المائدة

Al-Maaida

The Table · Surah 5 · Ayahs: 120 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَوۡفُواْ بِٱلۡعُقُودِۚ أُحِلَّتۡ لَكُم بَهِيمَةُ ٱلۡأَنۡعَٰمِ إِلَّا مَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ غَيۡرَ مُحِلِّي ٱلصَّيۡدِ وَأَنتُمۡ حُرُمٌۗ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ مَا يُرِيدُ

    Open ayah 5:1

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku cika alƙawura. An halatta muku dabbobin ni’ima, sai dai abin da ake karanta muku (haramcinsa), ba kuna masu halatta farauta ba alhalin kuna cikin Harami, lalle Allah Yana hukunta abin da Yake nufi.

  2. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحِلُّواْ شَعَٰٓئِرَ ٱللَّهِ وَلَا ٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَلَا ٱلۡهَدۡيَ وَلَا ٱلۡقَلَٰٓئِدَ وَلَآ ءَآمِّينَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّهِمۡ وَرِضۡوَٰنٗاۚ وَإِذَا حَلَلۡتُمۡ فَٱصۡطَادُواْۚ وَلَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ أَن صَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ أَن تَعۡتَدُواْۘ وَتَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

    Open ayah 5:2

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku halatta keta alfarmar alamomin addinin Allah, ko (ku wulaƙanta) Wata mai alfarma ko dabbobin hadaya ko dabbobin hadaya masu alama da (tare) masu nufin ziyarar Ɗaki mai alfarma, suna neman falala daga wurin Ubangijinsu da yardarsa. Idan kuwa kuka kwance Harami, to ku yi farauta (idan kuna so). Kuma kada ƙiyayyar wasu mutane da suka hana ku isa masallaci mai alfarma, ta sa ku yi ta’addanci. Kuma ku taimaki juna a kan aikin alheri da taƙawa; kada kuma ku taimaka wa juna a kan ayyukan saɓo da ta’addanci. Kuma ku kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar ne da umartar muminai kansu riƙa cika alƙawurran da suka ɗauka tsakaninsu da Allah da waɗanda suke tsakaninsu da ‘yan’uwansu mutane, amma alƙawuran da ba su saɓa wa shari’a ba. Sannan kuma ya bayyana musu cewa, ya halatta musu dabbobin ni’ima, irin su raƙuma da shanu da ƙananan dabbobi, sai dai waɗanda za a yi musu bayanin su nan gaba a aya ta 3. Kuma ba a halatta musu yin farauta ba lokacin da suke sanye haramin hajji ko umara, ko kuma sanda suke cikin Haramin Makka da Madina. Allah kuma yana hukunta abin da ya yi nufi ne, ya kuma zartar da hukuncin da ya ga dama. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya haramta wa muminai ƙetare iyakokinsa ta hanyar wulaƙanta abubuwa masu alfarma waɗanda ya yi umarnin a girmama su na addini, kamar ayyukan hajji da umra da kuma watannin nan masu alfarma, watau Shawwal da Zulƙi’ida da Zulhijja da Rajab, ta hanyar yin yaƙi a cikinsu ko aikata zalunci ko wasu laifuffuka. Hakanan ya haramta musu keta alfarmar dabbobin da aka ware don hadaya ta hanyar su yanka su kafin su ƙarasa mayankansu, ko kuma su hana dabbobin ƙarasawa can; haka kuma dabbobin da aka yi musu alamomi da rataye a wuyansu domin nuna cewa an keɓance su don yankan hadaya. Hakanan Allah ya hana muminai yaƙar waɗanda suka taho domin ziyarar Ɗakin Ka’aba don neman falarar Allah da yardarsa, wato masu niyyar hajji da umara ko niyyar kasuwanci, saboda duk wanda ya shiga garin Makka, to ya zama amintacce. Amma kuma Allah ya halatta musu su yin farauta yayin da suka sauke hiraminsu na hajji ko na umara da kuma lokacin da suka fita daga Haramin Makka ko Madina. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kada ƙiyayyar mutanen da suka cuce su suka hana su shiga garin Makka ta sa su su zalunce su ko su yi musu ta’addanci, domin shi mumini dole ne a komai ya ji tsoron Allah, kuma ya zama mai gaskiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su taimaki junansu a kan aikin alheri da taƙawa, kada su taimaki juna a kan aikata zunubi da zalunci, ya umarce su da su ji tsoron Allah ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi da barin abin da ya hana. Lalle Allah mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya saɓa masa.

  3. حُرِّمَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةُ وَٱلدَّمُ وَلَحۡمُ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦ وَٱلۡمُنۡخَنِقَةُ وَٱلۡمَوۡقُوذَةُ وَٱلۡمُتَرَدِّيَةُ وَٱلنَّطِيحَةُ وَمَآ أَكَلَ ٱلسَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيۡتُمۡ وَمَا ذُبِحَ عَلَى ٱلنُّصُبِ وَأَن تَسۡتَقۡسِمُواْ بِٱلۡأَزۡلَٰمِۚ ذَٰلِكُمۡ فِسۡقٌۗ ٱلۡيَوۡمَ يَئِسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن دِينِكُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِۚ ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗاۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ فِي مَخۡمَصَةٍ غَيۡرَ مُتَجَانِفٖ لِّإِثۡمٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 5:3

    An haramta muku (cin) mushe da jini da naman alade da abin da aka yanka shi da sunan wanin Allah, da (dabbar) da ta shaƙe, da wadda aka doke ta, da wadda ta gangaro (daga sama), da dabbar da aka tunkura da ƙaho, da kuma abin da namun daji masu farauta suka ci, sai dai abin da kuka samu damar yankawa (daga cikinsu), da kuma abin da aka yanka a kan gumaka, da kuma neman sanin sa’a da kibau. Wannan fasiƙanci ne. A yau kafirai sun ɗebe tsammani daga (karya) addininku, don haka kar ku ji tsoron su, ku ji tsoro Na Ni kaɗai. A yau Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni’imata, kuma Na yardar muku Musulunci ya zamo shi ne addininku. Duk wanda ya matsu (ya ci abin da aka ambata a baya) saboda yunwa, ba yana mai karkata zuwa ga zunubi ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A wannan ayar Allah ya bayyana dabbobin da aka haramta cin su. 1. Allah ya haramta cin naman mushen dabba. 2. Ya haramta jini mai kwarara, kamar jinin dabbar da aka yanka, ko jinin da ya zubo saboda katsewar wata jijiya a jikinta. 3. Ya haramta cin naman dabbar da aka yanka ta da sunan wani ba Allah ba. 4. Ya haramta cin naman dabbar da aka shaƙe ta ta mutu, ko ita da kanta ta sa kanta cikin wani wuri ya shaƙe ta ta mutu. 5. Ya haramta cin dabbar da aka doke ta har ta mutu. 6. Ya haramta cin dabbar da ta gangaro daga wani wuri mai tudu, ko ta gangara cikin rami ta mutu. 7. Ya haramta cin dabbar da ‘yar’uwarta ta soke ta da ƙaho ta mutu. 8. Ya haramta cin naman dabbar da wani naman daji mai farauta ya fara ci ta mutu a sanadiyyar haka. Sai dai idan waɗannan dabbobi da aka ambata aka same su ba su mutu ba aka yanka su, yanka na shari’a, to waɗannan ya halatta a ci su. 9. Hakanan an haramta cin dabbar da aka yanka wa wani gunki ko kuma duk wani abin da ake bauta wa ba Allah ba. An karɓo daga Adiyyu ɗan Hatim (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ce: “Ya Manzon Allah, ni nakan saki karnukan farauta sai su kamo mini abin farauta, to ko na iya ambaton Allah in ci?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ka saki karen farautarka, kuma ka ambaci sunan Allah, to ka ci abin da ya kamo maka.” Sai na ce: “Ko da karnukan sun kashe dabbar?” Ya ce: “E, ko da sun kashe ta, matuƙar dai wani karen da ba a cikinsu yake ba bai yi tarayya da su ba.” [Muslim #1929]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin abubuwan da ya haramta wa muminai, kamar neman sa’a da kibau. Wannan wata al’ada ce ta Larabawa a lokacin jahiliyya, wato idan mutum ya nufi aikata wani abu, sai ya ɗauko kibau guda uku, ta ɗaya an rubuta a kanta: “Aikata”, ta biyu kuma an rubuta: “Kada ka aikata”, ta uku kuma babu komai a jikinta. Sai ya karkaɗa su ya juya, idan wadda take ɗauke da rubutun ‘aikata’ ta fito, sai ya aikata abin; idan kuma mai ɗauke da ‘kada ka aikata’ ta fito, sai ya fasa aikata abin; idan kuma ta ukun ce marar rubutu a jikinta ta fito, to sai ya sake kaɗawa ya jujjuya har sai ɗaya daga cikin biyu na farko ta fito. To shi ne Allah ya haramta musu wannan mummunar al’ada, domin ta ƙunshi jingina wa wanin Allah tasirin samar da amfani ko rashinsa ga mutum, wanda yin haka kuwa shirka ne ga Allah. Allah kuma ya kira waɗannan abubuwa da ya haramta duka a matsayin fasiƙanci, wato fita daga biyayya ga Allah (Mai tsarki da daukaka) zuwa ga saɓa masa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labari a ranar Arfa ta hajjin ban-kwana da Annabi (ﷺ) ya yi da sahabbansa cewa, kafirai sun fitar da rai da ganin Musulmi za su yi ridda su bar addininsu, don haka kada mumimai su riƙa jin tsoron su, su ji tsoron Allah shi kaɗai. Sai Allah ya bayyana cewa, daga wannan rana ta Arfa, ya cika wa muminai addininsu, ya cika musu ni’imarsa, ya yarje musu Musulunci a matsayin addinin da za su kusance shi da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya dawo da batun waɗannan dabbobi da ya haramta cin su, ya bayyana cewa duk wanda ya shiga halin larura da matsuwa ta yadda sai ya ci wani abu daga cikin waɗannan dabbobi zai tsira da rayuwarsa ko lafiyarsa, to babu laifi ya ci gwargwadon abin da zai raba shi da wannan larurar, ba tare da ya yi nufin haramun ba. Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.

  4. يَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَآ أُحِلَّ لَهُمۡۖ قُلۡ أُحِلَّ لَكُمُ ٱلطَّيِّبَٰتُ وَمَا عَلَّمۡتُم مِّنَ ٱلۡجَوَارِحِ مُكَلِّبِينَ تُعَلِّمُونَهُنَّ مِمَّا عَلَّمَكُمُ ٱللَّهُۖ فَكُلُواْ مِمَّآ أَمۡسَكۡنَ عَلَيۡكُمۡ وَٱذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهِۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 5:4

    Suna tambayar ka, mene ne aka halatta musu? Ka ce: “An halatta muku kyawawan abubuwa da kuma abin da dabbobinku da kuka koyar da su (farauta) suka kamo muku, kuna koya musu abin da Allah Ya koya muku, don haka ku ci daga duk abin da suka kamo muku, sannan ku ambaci sunan Allah a kansa; kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne.

  5. ٱلۡيَوۡمَ أُحِلَّ لَكُمُ ٱلطَّيِّبَٰتُۖ وَطَعَامُ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ حِلّٞ لَّكُمۡ وَطَعَامُكُمۡ حِلّٞ لَّهُمۡۖ وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ إِذَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ مُحۡصِنِينَ غَيۡرَ مُسَٰفِحِينَ وَلَا مُتَّخِذِيٓ أَخۡدَانٖۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلۡإِيمَٰنِ فَقَدۡ حَبِطَ عَمَلُهُۥ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

    Open ayah 5:5

    A yau an halatta muku kyawawan abubuwa; kuma abincin waɗanda aka bai wa Littafi halal ne a gare ku, ku ma abincinku halal ne a gare su; sannan kuma (na halatta muku auren) mata kamammu daga cikin muminai, da kuma kamammu daga cikin waɗanda aka bai wa Littafi a gabaninku, idan har kun ba su sadakinsu, kuna masu kame kawunanku, ba kuna mazinata ba, ba kuma kuna masu yin daduro ba. Duk kuwa wanda ya kafirce wa imani, haƙiƙa aikinsa ya rushe, kuma a ranar lahira yana cikin asararru. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, sahabbansa suna yi masa tambaya game da abubuwan ci da aka halatta musu. Sannan ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa, Allah ya halatta musu cin kyawawan abubuwa, wato su ci duk abin da yake mai amfani ga ɗan’adam, kuma ba zai cutar da jikinsa ko hankalinsa ba. Hakanan ya halatta musu cin abin da dabbobinsu na farauta waɗanda suka koyar da su farauta suka kamo. Su koyar da su abin da Allah ya koya musu na ladubban farauta da ƙa’idojinta, su ci abin da waɗannan dabbobin suka kamo musu, kuma su riƙa ambaton sunan Allah yayin da za su sake su farautar. Su ji tsoron Allah ta hanyar kula da aiki da waɗannan hukunce-hukunce da aka sanar da su, su sani cewa Allah mai gaggawar hisabi ne. An karɓo daga Adiyyu ɗan Hatim (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ya Manzon Allah, nakan saki karen farautata, kuma in yi Bisimilla .” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ka saki karenka, kuma ka yi Bisimilla , sai ya kamo abin farauta ya kashe ya fara ci, to kada ka ci, domin kansa ya kamo wa.” Sai na ce: “Ya Manzon Allah, nakan saki karen farautata, to amma sai in same shi tare da wani kare, to sai in kasa ganewa cikinsu wane ne ya kama abin farautar.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Kada ka ci, domin karenka ka yi wa Bisimilla ba wani ba.” [Bukhari #5486, da Muslim #1929]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da kawo wasu alamomi na cikar addinin Musulunci, da kuma wasu ni’imominsa da sauƙin da ke tattare da wannan addini. Daga cikinsu, ya halatta wa muminai su more duk wasu kyawawan abubuwa na abinci da abin sha, kuma ya halatta musu cin yankan ma’abota littafi, wato Yahudu da Nasara, ya kuma halatta musu su auri mata ‘ya’ya, muminai, kamammu da kamammun matan Yahudawa da Nasara idan sun biya sadakinsu, su mazajen kuma suna kamammu ba mazinata ba, ba kuma masu ajiye dadiro ba suna zina da su a ɓoye. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya kafirce masa, to ladan ayyukansa masu kyau ya rushe idan har ya mutu bai tuba ba, a lahira kuma ya sami kansa cikin hasararru, waɗanda suka yi hasarar kawunansu da dukiyoyinsu da iyalansu, suka cancanci azaba ta har abada.

  6. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قُمۡتُمۡ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ فَٱغۡسِلُواْ وُجُوهَكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ إِلَى ٱلۡمَرَافِقِ وَٱمۡسَحُواْ بِرُءُوسِكُمۡ وَأَرۡجُلَكُمۡ إِلَى ٱلۡكَعۡبَيۡنِۚ وَإِن كُنتُمۡ جُنُبٗا فَٱطَّهَّرُواْۚ وَإِن كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوۡ جَآءَ أَحَدٞ مِّنكُم مِّنَ ٱلۡغَآئِطِ أَوۡ لَٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمۡ تَجِدُواْ مَآءٗ فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدٗا طَيِّبٗا فَٱمۡسَحُواْ بِوُجُوهِكُمۡ وَأَيۡدِيكُم مِّنۡهُۚ مَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيَجۡعَلَ عَلَيۡكُم مِّنۡ حَرَجٖ وَلَٰكِن يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمۡ وَلِيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

    Open ayah 5:6

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kun tashi za ku yi salla, to ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyinsu, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke) ƙafafunku zuwa idon sawu. Kuma idan kun kasance masu janaba, to sai ku tsarkaka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya, ko a halin tafiya, ko ɗaya daga cikinku ya dawo daga bayan gari, ko kuka sadu da mata, kuma sai ba ku sami ruwa ba, to ku yi taimama a doron ƙasa mai tsarki, ku shafi fuskokinku da hannayenku daga shi. Allah ba Yana nufin Ya sanya ƙunci a tare da ku ba ne, a’a, Yana nufi ne Ya tsarkake ku, kuma Ya cika ni’imarsa a gare ku, don ku zamo masu godiya. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da muminai wani babban alƙawari ne da ke tsakaninsu da shi, da yadda ya wajaba su kiyaye shi, watau al’amarin salla. Allah ya bayyana abin da yake wajaba a kan mumini ya yi yayin da ya tashi domin sauke nauyin alƙawarin salla da ke kansa, ya umarce shi da yin alwala watau ya wanke fuska da hannaye zuwa gwiwowinsu da shafar kai da wanke ƙafafuwa ko shafar su idan yana sanye da takalmin huffi. Sannan ya bayyana hukuncin wanda yake da janaba a jikinsa, shi kuma sai ya yi wankan janaba. Idan kuwa mutum yana rashin lafiyar da ba zai iya taɓa ruwa ba, ko yana cikin halin tafiya, ko ya sami ƙaramin kari, kamar bawali ko bahaya, ko kuma ya sadu da matarsa, duk waɗannan yayin da suka rasa ruwan da za su yi amfani da shi wajen yin alwala ko wanka, to sai su nemi doron ƙasa mai tsarki su yi taimama a kai, su shafi fuskokinsu da tafukan hannayensu. Allah ba ya nufin ya jefa bayinsa cikin ƙunci da takura; yana nufin tsarkake su ne da abin da ya farlanta musu na alwala da wanka da taimama, sannan yana son ya tsarkake musu baɗininsu ta hanyar kankare musu laifukansu, kuma ya cika musu ni’imarsa ta hanyar cika musu shari’o’insa da sassauta musu hukunce-hukuncensa, ko wataƙila sa yi wa Allah godiya a kan hakan da zukatansu da harsunansu da gaɓoɓinsu.

  7. وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَمِيثَٰقَهُ ٱلَّذِي وَاثَقَكُم بِهِۦٓ إِذۡ قُلۡتُمۡ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

    Open ayah 5:7

    Kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku, da alƙawarinsa wanda Ya ƙulla shi da ku, yayin da kuka ce: “Mun ji, kuma za mu yi biyayya!” Kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Masanin abin da ƙiraza suka ƙunsa ne.

  8. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُواْ قَوَّٰمِينَ لِلَّهِ شُهَدَآءَ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَلَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ عَلَىٰٓ أَلَّا تَعۡدِلُواْۚ ٱعۡدِلُواْ هُوَ أَقۡرَبُ لِلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 5:8

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku zamo masu tsayawa ƙyam da haƙƙoƙin Allah, kuna masu yin shaida da adalci; kuma kada ƙin waɗansu mutane ya hana ku yi musu adalci. Ku yi adalci shi ne mafi kusanci ga taƙawa. Kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne.

  9. وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٌ عَظِيمٞ

    Open ayah 5:9

    Allah Ya yi alƙawari ga waɗanda suka yi imani, kuma suka yi aiki nagari, suna da gafara da kuma lada mai girma.

  10. وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ 

    Open ayah 5:10

    Kuma waɗanda suka kafirta, suka kuma ƙaryata ayoyinmu, waɗannan su ne ‘yan wuta.

  11. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ هَمَّ قَوۡمٌ أَن يَبۡسُطُوٓاْ إِلَيۡكُمۡ أَيۡدِيَهُمۡ فَكَفَّ أَيۡدِيَهُمۡ عَنكُمۡۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 5:11

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku, yayin da waɗansu mutane suka yi niyyar shimfiɗa hannayensu a kanku, sai Ya kame muku hannayensu, kuma ku kiyaye dokokin Allah. To sai muminai su dogara ga Allah Shi kaɗai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tuna wa muminai ni’imar da ya yi musu da alƙawarin da ya yi da su na za su yi wa Annabi (ﷺ) mubaya’a, za su taimaka masa a kan yaɗa addinin Allah, kuma suka yarda da wannan alƙawari a wannan lokaci, suka ce: “Mun ji, kuma mun bi.” Sannan ya umarce su da jin tsoron sa, domin shi masanin abin da yake cikin zukata ne. Sai kuma ya umarci muminai da su kiyaye haƙƙoƙin Allah (Mai tsarki da daukaka), suna masu ikhlasi cikin duk ayyukansu. Hakanan su zama masu adalci lokacin da suke bayar da shaida, kada kuma ƙin wani ko wasu ya hana su yi musu adalci, a’a, su zama masu adalci koyaushe, domin yin haka shi zai wanzar musu da cikakken tsoron Allah a zukatansu. Don haka su kiyaye dokokin Allah, domin shi mai cikakken sanin abin da suke aikatawa ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya yi wa muminai masu aikata kyawawan ayyuka alƙawarin gafarar zunubansu da samun wani lada mai girma, wanda shi ne Aljanna. To amma waɗanda suka kafirce masa, kuma suka ƙaryata ayoyinsa, su ne ‘yan wuta masu dawwama a cikinta har abada. Sannan ya ƙara jan hankalin muminai su riƙa tuna ni’imomin da ya yi musu lokacin da wasu maƙiyansu suka ƙuduri aniyar auka musu, amma sai ya kare su daga sharrinsu, ya hana musu samun biyan mummunar buƙatarsu a kan muminai. Sai kuma ya rufe ayar da umarnin a ji tsoron sa ta hanyar kiyaye dokokinsa, sannan muminai su dogara da shi shi kaɗai.

  12. ۞وَلَقَدۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَبَعَثۡنَا مِنۡهُمُ ٱثۡنَيۡ عَشَرَ نَقِيبٗاۖ وَقَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مَعَكُمۡۖ لَئِنۡ أَقَمۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَيۡتُمُ ٱلزَّكَوٰةَ وَءَامَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرۡتُمُوهُمۡ وَأَقۡرَضۡتُمُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّكُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ فَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ

    Open ayah 5:12

    Kuma lalle haƙiƙa Allah Ya ɗauki alƙawari (daga) Banu-Isra’ila, kuma Mun aiko musu wakilai goma sha biyu daga cikinsu; kuma Allah Ya ce: “Lalle Ni Ina tare da ku; tabbas idan har kuka tsayar da salla, kuma kuka bayar da zakka, kuma kuka yi imani da manzannina, kuma kuka ƙarfafe su, kuma kuka bai wa Allah kyakkyawan rance, to lalle zan kankare muku kurakuranku, kuma zan shigar da ku gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. To duk wanda ya kafirce daga cikinku bayan haka, to haƙiƙa ya ɓace wa tafarki madaidaici.”

  13. فَبِمَا نَقۡضِهِم مِّيثَٰقَهُمۡ لَعَنَّٰهُمۡ وَجَعَلۡنَا قُلُوبَهُمۡ قَٰسِيَةٗۖ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ وَنَسُواْ حَظّٗا مِّمَّا ذُكِّرُواْ بِهِۦۚ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىٰ خَآئِنَةٖ مِّنۡهُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱصۡفَحۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 5:13

    Saboda yadda suke warware alƙawarin da aka yi da su, sai Muka la’ance su, kuma Muka sanya zukatansu suka zamo ƙeƙasassu; suna jirkita magana daga wurinta, kuma sun bar wani rabo na abin da aka yi musu wa’azi da shi. Kuma ba za ka gushe ba kana ganin ha’inci daga gare su, sai ‘yan kaɗan daga cikinsu. To sai ka yi musu afuwa, kuma ka kawar da kai, lalle Allah Yana son masu kyautatawa.

  14. وَمِنَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّا نَصَٰرَىٰٓ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَهُمۡ فَنَسُواْ حَظّٗا مِّمَّا ذُكِّرُواْ بِهِۦ فَأَغۡرَيۡنَا بَيۡنَهُمُ ٱلۡعَدَاوَةَ وَٱلۡبَغۡضَآءَ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَسَوۡفَ يُنَبِّئُهُمُ ٱللَّهُ بِمَا كَانُواْ يَصۡنَعُونَ

    Open ayah 5:14

    Kuma daga cikin waɗanda suka ce: “Lalle mu Nasara ne,” su ma Mun riƙi alƙawarinsu, sai suka bar wani kaso na abin da aka yi musu wa’azi da shi, sai Muka iza wutar gaba da ƙiyayya a tsakaninsu har zuwa ranar tashin alƙiyama. Kuma da sannu Allah zai ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, ya ɗauki wani alƙawari mai ƙarfi tare da Yahudawan da suka gabata. Kuma ya naɗa musu shugabanni goma sha biyu daidai adadin gidajen Banu Isra’ila, kuma ya umarci kowane shugaba da cewa, mutanen da suke ƙarƙashinsa su yi masa mubaya’a a kan cewa, za su saurari duk abin da aka faɗa musu, kuma za su yi biyayya tare da cika alƙawarin da suka ɗauka, shi kuma ya sa musu ido a kan haka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya faɗa wa Banu Isra’ila cewa yana tare da su da taimakonsa da nasararsa, matuƙar za su cika alƙawarin da suka yi da shi, ta hanyar tsayar da salla kamar yadda ya kamata, kuma su ba da zakkar dukiyoyinsu ga waɗanda suka cancanta a ba, kuma su yi imani da manzannin Allah da taimaka musu a kan maƙiyansu, da ciyar da dukiyoyinsu don neman yardar Allah. Idan sun yi duk waɗannan abubuwa da aka ambata, to Allah zai yafe musu zunubbansu, kuma zai shigar da su gidajen Aljanna, waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. To amma kuma duk wanda ya kafirce, ya karya alƙawarin da ya ɗauka, to haƙiƙa ya ɓace wa hanya madaidaiciya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kuma bayyana cewa, a dalilin rashin cika alƙawarinsu ne ya la’ance su, ya sanya zukatansu suka ƙeƙashe har wa’azi ba ya yi musu tasiri, alheri ba ya ratsa su, suka riƙa canza maganar Allah a Attaura, kuma suka yi watsi da mafi yawan abin da aka yi musu wahayin sa na faɗakarwa da tunatarwa da gangan. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, ba zai gushe ba yana bankaɗo makirce-makircen Yahudawa da cin amanarsu da yaudararsu, sai ‘yan kaɗan daga cikinsu ne za a same su suna cika alƙawari idan sun ɗauka. Sannan Allah ya umarce shi da ya yi musu afuwar laifukansu, kuma ya kawar musu da kai, Allah yana son masu kyautatawa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ɗauki alƙawari mai ƙarfi da mutanen da suka cika bakin cewa, wai su Nasara ne, ya umarce su da cewa, su yi wa Allah da manzanninsa biyayya, amma kuma sai suka yi watsi da abin da ake yi musu wa’azi da shi na wahayin Allah da gangan, sai Allah ya yi musu uƙuba ta hanyar sanya ƙiyayya da saɓani a tsakaninsu, suna faɗa da juna, suna kafirta juna, suna la’antar juna har zuwa ranar tashin ƙiyama. Kuma Allah zai ba su labarin duk abin da suka aikata a nan duniya, kuma zai yi musu azaba a kai.

  15. يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ قَدۡ جَآءَكُمۡ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمۡ كَثِيرٗا مِّمَّا كُنتُمۡ تُخۡفُونَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَيَعۡفُواْ عَن كَثِيرٖۚ قَدۡ جَآءَكُم مِّنَ ٱللَّهِ نُورٞ وَكِتَٰبٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 5:15

    Ya ku waɗanda aka bai wa Littafi, haƙiƙa Manzonmu ya zo muku, yana bayyana muku da yawa daga cikin abin da kuke ɓoyewa daga Littafin, yana kuma yin afuwa ga abubuwa da dama daga ciki. Haƙiƙa haske ya zo muku daga Allah, da kuma Littafi mai bayyanawa.

  16. يَهۡدِي بِهِ ٱللَّهُ مَنِ ٱتَّبَعَ رِضۡوَٰنَهُۥ سُبُلَ ٱلسَّلَٰمِ وَيُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِهِۦ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

    Open ayah 5:16

    Da shi ne Allah Yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyi na aminci, kuma Yake fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininsa, kuma Yana shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Yahudawa da Nasara cewa, ya aiko musu da Manzonsa Muhammadu (ﷺ) wanda da man sun riga sun karanci siffofinsa a cikin littattafansu, zai zo ya riƙa bayyana wasu hukunce-hukunce masu yawa da suke ɓoye wa mutane, kamar hukuncin jefe mazinacin da ya taɓa yin aure, da kuma canza maganar Allah, kuma zai bar wasu abubuwan waɗanda babu wani amfani don ya bayyana su. Sannan ya tunatar da su cewa wani Littafi babba daga Allah ya zo musu, watau Alƙur’ani mai girma, wanda yake haske ne da yake haskaka duffai na jahilci da ɓata, yana yi wa mutane bayanin duk abin da suke buƙata su sani na hukunce-hukuncen addininsu da rayuwarsu. Da shi ne yake nuna hanya ga duk wanda yake son isa ga yardar Allah (Mai tsarki da daukaka), sai ya datar da su wajen bin hanyar tsira a duniya da lahira da samun shiga Aljanna gidan aminci. Kuma da shi yake fitar da su daga duffai na ɓata da kafirci da saɓon Allah, zuwa ga hasken imani da biyayya ga Allah da Manzonsa da izinin Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma ya shiryar da su zuwa ga daidaitacciyar hanya wadda ita ce Musulunci.

  17. لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ أَن يُهۡلِكَ ٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗاۗ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 5:17

    Lalle haƙiƙa, waɗannan da suka ce: “Lalle Allah Shi ne Almasihu ɗan Maryamu” sun kafirta. Ka ce: “To wane ne ya isa ya hana Allah, idan Ya yi nufin Ya hallaka Almasihu ɗan Maryamu da mahaifiyarsa da duk wanda yake ban ƙasa gaba ɗaya? Allah kuwa Shi Yake mallakar abin da yake cikin sammai da ƙasa da kuma abin da yake tsakaninsu. Yana halittar abin da Ya ga dama. Kuma Allah Mai cikakken iko ne a kan komai.”

  18. وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ وَٱلنَّصَٰرَىٰ نَحۡنُ أَبۡنَٰٓؤُاْ ٱللَّهِ وَأَحِبَّٰٓؤُهُۥۚ قُلۡ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُمۖ بَلۡ أَنتُم بَشَرٞ مِّمَّنۡ خَلَقَۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 5:18

    Kuma Yahudawa da Nasara suka ce: “Mu ‘ya’yan Allah ne, kuma masoyansa.” Ka ce: “To don me Yake muku azaba a sanadiyyar zunubanku? Ba haka ne ba, ku mutane ne daga cikin waɗanda Ya halitta. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, kuma Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma mulkin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ne makoma take.”

  19. يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ قَدۡ جَآءَكُمۡ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمۡ عَلَىٰ فَتۡرَةٖ مِّنَ ٱلرُّسُلِ أَن تَقُولُواْ مَا جَآءَنَا مِنۢ بَشِيرٖ وَلَا نَذِيرٖۖ فَقَدۡ جَآءَكُم بَشِيرٞ وَنَذِيرٞۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 5:19

    Ya ku waɗanda aka bai wa Littafi, haƙiƙa Manzonmu ya zo muku, yana yi muku bayani bayan yankewar manzanci, don kar ku ce: “Ba wani mai bushara da ya zo mana, ko wani mai gargaɗi.” To haƙiƙa mai busharar, kuma mai gargaɗin, ya zo muku. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana rantsuwa a kan cewa Nasara masu cewa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) Allah ne sun kafirta. Kuma ya umarci Annabinsa (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, idan ma Allah ya nufi halakar da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mahaifiyarsa da mutanen duniya gaba ɗaya, wane ne ya isa ya hana shi? Babu wanda zai iya hana Allah ya zartar da duk abin da ya ga dama domin gaba ɗayansu suna ƙarƙashin ikonsa da mulkinsa. Wannan shi ya tabbatar da cewa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mahaifiyarsa ba alloli ne ba, su ma kamar kowa suke, halittu ne na Allah (Mai tsarki da daukaka). Kuma mulkin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu duk na Allah ne, kuma shi mai iko ne a kan komai, babu abin da yake gagarar sa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata katoɓara ta Yahudawa da Nasara ta cewa wai su ‘ya’yan Allah ne kuma su kaɗai ne masoyansa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa (ﷺ) da ya ƙalubalance su da cewa, idan har maganar da suke faɗa gaskiya ce, to me ya sa Allah yake azabtar da su a kan laifukansu? Maganar dai ba haka take ba, su dai mutane ne kamar kowa, halittar su Allah ya yi kamar yadda ya halicci kowa da komai; yana kuma gafarta wa wanda ya ga dama, ya azabtar da wanda ya ga dama, don haka su ma irin wannan mu’amalar yake yi musu. Mulkin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu kuma duk nasa ne, kuma makoma gaba ɗaya zuwa gare shi ne. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Yahudawa da Nasara cewa ya aiko musu da Manzonsa (ﷺ), yana nuna musu miƙaƙƙiyar hanya da addinin gaskiya a lokacin da ake cikin matsananciyar buƙatar zuwansa saboda yankewar manzanni tun bayan Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya aiko shi don ya yanke hanzarin kowa a gaban Allah, don kada su zo suna cewa, su fa babu wani manzo mai albishir ko mai gargaɗi da ya zo musu. To ga shi dai mai albishir kuma mai gargaɗi ya zo musu, wanda shi ne Annabi Muhammadu (ﷺ). Kuma Allah mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi, don haka halittar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya yi ba uba sai uwa, idan ya ga dama zai iya halaka shi tare da mahaifiyarsa da mutanen duniya gaba ɗaya, ba wanda ya isa ya hana shi.

  20. وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ جَعَلَ فِيكُمۡ أَنۢبِيَآءَ وَجَعَلَكُم مُّلُوكٗا وَءَاتَىٰكُم مَّا لَمۡ يُؤۡتِ أَحَدٗا مِّنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ 

    Open ayah 5:20

    Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce wa mutanensa: “Ya ku mutanena, ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku, yayin da Ya sanya annabawa da yawa a cikinku, kuma Ya sanya ku sarakuna, kuma Ya ba ku irin abin da bai ba wa wani cikin talikai ba.

  21. يَٰقَوۡمِ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡأَرۡضَ ٱلۡمُقَدَّسَةَ ٱلَّتِي كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمۡ وَلَا تَرۡتَدُّواْ عَلَىٰٓ أَدۡبَارِكُمۡ فَتَنقَلِبُواْ خَٰسِرِينَ

    Open ayah 5:21

    “Ya ku mutanena, ku shiga ƙasar nan mai tsarki, wadda Allah Ya wajabta muku (shigarta), kuma kada ku yarda ku juya baya, sai ku komo kuna hasararru.”

  22. قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّ فِيهَا قَوۡمٗا جَبَّارِينَ وَإِنَّا لَن نَّدۡخُلَهَا حَتَّىٰ يَخۡرُجُواْ مِنۡهَا فَإِن يَخۡرُجُواْ مِنۡهَا فَإِنَّا دَٰخِلُونَ

    Open ayah 5:22

    Suka ce, “Ya kai Musa, lalle a cikinta akwai waɗansu mutane masu tsananin ƙarfi, kuma mu ba za mu shige ta ba har sai sun fita daga cikinta, don haka idan suka fita daga cikinta, to lalle za mu shiga.”

  23. قَالَ رَجُلَانِ مِنَ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمَا ٱدۡخُلُواْ عَلَيۡهِمُ ٱلۡبَابَ فَإِذَا دَخَلۡتُمُوهُ فَإِنَّكُمۡ غَٰلِبُونَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَتَوَكَّلُوٓاْ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

    Open ayah 5:23

    Waɗansu mutane biyu daga cikin masu jin tsoron (Allah), waɗanda Allah Ya yi musu ni’ima (ta imani), suka ce: “Ku shigar musu ta ƙofar (garin); idan har kun shige shi, to lalle ku masu cin nasara ne. Kuma ga Allah kaɗai za ku dogara, idan kun kasance ku muminai ne.”

  24. قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّا لَن نَّدۡخُلَهَآ أَبَدٗا مَّا دَامُواْ فِيهَا فَٱذۡهَبۡ أَنتَ وَرَبُّكَ فَقَٰتِلَآ إِنَّا هَٰهُنَا قَٰعِدُونَ

    Open ayah 5:24

    Suka ce; “Ya kai Musa, lalle mu fa ba za mu taɓa shigar ta ba har abada, matuƙar suna cikinta; sai ka je kai da Ubangijinka ku yi yaƙin, lalle mu kam muna nan a zaune.”

  25. قَالَ رَبِّ إِنِّي لَآ أَمۡلِكُ إِلَّا نَفۡسِي وَأَخِيۖ فَٱفۡرُقۡ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡفَٰسِقِينَ

    Open ayah 5:25

    Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni ban mallaki kowa ba sai kaina da ɗan’uwana; don haka Ka yi hukunci tsakaninmu da mutanen da suke fasiƙai.”

  26. قَالَ فَإِنَّهَا مُحَرَّمَةٌ عَلَيۡهِمۡۛ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗۛ يَتِيهُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ فَلَا تَأۡسَ عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡفَٰسِقِينَ

    Open ayah 5:26

    Ya ce: “To lalle an haramta musu (shigarta) har tsawon shekara arba’in. Za su yi ta ɗimuwa a bayan ƙasa. Don haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutanen da suke fasiƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi (ﷺ) mugun halin Yahudawa na taurin kai da rashin bin umarnin annabawansa, don ya fahimci ba shi kaɗai ne suka yi wa taurin kai da bijire wa gaskiya bayan sun fahimce ta ba; sun yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) irin wannan bayan ni’imomi masu yawa da Allah ya yi musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Annabinsa (ﷺ) sa’adda Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake yi wa mutanensa Banu Isra’ila nasiha da cewa, su riƙa tuna ni’imar da Allah ya yi musu ta aiko musu da annabawa daga cikinsu, kuma ya sanya su sarakuna, ya ba su ni’imomi masu yawa na addini da na duniya waɗanda bai taɓa ba wata al’umma irinsu ba. Sannan bayan wannan tunatarwa da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mutanensa sai kuma ya umarce su da lalle su shiga ƙasar Baitul Maƙadis da shirin yaƙi, su ƙwato ta daga hannun maƙiyansu, kada kuma su ja da baya a kan hakan, domin yin haka zai jefa su cikin hasararru duniya da lahira. To amma sai suka mayar masa da amsa cewa, su fa ba za su iya shiga wannan ƙasar ba, saboda a cikinta akwai wasu mutane masu ƙarfin gaske masu girman jiki waɗanda ba za su iya tunkarar su da yaƙi ba, don haka ba za su shiga wannan gari ba matuƙar waɗannan mutane suna ciki; amma idan sun fita da kansu sannan ne za su shiga. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa cikin Banu Isra’ila a lokacin akwai wasu mutane su biyu masu tsoron Allah, masu biyayya a gare shi da haƙuri da hangen nesa, sai suka nuna wa ‘yan’uwansu Banu Isra’ila cewa, bai dace su noƙe su ƙi shiga Baitul Maƙadis don yaƙar waɗannan mutanen ba; abin da ya wajaba shi ne su bi umarni su shiga wannan garin ta ƙofar da ake shigarsa; idan har sun yi haka to za su yi nasara; su dogara ga Allah shi kaɗai, idan har su da gaske muminai ne. To amma abin takaici nasihar waɗannan mutanen ba ta shiga kunnuwan Banu Isra’ila ba, sai suka maimaita wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) maganarsu ta farko cewa, matuƙar dai waɗannan mutanen suna cikin garin, to fa su har abada ba za su shiga ba, sai dai shi Annabi Musa, idan har abin ya dame shi, to ya je shi da Ubangijinsa su yaƙi waɗannan ƙarfafan mutane, sannan su dawo su same su zaune suna jiran su, daga nan sai su shiga garin gaba ɗaya. Da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga tura ta kai bango, ya gane cewa ba zai iya tilasta wa kowa shiga wannan gari ba sai ɗan’uwansa Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kaɗai; su biyu kacal kuma ba za su iya tunkarar yaƙi ba, sai ya roƙi Allah ya yi hukunci tsakaninsa da mutanensa fasiƙai. Sai ko Allah ya karɓi addu’arsa, ya azabtar da su ta hanyar haramta musu shiga ƙasar, har tsawon shekaru arba’in suna cikin ɗimuwa da ragaita a cikin sahara, suna neman hanyar shiga wannan ƙasa amma sun kasa gano ta, sun kuma kasa zama wuri guda. Allah kuma ya hana Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nuna baƙin cikinsa game da wannan uƙubar da aka yi wa mutanensa, domin su ne suka jawo wa kansu, saboda sun ƙi bin umarnin Allah (Mai tsarki da daukaka).

  27. ۞وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱبۡنَيۡ ءَادَمَ بِٱلۡحَقِّ إِذۡ قَرَّبَا قُرۡبَانٗا فَتُقُبِّلَ مِنۡ أَحَدِهِمَا وَلَمۡ يُتَقَبَّلۡ مِنَ ٱلۡأٓخَرِ قَالَ لَأَقۡتُلَنَّكَۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 5:27

    Kuma ka karanta musu labarin gaskiya na ‘ya’yan Adamu su biyu, yayin da suka gabatar da wani abin neman lada, sai aka karɓi na ɗaya daga cikinsu, ɗayan kuma ba a karɓi nasa ba, sai ya ce: “Wallahi, sai na kashe ka!” Sai ya ce: “Allah Yana karɓar aiki ne kawai daga masu taƙawa.

  28. لَئِنۢ بَسَطتَ إِلَيَّ يَدَكَ لِتَقۡتُلَنِي مَآ أَنَا۠ بِبَاسِطٖ يَدِيَ إِلَيۡكَ لِأَقۡتُلَكَۖ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 5:28

    “Wallahi, idan har ka miƙa hannunka gare ni domin ka kashe ni, ni kam ba zan miƙa hannuna gare ka don in kashe ka ba; lalle ni ina jin tsoron Allah Ubangijin talikai.

  29. إِنِّيٓ أُرِيدُ أَن تَبُوٓأَ بِإِثۡمِي وَإِثۡمِكَ فَتَكُونَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِۚ وَذَٰلِكَ جَزَٰٓؤُاْ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 5:29

    “Lalle ni ina son ka ɗauki zunubina da zunubinka, sai ka kasance daga cikin ‘yan wuta. Kuma wannan shi ne sakamakon azzalumai.”

  30. فَطَوَّعَتۡ لَهُۥ نَفۡسُهُۥ قَتۡلَ أَخِيهِ فَقَتَلَهُۥ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ 

    Open ayah 5:30

    Sai zuciyarsa ta ƙawata masa ya kashe ɗan’uwansa, sai ya kashe shi, sai ya zama cikin hasararru.

  31. فَبَعَثَ ٱللَّهُ غُرَابٗا يَبۡحَثُ فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيُرِيَهُۥ كَيۡفَ يُوَٰرِي سَوۡءَةَ أَخِيهِۚ قَالَ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ أَعَجَزۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِثۡلَ هَٰذَا ٱلۡغُرَابِ فَأُوَٰرِيَ سَوۡءَةَ أَخِيۖ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلنَّٰدِمِينَ

    Open ayah 5:31

    Sai Allah Ya aiko da wani hankaka ya riƙa tona ƙasa don ya nuna masa yadda zai binne gawar ɗan’uwansa. Sai ya ce: “Kaicona! Yanzu na kasa zama kamar wannan hankakan, in je in binne gawar ɗan’uwana?” Sai ya wayi gari cikin masu nadama.

  32. مِنۡ أَجۡلِ ذَٰلِكَ كَتَبۡنَا عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ أَنَّهُۥ مَن قَتَلَ نَفۡسَۢا بِغَيۡرِ نَفۡسٍ أَوۡ فَسَادٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ ٱلنَّاسَ جَمِيعٗا وَمَنۡ أَحۡيَاهَا فَكَأَنَّمَآ أَحۡيَا ٱلنَّاسَ جَمِيعٗاۚ وَلَقَدۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡأَرۡضِ لَمُسۡرِفُونَ

    Open ayah 5:32

    Saboda wannan ne muka wajabta wa Banu-Isra’ila cewa, duk wanda ya kashe wani rai ba tare da (laifin kisan) kai ba, ko kuma wata ɓarna a bayan ƙasa, to kamar ya kashe mutane ne gaba ɗaya, wanda kuwa ya raya shi, to kamar ya raya mutane ne gaba ɗaya. Kuma lalle haƙiƙa manzanninmu sun zo musu da (hujjoji) mabayyana, amma sai ga shi da yawa daga cikinsu bayan hakan, lalle masu ɓarna ne a bayan ƙasa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabinsa (ﷺ) da ya ba wa Yahudawa da sauran mutane labarin ‘ya’yan Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) su biya labari na gaskiya wanda babu ƙari a cikinsa. Lokacin da kowane ɗaya daga cikinsu ya gabatar wa da Allah abin kusanta gare shi, sai Allah ya karɓi na ɗayan bai karɓi na ɗayan ba, sai hassada ta lulluɓe shi har ya rantse sai ya kashe ɗan’uwansa. Sai shi kuma ɗan’uwan nasa ya amsa da cewa: “Allah yana karɓar aikin masu taƙawa ne kawai. Kuma idan har kai za ka ɗaga hannunka da niyyar ka kashe ni, to ni ba zan ɗaga hannuna a kanka da niyyar na kashe ka ba, saboda ni ina jin tsoron Allah. Kuma ni manufata ita ce idan ka kashe ni ka ɗauki alhakin kashe ni tare da alhakin laifukanka na baya, wannan ya sanya sanadiyyar zamantowarka ɗan wuta, kuma wannan ita ce uƙubar duk wani azzalumi.” To amma daga ƙarshe sai zuciyarsa ta nuna masa ya kashe ɗan’uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sai ya wayi gari a cikin waɗanda suka yi hasara duniya da lahira. Bayan ya gama mugun aikinsa na kashe ɗan’uwansa, sai kuma ya daburce, ya rasa yadda zai yi da gawar ɗan’uwansa. A daidai lokacin ne sai Allah ya aiko wani hankaka ya riƙa tona ƙasa da ƙafafuwansa yana rami, shi kuma wannan mai laifi yana kallon sa, ta haka sai ya fahimci hanyar da zai binne gawar ɗan’uwansa a ƙabari. Daga nan sai ya riƙa zargin kansa, yana cewa: “Yaya aka yi na kasa yin rami tun da farko kamar yadda wannan hankakan ya yi, ni ma in binne gawar ɗan’uwana?” Sai ya wayi gari yana mai nadamar kashe ɗan’uwansa da kuma yadda da farko ya kasa gane yadda zai yi da gawarsa. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, saboda wannan laifi da ɗan’adam na farko ya yi na kashe ɗan’uwansa bisa zalunci, Allah ya hukunta wa Banu Isra’ila cewa, duk wanda ya kashe wani rai ba bisa wani haƙƙi ba, na ramuwa ko na aikin ɓarna a bayan ƙasa, to kamar ya kashe mutane ne gaba ɗaya. Wanda kuma ya raya rai ɗaya, to kamar ya raya rayukan mutane ne gaba ɗaya. Sannan Allah ya bayyana cewa, manzannin Allah sun kawo wa Banu Isra’ila hujjoji bayyanannu, sai ya zamana da dama daga cikinsu sun bijire suna aikata laifuka, suna keta iyakokin Ubangiji. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Ba wani rai da za a sake kashewa bisa zalunci, face ɗan’adam na farko (da ya yi kisa) yana da wani kamasho a cikin jinin da aka zubar, domin shi ne mutum na farko da ya sunnanta laifin kisa.” [Bukhari #3335, da Muslim #1677].

  33. إِنَّمَا جَزَٰٓؤُاْ ٱلَّذِينَ يُحَارِبُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوٓاْ أَوۡ يُصَلَّبُوٓاْ أَوۡ تُقَطَّعَ أَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم مِّنۡ خِلَٰفٍ أَوۡ يُنفَوۡاْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِۚ ذَٰلِكَ لَهُمۡ خِزۡيٞ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ

    Open ayah 5:33

    Lalle sakamakon waɗanda suke yaƙar Allah da Manzonsa, kuma suke ɓarna a bayan ƙasa, shi ne kawai a karkashe su ko kuma a giggicciye su ko kuma a yayyanke hannayensu da ƙafafuwansu a tarnaƙe ko kuma a kore su daga ƙasa. Wannan ƙasƙanci ne a gare su a nan duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma.

  34. إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِن قَبۡلِ أَن تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهِمۡۖ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 5:34

    Sai dai waɗanda suka tuba tun kafin ku sami damar kama su; to ku sani cewa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin sakamakon waɗanda suke yin fito-na-fito da Allah da Manzonsa, suna yaƙar addininsa, suna yaɗa ɓarna a bayan ƙasa, suna hana wa al’umma sakat, ta hanyar fashi da makami da ta’addanci da ƙwace wa mutane dukiyoyinsu da ƙarfi da sauran manyan laifuka. Allah ya bayyana hukuncinsu da cewa kisa ne ko a gicciye su, wato a ɗaure su a jikin wani miƙaƙƙen itace bayan an kashe su, ko kafin a kashe su, a shanya su kowa ya gama da ganin su. Ko a yanke musu hannayensu na dama da ƙafafuwansu na hagu, ko kuma a kore su daga ƙasar. An tanadar musu wannan hukunci ne don a kunyata su a nan duniya, a lahira kuma su gamu da azaba mai girma, ita ce wutar Jahannama. To amma waɗanda suka tuba suka bar yaƙar addinin Allah da yaɗa ɓarna a bayan ƙasa, suka kawo kawunansu kafin a kai ga kama su, suka yi nadama a kan abin da suka aikata a baya, to Allah ya tabbatar wa muminai cewa shi mai gafara ne, zai gafarta musu duniya da lahira, kuma mai jin ƙai ne, zai yi musu afuwa, ba zai azabtar da su ba.

  35. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱبۡتَغُوٓاْ إِلَيۡهِ ٱلۡوَسِيلَةَ وَجَٰهِدُواْ فِي سَبِيلِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

    Open ayah 5:35

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku nemi abin da zai sada ku da shi, kuma ku yi jihadi wajen yaɗa kalmarsa, don ku rabauta.

  36. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لِيَفۡتَدُواْ بِهِۦ مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَا تُقُبِّلَ مِنۡهُمۡۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 5:36

    Lalle waɗanda suka kafirta, in da a ce duk abin da yake ban ƙasa gaba ɗaya nasu ne, haɗe kuma da wani kamarsa, domin su fanshi kansu da shi daga azabar ranar tashin alƙiyama, da ba za a karɓa daga gare su ba; kuma suna da azaba mai raɗaɗi.

  37. يُرِيدُونَ أَن يَخۡرُجُواْ مِنَ ٱلنَّارِ وَمَا هُم بِخَٰرِجِينَ مِنۡهَاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّقِيمٞ

    Open ayah 5:37

    Suna nufin su fita daga cikin wuta, alhalin su ba masu fita ne daga cikinta ba; kuma suna da wata azaba madawwamiya. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai ne da su kiyaye dokokinsa, su nemi hanyoyin samun kusanci zuwa gare shi, kuma su yi jihadi don ɗaukaka kalmar Allah domin su sami rabauta duniya da lahira, kuma su kuɓuta daga azabar Allah, su sami abin da suke fatan samu na ni’ima ta har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, da a ce kafirai sun mallaki duk abin da yake cikin ƙasa, haɗe da wani kwatankwacinsa tare da shi, kuma suka so su bayar da shi domin su fanshi kansu da shi daga azabar Allah, to Allah ba zai karɓi wannan fansar ba, kuma an tanadar musu wata azaba mai raɗaɗi . An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ranar gobe ƙiyama za a kawo kafiri a ce masa: “Shin kana ganin idan abin a ce kana da zinari wanda yawansa ya cika ƙasa, za ka fanshi kanka da shi?” Sai ya ce: “E!” Sai a ce masa: “A baya can ai an buƙaci ka ba da abin da bai kai wannan ba (amma ka ƙi).” [Bukhari #6538, da Muslim #2805]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, kafirai za su so su fito daga cikin wuta bayan sun ɗanɗana matsananciyar azabarta, to amma ba za a fito da su daga cikinta ba har abada; za a ci gaba da gana musu azaba mai raɗaɗi.

  38. وَٱلسَّارِقُ وَٱلسَّارِقَةُ فَٱقۡطَعُوٓاْ أَيۡدِيَهُمَا جَزَآءَۢ بِمَا كَسَبَا نَكَٰلٗا مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

    Open ayah 5:38

    Kuma ɓarawo da ɓarauniya, sai ku yanke hannayensu, wannan sakamako ne na abin da suka aikata, uƙuba ce daga Allah. Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.

  39. فَمَن تَابَ مِنۢ بَعۡدِ ظُلۡمِهِۦ وَأَصۡلَحَ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَتُوبُ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

    Open ayah 5:39

    To (amma) wanda ya tuba bayan zaluncinsa, kuma ya gyara aikinsa, to lalle Allah zai karɓi tubansa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

  40. أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ 

    Open ayah 5:40

    Shin ba ka da masaniyar cewa, lalle Allah Shi ne Yake mallakar abin da yake cikin sammai da kuma ƙasa, Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama, kuma Yana gafarta wa wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai? A nan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zo da hukuncin ɓarawo, namiji ne ko mace, wato a yanke hannunsa na dama daga kan tsintsiyar hannu, sakamakon satar dukiyar da ba tasa ba, don wannan ya zama gargadi a gare shi, kuma ya zama darasi ga wani mai son aikata irin laifinsa. Kuma Allah Gagara badau ne, babu abin da ya fi ƙarfinsa, kuma Gwani ne mai hikima cikin duk hukunce-hukuncensa. To amma wanda ya tuba ya bar sata, ya daina zaluntar kansa da waninsa, ya koma ga Allah ya gyara halinsa, to wannan Allah zai karɓi tubansa. Lalle Allah mai gafara ne, mai jin ƙai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci buwayarsa da girman mulkinsa da zartuwar hukuncinsa, da cewa, shi ne fa mamallakin sammai da ƙasa, yana azabtar da wanda ya ga dama da adalcinsa, kuma ya yi gafara ga wanda ya ga dama da falalarsa; duk bayi kuma mulkinsa ne, kuma a hannunsa al’amuransu suke, kuma shi mai iko ne a kan komai; babu abin da zai gagare shi ko ya fi ƙarfinsa?

  41. ۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ لَا يَحۡزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡكُفۡرِ مِنَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَلَمۡ تُؤۡمِن قُلُوبُهُمۡۛ وَمِنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْۛ سَمَّٰعُونَ لِلۡكَذِبِ سَمَّٰعُونَ لِقَوۡمٍ ءَاخَرِينَ لَمۡ يَأۡتُوكَۖ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ مِنۢ بَعۡدِ مَوَاضِعِهِۦۖ يَقُولُونَ إِنۡ أُوتِيتُمۡ هَٰذَا فَخُذُوهُ وَإِن لَّمۡ تُؤۡتَوۡهُ فَٱحۡذَرُواْۚ وَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ فِتۡنَتَهُۥ فَلَن تَمۡلِكَ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۚ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَمۡ يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يُطَهِّرَ قُلُوبَهُمۡۚ لَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٞ

    Open ayah 5:41

    Ya kai wannan Manzo, kar waɗannan da suke gaggawa cikin kafirci su baƙanta maka rai, daga cikin waɗanda suka ce: “Mun yi imani” da bakunansu, amma zukatansu ba su yi imani ba; da kuma waɗanda suke Yahudawa, masu yawan sauraron ƙarya, masu yawan sauraron waɗansu mutanen da ba su zo wajenka ba; suna caccanja kalmomi daga wurarensu, suna cewa: “Idan an ba ku wannan, to ku karɓe shi, idan kuwa ba shi aka ba ku ba, to ku yi hattara.” Duk kuwa wanda Allah Ya nufi fitinar sa, to ba abin da za ka iya mallaka masa daga wurin Allah. Waɗannan su ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukatansu ba. A nan duniya suna da ƙasƙanci, a lahira kuma suna da azaba mai girma.

  42. سَمَّٰعُونَ لِلۡكَذِبِ أَكَّٰلُونَ لِلسُّحۡتِۚ فَإِن جَآءُوكَ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُمۡ أَوۡ أَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡۖ وَإِن تُعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ فَلَن يَضُرُّوكَ شَيۡـٔٗاۖ وَإِنۡ حَكَمۡتَ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُقۡسِطِينَ

    Open ayah 5:42

    (Su ne) masu yawan sauraron ƙarya, masu yawan cin haram. Don haka idan sun zo maka, to ka yi musu hukunci, ko ka kau da kai daga gare su; idan kuwa ka kawar da kai daga gare su, to ba za su cutar da kai da komai ba; idan kuwa za ka yi hukuncin, to ka yi hukunci tsakaninsu da adalci. Lalle Allah Yana son masu adalci.

  43. وَكَيۡفَ يُحَكِّمُونَكَ وَعِندَهُمُ ٱلتَّوۡرَىٰةُ فِيهَا حُكۡمُ ٱللَّهِ ثُمَّ يَتَوَلَّوۡنَ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۚ وَمَآ أُوْلَٰٓئِكَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 5:43

    Kuma ta yaya za su kawo maka hukunci, alhalin Attaura tana wurinsu, a cikinta akwai hukuncin Allah, sannan su juya baya bayan haka? Waɗannan kam ba muminai ba ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana rarrashin Annabinsa (ﷺ) ne da cewa, kada Yahudawa masu gaggawar shiga cikin kafirci su baƙanta masa rai, da kuma munafuƙai masu bayyana imaninsu a fatar baki kawai, amma bai shiga zukatansu ba, da Yahudawan da suke kasa kunnuwa su saurari ƙarairayin da malamansu da shugabanninsu suke faɗa musu ko da yaushe, suna kuma bin umarnin wasu malamansu da shugabanninsu waɗanda suka bijire wa Annabi (ﷺ) ba sa halartar majalisarsa. To waɗannan su ne masu canza maganar Allah (Mai tsarki da daukaka) su kawo wata wadda ta yi daidai da son ransu da gangan, alhalin sun san gaskiya. Suna faɗa wa mabiyansu cewa: “Ku je ku kai ƙara wajen Muhammadu, idan ya yi muku hukuncin da ya yi daidai da son ranku, to ku yarda, idan kuwa ya yi muku hukuncin da ya saɓa da son ranku, to kada ku yarda.” Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gaya wa Annabinsa cewa, wanda duk ya nufi ya fitine shi, to bai mallaki wani abu daga Allah ba, wanda zai kuɓutar da shi daga ɓata. Amma su Yahudawan da ba sa karɓar wata gaskiya sai wadda ta dace da son zukatansu, to waɗannan Allah bai nufi tsarkake zukatansu daga ƙazantar shirka da kafirci ba, kuma suna tare da wulaƙanci da ƙasƙanci a nan duniya, a lahira kuwa za su gamu da azaba mai tsanani ta wutar Jahannama. Waɗannan Yahudawa da ma sun saba da sauraron ƙarairayi da yawan cin dukiyar haram, kamar ta rashawa da riba da sauransu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabinsa (ﷺ) zaɓin cewa, idan waɗannan mutane sun kawo masa hukunci, to yana kuma da damar ya yi musu hukunci, yana da damar ya rabu da su ya ƙyale su, domin ko da ya ƙyale su, wannan ba zai cutar da shi da komai ba. Idan kuma ya zaɓi zai yi musu hukunci, to ya yi musu hukunci na adalci. Allah yana son mutane masu adalci. An karɓo daga Al-Bara’u ɗan Azib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An wuce ta gaban Annabi (ﷺ) da wani Bayahude, wanda aka shafe fuskarsa da baƙin gawayi, aka yi masa bulala, sai Annabi (ﷺ) ya kirawo su ya ce musu: “Haka kuka sami bayanin haddin mazinaci a littafinku?” Sai suka ce: “E!” Sai Annabi (ﷺ) ya kirawo ɗaya daga cikin malamansu, ya ce masa: “Na haɗa ka da Allah, haka kuka sami bayanin haddin mazinaci a cikin littafinku?” Sai ya ce: “A’a. Ba don ka haɗa ni da Allah ba, da ba zan faɗa maka ba. Hukuncin da yake cikin littafinmu shi ne jefewa, sai dai da yake zinace-zinace sun yi yawa a cikin manyan mutanenmu, sai ya zamana duk sa’adda muka kama babban mutum da laifin zina, sai mu ƙyale shi ba tare da mun hukunta shi ba, to amma idan muka kama talaka, sai mu tsayar masa da haddi. Sai kuma daga baya muka haɗu muka zartar da hukunci guda ɗaya, wanda zai shafi babban mutum da talaka. Sai muka musanya hukuncin jefewa da shafe fuska da baƙin gawayi da bulala.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ya Allah, ni ne farkon wanda ya raya wannan hukunci naka bayan sun kashe shi.” Sai ya ba da umarni aka jefe wannan Bayahude. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Ya kai wannan Manzo, kada waɗanda suke gaggawa cikin kafirci su baƙanta maka rai....” har zuwa faɗarsa: “….in an ba ku wannan, to ku karɓa.” Yana cewa: “Ku je ga Muhammadu (ﷺ), idan ya umarce ku da ku sanya ma mazinaci baƙin gawayi a fuska, ku yi masa bulala, to ku yarda da wannan hukunci, idan kuwa ya ba ku fatawa ne da jefewa, to ku guje shi.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, to waɗannan su ne kafirai…” [Muslim #1700]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, ta yaya waɗannan Yahudawa za su sanya ka mai hukunci a tsakaninsu, alhalin suna ƙaryata ka, sannan ga littafin Attaura nan a hannunsu, amma kuma sun bijire masa, sun yi watsi da shi, sun tafi neman wani hukunci daban wanda suke son ya yi daidai da son zukatansu? Mutanen da wannan shi ne aikinsu ai ba muminai ne ba.

  44. إِنَّآ أَنزَلۡنَا ٱلتَّوۡرَىٰةَ فِيهَا هُدٗى وَنُورٞۚ يَحۡكُمُ بِهَا ٱلنَّبِيُّونَ ٱلَّذِينَ أَسۡلَمُواْ لِلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلرَّبَّٰنِيُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ بِمَا ٱسۡتُحۡفِظُواْ مِن كِتَٰبِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ عَلَيۡهِ شُهَدَآءَۚ فَلَا تَخۡشَوُاْ ٱلنَّاسَ وَٱخۡشَوۡنِ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗاۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ

    Open ayah 5:44

    Lalle Mu Muka saukar da Attaura, (wadda) a cikinta akwai shiriya da haske. Annabawa waɗanda suka miƙa wuya suna hukunci da ita, ga waɗanda suke Yahudawa, da malamai na-Allah da malamai masana, saboda abin da aka ɗora musu na kiyaye Littafin Allah, kuma sun kasance masu ba da shaida a kansa. Don haka kada ku ji tsoron mutane, ku ji tsoro Na Ni kaɗai, kuma kada ku musanya ayoyina da wani ɗan farashi ƙanƙani. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waɗannan su ne kafirai.

  45. وَكَتَبۡنَا عَلَيۡهِمۡ فِيهَآ أَنَّ ٱلنَّفۡسَ بِٱلنَّفۡسِ وَٱلۡعَيۡنَ بِٱلۡعَيۡنِ وَٱلۡأَنفَ بِٱلۡأَنفِ وَٱلۡأُذُنَ بِٱلۡأُذُنِ وَٱلسِّنَّ بِٱلسِّنِّ وَٱلۡجُرُوحَ قِصَاصٞۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِۦ فَهُوَ كَفَّارَةٞ لَّهُۥۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ

    Open ayah 5:45

    Kuma Mun wajabta a kansu a cikinta (Attaura), lalle rai da rai, kuma ido da ido, kuma hanci da hanci, kuma kunne da kunne, kuma haƙori da haƙori, raunuka kuma a yi ramuwa. To duk wanda ya yi sadaka da shi, to wannan kaffara ce gare shi. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waɗannan su ne azzalumai. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa ya saukar wa Annabi Musa littafin Attaura, wanda yake ƙunshe da shiriya da haskensa, annabawa kuma waɗanda suka miƙa wuya ga Allah (Mai tsarki da daukaka) suna yin hukunci da shi a tsakanin Yahudawa. Hakanan malamai na Allah da manyan malaman Yahudawa su ma suna yin hukunci da shi saboda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su amanar kula da shi, ya umarce su da su kiyaye shi, su bayyana shi kuma su kare shi daga duk wani ƙari ko ragi, kuma masu shaidar cewa littafi ne da Allah ya saukar, wanda yake ƙunshe da hukuncin Allah, Allah kuma ya umarce su da kada su ji tsoron mutane wajen zartar da hukuncin Allah; su ji tsoron sa shi kaɗai. Ya kuma yi musu kashedi da musanya hukuncinsa da wani ɗan jin daɗi kaɗan na duniya. Sannan ya tabbatar musu da cewa duk wanda ya yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar ba, to waɗannan su ne kafirai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin cewa ya wajabta wa Yahudawa hukuncin ramuwa a cikin littafin Attaura, wato a kashe duk wanda ya kashe wani da gangan ba tare da haƙƙi ba, haka kuma wanda ya cire idon wani shi ma a cire masa, ko hanci a cire nasa, ko kunne a cire nasa, ko haƙori a cire nasa, kamar yadda ya wajabta yin ramuwa a rauni. Duk wanda ya yi wa wani rauni bisa zalunci, to ya nemi ramuwa kwatankwacin raunin da aka yi masa. Amma duk wanda ya yi afuwa, ya yafe wa wanda ya yi masa laifi, to Allah zai kankare masa laifukansa, sakamakon afuwar da ya yi. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya daɗa tabbatar da cewa duk wanda bai yi hukunci da abin da ya saukar ba, to waɗannan su ne azzalumai.

  46. وَقَفَّيۡنَا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم بِعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡإِنجِيلَ فِيهِ هُدٗى وَنُورٞ وَمُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَهُدٗى وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 5:46

    Sai Muka biyar da Isa ɗan Maryamu a bayansu wanda yake gaskata abin da ya gabace shi na Attaura, kuma Muka ba shi Linjila, a cikinta akwai shiriya da haske, kuma tana gaskata abin da ya gabace ta na Attaura, kuma shiriya ce, da wa’azi ga masu taƙawa.

  47. وَلۡيَحۡكُمۡ أَهۡلُ ٱلۡإِنجِيلِ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فِيهِۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

    Open ayah 5:47

    Lalle kuma ma’abota Linjila su yi hukunci da abin da Allah Ya saukar a cikinsa. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waɗannan su ne fasiƙai. A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ya aiko da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bayan annabawan Banu Isra’ila masu hukunci da Attaura. Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma ya yi imani da littafin Attaura, yana ba da shaidar cewa Attaura gaskiya ce. Shi kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi littafin Linjila, wanda shi ma cike yake da shiriya da haske, yana mai shaida da tabbatar da abin da yake cikin littafin Attaura, yana bayanin gaskiya, yana gargaɗin masu tsoron Allah da su ƙaurace wa haramun da aikata laifuka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Nasara da su yi hukunci da abin da yake cikin littafin Linjila wanda ya saukar wa Annabi Isa(Amincin Allah ya tabbata a gare shi), su yi aiki da shi, su yi imani da duk abin da ya ƙunsa, wanda ya haɗa har da albishir da Allah ya yi na aiko Annabi Muhammad (ﷺ) da umarni kan su yi imani da shi, kuma su yi masa biyyaya. Sannan Allah ya tabbatar da cewa duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, to waɗannan su ne fasiƙai.

  48. وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمُهَيۡمِنًا عَلَيۡهِۖ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۖ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ عَمَّا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ لِكُلّٖ جَعَلۡنَا مِنكُمۡ شِرۡعَةٗ وَمِنۡهَاجٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

    Open ayah 5:48

    Kuma Mun saukar maka da Littafin (Alƙur’ani) da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi na sauran littattafai, kuma mai ɗaukaka a kansu; don haka ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar; kuma kada ka bi soye-soyen zukatansu ka bar abin da ya zo maka na gaskiya don bin son zuciyarsu. Kowanne daga cikinku Mun sanya musu tsari na shari’a da tsari na rayuwa. Kuma in da Allah Ya ga dama, da sai Ya sanya ku ku zamo al’umma ɗaya, sai dai kuma don Ya jarrabe ku cikin abin da Ya ba ku; don haka sai ku yi gaggawar aikata ayyuka na alheri. Gaba ɗaya makomarku zuwa ga Allah take, kuma zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna saɓani a kansa.

  49. وَأَنِ ٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ وَٱحۡذَرۡهُمۡ أَن يَفۡتِنُوكَ عَنۢ بَعۡضِ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ إِلَيۡكَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَٱعۡلَمۡ أَنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُصِيبَهُم بِبَعۡضِ ذُنُوبِهِمۡۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ لَفَٰسِقُونَ

    Open ayah 5:49

    Kuma ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar, kuma kada ka bi soye-soyen zukatansu, kuma ka yi hattara da su, don kada su fitine ka ka bar wani sashi na abin da Allah Ya saukar maka; idan kuwa sun juya baya, to ka sani lalle Allah Yana nufin Ya kama su ne da wani sashi na zunubansu. Kuma lalle yawancin mutane fasiƙai ne.

  50. أَفَحُكۡمَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ يَبۡغُونَۚ وَمَنۡ أَحۡسَنُ مِنَ ٱللَّهِ حُكۡمٗا لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ 

    Open ayah 5:50

    Shin hukuncin jahiliyya suke nema ne? To wane ne ya fi Allah kyakkyawan hukunci ga mutanen da suke da sakankancewa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana jaddada cewa, shi ya aiko wa Annanbi (ﷺ) Alƙur’ani da gaskiya, yana shaida yana kuma gaskata littattafan da Allah ya saukar gabaninsa wanda yake ƙunshe da abin da suka zo da shi yana kuma hukunci a kansu. To sai Allah ya umarci Ma’aiki da ya yi hukunci tsakanin Ma’abota Littafi da shi wannan Alƙur’anin a duk sanda suka kawo masa hukunci. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya hana shi bin son zuciyarsu wanda ya ci karo da gaskiyar da ta zo masa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa, kowace alumma ya sanya mata tsarin shari’a da kuma tsarin rayuwa. Da ya ga dama da sai ya sanya mutane gaba ɗayansu a kan shari’a da tsarin rayuwa iri ɗaya; to amma saboda Allah ya jarrabi bayinsa, sai ya sanya wa kowace al’umma tsarin shari’arta da tsarin rayuwarta daban. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni ga bayinsa su riƙa yin rigegeniya wajen aikata alheri, domin makomar bayi gaba ɗayansu zuwa gare shi ne, kuma zai labarta wa mutane abin da suka kasance suna saɓani a kansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa (ﷺ) da ya yi musu hukunci da Alƙur’anin da ya saukar masa, kada ya bi son zuciyarsu, kuma ya yi hattara da su kada su kautar da shi, ya bar aiki da abin da Allah ya saukar masa. Idan sun bijire wa hukuncinsa, to ya sani cewa Allah ne zai yi musu uƙuba saboda laifukansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa mutane da dama ba sa yi wa Ubangijinsu biyayya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci waɗannan Yahudawa da cewa, shin suna so ne a riƙa yi musu hukuncin da ya saɓa wa gaskiya, wanda aka gina shi a kan zalunci da jahilci? Sai ya bayyana ƙarara cewa babu wani hukuncin da ya yi kyan hukuncin Allah ga duk wanda ya yi imani da Allah, ya zamanto mai sakankancewa da shi zai fahimci hakan cikin sauƙi.

  51. ۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلۡيَهُودَ وَٱلنَّصَٰرَىٰٓ أَوۡلِيَآءَۘ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمۡ فَإِنَّهُۥ مِنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 5:51

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi Yahudawa da Nasara masoya. Sashinsu masoya sashi ne. Duk kuwa cikinku wanda ya jiɓinci lamarinsu, to lalle shi yana cikinsu. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.

  52. فَتَرَى ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ يُسَٰرِعُونَ فِيهِمۡ يَقُولُونَ نَخۡشَىٰٓ أَن تُصِيبَنَا دَآئِرَةٞۚ فَعَسَى ٱللَّهُ أَن يَأۡتِيَ بِٱلۡفَتۡحِ أَوۡ أَمۡرٖ مِّنۡ عِندِهِۦ فَيُصۡبِحُواْ عَلَىٰ مَآ أَسَرُّواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ نَٰدِمِينَ

    Open ayah 5:52

    Sai ka ga waɗanda suke da cuta a cikin zukatansu suna gaggawa a ciki (jiɓintar su), suna cewa: “Muna jin tsoron kar wata musiba ta same mu.” To mai yiwuwa ne Allah Ya zo da buɗi ko wani lamari daga gare Shi, sai su wayi gari suna nadama kan abin da suka riƙa ɓoyewa a zukatansu.

  53. وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَهَٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ إِنَّهُمۡ لَمَعَكُمۡۚ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فَأَصۡبَحُواْ خَٰسِرِينَ

    Open ayah 5:53

    Kuma waɗanda suka yi imani suna cewa: “ Yanzu waɗannan su ne waɗanda suka rantse da Allah iya ƙurewar rantsuwarsu; cewa, lalle suna tare da ku?” Ayyukansu sun rushe, don haka sai suka wayi gari suna masu hasara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana hana muminai taimakon Yahudawa da Nasara da nuna musu ƙauna. Ya sanar da cewa Yahudawa suna taimaka wa Yahudawa ‘yan’uwansu, hakanan Nasara suna taimaka wa junansu wajen faɗa da Musulmai, don haka duk wani Musulmi da ya taimaka wa Yahudawa ko Nasara wajen faɗa da ‘yan’uwansa Musulmi, to ya zama ɗaya daga cikinsu. Allah ba ya shiryar da mutanen da suka zama azzalumai, masu irin wannan sabgar. Sannan Allah Ta’ala ya yi wa Annabinsa (ﷺ) hannunka-mai-sanda cewa, zai ga munafuƙai waɗanda zukatansu suka cika da shakka da kokwanto game da gaskiyar Musulunci, suna gaggawa wajen taimaka wa Yahudawa da Nasara, suna kare kansu da cewa su fa suna yin haka ne domin gudun kada wata musifa ta auko, a sami sauyin yanayi, kafirai su yi galaba a kan Musulmi. To idan har haka ya faru, su kam za su tsira; kafirai ba za su taɓa su ba, saboda taimakon da suka yi musu a baya. Sai Allah ya mayar musu da martani da cewa, tana yiwuwa Allah ya ba wa Musulmi nasara a kan Yahudawan da Nasaran, ko kuma ya saukar da wata azabarsa da za ta halaka munafuƙai, ko kuma ya kunyata su a duniya, sai su wayi gari suna ta nadama marar amfani a gare su. Idan kuma asirin munafuƙai ya tonu, sai muminai su yi ta mamakin cewa ashe da man waɗannan mutane maƙaryata ne, duk kuwa da irin rantse-rantsen da suke yi cewa, su ma kamar sauran muminai, sun yi imani, kuma suna son taimakon Musulunci da Musulmi. Amma ga shi yau ta bayyana manyan maƙaryata ne, don haka duk ayyukansu da suka yi a baya sun rushe, sun kuma tabbata cikin hasararru.

  54. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَن يَرۡتَدَّ مِنكُمۡ عَن دِينِهِۦ فَسَوۡفَ يَأۡتِي ٱللَّهُ بِقَوۡمٖ يُحِبُّهُمۡ وَيُحِبُّونَهُۥٓ أَذِلَّةٍ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ يُجَٰهِدُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوۡمَةَ لَآئِمٖۚ ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ

    Open ayah 5:54

    Ya ku waɗanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, to (ya sani) Allah zai kawo waɗansu mutane da Yake son su suna son Sa, suna masu ƙasƙantar da kai ga muminai, suna masu nuna wa kafirai isa, suna yin jihadi don ɗaukaka kalmar Allah, kuma ba sa jin tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce da Yake bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mayalwaci ne, Masani.

  55. إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُمۡ رَٰكِعُونَ

    Open ayah 5:55

    Allah ne kaɗai majiɓincin al’amarinku da Manzonsa da kuma waɗanda suka yi imani, waɗanda suke tsayar da salla, kuma suke bayar da zakka, suna kuma masu yin ruku’i.

  56. وَمَن يَتَوَلَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فَإِنَّ حِزۡبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ

    Open ayah 5:56

    Kuma duk wanda ya jiɓinci Allah da Manzonsa da waɗanda suka yi imani, to lalle rundunar Allah su ne masu rinjaye. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin halin wani rukuni na mutane masu yin ridda su bar addinin Musulunci, ko dai ta hanyar haɗa kai da Yahudawa da Nasara wajen yaƙar Musulunci da Musulmi, ko kuma ta wata hanyar daban. Allah ya bayyana cewa duk wanda ya yi ridda ya koma kafirci, to wannan riddar ba za ta cutar da addinin Allah ba, ba kuma zai iya cutar da Musulmi da ita ba. Hasali ma idan Allah ya ga dama zai iya maye gurbinsa da wasu mutane masu son Allah, shi ma yake son su, masu tausayin ‘yan’uwansu muminai, masu tawali’u gare su, kuma masu tsanani ga kafirai maƙiyansu, suna nuna musu isa saboda ɗaukakar addininsu, kuma suna yin jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu, don su ga kalmar Allah ita ce a sama. Ba abin da yake hana su wannan aiki, domin ba sa tsoron wani mai zargi ya zarge su, ba kuma yardar wani suke nema ba sai yardar Allah shi kaɗai. Sannan sai Allah ya bayyana cewa duk waɗannan kyawawan halaye da ya ba wa muminai, falala ce daga gare shi wadda yake ba da ita ga wanda ya ga dama, domin shi Allah (Mai tsarki da daukaka) mayalwaci ne, mai cikakken sani. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin mutanen da ya wajaba ga Musulmi su nisanci haɗa kai da su da taimaka musu, sai kuma ya bayyana waɗanda ya zama wajibi su jiɓince su, su nuna musu ƙauna. Allah (Mai tsarki da daukaka), shi ne na farko, domin shi ne mai taimakon su a koyaushe mai jiɓintar lamarinsu. Jiɓintar Allah kuwa ita ce taimakon addininsa da taimakon mabiya addininsa. Sannan kuma da jiɓintar Manzonsa (ﷺ) wanda ta hanyarsa ne Allah ya fitar da mutane daga duhun kafirci zuwa ga hasken Musulunci. Shi kuma jiɓintar sa da taimakonsa shi ne riƙon addinin da Allah ya aiko shi da shi da taimakon sunnarsa da ba ta kariya da yaɗa ta. Sannan sai jiɓintar muminai masu tsai da salla yadda take, masu fitar da zakkar dukiyoyinsu, su ba da ita ga waɗanda suka cancanta, kuma su ne masu ƙasƙantar da kansu a gaban Mahaliccinsu Allah. Sannan ya bayyana sakamakon waɗanda suka jiɓinci Allah da Manzonsa da muminai da cewa su ne rundunar Allah, waɗanda kuma su ne masu samun galaba a koyaushe. A ƙarƙashin wannan aya, mabiya addinin Shi’a suna da’awar cewa wannan ayar ta sauka ne game da Sayyadina Ali (Allah ya kara masa yarda), a lokacin da yana tsakiyar salla, ya yi ruku’u, sai wani mai bara ya zo yana bara, sai ya ciro zoben azurfa daga ɗan yatsansa ya ba shi sadaka, sai wannan ayar ta sauka. Suka ce ita wannan ayar wai tana nuna shugabancin Sayyadina Ali ne, wato shi ne ya cancanci ya zama halifan Manzon Allah (ﷺ) bayan cikawarsa, ba Sayyadina Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ba. Wannan batu nasu ƙarya ne saboda dalilai kamar haka: <b>Na ɗaya: </b> Ayar ƙarara tana magana ne a kan mutane da yawa, ba mutum ɗaya ba. <b>Na biyu </b>: Da a ce yadda suka fassara ayar cewa Ali (Allah ya kara masa yarda) yana cikin halin ruku’u ne ya ba da zakka, da sai ya kasance ba wanda zai yi shugabanci sai wanda ya ba da sadaka yana tsakiyar ruku’u, don haka ma sauran Ahalul-baiti ba za su zama shugabanni ba, tun da ba a ruwaito sun ba da zakka a cikin halin ruku’u ba. <b>Na uku </b>: Ana yin yabo ne a kan aikata wajibi ko mustahabbi. Mutum ya ba da zakka yana tsakiyar yin salla ba aiki ne na wajibi ko kuma mustahabbi ba, a wurin duk malaman Musulunci. <b>Na huɗu </b>: Da a ce bayar da zakka sanda ake salla abu ne mai kyau, to da babu wani bambanci tsakanin wanda ya bayar yana cikin ruku’u da wanda ya bayar yana tsaye ko yana zaune; wanda ma zai bayar yana tsaye ko zaune sai ya fi wanda ya bayar yana ruku’u. <b>Na biyar </b>: Sayyadina Ali (Allah ya kara masa yarda) zakka ba ta wajaba a kansa ba a zamanin Manzon Allah (ﷺ) domin ba shi da kuɗin da ya kai nisabin zakka a lokacin. <b>Na shida </b>: Fitar da zakka da wata dukiya ba zobe ba ya fi fitar da zobe, domin da yawa daga cikin malamai suna ganin fitar da zobe ba ya isarwa a zakka. <b>Na bakwai </b>: A bayaninsu sun ce, ya ba wa wani mai bara ne, alhali kuwa an fi yabon wanda zai bayar ba tare da an roƙe shi ba. <b>Na takwas </b>: Ayar ta zo ne a cikin jerin gwanon ayoyi masu magana a kan hana jiɓintar kafirai da taimakon su da yin umarni a kan jiɓintar muminai da ƙaunar su da taimakon su, don haka ba maganar shugabanci ne ake yi a ayoyin ba. Kuma kalmar [الوِلَايَة] mai ‘wau’ da wasali ƙasa ta sha bamban da kalmar [الوَلَايَة] mai ‘wau’ da wasali sama. Ta farko ita ce da ma’anar shugabanci, wadda kuma ba ta zo a wannan ayar ba. Ta biyu ita ce da ma’anar ƙauna da jiɓinta, wadda ita ce ta zo a wannan ayar. Mabiya addinin Shi’a sun fi kowa saɓa wa wannan ayar, domin su ne masu haɗa kai da Yahudawa da Nasara wajen cutar da Musulmi da yaƙar su a kowane lokaci. [Dubi, Ibni Taimiyya, Minhajus Sunnah , Juzu’i na 2, Shafi na 30-32].

  57. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَكُمۡ هُزُوٗا وَلَعِبٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَٱلۡكُفَّارَ أَوۡلِيَآءَۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

    Open ayah 5:57

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi waɗanda suke yin izgili da wasa da addininku, waɗanda aka bai wa Littafi tun kafinku, da kuma kafirai, a matsayin masoya, kuma ku kiyaye dokokin Allah, in har da gaske ku muminai ne.

  58. وَإِذَا نَادَيۡتُمۡ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ ٱتَّخَذُوهَا هُزُوٗا وَلَعِبٗاۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡقِلُونَ

    Open ayah 5:58

    Kuma idan kuka yi kiran salla, sai su ɗauke ta abin yi wa izgili da wasa. Suna yin hakan don su mutane ne da ba sa hankalta.

  59. قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ هَلۡ تَنقِمُونَ مِنَّآ إِلَّآ أَنۡ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلُ وَأَنَّ أَكۡثَرَكُمۡ فَٰسِقُونَ

    Open ayah 5:59

    Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, shin kuna da abin da kuke ƙi a tare da mu ne? Sai fa cewa, mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar kafinmu da kuma cewa, lalle yawancinku fasiƙai ne.”

  60. قُلۡ هَلۡ أُنَبِّئُكُم بِشَرّٖ مِّن ذَٰلِكَ مَثُوبَةً عِندَ ٱللَّهِۚ مَن لَّعَنَهُ ٱللَّهُ وَغَضِبَ عَلَيۡهِ وَجَعَلَ مِنۡهُمُ ٱلۡقِرَدَةَ وَٱلۡخَنَازِيرَ وَعَبَدَ ٱلطَّٰغُوتَۚ أُوْلَٰٓئِكَ شَرّٞ مَّكَانٗا وَأَضَلُّ عَن سَوَآءِ ٱلسَّبِيلِ 

    Open ayah 5:60

    Ka ce: “Shin ba na ba ku labarin sakamakon da ya fi wannan sharri a wurin Allah ba? Shi ne wanda Allah Ya la’anta, kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya mayar da wasu daga cikinsu birrai da aladu; kuma ya bauta wa gunki. Su waɗannan su ne matsayinsu ya fi sharri, kuma (su ne) suka fi ɓacewa daga tafarkin shiriya.”

  61. وَإِذَا جَآءُوكُمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَقَد دَّخَلُواْ بِٱلۡكُفۡرِ وَهُمۡ قَدۡ خَرَجُواْ بِهِۦۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا كَانُواْ يَكۡتُمُونَ

    Open ayah 5:61

    Kuma idan suka zo muku, sai su ce: “Mun yi imani”, alhali kuwa haƙiƙa sun shigo da kafirci ne, kuma haƙiƙa sun fita da shi ne. Allah kuwa Shi ne Mafi sanin abin da suka kasance suna ɓoyewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana hana muminai su yi ƙawance da abota da maƙiyansu kafirai masu yin izgili ga addinin Musulunci da wasu ayyuka na ibada da ya ƙunsa, suna wulaƙanta su, suna ɗaukar su kamar abin wasa. Waɗannan mutane kuwa ana samun su daga cikin Yahudawa da Nasara da sauran kafirai. Sannan ya umarce su da su kiyaye dokokin Allah idan har sun kasance muminai ne su, to kada su yarda su aikata duk abin da aka hana su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da irin izgilin da Yahudawa da Nasara suke yi wa muminai yayin da suka ji suna kiran salla, suna ɗaukar wannan ibada wani abin wasa, kuma ba komai ya sa suke yin haka ba sai don su mutane ne marasa hankali da ba su san girman Mahaliccinsu da hikimomin da suke ƙunshe cikin waɗannan ibadu da suke yi wa izgili ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya bayyana wa Ma’abota Littafi dalilin da ya sa suke gaba da shi da sahabbansa da sauran muminai, wato ba don komai ba sai don kawai sun yi imani da Allah, da Alƙur’anin da aka saukar musu, kuma sun yi imani da littafan Attaura da Linjila da aka saukar gabaninsu. Hasali ma da yawa daga cikin Ma’abota Littafi fasiƙai ne, ba sa bin hanyar Allah ta gaskiya; wannan kuwa ba dalili ba ne da zai sa su riƙa kushe addinin Allah, suna izgili da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa Yahudawa masu kushe wa addinin Musulunci da ƙirƙira masa ƙarya iri-iri cewa, ai nasu addini ne mai mummunar makoma saboda cancanza shi da suka yi, har ta kai Allah ya la’ance su saboda yawan saɓonsu, ya yi fushi da su, ya ma mayar da wasu daga cikinsu birrai, wasu kuma aladu, wasu kuma suka dinga bauta wa Ɗagutu, wanda shi ne duk wani abu da bawa zai saki hanyar Allah saboda shi. To waɗannan su ne mafi sharrin mutane a duniya da lahira, ba muminai ba waɗanda suka tsare addininsu suna biyayya ga Allah da Manzonsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya dawo kan sukar waɗansu halaye na munafuƙai, wato ɗabi’ar ƙarya. Duk lokacin da suke tare da muminai, za su ce sun yi imani alhali ƙarya ce suke yi, suna nan riƙe da aƙidarsu ta kafirci, da ita ce suka shigo cikin muminai hakanan da ita suke fita su bar su, duk maganganun da suke yi su ba sa musu wani amfani. Allah masanin sarari da ɓoye shi ne mafi sanin abin da suke ɓoyewa, kuma zai yi musu sakayya a kansa.

  62. وَتَرَىٰ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَأَكۡلِهِمُ ٱلسُّحۡتَۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 5:62

    Kuma za ka ga yawancinsu suna yin gaggawa wajen aikin saɓo da ƙetare iyaka da kuma cin haramun. Lalle tir da abin da suka kasance suna aikatawa.

  63. لَوۡلَا يَنۡهَىٰهُمُ ٱلرَّبَّٰنِيُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ عَن قَوۡلِهِمُ ٱلۡإِثۡمَ وَأَكۡلِهِمُ ٱلسُّحۡتَۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَصۡنَعُونَ

    Open ayah 5:63

    Me ya hana malamansu na Allah da masanansu ba su kwaɓe su daga yin maganar saɓo da cin haram ba? Tir da abin da suka kasance suna aikatawa.

  64. وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ يَدُ ٱللَّهِ مَغۡلُولَةٌۚ غُلَّتۡ أَيۡدِيهِمۡ وَلُعِنُواْ بِمَا قَالُواْۘ بَلۡ يَدَاهُ مَبۡسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيۡفَ يَشَآءُۚ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۚ وَأَلۡقَيۡنَا بَيۡنَهُمُ ٱلۡعَدَٰوَةَ وَٱلۡبَغۡضَآءَ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ كُلَّمَآ أَوۡقَدُواْ نَارٗا لِّلۡحَرۡبِ أَطۡفَأَهَا ٱللَّهُۚ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادٗاۚ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

    Open ayah 5:64

    Kuma Yahudawa suka ce: “Hannun Allah a ƙuƙunce yake.” To an ƙuƙunce hannayensu, kuma an la’ance su sakamakon abin da suka faɗa. Kuma ba haka ba ne. Hannayensa a shimfiɗe suke; Yana ciyarwa yadda Ya ga dama. Kuma abin da aka saukar maka daga wajen Ubangijinka lalle yana daɗa wa yawancinsu shisshigi da kafirci. Kuma Mun jefa gaba da ƙiyayya a tsakankaninsu har zuwa ranar tashin alƙiyama. Duk lokacin da suka yi yunƙurin rura wutar yaƙi, sai Allah Ya bice ta; kuma suna masu tafiya a bayan ƙasa suna aikata ɓarna. Allah kuwa ba ya son maɓarnata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi (ﷺ) wani mummunan halin yawancin Yahudawa ne, wato yadda za ka gan su suna rige-rige wajen aikata saɓon Allah da shiga haƙƙoƙin mutane ta hanyar yi musu ta’addanci da cin dukiyarsu ba bisa gaskiya ba. Allah ya yi tir da irin wannan mummunan aikin nasu. Sannan ya bayyana cewa, me ya sa malamansu na Allah da masanan cikinsu ba su hana su saɓon Allah da cin dukiyar haramun ba? Allah ya sake yin tir da irin wannan hali na malaman Yahudawa da suke yin shiru ba sa faɗa musu gaskiya, ba sa hana su aikata munanan ayyuka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata mummunar magana da Yahudawa suke furta masa, suna cewa, hannun Allah a ƙuƙunce yake, wato ba ya kyauta. Allah ya tsarkaka daga wannan mummunar maganar tasu. Allah ya mayar musu da martani da cewa su ne hannuwansu suke a ƙuƙunce, kuma an la’ance su a kan wannan furuci nasu, amma shi Allah hannayensa a shimfiɗe suke, koyaushe yana kyauta, yana baiwa yadda ya ga dama. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle hannun Allah na dama a cike yake, abin da yake cikinsa kuma ba ya raguwa saboda bayarwa. Allah mai kyautar dare da rana ne. Shin kun ga abin da ya ciyar tun lokacin da ya halicci sammai da ƙasa? Abin da yake a hannunsa bai ragu ba.” [Bukhari #7419, da Muslim #993]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa Muhammadu (ﷺ) cewa, idan Yahudawa suka saurari Alƙur’anin da aka saukar maka, sai abin ya ƙara musu shisshigi da kafirci. Kuma ya bayyana cewa ya sanya gaba da ƙiyayya a tsakanin Yahudawa su kansu, kuma za su ci gaba da rayuwa a haka har zuwa tashin alƙiyama. Duk sa’adda suka kunna wutar yaƙi da muminai sai Allah ya kashe ta, daga nan sai gwiwowinsu su yi sanyi. Ko da kuwa sun tayar da wani yaƙi a cikin al’umma to sai Allah ya mayar da muguwar aniyarsu a kansu, su faɗa ramin muguntar da suka haƙa da hannuwansu. Suna gaggawar yaɗa ɓarna a bayan ƙasa ta hanyar saɓon Allah da yaƙi da Musulunci, kuma Allah ba ya son maɓarnata.

  65. وَلَوۡ أَنَّ أَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَكَفَّرۡنَا عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأَدۡخَلۡنَٰهُمۡ جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ

    Open ayah 5:65

    Kuma in da a ce waɗanda aka bai wa Littafi sun yi imani, kuma sun kiyaye dokokin Allah, to lalle da Mun kankare musu zunubansu, kuma lalle da Mun shigar da su gidajen Aljanna na ni’ima.

  66. وَلَوۡ أَنَّهُمۡ أَقَامُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِم مِّن رَّبِّهِمۡ لَأَكَلُواْ مِن فَوۡقِهِمۡ وَمِن تَحۡتِ أَرۡجُلِهِمۚ مِّنۡهُمۡ أُمَّةٞ مُّقۡتَصِدَةٞۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ سَآءَ مَا يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 5:66

    Kuma da a ce sun tsaya a kan aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar musu daga Ubangijinsu, lalle da sun ci daga samansu da kuma ƙarƙashin ƙafafunsu. Daga cikinsu akwai wata al’umma madaidaiciya, (amma) kuma mafi yawa daga cikinsu, irin abin da suke aikatawa ya munana (matuƙa).

  67. ۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ بَلِّغۡ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ وَإِن لَّمۡ تَفۡعَلۡ فَمَا بَلَّغۡتَ رِسَالَتَهُۥۚ وَٱللَّهُ يَعۡصِمُكَ مِنَ ٱلنَّاسِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 5:67

    Ya kai wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka; idan kuwa ba ka yi ba, to ba ka isar da saƙonsa ba. Allah kuwa Shi ne Yake kare ka daga (sharrin) mutane. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutanen da suke kafirai.

  68. قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَسۡتُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۖ فَلَا تَأۡسَ عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 5:68

    Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, ba kwa kan wani abu (na addinin gaskiya), har sai kun tsaya a kan yin aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar muku daga wajen Ubangijinku.” Kuma abin da ake saukar maka daga Ubangijinka tabbas yana ƙara wa yawancinsu shisshigi da kafirci. Don haka kada ka yi baƙin ciki dangane da (abin da yake samun) mutane kafirai. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana cewa, da a ce da gaske Yahudawa da Nasara sun yi imani, sun kiyaye dokokin Allah, to da Allah ya kankare musu laifukansu da suke yi, kuma da ya shigar da su Aljanna mai cike da ni’imomi. Da kuma a ce sun yi aiki da umarnin Allaha da haninsa da yake cikin Attaura da Linjila da Alƙur’ani, to da ya kwararo musu arziki mai ɗimbin yawa ta ko’ina, kamar ruwan sama, ya fitar musu da amfanin gona mai yawa a gonakinsu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba duk Yahudawa ne da Nasara suka taru suka zama ɗaya ba; a cikinsu akwai mutanen kirki masu son gaskiya da aiki da ita, masu aikata abin da Allah ya wajabta musu, masu barin abin da ya hana su, su tsaya a kan haka; amma mafi yawa daga cikinsu mutanen banza ne, masu miyagun ayyuka. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya isar da duk saƙon da ya aiko shi da shi kada ya rage komai daga ciki; idan kuwa har bai yi hakan ba, to bai yi wa Allah biyayya ba wajen isar da saƙonsa ga mutane. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Duk wanda ya faɗa maka cewa Annabi (ﷺ) ya ɓoye wani abu daga abin da Allah ya saukar masa, to haƙiƙa ya faɗi ƙarya. Allah yana cewa: “Ya kai wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar maka....” [Bukhari #4612]. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Na bar muku abin da idan kun riƙe shi ba za ku ɓace ba bayana, shi ne Littafin Allah, kuma za a yi muku tambaya game da ni, to wace amsa za ku bayar?” Sai sahabbai suka ce: “Za mu ba da shaidar cewa ka isar da saƙo, ka bayar da amana, kuma ka yi nasiha.” Sai Annabi (ﷺ) ya ɗaga ɗan yatsansa sama, yana nuna mutane da shi yana cewa: “Ya Allah ka shaida, ya Allah ka shaida.” har sau uku. [Muslim #1218]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwantar wa da Annabinsa hankali, da cewa zai ba shi kariya daga mutane, kada tsoron wani mahaluƙi ya hana shi isar da saƙon da aka aiko shi da shi. Lalle Allah ba ya shiryar da mutanen da suke kafirai ne. Ya kuma umarce shi da ya faɗa wa Ma’abota Littafi cewa, abin da suke da’awar suna bi na addini ƙarya ce kawai suke faɗa, matuƙar ba za su yi aiki da Attaura da Linjila da Alƙur’ani ba. Ya ce da yawa daga cikin Yahudawa idan suka ji karatun Alƙur’ani, babu abin da yake ƙara musu sai ƙetare iyaka da kafirci, don haka kada ransa ya ɓaci saboda kafircinsu, shi dai ya isar da saƙon Ubangijinsa kawai, shi kuma zai isar masa daga gare su.

  69. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلصَّٰبِـُٔونَ وَٱلنَّصَٰرَىٰ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

    Open ayah 5:69

    Lalle waɗanda suka yi imani da waɗanda suke Yahudawa da Sabi’awa da Nasara, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe, kuma ya yi aiki nagari, to babu jin tsoro a tattare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.

  70. لَقَدۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمۡ رُسُلٗاۖ كُلَّمَا جَآءَهُمۡ رَسُولُۢ بِمَا لَا تَهۡوَىٰٓ أَنفُسُهُمۡ فَرِيقٗا كَذَّبُواْ وَفَرِيقٗا يَقۡتُلُونَ 

    Open ayah 5:70

    Lalle haƙiƙa Mun ɗauki alƙawari daga Bani-Isra’ila, kuma Muka aika musu da manzanni. Duk sa’adda wani manzo ya zo musu da abin da zukatansu ba sa so, sai su ƙaryata waɗansu kuma su riƙa kashe waɗansu.

  71. وَحَسِبُوٓاْ أَلَّا تَكُونَ فِتۡنَةٞ فَعَمُواْ وَصَمُّواْ ثُمَّ تَابَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ ثُمَّ عَمُواْ وَصَمُّواْ كَثِيرٞ مِّنۡهُمۡۚ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 5:71

    Kuma sun zaci cewa, babu wata fitina da za ta auku, sai suka makance kuma suka kurumce, sannan Allah Ya karɓi tubansu, sannan kuma da yawa daga cikinsu suka sake makancewa da kurumcewa. Allah kuma Mai ganin abin da suke aikatawa ne. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa ƙofarsa a buɗe take ga duk mabiya kowane addini; idan har sun yi imani da abin da ya saukar musu, to zai karɓe su a fadarsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo Musulmi, al’ummar Annabi Muhammadu (ﷺ) da Yahudawa mabiya Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kafin a shafe addininsu da kuma Sabi’awa, waɗanda su kuma ƙungiyoyi ne daban-daban, amma a nan ana nufin waɗanda su ba Yahudawa ba ne, ba kuma Nasara ba, kuma ba mushirikai ba ba majusawa ba; suna dai riƙe da Tauhidi, wato kaɗaita Allah (Mai tsarki da daukaka) da haramta zalunci da miyagun ayyuka, ba tare da suna bin wani addini ba. Da Nasara mabiya Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kafin a shafe addininsu. Waɗannan ƙungiyoyi huɗu, duk wanda a cikinsu ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya yi aiki na ƙwarai, to ba za su ji tsoron abin da za su fuskanta ba a nan gaba, kuma ba za su yi baƙin ciki a kan abin da za su bari a nan duniya ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa ya yi alƙawari mai ƙarfi da Bani-Isra’ila a kan yin imani da Allah da aiki da abin da ya wajabta musu aiki da shi, sannan ya aiko musu da manzanni masu kiran su zuwa ga Allah (Mai tsarki da daukaka), amma sai ga su duk lokacin da wani manzo ya zo musu da abin da ya saɓa wa son zuciyarsu, sai su ƙaryata wasu manzannin, wasu kuma su kashe su, kuma a zatonsu ba wani abu na uƙuba da zai same su a kan wannan mummunan aiki nasu, don haka sai suka ci gaba da shisshiginsu da zarmewarsu cikin saɓon Allah, suka makance da gangan, ba sa ganin gaskiyar da ake nuna musu, suka zama kuramen ƙarfi da yaji, ba sa jin gaskiyar da ake faɗa musu. Daga baya Allah ya yafe musu laifukansu; to amma sai da yawa daga cikinsu suka ƙara koma wa mummunan halinsu na farko, suka ci gaba da ɓarnarsu, suka sake makancewa, ba sa ganin gaskiya, suka kurumce, ba sa jin gaskiya. Allah kuma yana ganin duk abin da suke aikatawa, kuma zai yi musu sakayya a kai.

  72. لَقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ وَقَالَ ٱلۡمَسِيحُ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۖ إِنَّهُۥ مَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ ٱلۡجَنَّةَ وَمَأۡوَىٰهُ ٱلنَّارُۖ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ

    Open ayah 5:72

    Lalle haƙiƙa waɗanda suka ce: “Lalle Allah Shi ne Almasihu ɗan Maryamu” sun kafirta. Shi kuwa Almasihu cewa ya yi: “Ya ku Bani-Isra’ila, ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku. Lalle yadda al’amarin yake, duk wanda ya yi shirka da Allah, to haƙiƙa Allah Ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka.”

  73. لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ ثَالِثُ ثَلَٰثَةٖۘ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّآ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ وَإِن لَّمۡ يَنتَهُواْ عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

    Open ayah 5:73

    Lalle haƙiƙa waɗannan da suka ce: “Lalle Allah Shi ne na cikon (alloli) uku,” sun kafirta. Babu kuwa wani abin bauta wa na gaskiya, sai abin bauta Ɗaya tal. Idan ba su bar abin da suke faɗa ɗin nan ba, lalle azaba mai raɗaɗi za ta shafi waɗanda suka kafirta daga cikinsu.

  74. أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى ٱللَّهِ وَيَسۡتَغۡفِرُونَهُۥۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 5:74

    Shin yanzu ba za su tuba zuwa ga Allah ba, kuma su nemi gafararsa? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

  75. مَّا ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَ إِلَّا رَسُولٞ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِ ٱلرُّسُلُ وَأُمُّهُۥ صِدِّيقَةٞۖ كَانَا يَأۡكُلَانِ ٱلطَّعَامَۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ ثُمَّ ٱنظُرۡ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

    Open ayah 5:75

    Shi fa Almasihu ɗan Maryamu bai zamo ba face Manzo, wanda haƙiƙa manzanni sun shuɗe kafinsa. Mahaifiyarsa kuma Siddiƙa ce; shi da ita sun kasance suna cin abinci. Duba ka ga yadda Muke bayyana musu ayoyi, sannan ka sake dubawa, ta yaya ake kautar da su?

  76. قُلۡ أَتَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَمۡلِكُ لَكُمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗاۚ وَٱللَّهُ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

    Open ayah 5:76

    Ka ce: “Shin yanzu kwa riƙa bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba ya mallakar cutarwa ko amfanarwa a gare ku; Shi kuwa Allah Shi ne Mai ji, kuma Masani?”

  77. قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَلَا تَتَّبِعُوٓاْ أَهۡوَآءَ قَوۡمٖ قَدۡ ضَلُّواْ مِن قَبۡلُ وَأَضَلُّواْ كَثِيرٗا وَضَلُّواْ عَن سَوَآءِ ٱلسَّبِيلِ

    Open ayah 5:77

    Ka ce: “Ya ku ma’abota Littafi, kada ku zurfafa a ckin lamarin addiniku (ku ƙara) abin da ba gaskiya ba, kuma kada ku bi soye-soyen zukatan waɗansu mutanen da suka riga suka ɓata tun a da can, kuma sun ɓatar da mutane da yawa, kuma sun ɓace daga madaidaiciyar hanya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙara tabbatar da kafircin Nasara waɗanda suke da’awar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) Allah ne, alhalin shi bawansa ne kamar sauran mutane; an san mahaifiyarsa, an san asalinsa, kuma shi kansa bai ce musu shi Allah ne ba; ya kirawo su ne gaba ɗayansu zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, domin shi da su duka Allah ne Ubangijinsu. Ya kuma hana su haɗa Allah da wani, ya nuna musu cewa duk wanda ya kuskura ya yi shirka da Allah, kuma har ya mutu bai tuba ba, to fa shi da shiga Aljanna har abada, domin ba mai shigar ta sai wanda ya kaɗaita Allah; kuma makomarsa ita ce wutar Jahannama, inda ba wani mai taimakon sa ko ya cece shi daga wannan azabar. Hakanan ya tabbatar da kafircin Nasara saboda mummunar aƙidarsu ta cewa abu uku ne suka haɗu suka yi Allah, wato Isa da mahaifiyarsa da kuma Allah (Mai tsarki da daukaka). Suka mayar da Allah ɗayan abu uku. Allah ya ba su amsa da cewa babu wani abu da ya cancanci bauta sai Allah shi kaɗai. Sannan ya nuna musu hatsarin wannan muguwar aƙida da cewa wallahi in har ba su tuba suka yi watsi da ita ba to sun tabbata kafirai; su kuwa kafirai za su ɗanɗani azaba ce mai tsananin gaske. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu wannan gargaɗin, sai kuma ya buɗe musu ƙofar samun rahamarsa, ya kirawo su zuwa ga tuba da neman gafara, domin shi Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu wata ƙaƙƙarfar hujja a kan cewa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mahaifiyarsa ba alloli ne ba kamar yadda su suke faɗa; Shi Manzo ne daga cikin manzannin Allah da suka gabata waɗanda gaba ɗayansu bayin Allah ne. Mahaifiyarsa kuma ƙololuwar matsayinta shi ne ita siddiƙa ce, wato ba ta kai ma matsayin annabiya ba, balle a ce mata Allah. Ta gaskata ayoyin Allah, ta yi imani da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sannan ƙari a kan haka, Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mahaifiyarsa dukansu mutane ne suna cin abinci, ka ga ashe mabuƙata ne, Allah kuwa ba mabuƙaci ne ba. To idan haka ne, me ya sa za su yarda cewa su alloli ne, har ma su riƙa bautar su? Sannan ya ja hankalin mai karatu da cewa, ya dubi yadda Allah yake bayyana dalilai da hujjoji a kan rushe cewa Annabi Isa da mahaifiyarsa alloli ne ababen bauta, amma duk da haka ake karkatar da su daga gane gaskiya da fahimtar waɗannan ƙwararan dalilai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ƙalubalanci waɗannan kafirai da cewa, me ya sa suke bauta wa wanin Allah, wanda bai mallaki cutarwa ko amfanarwa ba, kuma Allah shi ne mai ji masani? Ya kuma umarce shi da ya yi musu kashedi da wuce gona da iri a cikin sha’anin addininsu har su riƙa kai wasu annabawa matsayin Allah; kada kuma su riƙa bin son zuciyar shugabanninsu da manyansu da jahilan masu ibada a cikinsu, waɗanda sun riga sun ɓace, kuma sun ɓatar da mutane masu yawa, kuma sun saki miƙaƙƙiyar hanya.

  78. لُعِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

    Open ayah 5:78

    An la’anci waɗanda suka kafirta daga cikin Bani-Isra’ila a bisa harshen Dawuda da kuma Isa ɗan Maryamu. Hakan kuwa saboda abin da suka riƙa yi ne na saɓo, kuma sun kasance suna ƙetare iyaka.

  79. كَانُواْ لَا يَتَنَاهَوۡنَ عَن مُّنكَرٖ فَعَلُوهُۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ

    Open ayah 5:79

    Sun kasance ba sa hana junansu wani mummunan aikin da suka yi. Lalle tir da irin abin da suka kasance suna aikatawa.

  80. تَرَىٰ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ يَتَوَلَّوۡنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ لَبِئۡسَ مَا قَدَّمَتۡ لَهُمۡ أَنفُسُهُمۡ أَن سَخِطَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَفِي ٱلۡعَذَابِ هُمۡ خَٰلِدُونَ 

    Open ayah 5:80

    Za ka ga yawancinsu suna nuna ƙauna ga waɗanda suka kafirta. Lalle tir da irin abin da kawunansu suka gabatar, don kuwa Allah Ya yi fushi da su, kuma su masu dawwama ne cikin azaba.

  81. وَلَوۡ كَانُواْ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلنَّبِيِّ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مَا ٱتَّخَذُوهُمۡ أَوۡلِيَآءَ وَلَٰكِنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ

    Open ayah 5:81

    Kuma da sun kasance suna imani da Allah da Annabi da abin da aka saukar masa, da ba su riƙe su a matsayin masoya ba, sai dai kuma yawancinsu fasiƙai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙara bayyana munanan halayen Banu Isra’ila, da cewa, Annabawa biyu daga cikin annabawansu sun la’ance su saboda kangarewarsu da yawan saɓon Allah da suke yi tare da danne haƙƙoƙin mutane, kuma duk da haka ba sa yi wa juna nasiha suna hana juna saɓon Allah. Sai Allah ya yi tir da irin wannan mummunan hali nasu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo labarin halin Yahudawa a Madina a zamanin Manzon Allah (ﷺ), yadda suka riƙa haɗa kai da kafiran Makka don su cutar da Musulmi. Kuma Annabi (ﷺ) yana ganin da yawa daga cikinsu suna ƙawance da mushirikai a kan wannan mummunar manufa. Allah ya yi tir da wannan mugun aiki nasu, wanda suka yi wa kawunansu guzuri da shi na zuwa lahira inda za su gamu da fushin Allah da kuma azabar wutar Jahannama wadda za su shige ta har abada. Da a ce Yahudawan da gaske sun yi imani da Allah da Annabi Muhammadu (ﷺ) da Alƙur’ani, to da ba su haɗa kai da kafirai ba, to amma yawancinsu fasiƙai ne.

  82. ۞لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ ٱلنَّاسِ عَدَٰوَةٗ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلۡيَهُودَ وَٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْۖ وَلَتَجِدَنَّ أَقۡرَبَهُم مَّوَدَّةٗ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّا نَصَٰرَىٰۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّ مِنۡهُمۡ قِسِّيسِينَ وَرُهۡبَانٗا وَأَنَّهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ

    Open ayah 5:82

    Tabbas lalle za ka samu cewa, mutanen da suka fi tsananin gaba da waɗanda suka yi imani, su ne Yahudawa da waɗanda suke mushirikai. Kuma tabbas lalle za ka sami waɗanda suka fi kusanci wajen nuna ƙauna ga waɗanda suka yi imani, su ne waɗanda suka ce: “Lalle mu Nasara ne.” Wannan kuwa saboda a cikinsu akwai malamai da masu yawan ibada, don kuma lalle su ba sa yin girman kai.

  83. وَإِذَا سَمِعُواْ مَآ أُنزِلَ إِلَى ٱلرَّسُولِ تَرَىٰٓ أَعۡيُنَهُمۡ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمۡعِ مِمَّا عَرَفُواْ مِنَ ٱلۡحَقِّۖ يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱكۡتُبۡنَا مَعَ ٱلشَّٰهِدِينَ

    Open ayah 5:83

    Kuma idan sun ji abin da aka saukar wa wannan Manzo, za ka ga idanunsu suna zubar da hawaye, saboda abin da suka gane na gaskiya; suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, don haka Ka rubuta mu cikin masu shaidawa.

  84. وَمَا لَنَا لَا نُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَا جَآءَنَا مِنَ ٱلۡحَقِّ وَنَطۡمَعُ أَن يُدۡخِلَنَا رَبُّنَا مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلصَّٰلِحِينَ

    Open ayah 5:84

    “Kuma me muke da shi da ba za mu yi imani da Allah da abin da ya zo mana na gaskiya ba, muna kuwa sa rai Ubangijinmu Ya shigar da mu cikin salihan bayi?”

  85. فَأَثَٰبَهُمُ ٱللَّهُ بِمَا قَالُواْ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 5:85

    Sai Allah Ya saka musu saboda abin da suka faɗa, da gidajen aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dauwama a cikinsu, kuma wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa.

  86. وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

    Open ayah 5:86

    Waɗanda kuwa suka kafirta, kuma suka ƙaryata ayoyinmu, waɗannan su ne ‘yan wuta. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana miyagun halayen Yahudawa da Nasara a ayoyin da suka gabata, a nan kuma sai ya yi bayanin cewa waɗanda suka fi kowa tsananin gaba ga muminai su ne Yahudawa da mushirikai, saboda tsananin ƙiyayyarsu da hassadarsu gare su. Sannan kuma waɗanda suka fi kusancin soyayya ga muminai su ne Nasara, saboda a cikinsu akwai malamai, akwai kuma masu bautar Allah, kuma ba sa girman kai game da karɓar gaskiya. Wasu masana Tafsiri, kamar Ibn Jarir At-Tabari da Al-Wahidi da kuma Al-Baghawi suna ganin Nasara da aka ambata a nan su ne waɗanda suka musulunta daga cikinsu, kamar Najashi Sarkin Habasha (Allah ya kara masa yarda). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan sun saurari karatun Alƙur’ani sai su riƙa zubar da hawaye, saboda sun fahimci cewa abin da ake karanta musu gaskiya ne, har ma suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, don haka ka rubuta mu tare da Annabi (ﷺ) da al’ummarsa.” Suna ƙarawa da cewa: “Me zai hana mu yin imani da Allah da abin da ya zo mana ta hanyar Manzon Allah (ﷺ) na Alƙur’ani mai shiryarwa zuwa ga gaskiya? Kuma muna fata a dalilin wannan imanin namu Allah ya haɗa mu da mutanen kirki.” To saboda imanin da suka yi da gaskiyar da suka faɗa sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu sakayya da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, kuma za su zauna a cikinsu zama na har abada. Wannan sakamako ne na wanda ya kyautata bautar Ubangijinsa, kuma ya kyautata wa mutane. Amma wanda ya kafirta, ya ƙaryata ayoyin Allah, to waɗannan su ne mazauna gidan wutar Jahannama har abada.

  87. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحَرِّمُواْ طَيِّبَٰتِ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكُمۡ وَلَا تَعۡتَدُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ

    Open ayah 5:87

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku haramta kyawawan abubuwan da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare iyaka. Lalle Allah ba Ya son masu ƙetare iyaka.

  88. وَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ أَنتُم بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 5:88

    Kuma ku ci daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, wanda yake halal, mai daɗi. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda kuke yin imani da Shi.

  89. لَا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ ٱلۡأَيۡمَٰنَۖ فَكَفَّٰرَتُهُۥٓ إِطۡعَامُ عَشَرَةِ مَسَٰكِينَ مِنۡ أَوۡسَطِ مَا تُطۡعِمُونَ أَهۡلِيكُمۡ أَوۡ كِسۡوَتُهُمۡ أَوۡ تَحۡرِيرُ رَقَبَةٖۖ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖۚ ذَٰلِكَ كَفَّٰرَةُ أَيۡمَٰنِكُمۡ إِذَا حَلَفۡتُمۡۚ وَٱحۡفَظُوٓاْ أَيۡمَٰنَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

    Open ayah 5:89

    Allah ba zai kama ku da yasassun rantse-rantsenku ba, sai dai Yana kama ku ne da laifin abin da kuka ƙudurce na rantsuwa; to kaffararsa ita ce ciyar da miskinai goma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalinku ko kuma tufatar da su ko ‘yantar da bawa; wanda kuwa bai sami iko ba, to sai ya yi azumin kwana uku. Wannan shi ne kaffarar rantsuwarku, in kun yi rantsuwa. Kuma ku kiyaye rantse-rantsenku. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ku zamo masu godiya. A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana kira ne ga muminai kada su haramta wa kansu kyawawan abubuwa da Allah ya halatta musu, kuma kada su tsallake halal su auka wa haram, domin Allah ba ya son masu ƙetare iyakokinsa. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Usman ɗan Maz’un (Allah ya kara masa yarda) ya yi niyyar ya ƙaurace wa aure, sai Manzon Allah (ﷺ) ya hana shi. Da a ce hakan ya halatta da mun fiɗiye kawunanmu.” [Bukhari #5073, da Muslim #1402]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu mutane su uku sun je gidajen matan Annabi (ﷺ) suna tambaya game da ibadarsa. Lokacin da aka faɗa musu yadda yake ibada, sai suka ga kamar ta yi musu kaɗan, sai suka ce: “Ina za mu haɗa kawunanmu da Manzon Allah (ﷺ), alhali shi Allah ya riga ya gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa da abin da ya jinkirta?” Sai ɗaya daga cikinsu ya ce: “Ni dai zan yi ta yin sallar dare har abada.” Ɗayan kuma sai ya ce: “Ni kuma zan yi ta azumi har abada ba zan ajiye ba.” Shi kuma na ukunsu sai ya ce: “Ni kuma zan ƙaurace wa mata, ba zan yi aure ba har abada.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya same su sai ya ce: “Ku ne masu faɗar maganganu iri kaza da kaza? Wallahi ni na fi ku tsoron Allah, kuma na fi ku taƙawa, tare da haka ina azumi ina sha, ina sallar dare ina kuma barci, kuma ina auren mata, don haka duk wanda ya ƙyamaci sunnata to ba ni ba shi.” [Bukhari #5063, da Muslim #1401]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su ci arziki na halal mai kyau wanda ya ba su shi kyauta, kuma su kiyaye dokokin Allah wanda da shi ne suka yi imani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da cewa ba ya kama mutane da yasasshiyar rantsuwa, ita ce rantsuwar da mutum yake yi ba da niyya ba; yana kama mutum ne da rantsuwar da ya ƙuduri niyya a kanta. Idan mutum ya yi rantsuwa sannan ya warware ta, to zai yi kaffara kamar haka: • Ciyar da mabuƙata goma daga matsakaicin abincin da yake ciyar da iyalinsa, ko ya tufatar da su, ko ya ‘yanta bawa ko baiwa. • Idan bai sami ikon ɗaya daga cikin ukun ba, to sai ya yi azumin kwanaki uku. Wannan shi ne kaffarar wanda ya warware rantsuwarsa. Sai kuma ya umarci muminai da su kiyaye rantse-rantsensu watau su guji rantsuwa a kan ƙarya, su bar yawaita rantsuwa, sannan su daina yin rantsuwa suna warware ta, sai fa idan ya kasance yin hakan wani alheri ne, to idan sun warware ta sai su yi kaffarar rantsuwa, kamar yadda aka ambata. Kamar haka ne Allah yake bayanin ayoyinsa filla-filla ga bayinsa domin su gode masa a bisa hakan.

  90. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡخَمۡرُ وَٱلۡمَيۡسِرُ وَٱلۡأَنصَابُ وَٱلۡأَزۡلَٰمُ رِجۡسٞ مِّنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَٱجۡتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ 

    Open ayah 5:90

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ita dai giya da caca da gumaka da kibau na neman sa’a, ba komai ba ne face ƙazanta daga aikin Shaiɗan, don haka ku nisance su domin ku sami rabauta.

  91. إِنَّمَا يُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُوقِعَ بَيۡنَكُمُ ٱلۡعَدَٰوَةَ وَٱلۡبَغۡضَآءَ فِي ٱلۡخَمۡرِ وَٱلۡمَيۡسِرِ وَيَصُدَّكُمۡ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَعَنِ ٱلصَّلَوٰةِۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّنتَهُونَ

    Open ayah 5:91

    Abin da kawai Shaiɗan yake nufi shi ne, ya jefa gaba da ƙiyayya a tsakankaninku, ta hanyar giya da caca, kuma ya hana muku ambaton Allah da yin salla. Shin ko kun hanu?

  92. وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَٱحۡذَرُواْۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

    Open ayah 5:92

    Kuma ku bi Allah, kuma ku bi wannan Manzon, kuma ku yi hattara. Idan kuka juya baya, to ku sani abin da kawai yake kan Manzonmu shi ne isar da saƙo filla-filla.

  93. لَيۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جُنَاحٞ فِيمَا طَعِمُوٓاْ إِذَا مَا ٱتَّقَواْ وَّءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ ثُمَّ ٱتَّقَواْ وَّءَامَنُواْ ثُمَّ ٱتَّقَواْ وَّأَحۡسَنُواْۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 5:93

    Babu wani laifi a kan waɗanda suka yi imani, kuma suka yi aiki nagari cikin abin da suka taɓa sha (na giya a baya), in dai sun yi taƙawa, kuma sun yi imani, kuma sun aikata aiki nagari, sannan suka yi taƙawa da imani, sannan suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa bayinsa muminai cewa giya da caca da gumakan da ake bauta wa ba Allah ba da kibau da ake neman sa’a da su, dukkansu ayyukan Shaiɗan ne, shi ne yake ƙawata su a idanun wasu mutane don ya hana su samun rabo a wurin Allah. Abin da ake nufi da kibau na neman sa’a shi ne, a lokacin jahiliyya Larabawa sun saba idan ɗayansu zai yi tafiya ko zai yi wani aiki, to sai ya shirya wasu kibau guda uku, ta farko an rubuta a kanta cewa: “Aikata”, ɗaya kuwa an rubuta mata: “Kada ka aikata”, ta ukun kuma ba a rubuta mata komai ba. Wasu kuma suka ce abin da aka rubuta a kibiyar farko: “Ubangijina ya umarce ni”, ta biyun kuma: “Ubangijina ya hana ni”, ta ukun ba a rubuta komai a jikinta ba. To sai ya karkaɗa waɗannan kibau uku, idan mai ɗauke da umarni ta fito, sai ya aikata abin da ya yi niyya, idan kuwa mai hanawa ce ta fito, sai ya fasa abin da ya yi niyya, idan kuwa marar rubutu ce a jiki ta fito, to sai ya sake kaɗawa har sai ɗaya daga cikin biyun nan (masu rubutun a jikinsu) ta fito. To shi ne Allah ya hana su irin wannan mummunan aikin. Duka waɗannan laifuka guda uku da aka ambata masu muni ne da ya wajaba duk masu hankali su nisance su, saboda huɗubar Shaiɗan ne, wanda ba ya son ya ga bayi sun rabauta a duniya da lahira. Manufar Shaiɗan har kullum ita ce ya haddasa adawa da ƙiyayya a tsakanin muminai ta hanyar giya da caca, saboda duk wanda ya sha giya ya bugu, ba abin da zai hana shi cutar da ‘yan’uwansa cutarwar da za ta iya kaiwa ga kisa. Wanda ya shiga caca kuma zai iya hasarar duk dukiyarsa har ya shiga jin haushin abokin cacarsa, gaba da ƙiyayya ta shiga tsakaninsu. Hakanan yana daga cikin miyagun manufofin Shaiɗan, ya hana ambaton Allah da tsayar da salla ta hanyar giya da caca. To idan muminai sun fahimci waɗannan illoli da ke cikin waɗannan miyagun ayyuka, to shin za su hanu daga aikata su ko kuwa a’a? An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: “Na zo wurin wata jama’a ta mutanen Makka masu hijira da mutanen Madina Al-Ansar, sai suka ce mini: “Zo mu je mu ba ka abinci, mu shayar da kai giya.” Wannan tun kafin a haramta shan giya ne. Ya ce: “Sai na same su a cikin wani lambu, sai na samu sun tanadi gasasshen kan raƙumi da tulu na giya.” Ya ce: “Sai na ci na ƙoshi, na sha giya, sai na yi magana a kan Muhajiruna mutanen Makka da kuma Al-Ansar mutanen Madina, sai na ce: “Al-Muhajiruna sun fi Al-Ansar.” Da jin haka sai wani mutum ya ɗaga ƙashin dasashin haƙoran raƙumin ya dake ni da shi, har ya yi mini rauni a hanci. Sai na zo na faɗa wa Manzon Allah (ﷺ) abin da ya faru. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar ta 91 a kan wannan abu da ya faru.” [Muslim #1748]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da su yi masa ɗa’a, kuma su yi wa Manzonsa (ﷺ) ɗa’a, kuma su guji saɓa wa umarnin Allah da Manzonsa, idan kuwa sun bijire ne, to su sani cewa isar da saƙo ne kawai a kan Manzo (ﷺ), amma uƙuba ga wanda ya bijire wannan aikin a wurin Allah yake. Sai kuma ya bayyana cewa waɗanda suka yi imani, suka yi aiki nagari, ba su da wani laifi a kan abin da suka sha ko suka ci wanda Allah ya haramta, idan sun yi haka ne kafin a saukar da haramcinsa ko kafin su san haramun ne, idan har sun nisanci abin da Allah ya haramta, kuma sun yi imani da Allah, sun yi ayyuka nagari, sannan suka ɗore a kan nisantar abin da Allah ya haramta da yin imani da Allah, sannan suka kuma doge a kan nisantar haramun har suka kai matakin ihsani, wato kyautayi, Allah kuwa yana son bayinsa masu kyautatawa. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na kasance ni ne mai shayar da mutane giya a gidan Abu Ɗalha, a lokacin suna yin giya ne da niƙaƙƙen dabino. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya umarci mai shela ya yi shela cewa, an haramta giya. Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: “Fita waje ka kwarar da ita.” Sai na fita na kwarar da ita, har ta riƙa gudana a hanyoyin Madina. Sai wasu mutane suka riƙa cewa: “Ga shi an kashe wasu mutane da giya a cikinsu.” Sai Allah ya saukar da wannan ayar ta 93.” [Bukhari #2464, da Muslim #1980].

  94. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَيَبۡلُوَنَّكُمُ ٱللَّهُ بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلصَّيۡدِ تَنَالُهُۥٓ أَيۡدِيكُمۡ وَرِمَاحُكُمۡ لِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَخَافُهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 5:94

    Ya ku waɗanda suka yi imani, lalle Allah zai jarrabe ku da wani abu na farauta, wanda hannayenku da masunku za su kai gare shi, don Allah Ya bayyana wanda yake jin tsoron Sa alhalin bai gan Shi ba. Don haka duk wanda ya ƙetare iyaka bayan haka, to lalle yana da azaba mai raɗaɗi.

  95. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡتُلُواْ ٱلصَّيۡدَ وَأَنتُمۡ حُرُمٞۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآءٞ مِّثۡلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحۡكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ هَدۡيَۢا بَٰلِغَ ٱلۡكَعۡبَةِ أَوۡ كَفَّٰرَةٞ طَعَامُ مَسَٰكِينَ أَوۡ عَدۡلُ ذَٰلِكَ صِيَامٗا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمۡرِهِۦۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَۚ وَمَنۡ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنۡهُۚ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ

    Open ayah 5:95

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku kashe abin farauta alhali kuna cikin Harami. Duk kuwa wanda ya kashe shi daga cikinku da gangan, to sakamakonsa shi ne (ya bayar) da kwatankwacin abin da ya kashe cikin dabbobin gida; waɗanda za su yi hukunci da wannan su ne mutum biyu adalai a cikinku, a matsayin hadaya wadda za ta isa Ka’aba, ko kuma ya yi kaffarar ciyar da miskinai, ko kuma ya yi azumi na kwatankwacin haka, don ya ɗanɗani kuɗar lamarinsa. Allah Ya yi afuwa dangane da abin da ya wuce. Duk kuwa wanda ya sake komawa, to Allah zai yi masa uƙuba. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma’abocin uƙuba.

  96. أُحِلَّ لَكُمۡ صَيۡدُ ٱلۡبَحۡرِ وَطَعَامُهُۥ مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِلسَّيَّارَةِۖ وَحُرِّمَ عَلَيۡكُمۡ صَيۡدُ ٱلۡبَرِّ مَا دُمۡتُمۡ حُرُمٗاۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

    Open ayah 5:96

    An halatta muku yin farautar naman ruwa da abincin cikinsa, don jin daɗi a gare ku da kuma matafiya; amma an haramta muku farautar naman daji matuƙar kuna cikin Harami. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda zuwa gare Shi za a tattara ku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa muminai cewa zai jarrabe su, lokacin da suke sanye da Harami na hajji ko na umara, da wani abin farauta wanda za su iya kamawa da hannuwansu ko su farauce shi da masunsu. Allah zai yi musu wannan jarrabawar ne don ya tantance mai jin tsoron sa duk da cewa ba ya ganin sa ido-da-ido, ko kuma ana nufin wanda yake tsoron Allah duk da ba ya cikin jama’a, wato yana shi kaɗai. Duk wanda ya ƙetare iyakokin Allah da dokokin da ya gindaya a kan sha’anin farauta, ya yi farauta alhali yana sanye da Harami, ko yana cikin Harami, to ya saɓa wa shari’a, kuma zai gamu da azaba mai raɗaɗi. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana hukuncin kashe abin farauta ga masu sanye da Harami, ko suke cikin yankin Harami, da gangan da cewa, wajibi ne su yanka wata dabba mai kama da irin wadda suka kashe, kuma za a sami mutum biyu ne muminai adalai waɗanda za su kwatanta irin dabbar da zai yanka. Kuma sai ta je Haramin Makka, a can ne zai yanka ta, ya raba wa mabuƙata namanta, ko kuma ya yi kaffara ta hanyar ciyar da miskinai, ko kuma in bai ɗauki wannan ba, to ya yi azumi a madadin kowane miskini da zai ciyar. Allah ya yi wannan hukunci ne domin wanda ya saɓa wa wannan umarni ya ɗanɗani uƙubar laifin da ya yi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wani nau’i na rahamarsa ga bayinsa, watau afuwar da ya yi musu ga abin da ya riga ya wuce kafin wannan haramci, to amma fa duk wanda ya sake aikata wannan laifi bayan ya san hukuncinsa, to Allah zai yi masa uƙuba. Allah Mabuwayi ne, kuma mai uƙuba ne. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci hukuncin farautar dabbar tudu, sai kuma ya bayyana cewa farautar naman ruwa da abincin cikinsa, wanda kogi ya yi ambaliyarsa cewa halal ne ga waɗanda suke sanye da Harami, kuma halal ne ga matafiya. Farautar naman ruwa shi ne duk abin da aka kama da rai, abincin ruwa kuwa shi ne abin da ya mutu a cikin kogi wanda ya furzo shi waje, ko ya taso saman ruwa. Allah ya halatta waɗannan ne ga bayinsa lokacin zaman gida ko cikin halin tafiyar. Don haka a ko’ina suke su kiyaye dokokin Allah, wanda za a tattara su a gabansa, makomarsu gaba ɗaya kuma zuwa gare shi take, kuma zai yi musu hisabi bisa ga ayyukansu.

  97. ۞جَعَلَ ٱللَّهُ ٱلۡكَعۡبَةَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ قِيَٰمٗا لِّلنَّاسِ وَٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَٱلۡهَدۡيَ وَٱلۡقَلَٰٓئِدَۚ ذَٰلِكَ لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ

    Open ayah 5:97

    Allah Ya sanya Ka’aba ɗaki ne mai alfarma, wuri mai matuƙar amfani ga mutane, haka watanni masu alfarma, da dabbar hadaya da dabbar hadaya mai rataye. Wannan kuwa don ku sani cewa, lalle Allah Ya san abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa, kuma lalle Allah Masanin komai ne.

  98. ٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ وَأَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 5:98

    Ku sani lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

  99. مَّا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُبۡدُونَ وَمَا تَكۡتُمُونَ

    Open ayah 5:99

    Babu abin da yake kan Manzo sai isarwa. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuke ɓoyewa.

  100. قُل لَّا يَسۡتَوِي ٱلۡخَبِيثُ وَٱلطَّيِّبُ وَلَوۡ أَعۡجَبَكَ كَثۡرَةُ ٱلۡخَبِيثِۚ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ يَٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ 

    Open ayah 5:100

    Ka ce: “Mummuna da kyakkyawa ba za su taɓa zama daidai ba, ko da kuwa yawan mummunan ya burge ka.” Don haka ku kiyaye dokokin Allah, ya ku ma’abota hankali, don ku sami rabauta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa ya sanya Ka’aba ɗaki mai alfarma, wani wuri mai amfani ga mutane inda suke samun biyan buƙatunsu na addini, kamar hajji da umara da salloli da ɗawafi da kuma sauran amfanin duniya, kamar gudanar da harkar kasuwanci da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun sanayya da taimakon juna a tsakanin Musulmi. Hakanan ya sanya wata mai alfarma wanda a cikinsa mutane suna samun aminci da kwanciyar hankali saboda haramta yaƙe-yaƙe a cikinsa. Hakanan da hadaya da dabbobi, kamar raƙuma da shanu da ƙananan dabbobi da waɗanda aka yi musu alamomi na musamman domin nuna keɓance su don bautar Allah. Dukkansu Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya su ababen kusantar sa da su ne, kuma mutane suna amfana da su tare da cim ma wasu buƙatunsu ta hanyarsu. Allah ya yi haka ne don mutane su san cewa, yana sane da abin da yake cikin sama da wanda yake ƙasa, don haka shi ne ya fi kowa sanin abin da yake maslaha ga bayinsa a addininsu da rayuwarsu, kuma Allah masanin komai ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da mutane uƙubarsa, ya kuma kwaɗaitar da su ladansa, ya umarce su da su san cewa shi mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya saɓa masa, kuma mai gafara ne ga wanda ya tuba ya koma gare shi, zai yafe masa laifukansa, kuma shi mai rahama ne ga bayinsa. Ya ƙara da cewa babu wani abu da ya rataya a wuyan Annabi (ﷺ) sai isar da saƙon da aka aiko shi da shi, kuma bai yi ƙasa a gwiwa ba, sai da ya isar da duk wani saƙo da aka umarce shi da ya isar. Kuma Allah yana sane da abin da bayinsa suke bayyanawa da wanda suke ɓoyewa na ayyukansu, kuma duk zai yi musu sakayya a kansu. Sai ya umarci Annabinsa da ya faɗa wa mutane cewa, mummuna da kyakkyawa ba za su taɓa zama daidai ba, ko da yawan mummunan yana burge mutum. Don haka, ya yi kira ga masu lafiyayyun hankula kan su kiyaye dokokin Allah domin su sami abin da suke fatan su samu, su kuma kuɓuta daga abin da suke ƙi duniya da lahira.

  101. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَسۡـَٔلُواْ عَنۡ أَشۡيَآءَ إِن تُبۡدَ لَكُمۡ تَسُؤۡكُمۡ وَإِن تَسۡـَٔلُواْ عَنۡهَا حِينَ يُنَزَّلُ ٱلۡقُرۡءَانُ تُبۡدَ لَكُمۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهَاۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ 

    Open ayah 5:101

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku yi tambaya game da waɗansu al’amurra, waɗanda idan aka bayyana muku su za su dame ku, idan kuwa kuka riƙa tambaya game da su yayin da Alƙur’ani yake sauka, za a bayyana muku su; Allah Ya yi rangwame game da su. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai haƙuri.

  102. قَدۡ سَأَلَهَا قَوۡمٞ مِّن قَبۡلِكُمۡ ثُمَّ أَصۡبَحُواْ بِهَا كَٰفِرِينَ 

    Open ayah 5:102

    Haƙiƙa waɗansu mutane gabaninku sun yi irin wannan tambayar, sannan suka wayi gari suna kafirce mata.

  103. مَا جَعَلَ ٱللَّهُ مِنۢ بَحِيرَةٖ وَلَا سَآئِبَةٖ وَلَا وَصِيلَةٖ وَلَا حَامٖ وَلَٰكِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَأَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ 

    Open ayah 5:103

    Allah bai sanya wata dabba bahîra ba ko sá’iba ko wasîla ko hám ba, sai dai waɗanda suka kafirta suna ƙirƙirar ƙarya su jingina wa Allah; kuma yawancinsu ba sa hankalta.

  104. وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَإِلَى ٱلرَّسُولِ قَالُواْ حَسۡبُنَا مَا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ءَابَآؤُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ شَيۡـٔٗا وَلَا يَهۡتَدُونَ 

    Open ayah 5:104

    Kuma idan aka ce da su: “Ku taho zuwa ga abin da Allah Ya saukar da kuma zuwa ga Manzo,” sai su ce: “Abin da muka sami iyayenmu a kai ya ishe mu.” Yanzu ko da iyayen nasu sun kasance ba su san komai ba, kuma ba sa shiryuwa?

  105. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ عَلَيۡكُمۡ أَنفُسَكُمۡۖ لَا يَضُرُّكُم مَّن ضَلَّ إِذَا ٱهۡتَدَيۡتُمۡۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ 

    Open ayah 5:105

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi ta kanku; wanda ya ɓata, ba zai cutar da ku ba idan har ku kun shiryu. Zuwa ga Allah ne makomarku take gaba ɗaya, sannan kuma zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa muminai kashedi game da yawan tambaya a kan wasu abubuwa da ba a saukar da hukunci a kansu ba; yin hakan zai jawo Allah ya bayyana musu wani hukuncin da ba zai yi musu daɗi ba. Amma idan sun yi tambayar ne a kan wani abu da Allah ya riga ya saukar musu da hukuncinsa a Alƙur’ani, to babu wata matsala a nan, saboda sun yi tambaya ne a kan gaɓa, sai Allah ya bayyana musu abin da suke tambaya a kansa. Allah ya yafe musu laifin tambayoyin da suka riƙa yi a baya. Allah mai gafara ne, mai haƙuri da bayinsa. An karɓo daga Anas (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce: “Wata rana Annabi (ﷺ) ya sami wani labari game da sahabbansa, sai ya je ya yi musu huɗuba. Ya ce: “An nuna mini Aljanna da wutar Jahannama, ban taɓa ganin wani alheri da wani sharri irin na yau ba. Da a ce kun san abin da na sani, da kun yi dariya ‘yar kaɗan, kun yi kuka mai yawa.” Anas ya ce: “Sahabban Manzon Allah (ﷺ) ba su taɓa shiga wani tsanani irin wannan rana ba, sai suka lulluɓe kawunansu suna kuka. Sai Umar ya miƙe tsaye ya ce: “Mun yarda da Allah ne Ubangiji, Musulunci ne addini, kuma Muhammadu Annabi ne.” Sai kuma wani mutum shi ma ya miƙe tsaye ya ce: “Wane ne babana?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Wane shi ne babanka.” Sai wannan ayar ta sauka. [Bukhari #7295, da Muslim #2359]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane, Allah ya wajabta muku aikin Hajji, don haka ku je ku yi hajji.” Sai wani mutum ya yi tambaya cewa: “A kowace shekara ne ya Manzon Allah?” Sai Manzon Allah ya yi shiru. Ya sake tambayar sa har sau uku, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Da na ce na’am, to da ta zama wajibi (wato hajji duk shekara), da kuma ba za ku iya ba.” Sannan ya ce: “Ku ƙyale ni matuƙar na ƙyale ku, domin waɗanda suka gabace ku sun halaka ne a dalilin yawan tambayoyinsu da sassaɓa wa annabawansu, don haka idan na umarce ku da wani abu, to ku aikata shi gwargwadon ikonku; idan kuma na hana ku abu, to ku nisance shi.” [Muslim #1337]. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Musulmin da ya fi kowa girman laifi shi ne wanda ya yi tambaya a kan wani abu da ba a haramta shi ba, sai aka haramta shi saboda tambayarsa.” [Bukhari #289, da Muslim #2358]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa wasu mutane da suka gabace su sun riƙa yin irin waɗannan tambayoyin da aka hana su, bayan an amsa musu tambayoyinsu sai suka kafirce wa amsoshin da aka ba su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin wasu ayyukan na kafirci da Larabawa suke yi kafin zuwan Musulunci. Sun riƙa ware wasu dabbobi suna haramta wa kawunansu cin namansu ko hawansu; daga cikinsu akwai: • <b>Bahira </b> , Ita ce taguwar da suka tsaga kunnuwanta saboda ta haihu har sau biyar, to namanta ya zama haramun ga mata suci, kuma nononta ya zama na gumaka, babu mai tatsar ta. • <b>Sa’iba </b> , ita ce taguwar da mai ita yake bar wa gumaka ita, yayin da ya yi bakance da cewa, idan ya dawo daga tafiyarsa lafiya, ko idan ya yi rashin lafiya ya ce idan ya warke daga rashin lafiyarsa, to zai ware wa gumaka wata taguwa wadda ba za a yanka ta a ci ba, kuma ba za a ɗora mata kaya ba; za a bar ta ta yi kiwo a duk inda take so, ta sha ruwan da take so, ba mai hana ta. • <b>Wasila </b> , ita ce dabbar da ta yi haihuwa bakwai, idan na bakwan ya zama namiji ne, to sai a yanka shi maza da mata su ci namansa, idan mace ce, sai su ƙyale ta, idan kuwa tagwaye ta Haifa; mace da namiji, sai su ce, macen ta ceci ɗan’uwanta, sai a ƙyale su duka biyun, namansu ya haramta ga mata, nonon tamacen ma ya haramta ga mata, sai idan sun mutu, to maza da mata suna iya cin namansu. • <b>Hamu </b> , shi ne namijin garke wanda aka haifi ‘ya’ya goma daga tsatsonsa, to shi ma suna cewa ya ‘yanta bayansa, sai a bar shi ga gumaka, ba a ɗora masa kaya, ba a hawansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, duk waɗannan hukunce-hukunce nasu ba daga Allah suke ba; ƙarya ce suka ƙirƙira kuma suka riƙa jingina wa Allah, kuma da dama daga cikinsu ba su da hankali. Idan aka ce musu, su zo ga Littafin Allah da Manzonsa (ﷺ) don ya bayyana musu addinin Allah da shari’arsa, sai kawai su amsa da cewa, abin da suka sami iyayensu a kai ya ishe su. To ta yaya za su riƙa faɗar irin wannan zance, duk da cewa iyayensu jahilai ne, ba su san komai ba, ɓatattu ne, ba su san shiriya ba? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, idan har su suka tsaya a kan abin da Allah ya umarce su da shi, to duk wanda ya zaɓi ya kama hanyar ɓata ba zai cuce su da komai ba; makomarsu gaba ɗaya zuwa ga Allah ne, kuma zai ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa.

  106. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ شَهَٰدَةُ بَيۡنِكُمۡ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ حِينَ ٱلۡوَصِيَّةِ ٱثۡنَانِ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ أَوۡ ءَاخَرَانِ مِنۡ غَيۡرِكُمۡ إِنۡ أَنتُمۡ ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةُ ٱلۡمَوۡتِۚ تَحۡبِسُونَهُمَا مِنۢ بَعۡدِ ٱلصَّلَوٰةِ فَيُقۡسِمَانِ بِٱللَّهِ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ لَا نَشۡتَرِي بِهِۦ ثَمَنٗا وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰ وَلَا نَكۡتُمُ شَهَٰدَةَ ٱللَّهِ إِنَّآ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡأٓثِمِينَ 

    Open ayah 5:106

    Ya ku waɗanda suka yi imani, shaidar da take tsakaninku idan alamun mutuwa suka zo wa ɗaya daga cikinku, yayin da ya so ya yi wasiyya, shi ne a samu mutum biyu masu adalci daga cikinku ko kuma waɗansu biyu daga wasunku (kafirai), yayin da kuka yi tafiya a bayan ƙasa, sai musibar mutuwa ta same ku. Za ku tsayar da su (shaidun) biyun ne bayan an kammala salla, sai su rantse da Allah- idan har kun yi shakka game da su-: “Wallahi, ba za mu musanya shi da wani farashi ba, ko da kuwa ya zamo ma’abocin kusanci ne, kuma ba za mu ɓoye shaidar Allah ba, lalle kuwa idan har muka yi haka, tabbas muna cikin masu laifi.”

  107. فَإِنۡ عُثِرَ عَلَىٰٓ أَنَّهُمَا ٱسۡتَحَقَّآ إِثۡمٗا فَـَٔاخَرَانِ يَقُومَانِ مَقَامَهُمَا مِنَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَحَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَوۡلَيَٰنِ فَيُقۡسِمَانِ بِٱللَّهِ لَشَهَٰدَتُنَآ أَحَقُّ مِن شَهَٰدَتِهِمَا وَمَا ٱعۡتَدَيۡنَآ إِنَّآ إِذٗا لَّمِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ 

    Open ayah 5:107

    Amma idan an gano cewa su biyun sun yi laifi, sai a nemi mutum biyu su tsaya su yi shaida a madadin waɗancan daga cikin waɗanda suka cancanta su ci gadonsa, sai su rantse da Allah: “Wallahi, shaidarmu ta fi shaidarsu, kuma wallahi ba mu ƙetare iyaka ba, lalle kuwa idan mun yi haka, tabbas da mun zama cikin azzalumai.”

  108. ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن يَأۡتُواْ بِٱلشَّهَٰدَةِ عَلَىٰ وَجۡهِهَآ أَوۡ يَخَافُوٓاْ أَن تُرَدَّ أَيۡمَٰنُۢ بَعۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱسۡمَعُواْۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ 

    Open ayah 5:108

    Yin haka shi ne ya fi kusa da su kawo shaida kamar yadda take, ko su ji tsoron a mayar da wannan shaidar bayan rantsuwarsu. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku saurari (umarninsa), kuma Allah ba Ya shiryar da mutanen da suke fasiƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana magana da muminai ne yayin da ɗayansu mutuwa ta zo masa, ya rubuta wasiyyarsa ta ƙarshe, to lalle a sami muminai biyu adalai su yi shaida a kai; idan kuwa a cikin halin tafiya ne mutuwar ta zo masa, kuma bai sami Musulmai masu yi masa shaidar ba, to sai ya sanya waɗanda ba Musulmi ba su zama shaida. To Musulmi za su tsayar da waɗannan shaidu waɗanda ba Musulmi ba, bayan sallar la’asar. Idan ana da shakka a kan shaidarsu ko aka ga wasu alamu da za su hana a nutsu da su, sai a nemi su yi rantsuwa da Allah cewa babu wani abu na duniya da suke nema da zai sa har su yi ƙarya, kuma ba za su yi wa wani ƙarya ba ko da ɗan’uwansu ne makusanci, ba kuma za su ɓoye wata shaida da suke tare da ita ba, kuma in har sun aikata haka, to sun tabbata daga cikin masu laifi. To idan daga baya an gano cewa sun faɗi ƙarya a shaidarsu ko sun canza wasiyyar mamacin ko sun ɓoye wani abu, to sun zama masu laifi, sai a sami wasu mutanen biyu daga cikin magadan mamaci, su tsaya a madadin waɗancan mutane biyu na farko, su rantse da Allah cewa shaidarsu ta fi shaidar waɗancan da ba Musulmi ba inganci, kuma ba su ƙetare iyaka ba wajen bayar da tasu shaidar ko zargin shaidar waɗancan da ba Musulmi ba, domin idan har sun yi musu ƙarya, to su ma sun zama azzalumai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, neman shaidun nan biyu su rantse yayin da ake da shakka a kansu, shi ne zai sa a samu kyakkyawar shaida mai inganci da babu ƙarya a cikinta kuma babu ha’inci. Sai kuma Allah ya umarci bayinsa da su ji tsoron sa ta hanyar kiyaye dokokinsa, kuma su saurari abin da ake umartar su da shi, su yi aiki da shi. Ya kuma nuna cewa ba ya datar da mutanen da suke fasiƙai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani mutum ɗan ƙabilar Banu Sahmin sun yi tafiya tare da Tamimuddari (lokacin bai musulunta ba) tare da Adiyyu ɗan Badda’u, sai wannan mutumin ya rasu a wani gari wanda babu Musulmi a cikinsa. Lokacin da aka kawo kayansa na gado, sai magadansa ba su ga wani ƙoƙon azurfa wanda aka yi masa kwalliya da zinari a cikin kayan ba. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya nemi Tamimuddari da Adiyyu da su rantse. Sai suka rantse. Daga baya aka gano wannan ƙoƙon a wurin wasu mutane a Makka, da aka tambaye su, ko ina suka same shi? Sai suka ce, sayensa suka yi a hannun Tamimuddari da Adiyyu. Sai mutum biyu cikin magadan wannan mamacin suka tashi tsaye suka yi rantsuwa cewa shaidarsu ta fi shaidar su Tamimuddari, kuma wannan ƙoƙo na ɗan’uwansu ne da ya mutu.” Abdullahi ɗan Abbas ya ce: “A kansu ne wannan aya ta 106 ta sauka.” [Dubi, Bukhari #2780]. An karɓo daga Amiru Assha’abi ya ce: Wani mutum mutuwa ta same shi a wani gari da ake kira Daƙuƙa’u , bai sami Musulmi da zai kafa shaida a kan wasiyyarsa ba, sai ya shaidar da wasu mutane biyu daga cikin Ma’abota Littafi. Da suka kawo kayan gadon da ya bari wurin Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda), sai suka ba shi labarin abin da ya faru. Sai Abu Musa Al-Ash’ari ya ce: “Wannan al’amari tun sa’adda ya faru a zamanin Manzon Allah (ﷺ) bai sake faruwa ba sai yanzu.” Sai ya saka su suka yi rantsuwa da Allah bayan sallar La’asar cewa, ba su ci amana ba kuma ba su faɗi ƙarya ba kuma ba su canza wasiyya ba; wannan kayan da suka kawo su ne abin da ya mutu ya bari. Sai Abu Musa ya zartar da shaidarsu. [Abu Dawud #3605].

  109. ۞يَوۡمَ يَجۡمَعُ ٱللَّهُ ٱلرُّسُلَ فَيَقُولُ مَاذَآ أُجِبۡتُمۡۖ قَالُواْ لَا عِلۡمَ لَنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّٰمُ ٱلۡغُيُوبِ 

    Open ayah 5:109

    (Ka tuna) ranar da Allah zai tara manzanni, sannan Ya ce: “Da me aka ba ku amsa?” sai su ce: “Ba mu da wata masaniya; lalle Kai ne kaɗai Masanin abubuwan da suke ɓoye.”

  110. إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱذۡكُرۡ نِعۡمَتِي عَلَيۡكَ وَعَلَىٰ وَٰلِدَتِكَ إِذۡ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِ تُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗاۖ وَإِذۡ عَلَّمۡتُكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَۖ وَإِذۡ تَخۡلُقُ مِنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ بِإِذۡنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِيۖ وَتُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ تُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ كَفَفۡتُ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ عَنكَ إِذۡ جِئۡتَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ 

    Open ayah 5:110

    (Ka tuna) lokacin da Allah zai ce: “Ya kai Isa ɗan Maryamu, ka tuna ni’imata da Na yi maka kai da mahaifiyarka, yayin da Na ƙarfafe ka da Ruhi mai tsarki, kana yi wa mutane magana lokacin kana cikin zanin goyo, da kuma lokacin da kake dattijo, kuma ka tuna lokacin da Na koyar da kai rubutu da hikima da Attaura da Linjila. Kuma ka tuna lokacin da kake ƙirƙirar (wani abu) kamar tsuntsu da taɓo da izinina, sai ka yi busa a cikinsa, sai ya zamo tsuntsu da izinina; kuma kake warkar da wanda aka haifa da makanta da mai albaras da izinina; kuma ka tuna lokacin da kake fito da matattu (daga cikin ƙaburburansu) da izinina; kuma ka tuna lokacin da Na kare ka (daga cutar) Bani Isra’ila yayin da ka zo musu da hujjoji bayyanannu, sai waɗanda suka kafirta daga cikinsu suka ce: “Ai wannan ba komai ba ne face sihiri mabayyani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wasu al’amura da za su faru a ranar Alƙiyama lokacin da zai tattara manzanni wuri guda ya tambaye su irin amsar da suka samu daga al’ummominsu bayan sun isar musu da kiran Allah. Sai manzanni su ba da amsa da cewa ba su da wani ilimi dangane da haka, Allah shi ne masanin gaibu. Sai kuma ya bayyana abin da ya faɗa wa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa: “Ya kai Isa ɗan Maryam, ka tuna ni’imar da na yi maka kai da mahaifiyarka, lokacin da na taimake ka, na ƙarfafe ka da Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kana magana da mutane tun kana ɗan ƙaraminka da kuma lokacin girmanka. Kuma ka tuna lokacin da na koyar da kai rubutu; na ba ka fahimtar sirrukan shari’a, na koyar da kai littafin Attaura da littafin Linjila. Kuma ka tuna lokacin da kake mulmula wani abu mai kama da tsuntsu da taɓo da izinina, sai kuma ka yi busa a cikinsa, sai ya zama tsuntsu mai rai da izinina. Kuma ka riƙa warkar da wanda aka haifa makaho da mai cutar albaras da izinina; kuma kake fito da matattu da ransu daga ƙaburburansu da izinina. Kuma na kare ka daga sharrin Banu Isra’ila lokacin da suka so kashe ka yayin da ka zo musu da hujjoji bayyanannu, sai kafiran cikinsu suka ce maka, abin da ka zo da shi sihiri ne a bayyane.”

  111. وَإِذۡ أَوۡحَيۡتُ إِلَى ٱلۡحَوَارِيِّـۧنَ أَنۡ ءَامِنُواْ بِي وَبِرَسُولِي قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَٱشۡهَدۡ بِأَنَّنَا مُسۡلِمُونَ

    Open ayah 5:111

    Kuma ka tuna lokacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawariyyawa: “Ku yi imani da Ni da Manzona,” sai suka ce: “Mun yi imani, kuma Ka shaida cewa, mu Musulmai ne.”

  112. إِذۡ قَالَ ٱلۡحَوَارِيُّونَ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ هَلۡ يَسۡتَطِيعُ رَبُّكَ أَن يُنَزِّلَ عَلَيۡنَا مَآئِدَةٗ مِّنَ ٱلسَّمَآءِۖ قَالَ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

    Open ayah 5:112

    Lokacin da Hawariyyawa suka ce: “Ya Isa ɗan Maryamu, shin Ubangijinka Yana iya saukar mana da kaɓaki daga sama?” Ya ce: “Ku kiyayi Allah, idan har kun kasance muminai.”

  113. قَالُواْ نُرِيدُ أَن نَّأۡكُلَ مِنۡهَا وَتَطۡمَئِنَّ قُلُوبُنَا وَنَعۡلَمَ أَن قَدۡ صَدَقۡتَنَا وَنَكُونَ عَلَيۡهَا مِنَ ٱلشَّٰهِدِينَ

    Open ayah 5:113

    Suka ce: “Mu muna nufin mu ci daga gare shi, kuma zukatanmu su sami nutsuwa, sannan mu haƙiƙance cewa, lalle ka faɗa mana gaskiya, kuma mu zamo masu ba da shaida a kansa.”

  114. قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ ٱللَّهُمَّ رَبَّنَآ أَنزِلۡ عَلَيۡنَا مَآئِدَةٗ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ تَكُونُ لَنَا عِيدٗا لِّأَوَّلِنَا وَءَاخِرِنَا وَءَايَةٗ مِّنكَۖ وَٱرۡزُقۡنَا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ

    Open ayah 5:114

    Isa ɗan Maryamu ya ce: “Ya Allah Ubangijinmu, Ka saukar mana da kaɓaki daga sama, wanda zai zame mana wani Idi, ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zamo wata aya daga gare Ka; kuma Ka arzuta mu, lalle Kai ne Fiyayyen masu arzutawa.”

  115. قَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مُنَزِّلُهَا عَلَيۡكُمۡۖ فَمَن يَكۡفُرۡ بَعۡدُ مِنكُمۡ فَإِنِّيٓ أُعَذِّبُهُۥ عَذَابٗا لَّآ أُعَذِّبُهُۥٓ أَحَدٗا مِّنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 5:115

    Allah Ya ce: “Lalle Ni Mai saukar muku da shi (kaɓakin) ne; amma duk wanda ya kafirta daga baya cikinku, to lalle Ni zan yi masa wata irin azaba wadda ba zan taɓa azabtar da wani daga cikin halittu irinta ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabinsa Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mabiyan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi da yadda ya kimsa wa zaɓaɓɓun cikinsu, su ne Hawariyyawa, da su yi imani da Allah (Mai tsarki da daukaka) da Manzonsa Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai suka shelanta imaninsu, suka neme shi ya zamo shaidarsu a kan su Musulmi ne masu miƙa wuya. Sannan ya tunatar da shi lokacin da Hawariyyawa suka tambaye shi cewa, idan ya roƙi Ubangijinsa ya saukar musu da kaɓakin abinci daga sama, zai iya yi masa haka? Sai Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ja kunnensu da cewa, lalle su ji tsoron Allah, su daina kawo irin waɗannan buƙatu idan har da gaske su muminai ne. Sai suka amsa masa da cewa, su suna so ne su ci daga wannan kaɓaki domin zukatansu su ƙara samun nutsuwa, su ƙara fahimtar cewa Annabi Isa mai gaskiya ne a kan abin da ya zo musu da shi, kuma su zama shaida a kan wannan mu’ujizar da za su gani da idanunsu cewa lalle daga Allah take, kuma su isar da labarinta ga sauran mutane. To sai Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi addu’a, ya roƙi Allah a kan ya saukar musu da wani kaɓaki daga sama da zai zama musu idi gare su da waɗanda za su zo daga baya, kuma ya zama wani dalili wanda yake nuna Ɗayantakar Allah (Mai tsarki da daukaka), yake kuma tabbatar da gaskiyar abin da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo da shi, kuma Allah ya arzuta su domin shi ne Fiyayyen masu arzutawa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa masa da cewa, zai saukar musu da wannan kaɓaki da suka nema, amma kuma duk wanda ya kafirce masa bayan ya saukar da shi, to fa zai gamu da wata matsananciyar azaba wadda wani a cikin halittun Allah bai taɓa shan irinta ba.

  116. وَإِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ءَأَنتَ قُلۡتَ لِلنَّاسِ ٱتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيۡنِ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالَ سُبۡحَٰنَكَ مَا يَكُونُ لِيٓ أَنۡ أَقُولَ مَا لَيۡسَ لِي بِحَقٍّۚ إِن كُنتُ قُلۡتُهُۥ فَقَدۡ عَلِمۡتَهُۥۚ تَعۡلَمُ مَا فِي نَفۡسِي وَلَآ أَعۡلَمُ مَا فِي نَفۡسِكَۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّٰمُ ٱلۡغُيُوبِ

    Open ayah 5:116

    Kuma (ka tuna) lokacin da Allah zai ce: “Ya kai Isa ɗan Maryamu, shin kai ne ka ce da mutane: ‘Ku riƙe ni, ni da mahaifiyata a matsayin alloli biyu ban da Allah?’” Sai ya ce: “Tsarki ya tabbata gare Ka, bai dace ba a gare ni in faɗi wani abu wanda ba ni da haƙƙin (faɗar sa). Idan har na faɗe shi, to haƙiƙa Ka riga Ka sani, Ka san abin da yake cikin raina, amma ni ban san abin da yake ranka ba. Lalle Kai ne Masanin abubuwan da suke ɓoye.

  117. مَا قُلۡتُ لَهُمۡ إِلَّا مَآ أَمَرۡتَنِي بِهِۦٓ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۚ وَكُنتُ عَلَيۡهِمۡ شَهِيدٗا مَّا دُمۡتُ فِيهِمۡۖ فَلَمَّا تَوَفَّيۡتَنِي كُنتَ أَنتَ ٱلرَّقِيبَ عَلَيۡهِمۡۚ وَأَنتَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

    Open ayah 5:117

    “Ban faɗa musu komai ba sai abin da Ka umarce ni da shi, cewa: ‘Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku.’ Kuma na kasance mai sa ido a kansu lokacin da nake cikinsu. Amma yayin da Ka karɓi rayuwata, Ka zama Kai ne Mai kula da su. Kuma lalle Kai Mai kula ne a kan komai.

  118. إِن تُعَذِّبۡهُمۡ فَإِنَّهُمۡ عِبَادُكَۖ وَإِن تَغۡفِرۡ لَهُمۡ فَإِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 5:118

    “Idan har Ka azabtar da su, haƙiƙa su bayinka ne; idan kuwa Ka yafe musu, to lalle Kai Mabuwayi ne, Mai hikima.”

  119. قَالَ ٱللَّهُ هَٰذَا يَوۡمُ يَنفَعُ ٱلصَّٰدِقِينَ صِدۡقُهُمۡۚ لَهُمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

    Open ayah 5:119

    Allah zai ce: “Wannan ita ce rana wadda gaskiya za ta amfani masu ita. Suna da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su dawwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, su kuma sun yarda da Shi. Wannan shi ne rabo mai girma.”

  120. لِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا فِيهِنَّۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرُۢ 

    Open ayah 5:120

    Mulkin sammai da ƙasa da abin da yake cikinsu na Allah ne. Kuma Shi Mai iko ne a kan komai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana abin da zai faru tsakaninsa da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a gaban Nasara mabiya addininsa, lokacin da Allah zai tambaye shi cewa, shi ne da mahaifiyarsa suka nemi mutane su riƙa bauta musu ba (bautar) Allah ba? Nan take Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zai ba da amsa da fara tsarkake Ubangijinsa daga duk abin da bai dace ba shi ba, cewa ba zai taɓa yiwuwa a gare shi ba ya faɗi abin da ba haƙƙinsa ba; idan kuwa har ya faɗa, to ai Allah ya sani, domin babu abin da yake ɓuya a gare shi, ya san abin da yake ɓoyewa a ransa, amma shi bai san abin da yake a ransa ba, shi ne masanin duk wani abu da yake ɓoye. Ya tabbatar wa Ubangiji cewa, ba abin da ya faɗa musu, face su bauta masa, domin shi ne Ubangijinsa, kuma Ubangijinsu. Kuma lokacin da yake tare da su yana ganin duk ayyukansu; amma yayin da Allah ya karɓe shi ta hanyar ɗaukarsa zuwa sama, shi kaɗai ya san abin da suke ciki, kuma shi ne mai shaida a kan komai. Idan Allah ya ga dama yana iya azabtar da su domin su bayinsa ne; idan kuma ya gafarta musu, to da ma shi mabuwayi ne, mai hikima cikin ayyukansa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi Muhammadu (ﷺ) ya karanta faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka) game da faɗar Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa: “Ya Ubangijina, lalle su (gumaka) sun ɓatar da mutane da yawa, don haka wanda ya bi ni, to shi nawa ne, wanda kuwa ya saɓa mini, to kai mai yawan gafara ne, mai yawan jin ƙai.” Sai kuma ya karanta ayar da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake cewa: “Idan kuwa ka yi musu azaba, to lalle su bayinka ne, idan kuwa ka yi musu gafara, to lalle kai ne mabuwayi mai hikima.” Sai Annabi Muhammadu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ɗaga hannuwansa sama ya ce: “Ya Allah, al’ummata, al’ummata!” Sai ya fashe da kuka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce da Jibrilu: “Ya Jibrilu, ka je wurin Muhammadu (Ubangijinka ya fi sanin halin da yake ciki), ka tambaye shi, me ya sa ka kuka?” Jibrilu ya zo ya tambaye shi. Sai Annabi (ﷺ) ya faɗa wa Jibrilu abin da Allah ya faɗa (a waɗannan ayoyi biyu). Sai Allah ya ce: “Ya Jibrilu, je ka wajen Muhammadu ka faɗa masa cewa, mu za mu yi maka abin da zai yardar da kai game da al’ummarka, ba za mu ɓata maka rai ba.” [Muslim #202]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa wa Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa, wannan rana wadda ita ce ranar alƙiyama, ita ce ranar da gaskiyar masu gaskiya za ta amfane su, suna da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, masu zama ne a cikinsu har abada, Allah ya yarda da su, su ma sun yarda da shi. Wannan shi ne babban rabo. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi kaɗai yake da mulkin sammai da ƙassai da abin da yake cikinsu, kuma shi mai iko ne a kan komai.