi, Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba mu labarin waɗansu dubban jama’a, waɗanda suka gudu daga gidajensu don tsoron mutuwa, ko dai saboda wata annoba da ta ɓarke a garin ko kuma saboda abokan gabansu da suka auka musu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kashe su gaba ɗayansu, sannan ya sake raya su bayan wani ɗan lokaci, don su fahimci cewa, babu wanda zai iya guje wa mutuwa idan ajalinsa ya zo. Allah ya sake tayar da su ne don ya nuna musu irin falalarsa mai yawa ga halittunsa, sai dai kuma da dama daga cikin mutane ba sa nuna godiya ga ni’imar da Allah ya yi musu. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa muminai da su fito su yi jihadi don ɗaukaka kalmar Allah, da ba da kariya ga addininsu da al’ummarsu, su sani kuma Allah yana jin duk maganganunsu, yana sane da duk wani hali da suke ciki, don haka su guji saɓa wa umarninsa. To kasancewar jihadi ba zai yiwu ba sai an fitar da dukiya, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɗaitar bisa ciyarwa domin shi, ya yi alƙawarin gwaggwaɓan sakamako ga duk wanda ya ba da dukiyarsa saboda Allah da cewa, zai ninka masa ita ninki mai yawa. Kuma saboda ma kar wani ya yi zaton cewa, fitar da dukiya da bayar da ita don Allah zai jawo masa talauci, sai Allah ya bayyana masa cewa, komai yana hannunsa, shi ne wanda yake yalwata wa wanda ya ga dama yake kuma ƙuntata wa wanda ya ga damar ya ƙuntata masa. Kuma kowa makomarsa zuwa ga Allah take ranar gobe ƙiyama, don ya yi wa kowa sakamako a kan aikinsa da ya aikata. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin wasu mutane daga cikin Banu Isra’ila, bayan rasuwar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), lokacin da dattawa da masu faɗa a ji daga cikinsu suka yi taro, suka nemi wani annabi daga cikinsu da ya naɗa musu shugaba wanda zai jagorance su, su yi yaƙi a ƙarƙashin tutarsa. Sai wannan Annabi ya tambaye su cewa, shin suna zaton idan Allah ya wajabta musu yaƙi, za su tsaya su yi yaƙin? Sai suka amsa masa da cewa, babu abin da zai hana su yin yaƙi don Allah, musamman ma bayan maƙiyansu sun kore su daga gidajensu, sun raba su da ‘ya’yansu, bayan sun kama su sun mayar da su bayi. To bayan Allah ya wajabta musu yaƙin, sai ga shi da yawa daga cikinsu sun noƙe, sun ƙi fita, sai ‘yan kaɗan ne suka cika alƙawarin da suka ɗauka. Allah ya san azzalumi daga cikinsu, mai saɓa alƙawari, kuma zai yi masa sakamako a kan zaluncinsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin yadda labarin waɗannan mutane ya kasance. Annabinsu ya sanar da su cewa, Allah ya karɓi buƙatarsu, ya naɗa musu Ɗaluta da ya zama Sarkinsu, wanda zai zama jagoransu a wannan yaƙin. Ɗaluta mutum ne daga cikin talakawan Banu Isra’ila, ba shi da dangantaka da gidan sarautarsu, don haka sai suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan zaɓi da aka yi wa Ɗaluta. Suka ce, ta yaya zai zama sarkinsu, alhali bai fi su da komai ba, hasali ma su suka fi shi cancantar sarautar, sannan ga shi ba mai dukiya ba, ballantana a sallama masa saboda yawan dukiyarsa. Sai wannan Annabin nasu ya mayar musu da jawabi, da cewa, wannan bawan Allah, Allah ne ya zaɓe shi ya ba shi wannan sarautar, ya kuma ba shi ilimi mai yawa, ga shi kuma da tsawo da ƙarfi da Allah ya hore masa. Kuma ai mulki duka na Allah ne shi kaɗai, yana ba da shi ga wanda ya ga dama, daga kowane irin rukuni na al’umma ya fito, ba lalle sai ya zama ɗan gidan sarauta ba, kuma ba lalle ne ya zama mai dukiya ba, domin falalar Allah mayalwaciya ce, ba wanda ba za ta iya shafa ba, Allah kuma mai cikakken sani ne game da komai, shi ya san wanda ya kamata ya ba wa mulki. Wannan Annabin kuma ya ci gaba da yi musu bayani game da wannan zaɓi da Allah ya yi wa Ɗaluta na sarauta. Ya ce musu, alamar ingancin naɗinsa a matsayin Sarkinsu, shi ne za a dawo musu da akwatinsu da aka taɓa ɗauke musu, wanda yin haka zai haifar musu da nutsuwa a zukatansu, sannan kuma abin da yake cikin akwatin yana ƙunshe da abin da zai kwantar musu da hankali; har ila yau a cikinsa akwai sauran kayan gado, wanda iyalan Annabi Musa da Annabi Haruna suka bari, kuma mala’iku ne za su ɗauko wannan akwatin su kawo shi. Tabbas wannan alama ce ta fili da za ta tabbatar musu gaskiyar zaɓin da Allah ya yi wa Ɗaluta a matsayin Sarkinsu, in dai har sun kasance muminai, sun ba da gaskiya da Allah, to za su gaskata labarin da ya ba su a matsayinsa na Annabinsu. To bayan da suka gamsu da naɗin Ɗaluta a matsayin Sarki wanda zai jagorance su su yaƙi abokan gabarsu, sai duk suka zama sojoji a ƙarƙashin tutarsa, ya kuma fita da su. Bayan sun bar garinsu, sai ya faɗa musu cewa, akwai wata ƙorama da za su ci karo da ita a hanya; wannan ƙorama jarabawa ce a gare su; idan sun iske ta, to duk irin ƙishin da suke ji, kada wanda ya sha ruwanta fiye da kamfatar cikin hannunsa ɗaya. Allah ya yi musu haka ne don ya tantance masu gaskiya daga cikinsu da kuma maƙaryatan cikinsu, a gane masu juriya da waɗanda ba su da juriya. Ɗaluta ya faɗa musu ƙarara cewa, duk wanda ya saɓa wa wannan dokar, ya kwankwaɗi ruwan wannan ƙoramar, to ba ya tare da shi. To suna zuwa wurin wannan ƙoramar kuwa, sai yawancinsu suka sha wannan ruwan, sai ‘yan kaɗan ne ba su sha ba, ko waɗanda ba su wuce kamfata ɗaya ba. Wannan ya sa sojojin Ɗaluta suka koma ‘yan kaɗan. To lokacin da Ɗaluta ya tsallaka wannan ƙoramar, shi da sojojinsa ‘yan kaɗan masu imani suka hango yawan sojojin abokan gabarsu, sai wasu daga cikinsu suka fara cewa, yau kam ba za mu iya fuskantar Jaluta da rundunarsa ba, saboda yawansu da yawan makamansu. To a nan ne masu ƙarfin imani da yaƙinin za su koma ga Allah suka ce, sau da yawa wata runduna ‘yar kaɗan takan yi rinjaye a kan wata runduna mai yawa da ikon Allah, don haka duk wanda Allah ya watsar da shi, yawansa ba zai amfana masa komai ba, hakanan wanda Allah ya yake tare da shi, rashin yawansa ba zai cutar da shi da komai ba, Allah kuma yana tare da masu haƙuri a kan yi masa biyayya da juriya a kan komai. To bayan rundunar Sarki Ɗaluta da rundunar Jaluta sun yi gaba-da-gaba da juna, sai muminai suka roƙi Ubangijinsu da ya kimsa musu haƙuri, ya ba su jajircewa, kada yawan abokan gabarsu ya sa su ji tsoro su gudu, kuma ya ba su nasara a kan kafirai. Sai ko Allah ya karɓi addu’arsu, ya ba su galaba, suka murƙushe mayaƙan Jaluta, kuma Allah ya ɗora Dawudu a kan Jaluta, ya kashe shi a filin daga, a dalilin haka Allah ya yi wa Dawudu kyautar mulki da ta annabta, ya sanar da shi ilimin da ya ga dama, kamar sanin fannin ƙira da sarrafa ƙarfe yadda yake so, kamar yadda Allah ya ambata a Suratul Anbiya’i , aya ta 80. Ba don Allah yana kare muminai daga makircin kafirai ta hanyar muminai masu jihadi ba, to da ɓarna ta yaɗu a bayan ƙasa, sai dai Allah mai yalwar falala ne a kan dukkan halittunsa, don haka ne ya shar’anta musu yin jihadi, domin su tashi su kare kansu, kuma su hana ɓarna yaɗuwa a bayan ƙasa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, duk waɗannan labarai da yake ba shi, na al’ummomin da suka gabata, na gaskiya ne, kuma sun yi daidai da abin da yake cikin littattafan manzannin da suka gabace shi. Waɗannan kuma alamomi ne da hujjoji masu tabbatar da cewa, shi Annabin Allah ne, kuma abin da yake karanta musu daga Allah yake, don haka Allah ya sake tabbatar masa da cewa, “Lalle kai kana cikin manzanni.”
۞تِلۡكَ ٱلرُّسُلُ فَضَّلۡنَا بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۘ مِّنۡهُم مَّن كَلَّمَ ٱللَّهُۖ وَرَفَعَ بَعۡضَهُمۡ دَرَجَٰتٖۚ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلَ ٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ وَلَٰكِنِ ٱخۡتَلَفُواْ فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ وَمِنۡهُم مَّن كَفَرَۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلُواْ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ
Open ayah 2:253Waɗannan manzanni, Mun fifita sashinsu a kan sashi. Cikinsu akwai wanda Allah Ya yi magana da shi, kuma Ya ɗaukaka wasunsu da darajoji. Kuma Mun bai wa Isa ɗan Maryam hujjoji bayyanannu, kuma Mun ƙarfafe shi da Ruhi mai tsarki. Da kuma Allah Ya ga dama da waɗanda suka zo bayansu ba su yaƙi juna ba bayan hujjoji bayanannu sun zo musu, sai dai kuma sun yi saɓani; cikinsu akwai wanda ya yi imani, kuma cikinsu akwai wanda ya kafirce, kuma da Allah Ya ga dama da ba su yaƙi juna ba, sai dai Allah Yana aikata abin da Yake nufi. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar da cewa, manzanninsa masu matsayi da daraja ne a wurinsa, darajojinsu da matsayinsu sun bambanta; wasu sun ɗara wasu daraja. Daga cikinsu akwai wanda Allah ya yi magana da shi, kamar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), akwai kuma wanda Allah ya ɗaukaka shi da darajoji masu yawa, kamar Annabi Muhammad (ﷺ), ya fifita shi a kan sauran annabawa. Sannan kuma akwai Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), wanda Allah ya ba shi mu’ujizoji da yawa, masu tabbatar da gaskiyar annabcinsa, sannan ya ba shi littafin Injila, kamar yadda ya ƙarfafe shi da Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Da Allah ya nufa, da babu wasu da za su zo bayan aiko da wani manzo, su yi yaƙi a junansu bayan hujjoji masu bayyana haƙiƙanin gaskiya sun zo musu. Sai dai saɓanin da suka yi a kan waɗannan hujjojin bayyanannu shi ya haifar da yaƙi a tsakaninsu; wasu daga cikinsu suka yi imani, wasu kuma suka kafirce. Da Allah ya yi nufin ya haɗa kansu gaba ɗaya, ya hana su yaƙar junansu, da ya yi hakan, sai dai Allah yana aikata abin da ya ga dama ne, kuma duk abin da yake nufi shi ne yake wakana.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا بَيۡعٞ فِيهِ وَلَا خُلَّةٞ وَلَا شَفَٰعَةٞۗ وَٱلۡكَٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 2:254Ya ku waɗanda suka yi imani, ku ciyar daga abin da Muka arzurta ku (da shi) tun kafin wani yini ya zo wanda babu ciniki a cikinsa kuma babu abokantaka, kuma babu ceto. Kafirai kuwa su ne azzalumai.
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 2:255Allah, babu wani abin bauta wa da cancanta sai Shi, Rayayye, Tsayayye da Zatinsa; gyangyaɗi ba ya kama shi, ballantana barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa nasa ne shi kaɗai. Wane ne ya isa ya yi ceto a wurinsa in ba da izininsa ba? Ya san abin da yake tare da su a yanzu da kuma abin da zai biyo bayansu; kuma ba sa iya sanin wani abu cikin iliminsa sai abin da Ya ga dama. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da ƙasa, kuma kiyaye su ba zai nauyaye Shi ba, kuma Shi ne Maɗaukaki Mai girma.
لَآ إِكۡرَاهَ فِي ٱلدِّينِۖ قَد تَّبَيَّنَ ٱلرُّشۡدُ مِنَ ٱلۡغَيِّۚ فَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلطَّٰغُوتِ وَيُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَاۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Open ayah 2:256Babu tilastawa a addini, haƙiƙa shiriya ta riga ta bayyana daban da ɓata. Don haka duk wanda ya kafirce wa Ɗagutu, kuma ya yi imani da Allah, to haƙiƙa ya yi riƙo da igiya mafi ƙarfi wadda ba ta tsinkewa. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
ٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡلِيَآؤُهُمُ ٱلطَّٰغُوتُ يُخۡرِجُونَهُم مِّنَ ٱلنُّورِ إِلَى ٱلظُّلُمَٰتِۗ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 2:257Allah Shi ne Majiɓincin lamarin waɗanda suka yi imani, Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske; waɗanda suka kafirce kuwa, majiɓinta lamarinsu su ne ɗagutai, suna fitar da su daga haske zuwa duffai. Waɗannan su ne ‘yan wuta; su masu dawwama ne a cikinta. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar bayinsa da su ciyar daga arzikin da Allah ya ba su, tun gabanin zuwan ranar alƙiyama, ranar da babu kasuwanci a cikinta, babu wani aboki da zai taimaka wa abokinsa, babu wanda zai ceci wani, a karɓi cetonsa, sai wanda Allah ya yi wa izinin ya yi ceto. Sannan Allah ya bayyana cewa, kafirai masu ƙaryata manzannin Allah da faɗa da gaskiya, su ne azzalumai. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin siffofin Abin bauta na gaskiya, ba wanda waɗancan azzalumai suka ɗauka abin bauta ba, wato ba irin yadda Larabawa suka mayar da gumakansu abubuwan bautawa, ba Allah ba, ba kuma irin yadda Yahudu da Nasara suke jingina wa Allah wasu siffofi waɗanda ba su dace da Abin bauta na gaskiya ba. Allah ya siffanta kansa da cewa, shi ne Abin bauta, wanda babu wani abin bauta na gaskiya in ba shi ba. Ya siffantu da cikakkiyar rayuwa, wadda rashi bai gabace ta ba, kuma gushewa ba za ta riske ta ba; shi ne Tsayayye da Zatinsa, ba shi da buƙata a wajen kowa, kowa da komai masu buƙata ne a wajensa. Rayuwarsa da tsayuwarsa da Zatinsa, su suka tabbatar da barci ba ya kama shi ko gyangyaɗi. Duk wani abu da ke cikin sammai da ƙasa nasa ne. Babu mai ikon ya yi ceto a gabansa, sai da izininsa. Ya san komai na bayinsa, wanda aka yi, da wanda za a yi a nan gaba; su kuma bayinsa babu abin da za su iya sani, sai ɗan abin da ya sanar da su bisa ganin damarsa. Saboda girmansa da buwayarsa, Kujerarsa ta yalwaci sammai da ƙasa duka, kuma faɗin sammai da ƙasa da girmansu, ba ya ba shi wata wahala wajen kula da su; kula da su da kiyaye su abu ne mai matuƙar sauƙi a wurinsa. Shi ne mai cikakkiyar ɗaukaka ta Zati, da ɗaukaka ta ƙarfi, da ɗaukaka ta siffofi, da ɗaukaka ta kowane ɓangare nasa, kamar yadda yake da cikakken girma a Zatinsa da siffofinsa. Hadisai na Annabi (ﷺ) ingantattu sun zo da bayanin falalar Ayatul Kursiyyu, wato aya ta 255 da ta gabata. Daga cikinsu akwai Hadisin Ubayyu ɗan Ka’ab, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce mini: “Ya baban Munzir, shin ka san wacce aya ce a littafin Allah ta fi girma?” Ya ce, sai na ce: “Allah da Manzonsa ne suka fi sani.” Sai ya ce: “Ya baban Munzir, shin ka san wacce aya ce a littafin Allah tare da kai ta fi girma?” Ya ce sai na ce: “Allah da Manzonsa ne mafi sani.” Sannan sai Ubayyu ya ce, sai na ce: Ita ce, “Allah, babu abin bauta wa da gaskiya sai shi, Rayayye, Tsayayye da Zatinsa....” Sai ya bugi ƙirjina, ya ce: “Na rantse da Allah, ina maka murna da samun wannan ilimi, ya baban Munzir.” [Muslim #810]. Hakanan ya zo a hadisin Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) cewa, Shaiɗan ya faɗa masa cewa, idan zai riƙa karanta Ayatul Kursiyyu har ƙarshenta, lokacin da ya zo kwanciya a shimfiɗarsa, to Allah zai sanya masa tsaronsa, kuma Shaiɗan ba zai iya matsawa kusa da shi ba har gari ya waye. Abu Hurairata ya je ya faɗa wa Annabi (ﷺ) wannan batu na Shaiɗan, Annabi (ﷺ) ya ce masa: “Ya faɗa maka gaskiya, duk kuwa da cewa shi babban mƙaryaci ne.” [Bukhari #2311]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi bayanin cewa, babu tilastawa a addini, don haka bai dace a tilasta wani sai ya zama Musulmi ba; shi addinin Musulunci a bayyane yake, ya sha bamban da duk wata hanyar ɓata, dalilan ingancinsa a fili suke ƙarara, don haka duk wanda zai shige shi, ya shige shi ne bayan ya gamsu da gaskiyarsa har zuciyarsa. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da bayani cewa, duk wanda ya kafirce wa Ɗagutu, wato duk wani abin bauta da bawa zai wuce iyaka da shi, ko abin bi ko abin yi wa ɗa’a, to duk wanda ya kafirce wa wannan, ya yi imani da Allah shi kaɗai, shi kam ya yi riƙo da addinin gaskiya. Allah yana jin duk wanda ya bayyana kafircewarsa ga Ɗagutu da imaninsa da Allah da wanda ba haka yake ba, ya san abin da kowa daga cikinsu ya ɓoye a zuciyarsa, kuma zai yi wa kowa sakamako gwargwadon aikinsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya zama mumini na gaskiya, to Allah mai jiɓintar lamarinsa ne a ko da yaushe, ya zamo mai taimakon sa, mai agajin sa, zai kuma tsame shi daga duhun ɓata zuwa hasken shiriya, daga duhun kafirci zuwa hasken imani, daga duhun munafunci zuwa ga hasken ikhlasi, daga duhun saɓon Allah zuwa ga hasken ɗa’a ga Allah, daga duhun bidi’a zuwa ga hasken sunna. Amma kafirai ba su da masu jiɓintar al’amuransu sai Ɗagutu, wanda shi ne abokin tafiyarsu. Babban Ɗagutu kuwa shi ne Shaiɗan la’ananne, shi ne zai riƙa fitar da su daga haske zuwa duffai na shirka da ɓata da saɓon Allah, kuma waɗannan su ne masu shiga wuta, su dawwama a cikinta ta har abada.
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِي حَآجَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ فِي رَبِّهِۦٓ أَنۡ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ إِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّيَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ قَالَ أَنَا۠ أُحۡيِۦ وَأُمِيتُۖ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَأۡتِي بِٱلشَّمۡسِ مِنَ ٱلۡمَشۡرِقِ فَأۡتِ بِهَا مِنَ ٱلۡمَغۡرِبِ فَبُهِتَ ٱلَّذِي كَفَرَۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 2:258Shin ba ka ga wanda ya yi jayayya da Ibrahim ba game da lamarin Ubangijinsa, don Allah ya ba shi mulki, yayin da Ibrahimu ya ce: “Ubangijina Shi ne Yake rayawa, kuma Yake kashewa.” Sai ya ce: “Ai ni ma ina rayawa, kuma ina kashewa.” Sai Ibrahim ya ce: “To Allah Yana zuwa da rana daga gabas, to kai ka zo da ita daga yamma.” Sai wanda ya kafirta ya kiɗime. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutanen da suke azzalumai.
أَوۡ كَٱلَّذِي مَرَّ عَلَىٰ قَرۡيَةٖ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحۡيِۦ هَٰذِهِ ٱللَّهُ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۖ فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِاْئَةَ عَامٖ ثُمَّ بَعَثَهُۥۖ قَالَ كَمۡ لَبِثۡتَۖ قَالَ لَبِثۡتُ يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۖ قَالَ بَل لَّبِثۡتَ مِاْئَةَ عَامٖ فَٱنظُرۡ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمۡ يَتَسَنَّهۡۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجۡعَلَكَ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِۖ وَٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡعِظَامِ كَيۡفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكۡسُوهَا لَحۡمٗاۚ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعۡلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 2:259Ko kuma kamar mutumin da ya wuce ta wata alƙarya alhalin ta zama kango, sai ya ce: “Ta yaya Allah zai raya wannan bayan mutuwarta?” Sai Allah Ya karɓi rayuwarsa tsawon shekara ɗari, sannan Ya tashe shi, Ya ce: “Mene ne tsawon lokacin da ka zauna?” Sai ya ce: “Ai na zauna yini ɗaya ne ko ma wani sashi na yinin.” Sai Ya ce: “Ai ka zauna tsawon shekara ɗari ne, don haka dubi abincinka da abin shanka bai canja ba, kuma ka dubi jakinka mana ka gani, don Mu sanya ka ka zamanto aya ga mutane, kuma ka dubi ƙasusuwan ka gani yadda za Mu haɗa su, sannan Mu lulluɓe su da nama.”To lokacin da komai ya bayyana a gare shi, sai ya ce: “Na sani lalle Allah Mai iko ne a kan komai.”
وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّ أَرِنِي كَيۡفَ تُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ قَالَ أَوَلَمۡ تُؤۡمِنۖ قَالَ بَلَىٰ وَلَٰكِن لِّيَطۡمَئِنَّ قَلۡبِيۖ قَالَ فَخُذۡ أَرۡبَعَةٗ مِّنَ ٱلطَّيۡرِ فَصُرۡهُنَّ إِلَيۡكَ ثُمَّ ٱجۡعَلۡ عَلَىٰ كُلِّ جَبَلٖ مِّنۡهُنَّ جُزۡءٗا ثُمَّ ٱدۡعُهُنَّ يَأۡتِينَكَ سَعۡيٗاۚ وَٱعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 2:260Kuma ka tuna lokacin da Ibarahimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka nuna mini yadda Kake rayar da matattu.” Sai ya ce: “Shin ko ba ka yi imani ba ne?” Ya ce: “A’a, (na yi imani), sai dai ina son zuciyata ta ƙara samun nutsuwa.” Sai Ya ce: “To ka kama tsuntsaye huɗu ka tara su wajenka, sannan ka sanya yanka ɗaya-ɗaya nasu a kan kowane saman dutse, sannan ka kira su; za su zo maka da gaggawa. Kuma ka sani cewa lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.” Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana a kan cewa imani haske ne kafirci kuma duffai ne, a waɗannan ayoyi sai ya kawo wasu hujjoji guda uku a kan hakan. Ta farko, kamar misali ne a kan hakan, domin labari ne da ya ƙunshi magana a kan ɓatan kafiri da shiriyar mumini. Allah yake gaya wa Annabinsa (ﷺ) labarin wani mutum da Allah ya ba shi mulki a zamanin Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), lokacin da giyar mulki ta kwashe shi, har ya yi da’awar allantaka. Ya tambayi Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), wane ne Ubangijinsa? Sai ya amsa masa da cewa: “Ubangijina shi ne wanda yake rayawa, yake kashewa.” Sai wannan sarki ya ce: “Ni ma ai ina rayawa, ina kuma kashewa.” Sai ya sa aka kawo masa wasu mutane su biyu, waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya sa aka zartar wa ɗayansu hukuncin kisa, ɗayan kuma ya sa aka sake shi. Sai ya ce, to ga shi ya raya wanda ya ga damar rayawa, kuma ya kashe wanda ya ga damar kashe shi. Sai Annabi Ibrahim ya fito masa ta wata hanyar daban, ya ce masa: “To ni Ubangijina a kullum yana fito da rana ta gabas, ta faɗi ta yamma, to kai sai ka fito da ita ta yamma idan za ka iya.” Jin haka ke da wuya, sai ya ruɗe, ya kiɗime, ya rasa hujjar riƙewa. To haka Allah yake yi wa azzalumai waɗanda suka zaɓi kafirci a kan imani, babu yadda za su sami wata hujja mai ƙarfi a kan kafircinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo misali na biyu, na wani bawan Allah da yake tsaka da tafiya, sai ya biyo ta wata alƙarya wadda mutanen cikinta gaba ɗaya sun mutu, ta zama kango babu komai cikinta sai kufai. Sai ya ka da baki ya ce: “Ta yaya Allah zai raya wannan alƙarya bayan mutuwarta?” Wato ta yaya wannan gari zai dawo ya ci gaba da rayuwa da mutanen cikinsa, kamar yadda yake a da? Nan take, sai Allah ya matar da shi, bai dawo masa da ransa ba, sai bayan shekara ɗari a mace. Bayan da ransa ya komo jikinsa, sai Allah ya tambaye shi: “Mene ne tsawon lokacin da ka zauna a wannan wuri?” Sai ya ce: “Ai na zauna yini ɗaya ne ko ma wani sashe na yini.” Wato ya zaci ɗan barci ne ya kwashe shi, kuma yanzu ya farka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa masa da cewa: “Ai ka zauna a nan tsawon shekara ɗari ne, don haka ka dubi abincinka da abin shanka ba su sauya ba....” duk kuwa da shuɗewar waɗannan shekaru masu yawa, tare da kasancewarsu abin da ya fi komai saurin lalacewa, ya canza, “....amma kuma dubi jakinka, shi ya mutu har ƙasusuwansa sun ratattake.” To Allah ya yi masa haka ne don ya zama hujja ga mutane game da ikon Allah na tayar da matattu ranar lahira don yi musu hisabi. Allah ya ce wa wannan mutum, ya sake duba ratattakakkun ƙasusuwan jakinsa matacce, ya ga yadda Allah zai sake dawo masa da rayuwarsa, yadda zai lulluɓe waɗannan ƙasusuwa da nama, sannan ya sake hura masa rai, ya tashi ya koma kamar yadda yake a da, tamkar bai taɓa mutuwa ba. Yayin da wannan mutum ya gane wa idonsa abin da a da yake zaton wuyar faruwarsa, yanzu ga shi ya faru, sai ya tabbatar da cewa, Allah mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi, ko zai wahalar da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo dalili na uku, mai tabbatar da cewa, akwai ranar alƙiyama, kuma Allah zai tashi matattu daga ƙaburburansu, ya yi musu hisabi. Ya ba wa Annabi (ﷺ) labarin Annabi Ibrahim lokacin da ya nemi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa yadda yake raya matattu, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye shi: “Shin ko ba ka yi imani ba ne?” Annabin Allah Ibrahim ya amsa masa cewa, shi mumini ne, ba ya shakka ko kaɗan game da Ƙudurar Allah, sai dai manufar tambayarsa ita ce yana son ya ƙara imani ne, zuciyarsa ta ƙara nutsuwa. Sai Allah ya umarce shi da ya samo tsuntsaye huɗu, ya yanka su gunduwa-gunduwa, sannan ya je ya rarraba su a kan duwatsu daban-daban, sannan ya kirawo su, za su taho wajensa da gaggawa. Sai ya aikata, kamar yadda Allah ya umarce shi, sai ga tsuntsayen nan kowane ɗaya ya haɗe da jikinsa, sun zo wurinsa da sauri. Sai Allah ya umarce shi da lalle ya sakankance cewa, Allah mabuwayi ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi sannan mai hikima ne, yana ajiye komai a muhallinsa da ya dace.
مَّثَلُ ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنۢبَتَتۡ سَبۡعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنۢبُلَةٖ مِّاْئَةُ حَبَّةٖۗ وَٱللَّهُ يُضَٰعِفُ لِمَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ
Open ayah 2:261Misalin waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, kamar misalin ƙwaya ɗaya ce da ta fitar da zangarniya bakwai, a cikinta kowace zangarniya kuma (aka sami) ƙwaya ɗari. Kuma Allah Yana ninninkawa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani.
ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ لَا يُتۡبِعُونَ مَآ أَنفَقُواْ مَنّٗا وَلَآ أَذٗى لَّهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 2:262Waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, sannan ba sa bin abin da suka ciyar da gori ko cuta, (waɗannan) suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.
۞قَوۡلٞ مَّعۡرُوفٞ وَمَغۡفِرَةٌ خَيۡرٞ مِّن صَدَقَةٖ يَتۡبَعُهَآ أَذٗىۗ وَٱللَّهُ غَنِيٌّ حَلِيمٞ
Open ayah 2:263Kyakkyawar magana da yafiya sun fi sadakar da cutarwa za ta biyo bayanta alheri. Kuma Allah Shi ne Wadatacce, Mai haƙuri.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُبۡطِلُواْ صَدَقَٰتِكُم بِٱلۡمَنِّ وَٱلۡأَذَىٰ كَٱلَّذِي يُنفِقُ مَالَهُۥ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ صَفۡوَانٍ عَلَيۡهِ تُرَابٞ فَأَصَابَهُۥ وَابِلٞ فَتَرَكَهُۥ صَلۡدٗاۖ لَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّمَّا كَسَبُواْۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:264Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku ɓata sadaƙoƙinku da gori da cutarwa, kamar wanda yake ciyar da dukiyarsa don mutane su gani, kuma ba ya imani da Allah da ranar lahira; to misalinsa kamar misalin kamfa ne da turɓaya take a kansa sai ruwan sama mamako ya same shi, sai ya bar shi tatas. Ba za su amfana da komai daga abin da suka aikata ba. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai.
وَمَثَلُ ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمُ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِ وَتَثۡبِيتٗا مِّنۡ أَنفُسِهِمۡ كَمَثَلِ جَنَّةِۭ بِرَبۡوَةٍ أَصَابَهَا وَابِلٞ فَـَٔاتَتۡ أُكُلَهَا ضِعۡفَيۡنِ فَإِن لَّمۡ يُصِبۡهَا وَابِلٞ فَطَلّٞۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ
Open ayah 2:265Kuma misalin waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu don neman yardar Allah da tabbatar da (imani) a zukatansu, kamar misalin gona ce a kan jigawa sai ruwan sama mamako ya same ta, sai ta ba da amfaninta riɓi-biyu. To idan mamakon ruwan bai same ta ba, sai yayyafi (ya wadatar da ita). Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama ambaton ƙissoshin da suke tabbatar da rayuwa bayan mutuwa, wato gaskiyar batun tashin alƙiyama, sai ya zo da ambaton abin da zai amfani mutum a wannan ranar, shi ne ciyar da dukiyarsa don Allah. Allah ya ba da misalin yadda yake ninka wa wanda ya yi sadaka da dukiyarsa sakamakonsa ninkin baninkin. Ya kwatanta shi da manomin da zai yafa ƙwaya ɗaya ta iri a cikin ƙasar noma mai kyau, idan ta zo fitowa sai ta fitar da zangarniya bakwai, kowace zangarniya kuma tana ɗauke da ƙwaya ɗari, ka ga zangarniya bakwai ta koma ƙwaya ɗari bakwai ke nan. Kuma ba nan abin ya tsaya ba; Allah yana ƙara ninka wa wanda ya ga dama fiye da hakan, domin shi Allah mai yalwar falala ne, ya san wanda ya cancanta a ninka masa ladansa. Uƙbatu ɗan Amr (Allah ya kara masa yarda) ya ce, wani mutum ya kawo wa Annabi (ﷺ) wata taguwa mai sanye da akalarta, ya ce, ya Manzon Allah (ﷺ), na ba da wannan taguwar don Allah. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ranar gobe ƙiyama kana da taguwa mai akala ɗari bakwai.” [Muslim #1892]. Annabi (ﷺ) kuma ya ce: “Duk wani aiki ɗaya na ɗan’adam ana ninka masa shi sau goma, har zuwa ninki ɗari bakwai. Allah ya ce: “Sai dai azumi, ni ne nake ba da sakayyarsa.” [Muslim #1151]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, duk waɗanda suke ba da dukiyarsu wajen ayyukan alheri, don neman yardar Allah, sannan ba su haɗa aikinsu da wani abun gori ko cutarwa ba, wato ba sa goranta wa wanda suka taimaka masa ko su riƙa nuna masa girman kai da wulaƙanci don sun taimake shi ko su riƙa wahalar da shi saboda alherin da suka taɓa yi masa a baya, to duk waɗanda suke da irin wannan siffa, suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, kuma kada su ji wani tsoron abin da za su tarar in sun mutu, kuma kada su yi wani baƙin ciki game da abin da suka bari a nan duniya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin cewa, yi wa mai neman taimkao magana mai daɗi, idan ba zai sami biyan buƙatarsa ba ko yi masa kyakkyawar addu’a ko magana mai faranta masa rai, da rufa masa asiri da yafe masa idan ya yi wata magana marar daɗi lokacin gabatar da buƙatarsa, yin haka ya fi zama alheri, fiye da a ba shi sadakar da za a biyo ta da gori ko cutarwa gare shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) Mawadaci ne, ba ya da buƙatar duk wata sadaka da bayi za su yi, ballantana wadda za a haɗa ta da gori da cutarwa, kuma Allah Mai haƙuri ne, yana yafe wa wanda ya yi sadaka da gori ko cutarwa idan ya tuba ya nemi gafara. An karɓo daga Abu Zarri (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce: “Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ba a ranar gobe ƙiyama: Mai gori, wanda ba zai yi kyauta ba sai ya haɗa da gori da mai sayar da hajarsa ta hanyar rantsuwar ƙarya da mai sakin tufarsa tana jan ƙasa.” [Muslim #106]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa muminai da kada su ɓata sadakarsu da gori da cutarwa ga wanda suka ba shi sadakar, sai aikinsu ya zama kamar aikin munafukin da yake yin sadaka da dukiyarsa ba don Allah ba, sai don mutane su gani su yabe shi, alhalin su ba su san cewa bai yi imani da Allah ba, bai yi imani da lahira ba, don haka kar ya sa rai a kan samun wani sakamako ranar lahira a wannan aikin nasa. Ƙeƙashewar zuciyar munafuki da bushewarta wajen rashin amfanuwa da aikin alherinsa saboda rashin imani da Allah da ranar lahira, kamar wani kamfan dutse ne wanda ƙasa ta rufe shi, duk wanda ya hango shi daga nesa, zai yi zaton za a iya shuka a wurin har ta tofo ta yi yaɗo. Da zarar ruwan sama ya sauka a kansa, sai duk ya wanke wannan ƙasar, sai dutsen ya fito tatas, babu wata ƙasa a kansa wadda ake zaton za ta iya fitar da tsiro. To haka sadakar munafuki take, za ta tafi ne a banza, babu wani lada a kanta, saboda ba a kafa ta a kan ginshiƙi na imani ba, ba a yi ta da wata kyakkyawar niyya ba. Idan alƙiyama ta tsaya, lokacin girbin ayyukan alheri ya yi, duk masu aiki suka riƙa karɓar ladan ayyukansu, to su waɗannan munafuƙan za su zo suna son su sami ladansu, amma sai su iske fayau ba komai, duk abin da suka aikata na sadaka ya bi iska, su neme shi sama da ƙasa su rasa, domin ba su yi shi don Allah ba. To sai aka yi kira ga muminai kada su zama kamar waɗannan munafuƙan, su ɓata ladan sadakokinsu ta hanyar gori da cutar da wanda suka ba wa sadakarsu. Kuma Allah ba ya datar da waɗanda suka kafirce masa, har su karɓi gaskiya, su yi sadakarsu don neman yardarsa, domin sun fi son zama cikin ɓarnarsu a kan shiriya, don haka sai ya kautar da zukatansu daga shiriya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci waɗanda suke ciyar da dukiyarsu a kan ayyukan alheri da neman yardarsa, ba tare da nuna gori ko cutar da wani ba. Sun fitar da dukiyoyinsu bisa ganin damarsu, ba don wani ya tilasta su ba, ba kuma don ganin idon wani ba; sun yi haka ne saboda sun yi imani da cewa, ranar lahira Allah zai yi musu sakayya a kan ayyukansu na alheri. To sai Allah ya sifanta waɗannan da wata gona mai yawan itatuwa da shuke-shuke masu yawa a cikinta, tana kan wani wuri mai tudu, don haka sai amfanin cikinta ya yi matuƙar kyau; sai kuma ta kasance tana samun ruwan sama, ko mai yawa, don haka amfaninta ya daɗa ƙaruwa ya ninku, kai ko ma ɗan yayyafi ta samu, wannan ma ya wadatar da ita, za ta fitar da ‘ya’yan itatuwa masu yawa, saboda kyan wurin da take. To haka sadakar mumini take, Allah yana riɓanya masa ladansa, ko ya bayar da mai yawa ne ko kuma kaɗan, ba za ta taɓa tafiya a banza ba, domin ya yi ne don Allah don neman yardarsa, bisa tabbatar da imani a zuciyarsa. Kuma Allah yana ganin duk abin da bayinsa suke yi, zai kuma yi musu sakayya a kai.
أَيَوَدُّ أَحَدُكُمۡ أَن تَكُونَ لَهُۥ جَنَّةٞ مِّن نَّخِيلٖ وَأَعۡنَابٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ لَهُۥ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَأَصَابَهُ ٱلۡكِبَرُ وَلَهُۥ ذُرِّيَّةٞ ضُعَفَآءُ فَأَصَابَهَآ إِعۡصَارٞ فِيهِ نَارٞ فَٱحۡتَرَقَتۡۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 2:266Shin yanzu ɗayanku zai so a ce yana da wata gona ta itacen dabino da kuma inabai, wadda ƙoramu suke gudana a ƙarƙashinta, yana da dukkan wasu nau’uka na ‘ya’yan itace a cikinta, sai kuma girma ya kama shi, kuma ga shi yana da yara raunana, sai kuma wata irin guguwa mai ɗauke da wuta ta same ta, sai (gonar gaba ɗaya) ta ƙone? Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyi don ku riƙa yin tunani.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنفِقُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا كَسَبۡتُمۡ وَمِمَّآ أَخۡرَجۡنَا لَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِۖ وَلَا تَيَمَّمُواْ ٱلۡخَبِيثَ مِنۡهُ تُنفِقُونَ وَلَسۡتُم بِـَٔاخِذِيهِ إِلَّآ أَن تُغۡمِضُواْ فِيهِۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٌ
Open ayah 2:267Ya ku waɗanda suka yi imani, ku ciyar daga daɗaɗan abin da kuka tsuwurwuta da kuma abin da muka fitar muku shi daga cikin ƙasa, kuma kar ku nufaci mummuna daga cikinsa ku ce daga gare shi ne za ku ciyar, alhalin ku ma kanku (idan an ba ku) ba za ku karɓe shi ba sai kun runtse idanu. Kuma ku sani cewa lalle Allah Mawadaci ne, Sha-yabo.
ٱلشَّيۡطَٰنُ يَعِدُكُمُ ٱلۡفَقۡرَ وَيَأۡمُرُكُم بِٱلۡفَحۡشَآءِۖ وَٱللَّهُ يَعِدُكُم مَّغۡفِرَةٗ مِّنۡهُ وَفَضۡلٗاۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 2:268Shaiɗan ne yake tsoratar da ku da talauci, kuma yana umartar ku da alfasha; Allah kuwa Yana yi muku alƙawarin gafara ta musamman daga gare Shi da kuma falala. Kuma Allah Mai yalwa ne, Masani.
يُؤۡتِي ٱلۡحِكۡمَةَ مَن يَشَآءُۚ وَمَن يُؤۡتَ ٱلۡحِكۡمَةَ فَقَدۡ أُوتِيَ خَيۡرٗا كَثِيرٗاۗ وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّآ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Open ayah 2:269Yana bayar da hikima ga wanda Ya ga dama; kuma dukkan wanda aka bai wa hikima, to haƙiƙa an ba shi alheri mai tarin yawa. Kuma ba wanda yake wa’azantuwa sai ma’abota hankula.
وَمَآ أَنفَقۡتُم مِّن نَّفَقَةٍ أَوۡ نَذَرۡتُم مِّن نَّذۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُهُۥۗ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٍ
Open ayah 2:270Kuma abin da kuka ciyar na abin ciyarwa ko kuka yi alwashi na bakance, to lalle Allah Yana sane da shi. Kuma azzalumai ba su da waɗansu mataimaka.
إِن تُبۡدُواْ ٱلصَّدَقَٰتِ فَنِعِمَّا هِيَۖ وَإِن تُخۡفُوهَا وَتُؤۡتُوهَا ٱلۡفُقَرَآءَ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۚ وَيُكَفِّرُ عَنكُم مِّن سَيِّـَٔاتِكُمۡۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ
Open ayah 2:271In da za ku bayyanar da sadakoki a fili, to madalla da hakan, kuma idan kuka ɓoye sadaƙar, kuma kuka ba da ita ga talakawa, to hakan shi ya fi alheri a gare ku, kuma zai kankare muku kurakurenku, kuma Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne.
۞لَّيۡسَ عَلَيۡكَ هُدَىٰهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يَشَآءُۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلِأَنفُسِكُمۡۚ وَمَا تُنفِقُونَ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ ٱللَّهِۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ يُوَفَّ إِلَيۡكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تُظۡلَمُونَ
Open ayah 2:272Shiryar da su ba a kanka yake ba, sai dai Allah ne Yake shiryar da wanda Ya ga dama, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to domin kawunanku ne, kuma ba za ku ciyar ba sai don neman yardar Allah; kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, za a cika muku ladansa, alhali kuma ba za a zalunce ku ba.
لِلۡفُقَرَآءِ ٱلَّذِينَ أُحۡصِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا يَسۡتَطِيعُونَ ضَرۡبٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ يَحۡسَبُهُمُ ٱلۡجَاهِلُ أَغۡنِيَآءَ مِنَ ٱلتَّعَفُّفِ تَعۡرِفُهُم بِسِيمَٰهُمۡ لَا يَسۡـَٔلُونَ ٱلنَّاسَ إِلۡحَافٗاۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ
Open ayah 2:273Ga mabuƙata waɗanda aka tsare saboda Allah, ba su da ikon yawatawa a bayan ƙasa, har wanda ya jahilci halinsu yana zato su mawadata ne saboda kame kai; za ka gane su ne da alamominsu, ba sa naciyar roƙar mutane, kuma duk abin da kuka ciyar na alheri, to Allah Yana sane da shi.
ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 2:274Waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana a ɓoye da kuma a sarari, to suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da misalin wanda yake gori a sadakarsa ko yake yin riya a cikinta, inda ya yi kira ga duk masu aikata irin wannan mummunan aiki da cewa, shin ɗaya daga cikinsu yana fatan a ce ya mallaki gona mai cike maƙil da itatuwan dabino da inabi, ga ƙoramu suna ta gudu a cikinta, sannan ta ƙunshi duk wani nau’i na ‘ya’yan itatuwa da shuke-shuke, bayan haka kuma mai gonar shekarunsa sun yi nisa, amma kuma ƙaunarsa da wannan gonar a kullum sai ƙaruwa take saboda ita ce gatansa; ba ya iya fita wani aikin ƙarfi ko kasuwanci, ga shi kuma da ‘ya’ya ƙanana, waɗanda shi ne mai ciyar da su. Yana cikin tsananin buƙata ga wannan gonar, sai Allah ya aiko da wata jarraba ta wata ƙaƙƙarfar iska mai ɗauke da wuta, wannan gonar duk ta ƙone ƙurmus? To idan mai wannan gonar ya zo ya ga yadda ta zama, wane irin baƙin ciki ne ba zai yi ba? Yaya zuciyarsa a lokacin za ta kasance? Ga shi dai ya tsiyace, ga tsufa ga tarin iyali da ƙarfinsu bai kawo ba, balle su amfane shi. To kamar haka ne misalin wanda ya ba da dukiyarsa sadaka da farko don Allah, sannan daga baya ya ɓata sadakar da gori da kuma cutarwa; sai ya zo lokacin da yake da tsananin buƙatar wannan ladan, wato bayan mutuwarsa, sai ya samu wannan aiki nasa duk ya lalace, babu wani abin da zai mora a cikinsa. Da irin waɗannan bayanai ne Allah yake fito da ayoyinsa sarari don bayinsa su yi tunani su faɗaka. Wata rana Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce wa sahabban Annabi (ﷺ): A zatonku wannan aya da Allah yake cewa: “Shin yanzu ɗayanku zai so a ce yana da wata gona....” a kan me ta sauka? Sai suka ce: “Allah ne mafi sani.” Sai Umar ya yi fushi, ya ce: “Kawai ku ce mun sani, ko kuma ba mu sani ba.” Sai Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ya Sarkin Muminai, ni akwai wani abu da nake tunani game da wannan ayar.” Sai Umar ya ce: “Ɗan ɗan’uwana, faɗi abin da yake ranka, kada ka raina kanka.” Sai Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Misalin wani aiki ne aka bayar.” Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wane irin aiki?” Sai Ibn Abbas ya ce: “Wani aiki dai.” Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Misalin wani mai kuɗi ne wanda yake aikin ɗa’a ga Allah (Mai tsarki da daukaka), sai Allah ya sallaɗa masa da Shaiɗan, ya koma ayyukan saɓon Allah, har sai da suka lalata ayyukan ɗa’arsa.” [Bukhari #4538]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɗaitar da bayinsa da su fitar da zakkar dukiyoyinsu kuma su yi sadaka daga mafi kyan dukiyar da suka mallaka ta halal da amfanin gonar da suka noma ko ma’adinan da suka haƙo; kada kuma su kuskura su fitar da zakkarsu ko su bayar da sadaka daga cikin gurɓatacciyar dukiyarsu wadda ta lalace, wadda idan su aka ba wa ita a matsayin sadaka ko kyauta, duk buƙatarsu ba za su so irinta ba, sai dai su karɓa hakanan, ba don suna so ba. Allah ya umarce su da su san da cewa shi Allah Mawadaci ne, ba ya da buƙatar komai a wurinsu, yana kwaɗaitar da su ne da su yi sadaka domin su ne za su amfana da ladan idan sun yi. Sannan kuma shi Allah Sha-yabo ne, saboda duk siffofinsa na kamala ne, kuma duk abin da yake umarni da shi mas’laha ce da rahama ga mutane. Albara’u ɗan Azib yana cewa game da faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka): “Kuma kada ku nufaci mummuna daga cikinsa, ku ce daga gare shi za ku ciyar....,” ya ce: “A kanmu ne mu mutanen Madina masu gonakin dabino wannan ayar ta sauka, kowannenmu yana fito da dabinon gonarsa gwargwadon yawansa da ƙanƙantarsa, nono ɗaya ko biyu ya rataye shi a cikin masallacin Annabi (ﷺ), su kuma ahlus-suffah, wato talakawan da suke kwana a masallacin, waɗanda ba su da wani abincin da suke samu su ci, don haka idan ɗayansu ya ji yunwa, sai ya sa sanda ya daki wannan nonon dabinon na rataye, sai dabinon ya zubo ƙasa, sai ya ɗauka ya ci. To akwai wasu mutane da ba sa ƙaunar aikata alheri, sai ɗayansu ya ɗauko nonon dabino wanda ya lalace, ya zo ya rataye shi a masallaci. Sai Allah ya saukar da wannan ayar, yana cewa: “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku ciyar daga daɗaɗan abin da kuka tsuwurwurta, da kuma abin da muka fitar muku daga ƙasa, kuma kar ku nufaci mummuna daga cikinsa, ku ce daga gare shi za ku ciyar, alhalin ku ma kanku (idan an ba ku) ba za ku karɓe shi ba, sai kun runtse idanu.” Al-Bara’u ya ce: “Da za a yi wa ɗayanku kyauta da abin da shi ya bayar kyauta, to da ba zai karɓa ba, sai ya runtse ido, ko ya karɓa cikin jin nauyi.” Al-Bara’u ya ce: “Daga wannan ranar kowa sai ya riƙa kawo dabino mai kyau.” [Tirmizi #2987]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa bayinsa muminai cewa, Shaiɗan ne yake tsoratar da su da cewa za su talauce idan suna sadaka da dukiyoyinsu, yana umartar su da rowa da aikata kowane irin saɓon Allah da miyagun ayyuka. Shi kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa bayinsa alƙawarin gafara ne game da laifin da za su yi, su tuba daga baya, kuma yana yi musu alƙawarin zai mayar musu da duk abin da suka bayar sadaka na dukiyarsu, kuma zai haɓaka musu arzikinsu, ya ƙara yawan ladansu, domin shi Allah mai yalwar falala ne, kuma mai cikakken sani. Yana ba da hikima ga wanda ya ga dama daga bayinsa, ya ba su damar fahintar manufofin hukunce-hukuncensa da sirrin da yake cikin yi masa ɗa’a da saɓa wa tafarkin Shaiɗan. Duk kuma wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa hikima cikin bayinsa, to lalle ya ba shi alheri mai yawa, amma ba kowa ne yake ganewa ya wa’azantu ba, sai masu cikakken hankali. Annabi (ﷺ) yana cewa: “Hassada ba ta halatta sai ga mutum biyu. Mutumin da Allah ya ba shi dukiya, sannan ya ba shi ikon kashe ta inda ya dace. Sai kuma mutumin da Allah ya ba shi hikima (ilimi), ya kasance yana hukunci da ita, yana kuma karantar da ita.” [Bukhari #73, Muslim #816]. Watau mutum ya ji a ransa shi ma yana son samun irin haka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da bayinsa cewa, duk wata sadaka da za su bayar ko wani bakance da za su wajabta wa kansu, to Allah yana sane da shi, babu abin da yake ɓoye masa, kuma zai yi sakayya a kai. Duk kuma wanda zai zo ranar alƙiyama, bai fitar da zakkarsa ba ko bai sauke bakancensa ba, to babu wanda zai iya taimaka masa a ranar, ya kuɓutar da shi daga kamun Ubangiji (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa bayinsa cewa, idan suka fitar da sadakarsu ta neman lada suka bayar da ita a fili, to madalla da abin da suka yi, matuƙar dai ba da nufin riya ba. Idan kuma sun fitar sun bayar da ita a ɓoye, to yin hakan shi ya fi falala a wurin Allah. Kuma Allah zai kankare musu laifukansu da irin wannan sadakar ta ɓoye, ko ta sarari, Allah yana ganin duk ayyukansu, kuma zai yi musu sakayya a kai. Malaman tafsiri sun haɗu a kan cewa, wannan ayar tana magana ne a kan sadakar da aka yi ta nafila, ba zakka ba. Ita zakka an fi son bayyana ta a fili, domin ita alama ce ta tabbatar Musuluncin mutum, kuma da wannan ne zai tsare dukiyarsa. Amma sadakar neman lada an fi son a ɓoye ta, sai dai idan akwai wata maslaha da aka hango game da bayyana ta, to sai a bayyana ta babu komai. Annabi (ﷺ) ya ambaci wasu mutane su bakwai da Allah zai saka su a inuwar Al’arshinsa, ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa; daga cikinsu akwai mutumin da ya yi sadaka da hannunsa na dama, ya ɓoye ta har hannunsa na hagu ma bai san abin da hannun damansa ya bayar ba.” [Bukhari #1423, da Muslim #1031]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, shiriyar mutane ba a hannunsa take ba; abin da yake wajibi a kansa shi ne ya isar musu da saƙon da Allah ya aiko shi da shi, shi kuma Allah shi ne yake kimsa shiriya a zuciyar wanda ya ga dama daga cikin bayinsa. Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Musulmi sun ji damuwa game da ba wa ‘yan’uwansu na jini kafirai sadakar dukiyarsu, saboda kafircinsu, sai suka tambayi Annabi (ﷺ) game da haka, sai Allah ya saukar da wannan ayar.” [Musnadul Bazzar #5042, At-Tabrani #12453, Alhakim 2:313]. Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) kuma yana cewa: “Da farko an umarce mu da kada mu bayar da sadaka sai ga Musulmi, har sai da wannan ayar ta sauka, sai Annabi (ﷺ) ya umarce mu da mu bayar da sadaka ga duk wanda ya nema, daga kowane addini yake.” [Ibni Abi Hatim, Tafsir 2:537]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, sadakar da masu dukiya suke yi, su za ta amfana, kuma sadakar da za ta amfani mai yin ta ita ce wadda mutum ya yi don Allah shi kaɗai, tare da fatan ya sami ganin fuskar Allah ranar alƙiyama. Kuma duk abin da bayinsa suka bayar sadaka a nan duniya, za su sami cikakken ladansa ranar lahira, babu abin da zai salwanta a ciki. A nan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin waɗanda suka fi cancantar a taimaka musu da sadaka, watau waɗanda aka tsare su ko suka ba da kansu domin jihadi saboda ɗaukaka kalmar Allah, da bayar da kariya ga Musulmi da Musulunci, don haka ba sa fita ko’ina don neman arziki ko don kasuwanci, ta yadda wanda bai san su ba idan ya gan su, ya ga kawaicinsu da kamewarsu da rashin nuna kwaɗayinsu ga abin duniya, sai ya zaci su masu kuɗi ne. Abin da kawai zai sa a gane su shi ne alamun buƙata da talauci, wanda sai mai nutsuwa da kaifin hankali zai gani a fuskarsu ko ya gane ta wasu maganganunsu, amma su kwata-kwata ba sa roƙon mutane, ballantana har su nace wajen roƙon su. Sannan Allah ya bayyana cewa, sadakar da muminai suka bayar kaɗan ne ko mai yawa, to Allah yana sane da ita, kuma zai yi musu sakamako a kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawari ga waɗanda suke ciyar da dukiyarsu dare da rana, a sarari da ɓoye cewa, suna da sakamako babba a wurin Ubangijinsu ranar lahira, babu wani abin tsoro da zai same su a nan gaba, kuma ba za su yi baƙin ciki ba game da abin da ya wuce, don haka dai za su sami abin da suke so, kuma za su tsira daga abin da suke ƙi.
ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ ٱلرِّبَوٰاْ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِي يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ مِنَ ٱلۡمَسِّۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡبَيۡعُ مِثۡلُ ٱلرِّبَوٰاْۗ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلۡبَيۡعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰاْۚ فَمَن جَآءَهُۥ مَوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّهِۦ فَٱنتَهَىٰ فَلَهُۥ مَا سَلَفَ وَأَمۡرُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَنۡ عَادَ فَأُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 2:275Waɗanda suke cin riba ba za su tashi ba (daga ƙaburburansu) sai kamar tashin mutumin da Shaiɗan yake bige shi da hauka. Hakan zai faru ne don sun ce: “Lalle kasuwanci kamar riba yake.” Kuma Allah Ya halatta kasuwanci, kuma Ya haramta riba. To duk wanda wa’azi ya zo masa daga wurin Ubangijinsa, sai ya daina, to abin da ya wuce a baya ya zama nasa, kuma al’amarinsa yana wurin Allah; wanda kuma ya sake komawa daga baya, to waɗannan su ne ma’abota wuta, suna masu dawwama a cikinta.
يَمۡحَقُ ٱللَّهُ ٱلرِّبَوٰاْ وَيُرۡبِي ٱلصَّدَقَٰتِۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ
Open ayah 2:276Allah Yana shafe albarkar riba, Yana kuma haɓaka sadaƙa. Kuma Allah ba Ya son dukkan wani mai yawan kafircewa, mai yawan saɓo.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 2:277Lalle waɗanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka nagari kuma suka tsayar da salla, kuma suka bayar da zakka, to suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu jin tsoro a gare su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَذَرُواْ مَا بَقِيَ مِنَ ٱلرِّبَوٰٓاْ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 2:278Ya ku waɗanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku rabu da abin da ya yi ragowa na riba in har kun kasance muminai.
فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُواْ فَأۡذَنُواْ بِحَرۡبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَإِن تُبۡتُمۡ فَلَكُمۡ رُءُوسُ أَمۡوَٰلِكُمۡ لَا تَظۡلِمُونَ وَلَا تُظۡلَمُونَ
Open ayah 2:279Idan kuwa ba ku aikata haka ba, to ku saurari wani yaƙi daga Allah da Manzonsa; idan kuwa kun tuba, to uwar kuɗin taku ce, ba za ku yi zalunci ba, ku ma kuma ba za a zalunce ku ba.
وَإِن كَانَ ذُو عُسۡرَةٖ فَنَظِرَةٌ إِلَىٰ مَيۡسَرَةٖۚ وَأَن تَصَدَّقُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 2:280Kuma idan (mai cin bashin) ya kasance ma’abocin matsi, to sai a yi masa jinkiri zuwa lokacin da zai sami sauƙi, kuma in da za ku yi sadaƙa shi ya fi alheri a gare ku in kun kasance kuna da masaniya.
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا تُرۡجَعُونَ فِيهِ إِلَى ٱللَّهِۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 2:281Kuma ku kiyayi wani yini da za a mayar da ku zuwa ga Allah a cikinsa, sannan kowane rai za a cika masa abin da ya aiwatar na aiki, kuma su ba za a zalunce su ba. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama bayanin mutanen kirki, masu ba da dukiyarsu don Allah, suna taimaka wa mabuƙata da talakawa, sai kuma ya kawo bayani cikin waɗannan ayoyi a kan masu cin dukiyar riba da dukiyar da aka tara ta haramtacciyar hanya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, maciya riba ranar alƙiyama ba za su tashi daga ƙaburburansu lafiya lau ba, a’a, za su tashi ne kamar waɗanda Shaiɗan ya shafe su da ciwon hauka, saboda a nan duniya sun riƙa da’awar cewa, ai da saye da sayarwa da Allah ya halatta, da kuɗin riba, duk abu ɗaya ne, wai duk hanya ce ta neman kuɗi, me zai sa a halatta ɗaya, a kuma haramta ɗayar? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata wannan da’awar tasu, ya ce, duk wata riba da mutum zai samu ta hanyar kasuwanci to ta halatta, amma an haramta masa cin kuɗin riba, watau ba da bashi da ruwa, domin ba ɗaya suke ba. Duk wanda hukuncin hana cin kuɗin riba ya zo masa, ya daina, to shi ke nan babu komai a kansa game da abin da ya riga ya wuce, kuma al’amarinsa yana wurin Allah, ko dai ya yi masa gyaɗar dogo ya ci gaba da tsayuwa a kan cin halal, ko kuma ya taɓar da shi, ya koma ruwa. To amma fa duk wanda ya kuskura ya koma ga cin riba bayan ya san da haramcinta, amma ya dage a kai, to wannan shi ya cancanta shiga wuta, ya dawwama a cikinta, babu abin da zai hana shi dawwama a wuta sai imaninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, yana shafe albarkar dukiyar riba, yana kuma haɓaka ladan wanda ya ba da dukiyarsa sadaka, har dukiyarsa ita ma za ta haɓaka a dalilin hakan. Allah ba ya son wanda yake yawan butulce wa ni’imominsa, yake kuma halatta cin kuɗin riba, ya zarce cikin saɓon Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi alƙawari ga waɗanda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka nagari, kuma suka tsayar da salla kamar yadda ya kamata, sannan kuma suka ba da zakkar dukiyarsu ga waɗanda ya dace su ba da cewa, ladansu yana nan wurin Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma ba tsoro a tattare da su game da abin da za su tarar bayan mutuwarsu, hakanan babu wani baƙin ciki da za su yi game da abin da suka bari a nan duniya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da yi wa muminai wa’azi da gargaɗi, da su ji tsoron Allah, su yi watsi da duk wata mu’amala ta riba wadda suke cikin ƙulla ta yayin da wannan gargaɗi ya zo musu, idan dai da gaske suke su muminai ne. Idan kuma sun ƙi ji, sun ƙi bari, to su sanar da kawunansu, su kuma sanar da wasu masu irin aikinsu cewa, Allah da Manzansa suna shelanta yaƙi da su. Idan kuma sun tuba, sun daina mu’amalar riba, to su karɓi uwar kuɗinsu da suka bayar bashi, kada su karɓi komai a kai, idan kuwa sun yi haka to sun yi zalunci, kamar yadda su ma kada wani ya zalunce su, ya ƙi biyan su kuɗaɗensu gaba ɗaya. Amma idan shi wanda ake bin sa bashi ba shi da abin biya, yana cikin hali na matsi, to su ɗan saurara masa har Allah ya hore masa, ko kuma su rage masa shi, wannan ya fi musu alheri in da a ce sun san irin gwaggwaɓar ladan da za su samu. Sahabin nan na Annabi (ﷺ), Abu Ƙatada (Allah ya kara masa yarda), an ce yana bin wani bashi, sai ya riƙa ɓuya, har wata rana ya same shi, sai ya ce masa: “Ina cikin halin matsi ne, ba ni da abin biya.” Sai Abu Ƙatada ya ce: “Za ka rantse da Allah?” Ya ce: “Na rantse da Allah.” Sai Abu Ƙatada ya ce: “Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Duk wanda zai yi farin ciki Allah ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar lahira, to ya sassauta wa wanda yake bi bashi yana cikin matsuwa ko ma ya yafe masa duka.” [Muslim #1563]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi gargaɗi da a kiyayi wani yini wanda idan ya zo, duk wani abu da mutum yake tinƙaho da shi a nan duniya, na dukiya ko waninta, zai gushe, kuma za a mayar da kowa zuwa ga mahalaccinsa Allah; a ranar lahira zai saka wa kowa a kan irin ayyukan da ya zo da su, don haka babu abin da zai amfani mutum a ran nan sai aikinsa na ƙwarai, kuma kowa za a ba shi sakamakonsa cikakke, ba tare da an tauye masa komai ba na ladansa, ko a ƙara masa wani laifi a kan laifukansa. Abdullahi ɗan Abbas yana cewa: “Wannan ayar ita ce ta ƙarshen sauka a Alƙur’ani.” [Dubi: An-Nasa’i: At-Tafsir #77, 78; Ibn Jarir #6311].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَدَايَنتُم بِدَيۡنٍ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى فَٱكۡتُبُوهُۚ وَلۡيَكۡتُب بَّيۡنَكُمۡ كَاتِبُۢ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَلَا يَأۡبَ كَاتِبٌ أَن يَكۡتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ ٱللَّهُۚ فَلۡيَكۡتُبۡ وَلۡيُمۡلِلِ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ وَلۡيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥ وَلَا يَبۡخَسۡ مِنۡهُ شَيۡـٔٗاۚ فَإِن كَانَ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ سَفِيهًا أَوۡ ضَعِيفًا أَوۡ لَا يَسۡتَطِيعُ أَن يُمِلَّ هُوَ فَلۡيُمۡلِلۡ وَلِيُّهُۥ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَٱسۡتَشۡهِدُواْ شَهِيدَيۡنِ مِن رِّجَالِكُمۡۖ فَإِن لَّمۡ يَكُونَا رَجُلَيۡنِ فَرَجُلٞ وَٱمۡرَأَتَانِ مِمَّن تَرۡضَوۡنَ مِنَ ٱلشُّهَدَآءِ أَن تَضِلَّ إِحۡدَىٰهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحۡدَىٰهُمَا ٱلۡأُخۡرَىٰۚ وَلَا يَأۡبَ ٱلشُّهَدَآءُ إِذَا مَا دُعُواْۚ وَلَا تَسۡـَٔمُوٓاْ أَن تَكۡتُبُوهُ صَغِيرًا أَوۡ كَبِيرًا إِلَىٰٓ أَجَلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ أَقۡسَطُ عِندَ ٱللَّهِ وَأَقۡوَمُ لِلشَّهَٰدَةِ وَأَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَرۡتَابُوٓاْ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً حَاضِرَةٗ تُدِيرُونَهَا بَيۡنَكُمۡ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَلَّا تَكۡتُبُوهَاۗ وَأَشۡهِدُوٓاْ إِذَا تَبَايَعۡتُمۡۚ وَلَا يُضَآرَّ كَاتِبٞ وَلَا شَهِيدٞۚ وَإِن تَفۡعَلُواْ فَإِنَّهُۥ فُسُوقُۢ بِكُمۡۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱللَّهُۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ
Open ayah 2:282Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka ba wa junanku bashi zuwa wani lokaci sananne, to ku rubuta shi, kuma a sami wani marubuci da zai rubuta a tsakaninku da adalci, kuma marubucin kar ya ƙi rubutawa kamar yadda Allah ya sanar da shi. Don haka ya rubuta, kuma shi wanda haƙƙi yake kansa sai ya yi shifta gare shi, kuma ya ji tsoron Allah Ubangijinsa, kuma kada ya tauye wani abu a cikinsa. To idan wanda haƙƙi yake kansa ya kasance wawa ne ko mai rauni ko ba shi da ikon ya yi shifta shi da kansa, to sai majiɓincin lamarinsa ya yi shifta (a madadinsa) da adalci, kuma ku kafa shaidu biyu cikin mazajenku; kuma idan ba su kasance mazaje biyu ba, to sai a nemi namiji ɗaya da mata biyu daga shaidun da kuka yarda da su, saboda idan ɗaya daga cikinsu ta manta sai ɗayar ta tuna mata, kuma kada shaidun su ƙi zuwa idan an kiraye su, kuma kada ku ƙosa, ku rubuta shi, kaɗan ne ko da yawa, zuwa cikar wa’adinsa. Abin da aka ambata mukun nan shi ne ya fi zama adalci a wajen Allah, kuma ya fi daidaita shaida, kuma shi ya fi kusata ku ta yadda ba za ku yi shakka ba, sai dai idan ya kasance ciniki ne hannu da hannu da kuke gudanar da shi tsakaninku; to babu laifi a kanku idan ba ku rubuta shi ba. Kuma ku kafa shaida idan kun yi hulɗa ta ciniki, kuma kada marubuci ya yi cuta, haka shi ma mai shaida (kada ya yi cuta). Idan kuwa har kuka aikata haka, to lalle wannan fasiƙanci ne a gare ku. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma Allah Yana sanar da ku (dokokinsa). Kuma Allah Masanin komai ne.
۞وَإِن كُنتُمۡ عَلَىٰ سَفَرٖ وَلَمۡ تَجِدُواْ كَاتِبٗا فَرِهَٰنٞ مَّقۡبُوضَةٞۖ فَإِنۡ أَمِنَ بَعۡضُكُم بَعۡضٗا فَلۡيُؤَدِّ ٱلَّذِي ٱؤۡتُمِنَ أَمَٰنَتَهُۥ وَلۡيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥۗ وَلَا تَكۡتُمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَۚ وَمَن يَكۡتُمۡهَا فَإِنَّهُۥٓ ءَاثِمٞ قَلۡبُهُۥۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ
Open ayah 2:283Kuma idan kun kasance a halin tafiya, kuma ba ku sami marubuci ba, to sai a ba da jingina da za a karɓa, kuma idan sashinku ya amince wa sashi, to shi wanda aka amincewan ya bayar da amanarsa, kuma ya kiyayi Allah Ubangijinsa. Kuma kada ku ɓoye shaida; duk wanda ya ɓoye ta kuwa, to lalle shi zuciyarsa a cike take da saɓo. Kuma Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin yadda ya kamata muminai su gudanar da harkar bashi a tsakaninsu, inda ya umarce su da cewa, idan sun yi wata mu’amala ta bashi a tsakaninsu zuwa wani lokaci sananne, to su rubuta abin da suka yi yarjejeniya a kansa a tsakaninsu, don gudun mantawa ko jayyaya a nana gaba. Wanda duk zai rubuta wannan yarjejeniyar tasu, ya zamana ya iya rubutu kuma adali ne, mai gaskiya. Wanda duk ya iya rubutu kuma aka neme shi da rubuta irin wannan yarjejeniya, to kada ya ce ba zai yi ba. Ya tuna cewa, Allah ne ya ba shi wannan ilimin na rubutu, kuma shi ne ya umarce shi da ya rubuta musu. Kuma wanda zai riƙa faɗa ana rubutawa, shi ne wanda ya ci bashin da kansa, kuma ya ji tsaron Allah, kada ya rage wa mai haƙƙi komai cikin haƙƙinsa. To idan wanda bashin yake kansa ya zamanto wawa ne ko yaro ne, wanda ba zai iya komai ba ko kuma mai taɓin hankali ne ko kuma dai ba zai iya shifta ba saboda wani dalili da zai hana shi yi, to sai waliyyinsa wanda yake kula da al’amuransa ya yi shiftar, kuma shi ma lalle ya yi gaskiya, ya yi adalci a yayin shiftar. Hakanan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiryar da bayinsa muminai a kan su kafa shaidu biyu maza Musulmai adalai, idan ba a samu maza ba, to sai a kafa shaida da namiji ɗaya da mata biyu su ma adalai amintattu, domin idan ɗaya ta manta, sai ɗayar ta tunatar da ita. Kuma su ma shaidun su sani bai dace a gare su ba, idan an kirawo su su zama shaidu, ko su bayar da shaidar da suka sani, su ce ba za su zo ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nusar da bayinsa cewa, kada su ƙosa wajen rubuta mu’amalar kowane irin bashi ne, kaɗan ne ko mai yawa, zuwa ga wa’adinsa, domin rubuta bashi da tantance lokacinsa, ya fi adalci a wurin Allah, kuma zai fi taimaka wa masu ba da shaida, ta yadda ba za a sami saɓani a tsakaninsu ba, domin dukkansu za su dogara da abin da aka rubuta ne, kamar yadda yin hakan zai kawar da duk wani kokwanto. Amma idan ciniki ne tsakanin mai saye da mai sayarwa kowa zai karɓi haƙƙinsa a nan take, to babu laifi don ba a rubuta komai a lokacin ba, amma dai yana da kyau duk da haka a sami shaidu. Haka kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana masu haƙƙi su cutar da mai rubutawa ko mai shaida; mai rubutun da mai shaidar su ma kada su cutar da masu haƙƙi ta kowace hanya, domin yin haka saɓa wa Allah ne. Sannan Allah ya umarce su da su zama masu taƙawa, ya kuma sanar da su cewa, yana koyar da su hukunce-hukuncen shari’arsa ne domin rahama gare su; shi kuma masanin komai ne, babu abin da yake ɓuya a gare shi, don haka zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shar’anta wa muminai cewa, yayin da suke cikin halin tafiya, kuma suka ƙulla mu’amalar bashi zuwa wani sanannen lokaci, kuma ba su sami wanda zai rubuta masu ba a daidai lokacin, to sai su bi wata hanyar daban don tabbatar da wannan bashi, watau wanda ya bayar da bashin ya karɓi wani kayan jingina daga wurin wanda ya ci bashin, ya ajiye a wurinsa, har sai ya biya bashin, sai ya mayar masa da abinsa. Idan kuwa shi mai bayar da bashin ya amince wa wanda zai karɓi bashin, ya ba shi ba tare da wata jingina ba, to shi wanda ya ci bashin ya yi ƙoƙari ya dawo masa da haƙƙinsa cikkake, ya guji saɓa wa Allah, don kada ya kama shi da laifin saɓa wa umarninsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana ɓoye shaida, ko dai ta hanyar rinto, ko kuma ta hanyar ƙari ko ragi a kan abin da yake gaskiya, Allah ya sifanta wanda yake ɓoye shaida a matsayin wanda zuciyarsa take cike da saɓon Allah, kuma Allah yana sane da duk ayyukan bayinsa, zai yi musu sakamako gwargwadon aikin kowa.
لِّلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَإِن تُبۡدُواْ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ أَوۡ تُخۡفُوهُ يُحَاسِبۡكُم بِهِ ٱللَّهُۖ فَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Open ayah 2:284Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa na Allah ne. Kuma in har kuka bayyana abin da yake cikin zukatanku ko kuka ɓoye shi, Allah zai yi muku hisabi a kansa, sai Ya yi gafara ga wanda Ya ga dama, Ya kuma yi azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai.
ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 2:285Manzon ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, muminai ma haka, kowanne ya yi imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa, (suna cewa) : “Ba ma nuna bambanci tsakanin ɗaya daga cikin manzanninsa.” Kuma suka ce: “Mun ji kuma mun bi ; muna neman gafararka ya Ubangijinmu, kuma zuwa gare Ka ne makoma take.
لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَعَلَيۡهَا مَا ٱكۡتَسَبَتۡۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذۡنَآ إِن نَّسِينَآ أَوۡ أَخۡطَأۡنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تَحۡمِلۡ عَلَيۡنَآ إِصۡرٗا كَمَا حَمَلۡتَهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلۡنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِۦۖ وَٱعۡفُ عَنَّا وَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَآۚ أَنتَ مَوۡلَىٰنَا فَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 2:286Allah ba Ya kallafa wa rai sai abin da zai iya. Abin da ya aikata (na alheri) nasa ne, hakanan sakamakon abin da ya aikata (na sharri) shi ma nasa ne. Ya Ubangijinmu, kada Ka riƙe mu da laifi idan mun yi mantuwa ko mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu, kada kuma Ka ɗora mana wani nauyi irin wanda ka ɗora wa waɗanda suke gabaninmu. Ya Ubangijinmu, kada kuma Ka ɗora mana abin da ba mu da iko a kansa, kuma Ka yi mana afuwa, kuma Ka yi mana gafara, kuma Ka ji ƙan mu; Kai ne Majiɓincin lamarinmu, don haka Ka taimake mu a kan mutane kafirai. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama bayanin abubuwan da wannan Sura ta ƙunsa, waɗanda suka ƙunshi dalilan kaɗaitar Ubangiji, da ingancin annabci da gaskiyar tashin alƙiyama da bayanin salla da zakka da ƙisasi da azumi da Hajji da jihadi da haila da saki da idda da khul’i da ila’i da shayarwa da riba da kasuwanci da hukuncin bashi, sai kuma a nan Allah yake bayinin cewa, shi ne mamallakin sammai da ƙasa, yana da damar ya lizimta wa bayinsa duk hukuncin da ya ga dama, saboda su bayinsa ne, kuma yana sane da duk abin da yake zukatansu, don haka zai yi musu hisabi a kan abin da suka bayyana da wanda suka ɓoye a zukatansu, daga nan sai ya gafarta wa wanda ya ga dama, ya azabtar da wanda ya ga dama, babu abin da zai gagare shi, domin shi mai iko ne a kan komai. Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da wannan ayar ta sauka, abin ya yi wa sahabbai tsanani, sai suka je wurin Annabi (ﷺ), suka gurfana a gabansa, suka ce: “Ya Manzon Allah, an kallafa mana ayyukan da za mu iya aikatawa, kamar salla da azumi da jihadi da sadaka, kuma ga shi an saukar maka da wannan ayar, wadda ba za mu iya ɗaukar ta ba.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce musu: “Kuna so ne ku faɗi irin abin da Yahudawa da Nasara suka faɗi a gabaninku cewa, sun ji kuma sun ƙi? A’a, ku sai ku ce: “Mun ji, mun bi, kuma ka yi mana gafara, ya Ubangijinmu, kuma zuwa gare ka makoma take.” To lokacin da sahabbai suka ci gaba da faɗar haka, har harshensu ya saba da haka, sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, muminai ma haka, kowanne ya yi imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa….” har zuwa ƙarshen ayar. Yayin da suka yi haka, sai Allah ya shafe wancan hukuncin da ya saukar da faɗarsa: “Allah ba ya kallafa wa rai sai abin da zai iya, abin da ya aikata na alheri nasa ne, hakanan sakamakon abin da ya aikata na sharri shi ma nasa ne. Ya Ubangijinmu, kada ka riƙe mu da laifi idan mun yi mantuwa, ko mun yi kuskure.” Allah ya ce: ‘Na’am!’ “Ya Ubangijinmu, kada kuma ka ɗora mana wani nauyi irin wanda ka ɗora wa waɗanda suke gabaninmu.” Allah ya ce: ‘Na’am!’ Ya Ubangijinmu, kada kuma ka ɗora mana abin da ba mu da iko a kansa. Allah ya ce: ‘Na’am!’ “Kuma ka yi mana afuwa, kuma ka yi mana gafara, kuma ka ji ƙan mu; kai ne majiɓincin lamarinmu, don haka ka taimake mu a kan mutanen da suke kafirai.” Allah ya ce: ‘Na’am!’ [Muslim #125]. Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Baƙara da daddare, sun ishe shi.” [Bukhari #5008]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas ya ce, wata rana mala’ika Jibrilu yana zaune tare da Manzon Allah (ﷺ), sai ya ji wata ƙara a samansa, sai ya ɗaga kansa ya ce: “Wannan wata ƙofa ce a sama da aka buɗe ta a yau, ba a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani mala’ika ya sauko ta wannan ƙofar, ya ce: “Wannan wani mala’ika ne da ya sauka ƙasa, bai taɓa saukowa ba sai yau, sai ya yi sallama ya ce: “Albishirinka, ga wani haske guda biyu da aka ba ka, ba a taɓa ba da su ga wani annabi ba gabaninka, su ne Fatihatul Kitabi, da ayoyin ƙarshen Suratul Baƙara, duk wani harafi da za ka karanta daga cikinsu sai an ba ka abin da ka roƙa.” [Muslim #806].