الأعراف
Al-A'raaf
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
الٓمٓصٓ
Open ayah 7:1Alif Laam Miim Saad .
كِتَٰبٌ أُنزِلَ إِلَيۡكَ فَلَا يَكُن فِي صَدۡرِكَ حَرَجٞ مِّنۡهُ لِتُنذِرَ بِهِۦ وَذِكۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 7:2(Wannan) Littafi ne da aka saukar maka, don haka kada wani ƙunci ya kasance a ƙirjinka a sanadiyyarsa, don ka yi gargaɗi da shi, kuma da tunatarwa ga muminai.
ٱتَّبِعُواْ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡ وَلَا تَتَّبِعُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَۗ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 7:3Ku bi abin da aka saukar muku daga Ubangijinku, kada kuma ku bi wasu masoya ba shi ba. Kaɗan ne ƙwarai kuke wa’azantuwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar mai girma da haruffa irin waɗanda ya buɗe surorin Al-Baƙara da Ali Imrana da su. Malaman tafsiri sun yi batutuwa masu yawa a kan bayanin manufofin waɗannan haruffa. Magana mafi rinjaye ita ce mai cewa, waɗannan harrufa an kawo su ne don bayyana mu’ujizar Alƙur’ani, wato shi littafi ne da ya ƙunshi haruffan da Larabawa suke magana da rubutu da su. To idan suna ganin Alƙur’ani ba daga Allah yake ba, to su kawo wata magana kwatankwacinsa idan za su iya. Shi ya sa a duk inda aka buɗe wata Sura da waɗannan haruffa, to magana a kan Alƙur’ani ne takan biyo bayansu, domin alaƙar da ke tsakaninsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, Alƙur’ani littafi ne da ya saukar masa, don haka kada ya samu wani ƙunci a ƙirjinsa game da isar da saƙon da yake cikinsa, kuma ya yi gargaɗi da wa’azi da shi, kada ya yi shakkar kasancewarsa saukakke ne daga Allah (Mai tsarki da daukaka). Allah ya saukar da shi ne domin ya tsoratar da kafirai da shi, ya kuma zama wa’azi ga muminai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mutane da su bi abin da ya zo a wannan Alƙur’ani, kuma su yi aiki da shi, kada su bi wasu majiɓinta ba shi ba, sai su raba su da koyarwar Alƙur’ani da sunnar Manzo (ﷺ). Allah ya ba da labarin cewa, kaɗan ne masu wa’azantuwa su ɗauki darasi su koma ga gaskiya.
وَكَم مِّن قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَا فَجَآءَهَا بَأۡسُنَا بَيَٰتًا أَوۡ هُمۡ قَآئِلُونَ
Open ayah 7:4Kuma nawa-nawa ne daga cikin alƙaryu waɗanda Muka (nufi) halaka su, sai azabar mu ta zo musu da daddare ko lokacin da suke barcin ƙailula?
فَمَا كَانَ دَعۡوَىٰهُمۡ إِذۡ جَآءَهُم بَأۡسُنَآ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ
Open ayah 7:5Sannan ba abin da suke faɗa, lokacin da azabarmu ta zo musu sai cewa: “Lalle mu mun kasance azzalumai.”
فَلَنَسۡـَٔلَنَّ ٱلَّذِينَ أُرۡسِلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَنَسۡـَٔلَنَّ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 7:6To lalle tabbas sai Mun tambayi waɗanda aka aiko musu manzanni, kuma lalle tabbas, sai mun tambayi manzannin (su kansu).
فَلَنَقُصَّنَّ عَلَيۡهِم بِعِلۡمٖۖ وَمَا كُنَّا غَآئِبِينَ
Open ayah 7:7Kuma lalle za Mu ba su labarin (komai) da ilimi; kuma ba Mu zamanto ba ma nan ba.
وَٱلۡوَزۡنُ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡحَقُّۚ فَمَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Open ayah 7:8Awo kuma a wannan ranar gaskiya ne. Don haka duk wanda ma’aunansa suka yi nauyi, to waɗannan su ne masu rabauta.
وَمَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُم بِمَا كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَظۡلِمُونَ
Open ayah 7:9Wanda kuwa ma’aunansa suka yi sakayau, to waɗannan su ne waɗanda suka yi hasarar kawunansu, saboda abin da suka kasance suna yi na zalunci da ayoyinmu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, a baya can ya halaka garuruwa masu yawa waɗanda mutanen cikinsu suka riƙa bautar wasu ba Allah ba, suka kuma ƙaryata manzannin da ya aiko musu. Azabar Allah kuma ta sauko musu ne ba zato ba tsammani, ta zo musu ne suna barci cikin dare, wasu kuma suna tsakiyar barci da rana, wato ƙailula. Yayin da azabar ta sauko musu, babu abin da suka riƙa faɗa sai iƙirarin cewa su kam lalle azzalumai ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana, cewa zai tsare duk wata al’umma ranar Alƙiyama ya tambaye su game da abin da manzanninsu suka je musu da shi, kuma shin sun yi musu biyayya ko ba su yi ba? Sun gaskata su ko kuma ƙaryata su suka yi? Hakanan su ma manzannin sai Allah ya tambaye su, shin sun isar da manzancin da ya ba su ko kuma a’a? Al’ummominsu sun yarda da su ko sun ƙaryata su? An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle kowannenku mai kiwo ne, kuma sai an tambayi kowa game da abin kiwonsa, mai mulkin mutane mai kiwo ne, kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa, magidanci mai kiwo ne ga iyalansa, kuma sai an tambaye shi game da su, mace mai kiwo ce a gidan mijinta da ‘ya’yansa, kuma sai an tambaye ta game da su, bawa mai kiwo ne a kan dukiyar maigidansa, kuma sai an tambaye shi a kan wannan. Don haka ku duka masu kiwo ne, kuma za a tambaye ku a kan abin kiwonku.” [Bukhari #893 da Muslim #1829]. An karɓo daga Abu Barzatul Aslami (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ranar alƙiyama digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an yi masa tambaya game da rayuwarsa, a me ya ƙarar da ita, iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa a ina ya same ta, kuma yaya ya kashe ta, da ganganr jikinsa yaya ya yi amfani da ita.” [Tirmizi #2417 da Darimi #537]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, zai ba wa bayinsa labari na ilimin ranar alƙiyama game da abin da suka faɗa ko suka aikata a duniya, kuma shi Allah babu wani lokaci da za a ce ba ya tare da bayinsa yana ganin abin da suke aikatawa. Hakanan kuma ya bayyana cewa, awon ayyuka a ranar alƙiyama gaskiya ne, Allah zai auna ayyukan bayinsa bisa adalci. Waɗanda ma’aunan kyawawan ayyukansu suka yi nauyi, to waɗannan su ne masu babban rabo; waɗanda kuwa ma’aunan ayyukansu masu kyau suka yi sakayau, wato munanan ayyukansu suka rinjayi kyawawansu, to waɗannan su ne suka tafka asara ga kawunansu sakamakon ƙaryata ayoyin Allah da jayayya da su da suka yi. An karɓo daga Abud Darda’i (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani abu da zai fi kyawawan halaye nauyi a ma’auni (ranar alƙiyama), da kyawawan halaye mutum zai kai matsayin mai yawan azumi da salla (na nafila).” [Abu Dawud #4799, da Tirmizi #2003, da Ahmad #27557].
وَلَقَدۡ مَكَّنَّٰكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَجَعَلۡنَا لَكُمۡ فِيهَا مَعَٰيِشَۗ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ
Open ayah 7:10Kuma lalle haƙiƙa Mun kafa ku a bayan ƙasa, kuma Muka sanya muku wuraren rayuwa a cikinta. Kaɗan ne ƙwarai kuke godiya.
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَٰكُمۡ ثُمَّ صَوَّرۡنَٰكُمۡ ثُمَّ قُلۡنَا لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ لَمۡ يَكُن مِّنَ ٱلسَّٰجِدِينَ
Open ayah 7:11Kuma lalle haƙiƙa Mun halicce ku, sannan kuma Muka suranta ku; sannan Muka ce wa mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu,” sai suka yi sujjada, sai Iblis ne kaɗai bai kasance cikin masu sujjada ba.
قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلَّا تَسۡجُدَ إِذۡ أَمَرۡتُكَۖ قَالَ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡهُ خَلَقۡتَنِي مِن نَّارٖ وَخَلَقۡتَهُۥ مِن طِينٖ
Open ayah 7:12(Allah) Ya ce: “Me ya hana ka yin sujada lokacin da Na umarce ka?” Sai ya ce: “Ai ni na fi shi alheri; Ka halicce ni da wuta, shi kuwa Ka halicce shi da taɓo.”
قَالَ فَٱهۡبِطۡ مِنۡهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَن تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَٱخۡرُجۡ إِنَّكَ مِنَ ٱلصَّٰغِرِينَ
Open ayah 7:13Sai Ya ce: “To ka sauka daga cikinta, bai dace gare ka ka yi girman kai a cikinta ba, don haka sai ka fita, lalle kai kana cikin ƙasƙantattu.”
قَالَ أَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
Open ayah 7:14Sai ya ce: “Ka yi min jinkiri zuwa ranar da za a tashe su (mutane).”
قَالَ إِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ
Open ayah 7:15Sai Ya ce: “Lalle kai kana cikin waɗanda za a yi wa jinkiri.”
قَالَ فَبِمَآ أَغۡوَيۡتَنِي لَأَقۡعُدَنَّ لَهُمۡ صِرَٰطَكَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ
Open ayah 7:16Ya ce: “Saboda ɓatar da ni da Ka yi, lalle sai na zaune musu tafarkinka madaidaici.
ثُمَّ لَأٓتِيَنَّهُم مِّنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ وَعَنۡ أَيۡمَٰنِهِمۡ وَعَن شَمَآئِلِهِمۡۖ وَلَا تَجِدُ أَكۡثَرَهُمۡ شَٰكِرِينَ
Open ayah 7:17“Sannan lalle zan zo musu ta gabansu da kuma ta bayansu da kuma ta damansu, da kuma ta hagunsu; kuma ba za Ka samu yawancinsu masu godiya ba.”
قَالَ ٱخۡرُجۡ مِنۡهَا مَذۡءُومٗا مَّدۡحُورٗاۖ لَّمَن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 7:18Ya ce: “Ka fita daga cikinta kana abin aibatawa, korarre (daga rahama); Na rantse duk wanda ya bi ka daga cikinsu, lalle zan cika Jahannama da ku gaba ɗaya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin wasu ni’imomin da ya yi wa bayinsa ne, wato ya samar musu da shimfiɗaɗɗiyar ƙasa, ya ba su damar amfana da ita da sauran buƙatun rayuwarsu, to amma duk da wannan bayinsa masu gode masa ‘yan kaɗan ne. Sannan kuma wata babbar ni’ima da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu wadda ba kowa ne yake tunawa da ita ba har ya gode ita ce, halittar Babansu Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da taɓo, ya suranta shi cikakken mutum, sai ya ce wa mala’iku su yi masa sujjada, sai su duka suka faɗi suka yi masa sujjada kamar yadda Allah ya umarce su, sai Iblisu ne kaɗai ya ƙi yin sujjada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye shi ya faɗi dalilin da ya hana shi yi wa Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sujjada bayan ya umarce shi da hakan. Sai ya amsa da cewa, ai shi wai ya fi Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daraja, domin shi an halicce shi da wuta, shi kuma Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) an halicce shi da taɓo. To saboda wannan girman kai da Iblisu ya nuna, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya sauko daga gidan Aljanna, domin ba a yarda da girman kai a cikinta ba, ya kuma sani cewa yana cikin ƙasƙantattu waɗanda ba za su ƙara martaba ba a wurin Allah. To bayan korar Iblisu daga gidan Aljanna, sai ya roƙi Allah ya jinkirta masa rayuwarsa har zuwa ranar tashin alƙiyama. Allah kuma ya ce ya je an saurara masa har zuwa wannan lokaci. Daga nan sai Iblis ya yi rantsuwa da Ubangijinsa cewa, saboda ɓatar da shi da Allah ya yi, lalle zai zauna ya yi kane-kane a kan madaidaiciyar hanya da Allah zai ɗora ‘yan’adam a kanta, ya hana musu bin ta, ya ƙawata musu hanyar ƙarya da ɓarna. Kuma ya sha alwashin sai ya ɓullo musu ta hanyoyi da dama, ta gabansu da ta bayansu da ta damansu da ta hagunsu, don ya tabbatar ya ɓatar da su daga kan madaidaiciyar hanya. Kuma da yawa ba zai bar mutane su riƙa gode wa Allah ba. An karɓo daga Sabra ɗan Abu Fakihin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Shaiɗan ya zauna ya yi kane-kane a kan hanyoyin ɗan’adam; ya zaune masa hanyar shiga Musulunci, ya ce masa: ‘Yanzu ka musulunta ka bar addininka kuma addinin iyayenka?’ Sai ya ƙi yarda, ya musulunta. Sai kuma ya zaune masa hanyar yin hijira, ya ce masa: ‘Yanzu ka yi hijira ka fita daga ƙasarka da samaniyarka. Misalin ɗan hijira kamar misalin doki ne a ɗaure a doguwar igiya.’ Sai ya ƙi yarda da shi, ya fita ya yi hijira. Sannan sai ya zaune masa hanyar fita jihadi, ya ce masa: ‘Shi jihadi wahalar da kai ne da kashe dukiya, yanzu ka fita yaƙi a kashe ka a aure matarka, a raba dukiyarka.’ Sai ɗan’adam ya saɓa masa, ya fita jihadi.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya aikata haka daga cikin mutane har ya mutu, to haƙƙi ne a kan Allah ya shigar da shi gidan Aljanna, ko aka kashe shi, haƙƙi ne a kan Allah ya shigar da shi Aljanna, ko ya nutse a cikin ruwa ya mutu, haƙƙi ne a kan Allah ya shigar da shi Aljanna, ko dabba ta harbe shi ya mutu, haƙƙi ne a kan Allah ya shigar da shi Aljanna.” [Nasa’i #3134, da Ahmad #16000, da Ibn Hibban #4593]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Iblis da ya fita daga gidan Aljanna yana abin zargi, korarre daga rahamar Allah. Ya kuma rantse cewa, duk wanda ya bi Iblis sai ya cika gidan wutar Jahannama da su gaba ɗaya.
وَيَٰٓـَٔادَمُ ٱسۡكُنۡ أَنتَ وَزَوۡجُكَ ٱلۡجَنَّةَ فَكُلَا مِنۡ حَيۡثُ شِئۡتُمَا وَلَا تَقۡرَبَا هَٰذِهِ ٱلشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 7:19“Kuma ya kai Adam, ka zauna cikin Aljanna, da kai da matarka, kuma ku ci duk abin da kuka ga dama, amma kada ku kusanci wannan bishiyar, sai ku kasance cikin azzalumai.”
فَوَسۡوَسَ لَهُمَا ٱلشَّيۡطَٰنُ لِيُبۡدِيَ لَهُمَا مَا وُۥرِيَ عَنۡهُمَا مِن سَوۡءَٰتِهِمَا وَقَالَ مَا نَهَىٰكُمَا رَبُّكُمَا عَنۡ هَٰذِهِ ٱلشَّجَرَةِ إِلَّآ أَن تَكُونَا مَلَكَيۡنِ أَوۡ تَكُونَا مِنَ ٱلۡخَٰلِدِينَ
Open ayah 7:20Sai Shaiɗan ya yi musu waswasi, domin ya bayyana musu abin da aka ɓoye musu na tsiraicinsu, kuma ya ce: “Ba abin da ya sa Ubangijinku Ya hane ku daga wannan bishiyar, sai don kawai kada ku zama mala’iku ko kuma ku zama daga cikin dawwamammu.”
وَقَاسَمَهُمَآ إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ ٱلنَّٰصِحِينَ
Open ayah 7:21Kuma ya yi musu rantsuwa cewa: “Lalle ni mai yi muku nasiha ne.”
فَدَلَّىٰهُمَا بِغُرُورٖۚ فَلَمَّا ذَاقَا ٱلشَّجَرَةَ بَدَتۡ لَهُمَا سَوۡءَٰتُهُمَا وَطَفِقَا يَخۡصِفَانِ عَلَيۡهِمَا مِن وَرَقِ ٱلۡجَنَّةِۖ وَنَادَىٰهُمَا رَبُّهُمَآ أَلَمۡ أَنۡهَكُمَا عَن تِلۡكُمَا ٱلشَّجَرَةِ وَأَقُل لَّكُمَآ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ لَكُمَا عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Open ayah 7:22Sai ya yaudare su da ruɗi. Don haka yayin da suka ɗanɗani wannan bishiyar, sai tsiraicinsu ya bayyana a gare su, sai suka fara lulluɓa da ganyayen Aljanna; sai Ubangijinsu Ya kira su: “Yanzu ban hana ku cin wannan bishiyar ba, ban kuma ce da ku ba lalle Shaiɗan maƙiyi ne a gare ku mabayyani?”
قَالَا رَبَّنَا ظَلَمۡنَآ أَنفُسَنَا وَإِن لَّمۡ تَغۡفِرۡ لَنَا وَتَرۡحَمۡنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Open ayah 7:23Sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, lalle kam mun zalunci kawunanmu, kuma idan har ba Ka yi mana gafara ba, kuma ba Ka ji ƙan mu ba, to lalle fa za mu kasance cikin hasararru.”
قَالَ ٱهۡبِطُواْ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ وَلَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُسۡتَقَرّٞ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ
Open ayah 7:24Sai Ya ce: “Ku sauka, sashinku zai zama abokin adawa ga sashi; kuma kuna da wurin zama a ƙasa da abin jin daɗi zuwa ɗan wani lokaci.”
قَالَ فِيهَا تَحۡيَوۡنَ وَفِيهَا تَمُوتُونَ وَمِنۡهَا تُخۡرَجُونَ
Open ayah 7:25Ya ce: “A cikinta za ku rayu, kuma a cikinta za ku mutu, kuma daga cikinta za a fito da ku.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da matarsa Hawwa’u da su zauna a gidan Aljanna, kuma su ci abin da suke so na ‘ya’yan itatuwanta, amma kada su kusanci wata bishiya da ya nuna musu, don yin hakan zai sanya su cikin azzalumai, wato waɗanda suka cuci kawunansu da rashin biyayya ga Allah da saɓa umarninsa. Sai Shaiɗan ya sa wa Annabi Adamu da matarsa Hawwa’u (() waswasi, domin ya yaudare su ya raba su da suturar da ta rufe musu tsiraicinsu. Ya yi musu ƙaryar cewa, Allah bai hana su cin wannan bishiya ba sai don kada su zama mala’iku ko kuma su dawwama a gidan Aljanna. Ya yi musu rantsuwa har da Allah cewa, wannan magana da yake faɗa musu nasiha ce yake yi musu. Har daga ƙarshe dai ya yaudare su, ya zuga su suka ci ‘ya’yan wannan bishiyar. To lokacin da suka ci sai tsiraicinsu ya bayyana gare su. To ganin haka sai suka riƙa lulluɓe jikinsu da ganyen bishiyoyin gidan Aljanna. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kiran su yana zargin su cewa, ashe ba ya hana su cin wannan bishiyar ba, kuma ya faɗa musu cewa Shaiɗan babban maƙiyinsu ne na sarari? Sai nan da nan suka amsa laifinsu, suka yarda cewa sun zalunci kawunansu; idan kuma ba Allah ya gafarta musu ya ji ƙan su ba, to lalle za su zama daga cikin waɗanda suka taɓe. Sai daga nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Hawwa’u har da Iblisu cewa, lalle su bar gidan Aljanna su sauko bayan ƙasa, junansu suna masu gaba da juna. A nan ƙasa suna da wurin da za su zauna su rayu, su ji daɗi har zuwa lokacin mutuwarsu, kuma a binne su a cikin ƙasar a kuma tashe su daga ƙaburburansu ranar alƙiyama don yi musu sakayya.
يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ قَدۡ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكُمۡ لِبَاسٗا يُوَٰرِي سَوۡءَٰتِكُمۡ وَرِيشٗاۖ وَلِبَاسُ ٱلتَّقۡوَىٰ ذَٰلِكَ خَيۡرٞۚ ذَٰلِكَ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ
Open ayah 7:26Ya ku ‘yan’adam, haƙiƙa Mun saukar muku da tufafi wanda zai suturce muku tsiraicinku, da kayan ado; tufafi na taƙawa kuwa wannan shi ya fi alheri. Wannan yana daga cikin ayoyin Allah, ko sa yi tuntuntuni.
يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ لَا يَفۡتِنَنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ كَمَآ أَخۡرَجَ أَبَوَيۡكُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ يَنزِعُ عَنۡهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوۡءَٰتِهِمَآۚ إِنَّهُۥ يَرَىٰكُمۡ هُوَ وَقَبِيلُهُۥ مِنۡ حَيۡثُ لَا تَرَوۡنَهُمۡۗ إِنَّا جَعَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 7:27Ya ku ‘yan’adam, kada Shaiɗan ya fitine ku kamar yadda ya fitar da iyayenku daga cikin Aljanna, yana mai cire musu tufafinsu don ya nuna musu tsiraicin junansu. Lalle shi yana ganin ku, shi da jama’arsa ta inda ku ba kwa ganin su. Lalle mu Mun sanya shaiɗanu su zamo masoya ga waɗanda ba sa yin imani.
وَإِذَا فَعَلُواْ فَٰحِشَةٗ قَالُواْ وَجَدۡنَا عَلَيۡهَآ ءَابَآءَنَا وَٱللَّهُ أَمَرَنَا بِهَاۗ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَأۡمُرُ بِٱلۡفَحۡشَآءِۖ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:28Idan kuma sun aikata wani mummunan aiki sai su ce: “Mun sami iyayenmu ne a kansa, kuma Allah ne Ya umarce mu da shi.” Ka ce: “Lalle Allah ba Ya umarni da mummunan aiki; yanzu kwa riƙa faɗin abin da ba ku sani ba kuna jingina wa Allah?”
قُلۡ أَمَرَ رَبِّي بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَقِيمُواْ وُجُوهَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۚ كَمَا بَدَأَكُمۡ تَعُودُونَ
Open ayah 7:29Ka ce: “Ubangijina Ya yi umarni da adalci; kuma ku tsai da fuskokinku (don Allah) a kowace salla, ku kuma roƙe Shi kuna masu tsantsanta addini gare Shi. Kamar yadda Ya fari halittarku, haka za ku koma (wurinsa).
فَرِيقًا هَدَىٰ وَفَرِيقًا حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلضَّلَٰلَةُۚ إِنَّهُمُ ٱتَّخَذُواْ ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُم مُّهۡتَدُونَ
Open ayah 7:30Wani sashi Ya shirye su, wani sashin kuma ɓata ya tabbata a kansu. Lalle su sun mayar da shaiɗanu masoya ba Allah ba, suna kuma tsammanin cewa lalle su shiryayyu ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa ‘yan’adam cewa, ya halitta musu tufafin sawa waɗanda suke rufe musu tsiraici da kuma kayan ado, amma su sani cewa tufa ta tsoron Allah ita ta fi alheri. Allah ya nuna cewa, wannan ni’ima da ya yi musu ɗaya ce daga cikin ayoyinsa, ko sa riƙa wa’azantuwa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da su hatsarin Shaiɗan cewa, su yi hattara kada ya ruɗe su kamar yadda ya ruɗi iyayensu Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Hawwa’u, ya ƙawata musu saɓon Allah, har ya fito da su daga gidan Aljanna, yana yaye musu tufafinsu domin ya nuna musu tsiraicinsu. Allah kuma ya faɗa musu cewa, Shaiɗan da zurriyarsa suna ganin su ta inda su ‘yan’adam ba sa ganin su, kuma ya sanya shaiɗanu masoya ga waɗanda ba sa yin imani. Kafirai kuma idan sun aikata wani mummunan aiki, kamar yin ɗawafi tsirara, sai su riƙa kare kansu da cewa, ai su ma haka suka ga iyayensu suna yi, kuma ma wai Allah ne ya umarce su da yin hakan. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya mayar musu da martani cewa, ai Allah ba ya umarni da mummunan aiki. Yaya za su riƙa ƙagar ƙarya suna jingina wa Allah? Kuma ya umarce shi ya faɗa musu cewa, Ubangijinsa (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni ne da yin adalci, kuma su fuskanci Allah da sallarsu a kowane masallaci, kuma a ko’ina suke, su kuma roƙi Allah suna masu tsantsanta addini gare shi. Sannan ya tunatar da su farkonsu da ƙarshensu cewa, kamar yadda a karon farko ya halicce su bayan babu su, to hakanan za su koma gare shi ranar alƙiyama. Allah ya shiryar da wani ɓangare daga cikinsu, wasu kuma ɓata ya tabbata a kansu, sun mayar da shaiɗanu masoyansu ba Allah ba, kuma suna tsammanin cewa su shiryayyu ne.
۞يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ خُذُواْ زِينَتَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ وَلَا تُسۡرِفُوٓاْۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Open ayah 7:31Ya ku ‘yan’adam, ku yi adonku a wurin kowane masallaci, ku ci, kuma ku sha, amma kada ku yi almubazzaranci. Lalle Shi (Allah) ba ya son masu almubazzaranci.
قُلۡ مَنۡ حَرَّمَ زِينَةَ ٱللَّهِ ٱلَّتِيٓ أَخۡرَجَ لِعِبَادِهِۦ وَٱلطَّيِّبَٰتِ مِنَ ٱلرِّزۡقِۚ قُلۡ هِيَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا خَالِصَةٗ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:32Ka ce: “Wane ne ya haramta kayan ado na Allah waɗanda (Allah) Ya fitar domin bayinsa da kuma daɗaɗan abubuwa na arziki?” Ka ce: “Waɗannan abubuwa na waɗanda suka yi imani ne a nan duniya, kuma nasu ne a keɓance a ranar lahira.” Kamar haka ne Muke rarrabe ayoyi ga mutanen da suke da sani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar ‘yan’adam da su sa kyakkyawar sutura, mai rufe tsiraici lokacin shiga masallaci domin yin salla, kuma su ci su sha daga abin da Allah ya halatta musu, kada kuma su yi almubazzaranci da abinci ko da abin sha ko ta hanyar barin abin da yake halal zuwa ga wanda ba halal ba ne, domin Allah ba ya son masu almubazzaranci. Wannan ayar ta sauka ne a kan mushirikai masu yin ɗawafi tsirara suna cewa, wai bai dace su bauta wa Allah da tufafin da suke yin saɓo da su ba. Sai ya zamana duk ƙabilun Larabawa tsirara suke yin ɗawafi, in ban da Ƙuraishawa su ne kaɗai suke yin ɗawafi da tufafinsu, kuma su ne suke ara wa mutane tufafin da za su yi ɗawafi da su, namiji ya ara wa ɗan’uwansa namiji, mace ta ara wa mace ‘yar’uwarta; wanda bai samu mai ba shi aro ba kuwa sai ya yi ɗawafi tsirara haihuwar uwarsa. Sai Allah ya rushe wannan mummunar al’adar, ya umarce su da sanya tufafinsu a lokacin da suka shiga ibada a kowane wurin ibada. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Annabi (ﷺ) ya shugabantar da Abubakar a aikin hajji (wato Amirul hajji) wanda aka yi kafin hajjin ban-kwana, ya umarce shi da ya fita a ranar Idi ya sanar da mutane cewa, daga wannan shekarar kada wani mushiriki ya sake zuwa aikin hajji, kuma kada wani mutum ya ƙara yin ɗawafi a Ɗakin Ka’aba tsirara.” [Bukhari #1622, da Muslim #1347]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya ƙalubalanci jahilan Larabawa masu yin ɗawafi tsirara suna haramta wa kansu abin da Allah ya halatta musu, cewa, wane ne ya haramta kayan sawa na ado da Allah ya hore wa bayinsa? Kuma wane ne ya haramta musu daɗaɗan abubuwa da Allah ya arzuta su da su? Ya kuma tabbatar musu cewa, kayan sawa na ado da daɗaɗan abubuwa na muminai ne a nan duniya, kuma kafirai ma suna tarayya da su wajen cin moriyarsu, amma a lahira za su zama na muminai ne su kaɗai. Da haka Allah yake bayanin ayoyinsa daki-daki ga mutanen da suka san gaskiya kuma suna yarda da ita.
قُلۡ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَ وَٱلۡإِثۡمَ وَٱلۡبَغۡيَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَأَن تُشۡرِكُواْ بِٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ سُلۡطَٰنٗا وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:33Ka ce, “Ubangijina kawai Ya haramta munanan ayyuka na sarari da na ɓoye da saɓo da cutar wani ba da haƙƙi ba, kuma (Ya haramta) ku haɗa Allah da wani, irin abin da bai saukar da wani dalili a kai ba, kuma (Ya haramta) ku faɗi wani abu game da Allah wanda ba ku sani ba.”
وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٞۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ لَا يَسۡتَأۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ
Open ayah 7:34Kuma kowace al’umma tana da lokaci ƙayyadajje; don haka idan ajalinsu ya zo, ba za a yi musu jinkirin sa’a ɗaya ba; ba kuma za a gaggauta musu ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa mushrikai cewa, abin da kawai ya hana shi ne aikata munanan ayyuka na sarari da na ɓoye da duk wani saɓon Allah wanda ya keɓanci mai aikata shi da zalunci ba da wani haƙƙi ba, kuma ya haramta a haɗa shi da wani wajen bauta, abin da babu wata hujja ta yin haka. Haka kuma Allah ya haramta yin magana ba da ilimi ba a jingina ta da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wata al’umma da take ƙaryata manzonta tana da wani ƙayyadajjen lokacin da azaba za ta sauko mata, wanda idan lokacin ya zo to za su halaka nan take, ba tare da an jinkirta musu daidai da sa’a ɗaya ba, kuma ba za a gaggauto musu da azabar kafin zuwan lokacinta ba.
يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ إِمَّا يَأۡتِيَنَّكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي فَمَنِ ٱتَّقَىٰ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 7:35Ya ku ‘yan’adam, idan har manzanni suka zo muku daga cikinku, suna karanta muku ayoyina, to duk wanda ya yi taƙawa, kuma ya kyautata aiki, to babu jin tsoro tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱسۡتَكۡبَرُواْ عَنۡهَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 7:36Waɗanda kuwa suka ƙaryata ayoyinmu, kuma suka yi girman kai gare su, waɗannan su ne ma’abota wuta; suna masu dawwama a cikinta.
فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ أُوْلَٰٓئِكَ يَنَالُهُمۡ نَصِيبُهُم مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوۡنَهُمۡ قَالُوٓاْ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا وَشَهِدُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰفِرِينَ
Open ayah 7:37To wa ya fi wanda ya yi wa Allah ƙarya zalunci, ko ya ƙaryata ayoyinsa? Waɗannan rabonsu da aka rubuta a cikin littafi zai same su; har ya zuwa lokacin da manzannimu za su zo su karɓi ransu, sai su ce: “Ina waɗanda kuka kasance kuna kira ba Allah ba?” Sai su ce: “Sun ɓace mana.” Kuma za su ba da shaida a kansu cewa, lalle su sun kasance kafirai.
قَالَ ٱدۡخُلُواْ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِكُم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ فِي ٱلنَّارِۖ كُلَّمَا دَخَلَتۡ أُمَّةٞ لَّعَنَتۡ أُخۡتَهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا ٱدَّارَكُواْ فِيهَا جَمِيعٗا قَالَتۡ أُخۡرَىٰهُمۡ لِأُولَىٰهُمۡ رَبَّنَا هَٰٓؤُلَآءِ أَضَلُّونَا فَـَٔاتِهِمۡ عَذَابٗا ضِعۡفٗا مِّنَ ٱلنَّارِۖ قَالَ لِكُلّٖ ضِعۡفٞ وَلَٰكِن لَّا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:38Sai Ya ce: “Ku shiga cikin jerin al’ummomin da suka shuɗe kafinku na aljannu da mutane a cikin wuta.” Ko da yaushe wata al’umma ta shiga (wutar) sai ta la’anci ‘yar’uwarta; har sai lokacin da suka haɗu a cikinta gaba ɗaya, sai na ƙarshensu su ce wa na farkonsu: “Ya Ubangijinmu, waɗannan ne suka ɓatar da mu, don haka Ka ninka musu azabar wuta.” Sai Ya ce: “Kowanne yana da ninki, sai dai ku ba ku sani ba ne.”
وَقَالَتۡ أُولَىٰهُمۡ لِأُخۡرَىٰهُمۡ فَمَا كَانَ لَكُمۡ عَلَيۡنَا مِن فَضۡلٖ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡسِبُونَ
Open ayah 7:39Sai kuma na farkonsu su ce wa na ƙarshensu: “Ai ba ku da wani fifiko a kanmu; to ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa ‘yan’adam cewa, idan manzanni daga cikin jinsinsu na mutane suka zo musu, suna karanta musu ayoyin littafinsa, to duk wanda ya ji tsoron Allah, ya yi kyakkyawan aiki, ya bar abin da aka haramta masa, to waɗannan babu wani tsoro tare da su game da abin da za su sadu da shi bayan mutuwarsu, kuma babu wani baƙin ciki da za su yi game da abin da za su bari a nan duniya. Amma waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah, suka nuna girman kai na ƙin yarda da su ko aiki da su, to waɗannan ‘yan wuta ne, za su shige ta su yi ta zama a cikinta har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu wani babban azzalumi da ya kai wanda ya ƙirƙiri ƙarya ya jingina wa Allah ko ya ƙaryata ayoyin da ya saukar; to waɗannan rabonsu da aka rubuta musu a Lauhul Mahfuz na arziki da ayyuka da shekaru da abin da zai same su na alheri ko na sharri, duk wannan zai same su kamar yadda aka rubuta musu shi, har zuwa lokacin da mala’ikun mutuwa za su zo karɓar rayukansu. To a sannan ne mala’iku za su tambaye su, ina abubuwan da suka bauta wa ba Allah ba? Sai su amsa musu cewa, ai sun ɓace musu; su yi iƙirari da kansu cewa su sun kasance kafirai ne. Sai daga nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su shiga cikin ayarin kafiran sauran al’ummomi da suka gabace su na aljanu da mutane. Sai gaba ɗayansu su shiga wutar Jahannama. To duk sa’adda wata al’umma ta shiga wutar kuma, sai ta la’anci ‘yar’uwarta, har sai na farkonsu da na ƙarshensu duk sun tattara a wuta, sai na ƙarshen su ce wa na farkon: “Ya Ubangijinmu, waɗannan su ne muka bi a duniya, suka ɓatar da mu daga bin hanyarka; to ka yi musu azabar wuta ninkin tamu!” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da amsa cewa: “Kowane daga cikinku za a ninka masa azabarsa, sai dai ku ba ku sani ba ne.” Sai na farkonsu su ce wa na ƙarshensu: “Ba ku fi mu da komai ba.” Sai Allah ya faɗa musu gaba ɗayansu: “Ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.” Wato na kafirci da saɓon Allah.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱسۡتَكۡبَرُواْ عَنۡهَا لَا تُفَتَّحُ لَهُمۡ أَبۡوَٰبُ ٱلسَّمَآءِ وَلَا يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ حَتَّىٰ يَلِجَ ٱلۡجَمَلُ فِي سَمِّ ٱلۡخِيَاطِۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 7:40Lalle waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu, kuma suka yi girman kai gare su, ba za a buɗe musu ƙofofin sama ba, ba kuma za su shiga Aljanna ba, har sai raƙumi ya shige ta ƙofar allura. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu laifi.
لَهُم مِّن جَهَنَّمَ مِهَادٞ وَمِن فَوۡقِهِمۡ غَوَاشٖۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 7:41Suna da shimfiɗa a cikin Jahannama daga samansu kuma akwai wuta mai lulluɓe su. Kuma kamar haka ne Muke saka wa azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, lalle waɗanda suka ƙaryata ayoyinsa, kuma suka yi girman kai gare su, to ayyukansu ba za su hau zuwa gare shi ba, ba kuma za a amsa musu addu’arsu ba, babu wata rahama ko albarka da za ta sauko musu. Yayin da kuma suka mutu, ba za a buɗe wa rayukansu ƙofofin sama ba, kuma ba za su shiga Aljanna ba har sai idan raƙumi zai shige ta ƙofar allura. To da irin wannan azaba ce Allah zai azabtar da kafirai masu laifi. Suna kuma da shimfiɗa ta wutar Jahannama a ƙarƙashinsu; daga samansu kuma akwai rufi na wuta ya lulluɓe su. Kamar haka ne Allah yake saka wa azzalumai. Ya zo a cikin wani hadisi mai tsawo na Bara’u ɗan Azib (Allah ya kara masa yarda), Annabi (ﷺ) yana cewa: “Idan mala’ikun mutuwa suka fizge ran kafiri suka sa shi a cikin wani buhu yana ɗoyi fiye da kowane irin mushe a duniya, sai su yi sama da ran nasa. Duk sa’adda suka wuce da shi ta gaban wani taron mala’iku sai su ce: “Wannan wane rai ne mai muni haka?” Sai mala’ikun mutuwa su amsa musu cewa: “Wane ne ɗan wane.” Su kira shi da mafi munin sunansa da ake kiran sa da shi a duniya, har sai sun isa sama ta farko da shi, sai su nemi a buɗe masa ƙofar, sai a ƙi buɗe masa.” Sannan sai Annabi (ﷺ) ya karanta wannan ayar: “Haƙiƙa waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu, suka kuma yi girman kai game da su, ba za a buɗe musu ƙofofin sama ba, kuma ba za su shiga Aljanna ba har sai raƙumi ya shige ta kafar allura.” [Ahmad #18534].
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 7:42Waɗanda kuwa suka yi imani, kuma suka aikata kyawawan ayyuka, ba ma ɗora wa rai, sai abin da zai iya, waɗannan su ne ‘yan Aljanna, su masu dawwama ne a cikinta.
وَنَزَعۡنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنۡ غِلّٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي هَدَىٰنَا لِهَٰذَا وَمَا كُنَّا لِنَهۡتَدِيَ لَوۡلَآ أَنۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُۖ لَقَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُ رَبِّنَا بِٱلۡحَقِّۖ وَنُودُوٓاْ أَن تِلۡكُمُ ٱلۡجَنَّةُ أُورِثۡتُمُوهَا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 7:43Muka kuma cire abin da yake cikin ƙirazansu na ƙullata, ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu; kuma za su ce: “Yabo ya tabbata ga Allah da Ya shiryar da mu ga wannan, kuma da ba za mu taɓa shiryuwa ba ba don Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle haƙiƙa manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya.” Sai a kira su da cewa: “Waccan Aljannar an gadar muku da ita saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, ba ya ɗora wa kowane rai abin da ba zai iya ɗauka ba, saboda haka waɗanda suka yi imani kuma suka yi kyawawan ayyuka, su ne ‘yan Aljanna, masu zama a cikinta har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya cire wa ‘yan Aljanna duk abin da yake cikin zukatansu na ƙullata da ƙiyayya da hassada, ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu. An karɓo daga Abu Sa’id Alkhudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Muminai za su kuɓuta daga shiga wuta, sai a tara su a kan wata gada tsakanin Aljanna da wuta, sai a yi ramuwa tsakanin waɗanda aka zalunta da waɗanda suka zalunce su a duniya, har sai an tsaftace su daga duk wani laifi, sai a yi musu izini su shiga Aljanna. Na rantse da wanda ran Muhammadu yake hannunsa, sai ɗayansu ya fi gane gidansa na Aljanna fiye da yadda ya kasance yana gane gidansa na duniya.” [Bukhari #6535]. To yayin da muminai suka sami wannan ni’imar, za su yi wa Allah godiya da ya yi musu gam-da-katar da imani da kyawawan ayyuka waɗanda suka yi sanadiyyar shigarsu Aljanna, suka tabbatar da cewa, ba don Allah ya shiriyar da su ba, to da su ba za su iya shiryar da kansu ba, kuma suka bayyana cewa, manzannin Ubangijinsu sun zo musu da gaskiya. To sai a kira ‘yan Aljanna a faɗa musu cewa, an gadar musu da wannan Aljannar ne a sanadiyyar imaninsu da ayyukansu na ƙwarai. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk ɗan Aljanna zai gano masaukinsa ne a wuta, sai ya ce: “Kai, ba don Allah ya shirye ni ba!” Sai wannan ya zame masa abin godiya. Duk kuma ɗan wuta shi ma zai ga masaukinsa a Aljanna, sai ya ce: “Ina ma Allah ya shirye ni!” Sai wannan ya zame masa nadama.” [Nasa’i, As-Sunan Al-Kubra #11390, da Ahmad #10652]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani wanda aikinsa ne zai kuɓutar da shi.” Sahabbai suka ce; “Har kai ma ya Ma’aikin Allah?” Ya ce: “Har ni ma, sai dai kawai Allah ya lulluɓe ni da rahama.” [Bukhari #6463, da Muslim #2816]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu mutum ɗaya daga cikinku, face yana da gida biyu, gida a Aljanna da gida a wuta. Idan ya mutu ya shiga wuta, sai ‘yan Aljanna su gaje gidansa na Aljanna, wannan shi ne ma’anar faɗar Allah: “Waɗannan su ne masu gado.” Suratul Mu’minun, aya ta 10.
وَنَادَىٰٓ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ أَن قَدۡ وَجَدۡنَا مَا وَعَدَنَا رَبُّنَا حَقّٗا فَهَلۡ وَجَدتُّم مَّا وَعَدَ رَبُّكُمۡ حَقّٗاۖ قَالُواْ نَعَمۡۚ فَأَذَّنَ مُؤَذِّنُۢ بَيۡنَهُمۡ أَن لَّعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 7:44Kuma ‘yan Aljanna za su kira ‘yan wuta cewa: “Haƙiƙa mu kam mun samu abin da Ubangijinmu Ya yi mana alƙawari gaskiya ne, shin ku ma kun sami abin da Ubangijinku Ya yi muku alƙawari gaskiya ne?” Sai su ce, “E.” Sai wani mai shela ya yi shela a tsakankaninsu cewa: “La’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai.
ٱلَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجٗا وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ كَٰفِرُونَ
Open ayah 7:45“(Su ne) waɗanda suke hana mutane bin tafarkin Allah, kuma suke neman ya zama karkatacce, alhali su masu kafircewa ne da ranar lahira.”
وَبَيۡنَهُمَا حِجَابٞۚ وَعَلَى ٱلۡأَعۡرَافِ رِجَالٞ يَعۡرِفُونَ كُلَّۢا بِسِيمَىٰهُمۡۚ وَنَادَوۡاْ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ أَن سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡۚ لَمۡ يَدۡخُلُوهَا وَهُمۡ يَطۡمَعُونَ
Open ayah 7:46A tsakaninsu kuma akwai wani shamaki. Kuma a kan katangar La’arafi akwai waɗansu mazaje suna gane kowane (ɗan Aljanna da ɗan wuta) da alamominsu. Kuma sai su kira ‘yan Aljanna cewa: “Amincin Allah ya tabbata a gare ku.” (Lokacin) ba su shige ta ba, amma suna kwaɗayin (shigar ta).
۞وَإِذَا صُرِفَتۡ أَبۡصَٰرُهُمۡ تِلۡقَآءَ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ قَالُواْ رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 7:47Idan kuma an juyar da idanuwansu ɓangaren ‘yan wuta sai su ce: “Ya Ubangijinmu, kada Ka sanya mu tare da mutane azzalumai.”
وَنَادَىٰٓ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأَعۡرَافِ رِجَالٗا يَعۡرِفُونَهُم بِسِيمَىٰهُمۡ قَالُواْ مَآ أَغۡنَىٰ عَنكُمۡ جَمۡعُكُمۡ وَمَا كُنتُمۡ تَسۡتَكۡبِرُونَ
Open ayah 7:48Sai ‘yan tozon La’arafi su kira waɗansu mazaje da suke gane su da alamominsu, sai su ce: “Taronku bai wadatar da ku da komai ba, da girman kan da kuka kasance kuna yi.
أَهَٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَقۡسَمۡتُمۡ لَا يَنَالُهُمُ ٱللَّهُ بِرَحۡمَةٍۚ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡكُمۡ وَلَآ أَنتُمۡ تَحۡزَنُونَ
Open ayah 7:49“Shin waɗannan ne waɗanda kuka riƙa yin rantsuwa cewa Allah ba zai sadar da rahamarsa zuwa gare su ba?” Ku shiga Aljanna babu wani tsoro tare da ku, kuma ba za ku yi baƙin ciki ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana tattaunawar da za ta gudana tsakanin ‘yan Aljanna da ‘yan wuta bayan kowa ya shiga makomarsa. ‘Yan Aljanna za su kira ‘yan wuta su faɗa musu cewa, su kam yanzu sun samu abin da Ubangijinsu ya yi musu alƙawarin zai ba su na sakamakon biyayyar da suka yi masa, gaskiya ne ya tabbata. To su ma ‘yan wuta sun samu alƙawarin da Allah ya yi musu na azaba gaskiya ne ya tabbata? Sai su amsa musu da cewa, na’am haka ne sun gani. Daga nan sai mai shela ya yi shelar cewa, la’anar Allah ta tabbata ga kafirai azzalumai, waɗanda a duniya suka ƙi karɓar Musulunci, kuma suka hana mutane su karɓe shi, suka yi ta ɓata shi da yi masa ƙazafi don mutane su ƙyamace shi, kuma ba su yi imani da ranar lahira ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, akwai wani shamaki tsakanin ‘yan wuta da ‘yan Aljanna, shi ne wata doguwar katanga wadda a kanta za a tsare mutanen da kyawawan ayyukansu suka yi daidai da munanansu. Waɗannan mutane suna gane ‘yan Aljanna da alamominsu, hakanan suna gane ‘yan wuta da alamominsu. Sai su kira ‘yan Aljanna, suna cewa, amincin Allah ya tabbata a gare su. Ga shi su ba su samu sun shiga Aljanna ba, amma suna kwaɗayin shiga cikinta. Idan kuma aka juyar da ganinsu wajen ‘yan wuta, sai su roƙi Allah kada ya saka su cikin azzaluman mutane ‘yan wuta. Sai kuma su kirawo wasu shuwagabannin mushirikai waɗanda sun san su tun a duniya, kuma a nan ma lahira sun shaida su da alamominsu na ‘yan wuta, su faɗa musu cewa, yanzu dukiyar da suka tara a duniya da ‘ya’ya da mabiya da irin girman kan da suka riƙa nunawa ya kuwa amfane su da wani abu? Yanzu sai su dubi waɗannan raunanan mutanen da suka raina su a duniya, suna rantsuwa har da Allah cewa, Allah ba zai yi musu wata rahama ba, ga shi yanzu Allah ya shigar da su Aljanna, su kuma ya sa su wuta. Daga nan sai a ce wa su waɗannan mutane na kan katangar La’arafi da ke tsakanin Aljanna da wuta, su shiga Aljanna babu wani tsoro tare da su, kuma ba wani ɓacin rai game da abin da suka bari a duniya.
وَنَادَىٰٓ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ أَنۡ أَفِيضُواْ عَلَيۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ أَوۡ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُۚ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ حَرَّمَهُمَا عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 7:50Sai ‘yan wuta su kira ‘yan Aljanna cewa: “Ku kwararo mana ruwa ko abin da Allah Ya arzuta ku da shi.” Sai su ce: “Lalle Allah Ya haramta su ga kafirai.”
ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَهُمۡ لَهۡوٗا وَلَعِبٗا وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ فَٱلۡيَوۡمَ نَنسَىٰهُمۡ كَمَا نَسُواْ لِقَآءَ يَوۡمِهِمۡ هَٰذَا وَمَا كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ
Open ayah 7:51(Su ne) waɗanda suka ɗauki addininsu sharholiya da wargi, kuma rayuwar duniya ta ruɗe su. To a yau za Mu manta da su, kamar yadda suka manta da saduwa da wannan yinin nasu, da kuma jayayya da suka kasance suna yi da ayoyinmu.
وَلَقَدۡ جِئۡنَٰهُم بِكِتَٰبٖ فَصَّلۡنَٰهُ عَلَىٰ عِلۡمٍ هُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 7:52Lalle haƙiƙa kuma Mun zo musu da littafin da Muka bayyana shi filla-filla bisa ilimi da shiriya da rahama ga mutanen da suke yin imani.
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا تَأۡوِيلَهُۥۚ يَوۡمَ يَأۡتِي تَأۡوِيلُهُۥ يَقُولُ ٱلَّذِينَ نَسُوهُ مِن قَبۡلُ قَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُ رَبِّنَا بِٱلۡحَقِّ فَهَل لَّنَا مِن شُفَعَآءَ فَيَشۡفَعُواْ لَنَآ أَوۡ نُرَدُّ فَنَعۡمَلَ غَيۡرَ ٱلَّذِي كُنَّا نَعۡمَلُۚ قَدۡ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 7:53Shin akwai abin da suke jira ne in ba aukuwar abin da ya labarta ba?. Ranar da haƙiƙanin al’amarin zai zo, waɗanda a da suka manta da shi za su ce: “Haƙiƙa manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya, shin za mu samu masu ceto da za su cece mu, ko kuma za a mayar da mu, sai mu yi aiki ba irin wanda muka kasance muna yi ba?” Haƙiƙa sun yi hasarar rayuwarsu, kuma abin da suka kasance suna ƙirƙira ya ɓace musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, ‘yan wuta za su kirawo ‘yan Aljanna, suna roƙon su da su kwararo musu ruwan sha daga gidan Aljanna, ko su sam musu kaɗan daga abincinsu wanda Allah ya ba su. Sai ‘yan Aljanna su amsa musu da cewa, ai Allah ya haramta wa kafirai ruwan Aljanna da abincinta, saboda sun ɗauki addinin Allah da ake kiran su su ba da gaskiya da shi sun mayar da shi abin wasa da izgili, kuma rayuwar duniya ta ruɗe su har suka manta da lahira. To a ranar lahira Allah zai faɗa musu cewa, zai manta da su su yi ta shan azaba kamar yadda su ma a duniya suka manta da wannan rana ta lahira, kuma suka riƙa jayayya da ayoyin Allah. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah zai sadu da bawansa sai ya ce masa: “Wane, ashe ban girmama ka ba, na ba ka shugabanci, na ba ka aure, na hore maka dukiya ta dawakai da raƙuma, na bar ka kana shugabantar mutanenka, kana karɓar harajin rubu’in ganima daga hannunsu?” Sai ya ce: “Haka ne ya Ubangiji.” Sai Allah ya ce masa: “To shin ka sakankance da cewa za ka gamu da ni?” Sai ya ce: “A’a.” Sai Allah ya ce masa: “To zan manta da kai kamar yadda kai ma ka manta da ni.” Sannan Allah ya sadu da bawansa na biyu, sai ya ce masa: “Wane, ashe ba na girmama ka ba, na ba ka shugabanci, na ba ka aure, na hore maka dukiya ta dawaki da raƙuma, na bar ka kana shugabantar mutanenka, kana karɓar harajin rubu’in ganima daga hannunsu?” Sai ya ce: “Haka ne ya Ubangiji.” Sai Allah ya ce masa: “Shin ka sakankance da cewa za ka gamu da ni?” Sai ya ce: “A’a.” Sai Allah ya ce: “To zan manta da kai kamar yadda kai ma ka manta da ni.” [Muslim #2968]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa cewa, ya saukar wa waɗannan kafirai littafin Alƙur’ani wanda a cikinsa ya yi bayanin komai da ɗan’adam yake buƙatar ya sani dangane da addini da rayuwa filla-filla da ilimi da shiriya ga muminai, don kuma ya zama rahama gare su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin ƙarshen lamarin kafirai da cewa, shin yanzu akwai wani abu da kafirai suke jira in ban da aukuwar abin da Alƙur’ani ya ba da labarin zai auku na zuwan ranar alƙiyama da tsayuwa domin hisabi da shigarsu cikin azabar Allah da shigar ‘yan Aljanna gidan Aljanna? To ranar da duk waɗannan abubuwa za su auku, kafirai da suka ƙi yin imani da Alƙur’ani da gaskiyar da ya zo da ita, za su yi nadama marar amfani, su riƙa cewa: A yau dai ga shi sun gane cewa, ashe manzannin Allah da gaskiya suka zo musu, amma sai suka ƙaryata su, to ko yanzu za su samu waɗanda za su cece su a wajen Ubangijinsu, ko kuma za a mayar da su duniya su yi aiki ba irin wanda suka yi a da ba na kafirci da saɓon Allah? Allah ya bayyana cewa, waɗannan kafirai sun tafka hasara ga kawunansu, kuma abin da suke riyawa a duniya cewa su abokan tarayya ne da Allah, a yau ga shi sun ɓace musu, ba su yi musu wani amfani ba.
إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَ يَطۡلُبُهُۥ حَثِيثٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ وَٱلنُّجُومَ مُسَخَّرَٰتِۭ بِأَمۡرِهِۦٓۗ أَلَا لَهُ ٱلۡخَلۡقُ وَٱلۡأَمۡرُۗ تَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 7:54Lalle Ubangijinku shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da ƙasa cikin kwanaki shida, sannan sai Ya daidaita a kan Al’arshi, Yana lulluɓe (duhun) dare da (hasken) yini, (kowannensu) yana neman sa (ɗan’uwansa) a gurguje, da rana da wata da taurari kuma abubuwan horewa ne da umarninsa. Haƙiƙa halitta da umarni nasa ne. Albarkatun Allah Ubangijin talikai sun yawaita.
ٱدۡعُواْ رَبَّكُمۡ تَضَرُّعٗا وَخُفۡيَةًۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ
Open ayah 7:55Ku roƙi Ubangijinku kuna masu ƙasƙantar da kai, kuma a ɓoye. Lalle Shi ba ya son masu ƙetare iyaka.
وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَا وَٱدۡعُوهُ خَوۡفٗا وَطَمَعًاۚ إِنَّ رَحۡمَتَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 7:56Kuma kada ku yi ɓarna a bayan ƙasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaɗayi. Lalle rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, shi ne wanda ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, sannan ya daidaita a kan Al’arshi, daidaito wanda ya dace da shi. Yana rufe hasken rana da duhun dare, ya kuma rufe duhun dare da hasken rana; kowane ɗaya daga cikinsu yana neman ɗayan da gaggawa ba ya jinkiri. Kuma ya halicci rana da wata da taurari waɗanda ya hore su da al’amarinsa da ikonsa don amfanin halittarsa. Haƙiƙa ƙirƙirar halitta da ba da umarni da hani duka nasa ne shi kaɗai. Albarkatunsa sun yawaita a ko’ina, shi ne Ubangijin talikai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mutane da su roƙe shi a cikin ƙasƙantar da kai da ɓoye addu’o’insu gare shi, ya nuna cewa, ba ya son masu wuce gona da iri a lokacin da suke yin addu’a. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Muna tare da Annabi (ﷺ) cikin wata tafiya, sai mutane suka riƙa ɗaga murya suna yin kabbara da ƙarfi, sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ku sauƙaƙa wa kanku ya ku mutane, domin ba kurma ko wanda ba ya nan kuke kira ba; kuna kiran mai ji ne kuma makusanci, yana nan tare da ku.” [Bukhari #2992, da Muslim #2704]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kashedi game da yaɗa ɓarna a bayan ƙasa bayan gyara ta, su kuma ji tsoron fushinsa da uƙubarsa, tare da kwaɗayin samun yardarsa da sakamakonsa. Rahamar Allah kuma tana kusa da masu kyautatawa.
وَهُوَ ٱلَّذِي يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ بُشۡرَۢا بَيۡنَ يَدَيۡ رَحۡمَتِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَقَلَّتۡ سَحَابٗا ثِقَالٗا سُقۡنَٰهُ لِبَلَدٖ مَّيِّتٖ فَأَنزَلۡنَا بِهِ ٱلۡمَآءَ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِۚ كَذَٰلِكَ نُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Open ayah 7:57Kuma Shi ne Wanda yake aiko da iska don albishir kafin zuwan rahamarsa; har lokacin da ta ɗauko gizagizai masu nauyi (cike da ruwa), sai Mu kora shi ga wani gari matacce, sai Mu saukar da ruwa da shi, Mu kuma fitar da dukkan ‘ya‘yan itace a sanadiyyarsa. Kamar haka ne Muke fito da matattu don ku wa’azantu.
وَٱلۡبَلَدُ ٱلطَّيِّبُ يَخۡرُجُ نَبَاتُهُۥ بِإِذۡنِ رَبِّهِۦۖ وَٱلَّذِي خَبُثَ لَا يَخۡرُجُ إِلَّا نَكِدٗاۚ كَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَشۡكُرُونَ
Open ayah 7:58Wuri kuma mai kyau, tsironsa yana fitowa (kyakkyawa) da izinin Ubangijinsa. Wuri kuwa lalatacce (shukarsa) ba ta fita sai da kyar. Kamar haka ne Muke sarrafa ayoyi ga mutanen da suke yin godiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar mana cewa, shi ne yake aiko da iska mai yin albishir da saukowar ruwan sama wanda rahama ne ga bayinsa. Har wannan iska ta ɗauko girgije mai nauyi cike da ruwa sai Allah ya kaɗa wannan girgijen zuwa ga wani gari matacce, wato wanda ya ƙeƙashe saboda rashin samun ruwan sama, sai ya saukar da wannan ruwa a wannan gari, ya fitar da tsirrai da ‘ya’yan itatuwa da shi bayan fari ya lahanta shi. To kamar haka ne Allah yake fitar da matattu da ransu daga ƙaburburansu, kuma yana yin haka ne domin mutane su wa’azantu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ƙasar da take kyakkyawa shukarta tana fita da kyau da izinin Allah, amma mummunar ƙasa shukarta ba ta fitowa sai da ƙyar kuma marar amfani marar albarka. To kamar haka ne Allah yake bayyana ayoyi ga mutane masu godiya.
لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 7:59Lalle haƙiƙa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: “Ya ku mutanena, ku bautata wa Allah, ba ku da wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, lalle ni ina ji muku tsoron azabar wani yini mai girma.”
قَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِهِۦٓ إِنَّا لَنَرَىٰكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 7:60Sai manyan gari cikin mutanensa suka ce: “Lalle mu tabbas muna ganin kana cikin ɓata mabayyani.”
قَالَ يَٰقَوۡمِ لَيۡسَ بِي ضَلَٰلَةٞ وَلَٰكِنِّي رَسُولٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 7:61Sai ya ce: “Ya ku mutanena, babu wata ɓata tare da ni, sai dai ni Manzo ne daga Ubangijin halittu.”
أُبَلِّغُكُمۡ رِسَٰلَٰتِ رَبِّي وَأَنصَحُ لَكُمۡ وَأَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:62“Ina isar muku da saƙonnin Ubangijina, ina kuma yi muku nasiha, na kuma san abin da ba ku sani ba daga Allah.
أَوَعَجِبۡتُمۡ أَن جَآءَكُمۡ ذِكۡرٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَلَىٰ رَجُلٖ مِّنكُمۡ لِيُنذِرَكُمۡ وَلِتَتَّقُواْ وَلَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Open ayah 7:63“Shin kun yi mamaki ne don wa’azi ya zo muku daga Ubangijinku, ta kan harshen wani mutum cikinku, don ya gargaɗe ku, don ku kuma kiyaye dokokin Allah domin a ji ƙan ku?”
فَكَذَّبُوهُ فَأَنجَيۡنَٰهُ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ وَأَغۡرَقۡنَا ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمًا عَمِينَ
Open ayah 7:64Sai suka ƙaryata shi, sai Muka tserar da shi da waɗanda suke tare da shi, a cikin jirgin ruwa, kuma Muka dulmiyar da waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu. Lalle su sun kasance mutane makafi. A waɗannan ayoyi da wasu masu zuwa nan gaba Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin annabawan da ya aiko wa al’ummomin da suka gabata. Daga cikin amfanin kawo waɗannan labarai shi ne: 1. Ba da labarin cewa, faɗa da gaskiya da bijire wa annabawa ba daga al’ummar Annabi Muhammadu (ﷺ) aka fara shi ba; wannan wata daɗaɗɗiyar al’ada ce a tarihin rayuwar ɗan’adam. A nan akwai rarrashin Annabi (ﷺ) da haƙurƙurtar da shi. 2. Bayanin cewa, ƙarshen duk wasu masu girman kai da faɗa da gaskiya shi ne taɓewa da la’anar Allah da ke tabbata a kansu da hasarar duniya da ta lahira. Amma masu gaskiya da aiki da ita ƙarshen al’amarinsu shi ne samun nasara da arzikin duniya da na lahira. 3. Bayani a kan cewa, Allah yana iya jinkirta wa masu laifi, amma ba zai ƙyale su ba sai ya saukar musu da azabarsa. 4. Waɗannan labaran suna ƙara tabbatar da annabcin Annabi (ﷺ), domin kasancewarsa ba ya rubutu kuma ba ya karatu, kuma ba shi da wani malami mutum ko aljan, to sai ga shi ana samun waɗannan labarai daga wajensa, wannan babu shakka ya tabbatar da cewa, wahayi yana zo masa ne daga Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fara bayyana mana cewa, ya aiko da Manzonsa Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa ga mutanensa domin ya kirawo su zuwa ga bautar Allah shi kaɗai da barin bauta wa wani ba shi ba. Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana wa mutanensa haka, ya kuma ja hankalinsu da su ji tsoron ranar lahira, domin kuwa yana jiye musu tsoron azabar wannan ranar. To amma sai shugabanni masu girman kai a cikin mutanensa suka ce masa, su fa lalle suna ganin sa yana cikin wani ɓata ne bayyananne. Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce musu, shi fa ba ya cikin wani ɓata; ya zo ne kawai ya yi kiran su zuwa ga Tauhidi da barin shirka, kuma Allah Ubangijin talikai ne ya aiko shi don ya isar musu da wannan saƙo, ya kuma yi musu nasiha, kuma shi ya san abin da su ba su sani ba, don shi ana yi masa wahayi ne, su kuma ba a yi musu. Ya sake nuna musu cewa, bai kamata su yi mamaki ba don an aiko musu da wani mutum daga cikinsu yana gargaɗin su yana tsoratar da su azabar Allah idan sun kafirce masa, yana horon su da su ji tsoron Allah su bi shi don su gamu da rahamarsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da mu cewa, mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙaryata shi, to amma sai ya saukar musu da azabar ruwan Ɗufana wanda ya halaka su, kuma ya kuɓutar da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanen da suke tare da shi a cikin jirgin ruwa. Allah ya bayyana cewa, mutanen Annabi Nuhu sun makance don haka sun kasa ganin gaskiya su bi ta, sai suka cancanci wannan azabar.
۞وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمۡ هُودٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 7:65Kuma Mun aika wa Adawa ɗan’uwansu Hudu. Ya ce: “Ya ku mutanena, ku bautata wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Shin ba za ku kiyaye dokokin Allah ba?”
قَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦٓ إِنَّا لَنَرَىٰكَ فِي سَفَاهَةٖ وَإِنَّا لَنَظُنُّكَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Open ayah 7:66Sai manyan gari waɗanda suka kafirce cikin mutanensa suka ce: “Lalle mu tabbas muna ganin ka kana cikin wauta, kuma lalle mu tabbas muna zaton kai kana cikin maƙaryata.
قَالَ يَٰقَوۡمِ لَيۡسَ بِي سَفَاهَةٞ وَلَٰكِنِّي رَسُولٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 7:67Sai ya ce <b>: </b>“Ya ku mutanena, babu wata wauta a tare da ni, sai dai ni kawai Manzo ne daga Ubangijin talikai.
أُبَلِّغُكُمۡ رِسَٰلَٰتِ رَبِّي وَأَنَا۠ لَكُمۡ نَاصِحٌ أَمِينٌ
Open ayah 7:68“Ina isar muku da saƙonnin Ubangijina, kuma ni mai nasiha ne a gare ku, amintacce.
أَوَعَجِبۡتُمۡ أَن جَآءَكُمۡ ذِكۡرٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَلَىٰ رَجُلٖ مِّنكُمۡ لِيُنذِرَكُمۡۚ وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ جَعَلَكُمۡ خُلَفَآءَ مِنۢ بَعۡدِ قَوۡمِ نُوحٖ وَزَادَكُمۡ فِي ٱلۡخَلۡقِ بَصۜۡطَةٗۖ فَٱذۡكُرُوٓاْ ءَالَآءَ ٱللَّهِ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Open ayah 7:69“Shin mamaki kuke yi wa’azi ya zo muku daga Ubangijinku a kan (harshen) wani mutum daga cikinku don ya gargaɗe ku? Kuma ku tuna yayin da Ya sa kuka zama masu maye gurbi bayan wucewar mutanen Nuhu, kuma Ya ƙara muku girman halitta; don haka ku tuna ni’imomin Allah, don ku rabauta.”
قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِنَعۡبُدَ ٱللَّهَ وَحۡدَهُۥ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا فَأۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 7:70Sai suka ce: “Yanzu ka zo mana ne don mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu ƙyale abin da iyayenmu suka kasance suna bautata wa? To ka kawo mana abin da kake yi mana alƙawarinsa idan ka kasance cikin masu gaskiya.”
قَالَ قَدۡ وَقَعَ عَلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡ رِجۡسٞ وَغَضَبٌۖ أَتُجَٰدِلُونَنِي فِيٓ أَسۡمَآءٖ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّا نَزَّلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٖۚ فَٱنتَظِرُوٓاْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُنتَظِرِينَ
Open ayah 7:71Sai ya ce: “Haƙiƙa azaba da fushi daga Ubangijinku sun faɗa a kanku. Yanzu kwa riƙa jayayya da ni a kan waɗansu sunaye da ku ne kuka ƙago su da iyayenku, alhalin Allah bai saukar da wata hujja a kansu ba? To ku jira (ku gani), lalle ni ma ina nan cikin masu jira tare da ku.”
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَقَطَعۡنَا دَابِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۖ وَمَا كَانُواْ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 7:72Sai Muka tserar da shi, da waɗanda suke tare da shi da rahamarmu, Muka kuma tumɓuke tushen waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu; kuma ba su kasance muminai ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin Adawa mutanen Annabi Hudu. Adawa wasu ƙabilu ne na Larabawa waɗanda suka zauna a ƙasar Al-Ahƙaf , kudancin tsibirin Larabawa, arewa da Hadaramaut ta ƙasar Yaman, kuma gabas da ƙasar Oman. A yanzu garuruwansu kango ne, babu wani ɗan’adam da yake rayuwa a wurin. Allah ya aiko musu ɗaya daga cikinsu shi ne Annabi Hudu domin ya yi kiran su zuwa bauta wa Allah shi kaɗai ba tare da yi masa shirka ba, ya nusar da su a kan su ji tsoron Ubangijinsu da azabarsa da fushinsa, amma sai shugabanninsu masu girman kai suka ce masa, su fa lalle suna ganin sa wani wawa ne marar cikakken hankali, kuma ma lalle suna zaton shi maƙaryaci ne. Sai Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar musu da martani cewa, shi ba ya da wata wauta ko ƙarancin hankali; shi Manzo ne da Allah ya aiko musu shi don ya isar musu da saƙon Ubangijinsu, kuma shi mai nasiha ne amintacce a gare su. Sai kuma Annabi Hudu ya nuna musu cewa, bai kamata su riƙa mamakin an aiko musu da wani mutum daga cikinsu domin ya tsoratar da su uƙubar Ubangijinsu gare su saboda kafircinsu ba. Kuma su tuna ni’imar da Allah ya yi musu yayin da ya sanya su suka maye gurbin mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bayan ya halaka su, sannan ya ƙara musu tsawo da ƙarfin jiki. Don haka su riƙa tuna ni’imomin Allah da ya yi musu don su sami rabauta duniya da lahira. To amma duk da irin wannan jan hankalin da Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mutanensa, sai suka bijire wa kiransa, suka nuna masa cewa, yaya za a yi su bar abin da iyayensu suke bauta wa? Sai dai Annabi Hudu ya zo musu da azabar da yake tsorata su da ita idan har shi mai gaskiya ne. Sai Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce musu, tabbas azabar Allah da fushinsa sun tabbata a kansu babu makawa, ya nuna musu mamakinsa da har suke jayayya da shi a kan wasu gumaka nasu waɗanda su da iyayensu ne suka raɗa musu suna suna bauta musu, babu wata hujja daga Allah da suke iya nunawa a kan bautar su. Don haka su jira azabar Allah da za ta auka musu, shi ma zai jira tare da su. Daga ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya tserar da Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka ba da gaskiya da shi, sannan ya halaka waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah, ba su yi imani da Annabi Hudu ba.
وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ قَدۡ جَآءَتۡكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡۖ هَٰذِهِۦ نَاقَةُ ٱللَّهِ لَكُمۡ ءَايَةٗۖ فَذَرُوهَا تَأۡكُلۡ فِيٓ أَرۡضِ ٱللَّهِۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 7:73Zuwa ga Samudawa kuwa Mun aika ɗan’uwansu Salihu. Ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; haƙiƙa hujja ta zo muku daga Ubangijinku. Wannan kuma taguwar Allah aya ce a gare ku; don haka ku ƙyale ta ta ci a bayan ƙasar Allah; kuma kar ku taɓa ta da wani mugun abu, sai wata azaba mai raɗaɗi ta shafe ku.
وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ جَعَلَكُمۡ خُلَفَآءَ مِنۢ بَعۡدِ عَادٖ وَبَوَّأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ تَتَّخِذُونَ مِن سُهُولِهَا قُصُورٗا وَتَنۡحِتُونَ ٱلۡجِبَالَ بُيُوتٗاۖ فَٱذۡكُرُوٓاْ ءَالَآءَ ٱللَّهِ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ
Open ayah 7:74“Kuma ku tuna lokacin da Ya sanya ku kuka zama masu maye gurbi bayan Adawa, kuma Ya zaunar da ku a bayan ƙasa, kuna yin benaye a wurarenta masu taushi, kuma kuna sassaƙa gidaje a duwatsu; don haka ku tuna ni’imomin Allah, kada kuma ku yi ɓarna a bayan ƙasa.”
قَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ لِلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ لِمَنۡ ءَامَنَ مِنۡهُمۡ أَتَعۡلَمُونَ أَنَّ صَٰلِحٗا مُّرۡسَلٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قَالُوٓاْ إِنَّا بِمَآ أُرۡسِلَ بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ
Open ayah 7:75Manyan gari waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa, suka ce wa waɗanda suke raunana waɗanda suka yi imani daga cikinsu: “Yanzu kun san cewa Salihu Manzo ne daga wajen Ubangijinsa?” Sai suka ce; “Lalle mu dai mun yi imani da abin da aka aiko shi da shi.”
قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا بِٱلَّذِيٓ ءَامَنتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ
Open ayah 7:76Waɗanda suka yi girman kai suka ce: “Lalle mu kuma mun kafirce wa abin da kuka yi imani da shi.”
فَعَقَرُواْ ٱلنَّاقَةَ وَعَتَوۡاْ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِمۡ وَقَالُواْ يَٰصَٰلِحُ ٱئۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 7:77Sai suka soke taguwar, suka kuma yi tsaurin kai game da umarnin Ubangijinsu, kuma suka ce: “Ya Salihu, ka zo mana da abin da kake mana alƙawarin zai same mu (na azaba) in ka kasance cikin manzanni.”
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دَارِهِمۡ جَٰثِمِينَ
Open ayah 7:78Sai wata girgizar ƙasa mai tsanani ta auka musu, sai suka wayi gari a gurfane kan gwiwoyinsu, (matattu) a cikin gidajensu.
فَتَوَلَّىٰ عَنۡهُمۡ وَقَالَ يَٰقَوۡمِ لَقَدۡ أَبۡلَغۡتُكُمۡ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحۡتُ لَكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُحِبُّونَ ٱلنَّٰصِحِينَ
Open ayah 7:79Sai ya juya ya rabu da su, kuma ya ce: “Ya ku mutanena, lalle haƙiƙa na isar muku da saƙon Ubangijina, kuma na yi muku nasiha, sai dai ku ba kwa son masu nasiha.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba mu labarin cewa ya aika wa ƙabilar Samudawa ɗan’uwansu na jini Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Samudawa ƙabila ce daga cikin ƙabilun Larabawa da suka rayu a wani wuri da ake kiran sa Al-Hijr , yana nan a tsakanin Madina da ƙasar Sham. Kufan Samudawa har yanzu akwai shi, kuma ana kiran wurarensu da suna ‘Mada’inu Salih’ . Allah ya hallaka su saboda sun kafirce wa Annabinsa Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aika wa Samudawa Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don ya kirawo su zuwa bauta wa Allah shi kaɗai da nisantar bautar wani abu ba shi ba, ya faɗa musu cewa, hujja mai ƙarfi daga Ubangijinsu ta zo musu tana tabbatar da kasancewarsa Manzo daga Allah. Wannan hujja kuwa ita ce taguwar da Allah ya ba shi don ta zama mu’ujiza mai nuna gaskiyar manzancinsa. Don haka ya gargaɗe su da cewa, su ƙyale ta ta ci arzikin Allah a bayan ƙasa, kada su kuskura su cutar da ita, za su gamu da azaba mai raɗaɗi. Annabi Salihu ya neme su da su tuna ni’imar da Allah ya yi musu lokacin da ya maye gurbin mutanen Annabi Hudu da su bayan ya halaka su, ya zaunar da su a Al-Hijr , wani wuri tsakanin Madina da ƙasar Sham, suka riƙa yin manya-manyan gine-gine a wurare masu taushin ƙasa, kuma suna sassaƙa duwatsu suna mayar da su gidaje, don haka su tuna ni’imomin da Allah ya yi musu don su bauta masa shi kaɗai, su yi imani da Manzonsa Annabi Salihu, kada su yi ɓarna a bayan ƙasa. Sai shugabanninsu masu girman kai suka ce wa raunanan muminai, wai yanzu su sun yarda Salihu Manzon Allah ne, ba ƙarya yake yi musu ba? Sai muminan suka amsa musu da cewa, su kam sun ba da gaskiya da shi. Sai shugabannin suka ce, su kam sun kafirce wa abin da muminai suka yi imani da shi, suka yi girman kai, suka ƙi bin umarnin Ubangijinsu, suka kashe wannan taguwar, suka ce da Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo musu da azabar da yake tsorata su da ita, idan har da gaske shi Manzon Allah ne. Sai kuwa azabar Allah ta auko musu, Allah ya aiko musu da wata tsawa mai ƙarfin gaske, mai girgiza ƙasa saboda tsananinta, sai duk suka zama gawarwaki a duddurƙushe kamar kututturen itacen dabino saboda tsawonsu da girman jikinsu. Sai Annabi Salihu ya juya ya rabu da su yana mai zargin su a kan abin da ya same su, yana cewa, haƙiƙa shi kam ya isar musu da saƙon Allah, ya kuma yi musu nasiha, to amma kuma saboda ba sa son masu yi musu nasiha, nasiharsa ba ta yi musu amfani ba.
وَلُوطًا إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَتَأۡتُونَ ٱلۡفَٰحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنۡ أَحَدٖ مِّنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 7:80Kuma ka tuna Luɗu lokacin da ya ce wa mutanensa: “Yanzu kwa riƙa aikata mummunan aikin da babu wani mahaluƙi a duniya da ya taɓa aikata irinsa gabaninku?
إِنَّكُمۡ لَتَأۡتُونَ ٱلرِّجَالَ شَهۡوَةٗ مِّن دُونِ ٱلنِّسَآءِۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ مُّسۡرِفُونَ
Open ayah 7:81“Lalle ku kuna zaike wa maza don sha’awa maimakon mata. A’a, ku mutane ne maɓarnata.”
وَمَا كَانَ جَوَابَ قَوۡمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَخۡرِجُوهُم مِّن قَرۡيَتِكُمۡۖ إِنَّهُمۡ أُنَاسٞ يَتَطَهَّرُونَ
Open ayah 7:82Ba kuwa amsar da ta fito daga bakin mutanensa sai kawai suka ce: “Ku fitar da su daga garinku; lalle su mutane ne da suke nuna su masu tsarki ne.”
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ كَانَتۡ مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ
Open ayah 7:83Sai Muka tserar da shi da iyalansa, in ban da matarsa, ita ta kasance cikin waɗanda suka rage (a cikin azaba).
وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 7:84Sai Muka yi musu ruwan azaba; to duba ka ga yaya ƙarshen masu babban laifi ya kasance? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Shi dai Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ɗan ɗan’uwan Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne, ya ba da gaskiya da baffansa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kuma ya yi hijira tare da shi daga ƙasar Iraƙi zuwa ƙasar Kan’ana, wato ƙasar Falasɗinu. Sai Allah ya ba shi manzanci tun lokacin rayuwar baffansa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya aike shi zuwa ga mutanen garin Sadum; sun kuma kasance mazauna wurin da a yanzu ake kira da Mataccen Teku ne (Dead Sea) da ke ƙasar Urdun (Jordan) . Waɗannan mutane sun shahara da wata mummunar ta’ada da ba a taɓa samun masu aikata irinta ba a gabaninsu. Wannan ta’ada kuwa ita ce zaike wa maza ta dubura. Kuma wani ƙarin abin takaicin suna gudanar da wannan ƙazantaccen laifi ne a gaban idon junansu. Bayan wannan kuma an san su da yawan aikata laifukan fashi da makami a kan hanyoyin matafiya, don haka sun hana matafiya da attajirai fatake sakat, suna tare su suna yi musu fashi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Annabi Muhammadu (ﷺ) cewa, ya aiko musu Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don ya hana su aikata waɗannan miyagun laifuka, to amma sai suka ƙi sauraron sa, har ta kai ya yi musu addu’ar Allah ya hallaka su. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ya karɓi addu’arsa ya aiko musu da ruwan azaba, ya kuma kifar da ƙasar, wato samanta ya koma ƙasa, ƙasanta ya koma sama, ya biyo su da ruwan duwatsu na wutar Jahannama. Allah kuma ya tserar da Annabi Luɗu da mutanensa in ban da matarsa wadda tana daga cikinsu waɗanda aka hallaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce wa Annabinsa Muhammadu (ﷺ), ya tuna Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya faɗa wa mutanensa cewa, yanzu sa riƙa aikata mummunan aikin da babu wani mahaluƙi da ya taɓa yin irinsa a gabaninsu? Ya faɗa musu cewa, suna zaike wa maza ta dubura domin buƙatar sha’awarsu, suna barin auren mata da Allah ya halatta musu, saboda kawai su mutane ne maɓarnatan gaske. To amma da mutanensa suka tashi mayar masa da martani, sai kawai suka ce, a kori Annabi Luɗu shi da iyalansa daga wannan gari, ba don komai ba sai don sun nuna su mutane ne masu ƙyamar irin aikin mutanen wannan gari. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kuɓutar da shi, shi da iyalansa, ban da matarsa kafira, ita an halakar da ita tare da waɗanda aka hallakar. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu ruwan duwatsu na taɓo mai tsananin ƙuna. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce wa, Annabi Muhammadu (ﷺ) ko mai karatu ya duba ya ga yadda ƙarshen masu laifi ya zama.
وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ قَدۡ جَآءَتۡكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡۖ فَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَاۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 7:85Kuma (Mun) aika wa mutanen Madyana ɗan’uwansu Shu’aibu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, haƙiƙa hujja ta zo muku daga Ubangijinku; don haka ku riƙa cika mudu, kuma ku (kiyaye) ma’auni, kuma kada ku tauye wa mutane abubuwansu, kuma kada ku yi ɓarna a bayan ƙasa bayan an gyara ta. Wannan shi ne mafi alheri a gare ku in kun kasance muminai.
وَلَا تَقۡعُدُواْ بِكُلِّ صِرَٰطٖ تُوعِدُونَ وَتَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ مَنۡ ءَامَنَ بِهِۦ وَتَبۡغُونَهَا عِوَجٗاۚ وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ كُنتُمۡ قَلِيلٗا فَكَثَّرَكُمۡۖ وَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 7:86“Kuma kada ku zauna a kan kowace hanya kuna tsoratar da (mutane), kuma kuna toshe hanyar Allah ga duk wanda ya yi imani da Shi, kuna kuma son ta zama karkatacciya. Kuma ku tuna (ni’imar Allah) lokacin da kuke ‘yan kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku duba ku ga yaya ƙarshen maɓarnata ya kasance?
وَإِن كَانَ طَآئِفَةٞ مِّنكُمۡ ءَامَنُواْ بِٱلَّذِيٓ أُرۡسِلۡتُ بِهِۦ وَطَآئِفَةٞ لَّمۡ يُؤۡمِنُواْ فَٱصۡبِرُواْ حَتَّىٰ يَحۡكُمَ ٱللَّهُ بَيۡنَنَاۚ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡحَٰكِمِينَ
Open ayah 7:87“Idan kuma an sami wata ƙungiya daga cikinku sun yi imani da abin da aka aiko ni da shi, wata ƙungiyar kuma ba su yi imani ba, to ku yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci a tsakaninmu. Kuma Shi ne Fiyayyen masu hukunci.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba mu labarin mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Su dai Larabawa ne, ana kiran su da mutanen Madyana. Madyana wani gari ne da ke tsakanin Hijaz da tekun Aƙaba (Gulf of Aqaba) kusa da gaɓar Bahar Maliya (Red Sea) . A yanzu garin ya mutu babu sauran mutane a wurin. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don ya kirawo su zuwa ga bautar Allah shi kaɗai da barin bautar gumaka, ya kuma yi musu wa’azi a kan muguwar al’adarsu ta tauye mudu ko sikeli lokacin awo, to amma ba su saurari kiransa ba, sun kangare masa, sai Allah ya hallaka su da wata girgizar ƙasa. Farkon abin da Annabi Shu’aibu ya fara tunkarar mutanensa da shi shi ne ya sanar da su cewa, ya zo musu da wata bayyananniyar hujja daga Ubangijinsu wadda take nuna gaskiyar manzancinsa. Don haka su cika ma’auni da sikeli kada su tauye wa mutane haƙƙoƙinsu, kada kuma su riƙa yaɗa ɓarna a bayan ƙasa bayan gyaranta. Wannan maganar da ake faɗa musu idan sun karɓe ta sun yi aiki da ita, ya fi musu alheri idan su muminai ne. Ya kuma ja kunnensu a kan su daina zama a hanya suna tsorata mutane da kisa ko azabtarwa, suna kuma hana wanda ya yi imani ya bi Allah ya bi Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), suna son hanyar Allah ta zama a karkace, wato ta yi daidai da soye-soyen zukatansu. Sannan ya buƙaci su tuna lokacin da adadinsu ba shi da yawa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yawaita su. Su kuma tuna yadda ƙarshen maɓarnata ya zama. Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya faɗa wa mutanensa cewa, idan wata ƙungiya daga cikinsu ta yi imani da abin da Allah ya aiko shi da shi na kaɗaita Allah da bauta da barin aikata ɓarna a bayan ƙasa, wata ƙungiyar kuma ba ta yi imani da hakan ba, to su yi haƙuri su saurara har lokacin da Allah zai yi hukunci a tsakaninsu, domin shi ne Fiyayyen masu hukunci, sai ya tseratar da muminai ya kuma halaka kafirai.
۞قَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ لَنُخۡرِجَنَّكَ يَٰشُعَيۡبُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَكَ مِن قَرۡيَتِنَآ أَوۡ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَاۚ قَالَ أَوَلَوۡ كُنَّا كَٰرِهِينَ
Open ayah 7:88Sai manyan gari, waɗanda suka yi girman kai daga cikin mutanensa suka ce: “Lalle za mu fitar da kai, ya kai Shu’aibu, da waɗanda suka yi imani tare da kai, daga alƙaryarmu, ko kuma ku dawo cikin addininmu.” (Shu’aibu) ya ce: “Ko da muna ƙin (hakan)?”
قَدِ ٱفۡتَرَيۡنَا عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا إِنۡ عُدۡنَا فِي مِلَّتِكُم بَعۡدَ إِذۡ نَجَّىٰنَا ٱللَّهُ مِنۡهَاۚ وَمَا يَكُونُ لَنَآ أَن نَّعُودَ فِيهَآ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّنَاۚ وَسِعَ رَبُّنَا كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمًاۚ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡنَاۚ رَبَّنَا ٱفۡتَحۡ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَ قَوۡمِنَا بِٱلۡحَقِّ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡفَٰتِحِينَ
Open ayah 7:89“Haƙiƙa mun ƙirƙiri ƙarya, mun jingina wa Allah, in har muka komo cikin addininku, bayan kuwa Allah Ya tserar da mu daga gare shi. Kuma ba ma zai yiwu ba mu koma cikinsa sai dai idan Allah Ubangijinmu ne Ya ga dama. Kuma ilimin Ubangijinmu Ya yalwaci komai. Ga Allah kaɗai muka dogara. Ya Ubangijinmu, Ka yi hukunci tsakaninmu da mutanenmu da gaskiya, kuma Kai ne Fiyayyen masu hukunci.”
وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ لَئِنِ ٱتَّبَعۡتُمۡ شُعَيۡبًا إِنَّكُمۡ إِذٗا لَّخَٰسِرُونَ
Open ayah 7:90Sai manyan gari waɗanda suka kafirce daga cikin mutanensa, suka ce: “Wallahi idan kun bi Shu’aibu fa, lalle ku tabbas kuna cikin hasararru.”
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دَارِهِمۡ جَٰثِمِينَ
Open ayah 7:91Sai girgizar ƙasa ta kama su, suka wayi gari a gidajensu gurfane a kan gwiwoyinsu (matattu).
ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ شُعَيۡبٗا كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَاۚ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ شُعَيۡبٗا كَانُواْ هُمُ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Open ayah 7:92Waɗanda suka ƙaryata Shu’aibu, kai ka ce ba su taɓa zama a cikinsu (gidajensu) ba, lalle waɗanda suka ƙaryata Shu’aibu sun kasance su ne hasararru.
فَتَوَلَّىٰ عَنۡهُمۡ وَقَالَ يَٰقَوۡمِ لَقَدۡ أَبۡلَغۡتُكُمۡ رِسَٰلَٰتِ رَبِّي وَنَصَحۡتُ لَكُمۡۖ فَكَيۡفَ ءَاسَىٰ عَلَىٰ قَوۡمٖ كَٰفِرِينَ
Open ayah 7:93Sai ya juya ya bar su, kuma ya ce: “Ya ku mutanena, lalle haƙiƙa na isar muku da saƙonnin Ubangijina, na kuma yi muku nasiha; to saboda me zan ji takaici a kan mutane kafirai?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin ƙissar Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa, yana bayyana lokacin da shugabanninsu masu girman kai suka yi masa barazanar korar sa tare da waɗanda suka yi imani da shi daga garinsu ko kuma in ba haka ba su koma tsohon addininsu da suka bari. Sai ya amsa musu da cewa, yanzu sai su iya mayar da su addininsu ko da kuwa ba sa son hakan? Ya ce, haƙiƙa shi da mutanensa sun yi wa Allah ƙarya idan har suka yarda suka koma addininsu na farko bayan Allah ya kuɓutar da su daga gare shi. Ya tabbatar musu da cewa, ba za ta yiwu su koma cikin wannan addini ba, sai dai idan Allah ne ya ga damar haka ta faru, domin iliminsa ya yalwaci komai. Ya ce sun dogara ga Allah (Mai tsarki da daukaka) shi kaɗai a cikin duk al’amuransu. Sannan ya yi addu’a cewa, ya Ubangijinmu, ka yi hukunci a tsakaninmu da mutanenmu, ka ba mu nasara, domin kai ne Fiyayyen masu hukunci. Sai shugabannin kafirai masu faɗa a ji suka faɗa wa waɗanda suke ƙarƙashinsu cewa, idan har suka yarda suka bi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), to lalle sun zama taɓaɓɓu hasararru. To yayin da tura ta kai bango, mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙi yin imani da shi, sun kuma sha alwashin cutar da shi har da mabiyansa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da wata girgizar ƙasa mai tsanani ta same su, sai suka wayi gari matattu a duddurƙushe a cikin gidajensu. Allah ya halaka su kamar ba su taɓa zama a cikin gidajensu ba. Lalle waɗanda suka ƙaryata Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun tabbata su ne taɓaɓɓu, hasararru. Daga nan Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rabu da su yana cewa, ya dai isar musu da saƙon da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko shi da shi, ya kuma yi musu nasiha, don haka me zai sa shi ya yi baƙin ciki a kan abin da ya same su saboda kafircinsu?
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّبِيٍّ إِلَّآ أَخَذۡنَآ أَهۡلَهَا بِٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ لَعَلَّهُمۡ يَضَّرَّعُونَ
Open ayah 7:94Kuma ba Mu taɓa aiko wani annabi cikin wata alƙarya ba, (mutanensa suka ƙaryata shi) sai Mun kama su da tsananin talauci da cututtuka, ko sa ƙasƙantar da kai.
ثُمَّ بَدَّلۡنَا مَكَانَ ٱلسَّيِّئَةِ ٱلۡحَسَنَةَ حَتَّىٰ عَفَواْ وَّقَالُواْ قَدۡ مَسَّ ءَابَآءَنَا ٱلضَّرَّآءُ وَٱلسَّرَّآءُ فَأَخَذۡنَٰهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 7:95Sannan sai Muka musanya mahallin tsanani da jin daɗi, har dai suka yawaita, suka ce: “Haƙiƙa da can cututtuka da kuma wadata sun samu iyayenmu.” Sai kawai Muka damƙe su (da azaba) ba zato ba tsammani alhalin ba sa jin (hakan zai faru).
وَلَوۡ أَنَّ أَهۡلَ ٱلۡقُرَىٰٓ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَفَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَرَكَٰتٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِن كَذَّبُواْ فَأَخَذۡنَٰهُم بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 7:96Kuma in da a ce mutanen alƙaryu sun yi imani kuma sun tsare dokokin Allah, to lalle da Mun buɗe musu albarkatu daga sama da kuma ƙasa, sai dai sun ƙaryata, Mu kuwa sai Muka kama su da abin da suka kasance suna aikatawa.
أَفَأَمِنَ أَهۡلُ ٱلۡقُرَىٰٓ أَن يَأۡتِيَهُم بَأۡسُنَا بَيَٰتٗا وَهُمۡ نَآئِمُونَ
Open ayah 7:97Yanzu mutanen alƙaryu sun amince azabarmu ta zo musu cikin dare alhali suna bacci?
أَوَأَمِنَ أَهۡلُ ٱلۡقُرَىٰٓ أَن يَأۡتِيَهُم بَأۡسُنَا ضُحٗى وَهُمۡ يَلۡعَبُونَ
Open ayah 7:98Ko kuma mutanen alƙaryun sun amince azabarmu ta zo musu da hantsi suna tsakiyar wasanni?
أَفَأَمِنُواْ مَكۡرَ ٱللَّهِۚ فَلَا يَأۡمَنُ مَكۡرَ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 7:99Yanzu sun amince da makarun Allah ne? To kuwa ba mai amince wa makarun Allah sai mutanen da suke asararru.
أَوَلَمۡ يَهۡدِ لِلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡأَرۡضَ مِنۢ بَعۡدِ أَهۡلِهَآ أَن لَّوۡ نَشَآءُ أَصَبۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡۚ وَنَطۡبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ
Open ayah 7:100Ko kuwa bai bayyana ba ga waɗanda suke gaje ƙasa bayan gushewar mutanenta (na farko) cewa, idan da Mun ga dama da Mun kama su da zunubansu. Kuma da Mun rufe zukatansu don haka ba za su iya ji ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙarin bayani ne game da ƙissoshin da suka gabata da dalilan da sukan jawo Allah ya hallakar da wata al’umma ko ya saukar musu da wata azaba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu wani garin da ya aiko musu da wani annabi kuma suka ƙaryata shi, sai ya kama su da azabar talauci da cututtuka, domin su ƙasƙantar da kansu gare shi, su roƙe shi don ya yaye musu wannan musifar. To amma sai ya zamanto hakan bai amfane su ba, sai su ci gaba da shisshigi cikin zunubi da kangara, sai Allah ya yi musu talala ya canza musu da jin daɗi maimakon wahalar da suke ciki, ya ba su lafiya, ya yawaita musu arzikinsu, har sai sun yi yawa, dukiyarsu da ‘ya’yansu ma sun bunƙasa sun yi yawa, sun manta da duk wahalhalun da suka taɓa samun su a baya, har suna ba da labarin cewa, a da can cututtuka da wadata sun sami iyayensu. To suna cikin haka kwatsam ba zato ba tsammani sai Allah ya kama su da azabarsa, alhali kuwa ba sa jin hakan zai faru. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da dai mutanen alƙaryu za su yi imani su kiyaye dokokin Allah, su gode wa ni’imominsa, da ya buɗe musu hanyoyin samun albarka daga sama da kuma ƙasa, to amma ba su yi hakan ba, maimakon hakan sai suka ƙaryata gaskiyar da ta zo musu, sai ko Allah ya hallakar da su saboda kafirci da manyan laifuka da suka aikata. To bayan wannan abu da ya faru, shin mutanen alƙaryun nan sun amince ne azabar Allah mai tsanani ta sauka a kansu cikin dare suna barci ko kuma ta zo musu da hantsi suna tsaka da wasa? Ko kuma sun amince wa makarun Allah ne? To babu mai amincewa da makarun Allah sai mutanen da suka tabbata taɓaɓɓu masu hasara. Shin ko kuwa waɗanda suka gaje ƙasa bayan halakar da mutanen cikinta na farko bai isa su gane cewa, Allah yana da iko idan ya ga dama ya halaka su saboda zunubansu, ya kuma rufe zukatansu, don haka ba za su ji gaskiya su karɓe ta ba?
تِلۡكَ ٱلۡقُرَىٰ نَقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآئِهَاۚ وَلَقَدۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُواْ بِمَا كَذَّبُواْ مِن قَبۡلُۚ كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 7:101Waɗancan alƙaryun Muna ba ka labarinsu ne. Kuma lalle haƙiƙa manzanninsu sun zo musu da hujjoji bayyananu, amma ba su kasance masu yin imani ba, saboda ƙaryatawar da suka yi a da. Kamar haka ne Allah Yake rufe zukatan kafirai.
وَمَا وَجَدۡنَا لِأَكۡثَرِهِم مِّنۡ عَهۡدٖۖ وَإِن وَجَدۡنَآ أَكۡثَرَهُمۡ لَفَٰسِقِينَ
Open ayah 7:102Kuma yawancinsu ba Mu same su da riƙe wani alƙawari ba; haƙiƙa kuma Mun samu yawancinsu fasiƙai ne.
ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَظَلَمُواْ بِهَاۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 7:103Sannan sai Muka aika Musa a bayansu da ayoyinmu, zuwa Fir’auna da manyan mutanensa, sai suka zalunci (kansu) da su; to duba ka ga, yaya ƙarshen maɓarnata ya kasance? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, waɗancan garuruwa da ƙissoshinsu suka gabata, yana ba shi labaransu ne don ya zama lallashi gare shi shi da muminai, ya kuma zama lallashi da kuma wa’azi ga masu wa’azantuwa, kuma su zama tsawatarwa da tsoratarwa ga kafirai. Manzanni sun zo wa mutanen waɗannan alƙaryu da hujjoji bayyanannu masu nuna gaskiyar manzancinsu, to amma sai suka ƙi yin imani, saboda sun ƙaryata gaskiya a lokacin da ta fara zuwa gare su. To kamar haka ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake doɗe zukatan kafirai, don haka har abada ba za su yi imani ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, bai samu yawancin al’ummomin da suka gabata suna cika alƙawarin da suka ɗauka ba; yawancinsu fasiƙai ne marasa tsoron Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, bayan wucewar waɗancan annabawa da ya ambaci ƙissoshinsu a baya, ya kuma aiko da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya ba shi mu’ujizoji da dalilai waɗanda suke tabbatar da gaskiyarsa, ya aika shi zuwa ga Fir’auna da manyan mutanensa, to amma sai girman kai ya sa suka kafirce wa ayoyin Allah, suka faɗa cikin zalunci a sanadiyyar haka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya duba ya ga yadda ƙarshen maɓarnata ya zama.
وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰفِرۡعَوۡنُ إِنِّي رَسُولٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 7:104Kuma Musa ya ce: “Ya kai Fir’auna, lalle ni Manzo ne daga Ubangijin talikai.
حَقِيقٌ عَلَىٰٓ أَن لَّآ أَقُولَ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ قَدۡ جِئۡتُكُم بِبَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ فَأَرۡسِلۡ مَعِيَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 7:105“Wajibi ne a kaina cewa ba zan faɗi wata magana game da Allah ba sai ta gaskiya. Haƙiƙa na zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku, don haka ka sakar min Banu Isra’ila.”
قَالَ إِن كُنتَ جِئۡتَ بِـَٔايَةٖ فَأۡتِ بِهَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 7:106Sai ya ce: “Idan har kana da wata alama, to ka zo da ita, idan har kana cikin masu gaskiya.”
فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٞ مُّبِينٞ
Open ayah 7:107Sai ya jefar da sandarsa, sai ga shi ta zama wani irin ƙaton kumurci a fili.
وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّٰظِرِينَ
Open ayah 7:108Kuma ya zaro hannunsa, sai ga shi fari ƙal ga masu kallo.
قَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٞ
Open ayah 7:109Sai manyan gari daga cikin mutanen Fir’auna suka ce: “Lalle wannan tabbas mai sihiri ne, masani.
يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُمۡۖ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ
Open ayah 7:110“Yana nufi ne ya fitar da ku daga ƙasarku, don haka me kuke yin umarni (da a yi)?”
قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَأَرۡسِلۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Open ayah 7:111Sai suka ce: “Ka dakatar da shi da ɗan’uwansa, ka kuma tura masu yin gangami cikin birane.
يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ
Open ayah 7:112“Za su zo maka da duk wani ƙwararren matsafi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana ƙissar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne da Fir’auna da mutanensa. Lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga wajen Fir’auna ya sanar da shi cewa shi Manzon Allah ne zuwa gare shi, kuma Allah shi ne Ubangijin kowa, mahaliccin kowa da komai, kuma wajibi ne a kansa ba zai faɗi wata magana ya jingina ta ga Allah ba, sai gaskiya, kuma ya zo masa da hujja bayyananniya daga Ubangijinsa, saboda haka lalle ya sakar masa Banu Isra’ila waɗanda ya kama ya tsare su yana gallaza musu azaba ba bisa wani haƙƙi ba. Sai Fir’auna ya ce masa, idan har da gaske ne ya zo da wata hujja, to ya bayyana ta kowa ya gan ta. Sai Annabi Musa ya jefar da sandarsa, sai ga shi ta zama wani ƙaton kumurci kowa yana ganin sa, ya kuma fito da hannunsa daga rigarsa, sai ga shi fari ƙal kowa yana kallo. To daga nan sai manyan mutane masu faɗa a ji daga cikin mutanen Fir’auna suka ce, lalle babu shakka Musa gogaggen matsafi ne wanda ya ƙware cikin sha’anin tsafi, kuma sun gane cewa so yake ya fitar da su daga ƙasarsu da wannan sihiri nasa, don haka me suke ganin ya kamata a yi masa? Sai manyan mutanen na Fir’auna suka ba shi shawarar cewa kamata ya yi, ya dakatar da Musa da ɗan’uwansa Haruna, ya tura gari-gari a yi masa gangami na manyan matsafa domin su tinkari Musa da tsafinsa.
وَجَآءَ ٱلسَّحَرَةُ فِرۡعَوۡنَ قَالُوٓاْ إِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ
Open ayah 7:113Matsafan kuwa suka zo wa Fir’auna suka ce: “Shin tabbas muna da wani lada idan muka kasance masu rinjaye?”
قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ لَمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
Open ayah 7:114Ya ce, “E, kuma ma tabbas kuna cikin makusanta.”
قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلۡقِيَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ نَحۡنُ ٱلۡمُلۡقِينَ
Open ayah 7:115Sai suka ce: “Ya kai Musa, ko dai ka (fara) jefawa, ko kuwa mu mu kasance mu ne masu (fara) jefawa.”
قَالَ أَلۡقُواْۖ فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ سَحَرُوٓاْ أَعۡيُنَ ٱلنَّاسِ وَٱسۡتَرۡهَبُوهُمۡ وَجَآءُو بِسِحۡرٍ عَظِيمٖ
Open ayah 7:116Ya ce: “Ku jefa”. To yayin da suka jefa (sandunansu) sai suka sihirce idon mutane, kuma suka gigita su, suka zo da wani tsafi babba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin abin da ya faru bayan an gayyato ƙwararrun matsafa daga gari-gari sun iso fadar Fir’auna ta Masar. Da suka iso sai suka nemi tabbacin ko zai biya su idan har su suka yi rinjaye a kan Musa? Fir’auna ya ce tabbas, ba ma lada kaɗai zai ba su ba; zai mayar da su makusantansa a fada. Sai matsafa suka tambayi Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, shi ne zai fara jefa sandarsa ko kuma su ne za su fara jefa nasu? Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarce su da su fara jefa sandunansu. To suna jefawa kuwa sai kawai suka sihirce idanun mutane, suka jefa musu tsoro, suka nuna sihiri mai girma.
۞وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۖ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ
Open ayah 7:117Muka kuma yi wahayi ga Musa cewa: “Jefa sandarka.” Sai ga shi nan take tana haɗiye abin da suke ƙagowa.
فَوَقَعَ ٱلۡحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 7:118Sai gaskiya ta tabbata, abin da kuma suka kasance suna aikatawa sai ya lalace.
فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُواْ صَٰغِرِينَ
Open ayah 7:119Sai aka rinjaye su a nan, suka kuma juya a ƙasƙance.
وَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ
Open ayah 7:120Matsafa kuwa suka faɗi suna masu sujjada.
قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 7:121Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai.
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Open ayah 7:122“Ubangijin Musa da Haruna.”
قَالَ فِرۡعَوۡنُ ءَامَنتُم بِهِۦ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّ هَٰذَا لَمَكۡرٞ مَّكَرۡتُمُوهُ فِي ٱلۡمَدِينَةِ لِتُخۡرِجُواْ مِنۡهَآ أَهۡلَهَاۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:123Sai Fir’auna ya ce: “Yanzu kun yi imani da shi tun kafin in yi muku izini? Lalle wannan tabbas wani makirci ne da kuka ƙulla shi a nan cikin garin, don ku fitar da mutanensa daga cikinsa; to da sannu za ku sani.
لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ ثُمَّ لَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 7:124“Lalle zan yanyanke hannayenku da ƙafafuwanku a tarnaƙe, sannan kuma gaba ɗaya zan gicciye ku.”
قَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
Open ayah 7:125Sai suka ce: “Mu kam lalle masu komawa ne ga Ubangijinmu.”
وَمَا تَنقِمُ مِنَّآ إِلَّآ أَنۡ ءَامَنَّا بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا لَمَّا جَآءَتۡنَاۚ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَتَوَفَّنَا مُسۡلِمِينَ
Open ayah 7:126“Kuma ba don komai za ka azabtar da mu ba sai don kawai mun yi imani da ayoyin Ubangijinmu yayin da suka zo mana. Ya Ubangijinmu, Ka zubo mana haƙuri, kuma Ka karɓi rayukanmu muna Musulmi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da hikaito mana abin da ya faru tsakanin Annabi Musa da matsafa bayan ya umarce su da su fara jefa sandunansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wahayi a lokacin ya jefa sandarsa bayan matsafa sun jefa sandunansu da igiyoyinsu, sai ga sandar tasa ta zama ƙaton kumurci tana ta haɗiye sanduna da igiyoyin matsafa waɗanda suka yi wa mutane rufa-ido har suna ganin su kamar wasu macizai ne na gaske. To a daidai lokacin ne gaskiya ta bayyana, tsafe-tsafensu duka suka lalace, aka kayar da su har da Fir’auna shi da fadawansa, suka zama ƙasƙantattu wulaƙantattu. Matsafa kuma da suka ga girman Ƙudurar Ubangiji, gaskiya kuma ta bayyana, sai duk suka faɗi suka yi wa Allah sujjada, suka ce: “Mun ba da gaskiya da Ubangijin talikai, Ubangijin Musa da Haruna”. Daga nan fa sai hankalin Fir’auna ya tashi, ya dinga yi wa matsafa faɗa, yana cewa, yaya za su ba da gaskiya da Musa ba tare da ya yi musu izini ba? Sai ya fara tuhumar matsafan da cewa, da ma sun ƙulla wani makirci ne tare da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a cikin gari kafin su iso wurinsa, don su kori Kibɗawa daga gari su maye gurbinsu da Banu-Isra’ila. Don haka ya tabbatar musu cewa, sai sun ɗanɗana kuɗarsu. Zai yanke hannayen matsafan da ƙafafuwansu a tarnaƙe, watau hannun dama da ƙafar hagu, sannan kuma ya gicciye su gaba ɗaya. To sai waɗannan matsafan da suka yi imani suka ce, lalle su kam zuwa ga Ubangijinsu za su koma, kuma ba wani abu da ya sa Fir’auna yake jin haushinsu sai don kawai sun yi imani da ayoyin Ubangijinsu da suka zo musu ta hannun Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sannan suka roƙi Allah ya ƙara musu haƙuri, kuma ya karɓi ransu suna Musulmi.
وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِ فِرۡعَوۡنَ أَتَذَرُ مُوسَىٰ وَقَوۡمَهُۥ لِيُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَۚ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَنَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡ وَإِنَّا فَوۡقَهُمۡ قَٰهِرُونَ
Open ayah 7:127Sai manyan gari cikin mutanen Fir’auna suka ce: “Yanzu za ka ƙyale Musa da mutanensa, don su yi ɓarna a bayan ƙasa, kuma ya watsar da kai da abubuwan bautarka?” Sai ya ce: “Lalle za mu karkashe ‘ya’yansu maza, mu ƙyale ‘ya’yansu mata da rai, kuma lalle mu masu rinjaye ne a kansu.”
قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱللَّهِ وَٱصۡبِرُوٓاْۖ إِنَّ ٱلۡأَرۡضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 7:128Sai Musa ya ce da mutanensa: “Ku nemi taimakon Allah, kuma ku yi haƙuri; lalle ƙasa mulkin Allah ce, Yana gadar da ita ga wanda Ya ga dama daga cikin bayinsa; kuma kyakkyawan ƙarshe yana tabbata ne ga masu taƙawa.”
قَالُوٓاْ أُوذِينَا مِن قَبۡلِ أَن تَأۡتِيَنَا وَمِنۢ بَعۡدِ مَا جِئۡتَنَاۚ قَالَ عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يُهۡلِكَ عَدُوَّكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرَ كَيۡفَ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 7:129Sai suka ce: “An cutar da mu tun kafin ka zo mana, da kuma bayan ka zo mana.” Sai ya ce: “Ta yiwu Ubangijinku Ya halakar da abokan gabarku, kuma Ya mayar da ku halifofi a bayan ƙasa, sai Ya ga kuma, me za ku aikata?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin abin da ya faru bayan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi nasara a kan matsafan Fir’auna, har sun yi imani da Allah Ubangijin talikai baki ɗaya. Sai manyan masu faɗa a ji daga mutanen Fir’auna suka ce masa, yanzu haka zai ƙyale Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka yi imani da shi daga Banu Isra’ila su ci gaba da ɓarna a bayan ƙasa, su yi watsi da shi da iyayen gijinsa? Sai Fir’auna ya amsa musu da cewa: Zai ɗauki matakin karkashe ‘ya’yansu maza, ya ƙyale matansu, kuma shi tabbas ya fi ƙarfinsu. To da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji wannan barazana ta Fir’auna, sai ya nemi mutanensa da su nemi taimakon Allah, kuma su yi haƙuri, domin ƙasa ta Allah (Mai tsarki da daukaka) ce, shi yake gadar da ita ga wanda ya ga dama daga bayinsa, kuma kyakkyawan ƙarshe yana ga masu kiyaye dokokin Allah. To amma su kuma Banu Isra’ila sai suka ce da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), su fa Fir’auna da mutanensa sun daɗe suna cutar su kafin zuwansa, yanzu ma kuma ga shi bayan zuwansa a matsayin Manzo daga Allah sun ci gaba da cutar da su. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya lallashe su, ya kwantar musu da hankali, ya bayyana musu cewa, yana sa ran cewa Allah zai halaka maƙiyansu, Fir’auna da jama’arsa, su kuma ya sanya su masu maye gurbinsu a bayan ƙasa, don ya ga yadda su kuma kamun ludayinsu zai kasance.
وَلَقَدۡ أَخَذۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ بِٱلسِّنِينَ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ
Open ayah 7:130Kuma lalle haƙiƙa Mun jarrabi iyalin gidan Fir’auna da shekaru na fari da kuma tawayar ‘ya’yan itace, ko sa yi tuntuntuni.
فَإِذَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡحَسَنَةُ قَالُواْ لَنَا هَٰذِهِۦۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةٞ يَطَّيَّرُواْ بِمُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓۗ أَلَآ إِنَّمَا طَٰٓئِرُهُمۡ عِندَ ٱللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:131Amma yayin da daddaɗan abu ya zo musu, sai su ce: “Da ma wannan namu ne.” Idan kuma mummunan abu ya same su, sai su camfa Musa da waɗanda suke tare da shi. Ku saurara, kawai dai mummunan abin da ya same su daga wajen Allah yake, amma yawancinsu ba sa sanin (haka).
وَقَالُواْ مَهۡمَا تَأۡتِنَا بِهِۦ مِنۡ ءَايَةٖ لِّتَسۡحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحۡنُ لَكَ بِمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 7:132Kuma suka ce: “Kowace irin aya ka zo mana da ita, don ka sihirce mu da ita, to fa mu ba za mu yi imani da kai ba.”
فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلۡجَرَادَ وَٱلۡقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَٰتٖ مُّفَصَّلَٰتٖ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ
Open ayah 7:133Sai Muka aika musu da ambaliyar ruwa da fara da ƙwarƙwata da kwaɗi da jini, a matsayin ayoyi daki-daki, sai suka yi girman kai, kuma suka kasance mutane masu babban laifi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, ya jarrabi mutanen Fir’auna da fari da ƙarancin kayan amfanin gona ko hakan zai zame musu wa’azi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su mutanen Fir’auna sun kasance duk sa’adda aka samu yalwa da abinci mai yawa a ƙasar Masar sai su riƙa cewa, wannan nasu ne, wato iyayen gijinsu ne suka yi musu karamci da kyauta domin sun cancanci hakan. Amma idan wata musiba ce ta same su, ta fari ko rashe-rashen lafiya ko rayuka, sai su riƙa camfe Annabi Musa da waɗanda suke tare da shi suna cewa, wai saboda addinin da suka zo da shi ne ya sa waɗannan musibu suke ta sauka, domin wai sun fusata allolinsu. Amma kuma a gaskiya duk wata musiba da za ta same su wani abu ne muƙaddari daga Allah, domin ya zamo uƙuba gare su saboda laifukansu; babu hannun Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a ciki, sai dai yawancinsu ba sa ganewa. Saboda izgili ma cewa suka yi kowace irin aya Annabi Musa zai zo musu da ita don ya raba su da addininsu, to su fa ba za su yi imani da shi ba. To sai ko Allah ya aiko musu da musibu kala-kala, wannan bayan wannan, ya fara da ambaliyar ruwa da ya riƙa cinye musu gidajensu da gonakinsu; ya aiko musu da fari, amfanin gonakinsu duka ya lalace; ya aiko musu da ƙwarƙwata ta riƙa cutar da su, ta hana su sakat; ya aiko musu kwaɗi suka riƙa cika gidajensu da kwanukan abincinsu; ya aiko musu da jini wanda har ruwan shansu sai da ya koma jini. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da waɗannan bala’o’i ne don su zama ayoyi daki-daki masu nuna gaskiyar manzancin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), to amma duk da haka sai suka yi girman kai, suka kangare, suka kasance masu laifi, suka ci gaba da saɓon Allah da kafirce wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيۡهِمُ ٱلرِّجۡزُ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَۖ لَئِن كَشَفۡتَ عَنَّا ٱلرِّجۡزَ لَنُؤۡمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرۡسِلَنَّ مَعَكَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 7:134Kuma yayin da azaba ta sauka a kansu, sai suka ce: “Ya kai Musa, ka roƙa mana Ubangijinka, saboda alƙawarin da Ya yi maka; lalle idan har ka yaye mana wannan azaba, to tabbas za mu yi imani da kai, kuma za mu sakar maka Banu Isra’ila.”
فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُمُ ٱلرِّجۡزَ إِلَىٰٓ أَجَلٍ هُم بَٰلِغُوهُ إِذَا هُمۡ يَنكُثُونَ
Open ayah 7:135To yayin da Muka yaye musu wannan azaba zuwa wani lokacin da za su kai gare shi, sai ga shi suna warware alƙawarin da suka yi.
فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ
Open ayah 7:136Sai Muka azabtar da su, Muka dulmiyar da su a cikin kogi saboda sun ƙaryata ayoyinmu, kuma sun kasance gafalallu game da su.
وَأَوۡرَثۡنَا ٱلۡقَوۡمَ ٱلَّذِينَ كَانُواْ يُسۡتَضۡعَفُونَ مَشَٰرِقَ ٱلۡأَرۡضِ وَمَغَٰرِبَهَا ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَاۖ وَتَمَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ ٱلۡحُسۡنَىٰ عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ بِمَا صَبَرُواْۖ وَدَمَّرۡنَا مَا كَانَ يَصۡنَعُ فِرۡعَوۡنُ وَقَوۡمُهُۥ وَمَا كَانُواْ يَعۡرِشُونَ
Open ayah 7:137Mutanen kuma da ake nuna musu fin ƙarfi a da, Muka gadar musu gabashi da yammacin ƙasar da Muka yi wa albarka; kuma kalmar Ubangijinka kyakkyawa sai ta tabbata a kan Banu Isra’ila saboda haƙurin da suka yi; kuma Muka rushe abin da Fir’auna ya kasance yana yi shi da mutanensa, da abin da suka kasance suna ginawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da mu cewa, lokacin da azabar Allah ta sauka a kan Fir’auna da jama’arsa da dangogin annoba da suka riƙa gani iri-iri, sai suka nemi Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙa musu Allah da abin da Allah ya yi masa wasiyya ya roƙe shi da shi, don ya yaye musu matsalolinsu. Suka kuma yi masa alƙawari har da rantsuwa cewa, idan har ya yaye musu wannan azabar, to lalle za su yi imani da shi, kuma za su sakar masa Banu Isra’ila da Fir’auna yake tsare da su bisa zalunci. To amma lokacin da Allah ya yaye musu wannan azabar, ya kuma jinkirta musu har zuwa lokacin da ya aje domin halakar da su, sai ga shi sun warware alƙawarin da suka yi masa na za su yi imani, kuma za su sako Banu Isra’ila, sai Allah ya nutsar da su cikin kogi suka halaka, saboda sun ƙaryata ayoyinsa, kuma sun kasance gafalallu daga gare su. Kuma mutanen da ake wulaƙantarwa, ana bautar da su a da, wato Banu Isra’ila, sai Allah ya gadar musu da gabashi da yammacin ƙasar Sham wadda Allah ya yi mata albarka, ya cika musu alƙawarin da ya yi musu na halaka maƙiyansu ya ba su iko a bayan ƙasa, saboda haƙurin da suka yi, ya rushe duk wani abu da Fir’auna da mutanensa suka riƙa aikatawa da abin da suka yi ta ginawa na manyan gine-gine da dangogin abubuwan jin daɗi.
وَجَٰوَزۡنَا بِبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱلۡبَحۡرَ فَأَتَوۡاْ عَلَىٰ قَوۡمٖ يَعۡكُفُونَ عَلَىٰٓ أَصۡنَامٖ لَّهُمۡۚ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱجۡعَل لَّنَآ إِلَٰهٗا كَمَا لَهُمۡ ءَالِهَةٞۚ قَالَ إِنَّكُمۡ قَوۡمٞ تَجۡهَلُونَ
Open ayah 7:138Kuma sai Muka tsallakar da Banu Isra’ila kogi, sai suka tarar da waɗansu mutane da suka duƙufa a kan (bautar) gumakansu, suka ce: “Ya kai Musa, ka sa mana wani abin bauta, irin yadda waɗannan suke da abubuwan bauta.” Sai ya ce: “Lalle ku mutane ne da kuke da jahilci.
إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ مُتَبَّرٞ مَّا هُمۡ فِيهِ وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 7:139“Lalle waɗannan abin da suke cikinsa halaka ne, kuma abin da suke aikatawa ɓarna ce.”
قَالَ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِيكُمۡ إِلَٰهٗا وَهُوَ فَضَّلَكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 7:140Ya ce: “Shin yanzu wani wanda ba Allah ba zan nemo muku a matsayin abin bauta, alhali Shi ne Ya fifita ku a kan sauran talikai?”
وَإِذۡ أَنجَيۡنَٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يُقَتِّلُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ
Open ayah 7:141Kuma ku tuna lokacin da Muka tserar da ku daga mutanen Fir’auna, (waɗanda) suke ɗanɗana muku mummunar azaba; suna karkashe ‘ya’yanku maza, kuma suna barin ‘ya’yanku mata da rai, kuma lalle a cikin wannan akwai wata jarraba babba daga Ubangijinku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, bayan ya halaka Fir’auna da jama’arsa, ya tserar da Banu-Isra’ila sun tsallake kogi, sai suka zo wucewa ta gaban wasu mutane mushirikai masu bautar gumaka ba Allah ba, sai suka nemi Annabi Musa su ma ya samar musu wani abin bauta ba Allah ba wanda za su riƙa bauta wa. Lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji wannan ɗanyar magana daga Banu-Isra’ila sai ya amsa musu da cewa, su dai mutane ne da har yanzu suke cikin jahilci, ba su san Allah ba. Waɗannan mutane abin da suke bauta wa ba Allah ba, halaka ce suke cikinta, kuma abin da suke yi ɓarna ne, aikin banza ne, ba zai amfane su da komai ba. An karɓo daga Abu Waƙid Al-Laisi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya bar Hunainu, ya wuce ta gaban wata bishiya wadda ake kira da suna Zatu Anwaɗin, mushirikai sun rataye takubbansu a jikinta wai suna neman albarka a wajenta, sai wasu daga cikin Musulmin da ke tare da shi suka ce: “Ya Manzon Allah, mu ma a samar mana irin wannan bishiyar da za mu riƙa rataye makamanmu a jikinta kamar yadda waɗannan mutane suke yi.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah, wannan ita ce irin maganar da mutanen Annabi Musa suka faɗa masa: ‘Ka sama mana abin bauta mana kamar yadda su ma suke da abin bauta.’ Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, lalle sai kun bi hanyar waɗanda suka gabace ku.” [Ahmad #21897, da Tirmizi #2180]. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi mamakin Bani Isra’ila da har suka fara manta ni’imar da Allah ya yi musu, ta fifita su a kan sauran halittu na zamaninsu, to amma yanzu su ne kuma suke son a kawo musu wani abin bauta daban ba shi ba. Sai ya sake tuna musu kaɗan daga ni’imomin da Allah ya yi musu, watau kuɓutar da su daga hannun mutanen Fir’auna yayin da suke ɗanɗana musu azaba da wulaƙanci, suna kashe musu ‘ya’yansu maza suna barin matan domin su riƙa bautar da su a gidajensu, kuma suna cin mutuncinsu. Wannan wata babbar jarraba ce Allah ya yi wa Banu-Isra’ila a lokacin, bai kamata har su manta da ita ba.
۞وَوَٰعَدۡنَا مُوسَىٰ ثَلَٰثِينَ لَيۡلَةٗ وَأَتۡمَمۡنَٰهَا بِعَشۡرٖ فَتَمَّ مِيقَٰتُ رَبِّهِۦٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَٰرُونَ ٱخۡلُفۡنِي فِي قَوۡمِي وَأَصۡلِحۡ وَلَا تَتَّبِعۡ سَبِيلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 7:142Mun kuma yi wa Musa alƙawarin dare talatin, muka kuma cika su da goma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika darare arba’in cif-cif. Sai Musa ya ce da ɗan’uwansa Haruna: “Ka wakilce ni a cikin mutanena, kuma ka daidaita (tsakaninsu), kada kuma ka bi tafarkin maɓarnata.”
وَلَمَّا جَآءَ مُوسَىٰ لِمِيقَٰتِنَا وَكَلَّمَهُۥ رَبُّهُۥ قَالَ رَبِّ أَرِنِيٓ أَنظُرۡ إِلَيۡكَۚ قَالَ لَن تَرَىٰنِي وَلَٰكِنِ ٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡجَبَلِ فَإِنِ ٱسۡتَقَرَّ مَكَانَهُۥ فَسَوۡفَ تَرَىٰنِيۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُۥ لِلۡجَبَلِ جَعَلَهُۥ دَكّٗا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقٗاۚ فَلَمَّآ أَفَاقَ قَالَ سُبۡحَٰنَكَ تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 7:143Lokacin Kuma da Musa ya zo wajen da muka yi alƙawari da shi, Ubangijinsa kuma Ya yi magana da shi, sai ya ce: “Ya Ubangijina, nuna mini kanka in gan Ka.” Sai ya ce: “Ba za ka iya gani Na ba, amma dubi dutsen nan, idan ya tabbata a bigirensa, to da sannu za ka gan Ni.” To lokacin da Ubangijinsa Ya bayyana (da haskensa) ga dutsen, sai Ya mayar da shi rugu-rugu, sai Musa ya faɗi sumamme. To yayin da ya farfaɗo, sai ya ce: “Tsarki ya tabbata gare Ka, na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon muminai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) alƙawarin ganawa da shi bayan shuɗewar dare talatin yana sauraro, kuma ya cika masa da wa’adin dare goma, wanda ya cika dare arba’in yana bauta wa Allah a cikinsu. Bayan ya gama ne Allah ya gana da shi, ya yi magana da shi, ya kuma ba shi littafin Attaura. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai tafi wannan ganawar ba sai da ya umarci ɗan’uwansa Annabi Haruna da ya zauna madadinsa a cikin Banu-Isra’ila yana kula da su, yana yi musu gyara a inda duk ya ga ya dace, kada ya bi wata hanyar ɓata. To lokacin ganawar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Ubanijinsa ya yi magana da shi ne kai-tsaye ba tare da wani a tsakaninsu ba, sai ya nemi alfarmar Ubangijinsa da ya ba shi damar ya gan shi a fili, sai ya faɗa masa cewa, ba zai yiwu ya gan shi a duniya ba, amma ya umarce shi da ya kalli wani dutse, idan ya tabbata a wurinsa, to zai iya ganin Allah. Yayin da Allah ya bayyana ga dutsen, sai ya dare ya yi rugu-rugu, Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuwa ya faɗi sumamme. To bayan ya farfaɗo ne sai ya tsarkake Allah, ya tuba zuwa gare shi, ya ce shi ne farkon muminai. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya tsaya cikinmu ya faɗa mana maganganu biyar. Ya ce: “Lalle Allah mai girma da buwaya ba ya barci, kuma bai dace ya yi barci ba; yana yin ƙasa da sikeli, kuma yana yin sama da shi; ana kai masa aikin dare kafin aikin rana, da aikin rana kafin na dare; shamakinsa haske ne – a wata ruwayar wuta ce – da a ce zai yaye shi, to da hasken fuskarsa ya ƙona ɗaukacin halittarsa da ganinsa yake zuwa gare ta.” [Muslim #179]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Mutane za su suma a ranar alƙiyama; ni ne zan fara farfaɗowa, sai kawai in ga Musa tsaye yana riƙe da ƙafa ɗaya daga cikin ƙafafuwan Al’arshi, to ban sani ba; shin ya riga ni farfaɗowa ne, ko kuma an saka masa ne a madadin suman da ya yi a wurin dutsen Ɗuri.” [Bukhari #3398, da Muslim #2374].
قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ إِنِّي ٱصۡطَفَيۡتُكَ عَلَى ٱلنَّاسِ بِرِسَٰلَٰتِي وَبِكَلَٰمِي فَخُذۡ مَآ ءَاتَيۡتُكَ وَكُن مِّنَ ٱلشَّٰكِرِينَ
Open ayah 7:144Ya ce: “Ya kai Musa, Lalle Ni na zaɓe ka a kan sauran mutane da saƙona da kuma zancena, don haka ka riƙe abin da na ba ka, kuma ka kasance cikin masu godiya.”
وَكَتَبۡنَا لَهُۥ فِي ٱلۡأَلۡوَاحِ مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡعِظَةٗ وَتَفۡصِيلٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ فَخُذۡهَا بِقُوَّةٖ وَأۡمُرۡ قَوۡمَكَ يَأۡخُذُواْ بِأَحۡسَنِهَاۚ سَأُوْرِيكُمۡ دَارَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Open ayah 7:145Mun kuma rubuta masa komai a cikin allunan (Attaura) don wa’azi da bayani filla-filla na kowane irin abu, don haka ka riƙe su da kyau, kuma ka umarci mutanenka su yi riƙo da mafi kyawun abin da yake cikinsu. Da sannu zan nuna muku gidajen fasiƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, ya zaɓe shi ya fifita shi a kan mutanen zamaninsa yayin da ya aiko shi da manzanci zuwa ga Banu-Isra’ila, kuma ya yi magana da shi ba tare da wani a tsakaninsu ba, ya kuma umarce shi ya riƙe littafin Attaura da ƙarfi, ya yi aiki da abin da yake cikinsa na shari’a, kuma ya zamanto cikin masu godiya ga Allah. Ya kuma sanar da shi cewa, a cikin allunan Attaura ya rubuta masa duk wani abu da zai buƙata na addini da rayuwa don ya zamanto wa’azi gare shi da al’ummarsa Banu-Isra’ila, ya kuma zamo bayani filla-filla ga duk wani abu mai buƙatar ƙarin bayani. Ya umarce shi da ya riƙe abin da aka rubuta masa da ƙarfi, kuma ya umarci mutanensa su yi riƙo da mafi kyan abin da yake cikin Attaura. Allah kuma ya faɗa musu cewa, zai nuna musu gidan fasiƙai. Wasu malamai sun ce ana nufin wutar Jahannama, wato a lahira ke nan. Wasu kuma sun ce ana nufin ƙasar Baitil Maƙadisi, saboda mazauna cikinta a wannan lokaci mushirikai ne, masu bautar wanin Allah, don haka alƙawari ne Allah ya yi musu cewa, zai nuna musu wannan ƙasar. Yayin da wasu malamai suna ganin wannan gidan ana nufin ƙasar Masar da Baitil Maƙadisi ne.
سَأَصۡرِفُ عَنۡ ءَايَٰتِيَ ٱلَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلرُّشۡدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلۡغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗاۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ
Open ayah 7:146Zan kautar da waɗanda suke yin girman kai a bayan ƙasa ba tare da haƙƙi ba daga (fahimtar) ayoyina; idan kuma za su ga kowace irin aya ba za su yi imani da ita ba, idan kuma da za su ga hanyar shiriya ba za su riƙe ta hanyar bi ba, (amma) idan kuwa za su ga hanyar ɓata, to za su riƙe ta hanyar bi. Wannan kuwa saboda sun ƙaryata ayoyinmu, kuma sun kasance gafalallu ga barin su.
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَلِقَآءِ ٱلۡأٓخِرَةِ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡۚ هَلۡ يُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 7:147Waɗanda kuma suka ƙaryata ayoyinmu da haɗuwa a ranar alƙiyama, ayyukansu sun rushe. Shin kuwa za a yi musu wani sakamako ne in ba abin da suka kasance suna aikatawa ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗin cewa, zai nesanta duk waɗanda suke girman kai a bayan ƙasa ba da wani dalili ba daga fahimtar ayoyinsa; idan kuma suka ga duk wata hujja mai nuna Allah ne kaɗai ya cancanta a bauta masa, ba za su yi imani da ita ba. Hakanan idan suka ga hanyar shiriya da gyaruwa ba za su yarda su bi ta ba, amma idan suka ga hanyar ɓata da lalacewa, to za su bi ta su riƙe ta. Hakan ya faru da su ne saboda sun ƙaryata ayoyin Allah, kuma sun kasance gafalallu daga gare su. Sannan ya bayyana cewa, waɗanda suka ƙaryata ayoyinsa, suka ƙi ba da gaskiya da ranar lahira da haɗuwa da shi a lahira, to duk ayyukansu sun ɓaci, kuma ba za a saka musu da komai ba sai da munanan ayyukan da suka yi a nan duniya.
وَٱتَّخَذَ قَوۡمُ مُوسَىٰ مِنۢ بَعۡدِهِۦ مِنۡ حُلِيِّهِمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٌۚ أَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّهُۥ لَا يُكَلِّمُهُمۡ وَلَا يَهۡدِيهِمۡ سَبِيلًاۘ ٱتَّخَذُوهُ وَكَانُواْ ظَٰلِمِينَ
Open ayah 7:148Mutanen Musa kuma a bayansa sun ƙera wani ɗan maraƙi daga kayan adonsu mai surar jiki yana wata ƙara (don su bauta masa). Shin ba su ga cewa ba ya yi musu Magana ba, kuma ba ya iya shiryar da su wani tafarki? Sun riƙe shi (a matsayin abin bauta), kuma sun tabbata azzalumai.
وَلَمَّا سُقِطَ فِيٓ أَيۡدِيهِمۡ وَرَأَوۡاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ ضَلُّواْ قَالُواْ لَئِن لَّمۡ يَرۡحَمۡنَا رَبُّنَا وَيَغۡفِرۡ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Open ayah 7:149Kuma lokacin da suka yi nadama, suka gane cewa sun ɓata, sai suka ce: “Matuƙar Ubangijinmu bai ji ƙan mu ba, kuma bai gafarta mana ba, lalle za mu kasance cikin hasararru.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana abin da ya faru ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya tafi domin ganawa da Allah kamar yadda ya yi masa alƙawari, ya bar Banu-Isra’ila tare da ɗan’uwansa Annabi Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai mutanensa suka ƙera wani ɗan maraƙi daga kayan adonsu na gwalagwalai, wanda suka samu daga mutanen Fir’auna. Wannan ɗan maraƙi jiki ne ba mai rai ba, amma yana fitar da wani sauti kamar yana kukan maraƙi, sai suka riƙa bauta masa ba Allah ba. To amma su ba sa ganin ba ya iya yi musu magana, kuma ba ya nuna musu wata shiriya ko wani aikin alheri? Sun riƙe shi abin bauta, suka kuwa zamo azzalumai da suka cuci kawunansu suna sane. To bayan sun yi nadama mai tsanani a kan bautar ɗan maraƙi da suka yi, suka kuma gane cewa sun ɓata, sun kauce hanyar da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bar su a kanta, to sai suka roƙi Allah gafararsa da rahamarsa, suna masu cewa, idan har Allah bai yi musu rahama ya kuma gafarta musu zunubbansu ba, to lalle za su tabbata cikin hasararru duniya da lahira.
وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ غَضۡبَٰنَ أَسِفٗا قَالَ بِئۡسَمَا خَلَفۡتُمُونِي مِنۢ بَعۡدِيٓۖ أَعَجِلۡتُمۡ أَمۡرَ رَبِّكُمۡۖ وَأَلۡقَى ٱلۡأَلۡوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأۡسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُۥٓ إِلَيۡهِۚ قَالَ ٱبۡنَ أُمَّ إِنَّ ٱلۡقَوۡمَ ٱسۡتَضۡعَفُونِي وَكَادُواْ يَقۡتُلُونَنِي فَلَا تُشۡمِتۡ بِيَ ٱلۡأَعۡدَآءَ وَلَا تَجۡعَلۡنِي مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 7:150Lokacin kuma da Musa ya dawo wajen mutanensa a fusace yana mai damuwa, sai ya ce: “Tir da abin da kuka aikata bayana. Yanzu kwa gaggauto al’amarin Ubangijinku?” Sai ya jefar da allunan, ya kama kan ɗan’uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Sai (Haruna) ya ce: “Ya kai ɗan’ummata, mutanen nan haƙiƙa sun raina ni, har ma sun kusa kashe ni, don haka kar ka sa maƙiya su yi min dariya, kuma kada ka sa ni cikin mutane azzalumai.”
قَالَ رَبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَلِأَخِي وَأَدۡخِلۡنَا فِي رَحۡمَتِكَۖ وَأَنتَ أَرۡحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ
Open ayah 7:151Sai ya ce: “Ya Ubangijina, Ka gafarta mini ni da ɗan’uwana, kuma Ka shigar da mu cikin rahamarka; kuma Kai ne Fiyayyen masu jin ƙai.”
إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ سَيَنَالُهُمۡ غَضَبٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَذِلَّةٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُفۡتَرِينَ
Open ayah 7:152Lalle waɗannan da suka riƙi ɗan maraƙi (abin bauta) fushin Ubangijinsu zai same su da ƙasƙanci a cikin rayuwar duniya. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu ƙage.
وَٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِهَا وَءَامَنُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 7:153Waɗanda kuma suka aikata munanan ayyuka, sannan suka tuba daga baya, kuma suka yi imani, lalle Ubangijinka bayansa (tuban), tabbas Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba mu labarin lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya dawo daga wajen ganawa da Ubangijinsa, bayan ya sanar da shi cewa, Assamiri ya ɓatar da mutanensa, domin ya ƙera musu ɗan maraƙi sun shiga bautar sa ka’in-da-na’in. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya dawo a fusace sosai, yana zargin mutanensa cewa, Allah wadaran abin da suka tsiri aikatawa a bayansa, yana cewa; yanzu sa gaggauto komowarsa gare su daga ganawa da Allah kafin cikar lokacin da Allah ya sanya su gana a cikinta? Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya jefar da allunan Attaura da suke hannunsa cikin tsananin fushi da ɓacin rai, ya damƙi gashin kan ɗan’uwansa Haruna da gemunsa yana ja. Sai Haruna ya ce masa: “Ya ɗan’ummata, mutanen nan fa sun riga sun raina ni, har ma sun kusa kashe ni, don haka kada ka sa maƙiyana su riƙa yi mini dariya saboda sun ga kana duka na, kana tozarta ni, kuma kada ka sanya ni cikin waɗannan mutanen azzalumai.” To daga nan ne sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) jikinsa ya yi sanyi, ya saki ɗan’uwansa, yana roƙon Allah ya gafarta musu shi da ɗan’uwansa, kuma ya shigar da su cikin rahamarsa, domin shi ne Fiyayyen masu jin ƙai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Gani ya kori ji. Allah ya sanar da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) abin da mutanensa suka yi na bautar ɗan maraƙi, amma bai jefar da alluna ba, sai da ya ga abin da suka aikata da idonsa ne sai nan take ya jefar da su.” [Ahmad #2447]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, waɗanda suka bauta wa ɗan maraƙi da sannu fushinsa zai auka musu da wulaƙanci a rayuwarsu ta duniya, kuma da irin haka zai saka wa duk masu ƙage a addini. Waɗanda kuma suka yi munanan ayyuka sannan suka tuba suka koma ga Allah, suka yi nadamar abin da suka aikata, suka yi imani da Allah da Manzonsa, to bayan wannan Allah zai gafarta musu, ya ji ƙan su, domin shi mai gafara ne, mai jin ƙai. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah mai girma da buwaya ya ce: “Ya kai ɗan’adam, lalle kai duk sa’adda ka roƙe ni, ko ka yi fata daga gare ni, to zan gafarta maka tare da abin da ya kasance na halayyarka, ban damu ba. Ya kai ɗan’adam, da zunubbanka za su taɓo girgije a sama, sannan ka nemi gafara, to da na gafarta maka, kuma ban damu ba. Ya kai ɗan’adam, da za ka zo mini da laifuffuka cikin ƙasa, sannan ka sadu da ni ba ka haɗa komai da ni a wajen bauta ba, da kuwa na zo maka da gafara cikin ƙasa.” [Tirmizi #3540].
وَلَمَّا سَكَتَ عَن مُّوسَى ٱلۡغَضَبُ أَخَذَ ٱلۡأَلۡوَاحَۖ وَفِي نُسۡخَتِهَا هُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلَّذِينَ هُمۡ لِرَبِّهِمۡ يَرۡهَبُونَ
Open ayah 7:154Yayin kuma da Musa ya huce, sai ya ɗauki allunan nan (na Attaura); kuma abin da aka rubuta a cikinsu shiriya ne da rahama ga waɗanda suke tsoron Ubangijinsu.
وَٱخۡتَارَ مُوسَىٰ قَوۡمَهُۥ سَبۡعِينَ رَجُلٗا لِّمِيقَٰتِنَاۖ فَلَمَّآ أَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ قَالَ رَبِّ لَوۡ شِئۡتَ أَهۡلَكۡتَهُم مِّن قَبۡلُ وَإِيَّٰيَۖ أَتُهۡلِكُنَا بِمَا فَعَلَ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَّآۖ إِنۡ هِيَ إِلَّا فِتۡنَتُكَ تُضِلُّ بِهَا مَن تَشَآءُ وَتَهۡدِي مَن تَشَآءُۖ أَنتَ وَلِيُّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَاۖ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡغَٰفِرِينَ
Open ayah 7:155Musa kuma ya zaɓi mutanensa, maza (na musamman) su saba’in don alƙawarinmu; to yayin da wata tsawa ta kama su, sai ya ce: “Ya Ubangijina, idan da Ka ga dama da tun tuni Ka hallakar da su har da ni kaina. Yanzu Ka halaka mu saboda abin da wasu wawaye daga cikinmu suka aikata? Lalle wannan ba komai ba ne face jarrabawa daga gare Ka, Kana ɓatar da wanda Ka ga dama; Kana kuma shiryar da wanda Ka ga dama; Kai ne Majiɓincin lamarinmu, don haka Ka gafarta mana, kuma Ka ji ƙan mu, kuma Kai ne Fiyayyen masu gafara.
۞وَٱكۡتُبۡ لَنَا فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِنَّا هُدۡنَآ إِلَيۡكَۚ قَالَ عَذَابِيٓ أُصِيبُ بِهِۦ مَنۡ أَشَآءُۖ وَرَحۡمَتِي وَسِعَتۡ كُلَّ شَيۡءٖۚ فَسَأَكۡتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِنَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 7:156“Kuma Ka rubuta mana kyakkyawan abu a cikin wannan duniyar, haka ma a lahira, lalle mu mun tuba zuwa gare Ka.” (Allah) Ya ce: “Ina saukar da azabata a kan wanda Na ga dama; rahamata kuwa ta yalwaci komai. Don haka da sannu zan rubuta ta ga waɗanda suke kiyaye dokokin Allah, kuma suke bayar da zakka da kuma waɗanda suke yin imani da ayoyinmu.
ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِيَّ ٱلۡأُمِّيَّ ٱلَّذِي يَجِدُونَهُۥ مَكۡتُوبًا عِندَهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ يَأۡمُرُهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَىٰهُمۡ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡخَبَٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنۡهُمۡ إِصۡرَهُمۡ وَٱلۡأَغۡلَٰلَ ٱلَّتِي كَانَتۡ عَلَيۡهِمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُواْ ٱلنُّورَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Open ayah 7:157“(Su ne) waɗanda suke bin Manzo Annabi Ummiyyi, wanda suke samun sa a rubuce a wurinsu a cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da kyakkyawan abu, kuma yana hana su mummuna, kuma yana halatta musu daɗaɗan abubuwa, yana kuma haramta musu ƙazantattu, kuma yana sauke musu nauyaye-nauyayensu da ƙuƙumce-ƙuƙumcen da suka kasance a kansu. Don haka waɗanda suka yi imani da shi, kuma suka ƙarfafe shi, suka kuma taimake shi, suka bi hasken da aka saukar tare da shi, waɗannan su ne masu rabauta.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bayan da ya huce daga fushin da ya yi saboda bautar ɗan maraƙi da mutanensa suka yi, sai ya ɗauki allunan littafin Attaura waɗanda ya jefar, waɗanda kuma a cikinsu akwai shiriya daga ɓata da rahama ga masu jin tsoron Ubangijinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake yin wani alƙawarin haɗuwa da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), amma a wannan karon ya umarce shi da ya zaɓi mutum saba’in daga Banu Isra’ila ya je ganawar da su. Malamai sun yi saɓani a kan dalilin wannan tafiya da su, amma zance mafi karɓuwa shi ne don su gabatar da uzurinsu game da bautar ɗan maraƙi da suka yi, su nemi gafarar Allah, a kansu da kuma ‘yan’uwansu da ba a zo da su ba. Wasu malaman kuma sun ce ya je da su ne karɓar Littafin Attaura, wasu kuma sun ce ya tafi da sun ne domin su yi addu’a, wasu kuma cikinsu cewa suka yi, saboda an samu wasu daga cikin Banu-Isra’ila da suka nuna ba su yarda cewa, Allah ya yi magana da Annabi Musa ba, idan har haka gaskiya ne, to su ma lalle ya tafi da su don su ji maganar Allah da kunnuwansu, sannan su yarda da shi su daina zargin sa. Sheikh Asshanƙiɗi ya ce: “Akwai maganganu da yawa irin waɗannan, amma ba su da wani dalili.” [Al-‘Azbun Namir , Juzu’i na 4, Shafi na 193]. To bayan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da jama’arsa sun isa wajen dutsen Ɗuri Sina sai wata girgiza mai tsanani ta kama su. Masana a nan ma sun yi maganganu daban-daban game da dalilin wannan girgiza; wasu suka ce saboda sun ƙi su daina bautar ɗan maraƙi ne, wasu kuma suka ce saboda sun tuhumi Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kisan ɗan’uwansa Annabi Haruna, wasu kuma cewa suka yi saboda sun wuce gona da iri wajen addu’a, yayin da wasu malaman cewa suka yi saboda sun ji maganar Allah amma sai suka ce wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) su ba su yarda ba har sai sun ga Allah da idanuwansu a fili, kamar yadda ya zo a Suratul Baƙara, aya ta 55-56. [Ibnul Jauzi, Zadul Masir , Juzu’i na 2, Shafi na 158-159]. Sheikh Asshanƙiɗi ya kawo waɗannan maganganu, amma daga ƙarshe ya ce: “Duk waɗannan maganganun malaman tafsiri ne, akwai ma wasu ban da waɗannan, babu wani dalili mai yanke shakka a kansu. Allah Ta’ala ne mafi sani.” [Al-Azbun Namir , Juzu’i na 4, Shafi na 195-196]. Da girgiza ta kama zaɓaɓɓun mutanen nan su saba’in, sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙi Ubangijinsa cewa: “Ya Ubangijina, da ka ga dama da sai ka halakar da su kafin wannan lokaci, ni ma ka karɓi raina tare da su kuma a gaban sauran ‘yan’uwansu don kada su tuhume ni da cewa ni ne na kashe musu ‘yan’uwa. Ya Allah, yanzu ka halaka mu saboda abin da wasu wawaye daga cikinmu suka aikata na bautar ɗan maraƙi? Bautar ɗan maraƙi da wawaye daga cikinmu suka yi ba komai ne ba sai jarraba daga gare ka; kana ɓatar da wanda ka ga dama da ita, ka shiryar da wanda ka ga dama. Kai ne mai taimakon mu, mai jiɓintar al’amuranmu, don haka ka gafarta mana, ka ji ƙan mu, kai ne Fiyayyen masu gafara, ka rubuta mana abu mai kyau a nan duniya, hakanan ma a lahira, haƙiƙa mu mun tuba zuwa gare ka.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa, azabarsa a nan duniya yana saukar da ita ga wanda ya ga dama, rahamarsa a duniya kuma ta yalwaci duk halittarsa, don haka da sannu zai tabbatar da ita ga waɗanda suke kiyaye dokokinsa, suke kuma fidda zakka, suka yi imani da ayoyinsa, suke bin Annabi Muhammadu (ﷺ) sau-da-ƙafa. Annabin da ba ya karatu da rubutu, wanda suke ganin siffofinsa a cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da kyakkyawan aiki, yana hana su mummuna, yana halatta musu daɗaɗan abubuwa, yana haramta musu munana, kuma yana sauke musu nauyaye-nauyayen abubuwa masu wuya da aka wajabta musu aiki da su a littafin Attaura, da abubuwan da aka tsananta musu haramcinsu masu kama da ƙuƙumi a wuyayensu. Don haka waɗanda suka yi imani da shi, suka girmama shi, suka taimake shi, suka bi Alƙur’anin da Allah ya saukar masa, to waɗannan su ne masu samun babban rabo a duniya da lahira. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru ya ce: Wallahi an siffanta Annabi Muhammadu (ﷺ) a Attaura da wasu siffofinsa da suka zo a Alƙur’ani, an kirawo shi: “Ya kai wannan Annabi, lalle mu mun aiko ka don ka zama mai shaida, mai albishir, kuma mai gargaɗi, ka zamo kariya ga Larabawa ummiyyai. Kai bawana ne kuma manzona, na raɗa maka suna Al-Mutawakkilu (wato mai dogaro ga Allah), shi ba mai kakkausan hali ba ne, ba mai ƙeƙasasshiyar zuciya ba, ba mai hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mugunta da mugunta, sai dai ya yi afuwa, ya yi gafara. Allah ba zai karɓi ransa ba har sai ya miƙar da karkataccen addini da shi, wato su ce: Babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Ya kuma buɗe makafin idanuwa da kuramen kunnuwa da rufaffun zukata da wannan Kalma ta Shahada.” [Bukhari #4838].
قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Open ayah 7:158Ka ce: “Ya ku mutane, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba ɗaya, wanda Yake da mallakar sammai da ƙasa, babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Yake rayawa, kuma Shi Yake kashewa; don haka ku yi imani da Allah da Manzonsa Annabi Ummiyyi, wanda yake yin imani da Allah da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku zama shiryayyu.” A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa mutane gaba ɗaya cewa, shi Manzon Allah ne zuwa gare su baki ɗaya. Kuma Allah wanda ya aiko shi shi ne mamallakin sammai da ƙasa da abin da yake cikinsu; babu abin bauta wa da gaskiya sai shi, yana rayawa yana kashewa, don haka su yi imani da Allah da Manzonsa Muhammadu (ﷺ) wanda shi ne Annabi Ummiyyi, wato ba ya karatu ba ya rubutu, shi ne wanda yake yin imani da Allah da kalmominsa, kuma lalle su bi shi ko sa samu shiriya. An karɓo daga Jabiru ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “An ba ni abubuwa biyar waɗanda ba a ba wa wani annabi su ba gabanina: An taimake ni da jefa tsoro a zukatan maƙiyana tun daga tazarar tafiyar wata ɗaya; kuma an sanya mini bayan ƙasa ya zama wurin salla da tsarki, kowane mutum a cikin al’ummata da salla za ta riske shi a ko’ina ne, to ya sallace ta; an halatta mini cin ganima; kowane annabi ya kasance ana aiko shi ne zuwa ga mutanensa kaɗai, to amma ni an aiko ni ne zuwa ga mutane gaba ɗaya; kuma an ba ni ceto ranar alƙiyama.” [Bukhari #438, da Muslim #521]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na rantse da wanda ran Muhammadu yake a hannunsa, ba wani daga cikin wannan al’umma da zai samu labarina, Bayahude ne ko Banasare, sannan har ya mutu bai yi imani da abin da aka aiko ni da shi ba, sai ya zamo cikin ‘yan wuta.” [Muslim #153].
وَمِن قَوۡمِ مُوسَىٰٓ أُمَّةٞ يَهۡدُونَ بِٱلۡحَقِّ وَبِهِۦ يَعۡدِلُونَ
Open ayah 7:159Kuma daga cikin mutanen Musa akwai wata jama’a waɗanda suke shiryarwa da gaskiya, da kuma ita ne suke yin hukunci na adalci.
وَقَطَّعۡنَٰهُمُ ٱثۡنَتَيۡ عَشۡرَةَ أَسۡبَاطًا أُمَمٗاۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ إِذِ ٱسۡتَسۡقَىٰهُ قَوۡمُهُۥٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡحَجَرَۖ فَٱنۢبَجَسَتۡ مِنۡهُ ٱثۡنَتَا عَشۡرَةَ عَيۡنٗاۖ قَدۡ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٖ مَّشۡرَبَهُمۡۚ وَظَلَّلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلۡغَمَٰمَ وَأَنزَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰۖ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 7:160Mun kuma karkasa su ƙabilu goma sha biyu daban-daban, sai Muka kuma yi wahayi ga Musa yayin da mutanensa suka nemi ya shayar da su ruwa cewa: “Ka doki dutse da sandarka,” sai idanun ruwa goma sha biyu suka ɓuɓɓugo daga jikinsa. Haƙiƙa kowace ƙabila ta san mashayarta. Muka kuma yi musu inuwa da girgije, kuma Muka saukar musu da darɓa da tsuntsayen salwa; (muka ce:) “Ku ci daga daddaɗan abin da Muka arzurta ku da shi.” Kuma ba su zalunce Mu ba, sai dai kansu suka kasance suna zalunta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa daga cikin mutanen Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) akwai na kirki waɗanda suke shiryuwa da gaskiyar da Allah ya aiko shi da ita, kuma suna yin hukunci a tsakaninsu da ita kuma su yi adalci, don haka ba su taru sun zama ɗaya ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin yadda ya karkasa Banu-Isra’ila gidaje har goma sha biyu, kowane gida a matsayin ƙabila mai zaman kanta, domin hakan zai taimaka wajen gudanar da harkokin shugabanci a cikin kowace ƙabila. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wahayi lokacin da mutanensa suka neme shi ya yi musu roƙon ruwa a daidai lokacin da suke cikin ɗimuwarsu a saharar Sina’a. Allah ya umarce shi da ya doki wani dutse da sandarsa, sai ya yi hakan, nan take kuma idanuwan ruwa goma sha biyu suka ɓuɓɓugo, daga nan kowace ƙabila ta gane idon ruwan da yake shi ne mashayarta, wanda su kaɗai za su yi amfani da shi wajen shan ruwa da wanka da wanki. Bayan wannan ni’imar kuma, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Banu Isra’ila wata ni’imar ta biyu, watau ya yi musu inuwa da girgije don ba su kariya daga tsananin zafin ranar sahara. Bugu da ƙari kuma ya saukar musu da darɓa da soyayyun tsuntsayen salwa, ya umarce su da su ci daddaɗan abin da Allah ya arzuta su da shi. To amma maimakon su gode wa Allah, sai suka saɓa wa umarninsa, to sai dai ba Allah suka zalunta ba da wannan ɗanyen aiki nasu, domin saɓon masu saɓo ba ya cutar da Allah da komai; kawunansu kaɗai suka zalunta don sun yi hasarar rabonsu na duniya da na lahira.
وَإِذۡ قِيلَ لَهُمُ ٱسۡكُنُواْ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةَ وَكُلُواْ مِنۡهَا حَيۡثُ شِئۡتُمۡ وَقُولُواْ حِطَّةٞ وَٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا نَّغۡفِرۡ لَكُمۡ خَطِيٓـَٰٔتِكُمۡۚ سَنَزِيدُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 7:161Kuma ka tuna lokacin da aka ce musu: “Ku zauna a wannan alƙarya, kuma ku ci daga gare ta a duk inda kuka ga dama, ku kuma ce: Hiɗɗa (wato Allah Ka share mana laifukanmu), ku kuma shiga ta ƙofar alƙaryar kuna masu sujjada, za Mu gafarta muku zunubanku, kuma za Mu ƙara wa masu kyautatawa.”
فَبَدَّلَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡ قَوۡلًا غَيۡرَ ٱلَّذِي قِيلَ لَهُمۡ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِجۡزٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُواْ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 7:162Sai waɗanda suka yi zalunci a cikinsu suka canja magana daban da wadda aka faɗa musu, sai Muka aiko musu da wata azaba daga sama, saboda abin da suka kasance suna yi na zalunci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayani ne game da umarnin da ya ba wa Banu-Isra’ila na shiga garin Baitil Maƙadis bayan sun fito daga Masar, ya umarce su da su ci daga ‘ya’yan itatuwan wannan gari da tsirransa a duk inda suke so, ya kuma umarce su da su nemi gafarar Allah lokacin da suke shiga garin, kuma su shiga a sunkuye suna masu ƙasƙantar da kansu ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Ya yi musu alƙawarin zai gafarta musu zunubansu idan har sun aikata hakan, sannan wanda ya kyautata daga cikinsu, zai ƙara masa ladansa. To amma saboda zaluncin Banu-Isra’ila ga kawunansu sai suka canza wannan umarni na Allah; maimakon su nemi gafarar Allah, sai suka riƙa cewa: “Ƙwaya a cikin gashi.” sannan suka shiga garin suna jan gindi. Sakamakon haka sai Allah ya saukar musu da azaba daga sama saboda zaluntar kansu da suka riƙa yi ta hanyar aikata saɓon Allah.
وَسۡـَٔلۡهُمۡ عَنِ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَتۡ حَاضِرَةَ ٱلۡبَحۡرِ إِذۡ يَعۡدُونَ فِي ٱلسَّبۡتِ إِذۡ تَأۡتِيهِمۡ حِيتَانُهُمۡ يَوۡمَ سَبۡتِهِمۡ شُرَّعٗا وَيَوۡمَ لَا يَسۡبِتُونَ لَا تَأۡتِيهِمۡۚ كَذَٰلِكَ نَبۡلُوهُم بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ
Open ayah 7:163Kuma ka tambaye su game da (mutanen) alƙaryar nan wadda take dab da gaɓar teku, yayin da suke ƙetare iyaka a ranar Asabar, yayin da kifayensu suke zuwa a ranar Asabar baja-baja, amma ranar da ba Asabar ba kuwa ba sa zuwa. Kamar haka ne muka jarrabe su saboda abin da suka kasance suna yi na fasiƙanci.
وَإِذۡ قَالَتۡ أُمَّةٞ مِّنۡهُمۡ لِمَ تَعِظُونَ قَوۡمًا ٱللَّهُ مُهۡلِكُهُمۡ أَوۡ مُعَذِّبُهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗاۖ قَالُواْ مَعۡذِرَةً إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Open ayah 7:164Kuma ka tuna lokacin da wata jama’a cikinsu suka ce: “Don me za ku riƙa wa’azi ga waɗansu mutanen da idan Allah Ya ga dama sai Ya hallakar da su ko Ya yi musu azaba mai tsanani?” Sai suka ce: “Don yanke hanzari ne a wurin Ubangijinku ko watakila kuma sa kiyaye dokokin Allah.”
فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦٓ أَنجَيۡنَا ٱلَّذِينَ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلسُّوٓءِ وَأَخَذۡنَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ بِعَذَابِۭ بَـِٔيسِۭ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ
Open ayah 7:165To yayin da suka yi watsi da abin da aka yi musu wa’azi da shi, sai Muka tserar da waɗanda suke hana mummunan aiki, Muka kuma kama waɗanda suka yi zalunci, da wata mummunar azaba, saboda abin da suka riƙa yi na fasiƙanci.
فَلَمَّا عَتَوۡاْ عَن مَّا نُهُواْ عَنۡهُ قُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ
Open ayah 7:166To yayin da suka yi tsaurin kai a kan abin da aka hana su, sai Muka ce da su: “Ku zama birrai, ƙasƙantattu.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin wata jarabawa da ya yi wa Banu-Isra’ila lokacin da ya haramta musu duk wani aiki a ranar Assabar wadda suka zaɓa su riƙa yin bauta a cikinta maimakon ranar Juma’a da Allah ya zaɓa musu da farko. Wannan ƙissa ce daga cikin ƙissoshin Banu-Isra’ila, na wata alƙarya wadda take a gaɓar kogi, mutanenta sun shahara da fasiƙanci da rashin ɗa’a. Sana’arsu ita ce kamun kifi, sai Allah ya yi nufin ya jarrabe su don ganin ko za su kiyaye alfarmar ranar Assabar wadda aka haramta musu yin kowane irin aiki na duniya a cikinta ko ba za su kiyaye ba? Sai Allah cikin hikimarsa ya ƙaddara kifayen wannan ruwa na kusa da su ba sa fitowa da yawa sai ranar Assabar; sauran ranakun kuwa sai a ga babu su gaba ɗaya. Mutanen wannan alƙarya suka kasa haƙuri su bi dokar barin aikin ranar Assabar domin suna ganin kamun kifi a wannan rana zai samar musu da riba mai tarin yawa, sai yawancinsu suka yi wa wannan doka tawaye, suka riƙa baza komarsu ranar Assabar suna kamun kifaye. Ganin haka sai malaman kirki daga cikinsu suka shiga yi musu wa’azi suna hana su wannan ɗanyen aikin, to amma sai suka bijire, suka ƙi saurarensu, suka ma ƙara dagewa wajen saɓa wa wannan doka. Wasu masu yin wa’azi da suka kula wa’azinsu ba ya shiga kunnuwan waɗannan mutane sai suka yanke shawarar su daina yin wa’azin. Amma wasu daga cikinsu sun ci gaba da yi musu wa’azi domin suna sa ran za su saurare su wata rana su karɓi nasiharsu su daina. Sai ɓangarorin biyu na mutanen kirki suka tattauna game da ci gaba da yin wa’azi ga kangararrun mutane, sai waɗanda suka daina yin wa’azin suka faɗa wa masu ci gaba da yin wa’azi cewa, me ya sa za su ci gaba da yin wa’azi ga mutanen da babu alamar shiryuwa tare da su, babu abin da ya rage musu sai Allah ya halaka su, ko ya yi musu azaba mai tsanani? Masu son ci gaba da yin wa’azi kuma suka amsa da cewa, suna yin wa’azin ne don yanke hanzari a gaban Allah, kuma su tabbatar sun yi iya ƙoƙarinsu wajen jawo hankulansu ko wataƙila za a samu masu haƙura su daina abin da suke yi na saɓon Allah. To lokacin da waɗannan mutane masu taurin kai suka ci gaba da kangarewarsu suna kamun kifi ranar Assabar, sai Allah ya saukar musu da azabarsa, ya shafe halittarsu ta mutane, ya mayar da su birrai ƙasƙantattu wulaƙantattu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tserar da waɗanda suka ci gaba da yi musu wa’azi daga wannan mummunan ƙarshen.
وَإِذۡ تَأَذَّنَ رَبُّكَ لَيَبۡعَثَنَّ عَلَيۡهِمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَن يَسُومُهُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِۗ إِنَّ رَبَّكَ لَسَرِيعُ ٱلۡعِقَابِ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 7:167Kuma ka tuna lokacin da Ubangijinka Ya yi shela, lalle zai aiko musu da wanda zai ɗanɗana musu mummunar azaba, har ya zuwa ranar tashin alƙiyama. Lalle Ubangijinka Mai gaggawar uƙuba ne, kuma lalle shi tabbas Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
وَقَطَّعۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُمَمٗاۖ مِّنۡهُمُ ٱلصَّٰلِحُونَ وَمِنۡهُمۡ دُونَ ذَٰلِكَۖ وَبَلَوۡنَٰهُم بِٱلۡحَسَنَٰتِ وَٱلسَّيِّـَٔاتِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Open ayah 7:168Kuma Mun rarraba su ƙabilu daban-daban a bayan ƙasa; a cikinsu akwai salihai, kuma daga cikinsu akwai koma bayan haka; kuma Mun jarrabe su da kyawawan abubuwa da munana, don su komo (zuwa hanya).
فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٞ وَرِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ يَأۡخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا ٱلۡأَدۡنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغۡفَرُ لَنَا وَإِن يَأۡتِهِمۡ عَرَضٞ مِّثۡلُهُۥ يَأۡخُذُوهُۚ أَلَمۡ يُؤۡخَذۡ عَلَيۡهِم مِّيثَٰقُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن لَّا يَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّ وَدَرَسُواْ مَا فِيهِۗ وَٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 7:169Sai waɗansu bara-gurbi suka maye bayansu, sun gaji littafin (Attaura), suna karɓar abin duniya, suna kuma cewa: “Za a gafarta mana.” Kuma idan wani abin duniyar irinsa ya zo musu sai su sake karɓar sa. Shin yanzu ba a ɗauki alƙawari daga wurinsu ba a cikin littafin (Attaura) cewa, kada su faɗi wata magana game da Allah sai gaskiya, kuma sun karanta abin da yake cikinsa? Kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga dukkan waɗanda suke da taƙawa. Shin ba za ku hankalta ba?
وَٱلَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِٱلۡكِتَٰبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُصۡلِحِينَ
Open ayah 7:170Waɗanda kuwa suke riƙo da Littafi, kuma suke tsayar da salla, to lalle Mu ba ma tozarta ladan masu gyara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya tuna lokacin da ya sanar wa Yahudawa abin da ya riga ya hukunta a kansu, wanda kuma sai ya faru da su babu makawa, wato yadda zai haɗa su da waɗanda za su yi ta gana musu azaba iri-iri a lokuta daban-daban saboda yawan saɓon Allah da zalunci da suke yi. Sun yi ta ganin haka a tsawon tarihinsu. An ce tun zamanin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sannan da zamanin sarakunan Girkawa da Kildaniyawa da lokacin sarkin Babila Bukhtanassar da kuma zamanin Manzon Allah da sahabbansa sun yi ta ganin ƙasƙanci da wulaƙanci iri-iri, tun daga kan kakanni har zuwa jikoki har kuma alƙiyama ta tashi, ko da sun samu sun yi ƙarfi a wani lokaci, to za su zo su sake faɗawa cikin ƙasƙanci a gaba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, ya rarraba su ƙabilu daban-daban sun watsu a bayan ƙasa saboda ɓarnarsu da fasiƙancinsu da son kansu. Wasu kaɗan daga cikinsu mutanen kirki ne, wasu kuma ba haka ba. Allah ya jarrabe su jarrabawa iri-iri, wata mai kyau wata marar kyau don su koma kan daidaitacciyar hanya. Daga baya sai wasu Yahudawa bara-gurbi suka zo suka maye gurbin magabatansu, babu alheri tare da su, ga shi sun gaji littafin Attaura daga iyayensu, sun karanta abin da yake cikinsa na hukunce-hukunce, amma son duniya ce kaɗai a zukatansu, suna karɓar kuɗaɗen haram, sun yi watsi da aiki da hukunce-hukuncen Attaura, suna ruɗar kawunansu da cewa, wai Allah zai gafarta musu zunubbansu, sannan idan suka ƙara cin karo da wata dukiyar ta haram irin ta farko sai su sake karɓewa su ci. Ashe yanzu Allah bai yi alƙawari mai ƙarfi da su a cikin Attaura ba cewa, kada su faɗi wani abu su dangana shi ga Allah sai gaskiya, sun kuma karanta abin da yake cikin Attaura sun fahimce shi, sun manta da cewa gidan lahira ya fi alheri ga masu kiyaye dokokin Allah, me ya sa ba za su hankalta ba? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suke riƙe da littafinsa ƙam-ƙam, suna aiki da shi, suka kuma tsayar da salla, to waɗannan mutane ne nagari masu gyara, Allah kuwa ba ya tozarta ladansu.
۞وَإِذۡ نَتَقۡنَا ٱلۡجَبَلَ فَوۡقَهُمۡ كَأَنَّهُۥ ظُلَّةٞ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُۥ وَاقِعُۢ بِهِمۡ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱذۡكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Open ayah 7:171Ka tuna kuma lokacin da Muka ɗaga dutse a samansu kamar girgije, kuma suka sakankance cewa zai rikito musu, (Muka ce da su): “Ku riƙe abin da Muka ba ku da kyau, kuma ku tuna abin da yake cikinsa, don su zamo masu kiyaye dokokin Allah.”
وَإِذۡ أَخَذَ رَبُّكَ مِنۢ بَنِيٓ ءَادَمَ مِن ظُهُورِهِمۡ ذُرِّيَّتَهُمۡ وَأَشۡهَدَهُمۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَلَسۡتُ بِرَبِّكُمۡۖ قَالُواْ بَلَىٰ شَهِدۡنَآۚ أَن تَقُولُواْ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ إِنَّا كُنَّا عَنۡ هَٰذَا غَٰفِلِينَ
Open ayah 7:172Ka tuna kuma lokacin da Ubangijinka Ya fitar da zurriyar ’yan’adam daga tsatsonsu, Ya kuma sa su suka yi wa kansu shaida, (Ya ce da su): “Yanzu ba Ni ne Ubangijinku ba?” Suka ce: “E Kai ne, mun shaida.” Don kada a ranar alƙiyama ku ce: “Lalle mu mun kasance gafalallu a kan wannan.”
أَوۡ تَقُولُوٓاْ إِنَّمَآ أَشۡرَكَ ءَابَآؤُنَا مِن قَبۡلُ وَكُنَّا ذُرِّيَّةٗ مِّنۢ بَعۡدِهِمۡۖ أَفَتُهۡلِكُنَا بِمَا فَعَلَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ
Open ayah 7:173Ko kuma ku ce: “Iyayenmu da suka gabace mu kawai suka yi shirka, mu kuma zurriya ce da muka kasance a bayansu; yanzu Ka hallakar da mu saboda abin da maɓarnata suka yi?”
وَكَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ وَلَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Open ayah 7:174Kuma kamar haka ne Muke bayyana ayoyi, don su komo wa (gaskiya). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tuna wa Annabi (ﷺ) labarin Banu-Isra’ila lokacin da suka nemi Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kawo musu littafin da za su riƙa karantawa suna aiki da shi. Lokacin da ya zo musu da littafin Attaura, wanda a ciki Allah ya yi alƙawura masu ƙarfi da su, to amma sai suka ƙi cika waɗannan alƙawura, suka bar aiki da koyarwar Attaura, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɗaga dutsen Ɗuri-Sina a kansu yana reto kamar girgije yana yi musu inuwa, sai kuwa suka tabbatar cewa zai faɗo musu. Sai Allah ya ce musu, lalle su riƙe littafin Attaura da ya ba su da kyau, su yi aiki da hukunce-hukuncen da suke cikinsa don su tsare dokokinsa. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tuna lokacin da ya fitar da zurriyyar ‘yan’adam daga tsatsonsu, ya sa suka yi wa kansu shaida da kansu, ya ce musu: “Yanzu ba ni ne Ubangijinku ba?” Suka amsa masa da cewa: “Kai ne, mun shaida.” Ya sa su sun yi wannan shaidar ne da kansu saboda gudun kada ranar alƙiyama su musanta faruwar hakan, su ce su ba su san cewa, Allah kaɗai ne ya cancanci a bauta masa ba, ko kuma su ce iyayensu ne suka fara yin shirka, su kuma ‘ya’ya ne da suka zo daga baya suka yi koyi da iyayensu a kan jahilci; don haka yaya Allah zai hallakar da su saboda iyayensu sun yi mummunan aiki sun bar Tauhidi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yayin da Allah ya halicci Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya shafa bayansa, sai duk wani rai da Allah zai halicce shi daga cikin zurriyarsa har zuwa tashin alƙiyama ya fito daga tsatsonsa.” [Tirmizi #3076]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Allah (Mai tsarki da daukaka) ya riƙe alƙawari daga tsatson Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a Na’amana (wato Arfa), ya fitar da duk wata zurriyya da zai halitta daga tsatsonsa, ya watsa su a gabansa kamar kiyashi, sannan ya yi magana da su baki da baki, ya ce: “Yanzu ba ni ne Ubangijinku ba?” Suka ce: “Kai ne Ubangijinmu, mun shaida.” Don kada ranar alƙiyama ku ce: “Haƙiƙa mu ba mu da masaniya game da wannan,” ko kuma ku ce: “Ai da ma can iyayenmu ne suka yi shirka mu kuma mun kasance zurriyya ne da muka biyo bayansu, yanzu ka kama mu da laifin da maɓarnata suka aikata?” [Ahmad #2455]. Abin nufi da wannan ayar shi ne, mutane tun suna tsatson Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ɗauki alƙawarin yin imani da Allah da kaɗaita shi wajen bauta, wannan ya sa duk wanda aka haifa daga cikinsu ake haihuwarsa a kan lafiyayyar halittarsa ta asali, to sai bayan sun girma ne sun mallaki hankalinsu Shaiɗan yake lalata musu ɗabi’arsu ta asali, ya kirawo su zuwa bautar wanin Allah da kafirce wa Allah da manzanninsa. Sai Allah ya bayyana cewa, kamar yadda ya bayyana wannan ayar, haka yake bayyana sauran ayoyin Alƙur’ani don mutane su shiryu su dawo kan miƙaƙƙiyar hanya.
وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱلَّذِيٓ ءَاتَيۡنَٰهُ ءَايَٰتِنَا فَٱنسَلَخَ مِنۡهَا فَأَتۡبَعَهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَكَانَ مِنَ ٱلۡغَاوِينَ
Open ayah 7:175Ka kuma karanta musu labarin wannan da Muka ba shi ayoyinmu, sai ya saluɓe (jikinsa) daga gare su, sai Shaiɗan ya bi shi, don haka ya kasance cikin halakakku.
وَلَوۡ شِئۡنَا لَرَفَعۡنَٰهُ بِهَا وَلَٰكِنَّهُۥٓ أَخۡلَدَ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُۚ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ ٱلۡكَلۡبِ إِن تَحۡمِلۡ عَلَيۡهِ يَلۡهَثۡ أَوۡ تَتۡرُكۡهُ يَلۡهَثۚ ذَّٰلِكَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۚ فَٱقۡصُصِ ٱلۡقَصَصَ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 7:176Kuma da Mun ga dama da mun ɗaukaka shi a sanadiyyarsu, amma kuma shi ya karkata zuwa ga duniya, don haka ya biye wa son zuciyarsa. To misalinsa kamar misalin kare ne, idan ka kai masa ɗauki ya yi lallage, idan ma ka ƙyale shi zai yi lallage, wannan shi ne misalin waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu. Don haka ka ba da labari don su yi tunani.
سَآءَ مَثَلًا ٱلۡقَوۡمُ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَأَنفُسَهُمۡ كَانُواْ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 7:177Misalin waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu ya munana, kuma kawunansu suka kasance suna zalunta.
مَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِيۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 7:178Wanda Allah Ya shiryar, to wannan shi ne shiryayye; wanda kuwa Ya ɓatar, to waɗannan su ne hasararru. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin wani mutum wanda Allah ya ba shi sanin hukunce-hukuncen shari’a, ya tumbatsa a ilimi wanda da a ce ya riƙe shi ya yi aiki da saninsa, to da Allah ya ba shi ɗaukaka a duniya da lahira, to amma sai ya take wannan ilimi nasa, ya tuɓe rigar sanin da Allah ya sanya masa, Shaiɗan ya bi shi ya ɓatar da shi, ya hana shi aiki da iliminsa, ya koma duniya ce kaɗai abin nemansa. Allah ya kwatanta halinsa da halin kare wanda kowane lokaci harshensa a waje yake yana lallage yana haki; idan ya yi gudu ya gaji ya yi, idan ma ya tsaya ya huta ci gaba da zaro harshe yake yana lallagen. To kamar haka wannan mutumin ya zama; duniya ce kaɗai a gabansa, yana bin ta yana neman ta ido rufe, da zarar ya samu abin da yake hanƙoron samu, to zai sake yunƙurawa yana neman wani ne daban. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan shi ne misalin mutanen da suke ƙaryata ayoyinsa a kowane zamani kuma a kowane wuri. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ci gaba da faɗa wa mutanensa da Yahudawa irin waɗannan ƙissoshi don ko sa yi tunani. Wannan misalin na mutanen da suka ƙaryata ayoyin Allah suka kuma zalunci kansu ya yi matuƙar muni. Wanda Allah ya shiryar da shi shi ne ya yi dace, wanda kuwa ya ɓatar da shi, to irinsu su ne suka yi hasarar duniya da ta lahira.
وَلَقَدۡ ذَرَأۡنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ لَهُمۡ قُلُوبٞ لَّا يَفۡقَهُونَ بِهَا وَلَهُمۡ أَعۡيُنٞ لَّا يُبۡصِرُونَ بِهَا وَلَهُمۡ ءَاذَانٞ لَّا يَسۡمَعُونَ بِهَآۚ أُوْلَٰٓئِكَ كَٱلۡأَنۡعَٰمِ بَلۡ هُمۡ أَضَلُّۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡغَٰفِلُونَ
Open ayah 7:179Kuma lalle haƙiƙa Mun halitta wa Jahannama da yawa daga cikin aljannu da mutane; ga su da zukata da ba sa hankalta da su, ga kuma idanu da ba sa kallo da su, ga kunnuwa da ba sa sauraro da su. Waɗannan kamar dabbobi suke; a’a, sun ma fi (dabbobi) ɓacewa. Waɗannan su ne gafalallu.
وَلِلَّهِ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ فَٱدۡعُوهُ بِهَاۖ وَذَرُواْ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ أَسۡمَٰٓئِهِۦۚ سَيُجۡزَوۡنَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 7:180Allah kuma Yana da sunaye mafiya kyau, don haka ku roƙe Shi da su; kuma ku rabu da waɗanda suke fanɗarewa game da sunayensa; da sannu za a yi musu sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa.
وَمِمَّنۡ خَلَقۡنَآ أُمَّةٞ يَهۡدُونَ بِٱلۡحَقِّ وَبِهِۦ يَعۡدِلُونَ
Open ayah 7:181Kuma akwai wata al’umma daga cikin waɗanda Muka halitta suna shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke adalci.
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا سَنَسۡتَدۡرِجُهُم مِّنۡ حَيۡثُ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:182Kuma waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu, za Mu yi musu talala ta inda ba su sani ba.
وَأُمۡلِي لَهُمۡۚ إِنَّ كَيۡدِي مَتِينٌ
Open ayah 7:183Kuma Ina yi musu jinkiri ne; lalle kaidina mai ƙarfi ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ya halicci mutane da aljannu masu yawa don wutar Jahannama, ya ba su zukata amma ba sa fahimtar gaskiya da su; ya ba su idanu amma ba sa ganin gaskiya da su; ya ba su kunnuwa amma ba sa sauraron maganar Allah su fahimta da su. Waɗannan halittu sun zamo kamar dabbobi ne waɗanda ba sa iya fahimtar komai. Kai sun ma fi dabbobi taɓarɓarewa da lalacewa, saboda su dabbobi da ma can Allah bai yi musu tanadin hankali irin na mutum da aljan ba; don haka bai ɗora musu komai na ibada ba, saɓanin mutane da aljannu da Allah ya ba su isasshen hankali da za su bambance ƙarya da gaskiya da shi; to amma sai suka yi watsi da shi, suka ƙi amfani da shi yadda ya dace. Waɗannan sun tabbata su ne gafalallu ga ayoyin Allah da ambaton sa, masu watsi da abin da zai amfane su na imani da aiki na ƙwarai. Sai kuma Allah ya bayyana cewa, yana da sunaye mafiya kyau waɗanda ya kira kansa da su a littafinsa ko Annabinsa ya kira shi da su a sunnarsa, sunaye masu ɗauke da siffofinsa mafi ɗaukaka na kamala, don haka ya umarci bayinsa su roƙe shi da su, su bar waɗanda suke fanɗarewa game da sunayensa, ko ta hanyar su raɗa wa wasu gumakansu sunayen Allah ko su ƙirƙira masa wasu sunayen daban ko su ƙi yarda da wasu. Allah ya ce zai saka musu da abin da suka kasance suna aikatawa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah yana da wasu sunaye tis’in da tara, ɗari ba ɗaya, duk wanda ya kiyaye su to zai shiga Aljanna.” [Bukhari #2736, da Muslim #2677]. Sai kuma Allah ya bayyana cewa, a cikin mutanen da ya halitta ana samun al’ummar da take shiryuwa da gaskiya, take kuma shiryar da mutane zuwa gare ta, take kuma yi musu hukunci a tsakaninsu da adalci. Amma waɗanda suke jayayya da ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka), zai yi musu talala ne har lokacin da ya yi niyyar halaka su, kuma ya ninka musu azaba ta inda ba su sani ba; zai jinkirta musu ya ba su tsawon rai don su ci gaba da kafircinsu da saɓon Allah. Lalle kuma kaidin Allah mai tsananin ƙarfi ne, duk wanda ya kama ba zai iya kuɓucewa ba.
أَوَلَمۡ يَتَفَكَّرُواْۗ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٌ
Open ayah 7:184Shin ba za su yi tunani ba. Lalle abokin nasu fa babu hauka a tattare da shi. Ba kowa ne shi ba, face mai gargaɗi, mai bayyanarwa?
أَوَلَمۡ يَنظُرُواْ فِي مَلَكُوتِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٖ وَأَنۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَدِ ٱقۡتَرَبَ أَجَلُهُمۡۖ فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 7:185Shin ba za su yi duba cikin mulkin sammai da ƙasa da kuma abin da Allah Ya halitta ba, kuma lalle ya kusata a ce ajalinsu yana gab da zuwa, to da wane zance ne za su yi imani bayansa (wato Alƙur’ani)?
مَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَا هَادِيَ لَهُۥۚ وَيَذَرُهُمۡ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ
Open ayah 7:186Wanda duk Allah Ya ɓatar, to ba shi da mai shiryar da shi. Kuma zai ƙyale su a cikin ƙetare iyakar da suke yi suna ɗimuwa. Kafin aiko Manzon Allah (ﷺ) duk mutanen Makka da ya tashi a gabansu sun san shi mutum ne mai hankali, mai kyawawan halaye; ba a san shi da wani abu na rashin kyautawa ba, kowa yana son sa, yana yabon halayensa. Bayan da Allah ya ba shi manzanci, ya umarce shi da ya kirawo mutanensa ya faɗa musu gaskiya, ya hana su bautar gumaka, su bauta wa Allah shi kaɗai, sai kawai suka fara jifan sa da cewa, yana da taɓin hankali, alhali kuwa sun san ƙarya suke, ba su da wani dalili na yin haka sai hassada. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana jan hankalinsu cewa, me ya sa ba za su tsaya su yi tunani ba su gane cewa, Manzon Allah (ﷺ) ba shi da wani taɓin hankali, shi kawai mai gargaɗi ne gare su, kuma duk mai son gaskiya idan ya ji maganganunsa ya san gaskiya yake faɗa, babu mai guje masa sai mai ƙin gaskiya. Hakanan su waɗannan masu ƙaryata saƙon da Annabi (ﷺ) ya zo da shi na Tauhidi, ashe ba za su tsaya su yi tunani game da mulkin sammai da ƙasa da duk wani abu da Allah ya halitta a cikinsu ba, su gane cewa, wanda ya yi wannan halittar kuma yake gudanar da ita shi kaɗai ne wanda ya cancanta a bauta masa? Hakanan su yi tunani game da ajalinsu mai yiwuwa ne ma ya matso kusa, don haka su gaggauta tuba zuwa ga Allah kafin mutuwarsu. To yanzu da wane irin zance ne za su yi imani bayan Alƙur’ani? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya ɓatar to babu wanda ya isa ya shiryar da shi; yakan bar kafirai cikin shisshiginsu suna ta ɗimuwa su kasa gane hanyar gaskiya.
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَاۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّيۖ لَا يُجَلِّيهَا لِوَقۡتِهَآ إِلَّا هُوَۚ ثَقُلَتۡ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَا تَأۡتِيكُمۡ إِلَّا بَغۡتَةٗۗ يَسۡـَٔلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِيٌّ عَنۡهَاۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ ٱللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 7:187Suna tambayar ka game da tashin alƙiyama yaushe ne matabbatarta take? Ka ce: “Sanin lokacinta yana wajen Ubangijina; ba mai bayyanar da lokacinta sai Shi. Ta yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Ba za ta zo muku ba sai katsahan.” Suna tambayar ka kamar ka nace a kanta, ka ce: “Iliminta yana wajen Allah kaɗai, sai dai da yawa daga cikin mutane ba su sani ba.
قُل لَّآ أَمۡلِكُ لِنَفۡسِي نَفۡعٗا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ وَلَوۡ كُنتُ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ لَٱسۡتَكۡثَرۡتُ مِنَ ٱلۡخَيۡرِ وَمَا مَسَّنِيَ ٱلسُّوٓءُۚ إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ وَبَشِيرٞ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 7:188Ka ce, “Ba na iya mallakar wa kaina wani amfani, ko wata cuta sai abin da Allah Ya ga dama. Kuma in da na kasance na san gaibu, lalle da na yawaita alheri, da kuma wani mummunan abu bai shafe ni ba. Ni ba wani ne ba face mai gargaɗi mai bushara ga mutanen da suke yin imani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana wata mas’ala da kafirai suka matsa wa Annabi (ﷺ) tambaya a kanta domin wai su ƙure shi su bayyana ƙaryarsa a fili don kowa ya fahimta; ita ce batun tashin alƙiyama, wadda suka ce ba su yi imanin akwai ta ba. Sun yi ta tambayar Manzon Allah (ﷺ) cewa, in har maganar da yake faɗa ta cewa akwai ranar alƙiyama gaskiya ce, to yaushe ne za ta zo? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗa musu cewa, sanin lokacinta yana wurin Allah, babu wanda ya isa ya bayyana lokacinta sai shi, hatta mala’iku da suke sammai da halittun da suke ƙasa ba wanda ya san lokacin zuwanta; za ta zo ba zato ba tsammani. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Annabi (ﷺ) yana zaune cikin jama’a sai Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo ya ce masa: “Yaushe ne lokacin tashin alƙiyama?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda aka tambaya bai fi mai tambayar sani ba.” [Bukhari #50, da Muslim #9]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai sun tsananta game da tambayar Manzon Allah lokacin tashin alƙiyama kamar shi kansa ya tsananta tambaya ne game da ita har ya samu amsa. To ya faɗa musu cewa, shi ba shi da wata masaniya game da lokacin zuwanta, Allah ne kaɗai ya keɓanta da sanin hakan, sai dai mafi yawancin mutane ba sa sanin hakan. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Alƙiyama ba za ta tsaya ba har sai rana ta fito daga mafaɗarta, idan ta hudo mutane suka gan ta duk sai su ba da gaskiya, to a wannan lokacin ne, “Ba wani rai da imaninsa zai amfane shi idan a da can bai yi imani ba, ko bai aikata wani abu na alheri ba a cikin imaninsa.” [Suratul An’am, aya ta 158]. Kuma lalle alƙiyama za ta tsaya a daidai lokacin da wasu mutane biyu za su baje hajarsu ta sayarwa a tsakaninsu, ba za su yi wannan cinikin ba kuma ba za su naɗe hajar ba. Kuma lalle alƙiyama za ta tsaya a daidai lokacin da mutum ya tatso nonon taguwarsa ya nufi gida, to amma ba zai samu damar ɗanɗanar sa ba. Kuma lalle alƙiyama za ta tsaya a lokacin da mutum yake gyara bakin tabkinsa, to amma ba zai sha ruwansa ba. Kuma lalle alƙiyama za ta tsaya lokacin da mutum zai ɗaga loma zuwa bakinsa, to amma ba zai samu damar ɗanɗanar ta ba.” [Bukhari #6506, da Muslim #4954]. Sai kuma Allah ya umarci Annabi da ya faɗa musu cewa, shi ba zai iya mallaka wa kowa wani abu na amfani ba, kuma ba zai iya kare kansa daga wata cuta ba sai abin da Allah ya ga dama; idan da ya san gaibi kuwa to da ya aikata abubuwan da ya san za su haifar masa da amfani mai yawa, kuma da ya kauce wa duk wani sharri da yake ƙoƙarin samun sa. Allah ya umarce shi ya tabbatar musu da cewa, shi mai gargaɗi ne kawai, kuma mai albishir ga mutanen da suka yi imani.
۞هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَجَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا لِيَسۡكُنَ إِلَيۡهَاۖ فَلَمَّا تَغَشَّىٰهَا حَمَلَتۡ حَمۡلًا خَفِيفٗا فَمَرَّتۡ بِهِۦۖ فَلَمَّآ أَثۡقَلَت دَّعَوَا ٱللَّهَ رَبَّهُمَا لَئِنۡ ءَاتَيۡتَنَا صَٰلِحٗا لَّنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّٰكِرِينَ
Open ayah 7:189Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma Ya halicci matarsa daga gare shi, don ya sami nutsuwa tare da ita; to yayin da ya kusance ta, sai ta ɗauki yaron ciki, sai ta ci gaba (da harkokinta) da shi, to yayin da (cikin) ya yi nauyi, sai suka roƙi Allah Ubangijinsu cewa: “Lalle idan Ka ba mu ɗa lafiyayye, lalle za mu kasance masu godiya.”
فَلَمَّآ ءَاتَىٰهُمَا صَٰلِحٗا جَعَلَا لَهُۥ شُرَكَآءَ فِيمَآ ءَاتَىٰهُمَاۚ فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 7:190To yayin da Ya ba su ɗa lafiyayye, sai suka sanya masa abubuwan tarayya cikin abin da ya ba su. Allah kuwa ya ɗaukaka ga barin abin da suke shirka da Shi.
أَيُشۡرِكُونَ مَا لَا يَخۡلُقُ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ
Open ayah 7:191Shin sa riƙa haɗa (Allah) da abin da ba ya halittar komai, hasali ma su ne ake halitta?
وَلَا يَسۡتَطِيعُونَ لَهُمۡ نَصۡرٗا وَلَآ أَنفُسَهُمۡ يَنصُرُونَ
Open ayah 7:192Kuma ba za su iya taimaka musu ba, ba kuma za su iya taimaka wa kawunansu ba?
وَإِن تَدۡعُوهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ لَا يَتَّبِعُوكُمۡۚ سَوَآءٌ عَلَيۡكُمۡ أَدَعَوۡتُمُوهُمۡ أَمۡ أَنتُمۡ صَٰمِتُونَ
Open ayah 7:193Kuma in da za ku kirawo su zuwa shiriya, to lalle ba za su bi ku ba. Duk ɗaya ne a gare ku kun kirawo su, ko kuma kun yi shiru? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, shi ne wanda ya halicci mutane daga rai guda ɗaya, wato Annabi Adam, sannan ya halitta masa matarsa Hauwa’u (() daga jinsinsa don ya samu nutsuwa da ita. To lokacin da ya sadu da ita sai ta ɗauki yaron ciki, ta ci gaba da harkokinta babu wata wahala, har lokacin da cikin ya tsufa ya yi mata nauyi, sai Annabi Adamu da matarsa Hauwa’u (() suka yi ta yin addu’ar Allah ya ba su lafiyayen ɗa kuma nagari; suka yi alƙawari idan har Allah ya karɓi addu’arsu ya biya musu buƙatarsu, za su gode masa da yin biyayya gare shi. To yayin da Allah ya karɓi addu’arsu ya ba su ɗa lafiyayye nagari, sai ‘ya’yansu ‘yan’adam suka sanya wa Allah abokan tarayya cikin ni’imar ‘ya’ya da arziƙi da ya ba su. Allah kuwa ya ɗaukaka game da abin da suke yin shirka da shi. Yanzu sa riƙa bauta wa wani abu tare da Allah wanda ba ya iya halittar komai, su ne ma ababen halitta, waɗanda wasu ne suka sassaƙa su ko suka gina su? Kuma ba za su iya taimakon masu bautar su da komai ba, ba za su iya kare su daga wani mummunan abu ba? Idan da waɗannan mushirikai za su kirawo waɗannan gumakan nasu zuwa shiriya ba za su amsa musu ba, saboda sandararrun abubuwa ne ba sa ji ba sa magana ba su da hankali. Duk ɗaya ne a gare su ko su roƙe su ko su yi shiru, ba za su amsa musu ko su saurare su ba. To saboda me za su riƙa bauta wa waɗanda haka siffarsu take?
إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ عِبَادٌ أَمۡثَالُكُمۡۖ فَٱدۡعُوهُمۡ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 7:194Lalle waɗanda kuke kira ba Allah ba bayi ne kamarku, to ku kirawo su mana, sai su kuma su amsa muku idan kun kasance masu gaskiya ne.
أَلَهُمۡ أَرۡجُلٞ يَمۡشُونَ بِهَآۖ أَمۡ لَهُمۡ أَيۡدٖ يَبۡطِشُونَ بِهَآۖ أَمۡ لَهُمۡ أَعۡيُنٞ يُبۡصِرُونَ بِهَآۖ أَمۡ لَهُمۡ ءَاذَانٞ يَسۡمَعُونَ بِهَاۗ قُلِ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ ثُمَّ كِيدُونِ فَلَا تُنظِرُونِ
Open ayah 7:195Shin wai suna da ƙafafun da suke tafiya da su ne; ko suna da hannayen da suke damƙa da su, ko kuma suna da wasu idanuwa da suke gani da su; ko suna da wasu kunnuwa da suke saurare da su? Ka ce: “Ku kirawo abokan tarayyarku, sannan ku shirya mini makirci kuma kada ku saurara mini.”
إِنَّ وَلِـِّۧيَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡكِتَٰبَۖ وَهُوَ يَتَوَلَّى ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 7:196“Lalle Majiɓincin lamarina Shi ne Allah Wanda Ya saukar da Littafi; kuma Shi Yake jiɓintar lamarin salihan bayi.”
وَٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَكُمۡ وَلَآ أَنفُسَهُمۡ يَنصُرُونَ
Open ayah 7:197Waɗanda kuke kira ba Shi ba kuwa, ba za su iya taimakon ku ba, kuma ba za su iya taimaka wa kawunansu ba.
وَإِن تَدۡعُوهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ لَا يَسۡمَعُواْۖ وَتَرَىٰهُمۡ يَنظُرُونَ إِلَيۡكَ وَهُمۡ لَا يُبۡصِرُونَ
Open ayah 7:198Kuma idan da za ku yi kiran su zuwa ga shiriya, to fa ba za su ji ba; kuma za ka gan su suna kallon ka, alhali kuwa ba sa gani. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙalubalantar mushirikai cewa, waɗanda suke bauta wa ba Allah ba su ma bayi ne kamarsu, in gaskiya ne su kirawo su su amsa musu a gani idan sun cancanci bauta. Sai Allah ya tabbatar musu da kasawar waɗannan abubuwan bauta nasu, yana mai tambayar su, wai shin waɗannan gumakan nasu suna da ƙafafuwa da suke tafiya da su, ko kuwa suna da hannaye da suke kama abu da su su riƙe da ƙarfi waɗanda za su iya taimakon su da su, ko kuma suna da wasu idanuwa ne da suke gani da su, ko kuma suna da kunnuwa ne waɗanda suke ji da su? Idan sun tabbatar da cewa ba su da ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, to ta yaya suke bautar su ba Allah ba? Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa waɗannan mushirikai cewa, su kirawo gumakansu da suke bauta su haɗa ƙarfi da su don su cutar da shi, kada kuma su saurara masa in har sun isa, ko kuma cutarwa a hannunsu take. Sannan ya tabbatar musu cewa, mai taimakon sa wanda yake jiɓintar lamarinsa shi ne Allah wanda ya saukar da Alƙur’ani kuma yake jiɓintar lamarin duk mutane nagari, don haka shi ne mai ba shi kariya daga duk wani macuci azzalumi. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mun fita wani yaƙi tare da Annabi (ﷺ) wajejen Najdu, sai lokacin barcin rana ya riske shi a wani kwazazzabo mai yawan itatuwa masu ƙaya, sai ya sami ƙarƙashin wata bishiya ya kwanta ya rataye takobinsa a jikinta, duk sauran sahabbai kowa ya tafi ya nemi inuwa ya kwanta. Muna tsakiyar hutawa sai muka ji Annabi (ﷺ) yana kiran mu, sai muka je inda yake, muna isa sai muka ga wani baƙauye, balarabe a gabansa zaune. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wannan mutum ya same ni ina barci, sai ya ɗauki takobina ya zare shi, sai na farka na gan shi tsaye a kaina yana riƙe da takobi a zare, sai ya ce: “Wane ne ya isa ya kare ka daga gare ni?” Sai na ce; “Allah ne.” Sai kawai ya mayar da takobi cikin kubensa ya zauna gabana. Ga shi nan zaune.” Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Sai Annabi ya ƙyale shi bai yi masa komai ba.” [Bukhari #4139, da Muslim #843]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa wa mushirikai cewa, gumakan da suke bauta wa ba Allah ba ba za su iya taimaka musu da komai ba, kamar yadda ba sa iya taimaka wa kansu; kuma ko da za su kirawo su zuwa gaskiya ba jin su za su yi ba, za ka ga kamar suna kallon ka amma ba sa ganin komai.
خُذِ ٱلۡعَفۡوَ وَأۡمُرۡ بِٱلۡعُرۡفِ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡجَٰهِلِينَ
Open ayah 7:199Ka yi riƙo da afuwa, kuma ka yi umarni da kyakkyawan abu, ka kuma kawar da kai daga wawaye.
وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ نَزۡغٞ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Open ayah 7:200Idan wani tunzuri daga Shaiɗan ya tunzura ka, to ka nemi tsarin Allah. Lalle Shi Mai ji ne, Masani.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ إِذَا مَسَّهُمۡ طَٰٓئِفٞ مِّنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ تَذَكَّرُواْ فَإِذَا هُم مُّبۡصِرُونَ
Open ayah 7:201Lalle waɗanda suka kiyaye dokokin Allah, idan wani Shaiɗan mai sa waswasi ya shafe su, sai su tuna (da Allah), sai ga su suna gani tar.
وَإِخۡوَٰنُهُمۡ يَمُدُّونَهُمۡ فِي ٱلۡغَيِّ ثُمَّ لَا يُقۡصِرُونَ
Open ayah 7:202‘Yan’uwansu kuwa suna ƙara kawo musu ɗauki na ɓata, sannan su ba sa taƙaitawa.
وَإِذَا لَمۡ تَأۡتِهِم بِـَٔايَةٖ قَالُواْ لَوۡلَا ٱجۡتَبَيۡتَهَاۚ قُلۡ إِنَّمَآ أَتَّبِعُ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ مِن رَّبِّيۚ هَٰذَا بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمۡ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 7:203Kuma idan ba ka kawo musu wata aya ba, sai su ce: “Don me ba ka ƙirƙiro ta ba?” Ka ce: “Ba abin da nake bi sai kawai abin da aka yi min wahayinsa daga Ubangijina. Waɗannan hujjoji ne daga Ubangijinku da kuma shiriya da kuma rahama ga mutanen da suke yin imani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabinsa (ﷺ) da ya dinga yin afuwa gwargwadon hali daga halayen mutane, kada ya matsa musu, idan wani ya yi abin kirki daga cikinsu ya yaba masa, wanda kuwa ya yi rashin kyautawa ya yafe masa, ya haƙura da nasa haƙƙin, kuma ya yi umarni da abin da shari’a ta zo da shi, ya kawar da kai daga jahilai masu wauta. Ya kuma umarce shi idan wani waswasin Shaiɗan ya same shi, to ya nemi tsari daga Allah, haƙiƙa shi Allah mai ji ne masani. Sai kuma ya bayyana cewa, mutane masu taƙawa, ta hanyar kiyaye dokokin Allah, idan Shaiɗan ya shafe su da wani waswasi ko fushi ko makamancin haka, nan da nan suke tuna Allah sai su dawo cikin hayyacinsu suna gani tar da zukatansu, don haka sai su yi watsi da waswasin Shaiɗan, su nisanci saɓon Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, kafirai da fajirai ‘yan’uwansu shaiɗanu ne suke ƙawata musu hanyar ɓata, suke taimaka musu a kan saɓon Allah da kafirci, kuma su shaiɗanun ba sa gajiya ko ƙosawa da wannan mummunan aiki nasu suna nan tare da su ba dare ba rana. Daga cikin irin ɓarnar da waɗannan shaiɗanu suke shukawa shi ne suna ingiza ‘yan’uwansu kafirai suna damun Manzon Allah (ﷺ) da ya zo musu da mu’ujizoji waɗanda su suke buƙatar gani kafin su ba da gaskiya da shi; to idan bai zo musu da abin da suka nema ba, sai su ce, don me shi ba zai ƙago wannan mu’ujizar ba, idan har da gaske shi Manzon Allah ne? Sai Allah ya umarce shi da ya amsa musu da cewa, shi yana bin abin da aka yi masa wahayinsa ne kawai. Kuma wannan Alƙur’anin ya ƙunshi dalilai ne na sarari masu tabbatar da gaskiya da kuma shiriya da rahama ta duniya da lahira ga mutanen da suke yin imani.
وَإِذَا قُرِئَ ٱلۡقُرۡءَانُ فَٱسۡتَمِعُواْ لَهُۥ وَأَنصِتُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Open ayah 7:204Kuma idan an karanta Alƙur’ani, to ku saurare shi, ku kuma yi tsit, don a ji ƙan ku.
وَٱذۡكُر رَّبَّكَ فِي نَفۡسِكَ تَضَرُّعٗا وَخِيفَةٗ وَدُونَ ٱلۡجَهۡرِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ ٱلۡغَٰفِلِينَ
Open ayah 7:205Kuma ka ambaci (sunan) Ubangijinka a ranka, kana mai ƙasƙantar da kai, kuma kana mai jin tsoro, ba kuma tare da ɗaga murya ba, safe da yamma, kada kuma ka zamo cikin gafalallu.
إِنَّ ٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَيُسَبِّحُونَهُۥ وَلَهُۥ يَسۡجُدُونَۤ۩
Open ayah 7:206Lalle waɗanda suke wajen Ubangijinka, ba sa girman kai wajen bautar Sa, kuma suna tsarkake Shi, kuma gare Shi kawai suke yin sujjada. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar bayinsa da su saurara su kasa kunnuwa su yi tsit su daina hayaniya ko surutu lokacin da ake karatun Alƙur’ani domin su sami rahamar Allah. Ya kuma umarci Annabi (ﷺ) da ya yi ta ambaton sa a ransa da kuma harshensa, ta yadda wani ma ba zai san me yake faɗa ba, yana mai ƙasƙantar da kansa ga Allah, yana mai cike da tsoron sa da tsoron azabarsa. Kuma ya ambace shi da harshensa ba tare da ɗaga murya ba da safe da yamma, kar kuma ya zama daga cikin gafalallu. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mun kasance tare da Manzon Allah (ﷺ) sai ya zamana duk sa’adda muka doso wani kwazazzabo sai mu yi ta hailala muna kabbara muna ɗaga muryarmu, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane, ku sawwaƙa wa kawunanku, domin wanda kuke kira ba kurma ba ne, ba wanda ba ya tare da ku ba ne, lalle shi yana tare da ku kuma mai ji ne makusanci.” [Bukhari #2993, da Muslim #2704]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya yi tsayuwar dare ya karanta ayoyi goma, to ba za a rubuta shi cikin gafalallu ba; wanda kuma ya yi tsayuwar dare ya karanta ayoyi ɗari, to za a rubuta shi a cikin masu ɗa’a (ga Allah), wanda kuma ya yi da ayoyi dubu, to za a rubuta shi cikin masu tsibi-tsibin lada.” [Abu Dawud #1398]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mala’ikun da suke wurinsa ba sa girman kai ga bauta masa, kuma suna tsarkake shi daga duk wata tawaya ta hanyar yi masa tasbihi, sannan gare shi kaɗai suke yin sujjada. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ni ina ganin abin da ku ba kwa gani, ina kuma jin abin da ku ba kwa ji; sama ta yi ƙara kuma ya cancanta gare ta ta yi ƙarar, na rantse da wanda raina yake a hannunsa, a sama babu wurin shimfiɗa ‘yan yatsu huɗu, face akwai mala’ikan da ya sanya goshinsa yana mai sujjada ga Allah....” [Ahmad #21516, da Tirmizi #2312].