الأنعام
Al-An'aam
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَجَعَلَ ٱلظُّلُمَٰتِ وَٱلنُّورَۖ ثُمَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡ يَعۡدِلُونَ
Open ayah 6:1Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Wanda Ya halicci sammai da ƙasa, kuma Ya halicci duffai da haske; sannan waɗanda suka kafirta suna daidaita Ubangijinsu da (wasu).
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن طِينٖ ثُمَّ قَضَىٰٓ أَجَلٗاۖ وَأَجَلٞ مُّسَمًّى عِندَهُۥۖ ثُمَّ أَنتُمۡ تَمۡتَرُونَ
Open ayah 6:2Shi ne Wanda Ya halicce ku daga taɓo, sannan Ya yanka (muku) ajali; da kuma wani ajalin sananne a wurinsa; sannan sai ga shi kuna jayayya.
وَهُوَ ٱللَّهُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَفِي ٱلۡأَرۡضِ يَعۡلَمُ سِرَّكُمۡ وَجَهۡرَكُمۡ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡسِبُونَ
Open ayah 6:3Kuma Shi ne Allah a cikin sammai da kuma cikin ƙasa; Yana sane da abin da kuke ɓoyewa da abin da kuke bayyanawa, kuma Yana sane da abin da kuke aikatawa. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da bayyana cikakken yabo da godiya marar iyaka ta tabbata gare shi shi kaɗai, domin shi ne wanda ya halicci sammai da ƙasa, kuma ya halicci duffai da haske; wannan ya ƙunshi duhun dare da hasken yini da duhun jahilci da hasken ilimi da duhun shirka da saɓon Allah da hasken imani da ɗa’a ga Allah. Amma duk da haka kafirai suna daidaita Allah da wasu abubuwan da suke bauta wa, duk kuwa da cewa sun yarda waɗannan ba su halicci komai ba. Sannan ya bayyana cewa, shi ne ya halicci mutane da taɓo, ta hanyar halittar mahaifinsu Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya kuma iyakance musu lokacin rayuwarsu ta duniya, sannan ita ma duniya ya iyakance mata lokacinta, wanda bayan ƙarewarsa za ta gushe gaba ɗayanta; wannan lokacin kuwa babu wanda ya san shi sai Allah shi kaɗai. Bayansa kuma sai lokacin tashi daga ƙabari domin yin hisabi da saka wa kowa da ayyukansa. To amma duk da irin wannan bayani, kafirai ba su daina shakkar al’amarin lahira ba. Sai kuma ya bayyana cewa, shi ne Allah abin bauta a sammai da ƙasa, yana sane da abin da bayinsa suke ɓoyewa da wanda suke bayyanawa, kuma yana sane da duk abin da suke aikatawa na alheri ne ko na sharri, kuma yana ƙididdige shi, kuma zai yi musu sakayya a kai.
وَمَا تَأۡتِيهِم مِّنۡ ءَايَةٖ مِّنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِمۡ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ
Open ayah 6:4Kuma babu wata aya cikin ayoyin Ubangijinsu da za ta zo musu, face sai sun kasance masu bijire mata.
فَقَدۡ كَذَّبُواْ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ فَسَوۡفَ يَأۡتِيهِمۡ أَنۢبَٰٓؤُاْ مَا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 6:5To haƙiƙa sun ƙaryata gaskiya lokacin da ta zo musu; don haka da sannu labaran abin da suka kasance suna izgili da shi zai zo musu.
أَلَمۡ يَرَوۡاْ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّن قَرۡنٖ مَّكَّنَّٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَا لَمۡ نُمَكِّن لَّكُمۡ وَأَرۡسَلۡنَا ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡهِم مِّدۡرَارٗا وَجَعَلۡنَا ٱلۡأَنۡهَٰرَ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قَرۡنًا ءَاخَرِينَ
Open ayah 6:6Shin ba su ga yawan al’ummun da Muka halakar a gabaninsu ba, waɗanda Muka kafa su a banƙasa suka yi ƙarfi irin kafawar da ba Mu yi muku ba, kuma Muka aiko musu da ruwan sama a kai a kai, kuma Muka sanya ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu, sai Muka hallakar da su saboda zunubansu, kuma bayan shuɗewarsu Muka halicci wata sabuwar al’ummar daban? Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana a kan Tauhidi, wato kaɗaita shi da bauta, da kuma tashin alƙiyama, sai kuma a waɗannan ayoyi yake bayanin tabbatar da annabci, tare da bayanin halayen kafirai waɗanda duk wata hujja da wani dalili da za a kawo musu don tabbatar da kaɗaitakar Allah da gaskiyar manzanninsa, sai sun sa ƙafa su shure shi, su kuma ƙaryata gaskiya bayan ta zo musu daga Allah. To su kwana da sanin cewa, wata uƙubar Allah (Mai tsarki da daukaka) tana nan tafe a kansu, saboda izgili da shaƙiyanci da suke yi wa gaskiya da waɗanda suka zo da ita. Yanzu ashe ba su ga yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa al’ummomin da suka gabace su ba? Ba su ga yawan waɗanda Allah ya halakar a cikinsu ba, waɗanda Allah ya ba su cikakken iko a bayan ƙasa irin wanda bai ba wa waɗannan kafiran na zamanin Manzon Allah ba? Allah ya ba su ƙarfin jiki da yawan dukiya da ‘ya’ya, kamar yadda ya nuna a cikin Suratur Rum , aya ta 9-10, da Suratus Saba’i , aya ta 45. Sannan ya hore musu albarkacin ruwan sama wanda ba ya yankewa, ya sanya ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashin gidajensu. To amma duk da haka ya halaka su saboda zunubansu, ya kawo wasu mutanen daban bayansu.
وَلَوۡ نَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ كِتَٰبٗا فِي قِرۡطَاسٖ فَلَمَسُوهُ بِأَيۡدِيهِمۡ لَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 6:7Kuma in da Mun saukar maka da wani littafin a rubuce a takardu, har suka taɓa shi da hannayensu, lalle da waɗanda suka kafirta sun ce: “Wannan ba komai ba ne, face sihiri bayyananne.”
وَقَالُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ مَلَكٞۖ وَلَوۡ أَنزَلۡنَا مَلَكٗا لَّقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ ثُمَّ لَا يُنظَرُونَ
Open ayah 6:8Kuma suka ce: “Don me ba a saukar masa da mala’ika ba?” Da kuwa Mun saukar da mala’ikan, to da ta faru ta ƙare (an hallaka su), sannan ba za a saurara musu ba.
وَلَوۡ جَعَلۡنَٰهُ مَلَكٗا لَّجَعَلۡنَٰهُ رَجُلٗا وَلَلَبَسۡنَا عَلَيۡهِم مَّا يَلۡبِسُونَ
Open ayah 6:9Kuma in da Mun yo shi mala’ika ne, to lalle da Mun mayar da shi mutum, kuma da lalle Mun rikitar da su kamar yadda suka rikitar da kansu.
وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَحَاقَ بِٱلَّذِينَ سَخِرُواْ مِنۡهُم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 6:10Kuma haƙiƙa an yi wa waɗansu manzanni da suka gabace ka izgili, sai sakamakon abin da suka kasance suna yin izgili da shi ya sauka kan masu izgilin.
قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ ٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 6:11Ka ce: “Ku yi tafiya a bayan ƙasa, sannan ku duba ku ga, yaya ƙarshen lamarin masu ƙaryatawa ya kasance?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana irin yadda kafirai suka kai matuƙa wajen ƙaryata gaskiya da ƙaryata Annabi (ﷺ) wanda ya zo musu da ita, ta yadda komai ƙarfin hujjar da za su gani ba za su yi imani ba, domin idanunsu sun rufe, suna so su ga bayan Manzon Allah (ﷺ) ko ta halin ƙaƙa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi bayanin cewa, da zai saukar wa Annabi (ﷺ) maganarsa a rubuce a takarda, kafirai su kama takardar da hannunsu, to da duk da haka sai sun ci gaba da jayayya da taurin kai, da kuma sun ce wannan abu ai sihiri ne, rufa-ido ne. Kuma sun ci gaba da nuna wa Annabi (ﷺ) taurin kai, har ma suka ce wai me ya hana a saukar da wani mala’ika tare da shi, yana gaskata shi idan ya faɗi wata magana, yana taimaka masa idan ya nemi taimako? Sai Allah ya mayar musu da martani cewa, da a ce Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da mala’ika kamar yadda suke buƙata, to da tuni azabar Allah ta sauka a kansu in sun ƙi yin imani, da ba za a jinkirta musu har su tuba ba. Ubangiji kuma ya ƙara tabbatar musu cewa, babu wani amfani a saukar da wani mala’ika yana gaskata Annabi (ﷺ), yana umarnin mutane su bi shi, domin ko da ya saukar da shi ne to zai saukar da shi ne cikin surar mutum irinsu, domin su iya kusantarsa su saurari abin da yake faɗa musu ba tare da sun ji wani tsoro ba. Kuma da ya saukar da mala’ika da surarsa, da ba za su iya tsayawa suna kallon sa ba; idan kuma ya saukar da shi a kamanni irin nasu na mutane to da al’amarinsa ya sake rikice musu sun ce su ba su yarda mala’ika ne ba, kamar yadda suka sanya wa kansu rikici ba gaira-ba dalili game da sha’anin Manzon Allah (ﷺ), suka ce su ba za su yarda a aiko musu mutum irinsu ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rarrashi Annabi (ﷺ) da cewa, ai an yi wa manzannin da suka gabace shi izgili, sai Allah ya saukar da uƙubarsa a kan waɗannan masu izgilin. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗa wa waɗannan masu ƙaryata shi cewa, me zai hana su yi tafiya a bayan ƙasa, su shiga duniya su gano kufaifai na al’ummomin da suka gabata, waɗanda suka ƙaryata manzanninsu, sannan su duba su ga yadda ƙarshensu ya kasance, su ga irin halakar da ta same su da yadda Allah ya rushe gidajensu, don haka su ɗauki izina da wa’azi daga gare su.
قُل لِّمَن مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ قُل لِّلَّهِۚ كَتَبَ عَلَىٰ نَفۡسِهِ ٱلرَّحۡمَةَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۚ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 6:12Ka ce: “Abin da yake cikin sammai da ƙasa na wane ne?” Ka ce: “Na Allah ne.” Ya wajabta wa kansa yin rahama. Lalle tabbas zai tattara ku zuwa ranar tashin alƙiyama wadda babu kokwanto game da ita. Waɗanda suka yi hasarar kawunansu ba za su yi imani ba.
۞وَلَهُۥ مَا سَكَنَ فِي ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 6:13“Kuma abin da ya nutsu a cikin dare ko rana nashi ne, kuma Shi ne Mai ji, Mai yawan sani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya tambayi masu ƙaryata shi cewa, mallakar duk abin da yake sammai da ƙasa na wane ne? Sannan ya umarce shi da ya ba da amsar wannan tambayar, ya ce musu: Mallakar wannan gaba ɗaya ta Allah ce, wanda shi ne ya cancanta a bauta masa shi kaɗai. Kuma ya wajabta wa kansa yin rahama wadda ta yalwaci kowa da komai. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yayin da Allah ya yi halitta ya rubuta a littafi wanda yake wurinsa a saman Al-arshi: “Lalle rahamata ta rinjayi fushina.” [Bukhari #7404, da Muslim #2715]. Allah kuma ya yi alƙawarin lalle zai tattara mutane gaba ɗaya, a ranar alƙiyama wadda babu kokwanto a cikinta. Kuma masu hasara na haƙiƙa su ne waɗanda suka tozarta kawunansu a duniya, ba su yi imani ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk wani abu da ya nutsu a mahallinsa da daddare ne ko da rana, to mallakarsa ne, halittarsa ne, komai a ƙarƙashin ikonsa yake (Mai tsarki da daukaka), shi kuma mai jin duk wani sauti ne, kuma masanin komai ne.
قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَتَّخِذُ وَلِيّٗا فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَهُوَ يُطۡعِمُ وَلَا يُطۡعَمُۗ قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ أَوَّلَ مَنۡ أَسۡلَمَۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 6:14Ka ce: “Shin yanzu wanin Allah ne zan riƙa a matsayin majiɓinci, alhalin Shi ne Ya halicci sammai da ƙasa, kuma Shi Yake ciyarwa, ba a ciyar da Shi?” Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in zamo farkon mai miƙa wuya; kuma lalle kada ka kasance daga masu shirka.”
قُلۡ إِنِّيٓ أَخَافُ إِنۡ عَصَيۡتُ رَبِّي عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 6:15Ka ce: “Lalle ni ina jin tsoron azabar rana mai girma, idan na saɓa wa Ubangijina.”
مَّن يُصۡرَفۡ عَنۡهُ يَوۡمَئِذٖ فَقَدۡ رَحِمَهُۥۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 6:16Wanda duk aka kawar masa da (azaba) a wannan rana, to haƙiƙa (Allah) Ya ji ƙan sa. Kuma wannan Shi ne rabo mabayyani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya ce: Yanzu shi za a ce ya riƙi wani ba Allah ba a matsayin majiɓincin lamarinsa, yana mai neman taimako da agaji a wurinsa ba Allah ba, alhalin kuwa ya san Allah ne mahaliccin sammai da ƙasa ba tare da ya kwaikwaya a wurin wani ba, kuma shi mawadaci ne, ba shi da buƙata a wurin kowa cikin halittunsa, kuma shi ne mai arzuta su, ya ciyar da su, ba tare da shi ya buƙaci ciyarwarsu ba? To sai Allah ya umarci Manzonsa da ya faɗa musu cewa, shi kam Ubangijinsa ya umarce shi da ya zama farkon mai miƙa wuya a gare shi, kuma an hana shi zama ɗaya daga cikin mushirikai masu haɗa Allah da wani abu wajen bauta. Kuma ya faɗa musu cewa, shi yana jin tsoron azabar Ubangijinsa ranar gobe ƙiyama. Wannan azabar tasa mai tsanani kuwa duk wanda aka kautar masa da ita ranar alƙiyama, to haƙiƙa Allah ya yi masa babbar rahama, kuma wannan shi ne rabo na haƙiƙa.
وَإِن يَمۡسَسۡكَ ٱللَّهُ بِضُرّٖ فَلَا كَاشِفَ لَهُۥٓ إِلَّا هُوَۖ وَإِن يَمۡسَسۡكَ بِخَيۡرٖ فَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 6:17Kuma idan Allah Ya shafe ka da wata cuta, to ba wanda ya isa ya yaye ta sai Shi; kuma idan Ya shafe ka da wani alheri, to Shi Mai iko ne a kan komai.
وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ
Open ayah 6:18Kuma Shi ne Mai rinjaye a kan bayinsa. Kuma Shi Mai hikima ne, Masani.
قُلۡ أَيُّ شَيۡءٍ أَكۡبَرُ شَهَٰدَةٗۖ قُلِ ٱللَّهُۖ شَهِيدُۢ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ لِأُنذِرَكُم بِهِۦ وَمَنۢ بَلَغَۚ أَئِنَّكُمۡ لَتَشۡهَدُونَ أَنَّ مَعَ ٱللَّهِ ءَالِهَةً أُخۡرَىٰۚ قُل لَّآ أَشۡهَدُۚ قُلۡ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَإِنَّنِي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ
Open ayah 6:19Ka ce: “Mene ne mafi girman shaida?” Ka ce; “Allah Shi ne shaida tsakanina da ku. Kuma an saukar mini wannan Alƙur’anin ne don in yi muku gargaɗi da shi da kuma duk wanda zai isa zuwa gare shi. Yanzu kuwa za ku shaida cewa, lalle akwai waɗansu allolin tare da Allah?” Ka ce: “Ni kam ba zan shaida ba.” Ka ce: “Allah Shi Ɗaya ne, kuma lalle ni ba ruwana da dukkan abin da kuke haɗa Allah da shi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, idan Allah ya nufi bawa da wata cuta, to babu mai raba shi da ita sai shi; idan kuma ya nufe shi da samun wani alheri, kamar lafiya ko ilimi ko dukiya ko \'ya\'ya, to shi mai iko ne a kan komai, babu abin da yake gagarar sa, kuma ba wanda zai iya hana wannan alheri ya same shi ko ya raba shi da shi sai shi kaɗai. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance idan ya ɗago daga ruku’u sai ya ce: “Ya Ubangijinmu, yabo da godiya sun tabbata a gare ka cikin sammai da ƙasa da cikin abin da ka ga dama bayansu, kai ne ka cancanci yabo da girmamawa; wannan shi ne mafi cancantar abin da bawa ya faɗa, dukkan mu bayinka ne. Ya Allah, babu mai hana abin da ka bayar, kuma babu mai bayar da abin da ka hana; wadatar mai wadata ba za ta amfane shi a wurinka ba.” [Muslim #477]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “...Ka sani, da a ce dukkan al’umma za su haɗu a kan su amfanar da kai da wani abu, to ba za su amfanar da kai da komai ba sai abin da Allah ya rubuta maka. Hakanan da za su taru a kan su cuce ka da wani abu, to ba za su cuce ka da komai ba sai da abin da Allah ya riga ya rubuta maka….” [Tirmizi #2516, da Ahmad #2669]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikar Ƙudurarsa da girman ikonsa, wato shi ne wanda ya fi ƙarfin kowa da komai, kuma shi ne maɗaukaki a saman halittunsa, ɗaukaka ta Zati da daraja da iko cikakke a kan bayinsa, kuma shi ne mai cikakkiyar hikima, mai cikakken sani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa Muhammadu (ﷺ) ya tambayi masu ƙaryata shi, wane abu ne ya fi girman shaida a kan gaskiyar da ya zo da ita? Kuma Allah ya umarce shi ya ba da amsa da cewa, shaidar da ta fi kowacce girma ita ce shaidar Allah, shi ne wanda kuskure ko mantuwa ko ƙarya ba sa faruwa a cikin shaidarsa, don haka shi ne shaida tsakaninsa da su, kuma shi ne wanda ya yi masa wahayin Alƙur’ani don ya yi musu gargaɗin azaba da shi, kuma ya gargaɗi duk wanda Alƙur’ani ya je masa. Kuma ya umarce shi ya tambayi waɗannan masu ƙaryatawar: Shin su ma za su yi shaida cewa, a tare da Allah akwai wasu ababen bauta? Idan sun bayar da irin wannan shaidar, to ya faɗa musu cewa, shi ba zai yi irin wannan shaidar tare da su ba. Abin bauta guda ɗaya ne tak, shi ne kaɗai ya cancanci a bauta masa, kuma shi Manzo (ﷺ) ba ruwansa da mushirikai masu haɗa Allah da wani wajen bauta.
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمُۘ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 6:20Waɗanda Muka ba su Littafi sun san shi kamar yadda suka san ‘ya’yansu. Waɗanda suka yi hasarar kawunansu, to su kam ba za su taɓa yin imani ba.
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 6:21Kuma ba mafi zalunci fiye da wanda ya ƙirƙiri ƙarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya ƙaryata ayoyinsa. Haƙiƙar lamarin dai su azzalumai ba za su taɓa rabauta ba.
وَيَوۡمَ نَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَيۡنَ شُرَكَآؤُكُمُ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Open ayah 6:22Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tattara su gaba ɗaya, sannan Mu ce da waɗanda suka yi shirka: “Ina abokan tarayyarku waɗanda kuka kasance kuna riyawa?”
ثُمَّ لَمۡ تَكُن فِتۡنَتُهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ وَٱللَّهِ رَبِّنَا مَا كُنَّا مُشۡرِكِينَ
Open ayah 6:23Sannan fitinarsu ba ta zamo komai ba, face cewar da suka yi: “Wallahi, ya Ubangijinmu, ba mu kasance masu yin shirka ba!”
ٱنظُرۡ كَيۡفَ كَذَبُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡۚ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 6:24Duba ka ga yadda suka yi wa kansu ƙarya. Kuma abin da suka kasance suna ƙirƙira ya ɓace musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, Yahudawa da aka ba su littafin Attaura da Nasara da aka ba su littafin Linjila sun san Annabi Muhammadu (ﷺ) Annabin Allah ne, kuma Manzonsa ne, kamar yadda ɗayansu ya san ɗan cikinsa. Waɗanda suka tafka hasara su ne waɗanda suka kafirce wa Annabi (ﷺ), suka ƙi yin imani da shi da manzancinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu wani babban azzalumi kamar wanda ya yi wa Allah ƙarya, ko kuma ya ƙaryata hujjojin da Allah ya saukar. Kuma lalle har abada azzalumai ba za su rabauta ba. Allah kuma zai tashi mushirikai gaba ɗaya a ranar alƙiyama, ya tambaye su, ina ababen tarayyarsu da suka ɗauke su a matsayin alloli, suna bauta musu? To a wannan tambayar dai ba su da wata amsar da za su bayar mai gamsarwa, sai kawai su fara rantsuwa da Allah cewa, ai su ba su taɓa zama mushirikai ba, a rayuwarsu ta duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ankarar da Annabi (ﷺ) da ya dubi yadda waɗannan mutane suka yi wa kawunansu ƙarya a ranar alƙiyama, kuma suka nemi abubuwan da suka bauta wa ba Allah ba a duniya suka rasa, sun ɓace musu ɓat, ba su amfane su da komai ba.
وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُ إِلَيۡكَۖ وَجَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۚ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوكَ يُجَٰدِلُونَكَ يَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 6:25Kuma daga cikinsu akwai wanda yake sauraren ka; kuma Mun sanya murafai a zukatansu, ta yadda ba za su iya fahimtar sa ba, haka kuma a kunnuwansu akwai wata toshiya. Kuma in da za su ga kowace irin aya ce, ba za su yi imani da ita ba. Har ma idan sun zo maka suna jayayya da kai, (sai) waɗanda suka kafirta su riƙa cewa: “Ai wannan ba komai ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko.”
وَهُمۡ يَنۡهَوۡنَ عَنۡهُ وَيَنۡـَٔوۡنَ عَنۡهُۖ وَإِن يُهۡلِكُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 6:26Kuma suna hana (mutane) sauraren sa (Alƙur’ani), kuma su kansu suna ƙara nesanta da shi; kuma ba kowa suke hallakarwa ba face kawunansu, sai dai su ba sa jin hakan. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana nusantar da Annabi (ﷺ) cewa, mushirikai da yake yi wa wa’azi ba dare ba rana, a cikinsu akwai waɗanda ba za su taɓa yin imani ba duk kuwa da irin ƙarfafan hujjoji da ya zo musu da su. Kuma a cikinsu akwai waɗanda suke sauraron sa lokacin da yake karanta musu Alƙur’ani, amma fa ba sa amfana da komai daga ayoyinsa, domin kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe zukatansu ruf, ba sa fahimtar komai, ya doɗe kunnuwansu ba sa yin sauraro mai amfani, kuma Allah ya yi musu hakan ne saboda taurin kansu da jayayyarsu bayan sun ga hujjoji da dalilai a bayyane amma sun ƙi yin imani. Idan ma sun zo fadar Manzon Allah (ﷺ), ba wani abu yake kawo su ba sai don su yi ta jayayya da shi a kan gaskiyar da yake faɗa musu, har ma suna cewa, ai duk abin da ya zo da shi ya ɗauko shi ne daga littattafan tatsuniyoyin mutanen farko. Allah (ﷺ) ya bayyana wa Manzonsa cewa, su waɗannan mushirikai ba wai kawai sun ƙi karɓar gaskiya ne a karan-kansu ba; suna ma hana mutane su karɓi gaskiyar bayan su sun guje ta; to amma ba kowa suke halakarwa ba sai kawunansu, kuma ba sa jin hakan ko a jikinsu.
وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ وُقِفُواْ عَلَى ٱلنَّارِ فَقَالُواْ يَٰلَيۡتَنَا نُرَدُّ وَلَا نُكَذِّبَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا وَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 6:27Da kuma za ka ga lokacin da ake tsayar da su a gaban wuta, sai su ce: “Kaiconmu, ina ma da za a mayar da mu (duniya), to da ba za mu sake ƙaryata ayoyin Ubangijinmu ba, kuma za mu zamanto cikin muminai.”
بَلۡ بَدَا لَهُم مَّا كَانُواْ يُخۡفُونَ مِن قَبۡلُۖ وَلَوۡ رُدُّواْ لَعَادُواْ لِمَا نُهُواْ عَنۡهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 6:28A’a, ba haka ba ne, abin da suke ɓoyewa a da shi ne ya bayyana a gare su; kuma in da za a mayar da su, to da sun koma kan abin da aka hana su. Kuma lalle su tabbas maƙaryata ne.
وَقَالُوٓاْ إِنۡ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا وَمَا نَحۡنُ بِمَبۡعُوثِينَ
Open ayah 6:29Kuma suka ce: “Ba wata (rayuwa) sai rayuwarmu ta duniya, kuma mu ba waɗanda za a sake tashin mu ba ne.”
وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ وُقِفُواْ عَلَىٰ رَبِّهِمۡۚ قَالَ أَلَيۡسَ هَٰذَا بِٱلۡحَقِّۚ قَالُواْ بَلَىٰ وَرَبِّنَاۚ قَالَ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ
Open ayah 6:30Kuma in da za ka ga lokacin da aka tsayar da su a gaban Ubangjinsu; ya ce: “Shin ashe wannan ba gaskiya ne ba?” Sai su ce: “Gaskiya ne, muna rantsuwa da Ubangijinmu.” Sai Ya ce: “To ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci.”
قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱللَّهِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَتۡهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةٗ قَالُواْ يَٰحَسۡرَتَنَا عَلَىٰ مَا فَرَّطۡنَا فِيهَا وَهُمۡ يَحۡمِلُونَ أَوۡزَارَهُمۡ عَلَىٰ ظُهُورِهِمۡۚ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ
Open ayah 6:31Haƙiƙa waɗanda suka ƙaryata haɗuwa da Allah sun yi hasara; har sai lokacin da alƙiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, sai su ce: “Kaiconmu kan irin sakacin da muka yi a cikinta (duniya),” alhalin kuwa suna ɗauke da kayan laifukansu a bayansu. Ku saurara, abin da suka ɗauka na laifi ya munana matuƙa.
وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا لَعِبٞ وَلَهۡوٞۖ وَلَلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 6:32Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face wasa da sharholiya; kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga waɗanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana nuna wa Annabi (ﷺ) irin halin da kafirai za su tsinci kawunansu ne a lahira, inda ya ce, da a ce zai ga lokacin da za a tattara waɗannan mushirikan ranar alƙiyama, a tsayar da su a gaban wutar Jahannama, tabbas da ya ga abin mamaki, lokacin da za su ga wutar Jahannama da abubuwan firgici da suke cikinta; lokacin za su fara nadama da raki, suna burin ina ma za a sake mayar da su duniya sai su yi imani da ayoyin Allah, su yi aiki nagari, su zamo daga cikin muminai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata su da cewa, abin ba haka ne ba, yanzu sun ga dahir ne; abin da suke ɓoyewa a da ne ya bayyana ya fito sarari. A duniya suna ɓoye gaskiyar manzancin Annabi (ﷺ) duk da cewa sun san gaskiyarsa, amma taurin kai da hassada sun hana su yin imani, to yau ga shi gaskiyar ta fito sarari kowa ya gan ta. Don haka ko da ma an dawo da su duniya, za su ci gaba ne da ƙaryatawa da saɓon Allah kamar yadda suka saba a baya, domin ƙarya suke yi da suke cewa za su yi imani idan sun sake komowa duniya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya daɗa fallasa wata ƙaryar da mushrikai suke yi a duniya na cewa wai babu wata rayuwa in ban da rayuwar duniya, kuma babu tashin alƙiyama balle wani abu hisabi. To sai Allah ya nuna wa Annabi (ﷺ) cewa, da a ce zai ga waɗannan maƙaryata a ranar alƙiyama lokacin da Allah zai tirke su a gabansa ya tambaye su: Shin har yanzu suna nan kan bakansu cewa, wannan tashin Alƙiyamar ba gaskiya ba ne? Sai nan take su yi rantsuwa da Allah Ubangijinsu su ce: Lalle gaskiya ne babu wani kokwanto a kai, domin sun ga dahir. Sai Allah ya ce musu: To ai yanzu kam sai su ɗanɗani azaba sakamakon kafircinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) tabbatar da cewa, duk waɗanda suka ƙaryata ranar gamuwa da shi sun yi babbar hasara, kuma sai ranar ta zo musu kwatsam ba zato ba tsammani ne za su riƙa cizon yatsa da nadama a bisa sakaci da rayuwarsu da suka yi a baya, ba su yi wa wannan ranar wani tanadi ba, ga shi yau sun haɗu da Ubangijinsu, suna ɗauke da kayan zunubansu a bayansu; to tir da wannan irin dako na kayan zunubi da suke yi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu haƙiƙanin wannan rayuwa ta duniya wadda suka nuna tsananin sonta ido-rufe suka ƙi sauraron duk wata gaskiya da ake faɗa musu, Allah ya nuna cewa wannan rayuwar ta duniya ba komai ba ce illa wasa da wargi da sharholiya marar amfani. Amma shi gidan lahira shi ne ya fi alheri ga wanda ya yi taƙawa, ya kiyaye dokokin Ubangijinsa. Yanzu ashe masu ƙaryata gamuwa da Allah ba za su hankalta ba, su fahimci mece ce duniya kuma mece ce lahira?
قَدۡ نَعۡلَمُ إِنَّهُۥ لَيَحۡزُنُكَ ٱلَّذِي يَقُولُونَۖ فَإِنَّهُمۡ لَا يُكَذِّبُونَكَ وَلَٰكِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ
Open ayah 6:33Haƙiƙa Muna da cikakkiyar masaniyar cewa, lalle irin abin da suke faɗa yakan baƙanta maka rai; to a gaskiya su ba kai suke ƙaryatawa ba, sai dai azzalumai suna jayayya ne da ayoyin Allah.
وَلَقَدۡ كُذِّبَتۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَ فَصَبَرُواْ عَلَىٰ مَا كُذِّبُواْ وَأُوذُواْ حَتَّىٰٓ أَتَىٰهُمۡ نَصۡرُنَاۚ وَلَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِۚ وَلَقَدۡ جَآءَكَ مِن نَّبَإِيْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 6:34Kuma lalle haƙiƙa an ƙaryata waɗansu manzanni a gabaninka, sai suka yi haƙuri a kan ƙaryata su da aka yi, kuma an cutar da su, har sai da taimakonmu ya zo musu. Kuma babu wanda ya isa ya musanya kalmomin Allah. Kuma lalle haƙiƙa wani sashi na labarin manzanni ya zo maka.
وَإِن كَانَ كَبُرَ عَلَيۡكَ إِعۡرَاضُهُمۡ فَإِنِ ٱسۡتَطَعۡتَ أَن تَبۡتَغِيَ نَفَقٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ أَوۡ سُلَّمٗا فِي ٱلسَّمَآءِ فَتَأۡتِيَهُم بِـَٔايَةٖۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَمَعَهُمۡ عَلَى ٱلۡهُدَىٰۚ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ
Open ayah 6:35Kuma idan bijirewarsu ta dame ka, to idan har kana iya haƙa rami a cikin ƙasa, ko kuma (ka samu) wani tsani ka hau sama, don ka zo musu da wata aya, (to ka yi hakan). Kuma in da Allah Ya ga dama, tabbas da Ya tara su gaba ɗaya a kan shiriya. Don haka kada ka kasance cikin jahilai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, yana sane da irin baƙaƙen maganganun da mushirikai suke faɗa masa waɗanda suke ɓata masa rai, ya tabbatar masa da cewa, ba fa shi ne suke ƙaryatawa ba kai-tsaye; sun yarda a zukatansu cewa gaskiya yake faɗa musu, to amma sai su fito a fili suna jayayya da shi domin su ƙaryata ayoyin Allah don tsabar girman kai da taɓewa. To sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashe shi ta hanyar cewa, waɗannan abubuwan da yake gani daga mutanensa na baƙin ciki da ɓacin rai, irinsu ne annabawan da suke gabaninsa suka riƙa gani daga al’ummominsu, domin su ma an ƙaryata su, an cutar da su, to amma sai suka yi ta haƙuri har zuwa lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su nasara. Don haka shi ma Manzon Allah (ﷺ) sai ya ci gaba da haƙuri har lokacin da nasarar Allah za ta zo. Sai kuma ya bayyana cewa, waɗannan masu ƙaryata shi ɗin ba ɗaya daga cikinsu da ya isa ya canza kalmomin Allah waɗanda ya riga ya rubuta na tabbatar da samun nasara ga Manzonsa (ﷺ). Sannan Allah ya tabbatar masa cewa, ai ya samu labaran manzanni da dama da suka shuɗe a gabaninsa da irin nasara da taimakon da ya yi musu. Ya ci gaba da faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, idan har bijirewar waɗannan mushirikai gare shi tana damun sa ainun, to idan har zai iya samun wani rami a ƙarƙashin ƙasa ko wani tsani da zai hau sama, don ya je ya kawo musu wata hujja ko wani dalili da zai gamsar da su a kan gaskiyarsa, to yana iya yin hakan. To amma ya sani cewa, da Allah ya ga dama da ya tara su dukansu a kan shiriya, ba a samu mai fanɗarewa ko ɗaya daga cikinsu ba. Don haka sai ya ja hankalinsa da kada ya kasance cikin jahilai waɗanda ba su san yadda al’amura suke ba, ba su san yadda aikin Allah yake gudana a cikin halittunsa ba, wanda hakan ne zai saka shi ya ci gaba da damuwa a kan bijirewarsu da rashin imaninsu.
۞إِنَّمَا يَسۡتَجِيبُ ٱلَّذِينَ يَسۡمَعُونَۘ وَٱلۡمَوۡتَىٰ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ ثُمَّ إِلَيۡهِ يُرۡجَعُونَ
Open ayah 6:36Lalle masu ji su ne kawai suke amsa (kiranka). Matattu kuwa Allah zai tashe su (ranar alƙiyama), sannan zuwa gare Shi za a mayar da su.
وَقَالُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يُنَزِّلَ ءَايَةٗ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 6:37Kuma suka ce: “Ina ma da an saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa ?” Ka ce: “Lalle Allah Mai iko ne a kan Ya saukar da kowace irin aya, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka).”
وَمَا مِن دَآبَّةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا طَٰٓئِرٖ يَطِيرُ بِجَنَاحَيۡهِ إِلَّآ أُمَمٌ أَمۡثَالُكُمۚ مَّا فَرَّطۡنَا فِي ٱلۡكِتَٰبِ مِن شَيۡءٖۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ يُحۡشَرُونَ
Open ayah 6:38Kuma babu wata dabba da take tafiya a bayan ƙasa, kuma babu wani tsuntsu da yake tashi da fukafukansa, face (su ma) al’ummomi ne irinku. Ba Mu yi sakacin barin wani abu ba a cikin littafi, sannan kuma zuwa ga Ubangijinsu ne za a tara su.
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا صُمّٞ وَبُكۡمٞ فِي ٱلظُّلُمَٰتِۗ مَن يَشَإِ ٱللَّهُ يُضۡلِلۡهُ وَمَن يَشَأۡ يَجۡعَلۡهُ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 6:39Waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu su kurame ne, kuma bebaye ne, suna cikin duffai. Wanda Allah Ya ga dama sai Ya ɓatar da shi, wanda kuwa Ya ga dama sai Ya ɗora shi a kan tafarki madaidaici. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, waɗanda suke amsa kiransa da na Manzonsa su ne kawai masu sauraro da kunnen basira kuma masu fahimta, amma kafirai masu matattun zukata ba a sa ran za su saurare shi, domin su ba su da bambanci da matattu babu abin da suke iya fahimta. Don haka Allah zai fito da su daga ƙaburburansu, ya tattara su a gabansa domin yi musu hisabi a kan ayyukansu. Har ta kai su waɗannan masu ƙaryata Manzo suna cewa, me ya hana Allah ya saukar wa Annabi (ﷺ) wata mu’ujiza ko aya daga wajensa ba, wadda za ta tabbatar da cewa, shi Manzon Allah ne? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa: Allah yana da cikakken ikon da zai saukar da kowace irin aya a duk sanda ya ga dama, to amma yana yin komai ne bisa tsari da hikima, sai dai yawancin irin waɗannan mutane ba su san hikimomin Allah a cikin ayyukansa da hukunce-hukuncensa ba, don haka ba abin da suka sani sai jayayya da musu. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani sashe na ayoyinsa a halittarsa, inda ya nuna cewa babu wata dabba da ke tafiya a bayan ƙasa ko wani tsuntsu mai tashi da fukafukansa, face su ma al’ummomi ne kamar mutane. Babu kuma abin da Allah ya bari face sai da ya rubuta shi cikin Lauhul Mahfuzu kuma zuwa gare shi za a tara su gaba ɗayansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, masu ƙaryata ayoyin Alƙur’ani da bayyanannun hujjojin Allah kurame ne, ba sa jin gaskiya, bebaye ne, ba sa iya faɗar gaskiya, kuma suna cikin duhun kafirci, ba sa ganin wani haske a rayuwarsu. Don haka wanda Allah ya yi nufin ɓatar da shi, zai ɓatar da shi, wanda kuma ya yi nufin ya shiryar da shi, to zai ɗora shi a kan miƙaƙƙen tafarki, don haka shiriya da ɓata duka a hannunsa suke shi kaɗai, yana yin komai bisa hikima.
قُلۡ أَرَءَيۡتَكُمۡ إِنۡ أَتَىٰكُمۡ عَذَابُ ٱللَّهِ أَوۡ أَتَتۡكُمُ ٱلسَّاعَةُ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ تَدۡعُونَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 6:40Ka ce; “Ku ba ni labari, idan da a ce azabar Allah za ta zo muku ko alƙiyama ta zo muku, shin wanin Allah za ku kira, in har kun kasance masu gaskiya?”
بَلۡ إِيَّاهُ تَدۡعُونَ فَيَكۡشِفُ مَا تَدۡعُونَ إِلَيۡهِ إِن شَآءَ وَتَنسَوۡنَ مَا تُشۡرِكُونَ
Open ayah 6:41Ba haka ba ne, (Allah) Shi kaɗai za ku kira, sai Ya yaye abin da kuke roƙonsa a kai idan Ya ga dama, kuma za ku manta abin da kuke haɗa Allah da shi wajen bauta.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰٓ أُمَمٖ مِّن قَبۡلِكَ فَأَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ لَعَلَّهُمۡ يَتَضَرَّعُونَ
Open ayah 6:42Kuma lalle Mun aika da (manzanni) zuwa ga al’ummomin da suka gabace ka, sai Muka ɗora musu tsananin talauci da cutuka ko sa ƙasƙantar da kai.
فَلَوۡلَآ إِذۡ جَآءَهُم بَأۡسُنَا تَضَرَّعُواْ وَلَٰكِن قَسَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 6:43To me ya hana lokacin da musibarmu ta zo musu, su ƙasƙantar da kai? Sai dai kuma zukatansu ne suka ƙeƙashe, Shaiɗan kuma ya ƙawata musu abin da suka kasance suna aikatawa.
فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦ فَتَحۡنَا عَلَيۡهِمۡ أَبۡوَٰبَ كُلِّ شَيۡءٍ حَتَّىٰٓ إِذَا فَرِحُواْ بِمَآ أُوتُوٓاْ أَخَذۡنَٰهُم بَغۡتَةٗ فَإِذَا هُم مُّبۡلِسُونَ
Open ayah 6:44To yayin da suka yi watsi da abin da aka yi musu wa’azi da shi, sai Muka buɗe musu ƙofofin kowane irin abu, har zuwa lokacin da suka yi fariya da abin da aka ba su, sai Muka damƙe su ba zato ba tsammani, sai ga su suna masu yanke ƙauna (daga kowane alheri).
فَقُطِعَ دَابِرُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْۚ وَٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 6:45Da haka ne aka tumɓuke tushen waɗanda suka yi zalunci. Kuma yabo da kirari sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi Muhammadu (ﷺ) ya tambayi kafirai cewa, idan wata azabar Allah ta afka musu ko ranar alƙiyama ta zo musu, shin za su kira wani ba Allah ba domin ya kuɓutar da su idan har sun kasance masu gaskiya ne wajen bautar wasu alloli ba Allah ba? A’a, ba wanda za su kira sai Allah don ya yaye musu baƙin cikin da ya same su, a wannan lokacin za su manta abubuwan da suke shirka da su sai Allah shi kaɗai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, ya aiko da annabawa kafin Annabi Muhammadu (ﷺ), to amma al’ummominsu sun ƙaryata su, sai Allah ya ɗanɗana musu wata masifa ta tsananin talauci da ƙuncin rayuwa, ya kuma jarrabe su da cututtuka iri-iri, ko wataƙila sa dawo su ƙasƙantar da kawunansu ga Allah, su bauta masa shi kaɗai. To amma me ya hana bayan ya jarrabe su da ire-iren waɗannan masifu, su koma gare shi su ƙasƙantar da kansu su bauta masa shi kaɗai? Sai dai kuma zukatansu sun riga sun ƙeƙashe, kuma Shaiɗan ya ƙawata musu miyagun ayyukansu suna ganin su kyawawa, don haka suka ci gaba da kafirci da shirka da saɓon Allah iri-iri. To lokacin da kafirai suka bar umarnin Allah da gangan, suka yi watsi da wa’azin da ake yi musu na su ji tsoron Allah, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya canza musu yanayin da suke ciki, ya kawo musu wadata maimakon talauci, lafiya madadin cututtuka, ya yi ta yi musu talala har sai da suka saki jiki, suna farin ciki da fariya da ɗagawa saboda ni’imar da suke ciki, sai kawai kwatsam azabar Allah ta zo musu, sai ga su gaba ɗaya sun halaka kamar ba a taɓa yin su ba a bayan ƙasa. Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai yin yadda ya ga dama. An karɓo daga Uƙubatu ɗan Amiru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ka ga Allah yana ba wa bawansa abin da yake so a duniya, tare da yana saɓa masa, to wannan talala ce Allah yake yi masa.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta wannan ayar ta 44. [Ahmad #17311].
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَخَذَ ٱللَّهُ سَمۡعَكُمۡ وَأَبۡصَٰرَكُمۡ وَخَتَمَ عَلَىٰ قُلُوبِكُم مَّنۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَأۡتِيكُم بِهِۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ ثُمَّ هُمۡ يَصۡدِفُونَ
Open ayah 6:46Ka ce: “Ku ba ni labari, yanzu idan Allah zai ɗauke jinku da ganinku, kuma Ya ɗora murfi a zukatanku, wane abin bauta ne wanda ba Allah ba, da zai dawo muku da shi?” Duba ka ga yadda Muke sarrafa ayoyi, amma duk da haka suna bijirewa.
قُلۡ أَرَءَيۡتَكُمۡ إِنۡ أَتَىٰكُمۡ عَذَابُ ٱللَّهِ بَغۡتَةً أَوۡ جَهۡرَةً هَلۡ يُهۡلَكُ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 6:47Ka ce: “Ku ba ni labari, idan da azabar Allah za ta zo muku ba zato ba tsammani ko kuma cikin sani, to shin za a hallakar da (wasu) ba azzaluman mutane ba?”
وَمَا نُرۡسِلُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَۖ فَمَنۡ ءَامَنَ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 6:48Kuma ba ma aiko da manzanni sai suna masu bushara masu gargaɗi; sannan duk wanda ya yi imani kuma ya kyautata aiki, to babu tsoro a tattare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَمَسُّهُمُ ٱلۡعَذَابُ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ
Open ayah 6:49Waɗanda kuwa suka ƙaryata ayoyinmu, azaba za ta shafe su saboda abin da suka kasance suna yi na fasiƙanci.
قُل لَّآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ وَلَآ أَقُولُ لَكُمۡ إِنِّي مَلَكٌۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّۚ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُۚ أَفَلَا تَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 6:50Ka ce: “Ni ba zan ce da ku a wajena taskokin Allah suke ba, kuma ni ban san gaibu ba, kuma ni ba zan ce da ku ni mala’ika ne ba; ni ba abin da nake bi sai abin da aka yi mini wahayinsa.” Ka ce: “Yanzu makaho da mai gani za su yi daidai? To me ya sa ba za ku yi tunani ba?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya tambayi mushrikai cewa, idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙwace musu jinsu ya mayar da su kurame ko ya ƙwace musu ganinsu ya mayar da su makafi, ya kuma toshe musu zukatansu suka daina fahimtar komai, to shin akwai wani ba Allah ba wanda zai dawo musu da waɗannan abubuwa sai su bauta masa, shi kuma Allah su yi shirka da shi? Allah ya faɗakar da Annabi (ﷺ) da cewa, ya duba ya ga yadda yake koro musu hujjoji, yake bayyana su a fili, amma kuma suna kawar da kawunansu, ba sa dubansu balle su yi aiki da su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa da cewa kafirai su ba shi labari idan har azabar Allah ta zo musu ba shiri ko wani bala’i ya sauka a kansu, shin akwai wanda zai ɗanɗani wannan azabar in ba su azzalumai ba? Sannan ya ƙara da cewa, bai aiko da manzanni ba sai don su yi albishir da Aljanna ga wanda ya bi Allah, su yi gargaɗi da Wuta ga wanda ya saɓa wa Allah (Mai tsarki da daukaka). To amma duk wanda ya yi imani babu wani tsoro a tare da shi game da abin da yake fuskanta, kuma babu damuwa a kan abin da ya bari a nan duniya. Waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah kuwa, za su gamu da wata azaba saboda kangarewa da kauce wa hanyar Allah da suka yi. To bayan da kafirai suka matsa wa Manzon Allah (ﷺ) da cewa, sai ya zo musu da wata aya wadda za ta sa su yin imani ko ba sa so, sai Allah ya umarce shi ya faɗa musu cewa, taskokin Allah ba a hannunsa suke ba ballantana ya kawo musu abubuwan da suke nema, kuma shi bai san gaibu ba, kuma bai yi da’awar shi mala’ika ne, mai iya aikata abin da mutane ba za su iya aikatawa ba; shi kawai Manzo ne da Allah ya aiko shi don ya kira mutane zuwa ga bautar Allah shi kaɗai. Duk abin da yake faɗa da abin da yake aikatawa yana yin su ne a bisa wahayin da Allah yake yi masa. To yanzu za a ce wanda ya bi gaskiya ya miƙa wuya gare ta zai yi daidai da wanda ya saki hanya, ya yi watsi da gaskiya? Ashe yanzu ba za su yi tunani ba su fahimta?
وَأَنذِرۡ بِهِ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَن يُحۡشَرُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ لَيۡسَ لَهُم مِّن دُونِهِۦ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ لَّعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Open ayah 6:51Kuma ka yi gargaɗi da shi (Alƙur’ani) ga waɗanda suke jin tsoron a tattara su a gaban Ubangijinsu, ba su da wani majiɓincin lamari in ba Shi ba, kuma ba su da wani mai ceto, don su kiyaye dokokin Allah.
وَلَا تَطۡرُدِ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ رَبَّهُم بِٱلۡغَدَوٰةِ وَٱلۡعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجۡهَهُۥۖ مَا عَلَيۡكَ مِنۡ حِسَابِهِم مِّن شَيۡءٖ وَمَا مِنۡ حِسَابِكَ عَلَيۡهِم مِّن شَيۡءٖ فَتَطۡرُدَهُمۡ فَتَكُونَ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 6:52Kuma kada ka kori waɗannan da suke bauta wa Ubangijinsu safe da yamma, suna nufin Fuskarsa (watau suna yi don Shi kaɗai); ba wani abu na haƙƙinsu a kanka, kuma babu wani abu na haƙƙinka a kansu, balle ka kore su, sai ka kasance cikin azzalumai.
وَكَذَٰلِكَ فَتَنَّا بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لِّيَقُولُوٓاْ أَهَٰٓؤُلَآءِ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنۢ بَيۡنِنَآۗ أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِٱلشَّٰكِرِينَ
Open ayah 6:53Kuma kamar haka ne Muka jarrabi sashinsu da sashi, domin su ce: “Yanzu waɗannan su ne Allah Ya yi wa baiwa daga cikinmu?” Ashe Allah ba Shi ne Mafi sanin masu godiya (gare Shi) ba?
وَإِذَا جَآءَكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِنَا فَقُلۡ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡۖ كَتَبَ رَبُّكُمۡ عَلَىٰ نَفۡسِهِ ٱلرَّحۡمَةَ أَنَّهُۥ مَنۡ عَمِلَ مِنكُمۡ سُوٓءَۢا بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ تَابَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَصۡلَحَ فَأَنَّهُۥ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 6:54Kuma idan waɗanda suke yin imani da ayoyinmu sun zo wurinka, to ka ce: “Sallama a gare ku;” Ubangijinku Ya wajabta wa kansa yin rahama cewa, lalle cikinku duk wanda ya aikata wani mummunan aiki bisa ga jahilci, sannan daga baya ya tuba kuma ya kyautata aiki, to Shi Mai gafara ne, Mai jin ƙai.”
وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ وَلِتَسۡتَبِينَ سَبِيلُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 6:55Kuma kamar haka ne Muke rarrabe ayoyi domin tafarkin masu laifuka ya bayyana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya yi wa’azi da Alƙur’ani ga mutanen da suke jin tsoron ranar da za a tattara su gaban Ubangijinsu, ba su da wani mai taimakonsu ba Allah ba, kuma ba su da wanda zai cece su daga azabar Allah, ko wataƙila sa yi taƙawa su aikata abin da ake umartar su da shi, su bar abin da ake hana su. Kuma Allah ya yi wa Annabi (ﷺ) kashedi da kada ya kori talakawan sahabbai waɗanda suke bautar Allah safe da yamma, suna masu tsarkake bautarsu ga Allah kawai da neman kusanci da shi. Dalilin saukar wannan ayar shi ne, abin da Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito cewa: “Mun kasance mu shida tare da Annabi (ﷺ) sai mushirikai suka ce wa Annabi (ﷺ): ‘Ka kori mutanen nan don kada su riƙa yi mana rashin kunya.’ Sa’ad ya ce: “Na kasance ni ne da Abdullahi ɗan Mas’ud da wani mutum daga ƙabilar Huzailu da Bilalu da wasu mutum huɗu da ba zan tuna sunayensu ba. To Sai abin da Allah ya ga dama ya auku a zuciyar Manzon Allah (ﷺ) ya auku, watau ya saƙa wani abu a ransa. Sai Allah ya saukar da wannan ayar.” [Muslim #2413]. Wato Manzo Allah (ﷺ) koyaushe yana kwaɗayin musuluntar waɗannan mushirikai, saboda maslahar da take ciki na kasancewarsu shugabanni ne; idan sun musulunta to mabiyansu ma duk za su musulunta, daga lokacin kuma za a daina gallaza wa Musulmi marasa gata, sai ya yi tunanin ya sallami talakawan da suke zuwa majalisarsa don ya samu nasarar farautar waɗancan manyan Ƙuraishawa, sai Allah ya hana shi aikata hakan, ya faɗa masa cewa, kowa hisabinsa na ga Allah, shi ne zai yi wa kowa sakayya a kan ayyukansa na alheri ko na sharri, don haka ba shi ne mai yi musu hisabi ba, su ma ba su ne masu yi masa hisabi ba ballantana ya kore su daga majalisarsa, kuma har idan ya aikata hakan, to ya zama daga cikin azzalumai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar haka ne yake jarrabar sashin wasu mutane da wani sashi; ya yi wani mai wadata wani kuma matalauci, wani mai daraja wani kuma ba kowa ba. To idan wani matalauci ko mai rauni ya musulunta, ya ba da gaskiya, shi kenan sai hakan ya zamanto fitina ga mai wadata da mai daraja har su riƙa cewa: Waɗannan mutanen su ne za a ce Allah ya yi musu baiwar shiriya mu kuma bai yi mana ba? Kuma da a ce wani abin kirki ne ai da mu ne za mu same shi kafin su. Sai Allah ya mayar musu da martani cewa, shi ne ya fi sanin bayinsa masu gode masa, don haka sai ya yi musu kyautar da bai yi wa waninsu ba komai martabarsa da wadatarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) cewa, ya yi maraba da muminai masu ba da gaskiya da ayoyinsa duk sa’adda suka zo wurinsa, ya ce musu, amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma ya yi musu albishir da samun rahamar Allah wadda ya wajabta wa kansa, kuma ya sanar da su cewa, duk wanda ya yi laifi bisa jahilci sannan daga bisani ya tuba ya gyara aikinsa, to Allah mai yawan gafara ne mai yawan jin ƙai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yana bayanin ayoyinsa ne ɓaro-ɓaro don kowa ya gane, don kuma hanyar masu laifi marasa gaskiya ta fito ƙarara kowa ya fahimce ta don ya nisance ta, a rarrabe tsakanin gaskiya da ɓata.
قُلۡ إِنِّي نُهِيتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِۚ قُل لَّآ أَتَّبِعُ أَهۡوَآءَكُمۡ قَدۡ ضَلَلۡتُ إِذٗا وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُهۡتَدِينَ
Open ayah 6:56Ka ce: “Lalle ni an hana ni in bauta wa abubuwan da kuke bauta wa ba Allah ba.” Ka ce: “Ba zan bi soye-soyen zukatanku ba, (idan har zan bi son zuciyarku), to haƙiƙa na ɓata, kuma da ban zama cikin shiryayyu ba kenan” .
قُلۡ إِنِّي عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَكَذَّبۡتُم بِهِۦۚ مَا عِندِي مَا تَسۡتَعۡجِلُونَ بِهِۦٓۚ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِۖ يَقُصُّ ٱلۡحَقَّۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡفَٰصِلِينَ
Open ayah 6:57Ka ce: “Lalle ni ina kan hujja mai ƙarfi daga Ubangijina, ku kuma kun ƙaryata ta. Abin da kuke so in gaggauto muku da shi, ba a hannuna yake ba. Hukunci yana hannun Allah ne Shi kaɗai; Shi ne Yake bayar da labarin gaskiya, kuma Shi ne Fiyayyen masu rarrabewa (tsakanin ƙarya da gaskiya)”.
قُل لَّوۡ أَنَّ عِندِي مَا تَسۡتَعۡجِلُونَ بِهِۦ لَقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۗ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 6:58Ka ce: “Da a ce abin da kuke nema a gaggauto muku da shi a wurina yake, to tabbas da ta faru ta ƙare tsakanina da ku. Kuma Allah Shi ne Mafi sanin su wane ne azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya bayyana wa mushirikai cewa, an hana shi ya bauta wa abin da su suke bauta wa ba Allah ba, kuma shi ba zai bi son zuciyarsu ba, domin idan ya yi hakan, to lalle ya ɓata, kuma ba ya daga cikin shiryayyun mutane. Haka kuma ya umarce shi ya faɗa musu cewa, shi yana kan wata ƙaƙƙarfar hujja daga Ubangijinsa, yayin da su kuma suka ƙaryata gaskiyar da ya zo musu da ita. Haka kuma azabar da suke neman a gaggauto musu da zuwanta ba a hannunsa take ba. Don haka hukunci gaba ɗaya na Allah ne; idan ya ga dama sai ya gaggauto musu da azabar da suka nema, idan kuma ya ga dama sai ya jinkirta zuwanta gwargwadon yadda hikimarsa ta zartar. Duk kuma abin da yake labartawa a littafinsa, gaskiya ne babu kokwanto a cikinsa, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne fiyayyen wanda yake bayyana mai gaskiya da mai ƙarya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya bayyana musu cewa, da a ce azabar da suke neman a gaggauto musu da ita a hannunsa take, da yanzu an gama magana, abin da suke nema ya auku gare su. To amma abin a hannun Allah yake, shi ya fi sanin azzalumai, ya fi sanin sanda ya dace ya saukar musu da azabarsa, domin yana yin komai ne cikin hikima.
۞وَعِندَهُۥ مَفَاتِحُ ٱلۡغَيۡبِ لَا يَعۡلَمُهَآ إِلَّا هُوَۚ وَيَعۡلَمُ مَا فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۚ وَمَا تَسۡقُطُ مِن وَرَقَةٍ إِلَّا يَعۡلَمُهَا وَلَا حَبَّةٖ فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡأَرۡضِ وَلَا رَطۡبٖ وَلَا يَابِسٍ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٖ
Open ayah 6:59“Kuma mabuɗan gaibu a wurinsa suke Shi kaɗai, babu wanda ya san su sai Shi. Kuma Ya san ƙididdigar abin da yake kan tudu da na ruwa. Kuma babu wani ganyen itace da zai faɗo, face sai Ya san da shi, kuma ba wata ƙwaya da take cikin duhun ƙasa, kuma ba wani ɗanyen abu ko busasshe, face (bayaninsa) yana cikin Littafi mabayyani.
وَهُوَ ٱلَّذِي يَتَوَفَّىٰكُم بِٱلَّيۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا جَرَحۡتُم بِٱلنَّهَارِ ثُمَّ يَبۡعَثُكُمۡ فِيهِ لِيُقۡضَىٰٓ أَجَلٞ مُّسَمّٗىۖ ثُمَّ إِلَيۡهِ مَرۡجِعُكُمۡ ثُمَّ يُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 6:60“Kuma Shi ne Yake karɓar rayukanku da daddare, kuma Ya san abin da kuka aikata da rana, sannan Ya tayar da ku a cikinta (ranar), har zuwa lokacin da zai zartar da wani ajali sananne, sannan zuwa gare Shi ne makomarku take, sannan zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۖ وَيُرۡسِلُ عَلَيۡكُمۡ حَفَظَةً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ تَوَفَّتۡهُ رُسُلُنَا وَهُمۡ لَا يُفَرِّطُونَ
Open ayah 6:61“Kuma Shi ne wanda Yake da iko a kan bayinsa, kuma Yana aiko muku masu tsaro, har zuwa lokacin da mutuwa za ta zo wa ɗayanku, sai manzanninmu su karɓi ransa, kuma su ba sa yin sakaci.
ثُمَّ رُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۚ أَلَا لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَهُوَ أَسۡرَعُ ٱلۡحَٰسِبِينَ
Open ayah 6:62“Sannan sai a mayar da su zuwa ga Allah Majiɓincin lamarinsu na gaskiya. Ku saurara, dukkan hukunci nasa ne, kuma Shi ne Mafi gaggawar masu hisabi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, shi kaɗai ne yake da taskokin gaibu waɗanda babu wanda ya san su sai shi kaɗai, ya san abin da yake kan tudun ƙasa, ya san na cikin teku, kuma babu wani ganye da zai faɗo daga itaciyarsa face ya san da shi, hakanan babu wata ƙwaya a cikin duffan ƙasa ko wani abu ɗanye ko ƙeƙasasshe face yana nan a rubuce a cikin Lauhul Mahfuzu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mabuɗan gaibu biyar ne, babu wanda ya san su sai Allah. Babu wanda ya san abin da mahaifa take ragewa (na lokaci) sai Allah; babu kuma wanda ya san me zai faru gobe sai Allah; babu wanda ya san yaushe ne ruwan sama zai sauka sai Allah; babu kuma wani rai da ya san inda zai mutu sai Allah; kuma babu wanda ya san lokacin tashin alƙiyama sai Allah.” [Bukhari #7379]. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Duk wanda ya riya cewa Annabi (ﷺ) yana ba da labarin abin da zai faru gobe, to lalle ya yi wa Allah ƙarya babba, Allah yana cewa: Ka ce: “Waɗanda suke sammai da waɗanda suke ƙasa babu wanda ya san gaibu sai Allah.” [Muslim #177]. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne kaɗai wanda yake karɓar rayukan halittunsa da daddare lokacin barcinsu, idan ya ga dama sai ya riƙe rayukan waɗanda ya riga ya hukunta musu mutuwa, ya sako waɗanda lokacin mutuwarsu bai yi ba, kamar yadda ya yi bayani a cikin Suratuz Zumar , aya ta 42. Kuma yana sane da ayyukan da bayi suka yi da rana. Sannan sai ya tashe su daga barcinsu yayin da gari ya waye, domin ya zartar da ajalin da ya iyakance musu na rayuwarsu, kowa ya cinye lokacinsa na duniya, sannan zuwa ga Allah ne shi kaɗai makomarsu take, shi kuma ne zai labarta musu abin da suka kasance suna aikatawa a rayuwarsu ta duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne wanda yake sama da bayinsa, dole kowa ya rusuna masa. Kuma shi ne mai aiko da mala’iku masu tsaron bayinsa, har lokacin da mutuwa za ta zo wa ɗaya daga cikinsu, sai mala’ikun Allah su karɓi ransa ba tare da yin sakaci ba a kan aikinsu, watau ba sa karɓar rai kafin lokacin karɓarsa ya yi, ko su bar shi har ya ƙara a kan lokacinsa. Sannan bayan mutuwa sai a mayar da su zuwa ga majiɓincinsu na gaskiya, wato Allah, wanda shi kaɗai ne mai yin hukunci tsakaninsu da adalci, kuma mafi gaggawar masu hisabi.
قُلۡ مَن يُنَجِّيكُم مِّن ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ تَدۡعُونَهُۥ تَضَرُّعٗا وَخُفۡيَةٗ لَّئِنۡ أَنجَىٰنَا مِنۡ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّٰكِرِينَ
Open ayah 6:63Ka ce: “Wane ne yake tserar da ku daga cikin duffai na tudu da na kogi, kuna roƙon sa a fili da a ɓoye (cewa): “Tabbas, in da zai tserar da mu daga wannan, to lalle za mu kasance cikin masu godiya.”
قُلِ ٱللَّهُ يُنَجِّيكُم مِّنۡهَا وَمِن كُلِّ كَرۡبٖ ثُمَّ أَنتُمۡ تُشۡرِكُونَ
Open ayah 6:64Ka ce: “Allah ne zai tserar da ku daga cikinsa (tsoron), da ma duk wani baƙin ciki, sannan sai ga ku kuna yin shirka.”
قُلۡ هُوَ ٱلۡقَادِرُ عَلَىٰٓ أَن يَبۡعَثَ عَلَيۡكُمۡ عَذَابٗا مِّن فَوۡقِكُمۡ أَوۡ مِن تَحۡتِ أَرۡجُلِكُمۡ أَوۡ يَلۡبِسَكُمۡ شِيَعٗا وَيُذِيقَ بَعۡضَكُم بَأۡسَ بَعۡضٍۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَفۡقَهُونَ
Open ayah 6:65Ka ce: “Shi ne Mai cikakken ikon Ya aiko muku da azaba ta samanku ko ta ƙarƙashin ƙafafuwanku ko Ya mayar da ku ƙungiyoyi daban-daban, kuma Ya ɗanɗana wa sashinku azabar sashi.” Duba ka ga yadda Muke bayyana ayoyi, don su fahimta.
وَكَذَّبَ بِهِۦ قَوۡمُكَ وَهُوَ ٱلۡحَقُّۚ قُل لَّسۡتُ عَلَيۡكُم بِوَكِيلٖ
Open ayah 6:66Kuma mutanenka sun ƙaryata shi (Alƙur’ani) alhali shi ne gaskiya. Ka ce: “Ni ba wakili ne a kanku ba.
لِّكُلِّ نَبَإٖ مُّسۡتَقَرّٞۚ وَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 6:67“Kowane labari yana da lokaci ne na musamman. Kuma da sannu za ku sani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya tambayi masu yin shirka suna bauta wa wasu abubuwa ba shi ba, idan wata musifa ta tunkaro su yayin da suke tafiya a cikin duffai a bayan ƙasa ko a cikin teku, wane ne zai kuɓutar da su daga wannan musifar in ba Allah ba? Don haka shi kaɗai suke roƙa suna masu ƙasƙantar da kai, suna sirranta addu’o’insu tare da ɗaukar alƙawarin cewa idan ya kuɓutar da su daga wannan musifa, to lalle za su zama daga cikin masu godiya gare shi. Sai Allah ya bayyana musu cewa, bayan ya kuɓutar da su suna komawa ne ga bautar wasu tare da shi. To sai Allah ya umarci Manzon Allah (ﷺ), ya faɗa musu cewa, Allah ne shi kaɗai yake kuɓutar da su daga duk wata musifa da za su shiga, ya yaye musu duk wani baƙin ciki da zai dame su, to amma duk wannan bai hana su koma suna haɗa shi da wasu wajen bauta ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, yana da ikon ya saukar musu da azabarsa ta samansu, kamar ruwan duwatsu ko iska mai tsanani ko ya sako musu da azabarsa ta ƙarƙashin ƙafafuwansu, kamar girgizar ƙasa ko ambaliyar ruwa, hakanan yana da ikon ya jefa rashin jituwa a tsakaninsu, su yi ta faɗa, suna kashe-kashen junansu ko ya ɗora wasunsu a kan wasu, su yi ta azabtar da su. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da Allah ya saukar da faɗarsa: “Ka ce shi mai iko ne a kan ya aiko muku da azaba ta samanku,” sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ina neman tsari da fuskarka.” Da ya ce: “Ko ta ƙarƙashin ƙafafuwanku,” sai Annabi ya ce: “Ina neman tsari da fuskarka.” Da ya ce: “Ko kuma ya mayar da ku ƙungiya-ƙungiya, ya kuma ɗanɗana wa wasu uƙubar wasu,” sai ya ce: “Waɗannan biyun sun fi sauƙi.” [Bukhari #7313]. An karɓo daga Saubanu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce; “Lalle Allah ya tattaro min duniya wuri guda, sai na ga gabashinta da yammacinta, kuma mulkin al’ummata sai ya kai har inda aka tattaro mini, kuma an ba ni dukiya iri biyu, ja da fara, kuma na yi wa al’ummata addu’ar kada Allah ya halakar da su da fari na gaba ɗaya, kuma kada ya ɗora maƙiyansu a kansu su ƙarar da su gaba ɗaya, kuma Ubangijina ya faɗa mini cewa: “Ya Muhammadu, ni idan na yanke wani hukunci, to ba a mayar da shi, kuma ni na ba wa al’ummarka cewa, ba zan halakar da su gaba ɗayansu ta hanyar fari ba, kuma ba zan ɗora maƙiyansu a kansu ba har su ƙarar da su gaba ɗayansu, ko da kuwa za su yi musu taron dangi daga ko’ina a duniya, sai dai su a junansu wani sashi ya riƙa kashe wani sashi, ko wasu daga cikinsu su riƙa kama wasu a matsayin bayi.” [Muslim #2889]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya duba ya ga yadda yake sarrafa hujjoji iri-iri, yake bayyana musu gaskiya, ko sa fahimta, su bar aikata shirka da Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, Ƙuraishawa mutanen Annabi (ﷺ) sun ƙaryata Alƙur’ani alhalin shi gaskiya ne, sai ya umarce shi ya ce musu: Shi ba mai tsaron su ba ne; shi kawai mai isar da saƙo ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da su da cewa, duk wani labarin da Allah ya bayar, to akwai lokacin aukuwarsa, wanda ba zai yi jinkirin zuwa ba, kuma ba zai gabaci lokacin ba, kuma ba da daɗewa ba mushirikai za su ga azabar da ake yi musu alƙawarin zuwanta idan lokacinta ya zo.
وَإِذَا رَأَيۡتَ ٱلَّذِينَ يَخُوضُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦۚ وَإِمَّا يُنسِيَنَّكَ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَلَا تَقۡعُدۡ بَعۡدَ ٱلذِّكۡرَىٰ مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 6:68Kuma idan ka ga waɗanda suke kutsawa cikin ayoyinmu (suna izgili), to ka rabu da su, har sai sun canja wani zancen da ba wancan ba. Amma in da Shaiɗan zai mantar da kai kuwa, to bayan ka tuna kar ka sake zama tare da azzalumai.
وَمَا عَلَى ٱلَّذِينَ يَتَّقُونَ مِنۡ حِسَابِهِم مِّن شَيۡءٖ وَلَٰكِن ذِكۡرَىٰ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Open ayah 6:69Kuma babu wani laifi a kan waɗanda suke tsoron haɗuwarsu da Allah (don sun zauna da su), sai dai kuma (dole su yi) musu wa’azi don su tsorata.
وَذَرِ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَهُمۡ لَعِبٗا وَلَهۡوٗا وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ وَذَكِّرۡ بِهِۦٓ أَن تُبۡسَلَ نَفۡسُۢ بِمَا كَسَبَتۡ لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ وَإِن تَعۡدِلۡ كُلَّ عَدۡلٖ لَّا يُؤۡخَذۡ مِنۡهَآۗ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أُبۡسِلُواْ بِمَا كَسَبُواْۖ لَهُمۡ شَرَابٞ مِّنۡ حَمِيمٖ وَعَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ
Open ayah 6:70Ka rabu da waɗanda suka ɗauki addininsu wasa da sharholiya, rayuwarsu ta duniya kuma ta ruɗe su. Ka kuma yi gargaɗi da shi (Alƙur’ani), saboda kada a jarrabi rai da abin da ya aikata wanda ba ya da wani mataimaki ko mai ceto ban da Allah, ko da kuwa (ran) ya ba da kowace irin fansa ba za a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan su ne waɗanda aka kange (don yi musu azaba) saboda abin da suka aikata; suna da abin sha na tafasasshen ruwa da kuma azaba mai raɗaɗi saboda abin da suka zamanto suna kafircewa (da shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya kawar da kansa daga masu yin izgili da ayoyin Allah suna ƙaryata su, idan ya gansu suna irin wannan aiki, to kada ya zauna a majalisarsu har sai sun daina abin da suke yi ɗin nan, sun shiga wata hirar daban. To amma lokacin da Shaiɗan ya mantar da shi har ya zauna cikinsu, sannan daga bisani ya tuna, to ya yi maza-maza ya tashi daga wannan majalisa, kada ya ci gaba da zama tare da azzalumai bayan ya tuna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin cewa, idan muminai masu tsoron Allah suka guje wa masu izgili da ayoyin Allah, to babu wani laifi a kansu, amma kuma wajibi ne a kansu su ci gaba da yi musu wa’azi ko sa ji tsoron Allah su bar kafirci. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya rabu da mutanen da suka mayar da addinin Allah abin wasa da izgili suna ƙaryata ayoyin Allah, ya umarce shi da ya yi musu wa’azi da Alƙur’ani don su yi imani su bi gaskiya, don kada a tsare wani rai saboda zunubin da ya yi, ya rasa samun tsira duniya da lahira, ya faɗa halaka da azabar Allah a lokacin da babu mai kuɓutar da shi daga gareta, kuma ba mai ceton da zai nema masa afuwa a wurin Allah (Mai tsarki da daukaka). Kuma wannan rai duk abin da zai bayar domin ya fanshi kansa daga azabar Allah, ba za a karɓa ba. To waɗannan mutane su ne waɗanda aka riga aka danƙa su ga azabar Allah, wadda ba su da wata mafita daga cikinta, saboda irin ayyukan laifi da suka tafka a duniya, kuma suna da abin sha mai tsananin zafi da wata azaba mai raɗaɗi sakamakon kafircinsu a duniya.
قُلۡ أَنَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَىٰٓ أَعۡقَابِنَا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ كَٱلَّذِي ٱسۡتَهۡوَتۡهُ ٱلشَّيَٰطِينُ فِي ٱلۡأَرۡضِ حَيۡرَانَ لَهُۥٓ أَصۡحَٰبٞ يَدۡعُونَهُۥٓ إِلَى ٱلۡهُدَى ٱئۡتِنَاۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۖ وَأُمِرۡنَا لِنُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 6:71Ka ce: “Shin yanzu ma riƙa bauta wa wani wanda ba Allah ba, abin da ba zai amfane mu ba, kuma ba zai cutar da mu ba, mu koma gidan jiya (kafirai) bayan kuwa Allah Ya shiryar da mu, (mu koma) kamar wanda shaiɗanu suka ɓatar da shi yana ta ɗimuwa a bayan ƙasa, ga shi da wasu abokai suna kiran sa zuwa ga shiriya, (suna cewa): “Ka zo (mu bi tafarkin shiriya).” Ka ce: “Lalle shiriyar Allah fa ita kaɗai ce shiriya; kuma mu an umarce mu da mu miƙa wuya ne kaɗai ga Ubangijin talikai.
وَأَنۡ أَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّقُوهُۚ وَهُوَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
Open ayah 6:72“Kuma ku tsayar da salla kuma ku kiyaye dokokinsa. Kuma Shi ne Wanda za a tara ku zuwa gare Shi.
وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۖ وَيَوۡمَ يَقُولُ كُن فَيَكُونُۚ قَوۡلُهُ ٱلۡحَقُّۚ وَلَهُ ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِۚ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ
Open ayah 6:73“Kuma Shi ne Wanda ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya; kuma (ku tuna) ranar da zai ce da abu: ‘Kasance!’ Nan take sai ya kasance. Maganarsa gaskiya ce. Kuma Shi ne Yake da cikakken mulki a ranar da za a busa ƙaho Masanin gaibu da sarari, kuma Shi ne Mai hikima, Mai cikakken sani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa mushirikai cewa, yanzu ta yaya ma za mu bauta wa wasu abubuwa ba Allah ba, waɗanda ba za su amfane mu da komai ba komai ƙanƙantarsa, hakanan ba za su iya cutar da mu da komai ba don mun saɓa musu? Haka kawai mu koma cikin ɓata da kafirci bayan Allah ya riga ya shiryar da mu zuwa ga Musulunci, mu zama kamar mutumin da shaiɗanu suka kautar da shi daga kan hanyarsa, alhalin abokansa suna ta kiran sa ya dawo kan hanya wadda ita ce za ta kai shi wajen buƙatarsa, suna ta roƙon sa da ya biyo su don su haɗu tare da shi a kan shiriya? Sai aka umarci Manzon Allah ya faɗa musu cewa, shiriyar Allah ita ce shiriya ta gaskiya, kuma an umarce mu mu miƙa wuyanmu ga Allah, mu sallama wa shiriyarsa, kuma mu tsayar da salla, kuma mu ji tsoron sa ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi da barin abin da ya hana, domin a gabansa za a tara kowa da kowa ranar alƙiyama, ya saka wa kowa da irin aikin da ya yi na alheri ko sharri. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne mahaliccin sammai da ƙasa da ranar lahira wadda za ta tsaya da faɗarsa: ‘Kasance’, sai ta kasance tamkar ƙiftawar ido ko fiye da haka. Maganarsa kuma gaskiya ce, babu kokwanto cikinta, kuma shi ne wanda ya kaɗaita da mulki a wannan ranar, babu mai ja da shi, shi ne masanin abin da ke ɓoye da wanda yake a fili, babu abin da yake ɓuya daga gare shi, kuma gwani ne mai cikakkiyar hikima da yake ajiye komai a muhallinsa da ya dace, masanin komai, cikinsa da wajensa; ya san duk ayyukan bayinsa, don haka zai yi wa kowa sakamako gwargwadon aikinsa na alheri ko na sharri.
۞وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ ءَازَرَ أَتَتَّخِذُ أَصۡنَامًا ءَالِهَةً إِنِّيٓ أَرَىٰكَ وَقَوۡمَكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 6:74Kuma (ka tuna) lokacin da Ibrahimu ya ce da babansa Azaru: “Yanzu ka riƙi gumaka a matsayin alloli? Lalle ni ina ganin ka kai da mutanenka, kuna cikin ɓata mabayyani.”
وَكَذَٰلِكَ نُرِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ مَلَكُوتَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلِيَكُونَ مِنَ ٱلۡمُوقِنِينَ
Open ayah 6:75Kuma kamar haka ne Muke nuna wa Ibrahimu halittun sammai da ƙasa, domin ya kasance cikin masu sakankancewa.
فَلَمَّا جَنَّ عَلَيۡهِ ٱلَّيۡلُ رَءَا كَوۡكَبٗاۖ قَالَ هَٰذَا رَبِّيۖ فَلَمَّآ أَفَلَ قَالَ لَآ أُحِبُّ ٱلۡأٓفِلِينَ
Open ayah 6:76To yayin da dare ya lulluɓe shi, ya ga tauraro, sai ya ce; “Wannan shi ne ubangijina;” sannan yayin da ya ɓace, sai ya ce: “Ni fa ba na son abubuwa masu gushewa.”
فَلَمَّا رَءَا ٱلۡقَمَرَ بَازِغٗا قَالَ هَٰذَا رَبِّيۖ فَلَمَّآ أَفَلَ قَالَ لَئِن لَّمۡ يَهۡدِنِي رَبِّي لَأَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلضَّآلِّينَ
Open ayah 6:77Sa’annan yayin da ya ga wata ya fito, sai ya ce; “Wannan shi ne ubangijina;” sannan yayin da ya gushe, sai ya ce: “Lalle idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙiƙa zan kasance daga cikin mutane ɓatattu.”
فَلَمَّا رَءَا ٱلشَّمۡسَ بَازِغَةٗ قَالَ هَٰذَا رَبِّي هَٰذَآ أَكۡبَرُۖ فَلَمَّآ أَفَلَتۡ قَالَ يَٰقَوۡمِ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ
Open ayah 6:78Sannan yayin da ya ga rana ta hudo, sai ya ce: “Wannan shi ne ubangijina, wannan shi ya fi girma;” sannan yayin da ta ɓace, sai ya ce: “Ya ku mutanena, haƙiƙa ni ba ruwana da abin da kuke haɗa Allah da shi.
إِنِّي وَجَّهۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ حَنِيفٗاۖ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 6:79“Lalle ni kam na juyar da fuskata ga Wanda Ya halicci sammai da ƙasa, ina mai kauce wa ɓarna kuma ni ba na cikin masu yin shirka.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba mu labarin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa masu bauta wa taurari da rana da wata, cikinsu har da mahaifinsa mai suna Azaru. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya koya wa Annabi Ibrahimu hanyar da zai yi wa mutanensa wa’azi cikin hikima da lalama don ya ja hankalinsu har su fahimci abin da suka ɗauka shi ne Ubangiji suna bautarsa ba haka abin yake ba. Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fara wa’azinsa ta kan mahaifinsa, yayin da ya ce masa: “Yanzu ka riƙa bauta wa gumaka ba Allah ba? Ni ina ganin ka kai da mutanenka masu bautar gumaka kuna cikin ɓata mabayyani.” Don haka sai Allah ya nuna wa Annabi Ibrahimu hallittun da sama ta ƙunsa masu nuna girman mulkinsa don ya kafa wa mutanensa hujja da su a kan kaɗaita Allah da bauta, kuma ya zama cikin masu tabbaci a kan Tauhidi da yaƙini a kan hakan. To lokacin da dare ya rufe da duhunsa, taurari suka fito, sai Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fito cikin mutanensa ya ce musu: “Wannan ne ubangijina.” Bayan tauraro ya ɓace an daina ganin sa, sai ya ce musu: “Ni kuma ba na son abin bauta mai gushewa ya ɓace wa wanda yake bauta masa.” Don hakan yana nuna ba zai samu biyan buƙatarsa a wajensa ba. To sai kuma ya ga wata ya fito, sai ya ce musu: “Wannan shi ne ubangijina.” Bayan ya ɓace an daina ganin sa, sai Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce, idan dai ba Allah ne ya shiryar da shi ba, to tabbas zai zama daga cikin waɗannan ɓatattun mutanen. To yayin kuma da ya ga rana ta fito sai ya ce: “To wannan kam shi ne ubangijina, domin ya fi sauran girma.” To bayan rana ta faɗi an daina ganin ta, sai ya ce: “To ni dai daga yanzu ba ruwana da duk abin da kuke bauta wa wanda ba Allah ba; ni na juyar da fuskata ga Allah shi kaɗai, wanda shi ne ya ƙagi halittar sammai da ƙasa ba tare da ya kwaikwayi wani ba; ba ni ba hanyar shirka, ina tsaye ƙyam a kan Tauhidi, kuma ba zan taɓa zama cikin masu shirka ba.”
وَحَآجَّهُۥ قَوۡمُهُۥۚ قَالَ أَتُحَٰٓجُّوٓنِّي فِي ٱللَّهِ وَقَدۡ هَدَىٰنِۚ وَلَآ أَخَافُ مَا تُشۡرِكُونَ بِهِۦٓ إِلَّآ أَن يَشَآءَ رَبِّي شَيۡـٔٗاۚ وَسِعَ رَبِّي كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمًاۚ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 6:80Kuma mutanensa sun yi jayayya da shi; (sai) ya ce: “Shin yanzu kwa riƙa jayayya da ni game da (kaɗaitakar) Allah, alhalin kuwa Ya shiryar da ni? Kuma ba na jin tsoron abin da kuke sanya wa Allah kishiya da shi, sai abin da Ubangijina Ya ga dama. Kuma ilimin Ubangijina ya yalwaci komai. Shin ba za ku wa’azantu ba?
وَكَيۡفَ أَخَافُ مَآ أَشۡرَكۡتُمۡ وَلَا تَخَافُونَ أَنَّكُمۡ أَشۡرَكۡتُم بِٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ عَلَيۡكُمۡ سُلۡطَٰنٗاۚ فَأَيُّ ٱلۡفَرِيقَيۡنِ أَحَقُّ بِٱلۡأَمۡنِۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 6:81“To ta ƙaƙa kuwa zan ji tsoron abin da kuka tara da (Allah), alhali ku kuma ba kwa jin tsoron kun sanya wa Allah kishiya, abin da kuwa bai saukar muku da wata hujja a kai ba? To wane ɓangare ne cikin ɓangarori biyu, ya fi dacewa da samun aminci; in har kun kasance kun sani?
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَمۡ يَلۡبِسُوٓاْ إِيمَٰنَهُم بِظُلۡمٍ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلۡأَمۡنُ وَهُم مُّهۡتَدُونَ
Open ayah 6:82“Waɗanda suka yi imani, kuma ba su garwaya imaninsu da zalunci ba, waɗannan su suke da aminci, kuma su ne shiryayyu.”
وَتِلۡكَ حُجَّتُنَآ ءَاتَيۡنَٰهَآ إِبۡرَٰهِيمَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦۚ نَرۡفَعُ دَرَجَٰتٖ مَّن نَّشَآءُۗ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٞ
Open ayah 6:83Kuma waɗancan su ne hujjojinmu da Muka ba wa Ibrahimu su a kan mutanensa. Muna ɗaukaka darajojin waɗanda Muka ga dama. Lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Mai yawan sani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana nuna mana cewa, bayan Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya gama nuna wa mutanensa hujjoji na ƙuru-ƙuru, masu tabbatar da lalacewar bautar gumaka da taurari da wata da rana ba Allah ba, sai mutanensa suka bijire, suka shiga jayayya da shi game da bayanin Tauhidin Allah da wajabcin guje wa bautar gumaka, da cewa, yanzu ta yaya za su riƙa jayayya da shi a kan kaɗaita Allah, alhali ya nuna masa hanyar gaskiya kuma ya bi? To sai ya tabbatar musu cewa shi ba ya jin tsoron gumakansu da suke bauta wa ba Allah ba, domin ya san ba sa amfanarwa ba sa kuma cutarwa. Don haka ba su isa su yi masa komai ba, sai abin da Ubangijinsa ya ga dama ya same shi; ilimin Ubangijinsa kuma ya kewaye komai. To yanzu ba za su wa’azantu ba? Kuma ma ta yaya shi zai ji tsoron gumakan da suke haɗawa da Allah wajen bauta, alhali su ba sa jin tsoron yi wa Allah shirka da abin da bai saukar musu wata hujja a kansa ba, kuma ya yi imani Allah shi ne mai iko a kan komai? To sai aka yi tambaya cewa cikin ƙungiyoyin nan guda biyu wane ne ya fi cancanta ya samu aminci? Wanda ya kaɗaita Allah da bauta, ko kuma wanda ya yi shirka da Allah? Ai sai su ba da amsa idan sun kasance sun sani. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa tambayar Annabi Ibrahimu wadda take a fili da cewa: “Waɗanda suka yi imani, kuma ba su cuɗanya imaninsu da shirka ba, to waɗannan su ne masu aminci, kuma su ne shiryayyu.” An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’udu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da faɗar Allah ta sauka mai cewa: “Waɗanda suka yi imani…” har zuwa ƙarshe sai wannan ya damu sahabban Annabi (ﷺ), suka ce: “Wane ne a cikinmu bai zalunci kansa ba?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abin ba kamar yadda kuke zato ba ne; al’amarin ai kamar yadda Lukumanu ne yake faɗa wa ɗansa cewa: ‘Ya kai ɗana, kada ka yi shirka da Allah, lalle shirka zalunci ne mai girma.’ [Bukhari #6933, da Muslim #124]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan hujjarsa ce wadda ya bai wa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a kan mutanensa, kuma shi Allah yana ɗaukaka darajar wanda ya ga dama ne. Lalle kuma shi mai hikima ne, kuma mai cikakken sani.
وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ كُلًّا هَدَيۡنَاۚ وَنُوحًا هَدَيۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَمِن ذُرِّيَّتِهِۦ دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَىٰ وَهَٰرُونَۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 6:84Kuma Muka ba shi Ishaƙa da Ya’aƙubu. Kowanne daga cikinsu Mun shiryar da shi, kuma Mun shiryar da Nuhu tun gabaninsu. Kuma daga cikin zurriyarsa akwai Dawudu da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu kyautata (ayyukansu).
وَزَكَرِيَّا وَيَحۡيَىٰ وَعِيسَىٰ وَإِلۡيَاسَۖ كُلّٞ مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 6:85Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Iliyasu; kowanne daga cikinsu yana cikin salihan bayi.
وَإِسۡمَٰعِيلَ وَٱلۡيَسَعَ وَيُونُسَ وَلُوطٗاۚ وَكُلّٗا فَضَّلۡنَا عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 6:86Da Isma’ilu da Alyasa’u da Yunusu da Luɗu. Kowanne daga cikinsu kuma Mun fifita shi a kan (sauran) talikai.
وَمِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَذُرِّيَّٰتِهِمۡ وَإِخۡوَٰنِهِمۡۖ وَٱجۡتَبَيۡنَٰهُمۡ وَهَدَيۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 6:87Kuma daga cikin iyayensu da zurriyarsu da ‘yan’uwansu; duka Mun zaɓe su, kuma Mun shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici.
ذَٰلِكَ هُدَى ٱللَّهِ يَهۡدِي بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۚ وَلَوۡ أَشۡرَكُواْ لَحَبِطَ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 6:88Wannan ita ce shiriyar Allah wadda da ita ne Yake shiryar da wanda Ya ga dama cikin bayinsa. Kuma da a ce sun yi shirka, to lalle da duk abin da suka kasance suna aikatawa ya rushe.
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَۚ فَإِن يَكۡفُرۡ بِهَا هَٰٓؤُلَآءِ فَقَدۡ وَكَّلۡنَا بِهَا قَوۡمٗا لَّيۡسُواْ بِهَا بِكَٰفِرِينَ
Open ayah 6:89Waɗannan su ne waɗanda Muka bai wa littattafai da hukunci da annabta. To idan waɗancan (mutanen Makka) suka kafirce mata (shiriya), to haƙiƙa Mun shirya musu waɗansu mutane waɗanda ba za su kafirce mata ba.
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۖ فَبِهُدَىٰهُمُ ٱقۡتَدِهۡۗ قُل لَّآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًاۖ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 6:90Waɗannan su ne waɗanda Allah Ya shiryar; don haka ka yi koyi da irin shiriyarsu. Ka ce: “Ba na roƙon ku wani lada game da shi (Alƙur’ani); shi ba komai ba ne face tunatarwa ga talikai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin baiwar da ya yi wa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ta zuriyya ta ƙwarai, ya zaɓi annabawa da yawa daga cikinsu. Wannan daraja ce da babu irinta. Allah ya yi masa kyautar ɗansa Annabi Ishaƙa da jikansa Annabi Ya’aƙubu ɗan Is’haƙu, ya kuma shiryar da su gaba ɗaya zuwa ga miƙaƙƙen tafarki. Kuma Allah ya shiryar da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) tun gabanin Annabi Ibrahimu da ɗansa Annabi Ishaƙa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da jikansa Annabi Ya’aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Daga cikin zuriyyar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma akwai Annabi Dawudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Sulaimanu ɗan Dawudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Ayyuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ɗan’uwansa Annabi Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). To kamar yadda Allah ya datar da waɗannan manzanni, suka zama masu bin hanyar gaskiya, to hakanan yake kyautata sakamakonsa ga duk wanda ya kyautata aikinsa, shi ma zai datar da shi ya kama hanyar gaskiya, kuma ya samu zuriya ta ƙwarai masu yi masa addu’a a bayansa. Hakanan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiryar da Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Yahaya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Ilyasu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi); dukansu suna cikin mutanen kirki. Hakanan ya shiryar da Annabi Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Al-Yasa’u (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya fifita darajar waɗannan annabawa a zamunansu. Har ila yau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiryar da sashin iyayen annabawan can da aka ambata, ya shiryar da wasu daga cikin zurriyyarsu da wasu ‘yan’uwansu, ya zaɓe su ya ɗora su akan miƙaƙƙiyar hanya. To wannan shiriyar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa waɗannan annabawa da zurriyarsu, ita ce shiriyar da babu irinta; da ita yake shiryar da wanda ya ga dama daga bayinsa. Duk da haka waɗannan annabawan da a ce sun aikata shirka, to da duk ayyukansu na alheri sun rushe, ba za su amfane su da komai ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan annabawa ya saukar musu da littattafai, ya sanar da su hukunce-hukuncen da suka ƙunsa, sun kuma isar da saƙonsa. To da a ce kafiran Ƙuraishawa da sauran kafiran duniya sun bijire wa Annabi da Alƙur’anin da Allah ya saukar masa, to lalle Allah ya tanadar masa wasu mutane waɗanda ba za su kafirce masa ba, su ne sahabbansa da sauran muminai har zuwa tashin alƙiyama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yaba wa waɗannan annabawan da manzanni cewa su ne waɗanda ya shiryar da su suka riƙe addini na gaskiya, suka yi aiki da shi. Don haka sai ya umarci Annabinsa (ﷺ) da ya yi koyi da shiriyarsu, kuma ya faɗa wa mushrikai cewa, ba ya neman su biya shi wani lada a kan isar musu da saƙon Allah da yake yi; wannan aiki nasa kuma ba wani abu ne ba wanda ya wuce wa’azi ga talikai.
وَمَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦٓ إِذۡ قَالُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَىٰ بَشَرٖ مِّن شَيۡءٖۗ قُلۡ مَنۡ أَنزَلَ ٱلۡكِتَٰبَ ٱلَّذِي جَآءَ بِهِۦ مُوسَىٰ نُورٗا وَهُدٗى لِّلنَّاسِۖ تَجۡعَلُونَهُۥ قَرَاطِيسَ تُبۡدُونَهَا وَتُخۡفُونَ كَثِيرٗاۖ وَعُلِّمۡتُم مَّا لَمۡ تَعۡلَمُوٓاْ أَنتُمۡ وَلَآ ءَابَآؤُكُمۡۖ قُلِ ٱللَّهُۖ ثُمَّ ذَرۡهُمۡ فِي خَوۡضِهِمۡ يَلۡعَبُونَ
Open ayah 6:91Kuma ba su girmama Allah haƙiƙanin girman da ya kamace shi ba, yayin da suka ce: “Allah bai saukar wa wani mutum da komai ba.” Ka ce: “Wane ne ya saukar da littafin da Musa ya zo da shi, mai haske, kuma mai shiryar da mutane; kuka riƙa mayar da takardunsa falle-falle, kuna bayyana (waɗanda kuke so), kuma kuna ɓoye wani kaso mai yawa; kuma aka sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ma iyayenku?” Ka ce: “Allah ne (Ya saukar da shi)” Sannan sai ka ƙyale su su yi ta kutsawa cikin ɓarnarsu, suna wasa.
وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ مُّصَدِّقُ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَلِتُنذِرَ أُمَّ ٱلۡقُرَىٰ وَمَنۡ حَوۡلَهَاۚ وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۖ وَهُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ
Open ayah 6:92Kuma wannan (Alƙur’ani) littafi ne mai albarka, wanda Muka saukar da shi mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma don ka gargaɗi uwar alƙaryu (mutanen Makka) da waɗanda suke kewaye da ita. Waɗanda kuwa suke yin imani da ranar lahira, suna yin imani da shi ne (Alƙur’ani), kuma su suna kiyaye sallolinsu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana magana ne da masu musun annabcin Annabi (ﷺ) da ƙaryata wahayin da aka yi masa, inda ya ce, waɗannan kangararru ba su girmama Allah yadda ya kamata a girmama shi ba, da har suke cewa, wai babu wani ɗan’adam da Allah ya saukar masa da wani littafi ko ya yi masa wahayi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambaye su, wane ne ya saukar da littafin Attaura wanda Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo wa mutanensa da shi a matsayin haske da shiriya gare su amma suka mayar da shi takardu falle-falle suna bayyana wa mutane abin da suke son su sani, amma suna ɓoye wani sashe mai yawa daga cikinsa wanda ba sa so mutane su gani saboda ya ƙunshi siffofin Manzon Allah (ﷺ) da wasu hukunce-hukunce da ya zo da su, waɗanda suka saɓa wa son ransu? Bugu da ƙari kuma Allah ya sanar da su abin da su da iyayensu a da ba su sani ba. Sai Allah ya umarci Annabi ya ba su amsar waccan tambaya cewa, Allah ne ya yi duk waɗannan abubuwan da aka ambata. Sannan ya umarce shi da ya ƙyale su su yi ta shisshiginsu da kutsawa cikin ƙarya da kafirci da izgili, Allah yana ganin su, kuma ba da jimawa ba zai damƙe su da azabarsa. Sai kuma Allah ya tabbatar da cewa, wannan Alƙur’anin da ya saukar wa Annabi (ﷺ) littafi ne mai albarka, yana kuma gaskata littattafan da suka gabace shi. Kuma ya saukar masa shi ne don ya gargaɗi mutanen Makka da maƙotansu da sauran garuruwa da shi. Sannan ya bayyana cewa, mutanen da suka yarda akwai ranar lahira, sun yarda da wannan Alƙur’anin, kuma suna kula da tsayar da sallolinsu kamar yadda aka umarce su.
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمۡ يُوحَ إِلَيۡهِ شَيۡءٞ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثۡلَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ
Open ayah 6:93Kuma wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya ƙagi ƙarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya ce: “An yiwo mini wahayi,” alhalin kuma ba a yi masa wahayin komai ba, da kuma wanda ya ce: “Zan saukar da irin abin da Allah Ya saukar?” Kuma da za ka ga lokacin da kafirai suke cikin magagin mutuwa, mala’iku kuma suna miƙa hannayensu suna cewa: “Ku fito da rayukanku (da kanku), a yau ne za a saka muku da azabar wulaƙanci, saboda irin abin da kuke faɗa game da Allah wanda ba gaskiya ba, kuma kun kasance kuna girman kai game da ayoyinsa.”
وَلَقَدۡ جِئۡتُمُونَا فُرَٰدَىٰ كَمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَتَرَكۡتُم مَّا خَوَّلۡنَٰكُمۡ وَرَآءَ ظُهُورِكُمۡۖ وَمَا نَرَىٰ مَعَكُمۡ شُفَعَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ أَنَّهُمۡ فِيكُمۡ شُرَكَٰٓؤُاْۚ لَقَد تَّقَطَّعَ بَيۡنَكُمۡ وَضَلَّ عَنكُم مَّا كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Open ayah 6:94Kuma lalle haƙiƙa kun zo Mana ɗaiɗai kamar yadda Muka halicce ku a karon fari, kuma kun baro abin da Muka ba ku a bayanku (a duniya), kuma har yanzu ba Ma ganin masu ceton ku waɗanda kuka riya cewa su ne abokanan tarayyarku. Lalle haƙiƙa dangantakar da take tsakaninku ta yanke, kuma abin da kuke riyawa ya ɓace muku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, babu babban azzalumi kamar wanda ya ƙagi ƙarya ya jingina wa Allah (Mai tsarki da daukaka) ko kuma ya bushi iska ya ce Allah ya yi masa wahayi, alhalin ƙarya yake ba wani wahayi da ya yi masa ko kuma ya riƙa cika baki yana cewa, shi ma zai iya saukar da irin abin da Allah ya saukar. Sai kuma Allah ya nusantar da Annabi (ﷺ) cewa, da ya ga azzalumai lokacin da suke cikin magagin mutuwa, da bala’in raɗaɗin fitar rai da baƙin ciki sun taru sun lulluɓe su, da ba shakka ya ga abin mamaki da mawuyacin halin da suke ciki. A lokacin mala’iku ne suke ta jibgar su suna ce musu: “Ku fito da rayukanku da kanku daga gangar jikinku, a yau ne za ku ɗanɗani azabar wulaƙanci da ƙasƙanci sakamakon ƙaryar da kuke yi wa Allah da girman kan da kuke nunawa wanda ya hana ku ku yi imani da ayoyin Allah.” Sannan a ranar alƙiyama Allah (Mai tsarki da daukaka) zai titse su ya ce da su, a wannan rana ga su nan an baje su da ɗai-ɗai kamar yadda aka halicce su da farko, kuma duk ni’imomi da dukiya da ‘ya’ya da suka mora a duniya sun baro su a baya. Kuma waɗanda suke da’awar cewa su abokan tarayyarsu ne waɗanda suka yarda cewa za su cece su a wannan rana duk sun ɓace musu; alaƙar da take tsakaninsu da su gaba ɗaya ta yanke, kuma abin da suka kasance suna riyawa a wannan rana ya ɓace musu ɓat.
۞إِنَّ ٱللَّهَ فَالِقُ ٱلۡحَبِّ وَٱلنَّوَىٰۖ يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَمُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتِ مِنَ ٱلۡحَيِّۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ
Open ayah 6:95Lalle Allah ne Yake tsaga ƙwaya da ƙwallon dabino (lokacin tsirowarsa) shi Yake fitar da rayayye daga matacce, kuma Mai fitar da matacce daga rayayye. Mai yin wannan aiki Shi ne Allah; to ta yaya ake kautar da ku?
فَالِقُ ٱلۡإِصۡبَاحِ وَجَعَلَ ٱلَّيۡلَ سَكَنٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ حُسۡبَانٗاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ
Open ayah 6:96(Shi ne) Mai keto da hasken safiya, kuma Ya sanya dare don nutsuwa; rana da wata kuma don ƙidayar lokatai. Wannan shiri ne na (Allah) Mabuwayi, Mai yawan sani.
وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلنُّجُومَ لِتَهۡتَدُواْ بِهَا فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۗ قَدۡ فَصَّلۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 6:97Kuma Shi ne Wanda Ya sanya muku taurari domin ku gane hanya da su a cikin duffan tudu da na ruwa. Haƙiƙa Mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke da sani.
وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ فَمُسۡتَقَرّٞ وَمُسۡتَوۡدَعٞۗ قَدۡ فَصَّلۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَفۡقَهُونَ
Open ayah 6:98Kuma Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai ɗaya, sannan Ya ajiye ku a wani wurin zama (tsatson namiji) da kuma wani wurin ajiya, (mahaifiyar mace). Haƙiƙa Mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke fahimta.
وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ نَبَاتَ كُلِّ شَيۡءٖ فَأَخۡرَجۡنَا مِنۡهُ خَضِرٗا نُّخۡرِجُ مِنۡهُ حَبّٗا مُّتَرَاكِبٗا وَمِنَ ٱلنَّخۡلِ مِن طَلۡعِهَا قِنۡوَانٞ دَانِيَةٞ وَجَنَّٰتٖ مِّنۡ أَعۡنَابٖ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلرُّمَّانَ مُشۡتَبِهٗا وَغَيۡرَ مُتَشَٰبِهٍۗ ٱنظُرُوٓاْ إِلَىٰ ثَمَرِهِۦٓ إِذَآ أَثۡمَرَ وَيَنۡعِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكُمۡ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 6:99Kuma Shi ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, sai Muka fitar da kowane irin dangin tsiro da shi, sannan Muka fitar da shi (tsiron) (wasu) koraye, daga gare shi kuma Muke fitar da ƙwayoyi a cunkushe daga gare shi. Kuma daga hudar dabino (ake samun) nonuna waɗanda suke dab da ƙasa; da kuma waɗansu lambuna na inabi da zaitun da ruman, masu kama da juna da kuma mabambanta. Ku kalli ‘ya’yansu idan suka yi ‘ya’ya da kuma lokacin da suka nuna. Lalle game da wannan akwai ayoyi ga mutanen da suka yi imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cikar ikonsa da hikimarsa da cewa, shi ne yake tsaga ƙwaya ya fitar da shuka daga cikinta, ya kuma tsaga ƙwallon dabino ya fitar da itaciya daga cikinsa. Yana kuma fitar da mai rai daga matacce, ya fitar da matacce daga mai rai, kamar yadda yake fitar da mutum daga ɗigon maniyyi kuma ya fitar da maniyyi daga mutum, ko kaza daga ƙwai ko ƙwai daga kaza. Hakanan kuma shi yake fitar da mumini daga tsatson kafiri, ko ya fitar da kafiri daga tsatson mumini. To wanda yake yin haka fa shi ne Allah (Mai tsarki da daukaka), to ta yaya ake kautar da kafirai daga gaskiya bayan bayyanar waɗannan hujjoji masu ƙarfi, har su riƙa bautar wasu ba Allah ba? Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma shi ne mai keto da hasken safiya daga duhun dare, kuma ya sanya dare ya zamo lokacin samun nutsuwa da hutu ga duk wani mai kujuba-kujuba da rana; rana da wata kuma ya nufa suna gudana a kan wani ƙididdigaggen lissafi wanda ba ya saɓawa. To wannan ƙaddarawa ce ta Allah Mabuwayi mai cikakken sani. Haka kuma ya sanya taurari a matsayin alamu da matafiya suke amfani da su wajen gane hanyoyi a cikin duffan tudu da teku. Haƙiƙa Allah ya bayyana ayoyi daki-daki ga mutane masu ilimi. Hakanan kuma ya halicci mutane gaba ɗaya daga tsatson Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), shi kuma ya halicce shi ne da taɓo tun farko. Amma su mutane daga ɗigon maniyyi ne da Allah ya sanya a tsatson iyayensu, sannan ya zaunar da ɗigon maniyyin a cikin mahaifun iyayensu mata har zuwa lokacin haihuwarsu. Allah yana bayanin ayoyinsa daki-daki ne don mutane masu tunani su fahimci manufofin Ubangiji. Wata ƙudurar ta Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ita ce saukar da ruwan sama, wanda da shi ne yake fitar da kowanne irin tsiro; daga kowane tsiro ne kuma Allah ya fitar da shukoki da itatuwa koraye, sannan ya halicci ƙwaya da ‘ya’yan itatuwa daga waɗannan tsirrai wasu kan wasu, kamar zangarniya da kuma hantsa-hantsa ta dabino daga hudarsa dab da ƙasa mai sauƙin tsinka. Kuma ya fitar da gonaki na inabi da bishiyoyin zaitun da rumman waɗanda ganyayensu suke kama da juna amma ‘ya’yansu da ɗanɗanonsu suka sha bamban. Ya kuma umarci bayinsa da su kalli ‘ya’yan itatuwan lokacin da suka fito da lokacin girmansu da nunarsu, kallo na tuntuntuni da ɗaukar darasi, domin a cikin waɗannan abubuwa akwai ayoyi ga mutane masu yin imani.
وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ ٱلۡجِنَّ وَخَلَقَهُمۡۖ وَخَرَقُواْ لَهُۥ بَنِينَ وَبَنَٰتِۭ بِغَيۡرِ عِلۡمٖۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يَصِفُونَ
Open ayah 6:100Kuma sun sanya wa Allah aljannu a matsayin abokanan tarayya, alhali kuwa Shi ya halicce su; kuma suka ƙago masa ‘ya’ya maza da mata, ba tare da wani ilimi ba. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga irin abin da suke siffanta (Shi da shi).
بَدِيعُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُۥ وَلَدٞ وَلَمۡ تَكُن لَّهُۥ صَٰحِبَةٞۖ وَخَلَقَ كُلَّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ
Open ayah 6:101(Shi ne) Maƙagin sammai da ƙasa; ta yaya zai zama Yana da ɗa, ga Shi kuma ba Shi da mata? Kuma Shi ne Ya halicci komai, kuma Shi Masanin komai ne.
ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ فَٱعۡبُدُوهُۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ
Open ayah 6:102Wannan Shi ne Allah Ubangijinku; ba wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Mahaliccin komai, don haka ku bauta masa. Kuma Shi Mai kiyayewa ne da komai.
لَّا تُدۡرِكُهُ ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَهُوَ يُدۡرِكُ ٱلۡأَبۡصَٰرَۖ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلۡخَبِيرُ
Open ayah 6:103Gannai ba sa riskar Sa, Shi ne Yake riskar gannai, kuma Shi Mai tausasawa ne, Mai cikakken sani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, mushirikai sun mayar da aljannu ababen bauta tare da Allah, alhalin shi ya halicce su, maimakon su bauta wa Allah mahaliccin kowa da komai. Sun kuma ƙira wa Allah ƙaryar cewa yana da ‘ya’ya maza da mata, ba tare da suna da wata hujja a kan haka ba, don kawai jahilci da rashin sanin girman Allah. Allah ya tsarkaka, kuma ya ɗaukaka daga duk abin da waɗannan mushirikai suke siffanta shi da shi. Shi ne kuma wanda ya ƙagi halittar sammai da ƙasa ba tare da ya kwaikwaya a wurin wani ba; ta yaya kuma za a ce yana da ɗa ko mata, alhali shi ne ya halicci komai? Don haka shi cikakken mawadaci ne, ba shi da buƙatar komai a wurin wani mahaluƙi, shi ne wanda ake da buƙata a wurinsa, kuma shi ne masanin komai, babu abin da yake ɓoye masa. To wannan fa shi ne Allah (Mai tsarki da daukaka) wanda shi kaɗai ya cancanta a bauta wa, shi ne Ubangijin talikai, babu wani abin bauta da gaskiya sai shi, mahaliccin komai. Don haka sai kowa ya bauta masa, ya amince da Kaɗaitakarsa, kuma shi wakili ne a kan komai; idanu kuma ba za su iya riskar sa da kallo ba, shi ne wanda iliminsa da jinsa da ganinsa suka kewaye komai, kuma shi ne mai tausasawa, mai cikakken sani.
قَدۡ جَآءَكُم بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَنۡ أَبۡصَرَ فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ عَمِيَ فَعَلَيۡهَاۚ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِحَفِيظٖ
Open ayah 6:104Haƙiƙa hujjoji sun zo muku daga Ubangijinku; don haka duk wanda ya gan su (ya bi su), to ya yi don amfanin kansa ne; duk kuwa wanda ya makance, to kansa ya cuta. Kuma ni ba mai tsaron ku ba ne.
وَكَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ وَلِيَقُولُواْ دَرَسۡتَ وَلِنُبَيِّنَهُۥ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 6:105Kuma kamar haka ne Muke bayyana ayoyi, don (kafirai) su ce: “Ka koya ne (daga wasu littattafai)”, kuma don Mu bayyana shi (Alƙur’ani) ga mutanen da suke ganewa.
ٱتَّبِعۡ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 6:106Ka bi abin da aka yi maka wahayi daga Ubangijinka; ba abin bautawa da gaskiya sai Shi; kuma ka kawar da kai daga mushrikai.
وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَآ أَشۡرَكُواْۗ وَمَا جَعَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظٗاۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٖ
Open ayah 6:107Kuma da Allah Ya ga dama, da ba su yi shirka ba. Ba Mu kuma sanya ka mai tsaro a kansu ba; kuma kai ba wakili ne a gare su ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar wa mutane cewa, bayyanannun dalilai da ƙarfafan hujjoji a kan gaskiyar Alƙur’ani sun zo musu; a cikinsu Allah ya bayyana ƙudurarsa da cikakken ikonsa. Duk wanda ya fahimci waɗannan hujjoji, ya yi imani da su, to kansa ne zai amfana, duk wanda kuma ya ƙi imani da su, ya yi watsi da abin da suke tabbatarwa, to kansa kaɗai zai cutar, Manzon Allah (ﷺ) ba shi ne mai tsaron su ko wanda yake lissafa ayyukansu ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma yana bayyana hujjoji da dalilai ta hanyoyi daban-daban a wannan Surar, domin tabbatar da Tauhidin Ubangiji. Da ma kuma Allah ya saba yin bayanin ayoyinsa ga mutane ta hanyoyi daban-daban a cikin wannan Alƙur’ani, domin kawar da zargin duk wani wanda zuciyarsa ta makance mai cewa, wai Annabi (ﷺ) ya koyo wannan Alƙur’ani ne daga malaman Yahudawa ko Nasara. Kuma Allah Ta’ala yana yin waɗannan bayanai ne domin mutane masu ilimi su fahimta, kuma su karɓa su yi aiki da su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) cewa, ya bi tafarkin Alƙur’ani wanda ya yi masa wahayinsa, tafarkin da yake tabbatar da Allah shi kaɗai ne abin bauta, babu wani abin bautawa ba shi ba, ya kuma umarce shi da ya yi watsi da tafarkin mushirikai masu haɗa Allah da wani cikin bauta. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, da ya ga dama da sai ya ɗora mushirikai a kan hanyar shiriya, sai dai kuma Allah bai nufe su da shiriya ba, sai suka taɓe. Kuma ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, bai saka shi mai tsaron kafirai, ya sa ido a kan ayyukansu ko rayuwarsu ba; wannan aikin Allah ne. Kuma bai wakilta shi a kan yi musu hisabi na ayyukan da suke yi ba.
وَلَا تَسُبُّواْ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ فَيَسُبُّواْ ٱللَّهَ عَدۡوَۢا بِغَيۡرِ عِلۡمٖۗ كَذَٰلِكَ زَيَّنَّا لِكُلِّ أُمَّةٍ عَمَلَهُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِم مَّرۡجِعُهُمۡ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 6:108Kuma kada ku zagi waɗanda suke bauta wa ba Allah ba, sai su zagi Allah saboda zalunci, ba tare da sanin (girmansa) ba. Kamar haka ne Muka ƙawata wa kowace al’umma ayyukansu (nagari da munana), sannan zuwa ga Ubangijinsu ne makomarsu take, sai Ya ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa.
وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَئِن جَآءَتۡهُمۡ ءَايَةٞ لَّيُؤۡمِنُنَّ بِهَاۚ قُلۡ إِنَّمَا ٱلۡأٓيَٰتُ عِندَ ٱللَّهِۖ وَمَا يُشۡعِرُكُمۡ أَنَّهَآ إِذَا جَآءَتۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 6:109Kuma sun rantse da Allah iyakar gaskiyarsu cewa, lalle idan har aya ta zo musu, tabbas za su yi imani da ita. Ka ce: “Ai ayoyi daga wajen Allah suke.” Kuma wa ya sanar da ku cewa, idan (ayoyin) sun zo ba za su yi imani ba?
وَنُقَلِّبُ أَفۡـِٔدَتَهُمۡ وَأَبۡصَٰرَهُمۡ كَمَا لَمۡ يُؤۡمِنُواْ بِهِۦٓ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَنَذَرُهُمۡ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ
Open ayah 6:110Kuma za Mu riƙa jujjuya zukatansu da gannansu, (daga fahimta da ganin gaskiya) kamar yadda ba su yi imani da shi ba da farko, Mu kuma bar su cikin shisshiginsu suna ɗimuwa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai su zagi abin bautar wasu don kada su ma su rama su zagi Allah (Mai tsarki da daukaka) saboda rashin sanin girmansa. Kamar yadda Allah ya ƙawata wa waɗannan mushirikan ayyukan da suke yi na shirka, hakanan ya ƙawata wa kowace al’umma ayyukanta. Sannan makomarsu gaba ɗaya zuwa ga Allah ne, zai kuma labarta musu duk abin da suka aikata kuma ya yi musu sakayya a kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, mushirkai sun rantse iya rantsuwarsu cewa, idan wata mu’ujiza da suka nema ta zo musu, to lalle za su yi imani da ita cewa daga Allah take. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, mu’ujizoji duka suna hannun Allah, shi ne idan ya ga dama zai nuna musu ita, idan kuma ya ga dama ya ƙi amsa buƙatarsu. Sai kuma Allah ya ankarar da muminai cewa, wa ya sanar da su cewa idan mu’ujizar ta zo za su ba da gaskiya su yi imani da ita? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, shi ne mai jujjuya zukatansu da gannansu su kasa fahimtar gaskiya, su kuma kasa ganin ta, saboda sun ƙi yin imani da Alƙur’ani tun lokacin da Annabi (ﷺ) ya zo musu da shi, kuma Allah zai ƙyale su cikin shisshiginsu da taurin kansu suna ta ɗimuwa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Zukatan ‘yan’adam gaba ɗaya suna tsakanin ‘yan yatsu biyu na Allah mai rahama ne, kamar zuciya ɗaya, yana jujjuya ta yadda ya ga dama.” Sai kuma Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya Allah mai jujjuya zukata, ka juya zukatanmu a kan ɗa’arka.” [Muslim #2654].
۞وَلَوۡ أَنَّنَا نَزَّلۡنَآ إِلَيۡهِمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ وَكَلَّمَهُمُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَحَشَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ كُلَّ شَيۡءٖ قُبُلٗا مَّا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُوٓاْ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ يَجۡهَلُونَ
Open ayah 6:111Kuma Mu ɗin nan da a ce lalle za Mu saukar musu da mala’iku, kuma matattu su yi musu magana, kuma Mu tattaro musu komai a gabansu, to da ba za su taɓa yin imani ba, sai dai idan Allah Ya ga dama, amma yawancinsu suna jahilta ne.
وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا شَيَٰطِينَ ٱلۡإِنسِ وَٱلۡجِنِّ يُوحِي بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ زُخۡرُفَ ٱلۡقَوۡلِ غُرُورٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ
Open ayah 6:112Kuma kamar haka ne Muka sanya wa kowane annabi maƙiya daga shaiɗanun mutane da aljannu, sashinsu yana kimsa wa wani sashi ƙayataccen zance, don ruɗi. Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da ba su aikata haka ba; don haka ka ƙyale su da irin abin da suke ƙagowa.
وَلِتَصۡغَىٰٓ إِلَيۡهِ أَفۡـِٔدَةُ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ وَلِيَرۡضَوۡهُ وَلِيَقۡتَرِفُواْ مَا هُم مُّقۡتَرِفُونَ
Open ayah 6:113Don kuma zukatan waɗanda ba su yi imani da lahira ba su karkata zuwa gare shi, kuma su yarda da shi (ruɗin) kuma su ci gaba da ƙago abin da suke ƙagowa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, da ya amsa buƙatar masu neman a nuna musu wata mu’ujiza mai tabbatar da gaskiyar Manzon Allah (ﷺ), da Allah ya amsa musu ya saukar musu da mala’iku su gan su ƙuru-ƙuru, ko ya tayar musu da matattu su sanar da su cewa, Annabi Manzon Allah ne da gaske, ko kuma ya tattara musu duk wata halitta dodo dodo a gabansu su gaya musu gaskiyar annabtar Annabi (ﷺ), to da ba za su ba da gaskiya ba sai Allah ya ga dama, sai dai kuma yawancinsu suna jahiltar hakan. Sai kuma Allah ya bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, kamar yadda ya jarrabe shi da maƙiya cikin mutane da aljannu waɗanda suke faɗa da shi da da’awarsa, to hakanan ya jarrabi sauran annabawa da maƙiya irin waɗannan. Ya zo cikin hadisin A’isha (Allah ya kara mata yarda) cewa, Waraƙatu ɗan Naufalu ya faɗa wa Annabi (ﷺ) lokacin da Nana Khadija (Allah ya kara mata yarda) ta je da shi wajensa cewa: “Babu wani mutum da ya zo da irin abin da ka zo da shi, face sai an yi gaba da shi.” [Bukhari #3, da Muslim #160]. Shaiɗanun aljannu a cikinsu suna kimsa wa shaiɗanun mutane maganganu na ƙarya waɗanda suke ƙawata kalmominsu don ruɗar mutane da su. Da Allah ya ga dama da ba za su yi hakan ba, sai dai ya riga ya ƙaddara komai yadda hikimarsa ta gudana. Sai kuma ya umarci Annabinsa (ﷺ) cewa, ya ƙyale su, ya kuma yi watsi da ƙarairayinsu da suke ƙagawa. Hakanan shaiɗanun aljannu suna saƙa wa shaiɗanun mutane wasu ƙawatattun maganganu na ƙarya domin zukatan waɗanda ba su yi imani da lahira ba su karkata gare su, kuma su yarda da su, kuma su aikata abin da za su aikata na kafirci da saɓon Allah a sanadiyarsu.
أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡتَغِي حَكَمٗا وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مُفَصَّلٗاۚ وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡلَمُونَ أَنَّهُۥ مُنَزَّلٞ مِّن رَّبِّكَ بِٱلۡحَقِّۖ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ
Open ayah 6:114(Ka ce) “Shin wanin Allah zan nema a matsayin mai yi mana hukunci, alhalin Shi ne wanda Ya saukar muku da littafi mai bayani dalla-dalla?” Waɗanda Muka ba su littafi kuwa suna sane da cewa, lalle shi saukakke ne daga Ubangijinka da gaskiya; don haka lalle kada ka kasance daga cikin masu kokwanto.
وَتَمَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ صِدۡقٗا وَعَدۡلٗاۚ لَّا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِهِۦۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 6:115Kuma kalmomin Ubangijinka cike suke da gaskiya da adalci. Babu kuma mai canza kalmominsa; kuma Shi ne Mai ji, Masani.
وَإِن تُطِعۡ أَكۡثَرَ مَن فِي ٱلۡأَرۡضِ يُضِلُّوكَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنۡ هُمۡ إِلَّا يَخۡرُصُونَ
Open ayah 6:116Kuma in da za ka yi biyayya ga mafiya yawan waɗanda suke a bayan ƙasa to za su ɓatar da kai daga tafarkin Allah. Babu abin da suke bi face zato, kuma ba abin da suke yi face ƙarya.
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ مَن يَضِلُّ عَن سَبِيلِهِۦۖ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ
Open ayah 6:117Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin waɗanda suke ɓace wa tafarkinsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabinsa (ﷺ) ya tambayi mushirikai cewa, wanin Allah suke so ya nema a matsayin mai yi masa hukunci, alhalin shi ne ya saukar masa da littafin Alƙur’ani, wanda yake cike da bayanan hukunce-hukunce daki-daki, har da bayanin abin da suke jayayya a kansa na lamarin aƙida da shari’a? Hasali ma Yahudawa da Allah ya ba su ilimin Attaura sun san cewa Alƙur’ani gaskiya ne daga Allah yake. Sai kuma ya hane shi da yin shakkar komai game da Alƙur’ani. Duk da cewa an yi wannan hani ne ga Annabi (ﷺ), amma ana nufin al’ummarsa, domin shi ba zai taɓa shakka ba game da kasancewar Alƙur’ani wahayi ne daga Allah zuwa gare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, kalmominsa cikakku ne babu tawaya a cikinsu, kuma suna ƙunshe da labaru na gaskiya da kuma hukunce-hukunce na cikakken adalci, don haka babu wata damar canza wani abu daga kalmominsa (Mai tsarki da daukaka); shi kuma mai jin duk maganganun bayinsa ne, kuma masanin ayyukansu, zai kuma saka musu gwargwadon ayyukansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fuskantar da maganarsa ga Annabi (ﷺ) da cewa, idan da zai yi biyayya ga yawancin mutanen duniya, to ba shakka da za su ɓatar da shi daga kan addinin Allah, domin kuwa ba wani abu suke bi ba sai zace-zacen ƙarya da shaci-faɗi. Sai kuma ya tabbatar da cewa, ya fi kowa sanin wanda ya kauce wa shiriya, ya kuma fi kowa sanin shiryayyu.
فَكُلُواْ مِمَّا ذُكِرَ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ إِن كُنتُم بِـَٔايَٰتِهِۦ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 6:118To ku ci abin da aka ambaci sunan Allah a kansa (lokacin yankansa), in har kun kasance masu imani da ayoyinsa.
وَمَا لَكُمۡ أَلَّا تَأۡكُلُواْ مِمَّا ذُكِرَ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَقَدۡ فَصَّلَ لَكُم مَّا حَرَّمَ عَلَيۡكُمۡ إِلَّا مَا ٱضۡطُرِرۡتُمۡ إِلَيۡهِۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا لَّيُضِلُّونَ بِأَهۡوَآئِهِم بِغَيۡرِ عِلۡمٍۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُعۡتَدِينَ
Open ayah 6:119Kuma me ya sa ba za ku ci abin da aka ambaci sunan Allah a kansa ba, alhali Ya bayyana muku abin da Ya haramta muku, sai fa abin da kuka matsu game da shi? Kuma lalle yawancinsu ba shakka suna ɓatar da waɗansu ne ta hanyar bin son zuciyarsu, ba tare da ilimi ba. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin masu ƙetare iyaka.
وَذَرُواْ ظَٰهِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَبَاطِنَهُۥٓۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡسِبُونَ ٱلۡإِثۡمَ سَيُجۡزَوۡنَ بِمَا كَانُواْ يَقۡتَرِفُونَ
Open ayah 6:120Kuma ku bar (aikata) laifuka na sarari da na ɓoye. Haƙiƙa waɗanda suke aikata saɓo, za a saka musu da irin abin da suke aikatawa.
وَلَا تَأۡكُلُواْ مِمَّا لَمۡ يُذۡكَرِ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَإِنَّهُۥ لَفِسۡقٞۗ وَإِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ لَيُوحُونَ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِهِمۡ لِيُجَٰدِلُوكُمۡۖ وَإِنۡ أَطَعۡتُمُوهُمۡ إِنَّكُمۡ لَمُشۡرِكُونَ
Open ayah 6:121Kuma kada ku ci daga abin da ba a ambaci sunan Allah a kansa ba, kuma lalle shi tabbas fasiƙanci ne. Haƙiƙa shaiɗanu tabbas suna kimsa wa masoyansu, don su yi jayayya da ku; idan kuwa kuka bi su to lalle tabbas ku mushirikai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin hukuncin yankan dabba ne da kuma mayar da martani ga mushirikan Larabawa masu yanka dabbobinsu da sunan gumakansu a madadin sunan Allah. Ya umarci bayinsa muminai da su ci abin da aka yanka da sunan Allah (Mai tsarki da daukaka) idan har sun yi imani da ayoyinsa da hujjojin da ya saukar musu a Alƙur’ani da kuma bayanan da Manzon Allah (ﷺ) yake yi musu. Ya kuma ƙara da cewa, me zai hana su cin dabbar da aka yanka ta da sunan Allah, alhalin ya riga ya yi musu bayani filla-filla na abubuwan da aka haramta musu cin su in dai ba bisa larura ba? Ya bayyana cewa, da yawan mutane suna ɓacewa kuma suna ɓatar da wasu ba tare da wata hujja ba, kuma Allah ne mafi sanin masu ƙetare iyakokinsa, su haramta abin da bai haramta ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa bayinsa kashedi da su guji saɓa masa a fili ko a ɓoye. Ya bayyana cewa, duk wanda ya saɓa wa wannan umarni nasa, ya aikata laifi, to zai ga sakamakon laifinsa. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana bayinsa cin naman dabbar da ba a yanka ta da sunansa ba, domin cin namanta rashin biyayya ne gare shi. Ya kuma bayyana cewa, shaiɗanu suna jefa wa ‘yan’uwansu mushirikai wani nau’i na ruɗani don su riƙa jayayya da muminai da su. Sukan yi wa muminai zolaya da cewa: “Shin yanzu ku kun yarda ku ci dabbar da kuka kashe da hannunku, amma ba ku yarda ku ci wadda Allah ya kashe da kansa ba?” Wato suna nufin mushen dabbobi. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Larabawa mushirikai suna cewa: “Duk abin da aka yanka shi da sunan Allah kada ku ci, amma ku ci wanda ba a ambaci sunan Allah ba lokacin yankansa.” Sai Allah ya saukar da faɗarsa: “Kuma kada ku ci abin da ba a ambaci sunan Allah a kansa ba.” [Abu Dawuda #2818, da Ibni Majah #3173]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa wa muminai cewa, idan har suka yarda suka yi biyayya ga mushirikai, suka halatta cin mushe da abin da Allah ya haramta musu, to su ma sun zama mushirikai kamarsu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu mutane sun zo wajen Manzon Allah (ﷺ) suka ce masa: “Ya Manzon Allah, yanzu ma riƙa cin abin da muka kashe, amma kuma ba za mu ci abin da Allah ya kashe ba?” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi.” [Tirmizi #3069].
أَوَمَن كَانَ مَيۡتٗا فَأَحۡيَيۡنَٰهُ وَجَعَلۡنَا لَهُۥ نُورٗا يَمۡشِي بِهِۦ فِي ٱلنَّاسِ كَمَن مَّثَلُهُۥ فِي ٱلظُّلُمَٰتِ لَيۡسَ بِخَارِجٖ مِّنۡهَاۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلۡكَٰفِرِينَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 6:122Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka ƙawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa.
وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا فِي كُلِّ قَرۡيَةٍ أَكَٰبِرَ مُجۡرِمِيهَا لِيَمۡكُرُواْ فِيهَاۖ وَمَا يَمۡكُرُونَ إِلَّا بِأَنفُسِهِمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 6:123Kuma kamar haka ne a cikin kowace ƙasa Muka sanya manyan masu laifinta, don su yi makirci a cikinta; kuma ba wanda suke ƙulla wa makirci sai kawunansu, amma su ba sa jin (haka).
وَإِذَا جَآءَتۡهُمۡ ءَايَةٞ قَالُواْ لَن نُّؤۡمِنَ حَتَّىٰ نُؤۡتَىٰ مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ رُسُلُ ٱللَّهِۘ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ حَيۡثُ يَجۡعَلُ رِسَالَتَهُۥۗ سَيُصِيبُ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ صَغَارٌ عِندَ ٱللَّهِ وَعَذَابٞ شَدِيدُۢ بِمَا كَانُواْ يَمۡكُرُونَ
Open ayah 6:124Kuma idan wata aya ta zo musu, sai su ce: “Ba za mu yi imani ba, har sai an ba mu kwatankwacin abin da aka ba wa manzannin Allah.” Ai Allah Shi ne Mafi sanin inda ya dace Ya sanya manzancinsa. Da sannu ƙasƙanci daga Allah zai auka wa waɗanda suka aikata manyan laifuka da kuma azaba mai tsanani, saboda abin da suka kasance suna shiryawa na makirci.
فَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يَهۡدِيَهُۥ يَشۡرَحۡ صَدۡرَهُۥ لِلۡإِسۡلَٰمِۖ وَمَن يُرِدۡ أَن يُضِلَّهُۥ يَجۡعَلۡ صَدۡرَهُۥ ضَيِّقًا حَرَجٗا كَأَنَّمَا يَصَّعَّدُ فِي ٱلسَّمَآءِۚ كَذَٰلِكَ يَجۡعَلُ ٱللَّهُ ٱلرِّجۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 6:125Sannan duk wanda Allah Ya yi nufin shiryar da shi, sai Ya yalwata ƙirjinsa ga karɓar Musulunci. Duk wanda kuwa Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa a ƙuntace ainun kamar wanda yake yunƙurin hawa sama. Kamar haka ne Allah Yake sanya ɓata a kan waɗanda ba sa yin imani.
وَهَٰذَا صِرَٰطُ رَبِّكَ مُسۡتَقِيمٗاۗ قَدۡ فَصَّلۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَذَّكَّرُونَ
Open ayah 6:126Kuma wannan shi ne tafarkin Ubangijinka miƙaƙƙe. Haƙiƙa Mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke tuntuntuni.
۞لَهُمۡ دَارُ ٱلسَّلَٰمِ عِندَ رَبِّهِمۡۖ وَهُوَ وَلِيُّهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 6:127Suna da gida na aminci a wurin Ubangijinsu, kuma Shi ne Majiɓincinsu, saboda abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yin gwaji tsakanin mutumin da yake kafiri, yana fagamniya cikin duhun ɓata da jahilci, sai Allah ya shiryar da shi ya musulunta, ya raya masa zuciya da imani, ya sanya masa haske na shiriya, yana tafiya da shi a cikin mutane; wannan ba zai taɓa zama daidai da wanda ya ci gaba da rayuwa cikin duhun kafirci da jahilci, ya kasa fita daga cikinsa ba. Kamar yadda aka ƙawata wa kafirai masu jayayya a kan cin mushe ayyukansu na jahiliyya, har suke ganin su kyawawa, to hakanan aka ƙawata wa masu kafirce wa Allah da ayoyinsa munanan aƙidunsu da ayyukansu na ɓata. Haka kuma a cikin kowace al’umma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya manyan masu laifi, waɗanda suke kiran mutanensu zuwa ɓata da kafirci, suke hana su bin addinin Allah da karɓar gaskiya. To duk wani makirci da suke ƙullawa kansu zai dawo, su ne ba su fahimci haka ba. Kuma idan wata hujja mai ƙarfi ta zo wa waɗannan manyan masu laifin, tana tabbatar da gaskiyar manzancin Annabi (ﷺ), sai su sa ƙafa su shure ta, su ce su ba za su taɓa yarda ba har sai su ma an ba su manzanci irin wanda aka ba wa Manzanin Allah. Sai Allah ya mayar musu da martani da cewa, shi ya fi sanin inda ya dace ya ajiye manzancinsa, da wanda ya cancanta ya aiko a matsayin manzo ga mutane. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ƙasƙanci da wulaƙanci da azabar Allah mai tsanani za su auka wa masu waɗannan laifukan saboda makircin da suka riƙa ƙulla wa Musulmi da Musulunci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya nufe shi da shiriya, to zai buɗa masa ƙirjinsa ya karɓi Musulunci, wanda kuma ya nufe shi da ɓata, to zai sanya ƙirjinsa ya ƙuntata, hasken imani ya ƙi shigar sa. Misalinsa kamar misalin wanda zai matsa wa kansa hawa sama amma ya kasa domin ba zai iya ba, sai dai ya yi ta numfashi sama-sama kamar ransa zai fita. To kamar haka ne Allah yake ɗora Shaiɗan a kan wanda ya ƙi karɓar gaskiya, ya ɓatar da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, duk abin da ya bayyana masa a cikin wannan Surar da sauran surorin Alƙur’ani, shi ne abin da ya riga ya zama addininsa, kuma miƙaƙƙiyar hanya wadda zai bi shi da mabiyansa, kuma Allah ya yi bayanin hujjojinsa daki-daki, masu nuna gaskiyar Musulunci ga mutane masu wa’azantuwa, kuma su ne suke da gidan aminci, wato gidan Aljanna a wajen Ubangijinsu, domin shi ne majiɓincin al’amuransu saboda abin da suka kasance suna aikatawa.
وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ قَدِ ٱسۡتَكۡثَرۡتُم مِّنَ ٱلۡإِنسِۖ وَقَالَ أَوۡلِيَآؤُهُم مِّنَ ٱلۡإِنسِ رَبَّنَا ٱسۡتَمۡتَعَ بَعۡضُنَا بِبَعۡضٖ وَبَلَغۡنَآ أَجَلَنَا ٱلَّذِيٓ أَجَّلۡتَ لَنَاۚ قَالَ ٱلنَّارُ مَثۡوَىٰكُمۡ خَٰلِدِينَ فِيهَآ إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٞ
Open ayah 6:128Kuma (ka tuna) ranar da zai tara su gaba ɗaya (Ya ce): “Ya ku jama’ar aljannu, haƙiƙa kun samu mabiya da yawa daga cikin mutane.” Sai majiɓinta lamarinsu cikin mutane su ce: “Ya Ubangijinmu; mun dai daɗaɗa wa junanmu kuma mun kawo ƙarshen lokacin da Ka yanka mana.” Sai Ya ce: “Wuta ita ce makomarku, za ku dawwama a cikinta, sai dai abin da Allah Ya ga dama.” Lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Mai yawan sani.
وَكَذَٰلِكَ نُوَلِّي بَعۡضَ ٱلظَّٰلِمِينَ بَعۡضَۢا بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 6:129Kuma kamar haka ne Muke ɗora wani sashi na azzalumai a kan wani sashi, saboda abin da suka kasance suna aikatawa.
يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي وَيُنذِرُونَكُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَاۚ قَالُواْ شَهِدۡنَا عَلَىٰٓ أَنفُسِنَاۖ وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَشَهِدُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰفِرِينَ
Open ayah 6:130Ya ku jama’ar aljannu da mutane, shin manzanni daga cikinku ba su zo muku ba, suna karanta muku ayoyina, kuma suna gargaɗin ku game da saduwarku da wannan yini?” Sai su ce: “Mun ba da shaida a kan kawunanmu;” rayuwar duniya kuma ta ruɗe su, kuma suka yi wa kansu shaidar cewa lalle su sun kasance kafirai.
ذَٰلِكَ أَن لَّمۡ يَكُن رَّبُّكَ مُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ بِظُلۡمٖ وَأَهۡلُهَا غَٰفِلُونَ
Open ayah 6:131Haka ta faru ne, saboda Ubangijinka bai zamanto Mai hallakar da wata alƙarya saboda kafircewarta ba, alhali mutanenta suna cikin gafala. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabi (ﷺ) ne ranar da zai tattara mushirikai tare da shaiɗanun aljannu iyayen gidansu, sai ya ce wa aljannu: Haƙiƙa sun ɓatar da mutane da yawa. Sai mabiyansu mutane su bayar da amsa suna shaida wa Ubangijinsu cewa, sun dai daɗaɗa wa junansu ne kawai; aljani ya ji daɗin biyayyar da mutum ya yi masa, shi kuma mutum ya ji daɗin hidimar da aljani ya yi masa da biya masa wasu buƙatunsa na son zuciya, kuma ga shi sun kawo ƙarshen lokacin da aka yanka musu na mutuwa ko na zaman duniya. Sai Allah ya tabbatar musu cewa, wuta ce makomarsu ta har abada, sai dai abin da Allah ya ga dama, kamar fitar da waɗanda laifinsu bai kai ga kafirci ba. Lalle Allah Ubangiji mai hikima ne a cikin duk ayyukansa, kuma masani ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda ya ɗora wasu shaiɗanun aljannu a kan wasu karkatattun mutane suka ɓatar da su, to hakanan yake ɗora wasu azzalumai a kan wasu su yi ta gallaza musu azaba iri-iri ba yadda suka iya, saboda irin abin da suka kasance suna aikatawa na zalunci da saɓa wa Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, a ranar alƙiyama zai kira taron aljannu da na mutane, ya tambaye su cewa, shin manzanni daga cikinsu ba su je musu suna karanta musu ayoyinsa ba, kuma suna gargaɗin su game da saduwarsu da wannan rana? Sai su tabbatar masa da cewa, lalle waɗannan manzanni sun je musu, kuma sun faɗa musu gaskiya, to amma sai suka ƙi yarda, suka ƙaryata su. Allah ya bayyana cewa, rayuwar duniya ce ta ruɗe su har suka ƙaryata annabawa, to ga su a wannan rana suna bayar da shaida da kansu cewa su kafirai ne masu laifi. Daga nan sai Allah ya nuna cewa, wannan gargaɗi da tsawatarwa da manzanni suka yi ta yi a duniya ya faru ne domin kada Allah ya halakar da wata ƙasa saboda kafircinta, alhali ba a gargaɗe su an yanke musu hanzari ba ta hanyar aiko musu da wani manzo da hujjoji bayyanannu.
وَلِكُلّٖ دَرَجَٰتٞ مِّمَّا عَمِلُواْۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ
Open ayah 6:132Kuma kowanne yana da nasa matsayi game da abin da suka aikata, kuma Ubangijinka bai zama Mai rafkana ba dangane da abin da suke aikatawa.
وَرَبُّكَ ٱلۡغَنِيُّ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۚ إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفۡ مِنۢ بَعۡدِكُم مَّا يَشَآءُ كَمَآ أَنشَأَكُم مِّن ذُرِّيَّةِ قَوۡمٍ ءَاخَرِينَ
Open ayah 6:133Kuma Ubangijinka Shi ne Mawadaci, Mai rahama. Idan Ya ga dama sai Ya tafiyar da ku, kuma Ya maye gurbinku da waɗanda Ya ga dama, kamar yadda Ya fare ku daga zurriyar waɗansu mutanen daban.
إِنَّ مَا تُوعَدُونَ لَأٓتٖۖ وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ
Open ayah 6:134Lalle abin da ake yi Muku alƙawarinsa mai zuwa ne; kuma ku ba za ku iya kuɓucewa (daga azabarmu) ba.
قُلۡ يَٰقَوۡمِ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنِّي عَامِلٞۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 6:135Ka ce: “Ya ku mutanena, ku yi aiki a kan irin hanyarku, lalle ni ma mai yin aiki ne (kan hanyata); don haka da sannu za ku san wanda zai yi kyakkyawan ƙarshe. Lalle su dai azzalumai ba za su rabauta ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa mutane suna da matsayi iri daban-daban a lahira, kowa gwargwadon aikinsa, gwargwadon matsayinsa, wanda ya yi aikin alheri ya ga alheri, wanda ya yi mummunan aiki kuma ya ga mummunan sakamako. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa shi mawadaci ne, ba ya buƙata a wurin kowa, shi ne ake da buƙata a wurinsa, kuma mai rahama ne ga bayinsa, yana saka musu da lada fiye da ayyukansu, yana yafe musu laifukansu bai damu ba. Idan ya ga dama yana iya hallaka duk wanda yake a bayan ƙasa, ya halicci wasu mutanen daban waɗanda za su yi masa biyayya, ba za su saɓa masa ba, kamar yadda ya samar da waɗannan mutanen daga zurriyyar wasu mutanen daban. An karɓo daga Abu Zarri (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ji daga Allah yana cewa: “….ya ku bayina, lalle ku ba ku isa ku cuce ni ba balle ku cutar da ni, kuma ba ku isa ku amfane ni ba, balle har ku amfanar da ni. Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljannunku, za su zama suna da zuciya irin ta wanda ya fi kowa tsoron Allah, wannan ba zai ƙara komai a cikin mulkina ba. Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljannunku, za su zama suna da zuciya irin ta wanda ya fi kowa fajirci, wannan ba zai rage komai daga mulkina ba....” [Muslim #2577]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, azabar da yake yi wa kafirai gargaɗi da ita tana nan tafe babu makawa, kuma su ba za su iya tsere mata ba. Sannan ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa mushirikan Ƙuraishawa cewa, idan ya yi kiran su kan su yi imani sun ƙi su amsa masa, to su ci gaba da aikin da suka zaɓar wa kansu, shi ma zai ci gaba da bin umarnin Ubangijinsa; lokacin da azaba ta zo musu za su gane wane ne yake kan hanyar shiriya, wanda kuma zai yi kyakkyawan ƙarshe a duniya da lahira, muminai ne ko kafirai? Haƙiƙa su dai azzalumai ba sa rabauta duniya da lahira. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah yana jinkirta wa azzalumi, amma duk sa’adda ya damƙe shi, to ba zai iya kuɓuce masa ba.” Sai Annabi (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: “Haka kuwa damƙar Ubangijinka take, idan ya damƙi alƙaryu yayin da suka yi zalunci, lalle damƙarsa mai raɗaɗi ce mai tsanani.” [Bukhari #4686].
وَجَعَلُواْ لِلَّهِ مِمَّا ذَرَأَ مِنَ ٱلۡحَرۡثِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ نَصِيبٗا فَقَالُواْ هَٰذَا لِلَّهِ بِزَعۡمِهِمۡ وَهَٰذَا لِشُرَكَآئِنَاۖ فَمَا كَانَ لِشُرَكَآئِهِمۡ فَلَا يَصِلُ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَا كَانَ لِلَّهِ فَهُوَ يَصِلُ إِلَىٰ شُرَكَآئِهِمۡۗ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ
Open ayah 6:136Kuma sun sanya wa Allah wani kaso cikin abin da Ya halitta na amfanin gona da dabbobin gida, sai suka riƙa cewa: “Wannan kaso na Allah ne”, a riyawarsu, “Wannan kuma na gumakanmu ne;” sannan abin da ya kasance na gumakansu ba zai isa ga Allah ba; abin da kuwa ya kasance na Allah, to shi zai isa ga gumakansu. Abin da suke hukuntawa ya munana.
وَكَذَٰلِكَ زَيَّنَ لِكَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ قَتۡلَ أَوۡلَٰدِهِمۡ شُرَكَآؤُهُمۡ لِيُرۡدُوهُمۡ وَلِيَلۡبِسُواْ عَلَيۡهِمۡ دِينَهُمۡۖ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ
Open ayah 6:137Kuma kamar haka ne abokan tarayyarsu suka ƙawata wa yawancin mushirikai su dinga kashe ‘ya’yansu, don su hallakar da su, kuma don su rikita musu addininsu. Kuma da Allah Ya ga dama da ba su aikata haka ba. To ka ƙyale su da irin abin da suke ƙagawa.
وَقَالُواْ هَٰذِهِۦٓ أَنۡعَٰمٞ وَحَرۡثٌ حِجۡرٞ لَّا يَطۡعَمُهَآ إِلَّا مَن نَّشَآءُ بِزَعۡمِهِمۡ وَأَنۡعَٰمٌ حُرِّمَتۡ ظُهُورُهَا وَأَنۡعَٰمٞ لَّا يَذۡكُرُونَ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَا ٱفۡتِرَآءً عَلَيۡهِۚ سَيَجۡزِيهِم بِمَا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 6:138Kuma suka ce: “Waɗannan dabbobi na gida da kuma amfanin gona haramtattu ne, ba wanda zai ci su sai wanda muka ga dama,” a riyawarsu. Waɗansu dabbobin kuma an haramta hawansu, waɗansu dabbobin kuma ba sa ambaton sunan Allah a kansu (yayin yankan su), don kawai su yi masa ƙage. Da sannu zai yi musu sakamakon abin da suka kasance suna ƙagawa.
وَقَالُواْ مَا فِي بُطُونِ هَٰذِهِ ٱلۡأَنۡعَٰمِ خَالِصَةٞ لِّذُكُورِنَا وَمُحَرَّمٌ عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِنَاۖ وَإِن يَكُن مَّيۡتَةٗ فَهُمۡ فِيهِ شُرَكَآءُۚ سَيَجۡزِيهِمۡ وَصۡفَهُمۡۚ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٞ
Open ayah 6:139Kuma suka ce: “Abin da yake cikin waɗannan dabbobi, a keɓance yake ga mazajenmu, amma haramun ne ga matayenmu.” Idan kuma ya zamo mushe, to su duka sai su yi tarayya a kansa. Da sannu (Allah) zai yi musu sakayyar wannan abin da suka siffanta. Lalle Shi Mai hikima ne, Mai yawan sani.
قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ قَتَلُوٓاْ أَوۡلَٰدَهُمۡ سَفَهَۢا بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَحَرَّمُواْ مَا رَزَقَهُمُ ٱللَّهُ ٱفۡتِرَآءً عَلَى ٱللَّهِۚ قَدۡ ضَلُّواْ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ
Open ayah 6:140Haƙiƙa waɗannan da suka kashe ‘ya’yansu don wauta, ba tare da ilimi ba sun taɓe, kuma suka haramta wa kansu abin da Allah Ya arzuta su da shi, don ƙage ga Allah. Haƙiƙa sun ɓata, kuma ba su kasance shiryayyu ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin irin rashin hankali da wautar da mushirikan Larabawa suka riƙa yi a lokacin jahiliyya kafin zuwan Musulunci. Watau amfanin gona da suka noma da dabbobinsu sukan kasa shi kaso biyu, kaso ɗaya su ce na Allah ne, kaso na biyu kuwa su ce na gumakansu, duk kuwa da cewa gaba ɗayansu Allah ne ya halicce su. Sannan kuma idan wani kason da suka ware wa gumakansu ya shiga cikin kason Allah, to sai su dawo da shi wurinsa, amma idan kason da suka ware wa Allah ya gauraya a cikin kason gumakansu, to ba za su dawo da shi wurinsa ba, sai su bar shi ba tare da sun damu ba. Wannan hukunci nasu kuwa ya yi muni. Hakanan shaiɗanun da suke bauta wa ba Allah ba sun ƙawata musu su riƙa kashe ‘ya’yansu, don su hallaka su, su rikirkita musu addininsu. Da kuwa Allah ya ga dama da ya hana su irin wannan ɗanyen aiki, to sai dai bisa hikimarsa ya ƙyale su suna ta biyayya ga shaiɗanunsu suna ci gaba da kashe ‘ya’yansu. Sai Allah ya umarci Annabi (ﷺ) ya rabu da su da irin ƙarairayin da suke ƙagawa suna jingina wa Allah, ba za su cuce shi da komai ba. Wata katoɓarar kuma ta mushirikai ita ce, sai su ware wasu dabbobi da wani amfanin gona su ce wannan haramun ne wani ya ci su, sai wanda suka ga dama suka yi wa izini. Suna yin haka kuwa ba tare da wata hujja ko madogara ba sai dai ƙarya kawai. Hakanan kuma suna ware wasu dabbobi su haramta a hau su; wasu kuma ba za su ambaci sunan Allah a kansu ba, don haka ba za a yi hajji a kansu ba, hakanan idan an hau su ko an zo tatsar nononsu ko za a yanka su, to ba za a kira sunan Allah ba. Sai Allah ya ce, zai saka musu a kan abin da suka kasance suna ƙirƙira. Wata ƙaryar kuma ita ce, mushirikai sukan ware wasu dabbobi su ce maza ne kaɗai ya halatta su ci abin da za su haifa ko su sha nononsu, amma wannan haramun ne ga mata. Amma kuma idan abin da suka haifa bai zo da rai ba ko ya mutu bayan an haife shi, to wannan maza da mata za su yi tarayya wajen cin namansa. Sai Allah ya bayyana cewa, zai saka wa masu yi masa ƙarya suna haramta abin da ya halatta, su halatta abin da ya haramta. Lalle kuma Allah masani ne mai hikima. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mushirikai masu kashe ‘ya’yansu don wauta da rashin hankali da rashin ilimi, suna haramta abin da Allah ya arzuta su da shi don ƙaga masa ƙarya, waɗannan sun yi muguwar asara, kuma sun kauce wa hanyar shiriya, ba su yi sa’ar dace da ita ba.
۞وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَ جَنَّٰتٖ مَّعۡرُوشَٰتٖ وَغَيۡرَ مَعۡرُوشَٰتٖ وَٱلنَّخۡلَ وَٱلزَّرۡعَ مُخۡتَلِفًا أُكُلُهُۥ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلرُّمَّانَ مُتَشَٰبِهٗا وَغَيۡرَ مُتَشَٰبِهٖۚ كُلُواْ مِن ثَمَرِهِۦٓ إِذَآ أَثۡمَرَ وَءَاتُواْ حَقَّهُۥ يَوۡمَ حَصَادِهِۦۖ وَلَا تُسۡرِفُوٓاْۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Open ayah 6:141Kuma Shi ne Wanda Ya halicci lambuna waɗanda suke da tsirrai masu yaɗo da marasa yaɗo da kuma dabino da shukoki waɗanda suka sha bamban da juna wajen ɗanɗanonsu, da kuma zaitun da ruman, mai kama da juna, da wanda ba ya kama da juna. Ku ci daga ‘ya’yansa, idan ya yi ‘ya’ya, kuma ku bayar da zakkarsa a ranar girbinsa, kuma kada ku yi almubazzaranci. Lalle Shi (Allah) ba Ya son masu almubazzaranci.
وَمِنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ حَمُولَةٗ وَفَرۡشٗاۚ كُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Open ayah 6:142Daga cikin dabbobin gida kuma akwai masu ɗaukan kaya da kuma ƙanana. Ku ci daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma kada ku bi hanyoyin Shaiɗan. Lalle shi maƙiyi ne mai bayyana ƙiyayya a gare ku. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin abubuwan da ya samar wa ɗan’adam na gonaki da lambuna waɗanda suke cike da itatuwa da shuke-shuke iri-iri masu ‘ya’ya da ganyayyaki daban-daban. Daga cikinsu akwai masu yaɗo suna bin ƙasa ko shinge da waɗanda suke tsaye a kan itatuwansu. Hakanan ya halicci itatuwan dabino da shuke-shuke mabambanta ɗanɗano da kuma zaitun da rumman waɗanda ganyayyakinsu suke kama da juna amma ‘ya’yansu da ɗanɗanonsu suka sha bamban. Allah ya umarci bayinsa da su ci ‘ya’yan itatuwansu idan sun yi ‘ya’ya, kuma su fitar da zakkarsu a ranar girbi, ya kuma hana su yin almubazzaranci domin shi ba ya son masu almubazzaranci da abinci ko dukiya. Da farko an umarci manoma da su ba da haƙƙin amfanin gonarsu ba tare da bayanin gwargwadon abin da za su fitar ba, sai daga baya ne shari’a ta yi bayanin gwargwadon abin da za a fitar na zakkar amfanin gona, wanda shi ne kaso ɗaya cikin goma (ushuri), idan noman damina ne, ko kaso ɗaya ciki ashirin (rabin ushuri), idan noman rani ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi ne ya halicci dabbobi masu ɗaukar kaya da mutane, kamar raƙuma da shanu da ƙananan dabbobi, ya kuma umarce su da su ci daga abin da ya arzuta su da shi, ya halatta musu cin sa. Ya kuma hana su bin hanyoyin Shaiɗan domin shi Shaiɗan maƙiyinsu ne na sarari.
ثَمَٰنِيَةَ أَزۡوَٰجٖۖ مِّنَ ٱلضَّأۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَمِنَ ٱلۡمَعۡزِ ٱثۡنَيۡنِۗ قُلۡ ءَآلذَّكَرَيۡنِ حَرَّمَ أَمِ ٱلۡأُنثَيَيۡنِ أَمَّا ٱشۡتَمَلَتۡ عَلَيۡهِ أَرۡحَامُ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۖ نَبِّـُٔونِي بِعِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 6:143(Dabbobin) nau’i takwas ne, daga tumaki akwai jinsi biyu, haka kuma daga awaki akwai jinsi biyu. Ka ce: “Shin mazan biyu ne Ya haramta ko kuma matan biyu ko kuma abin da yake cikin mahaifar matan biyu? Ku ba ni labari da ilimi in kun kasance ku masu gaskiya ne.”
وَمِنَ ٱلۡإِبِلِ ٱثۡنَيۡنِ وَمِنَ ٱلۡبَقَرِ ٱثۡنَيۡنِۗ قُلۡ ءَآلذَّكَرَيۡنِ حَرَّمَ أَمِ ٱلۡأُنثَيَيۡنِ أَمَّا ٱشۡتَمَلَتۡ عَلَيۡهِ أَرۡحَامُ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۖ أَمۡ كُنتُمۡ شُهَدَآءَ إِذۡ وَصَّىٰكُمُ ٱللَّهُ بِهَٰذَاۚ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا لِّيُضِلَّ ٱلنَّاسَ بِغَيۡرِ عِلۡمٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 6:144Haka kuma raƙuma akwai jinsi biyu, daga cikin shanu ma akwai jinsi biyu. Ka ce: “Shin mazan guda biyu Ya haramta ko matan biyu ko kuma abin da yake cikin mahaifar matan biyu ya haramta ko kuma kun zama shaidu yayin da Allah Ya yi muku wasicci da wannan abin?” To ba wanda ya fi zaluntar kansa fiye da wanda ya ƙirƙiri ƙarya, ya jingina wa Allah don ya ɓatar da mutane ba tare da ilimi ba. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin nau’ukan dabbobin da ya halatta cin namansu su takwas: Akwai tumakai guda biyu, wato rago da tinkiya, akwai kuma awaki su ma guda biyu, wato akuya da taure. Allah ya umarci Annabi Muhammad (ﷺ) ya tambayi kafirai masu haramta cin naman wasu keɓatattun dabbobi ko hawan su da ɗora musu kaya ko hana mata cin naman wasu dabbobi sai maza kaɗai ko hana mata cin naman ‘ya’yan da waɗannan dabbobi suka haifa, sai dai idan ba su zo da rai ba ko sun mutu bayan haihuwa, ya tambaye su wane jinsi ne Allah ya haramta a cikinsu, jinsin maza ko na mata ko abin da cikkunan matan suka ƙunsa? Ba ɗaya daga cikin waɗannan kashe-kashe da zai zama amsarsu. Don haka sai ya umarce shi da ya sa su kawo wani labari na gaskiya da ilimi a kan bambancin da ke tsakanin dabbobin da suka haramta da kuma waɗanda suka halatta, idan har sun kasance su masu gaskiya ne a da’awarsu da ƙaryar da suke jingina wa Allah da ƙage. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci sauran nau’ukan dabbobin guda huɗu, su ne raƙuma, wato raƙumi da taguwa, sai shanu, wato sa da saniya, su ma ya umarci Annabi (ﷺ) ya sake maimaita musu irin waccan tambayar domin su faɗa masa bambanci tsakanin dabbobin da suka haramta da waɗanda suka halatta. To idan ba su da amsar da za su bayar, me ya sa suka haramta wasu suka halatta wasu? Ko sun halarci wurin da Allah ya tara su ya yi musu wasiyya da hakan? Wannan ma bai faru ba. To daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu babban azzalumi kamar wanda yake yi wa Allah ƙarya don kawai ya ɓatar da mutane ba da wani ilimi ba. To haƙiƙa Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai.
قُل لَّآ أَجِدُ فِي مَآ أُوحِيَ إِلَيَّ مُحَرَّمًا عَلَىٰ طَاعِمٖ يَطۡعَمُهُۥٓ إِلَّآ أَن يَكُونَ مَيۡتَةً أَوۡ دَمٗا مَّسۡفُوحًا أَوۡ لَحۡمَ خِنزِيرٖ فَإِنَّهُۥ رِجۡسٌ أَوۡ فِسۡقًا أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ رَبَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 6:145Ka ce: “Daga cikin abin da aka sauƙar mini na manzanci ban samu wani abinci da aka haramta cinsa ba, sai fa idan ya zamo mushe ne ko jini mai kwarara, ko kuma naman alade, to lalle wannan ƙazanta ne, ko kuma abin da ya zamo fasiƙanci ne wanda aka yanka shi ba da sunan Allah ba.” Sannan wanda ya matsu, ba tare da shisshigi ba, kuma ba yana mai ƙetare iyaka ba, to lalle Ubangijinka Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
وَعَلَى ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا كُلَّ ذِي ظُفُرٖۖ وَمِنَ ٱلۡبَقَرِ وَٱلۡغَنَمِ حَرَّمۡنَا عَلَيۡهِمۡ شُحُومَهُمَآ إِلَّا مَا حَمَلَتۡ ظُهُورُهُمَآ أَوِ ٱلۡحَوَايَآ أَوۡ مَا ٱخۡتَلَطَ بِعَظۡمٖۚ ذَٰلِكَ جَزَيۡنَٰهُم بِبَغۡيِهِمۡۖ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ
Open ayah 6:146Kuma Mun haramta wa Yahudawa duk wata dabba mai kofato; daga shanu da tumaki kuwa Mun haramta musu kitsensu, sai abin da gadon bayansu yake ɗauke da shi ko kayan cikinsu ko abin da ya cakuɗu da ƙashi. Wannan Mun Yi musu sakamako da shi ne saboda zaluncinsu; kuma lalle Mu tabbas Masu gaskiya ne.
فَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل رَّبُّكُمۡ ذُو رَحۡمَةٖ وَٰسِعَةٖ وَلَا يُرَدُّ بَأۡسُهُۥ عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 6:147Sannan idan sun ƙaryata ka, to ka ce: “Ubangijinku Ma’abocin rahama mayalwaciya ne . Kuma ba a iya mayar da azabarsa daga mutanen da suke masu laifi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa waɗannan kafirai masu haramta abin da Allah ya arzuta su da shi cewa, shi dai bai ga wani abu da Allah ya haramta masa cin sa ba daga cikin abubuwan da suke haramtawa, sai guda huɗu, watau mushe da jini mai kwarara da naman alade, waɗannan ukun ƙazanta ce kuma najasa; na huɗu shi ne abin da aka yanka da sunan wanin Allah; shi kuma wannan saɓon Allah ne. To amma duk wanda ya shiga halin matsuwa, ya rasa abinci sai ɗayan waɗannan abubuwa da aka haramta, to sai ya ci ba da niyyar morewa ba ko barin halal zuwa haram; to lalle Allah mai gafara ne mai jin ƙai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata uƙubar da ya yi wa Yahudawa saboda yawan laifukansu, watau ya haramta musu cin naman duk wata dabba mai farata, da kitsen shanu da tumaki, sai dai kitsen dake gadon bayan waɗannan dabbobi ko wanda yake tare da kayan ciki, ko wanda yake haɗe da ƙashi, kamar kitsen naman cinya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu wannan uƙubar ce saboda kafircinsu da zaluncinsu, kuma lalle shi Allah tabbas mai gaskiya ne a duk maganganunsa da ayyukansa da hukunce-hukuncensa. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Annabinsa cewa, idan kafirai sun ƙaryata shi, to su sani Ubangijinsu mai yalwatacciyar rahama ne ga wanda ya bi shi, don haka su yi gaggawa wajen neman rahamarsa, su aikata abin da yake umartar su da shi, su bar abin da yake hana su. Yana daga cikin rahamarsa jinkirtawar da yake yi musu, ba ya gaggauto musu da azabarsa, to amma su sani idan har azabarsa ta zo, babu mai hana ta sauka a kan mutane masu laifi.
سَيَقُولُ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ لَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَآ أَشۡرَكۡنَا وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمۡنَا مِن شَيۡءٖۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ حَتَّىٰ ذَاقُواْ بَأۡسَنَاۗ قُلۡ هَلۡ عِندَكُم مِّنۡ عِلۡمٖ فَتُخۡرِجُوهُ لَنَآۖ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا تَخۡرُصُونَ
Open ayah 6:148Waɗanda suke yin shirka za su ce: “Da Allah Ya ga dama, da ba mu yi shirka ba, haka iyayenmu ma da ba su yi ba, kuma da ba mu haramta wani abu ba.” Kamar haka ne waɗanda suka gabace su suka ƙaryata (manzanni), har sai da suka ɗanɗani azabarmu. Ka ce: “Shin kuna da wata hujja ce da za ku fito mana da ita? Ba fa abin da kuke bi sai zato, kuma ku (ba a kan komai kuke ba) face shaci-faɗi.”
قُلۡ فَلِلَّهِ ٱلۡحُجَّةُ ٱلۡبَٰلِغَةُۖ فَلَوۡ شَآءَ لَهَدَىٰكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 6:149Ka ce: “To a wurin Allah ne cikakkiyar hujja take; kuma da Ya ga dama, tabbas da Ya shiryar da ku gaba ɗaya.”
قُلۡ هَلُمَّ شُهَدَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ يَشۡهَدُونَ أَنَّ ٱللَّهَ حَرَّمَ هَٰذَاۖ فَإِن شَهِدُواْ فَلَا تَشۡهَدۡ مَعَهُمۡۚ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ وَهُم بِرَبِّهِمۡ يَعۡدِلُونَ
Open ayah 6:150Ka ce: “Ku kawo shaidunku waɗanda za su ba da shaidar cewa, Allah Shi Ya haramta wannan.” Sannan idan har sun ba da shaidar, to kai kada ka bayar da shaida tare da su. Kuma kada ka bi soye-soyen zukatan waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu, waɗanda kuma ba sa yin imani da ranar lahira, su ne kuwa masu daidaita Ubangijinsu (da wani abu). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba mu labarin abin da mushrikai suke cewa, wai da Allah ya ga dama, da su da iyayensu ba za su yi shirka ba, kuma da ba za su haramta komai ba. Kuma tunda har ya ƙyale su suka aikata hakan, wannan a riyawarsu ya nuna cewa ya yarda da abin da suka yi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan bai zama abin mamaki ba, domin hanyar da suka bi ta ƙaryata Annabi (ﷺ) irinta ce dai kafiran da suka gabace su suka bi suka ƙaryata annabawa da ita, har sai da suka ɗanɗani azabar Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambaye su ko suna da wani ilimi na gaskiya wanda suka dogara da shi mai nuna cewa Allah ya yarda da abin da suke aikatawa? Idan akwai to su fito da wannan ilimin su nuna kowa ya gani. A ƙarshe dai Allah ya tabbatar da cewa, babu wani ilimi da suke da shi in banda zato da shaci-faɗi marar tushe. Ya kuma umarce shi da ya tabbatar musu cewa, Allah ne mai cikakkiyar hujja; da ya ga dama da ya shirye su gaba ɗaya. Kuma Allah ya ce, ya neme su da su zo da shaidunsu wanda zai nuna cewa abubuwan da suka ƙago suna cewa sun haramta Allah ne da kansa ya haramta su. To idan sun kawo shaidun, Allah ya hana Annabi ya yi shaida a kan haka tare da su. Hakanan ya yi masa kashedi da kada ya bi soye-soyen zukatan masu ƙaryata ayoyin Allah waɗanda suka kafirce wa ranar lahira, kuma suka ci gaba da yin shirka da Allah (Mai tsarki da daukaka).
۞قُلۡ تَعَالَوۡاْ أَتۡلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمۡ عَلَيۡكُمۡۖ أَلَّا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗاۖ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُم مِّنۡ إِمۡلَٰقٖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكُمۡ وَإِيَّاهُمۡۖ وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَۖ وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 6:151Ka ce: “Ku taho in karanta muku abin da Ubangijinku Ya haramta muku; kada ku haɗa Shi da wani; kuma ku kyautata wa mahaifa; kuma kar ku kashe ‘ya’yanku saboda talauci; Mu ne za Mu arzuta ku har da su; kuma kada ku kusanci munanan (ayyuka) na sarari da na ɓoye; kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (a kashe shi), sai idan da wani hakki. Wannan shi ne abin da (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi, don ku zamo masu hankali.
وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ بِٱلۡقِسۡطِۖ لَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۖ وَإِذَا قُلۡتُمۡ فَٱعۡدِلُواْ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰۖ وَبِعَهۡدِ ٱللَّهِ أَوۡفُواْۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Open ayah 6:152“Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai da kyakkyawar niyya, har sai ƙarfinsa ya kawo; kuma ku cika ma’auni na mudu da na nauyi bisa adalci; ba ma ɗora wa rai sai abin da zai iya. Kuma idan za ku yi magana to ku yi adalci, ko da kuwa a kan ɗan’uwa ne na kusa; kuma lalle ku cika alƙawarin Allah. Wannan ne abin da (Allah) Yake yi muku wasicci da shi, don ku wa’azantu.”
وَأَنَّ هَٰذَا صِرَٰطِي مُسۡتَقِيمٗا فَٱتَّبِعُوهُۖ وَلَا تَتَّبِعُواْ ٱلسُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمۡ عَن سَبِيلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Open ayah 6:153“Kuma lalle wannan shi ne tafarkina miƙaƙƙe, don haka ku bi shi; kada ku bi waɗansu hanyoyi daban, sai su raba ku da hanyarsa. Wannan shi ne abin da (Allah) Yake yi muku wasicci da shi don ku samu taƙawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya nemi mushirikai su taho ya karanta musu gaskiyar abubuwan da Allah ya haramta musu. Na farko, kada su yi shirka da Allah da komai; na biyu, su kyautata wa iyaye; na uku, kada su kashe ‘ya’yansu saboda tsoron talauci; su da `ya`yansu duka Allah shi ne mai azurta su; na huɗu, kada su kusanci munanan ayyuka na sarari da na ɓoye; na biyar, kada su kashe ran da Allah ya haramta a kashe shi sai da wani haƙƙi. Waɗannan duka wasiyya ce Allah yake yi musu ko sa hankalta. Na shida kuma, kada su kusanci dukiyar maraya sai da abin da ya zama maslaha ne a gare shi, har sai ya kawo ƙarfinsa sai su mayar masa da dukiyarsa; na bakwai, su cika ma’auni na mudu da nauyi bisa adalci, Allah ba ya ɗora wa mutum wani nauyi sai wanda zai iya ɗauka; na takwas, idan za su yi magana to su faɗi gaskiya ko da ta saɓa wa na kusa da su; na tara, su cika alƙawarin da ke tsakaninsu da Allah. Wannan wasiyya ce Allah yake yi musu don su wa’azantu. Wasiyya ta goma kuwa ita ce, wannan addini na Musulunci shi ne miƙaƙƙiyar hanyar Allah, don haka lalle su bi ta kada su bi wasu hanyoyin da suka saɓa mata sai su ɓatar da su daga hanyar Allah. Wannan ita ce wasiyyar da ya yi musu, don su samu taƙawa, watau su kiyaye dokokin Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya zana mana wani dogon zane, sai ya ce: “Wannan ita ce hanyar Allah.” Sai kuma ya zana wasu layuka a damansa da hagunsa, sai ya ce: “Waɗannan wasu hanyoyi ne daban-daban, kowacce daga cikinsu akwai Shaiɗan da yake kira zuwa gare ta.” Sai ya karanta wannan ayar ta 153. [Ahmad #4142].
ثُمَّ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ تَمَامًا عَلَى ٱلَّذِيٓ أَحۡسَنَ وَتَفۡصِيلٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لَّعَلَّهُم بِلِقَآءِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 6:154Sannan Muka bai wa Musa littafin (Attaura) don cika (ni’imarmu) ga wanda ya kyautata, kuma bayani ne na kowane irin abu, kuma shiriya ne da rahama, domin su zamo masu imani da haɗuwa da Ubangijinsu.
وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ فَٱتَّبِعُوهُ وَٱتَّقُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Open ayah 6:155Kuma wannan Littafi (Alƙur’ani) Mun saukar da shi, yana mai cike da albarka, don haka ku bi shi, kuma ku kiyaye dokokin (Allah), domin a ji ƙan ku.
أَن تَقُولُوٓاْ إِنَّمَآ أُنزِلَ ٱلۡكِتَٰبُ عَلَىٰ طَآئِفَتَيۡنِ مِن قَبۡلِنَا وَإِن كُنَّا عَن دِرَاسَتِهِمۡ لَغَٰفِلِينَ
Open ayah 6:156Don kada ku ce: “Ƙungiya biyu ne waɗanda suka gabace mu kawai aka sauƙar wa da Littafi, mu kuma ba mu san komai game da abin da suka karanta ba.”
أَوۡ تَقُولُواْ لَوۡ أَنَّآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا ٱلۡكِتَٰبُ لَكُنَّآ أَهۡدَىٰ مِنۡهُمۡۚ فَقَدۡ جَآءَكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞۚ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَصَدَفَ عَنۡهَاۗ سَنَجۡزِي ٱلَّذِينَ يَصۡدِفُونَ عَنۡ ءَايَٰتِنَا سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ بِمَا كَانُواْ يَصۡدِفُونَ
Open ayah 6:157Ko kuma ku ce: “In da mu aka saukar wa da littafin, to da lalle mun fi su shiryuwa.” To ai haƙiƙa hujja ta riga ta zo muku daga Ubangijinku, da kuma shiriya da rahama; don haka babu wanda ya fi zalunci fiye da wanda ya ƙaryata ayoyin Allah, kuma ya yi watsi da su. Da sannu za Mu saka wa waɗanda suke bijire wa ayoyinmu da mummunar azaba, saboda bijirewar da suke yi.
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ أَوۡ يَأۡتِيَ رَبُّكَ أَوۡ يَأۡتِيَ بَعۡضُ ءَايَٰتِ رَبِّكَۗ يَوۡمَ يَأۡتِي بَعۡضُ ءَايَٰتِ رَبِّكَ لَا يَنفَعُ نَفۡسًا إِيمَٰنُهَا لَمۡ تَكُنۡ ءَامَنَتۡ مِن قَبۡلُ أَوۡ كَسَبَتۡ فِيٓ إِيمَٰنِهَا خَيۡرٗاۗ قُلِ ٱنتَظِرُوٓاْ إِنَّا مُنتَظِرُونَ
Open ayah 6:158Sannan ba abin da suke sauraro face mala’iku su zo musu ko Ubangijinka Ya zo musu ko wani sashi na ayoyin Ubangijinka su zo. Ranar da wasu daga ayoyin Ubangijinka za su zo, to babu wani rai da imaninsa zai yi amfani, idan a da can bai yi imani ba ko bai yi aikin alheri ba cikin imaninsa. Ka ce: “Ku jira, mu ma masu jira ne.”
إِنَّ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمۡ وَكَانُواْ شِيَعٗا لَّسۡتَ مِنۡهُمۡ فِي شَيۡءٍۚ إِنَّمَآ أَمۡرُهُمۡ إِلَى ٱللَّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ
Open ayah 6:159Lalle waɗanda suka rarraba addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, to ba ruwanka da su. Al’amarinsu yana ga Allah ne kawai, sannan zai ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, ya ba wa Annabi Musa littafin Attaura wanda ya ƙunshi duk abubuwan da za a buƙata na shari’a a lokacinsa, ya kuma yi masa wannan tagomashi ne sakamakon ayyukansa na kirki, don kuma ya cika masa ni’imominsa, kuma ya yi masa bayanin komai da al’ummarsa suke buƙatar sani na addini da rayuwa filla-filla, kuma ya zamanto shiriya da rahama gare su, sannan kuma su yi imani da saduwa da Ubangijinsu ranar alƙiyama. Kuma ya yi bayanin cewa, ya saukar da wannan Alƙur’ani mai cike da albarka da alheri da ilimi mai tarin yawa, ya kuma umarci bayi su bi shi, kuma su kiyaye dokokinsa don su samu a yi musu rahama. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya saukar da shi wannan Alƙur’ani ne don ya yanke wa mushirikai duk wani hanzari da wata hujja da za su iya fakewa da ita, wato su ce an saukar da littafi ne ga al’ummomi biyu da suka gabace su, su ne Yahudawa da Nasara, kuma su ba su da wata masaniya da waɗannan al’ummomin, kuma ba sa fahimtar harshen da aka saukar da littafin da shi, kuma babu wani umarni a cikinsa da ya shafe su. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar musu da Alƙur’ani don a yanke abin da za su iya kafa hujja da shi, ta cewa da su ne aka saukar wa da littafi kamar yadda aka saukar wa Yahudawa da Nasara, da sun zama shiryayyu fiye da su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, Alƙur’ani ya zo musu da hujja bayyananniya da shiriya da rahama a gare su. Ya bayyana cewa, babu babban azzalumi kamar wanda ya ƙaryata ayoyin Allah, ya bijire musu bayan sun zo masa. Sai Allah ya yi alƙawarin narko mai tsanani na azaba ga waɗanda suke bijire wa ayoyinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da ma babu abin da mushirikai suke sauraro sai kawai su ga mala’iku sun zo karɓar rayukansu suna kafirai, ko Ubangiji ya zo musu su gan shi da idonsu ko kuma wasu ayoyi na mu’ujiza su zo musu. To sai Allah ya mayar musu da martanin cewa, ai ranar da Ubangiji zai zo musu ita ce alƙiyama don yi musu hisabi ko kuma idan rana ta hudo musu ta mafaɗarta. To duk lokacin da rana za ta fito daga mafaɗarta, to a wannan rana babu wani rai da bai yi imani ba wanda imaninsa zai amfane shi; a ranar ba za a karɓi tuban mai tuba ba ko wani aiki na ƙwarai ga wanda bai yi wani aiki na ƙwarai gabanin haka ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, su saurari zuwan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan, shi ma tare da muminani masu sauraro ne. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Manzon Allah (ﷺ) ya tambayi sahabbai cewa: “Kun san ina rana take tafiya?” Sai suka ce: “Allah da Manzonsa ne mafi sani.” Sai ya ce: “Lalle rana tana gudu har sai ta kai ƙarƙashin Al-Arshi, sai ta faɗi ta yi sujjada, ba za ta gushe ba cikin sujjada har sai an ce mata: “Ki ɗago, ki koma inda kika fito.” Sai gari ya waye ta fito ta mahudarta, sannan ta yi ta gudu har sai ta kai ƙarshen zangonta, wato ƙarƙashin Al-Arshi, sai ta faɗi ta yi sujjada, ba za ta gushe ba cikin sujjada har sai an ce mata: “Ɗago ki koma inda kika fito.” Sai a wayi gari ta fito daga mahudarta, mutane ba su ga wani canji tare da ita ba, sai ta yi ta gudu har sai ta kai ƙarshen zangonta, wato ƙarƙashin Al-Arshi, sai a ce mata: “Ɗago gobe da safe ki fito ta mafaɗarki.” Sai a wayi gari rana ta fito ta mafaɗarta.” Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ko kun san yaushe haka zai faru? Haka zai faru ne lokacin da imanin wani rai ba zai amfane shi ba, idan a da can bai yi imani ba ko bai aikata wani abu na alheri a cikin imaninsa ba.” [Muslim #159]. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suka bar addinin Allah ko suka rarrabu ƙungiya-ƙungiya, to ba ruwan Manzon Allah da su da abin da suke aikatawa; al’amarinsu da makomarsu suna ga Allah (Mai tsarki da daukaka), sannan a ranar alƙiyama zai ba su labarin duk abin da suka aikata, ya kuma yi musu sakamako a kan ayyukansu.
مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ عَشۡرُ أَمۡثَالِهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَا وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 6:160Wanda ya zo da kyakkyawan aiki ɗaya, to yana da ninkin ladansa goma; wanda kuwa ya zo da mummuna ɗaya, to ba za a saka masa ba sai daidai da shi, ba kuma za a zalunce su ba.
قُلۡ إِنَّنِي هَدَىٰنِي رَبِّيٓ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ دِينٗا قِيَمٗا مِّلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۚ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 6:161Ka ce: “Lalle ni, Ubangijina Ya shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, shi ne addini miƙaƙƙe, addinin Ibrahimu wanda ya karkace wa ɓarna, kuma bai zama daga masu shirka ba.”
قُلۡ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحۡيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 6:162Ka ce: “Lalle sallata da yankana da rayuwata da mutuwata, duk na Allah ne Ubangijin talikai.
لَا شَرِيكَ لَهُۥۖ وَبِذَٰلِكَ أُمِرۡتُ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 6:163“Ba Shi da abokin tarayya; kuma da hakan aka umarce ni, kuma ni ne farkon Musulmai.”
قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِي رَبّٗا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيۡءٖۚ وَلَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٍ إِلَّا عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 6:164Ka ce: “ Yanzu wanin Allah zan riƙa a matsayin ubangiji, alhalin kuwa Shi ne Ubangijin komai? Kuma ba wani rai da zai aikata wani abu face sai don kansa. Kuma ba wani rai da zai ɗauki laifin wani rai. Sannan kuma zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna saɓani a game da shi.
وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَكُمۡ خَلَٰٓئِفَ ٱلۡأَرۡضِ وَرَفَعَ بَعۡضَكُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ إِنَّ رَبَّكَ سَرِيعُ ٱلۡعِقَابِ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٞ رَّحِيمُۢ
Open ayah 6:165“Kuma Shi ne Ya sanya ku halifofi a bayan ƙasa, kuma Ya ɗaukaka darajar wasunku a kan wasu, don Ya jarrabe ku game da abin da Ya ba ku. Lalle Ubangijinka Mai gaggawar uƙuba ne, kuma lalle Shi tabbas Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin ƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, duk wanda ya yi wani kyakkyawan aiki, to ranar alƙiyama yana da riɓinsa goma, wanda kuwa ya yi mummuna, to ba za a saka masa ba sai da kwatankwacin abin da ya aikata, kuma babu wanda Allah zai zalunce shi da komai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ruwaito daga Ubangijinsa yana cewa: “Lalle Allah ya rubuta kyawawan ayyuka da munana sannan ya yi bayaninsu: Wanda ya ƙuduri aniyar aikata wani kyakkyawan aiki sai bai aikata ba, to za a rubuta masa cikakken lada a wurin Allah; idan kuwa ya yi niyyar aikatawa kuma ya aikata, to za a rubuta masa ladan kyawawan ayyuka goma har zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki ba iyaka; wanda kuwa ya yi niyyar aikata mummunan aiki sai bai aikata ba, to za a rubuta masa cikakken ladan kyakkyawan aiki; idan kuwa ya yi niyyar aikata mummunan aiki sai ya aikata, to Allah zai rubuta masa zunubin mummunan aiki ɗaya.” [Bukhari #6491, da Muslim #130]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya bayyana cewa, shi kam Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiryar da shi zuwa ga miƙaƙƙiyar hanya, addinin da yake tsaye da adalci wanda shi ne shari’ar Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya tsaya ƙyam a kan gaskiya, ya bar duk wata ɓarna da hanyoyin ɓata, kuma bai taɓa zamowa a cikin masu shirka ba. Ya kuma umarce shi ya bayyana musu cewa, sallarsa da yankansa da rayuwarsa da mutuwarsa duk a hannun Allah suke shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, ya jaddada musu cewa, shi ma da wannan ne aka umarce shi, kuma shi ne farkon masu miƙa wuya. Sannan ya umarce shi ya tambayi mushirikai cewa, shin yanzu su a ganinsu ya dace a ce ya riƙi wani ubangiji daban ban da Allah, wanda kuma shi ne Ubangijin kowa da komai? Kuma ya san cewa duk laifin da mutum zai aikata, alhakinsa yana kansa babu mai ɗauke masa, kuma babu wani rai da yake ɗauke wa wani rai komai na laifukansa, kowa shi ne mai ɗaukar nauyin zunubin aikinsa, kuma makomar kowa zuwa ga Allah ne, zai kuma yi musu bayanin abin da suka riƙa aikatawa a duniya, kuma zai warware musu abin da suke yin saɓani a kansa. Kuma shi ne wanda ya mayar da su halifofi a bayan ƙasa bayan ya halaka al’ummomin farko, ya kuma ɗaukaka darajar wasu a kan wasu, don ya jarraba su a kan abin da ya ba su na falalarsa da ni’imarsa, domin ya ga kamun ludayin kowa. Lalle Allah mai gaggauta azaba ne, kuma mai yawan gafara ne mai jin ƙai.