النساء

An-Nisaa

The Women · Surah 4 · Ayahs: 176 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَخَلَقَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَبَثَّ مِنۡهُمَا رِجَالٗا كَثِيرٗا وَنِسَآءٗۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِي تَسَآءَلُونَ بِهِۦ وَٱلۡأَرۡحَامَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَيۡكُمۡ رَقِيبٗا

    Open ayah 4:1

    <b>Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai </b> 1. Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku Wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma Ya halicci matarsa daga shi, kuma Ya yaɗa maza da mata masu yawa daga gare su. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda kuke yi wa juna magiya da Shi, kuma ku kiyaye (yanke) zumunci. Lalle Allah Mai kula da ku ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da umartar mutane gaba ɗaya da su ji tsoron Ubangijinsu, su kiyaye dokokin da ya gindaya musu a Littafinsa mai tsarki, ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi da barin abin da ya hana, domin shi ne mahaliccinsu, mamallakinsu, wanda yake kula da rayuwarsu. Ya halicce su ne gaba ɗayansu daga rai guda ɗaya, shi ne Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kuma daga wannan rai ya halicci abokiyar haɗinsa, wato Hauwa’u; ta hanyarsu kuma ya yaɗa mutane masu yawa maza da mata a bayan ƙasa. Ya sake umartar su kuma da su kiyaye dokokin Allah wanda da sunansa ne suke yi wa juna magiya, sannan su kula da haƙƙin sada zumunci, kada su yanke shi, domin shi ma yana da girma a wurin Allah, Allah kuma yana ganin duk ayyukansu, kuma zai saka musu a kansu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce; “Ku yi wasiyya da kulawa da mata, domin mace an halicce ta ne daga ƙashin haƙarƙari, kuma inda ya fi tanƙwara a haƙarƙari shi ne na samansa; idan ka ce sai ka miƙar da shi, to za ka karya shi, idan ka ƙyale shi, to zai ci gaba da zama a tanƙware, don haka ku yi wasiyyar kula da mata.” [Bukhari #3331, da Muslim #1468].

  2. وَءَاتُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰٓ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَتَبَدَّلُواْ ٱلۡخَبِيثَ بِٱلطَّيِّبِۖ وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَهُمۡ إِلَىٰٓ أَمۡوَٰلِكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حُوبٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 4:2

    Kuma ku bai wa marayu dukiyoyinsu; kuma kada ku musanya kyakkyawa da mummuna; kuma kada ku ci dukiyoyinsu haɗe da dukiyoyinku. Lalle yin hakan ya tabbata zunubi ne mai girma.

  3. وَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تُقۡسِطُواْ فِي ٱلۡيَتَٰمَىٰ فَٱنكِحُواْ مَا طَابَ لَكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ مَثۡنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تَعۡدِلُواْ فَوَٰحِدَةً أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَعُولُواْ

    Open ayah 4:3

    Kuma idan kun ji tsoron cewa ba za ku iya yin adalci ba dangane da marayu, to ku auri matan da kuke so, ko dai bibbiyu ko uku-uku ko kuma hurhuɗu. To idan kun ji tsoron ba za ku iya yin adalci ba, to sai ku taƙaita a kan ɗaya ko kuma abin da kuka mallaka na ƙwarƙwarori. Hakan shi ya fi nisanta ku daga zalunci.

  4. وَءَاتُواْ ٱلنِّسَآءَ صَدُقَٰتِهِنَّ نِحۡلَةٗۚ فَإِن طِبۡنَ لَكُمۡ عَن شَيۡءٖ مِّنۡهُ نَفۡسٗا فَكُلُوهُ هَنِيٓـٔٗا مَّرِيٓـٔٗا

    Open ayah 4:4

    Kuma ku bai wa mata sadakinsu kyauta. Amma idan suka ba ku wani abu cikin daɗin rai, to ku ci shi yana mai daɗi da sauƙin haɗiya.

  5. وَلَا تُؤۡتُواْ ٱلسُّفَهَآءَ أَمۡوَٰلَكُمُ ٱلَّتِي جَعَلَ ٱللَّهُ لَكُمۡ قِيَٰمٗا وَٱرۡزُقُوهُمۡ فِيهَا وَٱكۡسُوهُمۡ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

    Open ayah 4:5

    Kuma kada ku bai wa (marayu) wawaye dukiyoyinku wadda Allah Ya sanya rayuwarku take tsaye a kai, kuma ku ciyar da su, kuma ku tufatar da su daga cikinta, kuma ku faɗa musu magana mai daɗi.

  6. وَٱبۡتَلُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغُواْ ٱلنِّكَاحَ فَإِنۡ ءَانَسۡتُم مِّنۡهُمۡ رُشۡدٗا فَٱدۡفَعُوٓاْ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَأۡكُلُوهَآ إِسۡرَافٗا وَبِدَارًا أَن يَكۡبَرُواْۚ وَمَن كَانَ غَنِيّٗا فَلۡيَسۡتَعۡفِفۡۖ وَمَن كَانَ فَقِيرٗا فَلۡيَأۡكُلۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِذَا دَفَعۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡ فَأَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ حَسِيبٗا

    Open ayah 4:6

    Kuma ku jarraba hankulan marayu, har lokacin da suka isa aure, to idan kun ga alamar hankali tare da su, sai ku ba su dukiyoyinsu; kuma kada ku ci dukiyarsu ta hanyar almubazzaranci da kuma gaggawa don gudun kada su girma. Duk kuma wanda ya kasance mawadaci ne, to ya kame kansa; wanda kuma ya kasance mabuƙaci ne, to ya ci ta hanyar da ta dace. To idan za ku miƙa musu dukiyoyinsu, sai ku kafa musu shaidu. Kuma Allah Ya isa Mai hisabi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin haƙƙoƙin marayu da kulawa da dukiyoyinsu har lokacin da za su balaga su yi hankali. Maraya shi ne duk wani yaro ko yarinya da suka rasa iyayensu maza, sannan ba su balaga ba. ‘Ya mace tana da buƙatar kulawa har ta sami mijin aure. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci waɗanda kula da marayu ta rataya a wuyansu da cewa, su mayar musu da dukiyarsu da take hannuwansu gaba ɗaya da zarar sun balaga, kuma an ga alamun hankali tare da su. Ya hana su cin dukiyar maraya ba da wani haƙƙi ba, ko su musanya da dukiyar maraya mai inganci da tasu marar inganci, don sun ga shi yaro ne ba zai iya fahimta ba. Hakanan ya haramta musu su haɗa dukiyarsu da ta marayun da suke ƙarƙashinsu da niyyar su cinye musu ita ba bisa gaskiya ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce yin haka zalunci ne mai girma. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kuma yi magana a kan wani abu da ya riƙa faruwa a lokacin jahiliyya, dangane da ‘ya’ya mata marayu. Kamar mutum an bar masa wasiyyar wata marainiya da iyayenta suka bar mata dukiya mai yawa, sai wannan mutum saboda kwaɗayin dukiyarta, sai ya aure ta ba don yana son ta ba, sai don ya mallake mata dukiya, kamar yadda A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta yi bayani [Dubi Bukhari #4573 da Muslim #3018]. Ko kuma mutumin da marainiya take ƙarƙashinsa, sai ya yi kwaɗayin aurenta saboda dukiyarta, amma kuma ba ya son ya ba ta cikakken sadakin da ya dace da ita, sai Allah ya hana shi ya aure ta har sai idan zai yi mata adalci ya ba ta cikakken sadakinta. [Dubi Bukhari #4575]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da cewa, idan ba za su iya adalci ga mata marayu da suke ƙarƙashinsu ba, ba za su iya ba su cikakken sadakinsu ba, ko kuma ba za su kula da haƙƙoƙinsu ba, to su je su auri wasu matan da zukatansu suka kwanta musu da su; suna iya auren mata biyu ko uku ko huɗu. Su ma idan sun ga ba za su iya yin adalci a tsakaninsu ba, to su tsaya a kan auren mace ɗaya, ko ma su taƙaita a kan ƙwarƙwarorinsu, domin su ƙwarƙwarori babu rabon kwana a tsakaninsu. Taƙaitawa a kan mace ɗaya ko ƙwarƙwara ya fi kusa da tabbatar da adalci da kauce wa zalunci. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga maza da su ba wa mata sadakin aurensu wanda Allah ya wajabta a ba su idan an aure su. To amma idan su matan ne suka bar musu wani abu daga sadakinsu a matsayin kyauta, don ganin damarsu ba tare da an matsa musu ba, to su karɓa su ci, babu wata matsala. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana lokacin da bai dace a ba wa maraya wawa marar nutsuwa dukiyarsa ba yayin da ya umarci masu kula da su cewa kada su bayar da dukiyarsu wadda Allah ya sanya a hannunsu ga wani maraya wanda bai san yadda ya kamata ya kula da ita ba, saboda ƙuruciya ko rashin wayo, ko wani dalili. Lalle su tsaya su kula musu da dukiyarsu kamar yadda suke kula da tasu. Kuma su ciyar da su, su shayar da su, su tufatar da su daga cikinta, sannan su faɗa musu magana mai daɗi yayin da suka nuna buƙatar a ba su dukiyarsu. Suna iya sanar da su cewa sai sun yi wayo sannan ne za su ba su dukiyarsu gaba ɗaya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni cewa masu kula da marayu su jarraba hankulansu, idan sun ga alamar hankali tare da su bayan sun kai shekarun balaga, to su mayar musu da dukiyoyinsu gaba ɗaya. Hakanan kada su riƙa ɗiban dukiyarsu ba tare da wata buƙata ba har su ƙetare iyakar da Allah ya halatta musu. Kada kuma su yi gaggawar ci musu dukiya wai don gudun kada su girma su karɓe dukiyar su hana su komai daga cikinta. Allah kuma ya bayyana cewa, mai kula da dukiyar maraya, idan yana da wadata ba mabuƙacin komai ba ne daga wannan dukiyar, to ya yi kawaici kar ya taɓa wani abu na dukiyar ko da wanda aka halatta masa ne, kamar ladan kasuwanci da yake yi da wannan dukiya. Wanda kuwa yake mabuƙaci ne, to yana iya ɗiban wani abu daga dukiyar kamar ladan wahalar da yake yi a cikinta, gwargwadon abin da ya dace bisa ga yadda al’ada ta gudana. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Wannan ayar ta sauka ne game da mutumin da yake kula da maraya da dukiyarsa, to idan mabuƙaci ne sai ya ci daga wannan dukiyar gwargwadon yadda ya dace”. [Bukhari #2212 da Muslim #3019]. Har wa yau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da idan sun mayar wa marayu dukiyoyinsu gaba ɗaya, to su kafa shaida a kan hakan, don gudun samun wani saɓani nan gaba. Kuma Allah ya isa ya zama mai hisabi ga duk wani mai kula da dukiyar marayu, yana ganin duk abin da yake gudana har zuwa lokacin da zai miƙa dukiyar gaba ɗaya, don haka shi ma shaida ne game da abin da ya wakana.

  7. لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنۡهُ أَوۡ كَثُرَۚ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا

    Open ayah 4:7

    Mazaje suna da wani kaso daga abin da mahaifa da dangi mafiya kusanci suka bari, haka mata su ma suna da wani kaso cikin abin da mahaifa da dangi mafiya kusanci suka bari, daga abin da yake ɗan kaɗan ko mai yawa. Kaso ne wanda an riga an rarraba shi.

  8. وَإِذَا حَضَرَ ٱلۡقِسۡمَةَ أُوْلُواْ ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينُ فَٱرۡزُقُوهُم مِّنۡهُ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

    Open ayah 4:8

    Kuma idan dangi makusanta da marayu da mabuƙata suka halarci rabon gado, to ku arzurta su daga cikin wannan dukiya, kuma ku faɗa musu magana mai daɗi.

  9. وَلۡيَخۡشَ ٱلَّذِينَ لَوۡ تَرَكُواْ مِنۡ خَلۡفِهِمۡ ذُرِّيَّةٗ ضِعَٰفًا خَافُواْ عَلَيۡهِمۡ فَلۡيَتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡيَقُولُواْ قَوۡلٗا سَدِيدًا

    Open ayah 4:9

    Waɗanda suke jin tsoron za su mutu su bar ‘ya’ya raunana a bayansu, suna kuma jin tsoron a zalunce su, to su kiyaye dokokin Allah, kuma su faɗi magana ta daidai.

  10. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلۡيَتَٰمَىٰ ظُلۡمًا إِنَّمَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ نَارٗاۖ وَسَيَصۡلَوۡنَ سَعِيرٗا 

    Open ayah 4:10

    Lalle waɗanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci, wuta ce kawai suke ci a cikkunansu; kuma da sannu za su shiga wuta mai tsananin ƙuna. A nan kuma wani hukunci ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake bayyana wa wanda ya shafe abin da Larabawa suke yi a jahiliyya, na hana mata gado kwata-kwata. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, maza da mata duka suna gadon dukiyar da iyayensu ko ‘yan’uwansu suka mutu suka bari; kowa yana da kasonsa gwargwadon kusancinsa da mamacin; dukiyar da suka bari kaɗan ce ko mai yawa. Kuma wannan rabon da aka ambata ba na al’ada ne da za su yi shi kamar yadda suka ga dama ba; rabo ne wanda Allah ne da kansa ya yi shi, kuma ya wajabta aiki da shi. Idan wasu daga cikin dangin mamaci waɗanda ba su da gadonsa ko marayu ko miskinai suka halarci wurin rabon, to kada a ƙyale su su tafi ba tare da an yi musu wani ɗan hasafi ba; a ba su ɗan wani abu daga cikin wannan dukiyar ta fuskar ihsani da kyautatawa, domin su ma a daɗaɗa musu, sannan a faɗa musu magana mai daɗi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake nanata batun kiyaye haƙƙin marayu domin girman lamarinsu, yana mai umartar masu kula da dukiyoyin marayu da cewa, su ji tsoron Allah, su tsaya su kula da wannan amana da take hannayensu, su mu’amalanci waɗannan marayu kamar yadda suke so a mu’amalanci ‘ya’yansu raunana da za su mutu su bar su. Idan sun kyautata wa waɗannan, su ma za a kyautata wa ‘ya’yansu yayin da suka rasu suka bar su. Don haka su ji tsoron Allah su faɗi maganar da take ta daidai ce. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi alƙawarin narkon azaba ga masu cin dukiyoyin marayu ba bisa haƙƙi ba da cewa, suna cin wuta ne balbal a cikinsu, kuma za a ƙona su da wutar Sa’ira mai tsananin ƙuna. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku nisanci abubuwa masu halakarwa guda bakwai.” Sahabbai suka ce: “Waɗanne abubuwa ne?” Sai ya ce: “Shirka da Allah da sihiri da kashe rai wadda Allah ya haramta ba da haƙƙi ba da cin kuɗin riba da cin dukiyar maraya da gudu ranar yaƙi da yi wa mata muminai gafalallu ƙazafi.” [Bukhari #6807, da Muslim #89].

  11. يُوصِيكُمُ ٱللَّهُ فِيٓ أَوۡلَٰدِكُمۡۖ لِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۚ فَإِن كُنَّ نِسَآءٗ فَوۡقَ ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُنَّ ثُلُثَا مَا تَرَكَۖ وَإِن كَانَتۡ وَٰحِدَةٗ فَلَهَا ٱلنِّصۡفُۚ وَلِأَبَوَيۡهِ لِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن كَانَ لَهُۥ وَلَدٞۚ فَإِن لَّمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلَدٞ وَوَرِثَهُۥٓ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ ٱلثُّلُثُۚ فَإِن كَانَ لَهُۥٓ إِخۡوَةٞ فَلِأُمِّهِ ٱلسُّدُسُۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصِي بِهَآ أَوۡ دَيۡنٍۗ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُكُمۡ لَا تَدۡرُونَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ لَكُمۡ نَفۡعٗاۚ فَرِيضَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:11

    Allah Yana yi muku wasiyya game da ‘ya’yanku; namiji ɗaya yana da rabon ‘ya’ya mata biyu. Amma idan sun kasance mata ne biyu ko fiye da biyu, to suna da kaso biyu bisa uku na abin da ya bari; kuma idan ta kasance ‘ya ce guda ɗaya to tana da rabi. Kuma kowane ɗaya daga cikin mahaifansa biyu yana da kaso ɗaya bisa shida daga cikin abin da ya bari in ya kasance yana da ɗa ko ‘ya. Idan kuma ya kasance ba shi da ɗa ko ‘ya, kuma mahaifansa biyu ne za su ci gadonsa, to mahaifiyarsa tana da kaso ɗaya bisa uku. Amma idan yana da ‘yan’uwa, to mahaifiyarsa tana da kaso ɗaya bisa shida; bayan an fitar da wasiyyar da aka yi ko kuma bashi. Iyayenku da ‘ya’yanku, ba ku san daga cikinsu wane ne zai fi yi muku amfani ba. Rabo ne daga Allah. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai cikakkiyar hikima.

  12. ۞وَلَكُمۡ نِصۡفُ مَا تَرَكَ أَزۡوَٰجُكُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهُنَّ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَهُنَّ وَلَدٞ فَلَكُمُ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡنَۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصِينَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۚ وَلَهُنَّ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡتُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّكُمۡ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَكُمۡ وَلَدٞ فَلَهُنَّ ٱلثُّمُنُ مِمَّا تَرَكۡتُمۚ مِّنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ تُوصُونَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۗ وَإِن كَانَ رَجُلٞ يُورَثُ كَلَٰلَةً أَوِ ٱمۡرَأَةٞ وَلَهُۥٓ أَخٌ أَوۡ أُخۡتٞ فَلِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُۚ فَإِن كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِن ذَٰلِكَ فَهُمۡ شُرَكَآءُ فِي ٱلثُّلُثِۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصَىٰ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٍ غَيۡرَ مُضَآرّٖۚ وَصِيَّةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَلِيمٞ

    Open ayah 4:12

    Kuma kuna da rabin abin da matanku suka bari in ya kasance ba su da ɗa ko ‘ya, amma idan sun kasance suna da ɗa ko ‘ya, to kuna da kaso ɗaya bisa huɗu na abin da suka bari, bayan zartar da wasiyyar da suka yi ko kuma bashi. Kuma suna da kaso ɗaya bisa huɗu na abin da kuka bari, in ya kasance ba ku da ɗa ko ‘ya. Amma idan ya kasance kuna da ɗa ko ‘ya to (matanku) suna da kaso ɗaya cikin takwas na abin da kuka bari, bayan zartar da wasiyyar da kuka yi ko kuma bashi. Amma idan namiji ne za a gaje shi a matsayin kalala ko mace, kuma yana da ɗan’uwa guda ɗaya ko ‘yar’uwa guda ɗaya, to kowanne ɗaya yana da kaso ɗaya bisa shida. Amma idan sun fi haka yawa, to za su yi tarayya cikin kaso ɗaya bisa uku, bayan zartar da wasiyyar da aka yi ko kuma bashi, ba wanda zai cutar da (magadansa) ba. Allah Yana yi muku wasiyya matuƙar wasiyya. Allah kuma Mai cikakken sani ne, Mai haƙuri.

  13. تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

    Open ayah 4:13

    Waɗannan iyakoki ne na Allah. Wanda duk yake bin Allah da Manzonsa, to zai shigar da shi gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma wannan shi ne rabo mai girma.

  14. وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُۥ يُدۡخِلۡهُ نَارًا خَٰلِدٗا فِيهَا وَلَهُۥ عَذَابٞ مُّهِينٞ

    Open ayah 4:14

    Wanda kuma yake saɓa wa Allah da Manzonsa, yake kuma ƙetare iyakokinsa, to zai shigar da shi wuta, yana mai dawwama a cikinta, kuma yana da wata azaba mai wulaƙantarwa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin rabon gado ne filla-filla bayan ya yi bayaninsa a dunƙule a ayar da ta gabata. Allah ya kira wannan umarni da suna ‘wasiyya’, domin nuna girman sha’aninsa da muhimmancinsa. Larabawa a lokacin Jahiliyya suna hana mata da marasa ƙarfi kamar marayu gadonsu, sai Allah ya hana wannan zalunci, ya yi umarni a ba wa mace gado kamar yadda ake ba wa namiji gado, ko da kuwa ba a daidaita su wajen abin da ake ba su ba, kamar yadda ya hana cin dukiyar marayu. An karɓo daga Jabiru ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: Annabi (ﷺ) shi da Abubakar sun zo unguwar Banu Salima don su duba ni, ba ni da lafiya. Sai Annabi (ﷺ) ya same ni ba na cikin hayyacina, sai ya ce a kawo masa ruwan alwala, da aka kawo, ya yi alwala, sai ya zuba mini sauran a kaina sai na farfaɗo, sai na ce: “Me za ka umarce ni da in aikata dangane da dukiyata?” Sai wannan ayar ta sauka: “Allah yana yi muku wasiyya game da ‘ya’yanku….” [Bukhari #4577, da Muslim #1616]. An karɓo daga Jabiru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Matar Sa’ad ɗan Rabi’u (Allah ya kara masa yarda) ta zo wurin Annabi (ﷺ) tare da ‘ya’yanta mata biyu da suka haifa da Sa’ad, sai ta ce: “Ya Manzon Allah, waɗannan ‘ya’yan Sa’ad ɗan Rabi’u ne; babansu ya yi shahada a yaƙin Uhudu da ya fita tare da kai, to amma baffansu ya riƙe dukiyarsu, kuma ba wanda zai aure su sai idan suna da dukiya.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Allah zai yanke hukunci a kan haka.” Sai ayar gado ta sauka, sai Manzon Allah (ﷺ) ya aika wa baffansu ya zo, Annabi (ﷺ) ya ce masa: “Ka ba wa ‘ya’yan Sa’ad mata su biyu kaso biyu bisa uku na dukiyar, ita kuma mahaifiyarsu ka ba ta kaso ɗaya cikin takwas, sauran ka riƙe naka ne.” [Abu Dawud #2872, da Tirmizi #2029, da Ibn Maja #2720, da Ahmad #14840]. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda rabon gadon zai kasance, da kason kowa daga cikin magada. Idan mamaci ya mutu ya bar ‘ya’ya maza da mata, to za a ba namiji rabo daidai da na ‘ya’ya mata biyu, idan kuma mamaci ya bar ‘ya’ya mata ne zalla daga biyu abin da ya yi sama, to za a ba su kaso biyu bisa uku na abin da mamaci ya bari. Idan kuwa ‘ya mace ce ɗaya kawai ya bari, to tana da rabin abin da ya bari. Idan kuma ya rasu ne ya bar ‘ya’yansa da iyayensa biyu, to uwa da uba kowannensu za a ba shi kaso ɗaya cikin shida, su kuma ‘ya’yan su raba sauran kamar yadda ayar baya ta yi bayani. Idan kuwa bai bar ‘ya’ya ko jikoki na ɓangaren ‘ya’ya maza ba, to za a ba mahaifiyar kaso ɗaya cikin uku, sauran kuma a ba wa mahaifinsa gaba ɗaya. To amma idan ya bar ‘yan’uwansa shaƙiƙai ko li’abbai ko li’ummai tare da iyayensa biyu, to za a ba wa mahaifiyarsa kaso ɗaya cikin shida, sauran kuma mahaifinsa ya ɗauke, ‘yan’uwansa ba su da komai. To duk wannan rabo za a yi shi ne bayan an zartar da wasiyyar mamaci daga dukiyarsa, amma kada ta wuce kaso ɗaya cikin uku na dukiyar, kuma an biya bashin da ake bin sa. Sannan Allah ya bayyana cewa, ya ba wa kowa haƙƙinsa na gado daga cikin su iyaye da ‘ya’ya, domin ɗan\'adam bai san wane ne tsakanin mahaifinsa da ɗansa zai fi zama mai amfani a gare shi ba. Mahaifinsa zai iya zama shi ne mai amfani gare shi fiye da ɗansa, hakanan kuma ɗansa zai iya zama shi ne mafi amfani gare shi fiye da mahaifinsa, don haka bai dace a hana wani haƙƙinsa na gado ba. Wannan rabo daga Allah ne, kuma shi ne masanin komai, don haka ya fi kowa sanin wanda ya dace a ba wa gado da gwargwadon yadda ya dace a ba shi, kuma shi ne gwani mai hikima, wanda yake saka komai a muhallinsa da ya dace da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin gadon ma’aurata. Ya bayyana cewa, idan matar mutum ta rasu kuma ba ta da ɗa namiji ko ‘ya mace, to mijinta yana da gadon rabin dukiyar da ta bari. Idan kuwa tana da ɗa ko ‘ya ɗaya ko da yawa, to mijin yana da kaso ɗaya cikin huɗu na dukiyar da ta bari. Duk kuma wannan rabo za a yi shi ne bayan an cire wasiyyar da ita mai rasuwar ta bari, an kuma biya bashin da ake bin ta. Hakanan ita ma mace idan mijinta ya rasu bai bar ɗa namiji ko ‘ya mace ba, to za a ba ta kaso ɗaya cikin huɗu. Hakanan idan yana da mace fiye da ɗaya, to za su yi tarayya ne a wannan kason. Idan kuma mai rasuwar ya bar ɗa ko ‘ya ɗaya ko da yawa, to matarsa ko matansa suna da kaso ɗaya cikin takwas na abin da ya bari. Kuma duk wannan zai kasance ne bayan an cire wasiyyar da ya bari, an kuma biya bashin da yake kansa. Idan kuma mai rasuwar, mace ko namiji, ba shi da ‘ya’ya, ba shi da iyaye, amma yana da ɗan’uwa ko ‘yar’uwa na ɓangaren mahaifiyarsa; watau wanda suka uwa kawai; to kowanne ɗaya daga cikinsu yana da kaso ɗaya cikin shida na abin da ya bari. Amma idan ‘yan’uwan nasa da aka ambata suna da yawa, to gaba ɗayansu za a ba su kaso ɗaya ne cikin uku, su raba daidai, babu fifiko tsakanin mace da namiji. Duk kuwa wannan za a yi shi ne bayan an cire wasiyya da kuma bashi, kuma ba tare da an tauye wa wani magaji haƙƙinsa ko an ƙara wa wani fiye da abin da ya cancanta a ba shi ba. Wannan rabon gadon duk wasiyya ce daga Allah da ta wajaba muminai su rungume ta, su yi aiki da ita. Allah masani ne, ya san komai na masalahar bayinsa, ya kuma san abin da zai cutar da su, ya san wane ne ya cancanta a ba shi gado, ya san wanda bai cancanta a ba shi ba, kuma mai haƙuri ne, ba ya gaggawar yin uƙuba ga wanda ya saɓa masa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafa cewa, abin da ya shar’anta na rabon gado da kason da za a ba wa kowa, iyakokinsa ne, ya wajaba a kan bayi lalle kada su ƙetare su. Sannan ya bayyana sakamakon wanda ya yi biyayya gare shi da kuma Manzonsa, da cewa yana da gidajen Aljanna, waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarkashinsu, kuma za su dawwama a cikinsu har abada. Wannan kuma shi ne babban rabo. Amma wanda ya saɓa wa Allah da Manzonsa, kuma ya ƙetare iyakokin Allah, to Allah zai shigar da shi wutar Jahannama, zai yi ta zama a cikinta har abada, kuma yana da wata azaba ta wulaƙanci.

  15. وَٱلَّٰتِي يَأۡتِينَ ٱلۡفَٰحِشَةَ مِن نِّسَآئِكُمۡ فَٱسۡتَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِنَّ أَرۡبَعَةٗ مِّنكُمۡۖ فَإِن شَهِدُواْ فَأَمۡسِكُوهُنَّ فِي ٱلۡبُيُوتِ حَتَّىٰ يَتَوَفَّىٰهُنَّ ٱلۡمَوۡتُ أَوۡ يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلٗا

    Open ayah 4:15

    Kuma waɗannan da suke aikata zina daga cikin matanku, to ku kafa musu shaidu guda huɗu daga cikinku, sannan idan sun bayar da shaida, to sai ku tsare su a cikin gidaje har sai mutuwa ta ɗauke su ko kuma Allah Ya sanya musu wata mafita.

  16. وَٱلَّذَانِ يَأۡتِيَٰنِهَا مِنكُمۡ فَـَٔاذُوهُمَاۖ فَإِن تَابَا وَأَصۡلَحَا فَأَعۡرِضُواْ عَنۡهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ تَوَّابٗا رَّحِيمًا

    Open ayah 4:16

    Kuma maza biyu daga cikinku da za su yi zina, to ku muzguna musu; amma idan sun tuba kuma suka gyara ayyukansu, to ku kawar da kai daga gare su. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan karɓar tuba ne, Mai jin ƙai.

  17. إِنَّمَا ٱلتَّوۡبَةُ عَلَى ٱللَّهِ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ يَتُوبُونَ مِن قَرِيبٖ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَتُوبُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:17

    Tuban da Allah Yake karɓa kawai (ita ce) na waɗanda suke aikata mummunan aiki da jahilci, sannan su gaggauta tuba, to waɗannan Allah zai karɓi tubansu. Allah kuma Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima.

  18. وَلَيۡسَتِ ٱلتَّوۡبَةُ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ حَتَّىٰٓ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ إِنِّي تُبۡتُ ٱلۡـَٰٔنَ وَلَا ٱلَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمۡ كُفَّارٌۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا

    Open ayah 4:18

    Kuma ba a karɓar tuba daga waɗanda suke aikata munanan ayyuka har sai lokacin da mutuwa ta zo wa ɗayansu, sai ya ce: “Ni kam na tuba yanzu;” kuma ba a karɓar tuban waɗanda suke mutuwa alhalin suna kafirai. Waɗannan Mun yi musu tanadin azaba mai raɗaɗi. Kafin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da hukuncin bulala ga mazinatan da ba su taɓa yin aure ba, ko jefewa ga waɗanda suka taɓa yin aure, Allah ya yi umarni ne da a tsare matan da aka same su da laifin zina a gidaje, kada a bar su su fita har mutuwa ta zo musu, ko kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya samar musu da wata mafita. Kuma hukuncin bai bambance matan aure da waɗanda ba su yi aure ba. Za a yanke musu wannan hukunci ne bayan an samu shaidu maza Musulmi huɗu adalai sun bayar da shaida da cewa sun gan su suna zina. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su gallaza wa waɗanda suka yi zina daga cikinsu, maza ko mata, ta hanyar yi musu kakkausar magana da tsawatarwa da sauransu. Idan kuma sun tuba sun bar wannan babban laifi, sun gyara rayuwarsu, to sai muminai su ƙyale su, domin Allah mai karɓar tuban wanda ya tuba ne, kuma mai tausayi ne ga bayinsa, kuma ƙofar tuba koyaushe a buɗe take. Daga baya ne Allah ya saukar da hukuncin da ya shafe wannan, kamar yadda ya bayyana a cikin Suratun Nur , aya ta 2, da kuma hadisan Manzon Allah (ﷺ). An karɓo daga Ubadatu ɗan Samit (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Ku karɓa daga gare ni! Ku karɓa daga gare ni! Haƙiƙa Allah ya samar musu da mafita “Budurwa da saurayi a yi musu bulala ɗari a kuma tsare su shekara guda; bazawara da bazawari a yi musu bulala ɗari sannan a jefe su.” [Muslim #1690]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yana karɓar tuban wanda duk ya yi laifi cikin jahilci. Domin duk wanda ya saɓa wa Allah, to shi jahili ne ko da kuwa yana da ilimin haramcin laifin da ya yi, domin aikata laifin da ya yi shi ne jahilcin da wautar, kamar yadda Ƙatada ya ce: “Sahabban Manzon Allah (Mai tsarki da daukaka) sun haɗu a kan cewa, duk abin da aka saɓa wa Allah da shi jahilci ne.” [Tafsirin Abdurrazak 1:137]. Allah ya bayyana cewa, yana karɓar tubansu idan sun tuba kafin zuwan mutuwarsu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah yana karɓar tuban bawa matuƙar bai zo gargara ba.” [Tirmizi #3537, da Ibnu Maja #4253, da Ahmad #6160]. To waɗannan su ne Allah yake yafe musu, ya karɓi tubansu. Allah kuwa ya kasance mai cikakken ilimi ne a kan komai, kuma mai hikima. To amma waɗanda suke aikata saɓo, sannan ba su tashi tuba ba sai da suka yi ido huɗu da mutuwa sai a sannan su ce sun tuba, to waɗannan Allah ba ya karɓar tubansu, kamar yadda ba ya karɓar tuban wanda ya mutu yana kafiri. Waɗannan kuma Allah ya yi musu tanadin azaba mai raɗadi da take jiran su a lahira.

  19. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَرِثُواْ ٱلنِّسَآءَ كَرۡهٗاۖ وَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ لِتَذۡهَبُواْ بِبَعۡضِ مَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَعَاشِرُوهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِن كَرِهۡتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰٓ أَن تَكۡرَهُواْ شَيۡـٔٗا وَيَجۡعَلَ ٱللَّهُ فِيهِ خَيۡرٗا كَثِيرٗا

    Open ayah 4:19

    Ya ku waɗanda suka yi imani, bai halatta gare ku ku gaji mata a bisa ga tilas ba; kuma kada ku hana su aure don ku ƙwace wani sashi na abin da kuka ba su, sai fa in sun zo da wata alfasha ta sarari. Kuma ku yi musu kyakkyawar mu’amala. Amma idan har kun ƙi su, to mai yiwuwa ne ku ƙi wani abu, Allah kuma Ya sanya alheri mai yawa a cikinsa.

  20. وَإِنۡ أَرَدتُّمُ ٱسۡتِبۡدَالَ زَوۡجٖ مَّكَانَ زَوۡجٖ وَءَاتَيۡتُمۡ إِحۡدَىٰهُنَّ قِنطَارٗا فَلَا تَأۡخُذُواْ مِنۡهُ شَيۡـًٔاۚ أَتَأۡخُذُونَهُۥ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا 

    Open ayah 4:20

    Kuma idan kun yi nufin musanya wata mace a gurbin wata macen, kuma kun riga kun ba wa ɗayarsu dukiya mai yawa (ta sadaki), to kar ku karɓi komai daga cikinsa. Shin za ku karɓe shi ne a kan zalunci da laifi ƙarara?

  21. وَكَيۡفَ تَأۡخُذُونَهُۥ وَقَدۡ أَفۡضَىٰ بَعۡضُكُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ وَأَخَذۡنَ مِنكُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

    Open ayah 4:21

    Kuma ta yaya za ku karɓe shi alhali kuma kun riga kun sadu da juna, kuma sun riƙi wani alƙawari mai ƙarfi daga wajenku?

  22. وَلَا تَنكِحُواْ مَا نَكَحَ ءَابَآؤُكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا قَدۡ سَلَفَۚ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَمَقۡتٗا وَسَآءَ سَبِيلًا

    Open ayah 4:22

    Kuma kada ku auri wadda iyayenku maza suka aure ta cikin mata, sai fa abin da ya riga ya shuɗe. Lalle yin hakan ya kasance alfasha ce kuma abu ne da zai jawo fushin Allah, kuma tafarki ne wanda ya yi muni. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana rushe wasu miyagun al’adu ne na Larabawan zamanin jahiliyya, waɗanda suka ƙunshi zalunci ga mata. Larabawa kafin zuwan Musulunci, idan mutum ya mutu, to magadansa ne za su gaji matarsa da ya bari; idan magajin ya ga dama ya aure ta, ko kuma ya aurar da ita ga wanda yake so ko da kuwa ita ba ta so. Idan kuma ya ga dama ya ƙi auren ta, ya kuma ƙi aurar da ita, ya ƙyale ta nan haka ba aure. Sai Allah ya saukar da wannan ayar yana hana su gadon mata da ƙarfi, ko su hana su yin aure. An karɓo daga Abu Umamata ɗan Sahlu ɗan Hunaif ya ce: Lokacin da Abu Ƙais ɗan Al-Aslatu ya rasu, ɗansa ya so ya auri matarsa, domin haka suke yi a jahiliyya, sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Ba ya halatta a gare ku ku gaji mata bisa tilas.” [Nasa’i, As-Sunanul Kubra 11095, da Tafsirin At-Tabari 8:105]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, haramun ne ga muminai su gaji matan ubanninsu ko danginsu da suka mutu, don su aure su ko su aurar da su ga waɗanda su suka so, ko da matan ba sa son su. Hakanan ya hana su su takura wa matansu na aure har su gaji su fanshi kawunansu ta hanyar sadaukar da sadakinsu gaba ɗaya, ko wani abu daga cikinsa, ko su haƙura da wani haƙƙi nasu domin su ƙwaci kawunansu ta hanyar saki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yin haka bai halatta ba, sai dai idan su matan ne suka aikata wani laifi kamar na zina, ko suka bijire wa mijin ba tare da wani dalili ba, to a wannan lokacin ya halatta miji ya nemi a mayar masa da sadakinsa ko wani abu daga cikinsa domin ya sake ta. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mazaje da su yi kyakkyawar mu’amala ga matansu, ta hanyar nuna musu halaye na ƙwarai da magana mai daɗi da guje wa duk wani abin da zai sosa musu rai, kuma su kula da haƙƙoƙinsu na ciyarwa da tufatarwa da sauran abin da shari’a ta umarce su da shi da kuma abin da ya gudana a al’ada, kuma bai saɓa ma wata doka ta Musulunci ba. An karɓo daga Aisha (Allah ya kara masa yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mafifici daga cikinku shi ne mafifici ga iyalansa, kuma ni ne mafificinku ga iyalaina.” [Tirmizi #3895, da Darimi #2260]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, idan wani abu ya faru har mazaje suka ƙyamaci matansu, to kamata ya yi su yi haƙuri da su, domin tana iya yiwuwa ya zamana akwai wani alheri mai yawa tare da su, kamar su haifa musu ‘ya’ya waɗanda za su amfane su a rayuwarsu ta duniya da ta lahira, ko kuma daga baya su ji suna ƙaunar su. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada wani mumini ya ƙi wata mumina; idan ya ƙi wata ɗabi’a ce tata, to ai kuma zai so wata ɗabi’ar tata.” [Muslim #1469]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, idan mutum ya ga ba zai iya zama da matarsa ba, ya yi niyyar ya sake ta ya auro wata, alhalin ya ba ta sadaki mai yawa, to bai halatta ya ce zai ƙwace sadakin da ya ba ta ba, ko wani abu daga cikinsa, domin haƙƙinta ne. Allah ya ce, ta yaya za su ƙwace sadakin da suka ba su don za su rabu da su bisa zalunci alhali sun yi alaƙar auratayya a tsakaninsu, kuma sun ɗauki alƙawari mai ƙarfi na za su riƙe su da amana, su ba su duk haƙƙoƙinsu, ba za su cuce su ba? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya taɓo wata al’ada ta jahiliyya, wadda ɗa yake auren matar babansa. Allah ya yi wa muminai kashedi da kada su kuskura su yi wannan kwaɓa, sai dai abin da ya riga ya faru tun kafin zuwan Musulunci, ko kafin a haramta wannan al’adar, to wannan an yafe musu shi. Auren matan iyaye maza wata aika-aika ce mai matuƙar muni, kuma Allah yana ƙyamar wannan aiki, mutane masu hankali ma suna ƙyamar sa. Hasali ma gaba tana iya aukuwa tsakanin ɗan da mahaifinsa saboda kishi.

  23. حُرِّمَتۡ عَلَيۡكُمۡ أُمَّهَٰتُكُمۡ وَبَنَاتُكُمۡ وَأَخَوَٰتُكُمۡ وَعَمَّٰتُكُمۡ وَخَٰلَٰتُكُمۡ وَبَنَاتُ ٱلۡأَخِ وَبَنَاتُ ٱلۡأُخۡتِ وَأُمَّهَٰتُكُمُ ٱلَّٰتِيٓ أَرۡضَعۡنَكُمۡ وَأَخَوَٰتُكُم مِّنَ ٱلرَّضَٰعَةِ وَأُمَّهَٰتُ نِسَآئِكُمۡ وَرَبَٰٓئِبُكُمُ ٱلَّٰتِي فِي حُجُورِكُم مِّن نِّسَآئِكُمُ ٱلَّٰتِي دَخَلۡتُم بِهِنَّ فَإِن لَّمۡ تَكُونُواْ دَخَلۡتُم بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ وَحَلَٰٓئِلُ أَبۡنَآئِكُمُ ٱلَّذِينَ مِنۡ أَصۡلَٰبِكُمۡ وَأَن تَجۡمَعُواْ بَيۡنَ ٱلۡأُخۡتَيۡنِ إِلَّا مَا قَدۡ سَلَفَۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

    Open ayah 4:23

    An haramta muku auren iyayenku mata da ‘ya’yanku mata da ‘yan’uwanku mata da gwaggonninku da ‘yan’uwan mahaifanku mata da ‘ya’yan ɗan’uwanku da ‘ya’yan ‘yar’uwarku da iyayenku waɗanda suka shayar da ku da ‘yan’uwanku mata ta wajen shayarwa, da iyayen matanku da agololinku waɗanda suke cikin gidajenku, waɗanda matan da kuka taɓa saduwa da su suka haife su, in kuwa ba ku taɓa saduwa da su ba, to babu laifi a kanku, da matan ‘ya’yanku maza waɗanda suke na tsatsonku; haramun ne kuma ku haɗa ‘yan’uwa mata biyu, sai dai abin da ya wuce a baya. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai jin ƙai.

  24. ۞وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۖ كِتَٰبَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ وَأُحِلَّ لَكُم مَّا وَرَآءَ ذَٰلِكُمۡ أَن تَبۡتَغُواْ بِأَمۡوَٰلِكُم مُّحۡصِنِينَ غَيۡرَ مُسَٰفِحِينَۚ فَمَا ٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِهِۦ مِنۡهُنَّ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا تَرَٰضَيۡتُم بِهِۦ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡفَرِيضَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:24

    Haka ma da matan aure, sai dai ƙwaraƙwaranku; wannan hukuncin Allah ke nan a kanku. Kuma an halatta muku (sauran) matan da ba waɗannan ba, ku neme su da kuɗinku, kuna masu kame kanku, ba ma su zina ba. To waɗanda kuka sadu da su daga cikinsu ku ba su sadakinsu wanda kuka yanka musu. Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi yarjejeniya da shi bayan sadakin da kuka yanka. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana irin matan da aka haramta wa mutum ya aura saboda dangantaka ta tsatso ko ta shayarwa ko kuma ta surukutaka da waɗanda aka haramta haɗa su a tare da kuma matan da aka halatta auren su. Waɗanda aka haramta auren su saboda dangantaka ta tsatso su bakwai ne. Su ne: • Mahaifiya; kaka ta shiga ƙarƙashin wannan, komai nisanta. • ‘Ya; a ƙarƙashinta, duk matan da suka biyo ta tsatsonta sun shiga ciki, kamar jika mace da ‘yar jika da abin da ya yi ƙasa. • ‘Yar’uwa, wadda suka haɗa uwa ɗaya uba ɗaya, ko ta wajen uba, ko ta wajen uwa. • Gwaggo, wato ‘yar’uwar uba; yayarsa ko ƙanwarsa. • Inna, wato ‘yar’uwar mahaifiya; yayarta ko ƙanwarta. • ‘Yar ɗan’uwa, shaƙiƙi ko na wajen uba ko na wajen uwa. • ‘Yar ‘yan’uwa, shaƙiƙiya ko ta wajen uba ko ta wajen uwa. Sai kuma waɗanda aka haramta auren su saboda dangantaka ta shayarwa, su kuma su biyu ne: • Matar da ta shayar da kai nono ta zama mahaifiya ta fuskar shayarwa, mahaifiyarta ta zama kakarka. • Matar da kuka sha nono ɗaya ta zama ‘yar’uwarka, don haka ko ‘ya’yanta mata ba za ka aura ba, don ‘ya’yanka ne. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya faɗa dangane da ‘yar baffansa Hamza: “Ba ta halatta gare ni ba, abin da yake haramta saboda dangantaka ta jini, yana haramta saboda dangantaka ta shayarwa, ita ‘yar ɗan’uwana ce da muka sha nono ɗaya da shi.” [Bukhari #2645, da Muslim #1447]. Sannan sai waɗanda aka haramta saboda surukuta su ne: • Iyayen matanku na aure. Da zarar an ɗaura masa aure da ‘yarta, to ta haramta a gare shi, ya tare da ita ko bai tare ba. • Agola. Wato ‘yar matar da ya aura, kuma ya tare da ita, to ‘yar ta haramta a gare shi. Amma idan an ɗaura aure ne kawai ba su tare ba, ya saki uwarta, to zai iya auren ‘yar. • Matar ɗansa na cikinsa. Da zarar an ɗaura wa ɗansa aure da mata, to ta haramta a gare shi, ko da kuwa ɗan bai tare da ita ba ya sake ta. Sai kuma waɗanda aka hana auren su a tare lokaci guda, su ne ‘yan’uwan juna, wato ya da ƙanwa, ko tagwagaye. Idan mutum ya auri yaya ko ya auri ƙanwa, to ba zai auro yayarta ba, har sai in ya sake ta, to yana iya auren ɗayar. Duk matan da aka ambata kuma aka haramta auren su, Larabawa ma a jahiliyya suna haramta su in ban da biyu kawai, su ne matar uba da kuma haɗa ya da ƙanwa lokaci guda, kamar yadda Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya faɗa. [Dubi, Tafsirin Tabari 8:132]. Allah ya ce sai dai abin da ya riga ya wakana tun lokacin jahiliyya ko kafin a haramta hakan, to wannan Allah ya yi afuwa a kansa, domin Allah mai yawan gafara ne, kuma mai jin ƙai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci matan aure cewa su ma haramun ne wani ya aure su yayin da igiyar auren wani tana a wuyansu. Amma Allah ya togace ƙwaraƙwarai ko da kuwa suna da mazaje kafirai kafin a ci su da yaƙi, to su ya halatta a aure su bayan sun yi istibra’i, wato jini ɗaya. Sunnar Annabi (ﷺ) kuma, har wa yau ta zo da haramta wa mutum ya haɗa auren mace da gwaggonta ko innarta lokaci guda. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Ba a haɗa tsakanin mace ga gwaggonta, ko tsakanin mace da innarta.” [Bukhari #5109 da Muslim #1408]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cewa, duk abubuwan da ya yi bayani a baya wani farali ne da ya wajabta wa muminai, dole ne su riƙe shi gam-gam. A ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nusantar da cewa, baya ga matan da aka haramta aurensu, sauran matan da ba a ambata ba an halatta wa muminai da su biya sadakinsu, su aure su don su tsare mutuncinsu, ko kuma su sayi ƙwaraƙwarai da kuɗinsu don su tsare kawunansu daga faɗawa laifin zina. Duk matar da aka aura kuma aka sadu da ita, to Allah ya wajabta a biya ta sadakinta. Bayan an yanke sadaki kuma, to babu laifi ga ma’aurata idan suka yi wata yarjejeniya a kansa a tsakaninsu ta ƙari a kan asalin sadakin ko ragi ko yafe masa ko jinkirta biyansa. Lalle Allah masanin komai ne, kuma mai hikima ne a cikin duk hukunce-hukuncensa.

  25. وَمَن لَّمۡ يَسۡتَطِعۡ مِنكُمۡ طَوۡلًا أَن يَنكِحَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ فَمِن مَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُم مِّن فَتَيَٰتِكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِكُمۚ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۚ فَٱنكِحُوهُنَّ بِإِذۡنِ أَهۡلِهِنَّ وَءَاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِ مُحۡصَنَٰتٍ غَيۡرَ مُسَٰفِحَٰتٖ وَلَا مُتَّخِذَٰتِ أَخۡدَانٖۚ فَإِذَآ أُحۡصِنَّ فَإِنۡ أَتَيۡنَ بِفَٰحِشَةٖ فَعَلَيۡهِنَّ نِصۡفُ مَا عَلَى ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ مِنَ ٱلۡعَذَابِۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَشِيَ ٱلۡعَنَتَ مِنكُمۡۚ وَأَن تَصۡبِرُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 4:25

    Kuma daga cikinku wanda ba shi da yalwar dukiya da zai iya auren ‘ya’ya muminai, to ya aura daga cikin abin da kuka mallaka na kuyanginku muminai. Kuma Allah Shi ne Mafi sanin imaninku. Sashinku ‘yan’uwan sashi ne. To ku aure su da izinin iyayen gidansu. Sai ku ba su sadakinsu ta hanyar da ta dace, suna masu kame kawunansu ba mazinata ba, sannan ba waɗanda suke riƙar farka a ɓoye ba. To idan sun yi aure, sannan suka yi zina, to abin da za a yi musu na azaba, shi ne rabin abin da ake yi wa ‘ya’ya. Wannan ya shafi wanda ya ji tsoron matsatsi a cikinku. Amma ku yi haƙuri shi ya fi muku alheri. Allah kuma Mai yawan gafara ne, Mai jin ƙai. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin matan da ba su halatta mutum ya aura ba da waɗanda suka halatta ya aura, sai kuma ya kawo bayanin auren mata waɗanda suke bayi. Duk da cewa auren baiwa halal ne, sai dai shari’a ba ta ƙarfafa yin sa ba sai bisa larura, saboda matsalar da take tattare da shi, domin ɗan da mutum zai haifa zai zama bawa ne. Don haka sai Allah ya nuna cewa sai idan mutum ba shi da halin auren mace ‘yantacciya saboda rashin kuɗin sadaki ko wani dalili, to sannan ne zai auri baiwa mumina mallakar ‘yan’uwansa muminai, idan sun zamanto muminai ne kamar yadda ya bayyana gare ku a zahiri, Allah shi ne mafi sanin gaskiyar imaninku da nasu. Ku da sauran bayi duk daidai kuke wajen mutuntaka, domin dukkanku asalinku shi ne Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Hakanan mata ‘yantattu da mata bayi ta wannan fuskar ɗaya suke, don haka idan har akwai larura ta kasa auren mace ‘ya, to kada ku ƙyamaci auren baiwar mumina. Kuma a aure su bisa amincewar iyayen gijinsu, a ba su sadakinsu kamar yadda shari’a ta ajiye, kada a tauye musu komai, ko a yi ta wasa da hankulansu. A aure su bisa sharadin su zamanto masu kame kansu, kuma ba masu yin zina ba a bayyane ko a ɓoye. To idan suka yi aure, sannan kuma suka aikata zina, to sai a yi musu haddi rabin wanda ake yi wa mace ‘ya wadda ba ta yi aure ba, wato a yi musu bulala hamsin. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, ya halatta auren mata bayi ne kawai ga wanda ba zai iya daurewa ya zauna ba aure ba, saboda yana tsoron faɗawa cikin zinace-zinace. Da a ce mazan za su daure su yi haƙuri har Allah ya hore musu abin auren mace ‘yantacciya to da ya fi musu alheri. Lalle Allah mai gafara ne ya ɗauke laifi ga wanda ya cika sharuɗɗan da aka ambata, kuma mai rahama ne, ba ya takura wa bayinsa a cikin duk abin da yake shar’anta musu.

  26. يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُبَيِّنَ لَكُمۡ وَيَهۡدِيَكُمۡ سُنَنَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَيَتُوبَ عَلَيۡكُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

    Open ayah 4:26

    Allah Yana nufin yi muku bayani ne, kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waɗanda suka gabace ku, kuma Ya karɓi tubanku. Kuma Allah Mai yawan sani ne, Mai hikima.

  27. وَٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيۡكُمۡ وَيُرِيدُ ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلشَّهَوَٰتِ أَن تَمِيلُواْ مَيۡلًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:27

    Kuma Allah Yana nufin Ya karɓi tubanku ne, amma waɗanda suke bin sha’awace-sha’awace, su kuma suna nufin ku karkace karkacewa mai girma.

  28. يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُخَفِّفَ عَنكُمۡۚ وَخُلِقَ ٱلۡإِنسَٰنُ ضَعِيفٗا

    Open ayah 4:28

    Allah Yana nufin Ya sassauta muku. Kuma an halicci ɗan’adam mai rauni ne. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama bayanin wasu hukunce-hukuncen aure, sai kuma ya nuna cewa, yana nufin bayanan su zama shiriya da haske ga mutane, don su san hukunce-hukuncen shari’a dalla-dalla na halal da na haram. Wannan it ace hanyar bayin Allah na farko, waɗanda Allah ya yi musu ni’ima, su ne annabawa da mabiyansu. Allah kuma mai cikakken sani ne, ba abin da yake ɓuya gare shi, kuma mai hikima ne cikin duk shari’unsa da hukunce-hukuncensa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake nanata nufinsa na karɓan tuban bayinsa, kuma ya bayyana mugun nufi na ‘yan duniya, fasiƙai da kafirai, waɗanda ko da yaushe suke son ganin muminai sun saki hanyar gaskiya da tsoron Allah, sun bi tasu ta watsewa da saɓon Allah. Ya kuma nuna cewa, yana nufin ya sassauta wa muminai cikin duk abin da ya shar’anta musu, saboda Musulunci addini ne da ya kafu a kan sauƙi ba tsanani ba; domin shi kuma ɗan\'adam a ɗabi’arsa, Allah ya halicce shi mai rauni ne.

  29. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا

    Open ayah 4:29

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, sai dai in ya kasance kasuwanci ne bisa yarjejeniya a tsakaninku. Kuma kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah Ya kasance Mai tausaya muku ne.

  30. وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ عُدۡوَٰنٗا وَظُلۡمٗا فَسَوۡفَ نُصۡلِيهِ نَارٗاۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرًا 

    Open ayah 4:30

    Kuma duk wanda ya aikata haka don ƙetare iyaka da zalunci, to za Mu shigar da shi cikin wata wuta; kuma yin haka ya kasance abu ne mai sauƙi a wurin Allah.

  31. إِن تَجۡتَنِبُواْ كَبَآئِرَ مَا تُنۡهَوۡنَ عَنۡهُ نُكَفِّرۡ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَنُدۡخِلۡكُم مُّدۡخَلٗا كَرِيمٗا

    Open ayah 4:31

    Idan har kun nisanci manya-manyan laifuffukan da aka hana ku, to za Mu kankare muku ƙananan kurakuranku, kuma za Mu shigar da ku wata mashiga ta karamci. Bayan an gama bayani game da aure, sai kuma bayani a kan dukiya ya biyo baya, domin auren ana yin sa da dukiya ne, haka ma sayen ƙwarƙwara sai da dukiya. Bayan wannan kuma ayoyi da dama sun gabata game da sha’anin dukiyoyin marayu da sha’anin rabon gado, duk wannan ta sa aka zo da bayani a kan hanyar da ta dace a nemi wannan dukiya da kuma wadda ba ta dace ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai cin dukiyoyin ‘yan’uwansu ba bisa haƙƙi ba, wato kamar ta hanyar caca ko riba ko ciniki irin wanda shari’a ta haramta, sai dai ta hanyar kasuwanci na halal, wanda aka gina shi a kan yarjejeniya, to wannan ya halatta. Saboda kasancewar dukiya da rayuwa tare suke, sai bayan an hana cin dukiya ta hanyar ɓarna, sai Allah ya zo da bayanin haramta salwantar da rai ba da haƙƙi ba. Larabawa a lokacin jahiliyya yawancin dukiyoyinsu suna tara su ne ta hanyar fashi da makami ko kai hare-hare a kan jama’a da ƙwace musu dukiyoyinsu, wanda hakan sau tari yakan haifar da salwantar rayuka. Hakanan shi ma wanda za a ƙwatar masa dukiya ba tare da wani haƙƙi ba, yakan iya fusata ya nemi ƙwato dukiyarsa ta kowace irin hanya, wanda hakan ka iya kaiwa ga rasa rai. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana mutum ya kashe kansa da kansa, ko ya kashe ɗan’uwansa, domin duk wanda ya kashe ɗan’uwansa, kamar ya kashe kansa ne. An karɓo daga Sabit ɗan Dhahhak (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Wanda duk ya kashe kansa da wani abu a duniya, to da shi za a yi masa azaba a lahira.” [Bukhari #6047, da Muslim #110]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda duk ya kashe kansa da wani ƙarfe, to zai zo da wannan ƙarfen a hannunsa yana daɓa shi a cikinsa a wutar Jahannama ranar gobe ƙiyama, yana mai dawwama abin dawwamarwa a cikinta har abada. Wanda duk ya sha guba ya kashe kansa, to zai zo yana kwankwaɗar wannan gubar a cikin wutar Jahannama, yana mai dawwama abin dawwamarwa a cikinta har abada. Wanda ya jeho kansa daga ƙololuwar dutse ya kashe kansa, to zai yi ta gangarowa a cikin wutar Jahannama, yana mai dawwama abin dawwamarwa a cikinta har abada.” [Muslim #109]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lalle shi mai rahama ne ga bayinsa, don haka ya haramta musu kashe kawunansu ko kashe junansu ba bisa wani haƙƙi ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi gargaɗi mai tsanani ga mai cin dukiyar jama’a ta hanyar zalunci da ƙetare iyaka, cewa makomarsa ita ce wutar Jahannama mai tsananin ƙuna, kuma azabtar da shi abu ne mai matuƙar sauƙi a wurin Allah, don babu wanda ya isa ya hana shi. To bayan wannan gargaɗi kuma, sai Allah ya ambaci alƙawarinsa ga masu nisantar aikata alkaba’ira, ya bayyana musu cewa, idan har sun nisanci manyan laifuka, to shi kuma ya yi musu alƙawarin kankare musu ƙananan zunubbansu, daga ƙarshe kuma ya shigar da su gidan Aljanna, ya karrama su a cikinta.

  32. وَلَا تَتَمَنَّوۡاْ مَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بِهِۦ بَعۡضَكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا ٱكۡتَسَبُواْۖ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا ٱكۡتَسَبۡنَۚ وَسۡـَٔلُواْ ٱللَّهَ مِن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا

    Open ayah 4:32

    Kuma kada ku yi burin abin da Allah Ya fifita wasunku a kan wasu da shi, maza suna da kaso na abin da suka tsuwurwurta, haka mata ma suna da kaso na abin da suka tsuwurwurta. Kuma ku roƙi Allah daga falalarsa. Lalle Allah Ya kasance Masanin komai ne.

  33. وَلِكُلّٖ جَعَلۡنَا مَوَٰلِيَ مِمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَۚ وَٱلَّذِينَ عَقَدَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ فَـَٔاتُوهُمۡ نَصِيبَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدًا

    Open ayah 4:33

    Kuma kowa Mun sanya masa magadansa daga abin da mahaifa suka bari ko dangi mafiya kusanci. Su kuma waɗanda rantsuwar ƙulla (zumunci) ta haɗa tsakaninku, to ku ba su rabonsu. Lalle Allah Ya kasance Mai tsinkaye ne a kan komai. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana cin dukiyar mutane ba a kan gaskiya ba, ya kuma hana kashe rai, sai a waɗannan ayoyi kuma ya hana mutum ya riƙa burin falalar da Allah ya fifita ɗan’uwansa da ita; yin hakan yakan haifar da hassada; ita kuma hassada tana iya kai mai ita ga cin dukiyar ɗan’uwansa ba bisa gaskiya ba, mai yiwuwa ma ta kai shi ga kisan kai. Abubuwan da Allah ya hana mutum ya ƙwallafa ransa a kansu sun haɗa da dukiya ko matsayi ko mulki da makamantansu. Allah kuma ya umarci mutane maza da mata, kowa ya yi aiki irin wanda ya dace da shi, na alheri ko na sharri, tabbas kuma zai ga sakamakon aikinsa, ba tare da an tauye masa komai ba. Amma Allah ya faɗakar da su cewa, su roƙe shi falalarsa, don shi ne mai bayarwa, kuma duk wanda yake da wata falala to shi ya ba shi ita. Allah kuma mai cikakken ilimi ne, ya san wanda ya cancanta ya ba wa, da wanda ya cancanta ya hana masa, kuma mai hikima ne wajen ajiye komai a muhallinsa da ya dace da shi. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata mata ta zo wurin Annabi (ﷺ) ta ce: “Ya Annabin Allah, an ce kason namiji ɗaya daidai yake da kason mata guda biyu, kuma aka ce shaidar mace biyu daidai take da shaidar namiji ɗaya, to a wajen aiki ma haka muke? Idan mace ta yi aiki mai kyau sai a ba ta rabin ladan da za a ba namiji?” Sai wannan ayar ta sauka.” [Ibn Abi Hatim, At-Tafsir #5223 da Al-Dhiya, Al-Ahadithul Mukhtarah #115]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya dawo a kan zancen gado, inda ya ce, kowane mutum ya sanya masa masu cin gadonsa na dukiyar da ya mutu ya bari daga mahaifinsa da mahaifiyarsa da sauran danginsa. Wasu malamai sun ce, ana nufin magada masu ci da asibci, kamar ‘yan’uwansa da ‘ya’yan baffanninsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce, waɗanda kuka ƙulla alƙawari da su da yarjejeniyar zumunta ta hanyar rantse-rantse masu ƙarfi a tsakaninku, to ku ba su kason su na gado. Wannan gaɓar da dama daga cikin malaman tafsiri sun ce an shafe hukuncinta da ayar da take cikin Suratul Anfali , aya ta 75. Imam Ibn Jarir At-Tabari yana ganin hukuncinta yana nan ba a shafe shi ba, domin yana ganin tana magana ne a kan waɗanda suka ƙulla yarjejeniya ta ƙawance a kan za su taimaka wa juna; za su yi wa juna nasiha, to wannan hukuncin yana nan, don haka a fahimtarsa ‘rabonsu’ da aka ambata, ana nufin nasiha da taimakon juna, ba gado ake nufi ba. [Dubi, Ibn Jarir, Juzu’i na 3, Shafi na 281]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: ‘Faɗar Allah: “Kuma kowa mun sanya masa magadansa.” Ibn Abbas ya ce: “Ana nufin magada.” Sannan faɗar Allah: “… waɗanda rantsuwar ƙulla (zumunci) ta haɗa tsakaninku.” Ibn Abbas ya ce: “Lokacin da masu hijira suka zo Madina, sai ya zamanto ɗaya daga cikinsu zai iya cin gadon mutumin Madina, ban da sauran danginsa na jini, saboda ‘yan’uwantakar da Annabi (ﷺ) ya haɗa a tsakaninsu. Yayin da Allah ya saukar da faɗarsa: “Kuma kowa mun sanya masa magadansa.” sai aka shafe wancan hukunci. Sannan Allah ya ce: “…waɗanda rantsuwar ƙulla (zumunci) ta haɗa tsakaninku.” Ibn Abbas ya ce: “Na taimako da agaji, amma an shafe na gado, sai dai idan ya yi masa wasiyya.” [Bukhari #4581]. Wannan yana nufin an shafe abin da ya danganci gado a tsakaninsu, amma abin da ya danganci taimakon juna, wannan yana nan ba a shafe shi ba. Sannan Allah ya bayyana cewa, shi mai tsinkaye ne kan komai, babu abin da ba ya ganin yadda yake gudana a cikin halittunsa kakaf.

  34. ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ وَبِمَآ أَنفَقُواْ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡۚ فَٱلصَّٰلِحَٰتُ قَٰنِتَٰتٌ حَٰفِظَٰتٞ لِّلۡغَيۡبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُۚ وَٱلَّٰتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهۡجُرُوهُنَّ فِي ٱلۡمَضَاجِعِ وَٱضۡرِبُوهُنَّۖ فَإِنۡ أَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُواْ عَلَيۡهِنَّ سَبِيلًاۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيّٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 4:34

    Maza su ne tsayayyu a kan mata saboda abin da Allah Ya fifita sashinsu da shi a kan sashi, kuma saboda abin da suka ciyar na dukiyarsu. To salihan mata masu ɗa’a ne, masu tsare (haƙƙoƙin mazajensu) ne a bayan idon mazajensu da tsarewar Allah. Waɗanda kuwa kuke jin tsoron kangarewarsu, to ku yi musu wa’azi, kuma ku ƙaurace musu a wuraren kwanciya, kuma ku doke su; amma idan sun yi muku ɗa’a, to kada ku nemi wata hanyar cutar da su. Lalle Allah Ya kasance Maɗaukaki ne, Mai girma.

  35. وَإِنۡ خِفۡتُمۡ شِقَاقَ بَيۡنِهِمَا فَٱبۡعَثُواْ حَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهِۦ وَحَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن يُرِيدَآ إِصۡلَٰحٗا يُوَفِّقِ ٱللَّهُ بَيۡنَهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرٗا

    Open ayah 4:35

    Kuma idan kun ji tsoron ci gaba da samun saɓani a tsakaninsu, to sai ku aika da wani mai hukunci daga danginsa (mijin), da wani mai hukunci daga danginta (matar), in (su mahukuntan) suna nufin samar da gyara, to Allah zai daidaita tsakaninsu (ma’auratan). Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne Masanin abin da yake ɓoye. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, maza su ne suke da haƙƙin kula da matansu saboda abubuwa guda biyu: <b>Na farko </b>, saboda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fifita jinsin maza a kan jinsin mata cikin abubuwa da dama, kamar ƙarfin jiki da kaifin hankali. <b>Na biyu </b>, saboda su ne suke ɗaukar nauyin ciyarwa daga dukiyarsu, kuma wannan yana farawa tun daga lokacin da aka zo ɗaura aure; namiji shi ne mai biyan sadaki, sannan ya ci gaba da ɗaukar ɗawainiyar ci da sha da wurin zama na matarsa da abin da za ta haifa masa. Don haka matan da suka riƙe addininsu, suka bi Allah da Manzonsa (ﷺ), sannan suka yi wa mazajensu biyayya cikin duk abubuwan da ba su saɓa wa Allah ba, to waɗannan mata su ne masu kame mutuncinsu yayin da mazajensu ba sa nan, masu kulawa da dukiyoyin mazajensu, ba sa yi musu almubazzaranci ko ha’inci a ciki, saboda yadda Allah ya kiyaye su, ya ba su gamon-katar, ba wai yin su ba ne. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna mafita ga mazajen da suke tsoron kangarewar matansu ta hanyar yi musu tawaye. Ga hanyoyin da ya kamata su bi don magance abin tun da wuri: <b>Na farko </b>, su tunatar da su Allah, su yi musu wa’azi, su tsoratar da su azabar Allah ga matar da take saɓa wa mijinta, sannan su umarce su da su bi Allah da Manzonsa don su sami rabauta a wurinsa. <b>Na biyu </b>, idan wa’azinsu bai yi amfani ba, to sai su ƙaurace musu wajen kwanciya, ta hanyar juya musu baya ko da sun kwanta shimfiɗa ɗaya tare, ko kuma ta hanyar raba shimfiɗa. <b>Na uku </b>, idan wannan hanyar ma ba ta yi amfani ba, to sai su ɗan doke su, duka ba mai raunana jiki ba, domin su ladabtu, su fahimci girman fusatar mazajensu a kansu. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Haƙƙinku ne a kansu kada su bar wani ya hau muku shimfiɗarku; idan kuma har sun aikata hakan, to ku doke su duka ba mai raunanawa ba.” [Muslim #1218]. To idan matan sun saduda sun dawo ga yi wa mazansu biyayya, to kada su ci gaba da zarginsu a kan abin da ya riga ya wuce, ko su ce za su doke su bayan haka; su tuna cewa gaba da gabanta. Idan suna ganin su ne sama da matansu, sun fi ƙarfinsu, to su sani Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sama da su, yana sama da kowa da komai, kuma mai girma ne a kan kowa da komai. Sannan idan saɓanin da yake tsakanin ma’aurata ya ƙi ci ya ƙi cinyewa bayan mijin ya ɗauki waɗancan matakai guda uku ba su yi amfani ba, abin har yana so ya haifar da wata ɓaraka mai faɗi tsakaninsu, to sai a shirya zaman sulhu a tsakaninsu, a zaɓo mai hukunci daga ɓangaren mijin, a zaɓo wani daga ɓangaren matar, su zauna su duba matsalar, su yi wa tufkar hanci. Idan har masu sulhu sun zo ne da niyyar yin gyara, to Allah zai ba su dacewa ya zamana bakinsu ya haɗu a kan magana ɗaya da za ta dawo da komai daidai; su ma ma’auratan Allah zai ba su dace su dawo su ci gaba da zamantakewar aurensu cikin zaman lafiya da mutunta juna.

  36. ۞وَٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗا وَبِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡجَارِ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡجَارِ ٱلۡجُنُبِ وَٱلصَّاحِبِ بِٱلۡجَنۢبِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخۡتَالٗا فَخُورًا

    Open ayah 4:36

    Kuma ku bauta wa Allah (Shi kaɗai), kada ku haɗa Shi da komai; kuma ku kyautata wa iyaye da dangi makusanta da marayu da talakawa da maƙwabci makusanci da maƙwabci na nesa, da abokin da ake tare da kuma matafiyi da bayinku. Lalle Allah ba Ya son duk wanda ya kasance mai taƙama, mai yawan fariya.

  37. ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ وَيَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبُخۡلِ وَيَكۡتُمُونَ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا

    Open ayah 4:37

    Su ne waɗanda suke rowa kuma suke umartar mutane da rowa kuma suke ɓoye abin da Allah Ya ba su na falalarsa. Mun kuwa yi tanadin azaba mai wulaƙantarwa ga kafirai.

  38. وَٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ وَمَن يَكُنِ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَهُۥ قَرِينٗا فَسَآءَ قَرِينٗا

    Open ayah 4:38

    Waɗanda kuma suke ciyar da dukiyoyinsu don mutane su gani, kuma ba sa yin imani da Allah, ba sa kuma yin imani da ranar ƙarshe. Duk wanda Shaiɗan ya kasance shi ne abokinsa, to tir da aboki irin wannan.

  39. وَمَاذَا عَلَيۡهِمۡ لَوۡ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقَهُمُ ٱللَّهُۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِهِمۡ عَلِيمًا

    Open ayah 4:39

    Kuma me zai cutar da su da a ce sun yi imani da Allah da ranar ƙarshe, kuma suka ciyar daga abin da Allah Ya arzurta su da shi? Kuma Allah Ya kasance Mai yawan sani ne gare su.

  40. إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظۡلِمُ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖۖ وَإِن تَكُ حَسَنَةٗ يُضَٰعِفۡهَا وَيُؤۡتِ مِن لَّدُنۡهُ أَجۡرًا عَظِيمٗا 

    Open ayah 4:40

    Lalle Allah ba Ya zalunci ko da daidai da nauyin jaririyar tururuwa; kuma idan ya kasance aiki ne mai kyau to zai ninka shi, kuma Ya ba da lada mai girma daga wurinsa.

  41. فَكَيۡفَ إِذَا جِئۡنَا مِن كُلِّ أُمَّةِۭ بِشَهِيدٖ وَجِئۡنَا بِكَ عَلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِ شَهِيدٗا

    Open ayah 4:41

    To yaya al’amarin zai kasance idan Muka zo da kowace al’umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida kan waɗannan al’ummar?

  42. يَوۡمَئِذٖ يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَعَصَوُاْ ٱلرَّسُولَ لَوۡ تُسَوَّىٰ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضُ وَلَا يَكۡتُمُونَ ٱللَّهَ حَدِيثٗا

    Open ayah 4:42

    A wannan yini ne waɗanda suka kafirta kuma suka saɓa wa Manzo, za su yi burin ina ma a mayar da su ƙasa, kuma ba za su ɓoye wa Allah wani zance ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar bayinsa da su bauta masa shi kaɗai, kada su haɗa komai da shi cikin bauta. Kamar yadda ya umarce su da su kyautata wa mahaifa, ta hanyar yi musu biyayya a kan duk abin da bai saɓa wa Allah ba, da taimaka musu da abin da suke buƙata na rayuwa, da yi musu addu’a bayan mutuwarsu. Ya kuma yi umarni da kyautata wa dangi da marayu, waɗanda suka rasa iyayensu maza, kuma ba su balaga ba. Hakanan su kyautata wa mabuƙata, waɗanda ba sa samun abin da zai ishe su a rayuwa, hakanan maƙwabci wanda yake da dangantaka ta jini, da wanda ba shi da dangantaka ta jini da su. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Jibrilu bai gushe ba yana yi mini wasiyya da maƙwabci har sai da na yi zaton zai ce yana da gado.” [Bukhari #6015, da Muslim #2625]. Hakanan ya yi umarni da su kyautata wa duk wani wanda tafiya ta haɗa su da shi, ko kuma wanda zama ya haɗa su da shi, kamar mata. Hakanan ya yi umarnin kyautatawa ga matafiyi wanda ya zo wucewa, da kuma bayinsu da suke ƙarƙashinsu. An karɓo daga Khaisama (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Muna zaune tare da Abdullahi ɗan Umaru (Allah ya kara masa yarda), sai wani hadiminsa ya shigo, sai Abdullahi ya tambaye shi: “Shin ka ba wa bayin nan abincinsu?” Sai ya ce; “A’a.” Sai ɗan Umaru ya ce: “Maza je ka ka ba su, domin Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Ya ishi mutum girman laifi, ya hana bawansa abincinsa.” [Muslim # 996]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan hadimin ɗayanku ya kawo masa abincinsa, to idan har bai zaunar da shi sun ci tare ba, to ya ba shi loma ɗaya ko biyu, ko ci ɗaya ko biyu, domin shi ne ya tanadi wannan abincin.” [Bukhari #2557]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “A mallaka wa bawa abincinsa da suturarsa, kada a ɗora masa aikin da ya fi ƙarfinsa.” [Muslim #1662]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba ya son duk wani bawa mai ji-ji da kansa, mai yi wa mutane girman kai. An karɓo daga Iyadh (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ya yi min wahayin cewa: ‘Ku zama masu tawali’u, kada ɗayanku ya riƙa yi wa wani alfahari, kada kuma wani ya zalunci wani.’ [Muslim #2865]. An karɓo daga Abu Malik Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Abubuwa guda huɗu a cikin al’ummata suna daga ayyukan jahiliyya, kuma ba za su daina ba....” Daga cikinsu Annabi (ﷺ) ya ambaci alfahari da asali. [Muslim #934]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kashedi ga masu riƙe dukiyarsu suna rowar ta ga mabuƙata da yin aikin alheri, har ma kuma suna umartar wasu da su riƙa yin rowar dukiyarsu, kuma suna ɓoye dukiyar da Allah ya ni’imta su da ita don kada a san suna da ita a nemi taimakonsu, ko kada a zarge su da rowa, don haka ba sa barin wata alama a tare da su a tufafinsu ko a cimarsu ko muhallinsu ko abin hawansu. To masu irin wannan hali, Allah ya tanadar musu uƙuba ta wulaƙanci. Yana daga cikin siffofin waɗannan mutane, har ila yau, idan sun ba da dukiyarsu, to suna yin haka ne don mutane su gani su yaba musu, ba don Allah suke yi ba. Ga su kuma imaninsu da Allah bai taka kara ya karya ba, balle su nemi kusanci da shi, kuma ba sa imani da ranar lahira, ballantana su yi kwaɗayin ladan cikinta. Shaiɗan ne yake tare da su yana ƙawata musu waɗannan munanan ayyuka. To duk wanda yake Shaiɗan ne abokinsa, yana masa biyayya a kan abin da yake umartar sa da shi, to lalle wannan aboki ya yi matuƙar muni. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci waɗannan masu rowar da dukiyarsu, kuma suna umartar wasu da yin rowa, da cewa me, zai cutar da su idan sun yi imani da Allah, kuma sun ciyar daga dukiyar da Allah ya ba su? Kuma Allah masani ne game da halin waɗannan mutane. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, ba ya zaluntar kowa cikin bayinsa da kowane irin nau’i na zalunci. Hasali ma idan mutum ya yi aiki na ƙwarai guda ɗaya, to zai ninka masa ladansa, kuma ya ba shi wani sakamako mai girma daga wurinsa, watau gidan Aljanna da abin da ta ƙunsa na ni’ima. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk abin da zai wakana a ranar alƙiyama, zai wakana ne da shaidar manzannin Allah. Domin Allah zai fito wa kowace al’umma da annabinta ya yi mata shaida, ya tabbatar da cewa, ya isar musu da saƙon Allah; ita ma wannan al’umma ta Annabi Muhammadu (ﷺ), zai zo ya ba da shaida a kansu cewa, ya isar musu da saƙon Allah. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce masa: “Karanta mini Alƙur’ani.” Sai ɗan Mas’ud ya ce: “Ni zan karanta maka Alƙur’ani, alhali kai aka saukar wa da shi?” Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk da haka.” Sai na karanta masa Suratun Nisa’i, har sai da na zo daidai faɗarsa (Mai tsarki da daukaka): “To yaya al’amarin zai kasance idan muka zo wa kowace al’umma da mai mata shaida, kai kuma muka zo da kai a matsayin mai shaida a kan waɗannan?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ya ishe ka haka.” Sai na waiwaya na kalle shi, sai na ga idanuwansa suna zubar da hawaye.” [Bukhari #5050]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da zai faru a wannan ranar da cewa, waɗanda suka kafirce wa Allah, kuma suka saɓa wa wannan Manzo nasa, za su yi burin ina ma a daidaita su da ƙasa, wato ta haɗiye su, a binne su a cikinta, su zama ƙasa, domin su tsira daga fuskantar hisabi. Alhali kuwa ba su isa su ɓoye wa Allah komai ba daga ayyukansu da maganganunsu, za su fito su yi iƙirari da laifukansu. Idan ma harsunansu sun ƙi su furta laifukansu, to gaɓoɓinsu ne za su bayyana komai da komai, kamar yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa a Suratu Ya Sin , aya ta 65.

  43. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡرَبُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنتُمۡ سُكَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَعۡلَمُواْ مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغۡتَسِلُواْۚ وَإِن كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوۡ جَآءَ أَحَدٞ مِّنكُم مِّنَ ٱلۡغَآئِطِ أَوۡ لَٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمۡ تَجِدُواْ مَآءٗ فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدٗا طَيِّبٗا فَٱمۡسَحُواْ بِوُجُوهِكُمۡ وَأَيۡدِيكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا

    Open ayah 4:43

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku kusanci salla alhalin kuna cikin maye har sai kun san abin da kuke faɗa, haka mai janaba, sai dai in masu ƙetara hanya ne, har sai kun yi wanka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya ko a halin tafiya, ko ɗaya daga cikinku ya dawo daga bahaya ko kuma kuka sadu da mata kuma ba ku sami ruwa ba, to sai ku nufi doron ƙasa mai tsarki ku yi taimama, sai ku shafi fuskokinku da hannayenku. Lalle Allah Ya kasance Mai afuwa ne, Mai gafara. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga muminai cewa, kada su kusanci salla, watau kada su shige ta alhali suna cikin halin maye, har sai sun wartsake. An karɓo daga Ali ɗan Abu Talib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Abdurrahman ɗan Auf ya shirya mana abinci, ya gayyace mu, ya ba mu giya muka sha, har muka bugu, sai lokacin salla ya yi, sai suka sa ni limanci, sai na karanta Suratul Kafirun kamar haka: “Ya ku kafirai, ba zan bauta wa abin da kuke bauta wa ba, mu kuma nuna bautar abin da kuke bauta wa.” Sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku kusanci salla alhalin kuna cikin maye, har sai kun san abin da kuke faɗa.” [Tirmizi #3026]. Wannan ayar an shafe ta da ayar da ta haramta giya gaba ɗaya da ke cikin Suratul Ma’idah , aya ta 90. Haka kuma Allah ya hana su salla, ko shiga masallaci lokacin da suke cikin halin janaba, har sai sun yi wanka, sai dai wanda wucewa ya zo yi ta ciki ba zama ba. Amma ga wanda yake rashin lafiya, ba zai iya amfani da ruwa ba, ko matafiyi da ya rasa ruwa, ko wanda ya yi bawali ko bahaya, ya rasa ruwan wanka, to hukuncinsa shi ne ya yi taimama a doron ƙasa mai tsarki, ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Mun fita tare da Manzon Allah (ﷺ) a ɗaya daga cikin tafiye-tafiyensa, sai da muka isa wata sahara, ko wani wuri mai suna Zatul Jaishi, sai abin wuyana ya tsinke ya faɗi, sai Manzon Allah (ﷺ) ya tsaya neman sa, kuma ba ruwa tare da su. Sai sahabbai suka je wurin Abubakar suka ce: ‘Ba ka ga abin da A’isha ta yi ba, ta dakatar da Annabi (ﷺ) da sauran mutane, ga shi kuma ba ruwa tare da su?’ Sai Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya zo ya same ni, Annabi (ﷺ) ya ɗora kansa a kan cinyata yana barci, sai ya ce: ‘Kin dakatar da Annabi (ﷺ) tare da mutane, alhalin ba sa kusa da ruwa, kuma ba ruwa tare da su.’ Sai A’isha ta ce: “Sai Abubakar ya yi mini faɗa, ya faɗi abin da Allah ya ba shi damar faɗa, ya riƙa zungurin kwankwasona da hannunsa, ni kuma na kasa motsi saboda Manzon Allah (ﷺ) yana kwance a cinyata. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya wayi gari ba ruwa tare da shi, sai Allah ya saukar da ayar taimama, suka yi taimama.” Sai Usaidu ɗan Hudhairu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ba wannan ce farkon albarkarku ba, ya iyalan gidan Abubakar.” Ai’sha ta ce: “Sai muka tashi raƙumin da nake kansa, sai ga abin wuyan a ƙarƙashinsa.” [Bukhari #334, da Muslim #367]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, shi mai afuwa ne, mai gafara ga zunubban bayinsa da gajiyawarsu.

  44. أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبٗا مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ يَشۡتَرُونَ ٱلضَّلَٰلَةَ وَيُرِيدُونَ أَن تَضِلُّواْ ٱلسَّبِيلَ

    Open ayah 4:44

    Shin ba ka ga waɗannan da aka ba su wani rabo na ilimin Littafi ba, suna sayen ɓata, kuma suna nufin su ga kun ɓace daga kan hanya?

  45. وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِأَعۡدَآئِكُمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَلِيّٗا وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ نَصِيرٗا

    Open ayah 4:45

    Allah kuma Shi ne mafi sanin maƙiyanku. Kuma Allah Ya isa Ya zama majiɓinci (gare ku), kuma Ya isa Ya zama Mai taimako (gare ku).

  46. مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ وَيَقُولُونَ سَمِعۡنَا وَعَصَيۡنَا وَٱسۡمَعۡ غَيۡرَ مُسۡمَعٖ وَرَٰعِنَا لَيَّۢا بِأَلۡسِنَتِهِمۡ وَطَعۡنٗا فِي ٱلدِّينِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَا وَٱسۡمَعۡ وَٱنظُرۡنَا لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡ وَأَقۡوَمَ وَلَٰكِن لَّعَنَهُمُ ٱللَّهُ بِكُفۡرِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُونَ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 4:46

    Cikin waɗanda suka zama Yahudawa akwai waɗanda suke juyar da kalmomi daga bigirensu, kuma suna cewa: “Mun ji, kuma mun saɓa, kuma ka saurara, kai ba abin a saurare ka ba ne, kuma ‘ra’ina’ .” Suna masu karkatar da harashensu kuma don su soki addini. Da za su ce: “Mun ji, mun yi ɗa’a, kuma ka saurare mu, kuma ka jira mu.” da ya kasance mafi alheri gare su, kuma ya fi zama miƙaƙƙiyar (hanya), sai dai Allah Ya riga Ya tsine musu saboda kafircinsu, ba za su yi imani ba sai kaɗan. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana gaya wa Annabinsa (ﷺ) cewa, shin bai ga Yahudawa da Nasara ba, waɗanda Allah ya ba su wani rabo na ilimi, amma kuma suna zaɓar ɓata maimakon shiriya, sannan suna son ganin su ma muminai sun ɓace sun bar hanyar shiriya? Allah kuma shi ya fi sanin maƙiyansu, don haka shi ne zai kare su daga sharrinsu da makircinsu, ya ba su nasara a kansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Manzonsa (ﷺ) halin Yahudawa masu canza ayoyin Attaura, ko su canza musu ma’anoni. Kuma idan sun zo wurin Annabi (ﷺ), sai su riƙa yi masa gatse suna cewa: “Mun ji abin da kake faɗa, amma ba za mu bi ba;” su riƙa nuna masa rashin ladabi, suna cewa: “Ka saurare mu, Allah ya kurumtar da kai, ya hana ka ji,” suna zagin sa da waɗansu maganganu, suna ce masa ‘ra’ina’, wato kamar suna nufin: “Ka ba mu jinka,” amma ba haka suke nufi ba; suna karkatar da harshensu ne da wata mummunar ma’ana, watau ‘daƙiƙi’ da harshensu. Manufarsu kawai ita ce sukan addinin Musulunci, ta hanyar yi wa Annabi (ﷺ) shaƙiyanci. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Yahudawan cewa, ai da kamata ya yi su ce: “Mun ji kuma mun bi, kuma ka saurare mu, ka dakace mu don mu fahimci abin da kake faɗa mana,” domin faɗar haka ita ce ta fi musu alheri, kuma ta fi zama miƙaƙƙiyar magana. To amma ina! Ba za su faɗi haka ba, saboda Allah ya riga ya tsine musu, ya nisanta su daga rahamarsa saboda kafircinsu, ba sa yin imani sai ɗan kaɗan wanda ba zai amfana musu komai ba.

  47. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ ءَامِنُواْ بِمَا نَزَّلۡنَا مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُم مِّن قَبۡلِ أَن نَّطۡمِسَ وُجُوهٗا فَنَرُدَّهَا عَلَىٰٓ أَدۡبَارِهَآ أَوۡ نَلۡعَنَهُمۡ كَمَا لَعَنَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلسَّبۡتِۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ مَفۡعُولًا

    Open ayah 4:47

    Ya ku waɗanda aka ba su littafi, ku yi imani da abin da Muka saukar mai gaskata abin da yake tare da ku, tun kafin Mu shafe wasu fuskoki, Mu mayar da su bayansu, ko kuma Mu la’ance su irin yadda Muka la’anci ma’abota ranar Asabar. Kuma al’amarin Allah ya kasance abin zartarwa ne.

  48. إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱفۡتَرَىٰٓ إِثۡمًا عَظِيمًا

    Open ayah 4:48

    Lalle Allah ba Ya gafarta a yi shirka da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda Ya ga dama. Kuma duk wanda ya yi shirka da Allah, to haƙiƙa ya ƙirƙiri wani gagarumin laifi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana jan kunnen Yahudawa da Nasara ne, waɗanda ya saukar musu da littafin Attaura da Linjila, da lalle su yi imani da Alƙur’ani wanda ya saukar wa Annabinsa Muhammad (ﷺ), wanda kuma ya ƙunshi abin da yake gaskata littattafan da aka saukar musu, tun kafin ya shafe fuskokinsu, ya mayar musu da su bayansu, ko kuma ya kore su daga rahamarsa, ya azabtar da su, kamar yadda ya yi wa ma’abota ranar Assabar; watau waɗanda aka hana su kamun kifi ranar Asabar, sai suka riƙa yin dabara suna kamun kifi a ranar, sai Allah ya mayar da su birrai, kamar yadda ya ambata a Suratul Baƙara , aya ta 154, da Suratul A’araf aya ta 163-166. Kuma idan al’amarin Allah ya zo, to ba makawa sai ya tabbata. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba zai gafarta wa duk wanda ya yi shirka, watau ya haɗa wani da shi a wajen bauta ba, amma yana gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda ya ga dama. Duk wanda ya yi shirka, to haƙiƙa ya tafka babban laifi. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: Allah mai girma da buwaya yana cewa: “Duk wanda ya haɗu da ni da kimanin cikin ƙasa na laifuka, sannan ba ya haɗa wani da ni wajen bauta, to zan haɗu da shi da kimanin cikin ƙasa na gafara.” [Muslim #2687]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na tambayi Annabi (ﷺ): “Wane zunubi ne ya fi girma a wurin Allah?” Sai ya ce: “Ka sanya wa Allah kishiya, alhali shi ya halicce ka.” Sai na ce: “Lalle wannan babban abu ne....” [Bukhari #4477 da Muslim #86].

  49. أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يُزَكُّونَ أَنفُسَهُمۚ بَلِ ٱللَّهُ يُزَكِّي مَن يَشَآءُ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلًا

    Open ayah 4:49

    Shin ba ka ganin waɗannan da suke tsarkake kawunansu? Ba haka ba ne, Allah ne Yake tsarkake wanda Ya ga dama, kuma ba za a zalunce su ba ko da gwargwadon zaren ƙwallon dabino ne.

  50. ٱنظُرۡ كَيۡفَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَكَفَىٰ بِهِۦٓ إِثۡمٗا مُّبِينًا 

    Open ayah 4:50

    Duba ka ga yadda suke ƙirƙirar ƙarya su jingina wa Allah; kuma yin haka kaɗai ya isa zama wani zunubi mabayyani.

  51. أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبٗا مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡجِبۡتِ وَٱلطَّٰغُوتِ وَيَقُولُونَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ هَٰٓؤُلَآءِ أَهۡدَىٰ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ سَبِيلًا

    Open ayah 4:51

    Shin ba ka ganin waɗanda aka ba su wani rabo na ilimin Littafi, suna yin imani da Jibtu da Ɗagutu , kuma suna faɗa wa waɗanda suka kafirta cewa: “Waɗannan su suka fi waɗanda suka yi imani shiriya.”?

  52. أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُۖ وَمَن يَلۡعَنِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ نَصِيرًا

    Open ayah 4:52

    Waɗannan su ne waɗanda Allah Ya la’ance su; duk kuwa wanda Allah Ya la’anta, to ba za ka taɓa sama masa wani mataimaki ba.

  53. أَمۡ لَهُمۡ نَصِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُلۡكِ فَإِذٗا لَّا يُؤۡتُونَ ٱلنَّاسَ نَقِيرًا

    Open ayah 4:53

    Shin suna da wani kaso ne na mulki? To da haka ne da kuwa ba za su ba wa mutane ko da gwargwadon ɗigon bayan dabino ba.

  54. أَمۡ يَحۡسُدُونَ ٱلنَّاسَ عَلَىٰ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۖ فَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ ءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَءَاتَيۡنَٰهُم مُّلۡكًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:54

    Shin yanzu za su riƙa yi wa mutane hassada ne a kan abin da Allah Ya ba su na falalarsa? To haƙiƙa Mun bai wa zurriyar gidan Ibrahimu Littafi da kuma hikima, kuma Mun ba su wani mulki mai girma.

  55. فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ بِهِۦ وَمِنۡهُم مَّن صَدَّ عَنۡهُۚ وَكَفَىٰ بِجَهَنَّمَ سَعِيرًا

    Open ayah 4:55

    To daga cikinsu akwai wanda ya yi imani da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya bijire masa. Jahannama kuwa ta isa wurin ƙuna.

  56. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا سَوۡفَ نُصۡلِيهِمۡ نَارٗا كُلَّمَا نَضِجَتۡ جُلُودُهُم بَدَّلۡنَٰهُمۡ جُلُودًا غَيۡرَهَا لِيَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَزِيزًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:56

    Lalle waɗanda suka kafirce wa ayoyinmu, za Mu shigar da su wata wuta, duk lokacin da fatunsu suka ƙone, sai Mu musanya musu da wasu fatun daban, don su ɗanɗani azaba. Lalle Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima.

  57. وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ سَنُدۡخِلُهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَنُدۡخِلُهُمۡ ظِلّٗا ظَلِيلًا

    Open ayah 4:57

    Waɗanda suka yi imani kuwa, kuma suka yi aiki nagari, to za Mu shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada; suna da mata tsarkaka a cikinsu; kuma za Mu shigar da su cikin wata inuwa, inuwa mayalwaciya marar gushewa. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, kada ya yi mamakin waɗannan Yahudawa da Nasara da ire-irensu, waɗanda suke yabon kawunansu, suna wanke kansu daga laifuka, tare da cewa ba haka al’amarin yake ba, Allah ne kaɗai yake yabon waɗanda ya ga dama daga cikin bayinsa waɗanda suka cancanci yabo. Kuma shi Allah ba ya zaluntar bayinsa da komai duk ƙanƙantarsa. Dubi yadda waɗannan masu yabon kawunansu suke ƙagar ƙarya su jingina wa Allah. Ba shakka wannan laifi ne bayyananne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake ce wa Annabinsa, ashe ba zai yi mamakin halin Yahudawa ba waɗanda Allah ya ba su wani kaso na ilimin Attaura, amma kuma suna yin imani da Jibtu , shi ne duk wani abu marar amfani a addini, kamar sihiri da canfi da makamantansu? Hakanan suna yin imani da Ɗagutu , shi ne duk abin da bawa ya ƙetare iyakokin Allah ta dalilinsa, kamar wani abin bauta ko wani shugaba ko wani abin yi wa biyayya. Sannan kuma waɗannan Yahudawa su ne suke faɗa wa kafirai cewa, wai hanyar da suke a kai ta fi hanyar da muminai suke a kai zama hanyar shiriya, wato dai a wajensu mushrikai sun fi muminai bin hanyar shiriya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da masu wannan da’awar kuma ya la’ance su. Duk kuma wanda Allah ya la’ance shi, to ba za ka taɓa sama masa mai taimakon sa ko ya jiɓinci al’amarinsa ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da Ka’abu ɗan Ashrafu ya je Makka, sai Ƙuraishawa suka ce masa: “Kai ne ka fi kowa a Madina, kuma kai ne shugabansu.” Sai ya ce: “Haka ne.” Sai suka ce: “Shin ba ka ga wannan mutumin mai yankakken baya ba (watau wanda ba shi da ‘ya’ya) yana da’awar cewa ya fi mutanensa, alhalin mu ne masu kula da alhazai, mu ne masu hidimar ɗakin Ka’aba?” Sai aka saukar da ayar: “Lalle maƙiyinka shi ne mai yankakken baya.” Da kuma faɗar Allah: “Shin ba ka ga waɗanda aka ba wani rabo na littafi ba suna yin imani da Jibtu da Ɗagutu ....” har zuwa ƙarshen aya ta 52. [Nasa’i, As-Sunana Al-Kubra #11643]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, shin waɗannan Yahudawan suna da wani kaso ne na mulkin Allah da ya danƙa a hannunsu, wanda har za su fifita wanda suka ga dama da soye-soyen zukatansu, har kuma su iya hana Annabi (ﷺ) da sahabbansa wannan matsayi, su ba da shi ga waɗanda suke kafirai? Ma’ana dai, babu irin wannan rabon a hannunsu da za su iya yin wannan aika-aika. Domin da a ce wannan rabon mulki a hannunsu yake, da ba za su iya ba wa mutane ko da ɗan kaɗan ba, saboda tsananin rowarsu. Ko kuma abin da ya sa su irin wancan hukunci shi ne hassadarsu ga Annabi (ﷺ) da sahabbansa a kan annabcin da Allah ya ba shi, ga shi kuma Balarabe, ba daga gidan Banu Isra’ila ba. Me ya sa za su riƙa yi masa hassada, tare da cewa ba wannan ce farkon falalar da Allah yake yi wa bayinsa ba? Sun manta ne cewa, Allah ya ba wa kakanninsu daga cikin zurriyyar Annabi Ibrahim falala, ya ba su annabta, ya saukar musu da littattafai da hikima, kuma ya ba su mulki mai girman gaske, kamar irin wanda ya ba wa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi)? To amma duk da haka daga cikin ma’abota Littafi akwai wanda ya yi imani da Annabi (ﷺ) da Alƙur’anin da ya zo da shi, daga cikinsu kuma akwai wanda bai yi imani ba, kuma ya riƙa kange mutane yana hana su yin imani. To su sani cewa, azabar wuta mai ruruwa ta ishe su; Allah zai shigar da kafirai wutar Jahannama inda za a babbake su a cikinta. Duk sa’adda fatun jikinsu suka ƙone, sai Allah ya canza musu wasu fatun daban, domin su ci gaba da ɗanɗanar raɗaɗin azaba madawwamiya. Lalle Allah ya tabbata Gagara-badau ne, Gwani, mai hikima. To amma kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka yi kyawawan ayyuka, Allah zai shigar da su gidajen Aljanna, waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su ci gaba da zama a cikinsu har abada, kuma ni’imar da suke ciki ba mai yankewa ba ce har abada. Suna da matan aure tsarkaka a cikin waɗannan gidaje, kuma Allah zai shigar da su wata inuwa marar gushewa.

  58. ۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تُؤَدُّواْ ٱلۡأَمَٰنَٰتِ إِلَىٰٓ أَهۡلِهَا وَإِذَا حَكَمۡتُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحۡكُمُواْ بِٱلۡعَدۡلِۚ إِنَّ ٱللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا

    Open ayah 4:58

    Lalle Allah Yana umartar ku da ku mayar da amanoni ga masu su, kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, to ku yi hukunci da adalci. Lalle kam madalla da abin da Allah Yake muku wa’azi da shi. Lalle Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani.

  59. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا

    Open ayah 4:59

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi ɗa’a ga Allah, kuma ku yi ɗa’a ga Manzo da kuma majiɓinta lamarinku. Idan kun yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar ƙarshe. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi kyan makoma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar bayinsa muminai da su mayar da amana ga masu ita, kuma idan za su yi hukunci tsakanin mutane, to su yi musu adalci. Madalla da wannan umarni da Allah yake yi na mayar da amana ga masu ita da hukunci na adalci tsakanin mutane. Lalle Allah mai jin maganganun kowa ne, mai ganin duk ayyukansu, don haka zai yi musu sakayya a kansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya ci gaba da umartar muminai, da su yi masa ɗa’a, kuma su yi wa Manzonsa (ﷺ) ɗa’a, ta hanyar aiki da umarninsu da barin abin da suka hana. Hakanan su yi ɗa’a ga shugabanninsu na addini, watau malamai da shugabanni masu mulki, amma ɗa’ar da bata saɓa wa Allah da Manzonsa (ﷺ) ba. Duk sanda suka yi umarni da abin da ya saɓa wa Allah da Manzonsa, to ba za a yi musu ɗa’a a kai ba. An karɓo daga Ali ɗan Abu Ɗalib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Annabi (ﷺ) ya aiki wata runduna, ya shugabantar musu da wani mutumin Madina, ya umarce su da su yi masa biyayya. Sai wani lokaci suka ɓata masa rai, ya yi fushi, sai ya ce: Ba Annabi (ﷺ) ya umarce ku da ku yi mini ɗa’a ba?” Suka ce: “An yi haka.” Sai ya ce: “Ku tara mini ƙirare.” Sai suka tara masa. Sai ya ce: “Ku hura mini wuta.” Sai suka hura. Sai ya ce: “To ku faɗa cikinta.” Sai wasu suka yunƙura za su faɗa, sai wasu suka riƙe su, suna ce musu: “Saboda tsoron shiga wuta ne ya sa muka gudu zuwa ga Annabi (ﷺ).” Haka suka yi ta jayayya har wutar ta mutu, shi kuma Shugaban nasu ya huce. Sai labari ya je wa Annabi (ﷺ), sai ya ce: “Da sun kuskura sun shiga cikinta, to da ba za su fito ba har zuwa tashin alƙiyama. Ana yin ɗa’a ne ga abin da ya dace da shari’a.” [Bukhari #4340, da Muslim #1840]. Har wa yau dai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da cewa, idan sun yi saɓani a tsakaninsu, to su nemi warware wannan saɓani ta hanyar komawa ga littafin Allah, Alƙur’ani, da kuma sunnar Manzon Allah (ﷺ) idan har sun yi imani da Allah da ranar lahira. Yin haka shi ne mafi alheri gare su a addininsu da duniyarsu da lahirarsu.

  60. أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يَزۡعُمُونَ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوٓاْ إِلَى ٱلطَّٰغُوتِ وَقَدۡ أُمِرُوٓاْ أَن يَكۡفُرُواْ بِهِۦۖ وَيُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُضِلَّهُمۡ ضَلَٰلَۢا بَعِيدٗا 

    Open ayah 4:60

    Shin ba ka ganin waɗannan da suke riya cewa sun yi imani da abin da aka saukar maka, da abin da aka saukar gabaninka, suna nufin su kai hukunci gaban Ɗagutu (wanin Allah), alhalin an umarce su da su kafirce masa, Shaiɗan kuma yana nufin ya ɓatar da su ɓata mai nisa?

  61. وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَإِلَى ٱلرَّسُولِ رَأَيۡتَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ يَصُدُّونَ عَنكَ صُدُودٗا

    Open ayah 4:61

    Kuma idan an ce da su: “Ku zo ga abin da Allah Ya saukar, kuma ku zo ga wannan Manzo,” sai kawai ka ga munafuƙai suna bijire maka matuƙar bijirewa.

  62. فَكَيۡفَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ ثُمَّ جَآءُوكَ يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ إِنۡ أَرَدۡنَآ إِلَّآ إِحۡسَٰنٗا وَتَوۡفِيقًا

    Open ayah 4:62

    To yaya halinsu zai kasance idan wata musiba ta sauka a kansu saboda abin da hannayensu suka gabatar, sannan sai su zo maka suna rantsuwa da Allah, (suna cewa): “Ba ma nufin wani abu sai kyautatawa da kuma haɗin kai.”?

  63. أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَعِظۡهُمۡ وَقُل لَّهُمۡ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ قَوۡلَۢا بَلِيغٗا

    Open ayah 4:63

    Waɗannan su ne waɗanda Allah Yake sane da abin da ke cikin zukatansu, don haka ka kawar da kai daga kansu kuma ka yi musu wa’azi kuma ka faɗa musu magana a karan-kawunansu magana mai shiga zukata.

  64. وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ إِذ ظَّلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ جَآءُوكَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ ٱللَّهَ وَٱسۡتَغۡفَرَ لَهُمُ ٱلرَّسُولُ لَوَجَدُواْ ٱللَّهَ تَوَّابٗا رَّحِيمٗا

    Open ayah 4:64

    Kuma ba Mu taɓa aiko wani manzo ba, face sai don a yi masa ɗa’a da izinin Allah. Kuma da a ce lokacin da suka zalunci kawunansu sun zo maka, sun nemi Allah Ya gafarta musu, sannan Manzo ya roƙa musu gafara, to tabbas da sun sami Allah Yana Mai yawan karɓar tuba, Mai jin ƙai.

  65. فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَرَجٗا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمٗا

    Open ayah 4:65

    To ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba har sai sun kai hukunci a gabanka game da duk abin da ya faru na saɓani a tsakaninsu, sannan ba su ji wani ƙunci a cikin zukatansu ba game da abin da ka zartar na hukunci, kuma su miƙa wuya miƙawa gaba ɗaya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa Annabinsa (ﷺ) ishara da cewa, shin bai yi mamakin halin waɗanda suke ƙaryar sun yi imani da Alƙur’ani da littattafan da aka saukar a baya ba, amma duk da haka suna kai hukuncinsu ga wani abin da ya saɓa wa abin da Allah ya saukar, alhalin an umarce su da su kafirce masa, kuma Shaiɗan yana neman ya ɓatar da su su yi nesa da hanyar gaskiya? Duk sa’adda za a kirawo su don a yi musu hukunci da abin da Allah ya saukar a Alƙur’ani da sunnar Annabi (ﷺ), sai munafuƙan su riƙa bijire wa wannan kiran, suna kuma hana mutane sauraren sa. To yaya halinsu zai kasance yayin da wata musiba ta auko musu saboda kafircinsu da zunubbansu, sannan suka garzayo wajen shi Ma’aiki (ﷺ) suna ba da uzuri, tare da rantsuwar ƙarya cewa su fa ba su kai hukuncinsu ga masu hukuncin da ya saɓa wa na Allah ba, sai don su ga sun kyautata musu, kuma an sami fahimtar juna a tsakani, amma su ba su yarda da cewa wannan hukuncin gaskiya ne ba? An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Akwai wani boka sunanshi Abu Burdatul Aslami, Yahudawa suna kai ƙara wajensa ya yi musu hukunci. Sai wasu Musulmi daga ƙabilar Aslam suka yi rigima a tsakaninsu, sai suka kai ƙara wajensa. Sai wannan ayar ta sauka. [Ibn Abi Hatim, Tafsir #5547 da Ibn Jarir At-Tabari 8:510 (Shakir)]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya san abin da yake cikin zukatansu na munafunci da mummunar manufa, kuma zai yi musu sakayya a kai, kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi watsi da su, kuma ya yi musu wa’azi, ya faɗa musu magana mai ratsa jiki, mai shiga zukata. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimar aiko da annabawa zuwa mutanensu da cewa; ya aiko su ne don a yi musu ɗa’a, a aikata abin da suka yi umarni da shi, a bar abin da suka hana. Kuma Allah ya yi haka ne da izininsa da kuma ganin damarsa. Waɗannan munafuƙai masu kai ƙara wajen wasu masu saɓa wa Allah da Manzonsa, Allah ya faɗa musu cewa, da a ce lokacin da za su faɗa cikin wancan zunubi na kai ƙara ga wanin Allah da Manzonsa (ﷺ), da sun zo wajen Manzon Allah (ﷺ) sun faɗa masa laifin da suka aikata, sannan suka nemi gafarar Allah, suka tuba, kuma Manzon Allah (ﷺ) shi ma ya nema musu gafara a wurin Allah, da sun yi haka, da sun sami yafiya daga Allah da karɓar tubansu da yi musu rahama. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi rantsuwa da kansa cewa, Na rantse da Ubangijinka, ya kai wannan Annabi, babu wanda zai yi imani karɓaɓɓe, har sai sun sa ka mai yanke hukunci a tsakaninsu game da duk wani abu da zai faru a tsakaninsu na husuma, sannan idan ka yanke hukunci a tsakaninsu, kada su ji wani ƙunci ko takuruwa a zukatansu game da hukuncin da ka yanke, su kuma miƙa wuya su sallama gaba ɗaya. An karɓo daga Abdullahi ɗan Zubairu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani mutumin Madina rigima ta haɗa shi da Zubairu ɗan Awwam (Allah ya kara masa yarda) game da wata magudanar ruwa wadda suke shayar da dabinonsu daga gare ta. Sai mutumin nan na Madina ya ce wa Zubair: “Ka sako wannan ruwan ya ci gaba da wucewa.” Sai Zubairu ya ƙi yarda ya saki. Sai suka kai ƙara gaban Manzon Allah (ﷺ). Sai Manzon Allah (ﷺ) ya yanke hukunci da ce wa Zubairu: “Ka shayar da dabinonka, sannan ka saki ruwan zuwa gonar maƙocinka.” Sai wannan mutumin Madinan ya ji haushin wannan hukunci, ya ce: “Don yana ɗan goggonka ko?” Sai fuskar Annabi (ﷺ) ta canza, sai ya ce: “Ya Zubairu, shayar da gonarka, sannan ka toshe ruwan har sai ya koma tushen shingen gonarka.” Zubairu ya ce: “Ina tsammanin wannan ayar a kan haka ta sauka.” [Bukhari #2359, da Muslim #2357]. Wannan maganar ta ƙarshe ba ta nuna a dalilin wannan ƙissa ne ayar ta sauka, sai dai ayar ta shafi irin wannan abu da ya faru a wannan ƙissa.

  66. وَلَوۡ أَنَّا كَتَبۡنَا عَلَيۡهِمۡ أَنِ ٱقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ أَوِ ٱخۡرُجُواْ مِن دِيَٰرِكُم مَّا فَعَلُوهُ إِلَّا قَلِيلٞ مِّنۡهُمۡۖ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ فَعَلُواْ مَا يُوعَظُونَ بِهِۦ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡ وَأَشَدَّ تَثۡبِيتٗا

    Open ayah 4:66

    Kuma in da a ce lalle Mun wajabta musu cewa: “Ku kashe kawunanku ko ku fita daga gidajenku,” da ‘yan kaɗan ne daga cikinsu za su aikata hakan. Da a ce sun aikata abin da ake musu wa’azi da shi, to da ya fi alheri, kuma da ya fi tsananin tabbatar da su (a kan hanya madaidaiciya).

  67. وَإِذٗا لَّأٓتَيۡنَٰهُم مِّن لَّدُنَّآ أَجۡرًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:67

    Da sun yi hakan kuwa tabbas da Mun ba su wani babban lada daga wajenmu.

  68. وَلَهَدَيۡنَٰهُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

    Open ayah 4:68

    Kuma tabbas da Mun shiryar da su tafarki madaidaici.

  69. وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَٰٓئِكَ رَفِيقٗا

    Open ayah 4:69

    Kuma duk waɗanda suka yi wa Allah ɗa’a da wannan Manzon, to waɗannan suna tare da waɗanda Allah Ya yi musu ni’ima, su ne annabawa da siddiƙai da shahidai da salihan bayi. Kuma madalla da waɗannan abokai.

  70. ذَٰلِكَ ٱلۡفَضۡلُ مِنَ ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ عَلِيمٗا 

    Open ayah 4:70

    Wannan falala ce daga Allah. Kuma Allah Ya isa masanin (dukkan lamura). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, waɗannan mutane masu kai ƙara gaban waɗanda za su yi musu hukuncin da ba na Allah ba, da za a ce musu su kashe kansu, ko sashinsu ya kashe wani sashi, ko kuma su fita su bar gidajensu, to ‘yan kaɗan ne daga cikinsu za su aikata hakan. Da a ce za su yi aiki da wa’azin da ake yi musu kullum, su bi umarnin Allah da Manzonsa (ﷺ), su bar abin da suka hana su, to da shi ya fi zama alheri a gare su, kuma ya fi tabbatar da su kan tafarki na gaskiya, da kuma Allah ya ba su lada mai girma, kamar yadda ya alƙarwanta musu, kuma ya shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya bi Allah (Mai tsarki da daukaka), ya bi Manzonsa (ﷺ), to zai sami shiga Aljanna, kuma zai kasance tare da ƙungiyar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu ni’imar shiriya zuwa ga hanya madaidaiciya, watau annabawa da siddiƙai, waɗanda suka sami kamala wajen gaskata Allah da Manzonsa da aiki da gaskiya, da kuma shahidai waɗanda aka kashe su a wajen ɗaukaka addinin Allah, da salihai waɗanda suka gyara cikinsu da wajensu. Madalla da irin wannan ƙungiya ta arziki. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi (ﷺ) ya ce: “Ya Manzon Allah (ﷺ), na fi son ka fiye da kaina, kuma na fi son ka fiye da iyayena. Nakan kasance a gida a zaune, amma da zarar na tuna ka sai in kasa daurewa sai na zo na gan ka. To duk lokacin da na tuno mutuwata da mutuwarka, sai in fahimci cewa, idan ka shiga Aljanna, to za a ɗaga matsayinka tare da annabawa; ni kuma idan na shiga Aljanna, to ina tsoron ba zan ƙara ganin ka ba.” Annabi (ﷺ) ya yi shiru bai ba shi amsa ba, har sai da Mala’ika Jibrilu ya saukar da wannan ayar.” [At-Tabarani, Al-Mu’ujam Al-Ausat #477]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, wannan sakamako da ya yi wa masu biyayya ga Allah da Annabinsa, wata falala ce daga gare shi da yake ba da ita ga duk wanda ya cancanta ya ba shi. Allah kuma ya isa mai cikakken ilimi game da ayyukan bayinsa, kuma shi ya fi sanin wanda ya fi cancantar shiriya, ya shiryar da shi zuwa ga madaidaicin tafarki.

  71. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ خُذُواْ حِذۡرَكُمۡ فَٱنفِرُواْ ثُبَاتٍ أَوِ ٱنفِرُواْ جَمِيعٗا

    Open ayah 4:71

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi taka-tsantsan, kuma ku fita ƙungiya-ƙungiya, ko kuma ku fita gaba ɗaya.

  72. وَإِنَّ مِنكُمۡ لَمَن لَّيُبَطِّئَنَّ فَإِنۡ أَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةٞ قَالَ قَدۡ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيَّ إِذۡ لَمۡ أَكُن مَّعَهُمۡ شَهِيدٗا

    Open ayah 4:72

    Kuma lalle a cikinku akwai wanda yake daƙilewa, idan wata musiba ta same ku, sai ya ce: “Haƙiƙa Allah Ya yi mini ni’ima da ban halarci (yaƙin) tare da su ba.”

  73. وَلَئِنۡ أَصَٰبَكُمۡ فَضۡلٞ مِّنَ ٱللَّهِ لَيَقُولَنَّ كَأَن لَّمۡ تَكُنۢ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُۥ مَوَدَّةٞ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ مَعَهُمۡ فَأَفُوزَ فَوۡزًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:73

    Amma idan wata falala ta same ku daga Allah, tabbas zai riƙa cewa, kamar daɗai ba wata soyayya tsakaninku da shi: “Ina ma na kasance tare da su, don ni ma in rabauta rabo mai girma?”

  74. ۞فَلۡيُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ يَشۡرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا بِٱلۡأٓخِرَةِۚ وَمَن يُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَيُقۡتَلۡ أَوۡ يَغۡلِبۡ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:74

    To waɗanda suke sayen rayuwar lahira da ta duniya, sai su yi yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah. Duk wanda yake yin yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah kuwa, sai aka kashe shi ko kuma ya yi galaba, to za Mu ba shi lada mai girma.

  75. وَمَا لَكُمۡ لَا تُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلرِّجَالِ وَٱلنِّسَآءِ وَٱلۡوِلۡدَٰنِ ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَآ أَخۡرِجۡنَا مِنۡ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلظَّالِمِ أَهۡلُهَا وَٱجۡعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا وَٱجۡعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ نَصِيرًا

    Open ayah 4:75

    Kuma me ya same ku ne, da ba za ku yi yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah ba, da kuma kuɓutar da raunana maza da mata da yara ƙanana, waɗanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka fitar da mu daga wannan alƙaryar wadda mutanenta suke azzalumai, kuma Ka sanya mana wani majiɓincin lamari daga wurinka, kuma Ka sanya mana wani mai taimako daga wurinka?”

  76. ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱلطَّٰغُوتِ فَقَٰتِلُوٓاْ أَوۡلِيَآءَ ٱلشَّيۡطَٰنِۖ إِنَّ كَيۡدَ ٱلشَّيۡطَٰنِ كَانَ ضَعِيفًا

    Open ayah 4:76

    Waɗanda suka yi imani suna yaƙi ne don ɗaukaka kalmar Allah; waɗanda kuma suka kafirce suna yin yaƙi ne don kare Ɗagutu; to ku yaƙi masoya Shaiɗan; lalle makircin Shaiɗan rarrauna ne. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai ne da su yi taka-tsantsan game da maƙiyansu, ta hanyar zama cikin shiri ko da yaushe. Idan kuma sun zo fita yaƙi, to su fita ƙungiya-ƙungiya, ko kuma su fita gaba ɗaya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗakar da muminai cewa, a cikinsu fa akwai munafuƙai waɗanda ba sa son fita jihadi tare da Manzon Allah (ﷺ), suna kuma hana wasu fita. Duk lokacin da wata masifa ta auka wa muminai waɗanda suka fita jihadi, aka kashe wasu daga cikinsu, ko aka raunana wasu, sai ka ga ɗaya daga cikin munafuƙan nan yana cewa: “Ni dai Allah ya yi mini gyaɗar dogo da ban fita tare da su ba, da yanzu abin da ya same su ni ma ya same ni.” Amma idan Musulmi ne suka ci nasara, suka samo ganima, sai ya dawo yana magana kamar shi ba ɗan’uwa ba ne, kamar babu wani abu na soyayya a tsakaninsa da muminai, yana kuma cewa: “Ina ma na bi su a wannan karon da yanzu da ni za a raba wannan ganimar, ni ma in more sosai.” Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fuskantar da umarni na yin yaƙi don ɗaukaka kalmarsa ga duk masu kwaɗayin samun lada daga Ubangijinsu, waɗanda suka sayi lahira da duniyarsu. Kuma ya yi alƙawarin ba da gagarumin lada ga duk wanda ya yi yaƙi saboda shi, ko maƙiya sun kashe shi a fagen yaƙi, ko ba su kashe shi ba, shi kam ya yi nasara a kansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɗaitar da muminai da cewa, me zai hana su yin yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah da kuɓutar da raunana daga cikin maza da mata da yara, waɗanda koyaushe suke roƙon Ubangijinsu da ya fitar da su daga garin Makka, wanda mushirikan cikinta ba bin da suke yi sai zalunci. Addu’arsu ita ce Allah ya samar musu da wanda zai jiɓinci lamarinsu ya taimake su ya ceto su daga hannun waɗannan azzalumai. An karɓo daga Ubaidullahi ɗan Abdullahi ɗan Utba ya ce: Na ji Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Ni da mahaifiyata muna cikin waɗannan raunana, ni ina cikin yaran, mahaifiyata kuma tana cikin manyan mata.” [Bukhari #1357]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bambance tsakanin muminai masu yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah da ceto raunana daga zaluncin azzalumai, da kuma waɗanda suke yaƙi don biyayya ga wani abin bauta ba Allah ba. Sannan Allah ya yi umarni da a yaƙi duk wanda ya rungumi Shaiɗan, yana yi masa biyayya, Allah ya tabbatar da cewa, makircin Shaiɗan rarrauna ne ainun, don haka kada ya ba su tsoro.

  77. أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ قِيلَ لَهُمۡ كُفُّوٓاْ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُمۡ يَخۡشَوۡنَ ٱلنَّاسَ كَخَشۡيَةِ ٱللَّهِ أَوۡ أَشَدَّ خَشۡيَةٗۚ وَقَالُواْ رَبَّنَا لِمَ كَتَبۡتَ عَلَيۡنَا ٱلۡقِتَالَ لَوۡلَآ أَخَّرۡتَنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖۗ قُلۡ مَتَٰعُ ٱلدُّنۡيَا قَلِيلٞ وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّمَنِ ٱتَّقَىٰ وَلَا تُظۡلَمُونَ فَتِيلًا

    Open ayah 4:77

    Shin ba ka ganin waɗanda aka ce da su: “Ku kame hannayenku kuma ku tsayar da salla kuma ku bayar da zakka?” To yayin da aka wajabta musu yaƙi, sai ga wani ɓangare daga cikinsu suna jin tsoron mutane kamar yadda suke jin tsoron Allah, ko ma fiye da hakan. Kuma sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, don me Ka wajabta mana yin yaƙi, me ya hana Ka jinkirta mana zuwa wani lokaci makusanci?” Ka ce: “Jin daɗin duniya kaɗan ne, lahira kuwa ita ce mafi alheri ga wanda ya yi taƙawa, kuma ba za a zalunce ku ba, ko da gwargwadon zaren ƙwallon dabino ne.”

  78. أَيۡنَمَا تَكُونُواْ يُدۡرِككُّمُ ٱلۡمَوۡتُ وَلَوۡ كُنتُمۡ فِي بُرُوجٖ مُّشَيَّدَةٖۗ وَإِن تُصِبۡهُمۡ حَسَنَةٞ يَقُولُواْ هَٰذِهِۦ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةٞ يَقُولُواْ هَٰذِهِۦ مِنۡ عِندِكَۚ قُلۡ كُلّٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ فَمَالِ هَٰٓؤُلَآءِ ٱلۡقَوۡمِ لَا يَكَادُونَ يَفۡقَهُونَ حَدِيثٗا

    Open ayah 4:78

    Duk inda kuka kasance mutuwa za ta riske ku, ko da kuna cikin waɗansu ganuwoyi masu tsawo. Kuma idan wani kyakkyawan abu ya same su, sai su ce: “Wannan ai daga Allah ne.” Idan kuma wani mummunan abu ya same su, sai su ce: “Wannan daga wajenka ne.” Ka ce: “Dukkansu daga Allah ne.” Shin me ya sami waɗannan mutane ne ba sa kusa ma da su fahimci zance?

  79. مَّآ أَصَابَكَ مِنۡ حَسَنَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ وَمَآ أَصَابَكَ مِن سَيِّئَةٖ فَمِن نَّفۡسِكَۚ وَأَرۡسَلۡنَٰكَ لِلنَّاسِ رَسُولٗاۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدٗا

    Open ayah 4:79

    Duk wani kyakkyawan abu da ya same ka, to daga Allah ne; duk kuma wani mummunan abu da ya same ka, to daga wajen ka ne. Kuma Mun aiko ka Manzo ga mutane. Kuma Allah Ya isa Mai shaida (a kan haka). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayani ne game da wasu sahabbai waɗanda suka yi ta roƙon a farlanta musu jihadi, alhali ana faɗa musu cewa, su bar maganar yaƙar mushirikai, su dai su tsayar da salla, su ba da zakka, amma sai ba su daina roƙon ba. To yayin da aka farlanta musu yaƙin, sai ga wasu daga cikinsu suna tsoron mutane kamar yadda suke tsoron Allah, ko ma fiye da haka; suka riƙa cewa: Ya Ubangiji, me ya sa ka farlanta mana yaƙi a daidai wannan lokaci, me ya sa ba ka jinkirta shi zuwa wani lokaci daban ba? Sai Allah ya umarci Annabinsa da ya faɗa musu cewa: Komai na duniya wani ɗan jin daɗi ne ƙanƙani, kuma mai gushewa; abin da Allah ya tanadar wa masu taƙawaa da masu yi masa biyayya a lahira, ya fi duniya da abin da yake cikinta, kuma ba za a zalunce su da komai ba. Sannan Allah ya nuna cewa, mutuwar da suke guje wa sai ta riske su a ko’ina za su shiga a bayan ƙasa, ko da kuma za su ɓoye ne a waɗansu ganuwoyi masu dogayen gini da tsaro mai tsanani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin masu ƙaryata Annabi (ﷺ) da cewa, duk sa’adda wani alheri ya same su sai su ce wannan daga Allah ne, wato shi ne ya ba su; idan kuma wani mummunan abu ya same su, sai su camfa Manzon Allah (ﷺ), su ce ai saboda shi ne wannan musifar ta same su. Sai Allah ya umarci Annabi (ﷺ) ya mayar musu da martani cewa, duk abin da ya auku gare su, mai daɗi da maras daɗi, duk daga Allah ne, shi ne ya hukunta faruwarsa ba wani ba, to amma me ya sa masu irin waɗannan maganganu ba sa fahimtar duk wata Magana da ake faɗa musu? A ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa ɗan\'adam cewa, duk abin da ya same shi na farin ciki, kamar haihuwa da dukiya da mulki da sauransu, to ya sani daga Allah ne, falalarsa ce da rahamarsa a gare shi; abin da kuma ya same shi marar daɗi a rayuwarsa, to wannan shi ya jawo wa kansa ta hanyar zunubinsa. Allah kuma ya gaya wa Annabi Muhammadu (ﷺ), cewa shi ne ya aiko shi Manzo ga mutane gaba ɗaya, don ya isar musu da shari’arsa, kuma Allah ya isa ya zama shaida a kan cewa ya isar da wannan saƙo, bai ɓoye komai ba.

  80. مَّن يُطِعِ ٱلرَّسُولَ فَقَدۡ أَطَاعَ ٱللَّهَۖ وَمَن تَوَلَّىٰ فَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظٗا 

    Open ayah 4:80

    Duk wanda ya yi wa wannan Manzo ɗa’a, to haƙiƙa ya yi wa Allah ɗa’a ne; wanda kuwa ya bijire, to ba Mu aiko ka a matsayin mai tsaron su ba.

  81. وَيَقُولُونَ طَاعَةٞ فَإِذَا بَرَزُواْ مِنۡ عِندِكَ بَيَّتَ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ غَيۡرَ ٱلَّذِي تَقُولُۖ وَٱللَّهُ يَكۡتُبُ مَا يُبَيِّتُونَۖ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلًا

    Open ayah 4:81

    Kuma sukan ce: “Ai ba mu da wani abu sai biyayya.” To idan suka fita daga wajenka, sai wata ƙungiya daga cikinsu, su riƙa ƙulla wani abu daban cikin dare, saɓanin abin da suke faɗa; Allah kuwa Yana rubuta duk wani abu da suke ƙullawa da daddare; to ka kawar da kai daga kansu, kuma ka dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa abin dogaro.

  82. أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلۡقُرۡءَانَۚ وَلَوۡ كَانَ مِنۡ عِندِ غَيۡرِ ٱللَّهِ لَوَجَدُواْ فِيهِ ٱخۡتِلَٰفٗا كَثِيرٗا

    Open ayah 4:82

    Shin ba za su yi zuzzurfan tunani game da ayoyin Alƙur’ani ba ne? Kuma da a ce ya kasance daga wajen wani yake ba Allah ba, tabbas da sun sami saɓani mai yawa a cikinsa.

  83. وَإِذَا جَآءَهُمۡ أَمۡرٞ مِّنَ ٱلۡأَمۡنِ أَوِ ٱلۡخَوۡفِ أَذَاعُواْ بِهِۦۖ وَلَوۡ رَدُّوهُ إِلَى ٱلرَّسُولِ وَإِلَىٰٓ أُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنۡهُمۡ لَعَلِمَهُ ٱلَّذِينَ يَسۡتَنۢبِطُونَهُۥ مِنۡهُمۡۗ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَٱتَّبَعۡتُمُ ٱلشَّيۡطَٰنَ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 4:83

    Kuma idan wani lamari ya zo musu wanda ya shafi zaman lafiya ko tsoro, sai su yaɗa shi. Da a ce sun mayar da shi zuwa ga wannan Manzo da shugabanni daga cikinsu, da lalle wanɗanda suke bin ƙwaƙƙwafin al’amarin sun san (dacewar a yaɗa shi ko a’a). Kuma ba don falalar Allah da rahamarsa a gare ku ba, tabbas da kun bi Shaiɗan, in ban da ‘yan kaɗan (daga cikinku).

  84. فَقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا تُكَلَّفُ إِلَّا نَفۡسَكَۚ وَحَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَكُفَّ بَأۡسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَٱللَّهُ أَشَدُّ بَأۡسٗا وَأَشَدُّ تَنكِيلٗا

    Open ayah 4:84

    To ka yi yaƙi domin ɗaukaka kalmar Allah, ba a ɗora maka nauyin tilasta kowa ba sai kanka. Kuma ka zaburar da muminai; Allah zai dankwafe ƙarfin waɗanda suka kafirta; kuma Allah Shi ne Mafi tsananin ƙarfi, kuma Mafi tsananin uƙuba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar da cewa, duk wanda ya yi wa Manzon Allah (ﷺ) ɗa’a, to Allah ya yi wa; wanda kuwa ya bijire masa, to wannan kansa ya cuta, ba za a nemi wani bayani a kansa daga wurin Annabi (ﷺ) ba, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) bai aiko shi don ya zama mai tsaro a kan ayyukan bayinsa, ko mai hisabi a kansu ba. Ya dai aiko shi ne don kawai ya isar musu da saƙon Allah; idan ya isar da saƙon, to ya gama aikinsa, kuma ladansa yana wurin Allah, zai cika masa, ko sun yi masa ɗa’a ko ba su yi ba. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin abin da munafuƙai suke yi yayin da suka zo ga Annabi (ﷺ). Sai su riƙa nuna masa za su yi masa biyayya, kuma ba za su saɓa masa ba, to amma idan sun keɓance su-ya-su cikin dare sai su ƙulla abin da yake saɓanin maganar da suka yi wa Annabi (ﷺ). Sai Allah ya gargaɗe su, da cewa, duk abin da suke ɓoyewa suna saƙawa cikin dare, Allah ya san shi yana rubuta shi, don haka kada su zaci sun kuɓuta daga kamunsa. Ya kuma umarci Annabinsa da ya yi watsi da su, kada ya damu da su, ko ya ɓata lokacinsa a kansu; shi dai ya dogara ga Allah shi kaɗai ya ishe shi mai taimako, kuma mai jiɓintar al’amarinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga munafuƙai da sauran masu jayayya da Annabi (ﷺ), a kan Alƙur’ani da ya zo musu da shi wai ba maganar Allah ba ce, maganar wani ne can daban. Allah ya ja hankalinsu da su yi duba na tsanaki da karatu na ta-nutsu game da ma’anonin Alƙur’ani. Da a ce ba daga Allah yake ba, da sun gamu da ruɗani mai yawa a cikinsa, to amma ba su taɓa ganin wata tufka da warwara ba a cikinsa. Wannan babban dalili ne mai tabbatar da cewa, Alƙur’ani maganar Allah ne, ba ƙirƙirar sa Annabi (ﷺ) ya yi ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin wani mummunan hali na waɗannan munafuƙai, a cikin zamantakewarsu da al’umma. Watau duk lokacin da suka sami wani labari mai alaƙa da samun nasara da zaman lafiya, ko mai alaƙa da da tsoro ko yaƙi, to sai su shiga watsa shi tsakanin jama’a tun kafin ya isa ga Annabi (ﷺ) da manyan sahabbansa, waɗanda su ne ya kamata su duba labarai su tantance wanda ya kamata a saki don zai taimaka wa al’umma, da wanda bai kamata a watsa shi ba don ba zai taimaka wa al’umma ba. To amma su munafuƙai suna watsa kowanne irin labari da suka ji ne, don su kawo ruɗani da saka tsoro a zukatan muminai. Allah ya bayyana cewa, da a ce sun kai waɗannan labarun zuwa ga Annabi (ﷺ) da shugabanninsu, don su duba su tantance na gaskiya da na ƙarya, su kuma tantance wanda yaɗa shi cikin jama’a zai haifar da maslaha, da wanda babu wata maslaha a cikin yaɗa shi. Da sun yi haka, da lalle masu ilimi sun gane bakin zaren kowacce magana, sun fito da bayaninta yadda yake. Allah ya faɗa wa muminai cewa, ba don falalar Allah da ya yi musu ba, da su ma sun zama kamar munafuƙai, sun bi sahun Shaiɗan wajen yayata kowanne irin labari suka ji kafin su tantance shi, sai ‘yan kaɗan daga cikinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa da ya yi yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah, yana mai tabbatar masa cewa, ba a ɗora masa nauyin ba in ba nasa na kansa ba. Sannan ya umarce shi da ya kwaɗaitar da muminai su fita yaƙi, ya ƙarfafa musu gwiwa a kan hakan, tare da sa ran Allah zai dankwafar da duk wani yunƙuri na kafirai, domin ƙarfin Allah ya fi na kowa, kuma shi mai yin uƙuba ne ga wanda ya saɓa masa.

  85. مَّن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةً حَسَنَةٗ يَكُن لَّهُۥ نَصِيبٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةٗ سَيِّئَةٗ يَكُن لَّهُۥ كِفۡلٞ مِّنۡهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقِيتٗا

    Open ayah 4:85

    Duk wanda ya yi (ma wani) kyakkyawar alfarma, zai samu rabonsa na lada daga gare ta; kuma duk wanda ya yi wa wani mummunar alfarma, zai samu rabonsa na zunubi daga gare ta. Kuma Allah Ya kasance Mai kiyaye komai ne.

  86. وَإِذَا حُيِّيتُم بِتَحِيَّةٖ فَحَيُّواْ بِأَحۡسَنَ مِنۡهَآ أَوۡ رُدُّوهَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَسِيبًا

    Open ayah 4:86

    Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to ku amsa da gaisuwar da ta fi wadda aka yi muku kyau, ko ku mayar da irinta. Lalle Allah Ya kasance Mai hisabi ne a kan kowane abu.

  87. ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۗ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ حَدِيثٗا

    Open ayah 4:87

    Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Lalle zai tattara ku a ranar alƙiyama, wadda babu kokwanto a cikinsa. Kuma wane ne ya fi Allah gaskiyar zance? A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, wanda duk ya taimaki wani a kan wani kyakkyawan al’amari, to yana da lada a kansa. Hakanan wanda ya yi ƙoƙari wajen taimakon wani a kan abin da bai dace ba, to shi ma yana da nasa kamashon na zunubi. Allah mai iko ne, mai kiyayewa, kuma mai sakayya ne a kan komai; shi zai yi wa kowa hisabi bisa ga aikinsa kyakkyawa ko mummuna. An karɓo daga Abu Musa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan wani mai roƙo ya zo, ko aka nemi wata buƙata a wurinsa, sai ya ce: “Ku nema wa wasu alfarma, za a ba ku lada, kuma Allah yana zartar da abin da ya ga dama a bisa harshen Annabinsa.” [Bukhari #1432]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ladabi na gaisuwa, inda ya ce, idan aka gaishe ku da wata gaisuwa, to ku mayar da wadda ta fi ta, ko kuma ku amsa da irinta. Lalle Allah yana tattara ayyukan bayinsa, kuma shi mai yi musu hisabi ne a kansu. An karɓo daga Imrana ɗan Husain (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya zo ga Annabi (ﷺ) ya ce: “Assalamu alaikum.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya amsa masa, sannan ya zauna. Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Yana da lada goma.” Sannan wani ya zo ya ce: “Assalamu alaikum wa rahamatullahi.” Shi ma Annabi ya amsa masa, sannan ya zauna. Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Yana da lada ashirin.” Sannan wani ma ya zo ya ce: “Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.” Shi ma Manzon Allah (ﷺ) ya amsa masa, sannan ya zauna. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yana da lada talatin.” [Abu Dawud #5195, da Tirmizi #2689]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, shi ne kaɗai abin bauta, babu wani abin da ya cancanta a bauta masa da gaskiya sai shi kaɗai, kuma zai tattara ɗaukacin halittu gaba ɗaya ranar alƙiyama domin yi musu hisabi. Wannan rana babu makawa sai ta zo, domin Allah shi ne ya faɗa, kuma babu wanda ya kai Allah faɗar magana ta gaskiya.

  88. ۞فَمَا لَكُمۡ فِي ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِئَتَيۡنِ وَٱللَّهُ أَرۡكَسَهُم بِمَا كَسَبُوٓاْۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَهۡدُواْ مَنۡ أَضَلَّ ٱللَّهُۖ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلٗا

    Open ayah 4:88

    Shin me ya sa kuka kasu gida biyu dangane da lamarin munafuƙai, alhali Allah ne Ya mayar da su baya saboda abin da suka aikata? Shin kuna nufin ku shiryar da wanda Allah Ya riga Ya ɓatar da shi ne? Duk wanda Allah Ya ɓatar da shi kuwa, to ba za ka iya samar masa wata mafita ba.

  89. وَدُّواْ لَوۡ تَكۡفُرُونَ كَمَا كَفَرُواْ فَتَكُونُونَ سَوَآءٗۖ فَلَا تَتَّخِذُواْ مِنۡهُمۡ أَوۡلِيَآءَ حَتَّىٰ يُهَاجِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَخُذُوهُمۡ وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡۖ وَلَا تَتَّخِذُواْ مِنۡهُمۡ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرًا

    Open ayah 4:89

    Sun yi fatan ina ma za ku kafirta kamar yadda suka kafirta, sai ku zama ɗaya. Don haka kar ku riƙi masoya a cikinsu har sai sun yi hijira don Allah. Idan kuwa suka juya baya, to ku kama su, kuma ku kashe su a duk inda kuka same su; kuma kada ku riƙi wani masoyi ko mai taimako daga cikinsu.

  90. إِلَّا ٱلَّذِينَ يَصِلُونَ إِلَىٰ قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٌ أَوۡ جَآءُوكُمۡ حَصِرَتۡ صُدُورُهُمۡ أَن يُقَٰتِلُوكُمۡ أَوۡ يُقَٰتِلُواْ قَوۡمَهُمۡۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَسَلَّطَهُمۡ عَلَيۡكُمۡ فَلَقَٰتَلُوكُمۡۚ فَإِنِ ٱعۡتَزَلُوكُمۡ فَلَمۡ يُقَٰتِلُوكُمۡ وَأَلۡقَوۡاْ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَمَ فَمَا جَعَلَ ٱللَّهُ لَكُمۡ عَلَيۡهِمۡ سَبِيلٗا 

    Open ayah 4:90

    Sai dai (ban da) waɗanda suke fakewa a wajen waɗansu mutane da kuke da yarjejeniya ta zaman lafiya a tsakaninku (da su), ko kuma waɗanda suka zo muku zukatansu sun ƙuntata game da yaƙar ku ko yaƙar mutanensu. Da kuwa Allah Ya ga dama da Ya ɗora su a kanku, kuma tabbas da sun yaƙe ku. Don haka idan suka bar ku ba su yaƙe ku ba, kuma suka miƙa muku saƙo na sulhu, to Allah bai ba ku wata dama ta ku yaƙe su ba.

  91. سَتَجِدُونَ ءَاخَرِينَ يُرِيدُونَ أَن يَأۡمَنُوكُمۡ وَيَأۡمَنُواْ قَوۡمَهُمۡ كُلَّ مَا رُدُّوٓاْ إِلَى ٱلۡفِتۡنَةِ أُرۡكِسُواْ فِيهَاۚ فَإِن لَّمۡ يَعۡتَزِلُوكُمۡ وَيُلۡقُوٓاْ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَمَ وَيَكُفُّوٓاْ أَيۡدِيَهُمۡ فَخُذُوهُمۡ وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ ثَقِفۡتُمُوهُمۡۚ وَأُوْلَٰٓئِكُمۡ جَعَلۡنَا لَكُمۡ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 4:91

    Za ku sami wasu mutanen suna ƙoƙarin su sami amincewarku, kuma su sami amincewar mutanensu, amma duk sa’adda aka kira su zuwa kafirci sai su auka cikinsa. To idan ba su rabu da ku ba, kuma ba su neme ku da zaman lafiya ba, kuma ba su kame hannayensu ba, to ku kama su, kuma ku kashe su a duk inda kuka same su. Waɗannan kuwa Mun sanya muku bayyananniyar hujja a kansu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana magana da muminai a kan yadda suka rabu gida biyu dangane da sha’anin munafuƙai; wasu daga cikinsu suna kafirta su, wasu kuma ba sa kafirta su, alhalin Allah ya riga ya mayar da waɗannan munafuƙai sun dulmiya cikin kafirci saboda laifin da suka aikata, don haka bai dace a riƙa shakka game da kafircinsu ba. Ko kuma su masu shakkar kafircinsu suna nufin za su iya shiryar da wanda Allah bai nufe shi da shiriya ba? To duk wanda Allah ya riga ya ɓatar da shi, ba za ka iya samar masa wata hanyar shiriya ba. An karɓo daga Zaidu ɗan Sabit (Allah ya kara masa yarda), ya ce game da faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka): “Shin me ya same ku kuka kasu gida biyu dangane da lamarin munafuƙai?” Ya ce: “Wasu mutane da suka gudu daga yaƙin Uhudu, sai sahabbai suka kasu gida biyu dangane da lamarinsu, wasu suka ce kawai Annabi (ﷺ) ya kashe su, wasu kuma suka ce, a’a, kada ya kashe su. Sai wannan ayar ta sauka.” [Bukhari #4050]. Annabi (ﷺ) dai bai kashe su ba don gudun kada a yaɗa ji ta-ji tar cewa Annabi (ﷺ) yana kashe sahabbansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su fa waɗannan munafuƙai, so suke yi muminai su kafirta kamar yadda su ma suka kafirta, duk su zama ɗaya. Sannan kuma Allah ya hana muminai su riƙi munafuƙai masoya, har sai sun tuba sun yi hijira saboda Allah, sun bar garuruwan kafirci inda ba a barin su su yi bautar Allah, sun dawo cikin muminai; wannan shi ne zai tabbatar da cewa sun tuba sun yi imani na gaskiya. Idan kuwa har suka bijire, suka ƙi yin imani, suka ƙi yin hijira, to muminai su yaƙe su, su kama su a matsayin fursunonin yaƙi, su kashe su duk inda suka same su, kada kuma su ƙulla wata soyayya da ɗaya daga cikinsu, kada kuma su riƙi wani a cikinsu a matsayin mai taimakon su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya keɓance wasu ɓangarori biyu daga cikin munafuƙai, ya hana a yaƙe su. Su ne: • Waɗanda suka koma cikin kafirai waɗanda Musulmi suka yi sulhun dakatar da yaƙi a tsakaninsu da su, to sai a ƙyale su, kada a yaƙe su. • Waɗanda suka kawo kansu ga muminai, suka nuna ba za su yaƙe su ba, kuma ba za su yi yaƙi tare da su ba, to su ma sai a bar su kada a yaƙe su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da cewa, da ya ga dama da sai ya ɗora waɗannan munafuƙai a kan muminai, su yaƙe su, sai dai Allah cikin luɗufinsa da rahmarsa, ya dankwafar da su, ya hana musu yaƙar muminai. Idan munafuƙai suka ƙyale muminai suka yi sulhu da su na zaman lafiya, to bai halatta ga muminai su kashe su ba, ko su ci ganimar dukiyoyinsu, ko su kama matansu da ‘ya’yansu a matsayin bayi. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya ci gaba da bayyana wa muminai cewa, za su ci karo da wasu munafuƙai na daban, waɗanda suke son su zauna lafiya da Musulmi, don haka sai su riƙa nuna su ma Musulmi ne, amma kuma ta ɓangare guda suna son su zauna da ‘yan’uwansu kafirai lafiya, to sai su riƙa bauta wa abin da mutanensu kafirai suke bauta wa, duk sa’adda aka gayyace su zuwa ga wani aiki na kafirci ko shirka, nan da nan sai su amsa kira, don haka suka daɗa nutsuwa sosai cikin kafirci da shirka. To wannan nau’i na munafunci in har ba su bar yaƙar muminai ba, suka zaɓi zaman lafiya da su, to muminai su yaƙe su, su kama su fursunoni, su kashe su duk inda suka same su. Allah ya bai wa muminai hujja ƙarara ta yaƙar su.

  92. وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٍ أَن يَقۡتُلَ مُؤۡمِنًا إِلَّا خَطَـٔٗاۚ وَمَن قَتَلَ مُؤۡمِنًا خَطَـٔٗا فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖ وَدِيَةٞ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦٓ إِلَّآ أَن يَصَّدَّقُواْۚ فَإِن كَانَ مِن قَوۡمٍ عَدُوّٖ لَّكُمۡ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖۖ وَإِن كَانَ مِن قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٞ فَدِيَةٞ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ وَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖۖ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ شَهۡرَيۡنِ مُتَتَابِعَيۡنِ تَوۡبَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:92

    Kuma bai dace ga mumini ya kashe wani mumini ba, sai bisa kuskure. Wanda ya kashe mumini bisa ga kuskure, to zai ‘yanta bawa ko baiwa mumina da kuma diyya wadda za a miƙa wa iyalinsa, sai fa idan sun yafe. Amma idan wanda aka kashe yana cikin mutanen da suke maƙiyanku, alhalin kuma shi mumini ne, to za ku ‘yanta bawa ko baiwa mumina; idan kuwa ya kasance yana cikin mutanen da kuke da yarjejeniyar zaman lafiya da su, to za a bayar da diyya wadda za a miƙa wa iyalinsa, sannan za ku ‘yanta bawa ko baiwa mumina; wanda kuwa bai sami ikon haka ba, to sai ya yi azumin wata biyu a jere don tuba zuwa ga Allah. Allah kuwa Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima.

  93. وَمَن يَقۡتُلۡ مُؤۡمِنٗا مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآؤُهُۥ جَهَنَّمُ خَٰلِدٗا فِيهَا وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ وَلَعَنَهُۥ وَأَعَدَّ لَهُۥ عَذَابًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:93

    Duk kuwa wanda ya kashe mumini da gangan, to sakamakonsa wutar Jahannama ce, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi da shi, kuma Ya la’ance shi, kuma Ya yi masa tanadin azaba mai girma.

  94. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَتَبَيَّنُواْ وَلَا تَقُولُواْ لِمَنۡ أَلۡقَىٰٓ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَٰمَ لَسۡتَ مُؤۡمِنٗا تَبۡتَغُونَ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ مَغَانِمُ كَثِيرَةٞۚ كَذَٰلِكَ كُنتُم مِّن قَبۡلُ فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَتَبَيَّنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا

    Open ayah 4:94

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka fita yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah, to ku riƙa bincike, kuma kada ku ce ma wanda ya yi muku sallama: “Kai ba mumini ba ne,” don kawai kuna neman wani jin daɗi na rayuwar duniya, to a wurin Allah ne ganimomi masu yawa suke. Kamar haka ku ma a da kuka kasance, sai Allah Ya yi muku baiwa, don haka ku riƙa bincike. Lalle Allah Ya kasance Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukunce-hukuncen shari’a dangane da kisa na kuskure da kuma kisa na gangaci. Kisan kuskure shi ne kamar mutum ya nufi harbin wani abin farauta, sai ya harbe mutum ya mutu. Shi ya sa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, bai halatta mumini ya kashe ɗan’uwansa mumini ba, sai ta hanyar kuskure ba da niyya ba. To idan haka ta faru, sai wanda ya yi kisan ya yi kaffara ta hanyar ‘yanta bawa mumini ko baiwa mumina, kuma dole ya biya diyya cikakkiya, wadda shi da danginsa za su ɗauki nauyin biya, a bayar da ita ga magadan wanda aka kashe, sai dai idan sun yafe masa ita, to shi ke nan ba ta zama wajibi a kansa ba. To idan wanda aka kashe mumini ne, amma mutanensa kafiran yaƙi ne, to wanda ya yi kisan zai ‘yanta bawa ne mumini ko baiwa mumina kawai. Idan kuwa muminin da aka kashe ya fito ne daga mutanen da suke kafiran amana ne ko an yi sulhu da su, babu yaƙi tsakaninsu da muminai, to dole ne wanda ya yi kisa ya biya diyya ga magadan wanda ya kashe, kuma ya ‘yanta bawa mumini ko baiwa mumina. Wanda bai sami bawa ko baiwar da zai ‘yanta ba, ko ba shi da kuɗin sayen ta, to wajibi ne ya yi azumin wata biyu a jere. Allah ya shar’anta wa bayinsa waɗannan hukunce-hukunce don su zama tuba gare su da rahama, kuma Allah mai cikakken sani ne, kuma gwani mai hikima. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawarin narko mai tsanani ga wanda ya yi kisan kai na gangaci. Allah ya yi alƙawarin shigar da shi Jahannama, ya dawwama a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, sannan ya la’ance shi, baya ga haka kuma ya yi masa tanadin azaba mai girman gaske. Sai Allah ya umarci muminai da lalle su yi taka-tsantsan wajen kashe rai, ko da kuwa sun fita wajen yaƙi ne. Duk sanda suke shakka game da kafircin wani, to kada su kuskura su kashe shi, har sai sun sami tabbacin shi kafiri ne. Kada wani ya bayyana musu Musuluncinsa, ya miƙa wuya gare su, ba tare da ya yaƙe su ba, sannan su ce ai shi ba Musulmi ne ba. Su yi aiki da abin da ya bayyana na halinsa, kada su kashe shi don neman abin duniya, wato su karɓe dukiyar da ke tare da shi. Allah ya tunatar da su cewa, su ma fa a da haka suke, suna ɓoye imaninsu daga mutanensu mushirikai, sai Allah ya yi musu baiwa, ya ƙarfafa addininsu, har suka wayi gari suna iya bayyana Imaninsu da suke ɓoyewa. Don haka wajibi ne a kansu su yi bincike kafin su kashe wanda suke shakka a kan lamarinsa, Allah kuwa yana sane da duk abin da suke aikatawa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Musulmi sun fito yaƙi, sai suka ci karo da wani mutum yana kiwon dabbobinsa. Da ya gan su sai ya ce musu: “Assalamu alaikum.” Duk da haka sai suka kashe shi, suka kwashe dabbobinsa.” Sai Allah ya saukar da wannan ayar.” [Bukhari #4591, da Muslim #3025]. Usamatu ɗan Zaidu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya tura mu zuwa ga wata ƙabila mai suna Alhuraƙa , wani sashe na ƙabilar Juhainah , sai muka yi wa waɗannan mutanen dirar mikiya da sassafe, muka fatattake su.” Usamatu ya ce: “Sai ni da wani mutumin Madina muka bi wani mutum daga cikinsu, yana ganin mun cim masa, sai ya ce: “La ilaha illal lahu.” Usamatu ya ce: “Sai wannan mutumin Madina ya rabu da shi, amma ni sai na soke shi da mashina, na kashe shi. To lokacin da muka dawo, labari ya je wa Annabi (ﷺ), sai ya ce: “Yanzu Usamatu kashe shi ka yi bayan ya ce: “La ilaha illal lahu.”? Sai Usamatu ya ce: “Ya faɗe ta ne don kawai ya kare kansa.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya sake cewa: “Yanzu Usamatu kashe shi ka yi bayan ya ce: “La ilaha illal lahu.”? Usamatu ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) bai gushe ba yana maimaita mini wannan kalma, har sai da na yi burin ina ma ban musulunta ba kafin wannan rana.” [Bukhari #6872, da Muslim #96].

  95. لَّا يَسۡتَوِي ٱلۡقَٰعِدُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ غَيۡرُ أُوْلِي ٱلضَّرَرِ وَٱلۡمُجَٰهِدُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۚ فَضَّلَ ٱللَّهُ ٱلۡمُجَٰهِدِينَ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ عَلَى ٱلۡقَٰعِدِينَ دَرَجَةٗۚ وَكُلّٗا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَفَضَّلَ ٱللَّهُ ٱلۡمُجَٰهِدِينَ عَلَى ٱلۡقَٰعِدِينَ أَجۡرًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:95

    Waɗanda suka zauna a gida daga cikin muminai ba su fita yaƙi ba, in dai ba masu larura ba, ba za su yi daidai da masu jihadi don ɗaukaka kalmar Allah da dukiyoyinsu da kawunansu ba. Allah Ya fifita darajar masu jihadi da dukiyoyinsu da kawunansu a kan waɗanda suka zauna a gida. Kuma dukkansu Allah Ya yi masu alƙawarin Aljanna. Kuma Allah Ya fifita masu jihadi a kan waɗanda suka zauna a gida, da lada mai girma.

  96. دَرَجَٰتٖ مِّنۡهُ وَمَغۡفِرَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمًا

    Open ayah 4:96

    Wasu darajoji masu yawa daga gare Shi da gafara da kuma jin ƙai. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana falalar masu fita jihadi don ɗaukaka kalmarsa, watau yadda ya fifita darajarsu da matsayinsu a wurinsa. Allah ya nuna cewa, wanda zai fita jihadi don Allah da dukiyarsa da ransa, ba za a daidaita shi da wanda ya yi zamansa gida bai fita ba, kuma ba don yana tare da wata larura ba, kamar makanta ko gurgunta ko rashin lafiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fifita masu jihadi a kan waɗanda ba sa jihadi da wani lada mai girma. Amma su duka masu jihadin da waɗanda ba sa jihadi, Allah ya yi musu alƙawarin gidan Aljanna, sai dai kuma a Aljannar Allah ya fifita masu jihadi da wasu darajoji maɗaukaka da zai ɗaukaka su da su a Aljanna tare da gafarar zunubansu da samun rahamar Ubangijinsu. Allah kuwa mai yawan gafara ne, mai jin ƙai. An karɓo daga Zaidu ɗan Sabitu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya yi masa shiftar wannan ayar kamar haka: “Waɗanda suke zaune a gida ba su fita yaƙi ba daga cikin muminai, ba za su yi daidai da masu jihadi don ɗaukaka kalmar Allah ba.” Yana cikin karanto mini wannan ayar sai Abdullahi ɗan Ummu Maktum ya zo, sai ya ce: “Ya Manzon Allah, da zan iya yin jihadi da na yi.” Shi kuwa makaho ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Manzonsa faɗarsa: “Ban da masu larura.” A lokacin cinyarsa tana kan cinyata, sai ta yi mini nauyin gaske, har sai da na ji tsoron kada cinyata ta dagargaje. Sannan sai aka yaye masa.” [Bukhari #2832]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa, kuma ya tsayar da salla, ya yi azumin watan Ramadana, to haƙƙi ne a kan Allah ya shigar da shi Aljanna, daidai ne ya yi hijira domin Allah, ko ya yi zamansa a ƙasar haihuwarsa.” Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah (ﷺ), yanzu ba ma faɗa wa mutane haka ba?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “A cikin Aljanna akwai matakai na daraja ɗari, waɗanda Allah ya tanade su ne ga masu jihadi, tsakanin kowane mataki da na biye da shi, kamar tsakanin sama ne da ƙasa, don haka idan za ku roƙi Allah, to ku roƙe shi Aljannar Firdausi, domin ita ce mafi ɗaukaka, samanta Al-Arshin Allah mai rahama ne, daga nan ƙoramun gidan Aljanna suke ɓuɓɓugowa.” [Bukhari #7423, da Muslim #1884].

  97. إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡ قَالُواْ فِيمَ كُنتُمۡۖ قَالُواْ كُنَّا مُسۡتَضۡعَفِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ قَالُوٓاْ أَلَمۡ تَكُنۡ أَرۡضُ ٱللَّهِ وَٰسِعَةٗ فَتُهَاجِرُواْ فِيهَاۚ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرًا

    Open ayah 4:97

    Lalle waɗanda mala’iku suke karɓar rayukansu suna masu zaluntar kawunansu, (mala’ikun) za su ce (da su): “Cikin wane hali kuka kasance?” Sai su ce: “Mu mun kasance masu rauni a bayan ƙasa.” Sai su ce: “Ashe ƙasar Allah ba mai yalwa ba ce, ta yadda za ku sami damar yin hijira a cikinta?” To waɗannan, makomarsu ita ce wutar Jahannama, kuma wannan makoma ta munana.

  98. إِلَّا ٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلرِّجَالِ وَٱلنِّسَآءِ وَٱلۡوِلۡدَٰنِ لَا يَسۡتَطِيعُونَ حِيلَةٗ وَلَا يَهۡتَدُونَ سَبِيلٗا

    Open ayah 4:98

    Sai dai waɗanda suke raunana cikin maza da mata da yara ƙanana waɗanda ba su da wata dabara, kuma ba za su gane wata hanya (ta hijira) ba.

  99. فَأُوْلَٰٓئِكَ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَعۡفُوَ عَنۡهُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَفُوًّا غَفُورٗا

    Open ayah 4:99

    To waɗannan mai yiwuwa ne Allah Ya yi musu afuwa, Allah kuma Ya kasance Mai afuwa ne, Mai yawan gafara.

  100. ۞وَمَن يُهَاجِرۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يَجِدۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُرَٰغَمٗا كَثِيرٗا وَسَعَةٗۚ وَمَن يَخۡرُجۡ مِنۢ بَيۡتِهِۦ مُهَاجِرًا إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ يُدۡرِكۡهُ ٱلۡمَوۡتُ فَقَدۡ وَقَعَ أَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا 

    Open ayah 4:100

    Kuma duk wanda ya yi hijira saboda Allah, zai samu wuraren hijira masu yawa da yalwa a bayan ƙasa. Kuma duk wanda ya fita daga gidansa, yana mai hijira zuwa ga Allah da Manzonsa, sannan mutuwa ta riske shi, to haƙiƙa ladansa ya tabbata a wajen Allah. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana hukuncin waɗanda suka ƙi yin hijira su koma ƙasar Musulunci, suka ci gaba da zama a ƙasar kafirci, tare da cewa suna iya fita su yi hijirar, a inda suke kuma kafirai ba za su ƙyale su su tsayar da ibadun Musulunci yadda suke so ba. To shi ne Allah yake zargin masu wannan hali, yana bayyana musu haɗarin da suke ciki, musamman lokacin da mala’iku za su zo karɓar rayukansu, su ce musu: “Me ya sa kuka ci gaba da zama a cikin irin wannan hali?” Sai suka amsa musu da cewa: “Mu masu rauni ne, mun kasa fita mu yi hijira mu bi ‘yan’uwanmu Musulmi.” Sai mala’iku su mayar musu da cewa: “Ashe ƙasar Allah ba mai yalwa ce ba? Me ya sa ba ku tafi zuwa wani wuri ba inda za ku iya bautar Allah a can?” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan mutane da za su mutu a cikin irin wannan hali, to makomarsu Jahannama ce, kuma wannan makoma tasu ta yi muni. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wasu Musulmi sun ci gaba da zama cikin mushirikai, idan sun fita yaƙi suna fita da su, su ƙara musu yawan jama’a. To wani lokaci idan aka harbo kibiya sai ta sami wani daga cikinsu ta kashe, ko a sari wani a kashe shi. Sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Lalle waɗanda mala’iku suke karɓar rayukansu suna masu zaluntar kawunansu....” [Bukhari #7085]. Amma kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi togaciya ta waɗanda suke raunana ne maza da mata da yara, waɗanda kafirai suka hana su fita su yi hijira, su kuma ba su da wata dabara da za su iya yi su yi hijira, ba su da wata hanya da za su kuɓutar da kansu daga hannun mushirikai. To waɗannan Allah ya yafe musu, ba zai kama su da laifin ƙin yin hijira ba. Kuma Allah mai yawan gafara ne, mai yawan jin ƙai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) yana cewa game da faɗar Allah: “Sai dai waɗanda suke raunana...” Ya ce: “Ni da mahaifiyata muna daga cikin waɗanda Allah ya yi musu uzuri.” [Bukhari #4597]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance idan ya ɗago daga ruku’u a raka’arsa ta ƙarshe a sallar Isha’i, bayan ya ce: “Sami’ Allahu liman hamidah.” Sai ya ce: “Ya Allah ka kuɓutar da Ayyashu ɗan Rabi’atu, ya Allah ka kuɓutar da Alwalidu ɗan Alwalidu, ya Allah ka kuɓutar da Salamatu ɗan Hisham, ya Allah ka kuɓutar da muminai masu rauni, ya Allah ka tsananta uƙubarka a kan mutanen Makka, ya Allah ka jarrabe su da fari irin farin da ka jarrabi mutanen Annabi Yusufu da shi.” [Bukhari #6393, da Muslim #675]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɗaitar a kan yin hijira, inda ya bayyana cewa wanda duk ya yi hijira domin Allah, to zai sami wuraren hijira masu yawa da yalwa a bayan ƙasa, inda zai iya bautar Allah cikin tsanaki, ba tare da tsangwama ba, kuma ya sami abin da zai ci, ya sha, da sauran buƙatunsa na rayuwa. Amma wanda ya fita daga gidansa, ya bar ƙasarsa domin gudun hijira don Allah da Manzonsa (ﷺ), to amma kuma sai mutuwa ta riske shi kafin ya isa inda ya nufa, wato ƙasar Musulunci, to wannan ladansa ya tabbata a wurin Allah, kuma Allah mai gafara ne, mai jin ƙai. Wannan ayar ta sauka bayan wani sahabi mai suna Dhamratu ɗan Jundubu ya fito daga gidansa, ya ce wa iyalansa: “Ku ɗauke ni ku fitar da ni daga ƙasar mushirikai, ku kai ni ga Manzon Allah (ﷺ).” Sai suka ɗauke shi, suka fita da shi. Sai ya mutu a hanya kafin ya ƙarasa wurin Manzon Allah (ﷺ), sai wannan ayar ta sauka. [Dubi At-Tabari, Tafsir 7:392, da Ibn Kasir, Tafsir 2:391].

  101. وَإِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَقۡصُرُواْ مِنَ ٱلصَّلَوٰةِ إِنۡ خِفۡتُمۡ أَن يَفۡتِنَكُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْۚ إِنَّ ٱلۡكَٰفِرِينَ كَانُواْ لَكُمۡ عَدُوّٗا مُّبِينٗا 

    Open ayah 4:101

    Kuma idan kun yi tafiya a bayan ƙasa, to babu laifi a kanku ku yi sallar ƙasaru, in kun ji tsoron kafirai su fitine ku. Lalle kafirai sun kasance maƙiya ne, masu bayyana ƙiyayya a gare ku.

  102. وَإِذَا كُنتَ فِيهِمۡ فَأَقَمۡتَ لَهُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَلۡتَقُمۡ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُم مَّعَكَ وَلۡيَأۡخُذُوٓاْ أَسۡلِحَتَهُمۡۖ فَإِذَا سَجَدُواْ فَلۡيَكُونُواْ مِن وَرَآئِكُمۡ وَلۡتَأۡتِ طَآئِفَةٌ أُخۡرَىٰ لَمۡ يُصَلُّواْ فَلۡيُصَلُّواْ مَعَكَ وَلۡيَأۡخُذُواْ حِذۡرَهُمۡ وَأَسۡلِحَتَهُمۡۗ وَدَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ تَغۡفُلُونَ عَنۡ أَسۡلِحَتِكُمۡ وَأَمۡتِعَتِكُمۡ فَيَمِيلُونَ عَلَيۡكُم مَّيۡلَةٗ وَٰحِدَةٗۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِن كَانَ بِكُمۡ أَذٗى مِّن مَّطَرٍ أَوۡ كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَن تَضَعُوٓاْ أَسۡلِحَتَكُمۡۖ وَخُذُواْ حِذۡرَكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ أَعَدَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا 

    Open ayah 4:102

    Kuma idan ka kasance a cikinsu, sai ka yi musu limancin salla, to sai wata ƙungiya su tsaya tare da kai, kuma su riƙe makamansu, to yayin da suka yi sujada (wato salla), sai su koma bayanku, sai ɗaya ƙungiyar wadda ba su yi salla ba, su zo su yi salla tare da kai, kuma su ma su yi taka-tsantsan, su kuma riƙe makamansu. Kafirai kuwa suna burin ina ma za ku gafala ku ajiye makamanku da kayayyakin guzurinku, sai su far muku gaba ɗaya. Kuma idan akwai wata cuta tare da ku saboda ruwan sama ko kun kasance marasa lafiya, to babu laifi a gare ku ku ajiye makamanku, amma fa ku yi taka-tsantsan. Lalle Allah Ya yi wa kafirai tanadin wata azaba mai wulaƙantarwa.

  103. فَإِذَا قَضَيۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ قِيَٰمٗا وَقُعُودٗا وَعَلَىٰ جُنُوبِكُمۡۚ فَإِذَا ٱطۡمَأۡنَنتُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ كِتَٰبٗا مَّوۡقُوتٗا 

    Open ayah 4:103

    To idan kun kammala salla, to sai ku ambaci Allah a tsaye ko a zaune ko kuma a kwance. To idan kuka samu nutsuwa sai ku tsayar da salla (a yadda take). Lalle salla ta kasance wata farilla ce mai ƙayyadajjen lokaci a kan muminai.

  104. وَلَا تَهِنُواْ فِي ٱبۡتِغَآءِ ٱلۡقَوۡمِۖ إِن تَكُونُواْ تَأۡلَمُونَ فَإِنَّهُمۡ يَأۡلَمُونَ كَمَا تَأۡلَمُونَۖ وَتَرۡجُونَ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا يَرۡجُونَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا 

    Open ayah 4:104

    Kuma kada ku yi rauni wajen neman mutanen; in kun kasance kuna jin raɗaɗi, to ai su ma (kafirai) suna jin raɗaɗi kamar yadda kuke jin raɗaɗi; kuma kuna fatan wani lada a wurin Allah, wanda su ba sa fatan irinsa. Allah kuwa Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai yawan hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fara bayanin halaccin sallar ƙasaru ga matafiya. Sallar ƙasaru ita ce rage salloli masu raka’a huɗu su koma biyu. Allah ya bayyana cewa yin haka babu wani laifi ga matafiyi. Ko da yake ayar ta ambaci halin tsoron fitinar kafirai, to amma wannan ba sharaɗi ba ne, duk wanda yake cikin halin tafiya, an yi masa rangwamen yin sallar ƙasaru. An karɓo daga Ya’ala ɗan Umayya (Allah ya kara masa yarda) ya ce, na tambayi Umar ɗan Khattab (Allah ya kara masa yarda) game da faɗar Allah: “Babu laifi a kanku ku yi sallar ƙasaru in kun ji tsoron kafirai su fitine ku.” Ya ce: “To ga shi yanzu mutane sun aminta, babu wani tsoro.” Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce masa: “Ni ma na yi mamakin wannan abu kamar yadda ka yi mamaki, sai na tambayi Manzon Allah (ﷺ), sai ya ce: “Sadaka ce Allah ya ba ku, don haka ku karɓi sadakarsa.” [Muslim #686, da Abu Dawud #1199, da Ibn Maja #1065, da Ahmad #178]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin sallar tsoro, ya bayyana wa Annabinsa (ﷺ) yadda zai yi limancin salla da sahabbansa a lokacin da ake cikin halin yaƙi. Ya umarce su da su rabu kaso biyu, kashi na farko su shiga salla tare da Annabi (ﷺ), yayin da ɗaya kashin suna bayansu da makamansu, suna kare masu salla. Idan Annabi (ﷺ) ya yi raka’a ɗaya da su, sai ya tsaya a tsaye, su kuma sai su cika raka’a ɗayar, su yi sallama, su koma baya su canji masu kare su, su kuma waɗancan da ba su yi salla ba, sai su zo su shiga salla tare da Annabi (ﷺ), ya yi raka’arsa ɗaya da ta rage masa tare da su; idan ya yi sallama, sai su tashi su ciko raka’a ɗaya, su zauna su yi tahiya, su yi sallama. A duk cikin wannan yanayi kada su yi sakaci da riƙe makamansu. Sunnar Annabi (ﷺ) ta zo da bayanin wata hanyar daban ta sallar tsoro. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai sun yi burin ina ma muminai za su shagala da salla, su bar makamansu da kayayyakin guzurinsu, su kuma su auko musu gaba ɗaya su murƙushe su. To amma idan an sami wani uzuri da zai hana wasu ɗaukar makami domin sun yi musu nauyi, kamar wanda ruwa ya doke shi har ya sa masa rashin lafiya, ko kuma ba shi da lafiyar, to babu laifi ya ajiye makaminsa, amma duk da haka lalle su yi taka-tsantsan. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ya tanadar wa kafirai azaba ta wulaƙanci duniya da lahira. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Musulmi yayin da suka gama sallar tsoro, da cewa su ambaci Allah, a tsaye suke ko a zaune ko a kwance. Idan sun fita daga cikin halin tsoro, sun sami aminci, sai su yi cikakkiyar salla, domin kuwa salla wani farali ne mai lokaci ƙayyadadde a wurin Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Musulmi kashedi da kada su zama raunana ko masu kasala wajen neman maƙiyansu a fagen yaƙi. Kada rauni da zai sami wasu daga cikinsu ya sare musu gwiwa, domin idan har su muminai suna jin zafin kisa ko raunin da ya same su, to ai su ma kafiran suna jin zafin abin da yake samun su na kisa ko rauni. To amma su muminai sun fi su nesa ba kusa ba, domin suna sa ran samun wani lada da tagomashi daga Allah na cin nasara da taimakon addininsa, wanda su kafirai ba su da wannan tsammanin. Don haka su muminai ya kamata su zage dantse wajen taimakon addinin Allah, su bar kasala da mutuwar jiki. Lalle Allah mai cikakken ilimi ne game da duk halin da suke ciki, kuma mai hikima ne cikin duk abin da ya shar’anta musu ko ya ƙaddara musu.

  105. إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِتَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ بِمَآ أَرَىٰكَ ٱللَّهُۚ وَلَا تَكُن لِّلۡخَآئِنِينَ خَصِيمٗا 

    Open ayah 4:105

    Lalle Mu Mun saukar maka da Littafi da gaskiya domin ka yi hukunci a tsakanin mutane da abin da Allah Ya sanar da kai, kuma kada ka zamo mai ba da kariya ga maha’inta.

  106. وَٱسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا 

    Open ayah 4:106

    Kuma ka roƙi gafarar Allah, lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.

  107. وَلَا تُجَٰدِلۡ عَنِ ٱلَّذِينَ يَخۡتَانُونَ أَنفُسَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ خَوَّانًا أَثِيمٗا 

    Open ayah 4:107

    Kuma kada ka kare waɗanda suke ha’intar kawunansu. Lalle Allah ba Ya son duk wanda ya kasance mai yawan ha’inci ne, mai yawan saɓo.

  108. يَسۡتَخۡفُونَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَلَا يَسۡتَخۡفُونَ مِنَ ٱللَّهِ وَهُوَ مَعَهُمۡ إِذۡ يُبَيِّتُونَ مَا لَا يَرۡضَىٰ مِنَ ٱلۡقَوۡلِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطًا 

    Open ayah 4:108

    Suna ɓoye wa mutane (laifinsu), amma ba sa ɓoye wa Allah, alhali kuwa Yana tare da su yayin da suke kwana suna ƙulle-ƙullen maganar da bai yarda da ita ba. Kuma lalle Allah Ya kasance Mai kewayewa ne ga abin da suke aikatawa.

  109. هَٰٓأَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ جَٰدَلۡتُمۡ عَنۡهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَمَن يُجَٰدِلُ ٱللَّهَ عَنۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَم مَّن يَكُونُ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا 

    Open ayah 4:109

    Sai ga shi ku waɗannan kun ba su kariya a rayuwar duniya, to wane ne zai ba su kariya a gaban Allah a ranar alƙiyama, ko kuwa wane ne zai zama wakilinsu? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabinsa (ﷺ) cewa, shi ne ya saukar masa da littafi da gaskiya, wanda kuma ya ƙunshi gaskiya tsantsa, domin ya yi wa mutane hukunci da abin da Allah ya sanar da shi daga wannan littafi. Kuma kada ya kuskura ya zama mai kare marar gaskiya, mai ha’inci, sannan ya riƙa neman gafarar Allah, domin shi mai gafara ne, mai yawan rahama ga bayainsa. Har wa yau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Annabinsa (ﷺ) kashedi da kada ya zama mai bayar da kariya ga mutanen da suke ha’intar kawunansu, suke aikata laifuka, domin Allah ba ya son masu cin amana, masu laifi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin waɗannan masu laifi cewa, duk sanda za su yi mugun aikinsu, sai su riƙa ɓoye wa mutane don kar a gan su a hana su, amma sun manta ba za su iya ɓoye wa Allah ba, wanda koyaushe yana tare da su da ganinsa da iliminsa a duk inda suke, musamman lokacin da suke haɗuwa tsakar dare, su kwana suna tsara hanyoyin da za su saɓa wa Allah da ayyukan da Allah ba zai yarda da su ba. Sun manta da cewa ilimin Allah yana kewaye da su ta ko’ina. Sai kuma Allah ya yi wa bayinsa bayanin cewa, idan har sun ba wa waɗannan maciya amana kariya a nan duniya, kariyar kuma ta amfane su ba a yanke musu wani hukunci a kan laifinsu ba, to idan an je lahira a gaban Allah, wane ne suke da shi wanda zai zama wakilinsu, ya kare su daga laifukan da za a tuhume su a kansu?

  110. وَمَن يَعۡمَلۡ سُوٓءًا أَوۡ يَظۡلِمۡ نَفۡسَهُۥ ثُمَّ يَسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَ يَجِدِ ٱللَّهَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا 

    Open ayah 4:110

    Kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki ko ya zalunci kansa, sannan ya nemi gafarar Allah, to zai sami Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.

  111. وَمَن يَكۡسِبۡ إِثۡمٗا فَإِنَّمَا يَكۡسِبُهُۥ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:111

    Kuma duk wanda ya aikata wani laifi, to kansa ya yi wa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima.

  112. وَمَن يَكۡسِبۡ خَطِيٓـَٔةً أَوۡ إِثۡمٗا ثُمَّ يَرۡمِ بِهِۦ بَرِيٓـٔٗا فَقَدِ ٱحۡتَمَلَ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 4:112

    Kuma duk wanda ya aikata wani ƙaramin laifi, ko wani babban zunubi, sannan ya ɗora shi a kan wanda bai ji ba bai gani ba, to haƙiƙa ya ɗaukar wa kansa babban laifin ƙage da kuma wani zunubi mabayyani.

  113. وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ وَرَحۡمَتُهُۥ لَهَمَّت طَّآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ أَن يُضِلُّوكَ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡۖ وَمَا يَضُرُّونَكَ مِن شَيۡءٖۚ وَأَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمۡ تَكُن تَعۡلَمُۚ وَكَانَ فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ عَظِيمٗا

    Open ayah 4:113

    Ba don falalar Allah da rahamarsa a kanka ba kuwa, lalle da waɗansu jama’a daga cikinsu sun yi niyyar su ɓatar da kai, ba kuwa kowa za su iya ɓatarwa ba sai dai kawunansu; kuma ba za su cuce ka da komai ba. Kuma Allah Ya saukar maka da Littafi da hikima, kuma Ya sanar da kai abin da a da ba ka sani ba. Kuma falalar Allah mai girma ce gare ka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, duk wanda ya cuci wani ko ya zalunci kansa ta hanyar saɓon Allah, sannan daga baya ya tuba ya nemi gafarar Allah, to Allah zai yafe masa ya ji ƙan sa. Haka kuma duk wanda ya aikata wani laifi, to ya sani kansa ya yi wa, domin uƙubar a kansa za ta ƙare. Allah mai cikakken ilimi ne, ya san wanda ya yi masa laifi da dalilin yin laifin, kuma shi gwani ne mai hikima cikin duk ayyukansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, duk wanda ya aikata wani laifi babba ko ƙarami, sannan kuma ya ƙaga wa wani wanda bai ji ba, bai gani ba wannan laifin, to haƙiƙa ya shirga mummunar ƙarya, kuma ya ɗauki babban zunubi na wanda ya yi wa ƙagen. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabinsa (ﷺ) cewa, ba don falalar da ya yi masa, da rahamarsa ba, ya tsare shi daga aukawa cikin kowane irin laifi, to da waɗanda suke cin amanar kansu sun yi niyyar kautar da shi daga kan gaskiya, amma kuma ba kowa suke ɓatarwa ba sai kawunanasu. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya daɗa tuna wa Annabi (ﷺ) ni’imomin da ya yi masa na saukar masa da Alƙur’ani da sunna da koyar da shi sirrikan shari’a, da sauran abubuwan da a da bai sani ba; kuma falalar da Allah ya yi masa mai yawa ce, ba za ta lissafu ba.

  114. ۞لَّا خَيۡرَ فِي كَثِيرٖ مِّن نَّجۡوَىٰهُمۡ إِلَّا مَنۡ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوۡ مَعۡرُوفٍ أَوۡ إِصۡلَٰحِۭ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:114

    Babu wani alheri a cikin yawancin ganawarsu, sai fa wanda ya yi umarni da yin sadaka, ko wani aiki nagari ko kuma sulhuntawa tsakanin mutane. Wanda ya aikata haka don neman yardar Allah, to za Mu ba shi lada mai girma.

  115. وَمَن يُشَاقِقِ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ ٱلۡهُدَىٰ وَيَتَّبِعۡ غَيۡرَ سَبِيلِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ نُوَلِّهِۦ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصۡلِهِۦ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرًا

    Open ayah 4:115

    Kuma duk wanda yake saɓa wa wannan Manzo bayan shiriya ta bayyana a gare shi, yake kuma bin tafarkin da ba na muminai ba, to za Mu bar shi da abin da ya ɗaukar wa kansa, sannan Mu shigar da shi wutar Jahannama; makoma kuwa ta munana.

  116. إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا

    Open ayah 4:116

    Lalle Allah ba Ya gafartawa a yi masa shirka, Yana kuwa gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda Ya ga dama. Duk wanda ya yi wa Allah shirka, to haƙiƙa ya ɓata manisanciyar ɓata.

  117. إِن يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ إِنَٰثٗا وَإِن يَدۡعُونَ إِلَّا شَيۡطَٰنٗا مَّرِيدٗا

    Open ayah 4:117

    Ba waɗanda suke bauta wa, baya ga Allah, sai wasu gumaka masu sunan mata, kuma babu wanda suke bauta wa sai Shaiɗan mai taurin kai.

  118. لَّعَنَهُ ٱللَّهُۘ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنۡ عِبَادِكَ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا

    Open ayah 4:118

    Allah Ya la’ance shi. Sai kuma ya ce: “Tabbas sai na samu wani kaso ƙayyadajje daga bayinka.

  119. وَلَأُضِلَّنَّهُمۡ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمۡ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُبَتِّكُنَّ ءَاذَانَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلۡقَ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَّخِذِ ٱلشَّيۡطَٰنَ وَلِيّٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِ فَقَدۡ خَسِرَ خُسۡرَانٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 4:119

    “Kuma lalle sai na ɓatar da su, kuma lalle sai na sa musu dogon buri, kuma lalle zan umarce su, sai sun riƙa gutsuttsure kunnuwan dabbobin gida, kuma lalle zan umarce su, sai sun canja halittar Allah.” Duk wanda kuwa ya riƙi Shaiɗan a matsayin masoyi ba Allah ba, to haƙiƙa ya yi hasara bayyananniyar hasara.

  120. يَعِدُهُمۡ وَيُمَنِّيهِمۡۖ وَمَا يَعِدُهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ إِلَّا غُرُورًا 

    Open ayah 4:120

    Yana yi musu alƙawari kuma yana sa musu dogon buri; kuma babu abin da Shaiɗan yake yi musu alƙawari da shi sai ruɗi kawai.

  121. أُوْلَٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُ وَلَا يَجِدُونَ عَنۡهَا مَحِيصٗا

    Open ayah 4:121

    Waɗannan makomarsu wutar Jahannama ce, kuma ba za su sami wurin kauce mata ba.

  122. وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ سَنُدۡخِلُهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٗاۚ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ قِيلٗا

    Open ayah 4:122

    Kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka yi aiki nagari, za Mu shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada; kuma alƙawarin Allah tabbatacce ne. Kuma wane ne ya fi Allah gaskiyar zance? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fara bayyana cewa, duk wani lamari da mutane za su haɗu su keɓe suna tattaunawa a kansa, babu alheri a cikinsa sai in ya danganci umarni da yin sadaka ko kyakkyawan aiki ko sulhu tsakanin mutane. To duk wanda ya aikata waɗannan abubuwa don neman yardar Allah, to Allah zai ba shi gagarumin lada, wanda shi ne gidan Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kashedi ga duk wanda yake saɓa wa Manzon Allah (ﷺ), ko sunnarsa yana sane, ya yi watsi da gaskiya bayan ta bayyana gare shi, ya zaɓi ya bi wata hanya daban ba hanyar muminai ba, to wannan Allah zai bar shi da mummunan zaɓinsa, ya ɗora masa nauyin da ya ɗaukar wa kansa, makomarsa kuma wutar Jahannama ce, makoma kuwa ta munana. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ƙarara cewa, ba zai taɓa gafarta wa wanda ya mutu yana yi masa shirka bai tuba ba, amma kuma yana gafarta wa wanda ya aikata laifin da bai kai shirka ba idan ya ga dama. Duk ko wanda ya yi shirka, to haƙiƙa ya ɓata manesanciyar ɓata. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani nau’in shirka wanda kafirai suke bauta wa mata, ko dai wasu gumaka masu sunan mata, ko kuma mala’iku, da suka ce wai ‘ya’yan Allah ne mata. A gaskiyar lamari dai ba wasu suke bauta wa ba, sai Shaiɗan wanda ya kangare wa Ubangijinsa, wanda kuma Allah ya la’ance shi, ya nisantar da shi daga rahamarsa. Da ma shi Shaiɗan shi ne ya yi rantsuwa gaban Allah cewa lalle, sai ya ɗibi kasonsa daga bayin Allah, ya kautar da su daga kan tafarki madaidaici, ya sa musu yawan burace-burace, wanda hakan shi ne zai nisanta su daga tafarkin Tauhidi da ɗa’a ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma ya sa su su riƙa gutsuttsure kunnuwan dabbobinsu, don su nuna wannan alama ce ta `yanta dabbobin cewa an haramta amfani da su wajen hawa ko cin namansu, wai sun zama na gumakansu ne, babu mai taɓa su. Wannan da ma wata al’ada ce da Larabawa suka riƙa yi tun a jahiliyya kafin zuwan Musulunci. Shaiɗan kuma ya ci gaba da rantsuwar cewa sai ya umarci mutane sun riƙa canja halittar Allah ta asali watau fiɗra ta addinin gaskiya, ta hanyar aikata shirka da bidi’a da saɓon Allah sa sunan addini. Har ila yau canja halittar Allah ya ƙunshi canja wani yanayi na halitta da Allah ya yi musu, kamar ya ƙawata musu yin shasshawa a fuska, ko gyaran gira, ko yin wushirya ta ƙarya wai don ƙarin kyau. Wannan duk canza halittar Allah ne, wanda galibi mata ne suke yi, wanda kuma bin umarnin Shaiɗan ne, kamar yadda Abdullahi ɗan Mas’ud ya ruwaito. [Dubi, Bukhari #4886, da Muslim #2125]. Duk kuma wanda ya riƙi Shaiɗan masoyi, yana yi masa biyayya, to haƙiƙa ya halaka, duniya da lahira. Da ma shi Shaiɗan alƙawarin ƙarya yake yi wa mabiyansa, yana ruɗar su don ya halakar da su. Yakan yi musu alƙawarin zai taimaka musu, ko ya tsorata su da cewa, idan suna ciyar da dukiyarsu don Allah za su talauce, kuma ya dinga sa musu burin cewa in sun bi hanyarsa za su sami ɗaukaka ta duniya. To waɗanda suka riƙi Shaiɗan a matsayin masoyinsu, mai jiɓintar al’amuransu, makomarsu wutar Jahannama ce mai tsananin ƙuna, kuma ba za su taɓa samun mafaka ko wurin tsira ba daga gare ta. To amma waɗanda suka yi imani, suka yi ayyuka na ƙwarai, waɗannan ‘yan Aljanna ne, za su shige ta su dawwama a cikinta. Wannan shi ne alƙawarin Allah na gaskiya kuma babu wanda maganarsa ta fi zama gaskiya kamar Allah.

  123. لَّيۡسَ بِأَمَانِيِّكُمۡ وَلَآ أَمَانِيِّ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِۗ مَن يَعۡمَلۡ سُوٓءٗا يُجۡزَ بِهِۦ وَلَا يَجِدۡ لَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

    Open ayah 4:123

    (Al’amarin) ba wai ya dangaci burace-buracenku ba ne, ba kuma burace-buracen Ma’abota Littafi ba ne. Duk wanda ya aikata mummunan aiki, to za a saka masa da shi, kuma ba zai sami wani masoyi ko mai taimako ba Allah ba.

  124. وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ نَقِيرٗا

    Open ayah 4:124

    Kuma wanda ya yi wani aiki nagari, namiji ne ko mace, alhali yana mumini, to waɗannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a zalunce su gwargwadon ɗigon bayan ƙwallon dabino ba.

  125. وَمَنۡ أَحۡسَنُ دِينٗا مِّمَّنۡ أَسۡلَمَ وَجۡهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ وَٱتَّبَعَ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۗ وَٱتَّخَذَ ٱللَّهُ إِبۡرَٰهِيمَ خَلِيلٗا

    Open ayah 4:125

    Kuma wane ne mafi kyawun addini fiye da wanda ya miƙa fuskarsa ga Allah, yana kuma mai kaɗaita Allah, sannan ya bi addinin Ibrahimu yana mai karkacewa duk wata ɓarna? Allah kuwa Ya riƙi Ibrahimu a matsayin badaɗayi.

  126. وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٖ مُّحِيطٗا

    Open ayah 4:126

    Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa duk na Allah ne. Kuma Allah Ya kasance Yana kewaye da (sanin) komai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana shaida wa Musulmi da Yahudawa da Nasara cewa, samun tsira a ranar lahira ba yana samuwa ne ta hanyar burace-burace ba, ba tare da wani aiki ba. A cikinsu duk wanda ya yi wani mummunan aiki babba ko ƙarami, za a yi masa sakayya a kansa a duniya ko a lahira, kuma ba zai taɓa samun wani mai taimaka masa ya ba shi kariya in ba Allah ba. Wanda kuma ya yi kyakkyawan aiki, namiji ne shi ko mace, alhali yana mai imani da Allah da Manzonsa (ﷺ), to waɗannan su ne za su shiga Aljanna gidan ni’ima ba tare da an zalunce da su komai ba; za a ba su ladansu cikakke kamar yadda aka yi musu alƙawari. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, babu mutumin da addininsa ya fi kyau kamar wanda ya miƙa wuyansa ga Allah shi kaɗai, kuma ya bi shari’a sau-da-ƙafa, kuma ya bi addinin Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) mai kauce wa duk wata shirka kuma addini na Tauhidi. Allah kuma ya bayyana girman matsayin Annabi Ibrahim a wurinsa, yayin da ya riƙe shi badaɗayi, wanda yake muƙami ne na ƙoli da Allah yake ba wa masoyansa, muƙami na ƙololuwar soyayyar Allah ga bawansa, a dalilin yadda shi ma wannan bawan ya tsantsanta bautarsa da soyayyarsa ta ƙoli ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakken ikonsa a kan komai. Domin duk abin da yake cikin sammai da wanda yake ƙasa nasa ne, mulkinsa ne, bayinsa ne, shi ne yake yin yadda ya ga dama da su, kuma iliminsa ya game ko’ina.

  127. وَيَسۡتَفۡتُونَكَ فِي ٱلنِّسَآءِۖ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِيهِنَّ وَمَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ فِي يَتَٰمَى ٱلنِّسَآءِ ٱلَّٰتِي لَا تُؤۡتُونَهُنَّ مَا كُتِبَ لَهُنَّ وَتَرۡغَبُونَ أَن تَنكِحُوهُنَّ وَٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلۡوِلۡدَٰنِ وَأَن تَقُومُواْ لِلۡيَتَٰمَىٰ بِٱلۡقِسۡطِۚ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِهِۦ عَلِيمٗا

    Open ayah 4:127

    Kuma suna neman fatawarka game da lamarin mata. Ka ce: “Allah ne Yake ba ku fatawa game da lamarinsu da kuma abin da ake karanta muku a cikin Littafi dangane da marayu mata waɗanda ba kwa iya ba su sadakinsu cikakke, ga shi kuma kuna kwaɗayin ku aure su; hakanan da kuma (dukiyar) yara masu rauni. Kuma ku tsaya wajen kula da (dukiyar) marayu ta hanyar adalci. Kuma duk abin da kuka aikata na alheri, to lalle Allah Yana sane da shi.” Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, sahabbansa suna neman fatawarsa game da lamarin mata. Allah ya ce da shi ya faɗa musu cewa, shi ne zai ba su amsar fatawarsu game da hukunce-hukuncen mata, kuma zai ba su wannan fatawar ne da Alƙur’anin da ake karanta musu dangane da sha’anin mata marayu da suke ƙarƙashinsu, suna kula da su bayan mutuwar iyayensu; sai su riƙa zaluntar su ta ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi: • Su hana su gadonsu ko; • su hana su yin aure don su ci gaba da morar kuɗaɗensu ko; • su ƙwace musu sadakinsu da aka ba su lokacin aurensu. Wannan idan su ba sa sha’awar su aure su saboda su ba kyawawa ba ne. Amma idan sun gan su kyawawa ne masu dukiya, to sai su aure su, amma su hana su sadakinsu cikakke. To Allah ya haramta musu yin wannan. Haka kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba su fatawa dangane da yara ƙanana raunana da cewa, su ba su haƙƙoƙinsu na gado, kada su cinye musu gadonsu bisa ga zalunci. Sannan su yi cikakken adalci ga marayu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, yana sane da duk wanda ya aikata wani alheri, kuma zai ba shi cikakken sakamakonsa. An karɓo daga Urwatu ɗan Zubairu, ya tambayi A’isha (Allah ya kara mata yarda) game da faɗar Allah: “Kuma idan kuna jin tsoron cewa ba za ku iya yin adalci ba dangane da marayu, to ku auri matan da kuke so, ko dai biyu-biyu ko uku-uku ko huɗu-huɗu.” Sai ta ce: “Ya kai ɗan ‘yar’uwata, ana magana ne a kan marainiya da take wurin mai kula da ita (waliyyinta), tana tarayya da shi a dukiyarsa, sai ya yi sha’awar dukiyarta da kuma kyawunta, sai ya so ya aure ta amma ba tare da ya yi mata adalci wajen ba ta sadakinta ba, ya ba ta abin da idan wani ne zai aure ta ba shi zai ba ta ba. Sai aka hana musu auren su, sai fa idan za su yi musu adalci wajen biyan su sadakin da ya dace da a ba su a al’ada. Wannan ya sa aka umarce su da su auri wasu matan daban waɗanda suke so.” Urwatu ya ce: A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Sannan sahabbai suka nemi fatawa daga Manzon Allah game da su bayan wannan ayar, sai Allah ya saukar da faɗinsa: “Kuma suna tambayar ka dagane da lamarin mata…” Ta ce: “Ayar da Allah ya ambata cewa ana karanta musu ita a littafi ita ce waccan ayar ta farko.” [Bukhari #2494, da Muslim #3018].

  128. وَإِنِ ٱمۡرَأَةٌ خَافَتۡ مِنۢ بَعۡلِهَا نُشُوزًا أَوۡ إِعۡرَاضٗا فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَآ أَن يُصۡلِحَا بَيۡنَهُمَا صُلۡحٗاۚ وَٱلصُّلۡحُ خَيۡرٞۗ وَأُحۡضِرَتِ ٱلۡأَنفُسُ ٱلشُّحَّۚ وَإِن تُحۡسِنُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا

    Open ayah 4:128

    Kuma idan wata mace ta ji tsoron burtsewa daga mijinta, ko bijirewa, to babu laifi su yi sulhu a tsakaninsu. Kuma yin sulhu shi ya fi alheri. Kuma an kimsa wa rayuka tsananin rowa. Idan kuka kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to lalle Allah Ya kasance Masanin abin da kuke aikatawa ne.

  129. وَلَن تَسۡتَطِيعُوٓاْ أَن تَعۡدِلُواْ بَيۡنَ ٱلنِّسَآءِ وَلَوۡ حَرَصۡتُمۡۖ فَلَا تَمِيلُواْ كُلَّ ٱلۡمَيۡلِ فَتَذَرُوهَا كَٱلۡمُعَلَّقَةِۚ وَإِن تُصۡلِحُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

    Open ayah 4:129

    Kuma ba za ku iya yin adalci (na soyayya) a tsakankanin mata ba, ko da kuna matuƙar son yin hakan. To kada ku karkata, karkata ta gaba ɗaya, ta yadda za ku ƙyale ɗayar kamar ratayayya. Amma idan za ku kyautata kuma ku yi taƙawa, to lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.

  130. وَإِن يَتَفَرَّقَا يُغۡنِ ٱللَّهُ كُلّٗا مِّن سَعَتِهِۦۚ وَكَانَ ٱللَّهُ وَٰسِعًا حَكِيمٗا 

    Open ayah 4:130

    Idan kuwa suka rabu, to Allah zai wadatar da kowannensu daga yalwarsa. Kuma Allah Ya kasance Mayalwaci ne, Mai yawan hikima. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin wasu hukunce-hukuncen da suka shafi ma’aurata ne yayin da aka sami saɓani a tsakaninsu. Idan mace ta lura mijinta ya fara gajiya da ita, ko yana ja baya-baya da ita, saboda yawan shekarunta, to tana iya neman sa da sulhu, babu laifi ta sarayar da wani haƙƙinta, kamar na kwana ko ciyarwa ko tufatarwa, domin su ci gaba da zama da mijinta a matsayin ma’aurata, domin yin haka ya fi musu alheri fiye da su rabu gaba ɗaya. To sai dai kuma yin hakan wani abu ne mai wuyar gaske saboda yadda aka sanya wa zukata tsananin ƙanƙame abin da yake haƙƙi ne gare su. Sai dai yana da kyau mutum ya yi ƙoƙari ya danne zuciyarsa, ya haƙura da wani abu na haƙƙinsa domin a sami daidaito ta yin sulhu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɗaitar a kan kyautatawa ta kowane ɓangare; ta ɓangaren ibada da ta ɓangaren mu’amala da ta ɓangaren zamantakewar aure da kyautata wa mata ko da kuwa mazajensu sun fara gajiya da su, sai su yi haƙuri, su ba su haƙƙinsu cikakke, kuma su kiyaye dokokin Allah game da su. Idan sun yi haka, to su sani Allah yana da cikakken sanin duk abin da suke aikatawa, kuma zai musu sakayya a kai. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Wannan ayar tana magana ne game da mutumin da yake tare da matarsa, amma ba ya son ci gaba da zama da ita, ya fara tunanin ya sake ta, sai ita kuma matar ta ce masa: “Ka ƙyale ni na ɗauke maka duk wata ɗawainiyata.” Sai Allah ya saukar da wannan ayar.” [Bukhari #2450, da Muslim #3021]. A’isha (Allah ya kara mata yarda) kuma ta ruwaito cewa, Saudatu ‘yar Zam’ah lokacin da ta ga ta fara manyanta, ta ji tsoron ko Annabi (ﷺ) zai sawwaƙe mata, sai ta ce da shi: “Ya Manzon Allah (ﷺ), na ba wa A’isha kwanana, sai ko Annabi (ﷺ) ya karɓi wannan kyautar daga gare ta. A’isha ta ce: “Muna ganin a kanta ne da ire-irenta wannan ayar ta sauka.” [Abu Dawud #2135, da Al-Hakim #2760]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da cewa, duk yadda maza suka yi ƙoƙarin tabbatar da adalci a tsakanin matansu, ba za su iya ba, dole ne a sami fifikon soyayyar zukata dangane da su. To amma fa ba a yarda su karkata gaba ɗaya ga ɗayar su ƙyale ɗayar a rataye, ita ba a sake ta ba, ita kuma ba mai aure ba. Allah kuma ya ƙara jaddada batun sulhu da fahimtar juna tsakanin ma’aurata da kuma tsoron Allah cikin lamarin aure. Allah ya ce in sun yi haka, to shi mai gafara ne, mai jin ƙai. Idan kuma abu ya ci tura, sulhu ya ƙi yiwuwa, har an kai ga saki, to Allah zai haɗa kowa da rabonsa, domin falalar Allah tana da yalwa, ba ta da iyaka, kuma shi gwani ne, mai hikima cikin duk hukunce-hukuncensa.

  131. وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ وَصَّيۡنَا ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَإِيَّاكُمۡ أَنِ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ وَإِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَنِيًّا حَمِيدٗا

    Open ayah 4:131

    Kuma duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa na Allah ne. Kuma haƙiƙa Mun yi wasiyya ga waɗanda Muka bai wa Littafi gabaninku da ku kanku cewa, ku ji tsoron Allah. Idan kuwa kuka kafirce, to lalle abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa duka na Allah ne. Kuma Allah Ya kasance Mawadaci ne, Sha-yabo.

  132. وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلًا

    Open ayah 4:132

    Kuma duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa na Allah ne. kuma Allah Ya isa Abin dogaro.

  133. إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ أَيُّهَا ٱلنَّاسُ وَيَأۡتِ بِـَٔاخَرِينَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ قَدِيرٗا

    Open ayah 4:133

    Idan Ya ga dama sai Ya tafiyar da ku, ya ku mutane, kuma Ya kawo waɗansu daban. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan hakan.

  134. مَّن كَانَ يُرِيدُ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ ثَوَابُ ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا

    Open ayah 4:134

    Duk wanda ya kasance yana son ladan duniya, to ladan duniya da na lahira duk a hannun Allah suke. Kuma Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, shi kaɗai yake da mulkin abin da yake sammai da abin da yake ƙasa; shi ne mai sarrafa su yadda ya ga dama. Kuma haƙiƙa ya yi wa Yahudawa da Nasara wasiyya, har ma da Musulmi cewa, su kiyaye dokokin Allah, ta hanyar aikata umarninsa da guje wa haninsa. Idan kuwa suka kafirce masa, to ba za su cuce shi da komai ba, sai dai su cuci kawunansu, domin wannan ba zai tauye komai cikin mulkinsa ba. Duk abin da yake cikin sammai da na cikin ƙasa mulkinsa ne, kowa mai buƙata ne a wajensa, amma shi ba shi da buƙatar komai a wajen kowa; yana da siffofi na kamala, kuma shi ne sha-yabo a kan ni’imominsa da kyautatawarsa ga bayinsa. Idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ga dama duk sai ya halaka mutane gaba ɗaya, ya kawo wasu daban waɗanda suka fi tsoronSa da yi masa ɗa’a. Allah kuma yana da cikakken iko a kan yin hakan. Don haka duk wanda yake duniya ce a ransa, ba ya tunanin sakamakon lahira, to ya sani fa cewa sakamakon duniya da na lahira duka a hannun Allah suke, kuma yana ba da su ga duk wanda ya nema. Shi kuma wancan mai neman duniya kaɗai, me zai hana shi ya nemi duka biyun? Lalle Allah yana jin kowa, yana kuma ganin komai.

  135. ۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُواْ قَوَّٰمِينَ بِٱلۡقِسۡطِ شُهَدَآءَ لِلَّهِ وَلَوۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ أَوِ ٱلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَۚ إِن يَكُنۡ غَنِيًّا أَوۡ فَقِيرٗا فَٱللَّهُ أَوۡلَىٰ بِهِمَاۖ فَلَا تَتَّبِعُواْ ٱلۡهَوَىٰٓ أَن تَعۡدِلُواْۚ وَإِن تَلۡوُۥٓاْ أَوۡ تُعۡرِضُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا

    Open ayah 4:135

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku zamo masu tsayawa da adalci, kuna masu ba da shaida don Allah, ko da kuwa a kan kawunanku ne ko a kan mahaifanku ko a kan dangi makusanta. Idan ya kasance mawadaci ne ko matalauci, to Allah Shi ne Ya fi sanin abin da ya fi cancanta gare su; don haka kada ku bi son zuciyarku ku ƙi yin adalci. Idan kuwa kuka karkatar da shaida ko kuka ƙi ba da ita, to lalle Allah Ya kasance Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne.

  136. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِي نَزَّلَ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِن قَبۡلُۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا

    Open ayah 4:136

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi imani da Allah da Manzonsa da Littafin da Ya saukar ga Manzonsa da Littafin da Ya saukar gabaninsa. Duk wanda kuwa ya kafirce wa Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar ƙarshe, to haƙiƙa ya ɓace ɓata mai nisa.

  137. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ ثُمَّ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ ثُمَّ ٱزۡدَادُواْ كُفۡرٗا لَّمۡ يَكُنِ ٱللَّهُ لِيَغۡفِرَ لَهُمۡ وَلَا لِيَهۡدِيَهُمۡ سَبِيلَۢا

    Open ayah 4:137

    Lalle waɗanda suka yi imani, sannan daga baya suka kafirce, sannan kuma suka ƙara yin imani, sannan suka kafirce, sannan suka ƙara kafirci, waɗannan Allah ba zai yi musu gafara ba, ba kuma zai shiryar da su tafarki madaidaici ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar bayinsa da su zama masu adalci dangane da haƙƙoƙin Allah da na bayinsa, su bayar da shaida don Allah, ko da kuwa shaidar su kansu ta shafa ko iyayensu ko danginsu. Kada su yi la’akari da cewa wane mawadaci ne, bari su daɗaɗa masa, ko wane matalauci ne, bari su tausaya masa. Lalle su fahimta cewa da mai wadata da matalauci duk al’amurransu na ga Allah, ya fi kowa sanin abin da ya fi zama maslaha a gare su, don haka kada su bi son zuciya su ƙi yin adalci. Idan suka karkatar da shaida ko suka ƙi bayar da ita, to su sani cewa Allah yana da cikakkiyar masaniya game da abin da suke aikatawa kuma zai saka wa kowa a kan abin da ya aikata. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su tsaya ƙyam a kan imaninsu da Allah da Annabinsa (ﷺ), su riƙe addininsu, kuma su yi imani da Alƙur’ani da littattafan da suka gabata, waɗanda Allah ya saukar. Duk kuwa wanda ya kafirce wa Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar lahira, to haƙiƙa ya ɓata daga hanya madaidaiciya mummunar ɓacewa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk mutumin da ya ce shi mumini ne ya kafirta, bayan nan sannan ya sake dawowa mumini, sai kuma ya sake kafirta, ya ci gaba da kafircinsa, to wannan Allah ba zai taɓa gafarta masa ba, kuma ba zai yi masa katari na dacewa da bin tafarkin gaskiya ba, domin ya zaɓa wa kansa ɓata da kafirci a kan shiriya da imani.

  138. بَشِّرِ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ بِأَنَّ لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمًا

    Open ayah 4:138

    Ka yi albishir ga munafuƙai cewa, suna da wata azaba mai raɗaɗi.

  139. ٱلَّذِينَ يَتَّخِذُونَ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَيَبۡتَغُونَ عِندَهُمُ ٱلۡعِزَّةَ فَإِنَّ ٱلۡعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا

    Open ayah 4:139

    Su ne waɗanda suke riƙar kafirai a matsayin masoya, su ƙyale muminai. Shin suna neman wata ɗaukaka ce a wurinsu? To lalle ɗaukaka gaba ɗaya ta Allah ce.

  140. وَقَدۡ نَزَّلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أَنۡ إِذَا سَمِعۡتُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ يُكۡفَرُ بِهَا وَيُسۡتَهۡزَأُ بِهَا فَلَا تَقۡعُدُواْ مَعَهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦٓ إِنَّكُمۡ إِذٗا مِّثۡلُهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ جَامِعُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡكَٰفِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا 

    Open ayah 4:140

    Kuma haƙiƙa Ya saukar muku a cikin littafi cewa, idan kuka ji ayoyin Allah ana kafirce musu, ana izgili da su, to kar ku zauna tare da su har sai sun shiga cikin wani zancen daban ba wannan ba. Lalle in har kuka zauna tare da su, to kun zama kamarsu. Lalle Allah Mai tattara munafuƙai ne da kafirai cikin wutar Jahannama gaba ɗaya.

  141. ٱلَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمۡ فَإِن كَانَ لَكُمۡ فَتۡحٞ مِّنَ ٱللَّهِ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَكُن مَّعَكُمۡ وَإِن كَانَ لِلۡكَٰفِرِينَ نَصِيبٞ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَسۡتَحۡوِذۡ عَلَيۡكُمۡ وَنَمۡنَعۡكُم مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَلَن يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لِلۡكَٰفِرِينَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ سَبِيلًا

    Open ayah 4:141

    Su ne waɗanda suke fakon ku, idan kun sami wata nasara daga Allah sai su ce: “Shin ashe ba tare da ku muke ba?” Kuma idan kafirai ne suka samu wata nasara, sai su ce: “Ashe ba mu muka sami dama a kanku ba (amma muka ƙyale ku), kuma muka kare ku daga muminai?” To lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninku ranar alƙiyama, kuma Allah ba zai taɓa ba wa kafirai wata dama ba a kan muminai.

  142. إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَهُوَ خَٰدِعُهُمۡ وَإِذَا قَامُوٓاْ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ قَامُواْ كُسَالَىٰ يُرَآءُونَ ٱلنَّاسَ وَلَا يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 4:142

    Lalle munafuƙai suna yaudarar Allah, alhali kuwa Shi Mai mayar musu da sakamakon yaudararsu ne; kuma idan sun tashi zuwa salla, za su tashi suna masu kasala ne, suna yin aiki don mutane su gani, kuma ba su ambaton Allah sai kaɗan.

  143. مُّذَبۡذَبِينَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ لَآ إِلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِ وَلَآ إِلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلٗا

    Open ayah 4:143

    Suna ta kai-kawo tsakanin haka (kafirci da imani), su ba sa tare da waɗanan, kuma ba sa tare da waɗancan. Duk wanda Allah Ya ɓatar da shi kuwa, to babu yadda za ka iya sama masa wani tafarki na shiriya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana halayen munafuƙai ne na rashin gaskiya da ƙin yin imani da Allah da Manzonsa (ﷺ). A fili suna nuna su Musulmi ne, amma a ɓoye suna tare da kafirci da kafirai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi da ya yi musu albishir da wata azaba mai raɗaɗi, domin sun nuna ƙauna da goyon baya ga kafirai maimakon muminai. Wai me ya sa suke aikata hakan? Shin wani girma suke nema a wajen kafirai? To ai kuwa ba za su same shi ba, domin girma gaba ɗaya na Allah ne shi kaɗai, shi yake bayar da shi, kuma ga muminai kaɗai yake ba da shi, don haka munafuƙai ba za su same shi ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, ya zartar da hukunci a Alƙur’ani na cewa, idan suka ji ana yin izgili da ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka), ana kafirce musu, to kada su kuskura su zauna tare da masu izgilin har sai sun bari, sun shiga wata tattaunawar daban wadda ba ta izgili ba. Idan kuwa har suka yarda suka zauna tare da su cikin wannan hali na izgili da kafirce wa ayoyin Allah, to su ma sun zama kamar su, sun yi tarayya da su a cikin laifi. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ishara ne zuwa ga aya ta 68 cikin Suratul An’am , wadda ta haramta wa muminai zama inda ake yi wa shari’ar Allah izgili da rashin kunya. Waɗannan munafuƙan su ne koyaushe suke sa ido su ga abin da zai faru ga muminai, mai kyau ko marar kyau. Idan suka ga Allah ya ba wa muminai nasara a kan kafirai a wajen yaƙi, sun fatattaki kafirai, sun kwashi ganima, sai ka ji su suna ce wa muminai: “Shin ba tare da ku muke ba, kuma tare muka fita yaƙin?” Suna neman a ba su kasonsu daga ganimar. Idan kuwa kafirai ne suka sami nasara a kan muminai, har suka kwashe dukiyoyin muminai, to a nan ma sai ka ji munafuƙai suna ce wa kafirai: “Yanzu ashe ba mun taimaka muku ba, mun ba ku tsaro daga muminai?” Suna son a nan ma kafirai su yaga musu wani kaso daga dukiyar da suka samu ta muminai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ranar alƙiyama zai yi hukunci tsakanin muminai da kafirai, ya shigar da muminai gidajen Aljanna, ya shigar da kafirai da munafuƙai wutar Jahannama. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawarin cewa ba zai taɓa ba wa kafirai nasara a kan muminai gaba ɗaya ba. Wato suna iya samun nasara a kansu a wani wuri ban da wani wuri. Hakanan ba zai taɓa ba wa kafirai wata hujja ba wadda za su rinjayi muminai da ita a ranar lahira. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fallasa wani mummunan tunani na munafuƙai da yaudara ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Wato su tunda sun bayyana Musuluncinsu a fili don su samu kare rayukansu da dukiyoyinsu, a nan duniya, kuma har ma suna tunanin wannan dabarar za ta amfane su har a lahira, amma ba su san da cewa Allah ya fi su iya mayar da martanin yaudararsu ba, ya hana a kashe su ko a taɓa dukiyoyinsu a nan duniya, amma ya yi musu talala har su iske shi ranar lahira, ya kama su da laifinsu, ya shigar da su wutar Jahannama. Tir da wannan makoma. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan munafuƙai da ma ba addini suka damu da shi ba; duk sa’adda suka tashi salla, sukan yi ta ne cikin kasala da mutuwar jiki, domin a bisa dole ne suke yin ta don muminai su gan su suna salla, su yarda cewa, su ma suna tare da su, ba sa kuma ambaton Allah da harsunansu da gaɓoɓinsu da zukatansu cikin sallarsu, ba sa sanin ma abin da suke faɗa saboda zukatansu sun cika da gafala da riya da munafunci. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ji Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wannan ita ce sallar munafuki. Yakan zauna ya zuba wa rana ido har sai ta kasance tsakanin ƙahonnin Shaiɗan biyu (wato ta tafi faɗuwa), sai ya miƙe tsaye ya duddungura raka’a huɗu, ba ya ambaton Allah a ciki sai ɗan kaɗan.” [Muslim #22]. Har wa yau waɗannan munafukan mutane ne masu kai-kawo tsakanin imani da kafirci. Su ba su tare da muminai gaba ɗayansu, kuma ba sa tare da kafirai gaba ɗayansu; a fili suna tare da muminai, a ɓoye kuma suna tare da kafirai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Misalin munafuki kamar misalin akuya ce mai kai-komo tsakanin dabbobi, wani lokaci ta kaɗa ta shiga waɗannan, wani lokaci kuma ta kaɗa ta koma wajen waɗancan.” [Muslim #2784]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya ɓatar daga kan hanyar shiriya saboda laifukansa, to ba za ka taɓa sama masa wata hanyar shiriya ba har abada.

  144. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ عَلَيۡكُمۡ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينًا

    Open ayah 4:144

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi kafirai a matsayin masoya ku bar muminai. Shin kuna so ku ba wa Allah wata hujja mabayyaniya ne a kanku?

  145. إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِي ٱلدَّرۡكِ ٱلۡأَسۡفَلِ مِنَ ٱلنَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمۡ نَصِيرًا

    Open ayah 4:145

    Lalle munafuƙai suna cikin matakin ƙarshe na can ƙarƙashin wuta, kuma ba za ka taɓa sama musu wani mataimaki ba.

  146. إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَٱعۡتَصَمُواْ بِٱللَّهِ وَأَخۡلَصُواْ دِينَهُمۡ لِلَّهِ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَسَوۡفَ يُؤۡتِ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَجۡرًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:146

    Sai fa waɗanda suka tuba, kuma suka gyara aikinsu, kuma suka yi riƙo ga igiyar Allah; kuma suka tsantsanta addininsu don Allah; to waɗannan suna tare da muminai; kuma Allah zai bai wa muminai lada mai girma.

  147. مَّا يَفۡعَلُ ٱللَّهُ بِعَذَابِكُمۡ إِن شَكَرۡتُمۡ وَءَامَنتُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ شَاكِرًا عَلِيمٗا

    Open ayah 4:147

    Me Allah zai yi da azabtar da ku idan har kun yi godiya kuma kun yi imani? Allah kuwa Ya kasance Mai godiya ne, Mai yawan sani. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa muminai kashedi da su riƙi kafirai masoyansu, suna ƙawance da su, su bar ‘yan’uwansu muminai; yin haka zai ba wa Allah wata hujja bayyananniya ta yi musu uƙuba. Sai kuma ya bayyana makomar munafuƙai da cewa, suna can ƙarƙashin wutar Jahannama, kuma ba wanda zai taimaka ya ceto su daga wannan azabar. Sai dai idan sun tuba sun bar munafunci, sun gyara ayyukansu na fili da na ɓoye, suka tsantsanta addininsu ga Allah shi kaɗai, suka watsar da mugun halinsu na munafunci da riya; to da za su yi haka, da sun dawo cikin muminai, suna tare da su a duniya da lahira, su kuma shiga Aljanna tare. Kuma Allah zai ba wa muminai wani lada mai girma wanda babu wanda ya san haƙiƙaninsa sai Allah shi kaɗai. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, me zai sa ya yi wa bayinsa azaba, alhali sun yi godiya bisa ga ni’imominsa, sun yi masa biyayya, kuma sun yi imani na gaskiya? Allah ba shi da wata buƙata ta yin haka. Allah kuma mai godiya ne ga wanda ya gode masa, sai ya ba shi lada fiye da aikinsa, kuma masani ne ga wanda ya yi imani har zuciyarsa, kuma zai saka wa kowa a bisa aikinsa mai kyau ko mummuna.

  148. ۞لَّا يُحِبُّ ٱللَّهُ ٱلۡجَهۡرَ بِٱلسُّوٓءِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ إِلَّا مَن ظُلِمَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا

    Open ayah 4:148

    Allah ba Ya son bayyana mummunan zance, sai dai wanda aka zalunce shi. Kuma Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai yawan sani.

  149. إِن تُبۡدُواْ خَيۡرًا أَوۡ تُخۡفُوهُ أَوۡ تَعۡفُواْ عَن سُوٓءٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوّٗا قَدِيرًا

    Open ayah 4:149

    Idan har kuka bayyana wani alheri ko kuka ɓoye shi ko kuma kuka yi afuwa game da wata cutarwa, to lalle Allah Ya kasance Mai yawan afuwa ne, Mai cikakken iko.

  150. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيُرِيدُونَ أَن يُفَرِّقُواْ بَيۡنَ ٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيَقُولُونَ نُؤۡمِنُ بِبَعۡضٖ وَنَكۡفُرُ بِبَعۡضٖ وَيُرِيدُونَ أَن يَتَّخِذُواْ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا 

    Open ayah 4:150

    Lalle waɗanda suke kafirce wa Allah da manzanninsa, kuma suke nufin su nuna bambanci tsakanin Allah da manzanninsa, kuma suna cewa: “Mun yi imani da wasu, mun kuma kafirce wa wasu,” kuma suna son su riƙi wani tafarki tsakanin wannan (imani da kafirci).

  151. أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ حَقّٗاۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا

    Open ayah 4:151

    Waɗannan su ne kafirai na haƙiƙa. Kuma Mun yi wa kafirai tanadin wata azaba mai wulaƙantarwa.

  152. وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَلَمۡ يُفَرِّقُواْ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ أُوْلَٰٓئِكَ سَوۡفَ يُؤۡتِيهِمۡ أُجُورَهُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

    Open ayah 4:152

    Waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa, kuma ba su nuna bambanci tsakanin ɗaya daga cikinsu ba, waɗannan (Allah) zai ba su ladansu. Allah kuma Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan rahama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ba ya son wani daga bayinsa ya riƙa bayyana wata mummunar magana a kan wani, sai dai mutumin da aka zalunce shi, to shi babu laifi idan ya furta maganar zaluncin da aka yi masa, musamman idan yana so a bi masa haƙƙinsa, kamar yadda ba shi da laifi idan ya yi mummunar addu’a a kan wanda ya zalunce shi. Allah kuwa mai jin duk maganganun mutane ne masu kyau da marasa kyau, kuma masanin duk abin da yake cikin zukatansu na kyakkyawar aniya da mummuna, kuma zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya faɗa wa bayinsa cewa, idan suka bayyana wani alheri ko suka ɓoye shi, ko suka yi afuwa ga wanda ya ɓata musu, to su sani shi ma Allah mai yafe wa bayinsa laifuffukansu ne, duk da cewa yana da ikon ya kama su da waɗannan laifukan, don haka su ma su yafe wa waɗanda suka yi musu ba daidai ba, kamar yadda suke so Allah ya yafe musu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya dawo kan hukuncin kafiran da suke bijire wa Allah da manzanninsa, suke raba tsakanin Allah da manzanninsa, ta hanyar cewa sun yi imani da Allah, amma ba su yi imani da manzanninsa ba, ko kuma su ce sun yi imani da wasu manzannin, amma ba su yi imani da wasu ba, kuma wai so suke irin wannan imani ya zama wata hanya ce da za ta sada su da Ubangijinsu. Sai Allah ya bayyana cewa, waɗannan su ne kafirai na haƙiƙa: wannan mataki da suka ɗauka ba zai ta taɓa amfana musu komai ba, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) tuni ya tanadar musu azaba ta wulaƙanci tana nan tana jiran su, mutuwa ce kawai a tsakaninsu da ita. To amma muminai waɗanda suka yi imani da manzanni gaba ɗaya, ba su bambanta tsakaninsu ba, to su kam Allah ya yi musu alƙawarin sakamako mai girma saboda imanin da suka yi na gaskiya ne, don haka Allah zai yi musu sakayya a kansa, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbata mai yawan gafara ne, mai yawan jin ƙai.

  153. يَسۡـَٔلُكَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن تُنَزِّلَ عَلَيۡهِمۡ كِتَٰبٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِۚ فَقَدۡ سَأَلُواْ مُوسَىٰٓ أَكۡبَرَ مِن ذَٰلِكَ فَقَالُوٓاْ أَرِنَا ٱللَّهَ جَهۡرَةٗ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ بِظُلۡمِهِمۡۚ ثُمَّ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ فَعَفَوۡنَا عَن ذَٰلِكَۚ وَءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 4:153

    Ma’abota Littafi (Yahudawa da Nasara) suna tambayar ka cewa, ka saukar musu da wani cikakken littafi daga sama. To haƙiƙa da ma can sun tambayi Musa abin da ya fi wannan girma, da suka ce: “Ka nuna mana Allah a fili,” sai tsawa ta far musu a sanadiyyar zaluncinsu. Sannan kuma suka riƙi ɗan maraƙi abin bauta bayan hujjoji sun zo musu, sai Muka yi (musu) afuwa a kan haka. Kuma Muka bai wa Musa hujja bayyananniya.

  154. وَرَفَعۡنَا فَوۡقَهُمُ ٱلطُّورَ بِمِيثَٰقِهِمۡ وَقُلۡنَا لَهُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا وَقُلۡنَا لَهُمۡ لَا تَعۡدُواْ فِي ٱلسَّبۡتِ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

    Open ayah 4:154

    Kuma Muka ɗaga dutsen Ɗuri a kansu don su karɓi alƙawarinsu, kuma Muka ce da su: “Ku shiga ƙofar (garin) a sunkuye.” Kuma Muka ce da su: “Kada ku ƙetare iyaka (ta kamun kifi) a ranar Asabar,” kuma Muka yi alƙawari mai ƙarfi da su.

  155. فَبِمَا نَقۡضِهِم مِّيثَٰقَهُمۡ وَكُفۡرِهِم بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَقَتۡلِهِمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَقَوۡلِهِمۡ قُلُوبُنَا غُلۡفُۢۚ بَلۡ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَيۡهَا بِكُفۡرِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُونَ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 4:155

    To saboda warware alƙawarinsu da kafircewarsu ga ayoyin Allah da kuma kashe wasu annabawan ba tare da wani laifi ba da kuma faɗinsu cewa: “Zukatanmu a rufe suke.”A’a, ba haka ne ba, Allah ne Ya rufe su saboda kafircinsu, don haka ba za su yi imani ba sai ɗan kaɗan.

  156. وَبِكُفۡرِهِمۡ وَقَوۡلِهِمۡ عَلَىٰ مَرۡيَمَ بُهۡتَٰنًا عَظِيمٗا

    Open ayah 4:156

    Kuma saboda kafircinsu da kuma wata babbar ƙarya da suka yi wa Maryamu.

  157. وَقَوۡلِهِمۡ إِنَّا قَتَلۡنَا ٱلۡمَسِيحَ عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ رَسُولَ ٱللَّهِ وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَٰكِن شُبِّهَ لَهُمۡۚ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُۚ مَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍ إِلَّا ٱتِّبَاعَ ٱلظَّنِّۚ وَمَا قَتَلُوهُ يَقِينَۢا

    Open ayah 4:157

    Da kuma faɗarsu cewa: “Lalle mu mun kashe Almasihu Isa ɗan Maryamu Manzon Allah,” alhalin kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su gicciye shi ba, sai dai an kamanta musu (wani da shi ne). Kuma lalle waɗanda suka yi saɓani game da shi (Annabi Isa) suna cikin shakka game da (kashe) shi, ba su da wani ilimi face bin zato. Kuma a haƙiƙanin gaskiya ba su kashe shi ba.

  158. بَل رَّفَعَهُ ٱللَّهُ إِلَيۡهِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:158

    Ba haka ba ne, Allah ya ɗaga shi zuwa gare Shi ne. kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima.

  159. وَإِن مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ إِلَّا لَيُؤۡمِنَنَّ بِهِۦ قَبۡلَ مَوۡتِهِۦۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكُونُ عَلَيۡهِمۡ شَهِيدٗا

    Open ayah 4:159

    Kuma babu wani daga Ma’abota Littafi face sai ya yi imani da shi kafin mutuwarsa; kuma a ranar tashin alƙiyama zai zama mai ba da shaida a kansu.

  160. فَبِظُلۡمٖ مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا عَلَيۡهِمۡ طَيِّبَٰتٍ أُحِلَّتۡ لَهُمۡ وَبِصَدِّهِمۡ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ كَثِيرٗا 

    Open ayah 4:160

    To saboda zaluncin waɗanda suka zama Yahudawa, Muka haramta musu daɗaɗan abubuwan da aka halatta musu, kuma saboda suna yawan hana mutane bin hanyar Allah.

  161. وَأَخۡذِهِمُ ٱلرِّبَوٰاْ وَقَدۡ نُهُواْ عَنۡهُ وَأَكۡلِهِمۡ أَمۡوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡبَٰطِلِۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ مِنۡهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا

    Open ayah 4:161

    Da kuma cin riba da suke yi, tare da cewa an hana su cin ta, da kuma yadda suke cin dukiyar mutane ta hanyar cuta, Mun kuwa yi tanadin azaba mai raɗaɗi ga kafirai daga cikinsu.

  162. لَّٰكِنِ ٱلرَّٰسِخُونَ فِي ٱلۡعِلۡمِ مِنۡهُمۡ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَۚ وَٱلۡمُقِيمِينَ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَٱلۡمُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ أُوْلَٰٓئِكَ سَنُؤۡتِيهِمۡ أَجۡرًا عَظِيمًا

    Open ayah 4:162

    Amma masu zurfin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar gabaninka; musamman ma masu tsayar da salla, da kuma masu bayar da zakka, kuma masu imani da Allah da ranar ƙarshe. Waɗannan ba da jimawa ba za Mu ba su lada mai girma. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wani izgili ne na Yahudawa da Nasara; duk da cewa Allah ya saukar musu da littafi, amma kuma sai suka riƙa yi wa Annabi Muhammadu (ﷺ) tambaya ta ƙure cewa, suna son ya sauko musu da wani littafi cikakke daga sama. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa cewa, kada ma ya damu da wannan ta’annati nasu; ai wannan ba sabon abu ba ne a gare su tare da annabawa, domin sun taɓa neman buƙatar da ta fi wannan wajen Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi),inda suka neme shi ya nuna musu Allah ƙuru-ƙuru su gan shi da idanunsu kafin su gaskata shi. To a kan haka sai da Allah ya yi musu uƙuba da wata tsawa ta hallaka su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tserar da su ta hanyar sake hura musu rai; amma wannan bai hana su sake komawa gidan jiya ba, domin bauta wa ɗan maraƙi suka yi bayan sun ga hujjoji bayyanannu. Amma duk da haka Allah ya yi musu afuwa, kuma ya ba wa Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) hujjoji bayyanannu, masu tabbatar da gaskiyar abin da ya zo musu da shi. Game da ƙin yin imani da littafin Attaura da Yahudawa suka yi, sai da Allah ya ɗaga dutsen Ɗuri a samansu don ya tsoratar da su a kan lalle su cika alƙawarin da suka ɗauko na za yin aiki da Attaura da ya saukar wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Haka kuma Allah ya ba da labarin umarnin da ya ba su na cewa, in sun zo shiga Baitul Maƙdis, su shige ta a sunkuye. Da kuma hanin da ya yi musu na kamun kifi a ranar Asabar, ya yi alƙawari mai ƙarfi kan lalle su bi umarninsa, su kuma guji haninsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana laifukansu waɗanda suka yi musabbabin la’antar su da ya yi da cewa, ba wani abu ya jawo musu hakan ba, face warware alƙawarin da aka yi da su da kuma kafirce wa ayoyin Allah da kashe annabawa ba tare da wani haƙƙi ba, sannan da cewar da suka yi wai zukatansu a rufe suke, ba sa iya fahimtar komai, alhali kuwa ƙarya ce suke faɗa. Allah ya nuna cewa ya rufe musu zukata ne saboda kafircinsu. Kuma ga shi duk abin da aka nemi su yi imani da shi, sun bijire masa sai ɗan wani abu ƙanƙani a cikinsu. Wasu dalilan kuma da suka jawo musu la’anar Allah (Mai tsarki da daukaka) sun haɗa da, ƙage da tuhumar da suka yi wa Maryam (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), na cewa wai zina ta yi ta haifi Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da kuma cewar da suka yi wai sun kashe Isa ɗan Maryam, Manzon Allah. Allah ya ƙaryata su da cewa, ba su kashe shi ba, kuma ba su gicciye shi ba; abin da aka yi shi ne an jefa wa wani daga cikinsu kamanninsa ne, suka zaci shi ne Annabi Isa, suka kama shi suka kashe. Daga nan sai aka samu saɓani daga cikin Yahudawa da Nasara game da sha’anin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi); wasu na cewa shi ne aka kashe kuma aka gicciye; wasu kuma suka ce wani ne ba shi ba. To wannan dai ya jefa su cikin shakka da ruɗani da ɗimuwa, ba su da wani ilimi game da hakan sai tsantsar zato. Gaskiyar lamarin dai shi ne ba su kashe shi ba, Allah ne ya ɗauke shi zuwa sama, don haka ba su iya cutar da shi da komai ba. Kuma ai Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne Gagara-badau, ba mai iya ja da shi, ya fi ƙarfin maƙiyansa, kuma yana da hikima cikin ayyukansa, duk kuma abubuwan da ya zartar, yana ajiye komai ne a muhallinsa da ya dace da shi. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana gaya mana lokacin bayyanar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) watau sanda zai sauko ƙasa a ƙarshen zamani. A wannan lokaci babu wani daga cikin Yahudu da Nasara face sai ya yi imani da shi kafin mutuwarsa, sannan kuma zai zo a ranar gobe ƙiyama yana mai ba da shaida a kansu game da isar musu da saƙon Allah da kuma ayyukansu da ya gani lokacin da yake cikinsu kafin a ɗauke shi zuwa sama, da lokacin da aka sauko da shi kafin mutuwarsa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, lokaci ya kusa ɗan Maryam zai sauko cikinku yana mai hukunci mai adalci, ya karya kuros, ya kashe alade, ya soke jiziya, dukiya ta yawaita, har a rasa mai karɓar ta sadaka, har ya zama a lokacin sujjada guda ɗaya ta fi duniya da duk abin da yake cikinta.” Sannan sai Abu Huraira ya ce: “In kun ga dama ku karanta faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka): “Kuma babu wani Ma’abocin Littafi, face sai ya yi imani da shi kafin mutuwarsa, kuma a ranar alƙiyama zai zama mai ba da shaida a kansu.” [Bukhari #3448, da Muslim #155]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, saboda zaluncin Yahudawa da hana mutane bin hanyar Allah a mafi yawancin lokuta, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haramta musu wasu daɗaɗan abubuwa waɗanda da farko ya halatta musu su, domin wannan ya zama uƙuba a gare su saboda laifukansu, da laifin cin dukiyar riba bayan an hana su cin ta, da kuma laifin ƙwace wa mutane dukiyoyinsu ba tare da wani dalili na shari’a ba. Don haka wanda duk ya kafirta daga cikinsu, Allah ya yi masa tanadin wata azaba mai raɗaɗin gaske. Daga nan sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zo da bayanin cewa, ba duka Yahudawa ne suka taru suka zama ɗaya ba, daga cikinsu akwai masu ilimi kuma waɗanda suka kafu a cikin ilimi, kuma suke aiki da iliminsu, da waɗanda suka yi imani da Allah da littattafansa da manzanninsa gaba ɗaya. To waɗannan suna yin imani da abin da aka saukar wa Annabi (ﷺ) watau Alƙur’ani, hakanan suna yin imani da littattafan da aka saukar gabanin Annabi (ﷺ), kuma su ne masu tsayar da salla yadda ya kamata, kuma suke ba da zakkar dukiyoyinsu ga waɗanda suka cancanta su ba, kuma su ne masu yin imani da Allah da ranar lahira da abin da zai faru a cikinta. To waɗannan Allah ya yi musu alƙawarin zai ba su wani lada mai girma, wanda shi ne gidan Aljanna.

  163. ۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

    Open ayah 4:163

    Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaƙa da Ya’aƙubu da kuma jikokin (Ya’aƙubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura.

  164. وَرُسُلٗا قَدۡ قَصَصۡنَٰهُمۡ عَلَيۡكَ مِن قَبۡلُ وَرُسُلٗا لَّمۡ نَقۡصُصۡهُمۡ عَلَيۡكَۚ وَكَلَّمَ ٱللَّهُ مُوسَىٰ تَكۡلِيمٗا

    Open ayah 4:164

    (Muka) kuma aiko manzanni waɗanda Muka ba ka labarinsu tun da farko, da waɗansu manzannin daban da ba Mu ba ka labarinsu ba; kuma Allah Ya yi magana da Musa kai-tsaye.

  165. رُّسُلٗا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُۢ بَعۡدَ ٱلرُّسُلِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا

    Open ayah 4:165

    Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaɗi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima.

  166. لَّٰكِنِ ٱللَّهُ يَشۡهَدُ بِمَآ أَنزَلَ إِلَيۡكَۖ أَنزَلَهُۥ بِعِلۡمِهِۦۖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَشۡهَدُونَۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًا

    Open ayah 4:166

    Amma Allah Yana shaida game da abin da Ya saukar maka; Ya saukar da shi ne da iliminsa; haka mala’iku ma suna shaidawa. Kuma Allah Ya isa Mai shaida. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, ya saukar masa da wahayi irin wanda ya saukar wa Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kuma annabawan da suka zo bayan Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kuma Allah ya saukar da wahayi ga Annabi Ibrahimu da ‘ya’yansa Annabi Isma’ila da Annabi Ishaƙ da Annabi Ya’aƙubu ɗan Annabi Ishaƙ, da kuma annabawan da suke cikin zurriyar Annabi Ya’aƙubu, da kuma Annabi Isa da Annabi Ayuba da Annabi Yunusa da Annabi Haruna da Annabi Sulaimanu (amincin Allah ya tabbata a gare su baki ɗaya), kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabi Dawudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) littafin Zabura. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, ba duk manzannin Allah ya san labarinsu ba; daga cikinsu akwai waɗanda Allah ya ba shi labarinsu a cikin Alƙur’ani tun gabanin wannan ayar ta sauka, akwai kuma waɗanda bai ba shi labarinsu ba, don haka bai san komai a kansu ba. Kuma Allah ya yi magana da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) magana ta haƙiƙa, ba tare da ɗan saƙo ba. To waɗannan manzanni duk Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko su ne don su zama masu yin albishir ga waɗanda suka yi imani, suka yi musu biyayya, da kyakkyawan sakamako duniya da lahira, sannan su yi gargaɗi ga waɗanda suka kafirce suka bijire musu da azabar Allah a duniya da lahira. Kuma babu sauran wani hanzari da mutane za su kawo don kafa wa Allah hujja da shi bayan aiko da manzanni. Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne Gagara-badau, mai murƙushe duk wani maƙiyinsa, kuma mai hikima ne cikin duk lamuransu, wanda yana daga cikin hikimominsa, aiko da manzanni da ya yi zuwa ga mutum da aljan, don ya yanke musu duk wani hanzari da za su iya kawowa a gaban Allah (Mai tsarki da daukaka) ranar gobe ƙiyama, su ce da ya aiko musu da manzanni, da sun yi musu biyayya, kamar yadda ya faɗa a Suratu Ɗa Ha , aya ta 134. An karɓo daga Mughira ɗan Shu’uba (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Babu wani mai son yanke hanzari kamar Allah, saboda haka ne ma ya aiko (manzanni) masu bushara masu gargaɗi.” [Bukhari #7416, da Muslim #1499]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, idan har kafirai sun bijire masa, sun ƙi yarda da gaskiyar da ya zo da ita, suna tuhumarsa, to su sani cewa, Allah shi ne yake masa shaida a kan Alƙur’anin da ya saukar masa cewa, Allah ya saukar masa shi ne da iliminsa. Hakanan su ma mala’iku dukansu shaidu ne a kan gaskiyarsa da manzancinsa da gaskiyar Alƙur’anin da aka saukar masa, don haka kada kafircin kafirai ya dame shi, Allah ya isa shaida a kan gaskiyar duk abin da ya saukar masa.

  167. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ قَدۡ ضَلُّواْ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا

    Open ayah 4:167

    Lalle waɗanda suka kafirta, kuma suka kange mutane daga hanyar Allah, haƙiƙa sun ɓace ɓata mai nisa.

  168. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَظَلَمُواْ لَمۡ يَكُنِ ٱللَّهُ لِيَغۡفِرَ لَهُمۡ وَلَا لِيَهۡدِيَهُمۡ طَرِيقًا

    Open ayah 4:168

    Lalle waɗanda suka kafirta, kuma suka yi zalunci, Allah ba zai taɓa yi musu gafara ba, ba kuma zai shiryar da su wata hanya ta gari ba.

  169. إِلَّا طَرِيقَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٗا

    Open ayah 4:169

    Sai dai hanyar wutar Jahannama, suna masu dawwama a cikinta har abada. Yin hakan kuwa ya kasance abu ne mai sauƙi a wajen Allah.

  170. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُمُ ٱلرَّسُولُ بِٱلۡحَقِّ مِن رَّبِّكُمۡ فَـَٔامِنُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ وَإِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا 

    Open ayah 4:170

    Ya ku mutane, haƙiƙa Manzo ya zo muku da gaskiya daga wajen Ubangijinku, don haka ku yi imani shi ya fi alheri a gare ku. Idan kuwa kuka kafirce, to lalle abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa duk na Allah ne. kuma Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima. A nan ma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayani ne a kan kafiran da suka bijire wa gaskiya, suka kuma hana mutane su ba da gaskiya; waɗannan sun ɓata ɓata mai nisan gaske. Ya kuma tabbatar da cewa, waɗannan sun cuci kawunansu kuma ba zai taɓa gafarta musu ba, balle ya datar da su ga bin hanyar gaskiya wadda za ta kai su ga samun gidan Aljanna, sai dai zuwa ga bin hanyar ɓata wadda za ta kai su ga shiga wutar Jahannama, su dawwama a cikinta har abada. Kuma wannan al’amari ne mai sauƙi a wurin Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗakar da mutane baki ɗaya, yana mai cewa, duk abin da Annabi (ﷺ) ya zo musu da shi daga Allah gaskiya ne, don haka lalle su yi imani da shi; yin haka shi ne alheri a gare su duniya da lahira. Idan kuma sun ƙi sun kafirce to fa ba za su ragi Allah da komai ba, domin shi mawadaci ne, ba shi da wata buƙata a wajensu, shi ne mamallakin sammai da ƙasa, kuma shi mai cikkaken ilimi ne kuma mai cikakkiyar hikima ne da yake ajiye komai a inda ya dace. Don haka ya san wanda ya cancanci shiriya, ya kuma shiryar da shi, kuma ya san wanda ya cancanci ɓata, ya kuma ɓatar da shi.

  171. يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ رَسُولُ ٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥٓ أَلۡقَىٰهَآ إِلَىٰ مَرۡيَمَ وَرُوحٞ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُواْ ثَلَٰثَةٌۚ ٱنتَهُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ إِنَّمَا ٱللَّهُ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓ أَن يَكُونَ لَهُۥ وَلَدٞۘ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا

    Open ayah 4:171

    Ya ku Ma’abota Littafi, kada ku wuce iyaka cikin addininku, kuma kada ku faɗi wata magana game da Allah sai ta gaskiya. Almasihu Isa ɗan Maryamu Manzon Allah ne, kuma kalmarsa ce da ya jefa wa Maryamu, kuma Ruhi ne daga gare Shi; don haka ku yi imani da Allah da manzanninsa, kuma kada ku riƙa cewa su uku ne. Ku daina shi ya fi alheri a gare ku. Allah Shi ne kaɗai abin bauta da gaskiya, Ɗaya ne; Ya tsarkaka a ce Yana da ɗa. Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa nasa ne, kuma Allah Ya isa Abin dogaro.

  172. لَّن يَسۡتَنكِفَ ٱلۡمَسِيحُ أَن يَكُونَ عَبۡدٗا لِّلَّهِ وَلَا ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ ٱلۡمُقَرَّبُونَۚ وَمَن يَسۡتَنكِفۡ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَيَسۡتَكۡبِرۡ فَسَيَحۡشُرُهُمۡ إِلَيۡهِ جَمِيعٗا

    Open ayah 4:172

    Almasihu ba zai taɓa ƙyamar ya zama bawan Allah ba, hakanan su ma mala’iku makusanta. Duk wanda yake ƙyamar bautar Allah, kuma suke girman kai, to zai tattara su gaba ɗaya zuwa gare Shi.

  173. فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضۡلِهِۦۖ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱسۡتَنكَفُواْ وَٱسۡتَكۡبَرُواْ فَيُعَذِّبُهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

    Open ayah 4:173

    To amma waɗanda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka nagari, to zai cika musu ladansu, kuma Ya ƙara musu daga falalarsa. Amma waɗanda suka ƙyamaci bautar Allah kuwa, suka kuma yi girman kai, to zai azabtar da su azaba mai raɗaɗi, kuma ba za su taɓa samun wani masoyi ko mataimaki ba Allah ba.

  174. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُم بُرۡهَٰنٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ نُورٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 4:174

    Ya ku mutane, haƙiƙa hujja ta zo muku daga Ubangijinku, kuma Mun saukar muku wani haske mabayyani.

  175. فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱعۡتَصَمُواْ بِهِۦ فَسَيُدۡخِلُهُمۡ فِي رَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَفَضۡلٖ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَيۡهِ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

    Open ayah 4:175

    To amma waɗanda suka yi imani da Allah kuma suka yi garkuwa da Shi, to zai shigar da su cikin wata rahama tasa da kuma wata falala, kuma Ya shiryar da su tafarki madaidaici zuwa gare Shi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana gargaɗin Nasara ne, a kan wuce iyaka da suke yi wajen kuzuzuta lamarin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) har ta kai su ga cewa wai ɗan Allah ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, wannan ƙage ne suke yi wa Allah, domin shi ya fi ƙarfin a ce yana da mata balle ɗa. Shi kuwa Annabi Isa Almasihu ɗan Maryamu Manzon Allah ne, shi ya halicce shi ta hanyar kalmar da ya jefa ga Maryam (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), don haka lalle su yi imani da shi a matsayin bawan Allah, kuma Manzonsa, kamar yadda aka umarce su da su yi imani da Allah da duk manzanninsa, kada su riƙa cewa alloli uku ne, wato su mayar da Isa da mahifiyarsa ababen tarayya da Allah. An karɓo daga Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Kada ku kuzuzuta lamarina kamar yadda Nasara suka kuzuzuta lamarin Isa ɗan Maryam. Ni bawan Allah ne kawai, don haka ku ce: Bawan Allah kuma Manzonsa.” [Bukhari #3445]. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya zo yana yi wa Manzon Allah (ﷺ) kirari, yana cewa: “Ya Muhammadu, ya Shugabanmu, ya ɗan Shugabanmu, ya mafi alherinmu, ya ɗan mafi alherinmu.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane, ku lura da abin da kuke faɗa, kada Shaiɗan ya yi muku wasa da zukatanku. Ni Muhammadu ne ɗan Abdullahi, bawan Allah ne kuma Manzonsa, Wallahi ba na son ku ɗaga ni sama da matsayina da Allah ya ajiye ni.” [Ahmad #12573, da An-Nasa’i, As-Sunan Al-Kubra #10006, da Ibn Hibban #2640]. An karɓo daga Ubadatu ɗan Samit (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya shaida babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, kuma shi kaɗai ne ba shi da abokin tarayya, kuma Muhammadu bawansa ne Manzonsa, kuma Isa bawan Allah ne kuma Manzonsa, kuma kalmarsa ce da ya jefa ta ga Maryamu, kuma Ruhi ne daga gare shi, kuma ya shaida Aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce, to Allah zai shigar da shi Aljanna bisa aikinsa da ya kasance a kai na ƙwarai.” [Bukhari #3435, da Muslim #28]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da yi wa Nasara kashedi da cewa, su bar wannan mummunar aƙidar da suke kai na cewa, Isa ɗan Allah ne ko Allah uku ne, barin wannan aƙida shi ne alheri gare su, domin babu wani abin bauta na gaskiya sai Allah shi kaɗai, kuma ya tsarkaka a ce yana da ɗa. Me zai yi da ɗa, alhalin duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙassai nasa ne, halittarsa ce kuma bayinsa ne? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya isa abin dogaro, shi ne mai kula da kowa da komai, mai gudanar da al’amuran bayinsa ba tare da ya buƙaci taimakon wani ba, don haka me zai sa ya riƙi mata ko ɗa? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, su da suke irin wannan azarɓaɓi dangane da sha’anin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba su san cewa, shi da kansa bai taɓa ƙyamar ya zama bawan Allah ba, domin zamansa bawan Allah wata ɗaukaka ce gare shi. Su Mala’iku ba su taɓa ƙyamar bautar Allah ba. Don haka duk wanda ya ƙyamaci bautar Allah, to ya sani ya cuci kansa, Allah zai tattaro su gaba ɗaya ya hukunta su da irin hukuncin da suka cancanta. To amma wanda ya yi imani, kuma ya yi aiki na ƙwarai, to shi kam Allah (Mai tsarki da daukaka) zai ba shi cikakken ladansa daga yalwatacciyar falalarsa har ma da ƙari. Su kuma masu girman kai su ƙi bauta masa, Allah zai ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi, kuma ba su da wani mataimaki in ba Allah ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fuskantar da bayani zuwa ga mutane gaba ɗaya da cewa, hujjoji da dalilai ƙwarara sun zo musu, waɗanda suke bayyana ƙarya da gaskiya. Alƙur’ani mai haske ne ya nuna wa mutane hanya. Muminai waɗanda suka ba da gaskiya da Allah, kuma suka riƙe wannan hanyar da ƙarfi, to Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawarin zai shigar da su cikin rahamarsa da falalarsa da kuma samun yardarsa.

  176. يَسۡتَفۡتُونَكَ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِي ٱلۡكَلَٰلَةِۚ إِنِ ٱمۡرُؤٌاْ هَلَكَ لَيۡسَ لَهُۥ وَلَدٞ وَلَهُۥٓ أُخۡتٞ فَلَهَا نِصۡفُ مَا تَرَكَۚ وَهُوَ يَرِثُهَآ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهَا وَلَدٞۚ فَإِن كَانَتَا ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُمَا ٱلثُّلُثَانِ مِمَّا تَرَكَۚ وَإِن كَانُوٓاْ إِخۡوَةٗ رِّجَالٗا وَنِسَآءٗ فَلِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۗ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ أَن تَضِلُّواْۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ

    Open ayah 4:176

    Suna neman ka yi musu fatawa, ka ce: “Allah ne zai yi muku fatawa game da kalala . Idan mutum ya mutu ba shi da ɗa ko ‘ya, amma yana da ‘yar’uwa mace, to za a ba ta rabin abin da ya bari. Shi kuwa zai gaje (dukiyar) ta gaba ɗaya idan ya kasance ba ta da ɗa ko ‘ya. Amma idan suka kasance mata ne su biyu, to suna da biyu bisa uku na abin da ya bari. Idan kuwa sun kasance ‘yan’uwa masu yawa maza da mata, to duk namiji ɗaya yana da rabon mata biyu.” Allah Yana bayyana muku wannan ne don kar ku ɓace. Kuma Allah Masanin komai ne. A ayar ƙarshe ta wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) yana amsa fatawar da sahabban Annabi suke yi masa game da hukuncin gadon kalala, wato wanda ya mutu bai bar ɗa ko iyaye masu cin gadonsa ba. To sai Allah ya umarci Manzonsa da cewa shi ne zai ba su fatawa a kan wannan tambayar. Idan mutum ya mutu bai bar ‘ya’ya ko iyaye ba, sai ‘yar’uwarsa shaƙiƙiya ko li’abbiya, to za ta ci gadon rabin dukiyar da ya bari. Idan kuwa ita ce ta mutu kafin ɗan’uwanta, kuma ba ta bar ‘ya’ya ko iyaye masu cin gadonta ba, to shi zai ci gadon dukiyarta gaba ɗaya. Idan akwai wani mai cin gado tare da shi, kamar miji, to sai a ba shi kasonsa, shi kuma ɗan’uwan nata ya kwashe ragowar gadon. To amma kuma idan ‘yan’uwan nasa mata su biyu ne ko fiye da biyu, to za su ci gadon kaso biyu bisa uku na abin da ɗan’uwansu ya bari. Idan kuwa ‘yan’uwan da ya bari masu yawa ne maza da mata, to sai a ba namiji daga cikinsu kason mata biyu. Allah yana yi wa mutane bayanin hukunce-hukuncensa ne don kada su ɓata. Allah kuma masanin komai ne. An karɓo daga Albara (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Surar ƙarshe da ta sauka ita ce Suratu Bara’ah, kuma aya ta ƙarshe da ta sauka ita ce wannan ayar.” [Bukhari #4605]. An fassara wannan hadisi da cewa, yana nufin ƙarshe hukunce-hukuncen gado da aka saukar a Alƙur’ani. [Dubi, Alƙasɗalani, Irshadus Sari , Juzu’i na 7 shafi na 100]. An karɓo daga Jabiru ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (ﷺ) da Abubakar (Allah ya kara masa yarda) suka tako da ƙafa duba ni. Sai na suma, sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi alwala ya zuba mini sauran ruwan alwalarsa, sai na fardaɗo. Na ce: “Ya Manzon Allah, yaya zan yi hukunci game da dukiyata?” Sai bai ba ni wata amsa ba, har sai da wannan ayar ta sauka: “Suna yi maka fatawa. Ka ce: “Allah zai yi muku fatawa game da kalala.” [Bukhari #6723, da Muslim #1616].