الأنفال
Al-Anfaal
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 8:1Suna tambayar ka game da ganimomi; ka ce (da su): “Ganimomi na Allah ne da kuma Manzo; saboda haka ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma gyara tsakaninku, kuma ku bi Allah da Manzonsa, idan kun kasance muminai.”
إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَإِذَا تُلِيَتۡ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُهُۥ زَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Open ayah 8:2Muminai na haƙiƙa (su ne) kaɗai waɗanda idan aka ambaci Allah, sai zukatansu su raurawa, idan kuma aka karanta musu ayoyinsa, sai su ƙara musu imani, kuma ga Ubangijinsu ne kawai suke dogara.
ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Open ayah 8:3Waɗanda suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da muka arzurta su.
أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَمَغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ
Open ayah 8:4Waɗannan su ne muminai na haƙiƙa. Suna da muƙamai a wurin Ubangijinsu da kuma gafara da arziki na karamci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana buɗe wannan Surar ne da mayar da martani game da tambayar da sahabbai suke yi wa Annabi (ﷺ) dangane da hukuncin dukiyar ganima, musamman ganimar yaƙin Badar, wa ya kamata a ba wa? Kuma yaya za a raba ta? To shi ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi da ya faɗa musu cewa, ganima mallakinsa ce shi Allah (Mai tsarki da daukaka) da Manzonsa, watau shi Annabi (ﷺ) shi ne zai raba ya ba wa kowa kasonsa daga ciki. Don haka su ji tsoron Allah su kiyaye dokokinsa, su kuma sasanta tsakaninsu, kuma su bi Allah da Manzonsa, su yi aiki da umarninsa idan har su muminai ne da gaske. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffofin cikakkun muminai da cewa, su ne waɗanda idan sun ji an ambaci Allah sai zukatansu su girgiza don tsoron Allah; idan kuma aka karanta musu ayoyin Allah sai su ƙara musu imani da yaƙini, kuma ga Allah kaɗai suke dogara. Suna kuma masu tsayar da salla yadda ya kamata, sannan suna ciyar da dukiyarsu domin Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan su ne muminai na haƙiƙa, suna da darajoji maɗaukaka daga Ubangijinsu da gafara da arziki na karamci a Aljanna. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A ranar yaƙin Badar, Manzon Allah (ﷺ) ya zaburar da sahabbansa a kan yaƙi, har ya yi alƙawarin duk wanda ya yi wani abin bajinta to yana da wani sakamako na musamman daga cikin ganima. To sai samarin cikinsu suka wuce gaba, dattawa kuwa suka tsaya a wajen tutoci ba su ƙara gaba ba. To lokacin da aka ci nasarar yaƙi sai dattawa suka ce wa samari, su ne suka riƙa ba su kariya ta baya, da a ce an koro su to da wurinsu za su dawo, don haka ba za su yarda samarin su su kaɗai su kwashe ganimar da aka samu ba. Su kuma samarin sai suka ƙi yarda suka ce Annabi (ﷺ) ne ya mallaka musu. Sai Allah ya saukar da waɗannan ayoyi.” [Dubi, Abu Dawud #2737, da Nasa’i, As-Sunan Al-Kubra #11133]. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Ayoyi huɗu sun sauka a kaina: Na samu wani takobi a wurin yaƙi, sai na zo da shi wurin Manzon Allah (ﷺ) na ce masa: “Ka ba ni shi a matsayin ganima.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mayar da shi inda ka ɗauko shi.” Sai na kuma tashi na ce: “Ka ba ni shi a matsayin ganima ya Ma’aikin Allah?” Sai ya kuma cewa: “Ka mayar da shi.” Sai na kuma tashi na ce: “Ya Manzon Allah ka ba ni shi a matsayin ganima, za a bar ni hakanan ba ni da komai ne?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce masa: “Mayar da shi inda ka ɗauke shi.” Sai wannan ayar ta sauka: (Suna tambayar ka game da ganima, ka ce: \"Ganima ta Allah ce da Manzonsa\").” [Dubi, Muslim #1748]. Wannan ayar ta farko, wasu malamai sun ce an shafe hukuncinta da aya ta 41 a cikin wannan Surar. Wasu kuma suka ce hukuncinta yana nan ba a shafe shi ba, suka ce, ma’anarta shi ne ganima duk ta Allah ce, domin duk abin da yake cikin duniya da lahira mulkin Allah ne. Shi kuma Annabi (ﷺ) shi yake da ikon bayanin yadda za a yi da wannan ganimar kamar yadda Allah ya sanar da shi a aya ta 41 cikin wannan Surar.
كَمَآ أَخۡرَجَكَ رَبُّكَ مِنۢ بَيۡتِكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لَكَٰرِهُونَ
Open ayah 8:5Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka (na Madina) da gaskiya, alhali lalle wata jama’a daga muminai tabbas suna ƙin (haka).
يُجَٰدِلُونَكَ فِي ٱلۡحَقِّ بَعۡدَمَا تَبَيَّنَ كَأَنَّمَا يُسَاقُونَ إِلَى ٱلۡمَوۡتِ وَهُمۡ يَنظُرُونَ
Open ayah 8:6Suna jayayya da kai game da abin da yake tabbas, kai ka ce ana kora su ne wajen mutuwa, alhali kuwa suna kallo.
وَإِذۡ يَعِدُكُمُ ٱللَّهُ إِحۡدَى ٱلطَّآئِفَتَيۡنِ أَنَّهَا لَكُمۡ وَتَوَدُّونَ أَنَّ غَيۡرَ ذَاتِ ٱلشَّوۡكَةِ تَكُونُ لَكُمۡ وَيُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُحِقَّ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَيَقۡطَعَ دَابِرَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 8:7(Ka tuna) kuma lokacin da Allah Ya yi muku alƙawarin ɗayar jama’an nan guda biyu (na abokan gaba) cewa, lalle taku ce, sai kuka riƙa fatan marar wahalar ce za ta zama taku, alhali kuwa Allah Yana nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmominsa, Ya kuma tumɓuke tushen kafirai.
لِيُحِقَّ ٱلۡحَقَّ وَيُبۡطِلَ ٱلۡبَٰطِلَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 8:8Don (kuma) Ya tabbatar da gaskiya, Ya kuma lalata ɓarna ko da kuwa kafirai sun ƙi (hakan). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, kamar yadda wasu sahabbai ba su so yadda al’amarin rabon ganima ya kasance ba, to haka kuma lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fito da Annabi (ﷺ) daga gidansa domin haɗuwa da kafiran Ƙuraishawa, wasu muminai ba haka suka so ba, har ma suna jayayya da Annabi (ﷺ) a kan al’amarin gaskiya wanda Allah ya yi nufi, bayan ya bayyana a fili. Har sai da suka zama kamar ana jan su ne zuwa ga mutuwa saboda tsananin ƙinsu ga yaƙi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jawo hankalin muminai yana cewa, su tuna lokacin da ya yi musu alƙawarin samun abu ɗaya daga cikin biyu, wato ko dai su yi nasarar rutsawa da kayan ayarin fatauci da Abu Sufyan yake jagoranci, ko kuma su haɗu da rundunar mayaƙan Makka. Amma su muminai a lokacin sun fi son su haɗu da ayarin fatauci na Abu Sufyan domin su ne ba sa ɗauke da makaman faɗa, kuma ba su da yawa. Shi kuma Allah ya riga ya yi nufin zai haɗa su ne da mayaƙan Ƙuraishawa, domin ya ba wa muminai nasara a kansu, ya bayyana rinjayen Musulunci a kan kafirci, ya kuma halakar da manya-manyan kafirai, ya bayyana izzar Musulmi da Musulunci, ya rushe kafirci da shirka ko da kuwa kafirai masu manyan laifuka ba sa son hakan.
إِذۡ تَسۡتَغِيثُونَ رَبَّكُمۡ فَٱسۡتَجَابَ لَكُمۡ أَنِّي مُمِدُّكُم بِأَلۡفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ مُرۡدِفِينَ
Open ayah 8:9Ku tuna lokacin da kuke neman taimakon Ubangijinku, sai Ya amsa muku cewa: “Ni zan kawo muku ɗauki na mala’iku dubu masu bibiyar juna.”
وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشۡرَىٰ وَلِتَطۡمَئِنَّ بِهِۦ قُلُوبُكُمۡۚ وَمَا ٱلنَّصۡرُ إِلَّا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Open ayah 8:10Kuma (wannan taimakon) Allah bai sanya shi ba, sai don albishir a gare ku, don kuma zukatanku su nutsu da shi. Babu kuma wata nasara sai daga wurin Allah. Lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima.
إِذۡ يُغَشِّيكُمُ ٱلنُّعَاسَ أَمَنَةٗ مِّنۡهُ وَيُنَزِّلُ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ لِّيُطَهِّرَكُم بِهِۦ وَيُذۡهِبَ عَنكُمۡ رِجۡزَ ٱلشَّيۡطَٰنِ وَلِيَرۡبِطَ عَلَىٰ قُلُوبِكُمۡ وَيُثَبِّتَ بِهِ ٱلۡأَقۡدَامَ
Open ayah 8:11(Ku kuma tuna) lokacin da gyangyaɗi yake kwashe ku (Allah) Yana Mai amintar da ku (daga tunanin abokan gaba), Ya kuma riƙa saukar da ruwa daga sama don Ya tsarkake ku da shi, Ya kuma tafiyar muku da waswasin shaiɗan, don kuma Ya ƙarfafa zukatanku Ya kuma tabbatar da dugaduganku da shi. An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A ranar yaƙin Badar Annabi (ﷺ) ya kalli mushirikai ya ga yawansu ya kai dubu, ya kalli sahabbansa ya ga ba su fi mutum ɗari uku da sha tara ba, sai ya fuskanci alƙibla, ya ɗaga hunnayensa ya fara addu’a, yana cewa: “Ya Allah ka zartar mini alƙawarin da ka yi mini, ya Allah ka ba ni abin da ka yi mini alƙawari, ya Allah idan waɗannan jama’ar Musulmin suka halaka (a yau), to ba za a ci gaba da bauta maka a bayan ƙasa ba.” Bai gushe yana ta yin addu’a ba, ya ɗaga hannayensa sama, yana fuskantar alƙibla har sai da gwadonsa ya faɗi daga kafaɗunsa, Abubakar ya zo ya ɗauke shi ya mayar masa a kafaɗunsa, sannan ya rungumo shi ta bayansa, yana ce masa: “Ya Annabin Allah, addu’ar ta isa hakanan, lalle Allah zai cika maka alƙawarin da ya yi maka”. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyin.” [Muslim #1763]. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa muminai cewa, su tuna lokacin da suka nemi taimako wajen Allah a kan ya ba su nasara bisa abokan gabarsu, sai ko Allah ya karɓi addu’arsu, ya yi musu alƙawarin zai taimaka musu da mala\'iku har dubu waɗanda za su taho a jerin gwano don kawo musu ɗauki a yaƙin. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu wannan taimako ne don ya zama albishir na cin nasara a gare su, kuma zukatansu su ƙara natsuwa da zuwansu. Kuma nasara ba daga ko’ina take ba sai daga Allah, shi ne mabuwayi mai hikima. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A wannan rana ta yaƙin Badar wani mutum Musulmi ya bi wani kafiri a guje, sai kawai ya ji ƙarar duka da bulala ta samansa, ya kuma ji wani sadauki yana cewa: “Gaba dai Haizum.” Sai ya ga wannan kafirin da ke gabansa ya faɗi rigingine, yana dubawa sai ya ga an datse hancin wannan mutumin an tsaga masa fuskarsa, kamar dukan bulala, ya kuma yi baƙi ƙirin. Sai wannan Musulmi mutumin Madina ya zo ya shaida wa Manzon Allah (ﷺ) abin da ya faru. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Ka faɗi gaskiya; wannan taimako ne daga sama ta uku.” A ranar Musulmi suka kashe kafirai saba’in, suka kama saba’in.” [Muslim #1763]. An karɓo daga Rifa’a ɗan Rafi’u (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mala’ika Jibrilu ya zo wurin Annabi (ﷺ) ya ce masa: “Yaya kuke ganin waɗanda suka halarci yaƙin Badar daga cikinku?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce masa: “Muna ganin su cikin mafiya falalar Musulmi.” Ko ya faɗa masa wata magana mai kama da haka. Sai Jibrilu ya ce: “Mu ma haka muke ganin mala’ikun da suka halarci yaƙin Badar daga cikinmu.” [Bukhari #3992]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nemi muminai su tuna lokacin da ya saka musu gyangyanɗi a idanunsu don su samu nutsuwar zukata, ya kuma saukar musu da ruwan sama don ya tsarkake su daga duk wani kari ko janaba, kuma ya kawar musu da waswasin Shaiɗan, kuma ya ƙarfafa zukatansu, ya kuma tabbatar musu da dugadugansu ta hanyar ruwan sama da ya sauka ya sa rairayin wurin ya yi ƙarfi, don haka ƙafafuwansu ko na dawakansu ba za su riƙa nutsewa a cikinsa ba.
إِذۡ يُوحِي رَبُّكَ إِلَى ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ أَنِّي مَعَكُمۡ فَثَبِّتُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ سَأُلۡقِي فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلرُّعۡبَ فَٱضۡرِبُواْ فَوۡقَ ٱلۡأَعۡنَاقِ وَٱضۡرِبُواْ مِنۡهُمۡ كُلَّ بَنَانٖ
Open ayah 8:12(Ka kuma tuna) lokacin da Ubangijinka Yake wahayi zuwa ga mala’iku cewa: “Lalle Ni ina tare da ku, saboda haka ku ƙarfafa wa waɗanda suka yi imani gwiwa. Da sannu zan jefa tsoro cikin zukatan waɗanda suka kafirce, saboda haka ku doki wuyansu, kuma ku doki dukkanin gaɓoɓin hannaye da ƙafafu.”
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ شَآقُّواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَمَن يُشَاقِقِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Open ayah 8:13Wannan kuwa saboda sun saɓa wa Allah da Manzonsa. Duk wanda kuwa ya saɓa wa Allah da Manzonsa to lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne.
ذَٰلِكُمۡ فَذُوقُوهُ وَأَنَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابَ ٱلنَّارِ
Open ayah 8:14Wannan (uƙubar) sai ku ɗanɗane ta (a duniya), kuma ba shakka kafirai suna da azabar wuta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabi (ﷺ) lokacin da ya yi wa mala’iku wahayi da cewa, lalle yana tare da su da taimakonsa da nasararsa, ya kuma umarce su cewa, su ƙarfafa wa muminai gwiwa, ya sanar da su cewa zai jefa tsoro da firgici a zukatan kafirai, don haka yana umartar muminai da su yi ta saran wuyoyin kafirai, da gaɓoɓin hannayensu da ƙafafuwansu. Wannan kuwa saboda sun saɓa wa Allah da Manzonsa suna kuma yaƙar su, kuma duk wanda zai aikata haka, Allah ba zai bar shi ba sai ya yi masa uƙuba da ta dace da shi, Allah kuma mai tsananin uƙuba ne. Ana kuma yi wa kafirai albishir da su ɗanɗani wannan azaba tun a nan duniya, kafin a je lahira su gamu da wata azabar mafi raɗaɗi da take jiran su.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ زَحۡفٗا فَلَا تُوَلُّوهُمُ ٱلۡأَدۡبَارَ
Open ayah 8:15Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka haɗu da cincirindon waɗanda suka kafirta, to kada ku ba su baya.
وَمَن يُوَلِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ دُبُرَهُۥٓ إِلَّا مُتَحَرِّفٗا لِّقِتَالٍ أَوۡ مُتَحَيِّزًا إِلَىٰ فِئَةٖ فَقَدۡ بَآءَ بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 8:16Duk kuwa wanda ya ba su baya a wannan ranar idan dai ba wanda ya gudu da niyyar juyowa ya kai ɗauki ko kuma mai niyyar haɗuwa da wata jama’a (ta mayaƙa) ba, to haƙiƙa ya komo da fushin Allah, kuma makomarsa Jahannama ce; wannan makoma kuwa ta munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da cewa, idan sun haɗu da kafirai a filin yaƙi, suka kuma kusanci juna, to kada su kuskura su juya musu baya su gudu; lalle su tsaya su jajirce. Ya kuma yi gargaɗi mai tsanani ga duk wanda ya juya musu baya da cewa ya koma da fushin Allah, kuma makomarsa wutar Jahannama ce, tir kuwa da wannan makoma. To amma idan ya juya baya ne don yaudarar abokan gaba da niyyar zai sake kawo musu farmaki, ko kuma da niyyar ya koma ya haɗe da wata runduna ta Musulmi waɗanda zai dawo fagen fama tare da su ya taimaka a karya kafirai, to wannan babu komai ya halatta. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa.” Sai sahabbai suka ce, waɗanne irin abubuwa ne? Sai ya ce, su ne: “Shirka da Allah da sihiri da kashe ran da Allah ya hana kashewa ba da wani laifi ba da cin dukiyar riba da cin dukiyar maraya da gudu daga fagen yaƙi da kuma yi wa muminai mata ƙazafi waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.” [Bukhari #2766, da Muslim #89].
فَلَمۡ تَقۡتُلُوهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ قَتَلَهُمۡۚ وَمَا رَمَيۡتَ إِذۡ رَمَيۡتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ رَمَىٰ وَلِيُبۡلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ مِنۡهُ بَلَآءً حَسَنًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 8:17Saboda haka ba ku kuka kashe su ba, Allah ne Ya kashe su. Kuma ba ka jefa ba lokacin da ka jefa, sai dai Allah ne Ya jefa. Don kuma Ya jarrabi muminai da kyakkyawar jarrabawa. Lalle Allah Mai ji ne Masani.
ذَٰلِكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ مُوهِنُ كَيۡدِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 8:18Waccan (jarraba ku da aka yi gaskiya ne), kuma lalle Allah Mai raunana makircin kafirai ne.
إِن تَسۡتَفۡتِحُواْ فَقَدۡ جَآءَكُمُ ٱلۡفَتۡحُۖ وَإِن تَنتَهُواْ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَإِن تَعُودُواْ نَعُدۡ وَلَن تُغۡنِيَ عَنكُمۡ فِئَتُكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَوۡ كَثُرَتۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 8:19Idan kuna neman zuwan hukunci ne (watau azaba), to haƙiƙa hukuncin ya zo muku. Idan kuka daina to shi ya fi muku alheri, idan kuma kuka koma, to za Mu koma, jama’arku kuma ba za ta amfana muku komai ba, komai yawanta kuwa, lalle kuma Allah Yana tare da muminai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, Annabi (ﷺ) da sahabbansa waɗanda suka halarci yaƙin Badar tare da shi ba su ne suka kashe kafiran da aka halaka a yaƙin ba; Allah ne ya kashe su, domin komai ya faru ne da taimakonsa da agajinsa. Shi ma Manzon Allah (ﷺ) da ya danƙi ƙasa da tafin hannunsa ya watsa ta a fuskokin kafirai ta kuma cika musu ido, to a haƙiƙa ba shi ne ya yi wannan jifan ba, Allah ne ya yi, kuma Allah ya yi haka ne don ya ni’imta muminai da kyakkyawan sakamako da za su yi masa godiya a kansa. Lalle Allah mai ji ne kuma masanin duk abin da yake faruwa. An karɓo daga Hakim ɗan Hizam (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: “A ranar yaƙin Badar Manzon Allah (ﷺ) ya cika tafin hannunsa da tsakwankwani ya fuskanto mu, ya jefe mu da ita ya ce: “Fuskoki sun munana.” Sai dukkanmu muka bazama a guje. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Kuma ba ka yi jifa ba lokacin da ka yi jifa sai dai Allah ne ya yi jifan.” [Ibn Jarir, Tafsir #15822; da Ibn Abi Hatim, Tafsir , #8906; da Ɗabarani, Al-Mu’jamul Kabir #3128]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu haka ne domin zai raunana duk wani makirci da ƙulli na kafirai da suke yi wa Musulunci da Musulmi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana da mushirikai waɗanda suke yaƙar Annabi (ﷺ) da sahabbansa ranar yaƙin Badar, yana cewa, idan su ne suka roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) da ya yi hukunci tsakaninsu da muminai, kuma ya saukar da uƙubarsa a kan azzalumai marasa gaskiya, to ga shi nan abin da suka roƙa ya tabbata, Allah ya taimaka wa wanda aka zalunta a kan azzalumi, ya tabbatar da gaskiyar mai gaskiya, sun ga abin da ya faru da su a ranar yaƙin Badar. Amma idan su kafirai sun bar kafircin da suke yi, to hakan shi ne ya fi zama alheri a gare su; idan kuwa suka sake komawa yaƙar Annabi (ﷺ) da sahabbansa, to tabbas Allah zai karya su; a kashe wasu a kama wasu daga cikinsu, kuma yawan adadinsu ba zai amfane su da komai ba, Allah kuma yana tare da muminai.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَأَنتُمۡ تَسۡمَعُونَ
Open ayah 8:20Ya ku waɗanda suka yi imani, ku bi Allah da Manzonsa kada kuma ku ba shi baya alhali kuwa kuna ji.
وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ
Open ayah 8:21Kada kuma ku zama kamar waɗanda suka ce: “Mun ji,” alhalin kuwa su ba sa ji.
۞إِنَّ شَرَّ ٱلدَّوَآبِّ عِندَ ٱللَّهِ ٱلصُّمُّ ٱلۡبُكۡمُ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 8:22Lalle mafi sharrin masu tafiya a bayan ƙasa a wurin Allah (su ne) kurame (ga jin gaskiya) bebaye (ga faɗar gaskiya) waɗanda ba sa hankalta.
وَلَوۡ عَلِمَ ٱللَّهُ فِيهِمۡ خَيۡرٗا لَّأَسۡمَعَهُمۡۖ وَلَوۡ أَسۡمَعَهُمۡ لَتَوَلَّواْ وَّهُم مُّعۡرِضُونَ
Open ayah 8:23Da Allah Ya san da akwai wani alheri a tare da su, to da Ya jiyar da su (gaskiya); da kuma Ya jiyar da su ɗin ma, to da kuwa sun ba da baya suna masu bijirewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da su yi wa Allah da Manzonsa biyayya, kada su bijire musu alhalin suna jin abin da ake saukarwa na Alƙur’ani. Sai kuma ya yi musu kashedi da zama kamar mushirikai waɗanda idan sun ji an karanta littafin Allah sai su ce “mun ji”, to amma ba sa ɗaukar wani darasi daga abin da suka ji, suka zama kamar bebaye waɗanda ba sa jin komai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mafi sharrin masu tafiya a bayan ƙasa a wurin Allah su ne kafirai waɗanda suka zama kurame ba sa jin gaskiya, beyaye ba sa faɗar gaskiya, kuma ba sa hankaltar duk wani gargaɗi da Allah yake yi musu. Da kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya san da akwai wani alheri a tare da su, to da ya ba su damar fahimtar ayoyin nasa; da kuma za a ƙaddara ya fahimtar da su ayoyin, to da sun bijire musu sun ƙi karɓar gaskiyar da ke cikinsu, saboda zukatansu sun riga sun gurɓace har ta kai babu wani alheri da zai shige su.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱسۡتَجِيبُواْ لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمۡ لِمَا يُحۡيِيكُمۡۖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَحُولُ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَقَلۡبِهِۦ وَأَنَّهُۥٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
Open ayah 8:24Ya ku waɗanda suka yi imani, ku amsa kiran Allah da na Manzo idan ya yi kiran ku ga abin da zai raya ku; kuma ku sani cewa, lalle Allah Yana kange tsakanin mutum da zuciyarsa, kuma lalle wurinsa ne za a tattara ku.
وَٱتَّقُواْ فِتۡنَةٗ لَّا تُصِيبَنَّ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنكُمۡ خَآصَّةٗۖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Open ayah 8:25Ku kiyayi fitinar da ba kawai waɗanda suka yi zalunci za ta shafa ba, kuma ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne.
وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ أَنتُمۡ قَلِيلٞ مُّسۡتَضۡعَفُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ تَخَافُونَ أَن يَتَخَطَّفَكُمُ ٱلنَّاسُ فَـَٔاوَىٰكُمۡ وَأَيَّدَكُم بِنَصۡرِهِۦ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 8:26Kuma ku tuna lokacin da kuke ‘yan tsirari masu rauni a bayan ƙasa, kuna tsoron kada wasu mutane su fauce ku, sai Ya tattara ku (a Madina) Ya kuma ƙarfafa ku da taimakonsa, Ya kuma arzuta ku da tsarkakan abubuwa don ku godiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da su amsa kiran Allah da Manzonsa, su kuma yi biyayya duk sa’adda Manzo ya kirawo su zuwa ga abin da zai amfane su a addininsu da rayuwarsu, duniyarsu da lahirarsu. An karɓo daga Abu Sa’idu ɗan Al-Mu’alla (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kirawo ni sai ban amsa masa ba, sai na ce: “Ya Manzon Allah, ina salla ne a lokacin.” Sai ya ce: “Yanzu kai ba ka ji Allah ya ce ba: “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku amsa kiran Allah da na Manzo idan ya kira ku ga abin da zai raya ku?” Sannan Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Zan koya maka Surar da ta fi kowace sura a Alƙur’ani girma kafin ka fita daga masallaci.” Sannan ya kama hannuna, yayin da na ga zai fita sai na ce masa: “Ba ka ce za ka koya min Surar da ta fi kowace sura girma a Alƙur’ani ba?” Sai ya ce: “Ita ce ﴾الحَمدُ لِلَّهِ رَبِّ العالَمينَ﴿ ita ce ayoyi bakwai da ake maimaitawa, kuma ita ce Alƙur’ani mai girma wanda aka ba ni.” [Bukhari #4474]. Sai kuma Allah (ﷺ) ya sanar da bayinsa cewa, idan ya ga dama yana kange tsakanin mutum da zuciyarsa. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) yana yawaita cewa: “Ya (Allah) mai jujjuya zuciya, ka tabbatar da zuciyata a kan addininka.” Sai na ce: “Ya Annabin Allah, mun yi imani da kai da abin da ka zo da shi, shin kana jiye mana tsoro ne?” Sai ya ce: “Lalle zukata suna tsakankanin yatsu biyu daga ‘yan yatsun Allah mai rahama yana juya su yadda ya ga dama.” [Tirmizi #2140, da Ibn Maja #3834, da Ahmad #12107]. An karɓo daga Nawwas ɗan Sam’an (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Babu wata zuciya face tana tsakankanin ‘yan yatsu biyu daga yatsun Allah mai rahama; idan ya ga dama ya miƙar da ita, idan kuma ya ga dama ya karkatar da ita.” Ya kuma kasance yana cewa: “Ya mai jujjuya zukata, ka tabbatar da zukatanmu a kan addininka.” [Ibn Maja #199, da Ahmad #17613]. Kuma zuwa gare shi za su koma a ranar alƙiyama. Sai kuma Allah (ﷺ) ya umarce su su guji wani bala’i wanda idan ya zo ba zai tsaya a kan waɗanda suka jawo shi da zaluncinsu kaɗai ba; zai haɗo mai laifi da marar laifi gaba ɗaya, musamman waɗanda suka ga ana aikata ba daidai ba amma suka ƙi tsawatarwa tare da suna da iko a kan hakan. Kuma su sani cewa, Allah mai tsananin uƙuba ne. An karɓo daga Zainab ‘yar Jahshi (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Wata rana Annabi (ﷺ) ya tashi daga barci launin fuskarsa ya yi ja jawur yana cewa: “La’ilaha illal Lahu! Larabawa sun shiga uku saboda wani sharri da ya kusanto; a yau an buɗe ganuwar Yajuju da Majuju gwargwadon haka.” Sai Sufyanu ya ƙulla cas’in ko ɗari da ‘yan yatsunsa. Aka ce wa Annabi (ﷺ): “Yanzu za mu halaka alhalin a cikinmu akwai mutanen kirki?” Ya ce: “E, idan mutanen banza suka yi yawa.” [Bukhari #7059, da Muslim #2880]. An karɓo daga Nu’umanu ɗan Bashir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Misalin wanda yake tsaye a kan iyakokin Allah da wanda ya auka cikinsu, kamar mutanen da suka yi ƙuri’a ne wajen shiga jirgin ruwa, wasu suka samu gidan sama wasu kuma gidan ƙasa, sai ya zamanto waɗanda suke gidan ƙasa idan za su ɗebi ruwa sai sun hau ɓangaren na saman jirgin. Sai suka yi shawarar cewa: ‘Me zai hana mu fasa inda muke, ba sai mun dinga damun na samanmu ba?’ To idan har su na saman suka ƙyale su suka aikata abin da suka yi niyya, to fa za su halaka ne gaba ɗayansu. Idan kuwa suka hana su to sai su tsira gaba ɗayansu.” [Bukhari #2493]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su tuna lokacin da suke `yan kaɗan, maƙiyansu sun rena su, suna a tsorace kada kafirai su fauce su, su dinga kama su ɗaya bayan ɗaya suna kashe su, sai Allah ya tattaro su, ya sama musu wurin gudun hijira, wato Madina, ya ba su ƙarfi har suka ci nasara a kan abokan gabarsu, ya kuma arzuta su da abubuwan jin daɗi iri-iri don su yi wa Allah godiyar waɗannan ni’imomi da ya yi musu.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَخُونُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ وَتَخُونُوٓاْ أَمَٰنَٰتِكُمۡ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 8:27Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku ha’inci Allah da Manzo, (kada) kuma ku ha’inci amanoninku alhali kuna sane.
وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ
Open ayah 8:28Kuma ku sani cewa, dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne, Allah kuma lalle a wurinsa lada mai girma yake.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تَتَّقُواْ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّكُمۡ فُرۡقَانٗا وَيُكَفِّرۡ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۗ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 8:29</b>Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka kiyaye dokokin Allah, to zai sanya muku (hanyar) tsira Ya kuma kankare muku munanan ayyukanku kuma Ya gafarta muku. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da su nesanci cin amanarsa da ta Manzonsa (ﷺ) da kuma duk wata amana da suka danƙa a tsakaninsu alhalin suna sane. Amanar Allah ita ce bin dokokinsa ta hanyar aikata duk wani wajibi da barin duk wani abin da aka hana. Kiyaye amanar Manzon Allah (ﷺ) kuwa shi ne yi masa biyayya da girmama sunnarsa da aiki da ita. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah ya ce: “Alamomin munafuƙi uku ne: Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya, idan kuma aka yi alƙawari da shi sai ya saɓa, kuma idan an amince da shi sai ya ci amana.” [Bukhari #33, da Muslim #59]. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗakar da muminai cewa, dukiyarsu da ‘ya’yansu wata jarraba ce daga Allah gare su, domin ya ga shin za su bayar da haƙƙin Allah da ke cikinsu ko kuma son zuciya zai rufe musu ido su fifita son dukiyoyinsu da ‘ya’yansu a kan son Allah. Kuma ya kwaɗaitar da su cewa, duk wanda ya yi biyayya ga umarninsa yana da wani lada mai girma a wurinsa. Kuma idan har sun kiyaye dokokin Allah, sun bi umarninsa, sun guji haninsa, to zai sanya musu wata alama da za su bambance tsakanin ƙarya da gaskiya da ita, ya kuma sanya musu mafita daga duk wata damuwa ta duniya, ya ba su nasara, ya ƙarfafe su, kuma zai kankare musu laifukansu ya yafe musu. Allah kuwa ma’abocin babbar falala ne.
وَإِذۡ يَمۡكُرُ بِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيُثۡبِتُوكَ أَوۡ يَقۡتُلُوكَ أَوۡ يُخۡرِجُوكَۚ وَيَمۡكُرُونَ وَيَمۡكُرُ ٱللَّهُۖ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلۡمَٰكِرِينَ
Open ayah 8:30Kuma ka tuna lokacin da waɗanda suka kafirta suke ƙulla maka makirci don su tsare ka ko kuma su kashe ka ko su kore ka. Suna kuma shirya makirci Allah kuma Yana mayar musu sakamakon makircinsu. Allah kuma (Shi ne) Ya fi masu makirci iya (sakayyar) makirci.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا قَالُواْ قَدۡ سَمِعۡنَا لَوۡ نَشَآءُ لَقُلۡنَا مِثۡلَ هَٰذَآ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 8:31Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu sai su ce: “Haƙiƙa mun ji, ai da mun ga dama ba shakka da mun faɗi irin wannan, wannan ba komai ba ne sai tatsuniyoyin mutanen da.”
وَإِذۡ قَالُواْ ٱللَّهُمَّ إِن كَانَ هَٰذَا هُوَ ٱلۡحَقَّ مِنۡ عِندِكَ فَأَمۡطِرۡ عَلَيۡنَا حِجَارَةٗ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ أَوِ ٱئۡتِنَا بِعَذَابٍ أَلِيمٖ
Open ayah 8:32Ka tuna kuma lokacin da suka ce: “Ya Allah, idan wannan (Alƙur’ani) ya zamanto gaskiya ne daga wurinka yake, to sai Ka yi mana ruwan duwatsu daga sama ko kuma Ka kawo mana da wata azaba mai raɗaɗi.”
وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعَذِّبَهُمۡ وَأَنتَ فِيهِمۡۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ مُعَذِّبَهُمۡ وَهُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ
Open ayah 8:33Allah kuwa bai zamanto Mai yi musu azaba ba alhali kai kana cikinsu, kuma Allah ba zai yi musu azaba ba alhali suna neman gafara.
وَمَا لَهُمۡ أَلَّا يُعَذِّبَهُمُ ٱللَّهُ وَهُمۡ يَصُدُّونَ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَمَا كَانُوٓاْ أَوۡلِيَآءَهُۥٓۚ إِنۡ أَوۡلِيَآؤُهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُتَّقُونَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 8:34Me zai hana Allah Ya yi musu azaba alhali su suna hana mutane zuwa Masallaci mai alfarma, alhali kuwa ba su zamanto masu ƙaunar Sa na haƙiƙa ba. Masu ƙaunar Sa na haƙiƙa su ne masu taƙawa, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka).
وَمَا كَانَ صَلَاتُهُمۡ عِندَ ٱلۡبَيۡتِ إِلَّا مُكَآءٗ وَتَصۡدِيَةٗۚ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ
Open ayah 8:35Kuma sallarsu a Ɗakin (Ka’aba) ba ta zamanto ba sai fito da tafi. Sai ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka zamanto kuna yi na kafirci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin irin makirci da kafiran Ƙuraishawa suka shirya wa Annabi Muhammadu (ﷺ) lokacin da yake a Makka. Sun tattauna a tsakaninsu a Darul-Nadwa , sun shirya cewa, ko dai su tsare shi a wani wuri su hana shi fita har mutuwa, ko su kashe shi kowa ya huta, ko kuma su kore shi daga Makka ya tafi duk inda za shi. To amma daga ƙarshe ba su yi nasara ba. Allah ya sanar da Manzonsa (ﷺ) halin da ake ciki, kuma ya umarce shi ya yi hijira shi da sahabbansa. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wannan makirci nasu ne da yadda Allah ya kuɓutar da shi, su kuma Allah ya halakar da su, aka kashe yawancinsu a yaƙin Badar. Allah ne Fiyayyen mai mayar da makircin makirai a kansu, ya saka musu da abin da suka cancanta na sakamako. Sai kuma ya bayyana cewa, idan ana karanta wa waɗannan kafirai ayoyin Alƙur’ani sai su dinga hura hanci suna cewa sun ji, ai idan da sun ga dama da su ma za su iya faɗar irinsa. Suka ƙara da cewa, ai wannan Alƙur’ani ba komai ba ne sai tatsuniyoyin mutanen farko. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) Ya tunatar da Manzonsa lokacin da kafiran Ƙuraishawa suke addu’ar cewa, idan har Alƙur’anin da Annabi (ﷺ) yake karantawa gaskiya ne, to Allah ya yi musu ruwan azaba na duwatsu daga sama, ko ya aiko musu wata azaba mai raɗaɗi. An karɓo daga Anas ɗan Maliku (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Abu Jahlin ya ce: “Ya Allah, idan wannan (Alƙur’ani) ya zamanto gaskiya ne daga wurinka yake, sai ka yi mana ruwan duwatsu daga sama, ko kuma ka zo mana da wata azaba mai raɗaɗi.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “(Allah kuwa bai zamanto mai yi musu azaba ba alhalin kai kana cikinsu. Kuma Allah ba zai yi musu azaba ba da a ce suna neman gafara. Me zai hana Allah ya yi musu azaba alhalin suna hana mutane zuwa Masallaci mai alfarma….)” [Bukhari #4649, da Muslim #2796]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa musu da cewa, ba zai yi musu azaba ba alhalin Annabi (ﷺ) yana cikinsu, kuma ba zai saukar musu da wata azaba ba da a ce suna neman gafararsa a kan kafircinsu da zunubbansu, sai dai ba sa neman gafarar. Allah ya bayyana cewa, me zai hana ya yi musu azaba alhalin suna hana Musulmi zuwa Masallaci mai alfarma, alhali su ba masoyansa ne ba, masoyansa na haƙiƙa su ne masu tsoron Allah ta hanyar kiyaye dokokinsa, sai dai yawancin mutane ba su san haka ba. Sai kuma ya bayyana cewa, sallar kafiran Ƙuraishawa a Ɗakin Ka’aba ba wani abu ne ba sai fito da tafi, don haka Allah ya ce, su ɗanɗani azaba saboda kafircinsu.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ لِيَصُدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ فَسَيُنفِقُونَهَا ثُمَّ تَكُونُ عَلَيۡهِمۡ حَسۡرَةٗ ثُمَّ يُغۡلَبُونَۗ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ يُحۡشَرُونَ
Open ayah 8:36Lalle waɗanda suka kafirta suna kashe dukiyoyinsu don su toshe hanyar Allah. To da sannu za su kashe ta (dukiyar) sannan ta zama nadama a gare su, sannan kuma a rinjaye su. Waɗanda kuwa suka kafirta a Jahannama za a tattara su.
لِيَمِيزَ ٱللَّهُ ٱلۡخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِ وَيَجۡعَلَ ٱلۡخَبِيثَ بَعۡضَهُۥ عَلَىٰ بَعۡضٖ فَيَرۡكُمَهُۥ جَمِيعٗا فَيَجۡعَلَهُۥ فِي جَهَنَّمَۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 8:37Don Allah Ya ware mummuna daga kyakkyawa, Ya kuma haɗa mummuna wani a kan wani, sannan Ya tattara shi gaba ɗaya cikin Jahannama. Waɗannan su ne asararru. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, kafirai suna ɓatar da dukiyoyinsu don su samu ƙarfin yaƙar Musulmi, su hana mutane shiga addinin Musulunci. To za su kashe dukiyoyin nasu, amma daga ƙarshe wannan zai zama nadama a gare su, domin za su gane cewa sun yi aikin banza wanda ba zai amfane su ba, a ƙarshe kuma a karya su, a yi galaba a kansu. Waɗanda suka kafirta kuwa Allah zai tattara su cikin wutar Jahannama ya azabtar da su a cikinta, domin ya rarrabe tsakanin muminai masu kyakkyawan hali da kafirai masu mummunan hali. Muminai su tafi Aljanna kafirai kuma su tafi wutar Jahannama. Allah ya tattara kafirai masu miyagun halaye a cikin wutar Jahannama wasu kan wasu. Waɗannan kafiran su ne suka yi hasara duniya da lahira.
قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِن يَنتَهُواْ يُغۡفَرۡ لَهُم مَّا قَدۡ سَلَفَ وَإِن يَعُودُواْ فَقَدۡ مَضَتۡ سُنَّتُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 8:38Ka ce da waɗanda suka kafirta idan suka daina, to za a gafarta musu abin da ya riga ya wuce, idan kuma suka koma to fa ba shakka al’adar mutanen farko ta gabata.
وَقَٰتِلُوهُمۡ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتۡنَةٞ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ كُلُّهُۥ لِلَّهِۚ فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِمَا يَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Open ayah 8:39Kuma ku yaƙe su har sai ya zamanto ba wata fitina, addini kuma ya zamanto dukkaninsa na Allah. Sannan idan suka daina, to lalle Allah Mai ganin abin da suke aikatawa ne.
وَإِن تَوَلَّوۡاْ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَوۡلَىٰكُمۡۚ نِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ
Open ayah 8:40Idan kuma suka ba da baya, to ku sani cewa, Allah (Shi ne) Majiɓincin al’amarinku. Madalla da wannan Majiɓinci, kuma madalla da wannan Mai taimako. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya faɗa wa kafiran Ƙuraishawa cewa, idan sun bar kafircin da suke a kai, sun daina yaƙar Musulmi, to Allah zai gafarta musu zunubansu. Idan kuwa suka ci gaba, to sun ga dai abin da ya aikata gare su a ranar yaƙin Badar da kuma yadda ya hallaka al’ummomin da suka gabata waɗanda suka ƙaryata annabawansu. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai su yaƙi kafirai domin su kawar da shirka wadda za ta zama fitina ga mutane, kuma addini ya zamana na Allah ne tsantsa. Idan kuwa kafirai sun haɗu sun bar kafircin da suke yi da yaƙar muminai, to Allah yana ganin duk abin da suke aikatawa, kuma zai yi musu sakayya a kai. Idan kuwa sun bijire suka kafe a kan yaƙar muminai da kafircinsu, to Allah ya tabbatar wa muminai da su sakankance cewa, shi ne majiɓincinsu mai taimaka musu ya ba su nasara a kan waɗannan kafirai; madalla kuwa da mai taimakon masoyansa mai ba su nasara a kan maƙiyansu.
۞وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا غَنِمۡتُم مِّن شَيۡءٖ فَأَنَّ لِلَّهِ خُمُسَهُۥ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا يَوۡمَ ٱلۡفُرۡقَانِ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Open ayah 8:41Kuma ku sani cewa duk abin da kuka samu na ganima to lalle ɗaya bisa biyar na Allah ne da Manzo da kuma makusantan (Annabi), da marayu da kuma miskinai da kuma matafiya, idan kun kasance kun yi imani da Allah da kuma abin da Muka saukar wa bawanmu ranar rabewa (ranar yaƙin Badar) ranar da ƙungiyoyin nan biyu suka haɗu. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai.
إِذۡ أَنتُم بِٱلۡعُدۡوَةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُم بِٱلۡعُدۡوَةِ ٱلۡقُصۡوَىٰ وَٱلرَّكۡبُ أَسۡفَلَ مِنكُمۡۚ وَلَوۡ تَوَاعَدتُّمۡ لَٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِي ٱلۡمِيعَٰدِ وَلَٰكِن لِّيَقۡضِيَ ٱللَّهُ أَمۡرٗا كَانَ مَفۡعُولٗا لِّيَهۡلِكَ مَنۡ هَلَكَ عَنۢ بَيِّنَةٖ وَيَحۡيَىٰ مَنۡ حَيَّ عَنۢ بَيِّنَةٖۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَسَمِيعٌ عَلِيمٌ
Open ayah 8:42Ku tuna lokacin da kuke a gacin da ya fi kusa (da Madina) su kuma suna gacin da ya fi nisa, ayarin (Abu Sufyan) kuwa yana ƙasa da ku. Da kuwa kun yi alƙawarin (haɗuwa a Badar) to babu shakka da kun saɓa wajen cika alƙawarin, sai dai kuma wannan ya faru ne saboda Allah Ya zartar da al’amarin da ya zamanto mai faruwa ne, don wanda ya hallaka ya hallaka da dalili, kuma wanda kuma ya rayu ya rayu da dalili. Lalle Allah Mai ji ne Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da muminai cewa, dukiyar da suka samu daga kafirai abokan faɗansu bayan sun yi nasara a kansu ganima ce a gare su. Yadda rabonta zai kasance kuwa shi ne, ɗaya bisa biyar na Allah ne da Manzonsa (ﷺ) da makusantansa, wato ‘ya’yan Hashim da ‘ya’yan Al-Muɗɗalib da marayu da miskinai da kuma matafiya masu buƙatar guziri, sauran kashi huɗu kuwa na mayaƙa ne. Wannan shi ne tanadin da Allah ya yi wa muminai idan har sun yi imani da Allah (Mai tsarki da daukaka) da abin da ya saukar wa bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ) na ayoyin Alƙur’ani, ranar da Allah ya rabe tsakanin ƙarya da gaskiya, wato ranar da rundunar Musulmi ta haɗu da rundunar kafirai a filin Badar. Allah mai iko ne a kan komai, don haka ya ba wa Musulmi nasara a kan kafirai duk da rashin yawansu, ya karya kafirai duk da tarin yawansu da tanadinsu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Shaƙiƙu daga wani mutum daga ƙabilar Banu Ƙaini ya ce: “Na haɗu da Manzon Allah (ﷺ) a Wadil Ƙura yana taro wani doki sai na ce masa: “Ya Manzon Allah, me za ka ce a kan dukiyar ganima?” Sai ya ce: “Kaso ɗaya bisa biyar na Allah ne, kaso huɗun kuma na mayaƙa ne.” Sai na ce: “Wani bai fi wani cancanta ba?” Sai ya ce: “E, ko da kibiyar da ɗayanku zai ka ciro ta daga kwarinta, shi bai fi ɗan’uwansa Musulmi cancantarta ba.” [Abu Ya’ala #7179, At-Tahawi, Sharhu Ma’anil Athar #5198, Al-Baihaƙi, As-Sunan Al-Kubra #18012]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tuna wa muminai lokacin da suke filin Badar ta ɓangaren da ya fi kusa da Madina, su kuma kafirai suna ɓangaren da ya fi nisa da ita, su kuma ayarin da Abu Sufyan yake jagoranta mai ɗauke da kayan kasuwanci na Ƙuraishawa suna ƙasa da su, watau a gaɓar kwazazzabo. Allah ya nuna musu cewa, da a ce alƙawari ne su Musulmi suka yi da mushirikai a kan za su haɗu a filin Badar, to da sun saɓa wajen cika alƙawarin. Sai dai Allah ya riga ya shirya wannan haɗuwa don ya zartar da al’amarin da ya riga ya ƙaddara sai ya faru, don mai hallaka ya hallaka ta hanyar ci gaba da kafiricinsa bayan tsayuwar hujja a kansa, sannan wanda zai yi imani ya yi imani bayan hujja ta bayyana gare shi. Kuma lalle Allah mai ji ne masanin komai, zai yi wa kowa sakayya a kan aikinsa mai kyau ko mummuna.
إِذۡ يُرِيكَهُمُ ٱللَّهُ فِي مَنَامِكَ قَلِيلٗاۖ وَلَوۡ أَرَىٰكَهُمۡ كَثِيرٗا لَّفَشِلۡتُمۡ وَلَتَنَٰزَعۡتُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ سَلَّمَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Open ayah 8:43Ka tuna lokacin da Allah Yake nuna maka su cikin baccinka suna ‘yan kaɗan; da kuwa Ya nuna maka su da yawa fal, to ba shakka da kun tsorata kuma lalle da kun yi jayayya a cikin al’amarin, sai dai kuma Allah Ya kiyaye. Lalle Shi Masanin abin da ke zukata ne.
وَإِذۡ يُرِيكُمُوهُمۡ إِذِ ٱلۡتَقَيۡتُمۡ فِيٓ أَعۡيُنِكُمۡ قَلِيلٗا وَيُقَلِّلُكُمۡ فِيٓ أَعۡيُنِهِمۡ لِيَقۡضِيَ ٱللَّهُ أَمۡرٗا كَانَ مَفۡعُولٗاۗ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Open ayah 8:44Ku kuma tuna lokacin da Yake nuna muku su a yayin da kuka gamu suna ‘yan kaɗan a idanuwanku, Yake kuma ƙarantar da ku a idonsu, saboda Allah Ya hukunta al’amarin da yake mai afkuwa ne. Kuma wurin Allah ne ake mayar da duka al’amura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana magana a kan mafarkin da Annabi (ﷺ) ya yi ne, inda Allah ya nuna masa adadin kafirai ‘yan kaɗan. Da safe sai ya faɗa wa sahabbansa abin da ya gani a mafarki, sai suka yi murna sosai, suka samu ƙarfin gwiwa, suka yi ta zumuɗin haɗuwa da abokan gabarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma yake sanar da shi cewa, da ya nuna masa su suna da yawa a cikin barcinsa, sannan ya farka ya sanar da muminai abin da ya gani, to da sun tsorata, gwiwarsu kuma ta yi sanyi, sun yi jayayya game da al’amarin yaƙi da waɗannan kafirai, to amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kiyaye haka ba ta faru ba. Lalle Allah shi masanin abubuwan da ke cikin zukata ne na imani ko na kafirci ko waswasi. To domin a tabbatar da abin da Annabi (ﷺ) ya gani a mafarki sai Allah ya nuna wa Musulmi yawan kafirai ‘yan kaɗan domin su sami ƙarfin gwiwar shiga yaƙin. Su kuma kafirai sai ya nuna musu adadin Musulmi ‘yan kaɗan domin su rena su, su zaci yaƙar su ba wani abin a zo a gani ne ba, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zartar da al’amarin da ya ƙaddara babu makawa sai ya auku na wannan yaƙin da nasarar da Musulmi suka samu da hallaka kafirai. Wurin Allah ne kaɗai kuwa ake mayar da dukkan al’amura, shi ne mai yin hukunci da adalci.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا لَقِيتُمۡ فِئَةٗ فَٱثۡبُتُواْ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا لَّعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Open ayah 8:45Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka haɗu da wata ƙungiya (ta mayaƙa), to sai ku dage, ku kuma ambaci Allah da yawa, don ku rabauta.
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَنَٰزَعُواْ فَتَفۡشَلُواْ وَتَذۡهَبَ رِيحُكُمۡۖ وَٱصۡبِرُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 8:46Kuma ku bi Allah da Manzonsa, kada ku rarrabu sai ku zama matsorata kuma ƙarfinku ya tafi; ku kuma yi haƙuri. Lalle Allah Yana tare da masu haƙuri.
وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بَطَرٗا وَرِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطٞ
Open ayah 8:47Kada kuma ku zama kamar waɗanda suka fito daga gidajensu don fariya da kuma nuna wa mutane (watau riya), suna kuma hana (mutane) bin hanyar Allah. Allah kuwa Mai kewaye abin da suke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da cewa, idan sun haɗu da kafirai abokan faɗansu, to su dage wajen yaƙar su, su kuma dimanci ambaton Allah domin su rabauta. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Kada ku riƙa fatan haɗuwa da abokanan gaba, to amma idan kun haɗu da su, to sai ku yi haƙuri.” [Bukhari #3026, da Muslim #1741]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abu Aufa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) a wani yaƙi da aka fita ya tara sahabbai ya ce musu: “Ya ku mutane, kada ku riƙa fatan haɗuwa da abokan gaba, ku roƙi Allah lafiya, to amma idan kun haɗu da su, to ku yi haƙuri, ku sani Aljanna tana ƙarƙashin inuwowin takubba.” [Bukhari #2965, da Muslim #2509]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su yi masa biyayya, su yi wa Manzonsa (ﷺ) biyayya, kada su yi saɓani a tsakaninsu sai su samu matsala, ƙarfinsu ya gushe, gwiwoyinsu su yi sanyi, domin Allah yana tare da masu haƙuri. Ya kuma hana su su zamanto kamar kafiran Ƙuraishawa waɗanda suka baro gidajensu don kawai su yi yaƙi da gaskiya, kuma su riƙa yi wa mutane alfahari da yawansu, su hana su shiga addinin Musulunci. Allah kuma mai kewayewa ne game da duk abin da suke aikatawa.
وَإِذۡ زَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَقَالَ لَا غَالِبَ لَكُمُ ٱلۡيَوۡمَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَإِنِّي جَارٞ لَّكُمۡۖ فَلَمَّا تَرَآءَتِ ٱلۡفِئَتَانِ نَكَصَ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ وَقَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكُمۡ إِنِّيٓ أَرَىٰ مَا لَا تَرَوۡنَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَۚ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Open ayah 8:48Kuma ku tuna lokacin da Shaiɗan ya ƙawata musu ayyukansu, ya kuma ce: “Babu wasu mutane a yau da za su yi galaba a kanku, lalle kuma ni maƙocinku ne.” Saboda haka lokacin da ƙungiyoyin biyu suka haɗu sai ya tsere a guje, ya kuma ce: “Lalle ni ba ruwana da ku, lalle ni ina ganin abin da ku ba kwa gani, lalle ni ina tsoron Allah. Allah kuwa Mai tsananin azaba ne.”
إِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ غَرَّ هَٰٓؤُلَآءِ دِينُهُمۡۗ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 8:49Ka tuna lokacin da munafuƙai da kuma waɗanda suke da rauni a zukatansu suke cewa: “Waɗannan addininsu ne ya ruɗe su.” Duk wanda ya dogara ga Allah kuwa to lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya tuna lokacin da Shaiɗan ya ƙawata wa kafiran Ƙuraishawa miyagun ayyukansu, ya nuna musu cewa, a yau babu mai yin galaba a kansu, kuma shi mai ba su kariya ne. To amma lokacin da ƙungiyar Musulmi suka haɗu da ta kafirai, suka yi arba da juna, sai Shaiɗan ya dawo yana faɗa wa kafirai cewa, shi ba ruwansa da su domin ya ga abin da ya fi ƙarfinsa, shi yana jin tsoron Allah. Allah kuwa mai tsananin uƙuba ne. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A ranar yaƙin Badar Iblis ya zo cikin rundunar shaiɗanu yana ɗauke da tutarsa ta yaƙi. Shaiɗan ya zo a kamannin wani mutum daga ƙabilar Banu Mudlij, wanda ake kira Suraƙatu ɗan Maliku ɗan Ju’shumin, ya ce wa mushirikai: “A yau babu wasu mutane da za su yi galaba a kanku, haƙiƙa kuma ni mai ba ku kariya ne.” Yayin da mutane suka ja daga, sai Manzon Allah (ﷺ) ya danƙi ƙasa a tafin hannunsa ya watsa a fuskokin mushirikai, sai suka juya da baya a guje. Sai Mala’ika Jibrilu ya nufi Iblisu lokacin yana riƙe da hannun wani mutum mushiriki, yana ganin Mala’ika Jibrilu sai ya fincike hannunsa ya juya baya a guje shi da jama’arsa, sai wani mutum ya ce masa: ‘Ya kai Suraƙatu, ba kai ne kake cewa za ka ba mu kariya ba?’ Sai ya ce: ‘Lalle ni ina ganin abin da ba kwa gani, haƙiƙa ni ina tsoron Allah. Allah kuwa mai tsananin uƙuba ne.’ Wato lokacin da Shaiɗan ya ga mala’iku.” [Ibn Jarir, Al-Tafsir #1683; da Ibn Abi Hatim, At-Tafsir Juzi’i na 5, Shafi na 1715]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Annabi (ﷺ) ya tuna lokacin da munafuƙai masu cike da shakka a zukatansu suke cewa, addinin Musulmi ne ya ruɗe su har suka tarki yaƙar Ƙuraishawa alhalin sun fi su yawa da ƙarfi. To amma sun manta da cewa, duk wanda ya mayar da al’amari duka ga Allah, to lalle Allah mabuwayi ne mai hikima, babu abin da ya fi ƙarfinsa, kuma yana ajiye komai a muhallinsa da ya dace, yana karya duk wanda ya cancanci ya karya shi.
وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ يَتَوَفَّى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ
Open ayah 8:50Kuma da za ka ga lokacin da mala’iku suke ɗaukan ran waɗanda suka kafirta, suna dukan fuskokinsu da kuma bayansu, suna kuma (cewa da su): “Ku ɗanɗani azabar ƙuna.”
ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ
Open ayah 8:51“Wannan (ya faru gare ku ne) saboda abin da hannayenku suka aikata, kuma lalle Allah ba Mai zaluntar bayi ne ba.”
كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيّٞ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Open ayah 8:52(Al’adar kafiran Makka) kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waɗanda suke gabaninsu. Sun kafirce wa ayoyin Allah, saboda haka Allah Ya kama su da zunubansu. Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mai tsananin uƙuba.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ لَمۡ يَكُ مُغَيِّرٗا نِّعۡمَةً أَنۡعَمَهَا عَلَىٰ قَوۡمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنفُسِهِمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 8:53Wannan (kuwa) saboda Allah bai kasance Mai canza wata ni’ima da Ya yi wa wasu mutane ba har sai sun canja halayensu, lalle Allah kuma Mai ji ne Masani.
كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَۚ وَكُلّٞ كَانُواْ ظَٰلِمِينَ
Open ayah 8:54Kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waɗanda suke gabaninsu. Sun ƙaryata ayoyin Ubangijinsu, sai Muka hallaka su saboda zunubansu, Muka kuma nutsar da mutanen Fir’auna (a cikin kogi). Dukkaninsu kuwa sun kasance azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, da a ce ya ga lokacin da mala’ikun mutuwa suke cizgar rayukan kafirai daga gangar jikinsu, suna dukan fuskokinsu da bayansu, to da ya ga wani babban abin tsoro; mala’iku suna yi musu gatse da cewa, su ɗanɗani azaba mai ƙuna saboda abin da suka aikata na kafirci da saɓon Allah. Kuma shi ba mai zaluntar bayinsa ba ne. Ya zo cikin wani hadisi Ƙudusi Allah yana cewa: “Ya ku bayina, lalle ni na haramta wa kaina zalunci, kuma na sanya shi ya zamanto haramun a tsakaninku, don haka kada ku zalunci junanku....” [Muslim #2577]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, al’adar kafiran Ƙuraishawa dangane da kafircinsu ta yi kama da al’adar mutanen Fir’auna da sauran al’ummomin da suka ƙaryata ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) a gabaninsu, kuma Allah ya hallaka su saboda kafircinsu da yawan saɓon Allah da suke yi. Lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) mai ƙarfi ne kuma mai tsananin uƙuba, don haka ba wani kafiri da zai gagare shi. Sai kuma ya bayyana cewa, ya hallakar da su ne saboda sun yi wa ni’imarsa butulci, sun kafirce masa bayan ya yi musu ni’ima, Allah kuwa ba ya canza ni’imar da ya yi wa wasu mutane har sai sun canza abin da ke tare da su, sun auka cikin kafirci da munanan ayyuka. Lalle Allah mai ji ne masanin komai. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake ambaton cewa, al’adar mushirikan Ƙuraishawa wajen ƙaryata gaskiya ta yi kama da al’adar mutanen Fir’auna a gabaninsu, waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah yayin da suka zo musu, sai Allah ya hallakar da su saboda zunubansu, ya kuma nutsar da mutanen Fir’auna a kogi. To duk waɗanda Allah ya halakar cikin kafiran farko da na Ƙuraishawa sun tabbata azzalumai ne.
إِنَّ شَرَّ ٱلدَّوَآبِّ عِندَ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 8:55Lalle mafi sharrin masu tafiya a bayan ƙasa a wurin Allah (su ne) waɗanda suka kafirta, don haka kuma su ba sa yin imani.
ٱلَّذِينَ عَٰهَدتَّ مِنۡهُمۡ ثُمَّ يَنقُضُونَ عَهۡدَهُمۡ فِي كُلِّ مَرَّةٖ وَهُمۡ لَا يَتَّقُونَ
Open ayah 8:56Waɗanda idan ka yi alƙawari da su sai su warware alƙawarinsu ko da yaushe, ba sa kuma kiyaye dokokin Allah (dangane da alƙawari).
فَإِمَّا تَثۡقَفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡحَرۡبِ فَشَرِّدۡ بِهِم مَّنۡ خَلۡفَهُمۡ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ
Open ayah 8:57Sannan idan ka haɗu da su a wurin yaƙi, to sai ka fatattaki na bayansu da su, don su (na bayan) sa wa’azantu.
وَإِمَّا تَخَافَنَّ مِن قَوۡمٍ خِيَانَةٗ فَٱنۢبِذۡ إِلَيۡهِمۡ عَلَىٰ سَوَآءٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡخَآئِنِينَ
Open ayah 8:58Kuma idan kana jin tsoron wani ha’inci daga wasu mutane (da ka yi sulhu da su), to sai ka jefar musu shi (sulhun) a bayyane (ba da ha’inci ba). Lalle Allah ba Ya son masu ha’inci.
وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ سَبَقُوٓاْۚ إِنَّهُمۡ لَا يُعۡجِزُونَ
Open ayah 8:59Kuma kada waɗanda suka kafirta su yi tsammanin sun tsere, lalle su ba za su gagari (Allah) ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, mafi sharrin halittun da suke tafiya a bayan ƙasa su ne waɗanda suka kafirta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya riga ya san ba za su yi imani ba. Waɗanda Manzon Allah (ﷺ) ya yi alƙawarin zaman lafiya da su, to amma sai suke warware alƙawarin a lokuta da dama kuma ba sa kiyaye dokokin Allah wajen cika alƙawarin da suka ɗauka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya yi wa kafirai uƙuba mai tsanani idan har ya haɗu da su a wurin yaƙi, ya fatattake su, don su zama wa’azi ga na bayansu. Amma mutanen da ya yi yarjejeniya da su, sai kuma yake jin tsoron kada su yaudare shi su warware alƙawarin da suka ɗauka na zaman lafiya da Musulmi saboda irin take-takensu da za su bayyana, to Allah ya umarce shi da ya yi watsi da wannan alƙawarin na zaman lafiya, domin su duka ɓangarorin su san da cewa, yanzu babu sauran alƙawarin zaman lafiya a tsakaninsu, don haka daga baya babu mai tuhumar Annabi (ﷺ) da cin amana, domin Allah ba ya son maciya amana. An karɓo daga Sulaimu ɗan Amiru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An yi yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Mu’awiya (Allah ya kara masa yarda) da Rumawa, sai ya zamanto yana ta yawo a cikin garuruwansu, har sai da lokacin yajejeniyar ya ƙare, sannan ya kai musu hari. Sai ya haɗu da wani mutum haye a kan dokinsa yana cewa: ‘Allahu Akbar! A cika alƙawari ban da yaudara.’ Da aka duba sai aka ga ashe Amiru ɗan Absatu ne. Sai Mu’awiya ya tambaye shi game da abin da yake faɗa, sai ya ce ya ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: ‘Duk wanda ya yi yarjejeniyar zaman lafiya da wasu mutane to kada ya warware alƙawari, kada kuma ya ɗaure shi tamau, ya bari har lokacin da aka ƙayyade ya ƙare, ko kuma ya jefar musu da alƙawarinsu a sarari.’ Sai Mu’awiya ya janye rundunarsa.” [Abu Dawud #2759, da Tirmizi #1580, da Ahmad #17015]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk wani mayaudari yana da tutarsa a ranar alƙiyama, za a ɗaga masa ita gwargwadon yawan yaudararsa. Haƙiƙa babu mayaudarin da yaudararsa ta kai girman yaudarar shugaban jama’a.” [Muslim #1738]. Sai kuma Allah ya bayyana cewa, kada kafirai su taɓa tsammanin cewa sun kuɓuce wa Allah ba zai iya kama su ba; babu yadda za su yi su kuɓuce wa Allah ko su gagare shi domin shi mai cikakken iko ne a kan komai.
وَأَعِدُّواْ لَهُم مَّا ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن قُوَّةٖ وَمِن رِّبَاطِ ٱلۡخَيۡلِ تُرۡهِبُونَ بِهِۦ عَدُوَّ ٱللَّهِ وَعَدُوَّكُمۡ وَءَاخَرِينَ مِن دُونِهِمۡ لَا تَعۡلَمُونَهُمُ ٱللَّهُ يَعۡلَمُهُمۡۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِن شَيۡءٖ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يُوَفَّ إِلَيۡكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تُظۡلَمُونَ
Open ayah 8:60Ku yi musu tanadin abin da kuke iyawa na ƙarfi da kuma tanadin ɗaurarrun dawakai, kuna tsorata maƙiya Allah kuma maƙiyanku da shi (tanadin), har kuma da wasu ban da su da ba ku san su ba, Allah ne kawai Ya san su. Kuma duk irin abin da kuka ciyar cikin hanyar Allah za a cika muku (ladanku) ba kuwa za a zalunce ku ba.
۞وَإِن جَنَحُواْ لِلسَّلۡمِ فَٱجۡنَحۡ لَهَا وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 8:61Idan kuma suka karkato ga sulhu, to sai kai ma ka karkato gare shi, ka kuma dogara ga Allah. Lalle Shi Mai ji ne Masani.
وَإِن يُرِيدُوٓاْ أَن يَخۡدَعُوكَ فَإِنَّ حَسۡبَكَ ٱللَّهُۚ هُوَ ٱلَّذِيٓ أَيَّدَكَ بِنَصۡرِهِۦ وَبِٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 8:62Idan kuma suka yi niyyar yaudarar ka, to lalle Allah Ya ishe ka. Shi ne wanda Ya ƙarfafe ka da taimakonsa da kuma muminai.
وَأَلَّفَ بَيۡنَ قُلُوبِهِمۡۚ لَوۡ أَنفَقۡتَ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا مَّآ أَلَّفۡتَ بَيۡنَ قُلُوبِهِمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ أَلَّفَ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّهُۥ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 8:63Ya kuma haɗa tsakanin zukatansu. Idan da za ka kashe duk abin da yake bayan ƙasa gaba ɗaya ba za ka iya haɗa tsakanin zukatansu ba, amma kuma Allah Ya haɗe tsakaninsu. Lalle Shi Mabuwayi ne Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da su yi wa maƙiyansu kafirai kyakkyawan tanadi na ƙarfin makamai da dawakan yaƙi don ɗaukaka addinin Allah. Waɗanda da su ne za su riƙa tsorata maƙiya Allah kuma maƙiyansu da ma wasu mutanen da su ba su san su ba, Allah ne kawai ya san su. Kuma ya bayyana musu cewa, dukiyoyinsu da suke kashewa saboda Allah, zai ba su cikakken ladansu a ranar alƙiyama ba tare da ya rage musu komai ba. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya karkata ga sulhu idan ya ga kafiran da suke yaƙar sa su ma sun karkato ga neman sulhu, ya kuma miƙa duk al’amuransa ga Allah; lalle Allah mai ji ne masanin komai. Sannan ya sanar da shi cewa, idan kafiran suna neman sulhu ne da shi domin su yaudare shi, to Allah shi kaɗai ya ishe shi, kuma zai taimaka masa a kansu, kuma shi ne wanda ya ƙarfafe shi da nasararsa da kuma sahabbansa waɗanda suka yi imani da shi. Shi ya haɗa tsakanin zukatansu da Musulunci. Da a ce Manzon Allah (ﷺ) zai kashe duk dukiyar da take bayan ƙasa don ya haɗa tsakanin zukatansu da ba zai iya ba, to amma ga shi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haɗa tsakaninsu. Lalle shi mubuwayi ne mai hikima. An karɓo daga Abdullahi ɗan Zaidu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Yayin da Annabi (ﷺ) ya ci Hunainu da yaƙi, sai ya raba ganima, ya ba waɗanda ake lallashin zukatansu. Sai ya samu labarin su ma mutanen Madina suna son su samu nasu rabon na dukiyar ganima. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya tashi cikinsu ya yi musu huɗuba, ya gode wa Allah, ya kuma yabe shi, sannan ya ce: “Ya ku mutanen Madina, ashe ban same ku ɓatattu ba Allah ya shiryar da ku a sanadiyyata? Ban kuma same ku ba ku da komai ba, Allah ya wadatar da ku saboda ni? Ban same ku kawunanku a rarrabe ba, Allah ya haɗa kanku a dalilina?” Su kuma mutanen Madina suna amsa masa da cewa: Allah da Manzonsa su ne suka fi abin da za su goranta da shi. Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Ba za ku ba ni amsa ba?” Su kuma suna cewa: Allah da Manzonsa ne suka fi abin gorantawa. Sai ya ce: “Ai da kun ga dama sai ku ce kaza da kaza, abu kaza da kaza sun faru.” Ya ambaci wasu abubuwa. “Sai kuma ya ce: “Shin ba za ku so idan mutane sun tafi da awaki da raƙuma ku kuma ku koma gidajenku da Manzon Allah ba? Mutanen Madina riga ce ‘yar ciki, sauran mutane kuwa mayafi ne. Ba domin falalar hijira ba da na zaɓi in kasance ɗaya daga cikin mutanen Madina. Da a ce mutane za su bi wani kwazazzabo ko wata hanyar tsakanin duwatsu, da ni na bi kwazazzabon mutanen Madina da hanyarsu. Lalle ku a bayana za ku gamu da son kai, to ku yi haƙuri har ku haɗu da ni a Tabkina.” [Bukhari #4330, da Muslim #1061].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَسۡبُكَ ٱللَّهُ وَمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 8:64Ya kai wannan Annabi, Allah Ya ishe ka, kai da kuma muminai waɗanda suka bi ka.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ عَلَى ٱلۡقِتَالِۚ إِن يَكُن مِّنكُمۡ عِشۡرُونَ صَٰبِرُونَ يَغۡلِبُواْ مِاْئَتَيۡنِۚ وَإِن يَكُن مِّنكُم مِّاْئَةٞ يَغۡلِبُوٓاْ أَلۡفٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ
Open ayah 8:65Ya kai wannan Annabi, ka zaburar da muminai a kan yaƙi. Idan daga cikinku akwai (mutum) ashirin masu haƙuri to za su rinjayi (mutum) ɗari biyu (kafirai). Idan kuma daga cikinku akwai (mutum) ɗari to za su rinjayi (mutum) dubu daga waɗanda suka kafirta, saboda su mutane ne da ba sa ganewa.
ٱلۡـَٰٔنَ خَفَّفَ ٱللَّهُ عَنكُمۡ وَعَلِمَ أَنَّ فِيكُمۡ ضَعۡفٗاۚ فَإِن يَكُن مِّنكُم مِّاْئَةٞ صَابِرَةٞ يَغۡلِبُواْ مِاْئَتَيۡنِۚ وَإِن يَكُن مِّنكُمۡ أَلۡفٞ يَغۡلِبُوٓاْ أَلۡفَيۡنِ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 8:66Yanzu Allah Ya sassauta muku, Ya kuma san cewa a cikinku akwai raunana, saboda haka idan ya zamanto a cikinku akwai (mutum) ɗari masu haƙuri to za su rinjayi (mutum) ɗari biyu (kafirai). Idan kuma ya kasance akwai (mutum) dubu daga cikinku to za su rinjayi (kafirai) dubu biyu da izinin Allah. Allah kuma Yana tare da masu haƙuri. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar wa da Annabi (ﷺ) cewa, ya isar masa, kuma ya isar wa mabiyansa muminai, zai iya yi musu duk wani gatanci na al’amarin addini da rayuwa, kuma zai ba su nasara a kan maƙiyansu. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya kwaɗaitar da muminai sosai a bisa yaƙi, su yi haƙuri a lokacin arangama da maƙiyansu, su dage sosai wajen yaƙar su. Idan aka samu mutane ashirin masu haƙuri daga cikinsu, to za su rinjayi kafirai ɗari biyu. Idan kuma aka samu Musulmai ɗari to za su rinjayi kafirai dubu, saboda su kafirai mutane ne waɗanda suka jahilci sakamakon da Allah yake ba wa waɗanda suka yi imani da shi suka bi dokokinsa da abin da ya tanadar wa mayaƙa don ɗaukaka addininsa. Sai daga baya kuma aka sassauta wannan hukuncin, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yanzu an sassauta musu domin ya san a cikinsu akwai raunana waɗanda ɗayansu ba zai iya karawa da kafirai goma ba shi kaɗai, to sai ya wajabta wa kowane ɗaya daga cikinsu ya tsaya ya fuskanci kafirai biyu maimakon goma, tare da yi musu albishir cewa idan akwai Musulmi masu haƙuri ɗari, to za su yi galaba a kan kafirai ɗari biyu; idan kuma akwai Musulmi dubu, to za su rinjayi kafirai dubu biyu cikin taimakon Allah, kuma Allah yana tare da masu haƙuri. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: “Lokacin da faɗar Allah ta sauka cewa: “Idan daga cikinku akwai mutum ashirin masu haƙuri, to za su rinjayi mutum ɗari biyu,” wannan hukunci ya yi wa Musulmi nauyi sosai, yayin da aka wajabta wa mutum ɗaya kada ya guje wa mutum goma. To sai sauƙi ya zo daga baya, Allah ya saukar da faɗarsa cewa: (Yanzu Allah ya sassauta muku, ya kuma san cewa a cikinku akwai raunana, saboda haka idan ya kasance akwai mutum ɗari masu haƙuri daga cikinku, to za su rinjayi kafirai ɗari biyu da izinin Allah.) To yayin da ya yi musu sassaucin adadi sai haƙuri ya ragu gwargwadon sassaucin da aka yi musu.” [Bukhari #4653].
مَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَكُونَ لَهُۥٓ أَسۡرَىٰ حَتَّىٰ يُثۡخِنَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ تُرِيدُونَ عَرَضَ ٱلدُّنۡيَا وَٱللَّهُ يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 8:67Bai kamata ga wani annabi ya kasance yana da wasu fursunonin yaƙi ba har sai ya yi kisan (abokan gaba) sosai a bayan ƙasa. Kuna nufin abin duniya Allah kuma Yana nufin lahira. Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima.
لَّوۡلَا كِتَٰبٞ مِّنَ ٱللَّهِ سَبَقَ لَمَسَّكُمۡ فِيمَآ أَخَذۡتُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Open ayah 8:68Ba don wani hukunci ya riga ya gabata daga Allah ba, tabbas da azaba mai girma ta shafe ku game da abin da kuka karɓa (na fansa).
فَكُلُواْ مِمَّا غَنِمۡتُمۡ حَلَٰلٗا طَيِّبٗاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 8:69To sai ku ci daga abin da kuka samu na ganima halal, tsattsarka. Kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّمَن فِيٓ أَيۡدِيكُم مِّنَ ٱلۡأَسۡرَىٰٓ إِن يَعۡلَمِ ٱللَّهُ فِي قُلُوبِكُمۡ خَيۡرٗا يُؤۡتِكُمۡ خَيۡرٗا مِّمَّآ أُخِذَ مِنكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 8:70Ya kai wannan Annabi, ka ce da fursunonin da suke a hannayenku: “Idan dai har Allah Ya san akwai wani alheri a zukatanku, to zai ba ku fiye da abin da aka karɓa daga wurinku Ya kuma gafarta muku. Allah kuwa Mai gafara ne Mai jin ƙai.”
وَإِن يُرِيدُواْ خِيَانَتَكَ فَقَدۡ خَانُواْ ٱللَّهَ مِن قَبۡلُ فَأَمۡكَنَ مِنۡهُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Open ayah 8:71Idan kuwa suna nufin ha’intar ka ne, to haƙiƙa da can ma sun ha’inci Allah, saboda haka Ya ɗora (ka) a kansu. Allah kuwa Masani ne Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah yana bayanin hukunce-hukuncen da suka shafi fursunonin yaƙi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, bai kamata ya kama wasu ribatattun yaƙi ba har sai ya kwarar da jini a bayan ƙasa, wato ya yaƙe su ya raunana su ya ci nasara a kansu ta yadda ba za su iya sake tsokanar Musulmi da yaƙi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalance su da cewa, suna nufin samun wani ɗan abin duniya ne kaɗan don haka suka kama kafiran domin su biya fansa a sake su, alhali Allah yana nufin su da sakamakon lahira ne. Allah mubuwayi ne mai hikima cikin duk ayyukansa da hukunce-hukuncensa. Sannan ya bayyana cewa, ba don wani hukunci ya riga ya gabata ba daga Allah, ba shakka da wata azaba mai girma ta same su saboda kuɗin fansa da suka karɓa daga hannun kafiran Ƙuraishawa don su sakar musu ‘yan‘uwansu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Yayin da Manzon Allah (ﷺ) ya kama fursunonin yaƙi su saba’in, sai ya nemi shawarar Abubakar da Umar (Allah ya kara masa yarda) a kansu. Sai Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ya Annabin Allah, waɗannan mutane ‘ya’yan baffanninka ne da danginka, ina ganin zai fi kyau ka karɓi fansa daga wurinsu ka ƙara wa mayaƙanka ƙarfi da ita; ta yiwu Allah ya shirye su su karɓi Musulunci.” Sai shi kuma Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A’a, wallahi ya Manzon Allah, ni ba na tare da ra’ayin Abubakar. Ni ina ganin ka ba mu dama mu gama da su, ka sa Aliyyu ya sare kan Aƙilu ɗan Abu Ɗalibi, ni kuma ka ba ni umarni in sare kan wane.” ya ambaci sunan wani ɗan’uwansa, “Saboda waɗannan mutane su ne shugabannin kafirci kuma manyan kafirai.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya fi karkata ga shawarar Abubakar a kan ta Umar. Kashegari sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya zo ya samu Manzon Allah (ﷺ) da Abubakar (Allah ya kara masa yarda) zaune suna kuka, sai ya ce: “Ya Manzon Allah, ka faɗa min abin da kai da abokinka kuke yi wa kuka, idan na ji ni ma zan iya kukan sai in yi; idan ma na kasa yin kukan sai in ƙaƙaro shi don in taya ku.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ina kuka ne saboda shawarar da abokanka suka ba ni na karɓar fansa. Haƙiƙa an bijiro mini da azabarsu dab da ni fiye da wannan bishiyar.” Ya nuna masa wata bishiya da take kusa da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi. [Muslim #1763]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su ci abin da suka samu na ganima a matsayin halal tsarkakakke, su kuma kiyaye dokokin Allah, lalle Allah mai gafara ne mai jin ƙai. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ba a halatta wa waɗanda suka gabace mu cin dukiyar ganima ba, amma mu Allah Tabaraka wa Ta’ala ya dubi rauninmu da kasawarmu sai ya halatta mana ita.” [Bukhari #3124, da Muslim #521]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi da ya faɗa wa waɗannan kamammun yaƙin Badar cewa, idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya san akwai imani ingantacce a cikin zukatansu, to zai ba su abin da ya fi abin da aka karɓa daga hannuwansu na dukiyar fansa, kuma zai gafarta musu zunubbansu da suka yi a baya. Allah mai gafara ne mai jin ƙai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu mutanen Madina sun nemi izinin Manzon Allah (ﷺ) suka ce: “Ya Manzon Allah, ka ba mu izini mu fasa karɓar kuɗin baffanka Abbas.” Sai ya ce: “Wallahi kada ku bar masa ko dirhami guda.” [Bukhari #4018]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, idan so suke su ha’ince shi, to ai da ma can baya sun ha’inci Allah da kafircinsu da yaƙar Musulmi, sai Allah ya ɗora Musulmi a kansu. Allah kuma masani ne mai hikima.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُوٓاْ أُوْلَٰٓئِكَ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَمۡ يُهَاجِرُواْ مَا لَكُم مِّن وَلَٰيَتِهِم مِّن شَيۡءٍ حَتَّىٰ يُهَاجِرُواْۚ وَإِنِ ٱسۡتَنصَرُوكُمۡ فِي ٱلدِّينِ فَعَلَيۡكُمُ ٱلنَّصۡرُ إِلَّا عَلَىٰ قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٞۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Open ayah 8:72Lalle waɗanda suka yi imani kuma suka yi hijira, suka kuma yi yaƙi da dukiyoyinsu da kuma rayukansu don Allah, da waɗanda kuma suka sauki (muminai masu hijira) suka kuma taimaka (wajen yaƙi), to waɗannan masu ƙaunar juna ne. Waɗanda kuma suka yi imani ba su kuma yi hijira ba, to babu jiɓintar al’amari a tsakaninku har sai sun yi hijira. Idan kuma suka nemi taimakonku cikin (al’amarin) addini to lalle ne ku taimake su, sai dai idan game da wasu mutane ne waɗanda yake da akwai wani alƙawari a tsakaninku da su. Allah kuma Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.
وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٍۚ إِلَّا تَفۡعَلُوهُ تَكُن فِتۡنَةٞ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَفَسَادٞ كَبِيرٞ
Open ayah 8:73Waɗanda kuwa suka kafirta, su masu ƙaunar juna ne. Idan ku ma ba ku aikata haka ba, to za a samu wata fitina a bayan ƙasa da kuma wata ɓarna mai girma.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُوٓاْ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ
Open ayah 8:74Waɗanda kuma suka yi imani kuma suka yi hijira suka kuma yi yaƙi saboda Allah, da waɗanda kuma suka sauki (masu hijira) suka kuma taimaka, waɗannan su ne muminai na gaskiya. Suna da (sakamakon) gafara da kuma arziki na karamci.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنۢ بَعۡدُ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ مَعَكُمۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ مِنكُمۡۚ وَأُوْلُواْ ٱلۡأَرۡحَامِ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلَىٰ بِبَعۡضٖ فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ
Open ayah 8:75Waɗanda kuma suka yi imani daga baya, suka kuma yi hijira, suka kuma yi yaƙi tare da ku, to waɗannan suna cikinku. ‘Yan’uwa na jini kuma su ne suka fi cancantar (gadon) junansu a cikin Littafin Allah. Lalle Allah Masani ne ga komai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, lalle masu hijira waɗanda suka yi imani da duk abin da ya wajaba su yi imani da shi, suka bar garuruwansu da danginsu, suka ba da dukiyoyinsu don taimakon addinin Allah, kuma suka yi jihadi da rayukansu don Allah, da kuma mutanen Madina waɗanda suka ba wa Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa masu hijira masauki a gidajensu, suka taimaka musu a kan abokan gabansu, to waɗannan su ne masu ƙaunar juna. Ibnu Kasir yana cewa: “Manzon Allah (ﷺ) ya haɗa ‘yan’uwantaka tsakanin mutanen Makka masu hijira da mutanen Madina, mutum bibbiyu; suka kasance suna gadon juna fiye da yadda suke yi saboda dangantaka ta jini, har sai da Allah ya shafe wannan hukuncin da ayar gado.” [Ibn Kasir, Tafsir , Juzi’i na 4, Shafi na 95]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Masu hijira daga Makka lokacin da suka iso Madina, Musulmin Madina yana cin gadon mai hijira ban da danginsa na jini, saboda ‘yan’uwantakar da Annabi (ﷺ) ya ƙulla a tsakaninsu.” [Bukhari #6747]. Wasu malamai sun ce, abin nufi da cewa “waɗannan masu ƙaunar juna ne”, wato mutanen Makka da suka yiwo hijira da mutanen Madina da suka tarbe su masu taimakon junansu ne a kan mushirikai. A bisa wannan fassarar, hukuncin ayar yana nan ba a shafe shi ba. Amma yawancin malamai sun tafi ne a kan ra’ayin cewa an shafe ma’anar ayar da faɗin Allah (Mai tsarki da daukaka) cewa: “‘Yan’uwa na jini su ne suka fi cancantar (gadon) junansu a cikin Littafin Allah. Haƙiƙa Allah Masanin komai ne.” Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cewa, waɗanda suka yi imani amma suka ƙi baro garuruwansu na kafirci zuwa garin Musulunci, to su muminai babu wani al’amarinsu da za su jiɓinta ko su taimaka musu har sai sun bar garuruwan kafirci sun dawo garin Musulunci. Amma idan sun nemi muminai su taimake su a kan addini to su taimaka musu, sai dai idan abokan faɗan nasu wasu kafirai ne da muminai suke da yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu da su, to bai halatta su karya wannan yarjejeniya ba saboda waɗancan muminan da suka ƙi barin garuruwan kafirci. Allah mai ganin duk abin da suke aikatawa ne don haka kada su saɓa wa umarninsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗakar da muminai cewa, kafirai fa masoya ne ga junansu, to su ma muminai idan ba su aikata hakan ba, wato su ƙaunaci junansu, to lalle wata fitina za ta auku a bayan ƙasa da bazuwar ɓarna mai girma, tare da ɓata a cikin Musulmi, domin ƙarya za ta haɗe da gaskiya har wasu su kasa bambance su. Muminai da suka yi hijira suka yi yaƙi don ɗaukaka addinin Allah da mutanen Madina waɗanda suka ba wa masu hijira masaukai, suka taimaka musu suka taimaka wa addinin Allah, to waɗannan su ne muminai na haƙiƙa, kuma suna da gafara daga Allah da arziki na karamci. Waɗanda kuma suka yi imani bayan bayanin waɗancan hukunce-hukunce da suka gabata, kuma suka yi hijira daga garin kafirci zuwa garin Musulunci, suka kuma yi yaƙi don Allah, to waɗannan suna tare da masu hijira da mutanen Madina. Dangi su ne suka fi cancanta su gaji junansu a cikin hukuncin Allah. Lalle Allah masanin komai ne.