التوبة
At-Tawba
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بَرَآءَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦٓ إِلَى ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّم مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 9:1Allah da Manzonsa ba ruwansu da waɗanda kuka yi alƙawari da su daga cikin mushirikai.
فَسِيحُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ غَيۡرُ مُعۡجِزِي ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱللَّهَ مُخۡزِي ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 9:2To sai ku tafi ku wala a bayan ƙasa tsawon wata huɗu, kuma ku sani cewa ku ba za ku gagari Allah ba, kuma lalle Allah Mai wulaƙanta kafirai ne. A ayoyi goma sha biyar na farkon wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, shi da Manzonsa (ﷺ) ba ruwansu da alƙawarin da yake tsakanin Musulmi da mushirikai na zaman lafiya, sakamakon warware sharuɗɗan zaman lafiya da su mushirikai suka yi. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su tsawon wata huɗu su yi yawo a bayan ƙasa, su je duk inda suke so babu wani Musulmi da zai taɓa su. Lokacin kuma ya fara ne daga ranar sallar layya ta shekara ta tara, ya kuma ƙare a ranar goma ga watan Rabi’ul Akhir a shekara ta goma. Sai kuma Allah ya ja hankalinsu da cewa, su sani fa ba za su iya gagarar Allah ba, ba za su iya kuɓuce wa uƙubarsa ba idan ya yi nufin kama su. Kuma su sani Allah (Mai tsarki da daukaka) mai wulaƙanta kafirai ne.
وَأَذَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦٓ إِلَى ٱلنَّاسِ يَوۡمَ ٱلۡحَجِّ ٱلۡأَكۡبَرِ أَنَّ ٱللَّهَ بَرِيٓءٞ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ وَرَسُولُهُۥۚ فَإِن تُبۡتُمۡ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ غَيۡرُ مُعۡجِزِي ٱللَّهِۗ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
Open ayah 9:3Kuma sanarwa daga Allah da Manzonsa zuwa ga mutane ranar Babbar Salla cewa, lalle Allah da Manzonsa babu ruwansu da mushrikai. Amma idan kuka tuba, to shi ya fi alheri a gare ku, idan kuma kuka ba da baya, to ku sani lalle ku fa ba za ku gagari Allah ba. Kuma ka yi albishir ga waɗanda suka kafirta da azaba mai raɗadi.
إِلَّا ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّم مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ثُمَّ لَمۡ يَنقُصُوكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَمۡ يُظَٰهِرُواْ عَلَيۡكُمۡ أَحَدٗا فَأَتِمُّوٓاْ إِلَيۡهِمۡ عَهۡدَهُمۡ إِلَىٰ مُدَّتِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 9:4Sai fa waɗannan mushrikan da kuka yi alƙawari da su sannan kuma ba su rage muku wani abu ba (daga alƙawarin), ba su kuma taimaka wa wani a kanku ba, to sai ku cika musu alƙawarinsu har zuwa lokacinsu (da kuka ayyana). Lalle Allah Yana son masu taƙawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, wannan sanarwa ce daga Allah da Manzonsa zuwa ga mutane baki ɗaya, Musulmai da kafirai, a ranar sallar layya cewa, Allah ba ruwansa da mushirikai, hakanan Manzonsa ma ba shi ba su. Don haka idan sun yarda sun tuba, to hakan shi ne mafi alheri gare su, idan kuwa sun bijire to su sani cewa ba za su gagari Allah ba, kuma ba za su kuɓuta daga azabarsa ba. Don haka Annabi (ﷺ) ya yi wa kafirai albishir da wata azaba mai raɗaɗi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya togace wasu daga cikin kafirai waɗanda da ma akwai alƙawari tsakaninsu da muminai sannan suka cika wannan alƙawarin ba su warware shi ba; to waɗannan wajibi ne a kan muminai su cika musu alƙawarinsu har zuwa lokacin da aka yanka tsakaninsu da mushrikai ya zo ƙarshe. Lalle Allah yana son masu kiyaye dokokinsa kuma masu cika alƙawari ba sa warware shi. An karɓo daga Humaidu ɗan Abdurrahman ɗan Auf cewa, Abu Huraira yana cewa: Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya aike ni tare da masu shela a wannan aikin hajjin mu yi shela a Mina cewa: Daga wannan shekarar kada wani mushiriki ya sake zuwa aikin hajji, kuma kada wani ya sake yin ɗawafi a Ɗakin Allah tsirara. Sannan Manzon Allah (ﷺ) ya sake turo Aliyyu ɗan Abu Ɗalibi (Allah ya kara masa yarda) daga bisani ya sake yin wata shela cewa, ba ruwan Allah shi da Manzonsa da mushrikai. Abu Huraira ya ce: Sai Aliyyu ya yi shela tare da mu a ranar sallar layya ga mahajjata a Mina ya bayyana wannan bara’ar, kuma daga wannan shekarar kada wani mushiriki ya sake zuwa aikin hajji, kuma kada wani ya sake yin ɗawafi tsirara a Ɗakin Allah. [Bukhari #4655, da Muslim #1347].
فَإِذَا ٱنسَلَخَ ٱلۡأَشۡهُرُ ٱلۡحُرُمُ فَٱقۡتُلُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡ وَخُذُوهُمۡ وَٱحۡصُرُوهُمۡ وَٱقۡعُدُواْ لَهُمۡ كُلَّ مَرۡصَدٖۚ فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَخَلُّواْ سَبِيلَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 9:5To idan watanni masu alfarma suka wuce sai ku yaƙi mushrikai a duk inda kuka same su, ku kuma kama su ku tsare su ku kuma toshe musu kowace hanya. To amma idan sun tuba sun kuma tsai da salla kuma sun ba da zakka, to sai ku ƙyale su. Lalle Allah Mai gafara ne Mai jin ƙai.
وَإِنۡ أَحَدٞ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ٱسۡتَجَارَكَ فَأَجِرۡهُ حَتَّىٰ يَسۡمَعَ كَلَٰمَ ٱللَّهِ ثُمَّ أَبۡلِغۡهُ مَأۡمَنَهُۥۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 9:6Kuma idan wani daga mushrikai ya nemi mafaka a wurinka to sai ka ba shi mafaka har ya samu damar jin zancen Allah, sannan ka isar da shi wurin amincewarsa. Wannan kuwa saboda lalle su mutane ne da ba sa sanin (gaskiya). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai su kashe abokan gabarsu mushirikai duk inda suka same su bayan watanni masu alfarma sun shuɗe, kuma su kama su a matsayin fursinonin yaƙi, su kuma takura musu, su hana su yawatawa a bayan ƙasa, ko shigowa inda suke, su saka musu tsattsauran takunkumi, su tare duk wata hanyar bin su don su kama su su kashe ko su ɗaure. To amma idan sun tuba sun tsayar da sallolin farilla tare da cika sharuɗɗanta, suka kuma bayar da zakka ga waɗanda suka cancanta a ba, to sai Musulmi su ƙyale su kada su taɓa su. Lalle Allah mai gafara ne mai jin ƙai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bai wa Annabi (ﷺ) damar ya bayar da mafaka ga duk wani mushiriki da ya nemi a ba shi mafaka domin ya sami damar sauraren Alƙur’ani. Idan ya ƙi musulunta, to ya ƙyale shi ya koma ƙasarsa inda zai samu mafaka. Saboda su mutane ne waɗanda ba su san komai ba.
كَيۡفَ يَكُونُ لِلۡمُشۡرِكِينَ عَهۡدٌ عِندَ ٱللَّهِ وَعِندَ رَسُولِهِۦٓ إِلَّا ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّمۡ عِندَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۖ فَمَا ٱسۡتَقَٰمُواْ لَكُمۡ فَٱسۡتَقِيمُواْ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 9:7Ta yaya zai yiwu a samu wani alƙawari tsakanin Allah da Manzonsa da kuma mushirikai in ban da waɗanda kuka yi alƙawari da su a Masallaci mai alfarma? To matuƙar sun tsaya muku (bisa gaskiya) sai ku ma ku tsaya musu. Lalle Allah Yana son masu taƙawa.
كَيۡفَ وَإِن يَظۡهَرُواْ عَلَيۡكُمۡ لَا يَرۡقُبُواْ فِيكُمۡ إِلّٗا وَلَا ذِمَّةٗۚ يُرۡضُونَكُم بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَتَأۡبَىٰ قُلُوبُهُمۡ وَأَكۡثَرُهُمۡ فَٰسِقُونَ
Open ayah 9:8Ta yaya?! (haka zai faru) alhali idan suka yi nasara a kanku ba za su duba wani kusanci ba balle wani alƙawari game da ku? Suna yardar da ku ne da bakunansu, alhali kuwa zukatansu suna ƙi. Yawancinsu kuma fasiƙai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana dalilan da suka sa shi da Manzonsa (ﷺ) suka yi watsi da yarjejeniyar da suka ƙulla da kafirai. Allah kuma ya ba da umarnin yaƙar su da kama su. Yaya ma za a yi mushirikai su ƙulla wani alƙawari na zaman lafiya tsakaninsu da Allah da Manzonsa? Wannan ba abu ne mai yiwuwa ba, domin su mutane ne mayaudara, maciya amana. Don haka wajibi ne muminai su yaƙe su duk inda suka haɗu da su, sai dai an toge wasu mushirikai da suka yi yarjejeniyar zaman lafiya da su a Masallaci mai alfarma a ranar Sulhun Hudaibiyya, to matuƙar su sun tsaya a kan wannan alƙawarin ba su karya shi ba, to su ma Musulmi su tsaya musu a kansa kada ku karya shi, har zuwa lokacin ƙarewarsa. Lalle Allah yana son masu kiyaye dokokinsa. Annabi (ﷺ) ya yi alƙawarin zaman lafiya da ƙabilun Banu Bakra masu ƙawance da Ƙuraishawa a ranar Sulhun Hudaibiyya na tsawon lokacin da suka yi da Ƙuraishawan kansu. To bai warware wannan alƙawari ba, har sai da ƙabilar Ƙuraishawa da ƙabilar Banud Dil ɗan Bakara suka warware nasu. Sai Allah ya yi umarni da a cika wa sauran ƙabilun Banu Bakra alƙawarinsu har ƙarshen lokacin da aka ɗeba musu. Sannan Allah ya ci gaba da bayanin cewa, ta yaya ma wani alƙawarin zaman lafiya zai samu ga mushirikai waɗanda, idan suka samu nasara a kan muminai ba za su tausaya musu ko kaɗan ba, ba kuma za su duba wani kusanci ko dangantaka ko wani alƙawari ba? Da bakunansu kam za su riƙa faɗa wa muminai maganganu masu daɗi don su yarda da su, amma zukatansu sun ƙi amincewa da abin da bakunansu suke faɗa. Yawancincu kuma fasiƙai ne.
ٱشۡتَرَوۡاْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلٗا فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِهِۦٓۚ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 9:9Sun musanya ayoyin Allah da ɗan kuɗi ƙanƙani, sannan suka toshe hanyarsa. Lalle su dai abin da suke aikatawa ya munana.
لَا يَرۡقُبُونَ فِي مُؤۡمِنٍ إِلّٗا وَلَا ذِمَّةٗۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُعۡتَدُونَ
Open ayah 9:10Ba sa duban wani kusanci na zumunci da wani mumini ballantana kuma wani alƙawari. Waɗannan kuma su ne masu ƙetare iyaka.
فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَإِخۡوَٰنُكُمۡ فِي ٱلدِّينِۗ وَنُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 9:11To idan sun tuba, suka kuma tsayar da salla kuma suka ba da zakka, to sun zama ‘yan’uwanku a cikin addini. Muna kuwa bayanin ayoyi ne filla-filla ga mutane da suke da sani.
وَإِن نَّكَثُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُم مِّنۢ بَعۡدِ عَهۡدِهِمۡ وَطَعَنُواْ فِي دِينِكُمۡ فَقَٰتِلُوٓاْ أَئِمَّةَ ٱلۡكُفۡرِ إِنَّهُمۡ لَآ أَيۡمَٰنَ لَهُمۡ لَعَلَّهُمۡ يَنتَهُونَ
Open ayah 9:12Idan kuma suka warware rantsuwarsu bayan ɗaukar alƙawarinsu, suka kuma soki addininku, to sai ku yaƙi shugabannin kafirci, don kuwa ba su da alƙawari, ko yin haka zai sa su daina. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, mushirikai sun musanya ayoyin Allah da wani jin daɗi kaɗan na duniya, don haka suka hana kawunansu karɓar gaskiya kuma suka hana wasu su karɓa. Lalle wannan abin da suke yi ya yi muni matuƙa. Idan kuwa sun yi nasara a kan wani mumini, to fa ba ruwansu da duba Allah ko kusanci ko alƙawari. Ba shakka waɗannan mutane sune ‘yan ta’adda. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa muminai cewa, idan mushirikai suka tuba suka bar shirka, kuma suka tsayar da sallolin farilla yadda ya dace, suka fitar da zakkar dukiyoyinsu, to sun zama ‘yan’uwan muminai a Musulunci, domin Allah yana bayanin ayoyi ne ga mutanen da suke sanin gaskiya suke yin aiki da ita. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara da cewa, idan mushirikai suka karya alƙawarin da suka yi da Musulmi, suka soki addininsu suka wulaƙanta shi, to Musulmi su fito su yaƙi shugabannin kafirci, don kuwa sun nuna alƙawarin da suka ɗauka ba da gaske suke ba. Wannan shi zai sa su daina abin da suke yi na kafirci da ɓata Musulunci.
أَلَا تُقَٰتِلُونَ قَوۡمٗا نَّكَثُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ وَهَمُّواْ بِإِخۡرَاجِ ٱلرَّسُولِ وَهُم بَدَءُوكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٍۚ أَتَخۡشَوۡنَهُمۡۚ فَٱللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخۡشَوۡهُ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 9:13Yanzu ba za ku yaƙi mutanen da suka warware alƙawarinsu ba, kuma (tun farko) sun yi nufin fitar da Manzo (daga Makka), su ne kuma suka fara far muku da yaƙi? Yanzu kwa riƙa tsoron su? To Allah ne Ya fi cancantar ku ji tsoron Sa idan kun kasance muminai.
قَٰتِلُوهُمۡ يُعَذِّبۡهُمُ ٱللَّهُ بِأَيۡدِيكُمۡ وَيُخۡزِهِمۡ وَيَنصُرۡكُمۡ عَلَيۡهِمۡ وَيَشۡفِ صُدُورَ قَوۡمٖ مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 9:14Ku yaƙe su, Allah zai azabtar da su ta hannayenku, Ya kuma kunyatar da su, kuma Ya taimake ku a kansu, Ya kuma warkar da zukatan muminai.
وَيُذۡهِبۡ غَيۡظَ قُلُوبِهِمۡۗ وَيَتُوبُ ٱللَّهُ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Open ayah 9:15Ya kuma tafiyar da ɓacin ransu. Allah kuma Ya karɓi tuban duk wanda Ya ga dama. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima.
أَمۡ حَسِبۡتُمۡ أَن تُتۡرَكُواْ وَلَمَّا يَعۡلَمِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ جَٰهَدُواْ مِنكُمۡ وَلَمۡ يَتَّخِذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَا رَسُولِهِۦ وَلَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَلِيجَةٗۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 9:16Ko kuwa kuna tsammanin za a ƙyale ku ne (sakaka) alhali kuwa har yanzu Allah bai tantance waɗanda suka yi jihadi ba a cikinku, ba su kuma riƙi wasu masoya ba banda Allah da Manzonsa da muminai? Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa muminai cewa, me zai hana su yaƙi mushrikan da suka karya alƙawarin zaman lafiya da ke tsakaninsu suka yi niyyar korar Annabi (ﷺ) daga garin Makka, kuma su ne suka fara karya yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yi da su lokacin da suka yaƙi ƙabilar Khuza’ah waɗanda su kuma suke da ƙawance da Musulmi? Shin yanzu muminai suna jin tsoron su ne? To ai Allah ne ya fi cancanta su ji tsoro idan har sun kasance muminai na gaskiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su yaƙi waɗannan kafirai masu karya alƙawari; Allah ne zai azabtar da su ta hannayen muminai ya wulaƙanta su, ya ba muminai nasara a kansu, ya kuma warkar da zukatan muminai ta hanyar kawar musu da damuwa, ya tafiyar da ɓacin ransu. Allah kuma shi yake karɓar tubar wanda ya ga dama daga cikin mushirikai, kuma Allah masani ne mai hikima. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa kafirai cewa, shin suna zaton zai ƙyale su ne hakanan ba tare da ya jarrabe su da jihadi ba, don ya rarrabe tsakanin masu gaskiya wajen jihadinsu don Allah ba su riƙi wasu masoya na kusa a cikin kafirai ba maimakon Allah da Manzonsa da muminai waɗanda za su riƙa bayyana musu sirrin Musulmi? Allah mai cikakken sani ne game da duk abin da suke aikatawa.
مَا كَانَ لِلۡمُشۡرِكِينَ أَن يَعۡمُرُواْ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ شَٰهِدِينَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِم بِٱلۡكُفۡرِۚ أُوْلَٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ وَفِي ٱلنَّارِ هُمۡ خَٰلِدُونَ
Open ayah 9:17Ba zai taɓa yiwuwa mushrikai su raya masallatan Allah ba, alhalin kuwa suna masu iƙirarin kafirci ga kawunasu. Waɗannan ayyukansu sun ɓaci kuma a cikin wuta za su dawwama.
إِنَّمَا يَعۡمُرُ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَلَمۡ يَخۡشَ إِلَّا ٱللَّهَۖ فَعَسَىٰٓ أُوْلَٰٓئِكَ أَن يَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡتَدِينَ
Open ayah 9:18Lalle mai raya masallatan Allah shi ne kawai wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma tsayar da salla, kuma ya ba da zakka, bai kuma ji tsoron wani ba sai Allah. To waɗannan tabbas suna cikin shiryayyu.
۞أَجَعَلۡتُمۡ سِقَايَةَ ٱلۡحَآجِّ وَعِمَارَةَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ كَمَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَجَٰهَدَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ لَا يَسۡتَوُۥنَ عِندَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 9:19Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma yi jihadi saboda Allah? Ai ba za su zama ɗaya ba a wurin Allah. Allah kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, ba zai yiwu mushirikai su raya masallatan Allah ta hanyar gina su da bauta wa Allah a cikinsu da tsabtace su ba, alhalin suna yi wa kawunansu shaida da kafirci, wato suna iƙirarin bautar gumaka da ƙaryata manzancin Annabi (ﷺ), to waɗannan ayyukansu sun ɓaci kuma za su shiga wutar Jahannama su dawwama a cikinta har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, masallatai dai na Allah ne, wanda kawai yake raya su shi ne wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya kuma tsayar da sallar farilla da rukunanta, ya ba da zakka, kuma ba ya jin tsoron kowa sai Allah; to waɗannan tabbas sune shiryayyu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Mutum bakwai Allah zai saka su a inuwarsa ranar gobe ƙiyama….” daga cikinsu ya ambaci “….mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallaci.” [Bukhari #6806, da Muslim #1031]. An karɓo daga Usman ɗan Affanu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Wanda ya gina masallaci don Allah, to Allah zai gina masa kwatankwacinsa a Aljanna.” [Bukhari #450 da Muslim #533]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi mutane cewa, ta yaya za su gwada mutanen da suke shayar da alhazai ruwa a lokacin hajji da kula da masallaci mai alfarma da mutumin da ya yi imani da Allah da ranar lahira, ya kuma yi jihadi don ɗaukaka kalmar Allah? A’a; waɗannan ba za su taɓa zama ɗaya ba a wurin Allah. Allah kuma ba ya shiryar da mutanen da suke azzalumai. An karɓo daga An-Nu’uman ɗan Bashiru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ina zaune a kusa da minbarin Manzon Allah (ﷺ), sai wani mutum ya ce: “Babu abin da zai dame ni don ban yi wani aiki bayan musuluntata ba sai dai shayar da alhazai.” Wani kuma ya ce: “Babu abin da zai dame ni don ban yi wani aiki bayan musuluntata ba, sai dai in raya masallaci mai alfarma.” Sai kuma wani ya ce: “Jihadi don Allah ya fi duk abin da kuka faɗa.” Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya daka musu tsawa ya ce: “Ku daina ɗaga muryoyinku a wajen minbarin Manzon Allah (ﷺ), ga shi kuma yau Juma’a ce, amma idan na gama sallar Juma’a zan shiga wurin Manzon Allah (ﷺ) in yi masa fatawa game da abin da kuka yi saɓani a kai.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan aya ta 19.” [Muslim #1879].
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ أَعۡظَمُ دَرَجَةً عِندَ ٱللَّهِۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
Open ayah 9:20Waɗanda suka yi imani kuma suka yi hijira suka yi jihadi saboda Allah da dukiyoyinsu da kawunansu su suka fi girman daraja a wurin Allah kuma waɗannan su ne marabauta.
يُبَشِّرُهُمۡ رَبُّهُم بِرَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَرِضۡوَٰنٖ وَجَنَّٰتٖ لَّهُمۡ فِيهَا نَعِيمٞ مُّقِيمٌ
Open ayah 9:21Ubangijinsu Yana yi musu albishir da rahama da yarda daga gare Shi, kana da gidajen Aljanna (waɗanda) a cikinsu suke da ni’imomi masu ɗorewa.
خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ
Open ayah 9:22Su madawwama ne a cikinsu har abada. Lalle lada mai girma yana wurin Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, lalle sahabban Annabi (ﷺ) waɗanda suka yi imani kuma suka baro gidajensu suka yi hijira tare da Manzon Allah (ﷺ) zuwa Madina, kuma suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu don Allah, waɗannan sun fi ɗaukakar matsayi a wurin Allah fiye da mushirikai masu shayar da alhazai ruwa a lokacin aikin hajji da masu raya Masallaci. Waɗancan sahabban su ne masu samun babban rabo. Ubagijinsu yana yi musu albishir na samun wata rahama daga gare shi da yarda da su da kuma gidajen Aljanna masu cike da ni’imomi masu ɗorewa har abada, kuma za su zauna a cikinsu har abada. Lalle lada mai girma yana wurin Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah zai ce da ‘yan Aljanna: “Ya ku ‘yan Aljanna.” Sai su ce: “Amsawarka ya Ubangijinmu tare da biyayya bayan biyayya kuma a hannunka alheri yake.” Sai ya ce: “Kun yarda da sakamakon da na ba ku?” Sai su ce: “Me zai hana mu yarda ya Ubangiji, alhalin ka ba mu abin da ba ka ba wani daga cikin halittunka ba?” Sai ya ce: “Ba na ba ku abin da ya fi haka ba?” Sai su ce: “Ya Ubangiji, mene ne ya fi hakan?” Sai ya ce: “In yarda da ku, ba zan taɓa yin fushi da ku ba bayan haka har abada.” [Bukhari #7518 da Muslim #2829].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُوٓاْ ءَابَآءَكُمۡ وَإِخۡوَٰنَكُمۡ أَوۡلِيَآءَ إِنِ ٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡكُفۡرَ عَلَى ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 9:23Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku ɗauki iyayenku da ‘yan’uwanku masoya muddin dai sun fifita kafirci a kan imani. Duk kuwa waɗanda suka ɗauke su (masoya) daga cikinku to waɗannan su ne azzalumai.
قُلۡ إِن كَانَ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُكُمۡ وَإِخۡوَٰنُكُمۡ وَأَزۡوَٰجُكُمۡ وَعَشِيرَتُكُمۡ وَأَمۡوَٰلٌ ٱقۡتَرَفۡتُمُوهَا وَتِجَٰرَةٞ تَخۡشَوۡنَ كَسَادَهَا وَمَسَٰكِنُ تَرۡضَوۡنَهَآ أَحَبَّ إِلَيۡكُم مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَجِهَادٖ فِي سَبِيلِهِۦ فَتَرَبَّصُواْ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Open ayah 9:24Ka ce: “Idan iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan’uwanku da matanku da danginku da dukiyoyin da kuka tara da kasuwanci da kuke tsoron gurguncewarsa da kuma gidajen da kuke sha\'awa; idan har su kuka fi so fiye da Allah da Manzonsa da kuma jihadi saboda Shi, to sai ku saurara har Allah Ya zo da al’amarinsa. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane fasiƙai.” </b>A waɗannan ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai su ɗauki iyayensu ko ‘yan’uwansu na jini su zama majiɓinta al’amuransu muddin sun fifita kafirci a kan imani, ya kuma bayyana cewa duk wanda ya jiɓince su to waɗannan su ne azzalumai. Sannan ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa muminai cewa, idan ya zamanto sun fifita son iyayensu da ‘ya’yansu da ‘yan’uwansu da matansu na aure da sauran danginsu na jini da dukiyoyinsu da suka tara da kasuwancinsu da suke tsoron gurguncewarsa, sun fifita son su a kan son Allah da Manzonsa da jihadi don ɗaukaka kalmar Allah, to su jira har Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo azabarsa ta gaggawa ko mai jinkiri. Allah kuma ba ya shiryar da mutane fasiƙai. An karɓo daga Anas ɗan Maliku (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abubuwa guda uku duk wanda suka samu tare da shi, to ya samu ɗanɗanon imani: Wanda ya fi son Allah da Manzonsa fiye da komai, kuma ya so mutum don Allah kawai, kuma ya ƙyamaci koma wa kafirci bayan Allah ya kuɓutar da shi, kamar yadda yake ƙin a jefa shi cikin wuta.” [Bukhari #16 da Muslim #43]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ɗayanku ba zai yi imani ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi fiye da ‘ya’yansa da iyayensa da mutane baki ɗaya.” [Bukhari #15 da Muslim #44]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Hisham (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mun kasance tare da Annabi (ﷺ) yana riƙe da hannun Umaru ɗan Khaɗɗabi (Allah ya kara masa yarda) sai ya ce: “Ya Manzon Allah, na fi son ka fiye da komai in ban da raina.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A’a, na rantse da wanda raina yake a hannunsa, sai ka fi so na fiye da ranka.” Sai Umar ya ce: “To haka ne yanzu. Na rantse da wanda raina yake hannunsa, na fi son ka fiye da raina.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “To yanzu ne ya Umar.” [Bukhari #6632].
لَقَدۡ نَصَرَكُمُ ٱللَّهُ فِي مَوَاطِنَ كَثِيرَةٖ وَيَوۡمَ حُنَيۡنٍ إِذۡ أَعۡجَبَتۡكُمۡ كَثۡرَتُكُمۡ فَلَمۡ تُغۡنِ عَنكُمۡ شَيۡـٔٗا وَضَاقَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ ثُمَّ وَلَّيۡتُم مُّدۡبِرِينَ
Open ayah 9:25Lalle haƙiƙa Allah Ya taimake ku a wurare da yawa, da kuma ranar (yaƙin) Hunaini lokacin da yawanku ya ruɗe ku sai (yawan naku) bai amfana muku komai ba, ƙasa kuma ta yi muku ƙunci duk da yalwarta, sannan kuka juya kuna masu ba da baya.
ثُمَّ أَنزَلَ ٱللَّهُ سَكِينَتَهُۥ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَعَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَأَنزَلَ جُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَا وَعَذَّبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 9:26Sannan Allah Ya sauƙar wa da Manzonsa da kuma muminai nutsuwarsa, Ya kuma saukar da wasu rundunoni da ba kwa gani, Ya kuma azabtar da waɗanda suka kafirta. Wannan kuwa shi ne sakamakon kafirai.
ثُمَّ يَتُوبُ ٱللَّهُ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 9:27Sannan bayan wannan Allah zai karɓi tuban wanda Ya ga dama. Allah kuwa Mai gafara ne, Mai rahama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da muminai abin da ya faru gare su a ranar yaƙin Hunaini tsakaninsu da ƙabilun Hawazinu da Saƙifu da waɗanda suka goya musu baya, a watan Shawwal na shekara ta takwas bayan hijira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya taimaki muminai a wuraren yaƙi da yawa, hakanan ya taimake su a ranar yaƙin Hunainu lokacin da yawansu ya ruɗe su, to amma kuma sai yawan bai amfana musu komai ba, ƙasa kuma ta yi musu ƙunci duk kuwa da yalwarta saboda tsananin abin da ya same su; daga bisani suka gudu suna ba wa kafirai baya. Sai kuma daga baya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da nutsuwarsa da ƙarfin zuciya ga Manzonsa (ﷺ) da muminai, ya kuma saukar da wata runduna ta mala’iku waɗanda babu mai ganin su, ya kuma azabtar da kafirai a wannan rana ta hannun muminai. Wannan kuwa shi ne sakamakon kafirai. Bayan haka kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna zai karɓi tuban wanda ya ga dama daga cikin waɗannan kafiran, ya shiryar da shi zuwa ga Musulunci. Lalle kuwa Allah mai gafara ne mai jin ƙai. Hunainu wani kwari ne a tsakanin Makka da Ɗa’ifa. Lokacin da wasu ƙabilu na Larabawa da suke zaune a wannan kwari kamar ƙabilar Hawazinu da Saƙifu da Ghaɗafan da sauransu suka sami labarin Annabi (ﷺ) ya ci Makka da yaƙi, sai abin bai yi musu daɗi ba, saboda haka sai suka shirya yaƙar Musulmi, suka fito ƙwansu da kwarkwatarsu da matansu da ‘ya’yansu har da dabbobinsu, saboda kada wani daga cikinsu ya yi tunanin gudu ko ja da baya. Yawancin Musulmi a lokacin ba su da isassun makamai. Musulmi suna shiga cikin wannan kwarin na Hunaini, ba su ankara ba, ashe rundunar Hawazinu waɗanda gwanayen harbi ne sun yi musu kwanton-ɓauna, sai kawai suka far wa Musulmi da harbi da sara da suka, sai Musulmi suka tarwatse, sai aka bar Annabi (ﷺ) da wasu ‘yan tsirarun Musulmi tare da shi a tsakiyar kafirai. Da Manzon Allah (ﷺ) ya ga haka sai ya umarci baffansa Abbas wanda yake riƙe da linzamin alfadarar Annabi (ﷺ) ya kirawo Musulmi. Sai Abbas ya kwaɗa musu kira cewa su dawo, sai suka juyo wurin Manzon Allah (ﷺ). Annabi (ﷺ) kuma sai ya zaburi alfadarsa ya nufi kafirai; faɗa ya sake kaurewa tsakanin Musulmi da kafirai; nan ne fa ya damƙi tsakuwoyi da tafukan hannunsa ya watsa wa kafirai a fuska, ya ce: “Ku tarwatse, na rantse da Ubangijin Ka’aba.” Daga nan ko sai suka daina gani sosai, suka ɗimauce suka shiga juya baya suna guduwa. Bugu da ƙari kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Musulmi wata runduna ta mala’iku suka taya su yaƙi har nasara ta tabbata gare su. [Dubi, Bukhari #433, 2864, da Muslim #1059,1775, 2865].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡمُشۡرِكُونَ نَجَسٞ فَلَا يَقۡرَبُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ ٱلۡحَرَامَ بَعۡدَ عَامِهِمۡ هَٰذَاۚ وَإِنۡ خِفۡتُمۡ عَيۡلَةٗ فَسَوۡفَ يُغۡنِيكُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦٓ إِن شَآءَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Open ayah 9:28Ya ku waɗanda suka yi imani, lalle mushrikai najasa ne kawai, saboda haka kada su kusanci Masallaci mai alfarma bayan wannan shekarar tasu. Idan kuma kuna tsoron talauci ne to Allah zai wadata ku daga falalarsa idan Ya ga dama. Lalle Allah Masani ne, Mai hikima.
قَٰتِلُواْ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَلَا يُحَرِّمُونَ مَا حَرَّمَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَلَا يَدِينُونَ دِينَ ٱلۡحَقِّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ حَتَّىٰ يُعۡطُواْ ٱلۡجِزۡيَةَ عَن يَدٖ وَهُمۡ صَٰغِرُونَ
Open ayah 9:29Ku yaƙi waɗanda ba sa yin imani da Allah da ranar lahira, ba kuma sa haramta abin da Allah da Manzonsa suka haramta, kuma ba sa yin addini na gaskiya, daga waɗanda aka bai wa littafi har sai (sun yarda) za su ba da jizya da hannunsu a ƙasƙance. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, lalle mushirikai najasa ne domin zukatansu cike suke da kafirci da ƙaryatawa, sannan ba sa tsarkake jikinsu daga abin da yake samun su na najasa, don haka kada muminai su ƙara ba su damar shiga masallaci mai alfarma, wato haramin Makka bayan shekara ta tara da yin hijira wadda a cikinta ne Musulmi suka yi watsi da duk wani alƙawari da yake tsakaninsu da mushirikai a baya. Ya nuna musu cewa, idan suna jin tsoron talauci ne saboda sun hana mushirikai shiga harami da yankewar kasuwanci da su a sanadiyyar haka, to Allah (Mai tsarki da daukaka) zai wadatar da su daga falalarsa idan ya ga dama. Lalle Allah masani ne mai hikima. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su su yaƙi Yahudu da Nasara waɗanda ba sa yin imani da Allah da ranar lahira kuma ba sa haramta abin da Allah da Manzonsa suke haramtawa, ba sa kuma yin addini na gaskiya, wato Musulunci, har sai sun bayar da jiziya da hannunsu a wulaƙance.
وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ عُزَيۡرٌ ٱبۡنُ ٱللَّهِ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَى ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ ٱللَّهِۖ ذَٰلِكَ قَوۡلُهُم بِأَفۡوَٰهِهِمۡۖ يُضَٰهِـُٔونَ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَبۡلُۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ
Open ayah 9:30Yahudawa sun ce: “Uzairu ɗan Allah ne.” Nasara kuma suka ce: “Almasihu ɗan Allah ne.” Wannan faɗarsu ce kawai da bakunansu; suna kwaikwayon faɗar kafiran da suka gabace su ne. Allah Ya tsine musu. Ta ƙaƙa ake kautar da su daga gaskiya?
ٱتَّخَذُوٓاْ أَحۡبَارَهُمۡ وَرُهۡبَٰنَهُمۡ أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُوٓاْ إِلَٰهٗا وَٰحِدٗاۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ سُبۡحَٰنَهُۥ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 9:31Sun ɗauki malamansu da masu ibadarsu da kuma Almasihu ɗan Maryamu iyayengiji maimakon Allah, alhali kuwa ba abin da aka umarce su sai su bauta wa Abin bauta Ɗaya, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Ya tsarkaka daga abin da suke tara Shi da shi. A waɗannan ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mummunar aƙidar Yahudawa da Nasara ne ta kiran wasu mutane ‘ya’yan Allah. Yahudawa sun ce, wai Uzairu ɗan Allah ne, Nasara kuwa suka ce Isa Almasihu ɗan Allah ne. Uzairu, wasu masana sun ce ɗaya ne daga cikin annabawan Banu Isra’ila, wasu kuma sun ce wani babban malami ne a cikinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan faɗarsu ce kawai ta fatar baki, suna kwaikwayon maganar kafiran da suka gabace su ne. Allah kuwa ya la’ance su; ta ƙaƙa har ake kautar da su daga kan gaskiya, har su riƙa jingina wa Allah ɗa ba tare da wata hujja ba? An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “A ranar alƙiyama mai shela zai yi shela yana cewa: “Kowace al’umma ta bi abin da take bauta wa.” Daga nan ba wani wanda yake bautar wanin Allah kamar masu bautar gumaka face sai sun yi ta aukawa cikin wutar Jahannama. Har ya zama babu sauran kowa sai masu bautar Allah cikin mutanen kirki da ba na kirki ba da sauran ma’abota littafi. Sai a kirawo Yahudawa a ce musu: “Me kuke bauta wa?” Sai su ce: “Mun kasance ne muna bauta wa Uzairu ɗan Allah.” Sai a ce musu: “Ƙarya kuke yi, Allah ba ya da mata ba ya da ɗa, to me kuke nema?” Sai su ce: “Ƙishirwa muke ji ya Ubangijinmu, ka shayar da mu.” Sai a nuna su a ce musu: “Ga shi can ba za ku je ku sha ba?” Sai a tattara su a tura su wuta, idan ka gan ta kamar kawalwalniya, sashinta yana rugurguzar sashi, sai su yi ta faɗawa cikinta. Sannan sai a kirawo Nasara, a ce musu: “Me kuke bauta wa?” Sai su ce: “Muna bautar Almasihu ɗan Allah ne.” Sai a ce musu: “Ƙarya kuke, Allah ba ya da mata ba ya da ɗa.” Sai kuma a ce musu: “To me kuke nema?” Sai su ce: “Ƙishirwa muke ji ya Ubangijinmu, ka shayar da mu.” Sai a nuna musu (wani wuri) a ce: “Ga shi can ba za ku je ku sha ba?” Sai a tattara su zuwa Jahannama kai ka ce kawalwalniya ce sashinta yana rugurguza sashi, sai su yi ta faɗawa cikinta.” [Bukhari #4581, da Muslim #183]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, sun mayar da malamansu da masu bauta a cikinsu shugabannin da suke yi wa biyayya ba Allah ba wajen halatta haram da haramta halal. Kuma Nasara sun ɗauki Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a matsayin abin bauta ba Allah ba, alhalin ba a yi musu wani umarni ba sai na su bauta wa abin bauta ɗaya shi ne Allah wanda ba ya da abokin tarayya. Ya tsarkaka kuma ga duk wata shirka da suke yi.
يُرِيدُونَ أَن يُطۡفِـُٔواْ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَيَأۡبَى ٱللَّهُ إِلَّآ أَن يُتِمَّ نُورَهُۥ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 9:32Suna nufi ne su dushashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa ba zai ƙyale ba har sai Ya cika haskensa ko da kuwa kafirai sun ƙi.
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ
Open ayah 9:33Shi ne wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya don Ya ɗora shi a kan dukkanin addinai, ko da kuwa mushrikai sun ƙi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ma’abota littafi suna ƙoƙarin ɓata addinin Musulunci saboda ƙarerayi da ƙage da suke yi a kansa. To amma duk da haka ba za su yi wata nasara ba, Allah ba zai yarda ba sai ya cika haskensa ya ɗora addininsa a kan sauran addinai ko da kuwa kafirai suna ƙin hakan. Sai kuma ya bayyana cewa, shi ne wanda ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (ﷺ) da shiriya da addinin gaskiya don ya ɗora shi a kan sauran addinai ko da kuwa mushirikai ba sa so. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Dare da rana ba za su gushe ba har sai an bauta wa gumakan Lata da Uzza.” Ta ce na ce: “Ya Manzon Allah, ni a da ina zaton cewa yayin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Shi ne wanda ya aiko da Manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya don ya ɗora shi a kan dukkanin addinai ko da kuwa mushirikai sun ƙi,” na zaci cewa hakan ya cika.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Nan gaba hakan zai kasance lokacin da Allah ya ga dama.” [Muslim #2907]. An karɓo daga Saubanu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya tattaro mini duniya wuri guda sai na ga gabashinta da yammacinta, kuma Lalle sai mulkin al’ummata ya kai inda aka tattaro mini daga gare ta.” [Muslim #2889]. An karɓo daga Tamimuddari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle wannan al’amari (Musulunci) sai ya kai duk inda dare da rana suka kai, Allah ba zai bar wani gidan laka ba ko na gashin raƙuma (wato birni da ƙauye) face sai ya shigar da wannan addinin cikinsa, da izzar mai izza ko da ƙasƙancin ƙasƙantacce, izzar da Allah zai ɗaukaka Musulunci da ita da ƙasƙancin da zai ƙasƙantar da kafirci da shi.” [Ahmad #16957].
۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡأَحۡبَارِ وَٱلرُّهۡبَانِ لَيَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡبَٰطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۗ وَٱلَّذِينَ يَكۡنِزُونَ ٱلذَّهَبَ وَٱلۡفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٖ
Open ayah 9:34Ya ku waɗanda suka yi imani, lalle da yawa daga malaman (Yahudawa) da masu ibada (Nasara) tabbas suna cin dukiyoyin mutane ta hanyar cuta, suna kuma toshe hanyar Allah. Waɗanda kuma suke ɓoye zinariya da azurfa ba sa ciyar da ita saboda Allah, to ka yi musu albishir da wata azaba mai raɗaɗi.
يَوۡمَ يُحۡمَىٰ عَلَيۡهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكۡوَىٰ بِهَا جِبَاهُهُمۡ وَجُنُوبُهُمۡ وَظُهُورُهُمۡۖ هَٰذَا مَا كَنَزۡتُمۡ لِأَنفُسِكُمۡ فَذُوقُواْ مَا كُنتُمۡ تَكۡنِزُونَ
Open ayah 9:35Ranar da za a narkar da su (zinariya da azurfa) cikin wutar Jahannama sannan a yi wa fuskokinsu da kuyaɓunsu da bayansu lalas da su, (a ce da su): “Wannan shi ne abin da kuka taskace wa kanku, sai ku ɗanɗani abin da kuka kasance kuna taskacewa.” </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin wani mugun hali na manyan malaman Yahudawa da masu ibada a cikin Nasara, watau yadda suke cin dukiyoyin mutane ta hanyar ƙarya da ɓarna, suke take gaskiya suna hana mutane karɓar ta. Sai kuma ya bayyana cewa, waɗanda suke tara zinariya da azurfa su ɓoye ba sa fitar musu da haƙƙin Allah, ba sa ciyar da su don taimakon addinin Allah, ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi wa irin waɗannan mutane albishir da wata azaba mai raɗaɗi, a ranar da za a narka wannan dukiyar tasu da wutar Jahannama, a yi musu lalas da ita a goshinsu da geffansu da bayansu, sannan ana faɗa musu maganar ɓacin rai, ana cewa: Wannan shi ne abin da kuka tara kuka kuma ɓoye domin kawunanku, don haka sai ku ɗanɗani sakamakon abin da kuka tara a ɓoye. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani ma’abocin zinare ko azurfa wanda ba ya fitar da zakka, face sai ya kasance a ranar alƙiyama an mayar masa su wata shimfiɗa ta wuta, a narka su a wutar Jahannama, sai a yi ta yi masa lalas da su a kwiɓinsa da goshinsa da bayansa. Duk sa’adda suka yi sanyi sai a sake dawo masa da su yadda suke, haka za a yi ta yi masa a cikin wani yini wanda gwargwadonsa shekara dubu hamsin ne, har sai an gama yin hukunci tsakanin bayi, sannan za a nuna masa hanyarsa, ko zuwa Aljanna ko kuma zuwa wuta.” [Muslim #987]. An karɓo daga Khalid ɗan Aslam ya ce: Mun fita tare da Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda), sai wani baƙauye ya yi masa tambaya game da wannan ayar. Sai Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce masa: “Duk wanda ya tara wannan dukiyar ya ɓoye ya hana zakkarta, to bone ya tabbata gare shi. Wannan ayar ta sauka kafin a saukar da hukuncin zakka ne. To bayan an saukar da hukuncin zakka sai Allah ya sauya zakka ta zamanto tsarkakewa ce ga dukiya.” [Bukhari #1504]. Wato Abdullahi ɗan Umar yana nufin wannan hukuncin ya kasance ne a farkon Musulunci kafin a farlanta zakka: Duk wani wanda yake da dukiya da ta fi ƙarfin buƙatarsa, to bai halatta a gare shi ya ɓoye ta ya ƙi taimaka wa mabuƙata da ita ba. Daga bisani aka farlanta zakka sai aka shafe wannan hukunci. [Dubi, Ibn Hajar, Fathul Bari , Juzu’i na 3]. Amma yawanci malaman tafsiri sun tafi ne a kan cewa, tana nufin mutanen da suke tara dukiya su ɓoye ba sa fitar mata da zakka. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Na rantse da Ubangijin Ka’aba su ne mafiya asara.” Sai Abu Zarrin ya tambaye shi: “Na ba da mahaifina da mahaifiyata fansa a gare ka, su wane ne waɗannan?” Sai ya ce: “Su ne masu yawan dukiya, sai dai wanda ya bayar da dukiyarsa nan da can da can, watau ta gabansa da bayansa da damansa da hagunsa; waɗannan kuwa ‘yan kaɗan ne. Babu wani mai raƙuma ko shanu ko ƙananan dabbobi sannan ba ya fitar musu da zakka face sai sun zo a ranar gobe ƙiyama da girma da ƙiba fiye da yadda suke a duniya, suna tunkuyin sa da ƙahonninsu, suna taka shi da kofatansu, duk sa’adda na ƙarshe suka ƙare sai na farko su kuma dawo musu, haka za a yi ta yi masa har sai an yi hukunci a tsakanin mutane.” [Bukhari #6638, da Muslim #990]. An karɓo daga Ummu Salamah (Allah ya kara masa yarda) ta ce: “Na kasance nakan sanya kayan kwalliya na zinariya, sai na ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Shin shi ma yana daga cikin ɓoyayyiyar dukiya?” Sai ya ce: “Matuƙar ya isa zakka, kuma aka cire masa, to ba ya daga cikin taskakakkiyar dukiya.” [Abu Dawud #1564, da Ɗabarani, Almu’ujamul Kabir , Juzu’i na 23, Shafi na 281, hadisi na 613]. An karɓo daga Sauban (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da wannan ayar ta sauka, sai suka ce: “To wace dukiya za mu riƙe?” Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ni zan nemo muku ilimi a kan haka.” Sai ya hau raƙuminsa ya isa wajen Annabi (ﷺ) ni kuma ina bin sa a baya, sai ya ce: “Ya Manzon Allah, wacce dukiya za mu riƙa?” Sai ya ce: “Ɗayanku ya riƙi zuciya mai godiya da harshe mai ambaton Allah da mata mumina wadda za ta taimaka masa a kan al’amarin lahira.” [Tirmizi #3094, da Ibn Maja #1856, da Ahmad #22437].
إِنَّ عِدَّةَ ٱلشُّهُورِ عِندَ ٱللَّهِ ٱثۡنَا عَشَرَ شَهۡرٗا فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِ يَوۡمَ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ مِنۡهَآ أَرۡبَعَةٌ حُرُمٞۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُۚ فَلَا تَظۡلِمُواْ فِيهِنَّ أَنفُسَكُمۡۚ وَقَٰتِلُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ كَآفَّةٗ كَمَا يُقَٰتِلُونَكُمۡ كَآفَّةٗۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 9:36Lalle adadin watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin littafin Allah, tun ranar da Ya halicci sammai da ƙasa, daga cikinsu akwai (wata) huɗu masu alfarma. Wannan shi ne addini madaidaici. To kada ku zalunci kanku a cikinsu, kuma ku yaƙi mushrikai gaba ɗaya kamar yadda suke yaƙar ku gaba ɗaya. Ku kuma sani cewa Allah Yana tare da masu taƙawa.
إِنَّمَا ٱلنَّسِيٓءُ زِيَادَةٞ فِي ٱلۡكُفۡرِۖ يُضَلُّ بِهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُحِلُّونَهُۥ عَامٗا وَيُحَرِّمُونَهُۥ عَامٗا لِّيُوَاطِـُٔواْ عِدَّةَ مَا حَرَّمَ ٱللَّهُ فَيُحِلُّواْ مَا حَرَّمَ ٱللَّهُۚ زُيِّنَ لَهُمۡ سُوٓءُ أَعۡمَٰلِهِمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 9:37Lalle jinkiri ba wani abu ba ne ban da ƙari cikin kafirci, wanda da shi (jinkirin) ake ɓatar da waɗanda suka kafirta, suna halatta shi a wata shekarar, su kuma haramta shi a wata, wai don su daidaita adadin abin da Allah Ya haramta, sai su halatta abin da Allah Ya haramta. An ƙawata musu munanan ayyukansu. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane kafirai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, adadin watanni a wurinsa wata goma sha biyu ne, haka ya hukunta kuma ya ƙaddara a cikin Lauhul Mahfuz tun lokacin da ya halicci sammai da ƙasa. Daga cikinsu akwai wata huɗu masu alfarma da ya haramta yin yaƙi a cikinsu, su ne Rajab da Zulƙi’ida da Zulhijja da Muharram. An karɓo daga Abu Bakrata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle zamani ya juyo kamar siffarsa yadda yake ranar da Allah ya halicci sammai da ƙasa: Shekara wata goma sha biyu ne, daga cikinsu akwai huɗu masu alfarma, uku a jere su ne Zulƙa’ada da Zulhijja da Muharram, sai kuma watan Rajab, watan ƙabilar Mudhar wanda yake a tsakanin watan Jumada da watan Sha’aban.” [Bukhari #7447, da Muslim #1679]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan shi ne addinin gaskiya shi ne kuma lissafi na daidai, don haka ya yi umarni da kada su zalunci kawunansu a cikin waɗannan watanni ta hanyar shiga yaƙi ko aikata miyagun laifuffuka. Sai kuma ya umarci muminai da su yaƙi mushirikai gaba ɗayansu kamar yadda su ma suke yaƙar su gaba ɗaya, kuma su sani Allah yana tare da masu taƙawa, watau masu kiyaye dokokinsa. Sannan kuma ya yi bayanin cewa, abin da Larabawa mushirikai suke yi na jinkirta watanni masu alfarma da canza shari’ar Allah a kansu, wannan wani ƙari ne a cikin kafircinsu. Watau sai su halatta yin yaƙi a watan Muharram a wata shekarar watau su canza shi da watan Safar maimakon watan Muharram. Bayan shekara ta zagayo sai su dawo da haramcin watan Muharram kamar yadda yake, wai don su daidaita abin da Allah ya haramta musu kowace shekara ba daɗi ba ragi a lissafi, wato watannin haramci sun cika huɗu cif-cif, to amma an jinkirta watan Muharram ya koma Safar, don haka sun halatta abin da Allah ya haramta, an ƙawata musu munanan ayyukansu. Allah kuwa ba ya shiryar da mutane kafirai masu kafewa a kan miyagun aƙidu da munanan ayyuka.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَا لَكُمۡ إِذَا قِيلَ لَكُمُ ٱنفِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱثَّاقَلۡتُمۡ إِلَى ٱلۡأَرۡضِۚ أَرَضِيتُم بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا مِنَ ٱلۡأٓخِرَةِۚ فَمَا مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا قَلِيلٌ
Open ayah 9:38Ya ku waɗanda suka yi imani, me ya same ku ne idan aka ce da ku ku fita yaƙi saboda Allah sai ku yi nauyin jiki? Yanzu kun zaɓi rayuwar duniya a kan ta lahira? Ai jin daɗin rayuwar duniya abu ne ƙanƙani dangane da na lahira.
إِلَّا تَنفِرُواْ يُعَذِّبۡكُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا وَيَسۡتَبۡدِلۡ قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ وَلَا تَضُرُّوهُ شَيۡـٔٗاۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Open ayah 9:39Idan ba za ku fita (yaƙi ba to (Allah) zai azabtar da ku da azaba mai raɗaɗi, Ya kuma canja wasu mutanen daban, ba kuwa za ku cutar da Shi da komai ba. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai.
إِلَّا تَنصُرُوهُ فَقَدۡ نَصَرَهُ ٱللَّهُ إِذۡ أَخۡرَجَهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ثَانِيَ ٱثۡنَيۡنِ إِذۡ هُمَا فِي ٱلۡغَارِ إِذۡ يَقُولُ لِصَٰحِبِهِۦ لَا تَحۡزَنۡ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَنَاۖ فَأَنزَلَ ٱللَّهُ سَكِينَتَهُۥ عَلَيۡهِ وَأَيَّدَهُۥ بِجُنُودٖ لَّمۡ تَرَوۡهَا وَجَعَلَ كَلِمَةَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلسُّفۡلَىٰۗ وَكَلِمَةُ ٱللَّهِ هِيَ ٱلۡعُلۡيَاۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Open ayah 9:40Idan ba ku taimake shi ba (watau Manzon Allah) to haƙiƙa Allah Ya taimake shi lokacin da kafirai suka fitar da shi (daga Makka), alhalin suna su biyu, lokacin da suke a cikin kogo, yayin da yake ce wa abokinsa (Abubakar): “Kada ka damu, lalle Allah yana tare da mu,” sai Allah Ya saukar masa da nutsuwarsa Ya kuma ƙarfafe shi da runduna wadda ba ku gan ta ba, Ya kuma sanya kalmar waɗanda suka kafirta ta zama ƙaskantacciya. Kalmar Allah kuwa ita ce maɗaukakiya. Allah kuma Mabuwayi ne, Mai hikima. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙara zaburar da muminai da su tashi su yi jihadi don Allah su daina nauyin jiki, ya kirawo su da sunan ‘imani’, yana faɗa musu cewa, me ya sa idan aka kirawo su su fito domin tafiya yaƙin ɗaukaka addinin Allah sai su riƙa nauyin jiki su fifita zaman gida da more rayuwar duniya a kan ta lahira da ni’imar cikinta? Jin daɗin duniya ƙanƙani ne dangane da na lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsorata su da cewa idan ba su fita jihadi ba, to zai yi musu azaba mai tsanani, ya kuma musanya su da wasu mutane daban waɗanda idan an kira su zuwa jihadi su amsa a guje, kuma ba za su cutar da Allah da komai ba don sun ƙi amsa kiransa. Kuma Allah mai iko ne a kan komai. Sai kuma ya ci gaba da cewa, idan sun ƙi taimakon Annabi (ﷺ) to ai Allah zai taimake shi kamar yadda ya taimake shi a baya lokacin da kafiran Ƙuraishawa suka fitar da shi daga ƙasar haihuwarsa Makka, a lokacin da suke su biyu, ba kowa tare da shi sai Abubakar As-Siddiƙ (Allah ya kara masa yarda), lokacin da suka shiga kogon dutsen Sauru don ɓoye wa abokan gaba masu neman su ruwa-a-jallo. A lokacin ne yake lallashin Abubakar yana ce masa, kada ya yi baƙin ciki, Allah yana tare da su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da nutsuwarsa ga Manzonsa (ﷺ) ya kuma ƙarfafe shi da rundunar mala’iku waɗanda ba wanda ya gan su, Allah kuma ya mayar da kalmar kafirai ta zama a ƙasa; kalmar Allah kuwa ita ce a sama. Allah kuma mabuwayi ne gwani mai hikima, saboda haka yana da ikon azabta kafirai ya karya ƙadarinsu, don ko babu abin da ya fi ƙarfinsa, mai hikima ne cikin dukkan ayyukansa da maganganunsa. Bayan kafiran Ƙuraishawa sun addabi Annabi (ﷺ) da tsangwama da wulaƙanci har ta kai sun shirya kashe shi, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya yi hijira tare da sahabbansa zuwa garin Madina. Sahabban Annabi (ﷺ) ne suka fara yin hijira zuwa can, sannan daga baya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da yin hijira tare da Sahabinsa kuma babban amininsa Abubakar (Allah ya kara masa yarda). Bayan sun fita daga garin Makka sai suka fara fakewa a kogon wani dutse da ake kiran sa Dutsen Sauru . Da aka wayi gari Ƙuraishawa ba su ga Annabi (ﷺ) da Abubakar ba sai suka fita suka bazama neman su. Suka iso dab da wannan kogon suka tsaya. Sayyidina Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya tsorata ƙwarai ya kiɗime hankalinsa ya tashi, yana zaton ko za su iya ganin su, har ya ce: “Wallahi da abin a ce ɗayansu zai duba ƙarƙashin ƙafarsa ne to da Lalle ya gan mu.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce da shi: “Kada ka damu, haƙiƙa Allah yana tare da mu.... Me kake tsammanin kuwa zai samu mutum biyu da Allah ne na ukunsu?” [Dubi, Bukhari #4663, da Muslim #2381].
ٱنفِرُواْ خِفَافٗا وَثِقَالٗا وَجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 9:41Ku fita yaƙi kuna da kuzari ko ba ku da shi, ku kuma yi yaƙi da dukiyoyinku da kawunanku saboda Allah. Wannan ya fi alheri a gare ku, in kun kasance kun san (haka).
لَوۡ كَانَ عَرَضٗا قَرِيبٗا وَسَفَرٗا قَاصِدٗا لَّٱتَّبَعُوكَ وَلَٰكِنۢ بَعُدَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلشُّقَّةُۚ وَسَيَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ لَوِ ٱسۡتَطَعۡنَا لَخَرَجۡنَا مَعَكُمۡ يُهۡلِكُونَ أَنفُسَهُمۡ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 9:42Da (abin da za su samu) amfani ne na kusa, ko tafiya gajeriya, to lalle da sun bi ka, sai dai kuma tafiyar ta yi musu tsawo; kuma za su zo suna rantsuwa da Allah cewa: “Da mun sami hali da lalle mun fita tare da ku”, suna hallaka kansu ne kawai, Allah kuwa Yana sane da cewa lalle su tabbas maƙaryata ne.
عَفَا ٱللَّهُ عَنكَ لِمَ أَذِنتَ لَهُمۡ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَتَعۡلَمَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Open ayah 9:43Allah Ya yafe maka; don me ka yi musu izini? Ai har sai ka gane musu gaskiya ka kuma san maƙaryata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da su yi gaggawar fita yaƙi don Allah, suna cikin kuzari ko ba sa ciki, kuma su yi jihadi da dukiyoyinsu da kawunansu don su ɗaukaka kalmar Allah (Mai tsarki da daukaka), saboda yin haka shi ne alheri gare su in sun san hakan. An karɓo daga Ubadatu ɗan Samitu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku yi jihadi don Allah, domin jihadi don Allah wata ƙofa ce daga cikin ƙofofin Aljanna, da shi ne Allah yake raba mutum da damuwa ko baƙin ciki.” [Ahmad #22699]. An karɓo daga Sahlu ɗan Sa’adu As-Sa’idi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yin dako (ribaɗi) na rana ɗaya don Allah ya fi duniya da abin da yake cikinta. Wurin ajiyar bulalar ɗayanku a Aljanna ya fi duniya da abin da yake cikinta. Fitar maraice da bawa zai yi don Allah ko sammako don Allah ya fi duniya da abin da yake cikinta.” [Bukhari #2892, da Muslim #1881]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, da a ce abin da yake kiran munafukai zuwa gare shi wata ganima ce da ke kusa mai sauƙin samuwa ko wata tafiya marar wahala to da sun fita tare da shi. To amma sai ya zamanto tafiyar mai tsawo ce, domin tafiya ce daga Madina da nufin yaƙi da Rumawa, don haka sai waɗannan munafukai suka noƙe suka ƙi bin Annabi (ﷺ). Sannan Allah ya faɗa masa cewa, bayan sun je sun dawo munafukan za su zo suna ta rantsuwa da Allah cewa, da sun sami hali da sun fita tare da Manzon Allah (ﷺ); suna hallaka kansu da gangan alhali suna sane. Allah ya san cewa, haƙiƙa maganar da suke faɗa ƙarya suke yi. Wasu munafukai kuma kamar su Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan Salulu da Aljaddu ɗan Ƙaisu da Rifa’atu ɗan Tabutu, su kimanin mutum talatin da tara, sun zo wurin Annabi (ﷺ) suka gabatar masa da uzurinsu na cewa ba za su iya fita yaƙin Tabuka ba, suka shirya masa ƙarerayi, Annabi kuma ya karɓi uzuransu ya musu izini su yi zamansu a gidajensu. To shi ne sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɓe shi game da wannan cikin ruwan sanyi, ya ce ya yi masa afuwa, don me ya yi musu izini su zauna gidajensu kada su bi shi yaƙi? Ya dace a ce kada ya yi musu izini har sai ya gane masu gaskiya a cikinsu ya kuma gane maƙaryata.
لَا يَسۡتَـٔۡذِنُكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ أَن يُجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 9:44Waɗanda suka yi imani da Allah da ranar lahira ba sa neman izininka don kada su yi yaƙi da dukiyoyinsu da kawunansu. Allah kuwa yana sane da masu taƙawa.
إِنَّمَا يَسۡتَـٔۡذِنُكَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱرۡتَابَتۡ قُلُوبُهُمۡ فَهُمۡ فِي رَيۡبِهِمۡ يَتَرَدَّدُونَ
Open ayah 9:45Waɗanda kawai suke neman izininka su ne waɗanda ba sa imani da Allah da ranar lahira, zukatansu kuma suka yi kokwanto, saboda haka suke ta dawurwuri a cikin kokwantonsu.
۞وَلَوۡ أَرَادُواْ ٱلۡخُرُوجَ لَأَعَدُّواْ لَهُۥ عُدَّةٗ وَلَٰكِن كَرِهَ ٱللَّهُ ٱنۢبِعَاثَهُمۡ فَثَبَّطَهُمۡ وَقِيلَ ٱقۡعُدُواْ مَعَ ٱلۡقَٰعِدِينَ
Open ayah 9:46Da kuwa sun yi niyyar fita to da sun yi masa tanadi, sai dai kuma Allah Ya ƙi zaburar da su, sai Ya dankwafar da su, aka kuma ce (da su): “Ku zauna tare da mazauna (gida).”
لَوۡ خَرَجُواْ فِيكُم مَّا زَادُوكُمۡ إِلَّا خَبَالٗا وَلَأَوۡضَعُواْ خِلَٰلَكُمۡ يَبۡغُونَكُمُ ٱلۡفِتۡنَةَ وَفِيكُمۡ سَمَّٰعُونَ لَهُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 9:47Da sun fito cikinku ɗin, to ba abin da za su ƙare ku da shi sai taɓarɓarewa, kuma lalle da sun yi ta shige da fice a tsakaninku suna ƙoƙarin haifar muku da fitina, a cikinku kuma akwai masu jiyo musu (wato abokan gaba) magana. Allah kuwa Masanin azzalumai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, babu yadda za a yi muminan da suka yi imani da Allah da ranar lahira su riƙa neman izini a wajensa na ya amince musu su ƙi fita yaƙi su yi zamansu a gidajensu, saboda su mutane ne masu kiyaye dokokin Allah, Allah kuwa yana sane da su. Ya bayyana cewa, masu neman izinin a ba su dama su ƙi fita yaƙi su ne munafukai masu kawo uzurori na ƙarya, domin ba su yi imani da Allah da ranar lahira ba, zukatansu suna cike da shakku, don haka suna cikin wannan shakkun nasu suna ta dawurwuri, su ba su tsaya a kan imani ba su kuma ba su koma cikin kafirci gaba ɗaya ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Misalin munafuki kamar misalin akuya ce mai kai-komo tsakanin garke biyu na dabbobi, wani lokaci ta bi waɗannan, wani lokaci kuma ta bi waɗancan.” [Muslim #2784]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da a ce waɗannan munafukai sun yi niyyar fita yaƙin da sun yi tanadi dominsa, sai dai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙi zaburar da su tare da muminai, sai ya daɗa danƙwafar da su ya saka musu mutuwar jiki da kasala, kuma aka ce da su su zauna tare da mazauna gida, wato mata da yara da marasa lafiya da masu larura waɗanda ba za su iya fita yaƙi ba. Sai kuma aka bayyana illar da fitarsu za ta haifar da cewa, da a ce ma za su fita tare da muminai to babu abin da za su ƙara musu sai sharri da ɓarna da ruɗani a tsakaninsu, sannan kuma ko shakka babu da sun yi ta shige-da-fice a tsakanin muminai suna yaɗa gulma da ƙiyayya a cikinsu, wanda yin hakan zai iya yin mummunar illa a cikin muminai, saboda a cikinsu akwai waɗanda sun yarda da su. Allah kuma yana sane da azzalumai.
لَقَدِ ٱبۡتَغَوُاْ ٱلۡفِتۡنَةَ مِن قَبۡلُ وَقَلَّبُواْ لَكَ ٱلۡأُمُورَ حَتَّىٰ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَظَهَرَ أَمۡرُ ٱللَّهِ وَهُمۡ كَٰرِهُونَ
Open ayah 9:48Haƙiƙa tun da can sun nemi yaɗa fitina, suka hargitsa maka al’amari, har sai da gaskiya ta zo, al’amarin Allah kuma ya bayyana, su kuwa suna masu ƙin (haka).
وَمِنۡهُم مَّن يَقُولُ ٱئۡذَن لِّي وَلَا تَفۡتِنِّيٓۚ أَلَا فِي ٱلۡفِتۡنَةِ سَقَطُواْۗ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةُۢ بِٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 9:49Daga cikinsu kuma akwai wanda yake cewa: “Ka yi mani izinin (zama), kada ka jefa ni cikin fitina.” Tabbas, ai cikin fitinar suka faɗa. Lalle Jahannama kuwa mai kewaye kafirai ce.
إِن تُصِبۡكَ حَسَنَةٞ تَسُؤۡهُمۡۖ وَإِن تُصِبۡكَ مُصِيبَةٞ يَقُولُواْ قَدۡ أَخَذۡنَآ أَمۡرَنَا مِن قَبۡلُ وَيَتَوَلَّواْ وَّهُمۡ فَرِحُونَ
Open ayah 9:50Idan wani alheri ya same ka sai ya baƙanta musu rai; idan kuwa musiba ce ta same ka sai su riƙa cewa: “Haƙiƙa mu da ma tuni mun ɗauki matakin kauce mata,” sai kuma su juya baya suna masu farin ciki.
قُل لَّن يُصِيبَنَآ إِلَّا مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَنَا هُوَ مَوۡلَىٰنَاۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Open ayah 9:51Ka ce: “Ba abin da zai same mu sai abin da Allah Ya rubuta mana, shi ne Majiɓincin al’amuranmu; kuma ga Allah kaɗai muminai sai su dogara.”
قُلۡ هَلۡ تَرَبَّصُونَ بِنَآ إِلَّآ إِحۡدَى ٱلۡحُسۡنَيَيۡنِۖ وَنَحۡنُ نَتَرَبَّصُ بِكُمۡ أَن يُصِيبَكُمُ ٱللَّهُ بِعَذَابٖ مِّنۡ عِندِهِۦٓ أَوۡ بِأَيۡدِينَاۖ فَتَرَبَّصُوٓاْ إِنَّا مَعَكُم مُّتَرَبِّصُونَ
Open ayah 9:52Ka ce: “Shin akwai abin da kuke jira ya same mu in ban da ɗayan kyawawan abubuwa biyu (wato nasara ko shahada). Mu kuwa muna jiran (mu ga) Allah Ya aukar muku da wata azaba daga wurinsa ko kuwa ta hannunmu? To sai ku jira, lalle mu ma masu jira ne tare da ku.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana fallasa munafukai ne da cewa tun da can sun nemi yaɗa fitina da yamutsi a tsakanin Musulmi, sun yi nufin sharri ga Annabi (ﷺ) suka yi ta tunani iri-iri da ƙulle-ƙulle daban-daban don su cim ma burinsu, har sai da nasarar Allah ta zo addinin Musulunci ya yi galaba ba tare da suna son hakan ba. Munafukai a baya can kamar lokacin yaƙin Uhudu sun yi ƙoƙarin haddasa yamutsi tsakanin Musulmi da kawo musu rabuwar kai lokacin da Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan Salulu ya sulale da wani kaso na rundunar Musulmi, don ya haddasa rauni a rundunar Musulmi, kafirai su yi galaba a kansu, amma bai yi nasara ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a cikin munafukai akwai wanda yake faɗa wa Annabi cewa, shi a ba shi izini ya zauna kada a fita yaƙar Rumawa da shi, wai don kada a jefa shi cikin fitinar kallon matan Rumawa, wai shi ba zai iya ganin su ya yi haƙuri ba tare da ya neme su ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ai lalle waɗannan sun riga sun faɗa cikin wata babbar fitina, saboda sun yarda su ci gaba da zama a cikin kafirci da guje wa fita jihadi tare da Manzon Allah (ﷺ) da saɓa masa, kuma lalle Jahannama a kewaye take da kafirai. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa Aljaddu ɗan Ƙaisu: “Shin za ka fita yaƙar Rumawa?” Sai Jaddu ya ce: “Ko za ka yi min izinin in yi zamana ya Manzon Allah, saboda ni mutum ne mai sha’awar mata, kuma ina jin tsoron kada in ga matan Rumawa in faɗa cikin fitina.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ɗauke masa kai ya ce masa: “Je ka na yi maka izini.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar. [Dubi, Ibn Abi Hatim, Tafsir , Juzi’i na 6, Shafi na 1809]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, idan muminai suka fita yaƙi, suka kuma ci nasara a kan kafirai suka samo ganimar yaƙi, rayuwarsu ta ƙara yalwa, wannan zai baƙanta wa munafukai sosai, za su ji haushin faruwar haka ga muminai. Amma kuma da musifa ce ta kisa ko rauni za ta samu Musulmi, ko a yi nasara a kansu, to da za ka gan su suna cewa, ai su da man sun riga sun ɗauki matakin kare kansu, sun yi taka-tsantsan don haka abin da ya samu Musulmi su bai same su ba, saboda haka sai su juya su tafi suna farin ciki. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, babu wata musiba da za ta same shi, shi da sahabbansa sai dai abin da Allah ya riga ya rubuta musu, domin shi ne majiɓincin al’amarinsu mai taimakon su a koyaushe, don haka muminai su dogara ga Allah shi kaɗai, su fawwala masa al’amuransu. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗawa munafukai cewa abin da suke jira ya sami muminai bai wuce ɗayan abubuwa biyu kyawawa ba, wato samun nasara a kan maƙiya ko kuma mutuwar shahada. Amma su muminai suna jiran Allah ya saukar wa da munafukai azaba daga wurinsa ko kuma ta hannunsu. Don haka su yi ta jira su ma muminai suna nan suna jira tare da su. An karɓo daga Suhaibu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Al’amarin mumini yana da ban mamaki, domin duk al’amuransa alheri ne, babu mai samun haka kuwa sai mumini. Idan abin farin ciki ya same shi sai ya yi godiya sai wannan ya zame masa alheri; idan kuma wata cuta ta same shi sai ya yi haƙuri, wannan ma sai ya zame masa alheri.” [Muslim #2999]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Allah ya rubuta abubuwan da ya ƙaddara wa halittunsa kafin ya halicci sammai da ƙasa da shekara dubu ɗari biyar.” [Muslim #2653].
قُلۡ أَنفِقُواْ طَوۡعًا أَوۡ كَرۡهٗا لَّن يُتَقَبَّلَ مِنكُمۡ إِنَّكُمۡ كُنتُمۡ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Open ayah 9:53Ka ce: “Ku ciyar (da dukiyarku) cikin daɗin rai ko a bisa dole (duka ɗai suke), ba za a karɓa muku ba; don kuwa lalle kun kasance ku mutane ne fasiƙai.
وَمَا مَنَعَهُمۡ أَن تُقۡبَلَ مِنۡهُمۡ نَفَقَٰتُهُمۡ إِلَّآ أَنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِٱللَّهِ وَبِرَسُولِهِۦ وَلَا يَأۡتُونَ ٱلصَّلَوٰةَ إِلَّا وَهُمۡ كُسَالَىٰ وَلَا يُنفِقُونَ إِلَّا وَهُمۡ كَٰرِهُونَ
Open ayah 9:54Ba kuwa abin da ya hana a karɓi ciyarwar tasu sai don sun kafirce wa Allah da Manzonsa, ba sa kuma zuwa salla sai suna cikin kasala, ba kuma sa ciyarwa sai ala tilas. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya bayyana wa munafukai cewa, duk ɗaya ne a gare shi ko su yarda su ciyar da dukiyarsu ko kada su yarda, Allah dai ba zai taɓa karɓar sadakarsu ba saboda sun tabbata su mutane ne fasiƙai. Kuma ba wani abu ya jawo aka ƙi karɓar sadakarsu ba sai don sun kafirce wa Allah da Manzonsa; idan ma sun tashi za su yi salla sai su tashi cikin kasala da nauyin jiki, kuma duk wani aikin alheri da za a zo da shi ba za su taimaka da dukiyarsu ba sai da ɓacin rai, suna yi amma ba da son ransu ba.
فَلَا تُعۡجِبۡكَ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُمۡۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُعَذِّبَهُم بِهَا فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَتَزۡهَقَ أَنفُسُهُمۡ وَهُمۡ كَٰفِرُونَ
Open ayah 9:55To kada dukiyoyinsu da ‘ya’yansu su ƙayatar da kai. Allah Yana nufin kawai Ya azabta su ne da su a rayuwar duniya, rayukansu kuma su zazzago a halin suna kafirai.
وَيَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ إِنَّهُمۡ لَمِنكُمۡ وَمَا هُم مِّنكُمۡ وَلَٰكِنَّهُمۡ قَوۡمٞ يَفۡرَقُونَ
Open ayah 9:56Sukan kuma rantse da Allah cewa lalle suna tare da ku, alhali kuwa ba sa tare da ku, kawai dai su wasu mutane ne matsorata.
لَوۡ يَجِدُونَ مَلۡجَـًٔا أَوۡ مَغَٰرَٰتٍ أَوۡ مُدَّخَلٗا لَّوَلَّوۡاْ إِلَيۡهِ وَهُمۡ يَجۡمَحُونَ
Open ayah 9:57Da za su sami wata mafaka ko wani kogo ko wata mashiga, to da sun juya zuwa gare shi suna gaggawar (shiga). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin halayen munafukai, tare da hana Annabi (ﷺ) ya yi sha’awar dukiyoyinsu da ‘ya’yansu, ya bayyana masa cewa ya ba su su ne ba don komai ba sai don ya yi musu azaba da su a duniya, ta hanyar su yi ta yi musu wahala da bauta da ɗawainiyar kula da su, sannan kuma idan sun zo mutuwa su mutu kafirai. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda yake lahira ce abin damuwarsa, to Allah zai ba shi wadatar zuci, ya tattaro masa jama’arsa wuri guda, duniya kuma ta zo masa a wulaƙance. Wanda kuwa duniya ce abin damuwarsa, sai Allah ya sanya masa talaucinsa a gaban idanunsa (watau ya jefa masa tsoron talauci a zuciyarsa), ya tarwatsa masa jama’arsa, kuma ba abin da zai samu a duniya sai iya abin da aka ƙaddara masa.” [Ibn Maja #4105, da Ibn Hibban #680]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya ba da labari cewa, munafukai maƙaryatan gaske ne sannan ga su da tsoro, don haka suke yawan rantse wa muminai cewa suna tare da su, amma alal haƙiƙa ba sa cikinsu, sai dai kawai suna jin tsoron muminai ne shi ya sa suke rantsuwar cewa suna cikinsu don su sami aminci da zaman lafiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa da munafukan nan za su sami wani wuri da za su fake a ciki su kare kansu ko wani kogo ko wani rami a ƙasa to da sun gudu can sun ɓoye saboda tsananin ƙiyayyar da suke yi wa Musulmi da ƙoƙarin guje wa fita yaƙi tare da Annabi (ﷺ).
وَمِنۡهُم مَّن يَلۡمِزُكَ فِي ٱلصَّدَقَٰتِ فَإِنۡ أُعۡطُواْ مِنۡهَا رَضُواْ وَإِن لَّمۡ يُعۡطَوۡاْ مِنۡهَآ إِذَا هُمۡ يَسۡخَطُونَ
Open ayah 9:58Daga cikinsu kuma akwai waɗanda suke aibata ka game da rabon sadaka; idan an ba su wani abu daga cikinta to sai su gamsu, idan kuwa ba a ba su daga cikinta ba sai ka gan su suna fushi.
وَلَوۡ أَنَّهُمۡ رَضُواْ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَقَالُواْ حَسۡبُنَا ٱللَّهُ سَيُؤۡتِينَا ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ وَرَسُولُهُۥٓ إِنَّآ إِلَى ٱللَّهِ رَٰغِبُونَ
Open ayah 9:59Da kuwa za su yarda da abin da Allah da Manzonsa suka ba su, su kuma ce: “Allah ya ishe mu, kuma Allah zai ba mu daga falalarsa Manzonsa ma (zai ba mu), lalle mu masu kwaɗayi ne a wurin Allah kaɗai.”
۞إِنَّمَا ٱلصَّدَقَٰتُ لِلۡفُقَرَآءِ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡعَٰمِلِينَ عَلَيۡهَا وَٱلۡمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمۡ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَٱلۡغَٰرِمِينَ وَفِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِۖ فَرِيضَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Open ayah 9:60Dukiyoyin zakka na matalauta ne kaɗai da miskinai da ma’aikatanta da waɗanda ake lallashin zukatansu da kuma game da ‘yanta bayi da waɗanda ake bi bashi da kuma wajen jihadi saboda Allah da matafiyi. Farilla ce daga Allah. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da fayyace miyagun halayen munafukai ne, waɗanda suka haɗa da sukan Manzon Allah (ﷺ) game da rabon dukiyar zakka; idan an ba su yadda ransu yake so sai su karɓa su gamsu da rabon ba tare da wani ƙorafi ba, amma idan ba a ba su yadda suke so ba, to sai su yi fushi, su riƙa wasu ƙananan maganganu. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Muna tare da Annabi (ﷺ) yana rabon sadaka, sai wani mutum mai suna Zul Khuwaisira ya zo wajensa ya ce: “Ya Manzon Allah, ka yi adalci.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Kaiconka! Wane ne zai yi adalci idan ni ban yi ba? Ka halaka, ka yi hasara idan har ban yi adalci ba…” [Dubi Bukhari #6933 da Muslim #1065]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da a ce waɗannan munafukan sun gamsu da abin da Allah ya ba su, kuma Annabi (ﷺ) ya raba musu, suka ce Allah ya ishe su, kuma Allah zai yi musu baiwa da falalarsa, Annabi (ﷺ) kuma zai raba musu, kuma wurin Allah kaɗai suke kwaɗayi, to da hakan ya fi zame musu alheri a duniyarsu da addininsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin waɗanda suka cancanci a ba su dukiyar zakka kamar haka: 1. Faƙirai: Su ne waɗanda ba su mallaki abin da za su yi rabin shekara suna ci ba. 2. Miskinai: Su ne waɗanda ba su mallaki abin da za su shekara suna ci ba. A wurin wasu malamai miskinai sun fi faƙirai tsananin buƙata. 3. Ma’aikatan zakkar: Su ne waɗanda suke tattara zakka su kula da ita har a raba wa waɗanda suka cancanta. Waɗannan ma ana ba su ladansu daga dukiyar zakka ko da kuwa su mawadata ne. 4. Waɗanda ake lallashin zukatansu: Su ne kafiran da ake ƙoƙarin jawo hankalinsu zuwa ga Musulunci, da waɗanda ba su daɗe da karɓar Musulunci ba, imaninsu bai yi ƙarfi ba. Su ma ana ba su zakka don a nuna musu cewa Musulunci addini ne mai tausayi da jin ƙai. 5. ‘Yanta bayi: Su ne bayin da aka ɗora musu fansa, sai a taimaka masa da abin da zai fanshi kansa da shi; ko kuma a fanshi Musulmin da ya faɗa hannun maƙiya suka riƙe shi fursunan yaƙi; ko a sayi bawa a ‘yanta shi. 6. Masu bashi a kansu: Su ne waɗanda suka ci bashi suka kasa biya, ko wanda ya ɗauki bashin wani don tabbatar da sulhu tsakanin masu husuma. Waɗannan ma ana ba su daga cikin dukiyar zakka don su warware bashin da ke kansu. 7. A wajen jihadi don ɗaukaka addinin Allah: Ana amfani da dukiyar zakka wajen shirya rundunar masu jihadi da sayen makamai da ababen hawa don fita yaƙi da guzirin mayaƙan. 8. Matafiyi: Shi ne matafiyin da guzurinsa ya ƙare bai kai garinsa ba. Ana taimaka masa daga cikin dukiyar zakka da gwargwadon abin da zai ƙarasa da shi garinsu. Waɗannan su kaɗai ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yarda a ba su dukiyar zakka. Zakka wata farilla ce daga Allah, Allah kuwa masani ne mai hikima. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ba mai yawo yana roƙon mutane ne miskini ba, wanda idan aka ba shi loma ɗaya ko biyu, ko dabino ɗaya ko biyu an sallame shi ba; miskini shi ne wanda ba ya samun abin da zai ishe shi, ba a san ma da shi ba balle har a ba shi sadaka, shi kuma ba ya miƙewa tsaye cikin mutane ya roƙe su.” [Bukhari #1479, da Muslim #1039]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Zakka ba ta halatta ga mai wadata ba, ko mutum ƙaƙƙarfa lafiyayye.” [Ahmad #9061, da Nasa’i #2597, da Ibn Maja #1839]. An karɓo daga Ubaidullahi ɗan Adiyyu ɗan Khiyar ya ce: Wasu mutane su biyu sun ba shi labarin cewa, sun je wajen Manzon Allah (ﷺ) suka roƙe shi ya ba su zakka, sai ya ɗaga kansa ya dube su da kyau, ya gan su ƙarfafa ne sai ya ce: “In kuna so in ba ku, amma ku sani cewa mawadaci da ƙaƙƙarfan da zai iya yin sana’a ba su da rabo a cikinta.” [Ahmad #17972, da Abu Dawud #1633, da Nasa’i #2598]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Aliyyu (Allah ya kara masa yarda) ya aiko da dukiyar zinare daga Yaman zuwa ga Manzon Allah (ﷺ) sai Annabi (ﷺ) ya raba ta ga mutum huɗu, su ne: Al-Aƙara’u ɗan Habisu Al-Hanzali da Uyainatu ɗan Badr Al-Fazari da Alƙamatu ɗan Ulasatu Al-Amiri da Zaidul Khairi Aɗɗa’i. Sai Ƙuraishawa suka yi fushi suka ce: “Yanzu yaya za ka ba shugabannin Najadu mu kuma ka bar mu hakanan?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle ni na yi haka ne don lallashin su.” [Bukhari #7432, da Muslim #1064].
وَمِنۡهُمُ ٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱلنَّبِيَّ وَيَقُولُونَ هُوَ أُذُنٞۚ قُلۡ أُذُنُ خَيۡرٖ لَّكُمۡ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَيُؤۡمِنُ لِلۡمُؤۡمِنِينَ وَرَحۡمَةٞ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡۚ وَٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ رَسُولَ ٱللَّهِ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 9:61Daga cikinsu kuma akwai waɗanda suke cutar Annabi suna kuma cewa: “Shi mai saurare ne kawai.” Ka ce (da su: Shi) “Mai sauraren alheri ne dominku; yana imani da Allah, yana kuma gaskata muminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi imani daga cikinku.” Waɗanda kuwa suke cutar Manzon Allah suna da azaba mai raɗaɗi.
يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ لَكُمۡ لِيُرۡضُوكُمۡ وَٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ أَحَقُّ أَن يُرۡضُوهُ إِن كَانُواْ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 9:62Suna rantse muku da Allah don su samu yardarku, Allah da Manzonsa kuwa su suka fi cancanta su yardar da su in sun kasance muminai.
أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّهُۥ مَن يُحَادِدِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَأَنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدٗا فِيهَاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡخِزۡيُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 9:63Yanzu ba su sani ba cewa, wanda yake jayayya da Allah da Manzonsa, to lalle yana da wutar Jahannama da zai dawwama a cikinta? Wannan kuwa kunyata ce mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da fallasa munafukai ne ta hanyar bayanin wasu miyagun ɗabi’unsu, yana cewa daga cikinsu akwai masu cutar da Annabi (ﷺ) suna cewa, wai shi mai ɗaukan maganganu ne kawai yana yarda da su ba tare da ya tantance gaskiyarsu da rashinta ba. Don haka suke ganin idan sun je sun rantse masa sun faɗa masa kowace irin ƙarya yana yarda da su ya karɓi hanzarinsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya mayar musu da martani cewa, ai shi mai sauraren alheri ne ba sharri ba; idan ya samu wani mummunan labari a kansu ba ya kama su da shi saboda yawan haƙurinsa, don haka yake sauraron hanzarinsu yana karɓa saboda kyawawan ɗabi’unsa. Yana yin imani da Allah yana kuma gaskata abin da muminai suke faɗa masa, amma ba abin da ya ji daga bakin kafirai ko munafukai ba, kuma shi rahama ne ga muminai masu gaskiya. Amma munafukai masu cutar da shi (ﷺ) to suna da azaba mai raɗaɗi a duniya da lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, munafukai suna rantse wa muminai da Allah don su sami yardarsu da amincewarsu, ya nuna cewa Allah ne da Manzonsa ya fi cancanta su nemi yardarsu idan har da gaske su muminai ne kamar yadda suke nunawa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Manzon Allah (ﷺ) yana zaune a inuwar ɗaya daga cikin ɗakunansa tare da wasu Musulmi, har ma inuwar ta kusa janyewa gaba ɗaya, sai ya ce: “Yanzu za ku ga wani mutum zai zo yana kallon ku da idanun Shaiɗan, idan ya zo muku kada kowa ya yi masa magana.” Sai ga wani mutum mai jajayen idanuwa ya zo. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya kirawo shi ya ce masa: “Me ya sa kai da wane da wane kuke zagi na?” Annabi (ﷺ) ya ambaci sunayensu. Sai wannan mutumin ya tafi ya kirawo su, suka zo suka dinga yi wa Manzon Allah rantsuwa da Allah cewa ba haka ne ba, suka gabatar da hanzarinsu, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Sai su rantse masa (da Allah) kamar yadda suke rantse muku, suna kuma zaton cewa a kan wani abu suke….” [Ahmad #2407, da Al-Hakim #3795]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba yi wa waɗannan munafukai kashedi da cewa, ba su san duk wanda ya saɓa wa Allah da Manzonsa yake kuma gaba da su ba cewa, yana da sakamakon wutar Jahannama wadda zai dawwama a cikinta har abada, kuma wannan ita ce kunyata mai girma?
يَحۡذَرُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ أَن تُنَزَّلَ عَلَيۡهِمۡ سُورَةٞ تُنَبِّئُهُم بِمَا فِي قُلُوبِهِمۡۚ قُلِ ٱسۡتَهۡزِءُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ مُخۡرِجٞ مَّا تَحۡذَرُونَ
Open ayah 9:64Munafukai suna tsoron a saukar musu da wata sura mai ba su labarin abin da yake cikin zukatansu. Ka ce : “Ku yi ta izgili, lalle Allah Mai bayyana abin da kuke tsoron (bayyanarsa) ne.”
وَلَئِن سَأَلۡتَهُمۡ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلۡعَبُۚ قُلۡ أَبِٱللَّهِ وَءَايَٰتِهِۦ وَرَسُولِهِۦ كُنتُمۡ تَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 9:65Kuma lalle idan har ka tambaye su, tabbas za su ce: “Kawai muna kutse ne da wasa.” To ka ce (da su): “Yanzu Allah ne da ayoyinsa da Manzonsa kuka kasance kuna yi wa izgili?”
لَا تَعۡتَذِرُواْ قَدۡ كَفَرۡتُم بَعۡدَ إِيمَٰنِكُمۡۚ إِن نَّعۡفُ عَن طَآئِفَةٖ مِّنكُمۡ نُعَذِّبۡ طَآئِفَةَۢ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ مُجۡرِمِينَ
Open ayah 9:66Kada ku kawo wani uziri, haƙiƙa kun dai kafirta bayan imaninku. Idan Muka yafe wa wata ƙungiya daga cikinku to za Mu azabtar da wata ƙungiyar saboda kuwa sun kasance masu laifi ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da bankaɗo wasu miyagun halaye ne na munafukai, inda ya bayyana cewa su koyaushe a tsorace suke suna fargabar kada wata sura ta Alƙur’ani ta sauko wadda za ta bayyana abin da suka ɓoye na munafinci da kafirci a zukatansu, sai Allah ya umarci Annabinsa (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, su ci gaba da yin izgilin da suke yi kar su fasa, to amma su sani cewa lalle sai Allah ya fallasa abin da suke jin tsoron bayyanarsa ga muminai. Sai ya bayyana cewa, idan Annabi (ﷺ) ya tambayi munafukai game da irin miyagun maganganun da suke yi na sukansa shi da sahabbansa da addinin Musulunci, to za su haƙiƙance a kan cewa su fa ba da gaske suke yi ba, su kawai kutse ne da wasa suke yi. Sai Allah ya umarci Annabi ya ƙalubalance su da cewa, yanzu Allah da ayoyinsa da Manzonsa suka mayar ababen wasa da izgili? To su daina kawo wani hanzari, domin sun kafirta bayan imaninsu. Idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa wasu daga cikinsu afuwa saboda sun tuba har a zuci ya karɓi tubansu, to amma zai yi wa wasu daga cikinsu azaba saboda sun tabbata masu laifi ne. An karɓo daga Abdullah ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A lokacin yaƙin Tabuka, wata rana ana zaune sai wani mutum ya buɗi baki ya ce: “Ban taɓa ganin mutane haɗamammu masu yawan ƙarya matsorata a wurin yaƙi irin waɗannan alarammomin namu ba?” (Yana nufin sahabban Annabi (ﷺ)). Sai wani mutum a majalisin ya ce masa: “Ƙarya kake, kai dai kawai mutum ne munafuki, kuma tabbas sai na faɗa wa Manzon Allah abin da ka faɗa (ﷺ).” Sai labari ya iske Annabi (ﷺ) kuma Alƙur’ani ya sauko.” Abdullahi ɗan Umar ya ce: “Na ga wannan mutumin riƙe da igiyar sirdin taguwar Manzon Allah (ﷺ) yana bin Manzon Allah yana tuntuɓe da duwatsu yana cewa: “Ya Manzon Allah, kutse ne kawai da wasa muke yi.” Manzon Allah (ﷺ) yana ce masa: “Yanzu da Allah ne da ayoyinsa da Manzonsa kuke yi wa izgili?” [Ibn Jarir, Tafsir #16912, da Ibn Abi Hatim, Juzu’i na 6 Shafi na 1830].
ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتُ بَعۡضُهُم مِّنۢ بَعۡضٖۚ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡمُنكَرِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَقۡبِضُونَ أَيۡدِيَهُمۡۚ نَسُواْ ٱللَّهَ فَنَسِيَهُمۡۚ إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ
Open ayah 9:67Munafukai maza da munafukai mata sun yi kama da juna (wajen munafunci). Suna umurni da mummunan aiki suna kuma hana kyakkyawan aiki, kuma suna damƙe hannayensu (wajen yin alheri); sun manta da Allah, sai Shi ma Ya yi watsi da su. Lalle munafikai su ne fasiƙai.
وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ هِيَ حَسۡبُهُمۡۚ وَلَعَنَهُمُ ٱللَّهُۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّقِيمٞ
Open ayah 9:68Allah kuwa Ya yi wa munafukai maza da mata da kuma kafirai alƙawarin wutar Jahannama wadda za su dawwama a cikinta. Ita ta ishe su. Allah kuma Ya tsine musu, suna kuma da azaba mai ɗorewa.
كَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ كَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنكُمۡ قُوَّةٗ وَأَكۡثَرَ أَمۡوَٰلٗا وَأَوۡلَٰدٗا فَٱسۡتَمۡتَعُواْ بِخَلَٰقِهِمۡ فَٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِخَلَٰقِكُمۡ كَمَا ٱسۡتَمۡتَعَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُم بِخَلَٰقِهِمۡ وَخُضۡتُمۡ كَٱلَّذِي خَاضُوٓاْۚ أُوْلَٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 9:69(Kun yi) kama da waɗanda suke gabaninku; sun fi ku ƙarfi da yawan dukiyoyi da kuma ’ya’ya; sai suka more rabonsu (na duniya), to ku ma sai kuka more da naku rabon, kamar yadda waɗanda suke gabaninku suka more da irin nasu rabon, kuka kuma kutsa (cikin ɓarna) kamar yadda suka kutsa. Waɗannan, ayyukansu sun ruguje a duniya da lahira. Waɗannan kuwa su ne hasararru.
أَلَمۡ يَأۡتِهِمۡ نَبَأُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ قَوۡمِ نُوحٖ وَعَادٖ وَثَمُودَ وَقَوۡمِ إِبۡرَٰهِيمَ وَأَصۡحَٰبِ مَدۡيَنَ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَٰتِۚ أَتَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 9:70Yanzu labarin waɗanda suke gabaninsu bai zo musu ba: Mutanen (Annabi) Nuhu da Adawa da Samudawa, da mutanen (Annabi) Ibrahimu da kuma mutanen Madyana da waɗanda aka kifar (watau mutanen Annabi Luɗu)? Manzanninsu sun zo musu da (ayoyi) mabayyana; ba kuma zai zamana Allah Ya zalunce su ba sai dai kawunansu ne kawai suke zalunta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da labarta wa muminai wani abin kunyar daban na munafukai, da cewa, munafukai mazansu da matansu halinsu guda ne, ɗabi’arsu ta munafunci iri ɗaya ce, suna umarni da mummunan aiki suna kuma hana kyakkyawan aiki, sannan suna damƙe hannayensu wajen yin alheri, ba sa bayar da abin da ya wajaba su bayar daga dukiyoyinsu, sun kuma manta da ambaton Allah, sai su ma Allah ya yi watsi da su, ya ƙi shiryar da su, ya ƙi yi musu rahama, to kuma haka zai bar su a wutar Jahannama su dawwama cikin azaba har abada. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi wa munafukai maza da mata narko na wutar Jahannama wadda za su shige ta su zauna cikinta har abada. Ta ishe su uƙuba. Allah kuma ya nisanta su daga rahamarsa, suna da wata azaba ta har abada wadda babu ƙaƙƙautawa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fuskantar da maganarsa ga munafukai da kafirai ya faɗa musu cewa, suna yin irin ayyukan al’ummomin da suka gabace su, waɗanda kuma sun fi su ƙarfi da tarin dukiya da yawan ‘ya’ya, don haka suka more rabonsu na jin daɗin duniya, suka fifita shi a kan ni’imar lahira. To su ma munafukai haka suka more rabonsu na jin daɗin duniya suka bijire wa lahira kamar yadda kafiran da suka gabace su suka yi, kuma suka kutsa cikin irin abin da kafiran suka kutsa cikinsa. To waɗannan ayyukansu gaba ɗaya sun rushe a duniya da lahira, kuma su ne hasararru. Har wa yau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fuskantar da tambayarsa ga mushirikai da kafirai cewa, ba su samu labarin yadda Allah ya hallaka al’ummomin da suka shuɗe ba; watau mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanen Madyana, wato mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda Allah ya kifar da ƙasarsu, ya mayar da samanta ta koma ƙasa? Duk waɗannan al’ummomi manzanninsu sun je musu da mu’ujizoji bayyanannu, to amma sai suka ƙaryata su. A kan haka sai Allah ya hallakar da su, kuma Allah ba zai taɓa zaluntar su ya yi musu azabar da ba su cancanta ba, sai dai kawunansu kawai suka riƙa zalunta ta hanyar kafirce wa Allah da saɓa wa manzanninsa, don haka suka cancanci Allah ya halaka su.
وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَيُطِيعُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَٰٓئِكَ سَيَرۡحَمُهُمُ ٱللَّهُۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 9:71Muminai maza da muninai mata kuwa masoyan juna ne: Suna yin umurni da kyakkyawa abu suna kuma hana mummunan, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima.
وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَمَسَٰكِنَ طَيِّبَةٗ فِي جَنَّٰتِ عَدۡنٖۚ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِ أَكۡبَرُۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 9:72Allah Ya yi wa muninai maza da muminai mata alƙawarin gidajen Aljanna da ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu, da kuma wuraren zama masu kyau a cikin gidajen Aljanna na dawwama. Yardar Allah kuwa ita ce fiye da komai. Wannan shi ne rabo mai girma. A waɗannan ayoyi bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci mugun halin munafukai maza da mata da mummunan sakamakonsu, sai kuma ya bayyana kyakkyawan halin muminai maza da mata, ya siffanta su da cewa, su masu ƙaunar junansu ne da son taimaka wa juna, suna umarni da kyakkyawan aiki suna kuma hana mummunan aiki, suna kuma tsayar da salla da haƙƙoƙinta kamar yadda aka umarce su, suna kuma bayar da zakka ga mutanen da suka cancanta a ba wa, sannan kuma suna yi wa Allah da Manzonsa biyayya. To waɗannan Allah ya yi alƙawalin zai yi musu rahama, lalle kuma Allah mabuwayi ne mai hikima. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mumini dangantakarsa da ɗan’uwansa mumini kamar gini guda ne da sashensa yake ƙarfafar sashe.” [Bukhari #2446, da Muslim #2585]. An karɓo daga Nu’umanu ɗan Bashir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Misalin muminai wajen ƙauna da jin ƙai da tausayin junansu kamar jiki guda ne, wanda idan wata gaɓa ba ta da lafiya sai sauran gaɓoɓin jiki su ɗauka su kamu da rashin barci da zazzaɓi.” [Muslim #2587]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa muminai alƙawarin gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; za su zauna a cikinsu har abada. Haka kuma zai ba su wasu kyawawan masaukai a cikin gidajen Aljanna, amma kuma yardar Allah a garesu ta fi musu ni’imar Aljannar. Wannan alƙawari kuwa shi ne babban rabo a gare su. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Akwai gidajen Aljanna iri biyu waɗanda ƙoransu da abin da yake cikinsu na azurfa ne, akwai kuma wasu biyu waɗanda ƙoransu da abin da yake cikinsu na zinare ne. Kuma babu abin da ya zama shamaki tsakanin ‘yan Aljanna da ganin Ubangijinsu (a Aljanna) sai gwadon isa da ke kan fuskarsa, a cikin Aljanna ta dawwama”. [Bukhari #7444, da Muslim #186]. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle mumini a Aljanna yana da wani tanti na rarakakken dutsen lu’u-lu’u guda ɗaya, tsawonsa mil sittin ne. Mumini yana da iyalinsa muminai a cikinsa, zai zagaya su amma sashensu ba zai ga ɗaya sashin ba.” [Bukhari #3243, da Muslim #2838]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah zai ce wa ‘yan Aljanna: “Ya ku ‘yan Aljanna.” Sai su ce: “Amsawarka ya Ubangijinmu, duk alheri yana hannunka.” Sai ya ce: “Kun kuwa gamsu?” Sai su ce: “Me zai sa ba za mu gamsu ba ya Ubangijinmu, alhalin ka ba mu abin da ba ka taɓa ba wani daga cikin halittarka ba?” Sai ya ce: “To ba na ba ku abin da ya fi wannan ba?” Sai ya ce: “Zan saukar muku da yardata ba zan yi fushi da ku ba har abada.” [Bukhari #7518, da Muslim #2829]. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ‘yan Aljanna suka shiga Aljanna sai Allah mai girma da buwaya ya ce: “Kuna sha’awar wani abu in ƙara muku?” Sai su ce: “Ya Ubangijinmu, mene ne ya fi abin da ka ba mu?” Sai ya ce: “Yardata ce mafi girma.” [Ibn Hibban #7439, da Al-Hakim #276].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 9:73Ya kai wannan Annabi, ka yaƙi kafirai da munafukai ka kuma tsananta musu. Jahannama ce kuma makomarsu. Makoma kuwa ta munana.
يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ مَا قَالُواْ وَلَقَدۡ قَالُواْ كَلِمَةَ ٱلۡكُفۡرِ وَكَفَرُواْ بَعۡدَ إِسۡلَٰمِهِمۡ وَهَمُّواْ بِمَا لَمۡ يَنَالُواْۚ وَمَا نَقَمُوٓاْ إِلَّآ أَنۡ أَغۡنَىٰهُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ مِن فَضۡلِهِۦۚ فَإِن يَتُوبُواْ يَكُ خَيۡرٗا لَّهُمۡۖ وَإِن يَتَوَلَّوۡاْ يُعَذِّبۡهُمُ ٱللَّهُ عَذَابًا أَلِيمٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَمَا لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ
Open ayah 9:74Suna rantsewa da Allah kan ba su faɗi (komai) ba, alhali kuwa tabbas sun faɗi kalmar kafirci, suka kuma kafirta bayan musuluntarsu, suka kuma yi ƙudirin aikata abin da ba su samu (dama) ba; ba kuwa abin da suke jin haushi sai kawai don Allah da Manzonsa sun wadata su daga falalarsa. To idan suka tuba zai fi musu alheri; idan kuwa suka juya baya to Allah zai azabtar da su azaba mai raɗaɗi a duniya da lahira; ba su da kuwa wani majiɓincin lamari ko wani mataimaki a bayan ƙasa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya yaƙi kafirai da munafukai, ya kuma matsa musu lamba sosai wajen wa’azi da tunkarar su da ƙarfafan hujjoji, kuma makomarsu a lahira ita ce wutar Jahannama idan har sun bijire. Tir da wannan wuri da za su tsinci kansu a cikinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa munafukai suna rantsuwa da Allah a kan ƙaryar cewa su ba su furta komai ba da ya danganci kafirci, alhali kuwa sun furta kalmar kafirci, suka kuma kafirta bayan musuluntarsu, suka kuma ƙudurta mugun nufi na shirin kashe Manzon Allah (ﷺ) lokacin da yake komawa gida Madina daga yaƙin Tabuka, amma ba su ci nasara ba, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi kariya ya tsare shi daga sharrinsu. Babu kuma abin da yake baƙanta musu rai irin abin da ya kamata su yi godiya a kansa su yaba da shi, wato shi ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wadata su da falalarsa a dalilin aiko da Manzonsa (ﷺ) bayan a da suna matalauta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, idan har suka tuba suka daina munafunci da kafirci, to wannan shi ya fi musu alheri; idan kuma suka bijire suka ƙi ba da gaskiya suka ƙi tuba, to Allah zai yi musu azaba mai raɗaɗi a duniya da lahira, kuma ba su da wani mai jiɓintar su da zai sama musu wani alheri, kuma babu mai taimakon su ya kare su daga azaba.
۞وَمِنۡهُم مَّنۡ عَٰهَدَ ٱللَّهَ لَئِنۡ ءَاتَىٰنَا مِن فَضۡلِهِۦ لَنَصَّدَّقَنَّ وَلَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 9:75Daga cikinsu kuma akwai waɗanda suka yi wa Allah alƙawarin cewa: “Idan Ya arzuta mu daga falalarsa, to lalle tabbas za mu riƙa ba da sadaka, kuma lalle tabbas za mu zama cikin mutane salihai.”
فَلَمَّآ ءَاتَىٰهُم مِّن فَضۡلِهِۦ بَخِلُواْ بِهِۦ وَتَوَلَّواْ وَّهُم مُّعۡرِضُونَ
Open ayah 9:76To lokacin da Ya arzuta su ɗin sai suka yi rowa da ita ( sadakar) suka kuma ba da baya suna masu bijirewa.
فَأَعۡقَبَهُمۡ نِفَاقٗا فِي قُلُوبِهِمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ يَلۡقَوۡنَهُۥ بِمَآ أَخۡلَفُواْ ٱللَّهَ مَا وَعَدُوهُ وَبِمَا كَانُواْ يَكۡذِبُونَ
Open ayah 9:77Sai Ya gadar musu da munafunci a cikin zukatansu har zuwa ranar da za su gamu da Shi, saboda saɓa wa alƙawarin da suka yi wa Allah da kuma ƙaryatawar da suka zamanto suna yi.
أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ عَلَّٰمُ ٱلۡغُيُوبِ
Open ayah 9:78Yanzu ba su sani ba cewa, lalle Allah Ya san asirinsu da kuma ganawar da suke yi, lalle kuma Allah Shi ne cikakken Masanin gaibu? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da tona asirin munafukai, yana bayyana ƙarin wasu miyagun siffofinsu, da cewa, daga cikin munafukai akwai wanda ya yi wa Allah alƙawarin cewa, idan ya azurta shi daga falalarsa, to lalle zai yi sadaka ya fitar da haƙƙin Allah da ke cikin dukiyarsa da haƙƙin bayin Allah, to lokacin da Allah ya arzuta su daga falalarsa sai suka yi rowa suka juya wa Allah baya suka ƙi cika alƙawarin da suka yi, sai Allah ya saka musu a kan haka, ya jefa musu munafunci a zukatansu wanda zai ci gaba da kasancewa tare da su har zuwa ranar mutuwarsu, su sadu da Allah suna munafukai, saboda saɓa alƙawarin da suka ɗauka tsakaninsu da Allah da kuma ƙaryar da suke sharawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da cewa, yanzu su munafukai ba su san da cewa Allah yana sane da abin da suke ɓoyewa a zukatansu ba, da wanda suke asirta wa junansu, kuma Allah mai cikakken sanin gaibu ne? An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Alamomin munafuki uku ne: Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya; idan kuma ya yi alƙawari sai ya saɓa; idan kuma aka amince masa sai ya ci amana.” [Bukhari #33, da Muslim #59].
ٱلَّذِينَ يَلۡمِزُونَ ٱلۡمُطَّوِّعِينَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ فِي ٱلصَّدَقَٰتِ وَٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ إِلَّا جُهۡدَهُمۡ فَيَسۡخَرُونَ مِنۡهُمۡ سَخِرَ ٱللَّهُ مِنۡهُمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Open ayah 9:79Waɗanda kuma suke aibata muminai masu yin sadaka (mai yawa) don neman lada da kuma waɗanda ba su da abin da za su bayar sai (kaɗan) gwargwadon wahalarsu, sannan su riƙa yi musu izgili, to Allah zai mayar musu da sakamakon izgilinsu, suna kuma da azaba mai raɗaɗi.
ٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ أَوۡ لَا تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ إِن تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ سَبۡعِينَ مَرَّةٗ فَلَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Open ayah 9:80Ko ka nema musu gafara ko ba ka nema musu gafara ba (duk ɗaya ne). In da za ka nema musu gafara sau saba’in to Allah ba zai gafarta musu ba. Wannan kuwa saboda sun kafirce wa Allah da Manzonsa. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane fasiƙai. Waɗannan ayoyi suna ci gaba da bayanin siffofin munafukai ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana cewa, munafukai suna aibata muminai mawadata da suke sadaka mai yawa da dukiyoyinsu, suna ce musu wai ba don Allah suke yi ba; wai suna yi ne don riya; hakanan suna aibata muminai talakawa waɗanda suke sadaka da ɗan gwargwadon abin da Allah ya hore musu, sai su riƙa yi musu izgili da cewa, me Allah zai yi da ‘yar wannan sadaka tasu; to su sani Allah zai saka musu a kan izgilinsu, kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi a lahira. An karɓo daga Abu Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da aka umarce mu da ba da sadaka a lokacin muna yin dako ne, sai Abu Aƙil ya kawo rabin sa’i (na dabino), wani mutum kuma ya kawo fiye da haka, sai munafukai suka ce: “Ai Allah ba ya buƙatar sadakar wannan (talakan), wannan kuwa riya ce kawai ya yi.” Sai Allah ya saukar da wannan ayar. [Bukhari #4668, da Muslim #1018]. Ya zo a cikin hadisin Ka’abu ɗan Malik mai magana a kan yaƙin Tabuka cewa, Abu Khaisamata Al-Ansari shi ne ya kawo sadakar sa’i ɗaya na dabino, munafukai suka riƙa zunɗen sa. [Dubi, Muslim #1018]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Annabi cewa, ko ya nema wa munafukai gafarar Allah ko kada ya nema musu, Allah dai ba zai gafarta musu ba, ko da kuma ya nema musu gafara sau saba’in. Ba don wani abu ba sai don sun kafirce wa Allah da Manzonsa, Allah kuwa ba ya shiryar da mutane fasiƙai. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Da na san cewa idan na ƙara a kan saba’in za a gafarta musu, to lalle da na ƙara.” [Dubi, Bukhari #1366].
فَرِحَ ٱلۡمُخَلَّفُونَ بِمَقۡعَدِهِمۡ خِلَٰفَ رَسُولِ ٱللَّهِ وَكَرِهُوٓاْ أَن يُجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَالُواْ لَا تَنفِرُواْ فِي ٱلۡحَرِّۗ قُلۡ نَارُ جَهَنَّمَ أَشَدُّ حَرّٗاۚ لَّوۡ كَانُواْ يَفۡقَهُونَ
Open ayah 9:81(Munafukai) waɗanda suka ƙi fita (yaƙi) sun yi farin ciki da zamansu (a gida) suna masu saɓa wa Manzon Allah, suka kuma ƙi su yi yaƙi da dukiyoyinsu da kawunansu saboda Allah, suka kuma ce (da junansu): “Kada ku fita yaƙi cikin zafin nan.” Ka ce da su: “Wutar Jahannama ta fi tsananin zafi.” Da sun zamanto suna ganewa.
فَلۡيَضۡحَكُواْ قَلِيلٗا وَلۡيَبۡكُواْ كَثِيرٗا جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 9:82Sai su yi dariya kaɗan su kuma yi kuka mai yawa a sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa. A ci gaba da fallasar munafukai, Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, munafukai waɗanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi watsi da su, bai datar da su a kan fita jihadi ba, sun riƙa nuna farin cikin zamansu a gida ba su fita yaƙi tare da Manzon Allah (ﷺ) zuwa Tabuka ba, don saɓa wa Manzon Allah, suka kuma ƙi su yi yaƙi ta hanyar ba da dukiyoyinsu da kawunansu don taimakon addinin Allah da ɗaukaka kalmarsa, suka ce wa junansu: Kada su kuskura su fita yaƙi tare da Musulmi zuwa birnin Tabuka cikin wannan tsananin zafin rana.” Allah ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, wutar Jahannama ai ta fi tsananin zafi da a ce suna ganewa suna kuma fahimtar abin da Allah yake faɗa musu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wutar da ɗan’adam yake kunnawa a duniya kaso ɗaya ne cikin saba’in na wutar Jahannama.” Sahabbai suka ce: “Wallahi wutar duniya ma ta isa azaba.” Sai ya ce: “To wutar Jahannama ta fi ta duniya da kaso sittin da tara, kowane kaso nata zafinsa kamar ta duniya ce.” [Bukhari #6561, da Muslim #213]. Sannan Allah ya yi wa munafukai gatse da cewa, su yi dariya kaɗan a nan duniya, za su yi kuka mai yawa a ranar lahira yayin da aka jefa su wutar Jahannama. Wannan shi ne sakamakon kafircinsu da munafunci da saɓon Allah da suka dinga yi a duniya.
فَإِن رَّجَعَكَ ٱللَّهُ إِلَىٰ طَآئِفَةٖ مِّنۡهُمۡ فَٱسۡتَـٔۡذَنُوكَ لِلۡخُرُوجِ فَقُل لَّن تَخۡرُجُواْ مَعِيَ أَبَدٗا وَلَن تُقَٰتِلُواْ مَعِيَ عَدُوًّاۖ إِنَّكُمۡ رَضِيتُم بِٱلۡقُعُودِ أَوَّلَ مَرَّةٖ فَٱقۡعُدُواْ مَعَ ٱلۡخَٰلِفِينَ
Open ayah 9:83To idan Allah Ya dawo da kai zuwa ga wata jama’a daga cikinsu sai suka nemi izinin fita a wajenka, to sai ka ce (da su): “Ba za ku fita tare da ni ba har abada, kuma ba za ku yaƙi wani abokin gaba ba tare da ni ba har abada. Lalle kun yarda da zama tun farko, to sai ku zauna tare da masu zama.” (wato mata da yara).
وَلَا تُصَلِّ عَلَىٰٓ أَحَدٖ مِّنۡهُم مَّاتَ أَبَدٗا وَلَا تَقُمۡ عَلَىٰ قَبۡرِهِۦٓۖ إِنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَمَاتُواْ وَهُمۡ فَٰسِقُونَ
Open ayah 9:84Kada ka ƙara yi wa ɗaya daga cikinsu da ya mutu salla har abada, kada kuma ka tsaya a kan ƙabarinsa (don addu’a). Lalle su sun kafirce wa Allah da Manzonsa, suka kuma mutu suna fasiƙai.
وَلَا تُعۡجِبۡكَ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَأَوۡلَٰدُهُمۡۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُعَذِّبَهُم بِهَا فِي ٱلدُّنۡيَا وَتَزۡهَقَ أَنفُسُهُمۡ وَهُمۡ كَٰفِرُونَ
Open ayah 9:85Kada kuma dukiyoyinsu da ‘ya’yansu su ƙayatar da kai. Lalle kawai Allah Yana nufin azabtar da su ne da su (dukiyoyin da ‘ya’yan), rayukansu kuma su zazzago suna kafirai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, idan Allah ya dawo da shi daga yaƙin Tabuka zuwa ga jama’a ta munafukai waɗanda suka yi zamansu a Madina suka ƙi bin sa ba tare da wani uzuri ba, sai kuma suka zo suna neman izinin fita wani yaƙin tare da shi, to ya faɗa musu cewa, ba za su ƙara fita yaƙi tare da shi ba har abada kuma ba za su ƙara yaƙar abokan gaba tare ba, saboda da farko sun yarda su zauna a gida su ƙi fita yaƙi a lokacin da aka nemi su fito tare da Annabi (ﷺ) zuwa yaƙin Tabuka. Don haka sai dai su yi ta zama a gida tare da yara da mata kamar yadda suka zaɓa a baya. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana Annabi (ﷺ) yi wa wani munafuki da ya mutu salla, ko ma ya tsaya a kan ƙabarinsa ya yi masa addu’a, saboda su munafukai sun kafirce wa Allah da Manzonsa sun kuma mutu suna fasiƙai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lokacin da Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan Salulu ya mutu an kirawo Annabi (ﷺ) don ya sallace shi. To yayin da ya tsaya domin aikata hakan sai na zabura zuwa wajensa na ce: “Ya Manzon Allah (ﷺ), yanzu kai za ka sallaci ɗan Ubayyu alhalin a rana kaza da kaza ya faɗi kaza da kaza?” Na riƙa lissafa masa miyagun maganganunsa da ya taɓa faɗa ga Annabi (ﷺ). Sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi fushi, ya ce: “Kauce mini daga nan ya Umar.” Lokacin da na nace masa sai ya ce: “Haƙiƙa an ba ni zaɓi, ni kuma na zaɓa. Da a ce na san idan na ƙara a kan nema musu gafara sau saba’in za a gafarta musu to da na ƙara.” Annabi (ﷺ) ya sallace shi ya juya ya tafi. To ba da jimawa ba sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyin biyu na wannan Sura (aya ta 84-85).” Sai Umar ya ce: “Na yi mamakin irin ƙarfin hali da na nuna wa Manzon Allah (ﷺ) a ranar. Allah da Manzonsa su ne mafi sani.” [Bukhari #1366]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa wa Manzonsa cewa, kada dukiyoyinsu da ‘ya’yansu su ƙayatar da shi, Allah yana nufin ya azabtar da su ne da waɗannan dukiyoyin da ‘ya’yan a nan duniya, sannan idan mutuwarsu ta zo rayukansu su fita daga jikkunansu suna kafirai.
وَإِذَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٌ أَنۡ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَجَٰهِدُواْ مَعَ رَسُولِهِ ٱسۡتَـٔۡذَنَكَ أُوْلُواْ ٱلطَّوۡلِ مِنۡهُمۡ وَقَالُواْ ذَرۡنَا نَكُن مَّعَ ٱلۡقَٰعِدِينَ
Open ayah 9:86Idan kuma aka saukar da wata sura mai cewa: “Ku yi imani da Allah kuma ku yi yaƙi tare da Manzonsa,” sai masu wadata daga cikinsu su nemi izininka su ce: “Ƙyale mu mu kasance tare da masu zama (a gida, wato mata da yara).”
رَضُواْ بِأَن يَكُونُواْ مَعَ ٱلۡخَوَالِفِ وَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَفۡقَهُونَ
Open ayah 9:87Sun yarda da su kasance tare da mata masu zaman gida, an kuma doɗe zukatansu, saboda haka ba sa ganewa.
لَٰكِنِ ٱلرَّسُولُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ جَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلۡخَيۡرَٰتُۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Open ayah 9:88Sai dai shi Manzo da waɗanda suka yi imani tare da shi sun yi yaƙi da dukiyoyinsu da kuma kawunansu. Waɗannan kuwa suna da alherai; kuma waɗannan su ne marabauta.
أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 9:89Allah Ya tanadar musu da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma. A waɗannan ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi cewa, idan aka saukar da wata sura ta Alƙur’ani wadda a cikinta aka yi umarni da yin imani da Allah da fita jihadi tare da Manzonsa (ﷺ), to sai ka ga munafukai masu wadata sun zo suna neman izinin zama a gida, suna cewa a rabu da su su zauna a gida tare da mata da yara. Sun yarda su yi zamansu a gidajensu tare da mata ne, saboda Allah ya rufe musu zukatansu ruf don haka ba sa gane duk wani wa’azi da ake yi musu. Sai dai waɗannan munafukai ya kamata su sani cewa, don sun yi zamansu sun ƙi fita yaƙi, wannan ba zai cutar da addinin Allah da komai ba, domin waɗanda suka fi su daraja a wurin Allah sun zabura wajen kare addinin Allah, su ne Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa, sun yi jihadi da dukiyoyinsu da kawunansu; to waɗannan Allah ya yi musu alƙawarin samun ni’imomi masu yawa a duniya da lahira, kuma su ne suka rabauta da ni’imar Aljanna. Allah ya yi musu tanadin gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudu ta ƙarƙashinsu, suna masu zama a cikinsu har abada; wannan kuwa shi ne babban rabo.
وَجَآءَ ٱلۡمُعَذِّرُونَ مِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ لِيُؤۡذَنَ لَهُمۡ وَقَعَدَ ٱلَّذِينَ كَذَبُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ سَيُصِيبُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 9:90Masu kawo uzurin ƙarya daga mutanen ƙauye kuma suka zo don a yi musu izini, sai kuma waɗanda suka yi wa Allah da Manzonsa ƙarya suka yi zamansu (ba tare da kawo hanzari ba). To azaba mai raɗaɗi za ta samu waɗanda suka kafirta daga cikinsu.
لَّيۡسَ عَلَى ٱلضُّعَفَآءِ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرۡضَىٰ وَلَا عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ مَا يُنفِقُونَ حَرَجٌ إِذَا نَصَحُواْ لِلَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ مَا عَلَى ٱلۡمُحۡسِنِينَ مِن سَبِيلٖۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 9:91Babu wani laifi a kan raunana ko marasa lafiya ko kuma waɗanda ba su samu abin da za su ciyar ba (don talauci), matuƙar dai sun tsarkake zuciyarsu ga Allah da Manzonsa. Babu wata hanya (ta ɗora laifi) ga masu kyautatawa. Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
وَلَا عَلَى ٱلَّذِينَ إِذَا مَآ أَتَوۡكَ لِتَحۡمِلَهُمۡ قُلۡتَ لَآ أَجِدُ مَآ أَحۡمِلُكُمۡ عَلَيۡهِ تَوَلَّواْ وَّأَعۡيُنُهُمۡ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمۡعِ حَزَنًا أَلَّا يَجِدُواْ مَا يُنفِقُونَ
Open ayah 9:92Haka kuma babu (laifi) a kan waɗanda idan sun zo maka don ka ba su abin hawa sai ka ce: “Ba ni da abin hawan da zan ba ku,” sai suka juya idanuwansu suna kwararar da hawaye don baƙin cikin ba su sami abin da za su ciyar ba.
۞إِنَّمَا ٱلسَّبِيلُ عَلَى ٱلَّذِينَ يَسۡتَـٔۡذِنُونَكَ وَهُمۡ أَغۡنِيَآءُۚ رَضُواْ بِأَن يَكُونُواْ مَعَ ٱلۡخَوَالِفِ وَطَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 9:93Zargi kawai yana kan waɗanda suke neman izininka alhali kuwa suna mawadata. Sun yarda da su kasance tare da masu zaman gida (mata da yara). Allah kuma Ya doɗe zukatansu, saboda haka ba sa sanin (gaskiya). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa Larabawan ƙauye sun yi ta zuwa wurin Manzon Allah (ﷺ) suna kawo masa uzurin ƙarya da ya ba su izinin zama a gida kada su fita yaƙi tare da shi, su kuma munafukai waɗanda suka yi wa Allah da Manzonsa ƙaryar da’awar imani suka yi zamansu ba su ma zo da wani uzuri ba. Allah ya ba da labarin cewa wata azaba mai raɗaɗi za ta sami waɗanda suka kafirta daga cikin Larabawan ƙauyen nan masu kawo uzurin ƙarya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zayyana uzururrukan da za su hana fita jihadi, inda ya ce, babu laifi a kan raunanan mutane da marasa lafiya da waɗanda ba su da guzurin fita don sun zauna ba su fita tare da Annabi (ﷺ) ba, matuƙar dai sun kansance sun tsarkake imaninsu da ayyukansu da niyyoyinsu ga Allah da taimakon addininsa da Annabinsa (ﷺ). Don haka babu wata hanya ta ɗora laifi a kan masu kyautatawa. Allah kuma mai yawan gafara ne mai jin ƙai, yana kuma yafe wa wanda ya yi laifi ya tuba, yana jin ƙan su ba ya yi musu azaba. Sannan aka bayyana hukuncin masu kawo uzurin ƙarya domin kada su fita jihadi tare da Manzon Allah (ﷺ), aka tabbatar da cewa, su ne za a azabtar domin suna ƙin fita ne duk da cewa su mawadata ne suna da abin hawa da makaman yaƙi da guzuri, amma sun yarda su zauna gida tare da mata. Allah kuma ya rufe zukatansu ruf wani alheri ba ya shigar su, saboda haka ba sa sanin gaskiya su yi aiki da ita.
يَعۡتَذِرُونَ إِلَيۡكُمۡ إِذَا رَجَعۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡۚ قُل لَّا تَعۡتَذِرُواْ لَن نُّؤۡمِنَ لَكُمۡ قَدۡ نَبَّأَنَا ٱللَّهُ مِنۡ أَخۡبَارِكُمۡۚ وَسَيَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 9:94Za su kawo muku uzurinsu idan kuka dawo musu. Ka ce: “Kada ku kawo wani uziri, mu ba za mu gaskata ku ba har abada, haƙiƙa Allah ya faɗa mana labarinku. Allah kuwa zai ga ayyukanku Shi da Manzonsa, sannan a komar da ku zuwa ga Masanin abin da yake ɓoye da na sarari, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.”
سَيَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ لَكُمۡ إِذَا ٱنقَلَبۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡ لِتُعۡرِضُواْ عَنۡهُمۡۖ فَأَعۡرِضُواْ عَنۡهُمۡۖ إِنَّهُمۡ رِجۡسٞۖ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 9:95Za su rantse muku da Allah idan kuka dawo wurinsu don ku ƙyale su. To ku ƙyale su ɗin. Lalle su najasa ne; makomarsu kuma wutar Jahannama ce sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa.
يَحۡلِفُونَ لَكُمۡ لِتَرۡضَوۡاْ عَنۡهُمۡۖ فَإِن تَرۡضَوۡاْ عَنۡهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يَرۡضَىٰ عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Open ayah 9:96Suna rantse muku don ku yarda da su; to idan ma kun yarda da su ɗin, lalle (Shi) Allah ba zai yarda da mutane fasiƙai ba. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa muminai cewa, munafukan da suka ƙi fita yaƙi ba tare da suna da wani uzuri ba, idan muminai sun dawo daga jihadinsu za su zo suna kawo musu uzururruka na ƙarya, sai Allah ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, kada ma su ce za su kawo wani uzuri, Annabi da sauran muminai ba za su yarda da su ba, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da su asirinsu, sun gane ƙarairayinsu, kuma Allah zai ga aikinsu, hakanan Manzonsa zai gani inda gaskiyarsu da ƙaryarsu za su bayyana. Sannan bayan mutuwarsu za a mayar da su ga Masanin ɓoye da sarari shi ne Allah, kuma zai ba su labarin duk abin da suka riƙa aikatawa a duniya kuma ya yi musu sakayya a kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan munafukai za su yi wa muminai rantsuwa da Allah yayin da suka dawo daga Tabuka, su nuna musu cewa su ba sun ƙi fita ne da gangan ba, abin ne ya fi ƙarfinsu, domin muminai su ƙyale su, ba za su zarge su a kan ƙin fita da gangan ba. Allah ya umarci muminai da cewa su ƙyale su ɗin, don wannan ya zamo wulaƙanci gare su, domin su najasa ne, makomarsu kuma a ranar lahira ita ce wutar Jahannama saboda abin da suka riƙa aikatawa na kafirci da munafunci da saɓon Allah da Manzonsa. Ya kuma ƙara da cewa, munafukan za su yi ta yi musu rantsuwa don su yarda da su, to amma ko da sun yarda da su, yardar ba za ta amfane su da komai ba, don haka su ma muminai kada su yarda da su domin Allah ba zai taɓa yarda da mutane fasiƙai ba.
ٱلۡأَعۡرَابُ أَشَدُّ كُفۡرٗا وَنِفَاقٗا وَأَجۡدَرُ أَلَّا يَعۡلَمُواْ حُدُودَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Open ayah 9:97Mutanen ƙauye sun fi tsananin kafirci da munafunci, kuma su suka fi dacewa da rashin sanin dokokin da Allah Ya saukar wa Manzonsa. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima.
وَمِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مَن يَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ مَغۡرَمٗا وَيَتَرَبَّصُ بِكُمُ ٱلدَّوَآئِرَۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 9:98Daga mutanen ƙauye kuma akwai waɗanda suke ɗaukar abin da suke ciyarwa tara ne, suke kuma jiran faruwar masifu gare ku. To mummunar masiba ta tabbata a kansu. Allah kuma Mai ji ne, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, ƙauyawa sun fi tsananin kafirci da munafunci fiye da ‘yan birni, sannan su suka fi dacewa da rashin sanin halal da haram da sauran dokokin da Allah ya saukar wa Annabi (ﷺ). Allah kuwa masani ne mai hikima cikin dukkan lamarinsa. Daga cikin ƙauyawa akwai wanda yake ɗaukar dukiyar da yake bayarwa wajen aikin alheri kamar tara ce Annabi (ﷺ) yake karɓa a hannunsa, don haka yana ganin hasara kawai yake yi; yana dai bayarwa ne kawai ba don yana so ko yana fatan samun wani lada daga Allah ba. Hasali ma yana sauraron faruwar wani mummunan abu ne ga Musulmi, kamar a ce maƙiyansu sun yi nasara a kansu, har ma duk al’amuransu su lalace. To amma sai Allah ya mayar musu da aniyarsu, mummunan abu ya tabbata a kansu wanda zai dugunzuma rayuwarsu gaba ɗaya. Allah kuma mai ji ne ga dukkan maganganunsu, kuma masanin abin da yake cikin zukatansu ne, don haka zai yi musu sakayya da abin da suka cancanta.
وَمِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ قُرُبَٰتٍ عِندَ ٱللَّهِ وَصَلَوَٰتِ ٱلرَّسُولِۚ أَلَآ إِنَّهَا قُرۡبَةٞ لَّهُمۡۚ سَيُدۡخِلُهُمُ ٱللَّهُ فِي رَحۡمَتِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 9:99Daga mutanen ƙauye ɗin kuma akwai waɗanda suke yin imani da Allah da ranar lahira, suke kuma ɗaukar abin da suke ciyarwa (hanyoyi ne) na samun kusanci ga Allah da kuma addu’o’in Manzo. Lalle wannan ibada ce gare su. Allah zai shigar da su cikin rahamarsa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلۡأَوَّلُونَ مِنَ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ وَٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُم بِإِحۡسَٰنٖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي تَحۡتَهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 9:100Magabata kuwa na farko daga cikin masu hijira da Ansaru da kuma waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa, (duka) Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi, Ya kuma tanadar musu gidajen Aljanna da ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wannan shi ne rabo mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, mutanen ƙauye ba duka suka taru suka zama ɗaya ba; daga cikinsu akwai ƙauyawa masu imani da Allah da Manzonsa (ﷺ) da ranar alƙiyama, sannan suke yarda cewa abin da suke ciyarwa na dukiyarsu wasu hanyoyi ne masu kusanta su da Allah, suke kuma neman addu’o’in Manzon Allah (ﷺ) da wannan sadakar tasu, wato lokacin da zai karɓi zakkarsu ko sadakarsu. Tabbas wannan sadakar tasu da kuma addu’o’in Annabi (ﷺ) ibada ce babba mai kusantar da su ga Allah, don haka Ubangijinsu zai shigar da su cikin rahamarsa. Lalle Allah mai gafara ne mai jin ƙai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matsayin sahabban Annabi (ﷺ) waɗanda su ne magabata na farko da suka yi imani kuma suka yi hijira daga Makka zuwa Madina, da kuma su muminai mutanen Madina waɗanda suka taimaka wa Annabi (ﷺ) da sahabbansa lokacin da suka je Madina suna baƙi ba su san kowa ba, da kuma sauran muminai waɗanda suka biyo bayansu, suka kuma bi hanyarsu madaidaiciya ta imani da kyakkyawan aiki, to duka waɗannan Allah ya yarda da su, su ma sun yarda da Allah, ya kuma yi musu tanadin gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su shige su, su kuma dawwama a cikinsu har abada; wannan kuwa shi ne babban rabo.
وَمِمَّنۡ حَوۡلَكُم مِّنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مُنَٰفِقُونَۖ وَمِنۡ أَهۡلِ ٱلۡمَدِينَةِ مَرَدُواْ عَلَى ٱلنِّفَاقِ لَا تَعۡلَمُهُمۡۖ نَحۡنُ نَعۡلَمُهُمۡۚ سَنُعَذِّبُهُم مَّرَّتَيۡنِ ثُمَّ يُرَدُّونَ إِلَىٰ عَذَابٍ عَظِيمٖ
Open ayah 9:101Kuma daga mutanen ƙauye waɗanda suke kewaye da ku akwai munafukai, haka kuma daga mutan Madina; sun ƙware a kan munafunci, kai ba ka san su ba; Mu ne Muka san su. Za Mu azabtar da su sau biyu, sannan a komar da su zuwa ga azaba mai girma.
وَءَاخَرُونَ ٱعۡتَرَفُواْ بِذُنُوبِهِمۡ خَلَطُواْ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَءَاخَرَ سَيِّئًا عَسَى ٱللَّهُ أَن يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Open ayah 9:102Wasu kuwa sun yi iƙirari da laifinsu, sun gauraya kyakkyawan aiki da wani mummuna, to tabbas Allah zai karɓi tubansu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, daga cikin mazauna ƙauyukan da suke zagaye da Madina akwai munafukai, hakanan a cikin mazauna Madina ma akwai su, sun ƙware sosai a kan munafunci har ya zamar musu jiki, kuma sun doge a kansa sun ƙi su tuba. Amma Allah ya ce shi ya san su Annabi (ﷺ) ne bai san su ba, Allah kuma ya yi alƙawarin sai ya yi musu azaba sau biyu, azabar duniya da ta ƙabari, sannan ranar alƙiyama ya mayar da su zuwa azaba mai girma. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, akwai mutanen da suka yi iƙirari da laifinsu, watau sun haɗa kyakkyawan aiki da mummuna, su kam wataƙila Allah ya karɓi tubansu. Waɗannan su ne mutanen kirki waɗanda su ba munafukai ne ba, suna da ayyukan ƙwarai amma sai ba su fita yaƙin Tabuka tare da Manzon Allah (ﷺ) ba, daga baya suka tuba Allah kuma ya karɓi tubansu. Haƙiƙa Allah mai gafara ne ga duk wanda ya tuba, mai jin ƙai ne gare su ba zai yi musu azaba ba. An karɓo daga Samuratu ɗan Jundab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce mana: “A daren jiya wasu mala’iku biyu sun zo mini, suka tashe ni daga barci, suka tafi da ni har zuwa wani birni wanda aka gina shi da tubalan zinare da na azurfa, sai wasu mutane suka tarye mu, rabin halittarsu na da kyau matuƙa, rabinta kuwa yana da matuƙar muni, sai mala’ikun nan biyu suka ce musu: ‘Ku je ku faɗa cikin waccan ƙoramar.’ Sai suka je suka tsunduma cikinta, suka dawo duk wannan munin ya rabu da su, sun yi matuƙar kyan kamanni. Sai mala’ikun suka ce mini: ‘Wannan ita ce Aljannar dawwama, wancan kuma gidanka ne, waɗannan mutanen kuwa waɗanda rabinsu mai kyau ɗaya rabin nasu mummuna su ne waɗanda suka gauraya aiki mai kyau da mummunan aiki, sai kuma Allah ya yafe musu.’ [Bukhari #4674].
خُذۡ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡ صَدَقَةٗ تُطَهِّرُهُمۡ وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ عَلَيۡهِمۡۖ إِنَّ صَلَوٰتَكَ سَكَنٞ لَّهُمۡۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Open ayah 9:103Ka karɓi sadaka daga dukiyoyinsu da za ka tsarkake su kuma ka gyara musu halaye da ita, ka kuma yi musu addu’a. Lalle addu’arka nutsuwa ce a gare su. Allah kuwa Mai ji ne, Masani.
أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ هُوَ يَقۡبَلُ ٱلتَّوۡبَةَ عَنۡ عِبَادِهِۦ وَيَأۡخُذُ ٱلصَّدَقَٰتِ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 9:104Shin yanzu ba su sani ba ne cewa Allah shi Yake karɓar tuba daga bayinsa Yake kuma karɓar sadakoki, kuma lalle Shi ne Mai yawan karɓar tuba, Mai jin ƙai? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya karɓi zakka daga dukiyoyin Musulmi mawadata, don ya tsarkake su daga dauɗar zunubansu da wannan zakkar, kamar yadda ya umarce shi da yi musu addu’a lokacin da yake karɓar zakkarsu, domin addu’arsa nutsuwa ce a gare su da hutu ga zukatansu. Allah mai ji ne masani. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Sadaka kuwa tana gusar da laifi kamar yadda ruwa yake kashe wuta.” [Ahmad #15284, da Abu Ya’la #1999, da Ibn Hibban #1723]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abu Aufa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan mutane suka zo masa da sadakarsu sai ya karɓa ya ce: “Ya Allah, ka yi musu salati.” Sai baban Abu Aufa ya zo masa da sadakarsa sai ya ce: “Allah ka yi salati ga iyalan Abu Aufa.” [Bukhari #1497, da Muslim #1078]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da cewa, shin yanzu ba su sani ba ne cewa Allah ne kaɗai yake karɓar tuban waɗanda suka tuba, kuma yake karɓar sadakar bayinsa, kuma shi ne mai yawan karɓar tuba mai yawan rahama? An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Babu wanda zai bayar da sadaka daga dukiyarsa ta halal mai tsarki-Allah ba ya karɓa sai mai tsarki-face Allah mai rahama ya karɓe ta da hannunsa na dama, ko da kuwa ƙwayar dabino ne, haka zai karɓe shi ya yi ta haɓaka a hannun Allah mai rahama har sai ya fi tsauni girma, kamar yadda ɗayanku yake rainon dukushin dokinsa ko ɗan maraƙinsa.” [Bukhari #1410, da Muslim #1014].
وَقُلِ ٱعۡمَلُواْ فَسَيَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۖ وَسَتُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 9:105Ka kuma ce: “Ku yi aiki, Allah ne zai ga aikinku shi da Manzonsa da kuma muminai, kuma za a mayar da ku zuwa ga Masanin abin da yake ɓoye da na sarari, sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
وَءَاخَرُونَ مُرۡجَوۡنَ لِأَمۡرِ ٱللَّهِ إِمَّا يُعَذِّبُهُمۡ وَإِمَّا يَتُوبُ عَلَيۡهِمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Open ayah 9:106Wasu kuwa an jinkirta lamarinsu ne ga hukuncin Allah, ko dai ya azabtar da su ko kuma Ya karɓi tubarsu. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) cewa, ya faɗa wa waɗannan da suka ƙi fita yaƙi kuma suka zo suka ba da hanzari sannan suka tuba cewa, su yi aiki Allah ne zai ga aikinsu na zahiri da na baɗini, ya kuma yi musu sakayya a kai, hakanan Manzonsa (ﷺ) da muminai su ma za su ga abin da Allah ya nuna musu na ayyukansu don su yi musu shaida a kai mai kyau ko marar kyau. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu mutane sun wuce ɗauke da wata gawa sai sahabbai suka faɗi alherin wannan mamacin, sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ta wajaba.” Sai wasu kuma suka sake wucewa da wata gawar, sai sahabbai suka yi mata mummunar shaida, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ta wajaba.” Sai Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mece ce ta wajaba?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Kun faɗi alheri a kan na farko sai Aljanna ta wajaba gare shi. Wannan kuwa kun bayar da mummunar shaida a kansa sai wuta ta wajaba a kansa; ku ne masu bayar da shaida a bayan ƙasa.” [Bukhari #1367]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, za a mayar da su zuwa ga Allah ranar alƙiyama, wanda shi ne masanin abin da yake ɓoye da na sarari, zai kuma ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, cikin waɗanda suka ƙi fita yaƙin Tabuka akwai wasu mutane da aka jinkirtar da lamarinsu aka mayar da hukuncinsu ga Allah, shi ne wanda zai yi musu hukunci ranar alƙiyama da abin da ya ga dama; ko dai ya yi musu azaba ko kuma ya karɓi tubarsu. Allah kuma masani ne mai hikima; ya san kowane ɓangare da halayyarsa da abin da yake cikin zukatansu, ko sun cancanci uƙuba ko kuma sun cancanci afuwa, yana sanya hukuncinsa a inda ya dace, yana kuma da hikima cikin duk maganganunsa da ayyukansa.
وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مَسۡجِدٗا ضِرَارٗا وَكُفۡرٗا وَتَفۡرِيقَۢا بَيۡنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَإِرۡصَادٗا لِّمَنۡ حَارَبَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ مِن قَبۡلُۚ وَلَيَحۡلِفُنَّ إِنۡ أَرَدۡنَآ إِلَّا ٱلۡحُسۡنَىٰۖ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 9:107Waɗanda kuwa suka gina masallaci don cutarwa da kafirci da rarraba kawunan muminai da kuma ba da mafaka ga wanda ya yaƙi Allah da Manzonsa tun da can. Kuma lalle za su rantse da Allah cewa ba su yi nufin komai ba sai abu mafi kyau, Allah kuwa Yana ba da shaidar cewa lalle su tabbas maƙaryata ne.
لَا تَقُمۡ فِيهِ أَبَدٗاۚ لَّمَسۡجِدٌ أُسِّسَ عَلَى ٱلتَّقۡوَىٰ مِنۡ أَوَّلِ يَوۡمٍ أَحَقُّ أَن تَقُومَ فِيهِۚ فِيهِ رِجَالٞ يُحِبُّونَ أَن يَتَطَهَّرُواْۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُطَّهِّرِينَ
Open ayah 9:108Kada ka yi salla a cikinsa har abada. Haƙiƙa masallacin da aka ɗora harsashinsa tun daga ranar farko a kan taƙawa shi ya cancanci ka yi salla a cikinsa. A cikinsa akwai wasu mazaje da suke so su tsarkaka. Allah kuwa Yana son masu tsarkaka.
أَفَمَنۡ أَسَّسَ بُنۡيَٰنَهُۥ عَلَىٰ تَقۡوَىٰ مِنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٍ خَيۡرٌ أَم مَّنۡ أَسَّسَ بُنۡيَٰنَهُۥ عَلَىٰ شَفَا جُرُفٍ هَارٖ فَٱنۡهَارَ بِهِۦ فِي نَارِ جَهَنَّمَۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 9:109Yanzu wanda ya sanya harhashin gininsa a kan taƙawa ga Allah da (neman) yardarsa shi ya fi ko kuwa wanda ya sanya harshashin gininsa a gefen rami mai zabtarewa, sai ya rubta da shi cikin wutar Jahannama? Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai.
لَا يَزَالُ بُنۡيَٰنُهُمُ ٱلَّذِي بَنَوۡاْ رِيبَةٗ فِي قُلُوبِهِمۡ إِلَّآ أَن تَقَطَّعَ قُلُوبُهُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Open ayah 9:110Ginin nasu da suka yi ba zai daina zama abin kokwanto a zukatansu ba har sai zukatan nasu sun tsittsinke. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin wasu munafukai ne da suka gina wani masallaci a Madina da nufin cutar da muminai domin su riƙa haɗuwa a cikinsa suna ƙulle-ƙullen sharri da makirci, da aikata kafirci da rarraba kan muminai da kuma bayar da mafaka ga wanda yake yaƙar Allah da Manzonsa tun kafin gina masallacin. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk da waɗannan munanan manufofin da suke da su waɗanda Allah ya fallasa su a kai, za su yi ta rantsuwa da Allah cewa ba su yi nufin komai ba sai kyautatawa. Amma Allah yana ba da shaidar cewa lalle su maƙaryata ne. Ibnu Ishaƙa babban malamin Siran nan ya bayyana yadda wannan lamari ya kasance. Watau tun kafin Annabi (ﷺ) ya yi hijira zuwa Madina akwai wani mutum ɗan ƙabilar Khaza’atu mai suna Abu Amir Ar-Rahib wanda ya karɓi addinin Nasaranci. Yayin da Musulunci ya zo sai ya ƙi ba da gaskiya da shi. To bayan Manzon Allah (ﷺ) ya yi hijira zuwa Madina, Musulunci ya yaɗu ya kuma yi ƙarfi, sai Abu Amir ya gudu ya koma cikin Rumawa yana neman su taimaka masa don ya yaƙi Musulunci. Sannan ya koma Makka wajen kafiran Ƙuraishawa ya ci gaba da zuga su don su ci gaba da yaƙar Annabi (ﷺ) da sahabbansa, har zuwa lokacin da aka yi yaƙin Uhudu. To bayan an ƙare yaƙin Uhudu Abu Amir ya ga yadda al’amarin Musulunci yake ƙara bunƙasa, sai ya gudu zuwa wurin Hiraƙla sarkin Rumawa yana neman taimakonsa a kan yaƙar Annabi (ﷺ), shi kuma ya yi masa alƙawarin taimakawa. Sai Abu Amir ya rubuto wa mutanensa munafukai, yana sanar da su cewa, ga shi nan tafe da rundunar mayaƙa da za su yaƙi Annabi su kuma ci nasara a kansa. Har ma ya umarce su da su gina masa wata mafaka inda jakadunsa za su riƙa kai-kawo kafin lokacin isowarsa ya yi. Saboda haka sai suka fara gina wani masallaci kusa da Masallacin Ƙuba. Bayan da suka gama ginin sai suka nemi Manzon Allah (ﷺ) kan ya zo ya albarkace shi da yin salla a cikinsa, suka kuma ce, wai sun gina shi ne saboda tsofaffi da raunana da masu wata larura su sami yin salla a cikinsa, musamman ma a lokacin sanyi. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ba su amsar cewa, ba zai samu damar yin salla ba a wannan lokacin, saboda yana kan hanyarsa ne ta zuwa yaƙin Tabuka, sai dai idan Allah ya dawo da shi da yardar Allah zai yi. To lokacin da Manzon Allah (ﷺ) yake komowa daga Tabuka ne wahayi ya zo masa yana ba shi labarin manufar gina wannan masallacin, wato an gina shi ne don cutar da addinin Musulunci da raba kawunan Musulmi da bayar da mafaka ga maƙiyansu. Sai Annabi (ﷺ) ya umarci Malik ɗan Dukhshum da Ma’anu ɗan Adiyyu da Wahshi da su je su rushe wannan masallaci. Suka kuma je suka cika aiki, suka ƙona shi ƙurmus, aka mayar da kufansa juji wurin zubar da shara, don kawai a wulaƙanta su tare da wannan mummunan aiki da suka yi. [Dubi, Ibn Kasir, Tafsir , Juzu’i na 2, Shafi na 388]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana Annabi (ﷺ) ya yi salla a masallacin munafukai a kowane lokaci, ya bayyana cewa, masallacin da aka ɗora harsashinsa a kan tsoron Allah tun daga ranar farko shi ya fi cancanta Annabi (ﷺ) ya yi salla a cikinsa, domin a cikinsa akwai wasu mazaje da suke son su tsarkaka daga kowace najasa da zunubi. Allah kuwa yana son masu tsarkaka. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na shiga wajen Manzon Allah (ﷺ) a ɗaya daga cikin gidajen matansa sai na ce: “Wane masallaci ne aka ɗora harsashinsa a kan tsoron Allah?” Ya ce: Sai ya ɗebi tsakuwoyi a tafin hannunsa ya zubar da su ƙasa, sannan ya ce: “Shi ne wannan masallacin naku, wato masallacin Madina.” [Muslim #1398]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ɗan ƙabilar Banu Khudra ya yi jayayya da wani ɗan ƙabilar Banu Amri ɗan Auf a kan ko wane masallaci ne aka sanya harsashinsa a kan tsoron Allah? Sai ɗan ƙabilar Banu Khudra ya ce, shi ne masallacin Manzon Allah (ﷺ), sai ɗayan ya ce shi ne masallacin Ƙuba. Sai suka je wajen Annabi (ﷺ) suka tambaye shi sai ya ce: “Shi ne wannan masallacin.” Yana nufin masallacinsa, sai kuma ya ce: “Wancan ma yana tattare da alheri mai yawa.” [Tirmizi #323, da Nasa’i #796, da Ahmad #11178]. Da yawa daga cikin malaman tafsiri suna ganin wannan ayar tana nufin masallacin Ƙuba ne. Wasu kuma cikinsu suna ganin tana nufin masallacin Manzon Allah ne. To amma ko da ta sauka ne a kan masallacin Ƙuba sai dai hukuncita ya haɗo har da masallacin Manzon Allah (ﷺ) domin shi ne ya fi cancanta a siffanta shi da wannan sifa. Wasu malamai suna ganin ayar tana iya nufin duka masallatan biyu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba za a taɓa daidaita ginin da aka sanya harsashinsa a kan tsoron Allah da neman yardarsa da wanda aka sanya harsashin gininsa a gaɓar rami mai zaftarewa wanda yake gab da ya rufta da ginin da ke kansa, daga ƙarshe kuma ya rufta da wannan ginin da mai ginin cikin wutar Jahannama. Allah kuma ba ya shiryar da mutane azzalumai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan gini na masallacin bogi da nufin cutarwa da suka yi ya gadar musu da shakka da munafunci a zukatansu waɗanda ba za su gushe ba, har sai zukatan nasu sun tsuntsunke su mutu a kan haka. Allah kuwa Masani ne Mai hikima.
۞إِنَّ ٱللَّهَ ٱشۡتَرَىٰ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَنفُسَهُمۡ وَأَمۡوَٰلَهُم بِأَنَّ لَهُمُ ٱلۡجَنَّةَۚ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَيَقۡتُلُونَ وَيُقۡتَلُونَۖ وَعۡدًا عَلَيۡهِ حَقّٗا فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ وَٱلۡقُرۡءَانِۚ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِعَهۡدِهِۦ مِنَ ٱللَّهِۚ فَٱسۡتَبۡشِرُواْ بِبَيۡعِكُمُ ٱلَّذِي بَايَعۡتُم بِهِۦۚ وَذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 9:111Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaƙi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alƙawari ne na gaskiya da Ya ɗaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alƙur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alƙawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan kuwa shi ne rabo mai girma.
ٱلتَّٰٓئِبُونَ ٱلۡعَٰبِدُونَ ٱلۡحَٰمِدُونَ ٱلسَّٰٓئِحُونَ ٱلرَّٰكِعُونَ ٱلسَّٰجِدُونَ ٱلۡأٓمِرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَٱلنَّاهُونَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡحَٰفِظُونَ لِحُدُودِ ٱللَّهِۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 9:112Masu tuba, masu bauta, masu godiya, masu azumi, masu ruku’i, masu sujjada, masu yin umarni da aikin alheri masu kuma hani ga mummunan aiki, da masu kiyaye iyakokin Allah. To sai ka yi wa muminai (masu irin waɗannan siffofin) albishir. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, ya yi wani babban ciniki tsakaninsa da muminai, inda ya ce ya sayi rayukansu da dukiyoyinsu daga wurinsu, ya kuma sanya Aljanna ita ce farashin biyansu, a kan za su yi yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah, ko su kashe kafirai ko kuma su a kashe su, to tabbas Aljanna ta wajaba gare su, wannan alƙawari ne na Allah tabbatacce a cikin littafin Attaura da Linjila da Alƙur’ani. Babu kuwa wanda ya fi Allah kyan cika alƙawari. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai masu jihadi da su yi farin ciki da wannan ciniki da suka ƙulla da Allah, wannan kuma shi ne babban rabo. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta muminai waɗanda ya sayi rayukansu da dukiyoyinsu daga wurinsu da cewa, su ne masu tuba daga saɓon Allah, masu bautar Allah cikin ƙauna da ƙasƙantar da kai, masu yabo da godiya ga Allah a kowane hali nasu, masu yin azumi, masu salla suna ruku’i da sujjada a sallolinsu na farilla da na nafila, masu yin umarni da kyakkyawan aiki, wato abin da Allah da Manzonsa suke umarni da shi na imani da Allah da ayyuka na ƙwarai, suna kuma hana mummunan aiki, watau duk abin da Allah da Manzonsa (ﷺ) suka hana, masu kiyaye iyakokin Allah, suna aiki da umarninsa da haninsa, ba sa tozarta wani hukunci na cikin shari’ar Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da cewa ya yi wa waɗannan muminai albishir da samun duk wani alheri na duniya da na lahira.
مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن يَسۡتَغۡفِرُواْ لِلۡمُشۡرِكِينَ وَلَوۡ كَانُوٓاْ أُوْلِي قُرۡبَىٰ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمۡ أَنَّهُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 9:113Bai kamata ba ga Annabi da waɗanda suka yi imani su nema wa mushrikai gafara, ko da kuwa sun kasance dangi ne na kusa, bayan kuwa ya riga ya bayyana gare su cewa lalle su ‘yan wuta ne.
وَمَا كَانَ ٱسۡتِغۡفَارُ إِبۡرَٰهِيمَ لِأَبِيهِ إِلَّا عَن مَّوۡعِدَةٖ وَعَدَهَآ إِيَّاهُ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥٓ أَنَّهُۥ عَدُوّٞ لِّلَّهِ تَبَرَّأَ مِنۡهُۚ إِنَّ إِبۡرَٰهِيمَ لَأَوَّٰهٌ حَلِيمٞ
Open ayah 9:114Neman gafarar Ibrahimu kuwa ga babansa bai kasance ba sai don kawai alƙawarin da ya yi masa ne. To lokacin da ya bayyana gare shi cewa shi maƙiyin Allah ne sai ya nesanta kansa da shi. Lalle Ibrahimu ya tabbata mai yawan bautar Allah ne, mai haƙuri.
وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِلَّ قَوۡمَۢا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰهُمۡ حَتَّىٰ يُبَيِّنَ لَهُم مَّا يَتَّقُونَۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ
Open ayah 9:115Allah kuwa ba zai taɓa ɓatar da wasu mutane ba bayan Ya riga Ya shiryar da su, har sai Ya bayyana musu abin da za su kiyaye. Lalle Allah Masanin komai ne.
إِنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۚ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ
Open ayah 9:116Lalle Allah Shi ne Mai mulkin sammai da ƙasa, Yana rayawa kuma Yana kashewa. Ba ku da wani majiɓincin lamarinku in ban da Allah, ba ku kuma da wani mai taimako. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana hukuncin nema wa waɗanda suka mutu a kan shirka gafarar Allah, ya bayyana cewa, bai dace ba ga Annabi (ﷺ) da muminai su nema wa mushirikai gafarar Allah ko da kuwa sun kasance dangi ne na kusa, bayan sun gane cewa su ‘yan wuta ne domin sun mutu suna kafirci ba su tuba ba. Sai Allah Ta’ala ya bayyana cewa, neman gafarar da Annabi Ibrahimu ya yi wa mahaifinsa, ya yi shi ne kawai don alƙwarin da ya ɗaukar masa na cewa zai nema masa gafarar Allah, kamar yadda ya zo a cikin Suratu Maryam , aya ta 47. To amma lokacin da Annabi Ibrahimu ya tabbatar da cewa mahaifin nasa maƙiyin Allah ne sai ya nesanta kansa daga gare shi. Lalle Annabi Ibrahimu mai yawan ƙasƙantar da kansa ne ga Allah da yawan roƙon Allah, zuciyarsa kuma na cike da tsoro da fata, kuma mai yawan juriya ne da haƙuri a kan duk abin da ake yi masa na musgunawa. An karɓo daga Sa’idu ɗan Musayyab shi kuma daga mahaifinsa ya ce: Lokacin da Abu Ɗalibi yake dab da barin duniya, Manzon Allah (ﷺ) ya je wajensa, sai ya samu Abu Jahlin da Abdullahi ɗan Abu Umayya a wurinsa, sai ya ce da shi: “Baffa, ka ce: Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Da wannan kalmar ne zan yi maka shaida a wurin Allah.” Sai Abu Jahlin da Abdullahi ɗan Abu Umayyata suka ce masa: “Ya Abu Ɗalibi, yanzu ashe za ka guji tafarkin Abdulmuɗɗalib?” Annabi (ﷺ) ya ci gaba da bijirar masa da Kalmar Shahada, su kuma suna ci gaba da nanata masa waccan maganar har daga ƙarshe dai Abu Ɗalibi ya ce shi yana nan a kan tafarkin Abdulmuɗɗalib, ya ƙi karɓar Kalmar Shahada. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle zan nema maka gafara muddin dai ba a hana ni ba.” To a sannan ne wannan ayar ta sauka. [Bukhari #3884, da Muslim #24]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ba zai ɓatar da wasu mutane ba bayan ya shiryar da su sun yi imani, har sai ya bayyana musu abin da ya wajaba a kansu su kiyaye. Lalle kuwa Allah masanin komai ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya ba da labarin cewa, lalle shi ne kaɗai mai mulkin sammai da ƙasa, yana rayawa yana kashewa, kuma mutane ba su da wani majiɓincin al’amuransu wanda zai amfanar da su in ban da shi Allah (Mai tsarki da daukaka), shi ne kuma kaɗai mai taimakon su.
لَّقَد تَّابَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلنَّبِيِّ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ ٱلۡعُسۡرَةِ مِنۢ بَعۡدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٖ مِّنۡهُمۡ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّهُۥ بِهِمۡ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 9:117Tabbas haƙiƙa Allah Ya yafe wa Annabi da masu hijira da kuma Ansaru waɗanda suka bi shi a lokacin tsanani bayan har zukatan wasu ƙungiyoyi daga cikinsu sun kusa su karkace, sannan (Allah) Ya karɓi tubansu. Lalle Shi Mai tausasawa ne, Mai jin ƙai a gare su.
وَعَلَى ٱلثَّلَٰثَةِ ٱلَّذِينَ خُلِّفُواْ حَتَّىٰٓ إِذَا ضَاقَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ وَضَاقَتۡ عَلَيۡهِمۡ أَنفُسُهُمۡ وَظَنُّوٓاْ أَن لَّا مَلۡجَأَ مِنَ ٱللَّهِ إِلَّآ إِلَيۡهِ ثُمَّ تَابَ عَلَيۡهِمۡ لِيَتُوبُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 9:118Kuma (Ya yafe wa) mutanen nan guda uku waɗanda aka dakatar da karɓar tubansu, har sai yayin da duniya ta yi musu ƙunci duk da yalwarta, kuma zukatansu suka ƙuntata, suka tabbatar da cewa dai babu wata mafaka daga Allah sai dai a wajensa. Sannan sai Ya yi musu muwafaƙar tuba don su tuba. Lalle Allah Shi ne Mai yawan karɓar tuba, Mai jin ƙai.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَكُونُواْ مَعَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 9:119Ya ku waɗanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah kuma ku zama tare da masu gaskiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da batun waɗanda suka fita yaƙin Tabuka tare da Manzon Allah (ﷺ) da waɗanda suka ƙi fita ba tare da wata lalura ba, sannan su kuma ba munafukai ne ba; Shaiɗan ne kawai ya ribace su ya hana su bin Manzon Allah (ﷺ). Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labari cewa, ya yafe wa Annabi da waɗanda suka yi hijira da mutanen Madina waɗanda suka fita tare da shi zuwa yaƙin Tabuka a lokacin da ake tsananin zafin rana ga kuma tafiya mai nisa sannan ga ƙarancin guzuri da abin hawa. Haƙiƙa Allah ya yafe musu bayan zukatan wasu sahabbai sun kusa su kauce wa gaskiya, to amma sai ya karɓi tubarsu. Lalle Allah mai tausaya musu ne mai jin ƙan su. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) game da labarin Rundunar Tsanani (mayaƙan da suka fita yaƙin Tabuka) sai ya ce: “Mun fita tare da Manzon Allah (ﷺ) cikin tsananin zafi zuwa Tabuka sai muka sauka wani masauki inda muka haɗu da ƙishirwa mai tsanani, har sai da muka riƙa tsammanin wuyoyinmu za su tsinke, har ta kai mutum zai fita neman ruwa ba zai dawo ba sai yana jin kamar wuyansa zai tsinke. Har sai da ta kai mutum zai yanka raƙuminsa ya tatse tumbinsa don ya samu ruwan da zai sha. Sai Abubakar ya ce: “Ya Manzon Allah (ﷺ), Allah ya saba da yi maka alheri idan ka roƙe shi, to ka roƙa mana Allah.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kana son hakan?” Sai ya ce: “E.” Sai ya ɗaga hannayensa yana addu’a, bai saukar da su ba har sai da hadari ya gangamo sama ta kece da ruwa. Sahabbai suka cika abubuwan da ke tare da su, sannan muka dawo muna duba sama sai muka ga hadarin bai wuce wannan rundunar tamu ba.” [Ibnu Khuzaima #101, da Ibnu Hibban #1383]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya karɓi tuban wasu sahabbai waɗanda suka ƙi fita yaƙin Tabuka tare da Manzon Allah (ﷺ) ba tare da wani dalili ba, wato Ka’abu ɗan Maliki da Muraratu ɗan Rabi’atu Al-Amiri da Hilalu ɗan Umayyata Al-Waƙifi. Bayan dawowar Manzon Allah (ﷺ) garin Madina, munafukai suka yi ta zuwa wurinsa suna bayyana masa uzururrukan ƙarya, yana karɓa yana nema musu gafarar Allah, to amma su waɗannan ukun suka ƙi yarda su yi masa ƙarya, suka fito fili suka faɗa masa gaskiya cewa ba su da wani dalilin da ya hana su fita yaƙi tare da shi, sai dai kawai ruɗin Shaiɗan. Annabi (ﷺ) ya umarci sahabbai da su ƙaurace musu har sai Allah ya saukar da hukunci a kansu, su ma daga ƙarshe ya umarci matansu da su ƙaurace musu, suka kuwa ƙaurace musu, sai matar Hilalu ce kaɗai ta nemi alfarmar Annabi (ﷺ) a kan ya yi mata izini ta zauna tare da shi tana yi masa hidima saboda kasancewarsa tsoho ne yana buƙatar wani tare da shi, Annabi (ﷺ) ya yi mata izini amma ya faɗa mata cewa kada ta yarda ya kusance ta. Saboda haka suka zauna cikin ƙunci da wahalar rayuwa lokaci mai tsawo, duniya kuma ta yi musu zafi, suka rasa inda za su sa kansu; suka tabbatar da cewa babu wata mafaka sai dai wurin Allah, saboda haka suka koma gare shi suna neman gafara da afuwa game da laifin da suka aikata. [Dubi, Bukhari #4418, da Muslim #2769]. Bayan waɗannan sahabbai su uku sun kwana hamsin a cikin wannan hali mawuyaci, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya dube su da rahamarsa da afuwarsa ya yi musu katari ya karɓi tubansu, ya saukar da waɗannan ayoyi inda ya bayyana cewa, ya yafe wa sahabban nan guda uku waɗanda Annabi (ﷺ) ya dakatar da hukunci a kansu har sai Allah ya yi hukunci a kansu, har lokacin da duniya ta yi musu ƙunci duk kuwa da yalwarta, kuma zukatansu suka ƙuntata gare su, saboda abin da suke ciki na baƙin ciki da damuwa da tashin hankali; suka tabbatar da cewa dai babu wata mafaka da za su fake a wurinta sai Allah, sai Allah ya musu gamon-katar da samun tuba, suka tuba Allah ya karɓi tubansu don su koma su ci gaba da bin umarninsa. Lalle Allah mai yawan karɓar tuba ne mai jin ƙai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai gaba ɗaya da su kiyaye dokokinsa kuma a koyaushe su kasance tare da masu gaskiya. An karɓo daga Ka’abu ɗan Malik ya ce: Lokacin da ayoyin yafiya gare su suka sauka ya zo gaban Manzon Allah (ﷺ) ya zauna ya ce: “Yana daga cikin tuban da zan yi in bayar da dukiyata gaba ɗayanta ga Allah da Manzonsa.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce da shi: “Ka riƙe wani ɓangare na dukiyarka ya fi maka alheri.” Sai ya ce: “To zan riƙe kaso na Khaibar.” Ya kuma ce: “Ya Manzon Allah, Allah ya tserar da ni ne kawai saboda faɗar gaskiya da na yi, to yana daga sharaɗin tubana cewa ba zan ƙara faɗar abin da ba gaskiya ba har abada.” Ya ce: “Na rantse da Allah, babu wani Musulmin da Allah ya jarrabe shi a kan faɗar gaskiya tun lokacin da na faɗa wa Manzon Allah abin da na faɗa masa har zuwa yau ɗin nan da irin kyakkyawar jarraba da ya yi min. Wallahi ban ƙara yin ƙarya da gangan ba tun lokacin da na faɗa wa Manzon Allah (ﷺ) wannan magana har zuwa yau. Ina kuma roƙon Allah ya ci gaba da tsare ni a cikin abin da ya yi saura na rayuwata.” [Dubi, Bukhari #4418, da Muslim #2769].
مَا كَانَ لِأَهۡلِ ٱلۡمَدِينَةِ وَمَنۡ حَوۡلَهُم مِّنَ ٱلۡأَعۡرَابِ أَن يَتَخَلَّفُواْ عَن رَّسُولِ ٱللَّهِ وَلَا يَرۡغَبُواْ بِأَنفُسِهِمۡ عَن نَّفۡسِهِۦۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ لَا يُصِيبُهُمۡ ظَمَأٞ وَلَا نَصَبٞ وَلَا مَخۡمَصَةٞ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَطَـُٔونَ مَوۡطِئٗا يَغِيظُ ٱلۡكُفَّارَ وَلَا يَنَالُونَ مِنۡ عَدُوّٖ نَّيۡلًا إِلَّا كُتِبَ لَهُم بِهِۦ عَمَلٞ صَٰلِحٌۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 9:120Bai kamata ba ga mutanen Madina da waɗanda suke kewaye da su daga mazauna ƙauye su noƙe su ƙi bin Manzon Allah, ko kuma su zaɓi kansu fiye da shi. Wannan kuwa saboda ba wata ƙishirwa ko wahala ko yunwa da za ta same su a kan hanyar Allah, kuma ba za su taka wani wuri ba da zai ɓata wa kafirai rai, kuma ba za su tafka wa abokan gaba wata hasara ba sai an rubuta musu lada saboda shi (wato kowane ɗaya daga abubuwan da aka zana). Lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa.
وَلَا يُنفِقُونَ نَفَقَةٗ صَغِيرَةٗ وَلَا كَبِيرَةٗ وَلَا يَقۡطَعُونَ وَادِيًا إِلَّا كُتِبَ لَهُمۡ لِيَجۡزِيَهُمُ ٱللَّهُ أَحۡسَنَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 9:121Ba kuma za su bayar da wata sadaka ba, ƙarama ko kuma babba, kuma ba wani kwazazzabo da za su keta sai an rubuta musu ladansu don Allah Ya saka musu da mafi kyawun abin da suka zamanto suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa bai dace ba ga mutanen Madina da mazaunan ƙauyukan da ke zagaye da su su noƙe su ƙi fita tare da Manzon Allah (ﷺ) zuwa yaƙin Tabuka ko kuma su fifita kansu a kansa, su zaɓi su huta shi kuma yana cikin wahala, wannan bai dace da su ba. Saboda ba wata ƙishirwa ko wahala ko yunwa mai tsanani da za su same su a kan hanyar Allah, kuma ƙafafunsu ba za su taka wata ƙasa ba da wannan zai zama musabbabin ɓata wa kafirai rai, kuma ba za su tafka wa maƙiyansu wata asara ba ta kisa ko cinye su da yaƙi ko makamancin haka, face sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rubuta musu kyakkyawan sakamako saboda wannan, lalle Allah ba ya tozarta ladan masu kyautatawa. Hakanan ba za su bayar da wata sadaka ba ƙarama ko babba, kuma ba wani kwari da za su haye yayin fitarsu yaƙi, face sai an rubuta musu ladansa, don Allah ya saka musu da mafi kyan ayyukan da suka zamanto suna aikatawa. An karɓo daga Abdurrahman ɗan Jabrin ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Dugadugan bawa ba za su yi ƙura a kan hanyar Allah ba sannan kuma wuta ta shafe shi.” [Bukhari #2811].
۞وَمَا كَانَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لِيَنفِرُواْ كَآفَّةٗۚ فَلَوۡلَا نَفَرَ مِن كُلِّ فِرۡقَةٖ مِّنۡهُمۡ طَآئِفَةٞ لِّيَتَفَقَّهُواْ فِي ٱلدِّينِ وَلِيُنذِرُواْ قَوۡمَهُمۡ إِذَا رَجَعُوٓاْ إِلَيۡهِمۡ لَعَلَّهُمۡ يَحۡذَرُونَ
Open ayah 9:122Bai kamata muminai su fita yaƙi gaba ɗaya ba. Me zai hana wasu jama’a daga kowace ƙabila (su zauna) don su koyi ilimin addini, su kuma yi wa mutanensu gargaɗi idan sun dawo musu don su kiyaye (dokokin Allah)?.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قَٰتِلُواْ ٱلَّذِينَ يَلُونَكُم مِّنَ ٱلۡكُفَّارِ وَلۡيَجِدُواْ فِيكُمۡ غِلۡظَةٗۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 9:123Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yaƙi kafirai waɗanda suke maƙota da ku, kuma su sami kausasawa daga wajenku. Ku kuma sani cewa Allah Yana tare da masu taƙawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, bai kamata ga muminai su fita wajen yaƙi gaba ɗayansu ba a lokaci guda. Me zai hana a cikin kowace ƙabila a sami wata jama’a da su ne za su fita yaƙi, wasu kuma su zauna don su karanci ilimi na addinin Allah don su yi karantarwa da gargaɗi ga waɗanda suka fita yaƙi idan sun dawo gare su, ko sa kiyaye abin da zai jawo musu fushin Allah da azabarsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su yaƙi kafiran da suke kusa da garuruwansu, kuma su tsananta musu wajen yaƙi, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa yana tare da masu taƙawa, wato masu kiyaye dokokin Allah a cikin komai har da sha’anin jihadi.
وَإِذَا مَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٞ فَمِنۡهُم مَّن يَقُولُ أَيُّكُمۡ زَادَتۡهُ هَٰذِهِۦٓ إِيمَٰنٗاۚ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فَزَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَهُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ
Open ayah 9:124Idan kuwa aka saukar da wata sura, daga cikinsu akwai waɗanda suke cewa: “Wane ne daga cikinku wannan ta ƙara masa imani?” To amma waɗanda suka yi imani su kam ta ƙara musu imani alhali suna cike da farin ciki.
وَأَمَّا ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ فَزَادَتۡهُمۡ رِجۡسًا إِلَىٰ رِجۡسِهِمۡ وَمَاتُواْ وَهُمۡ كَٰفِرُونَ
Open ayah 9:125Amma kuma waɗanda suke da munafunci a zukatansu sai (surar) ta ƙara musu wata dauɗa a kan dauɗarsu (ta munafunci) suka kuma mutu suna kafirai.
أَوَلَا يَرَوۡنَ أَنَّهُمۡ يُفۡتَنُونَ فِي كُلِّ عَامٖ مَّرَّةً أَوۡ مَرَّتَيۡنِ ثُمَّ لَا يَتُوبُونَ وَلَا هُمۡ يَذَّكَّرُونَ
Open ayah 9:126Shin yanzu ba sa ganin cewa ana jarrabar su a kowace shekara sau ɗaya ko sau biyu, sannan ba sa tuba kuma ba sa wa’azantuwa?
وَإِذَا مَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٞ نَّظَرَ بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٍ هَلۡ يَرَىٰكُم مِّنۡ أَحَدٖ ثُمَّ ٱنصَرَفُواْۚ صَرَفَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُم بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ
Open ayah 9:127Idan kuma an saukar da wata surar sai su kalli junansu (su ce): “Shin akwai wani mai ganin ku?” Sannan sai su juya. To Allah Ya juyar da zukatansu saboda su mutane ne da ba sa fahimta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, idan ya saukar wa Annabi (ﷺ) wata sura ta Alƙur’ani, sai wasu daga cikin munafukai su riƙa ce wa juna: “Wane ne daga cikinku wannan surar ta ƙara masa imani?” Suna kuma faɗar haka cikin izgili da gatse da reni ga Alƙur’ani. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan surar tana ƙara wa muminai imaninsu domin za su rungumi abin da ta zo da shi na umarni da hani kuma za su yi aiki da su kuma imaninsu zai ƙaru, suna kuma masu farin ciki da hakan. Amma waɗanda munafinci ya lulluɓe zukatansu, sai surar ta ƙara musu kafirci da shakka a kan kafircinsu da shakkarsu ta farko, su kuma mutu suna kafirai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shin yanzu su waɗannan munafukan ba sa ganin a duk shekara sai an jarrabe su sau ɗaya ko sau biyu, sannan ba sa tuba kuma ba sa wa’azantuwa? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa, idan ya saukar da wata sura wadda take fallasa asirin munafikai sai su kalli junansu su ce: “Shin ko akwai mai ganin ku wanda zai kai wa Muhammadu labarinku asirinmu ya tonu a wurinsa?” To daga nan sai su juya wa wannan surar baya, su ƙi ba da gaskiya da ita ko su yi aiki da ita, tare da cewa Alƙur’ani ya tona asiransu, amma wannan bai sa su sun shiryu ba, sai Allah ya juyar da zukatansu saboda sun zamanto mutane ne da ba sa fahimtar littafin Allah, suna nuna girman kai da bijire wa aiki da shi.
لَقَدۡ جَآءَكُمۡ رَسُولٞ مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ عَزِيزٌ عَلَيۡهِ مَا عَنِتُّمۡ حَرِيصٌ عَلَيۡكُم بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 9:128Haƙiƙa Manzo ya zo muku daga jinsinku; abin da zai wahalar da ku yana damun sa; mai kwaɗayin alheri ne gare ku, mai tausayawa kuma mai jin ƙai ga muminai.
فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَهُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 9:129To idan sun ba da baya sai ka ce: “Allah Ya ishe ni, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, a gare Shi kaɗai na dogara; kuma Shi ne Ubangijin Al’arshi mai girma.” </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da Larabawa cewa, wani Manzo daga cikinsu ya zo musu; shi ne Annabi Muhammadu (ﷺ). Daga siffofinsa ya kasance duk wani abu da zai wahalar da su yana yi masa girma, wato yana damun sa, sannan shi mai kwaɗayin shiriyarsu ne da isar musu da alheri, kuma shi mai tausayi ne da jin ƙai ga muminai. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya bar mu, babu wani tsuntsu da yake jujjuya fukafukansa a cikin iska, face sai da ya ba mu wani ilimi a kansa.” Ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani abu wanda zai kusantar da ku ga Aljanna ya kuma nisanta ku daga wuta, face an yi muku bayaninsa.” [Ɗabarani #1647]. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Misalin zamana da al’ummata shi ne kawai kamar wani mutum da ya hura wuta, sai ƙwarin nan faɗa-wuta suka riƙa faɗawa cikinta, to haka ni ma nake riƙe kwankwasonsu ina hana su amma suna kutsa kansu suna faɗawa cikin wutar.” [Bukhari #6483, da Muslim #2284]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fuskantar da bayaninsa ga Manzon Allah (ﷺ) cewa, idan sun bijire sun ƙi yin imani da shi sun ƙi yi masa ɗa’a, to ya ce musu Allah ya ishe shi komai, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi, gare shi shi kaɗai ya dogara ya miƙa al’amarinsa duka gare shi, shi ne Ubangijin Al’arshin nan mai girma. Waɗannan ayoyi biyu na ƙarshe, lokacin da Sayyidina Abubakar ya kafa kwamitin tattara Alƙur’ani wuri ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Zaidu ɗan Sabitu Al-Ansari (Allah ya kara masa yarda), da suka zo rubuta su sai aka rasa samun su a wurin kowa a rubuce sai a wurin Sahabin nan mai suna Abu Khuzaima Al-Ansari. [Dubi, Bukhari #4989].