آل عمران

Aal-i-Imraan

The Family of Imraan · Surah 3 · Ayahs: 200 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓمٓ

    Open ayah 3:1

    Alif Laam Miim .

  2. ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُ

    Open ayah 3:2

    Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Shi Rayayye ne, Tsayayye da Zatinsa.

  3. نَزَّلَ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَأَنزَلَ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

    Open ayah 3:3

    Ya saukar maka da Littafi da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi, kuma Ya saukar da Attaura da Linjila.

  4. مِن قَبۡلُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَأَنزَلَ ٱلۡفُرۡقَانَۗ إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ

    Open ayah 3:4

    Tun kafin (Alƙur’ani), (don su zama) shiriya ga mutane, kuma Ya saukar da mai rarrabewa (tsakanin ƙarya da gaskiya). Lalle waɗanda suka kafirce wa ayoyin Allah, suna da azaba mai tsanani, kuma Allah Mabuwayi ne, Ma’abocin ɗaukar fansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da haruffa kamar yadda ya yi a Suratul Baƙara , domin bayanin mu’ujizar Alƙur’ani, don nuna babu mai iya kawo kamarsa, duk kuwa da cewa magana ce da ta ƙunshi haruffa na Larabawa irin waɗanda suke rubutu da su. Sannan Allah ya yi bayanin Allantakarsa da cewa, shi ne abin bauta na gaskiya, wanda daga cikin siffofinsa, shi ne Rayayye, mai cikakkiyar rayuwa, wadda ta siffantu da dukkan siffofi na kamala, Tsayayye da Zatinsa, ba shi da buƙata a wurin wani cikin halittarsa, kuma shi ne mai tsayawa da taimakon kowa da komai, don haka kowa yana da buƙata a wurinsa. Daga cikin taimakonsa da rahamarsa ga bayinsa, shi ne ya aiko musu da Annabi (ﷺ), ya kuma saukar masa da Alƙur’ani, wanda yake cike da gaskiya, kuma yake gaskata littattafan da suka gabace shi. Kuma Allah ya saukar da Attaura ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Linjila ga Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) tun kafin saukar da Alƙur’ani. Allah ya saukar da littattafan nan ne dukkansu saboda shiriyar da mutane. A cikinsu Allah ya saukar da abin da yake bambancewa tsakanin ƙarya da gaskiya da tsakanin shiriya da ɓata, saboda haka Allah ya yi alƙawarin azaba mai tsanani ga waɗanda suka kafirce wa ayoyinsa a ranar gobe ƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) babu wanda zai iya rinjayar sa, kuma babu abin da zai gagare shi, kuma shi mai gaggawar ɗaukar fansa ne ga wanda ya saɓa masa.

  5. إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَخۡفَىٰ عَلَيۡهِ شَيۡءٞ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ

    Open ayah 3:5

    Lalle Allah babu abin da yake ɓoyuwa a gare Shi a ƙasa ko a sama.

  6. هُوَ ٱلَّذِي يُصَوِّرُكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ كَيۡفَ يَشَآءُۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 3:6

    Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu irin yadda Ya ga dama, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima.

  7. هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ مِنۡهُ ءَايَٰتٞ مُّحۡكَمَٰتٌ هُنَّ أُمُّ ٱلۡكِتَٰبِ وَأُخَرُ مُتَشَٰبِهَٰتٞۖ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمۡ زَيۡغٞ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَٰبَهَ مِنۡهُ ٱبۡتِغَآءَ ٱلۡفِتۡنَةِ وَٱبۡتِغَآءَ تَأۡوِيلِهِۦۖ وَمَا يَعۡلَمُ تَأۡوِيلَهُۥٓ إِلَّا ٱللَّهُۗ وَٱلرَّٰسِخُونَ فِي ٱلۡعِلۡمِ يَقُولُونَ ءَامَنَّا بِهِۦ كُلّٞ مِّنۡ عِندِ رَبِّنَاۗ وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّآ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

    Open ayah 3:7

    Shi ne Wanda ya saukar maka da Littafi, a cikinsa akwai ayoyi masu bayyanannun hukunce-hukunce, su ne asalin Littafin, akwai kuma waɗansu masu rikitarwa; to amma waɗanda suke da karkata a zukatansu sai su riƙa bin abin da yake rikitarwar a cikinsu don neman fitina da kuma neman sanin haƙiƙanin fassararsa. Kuma babu wanda ya san haƙiƙanin fassararsa sai Allah. Kuma masu zurfi cikin ilimi kuma suna cewa: “Mun yi imani da shi, dukkaninsa daga wurin Ubangijinmu yake.” Kuma ba mai wa’azantuwa sai masu hankali.

  8. رَبَّنَا لَا تُزِغۡ قُلُوبَنَا بَعۡدَ إِذۡ هَدَيۡتَنَا وَهَبۡ لَنَا مِن لَّدُنكَ رَحۡمَةًۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡوَهَّابُ

    Open ayah 3:8

    “Ya Ubangijinmu, kada Ka karkatar da zukatanmu bayan Ka shiryar da mu, kuma Ka yi mana rahama daga gare Ka. Lalle kai Mai yawan baiwa ne.”

  9. رَبَّنَآ إِنَّكَ جَامِعُ ٱلنَّاسِ لِيَوۡمٖ لَّا رَيۡبَ فِيهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ

    Open ayah 3:9

    “Ya Ubangijinmu, lalle Kai ne Mai tattara mutane a yinin da babu kokwanto a cikinsa. Lalle Allah ba Ya saɓa alƙawari.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin gamammen iliminsa, wanda ya kewaye komai, don babu wani abu da yake ɓuya a gare shi, a sama yake ko a ƙasa. Shi ne yake halittar ku bisa kamanni daban-daban a cikin cikin iyayenku yadda ya ga dama, don haka shi ne kaɗai ya cancanta a bauta wa; ba shi da wani abokin tarayya. Shi ne Mabuwayi a cikin mulkinsa; ba mai iya ja da shi ko ya fi ƙarfinsa, kuma shi mai hikima ne a cikin ayyukansa da shari’unsa, babu wani tasgaro a cikinsu ko kaɗan. Shi ne wanda ya saukar wa Annabi (ﷺ) Alƙur’ani, wanda ya ƙunshi ayoyin da suke a fili, ma’anoninsu a bayyane suke, babu wani abu mai rikitarwa tare da su, su ne kuma tushen wannan littafi, kuma su ne mafiya yawa a cikinsa. A cikinsa kuma akwai waɗansu ayoyi waɗanda ma’anarsu take da rikitarwa ga wasu mutane. To amma sai a samu waɗansu karkatattun mutane masu cutar kauce wa gaskiya a zukatansu, suna bibiyar waɗannan ayoyi masu rikitarwa, suna barin ayoyin da ma’anoninsu suke a fili, ba don komai ba sai don su ɓatar da mutane, su jefa shakka a zukatansu, don su sami wani abu da za su kafa hujja da shi a kan soye-soyen zukatansu. Su kuwa waɗannan ayoyi masu rikitarwa, babu wanda ya san haƙiƙanin fassararsu sai Allah (Mai tsarki da daukaka). Malamai masu zurfin ilimi na Alƙur’ani su ma sukan san tafsirin ma’anonin ayoyin, amma ba za su iya sanin haƙiƙanin al’amarin ba, da yadda ƙarshen zai kasance, domin wannan Allah ne kaɗai ya san shi. Malamai masu zurfin ilimi sukan shelanta imaninsu da waɗannan ayoyi masu rikitarwa. Duk kuma ayoyin na Alƙur’ani daga Allah ne, amma ba kowa ne yake wa’azantuwa ba sai masu lafiyayyen hankali. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Annabi (ﷺ) ya karanta wannan ayar, sai ya ce: “Idan kika ga waɗanda suke bibiyar ayoyi masu rikitarwa a cikin Alƙur’ani; to su ne waɗanda Allah ya ambata, don haka ki guje su.” [Bukhari #4547, Muslim #2665]. Malamai masu zurfin ilimi addu’a suke yi ko da yaushe, suna roƙon Allah (Mai tsarki da daukaka) kada ya karkatar da zukatansu su saki shiriya bayan Allah ya shiryar da su, ya yi musu rahama, ya ƙara musu imani da tsayuwa a kan gaskiya, domin Allah shi ne mai yawan kyauta da ihsani ga bayinsa. Kuma suna addu’a suna cewa: “Ya Allah kai ne za ka tara mutane a ranar Alƙiyama, ranar da babu shakka a zuwanta, domin yin hukunci da sakayya ga kowa a kan aikinsa, don haka ka gafarta mana a wannan ranar, ka yi mana afuwa.” Sun kuma yi Imani da cewa, lalle Allah ba ya saɓa alƙawarinsa na cewa, wanda duk ya yi imani da shi, ya bi Manzonsa; to zai gafarta masa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle zukatan ‘yan’adam duka suna tsakanin yatsu biyu ne daga yatsun Allah Mai rahama, tamkar zuciya ɗaya, yana sarrafa su yadda ya ga dama.” Sannan sai Annabi (ﷺ) ya yi addu’a yana cewa: “Ya Allah Mai sarrafa zukata, ka sarrafa zukatanmu a kan ɗa’arka.” [Muslim #2654].

  10. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَن تُغۡنِيَ عَنۡهُمۡ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗاۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ وَقُودُ ٱلنَّارِ 

    Open ayah 3:10

    Lalle waɗanda suka kafirta, dukiyoyinsu da ‘ya’yansu ba za su wadatar da su da komai ba a wajen Allah; kuma waɗannan su makamashi ne na wuta.

  11. كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡۗ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

    Open ayah 3:11

    Kamar dai halin abin da ya gudana ga mutanen Fir\'auna da waɗanda suka gabace su. Sun ƙaryata ayoyinmu, sai Allah Ya kama su da zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙuba ne. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci ranar lahira, ya kuma tabbatar da cewa, rana ce da babu kokwanto ga zuwanta, ya kuma ambaci halin muminai na neman gafara da afuwar Allah a wannan ranar, sai kuma a waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo bayanin kafirai da yadda halinsu zai zamanto a wannan ranar. Allah Ta’ala ya bayyana cewa waɗanda suka kafirce wa Allah da ayoyinsa, kuma suka ƙaryata manzanninsa, suka nuna musu ƙiyayya, kuma suka bijire wa addinin Allah; to waɗannan dukiyoyinsu da ‘ya’yansu ba za su taɓa yi musu amfani ba, kuma ba za su kuɓutar da su daga azabar Allah ba, yayin da ta zo musu. Makomarsu ita ce wutar Jahannama, su ne makamashinta da za a riƙa rura ta, kuma za su dawwama a cikinta har abada, babu ranar fitarsu. Wannan sunnar Allah ce wadda ba ta canzawa. Al’amarin waɗannan daidai yake da al’amarin Fir’auna da jama’arsa da sauran al’ummomin da suka ƙaryata Allah da manzanninsa, su ma haka Allah ya halakar da su saboda zaluncinsu, haka da ma Allah yake, mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya bijire masa, ya ƙi tuba ya dawo gare shi.

  12. قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ سَتُغۡلَبُونَ وَتُحۡشَرُونَ إِلَىٰ جَهَنَّمَۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

    Open ayah 3:12

    Ka ce wa waɗanda suka kafirta: \"Da sannu za a rinjaye ku, kuma za a tara ku zuwa Jahannama. Kuma tir da wannan mashimfiɗi.

  13. قَدۡ كَانَ لَكُمۡ ءَايَةٞ فِي فِئَتَيۡنِ ٱلۡتَقَتَاۖ فِئَةٞ تُقَٰتِلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَأُخۡرَىٰ كَافِرَةٞ يَرَوۡنَهُم مِّثۡلَيۡهِمۡ رَأۡيَ ٱلۡعَيۡنِۚ وَٱللَّهُ يُؤَيِّدُ بِنَصۡرِهِۦ مَن يَشَآءُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّأُوْلِي ٱلۡأَبۡصَٰرِ

    Open ayah 3:13

    Haƙiƙa wata izina ta bayyana a gare ku game da wasu rundunoni biyu da suka gwabza, ɗaya rundunar tana yaƙi saboda Allah, ɗayar kuma kafira ce, suna kallon su (musulmi) kamar ninki biyu a ganin ido; kuma Allah Yana ƙarfafar wanda Ya ga dama da nasararsa. Lalle a cikin hakan akwai izina ga ma\'abota basira. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa wa kafirai cewa, muminai sai sun yi rinjaye a kansu a rayuwarsu ta duniya, sannan idan ranar alƙiyama ta tsaya, a tarkata su gaba ɗaya cikin wutar Jahannama, domin ita ce shimfiɗar da suka tanadar wa kawunansu tun a nan duniya. Tir kuwa da wannan shimfiɗa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wa kafirai ko kuma muminai cewa, sun ga alama a fili da ta nuna muminai ne za su yi rinjaye a kan kafirai, kuma Allah ya yi alƙawarin zai ɗaukaka addininsa, kuma ya ƙarfafi Manzonsa. Wannan alama ita ce, ƙungiyoyin mayaƙa biyu da suka haɗu don kafsa yaƙi a tsakaninsu. Ƙungiyar farko muminai ne, masu yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah, su ne Annabi da Musulmi a yaƙin Badar; ɗaya ƙungiyar kuma kafirai ne, suna yaƙi ba don Allah ba, su ne Ƙuraishawa kafiran Makka a ranar Badar. A lokacin muminai suna ganin kafirai a ido, sun ninka su gida biyu. Wannan kuwa ya ƙara musu dogaro ga Allah da neman taimakonsa, wanda yin hakan yana daga cikin dalilan samun nasara. Haka Allah yake ƙarfafar wanda ya ga dama da samun nasara. To yadda Allah ya ba wa waɗannan muminai ‘yan kaɗan nasara a kan abokan gabarsu masu yawa, akwai darasi da wa’azi ga duk wanda Allah ya ba shi basira da hangen nesa.

  14. زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ ٱلشَّهَوَٰتِ مِنَ ٱلنِّسَآءِ وَٱلۡبَنِينَ وَٱلۡقَنَٰطِيرِ ٱلۡمُقَنطَرَةِ مِنَ ٱلذَّهَبِ وَٱلۡفِضَّةِ وَٱلۡخَيۡلِ ٱلۡمُسَوَّمَةِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ وَٱلۡحَرۡثِۗ ذَٰلِكَ مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلۡمَـَٔابِ

    Open ayah 3:14

    An ƙawata wa mutane son sha’awace-sha’awace na mata da \'ya\'ya da dukiya mai yawa abar tarawa ta zinariya da azurfa da kuma kiwatattun dawaki da dabbobi na gida da amfanin gona. Waɗannan duk morewa ce ta rayuwar duniya; Allah kuwa a wurinsa ne kyakkyawar makoma take.

  15. ۞قُلۡ أَؤُنَبِّئُكُم بِخَيۡرٖ مِّن ذَٰلِكُمۡۖ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَأَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ

    Open ayah 3:15

    Ka ce: \"Shin in ba ku labarin da abin da ya fi waɗancan alheri? Waɗanda suka yi taƙawa, suna da wasu aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, a wurin Ubangijinsu, suna masu zama a cikinsu dindindin da mata na aure tsarkaka da kuma yarda daga Allah. Kuma Allah Yana ganin bayinsa.\"

  16. ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَآ إِنَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ

    Open ayah 3:16

    Su ne waɗanda suke cewa: \"Ya Ubangijinmu, lalle mu mun yi imani, don haka Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka tserar da mu daga azabar wuta.”

  17. ٱلصَّٰبِرِينَ وَٱلصَّٰدِقِينَ وَٱلۡقَٰنِتِينَ وَٱلۡمُنفِقِينَ وَٱلۡمُسۡتَغۡفِرِينَ بِٱلۡأَسۡحَارِ

    Open ayah 3:17

    (Su ne) masu haƙuri, masu gaskiya, kuma masu ɗa\'a, kuma masu ciyarwa, kuma masu neman gafara lokacin sahur. Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) a baya ya nuna cewa, dukiya da ‘ya’ya ba za su amfani waɗanda suka kafirce masa ba, sai kuma a waɗannan ayoyin yake gargaɗi ga waɗanda ƙyale-ƙyalin rayuwar duniya za su shagaltar da su, har su manta da lahira. Allah ya bayyana cewa, ya sanya wa mutane son wasu abubuwa na sha’awa, kamar mata da ‘ya’ya maza da tara nau’ukan dukiyoyi iri-iri, kamar zinare da azurfa, da kiwatattun dawakai da raƙuma da shanu da ƙananan dabbobi da gonakin noma. Allah ya bayyana duk waɗannan abubuwan na more daɗin duniya ne, daga ƙarshe su tafi su bar su, kuma a wurin Allah kaɗai ake samun kyakkyawar makoma da sakamako mai yawa marar yankewa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wa Annabinsa (ﷺ) cewa, akwai abin da ya fi waɗannan ƙyale-ƙyali kayan sha’awar na duniya a wurin Allah, waɗanda su ne aljannatai na ni’ima, da abin da yake cikinsu na gidaje manya-manya, waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, ga kuma tsarkakan mata a cikinsu. Kuma wannan ni’imar ta har abada ce, ba mai yankewa ba, za su yi ta zama a cikinta har abada. Tare da waɗannan ni’imomi kuma akwai wata babbar ni’ima, wadda ta zarce kowace ni’ima girma, ita ce samun yardar Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Abu Sa’id Alkhudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah Ta’ala zai ce wa ‘yan Aljanna: “Ya ku ‘yan Aljanna.” Sai su ce: “Mun amsa maka, ya Ubangijinmu.” Sai ya ce: “Shin kun yarda?” Sai su ce: “Me zai sa ba za mu yarda ba, alhalin ka ba mu abin da babu wanda ka taɓa ba shi irinsa a cikin halittarka?” Sai Allah ya ce: “To zan ba ku abin da ya fi wannan da na ba ku.” Sai su ce: “Ya Ubangiji, mene ne kuma ya fi wannan da ka ba mu?” Sai ya ce: “Zan halatta muku yardata, daga yanzu ba zan yi fushi da ku ba har abada.” [Bukhari #6549, da Muslim #2829]. Kuma Allah mai ganin duk bayinsa ne, muminai da kafirai, da mutanen kirki da na banza, yana sane da halin da kowannensu yake ciki, don haka mai yi musu sakayya ne a kan ayyukansu kyawawa da munana. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci waɗanda suka cancanci samun waccan ni’ima da ya ambata ta lahira. Ya nuna cewa, su ne masu kamun-ƙafa a wurinsa da imanin da suka yi da shi, da littafinsa da Manzonsa, suna roƙon sa da ya yi musu baiwar gafarar zunubansu, ya kuma tsare su shiga azabar wuta. Sannan ya ƙara ambatar wasu siffofin nasu da cewa, su masu haƙuri ne, wajen aikata ɗa’a da barin saɓon Allah, da haƙuri a kan ƙaddara marar daɗi, kuma masu gaskiya ne a maganganunsu da ayyukansu, masu ɗa’a ne ga Allah, masu ciyar da dukiyoyinsu don Allah a duk inda ya zama wajibi, ko ta hanyar neman lada, sannan masu neman gafarar Allah ne a ƙarshen dare. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ubangijinmu Tabaraka wa Ta’ala yana sauka a sama ta kusa a kowane dare, yayin da sulusin ƙarshe na daren ya yi saura, yana cewa: “Wane ne zai roƙe ni, in amsa masa, wane ne zai tambaye ni, in ba shi, wane ne zai nemi gafarata, in gafarta masa?” [Bukhari #1145, Muslim #758].

  18. شَهِدَ ٱللَّهُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَأُوْلُواْ ٱلۡعِلۡمِ قَآئِمَۢا بِٱلۡقِسۡطِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 3:18

    Allah Ya shaida cewa, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi, haka mala\'iku ma da ma\'abota ilimi, Tsayayye ne da adalci. Babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi, Mabuwayi, Mai hikima. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi bayinsa muminai, sai kuma ya ambaci dalilai na zahiri masu ƙarfi, waɗanda suke tabbatar da kaɗaitakar Allah (Mai tsarki da daukaka). Waɗannan dalilai su ne; shaidar Allah (Mai tsarki da daukaka), inda ya ba da shaidar cewa, babu abin bauta wa da gaskiya sai shi. Sannan ya biyo ta da shaidar mala’ikunsa da ta malamai a cikin bayinsa, wanda kuma shi yake tsaye da adalci cikin dukkanin lamura da kuma dukkan ayyukansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake tabbatar da wajabcin a bauta masa shi kaɗai, ba tare da an haɗa shi da abokin tarayya ba. Ya kuma bayyana cewa, shi Mabuwayi ne, ba wanda zai iya ja da shi, ko ya gagare shi, kuma Mai hikima ne a cikin duk maganganunsa da ayyukansa.

  19. إِنَّ ٱلدِّينَ عِندَ ٱللَّهِ ٱلۡإِسۡلَٰمُۗ وَمَا ٱخۡتَلَفَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 3:19

    Lalle addini a wurin Allah shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka ba wa Littafi ba su yi saɓani ba sai bayan da ilimi ya zo musu saboda zalunci a tsakaninsu. Wanda kuwa duk ya kafirce wa ayoyin Allah, to lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne.

  20. فَإِنۡ حَآجُّوكَ فَقُلۡ أَسۡلَمۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّهِ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِۗ وَقُل لِّلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡأُمِّيِّـۧنَ ءَأَسۡلَمۡتُمۡۚ فَإِنۡ أَسۡلَمُواْ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ 

    Open ayah 3:20

    To idan sun yi jayayya da kai, sai ka ce: “Ni na miƙa wuyana ne ga Allah, haka ma wanda ya bi ni.” Kuma ka faɗa wa waɗanda aka bai wa Littafi da Ummiyyai: \"Shin kun miƙa wuya?\" To idan sun miƙa wuya, haƙiƙa sun shiryu; idan kuwa suka juya baya, to babu abin da yake a kanka sai isar da saƙo. Kuma Allah Shi ne Mai ganin bayinsa. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi kaɗai ne ya cancanta a bauta masa, sai kuma ya zo da bayani a kan addinin da za a bauta masa da shi. Allah ya tabbatar da cewa, lalle addinin gaskiya, kuma karɓaɓɓe a wurin Allah, shi ne Musulunci, Allah ba zai yarda a bauta masa da wani addinin ba Musulunci ba. Sannan ya bayyana dalilin saɓanin ma’abota littafi da cewa, ya faru ne bayan an tsayar musu da hujja ta hanyar aiko musu da annabawa da saukar musu da littattafai, kuma abin da ya kai su ga sassaɓawa shi ne zalunci da ƙetare haddi da ya riƙa faruwa a tsakaninsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo batun sakamakon wanda ya kafirce wa ayoyinsa da cewa, Allah zai yi masa hisabi a kan wannan, cikin gaggawa, zai lissafa dukkan ayyukan bayinsa ba tare da buƙatar amfani da wata na’ura ta lissafi ba, kuma duk yawansu a lokaci guda, a kuma wuri guda, a ɗan taƙaitaccen lokaci. Sannan ita kanta ranar hisabin dab take da zuwa, domin rayuwar duniya gajeriya ce. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karkatar da akalar magana zuwa ga Annabinsa (ﷺ) cewa, idan kafirai sun yi jayayya da shi a kan gaskiyar da ya zo musu da ita, to ya fito ya faɗa musu cewa, shi dai yana yin aikinsa ne don Allah shi kaɗai, hakanan ma duk wanda ya bi shi yana aikinsa ne ga Allah shi kaɗai. Ya kuma umarce shi da ya fito ya faɗa wa Yahudawa da Nasara waɗanda Allah ya ba su littafi da kuma mushirikai waɗanda ba su da wani littafi: Shin sun miƙa wuya ga Allah, kuma za su bauta masa shi kaɗai? Idan sun miƙa wuya kamar yadda su Musulmi suka miƙa wuya, to sun shiryu, sun hau turbar gaskiya. Idan kuwa suka bijire wa wannan kira da ake yi musu, to ba wani laifi a kan shi Ma’aiki, domin isar da saƙo ne kawai aikinsa. Allah yana ganin duk bayinsa, ya san wanda zai karɓi shiriya da wanda ba zai karɓa ba, kuma makomar kowa ga Allah take, zai yi wa kowa hisabi bisa aikinsa na alheri ko na sharri.

  21. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَيَقۡتُلُونَ ٱلَّذِينَ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡقِسۡطِ مِنَ ٱلنَّاسِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

    Open ayah 3:21

    Lalle waɗanda suke kafirce wa ayoyin Allah, kuma suke kashe annabawa ba tare da wani haƙƙi ba, kuma suke kashe waɗanda suke yin umarni da adalci cikin mutane, to ka yi musu albishir da wata azaba mai raɗaɗi.

  22. أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّٰصِرِينَ

    Open ayah 3:22

    Waɗannan su ne waɗanda ayyukansu suka lalace a duniya da lahira, kuma ba su da wasu mataimaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin waɗanda suka kafirce wa ayoyinsa cewa, ba a nan suka tsaya ba; sun ci gaba da kutsawa cikin shisshiginsu da kafircinsu, har suka kai ga kashe wasu annabawa da manzanni, ba tare da sun yi musu wani laifi ba. Hakanan suka riƙa kashe bayin Allah nagari masu yin umarni da a yi adalci, kuma a yi kyakkyawan aiki, suke hana mummuna. Kashe irin waɗannan bayin Allah shi ne ƙololuwar girman kai, kamar yadda Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Girman kai shi ne watsi da gaskiya da wulaƙanta mutane.” [Muslim #91]. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa (ﷺ), da ya yi musu albishir da wata azaba mai raɗaɗi, sakamakon kafircinsu da miyagun ayyukansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ayyukan waɗannan mutane duk sun rushe, sun lalace, ba abin da zai amfane su a duniya ko a lahira, kuma har ila yau ba za su sami mai taimakon su ba, wanda zai kuɓutar da su daga azabar Allah.

  23. أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبٗا مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ يُدۡعَوۡنَ إِلَىٰ كِتَٰبِ ٱللَّهِ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ يَتَوَلَّىٰ فَرِيقٞ مِّنۡهُمۡ وَهُم مُّعۡرِضُونَ

    Open ayah 3:23

    Shin ba ka ga waɗannan da aka ba su wani kaso na ilimin Littafi ba, ana kiran su zuwa ga Littafin Allah don Ya yi hukunci a tsakaninsu, sannan sai wani ɓangare daga cikinsu suna juya baya, suna masu bijirewa.

  24. ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لَن تَمَسَّنَا ٱلنَّارُ إِلَّآ أَيَّامٗا مَّعۡدُودَٰتٖۖ وَغَرَّهُمۡ فِي دِينِهِم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

    Open ayah 3:24

    Wannan kuwa saboda su sun ce: \"Wuta ba za ta shafe mu ba sai a waɗansu ‘yan kwanaki ƙididdigaggu.\" kuma abin da suka kasance suna ƙirƙira a addininsu shi ne ya ruɗe su.

  25. فَكَيۡفَ إِذَا جَمَعۡنَٰهُمۡ لِيَوۡمٖ لَّا رَيۡبَ فِيهِ وَوُفِّيَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

    Open ayah 3:25

    To yaya halinsu zai kasance idan Muka tara su a wani yini da babu shakka game da shi, kuma kowane rai za a saka masa da abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba? A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin waɗanda aka ba su wani kaso na ilimin littafin da Allah ya saukar, su ne Yahudawa cewa, lokacin da ake kiran su su zo ga hukuncin littafin da suka yi imani da shi, suka yarda da abin da yake cikinsa cewa daga Allah yake, sai wasu daga cikinsu suka riƙa bijirewa, suna goce wa hukuncin wannan littafin. Kuma abin da ya jawo har suka yi haka shi ne ƙaryar da suka yarda da ita na cewa, Allah ba zai yi musu azaba ba, sai ta ‘yan kwanaki kaɗan ƙididdigaggu, sai ya fito da su. To wannan ƙaryar ce ta ruɗe su a addininsu, har ma suke ganin cewa, suna iya saɓa wa hukuncin Allah, ko su bijire masa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Yahudawa sun je wurin Annabi (ﷺ) suka faɗa masa cewa wani namiji da wata mata daga cikinsu sun yi zina, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce musu: “Me kuka sani a cikin littafin Attaura dangane da jefe mazinata?” Sai suka ce: “Ai kunyata su muke yi, kuma a yi musu bulala.” Sai Abdullahi ɗan Salam ya ce: “Ƙarya kuke yi, a cikin Attaura akwai ayar hukuncin jefe mazinaci.” Sai suka ɗauko Attaurah suka buɗe ta, sai ɗaya daga cikinsu ya sa hannunsa ya danne ayar jefewa, ya riƙa karanta abin da yake gabanta, da abin da yake bayanta. Sai Abdullahi ɗan Salam ya ce: “Cire hannunka!” Yana cire hannunsa, sai ga ayar, sai kuma dukansu suka ce: “E, gaskiya ya faɗa, ya Muhammadu, akwai ayar jefe mazinaci a cikin Attaura.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce a je a jefe su. Aka jefe su.” [Bukhari #3635, da Muslim #1699]. Dangane da batun Yahudawa na cewa ba za a sa su wuta ba sai na ‘yan kwanaki kaɗan, Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya tambayi Yahudawa: “Su wane ne ‘yan wuta?” Sai suka ce: “Za mu shiga wuta na wani ɗan lokaci kaɗan, sannan sai a cire mu, a sa ku a madadinmu.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce musu: “Ku yi mana shiru, wallahi har abada ba za mu maye gurbinku a cikinta ba.” [Bukhari #3169]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar da su azabar ranar da za a tattaro su gaba ɗayansu, yana mai cewa, yaya halinsu zai kasance tare da waɗannan miyagun ayyuka nasu, lokacin da za a zartar da hukunci a tsakaninsu, ranar da babu kokwanto a zuwanta, ita ce ranar alƙiyama? A wannan rana za a cika wa kowane rai sakamakon aikinsa na alheri ko na sharri, babu wanda za a zalunta ta hanyar a tauye masa ladansa ko a ƙara masa laifin da ba shi ya yi ba ko a hukunta shi da laifin wani. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa a hadisi Ƙudusi: “Ya ku bayina, ni na haramta wa kaina zalunci....” [Muslim #2577].

  26. قُلِ ٱللَّهُمَّ مَٰلِكَ ٱلۡمُلۡكِ تُؤۡتِي ٱلۡمُلۡكَ مَن تَشَآءُ وَتَنزِعُ ٱلۡمُلۡكَ مِمَّن تَشَآءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَآءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَآءُۖ بِيَدِكَ ٱلۡخَيۡرُۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 3:26

    Ka ce: \"Ya Allah, Kai ne Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Ka ga dama, kuma Kana ƙwace mulki daga wanda Ka ga dama, kuma Kana ɗaukaka wanda Ka ga dama, kuma Kana ƙasƙantar da wanda Ka ga dama; duk alheri yana hannuka, lalle Kai Mai iko ne a kan komai.

  27. تُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَتُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِۖ وَتُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَتُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّۖ وَتَرۡزُقُ مَن تَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

    Open ayah 3:27

    “Kana shigar da dare a cikin yini, kuma Kana shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga cikin matacce, kuma Kana fitar da matacce daga cikin mai rai; kuma Kana arzurta wanda Ka ga dama ba tare da lissafi ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabinsa (ﷺ) da ya roƙe shi, ya girmama sunansa, ya ce: Ya Allah wanda mulkin komai naka ne, kai ne Mamallakin duniya da lahira da duk abin da yake cikinsu, kai kake bayar da mulki ga wanda ka ga dama ka kuma ƙwace mulki daga wanda ka ga dama; kana ɗaukaka wanda ka ga dama ta hanyar hore masa aikin ɗa’a gare ka ko ta hanyar ba shi mulki da iko ko ka ba shi nasara ko wanin haka. Kuma kana ƙasƙantar da wanda ka ga dama ta hanyar ya zama mai saɓa maka ko ta hanyar ƙwace mulkinsa ko ɗora maƙiyansa a kansa, ko makamancin haka. Alheri duka yana hannunka. Lalle Allah kai mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare ka aiwatarwa idan ka ga damar aiwatar da shi. Yana daga cikin cikakken ikonka ya Allah, ka shigar da dare a cikin yini, kuma ka shigar da yini a cikin dare, watau ka sanya wasu sa’o’in dare a cikin sa’o’in yini, ko wasu sa’o’in yini ka ƙara su a kan sa’o’in dare. Kuma kana fitar da mai rai daga matacce, kamar fitar da mutum ko dabba mai rai daga ruwan maniyyi ko ka fitar da shuka daga ƙwayar iri ko kaza daga ƙwai ko kuma ka fitar da mumini daga kafiri. Hakanan kuma kana fitar da matacce daga mai rai, kamar fitar da ruwan maniyyi daga mutum ko dabba mai rai, ko ka fitar da ƙwaya daga shuka ko ka fitar da ƙwai daga kaza ko ka fitar da kafiri daga tsatson mumini. Kuma kana arzuta wanda ka ga dama cikin bayinka da arziki mai yawa, ba tare da ƙuntata masa ba.

  28. لَّا يَتَّخِذِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَلَيۡسَ مِنَ ٱللَّهِ فِي شَيۡءٍ إِلَّآ أَن تَتَّقُواْ مِنۡهُمۡ تُقَىٰةٗۗ وَيُحَذِّرُكُمُ ٱللَّهُ نَفۡسَهُۥۗ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 3:28

    Kada muminai su riƙi kafirai a matsayin masoya su ƙyale muminai; wanda kuwa duk ya aikata haka, to shi ba komai ne ba a wurin Allah, sai dai in don ku kare kanku ne daga gare su. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa. Kuma zuwa ga Allah makoma take. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai su riƙi kafirai masoyansu, watau majiɓinta al’amuransu, suna taimakon su, su yi watsi da ‘yan’uwansu muminai. Allah ya bayyana cewa, duk wanda ya yi haka; to babu ruwan Allah da shi. Amma kuma sai Allah ya yi togaciyar lokacin da ake tsoron wani sharrin nasu, to a wannan lokaci za a iya nuna musu ƙauna da baki, ba da zuciya ɗaya ba, ba kuma tare da taimakon su a kan kafircinsu ko taya su aikata saɓon Allah ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi muminai game da kansa, watau kada su aikata abin da zai jawo musu fushinsa, yana mai bayyana musu cewa, makomarsu gaba ɗaya zuwa gare shi ne, kuma zai yi musu hisabi a kan ayyukansu.

  29. قُلۡ إِن تُخۡفُواْ مَا فِي صُدُورِكُمۡ أَوۡ تُبۡدُوهُ يَعۡلَمۡهُ ٱللَّهُۗ وَيَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 3:29

    Ka ce: “In za ku ɓoye abin da yake cikin ƙirazanku ko kuma ku bayyana shi, Allah Ya san shi, kuma Yana sane da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai.”

  30. يَوۡمَ تَجِدُ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ مِنۡ خَيۡرٖ مُّحۡضَرٗا وَمَا عَمِلَتۡ مِن سُوٓءٖ تَوَدُّ لَوۡ أَنَّ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَهُۥٓ أَمَدَۢا بَعِيدٗاۗ وَيُحَذِّرُكُمُ ٱللَّهُ نَفۡسَهُۥۗ وَٱللَّهُ رَءُوفُۢ بِٱلۡعِبَادِ 

    Open ayah 3:30

    Ranar da kowane rai zai sami abin da ya aikata na alheri an halarto da shi, abin da kuwa ya aikata na mummunan aiki, zai so ina ma da a ce tsakaninsa da shi akwai wata tazara mai nisa. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa, kuma Allah Mai tausayi ne ga bayi. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Manzonsa da ya faɗa wa muminai cewa, ko da za su ɓoye abin da yake cikin zukatansu na alheri ko na sharri, na soyayya ko na ƙiyayya, ko kuma su bayyana hakan a maganganunsu ko ayyukansu; to Allah ya san da hakan, kuma zai yi musu sakayya a kai; wanda ya shuka alheri ya girbi alheri; wanda kuma ya shuka sharri ya girbi sharri. Allah shi ne wanda iliminsa ya kewaye da duk abin da yake sama da abin da yake ƙasa, babu abin da yake ɓoye masa, kuma yana da cikakken iko a kan komai, babu abin da zai gagare shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana lokacin wannan sakayyar, watau ranar alƙiyama, ranar da kowane rai zai ga abin da ya aikata, kaɗan ne ko mai yawa, an kawo masa shi cikakke, ba tare da tawaya ba, ko wani canji. To amma abin da mutum ya aikata na sharri, zai riƙa burin ina ma akwai tazara mai nisa a tsakaninsa da mummunan aikinsa. Sai kuma Allah ya sake jaddada tsoratarwarsa da gargaɗinsa game da kansa, yana mai bayyana cewa, yana yi musu wannan gargaɗin ne saboda shi mai yawan rahama ne gare su, mai yawan jin ƙai.

  31. قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 3:31

    Ka ce: \"In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.”

  32. قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 3:32

    Ka ce: “Ku yi ɗa\'a ga Allah da Manzo; to in kuwa kuka juya baya, to lalle Allah ba Ya son kafirai.” A waɗannan ayoyi, Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umarnin Annabinsa (ﷺ) da ya faɗa wa masu da’awar son Allah da baki, amma ayyukansu suna ƙaryata haka cewa, idan har da gaske suna son Allah, to alamar da za ta tabbatar da gaskiyar da’awarsu ita ce su bi Manzon Allah (ﷺ), su gaskata shi, su yi masa ɗa’a a kan abin da yake umarni da shi da abin da ya hana, domin son Allah da biyayya ga Manzon Allah (ﷺ) abubuwa ne da suke a haɗe ba sa rabuwa. To idan har wannan ya tabbata to a lokacin ne su ma Allah zai so su, kuma ya gafarta musu zunubansu, domin Allah mai gafarta zunubai ne, mai jin ƙai ga bayinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya umarce su da su tabbatar da haka; watau su yi wa Allah ɗa’a, kuma su yi wa Manzon Allah (ﷺ) ɗa’a; wannan kuwa shi zai fisshe su;, idan kuwa har suka bijire wa wannan umarni, to su san da sanin cewa sun kafirta, sun jefa kansu cikin fushin Allah, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya son kafirai.

  33. ۞إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰٓ ءَادَمَ وَنُوحٗا وَءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ وَءَالَ عِمۡرَٰنَ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 3:33

    Lalle Allah Ya zaɓi Adamu, da Nuhu da iyalan gidan Ibrahimu da iyalan gidan Imrana Ya fifita su a kan sauran talikai.

  34. ذُرِّيَّةَۢ بَعۡضُهَا مِنۢ بَعۡضٖۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

    Open ayah 3:34

    Wata zurriya ce, sashinsu ‘ya’ya ne ga sashi. Kuma Allah Mai ji ne, Mai yawan sani.

  35. إِذۡ قَالَتِ ٱمۡرَأَتُ عِمۡرَٰنَ رَبِّ إِنِّي نَذَرۡتُ لَكَ مَا فِي بَطۡنِي مُحَرَّرٗا فَتَقَبَّلۡ مِنِّيٓۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

    Open ayah 3:35

    Tuna lokacin da matar Imrana ta ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na yi maka bakancen abin da yake cikina ya zamanto ‘yantacce, don haka Ka karɓa daga gare ni, lalle Kai ne Mai ji, Mai yawan sani.”

  36. فَلَمَّا وَضَعَتۡهَا قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي وَضَعۡتُهَآ أُنثَىٰ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا وَضَعَتۡ وَلَيۡسَ ٱلذَّكَرُ كَٱلۡأُنثَىٰۖ وَإِنِّي سَمَّيۡتُهَا مَرۡيَمَ وَإِنِّيٓ أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ

    Open ayah 3:36

    To yayin da ta haife ta sai ta ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na haife ta ‘ya mace,” kuma Allah ne Ya fi sanin abin da ta haifa “Kuma ɗa namiji ba daidai yake da ‘ya mace ba; kuma lalle ni na raɗa mata suna Maryamu, kuma lalle ni ina nema mata tsarinka da zurriyarta daga Shaiɗan korarre.”

  37. فَتَقَبَّلَهَا رَبُّهَا بِقَبُولٍ حَسَنٖ وَأَنۢبَتَهَا نَبَاتًا حَسَنٗا وَكَفَّلَهَا زَكَرِيَّاۖ كُلَّمَا دَخَلَ عَلَيۡهَا زَكَرِيَّا ٱلۡمِحۡرَابَ وَجَدَ عِندَهَا رِزۡقٗاۖ قَالَ يَٰمَرۡيَمُ أَنَّىٰ لَكِ هَٰذَاۖ قَالَتۡ هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٍ

    Open ayah 3:37

    Sai Ubangijinta Ya karɓe ta da kyakkyawar karɓa, kuma Ya yi mata kyakkyawar tarbiyya, kuma Ya danƙa renonta a hannun Zakariyya; duk lokacin da Zakariyya ya shiga wurinta a ɗakin ibada, sai ya sami abinci a wurinta, sai ya ce: “Ya ke Maryamu, wannan daga ina kika samu?” Sai ta ce: “Wannan daga Allah ne; lalle Allah Yana arzurta wanda Ya ga dama ba tare da lissafi ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin irin zaɓin da ya yi a cikin bayinsa, watau ya zaɓi wasu ɗaiɗaikun mutane, ya kuma zaɓi wasu iyalai ya yi musu baiwa da falalarsa, ya fifita su a kan al’ummomin zamaninsu, ya ware su don bautar sa shi kaɗai. Cikin ɗaiɗaikun mutane Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zaɓi Annabi Adamu da Annabi Nuhu; a cikin gidaje ko iyali kuma, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zaɓi Annabi Ibrahimu da iyalinsa da Imrana da iyalinsa. Waɗannan zaɓaɓɓu Allah ya sanya nagarta da ayyukan ƙwarai a cikin zuriyyarsu. Allah shi ne mai cikakken ilimi game da wanda ya cancanci zaɓinsa a cikin bayinsa, domin shi ne mai ji, kuma mai cikakken sani. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin wasu ƙissoshi guda huɗu, masu ban mamaki wanda ya saɓa da yadda ɗan’adam ya saba gani. Allah ya fara da ƙissar Maryam, mahaifiyar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), yadda ta kasance keɓantacciya ga Allah (Mai tsarki da daukaka) tun lokacin da mahaifiyarta ta ɗauki cikinta har ta haife ta, ta dimanci zama a wurin bautar Allah. Lokacin da mahaifiyarta ta ɗauki cikinta, ta yi wa Allah bakance cewa, abin da yake cikinta, za ta sadaukar da shi ga Allah (Mai tsarki da daukaka) don yi masa hidima a masallacin Baitul Maƙdis. Ta roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karɓi wannan bakance nata, domin shi mai jin addu’ar wanda ya roƙe shi ne, ya karɓa masa, kuma masani ne ga halin da kowane bawa yake ciki. To tana zaton abin da za ta haifa namiji ne; amma tana haihuwa, sai ta ga mace, sai take neman uzuri a wurin Allah, tana mai cewa, ga shi abin da ta haifa ya zamanto mace, ba namiji ba; mace kuma ba za ta iya yin abin da namiji zai iya ba na hidima da lazimtar wurin ibada a ko da yaushe, saboda raunin da take da shi da kuma larurar da take samun ta a duk wata, watau jinin al’ada. Sannan sai ta sanya wa ‘yar tata suna Maryam, ta kuma roƙi Allah da ya tsare ta har da zuriyar da za ta haifa nan gaba, daga sharrin Shaiɗan la’ananne. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Babu wani jariri da aka haifa, face sai da Shaiɗan ya shafe shi lokacin haihuwarsa, sai ku ji yaro ya fashe da kuka saboda shafar Shaiɗan, in ban da Maryam da ɗanta (Annabi Isa).” Sai Abu Huraira ya ce: “In kun ga dama ku karanta faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka): “Lalle ni ina nema mata tsari da zuriyyarta daga Shaiɗan korarre.” [Bukhari #3431, da Muslim #2366]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karɓi addu’arta, kuma ya karɓi wannan bakancen da ta yi, kyakkyawar karɓa, ya taso da Maryamu cikin kyakkyawar tarbiyya, mai ban sha’awa ga kowa, kuma Allah ya ɗora nauyin kula da tarbiyyarta a kan Zakariyya. To duk lokacin da Zakariyya ya kai mata ziyara wajen ibadarta, sai kawai ya tarar da abinci iri-iri a wurinta, sai abin ya riƙa ba shi mamaki, sai yake tambayar ta cewa, daga ina take samun abinci irin wannan? Sai ta amsa masa da cewa: “Daga wurin Allah ne, kuma shi Allah yana ba da arzikinsa ne ga wanda ya ga dama, ba tare da lissafi ba.”

  38. هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُۥۖ قَالَ رَبِّ هَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ ذُرِّيَّةٗ طَيِّبَةًۖ إِنَّكَ سَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

    Open ayah 3:38

    A wannan lokacin sai Zakariyya ya roƙi Ubangijinsa, ya ce: “Ya Ubangijina, Ka ba ni zurriyya ta gari daga gare Ka, lalle Kai Mai amsa roƙo ne.”

  39. فَنَادَتۡهُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَهُوَ قَآئِمٞ يُصَلِّي فِي ٱلۡمِحۡرَابِ أَنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكَ بِيَحۡيَىٰ مُصَدِّقَۢا بِكَلِمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَسَيِّدٗا وَحَصُورٗا وَنَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

    Open ayah 3:39

    Sai mala’iku suka kira shi, lokacin yana tsaye yana salla a cikin ɗakin ibada, (suka ce): “Lalle Allah Yana yi maka albishir da Yahaya, wanda yake mai gaskatawa da wata kalma daga Allah, kuma zai zama shugaba, kuma mai tsare kansa daga mata, kuma Annabi daga cikin salihan bayi.”

  40. قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَقَدۡ بَلَغَنِيَ ٱلۡكِبَرُ وَٱمۡرَأَتِي عَاقِرٞۖ قَالَ كَذَٰلِكَ ٱللَّهُ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ 

    Open ayah 3:40

    Ya ce: “Ya Ubangijina, ta yaya zan sami ɗa, ga shi tsufa ya riga ya cim mini, kuma ga shi matata juya ce?” Sai ya ce: “Kamar haka ne Allah Yake aikata abin da Ya ga dama.”

  41. قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَةَ أَيَّامٍ إِلَّا رَمۡزٗاۗ وَٱذۡكُر رَّبَّكَ كَثِيرٗا وَسَبِّحۡ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِبۡكَٰرِ

    Open ayah 3:41

    Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya mini wata alama.” Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana yini uku sai dai da nuni. Kuma ka ambaci Ubangijinka ambato mai yawa, kuma ka yi tasbihi yammaci da safiya.” Sai kuma a nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo ƙissa ta biyu, watau ƙissar Annabi Zakariyya, da yadda ya yi masa kyautar ɗa bayan har ya tsufa, ba tare da haihuwa ba, kuma ga shi matarsa bakarara, ba ta haihuwa. Lokacin da Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga irin karama da baiwar da Allah ya yi wa Maryamu sai shi ma ya ji son haihuwa ya dawo masa, ya sa rai ga samun biyan buƙatarsa, duk kuwa da halin da yake ciki na manyanta shi da matarsa. Sai ya ɗaga hannu ya yi addu’a yana cewa: “Ya Ubangijina, ka ba ni zurriyya ta gari daga gare ka, lalle kai mai amsa roƙo ne.” Sai ko Allah ya amsa masa addu’arsa, ya aiko wasu mala’iku don su yi masa albishir, suka same shi yana tsaye a masallaci yana salla, suka yi masa wannan albishir da cewa, zai haifi ɗa mai suna Yahya, wanda zai siffantu da siffofi masu girma, domin zai zama Shugaba wanda zai shugabanci mutanensa da halayensa na ƙwarai da iliminsa da addininsa, kuma mai ƙaurace wa mata da duk wani abu da zai tayar masa da sha’awa, mai shagala da bautar Allah (Mai tsarki da daukaka), sannan kuma zai zama Annabi daga cikin salihan bayi. Yayin da Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji wannan albishir na samun haihuwa, sai mamakin Ƙudurar Allah ya rufe shi, sai yake tambayar Allah, yana cewa: “Ya Ubangijina, ta yaya zan sami ɗa, alhalin ga shi ni na tsufa, na kai shekarun da ba zan iya haihuwa ba, sannan kuma ga matata bakarara ce da ma can ba mai haihuwa ba ce?” Sai Allah ya amsa masa da cewa, ai Allah yana aikata abin da ya ga dama ne. Daga nan sai Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nemi sanin wata alama da Allah zai nuna masa ta samun haihuwa, don ƙarin samun nutsuwar zuciya. Sai Allah ya sanar da shi cewa, alamar da zai gani ita ce, zai kasa magana da kowa har tsawon kwana uku, ba kuma don rashin lafiya, ko wani abu ya sami harshensa ba. Idan zai yi magana da mutane, sai dai ya riƙa nuni da hannunsa, amma kuma zai iya furta ambaton Allah a lokacin. Don haka Allah ya umarce shi da ya yi ta ambaton Ubangijinsa tare da tsarkake shi ta hanyar tasbihi da bautar sa yammaci da safiya.

  42. وَإِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰكِ وَطَهَّرَكِ وَٱصۡطَفَىٰكِ عَلَىٰ نِسَآءِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 3:42

    Kuma ka tuna lokacin da mala’iku suka ce: “Ya ke Maryamu, lalle Allah Ya zaɓe ki, Ya kuma tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan sauran mata na talikai.

  43. يَٰمَرۡيَمُ ٱقۡنُتِي لِرَبِّكِ وَٱسۡجُدِي وَٱرۡكَعِي مَعَ ٱلرَّٰكِعِينَ

    Open ayah 3:43

    “Ya ke Maryamu, ki yi ɗa’a ga Ubangijinki, kuma ki riƙa yin sujada, kuma ki riƙa yin ruku’u tare da masu ruku’u.

  44. ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهِ إِلَيۡكَۚ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ يُلۡقُونَ أَقۡلَٰمَهُمۡ أَيُّهُمۡ يَكۡفُلُ مَرۡيَمَ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ يَخۡتَصِمُونَ

    Open ayah 3:44

    Wancan (abin da ya gabata a baya) yana cikin labaru na gaibi da Muke yi maka wahayinsa, kuma kai ba ka wurinsu lokacin da suka jefa alƙalumansu don tantance wane ne cikinsu zai karɓi renon Maryamu, kuma kai ba ka nan tare da su yayin da suke jayayya da juna. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana shimfiɗa ne game da ƙissa ta uku, wato ta Maryamu da ta haifi Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba tare da namiji ba. Allah ya yi shimfiɗa da bayanin zaɓin da ya yi wa Maryamu (() don ta zama ita ce wadda Allah (Mai tsarki da daukaka) zai gudanar da wannan al’amari nasa da ya saɓa wa al’adar da ɗan’adam ya saba gani, na halittar mutum daga haɗuwar ɗa namiji da ‘ya mace. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabinsa labarin Maryamu (() lokacin da mala’iku suka kirawo ta, suna faɗa mata cewa, Allah ya zaɓe ta a cikin duka matan zamaninta, ya fifita ta a kansu, ya tsarkake ta da kyawawan halaye da riƙo da addini. Wannan zaɓin da aka yi mata, ba ƙaramar ni’ima ce gare ta ba, saboda haka akwai buƙatar ta yi wa Allah godiya a kai, ta tsarkake ɗa’arta ga Allah, ta zama mai bauta masa a ko da yaushe, kuma ta dinga yin salla tare da masallata. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa, waɗannan labarai da yake ba shi, na gaibu, waɗanda shi da mutanensa ba wanda ya san su, amma ga shi yanzu Allah ya sanar da shi su, don tabbatarr da shaida da dalili a kan gaskiyar annabcinsa, da ingancin wahayin da ya zo musu da shi. Allah ya ci gaba da faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, ba ya wurin lokacin da Annabi Zakariyya da sauran dangin Maryamu (() suka yi taro, suka tattauna batun wanda zai kula da rainonta, har ta kai su ga samun saɓani a tsakaninsu game da batun, har sai da aka yi ƙuri’a sannan aka zaɓi wanda zai riƙe ta, watau Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya gaya wa Annabinsa cewa wannan gaibu ne ya yi masa wahayinsa; Allah kuwa shi ne ya keɓanta da sanin gaibu yake kuma sanar da wanda ya ga damar sanar da shi.

  45. إِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَةٖ مِّنۡهُ ٱسۡمُهُ ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ وَجِيهٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

    Open ayah 3:45

    Ka tuna lokacin da mala’iku suka ce: “Ya ke Maryamu, lalle Allah Yana yi miki albishir da wata kalma daga gare shi, sunansa Almasihu Isa ɗan Maryamu, mai daraja a duniya da lahira, kuma yana cikin bayi makusanta.

  46. وَيُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗا وَمِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

    Open ayah 3:46

    “Kuma zai riƙa yi wa mutane magana tun yana cikin shimfiɗar jego da kuma lokacin dattijantaka, kuma yana cikin salihan bayi.”

  47. قَالَتۡ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي وَلَدٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞۖ قَالَ كَذَٰلِكِ ٱللَّهُ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

    Open ayah 3:47

    Sai ta ce: “Ya Ubangijina, ta yaya zan sami ɗa alhalin wani namiji bai kusance ni ba?” Sai ya ce: “Kamar haka ne Allah Yake halittar abin da Ya ga dama. Idan Ya yi nufin wani al’amari, sai Ya ce da shi: “Kasance” Nan take sai ya kasance.

  48. وَيُعَلِّمُهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

    Open ayah 3:48

    “Kuma zai sanar da shi rubutu da hikima da Attaura da Linjila.

  49. وَرَسُولًا إِلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ أَنِّي قَدۡ جِئۡتُكُم بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ أَنِّيٓ أَخۡلُقُ لَكُم مِّنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ فَأَنفُخُ فِيهِ فَيَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ وَأُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُنَبِّئُكُم بِمَا تَأۡكُلُونَ وَمَا تَدَّخِرُونَ فِي بُيُوتِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

    Open ayah 3:49

    “Kuma zai aiko shi a matsayin Manzo ga Banu Isra’ila (yana mai cewa): “Lalle ni na zo muku da wata aya daga Ubangijinku; lalle ni zan riƙa mulmula muku taɓo a siffar tsuntsu, sai in yi busa a cikinsa sai ya zama tsuntsu da izinin Allah; kuma zan warkar da wanda aka haifa makaho da mai cutar albaras, kuma in rayar da matattu da izinin Allah; kuma zan riƙa ba ku labarin abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a gidajenku. Lalle a cikin hakan akwai aya a gare ku in har kun kasance muminai.

  50. وَمُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَلِأُحِلَّ لَكُم بَعۡضَ ٱلَّذِي حُرِّمَ عَلَيۡكُمۡۚ وَجِئۡتُكُم بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ 

    Open ayah 3:50

    “Kuma zan zama mai gaskata abin da ya gabace ni na Attaura, kuma don in halatta muku sashin abubuwan da aka haramta muku. Kuma na zo muku da wata aya daga Ubangijinku, don haka ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku yi mini biyayya.

  51. إِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

    Open ayah 3:51

    “Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, don haka ku bautata masa Shi kaɗai. Wannan shi ne tafarki madaidaici.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba wa Annabinsa labarin Maryamu ((), da haihuwar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Wannan shi ne na uku cikin ƙissoshi huɗu masu tattare da abubuwan mamaki. Allah ya fara da mala’ikun da suka zo ga Maryamu ((), suna yi mata albishir na za ta haifi yaro, wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) zai halicce shi da kalmarsa, wato kalmar (كن), ‘kasance’, sai ya kasance, sunansa Almasihu Isa ɗan Maryam. Ana jingina shi ga mahaifiyarsa ne domin ba shi da uba. Yaro wanda daga siffofinsa zai zamo mai daraja ne da matsayi a wurin Allah, duniya da lahira, kuma yana cikin makusantan Allah. Daga cikin mu’ujizojinsa kuma, zai riƙa magana da mutane tun yana jariri cikin zanin haihuwarsa, don ya wanke mahaifiyarsa daga zargin ta haihu ba tare da mijin aure ba, kuma ya yi kira zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, ba tare da haɗa shi da wani abokin tarayya ba. Bayan ya zama dattijo kuma, zai ci gaba da yi wa mutane magana irin ta annabawan Allah masu karantar da jama’arsu abin da Allah ya yi masa wahayi da shi, sannan yana cikin mutanen kirki. Sai Maryamu ta amsa da cewa, ta yaya za ta haifi ɗa, alhali ba wani namiji da ya taɓa kusantar ta ta hanyar aure, ko ta hanyar zina? Sai Allah ya mayar mata da amsa cewa, haka dai Allah zai zartar da wannan al’amari da take mamaki, domin da haka Allah yake halittar abin da ya ga damar halitta, kuma babu abin da yake gagarar sa aikatawa, duk sa’adda ya yi nufin samar da wani abu, sai ya ce masa, ‘kasance’, sai nan take abin ya samu, ba tare da ɓata lokaci ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin irin baiwar da ya yi wa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a rayuwarsa ta ilimi da hikimomi iri-iri masu ban al’ajabi. Wannan ƙissa tana bayanin rayuwar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne, musamman bayan girmansa, wadda ita ma take cike da abubuwan ban mamaki, waɗanda har ma suka fi haihuwarsa ba tare da uba ba zama abin mamaki. Allah ya ce, ya yi masa baiwar koya masa rubutu da hikima, wadda ta ƙunshi shari’o’i da siyasar tafiyar da jama’a, ya kuma ba shi ilimin Attaura da Linjila, sannan ya aiko shi zuwa ga al’ummar Banu Isra’ila, yana mai faɗa musu cewa: “Lalle na zo muku da wasu hujjoji daga Ubangijinku, waɗanda suke tabbatar da gaskiyar abin da nake faɗa muku cewa ni Manzon Allah ne zuwa gare ku. Hujjojin kuwa su ne, Allah Ya hore mini wasu mu’ujizoji, daga cikin ina iya gina surar mutun-mutumi na tsuntsu da taɓo, sannan in yi busa cikinsa, nan take ya zama tsuntsu mai tashi da izinin Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma in warkar da mutumin da aka haife shi makaho da mai cutar baras, sannan in tayar da matattu, duk dai da izinin Allah (Mai tsarki da daukaka). Bugu da ƙari kuma zan iya ba ku labarin irin abincin da kuka ci a gidajenku, da abin da kuke ajiyewa, ba tare da na gani da idona ko wani ya ba ni labari ba. Duk waɗannan hujjoji ne a gare ku waɗanda suke tabbatar muku gaskiyar abin da na faɗa muku na labarin manzancina gare ku, in har kun kasance masu imani. Sannan kuma ina mai gaskata littafin Attaura da aka saukar a gabanina da kuma Linjila da aka saukar mini. Kuma na zo don in halatta muku wasu abubuwa da aka haramta muku. Na kuma zo muku da wata aya daga Ubangijinku, wadda take nuna gaskiyata, don haka ku kiyaye dokokin Allah, ku bi ni a kan abin da nake kiran ku zuwa gare shi. Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, don haka ku bauta masa shi kaɗai; wannan ita ce hanyar Allah miƙaƙƙiya, wadda za ta kai ku ga samun yardar Allah (Mai tsarki da daukaka).”

  52. ۞فَلَمَّآ أَحَسَّ عِيسَىٰ مِنۡهُمُ ٱلۡكُفۡرَ قَالَ مَنۡ أَنصَارِيٓ إِلَى ٱللَّهِۖ قَالَ ٱلۡحَوَارِيُّونَ نَحۡنُ أَنصَارُ ٱللَّهِ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَٱشۡهَدۡ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ

    Open ayah 3:52

    To yayin da Isa ya ga alamun kafirci a tare da su sai ya ce: “Su wane ne za su taimake ni wajen kira zuwa ga Allah?” Sai Hawariyawa suka ce: “Mu ne mataimaka addinin Allah, mun yi imani da Allah, kuma ka ba da shaida cewa, mu Musulmai ne.

  53. رَبَّنَآ ءَامَنَّا بِمَآ أَنزَلۡتَ وَٱتَّبَعۡنَا ٱلرَّسُولَ فَٱكۡتُبۡنَا مَعَ ٱلشَّٰهِدِينَ

    Open ayah 3:53

    “Ya Ubangijinmu, mun yi imani da abin da Ka saukar, kuma mun yi ɗa’a ga Manzo, don haka Ka rubuta mu tare da masu shaida.”

  54. وَمَكَرُواْ وَمَكَرَ ٱللَّهُۖ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلۡمَٰكِرِينَ

    Open ayah 3:54

    Sai suka shirya makirci, sai Allah Ya mayar musu da martani game da makircinsu; kuma Allah Shi ne Fiyayyen masu mayar da martanin makirci.

  55. إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَىٰٓ إِنِّي مُتَوَفِّيكَ وَرَافِعُكَ إِلَيَّ وَمُطَهِّرُكَ مِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَجَاعِلُ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوكَ فَوۡقَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ فِيمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

    Open ayah 3:55

    Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya ce: “Ya kai Isa, lalle Ni Mai karɓar ranka ne, kuma Ni Mai ɗaukaka ka ne zuwa gare Ni, kuma zan tsarkake ka daga (cutarwar) waɗanda suka kafirta, kuma zan ɗora waɗanda suka bi ka a kan waɗanda suka kafirce maka har zuwa ranar tashin alƙiyama; sannan zuwa gare Ni ne makomarku take, sai In yi hukunci a tsakaninku game da abin da kuke saɓani a kansa.

  56. فَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَأُعَذِّبُهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّٰصِرِينَ

    Open ayah 3:56

    Amma waɗanda suka kafirce, zan yi musu azaba mai tsanani a duniya da lahira, kuma ba su da wasu mataimaka.”

  57. وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 3:57

    Amma kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka nagari, to (Allah) zai cika musu ladansu. Kuma Allah ba Ya son azzalumai.

  58. ذَٰلِكَ نَتۡلُوهُ عَلَيۡكَ مِنَ ٱلۡأٓيَٰتِ وَٱلذِّكۡرِ ٱلۡحَكِيمِ

    Open ayah 3:58

    “Wannan (labara) Muna karanta maka shi ne daga ayoyi da kuma Alkur’ani mai hikima.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba mu labarin cewa, lokacin da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga alamar bijirewa da kafircewa daga Banu Isra’ila da ƙaryata annabcinsa, sai ya nemi taimako daga zaɓaɓɓu cikin almajiransa, yana mai kiran su da cewa, wane ne zai taimaka masa a kan wannan kira da yake yi zuwa ga addinin Allah? Sai suka amsa da cewa, su za su zama masu taimakon addinin Allah, sannan suka shelanta imaninsu a fili, kuma suka kafa shi shaida a kan Musuluncinsu, suka kuma roƙi Ubangijinsu, suna masu kamun ƙafa da imaninsu da littafin Linjila da ya saukar ga Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kuma biyayyarsu gare shi da cewa, Allah ya rubuta su cikin waɗanda suka ba da gaskiya da Kaɗaitakar Allah da gaskiyar manzannin Allah, kuma suka bi umarninsa, suka kauce wa abin da ya hana. An karɓo daga Abdullah ɗan Mas\'ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: \"Babu wani annabi gabanina da Allah ya aiko shi cikin wata al\'ummarsa sai ya kasance a cikin al\'ummar tasa yana da hawariyawa da sahabbai waɗanda suke riƙo da sunnarsa suke kuma koyi da umarninsa...\" [Muslim #50]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma sai ya ba da labarin irin makircin da Banu Isra’ila suka ƙulla ga Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), na ƙoƙarin hallaka shi. Su suna ƙulla makircinsu, Allah kuma yana shirya musu martani a kan makircinsu, domin Allah shi ne mafi iya mayar da martanin makirci, kuma mafi ƙarfi, mafi sani. Don haka sai Allah ya jefa kamannin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a kan ɗaya daga cikinsu, sai suka kama shi suka kashe shi, suna zaton Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne suka kashe. Shi kuma Allah ya jefa masa barci, sannan ya ɗauke shi zuwa sama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa game da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, zai karɓi ransa irin karɓar ran mai barci, sannan zai ɗaukaka shi zuwa gare shi da gangar jikinsa da kuma ruhinsa, sannan zai kuɓutar da shi daga waɗanda suka kafirta, ya fitar da shi, ya ɗaga shi zuwa sama, sannan zai sanya mabiyansa su zama su ne masu rinjaye a kan kafirai da ƙarfin hujja da izza da ɗaukaka har zuwa tashin alƙiyama. Waɗannan mabiyan nasa da Allah yake yi wa wannan alƙawari, su ne Nasara, waɗanda suka tsaya daidai a kan koyarwarsa har zuwa lokacin aiko Annabi Muhammad (ﷺ), sai kuma Musulmi waɗanda su ne mabiya na gaskiya ga Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), waɗanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafe su, ya ba su nasara a kan Yahudawa da Nasara da sauran kafirai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa masu saɓani cikin lamarin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, dukkansu makomarsu zuwa gare shi take, kuma zai yi hukunci a tsakaninsu game da wannan saɓani da suke yi. Hukuncinsa kuwa shi ne, zai yi musu azaba mai tsanani a nan duniya, ta hanyar kisa da ɗauri da ƙasƙanci da wulaƙanci da raba su da dukiyoyinsu da ƙuncin zukata da za su yi ta fama da shi, sannan kuma a lahira su gamu da azabar Jahannama, a lokacin da babu wanda zai taimaka musu, ya kare su daga azabar Allah (Mai tsarki da daukaka). Su kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka yi aiki na ƙwarai, hukuncinsa a kansu shi ne, zai cika musu ladansu babu ragi ko tawaya a duniya da lahira. A nan duniya ta hanyar ba su nasara kan abokan gabarsu, da izza da rayuwa mai kyau da kyakkyawan ambato da sauransu, a lahira kuwa ya saka musu da gidan Aljanna cikin ni’ima ta har abada. Kuma Allah ba ya son azzalumai, don haka shi kansa babu yadda za a yi ya yi zalunci cikin hukuncinsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce da Annabinsa waɗannan labarai da yake ba shi na Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mahaifiyarsa Maryamu (() da sauran ƙissoshi da aka ambata an karanta masa su ne don su zama hujjoji masu nuna gaskiyarsa da gaskiyar annabinsa, sannan kuma suna daga cikin ƙissoshin Alƙur’ani ne, mai cike da hikimomi, kuma mai yanke hukunci.

  59. إِنَّ مَثَلَ عِيسَىٰ عِندَ ٱللَّهِ كَمَثَلِ ءَادَمَۖ خَلَقَهُۥ مِن تُرَابٖ ثُمَّ قَالَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

    Open ayah 3:59

    Lalle misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne; Ya halicce shi daga turɓaya, sannan Ya ce da shi: “Kasance.” nan take sai ya kasance.

  60. ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُن مِّنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ 

    Open ayah 3:60

    Gaskiya ce daga wajen Ubangijinka, don haka kar ka kasance cikin masu yin kokwanto.

  61. فَمَنۡ حَآجَّكَ فِيهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ فَقُلۡ تَعَالَوۡاْ نَدۡعُ أَبۡنَآءَنَا وَأَبۡنَآءَكُمۡ وَنِسَآءَنَا وَنِسَآءَكُمۡ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَكُمۡ ثُمَّ نَبۡتَهِلۡ فَنَجۡعَل لَّعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَى ٱلۡكَٰذِبِينَ

    Open ayah 3:61

    To duk wanda ya yi jayayya da kai cikin lamarinsa (Isa) bayan abin da ya zo maka na ilimi, to ka ce: “Ku zo mu kirawo ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da mu kanmu da ku kanku, sannan mu ƙasƙantar da kawunanmu cikin addu’a don mu roƙi tsinuwar Allah ta tabbata a kan maƙaryata”.

  62. إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡقَصَصُ ٱلۡحَقُّۚ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّا ٱللَّهُۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 3:62

    Lalle wannan shi ne ba da labari na gaskiya. Kuma babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Kuma lalle Allah Shi ne Mabuwayi, Mai hikima.

  63. فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُفۡسِدِينَ

    Open ayah 3:63

    To idan sun ba da baya, to lalle Allah Yana sane da maɓarnata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tsayar da hujja a kan Nasara waɗanda suke bautar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da sunan shi Allah ne, ko kuma ɗan Allah ne, saboda an same shi ba uba. Allah yana kwatanta musu cewa, samar da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba uba da samar da Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba uwa ba uba, Allah ya halicce shi kawai da ƙasa, ya ce masa, ‘kasance’, sai ya kasance kamar yadda Allah ya yi nufinsa duka abu ɗaya ne a wurin Allah. To idan har suna ganin samuwar Annabi Isa ba uba dalili ne da zai sa su riƙe shi Allah, ko ɗan Allah; to me ya sa ba su yi haka ga Annabi Adamu ba, alhali ga shi samuwarsa ta fi ta Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ban al’ajabi? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shaida wa Annabinsa cewa, wannan labarin da ya ba shi na Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) gaskiya ce daga Ubangijinsa, don haka kada ya zama cikin masu shakka. Hasali ma idan har wani ya zo yana jayayya da shi cikin lamarin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), bayan abin da ya zo masa na ilimi da gamsasshen bayani a kan wannan batu; to ya faɗa wa masu jayayya da shi cewa, shi da su gaba ɗaya, su fito da ‘ya’yansu, da matansu, da su kansu, sai a taru a yi addu’a, Allah ya la’anci maƙaryaci a tsakaninsu. Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas yana cewa: “Lokacin da wannan ayar ta sauka, Manzon Allah (ﷺ) ya kirawo Aliyyu da Faɗimatu da Hasan da Husaini, ya ce: “Ya Allah, waɗannan iyalaina ne.” [Muslim #2404]. An karɓo daga Huzaifa ya ce: “Wasu mutane su biyu daga mutanen Najarana ɗaya ana ce masa Al-Aƙibu, ɗayan kuwa Assayyidu, sun zo ga Annabi (ﷺ) suna so su yi tsinuwa tsakaninsa da su (game da sha’anin Annabi Isa), sai ɗayansu ya ce wa ɗan’uwansa: ‘Kada ka yi wannan aikin, Wallahi idan ya zamanto Annabi ne da gaske, sannan muka yi tsinuwa tsakaninmu da shi; to da mu da zurriyyarmu ba za mu rabauta ba har abada.’ Daga nan sai suka fasa, suka nemi sulhu da Annabi (ﷺ) a kan za su ba shi duk abin da ya nema daga gare su na dukiyar sulhu.” [Dubi, Bukhari #4350, da Muslim #2420]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara jaddada wa Annabinsa (ﷺ) cewa, wannan labari da yake ba shi na Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ne labarin gaskiya, duk wani labari da ya ci karo da shi, to ba gaskiya ba ne, ƙarya ne. Kuma babu wani wanda ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kaɗai, Mabuwayi da ya gagari kowa da komai, Mai hikima cikin duk ayyukansa. To idan waɗannan sun bijire wa gaskiya, sun riƙi ƙarya; to sun tabbata maɓarnata, Allah kuwa yana sane da su, kuma zai yi musu sakayya a kan ayyukansu.

  64. قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۭ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـٔٗا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ

    Open ayah 3:64

    Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, ku taho ga wata kalma mai daidaitawa tsakaninmu da ku cewa, kar mu bauta wa kowa sai Allah, kuma kar mu haɗa Shi da wani, kuma kada wani sashi a cikinmu ya riƙi wani sashi a matsayin abin bauta ba Allah ba.” Idan kuwa sun ba da baya, to ku ce: “Ku shaida cewa, lalle mu Musulmi ne.”

  65. يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تُحَآجُّونَ فِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمَآ أُنزِلَتِ ٱلتَّوۡرَىٰةُ وَٱلۡإِنجِيلُ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِهِۦٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

    Open ayah 3:65

    Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke yin jayayya game da Ibrahimu, alhalin ba a saukar da Attaura da Linjila ba sai bayan shuɗewarsa? Yanzu ba za ku hankalta ba?

  66. هَٰٓأَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ حَٰجَجۡتُمۡ فِيمَا لَكُم بِهِۦ عِلۡمٞ فَلِمَ تُحَآجُّونَ فِيمَا لَيۡسَ لَكُم بِهِۦ عِلۡمٞۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 3:66

    Ga ku nan ku waɗannan kun yi jayayya kan abin da kuke da ilimi a kai, to don me kuma kuke jayayya a kan abin da ba ku da ilimi a kansa? Kuma Allah Yana sane ku ba ku sani ba.

  67. مَا كَانَ إِبۡرَٰهِيمُ يَهُودِيّٗا وَلَا نَصۡرَانِيّٗا وَلَٰكِن كَانَ حَنِيفٗا مُّسۡلِمٗا وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

    Open ayah 3:67

    Ibrahimu bai taɓa zama Bayahude ba, sannan bai taɓa zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin ɓarna ne, Musulmi, kuma bai kasance ɗaya daga cikin mushirikai ba.

  68. إِنَّ أَوۡلَى ٱلنَّاسِ بِإِبۡرَٰهِيمَ لَلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ وَهَٰذَا ٱلنَّبِيُّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۗ وَٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 3:68

    Lalle mafi kusancin mutane da Ibrahimu su ne waɗanda suka bi shi, sai kuma wannan Annabin, da kuma waɗanda suka yi Imani. Kuma Allah shi ne Majiɓincin al’amuran muminai. Bayan an kira Ma’abota Littafi zuwa ga addu’ar tsinuwa amma sun ƙi yarda, sannan an kawo musu hujjoji iri-iri waɗanda suka nuna ɓacin addinin da suke kai, sun kuma kasa kare ɓatansu, kuma Allah ya riga ya san yadda Annabi (ﷺ) yake matuƙar tausayin su, yana kwaɗayin shiriyarsu, sai Allah ya umarce shi da ya kirawo su gaba ɗaya zuwa ga kalma ta bai-ɗaya, wadda kowa da kowa zai daidaita a kanta, kuma za su haɗa kai a kanta. Wannan kalma ita ce kaɗaita Allah (Mai tsarki da daukaka) da bauta, watau kada a bauta wa wani ba shi ba, mala’ika ne, ko wani annabi, ko waliyyi, ko wani gunki. Kada kuma su ɗauki wasu iyayen giji, suna bauta musu ba Allah ba, har su riƙa halatta musu haram ko su haramta musu halal su kuma yarda. To idan sun bijire, sun ƙi yarda da wannan kiran; to ku muminai ku kafa su shaida cewa, ku Musulmi ne, kuma za ku ci gaba da bin wannan addinin da Allah ya zaɓa muku. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fuskantar da maganarsa ga Yahudawa da Nasara cewa, don mene ne suke jayayya game da lamarin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi); kowanne yana da’awar cewa a kan addininsa yake, Yahudawa suna cewa shi Bayahude ne, Nasara ma suna cewa shi Banasare ne, alhalin yadda gaskiyar al’amarin take, littafin Attaura da littafin Linjila, ba a saukar da su ba sai bayan mutuwarsa da lokaci mai tsawo. Yanzu ba za su yi aiki da hankulansu ba, su gane cewa, abin da suke faɗa ƙarya ne? To ga shi yanzu su Yahudu da Nasara suna jayayya a kan abin da suke da ilimi a kansa na al’amarin addininsu, da abin da aka ambata a littattafansu. To amma me ya sa za su riƙa jayayya a kan abin da ba su da ilimi a kansa na lamarin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da addinin da ya rayu a kansa? Allah kam iliminsa ya kewaye komai, ya san abin da su ba su sani ba, amma su ba su san komai ba daga abin da Allah ya sani. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana musu gaskiyar al’amarin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ƙaryata maganar cewa shi Bayahude ne, ko Banasare. Allah ya tabbatar da cewa, Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) tsaye yake ƙyam a kan addinin gaskiya, ba ruwansa da duk wata ɓarna da shirka, yana bin umarnin Allah cikin ikhlasi, kuma ba ya cikin masu haɗa Allah da wani, masu bautar gumaka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci waɗanda suka fi cancantar su zama tare da Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya bayyana cewa, su ne waɗanda suka bi addininsa, suka kuma bi hanyarsa ta kaɗaita Allah a wajen bauta, waɗanda su ne Annabi (ﷺ), da sahabbansa, da muminai da za su zo bayansu. To waɗannan su suka fi cancanta su zama masoyansa, majiɓintansa, kuma Allah shi ne yake jiɓintar lamarin muminai, ya taimaka musu, ya ba su nasara a kan abokan gabarsu.

  69. وَدَّت طَّآئِفَةٞ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَوۡ يُضِلُّونَكُمۡ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ

    Open ayah 3:69

    Wata ƙungiya daga cikin Ma’abota Littatafi sun yi burin ina ma sun ɓatar da ku, kuma ba za su ɓatar da kowa ba sai kawunansu, amma ba sa sanin hakan.

  70. يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَأَنتُمۡ تَشۡهَدُونَ 

    Open ayah 3:70

    Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke kafirce wa ayoyin Allah, alhalin ku kuna shaidawa (cewa gaskiya ne)?

  71. يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تَلۡبِسُونَ ٱلۡحَقَّ بِٱلۡبَٰطِلِ وَتَكۡتُمُونَ ٱلۡحَقَّ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 3:71

    Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke cakuɗa gaskiya da ƙarya, kuma kuke ɓoye gaskiya, alhalin ku kuna sane? Allah (Mai tsarki da daukaka) a nan yana gargaɗin bayinsa muminai ne game da makircin wata ƙungiya ta Yahudawa da Nasara, waɗanda ba su da wani buri a rayuwarsu, sai na ganin Musulmai sun lalace sun ɓace, sun yi watsi da addininsu na Musulunci, ba don komai ba sai don hassada da suke nuna musu. Sai dai makircinsu su kaɗai zai ci, domin kansu kawai suke ƙara ɓatarwa, don haka duk ƙoƙarin da suke yi na ɓatar da Musulmi yana komawa ne a kansu, suna ƙara dulmiya ne cikin ɓata da taɓewa, amma su ba su san hakan ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya soki abin da Ma’abota Littafi suke aikatawa, yana cewa, don me suke kafirce wa Alƙur’ani, alhalin sun san gaskiya ne, suna kuma shaidawa a kan hakan, domin sun karanta siffofin Annabi (ﷺ) a littattafansu? Kuma don me suke cakuɗa ƙarya da gaskiya, har a kasa bambancewa tsakaninsu, kuma su ɓoye gaskiya alhalin suna sane da ɓarnar da suke yi?

  72. وَقَالَت طَّآئِفَةٞ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ ءَامِنُواْ بِٱلَّذِيٓ أُنزِلَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَجۡهَ ٱلنَّهَارِ وَٱكۡفُرُوٓاْ ءَاخِرَهُۥ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

    Open ayah 3:72

    Kuma wata ƙungiya cikin Ma’abota Littafi suka ce: “Ku yi imani mana da abin da aka saukar wa waɗanda suka yi imani a farkon yini, kuma ku kafirce a ƙarshen yini, mai yiwuwa ne su dawo (daga rakiyar addininsu).

  73. وَلَا تُؤۡمِنُوٓاْ إِلَّا لِمَن تَبِعَ دِينَكُمۡ قُلۡ إِنَّ ٱلۡهُدَىٰ هُدَى ٱللَّهِ أَن يُؤۡتَىٰٓ أَحَدٞ مِّثۡلَ مَآ أُوتِيتُمۡ أَوۡ يُحَآجُّوكُمۡ عِندَ رَبِّكُمۡۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

    Open ayah 3:73

    “Kuma kada ku amince da kowa sai wanda ya bi addininku.” Ka ce: “Lalle shiriya ita ce shiriyar Allah, domin kar (ku yarda a ce) an ba wani mutum irin abin da aka ba ku, ko kuma ku ba su dama su yi jayayya da ku a wajen Ubangijinku.” Ka ce: “Lalle falala a hannun Allah take, Yana bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai yalwa ne, Mai yawan sani.

  74. يَخۡتَصُّ بِرَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

    Open ayah 3:74

    “Yana keɓantar wanda Ya ga dama da rahamarsa, kuma Allah Ma’abocin falala ne wadda take mai girma.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin wasu miyagun mutane ne a cikin Yahudawa da Nasara, waɗanda suke ta ƙulle-ƙullen makirci ga Musulmi ta hanyar kawo ruɗu na addini ga wasu raunanan Musulmi. Sun yanke shawara a tsakaninsu cewa, su bayyana imaninsu da abin da Manzon Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zo da shi a farkon yini; idan yamma ta yi kuma su kafirce masa. Yin haka shi zai sa masu raunin fahinta cikin muminai su riƙa cewa, da a ce wannan addinin gaskiya ne, da waɗanda suka yi imani da shi cikin Ma’abota Littafi, ba su yi ridda ba. Manufarsu ita ce Musulmi su watsar da addininsu gaba ɗaya. Sannan magana ta dawo kan tattaunawar Yahudawa a tsakaninsu, da irin yadda suke yi wa junansu wasiyya, yayin da wasunsu suka faɗa wa wasu cewa, kada su yarda da kowa idan ba wanda yake bin addininsu ba, kada kuma su yarda su bayyana sirrinsu ga wani Musulmi don kada ya samu irin ilimin abin da suka samu; idan har sun yi haka to za su koye shi, su ma sai su zama masu ilimi ko kuma su riƙe shi a matsayin abin da za su kafa musu hujja da shi a gaban Allah, sai su ba da shaidar cewa, gaskiya ta bayyana gare su, ƙin bi suka yi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce wa Annabinsa ya faɗa musu cewa, shiriya a hannun Allah take, yana bayar da ita ga wanda ya ga dama daga bayinsa. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) mai yalwar falala ne, mai yawan kyauta, kuma mai cikakken sani ne game da waɗanda suka cancanci a kyautata musu, don haka yana yin kyautarsa ne ga wanda ya cancanta, ya kuma hana wanda bai cancanta ba kuma yana keɓance wanda ya ga dama da rahamarsa, kuma shi ma’abocin falala ne mai yawa.

  75. ۞وَمِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مَنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِقِنطَارٖ يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِدِينَارٖ لَّا يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ إِلَّا مَا دُمۡتَ عَلَيۡهِ قَآئِمٗاۗ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لَيۡسَ عَلَيۡنَا فِي ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ سَبِيلٞ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 3:75

    Kuma daga cikin Ma’abota Littafi akwai wanda in da za ka ba shi amana ta dukiya mai yawa, zai dawo maka da ita, daga cikinsu kuwa akwai wanda idan da za ka ba shi amana ta dinare ɗaya, ba zai dawo maka da shi ba, sai fa idan ka tashi tsaye a kansa. Wannan kuwa saboda sun ce: “Babu wani laifi a kanmu (don mun ci dukiyar) bobayin mutane.” Kuma suna faɗin ƙarya su jingina wa Allah, alhalin su suna sane.

  76. بَلَىٰۚ مَنۡ أَوۡفَىٰ بِعَهۡدِهِۦ وَٱتَّقَىٰ فَإِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 3:76

    Ba haka ba ne, duk wanda ya cika alƙawarinsa, kuma ya tsare dokar Allah, to lalle Allah Yana son masu taƙawa. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana irin ƙaryar da Yahudawa suke yi na cewa an ba su matsayi na ilimi da addini wanda ba wanda aka ba irinsa, da kuma nuna cewa bin addininsu kaɗai shi ne shiriya, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) a nan ya ƙaryata su, ya nuna su a matsayin maciya amana, waɗanda mu’amalarsu da mutane babu gaskiya a cikinta, kamar yadda mu’amalarsu da Allah (Mai tsarki da daukaka) ita ma babu gaskiya a cikinta ko kaɗan. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a cikin ma’abota Littafi akwai mai amana, wanda idan da za ka ba shi amanar dukiya komai yawanta, ba zai ci komai daga cikinta ba, zai dawo maka da ita kamar yadda ka ba shi. Daga cikinsu kuma akwai maci amana wanda da za ka ba shi ɗan kuɗi kaɗan, kamar Dinari ɗaya; to ba zai taɓa dawo maka da kayanka ba, sai ka yi tsayuwar daka a kansa, ka matsa masa, sannan zai dawo da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin wannan mugun hali nasu da cewa, saboda suna riyawa ne cewa, ba su da wani laifi don sun ci dukiyar waɗanda ba Yahudawa ba, wato suna nufin Musulmi. Watau a nan sun haɗa laifuka biyu: Laifin cin dukiyar haram da kuma laifin halatta haram. To wannan ita ce ƙaryar da suka yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka), alhalin sun san ƙarya suke. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rushe wannan da’awar tasu, da cewa, al’amarin ba haka yake ba. Duk wani Bayahude ko Banasare idan ya cika alƙawarin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi da su, ya yi imani da Annabi (ﷺ) da Alƙur’anin da ya saukar masa, ya kiyaye dokokin Allah (Mai tsarki da daukaka) ta hanyar aikata abin da aka umarce shi da barin abin da aka hana shi; to lalle ya sani Allah (Mai tsarki da daukaka) yana son masu taƙawa cikin bayinsa.

  77. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَشۡتَرُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَأَيۡمَٰنِهِمۡ ثَمَنٗا قَلِيلًا أُوْلَٰٓئِكَ لَا خَلَٰقَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَلَا يُكَلِّمُهُمُ ٱللَّهُ وَلَا يَنظُرُ إِلَيۡهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَلَا يُزَكِّيهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 3:77

    Lalle waɗanda suke musanya alƙawarin Allah da rantse-rantsensu da wani ɗan farashi ƙanƙani, waɗannan ba su da wani rabo a lahira, kuma Allah ba zai yi musu magana ba, kuma ba zai dube su (duba na rahama) ba a ranar alƙiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi.

  78. وَإِنَّ مِنۡهُمۡ لَفَرِيقٗا يَلۡوُۥنَ أَلۡسِنَتَهُم بِٱلۡكِتَٰبِ لِتَحۡسَبُوهُ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمَا هُوَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَيَقُولُونَ هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ وَمَا هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 3:78

    Kuma lalle daga cikinsu akwai wani ɓangare da suke karkatar da harshensu lokacin karanta Littafin (Attaura), don ku yi zaton yana cikin Littafin, alhali kuwa ba ya cikin Littafin, kuma za su riƙa cewa, shi (wahayi ne saukakke) daga wurin Allah, alhalin kuwa ba daga wurin Allah yake ba, kuma za su riƙa faɗar ƙarya suna jingina wa Allah, alhalin suna sane.

  79. مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُؤۡتِيَهُ ٱللَّهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُواْ عِبَادٗا لِّي مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن كُونُواْ رَبَّٰنِيِّـۧنَ بِمَا كُنتُمۡ تُعَلِّمُونَ ٱلۡكِتَٰبَ وَبِمَا كُنتُمۡ تَدۡرُسُونَ

    Open ayah 3:79

    Bai dace ba ga wani mutum wanda Allah zai ba shi littafi da hukunci da annabci, sannan ya ce wa mutane: “Ku zama bayina ba na Allah ba,” sai dai (ya ce): “Ku zamo malamai na Allah saboda abin da kuke karantarwa na littafi, kuma saboda abin da kuka kasance kuna karantawa.”

  80. وَلَا يَأۡمُرَكُمۡ أَن تَتَّخِذُواْ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ أَرۡبَابًاۚ أَيَأۡمُرُكُم بِٱلۡكُفۡرِ بَعۡدَ إِذۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ 

    Open ayah 3:80

    Kuma ba zai umarce ku da ku riƙi mala’iku ko annabawa a matsayin iyayengiji ba; yanzu zai umarce ku da kafirci ne bayan kuna Musulmi? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin irin uƙubar da ya tanadar wa waɗanda suke karya alƙawarin da suka yi tsakaninsu da shi, su canja shi don wani abu na duniya da bai taka kara ya karya ba, maimakon su yi biyayya ga Annabi (ﷺ), su yi imani da shi, sai su riƙa rantsuwar ƙarya don su samu wani abin duniya. Allah ya ce, waɗannan ne ba su da wani rabo na alheri a lahira, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ba zai yi magana da su ba, kuma ba zai dube su ba, sannan ba zai tsarkake su daga zunubansu ba, kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi. Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wanda ya yi rantsuwa don ya ci wata dukiya da ba tasa ba; to zai haɗu da Allah yana mai fushi da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gaskata wannan magana tasa, ya saukar da wannan ayar: “Lalle waɗanda suke musanya alƙawarin Allah da rantse-rantsensu da wani ɗan farashi ƙanƙani….” har zuwa ƙarshen ayar. Abu Wa’il ya ce: Sai Al-Ash’as ɗan Ƙaisu ya fito gare mu ya ce: Me Baban Abdurrahman yake faɗa muku (yana nufin Ibn Mas’ud)? Sai muka faɗa masa. Sai ya ce: “Gaskiya ya faɗa, a kaina wannan ayar ta sauka. Mun yi rigima da wani mutum a kan wata rijiya, sai muka je gaban Annabi (ﷺ) domin ya yi mana hukunci, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kawo shaidunka biyu, ko kuma shi ya rantse.” Sai na ce: In dai haka ne; to fa shi zai rantse ba tare da ya damu ba. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya yi rantsuwa don ya cancanci wata dukiya alhalin ƙarya yake; to zai haɗu da Allah alhalin yana mai fushi da shi.” Sai Allah ya gaskata wannan magana, ya saukar da wannan ayar. [Bukhari #2515-2516, da Muslim #136]. Abdullahi ɗan Abu Aufa (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: Wani mutum a kasuwa, ya tsaya a kan hajarsa yana rantsuwar cewa, an saya da kuɗi kaza da kaza, alhalin ƙarya yake, don kawai ya zurma wani Musulmi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar. [Bukhari #2088]. Babu cin karo tsakanin ruwayoyin nan guda biyu, domin zai iya yiwuwa ayar ta sauka a kan ƙissoshin biyu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai halin wasu mutane daga cikin Yahudu da Nasara cewa, idan suna karanta littafin da aka saukar musu, sai su riƙa karkata harshensu suna jirkita wasu lafuzan littafin, suna wasa da ma’anoninsa, da nufin ɓatar da muminai, don su zaci cewa maganar Allah ce abin da suke karantawa, alhalin ba ita ba ce; kawai wannan wata bidi’a ce suka shigo da ita a cikin addini. Da wannan aiki nasu, suna yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka) ƙarya ne tare da suna sani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba abu ne mai yiwuwa ba, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zaɓi wani mutum, ya ba shi littafi da hikima, ya yi masa baiwar annabci, sannan ya riƙa kiran mutane kan su bauta masa ba Allah ba. Idan har Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa wasu bayinsa irin wannan baiwa; to zai umarce su ne da su zamo malamai na Allah, masu aiki da iliminsu, masu ikhlasi da bautar Allah, suna koyar da mutane ilimi da tarbiyya ta ƙwarai, saboda littafin Allah (Mai tsarki da daukaka) ne suke koyarwa. Hakanan kuma ba zai umarce su su riƙa bauta wa mala’iku ko annabawa ba Allah (Mai tsarki da daukaka) ba. Domin babu yadda za a yi ya umarce su da su kafirce wa Allah (Mai tsarki da daukaka) bayan sun musulunta, sun miƙa wuya ga Allah (Mai tsarki da daukaka).

  81. وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ لَمَآ ءَاتَيۡتُكُم مِّن كِتَٰبٖ وَحِكۡمَةٖ ثُمَّ جَآءَكُمۡ رَسُولٞ مُّصَدِّقٞ لِّمَا مَعَكُمۡ لَتُؤۡمِنُنَّ بِهِۦ وَلَتَنصُرُنَّهُۥۚ قَالَ ءَأَقۡرَرۡتُمۡ وَأَخَذۡتُمۡ عَلَىٰ ذَٰلِكُمۡ إِصۡرِيۖ قَالُوٓاْ أَقۡرَرۡنَاۚ قَالَ فَٱشۡهَدُواْ وَأَنَا۠ مَعَكُم مِّنَ ٱلشَّٰهِدِينَ

    Open ayah 3:81

    Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya yi alƙawari da annabawa cewa: “Duk irin abin da Na ba ku na littafi da wata hikima, sannan sai wani Manzo ya zo muku mai gaskata abin da yake tare da ku, to lalle ku yi imani da shi, kuma lalle ku taimake shi.” Ya ce: “Shin kun yarda da hakan, kuma kun ɗauki alƙawarina a kan hakan?” Suka ce: “Mun yarda da haka.” Ya ce: “To ku shaida, kuma Ni ma Ina tare da ku cikin masu shaidawa.”

  82. فَمَن تَوَلَّىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

    Open ayah 3:82

    To duk wanda ya juya baya bayan wannan, to waɗannan sune fasiƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabinsa (ﷺ) lokacin da ya ɗauki alƙawari mai ƙarfi tsakaninsa da annabawa cewa, duk da annabcin da ya aiko su da shi da littattafai da hikima da ya ba su, sannan daga baya ya aiko da wani manzo ya zo musu, su da al’ummominsu, yana tabbatar da gaskiyar da suka zo da ita, to wajibi ne su yi imani da shi su gaskata abin da ya zo da shi, su taimaka masa. Ana nufin Manzon Allah Muhammadu (ﷺ). Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara ƙarfafa musu cewa, sun yarda da wannan alƙawari, kuma sun riƙe shi da ƙarfi?! Dukkansu suka amsa da cewa, sun yarda kuma sun tabbata. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kafa su da su zama masu shaidar kansu da kansu a kan haka da kuma al’ummominsu. Duk kuma wanda ya bijire bayan wannan alƙawari da ya ɗauka; to masu yin haka su ne fasiƙai, waɗanda suka fita daga ɗa’ar Allah (Mai tsarki da daukaka). Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Da a ce ɗan’uwana Musa yana nan da ransa, da babu abin da zai fisshe shi, dole sai yi min biyayya.” [Ahmad #5195].

  83. أَفَغَيۡرَ دِينِ ٱللَّهِ يَبۡغُونَ وَلَهُۥٓ أَسۡلَمَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ طَوۡعٗا وَكَرۡهٗا وَإِلَيۡهِ يُرۡجَعُونَ

    Open ayah 3:83

    To shin yanzu wani addini suke nema ba na Allah ba, alhalin duk wanda yake cikin sammai da ƙasa gare Shi ne ya miƙa wuya yana so ko yana ƙi, kuma zuwa gare Shi za a komar da su?

  84. قُلۡ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ

    Open ayah 3:84

    Ka ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar wa Ibrahimu da Isma’ila da Ishaƙa da Ya’aƙubu da jikokin Ya’aƙubu, da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba wa annabawa daga Ubangijinsu; ba ma nuna bambanci a kan ɗaya daga cikinsu, kuma mu muna masu miƙa wuya gare Shi.”

  85. وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

    Open ayah 3:85

    Duk kuma wanda ya nemi (bin) wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karɓa daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, duk wanda ya nemi wani addini ba Musuluncin da Allah ya aiko Annabinsa Muhammad (ﷺ) da shi ba; to ya yi aikin banza. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sukar duk wanda ya nemi wani addini ba na Allah ba, kuma ba shari’arsa ba, alhalin duk waɗanda suke sama da waɗanda suke ƙasa, gare shi suka miƙa wuya, sun so hakan, ko ba su so ba, duk suna ƙarƙashin ikonsa ne, shi ne mai sarrafa su yadda ya ga dama. Kuma idan suka mutu zuwa gare shi ne makomarsu take, zai yi wa kowa hisabi da gwargwadon aikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya fuskantar da maganarsa zuwa ga Annabi (ﷺ), yana umartar sa da ya gaya wa waɗanda suke neman wani addini daban ba Musulunci ba cewa, mu mun yi imani da Allah da Alƙur’anin da aka saukar mana, da kuma sunna, da duk abin da Allah ya saukar wa annabawansa, Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ‘ya’yansa, Annabi Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Is’haƙa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da Annabi Yaƙuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ɗan Annabi Is’haƙa, da kuma abin da aka saukar wa annabawan Banu Isra’ila, waɗanda suka fito daga zurriyar ‘ya’yan Annabi Yaƙubu, su goma sha biyu. Hakanan mun yi imani da littafin Attaura da Allah ya saukar wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da littafin Linjila da Allah ya saukar wa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kuma mu’ujizojin da Allah ya ba su domin tabbatar da gaskiyarsu. Mun yi imani da duk annabawa gaba ɗayansu, da abin da aka saukar musu na littattafai daga Ubangijinsu, ba za mu bambanta tsakaninsu ba wajen imani, ta hanyar yin imani da wasu, mu kafirce wa wasu; mu gaba ɗayanmu ciki da waje, mun miƙa wuya ga Allah (Mai tsarki da daukaka), ba za mu yarda da wani addini in ba Musulunci ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya bi wani addini ba na Musulunci ba; to ba za a taɓa karɓar sa daga gare shi ba, kuma a lahira yana cikin hasararru, wannan kuma ita ce hasara ta haƙiƙa, domin ya wahalar da kansa a kan abin da bai amfane shi ba.

  86. كَيۡفَ يَهۡدِي ٱللَّهُ قَوۡمٗا كَفَرُواْ بَعۡدَ إِيمَٰنِهِمۡ وَشَهِدُوٓاْ أَنَّ ٱلرَّسُولَ حَقّٞ وَجَآءَهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 3:86

    Ta yaya Allah zai shiryar da mutanen da suka kafirta bayan imaninsu, kuma bayan sun shaida cewa, Manzon gaskiya ne, kuma hujjoji sun zo musu? Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai.

  87. أُوْلَٰٓئِكَ جَزَآؤُهُمۡ أَنَّ عَلَيۡهِمۡ لَعۡنَةَ ٱللَّهِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 3:87

    Waɗannan sakamakonsu shi ne, la’antar Allah za ta tabbata a kansu da ta mala’iku da mutane gaba ɗaya.

  88. خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

    Open ayah 3:88

    Suna masu dawwama a cikinta, ba za a sassauta musu azaba ba, kuma ba za a jinkirta musu ba.

  89. إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

    Open ayah 3:89

    Sai fa waɗanda suka sake tuba bayan haka, kuma suka gyara (ayyukansu), to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ba zai shiryar da mutanen da suka yi ridda ba, suka juya wa Musulunci baya, alhalin da farko sun yi imani, kuma sun tabbatar da cewa, Annabi Muhammad (ﷺ) gaskiya ne, saboda hujjoji bayyanannu, kuma gamsassu, masu ƙara tabbatar da gaskiyarsa. Ta yaya irin waɗannan za su cancanci shiriya? Allah ba ya shiryar da waɗanda suka zalunci kawunansu, ta hanyar barin gaskiya bayan sun fahince ta, suka kama ƙarya bayan sun gane ƙarya ce a fili. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗi uƙubar waɗannan azzaluman a duniya da lahira, wadda ita ce la’anar Allah da mala’iku da duk halittun Allah a kansu, kuma za su ci gaba da zama cikin wannan la’anar, da wannan uƙubar, har abada, kuma ba za a taɓa sassauta musu azaba ba, kuma ba za a saurara musu ba. Amma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi togaciya ta waɗanda suka tuba, suka yi ayyuka na ƙwarai, kuma suka gyara kurakuren da suka yi; to waɗannan Allah yana yafe musu, saboda shi mai yawan gafara ne, mai yawan jin ƙai ga bayinsa masu tuba su gyara. Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Wani mutumin Madina ya musulunta, daga baya kuma sai ya yi ridda, ya koma shirka. Sannan ya dawo ya yi nadama, sai ya aika wa mutanensa yana cewa: ‘Ku tambayar mini Manzon Allah (ﷺ), shin zan iya sake tuba?’ Mutanensa suka sami Manzon Allah (ﷺ), suka faɗa masa cewa: ‘Wane da ya yi ridda ya yi nadama, kuma ya aiko mu mu tambaya masa cewa, shin zai iya sake tuba?” Sai wannan ayar ta sauka: ‘Ta yaya Allah zai shiryar da mutanen da suka kafirta bayan imaninsu...’ har inda ya ce: ‘...to lalle Allah mai gafara ne, mai jin ƙai.’ Sai Annabi (ﷺ) ya aika masa ya zo ya sake shiga Musulunci.” [Nasa’i #4068, da Ahmad #2218].

  90. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَعۡدَ إِيمَٰنِهِمۡ ثُمَّ ٱزۡدَادُواْ كُفۡرٗا لَّن تُقۡبَلَ تَوۡبَتُهُمۡ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلضَّآلُّونَ 

    Open ayah 3:90

    Lalle waɗanda suka kafirta bayan imaninsu, sannan suka ƙara zurfi cikin kafirci, to ba za a karɓi tubansu ba, kuma waɗannan su ne ɓatattu.

  91. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَمَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٞ فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡ أَحَدِهِم مِّلۡءُ ٱلۡأَرۡضِ ذَهَبٗا وَلَوِ ٱفۡتَدَىٰ بِهِۦٓۗ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ وَمَا لَهُم مِّن نَّٰصِرِينَ

    Open ayah 3:91

    Lalle waɗanda suka kafirta, kuma suka mutu alhali suna kafirai, to ba za a karɓi cikin ƙasa na zinari daga ɗaya daga cikinsu ba, ko da zai fanshi kansa da shi. Waɗannan suna da wata azaba mai raɗaɗi kuma ba su da wasu mataimaka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin uƙubar waɗanda suka yi imani, sannan daga baya suka yi ridda, suka kafirta, sannan suka yi ta ƙara nutsawa cikin kafirci, suka kuma zauna a haka, har suka mutu cewa, Allah ba zai taɓa karɓar tubansu ba, domin su ne suka zaɓi su bar hanyar gaskiya, su bi hanyar ɓata. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da cewa, waɗanda suka kafirta, kuma suka mutu a kan kafirci, ba su tuba ba; to Allah ba zai karɓi aikin da suka yi ba, ko da kuwa zai yi sadaka da kwatankwacin cikin ƙasa na zinariya domin ya kusanci Allah da wannan sadakar, Allah ba zai karɓa ba, ko kuma ya ce zai fanshi kansa da wannan, to Allah ba zai karɓa ba. Sakamakon waɗannan a lahira shi ne azabar wuta mai raɗaɗi, kuma babu wanda ya isa ya kuɓutar da su daga wannan azabar.

  92. لَن تَنَالُواْ ٱلۡبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُواْ مِمَّا تُحِبُّونَۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِن شَيۡءٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٞ

    Open ayah 3:92

    Ba za ku taɓa dacewa da aiki na alheri ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so, kuma abin da duk kuka ciyar kowane iri ne, to lalle Allah Yana sane da shi. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) a ayar baya ya yi bayanin cewa, ba zai karɓi sadakar kafiri ba, ko da zai ciyar da kwatankwacin cikin duniya na zinari, don ya kuɓutar da kansa daga azabar Allah a ranar alƙiyama, sai a wannan ayar Allah yake kwaɗaitar da muminai kan su ciyar da dukiyarsu, kuma ya bayyana cewa, abin da ya fi son bawa ya yi sadaka da shi, shi ne abin da shi ya fi so; wannan ne zai kai shi matakin samun alheri mai yawa. Allah yana cewa: “Ba za ku kai ga samun alheri mai yawa ba daga Allah, har sai kun yi sadaka da dukiyar da kuke ƙauna a zukatanku. Duk abin da kuka ciyar na dukiyarku; to Allah ya sani, kuma a ranar lahira zai saka wa wanda ya yi haka da cikakken sakamako.” An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Abu Ɗalha mutumin Madina ne mai yawan dukiya; abin da kuma ya fi ƙauna cikin dukiyarsa ita ce gonarsa mai suna Bairuha , tana kallon masallacin Annabi (ﷺ). Hasali ma Annabi (ﷺ) yakan shiga cikinta ya sha ruwanta mai daɗi. To lokacin da wannan ayar ta sauka, sai Abu Ɗalha ya ce: ‘Ya Manzon Allah, Allah yana cewa: ‘Ba za ku taɓa dacewa da aiki na alheri ba, har sai kun ciyar daga abin da kuke so...’, ni kuma a cikin dukiyata na fi son Bairuha , don haka na bayar da ita sadaka don Allah, ina fatan samun alherinta da ajiyayyen ladanta a wurin Allah Ta’ala, don haka ya Ma’aikin Allah, ka saka ta inda Allah Ta’ala ya nuna maka.’ Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Taɓdi! Wannan fa dukiya ce mai riba, wannan dukiya ce mai riba; to lalle na ji abin da ka ce, amma ni ina ganin ka yi kyautar ta ga danginka mafi kusanci da kai shi ya fi riba.” Sai Abu Ɗalha ya ce: ‘Zan yi hakan, ya Ma’aikin Allah.’ Sai Abu Ɗalha ya raba wa danginsa da ‘ya’yan baffanninsa wannan gonar.” [Bukhari #2769, da Muslim #998, da Ahmad #12461].

  93. ۞كُلُّ ٱلطَّعَامِ كَانَ حِلّٗا لِّبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ إِلَّا مَا حَرَّمَ إِسۡرَٰٓءِيلُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ مِن قَبۡلِ أَن تُنَزَّلَ ٱلتَّوۡرَىٰةُۚ قُلۡ فَأۡتُواْ بِٱلتَّوۡرَىٰةِ فَٱتۡلُوهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 3:93

    Duk wani abinci ya kasance halal ne ga Banu Israila sai abin da shi Isra’ilu ya haramta wa kansa tun kafin a saukar da Attaura. Ka ce: “To ku zo da Attaura, sai ku karanta ta in kun kasance masu gaskiya.”

  94. فَمَنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ

    Open ayah 3:94

    To duk wanda ya ƙirƙiri ƙarya ya jingina wa Allah bayan wannan, to waɗannan su ne azzalumai. Allah (Mai tsarki da daukaka) a waɗannan ayoyi yana ba da labarin cewa, kafin a saukar da Attaura ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), duk wani nau’i na abinci halal ne ga Banu Isra’ila su ci, sai nau’i guda ɗaya wanda shi Isra’ilu, wato Annabi Ya’aƙubu ya haramta wa kansa, ba Allah ne ya haramta masa ba, sannan daga baya ‘ya’yansa su ma suka yi koyi da shi, suka haramta wa kawunansu cin wannan nau’i na abinci. Wannan kuwa shi ne naman raƙuma da nononsu. To bayan saukar da Attaura, sai Allah ya haramta musu abin da ya ga dama a cikinta, ya kuma halatta musu abin da ya ga dama. Don haka wannan hukuncin ya shafe wancan hukunci na halatta musu komai, sai raƙuma da nononsu. Sai Allah Ta’ala ya umarci Annabinsa da ya nemi Yahudawa su ɗauko littafin Attaura su karanta idan abin da suke faɗa gaskiya ne, wanda kuma ba za su gan shi ba. To bayan Allah ya tsayar musu da hujja, sai ya faɗa musu cewa, duk wanda ya kuskura ya yi masa ƙarya bayan wannan bayanin da suka ji; to waɗannan su ne azzalumai. Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: Wata ƙungiyar Yahudawa sun je gaban Annabi (ﷺ) suka ce: “Ya Baban Alƙasim, za mu tambaye ka wasu abubuwa, ka ba mu amsarsu, domin babu wanda ya san su sai annabi.” Daga cikin abin da suka tambaye shi, sun ce: “Wane abinci ne Isra’ilu (Ya’aƙubu) ya haramta wa kansa tun kafin a saukar da Attaura?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Na haɗa ku da Allah, shin kun san cewa, Isra’ilu (Annabi Ya’aƙubu) ya daɗe yana rashin lafiya mai tsanani, sai ya yi bakance na cewa, idan Allah ya ba shi lafiya to zai haramta wa kansa abin shan da ya fi so da abincin da ya fi so, kuma abincin da ya fi so shi ne naman raƙuma, abin shan da ya fi so kuma shi ne nononsu?” Sai Yahudawan nan suka ce: “Gaskiya ne, haka ne.” [Ahmad #2471, da Tafsirin Tabari #7420, da Almu’ujamul Kabir 12:246 #13012].

  95. قُلۡ صَدَقَ ٱللَّهُۗ فَٱتَّبِعُواْ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

    Open ayah 3:95

    Ka ce: “Allah Ya yi gaskiya. Don haka ku bi addinin Ibrahimu, mai karkace wa ɓarna, kuma bai taɓa zama ɗaya daga cikin mushirikai ba.”

  96. إِنَّ أَوَّلَ بَيۡتٖ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكٗا وَهُدٗى لِّلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 3:96

    Lalle farkon ɗaki da aka tanada don mutane (su yi ibada a cikinsa) shi ne wanda yake cikin Bakka, (ɗaki ne) mai albarka, kuma shiriya ne ga talikai.

  97. فِيهِ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ مَّقَامُ إِبۡرَٰهِيمَۖ وَمَن دَخَلَهُۥ كَانَ ءَامِنٗاۗ وَلِلَّهِ عَلَى ٱلنَّاسِ حِجُّ ٱلۡبَيۡتِ مَنِ ٱسۡتَطَاعَ إِلَيۡهِ سَبِيلٗاۚ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 3:97

    A cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, (kuma akwai) Maƙamu Ibrahimu; wanda duk ya shige shi ya zama amintacce. Kuma Allah Ya wajabta wa mutane ziyarar wannan ɗakin ga wanda ya sami iko. Wanda kuwa ya kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin talikai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya ce wa Yahudawa, duk abin da Allah ya labarta ko ya shar’anta na hukunci; to gaskiya ne, kamar abin da ya faɗa musu cewa, babu wani abin da Allah ya haramta musu kafin saukar da Attaura, sai nau’i biyu, watau naman raƙumi da nononsa. Don haka su zo su bi addinin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), idan har su masu gaskiya ne game da tutiyar su ta cewa su jikokinsa ne; domin shi mai kaɗaita Allah ne, ba ya shirka, ba ya kuma tare da masu yin ta. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, farkon ɗakin da aka gina shi domin mutane su bauta masa a cikinsa, kuma su yi ɗawafi su yi salla, su yi i’itikafi shi ne Ɗakin Ka’aba. Ɗakin Allah ne mai alfarma da ke garin Makka, mai ɗimbin albarka da abubuwan amfani masu yawa, na addini da na rayuwa, kamar riɓanyar lada a wurinsa da kuma arziki mai ɗimbin yawa da Allah ya kawo a garin, kuma shiriya ne ga ɗaukacin talikai, musamman zamantowarsa alƙibla ga Musulmi baki ɗaya lokutan sallolinsu. Kuma shi ne wurin hajjinsu da umararsu. To amma Yahudawa da Nasara masu tutiyar su ne a kan addinin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai ga shi ba sa zuwa Ɗakin da ya gina domin aikin hajji da umara, wanda hakan yake nuna sun yi hannun riga da shi, ba su ba addininsa. An karɓo daga Abu Zarri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: “Wane masallaci aka fara ginawa a bayan ƙasa?” Sai ya ce: “Masallaci mai alfarma.” Sai na ce: “Sai kuma wanne?” Sai ya ce: “Masallacin Ƙudus.” Sai na ce: “Shekaru nawa ne a tsakaninsu?” Sai ya ce: “Shekaru arba’in. Sannan duk inda salla ta kama ka bayan haka; to ka fuskance shi a sallarka, a nan falalar take.” [Bukhari #3366, da Muslim #520]. A cikin wannan Ɗakin akwai dalilai bayyanannu masu nuna kaɗaitakar Allah (Mai tsarki da daukaka) da hikimarsa da adalcinsa da girman Ƙudirarsa da sauran siffofinsa maɗaukaka, da kuma wasu alamomi masu nuna girman darajar wannan Ɗakin, daga cikinsu har da wuraren da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tsaya domin aikin hajji, kuma duk wanda ya shiga cikinsa; to ya aminta daga duk wani abin ƙi. Allah ya farlanta zuwa wannan Ɗaki domin gabatar da aikin hajji ga duk wanda Allah ya ba shi iko, na lafiya da guziri da abin hawa. Amma duk wanda ya ƙaryata hajji ko ya bijire, to ya sani Allah mawadaci ne, ba ya buƙatar hajjinsa, ba ya ma da buƙata a wurin dukkan talikai.

  98. قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَٱللَّهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 3:98

    Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke kafirce wa ayoyin Allah, kuma alhalin Allah Mai ba da shaida ne ga abin da kuke aikatawa?”

  99. قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ مَنۡ ءَامَنَ تَبۡغُونَهَا عِوَجٗا وَأَنتُمۡ شُهَدَآءُۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 3:99

    Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke kange wanda ya yi imani daga hanyar Allah, kuna son ta zamo karkatacciya, kuma alhali ku da kanku masu shaida ne, kuma Allah ba gafalalle ne game da abin da kuke aikatawa ba?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabinsa (ﷺ) da ya tambayi Yahudawa da Nasara, me ya sa suke musanta hujjojin da Allah ya saukar da su a littattafansu masu ɗauke da tabbatar da gaskiyar annabcin Annabi (ﷺ) da gaskiyar abin da ya zo da shi, tare da sun san cewa babu wani aikinsu da zai ɓuya a wurin Allah? Allah yana ganin duk irin ayyukan da suke yi. Kuma ya umarce shi da ya ƙara tambayar Yahudawa, me ya sa suke ƙoƙarin ɓatar da muminai daga kan hanyar Allah, suke kuma ƙoƙarin su ga wannan hanyar ta gaskiya ta karkace, alhalin sun san gaskiyar, kuma sun san munin abin da suke aikatawa? To su sani Allah ba rafkananne ne game da abin da suke aikatawa ba, yana sane da komai, kuma duk zai yi musu hisabi a kai ranar alƙiyama.

  100. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تُطِيعُواْ فَرِيقٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ يَرُدُّوكُم بَعۡدَ إِيمَٰنِكُمۡ كَٰفِرِينَ 

    Open ayah 3:100

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka bi wani ɓangare na waɗanda aka ba wa Littafi, to za su mayar da ku kafirai bayan imaninku.

  101. وَكَيۡفَ تَكۡفُرُونَ وَأَنتُمۡ تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ وَفِيكُمۡ رَسُولُهُۥۗ وَمَن يَعۡتَصِم بِٱللَّهِ فَقَدۡ هُدِيَ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ 

    Open ayah 3:101

    Ta yaya kuma za ku kafirce, ga shi kuwa ana karanta muku ayoyin Allah, kuma Manzonsa yana tare da ku? Duk kuwa wanda ya riƙi Allah, to haƙiƙa an shiryar da shi tafarki madaidaici. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana gargaɗin muminai da cewa, idan suka kuskura suka nuna biyayyarsu ga Yahudawa da Nasara, waɗanda suke yi musu hassadar Alƙur’ani da Allah ya ba su da falalar Musulunci; to tabbas za su raba su da imaninsu, su mayar da su kafirai suna ji suna gani. Amma Allah ya nuna cewa, da wahala ƙwarai muminai su yarda su koma kafirci bayan ga Alƙur’ani nan kullum suna ji ana karanta musu ayoyinsa, sannan ga Manzon Allah nan a tsakaninsu, yana isar musu duk wani saƙo da aka saukar dominsu. Shi imani idan har ya ratsa ƙoƙon zuciya; to abu ne mai wuyar gaske a iya cire shi, sai dai wani iko na Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu wata hanya wadda idan suka bi ta, za su tsare kawunansu daga faɗawa ramin kafirci. Wannan hanya ita ce, riƙe Allah da dogaro da shi, domin shi ne madogara ta samun shiriya. Duk wanda ya koma ga Allah a cikin kowanne hali nasa, ya nemi mafaka a wurinsa, ya dogara da shi dogaro na gaskiya, ya riƙe addininsa; to haƙiƙa wannan an shiryar da shi ga hanya miƙaƙƙiya ɗoɗar, wadda babu karkata ko kaɗan a cikinta, ita ce za ta yi masa jagoranci har ta kai shi gidan Aljanna.

  102. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِۦ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ 

    Open ayah 3:102

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi taƙawa ga Allah haƙiƙanin taƙawa, kuma lalle kada ku mutu face kuna Musulmi.

  103. وَٱعۡتَصِمُواْ بِحَبۡلِ ٱللَّهِ جَمِيعٗا وَلَا تَفَرَّقُواْۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ كُنتُمۡ أَعۡدَآءٗ فَأَلَّفَ بَيۡنَ قُلُوبِكُمۡ فَأَصۡبَحۡتُم بِنِعۡمَتِهِۦٓ إِخۡوَٰنٗا وَكُنتُمۡ عَلَىٰ شَفَا حُفۡرَةٖ مِّنَ ٱلنَّارِ فَأَنقَذَكُم مِّنۡهَاۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ 

    Open ayah 3:103

    Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni\'imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya haɗa tsakanin zukatanku, sai kuka zamo \'yan’uwan juna a sakamakon ni\'imarsa, a da kuma kun kasance a kan gaɓar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ku shiriya.

  104. وَلۡتَكُن مِّنكُمۡ أُمَّةٞ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلۡخَيۡرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ 

    Open ayah 3:104

    A cikinku lalle a sami wata al\'umma waɗanda suke kira zuwa ga alheri, kuma suke umarni da kyakkyawa, kuma suke hana mummuna. Waɗannan su ne masu rabauta.

  105. وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱخۡتَلَفُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ 

    Open ayah 3:105

    Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu, kuma suka sassaɓa bayan hujjoji sun zo musu. Waɗannan kuwa suna da azaba mai girma.

  106. يَوۡمَ تَبۡيَضُّ وُجُوهٞ وَتَسۡوَدُّ وُجُوهٞۚ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱسۡوَدَّتۡ وُجُوهُهُمۡ أَكَفَرۡتُم بَعۡدَ إِيمَٰنِكُمۡ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ 

    Open ayah 3:106

    Ranar da waɗansu fuskoki za su yi fari, waɗansu fuskokin kuma za su yi baƙi. Amma waɗanda fuskokinsu suka yi baƙi, (za a ce da su): “Shin ku ne kuka kafirce bayan imaninku? To ku ɗanɗani azaba, saboda kafircin da kuka kasance kuna yi.”

  107. وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱبۡيَضَّتۡ وُجُوهُهُمۡ فَفِي رَحۡمَةِ ٱللَّهِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ 

    Open ayah 3:107

    Amma waɗanda fuskokinsu suka yi fari kuwa, to suna cikin rahamar Allah, suna masu dawwama a cikinta.

  108. تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۗ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلۡمٗا لِّلۡعَٰلَمِينَ 

    Open ayah 3:108

    Waɗannan ayoyin Allah ne Muke karanta maka su da gaskiya. Kuma Allah ba Ya nufin zalunci ga talikai.

  109. وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ 

    Open ayah 3:109

    Kuma duk abin da yake cikin sammai da ƙasa na Allah ne. Kuma zuwa ga Allah ne ake mayar da duk al’amura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar bayinsa muminai da su kiyaye dokokinsa gwargwadon ikonsu, sannan su ci gaba da riƙe wannan addini ƙam-ƙam har mutuwa ta zo musu. Kuma lalle su haɗa kansu, su zama abu guda a kan gaskiya, su taru su riƙe igiyar Allah, wadda ita ce Alƙur’anin da Manzo ya zo musu da shi da sunnarsa; kada su yarda su rarrabu. An karɓo daga Abu Huraira ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ya yarje muku abubuwa uku, kuma ya ƙi muku abubuwa uku. Ya yarje muku da ku bauta masa, kuma kada ku haɗa komai da shi, kuma duk ilahirinku ku yi riƙo da igiyar Allah, kada ku rarrabu, kuma ya ƙi muku bin jita-jita da yawan tambaya da ɓarnata dukiya.” [Muslim #1715]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su tuna ni’imarsa da ya yi musu lokacin da suka haɗu a kan Musulunci, suka zama ‘yan’uwan juna, bayan a da kafin zuwan Musulunci a rarrabe suke, suna gaba da faɗa da junansu a kan abin da bai taka kara ya karya ba, sai ga shi Allah ya haɗa zukatansu gaba ɗaya sun zama ‘yan’uwa masu ƙaunar junansu, kamar yadda ya bayyana hakan a Suratul Anfali , aya ta 62-63. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da su cewa, suna dab da faɗawa ramin wuta, sai Allah ya ceto su, domin babu abin da ya rage musu su faɗa cikinta sai mutuwa idan har suna cikin wannan hali na kafirci. To kamar irin wannan bayani da ya yi musu filla-filla har suka fahimta; to haka yake fayyace musu sauran ayoyin nasa, don su zame musu fitilar gane hanyar shiriya da gaskiya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da cewa, lalle a sami wata ƙungiya daga cikinsu, waɗanda za su ɗauki nauyin yin umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna a cikin al’umma; wannan shi ne maganin rabuwar kai a tsakaninsu. Domin duk al’ummar da take rayuwa kara-zube, kowa yana yin abin da ya ga dama, babu mai tsawata masa yayin da ya yi ba daidai ba, to wannan al’umma za ta rasa haɗuwar kai a tsakanin ‘ya’yanta, domin soye-soyen zukatan mutane mabambanta ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suka siffantu da sifar nan ta umarni da kyakkyawan abu, da hana mummuna, su ne masu samun babban rabo a duniya da lahira. An karɓo daga Huzaifa ɗan Alyaman (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunsa, Wallahi, ko dai ku yi umarni da kyakkyawan aiki, ku hana mummuna, ko kuma ba da daɗewa ba Allah ya aiko muku da wata uƙuba daga gare shi, ku yi ta addu’a ya ƙi amsa muku!” [Ahmad #23349, da Tirmizi #2169]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai rarrabuwa, kamar yadda Yahudu da Nasara a gabaninsu suka rarraba a addininsu, bayan hujjoji bayyanannu sun zo musu. To waɗannan suna da wata babbar azaba daga Allah, a ranar da fuskokin ‘yan Aljanna za su yi fari, fuskokin ‘yan wuta kuma su yi baƙi. Sai cikin zargi a ce wa masu baƙaƙen fuskoki: “Shin ku ne kuka kafirce bayan imaninku? To ku ɗanɗani azaba saboda kafircinku.” Amma masu fararen fuskoki, za su kasance ne a cikin rahamar Allah, tare da jin daɗin da Allah ya tanadar musu a Aljanna na ni’imomi masu yawa, za su ci gaba da rayuwa a cikinsu har abada. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Annabinsa (ﷺ) cewa; waɗancan ayoyi da ya karanta masa su ne gaskiya, kuma tabbas Allah ba wanda yake zalunta cikin halittunsa. Duk abubuwan da suke cikin sammai, da waɗanda suke ƙasa na Allah ne shi kaɗai, kuma duk al’amura gaba ɗaya gare shi za a mayar da su ranar alƙiyama, domin ya saka wa kowa aikin da ya yi; idan ya aikata alheri, ya ga alheri, idan kuwa sharri ya aikata, to ya ga sharri.

  110. كُنتُمۡ خَيۡرَ أُمَّةٍ أُخۡرِجَتۡ لِلنَّاسِ تَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَتَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَتُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِۗ وَلَوۡ ءَامَنَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۚ مِّنۡهُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَأَكۡثَرُهُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ 

    Open ayah 3:110

    Ku ne mafi alherin al\'umma waɗanda aka fitar ga mutane, kuna umarni da kyakkyawan aiki, kuma kuna hana mummuna, kuma kuna yin imani da Allah. Da a ce kuwa Ma’abota Littafi za su yi imani da ya fi alheri a gare su. A cikinsu akwai muminai, amma mafiya yawansu fasiƙai ne.

  111. لَن يَضُرُّوكُمۡ إِلَّآ أَذٗىۖ وَإِن يُقَٰتِلُوكُمۡ يُوَلُّوكُمُ ٱلۡأَدۡبَارَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ

    Open ayah 3:111

    Ba za su taɓa iya cutar da ku ba sai dai cutarwa kaɗan; kuma in da za su yaƙe ku, sai sun juya muku baya, sannan ba za a taimake su ba.

  112. ضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ أَيۡنَ مَا ثُقِفُوٓاْ إِلَّا بِحَبۡلٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَحَبۡلٖ مِّنَ ٱلنَّاسِ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَسۡكَنَةُۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

    Open ayah 3:112

    An haɗa su da ƙasƙanci a duk inda aka same su, sai dai waɗanda suke riƙe da wani alƙawari daga Allah ko wani alƙawari daga mutane, kuma sun dawo da wani fushi daga Allah, kuma an haɗa su da talauci. Hakan kuwa saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haƙƙi ba, hakan yana faruwa ne saboda saɓo da suka yi, kuma sun kasance suna ƙetare iyaka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana magana da waɗannan al’umma. Farkon waɗanda suka shiga cikin wannan kiran, su ne sahabban Annabi, domin su ne farkon waɗanda ayar ta yi magana da su. Wannan matsayi mai girma sun cancance shi ne saboda sun siffantu da yin umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna da kuma imani da Allah (Mai tsarki da daukaka). Wannan ne ya sanya suka tsere wa al’ummomin da suka gabace su. Da a ce Yahudawa da Nasara sun yi imani da Annabi (ﷺ) da abin da ya zo da shi daga Ubangijinsa, to da ya fi musu alheri. Sai dai waɗanda suka yi imani a cikinsu ‘yan kaɗan ne, da dama daga cikinsu sun ci gaba ne da zama a kan kangare wa Allah da Manzonsa (ﷺ). Wannan shi zai hana su ƙaunaci muminai sai dai su yi ta gaba da su da ƙoƙarin cutar da su duk sanda suka sami dama. Amma dai duk yadda suka kai ga nuna musu ƙiyayya da ƙoƙarin cin zarafinsu, ba za su iya ba in banda cutarwa da fatar baki ba. Idan ma da faɗa zai haɗa su da muminai; to ba za su iya taɓuka komai ba sai dai su gudu, kuma ba za a taimaka musu ba, domin kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haɗa su da ƙasƙanci da wulaƙanci a duk inda suke a bayan ƙasa, ba sa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, sai da wani alƙawari daga Allah ko daga mutane. Sannan kuma sun cancanci fushin Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma ga alamun talauci sun bayyana a tare da su. Irin wannan sakamakon ya faru da su ne saboda kafirce wa ayoyin Allah da suke yi, da kuma kashe annabawa ba tare da wani laifi ba, sai don zalunci kawai. Kuma abin da ya kai su ga wannan hali na kafirci da kisa, shi ne saɓon Allah da suke yi da ƙetare iyakokinsa da shari’arsa.

  113. ۞لَيۡسُواْ سَوَآءٗۗ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ أُمَّةٞ قَآئِمَةٞ يَتۡلُونَ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ وَهُمۡ يَسۡجُدُونَ

    Open ayah 3:113

    Ba dukansu ne suka zama ɗaya ba. Cikin Ma’abota Littafi akwai al\'umma tsayayya, suna karanta Littafin Allah a cikin dare alhalin suna sujada.

  114. يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

    Open ayah 3:114

    Suna yin imani da Allah da ranar ƙarshe, kuma suna umarni da kyakkyawan aiki, kuma suna hana mummuna, kuma suna hanzari wajen ayyukan alheri, waɗannan kuwa suna cikin salihan bayi.

  115. وَمَا يَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلَن يُكۡفَرُوهُۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 3:115

    Kuma duk abin da suka aikata na alheri, to ba za a hana musu ladansa ba. Kuma Allah Yana sane da masu taƙawa. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci ƙungiyar fasiƙai daga Ma’abota Littafi, sai kuma a waɗannan ayoyi ya bayyana cewa, ba dukkansu suka taru suka zama ɗaya ba; a cikinsu akwai mutanen kirki, waɗanda Allah ya shirye su suka musulunta, suka riƙe gaskiya, suna kuma karanta littafin Allah a cikin sallolinsu na dare, kuma suna yin imani da Allah da ranar lahira. Kuma ba su tsaya ga gyara zukatansu su kaɗai ba; suna yin nasu ƙoƙarin su gyara wasu ta hanyar umartar su da kyawawan ayyuka da hana su aikata munana suna kuma gaggawa wajen aikata ayyukan alheri. Irin waɗannan mutane su ne mutanen kirki salihai, kuma duk wani aikin alheri da za su yi ba za a haramta musu ladansa ba a wajen Allah. Allah kuma ya san masu taƙawa, yana ganin ayyukansu, kuma zai yi musu kyakkyawan sakamako a lahira.

  116. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَن تُغۡنِيَ عَنۡهُمۡ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗاۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

    Open ayah 3:116

    Lalle waɗanda suka kafirta, dukiyoyinsu da ‘ya’yansu ba za su wadatar da su komai ba a wurin Allah; kuma waɗannan su ne ma’abota wuta; suna masu dawwama a cikinta.

  117. مَثَلُ مَا يُنفِقُونَ فِي هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَثَلِ رِيحٖ فِيهَا صِرٌّ أَصَابَتۡ حَرۡثَ قَوۡمٖ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَأَهۡلَكَتۡهُۚ وَمَا ظَلَمَهُمُ ٱللَّهُ وَلَٰكِنۡ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

    Open ayah 3:117

    Misalin abin da suke ciyarwa a wannan rayuwa ta duniya kamar misalin iska ce mai tsananin sanyi, wadda ta auka kan shukar waɗansu mutanen da suka zalunci kawunansu, sai ta lalata ta. Kuma Allah bai zalunce su ba, sai dai kawunansu suke zalunta. Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci siffofin waɗanda suka yi imani daga cikin kafirai, sai kuma a waɗancan ayoyi Allah ya bayyana siffofin kafirai da azabar da ya tanada musu a ranar Alƙiyama, domin a gane bambancin da ke tsakanin mumini da kafiri. Allah ya bayyana cewa yawan dukiya da `ya`ya da kafirai suke taƙama da shi a duniya, a wurin Allah ba zai wadatar da su komai ba, domin ba zai kare su daga azabar Allah ba; za a jefa su wutar Jahannama ne, su dawwama a cikinta har abada. Kuma dukiyar da kafirai suke ta ɓatarwa a nan duniya, da nufin yaƙar gaskiya da masu kira zuwa gareta, za su kashe ta ne a banza, domin ba za su taɓa cin nasara ba. Domin misalin wannan ta’asar da suke yi ta yi kama ne da wanda ya yi shuka, yana fatan samun amfaninta, sai wata guguwa mai ƙarfi da sanyi ta taso ta halaka shukar gaba ɗaya, bai tsira da komai ba daga amfaninta, kamar yadda Allah ya bayyana a Suratu Anfali , aya ta 36. Kuma wannan sakamako da Allah ya yi wa kafirai bai zalunce su da komai ba, su ne suka zalunci kawunansu ta hanyar kafirci da fafutukar sai sun bice hasken Allah.

  118. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ بِطَانَةٗ مِّن دُونِكُمۡ لَا يَأۡلُونَكُمۡ خَبَالٗا وَدُّواْ مَا عَنِتُّمۡ قَدۡ بَدَتِ ٱلۡبَغۡضَآءُ مِنۡ أَفۡوَٰهِهِمۡ وَمَا تُخۡفِي صُدُورُهُمۡ أَكۡبَرُۚ قَدۡ بَيَّنَّا لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡقِلُونَ

    Open ayah 3:118

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi abokanan shawara waɗanda ba a cikinku suke ba, ba za su sassauta muku mugunta ba, sun yi burin duk abin da zai ƙuntata muku, haƙiƙa ƙiyayya ta bayyana daga bakunansu; amma abin da zukatansu suke ɓoyewa ya fi girma. Haƙiƙa Mun bayyana muku ayoyi; in kun kasance kuna hankalta.

  119. هَٰٓأَنتُمۡ أُوْلَآءِ تُحِبُّونَهُمۡ وَلَا يُحِبُّونَكُمۡ وَتُؤۡمِنُونَ بِٱلۡكِتَٰبِ كُلِّهِۦ وَإِذَا لَقُوكُمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَوۡاْ عَضُّواْ عَلَيۡكُمُ ٱلۡأَنَامِلَ مِنَ ٱلۡغَيۡظِۚ قُلۡ مُوتُواْ بِغَيۡظِكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

    Open ayah 3:119

    Sai ga shi ku ɗinnan kuna son su, su kuwa ba sa son ku, kuma ku kuna yin imani da Littattafai gaba ɗayansu, kuma idan sun gamu da ku, sai su ce: “Mun yi imani.” Idan kuma sun keɓanta, sai su riƙa cizon ‘yan yatsu a kanku saboda baƙin ciki. Ka ce: “Sai dai ku mutu da baƙin cikinku.” Lalle Allah Masanin abin da yake cikin ƙiraza ne.

  120. إِن تَمۡسَسۡكُمۡ حَسَنَةٞ تَسُؤۡهُمۡ وَإِن تُصِبۡكُمۡ سَيِّئَةٞ يَفۡرَحُواْ بِهَاۖ وَإِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ لَا يَضُرُّكُمۡ كَيۡدُهُمۡ شَيۡـًٔاۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطٞ 

    Open ayah 3:120

    Idan wani kyakkyawan abu ya same ku sai ya baƙanta musu rai, amma idan wani mummunan abu ya same ku, sai su riƙa farin ciki da shi; amma idan kuwa kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, makircinsu ba zai cutar da ku komai ba. Lalle Allah Yana kewaye da sanin abin da suke aikatawa. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama bayani a kan halayen muminai da na kafirai, sai kuma a waɗannan ayoyi yake gargaɗin muminai da kada su ɗauki kafirai abokan shawararsu, watau su janyo su kusa da su, suna nuna musu asirinsu, su bar ‘yan’uwansu muminai domin waɗannan kafiran bai kamata a amince musu ba; duk sa’adda suka sami wata dama ta cutar da muminai; to sai sun yi amfani da ita. Kullum kuma suna jiran su ga muminai sun faɗa cikin wata wahala su kuma su samu abin yi musu dariya. Saboda tsananin ƙiyayyarsu ga muminai, har ta kai ba za su iya ɓoye ƙiyayyar a zuciyarsu ba, sai su riƙa suɓutar baki suna fito da ita a fili, duk da haka kuma ƙiyayyar da ke cikin zukatansu ta fi girma fiye da wadda bakunansu suka furta har muminai suka ji. Allah ya bayyana ayoyinsa ga muminai a fili, kuma bayanin zai amfane su har idan sun saurare shi, sun kuma fahimce shi. An karɓo daga Abu Sa’id Alkhudiri (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce: “Babu wani annabi da Allah ya taɓa aiko shi, ko wani halifa da Allah ya ba shi halifanci, face yana da kashi biyu na masu ba shi shawara; kashin farko suna umartar sa da kyakkyawan aiki, suna kwaɗaitar da shi a kai; kashi na biyu kuwa suna umartarsa da sharri, kuma suna kwaɗaitar da shi a kan aikata shi. To tsararre shi ne wanda Allah ya tsare.” [Bukhari #7198]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani abu da ya wajaba muminai su yi hattara da shi dangane da sha’anin kafirai da munafuƙai; wannan abu kuwa shi ne saboda tsananin ƙiyayya da hassadar da ke cikin zukatansu ga muminai, ba za su taɓa jin suna son su a zukatansu ba. Su muminai kam suna nuna suna ƙaunar su su kuma kafirai ba sa son su, ba sa kuma ƙaunar su; tsakaninsu da su ƙiyayya ce kawai. Kamar yadda muminai suka yi imani da duk littattafan da Allah ya saukar wa annabawa, amma su kafirai na Yahudu da Nasara sun ƙi yin imani da abin da aka saukar ga Annabi (ﷺ), bayan kuma sun jirkita nasu littattafan. To duk wanda irin wannan ne halinsa; to kamata ya yi a ƙi shi, ba a so shi ba. Ba a nan halinsu ya tsaya ba; yana daga cikin miyagun halayensu na munafirci, duk sa’adda za su haɗu da muminai sai su riƙa nuna musu sun yi imani, amma kuma da zarar sun ware, sun kaɗaita da junansu, sai su riƙa cizon ‘yan yatsunsu, saboda tsananin baƙin ciki da haushin muminai, domin suna ganin irin haɗin kan muminai da ƙaunar da ke tsakaninsu. Sai Allah ya umarci Annabinsa (ﷺ) ya gaya musu: “Sai dai ku mutu da baƙin cikinku,” domin Allah ya yi alƙawarin sai ya cika wannan ni’imar tasa, ya ɗaukaka addininsa ko ba sa so, sai dai baƙin ciki ya kashe su. Allah kuma yana sane da abin da yake ɓoye a cikin ƙirazan bayinsa, don haka zai yi wa kowa sakayya a kan abin da ya aikata. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da yake ƙara tsananin gabar kafiran ga muminai, watau duk lokacin da wani abin farin ciki ya sami muminai, sai su riƙa jin haushi, suna damuwa; yayin da kuma wani abin baƙin ciki ya same su, sai su riƙa murna, suna jin daɗi. Sai Allah ya koyar da muminai abin da zai taimaka musu wajen jure irin wannan hali na kafirai, watau su zama masu haƙuri, kuma masu taƙawa, domin idan har sun rungumi waɗannan siffofi guda biyu, to babu wani makirci da zai cutar da su. Allah yana kewaye da saninsa game da abin da waɗannan kafiran da munafuƙan suke yi, kuma zai saka musu a kan hakan.

  121. وَإِذۡ غَدَوۡتَ مِنۡ أَهۡلِكَ تُبَوِّئُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ مَقَٰعِدَ لِلۡقِتَالِۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

    Open ayah 3:121

    Kuma ka tuna lokacin da ka yi sammako daga wajen iyalinka, ka je kana shirya wa muminai wuraren tsayuwarsu don yaƙi. Allah kuwa Mai ji ne, Masani.

  122. إِذۡ هَمَّت طَّآئِفَتَانِ مِنكُمۡ أَن تَفۡشَلَا وَٱللَّهُ وَلِيُّهُمَاۗ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 3:122

    Tuna lokacin da waɗansu ƙungiyoyi guda biyu daga cikinku suka yi niyyar su ja da baya, amma Allah ne Majiɓincin lamarinsu. Sai muminai su dogara ga Allah kaɗai.

  123. وَلَقَدۡ نَصَرَكُمُ ٱللَّهُ بِبَدۡرٖ وَأَنتُمۡ أَذِلَّةٞۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

    Open ayah 3:123

    Kuma tabbas haƙiƙa Allah Ya taimake ku a (yaƙin) Badar, alhalin kuna raunana, to ku ji tsoron Allah don ku zamanto masu godiya a gare Shi.

  124. إِذۡ تَقُولُ لِلۡمُؤۡمِنِينَ أَلَن يَكۡفِيَكُمۡ أَن يُمِدَّكُمۡ رَبُّكُم بِثَلَٰثَةِ ءَالَٰفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ مُنزَلِينَ

    Open ayah 3:124

    Ka tuna lokacin da kake ce wa muminai: “Shin bai ishe ku ba idan Ubangijinku Ya kawo muku agajin mala’iku dubu uku waɗanda za a saukar da su (daga sama)?”

  125. بَلَىٰٓۚ إِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ وَيَأۡتُوكُم مِّن فَوۡرِهِمۡ هَٰذَا يُمۡدِدۡكُمۡ رَبُّكُم بِخَمۡسَةِ ءَالَٰفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ مُسَوِّمِينَ

    Open ayah 3:125

    Haka ne, idan har za ku yi haƙuri, kuma ku yi taƙawa, kuma (kafirai) suka auko muku cikin gaggawa a wannan lokacin, to Ubangijinku zai ƙaro muku agaji da mala’iku dubu biyar masu alamomi.

  126. وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشۡرَىٰ لَكُمۡ وَلِتَطۡمَئِنَّ قُلُوبُكُم بِهِۦۗ وَمَا ٱلنَّصۡرُ إِلَّا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

    Open ayah 3:126

    Kuma Allah bai sanya wannan ba sai don albishir a gare ku, kuma domin zukatanku su nutsu da shi. Kuma nasara ba ta zuwa daga kowa sai daga Allah Mabuwayi, Mai hikima.

  127. لِيَقۡطَعَ طَرَفٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡ يَكۡبِتَهُمۡ فَيَنقَلِبُواْ خَآئِبِينَ

    Open ayah 3:127

    Domin Ya karya lagon wani ɓangare na kafirai ko Ya ƙasƙantar da su, sai su juya da baya suna taɓaɓɓu.

  128. لَيۡسَ لَكَ مِنَ ٱلۡأَمۡرِ شَيۡءٌ أَوۡ يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡ أَوۡ يُعَذِّبَهُمۡ فَإِنَّهُمۡ ظَٰلِمُونَ

    Open ayah 3:128

    Ba ka da komai cikin lamarin, ko dai (Allah) Ya karɓi tubansu, ko Ya yi musu azaba, lalle su dai azzalumai ne.

  129. وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 3:129

    Kuma abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin ƙasa na Allah ne. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, Yana kuma yin azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, haƙuri da taƙawa su ne makamin da mumini zai tsare kansa da shi daga cutarwar maƙiyansa, sai kuma a waɗannan ayoyi Allah ya fito da bayanin abubuwan da kan sabbaba rashin samun nasara a kan maƙiya. Allah yana tunatar da Annabinsa Muhammadu (ﷺ) lokacin da ya fito daga gidansa domin haɗuwa da kafiran Makka a ranar yaƙin Uhudu, lokacin da yake shirya rundunar muminai domin fita yaƙi, yana sanya kowa a muhallin da ya dace da shi. Domin Allah yana jin komai, yana jin shawarar da Annabi (ﷺ) ya yi da sahabbansa a kan wurin da ya kamata a yi wannan yaƙi. Kuma Allah shi ne masani dangane da ra’ayin da ya fi dacewa daga cikin ra’ayoyin da aka kawo a lokacin. Kuma yana sane da irin mugun nufin da kafirai da munafuƙai suka ɓoye a zukatansu, har ma da abin da daukacin halittunsa suka ɓoye a zukatansu. Allah yana tunatar da Annabi (ﷺ) lokacin da wasu ƙungiyoyi biyu daga cikin muminai, suka yi nufin su janye daga wannan yaƙi, su ne ƙabilun Banu Salima da na Banu Harisa, sai dai kuma Allah ya kafe dugadugansu. Allah ya sanar wa Annabi (ﷺ) cewa, gare shi shi kaɗai ya wajaba muminai su dogara. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: A kanmu wannan ayar ta sauka: “Ka tuna lokacin da wasu ƙungiyoyi biyu daga cikinku suka yi nufin su ja da baya, amma Allah ne majiɓincin lamarinsu…” Jabir ya ce: Mu ne ƙungiyoyin biyu, watau ƙabilar Banu Harisa da ƙabilar Banu Salima, kuma saukar da wannan ayar ya faranta mini rai, saboda faɗarsa (Mai tsarki da daukaka): “...amma Allah ne majiɓincin lamarinsu…” [Bukhari #4558]. Allah yana goranta wa muminai nasarar da ya ba su a ranar yaƙin Badar ne a yayin da suke ‘yan kaɗan, masu rauni. Don haka ya dace su ji tsoron sa, su kiyaye dokokinsa, don su gode masa da baiwar da ya yi musu. Sannan ya sake tunatar da Annabinsa Muhammad (ﷺ), lokacin da yake yi wa sahabbansa albishir, yana cewa: “Shin ba zai ishe ku ba, Allah ya kawo muku ɗauki na mala’iku dubu uku, waɗanda zai sauko da su daga sama su taya ku yaƙi?” To hakanan zai kawo muku tallafi na mala’iku dubu biyar, waɗanda suke da alamar jarunta tare da su, idan har kun yi haƙuri, kuma kun yi taƙawa, kuma mushirikai sun ɓullo muku ta inda suka ɓullo cikin gaggawa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, sanar da su da ya yi cewa, zai kawo musu agaji na mala’iku, wani albishir ne yake yi musu, domin su sami nutsuwar zukata. Daga ƙarshe, nasara daga Allah take shi kaɗai, shi ne Mabuwayi, wanda ya fi ƙarfin kowa, kuma mai hikima, zai ba su nasara ya kuma halakar da wasu kafiran, ko ya tozartar da wasu daga cikinsu, ya wulaƙanta su, daga ƙarshe su koma garuruwansu a wulaƙance, ba tare da sun cim ma wata nasara ba. Ko kuma idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ga dama ya shiryar da su su musulunta, ko kuma ya yi musu azaba saboda zaluncinsu. Duk dai al’amuransu gaba ɗaya suna komawa ne ga Allah (Mai tsarki da daukaka), babu komai na al’amarinsu da yake a hannun wannan Annabi (ﷺ). An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An karya wa Annabi (ﷺ) haƙorinsa na gaba ranar yaƙin Uhudu, aka kuma fasa masa kai, sai ya riƙa share jini daga jikinsa yana cewa: “Ta yaya mutanen da suka fasa kan Annabinsu, suka karya masa haƙorinsa na gaba za su rabauta, alhalin yana kiran su zuwa ga Allah?” Sai Allah Ta’ala ya saukar da faɗarsa: “Babu wani al’amari da yake hannunka....” [Muslim #1791]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, shi kaɗai ne mai mulkin duk wani abu da yake sama, da wanda yake ƙasa, yana kuma yafe wa wanda ya ga damar yafe masa daga cikin bayinsa, ya kuma yi uƙuba ga wanda ya ga damar yi masa uƙuba, amma duk da haka shi mai yawan gafara ne, mai yawan rahama.

  130. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُواْ ٱلرِّبَوٰٓاْ أَضۡعَٰفٗا مُّضَٰعَفَةٗۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ 

    Open ayah 3:130

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku ci riba ninki-ba-ninkin, kuma ku kiyaye dokokin Allah don ku rabauta.

  131. وَٱتَّقُواْ ٱلنَّارَ ٱلَّتِيٓ أُعِدَّتۡ لِلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 3:131

    Kuma ku kiyayi wuta wadda aka riga aka yi tanadinta domin kafirai.

  132. وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

    Open ayah 3:132

    Kuma ku bi Allah da Manzo don a ji ƙan ku (a ranar tashin alƙiyama). Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya taimaka wa muminai yayin da suke raunana, kuma ya taimake su ne saboda taƙawarsu da bin umarninsa; haka kuma lokacin da suka sami matsala a yaƙin Uhudu saboda saɓa wa umarnin Manzon Allah (ﷺ) da suka yi, sai kuma a nan Allah ya tsawace su da su guji tsananin kwaɗayin tara dukiya, musamman ta hanyar cin dukiyar riba ninkin-ba-ninkin, wanda yana daga manyan laifukan da suka yaɗu a wannan lokacin. Sannan kuma ya nuna musu hanyar samun taƙawa, wadda ita ce tafarkin samun duk wata nasara. Taƙawa da ma ita ce aikata umarnin Allah da guje wa haninsa. Don haka a ƙarshen waɗannan ayoyi, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin muminai da su ji tsoron Allah, don su sami rabauta duniya da lahira, kuma su kiyayi wuta, ta hanyar sanya shamaki tsakaninsu da ita, wadda an shirya ta ne musamman domin kafirai, waɗanda suka bijire wa imani da Allah da abin da ya saukar wa Annabinsa (ﷺ). Ya umarci muminai da su yi wa Allah ɗa’a da Manzonsa, domin da haka ne za su sami rahama duniya da lahira.

  133. ۞وَسَارِعُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 3:133

    Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faɗinta yake daidai da sammai da ƙasa, an yi tanadinta domin masu taƙawa.

  134. ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي ٱلسَّرَّآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَٱلۡكَٰظِمِينَ ٱلۡغَيۡظَ وَٱلۡعَافِينَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 3:134

    Su ne waɗanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin ƙunci, kuma masu ɓoye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa.

  135. وَٱلَّذِينَ إِذَا فَعَلُواْ فَٰحِشَةً أَوۡ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ ذَكَرُواْ ٱللَّهَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ لِذُنُوبِهِمۡ وَمَن يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ إِلَّا ٱللَّهُ وَلَمۡ يُصِرُّواْ عَلَىٰ مَا فَعَلُواْ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 3:135

    Su ne kuma waɗanda idan sun aikata mummunan aiki, ko suka zalunci kansu, nan take sai su tuna da Allah, sai su nemi gafarar zunubansu. Wane ne kuwa mai gafarta zunubbai in ba Allah ba? Kuma ba sa zarcewa a kan abin da suka yi, alhali suna sane.

  136. أُوْلَٰٓئِكَ جَزَآؤُهُم مَّغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَجَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ

    Open ayah 3:136

    Waɗannan sakamakonsu shi ne gafara ta musamman daga Ubangijinsu, da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma madalla da sakamakon masu aiki. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da yin gaggawa wajen samun gafarar Allah (Mai tsarki da daukaka), da samun shiga Aljanna, wadda faɗinta ya kai girman sammai da ƙassai. An tanade ta domin masu taƙawa, su ne masu ba da dukiyarsu taimako a halin suna cikin yalwa ko halin ƙunci, ba sa rowar abin da suka mallaka. Kuma suna iya mallakar zukatansu lokacin fushi, suna danne ɓacin ransu, kuma masu afuwa ga waɗanda suka munana musu. Waɗannan siffofi ne na masu kyautatawa, Allah kuwa yana son masu kyautatawa. Har wa yau, yana daga cikin siffofin muminai idan sun aikata wani laifi, ko saɓo sai su tuna Allah, su nemi gafararsa domin babu mai gafarta zunuban bawa, sai Allah shi kaɗai, kuma ba sa ci gaba da aikata wannann laifin alhalin suna sane da cewa Allah zai yi musu uƙuba, kuma suna sane da cewa, tuba wajibi ne a kan duk wanda ya saɓa wa Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma Allah yana karɓar tuban wanda ya tuba. Masu waɗannan siffofi suna da wata gafara daga Allah, kuma za su shiga gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; masaukansu ke nan na har abada. Madalla da sakamakon masu aiki.

  137. قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِكُمۡ سُنَنٞ فَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ

    Open ayah 3:137

    Haƙiƙa sunnoni (na Allah) sun riga sun shuɗe gabaninku, to sai ku yi tafiya cikin ƙasa, sai ku duba ku ga yaya ƙarshen masu ƙaryatawa ya zama?

  138. هَٰذَا بَيَانٞ لِّلنَّاسِ وَهُدٗى وَمَوۡعِظَةٞ لِّلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 3:138

    Wannan bayani ne don mutane, kuma shiriya ce da kuma wa’azi ga masu taƙawa.

  139. وَلَا تَهِنُواْ وَلَا تَحۡزَنُواْ وَأَنتُمُ ٱلۡأَعۡلَوۡنَ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

    Open ayah 3:139

    Kuma kada ku yi rauni, kada kuma ku yi baƙin ciki, kuma ku ne mafiya ɗaukaka in dai har kun kasance muminai.

  140. إِن يَمۡسَسۡكُمۡ قَرۡحٞ فَقَدۡ مَسَّ ٱلۡقَوۡمَ قَرۡحٞ مِّثۡلُهُۥۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيۡنَ ٱلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَيَتَّخِذَ مِنكُمۡ شُهَدَآءَۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّٰلِمِينَ 

    Open ayah 3:140

    Idan ma wani miki ne ya same ku a jiki, to haƙiƙa miki irinsa ya sami mutanen (Makka). Kuma waɗannan kwanaki ne da muke jujjuya su tsakanin mutane domin Allah Ya bayyanar da waɗanda suka yi imani (a gane su), kuma Ya riƙi shahidai a cikinku. Allah kuwa ba Ya son azzalumai.

  141. وَلِيُمَحِّصَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَيَمۡحَقَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 3:141

    Kuma don Allah Ya tace waɗanda suka yi imani, kuma don Ya halakar da kafirai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana lallashin zukatan Musulmi ne bayan abin da ya faru gare su a yaƙin Uhudu, na kashe da dama daga cikinsu da kafirai suka yi. Allah yana bayyana musu cewa, su zagaya a bayan ƙasa don su ga yadda sunnonin Allah suka faru ga al’ummomin da suka gabace su, su ga yadda Allah ya yi wa kafiran farko. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma yana nusar da su cewa, shi Alƙur’ani bayani ne ga ɗaukacin mutane, yana fayyace musu gaskiya, yana kuma nuna musu hanyar ɓarna don su guje ta, sannan yana shiryar da masu taƙawa zuwa miƙaƙƙiyar hanya, yana gargaɗin su da nisantar hanyoyin ɓata. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya umarci Musulmi da kada su yi rauni domin abin da ya same su a yaƙin Uhudu; su ne ko yaushe suke a sama, kuma masu rinjaye matuƙar suna riƙe da imaninsu. Idan suna ganin an kashe musu ‘yan’uwa a yaƙin Uhudu ko an yi wa wasu raununnika, to su tuna su ma kafiran irin haka ya faru gare su, an kashe wasu da dama daga cikinsu, an raunana wasu a yaƙin Uhudu da yaƙin Badar. Don haka kada su ci gaba da wannan damuwar da suke ciki, su sani wannan sunna ce ta Allah, haka yake jujjuya kwanaki a tsakanin mutane, yau ku yi nasara, gobe kuma maƙiyanku su yi nasara a kanku. To amma hikimar Allah a irin wannan aiki nasa ita ce don ya rarrabe tsakanin muminai na gaskiya da waɗanda suke na jabu, kuma Allah ya nufi wasu muminai da yin shahada, watau waɗanda za a kashe don ɗaukaka addininsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya son azzalumai, waɗanda su ne kafirai da munafuƙai fanɗararru waɗanda suka zalunci kawunansu. Kuma yana daga hikimar Allah a wannan aiki nasa, ya tsarkake muminai daga zunubbansu a dalilin abin da ya same su na kisa da raunatarwa, domin idan ya zamanto koyaushe su suke ta samun nasara, to sai ji-ji-da-kai ya shiga zukatansu, sai kuma su sami raunin imani, wanda kuma shi ne zai jawo musu fushin Allah da azabarsa. Sannan kuma Allah ya yi alƙawarin sai ya halakar da kafirai saboda ɗagawarsu da zurfafawa cikin zalunci da kafirci, wanda shi zai sa Allah ya kawar da su daga bayan ƙasa gaba ɗayansu.

  142. أَمۡ حَسِبۡتُمۡ أَن تَدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ وَلَمَّا يَعۡلَمِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ جَٰهَدُواْ مِنكُمۡ وَيَعۡلَمَ ٱلصَّٰبِرِينَ

    Open ayah 3:142

    Yanzu kuna tsammanin za ku shiga Aljanna ne alhalin Allah bai bayyanar da masu yin jihadi daga cikinku ba, kuma bai bayyanar da masu haƙuri ba.

  143. وَلَقَدۡ كُنتُمۡ تَمَنَّوۡنَ ٱلۡمَوۡتَ مِن قَبۡلِ أَن تَلۡقَوۡهُ فَقَدۡ رَأَيۡتُمُوهُ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ

    Open ayah 3:143

    Kuma haƙiƙa kun kasance a da can kuna ta burin mutuwa tun kafin ku gamu da ita, to haƙiƙa (a yau) ga ta kun gan ta alhali kuna kallo da ido.

  144. وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٞ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِ ٱلرُّسُلُۚ أَفَإِيْن مَّاتَ أَوۡ قُتِلَ ٱنقَلَبۡتُمۡ عَلَىٰٓ أَعۡقَٰبِكُمۡۚ وَمَن يَنقَلِبۡ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ فَلَن يَضُرَّ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۚ وَسَيَجۡزِي ٱللَّهُ ٱلشَّٰكِرِينَ

    Open ayah 3:144

    Kuma Muhammadu ba wani ne ba face Manzo kawai wanda manzanni haƙiƙa sun shuɗe gabaninsa. Shin yanzu idan ya mutu ko aka kashe shi, sai ku juya baya a kan dugaduganku? Duk kuwa wanda ya juya baya a kan dugadugansa to ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma da sannu Allah zai saka wa masu godiya.

  145. وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تَمُوتَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِ كِتَٰبٗا مُّؤَجَّلٗاۗ وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلۡأٓخِرَةِ نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَاۚ وَسَنَجۡزِي ٱلشَّٰكِرِينَ

    Open ayah 3:145

    Kuma babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, rubutaccen abu ne ƙayyadajje. Kuma duk wanda yake nufin sakamakon duniya, za Mu ba shi ita, wanda kuma yake nufin sakamakon lahira, to za Mu ba shi ita. Kuma da sannu za Mu saka ma masu godiya. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana nuna kuskuren muminai masu zaton cewa za su shiga Aljanna don kawai sun yi imani, ba tare da Allah ya jarrabe su ya tantance masu jihadi dominsa da kuma masu haƙuri. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tuna musu cewa, sun kasance a baya suna fatan haɗuwarsu da abokan gabarsu, suna mararin su yi mutuwar shahada; to ga shi a ranar Uhudu sun ga mutuwar da idanunsu, kuma sun kasa jurewa su yi haƙuri, har su kai ga samun abin da suke fatan su samu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, Annabi (ﷺ) ba mai dawwama ne a duniya ba; shi ma kamar sauran annabawa yake; wasu daga cikinsu mutuwa suka yi, wasu kuma kashe su aka yi. To yanzu idan shi ma ajalinsa ya ƙare ta hanayar mutuwa ko kisa, shi ke nan sai su yi ridda su bar addininsu? To wanda duk ya yi ridda ya bar addinin Allah, to ba zai cutar da Allah (Mai tsarki da daukaka) da komai ba, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) zai saka wa masu godiya daga cikin bayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, babu wani rai a duniya da zai mutu sai da izinin Allah, wato idan ajalinsa ya yi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yana ba wa kowa sakamakon aikinsa daidai da niyyarsa; wanda ya yi aikinsa don neman duniya, to sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi wani abu daga cikinta; wanda kuma ya yi aikinsa don neman ladan lahira, shi ma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi wani abu daga cikinta, kuma zai saka wa masu godiya.

  146. وَكَأَيِّن مِّن نَّبِيّٖ قَٰتَلَ مَعَهُۥ رِبِّيُّونَ كَثِيرٞ فَمَا وَهَنُواْ لِمَآ أَصَابَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَمَا ضَعُفُواْ وَمَا ٱسۡتَكَانُواْۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلصَّٰبِرِينَ

    Open ayah 3:146

    Kuma sau da yawa an sami wani annabi (daga cikin annabawa), mabiya masu yawa sun yi yaƙi tare da shi, amma ba su taɓa yin rauni ba saboda abin da ya same su a tafarkin Allah, kuma ba su taɓa yin ragwanci ba, kuma ba su taɓa miƙa wuya ba. Kuma Allah Yana son masu haƙuri.

  147. وَمَا كَانَ قَوۡلَهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَإِسۡرَافَنَا فِيٓ أَمۡرِنَا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 3:147

    Kuma ba su da wata magana sai faɗar: “Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu da ƙetare iyakar da muka yi cikin lamurranmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutunen da suke kafirai.

  148. فَـَٔاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا وَحُسۡنَ ثَوَابِ ٱلۡأٓخِرَةِۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 3:148

    Sai Allah Ya ba su ladan duniya da kyakkyawan lada na lahira. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin abin da ya faru ga muminai a ranar yaƙin Uhudu, sanda aka samu cikas a yaƙin, har wasu daga cikinsu suka gudu daga fagen daga, sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, hanyar mabiya annabawa iri ɗaya ce, watau haƙuri da juriya a wurin jihadi, saboda haka su ma bai dace da su gudu ba. A kan wannan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake ba da labarin cewa, sau da yawa wani annabi daga cikin annabawa yakan yi yaƙi tare da mabiyansa masu yawa, kuma wani rauni ya same su a yaƙin, amma hakan bai sa sun karaya sun rabu da addininsu ko sun watsar da jihadin ɗaukaka kalmar Allah ba; jikinsu bai yi sanyi ba, zukatansu ba su yi rauni ba, himmarsu ba ta dakushe ba, ba su ba maƙiyansu kai bori ya hau ba. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) yake son masu haƙuri irin waɗannan. Bugu da ƙari, duk irin abin da ya sami waɗannan jarumai a yaƙe-yaƙensu, ba abin da suke furtawa da bakunansu sai kawai neman gafarar Allah (Mai tsarki da daukaka) a kan zunubbansu ko abin da suka ƙetare iyakar Ubangijinsu a cikin lamuransu. Suna kuma roƙon sa ya ba su ikon jajircewa, ya kuma ba su nasara a kan maƙiyansu kafirai. A sakamakon haka, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu kyakkyawar sakayya ta duniya, ya ba su nasara da ganima da ɗaukaka, kuma ga kyakkyawan sakamako na lahira, suka cim ma yardar Allah (Mai tsarki da daukaka) da dawwama a gidan Aljanna. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa yana son masu kyautatawa, don haka ne ya yi musu kyautayinsa a duniya da lahira.

  149. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تُطِيعُواْ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَرُدُّوكُمۡ عَلَىٰٓ أَعۡقَٰبِكُمۡ فَتَنقَلِبُواْ خَٰسِرِينَ

    Open ayah 3:149

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan har kuka yi biyayya ga waɗanda suka kafirta, to za su mayar da ku baya a kan dugaduganku, sai ku juya kuna hasararru.

  150. بَلِ ٱللَّهُ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلنَّٰصِرِينَ 

    Open ayah 3:150

    A’a, Allah Shi ne Majiɓincin lamarinku; kuma Shi ne Fiyayyen masu taimako.

  151. سَنُلۡقِي فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلرُّعۡبَ بِمَآ أَشۡرَكُواْ بِٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ سُلۡطَٰنٗاۖ وَمَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُۖ وَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 3:151

    Da sannu za Mu jefa tsoro a cikin zukatan waɗanda suka kafirta saboda abin da suka yi na sanya wa Allah kishiya, abin da bai saukar da hujja a kai ba; kuma makomarsu ita ce wuta. Kuma tir da makomar azzalumai (idan ta zama wuta).

  152. وَلَقَدۡ صَدَقَكُمُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥٓ إِذۡ تَحُسُّونَهُم بِإِذۡنِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَا فَشِلۡتُمۡ وَتَنَٰزَعۡتُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِ وَعَصَيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ مَآ أَرَىٰكُم مَّا تُحِبُّونَۚ مِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلدُّنۡيَا وَمِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَۚ ثُمَّ صَرَفَكُمۡ عَنۡهُمۡ لِيَبۡتَلِيَكُمۡۖ وَلَقَدۡ عَفَا عَنكُمۡۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 3:152

    Kuma tabbas haƙiƙa Allah Ya cika muku alƙawarinsa yayin da kuka dinga kisan su da yawa da izininsa; har zuwa lokacin da kuka yi rauni, kuma kuka yi jayayya a cikin umarnin (Manzo), kuma daga ƙarshe kuka saɓa bayan (Allah) Ya nuna muku irin abin da kuke so. Cikinku akwai waɗanda suke nufin duniya, kuma cikinku akwai waɗanda suke nufin lahira. Sannan sai Ya kautar da ku kuka bar su don ya jarrabe ku; kuma tabbas haƙiƙa Allah Ya yi muku afuwa. Kuma Allah Ma’abocin falala ne ga muminai.

  153. ۞إِذۡ تُصۡعِدُونَ وَلَا تَلۡوُۥنَ عَلَىٰٓ أَحَدٖ وَٱلرَّسُولُ يَدۡعُوكُمۡ فِيٓ أُخۡرَىٰكُمۡ فَأَثَٰبَكُمۡ غَمَّۢا بِغَمّٖ لِّكَيۡلَا تَحۡزَنُواْ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمۡ وَلَا مَآ أَصَٰبَكُمۡۗ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 3:153

    Ka tuna lokacin da kuke gudowa ba kwa waiwaye ma ku ga wanda yake baya da ku, kuma Manzo yana can bayanku yana ta kiran ku, sai (Allah) Ya saka muku da damuwa bisa damuwa domin kar ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, da abin da ya same ku. Allah kuma Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne.

  154. ثُمَّ أَنزَلَ عَلَيۡكُم مِّنۢ بَعۡدِ ٱلۡغَمِّ أَمَنَةٗ نُّعَاسٗا يَغۡشَىٰ طَآئِفَةٗ مِّنكُمۡۖ وَطَآئِفَةٞ قَدۡ أَهَمَّتۡهُمۡ أَنفُسُهُمۡ يَظُنُّونَ بِٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ ظَنَّ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِۖ يَقُولُونَ هَل لَّنَا مِنَ ٱلۡأَمۡرِ مِن شَيۡءٖۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَمۡرَ كُلَّهُۥ لِلَّهِۗ يُخۡفُونَ فِيٓ أَنفُسِهِم مَّا لَا يُبۡدُونَ لَكَۖ يَقُولُونَ لَوۡ كَانَ لَنَا مِنَ ٱلۡأَمۡرِ شَيۡءٞ مَّا قُتِلۡنَا هَٰهُنَاۗ قُل لَّوۡ كُنتُمۡ فِي بُيُوتِكُمۡ لَبَرَزَ ٱلَّذِينَ كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَتۡلُ إِلَىٰ مَضَاجِعِهِمۡۖ وَلِيَبۡتَلِيَ ٱللَّهُ مَا فِي صُدُورِكُمۡ وَلِيُمَحِّصَ مَا فِي قُلُوبِكُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

    Open ayah 3:154

    Sannan bayan damuwa sai (Allah) Ya saukar muku da kwanciyar hankali har gyangyaɗi yana ɗaukar wasu daga cikinku; amma wani sashin kuma tasu ta ishe su, suna yi wa Allah zato wanda ba na gaskiya ba, zato irin na jahiliyya; suna cewa: “Anya kuwa muna da ta cewa cikin wannan lamari?” Ka ce: “Lalle al’amari gaba ɗaya na Allah ne.” Suna ɓoyewa a cikin rayukansu abin da ba sa bayyana maka shi; suna cewa: “In da al’amarin a hannunmu yake ai da ba a kashe mu a nan ba.” Ka ce: “Ko da kun kasance kuna cikin gidajenku, tabbas da waɗanda aka rubuta za su mutu sun fito da kansu, sun zo inda nan ne za su kwanta (dama).” Kuma Allah (Ya ƙaddara haka) don Ya jarraba abin da yake cikin ƙirazanku, kuma don Ya tace abin da yake cikin zukatanku. Kuma Allah Masanin abin da yake cikin zukata ne.

  155. إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ مِنكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ إِنَّمَا ٱسۡتَزَلَّهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِبَعۡضِ مَا كَسَبُواْۖ وَلَقَدۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

    Open ayah 3:155

    Lalle waɗanda suka gudu daga cikinku yayin da runduna biyu suka haɗu, Shaiɗan ne ya so ya zamar da su saboda wani laifi da suka yi; kuma tabbas haƙiƙa Allah Ya yi musu afuwa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai haƙuri. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana gargaɗin muminai ne da kada su boye wa ta kafirai, domin yi musu biyayya zai iya jefa su cikin kafirci, su halaka duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne mai jiɓintar lamarin bayinsa, kuma shi ne mai ba da nasara; su kuma kafirai ba wata nasara ko taimako da za su iya ba muminai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa muminai albishir cewa, zai jefa tsoro a cikin zukatan kafirai, saboda shirkar da suke yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka) ba tare da wata hujja ko wani dalili ba, a lahira kuma wutar Jahannama ce makomarsu, tir kuwa da wannan irin makoma ta azzalumai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da tunatar da sahabban Annabi (ﷺ) matsalar da aka samu a yaƙin Uhudu ta ɓangaren wasu daga cikinsu saboda saɓa wa umarnin Annabi (ﷺ) da suka yi, bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya cika musu alƙawarin da ya yi musu na ba su nasara a kan abokan gabarsu. Da farko Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɗora muminai a kan kafirai, har sun fara kashe su, sai kuma Musulmi suka fara ja da baya a sakamakon saɓanin da ya ɓarke tsakanin maharba hamsin da Annabi (ﷺ) ya ajiye su a kan wani ɓangare na dutsen Uhudu, ya umarce su da kada su bar wannan wurin ko da kuwa sun ga alamun cin nasara tare da Musulmi. To amma sai suka saɓa wannan umarni yayin da suka ga Musulmi sun fara cin nasara a kan kafirai, suna bin su da sara da suka, sai kuma wasu suka tafi suna kwasar ganima, suka bar wurin tsayuwarsu, amma wasu sun ci gaba da tsayuwa inda aka tsayar da su. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya juyar da lamarin muminai, galaba ta tabbata ga kafirai, suka juyo kan Musulmi da sara da suka ta gaba ta baya. Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ba mu labarin abin da ya faru a ranar Uhudu ya ce: “Mun haɗu a filin yaƙi tare da mushrikai, Annabi (ﷺ) ya ajiye wasu maharba a kan wani dutse, ya shugabantar musu da wani sahabi ana kiran sa Abdullahi ɗan Jubair (Allah ya kara masa yarda), ya kuma faɗa musu cewa: “Kada ku bar wurarenku ko da kuwa kun ga mu ne muka yi galaba a kansu ko kuma kun ga sun yi galaba a kanmu, to kada ku taho taimaka mana.” Jabir ya ce: “Yayin da muka fara fafatawa da su, sai suka ranta a na kare, muka ga mata suna ta gudu suna hawan duwatsu, sun buɗe ƙwaurinsu ana ganin mundayensu. Da maharban nan na kan dutse suka ga haka, sai suka riƙa cewa: “Ganima! Ganima!!” Sai Shugabansu Abdullahi ya ce musu: “Annabi (ﷺ) fa ya umarce mu da kada mu bar wurarenmu.” Sai suka ƙi jin maganarsa, suka shiga kwasar ganima. Haka na faruwa, sai reshe ya juye da mujiya, mushirikai suka yiwo kansu, har suka kashe sahabbai saba’in. Daga nan Abu Sufyan ya leƙo yana cewa: “Muhammadu na cikinku? Ɗan Abu Ƙuhafata yana cikinku? Ɗan Khaɗɗab yana cikinku?” Duk Annabi (ﷺ) yana ce wa sahabbai: “Kada ku amsa masa.” Sai Abu Sufyan ya ce: “Duk an kashe waɗannan. Da a ce suna da rai, da sun amsa.” Sai Umar ya kasa haƙuri, ya ce: “Ƙarya kake maƙiyin Allah! Allah ya bar maka abin da zai ci gaba da tozarta ka.” Sai Abu Sufyan ya ce: “Sama dai, sama dai gunkin Hubal.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ku ba shi amsa.” Sai suka ce: “Me za mu ce masa?” Sai ya ce: “Ku ce: “Allah (Mai tsarki da daukaka) ne mafi ɗaukaka, kuma mafi girma.” Sai Abu Sufyan ya ce: “Muna da Uzza, amma ku ba ku da Uzza.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ku ba shi amsa.” Sai suka ce: “Me za mu ce?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ku ce Allah ne mai jiɓintar mu, ku ba ku da mai jiɓintar ku.” Sai Abu Sufyan ya ce: “Wannan rana ta zama a madadin ranar Badar. Yaƙi yau nasara gare ka ne, gobe ga maƙiyanka. Za ku ga wanda aka daddatsa shi bayan an kashe shi cikin mutanenku, ba ni ne na yi umarni da hakan ba, amma kuma bai baƙanta mini rai ba.” [Bukhari #4043]. Yana nufin abin da aka yi wa Sayyidina Hamza na fasa cikinsa da ciro kayan cikinsa. Wannan jarraba ce da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa muminai don ya bambance mai biyayya daga cikinsu da wanda ya fanɗare. To amma kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce ya yafe musu, domin haka yake yin falalarsa ga muminai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da tunatar da su lokacin da suka fita a guje ba mai waiwayen wani, a lokacin kuma Annabi (ﷺ) yana ta kiran su, yana neman su da su tsaya su daina gudu; to amma ina, sun bar shi a bayansu, ba sa amsa kiransa, sai a sakamakon haka Allah ya jefa musu wani baƙin ciki a zukatansu, inda aka baza jita-jitar cewa an kashe Annabi (ﷺ), Wannan ya zarce sauran ababen baƙin cikin da ya same su a wannan ranar, na rashin samun nasara ko ganima, da kashe wasu daga cikinsu, da yi wa wasu rauni. Bayan wannan baƙin ciki ne sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa muminai nutsuwa, har wasu daga cikinsu suka riƙa gyangyaɗi. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Abu Ɗalhata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ɗaga kaina ranar yaƙin Uhudu na duba, kowa na gani a ranar gyangyaɗi yake ta bayan garkuwarsa, shi ya sa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Sannan ya saukar muku da aminci bayan damuwar da kuka sami kanku a ciki, har gyangyaɗi ya riƙa lulluɓe wasu daga cikinku.” [Tirmizi #3007]. Wasu kuwa suka kasa samun nutsuwa suna tunanin kada a kashe su, waɗannan su ne munafuƙai, waɗanda suka riƙa yi wa Allah mummunan zato suna cewa, ba zai taimaka wa muminai da nasara ba. Wannan kuwa zato ne irin na jahilai waɗanda ba su san Allah ba. Har ma ta kai suna cewa, su tilas ce ta sa suka fito wannan yaƙin, don maganar ba a hannunsu take ba, da a hannunsu take da ba a fito ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa ya mayar musu da martini da cewa, ai duk al’amura suna hannun Allah (Mai tsarki da daukaka) ne shi kaɗai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana siffofin munafuƙai da cewa, suna ɓoye wani abu a ransu wanda ba sa bayyana shi ga Annabi (ﷺ), watau maganar da suke yi a tsakaninsu cewa, da a ce suna da zaɓi a kan fitowa wannan yaƙi, da ba su zaɓi fitowa daga Madina ba, kuma da yanzu ba a kashe kowa ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa ya faɗa musu cewa, ai ko da suna gidajensu ba su fito wurin yaƙi ba, da sai waɗanda Allah ya rubuta mutuwarsu sun fito zuwa inda za su mutu, don haka ya kamata su san da cewa, daga Allah ne ƙaddara fitowarsu take, ba daga gare su ba, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi haka ne don ya jarraba abin da yake cikin zukatansu, ya fito da mai kyau da maras kyau. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya san abin da bayinsa suke ɓoyewa a zukatansu, zai yi wa kowa hisabi gwargwadon aikinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, gudun da wasu sahabbai suka yi daga fagen yaƙi a wannan rana, ai Shaiɗan ne ya ingiza su ciki, kuma ya sami wannan damar ne a kansu saboda wasu laifuffukansu, amma duk da haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce ya yafe musu. Allah kuma mai yawan gafara ne, mai yawan haƙuri.

  156. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَقَالُواْ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ إِذَا ضَرَبُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَوۡ كَانُواْ غُزّٗى لَّوۡ كَانُواْ عِندَنَا مَا مَاتُواْ وَمَا قُتِلُواْ لِيَجۡعَلَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ حَسۡرَةٗ فِي قُلُوبِهِمۡۗ وَٱللَّهُ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

    Open ayah 3:156

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku kasance kamar waɗanda suka kafirta, kuma suka riƙa faɗa wa ‘yan’uwansu yayin da suka yi tafiya a bayan ƙasa, ko kuma suka kasance mayaƙa: “In da sun kasance tare da mu, ai da ba su mutu ba, kuma da ba a kashe su ba,” don Allah Ya sanya waccan (maganar) ta zamo nadama a cikin zukatansu. Kuma Allah Shi ne Mai rayawa, kuma Shi ne Mai kashewa. Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.

  157. وَلَئِن قُتِلۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوۡ مُتُّمۡ لَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَحۡمَةٌ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

    Open ayah 3:157

    Kuma lalle idan ma har an kashe ku a hanyar Allah ko kuma kuka mutu, to kuna da gafara ta musamman a wajen Allah da kuma rahama, wanda shi ne mafi alheri fiye da abin da suke tarawa.

  158. وَلَئِن مُّتُّمۡ أَوۡ قُتِلۡتُمۡ لَإِلَى ٱللَّهِ تُحۡشَرُونَ

    Open ayah 3:158

    Kuma lalle in kuka mutu ko aka kashe ku, lalle zuwa ga Allah dai za a mayar da ku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa muminai kashedi daga yin munanan maganganu irin na kafirai masu nuna rashin imani da Ƙaddarar Allah (Mai tsarki da daukaka). Watau sun saba duk lokacin da ‘yan’uwansu kafirai suka yi tafiya ta kasuwanci ko yaƙi, sai Allah ya ƙaddari mutuwarsu a can, sai ‘yan’uwan nasu kafirai su riƙa cewa, da ba su fita ko’ina ba sun yi zamansu a garuruwansu da hakan bai faru gare su ba. Wannan irin muguwar aƙida ita ta sa Allah ya sanya musu nadama a zukatansu, masifarsu kuma ta yi ta ƙaruwa. Sun manta da cewa Allah shi kaɗai yake da ikon rayawa da kashewa; babu wani rai da zai mutu har sai ajalinsa ya cika, Allah kuma yana ganin duk abin da bayinsa suke aikatawa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa muminai cewa, duk wanda aka kashe shi ko ya mutu wajen ɗaukaka Kalmar Allah, to abin da zai samu na gafarar Allah da rahamarsa, ya fi masa alheri fiye da zamansa a duniya da abin da masu tara dukiya a duniya suke tarawa. Allah kuma ya sake tuna musa cewa, ko mutuwa suka yi ko kuma kashe su aka yi, to makoma dai zuwa ga Allah take.

  159. فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ

    Open ayah 3:159

    To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu’amala, mai ƙeƙasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka ƙulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi.

  160. إِن يَنصُرۡكُمُ ٱللَّهُ فَلَا غَالِبَ لَكُمۡۖ وَإِن يَخۡذُلۡكُمۡ فَمَن ذَا ٱلَّذِي يَنصُرُكُم مِّنۢ بَعۡدِهِۦۗ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ 

    Open ayah 3:160

    Idan Allah Ya ba ku nasara, to ba wanda ya isa ya rinjaye ku, amma idan Ya taɓar da ku, to wane ne ya isa ya taimake ku in ba shi ba? Kuma muminai wajibi ne su dogara ga Allah Shi kaɗai.

  161. وَمَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَغُلَّۚ وَمَن يَغۡلُلۡ يَأۡتِ بِمَا غَلَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

    Open ayah 3:161

    Kuma bai dace ba ga wani annabi ya yi ha’inci. Duk wanda ya yi ha’inci kuwa zai zo da abin da ya ha’inta ranar tashin alƙiyama. Sannan kowane rai a cika masa (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su (halitta) ba za a zalunce su ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa cewa, saboda rahamar da Allah ya yi masa ne, ya sa ya zama mai sauƙin kai ga sahabbansa, mai tausasa musu mu’amala, don haka duk suka tattaru a wurinsa, suna bin umarninsa. Da abin a ce shi mai mummunan hali ne, mai kakkausar zuciya, to da duk sun watse sun bar shi. An karɓo daga Aɗa’u ɗan Yasar ya ce: “Na gamu da Abdullahi da Amru ɗan Asi (Allah ya kara masa yarda), sai na ce masa: “Faɗa mini siffar Annabi (ﷺ) da take cikin littafin Attaura.” Sai ya ce: “Ƙwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alƙur’ani, inda Allah yake cewa: “Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin mai shaida, kuma mai albishir mai gargaɗi, kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona, na sa maka suna ‘Mai dogaro’, ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa, ya yi gafara. Kuma Allah ba zai karɓi rayuwarsa ba, har sai bayan ya tsaida addini da shi, har mutane su furta Kalmar Shahada, wadda ita za ta buɗe idanun da suka makance da kunnuwan da suka kurumce da zukatan da suka toshe.” [Bukhari #2124]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya yi afuwa a kan kurakuransu da gajiyawarsu, kuma ya nema musu gafarar Allah (Mai tsarki da daukaka), ya kuma nemi shawararsu cikin abubuwan da kan taso masu buƙatar sai an yi shawara. Bayan shawara kuma, duk abin da ya ga shi ne ya fi maslaha, to ya ci gaba da zartar da shi, ya dogara ga Allah, Allah yana son masu dogara da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, idan har ya ƙaddara musu samun wata nasara, to babu wanda ya isa ya karya su ko ya ci galaba a kansu; idan kuwa ya yi watsi da su, ya ƙyale su, to har abada babu mai iya taimakon su, don haka lalle muminai su dogara da Allah shi kaɗai. Sannan Allah ya faɗakar da cewa, ba ya daga cikin halayen annabawa su saci dukiyar ganima, domin Allah ya tsare su daga cin amana ko wani mugun hali, don haka bai dace a tuhume su da wani abu irin wannan ba. Yawancin makaranta sun karanta ayar kamar haka: (أنْ يُغَلّ) watau suka yi rufu’a a kan (يُـ), suka kuma yi fataha a kan غَـ)). Ma’ana: “Bai kamata ba a ha’inci wani annabi.…” Sai kuma ya ambaci sakamakon wanda ya saci dukiyar ganima da cewa, zai zo ɗauke da kayanta a ranar gobe ƙiyama a gadon bayansa, sannan kowane rai za a yi masa sakayya a kan aikinsa, kuma babu wanda za a zalunta komai. An karɓo daga Mu’azu ɗan Jabal (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya aike ni, bayan na kama hanya na tafi, sai kuma ya aika a kirawo ni. Da na dawo sai ya ce: “Ko ka san don me na aika a kirawo ka? Kada ka kuskura ka ɗauki wani abu na ganima ba tare da izinina ba, domin yin haka satar dukiyar ganima ce wanda duk ya saci dukiyar ganima, to zai zo da abin da ya sata ranar alƙiyama. Don haka ne na kirawo ka, sai ka tafi wurin aikinka.” [Bukhari #200]. An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ranar yaƙin Khaibara, wasu sahabbai sun zo suna lissafa wa Manzon Allah (ﷺ) cewa, wane ya yi shahada, wane ma ya yi shahada, har suka zo kan wani mutum, sai suka ce, wane ma ya yi shahada.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A’a, ba haka ba ne, ni na gan shi a wutar Jahannama saboda wani mayafi da ya sata daga dukiyar ganima.” Sannan Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya kai ɗan Khaɗɗab, tafi ka yi shela a cikin mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai muminai kaɗai.” Ya ce: “Sai na fita na shelanta wa mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai mumini kaɗai.” [Muslim #114].

  162. أَفَمَنِ ٱتَّبَعَ رِضۡوَٰنَ ٱللَّهِ كَمَنۢ بَآءَ بِسَخَطٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 3:162

    Shin yanzu wanda ya bi yardar Allah, zai yi kamar wanda ya dawo da fushin Allah, kuma makomarsa ta zamo Jahannama? Kuma tir da wannan makoma.

  163. هُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 3:163

    Su darajoji ne a wajen Allah. Allah kuma Mai ganin abin da suke aikatawa ne.

  164. لَقَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ بَعَثَ فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡ أَنفُسِهِمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُزَكِّيهِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

    Open ayah 3:164

    Lalle haƙiƙa Allah Ya yi ni’ima ga muminai yayin da Ya aiko musu Manzo daga cikinsu, wanda yake karanta musu ayoyinsa, kuma yake tsarkake su, kuma yake koyar da su Littafi da Hikima, lalle kuma sun kasance kafin (zuwansa) tabbas suna cikin ɓata mabayyani.

  165. أَوَلَمَّآ أَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةٞ قَدۡ أَصَبۡتُم مِّثۡلَيۡهَا قُلۡتُمۡ أَنَّىٰ هَٰذَاۖ قُلۡ هُوَ مِنۡ عِندِ أَنفُسِكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 3:165

    Shin yayin da wata musifa ta same ku, wadda kuma haƙiƙa kun yi wa (kafirai) irinta ninki biyu, sai ku riƙa cewa: “Yaya haka ta faru?” Ka ce: “Ai wannan daga kanku ne.” Lalle Allah Mai iko ne a kan komai.

  166. وَمَآ أَصَٰبَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ فَبِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَلِيَعۡلَمَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 3:166

    Kuma abin da ya same ku ranar da ƙungiyoyin nan biyu suka haɗu, to da izinin Allah ne, kuma don Ya bayyana muminai.

  167. وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ نَافَقُواْۚ وَقِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ قَٰتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوِ ٱدۡفَعُواْۖ قَالُواْ لَوۡ نَعۡلَمُ قِتَالٗا لَّٱتَّبَعۡنَٰكُمۡۗ هُمۡ لِلۡكُفۡرِ يَوۡمَئِذٍ أَقۡرَبُ مِنۡهُمۡ لِلۡإِيمَٰنِۚ يَقُولُونَ بِأَفۡوَٰهِهِم مَّا لَيۡسَ فِي قُلُوبِهِمۡۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يَكۡتُمُونَ

    Open ayah 3:167

    Kuma don Ya bayyana waɗanda suka yi munafunci; kuma aka riƙa cewa da su: “Ku zo ku yi yaƙi don Allah ko don kariya.” Sai suka ce: “Da mun san za a yi yaƙi ai da lalle mun biyo ku.” Su a wannan lokacin sun fi kusanci ga kafirci fiye da imani, suna faɗi da bakunansu abin da ba ya cikin zukatansu. Kuma Allah Ya san abin da suke ɓoyewa.

  168. ٱلَّذِينَ قَالُواْ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ وَقَعَدُواْ لَوۡ أَطَاعُونَا مَا قُتِلُواْۗ قُلۡ فَٱدۡرَءُواْ عَنۡ أَنفُسِكُمُ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 3:168

    Su ne waɗanda suka faɗa wa ‘yan’uwansu, alhalin suna zaune a gida cewa: “In da sun bi (shawarar) mu da ba a kashe su ba.” Ka ce: “To ku kare kanku daga mutuwa in har kun kasance masu gaskiya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, wanda ya kasance yardar Allah ce abin nemansa da wanda ya riga ya dulmiya cikin saɓon Allah, ya dawo da fushinsa ba za su taɓa zama ɗaya ba, waɗannan kuma wutar Jahannama ita ce makomarsa. Tir kuma da wannan makoma. Allah kuma ya ƙara jaddada cewa, waɗanda suka nemi yardar Allah suna da matakai daban-daban na ɗaukaka; waɗanda kuma Allah ya yi fushi da su su ma suna da matakai daban-daban na ƙasƙanci. Kuma Allah yana ganin duk abin da bayinsa suke aikatawa, kuma zai yi musu sakayya a kansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin ni’imar da ya yi wa muminai, ta hanyar aiko musu da Manzo daga cikin jinsinsu na mutane, yana karanta musu Alƙur’ani, yana tsarkake su daga shirka da saɓon Allah da miyagun halayya, kuma yana koya musu ma’anonin Alƙur’ani da sunnarsa, duk da cewa kafin zuwan wannan Manzo, suna cikin ɓata mabayyani. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci muminai, lokacin da musiba ta same su a ranar yaƙin Uhudu, ta yi musabbabin kashe mutum saba’in, alhali su kuma sun yi sanadiyyar jawo musu musifa riɓi biyu, ta hanyar kashe musu mutum saba’in da kama mutum saba’in a yaƙin Badar, amma kuma sai suka riƙa tambayar yaya aka yi wannan musibar ta same su? Sai Allah ya umarci Annabinsa (ﷺ) ya faɗa musu cewa, abin da ya same su fa su ne suka jawo shi da kansu, lokacin da suka riƙa jayayya a kan umarnin Annabi (ﷺ), kuma suka saɓa wa umarninsa. Don haka Allah mai iko ne a kan yi musu uƙuba irin ta ranar yaƙin Uhudu, kuma yana da ikon ba su nasara, don haka kada su yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka) zaton da ba na gaskiya ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gaya wa muminai cewa, abin da ya same su a yaƙin Uhudu, lokacin haɗuwarsu da rundunar mushirikai, ya faru ne da nufin Allah (Mai tsarki da daukaka) da hukuncinsa, don ya tantance tsakanin muminai na gaskiya da munafuƙan da suke ɓoye cikin sahun Musulmi. Kuma ai asirinsu ya tonu lokacin da aka kirawo su su fito yaƙi na ɗaukaka addinin Allah, ko kuma don kare ƙasa da mutanen cikinta, sai kawai suka riƙa ba da wani hanzari na banza suna cewa, da sun san idan an fita za a fafata tsakanin musulmai da kafirai, da sai su fita, to amma suna ganin hakan ba zai faru ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, munafuƙai a wannan lokacin sun fi kusa da kafirci fiye da imani. Suna ɓoyewa a ransu, saɓanin abin da suke bayyanawa, kuma Allah yana ganin duk abin da suke ɓoyewa. Munafuƙan da suka ƙi fita yaƙi dai sun riƙa ce wa danginsu da suka fita, aka kashe su, cewa: “Da sun karɓi shawararmu sun ƙi fita, ai da ba a kashe su ba.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa ya faɗa musu cewa, su masu ba da shawarar ai sai su kare kawunansu daga mutuwa, idan har su masu gaskiya ne, cewar da sun yi musu biyayya da ba a kashe su ba.

  169. وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتَۢاۚ بَلۡ أَحۡيَآءٌ عِندَ رَبِّهِمۡ يُرۡزَقُونَ

    Open ayah 3:169

    Kuma kada ka yi tsammanin waɗanda aka kashe su a wajen yaɗa kalmar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu, ana arzurta su.

  170. فَرِحِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ وَيَسۡتَبۡشِرُونَ بِٱلَّذِينَ لَمۡ يَلۡحَقُواْ بِهِم مِّنۡ خَلۡفِهِمۡ أَلَّا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ 

    Open ayah 3:170

    Suna cike da farin cikin abin da Allah Ya ba su na falalarsa, kuma suna masu yin albishir ga waɗanda ba su riga sun riske su ba daga bayansu cewa, babu jin tsoro a gare su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.

  171. ۞يَسۡتَبۡشِرُونَ بِنِعۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَضۡلٖ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 3:171

    Suna ta farin ciki da ni’ima daga Allah da falala, kuma Allah ba Ya tozarta ladan masu imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabinsa da kada ya yi zaton cewa, sahabbansa da aka kashe a ranar Uhudu matattu ne; a’a su rayayyu ne wata rayuwa ta musamman a wurin Ubangijinsu, suna nan kusa da shi, suna jin daɗi da ni’imar da ya tanadar musu a gidan Aljanna, suna cike da farin ciki da irin manya-manyan ni’imomi da ya ba su. Hakanan suna yin albishir ga ‘yan’uwansu waɗanda suka baro a duniya suna fafata yaƙin ɗaukaka kalmar Allah, suna cewa, su ma da zarar an kashe su a wannan yanayi, to za su sami saduwa da su, ba tare da sun ji tsoron abin da za su iske ba, ko baƙin cikin abin da suka bari a duniya. Za su yi farin ciki da albishir da karramawa da falalar da Allah ya yi musu. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya tozarta ladan muminai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lokacin da aka kashe ‘yan’uwanku a yaƙin Uhudu, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya rayukansu a cikin cikkunan wasu korayen tsuntsaye, suna zuwa ƙoramun Aljanna suna sha, kuma suna cin kayan marmarinta, sannan su koma ga wasu fitilu na zinariya da ke rataye a inuwar Al-Arshi. Lokacin da suka sami abinci mai daɗi da abin sha mai daɗi da makwanci na alfarma, sai suka ce: ‘Wane ne zai kai labarinmu ga ‘yan’uwanmu cewa muna nan a Aljanna ana ciyar da mu, domin kada su guji jihadi su bar yaƙi?’ Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: ‘Ni ne zan kai musu labarinku.’ Sai ya saukar da faɗarsa: ‘Kuma kada ku yi tsammanin waɗanda aka kashe a wajen ɗaukaka kalmar Allah matattu ne, a’a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu ana arzuta su.’ [Ahmad #2388, da Abu Dawud #2520].

  172. ٱلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِ مِنۢ بَعۡدِ مَآ أَصَابَهُمُ ٱلۡقَرۡحُۚ لِلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ مِنۡهُمۡ وَٱتَّقَوۡاْ أَجۡرٌ عَظِيمٌ

    Open ayah 3:172

    Su ne waɗanda suka amsa kiran Allah da Manzo bayan miki ya same su a jikinsu. Lalle waɗanda suka kyautata a cikinsu, kuma suka yi taƙawa, suna da lada mai girma.

  173. ٱلَّذِينَ قَالَ لَهُمُ ٱلنَّاسُ إِنَّ ٱلنَّاسَ قَدۡ جَمَعُواْ لَكُمۡ فَٱخۡشَوۡهُمۡ فَزَادَهُمۡ إِيمَٰنٗا وَقَالُواْ حَسۡبُنَا ٱللَّهُ وَنِعۡمَ ٱلۡوَكِيلُ

    Open ayah 3:173

    Su ne waɗanda mutane suka ce da su: “Lalle mutanen (Makka) fa sun tara muku runduna, to sai ku tsorace su.” Amma sai hakan ya ƙara musu imani, sai suka riƙa cewa: “Allah Ya wadace mu, kuma madalla da abin dogara (idan har Shi ne Allah).”

  174. فَٱنقَلَبُواْ بِنِعۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَضۡلٖ لَّمۡ يَمۡسَسۡهُمۡ سُوٓءٞ وَٱتَّبَعُواْ رِضۡوَٰنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضۡلٍ عَظِيمٍ

    Open ayah 3:174

    (A sakamakon haka) sai suka dawo da ni’ima ta musamman daga Allah da falala, wani abin ƙi bai shafe su ba, kuma (suka dace da cewa) sun bi yardar Allah. Allah kuma Ma’abocin falala ne wadda take mai girma.

  175. إِنَّمَا ذَٰلِكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ يُخَوِّفُ أَوۡلِيَآءَهُۥ فَلَا تَخَافُوهُمۡ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

    Open ayah 3:175

    Wannan (labarin), Shaiɗan ne kawai yake tsoratar da ku masoyansa, don haka kar ku ji tsoron su, amma ku ji tsoro Na in dai har ku muminai ne.

  176. وَلَا يَحۡزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡكُفۡرِۚ إِنَّهُمۡ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۚ يُرِيدُ ٱللَّهُ أَلَّا يَجۡعَلَ لَهُمۡ حَظّٗا فِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٌ

    Open ayah 3:176

    Kuma kada waɗanda suke gaggawar shiga cikin (ayyukan) kafirci, su fusata ka. Haƙiƙa su ba za su cutar da Allah komai ba. Allah Ya yi nufin ba zai sanya musu wani rabo a lahira ba; kuma suna da azaba mai girma. Yayin da Annabi (ﷺ) ya dawo Madina daga yaƙin Uhudu, sai ya sami labarin cewa, Abu Sufyana da mutanensa suna ƙoƙarin dawowa Madina, sai Annabi (ﷺ) ya nemi sahabbansa kowa ya fito har da masu raunuka, don su amsa kiran Allah da Manzonsa, suka nufi wani wuri da ake kira Hamra’ul Asad. Da suka isa wurin, sai wani ya zo yana ce musu: “Mutane fa sun yi muku taron dangi da nufin sai sun ga bayanku gaba ɗaya.” Ya kuwa faɗa musu haka ne don ya tsorata su; to amma a maimakon su tsorata, sai wannan ya ƙara musu imani da dogaro ga Allah, suka ce: “Mu dai Allah ya ishe mu, kuma madalla da abin dogaro Allah.” Sai ga shi sun dawo daga wannan wurin da wata ni’ima daga Allah da falala, ba abin da ya same su na cutarwa daga ɓangaren maƙiyansu, kuma sun bi yardar Allah lokacin da suka karɓa kiran Allah da Manzonsa, suka sake fitowa. Allah ma’abocin falala ne wadda take mai girma. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan da yake tsoratar da su ba wani ne ba Shaiɗan ne, kuma yana so ne ya shuka tsoron jama’arsa mushirikai a zukatan muminai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce, kar wanda ya ji tsoron mushirikai; Allah kaɗai za su ji tsoro idan har su muminai ne.

  177. إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلۡكُفۡرَ بِٱلۡإِيمَٰنِ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 3:177

    Lalle waɗanda suka musanya imani da kafirci ba za su cutar da Allah da komai ba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi.

  178. وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّمَا نُمۡلِي لَهُمۡ خَيۡرٞ لِّأَنفُسِهِمۡۚ إِنَّمَا نُمۡلِي لَهُمۡ لِيَزۡدَادُوٓاْ إِثۡمٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

    Open ayah 3:178

    Kuma waɗanda suka kafirta kar su yi tsammanin cewa, jinkiri da Muke yi musu wani alheri ne ga kawunansu. Ai Muna saurara musu ne kawai don su ƙara laifi (a kan laifinsu). Kuma suna da azaba mai wulaƙantarwa.

  179. مَّا كَانَ ٱللَّهُ لِيَذَرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ عَلَىٰ مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ حَتَّىٰ يَمِيزَ ٱلۡخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُطۡلِعَكُمۡ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَجۡتَبِي مِن رُّسُلِهِۦ مَن يَشَآءُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۚ وَإِن تُؤۡمِنُواْ وَتَتَّقُواْ فَلَكُمۡ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

    Open ayah 3:179

    Da ɗai Allah ba zai ƙyale muminai a yadda kuke ɗin nan ba har sai Ya rarrabe tsakanin lalatacce da kyakkyawa. Kuma Allah ba zai sanar da ku gaibu ba, sai dai Allah Yana zaɓar wanda Ya so cikin manzanninsa ne; don haka ku ƙara yin imani da Allah da manzanninsa. Idan kun yi imani, kun yi taƙawa kuwa, to kuna da lada mai girma.

  180. وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ هُوَ خَيۡرٗا لَّهُمۖ بَلۡ هُوَ شَرّٞ لَّهُمۡۖ سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُواْ بِهِۦ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ 

    Open ayah 3:180

    Kuma waɗanda suke yin rowar abin da Allah Ya ba su na falalarsa kar su yi tsammanin hakan alheri ne a gare su; a’a, hakan sharri ne a gare su; da sannu za a yi musu saƙandami da abin da suka yi rowa da shi a ranar alƙiyama. Kuma Allah Shi ne Mai gadon sammai da ƙasa. Kuma Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin waɗanda suka musanya imani da kafirci cewa, ba za su cuci Allah da komai ba; kawunansu kaɗai za su cuta, domin za su cancanci uƙubar Allah ne mai tsanani. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabinsa (ﷺ) cewa, kada ya yi zato, su ma kafirai kar su yi zaton rashin gaggauto musu da azabar Allah da ƙyale su suna more rayuwarsu yadda suke so, su ɗauka wannan falala ko alheri Ubangiji yake yi musu; Allah ya yi musu haka ne don su ƙara ɗaukar wa kawunansu wasu tarin laifuka, sannan za su fuskanci azaba mai wulaƙantarwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, ba ya daga cikin hikimarsa ya ƙyale muminai da munafuƙai su ci gaba da zama a gauraye, ba tare da ya ware kowanne daga cikinsu ba. Dole ne a sami jarrabawa iri-iri wadda ta hanyarta ne za a gane mumini na gaskiya, kuma a gane munafuƙi. Hakanan ba ya daga cikin hikimar Allah, ya bayyana wa wani abin da yake cikin zukatan bayinsa, har ya iya gane muminai da munafuƙai; sai dai Allah ya kawo wata jarrabawa wadda ta hanyarta ne zai bambance tsakanin mumini da munafuƙi. Amma duk da haka Allah yakan zaɓi wasu manzanni nasa ya sanar da su wani gaibu da izininsa da yardarsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su ƙara tabbata a kan imani da Allah da manzanninsa, ya kuma yi musu alƙawarin idan har sun yi hakan, to suna da wani lada mai girma. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Annabinsa (ﷺ), da cewa, waɗanda suke rowa da dukiyar da Allah ya ba su daga falalarsa, kada su yi tsammani wannan rowar alheri ne gare su; a’a, sharri ne gare su, domin Allah ya yi musu tanadin azaba mai tsanani, wadda a lahira zai mayar musu da wannan dukiyar wani saƙandami, watau abin wuya na wutar Jahannama da zai rataya musu a wuyoyinsu, a yi ta yi musu azaba da shi ba ƙaƙƙautawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, sammai da ƙasa duk nasa ne, don haka duk abin da halittunsa suka mallaka zai koma gare shi ne bayan sun halaka, shi zai gaje shi, kuma Allah yana da cikakken sanin bayinsa, kuma zai saka wa kowa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk wanda Allah ya ba shi dukiya bai fitar da zakka ba, to ranar alƙiyama za a mayar da wannan dukiyar wani tsohon kumurci mai koɗaɗɗen kai da ɗigon baƙi a idanunsa, a rataya masa shi, ya riƙa fincikar haɓarsa yana cewa: “Ni ne dukiyarka, ni ne ajiyayyar taskarka.” Sannan Annabi (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: “Kuma waɗanda suke yin rowa da abin da Allah ya ba su na falalarsa, kar su yi tsammanin hakan alheri ne a gare su….” [Bukhari #4565].

  181. لَّقَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ فَقِيرٞ وَنَحۡنُ أَغۡنِيَآءُۘ سَنَكۡتُبُ مَا قَالُواْ وَقَتۡلَهُمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَنَقُولُ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

    Open ayah 3:181

    Tabbas haƙiƙa Allah ya ji maganar waɗannan da suka ce: “Lalle Allah mataulaci ne, mu ne mawadata.” Da sannu za Mu rubuta abin da suka faɗa, da kuma kisan da suka dinga yi wa annabawa ba tare da wani haƙƙi ba, kuma za Mu ce: “Ku ɗanɗani azaba mai ƙuna.

  182. ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّامٖ لِّلۡعَبِيدِ

    Open ayah 3:182

    “Wannan kuwa, saboda abin da hannayenku suka gabatar ne, kuma lalle Allah ba mai zaluntar bayinsa ne ba.”

  183. ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ عَهِدَ إِلَيۡنَآ أَلَّا نُؤۡمِنَ لِرَسُولٍ حَتَّىٰ يَأۡتِيَنَا بِقُرۡبَانٖ تَأۡكُلُهُ ٱلنَّارُۗ قُلۡ قَدۡ جَآءَكُمۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِي بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَبِٱلَّذِي قُلۡتُمۡ فَلِمَ قَتَلۡتُمُوهُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 3:183

    Su ne waɗanda suka ce: “Lalle Allah Ya yi alƙawari da mu kar mu yarda da kowane manzo har sai ya zo mana da wata sadaka wadda wuta za ta cinye ta.” Ka ce: “Haƙiƙa manzanni sun zo muku tun kafin ni, da hujjoji da kuma abin da kuka ce ɗin, to don me kuka kashe su in kun kasance masu gaskiya?”

  184. فَإِن كَذَّبُوكَ فَقَدۡ كُذِّبَ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَ جَآءُو بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُنِيرِ

    Open ayah 3:184

    To idan sun ƙaryata ka, to haƙiƙa an ƙaryata manzanni kafinka, waɗanda suka zo da hujjoji da littattafai da Littafi mai haskakawa. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, ya ji irin rashin kunyar da Yahudawa suka yi wa Allah suna cewa, wai Allah shi ne matalauci, su kuma mawadata ne. Allah ya tabbatar musu cewa, zai rubuta waɗannan miyagun maganganu nasu, har ma da ta’asar da suka yi ta kashe annabawa ba da wani haƙƙi ba, sannan ranar alƙiyama zai ce musu: Ku ɗanɗani azabar wuta mai ƙuna, saboda laifukan da kuka aikata a duniya, kuma Allah ba mai zaluntar bayinsa ne ba. Dalilin saukar wannan ayar shi ne, kamar yadda Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito cewa: Wata rana Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya ce wa wani babban malamin Yahudawa, mai suna Finhasu, cewa: “Ka ji tsoron Allah ka musulunta. Wallahi ka san cewa, Annabi (ﷺ) Manzo ne daga Allah, ya zo muku da gaskiya daga gare shi, kuma kun karanta siffofinsa a cikin Littafin Attaura da Linjila.” Sai Finhasu ya ce: “Ya Ababakar, mu fa ba mu da wata buƙata a wurin Allah, shi ne ma yake da buƙata a wurinmu, kuma mu ba ma marairaice masa, kamar yadda shi yake marairaice mana. Mu mun wadatu, ba mu da wata buƙata a wurinsa, kuma shi ma da ya wadatu, ba shi da wata buƙata a wurinmu, to da bai karɓi rance a wurinmu ba, kamar yadda mutumin naku yake riyawa. Shi ya hana ku ci riba, shi kuma yana ba mu, da ba ya da buƙatarmu, da bai ba mu riba ba.” Sai Sayyidina Abubakar ya fusata, har ya mari Finhasu, sai Finhasu ya je ya faɗa wa Manzon Allah (ﷺ) cewa, Abubakar ya mare shi. Sai Annabi (ﷺ) ya tambayi Abubakar, me ya sa ya yi haka? Sai Abubakar ya faɗa masa duk abin da ya faru. Sai Finhasu ya musanta, ya ce shi bai faɗi haka ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar: “Tabbas haƙiƙa, Allah ya ji maganar waɗanda suka ce lalle Allah matalauci ne, mu ne mawadata....” [Aɗ-Ɗabari 7:441]. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fallasa wata ƙaryar ta Yahudawa, wadda suka yi da’awar cewa, Allah ya yi musu wasiyya da kada su yi imani da wani Manzo har sai ya zo musu da wata sadaka wadda wuta za ta zo ta cinye ta a gabansu suna gani, sannan ne za su yarda shi Manzon Allah ne, su yi imani da shi. Sai Allah ya umarci Annabinsa ya mayar musu martani da cewa, ai akwai manzanni da yawa a gabaninsu, waɗanda suka zaike wa jama’arsu suna ɗauke da mu’ujizoji da dama, waɗanda suka haɗa har da irin wannan mu’ujizar da suka nema, to amma sai ba su yi imani ba. Hasali ma kashe wasu annabawan suka yi. To don me suka kashe su, in har da gaske suke cewa, Allah ya umarce su da kada su yi imani sai da wanda ya zo musu da irin wannan mu’ujizar? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Annabinsa da kada ya damu don ƙaryatawar da waɗannan Yahudawan suke yi masa, domin ba shi ne farau ba; manzanni da dama da suka gabace shi, sun zo da mu’ujizoji da littattafai da aka saukar musu, waɗanda ke ɗauke da wa’azuzzuka da nasihu masu ratsa zukata.

  185. كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ أُجُورَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ فَمَن زُحۡزِحَ عَنِ ٱلنَّارِ وَأُدۡخِلَ ٱلۡجَنَّةَ فَقَدۡ فَازَۗ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ

    Open ayah 3:185

    Kowane rai zai ɗanɗani mutuwa. Kuma a ranar alƙiyama ne za a cika muku ladan ayyukanku; to duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to haƙiƙa ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daɗi mai ruɗarwa.

  186. ۞لَتُبۡلَوُنَّ فِيٓ أَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡ وَلَتَسۡمَعُنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَذٗى كَثِيرٗاۚ وَإِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

    Open ayah 3:186

    Lalle za a jarrabe ku a cikin dukiyoyinku da rayukanku, kuma lalle za ku riƙa jin cutarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littafi kafinku, haka kuma daga waɗanda suke mushirikai. Amma idan har kuka yi haƙuri, kuma kuka tsare dokar Allah, to lalle wannan yana daga cikin manyan al’amura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, kowane rai dole ne sai ya mutu, kuma Allah ne ke yi wa kowa cikakken sakamako na aikinsa ranar gobe ƙiyama. To duk wanda aka tserar da shi daga shiga wuta, sannan aka shigar da shi Aljanna, to haƙiƙa wannan mutum ya rabauta. Kuma rayuwar duniya wani ɗan jin daɗi ne ƙanƙani, mai gushewa da gaggawa bayan ya ruɗi ma’abocinsa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle gurbin bulala a Aljanna ya fi duniya da abin da yake cikinta. Ku karanta wannan ayar in kun ga dama: “To duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to haƙiƙa ya rabauta, kuma rayuwar duniya ba komai ba ce, face ɗan jin daɗi mai ruɗarwa.” [Tirmizi #3013, da Nasa’i, As-Sunan Alkubra #11085]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa muminai cewa za a jarrabe su da aukawar masifu a dukiyoyinsu, ta hanyar lalacewarsu ko hasarar kasuwanci, kuma za a jarrabe su a rayukansu, ta hanyar mutuwa ko kisa ko samun raunuka ko rashin lafiya. Sannan kuma za su dinga jin maganganu na cutarwa da gallazawa daga maƙiyansu waɗanda aka ba wa Littafi gabaninsu, wato Yahudawa da Nasara, da kuma mushirikai, saboda za su riƙa zagin su, suna sukar addininsu, suna jifar su da tuhumce-tuhumce iri-iri da yin izgili ga shari’arsu. To amma idan sun yi haƙuri a kan hakan, kuma suka kiyaye dokokin Allah, to yin hakan yana daga cikin manyan al’amura da suke buƙatar juriya da himma.

  187. وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَتُبَيِّنُنَّهُۥ لِلنَّاسِ وَلَا تَكۡتُمُونَهُۥ فَنَبَذُوهُ وَرَآءَ ظُهُورِهِمۡ وَٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلٗاۖ فَبِئۡسَ مَا يَشۡتَرُونَ

    Open ayah 3:187

    Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya ɗauki alƙawari daga waɗanda aka bai wa Littafi cewa: “Lalle ku bayyana shi ga mutane, kuma kada ku ɓoye shi.” Sai suka jefar da shi can bayansu, kuma suka musanya shi da wani ɗan farashi ƙanƙani. To tir da abin da suke yin musanye da shi

  188. لَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أَتَواْ وَّيُحِبُّونَ أَن يُحۡمَدُواْ بِمَا لَمۡ يَفۡعَلُواْ فَلَا تَحۡسَبَنَّهُم بِمَفَازَةٖ مِّنَ ٱلۡعَذَابِۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 3:188

    Kada ka yi tsammanin waɗanda suke yin farin ciki da irin abin da suka aikata, kuma suna son a riƙa yabon su da abin da ba su aikata ba, to kada ka yi tsammanin za su tsira daga azaba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tuna wa Annabinsa (ﷺ) wani mummunan aiki na Yahudawa da Nasara, lokacin da Allah ya yi ƙaƙƙarfan alƙawari da su na cewa, za su fito su bayyana wa mutane abin da yake cikin littattafan da aka saukar wa annabawansu, kuma ba za su ɓoye komai daga ciki ba. Daga ciki kuwa har da siffofin Annabi (ﷺ) da suka zo a Attaura da Linjila; to amma sai suka saɓa wannan alƙawari, suka ɓoye waɗannan siffofin Annabi (ﷺ), ba don komai ba, sai don ɗan abin da za su samu na duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da irin wannan aiki nasu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk wanda aka yi masa tambaya ta ilimi, sannan ya ɓoye, to za a sa masa linzamin wuta ranar gobe ƙiyama.” [Abu Dawud #3658, da Tirmizi #2649, da Ibnu Maja #266]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, kada ya yi zaton mutanen da suke farin ciki da miyagun ayyukan da suka yi na ɓoye ilimin da Allah ya ba su, kuma suke son a riƙa yaba musu a kan aikin da ba su yi ba, kada ya yi zaton waɗannan mutane za su tsira daga azabar Allah ranar alƙiyama; tabbas suna da wata azaba mai raɗaɗi. An karɓo daga Abu Sa’id Alkhudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu munafuƙai duk sanda Annabi (ﷺ) ya fita yaƙi, sai su noƙe su ƙi fita tare da shi, kuma su riƙa farin ciki da hakan. Idan Annabi (ﷺ) ya dawo daga yaƙi, sai su je suna rantsuwa, suna faɗar hanzari na ƙarya, sannan kuma su riƙa son a yabe su da aikin da ba su yi ba, sai wannan ayar ta sauka: “Kada ku yi tsammanin waɗanda suke farin ciki da abin da suka yi, kuma suna son a riƙa yabon su da abin da ba su aikata ba....” [Bukhari #4567, da Muslim #2777].

  189. وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

    Open ayah 3:189

    Kuma ga Allah ne mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai.

  190. إِنَّ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ 

    Open ayah 3:190

    Lalle a cikin halittar sammai da ƙasa da sassaɓawar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma’abota hankula.

  191. ٱلَّذِينَ يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ قِيَٰمٗا وَقُعُودٗا وَعَلَىٰ جُنُوبِهِمۡ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ رَبَّنَا مَا خَلَقۡتَ هَٰذَا بَٰطِلٗا سُبۡحَٰنَكَ فَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ

    Open ayah 3:191

    Su ne waɗanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma zaune da kuma kishingiɗe, suna kuma tunani a kan halittar sammai da ƙasa, (suna cewa): “Ya Ubangijinmu, ba Ka halicci wannan a banza ba, tsarki ya tabbata gare Ka, Ka tserar da mu daga azabar wuta.

  192. رَبَّنَآ إِنَّكَ مَن تُدۡخِلِ ٱلنَّارَ فَقَدۡ أَخۡزَيۡتَهُۥۖ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ

    Open ayah 3:192

    “Ya Ubangijinmu, lalle duk wanda Ka shigar da shi wuta, to haƙiƙa Ka kunyata shi; kuma azzalumai ba su da mai taimakon su.

  193. رَّبَّنَآ إِنَّنَا سَمِعۡنَا مُنَادِيٗا يُنَادِي لِلۡإِيمَٰنِ أَنۡ ءَامِنُواْ بِرَبِّكُمۡ فَـَٔامَنَّاۚ رَبَّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرۡ عَنَّا سَيِّـَٔاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ ٱلۡأَبۡرَارِ

    Open ayah 3:193

    “Ya Ubangijinmu, lalle mu mun ji wani mai kira yana yin kira zuwa imani cewa: “Ku yi imani da Ubangijinku;” sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare mana kurakuranmu, kuma Ka karɓi rayukanmu tare da mutane masu ɗa’a.

  194. رَبَّنَا وَءَاتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَىٰ رُسُلِكَ وَلَا تُخۡزِنَا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ إِنَّكَ لَا تُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ

    Open ayah 3:194

    “Ya Ubangijinmu, kuma Ka ba mu abin da Ka yi mana alƙawari da shi ta harshen manzanninka, kuma kada Ka kunyatar da mu ranar alƙiyama. Lalle Kai ba Ka saɓa alƙawari.”

  195. فَٱسۡتَجَابَ لَهُمۡ رَبُّهُمۡ أَنِّي لَآ أُضِيعُ عَمَلَ عَٰمِلٖ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰۖ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۖ فَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَٰتَلُواْ وَقُتِلُواْ لَأُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ ثَوَابٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلثَّوَابِ

    Open ayah 3:195

    Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): “Lalle Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashinku yana tare da sashe. To waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su wajen bin tafarkina kuma suka yi yaƙi kuma aka kashe su, lalle zan kankare musu kurakuransu, kuma lalle zan shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Wannan lada ne daga wajen Allah, kuma a wurin Allah ne mafi kyawun lada yake.” A cikin waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, shi kaɗai ne mai mulkin sammai da ƙasa da abin da yake cikinsu, kuma shi ne mai cikakken iko a kan komai. Sannan ya sanar da cewa, a cikin halittar sammai da ƙasa da abubuwan da suka ƙunsa da cancanzawar dare da rana, wannan ya zo, wannan ya tafi, lalle akwai manya-manyan ayoyi da dalilai ga masu lafiyayyen hankali, da suke tabbatar da samuwar Mahalicci da siffofinsa. Waɗannan kuwa su ne masu ambaton Allah koyaushe, a cikin kowane yanayi, a tsaye suke ko a zaune ko a kwance. Suna tunani game da halittar sammai da ƙasa, suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani ba ka yi wannan halittar a banza ba; ka tsarkaka daga yin wannan, don haka ka tsare mu daga azabar wuta; duk kuwa wanda ka saka shi cikinta, to tabbas ka tozartar da shi, kuma azzalumai ba su da masu taimaka musu.” Suka ci gaba da cewa: “Ya Ubangijinmu, mun ji Annabinka yana kira zuwa ga yin imani da kai, kuma mun amsa kiransa, mun yi imani, don haka ka gafarta mana laifukanmu, kuma ka kankakre mana munanan ayyukanmu, kuma ka karɓi rayukanmu tare da mutanen kirki. Ya Ubangijinmu, alƙawarin da ka yi ta harshen manzanninka, na ba mu kyakkyawan sakamako ka zartar da shi, kada kuma ka kunyata mu a ranar alƙiyama a gaban halittunka; lalle mun tabbatar ba ka saɓa alƙawari.” Sai ko Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya karɓi wannan roƙo nasu, kuma ya yi alƙawarin ba zai taɓa tozarta aikin mai aiki ba, namiji ne shi ko mace ce. Don haka waɗanda suka baro garuruwansu na kafirci ko kuma kafirai suka koro su, aka cutar da su saboda sun riƙe gaskiya, sun yi imani da Allah da Manzonsa, suka kuma yi yaƙi don Allah, kuma aka kashe su, to waɗannan Allah zai kankare musu laifukansu, kuma zai saka su gidajen Aljanna, waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; wannan babban sakamako ne a gare su, saboda ƙoƙarin da suka yi na aikin alheri a duniya. Allah shi ne mai kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya yi aikin ƙwarai; zai saka masa da abin da ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, zuciyar wani ɗan’adam ba ta taɓa tunaninsa ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani dare na kwana a ɗakin Maimuna uwar muminai (Allah ya kara mata yarda), kuma a ranar Annabi (ﷺ) yana ɗakinta, domin in ga yadda yake sallarsa ta dare. Annabi (ﷺ) ya yi hira da iyalinsa na wani ɗan lokaci, sannan ya kwanta ya yi barci. A sulusin ƙarshe na dare, sai ya tashi zaune, ya ɗaga kai sama, sai ya karanta wannan aya (aya ta 190), sannan ya tashi ya yi alwala, ya yi asiwaki, sannan ya yi salla raka’a goma sha ɗaya, sannan Bilal ya kira sallar Asuba. Sai Annabi (ﷺ) ya sallaci raka’a biyu, sannan ya fita ya jagoranci sallar Asuba. [Bukhari #7452].

  196. لَا يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ

    Open ayah 3:196

    Kada zirga-zirgar kafirai a cikin garuruwa ta ruɗe ka.

  197. مَتَٰعٞ قَلِيلٞ ثُمَّ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

    Open ayah 3:197

    Wani ɗan jin daɗi ne ƙanƙani, sannan makomarsu Jahannama. Kuma tir da wannan shimfiɗar.

  198. لَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ لَهُمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا نُزُلٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۗ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّلۡأَبۡرَارِ

    Open ayah 3:198

    Amma waɗanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan liyafa ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mafi alheri ga masu biyayya.

  199. وَإِنَّ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَمَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِمۡ خَٰشِعِينَ لِلَّهِ لَا يَشۡتَرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 3:199

    Kuma lalle a cikin Ma’abota Littafi, tabbas akwai waɗanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu ƙasƙantar da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani ɗan farashi ƙanƙani. Waɗannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne.

  200. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱصۡبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ 

    Open ayah 3:200

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi haƙuri, kuma ku jure matuƙa ga yin haƙuri, kuma ku tsare iyakokin ƙasa, kuma ku kiyaye dokokin Allah don ku sami rabauta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa Annabinsa (ﷺ) kashedi da ruɗuwa da kai-komon kafirai a duniya da tinƙahon da suke yi da bunƙasar harkar kasuwanci da ƙarfin tattalin arziki da ƙarfin sojoji. Duk waɗannan wani ɗan taƙaitaccen jin daɗi ne; nan da nan zai ƙare, sannan daga ƙarshe wutar jahannama ce makomarsu tir kuwa da irin wannan makoma. To amma masu bin dokokin Ubangijinsu ta hanyar aikata abin da ya wajabta musu da barin abin da ya haramta musu; to an tanadar musu gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, kuma su zauna cikinsu har abada. Wannan wata liyafa ce Allah ya shirya musu. Don haka abin da yake wurin Allah na kyakkyawan sakamako ga waɗanda suka bi shi, ya fi alheri fiye da wani ɗan gajeren jin daɗi na duniya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a cikin Ma’abota Littafi akwai waɗanda sun yi imani da Allah, suna kaɗaita shi da bauta, kuma sun yi imani da Manzonsa da Alƙur’anin da aka saukar masa da kuma littattafan da aka saukar musu, suna masu ƙasƙantar da kansu ga Allah, ba sa canza abin da yake cikin littattafansu, ba sa kuma ɓoye gaskiyar da take ciki, domin samun ɗan wani taƙaitaccen jin daɗi na duniya; to waɗannan suna da babban sakamako a wurin Allah (Mai tsarki da daukaka). Lalle kuma Allah mai gaggawar sakamako ne. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da labarin rasuwar Najashi ta zo mana, Annabi (ﷺ) ya ce mana: “Ku yi masa salla.” Sai sahabbai suka ce: “Yanzu ma yi wa wani bawa mutumin Habasha salla?” Sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Kuma lalle cikin ma’abota Littafi, tabbas akwai waɗanda suka yi imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu ƙasƙantar da kansu ga Allah.” [An-Nasa’i, As-Sunanul Kubra #11088, da Bazzar #6556]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa muminai da yin haƙuri da kuma dauriya a kan rinjayar maƙiya addinin Allah, su jajirce har su ma su sami nasara a kan maƙiyansu kuma su tsare kan iyakokin da ake tsoron shigowar maƙiya daga gare su, sannan su kiyaye dokokin Allah, ta hanyar aikata umarninsa da barin haninsa; da wannan ne za su sami rabauta duniya da lahira.