يونس
Yunus
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡحَكِيمِ
Open ayah 10:1<ITALIC>ALIF LAM RA</ITALIC>. Waɗannan ayoyin littafi ne (wato Alƙur’ani) mai hikima.
أَكَانَ لِلنَّاسِ عَجَبًا أَنۡ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ رَجُلٖ مِّنۡهُمۡ أَنۡ أَنذِرِ ٱلنَّاسَ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنَّ لَهُمۡ قَدَمَ صِدۡقٍ عِندَ رَبِّهِمۡۗ قَالَ ٱلۡكَٰفِرُونَ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٞ مُّبِينٌ
Open ayah 10:2Shin ya zama abin mamaki ga mutane cewar Mun yi wahayi zuwa ga wani mutum daga cikinsu, cewa: “Ka gargaɗi mutane, kuma ka yi wa waɗanda suka yi imani albishir cewa suna da babban matsayi wurin Ubangijinsu? Sai kafirai suka ce: “Lalle wannan tabbas mai sihiri ne mai bayyana (sihirinsa).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa domin bayanin mu’ujizar Alƙur’ani. Da waɗannan haruffa ne Larabawa suke rubutu suna karatu, to amma sun kasa kawo kamarsa. Haka kuma waɗannan ayoyi masu girman daraja ayoyi ne na Alƙur’ani mai cike da hikima. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, shin yanzu wannan ya zama abin mamaki ga kafiran Ƙuraishawa da sauran Larabawa don Allah ya yi wahayi ga wani mutum daga cikinsu, don ya zama mai gargaɗi ga dukkan mutane game da uƙubar kafirci da saɓa wa Allah, kuma ya yi wa muminai albishiri da cewa suna da wani cikakken lada wanda shi ne Aljanna, saboda kyawawan ayyukan da suka aikata? To amma sai kafirai suka riƙa mamakin wannan Manzo, har suka ce lalle shi wani matsafi ne mabayyani.
إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۖ مَا مِن شَفِيعٍ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ إِذۡنِهِۦۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 10:3Lalle Ubangijinku Shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da ƙasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi; Yana tsara al’amari (yadda Ya ga dama). Babu wani mai ceto sai da izininsa. Wannan Shi ne Allah Ubangijinku. To sai ku bauta masa. Ashe ba za ku wa’azantu ba?
إِلَيۡهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقًّاۚ إِنَّهُۥ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ بِٱلۡقِسۡطِۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمۡ شَرَابٞ مِّنۡ حَمِيمٖ وَعَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ
Open ayah 10:4Zuwa gare Shi ne makomarku take gaba ɗaya; alƙawarin Allah ne da gaske. Lalle Shi ne Yake farar da halitta sannan Ya maido da ita (bayan mutuwa) don Ya saka wa waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari da adalci. Waɗanda suka kafirce kuwa suna da abin sha mai tsananin ƙuna da kuma azaba mai raɗaɗi saboda kafircewa da suke yi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, shi ne Ubangijin talikai duka shi ne kuma wanda ya halicci sammai da ƙasa cikin kwana shida, sannan ya ɗaukaka a kan Al’arshinsa, yana tsara al’amuran halittarsa gaba ɗaya, ba kuma wanda zai yi ceto a gabansa sai da izininsa. To wannan shi ne Allah Ubangijin mutane, don haka sai su bauta masa shi kaɗai, kuma me ya sa ba za su wa’azantu ba? Sai kuma ya bayyana cewa, makomar kowa da komai gare shi take shi kaɗai ranar da zai fitar da mutane daga ƙaburburansu rayayyu; kuma alƙawarin Allah gaskiya ne, ba ya saɓa shi, shi ne maƙagin halitta kuma ya sake mayar da ita bayan mutuwa a ranar lahira, don ya saka wa muminai da suka yi kyawawan ayyuka da adalci. Su kuwa waɗanda suka kafirta suna da sakamakon wani abin sha mai tsananin ƙuna, saboda kafircinsu a duniya.
هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ ٱلشَّمۡسَ ضِيَآءٗ وَٱلۡقَمَرَ نُورٗا وَقَدَّرَهُۥ مَنَازِلَ لِتَعۡلَمُواْ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلۡحِسَابَۚ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ يُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 10:5Shi ne Wanda Ya sanya muku rana ta zamo mai haske da kuma wata ya zamo mai haskakawa, Ya kuma sanya shi mai masaukai don ku san adadin shekaru da kuma (sanin) lissafi (na lokuta). Allah bai halicci wannan ba sai da gaskiya. Yana bayyana ayoyi ne ga mutanen da suke da sani.
إِنَّ فِي ٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَّقُونَ
Open ayah 10:6Lalle game da sassaɓawar dare da rana da kuma abubuwan da Allah Ya halitta cikin sammai da ƙasa akwai ayoyi ga mutanen da suke kiyaye dokokin Allah. </b>A waɗannan ayoyi bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da Rububiyyarsa da Uluhiyyarsa, sai kuma ya bayyana wasu dalilai da duk masu hankali suke gani kullum waɗanda kuma suke tabbatar da Rububiyyarsa da Uluhiyyarsa. Ya bayyana cewa, shi ne Allah wanda ya sanya rana mai haske da rana, ya kuma mayar da wata mai haskakawa da daddare, ya kuma ƙaddara tafiyar wannan watan a cikin manziloli (masaukai) don mutane su san adadin yawan shekaru, kuma su san lissafin yawan darare da watanni. Allah bai halicci wannan ba sai bisa gaskiya, yana kuma bayyana wa mutane masu ganewa hujjoji da dalilai. Allah kuma ya ci gaba da bayanin cewa, shi kuma sassaɓawar dare da yini, watau wannan ya zo wannan ya tafi wannan ya tafi wannan ya zo, hakanan da abin da ya halitta a cikin sammai da ƙasa, tabbas waɗannan duka dalilai ne ƙarara masu nuna samuwar Allah mahalicci wanda shi kaɗai ne ya cancanci a bauta masa, kuma zuwa gare shi makoma take a ranar gobe ƙiyama, amma ga mutane masu taƙawa suna kiyaye dokokin Allah Ta’ala.
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا وَرَضُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَٱطۡمَأَنُّواْ بِهَا وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِنَا غَٰفِلُونَ
Open ayah 10:7Lalle waɗanda ba sa tsammanin gamuwa da Mu, suka kuma yarda da rayuwar duniya, kuma suka nutsu da ita, da kuma waɗanda suke gafala daga ayoyinmu.
أُوْلَٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 10:8Waɗanan makomarsu wuta ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ يَهۡدِيهِمۡ رَبُّهُم بِإِيمَٰنِهِمۡۖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 10:9Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, Ubangijinsu zai shirye su saboda imaninsu: ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu cikin aljannatai na ni’ima.
دَعۡوَىٰهُمۡ فِيهَا سُبۡحَٰنَكَ ٱللَّهُمَّ وَتَحِيَّتُهُمۡ فِيهَا سَلَٰمٞۚ وَءَاخِرُ دَعۡوَىٰهُمۡ أَنِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 10:10Addu’arsu a cikinta: “Muna tsarkake Ka ya Allah”, gaisuwarsu kuma a cikinta “Salamun” (watau aminci). Ƙarshen addu’arsu kuma ita ce: “Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin waɗanda suka kafirce wa Allah Ta’ala duk kuwa da bayyanar dalilai ƙarara gare su. Ya bayyana cewa, waɗanda ba sa tsammanin gamuwa da Allah a ranar alƙiyama, suka kuma yarda da rayuwar duniya maimakon ta lahira, suka nutsu da ita da kuma waɗanda suka bijire wa ayoyin Allah, to waɗannan makomarsu da mazauninsu ita ce wutar Jahannama a ranar lahira, saboda abin da suka kasance suna aikatawa na kafirci da saɓon Allah. Sannan kuma ya bayyana cewa, tabbas waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, Ubangijinsu zai shiryar da su a lahira ga gidajen Aljanna saboda imaninsu; ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu cikin gidajen Aljanna na ni’ima. Addu’arsu a cikin Aljanna ita ce, za su riƙa cewa: “Tsarki ya tabbata gare ka ya Allah.” Gaisuwarsu ga junansu kuwa ita ce: “Salamun”, watau aminci ya tabbata a gare ku. Ƙarshen addu’arsu kuwa ita ce: “Godiya da yabo sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.” An karɓo daga Jabiru ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Lalle ‘yan Aljanna suna ci suna kuma sha a cikinta, amma ba sa tofar da yawu ba kuma sa yin fitsari, kuma ba sa bahaya, ba kuma sa yin kaki.” Sai sahabbai suka ce: “To ta ƙaƙa za su fitar da abinci?” Sai ya ce: “Ta hanyar gyatsa da gumi mai ƙanshin turaren almiski, za a kimsa musu yin tasbihi da godiya ga Allah kamar yadda suke yin numfashi.” [Muslim #2835].
۞وَلَوۡ يُعَجِّلُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ ٱلشَّرَّ ٱسۡتِعۡجَالَهُم بِٱلۡخَيۡرِ لَقُضِيَ إِلَيۡهِمۡ أَجَلُهُمۡۖ فَنَذَرُ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ
Open ayah 10:11Da dai Allah zai gaggauta (karɓar addu’ar) mutane ta sharri kamar yadda yake gaggauta ta alheri to da ƙarshen rayuwarsu ya zo. Sai dai Mukan bar waɗanda ba sa tsammanin haɗuwa da Mu cikin shisshiginsu su yi ta faganniya.
وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ٱلضُّرُّ دَعَانَا لِجَنۢبِهِۦٓ أَوۡ قَاعِدًا أَوۡ قَآئِمٗا فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُ ضُرَّهُۥ مَرَّ كَأَن لَّمۡ يَدۡعُنَآ إِلَىٰ ضُرّٖ مَّسَّهُۥۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلۡمُسۡرِفِينَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 10:12Idan kuma wata cuta ta sami mutum, sai ya roƙe Mu, a kishingiɗe ne ko a zaune ko kuwa a tsaye. To lokacin da Muka yaye masa cutarsa sai ya ci gaba (da halinsa) kamar bai taɓa roƙon Mu game da wata cuta da ta shafe shi ba. Kamar haka ne aka ƙawata wa maɓarnata abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, da zai gaggauta karɓar addu’ar mutane ta sharri kamar yadda yake gaggauta karɓar ta alhairi, to da sun halaka gaba ɗaya. Allah kuma zai bar waɗanda ba sa sa ran haɗuwarsu da shi a lahira cikin ɗimuwa da fagamniya cikin ɓatansu. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku yi wa kawunanku mummunar addu’a, kada kuma ku yi ga ‘ya’yanku ko dukiyoyinku, don kada ku dace da wani lokaci da ake roƙon Allah a cikinsa sai ya amsa muku addu’arku.” [Muslim #3009]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, idan wata cuta ta sami mutum sai ya roƙi Allah don ya yaye masa, a tsaye yake ko a zaune ko a kishingiɗe, watau a cikin kowane hali ya samu kansa yakan yi addu’a, to amma idan Allah ya yaye masa cutarsa sai ya ci gaba da kafircinsa da saɓon Allah, ya manta halin da ya shiga a baya na tsanani, ba kuma zai gode wa Allah da ya yaye masa cutarsa ba, ya nuna kamar ma bai taɓa roƙon Allah ba game da wata cuta da ta same shi. Allah ya bayyana cewa kamar haka ne aka ƙawata wa kafirai masu azarɓaɓi cikin kafircinsu da saɓon Allah abin da suka kasance suna aikatawa.
وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَا ٱلۡقُرُونَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَمَا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُواْۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 10:13Haƙiƙa kuma Mun hallaka al\'ummun da suka gabace ku, lokacin da suka yi zalunci, kuma manzanninsu suka zo musu da (hujjoji) mabayyana, sai ba su zamana sun yi imani ba. Kamar haka ne Muke saka wa mutane masu laifi.
ثُمَّ جَعَلۡنَٰكُمۡ خَلَٰٓئِفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ لِنَنظُرَ كَيۡفَ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 10:14Sannan bayansu Muka mayar da ku madadinsu a bayan ƙasa don Mu ga me za ku aikata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yi wa mushirikai kashedi da cewa, shi ne fa ya hallaka al\'ummun da suka gabace su lokacin da suka yi zalunci ta hanyar shirka da Allah da ƙaryata annabawa da zaluntar masu rauni. Manzannin Allah sun kawo wa waɗannan al\'ummu mu’ujizoji bayyanannu, to amma sai suka ƙi su yi imani domin Allah ya toshe musu zukatansu saboda kafircinsu da tsaurin kansu ga gaskiya, to kamar haka ne Allah yake saka wa mutane masu manyan laifuka. Sannan bayan hallakar da waɗancan, sai ya mayar da waɗannan suka maye gurbinsu don ya ga me su kuma za su aikata.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَاتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا ٱئۡتِ بِقُرۡءَانٍ غَيۡرِ هَٰذَآ أَوۡ بَدِّلۡهُۚ قُلۡ مَا يَكُونُ لِيٓ أَنۡ أُبَدِّلَهُۥ مِن تِلۡقَآيِٕ نَفۡسِيٓۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّۖ إِنِّيٓ أَخَافُ إِنۡ عَصَيۡتُ رَبِّي عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 10:15Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu bayyanannu sai waɗanda ba sa tsammanin haɗuwa da mu su ce: “Ka zo da wani alƙur’anin ba wannan ba, ko kuma ka canja shi.” Ka ce (da su): “Bai dace da ni ba in canja shi da raɗin kaina. Ni ba abin da nake bi sai abin da kawai aka yo mini wahayi. Lalle ni dai ina tsoron azabar rana mai girma idan na saɓa wa Ubangijina.”
قُل لَّوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا تَلَوۡتُهُۥ عَلَيۡكُمۡ وَلَآ أَدۡرَىٰكُم بِهِۦۖ فَقَدۡ لَبِثۡتُ فِيكُمۡ عُمُرٗا مِّن قَبۡلِهِۦٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 10:16Ka ce: “Da Allah Ya ga dama da ban karanta muku shi ba, kuma da (Allah) bai sanar da ku shi ba, domin haƙiƙa na zauna cikinku shekaru masu yawa tun gabaninsa. Me ya sa ba za ku hankalta ba?”
فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 10:17To ba wanda ya fi zalunci irin wanda ya ƙirƙira wa Allah ƙarya ko kuma ya ƙaryata ayoyinsa. Lalle masu babban laifi ba za su rabauta ba. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, idan ana karanta wa mushirikai ayoyin Alƙur’ani sai waɗanda ba sa tsammanin haɗuwa da Allah, masu ƙaryata ranar alƙiyama su ce wa Manzon Allah (ﷺ) ya zo da wani alƙur’anin wanda a cikinsa babu abin da ba sa so, ko kuma ya canja shi shi da kansa yadda yake so. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya ba su amsa da cewa, al’amarin canja Alƙur’ani da wani ko canja wasu ayoyinsa ba a hannunsa yake ba, shi ma ba abin da yake bi sai abin da kawai aka yi masa wahayinsa, kuma shi haƙiƙa yana jin tsoron azabar rana mai girma, watau alƙiyama, idan har ya saɓa wa Ubangijinsa. Allah kuma ya umarce shi, har ila yau, ya faɗa musu cewa, da Allah ya ga dama da Annabi bai karanta musu Alƙur’ani ba, kuma da Allah bai sanar da su shi ba. Haƙiƙa kuma ya zauna a cikinsu -su mutanen Makka- shekaru masu yawa, kimanin arba’in, tun kafin a yi masa wahayin Alƙur’ani, amma ba su taɓa kama shi da laifin ƙarya ba; sun san shi mai gaskiya ne mai amana; to me ya sa ba za su hankalta ba su fahimci cewa Alƙur’ani wahayi ne daga Allah? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu wanda ya fi zalunci irin wanda ya ƙirƙira wa Allah ƙarya, ko kuma ya ƙaryata ayoyinsa. Lalle kuwa masu manyan laifuka irin waɗannan ba sa rabauta.
وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡ وَيَقُولُونَ هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِۚ قُلۡ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 10:18Suna kuma bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai cutar da su ba ba kuma zai amfane su ba, suna kuma cewa: “Waɗannan su ne masu ceton mu a wurin Allah.” Ka ce: “Shin yanzu za ku ba Allah labarin abin da bai sani ba ne a cikin sammai ko kuma a bayan ƙasa? Tsarki ya tabbata a gare Shi Ya kuma ɗaukaka daga abin da suke shirka da Shi.”
وَمَا كَانَ ٱلنَّاسُ إِلَّآ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَٱخۡتَلَفُواْۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡ فِيمَا فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 10:19A da can mutane sun zamanto al’umma ɗaya ce, to sai suka sassaɓa. Da ba don wata kalma da ta gabata daga Ubangijinka ba, to da an yi hukunci a tsakaninsu game da abin da suke sassaɓawa a kai.
وَيَقُولُونَ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۖ فَقُلۡ إِنَّمَا ٱلۡغَيۡبُ لِلَّهِ فَٱنتَظِرُوٓاْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُنتَظِرِينَ
Open ayah 10:20Suna kuma cewa: “Don me ba a saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa ba?” To ka ce: “Sanin gaibu na Allah ne kawai, sai ku saurara, lalle ni ma ina tare da ku cikin masu sauraro.” </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin cewa, mushirikai suna bauta wa wanin Allah wanda ba zai iya cutar da su ba kuma ba zai amfane su da komai ba, suna cewa, wai suna bauta wa gumakan ne don za su cece su a wurin Allah, to amma Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Muhammadu (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, shin yanzu su za su ba wa Allah labarin abin da bai sani ba ne a cikin sammai ko a ƙasa? Allah ya tsarkaka daga duk wata shirka da suke yi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a da mutane gaba ɗaya suna bin addini ɗaya ne na kaɗaita Allah, sai suka sassaɓa a addininsu, suka fara haɗa Allah da wasu wajen bauta. Ba don Allah ya riga ya yanke hukuncin cewa zai saurara wa mushirikai da masu saɓon Allah ba, watau zai jinkirta yi musu sakamako zuwa ranar alƙiyama, to da tabbas ya yi hukunci a kan waɗanda suka sassaɓa tun a nan duniya, ya tserar da muminai ya kuma gaggauto azabarsa ga kafirai. Sannan Allah ya bayyana cewa, su waɗannan mushirikai suna cewa me ya hana a saukar wa da Annabi (ﷺ) irin mu’ujizojin da suke neman a saukar masa domin su tabbatar da cewa shi da gaske Manzo ne daga Allah? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, ai saukar da waɗannan mu’ujizoji yana daga cikin lamura na gaibu wanda babu wanda ya san shi sai Allah, kuma babu mai iya saukar da su sai shi idan ya ga dama, idan kuma ya ga dama ya ƙi saukarwa, don haka Allah ya umarce shi ya faɗa musu cewa, su saurara su ga irin uƙubar da Allah zai yi wa masu ƙarya daga cikinsu da kuma nasarar da zai ba masu gaskiya, Annabi da sahabbansa ma suna tare da su suna sauraro.
وَإِذَآ أَذَقۡنَا ٱلنَّاسَ رَحۡمَةٗ مِّنۢ بَعۡدِ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُمۡ إِذَا لَهُم مَّكۡرٞ فِيٓ ءَايَاتِنَاۚ قُلِ ٱللَّهُ أَسۡرَعُ مَكۡرًاۚ إِنَّ رُسُلَنَا يَكۡتُبُونَ مَا تَمۡكُرُونَ
Open ayah 10:21Idan kuma Muka ɗanɗana wa mutane daɗi bayan wahala ta same su, sai ga su suna ƙulla makirci ga ayoyinmu. Ka ce: “Allah Ya fi gaggawar (sakayya a kan) makirci.” Lalle manzanninmu suna rubuta abin da kuke ƙullawa na makirci.
هُوَ ٱلَّذِي يُسَيِّرُكُمۡ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا كُنتُمۡ فِي ٱلۡفُلۡكِ وَجَرَيۡنَ بِهِم بِرِيحٖ طَيِّبَةٖ وَفَرِحُواْ بِهَا جَآءَتۡهَا رِيحٌ عَاصِفٞ وَجَآءَهُمُ ٱلۡمَوۡجُ مِن كُلِّ مَكَانٖ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ أُحِيطَ بِهِمۡ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ لَئِنۡ أَنجَيۡتَنَا مِنۡ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّٰكِرِينَ
Open ayah 10:22Shi ne Wanda Yake tafiyar da ku a tudu da cikin ruwa, har lokacin da kuka shiga cikin jiragen ruwa, (jiragen) kuwa suka yi gudu da su tare da iska mai daɗi, suka kuma yi farin ciki da su (jiragen) sai kuma wata iska mai ƙarfi ta zo musu; raƙumin ruwa kuma ya zo musu ta kowane wuri, suka kuma tabbatar cewa dai su kam an rutsa da su, sai kuma suka roƙi Allah suna masu tsarkake addini gare Shi (suna cewa): “Tabbas idan Ka tserar da mu daga wannan, lalle haƙiƙa za mu zamo cikin masu godiya.”
فَلَمَّآ أَنجَىٰهُمۡ إِذَا هُمۡ يَبۡغُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۗ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَا بَغۡيُكُمۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۖ مَّتَٰعَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ ثُمَّ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُكُمۡ فَنُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 10:23To lokacin da Ya tserar da su sai ga su suna ɓarna a bayan ƙasa ba da gaskiya ba. Ya ku mutane, haƙiƙa (sakamakon) ɓarnarku a kanku kawai yake; ku ɗan ji daɗin rayuwar duniya; sannan (daga ƙarshe) zuwa gare Mu ne makomarku take, sannan mu ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin halin mushirikai ne cewa, idan ya ɗanɗana musu wani daɗi bayan wahala da musiba da ta same su, sai ka gan su suna ta ƙoƙarin ƙulle-ƙullen makircin yadda za su rusa gaskiya su kafa ƙarya; to Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabinsa (ﷺ) ya faɗa musu cewa, Allah ya fi su gaggawar zartar da kowane irin makirci, manzanninsa kuma daga cikin mala’iku suna nan suna rubuta duk wani makirci da kafirai suke ƙullawa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi ne wanda yake tafiya da su a kan tudu da kuma cikin ruwa, har lokacin da suka kasance cikin jiragen ruwa, waɗanda suke yin gudu da su tare da iska mai daɗi, mahaya jiragen kuma suka yi murna da su, sai kuma ga wata iska mai ƙarfi ta taso musu, raƙumin ruwa ya zo musu ta kowane ɓangare, a nan suka tabbatar halaka ta kewaye su ta ko’ina, sai suka shiga roƙon Allah suna masu tsantsanta addini gare shi cewa, lalle idan har ya tserar da su daga wannan halakar, to tabbas suna rantsuwa za su zama cikin masu godiya. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A ranar da aka buɗe garin Makka sai Annabi (ﷺ) ya amintar da kowa in ban da maza huɗu da mata biyu, ya ce: “Ku kashe su ko da kuwa kun same su ne maƙale a jikin rigar ɗakin Allah (Ka’aba).” Waɗannan mutane kuwa su ne Ikrima ɗan Abu Jahlin da Abdullahi ɗan Khaɗal da Abdullahi ɗan Sahal ɗan Abus-Sarh. To amma shi Ikrima sai ya gudu ya hau jirgin ruwa sai guguwa mai tsanani ta taso musu, sai mutanen cikin jirgin suka ce wa junansu: “Ku tsantsanta addu’a ga Allah shi kaɗai domin kuwa a yau dai gumakanku ba za su tsinana muku komai ba.” Sai Ikrima ya ce a ransa: “Idan dai har a yau cikin wannan teku babu abin da zai kuɓutar da ni sai tsantsanta addu’a ga Allah shi kaɗai, watau ikhlasi, to har a waje ma babu abin da zai kuɓutar da ni sai ikhlasi kaɗai. Ya Allah, na yi maka alƙawari idan har ka tserar da ni daga wannan musiba da nake ciki a yanzu, to zan je wurin Muhammadu (ﷺ) in saka hannuna a cikin hannunsa, na tabbata lalle zan same shi mai yafiya ne mai karamci.” Sai ya zo wurinsa ya musulunta.” [Nasa’i #4067 da Al-Bazzar #1151]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su waɗannan kafirai idan Allah ya tserar da su sai su saɓa masa alƙawarin da suka yi masa, kuma su yi ta ɓarna a bayan ƙasa suna haɗa Allah da wasu wajen bauta, suna saɓon Allah da zalunci ba tare da wani haƙƙi ba. Allah ya sanar da su cewa waɗannan abubuwa duk da suke yi na zalunci da shirka da saɓon Allah ana ƙyale su, musibar daga ƙarshe kansu za ta dawo, kuma duk wannan abu na cuta da suke yi za su ji ɗan daɗinsa ne kaɗan na duniya ba mai ɗorewa ba, sannan makomarsa gaba ɗaya zuwa ga Allah ne ranar alƙiyama, ya ba su labarin abin da suka aikata a duniya mai kyau da marar kyau, sannan ya yi musu sakayya a kansa.
إِنَّمَا مَثَلُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ مِمَّا يَأۡكُلُ ٱلنَّاسُ وَٱلۡأَنۡعَٰمُ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذَتِ ٱلۡأَرۡضُ زُخۡرُفَهَا وَٱزَّيَّنَتۡ وَظَنَّ أَهۡلُهَآ أَنَّهُمۡ قَٰدِرُونَ عَلَيۡهَآ أَتَىٰهَآ أَمۡرُنَا لَيۡلًا أَوۡ نَهَارٗا فَجَعَلۡنَٰهَا حَصِيدٗا كَأَن لَّمۡ تَغۡنَ بِٱلۡأَمۡسِۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 10:24Misalin rayuwar duniya kawai kamar ruwa ne da Muka saukar da shi daga sama, to sai shukokin da suke kan ƙasa suka cuɗanya da shi daga abin da mutane da dabbobi suke ci; har lokacin da ƙasa ta ƙawata (da shi) ta kuma yi ado; masu ita kuma suka sakankance cewa su masu ikon cin amfaninta ne, sai ƙaddararmu ta zo mata cikin dare ko rana, sai Muka mayar da ita girbabbiya kamar daɗai ba ta rayu ba a jiya. Kamar haka Muke bayyana ayoyi ga mutanen da suke tunani.
وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَىٰ دَارِ ٱلسَّلَٰمِ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 10:25Allah kuwa Yana kira ne zuwa gidan aminci (wato Aljanna), Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama zuwa tafarki madaidaici. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, misalin ƙyale-ƙyalen duniya da saurin gushewarsa kamar ruwan sama ne da Allah ya saukar da shi a ƙasa; to sai shukoki iri-iri suka fito a sanadiyyarsa, sashinsu ya cuɗanya da sashi daga abin da mutane da dabbobi suke ci, har lokacin da ƙasa ta yi kyau ta kuma yi ado da nau’ukan tsirrai daban-daban da furanni masu mabambantan launi, masu ita kuma suka sakankance cewa su masu ikon girbe ta ne su ci amfaninta, sai kwatsam ƙaddarar Allah ta afkar mata, Allah ya mayar da amfaninta girbabbe kuma lalatacce kamar daɗai ba a taɓa yin wata gona a wurin ba. To kamar haka ne Allah yake bayyana ayoyinsa daki-daki ga mutanen da suke tunani. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi yana kiran bayinsa su zo su shiga gidan Aljanna wanda babu wata cutarwa a cikinsa, yana kuma datar da wanda ya ga dama daga cikin bayinsa a kan bin wannan hanyar miƙaƙƙiya har zuwa ga gidan Aljanna, watau addinin Musulmi. An karɓo daga Jabiru ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mala’iku sun zo wa Annabi (ﷺ) yana barci, sai wasu daga cikinsu suka ce: “Lalle yana barci ne.” Sai wasu suka ce: “Lalle idon ne yake barci amma zuciyar a farke take.” Sai wasu suka ce: “Mutumin nan naku yana da wani misali, ku faɗi misalinsa.” Sai wasu suka ce: “Ai barci yake.” Sai wasu suka ce: “Lalle idon ne yake barci amma zuciyar a farke take.” Sai suka ce: “Misalinsa kamar wani mutum ne da ya gina gida, ya shirya kaɓakin abinci a cikinsa, ya kuma aika mai gayyata, to duk wanda ya amsa kiran mai gayyatar, zai shiga wannan gida ya ci abincin wannan kaɓakin, wanda kuwa bai amsa kiran mai gayyata ba, to ba zai sami shiga wannan gida ba har ya ci abincin wannan kaɓaki.” Sai suka ce wa juna: “Ku fassara wannan maganar don ya fahimce ta.” Sai wasu suka ce: “Barci yake yi.” Sai wasu suka ce: “Idon ne mai barci amma zuciyar a farke take.” Sai suka ce: “Wannan gidan shi ne Aljanna, wannan mai gayyata kuma shi ne Muhammadu (ﷺ), to duk wanda ya bi Muhammadu (ﷺ) to lalle ya bi Allah, wanda kuwa ya saɓa wa Muhammadu (ﷺ) to haƙiƙa ya saɓa wa Allah; Muhammadu kuma mai rarrabewa ne tsakanin mutane (watau tsakanin ‘yan wuta da ‘yan Aljanna.” [Bukhari #7281].
۞لِّلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ ٱلۡحُسۡنَىٰ وَزِيَادَةٞۖ وَلَا يَرۡهَقُ وُجُوهَهُمۡ قَتَرٞ وَلَا ذِلَّةٌۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 10:26Waɗanda suka kyautata aiki suna da sakamako mafi kyau (watau Aljanna) da kuma ƙari. Wani ƙunci da ƙasƙanci kuma ba za su same su ba. Waɗannan su ne ‘yan Aljanna; su masu dawwama ne a cikinta.
وَٱلَّذِينَ كَسَبُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ جَزَآءُ سَيِّئَةِۭ بِمِثۡلِهَا وَتَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۖ مَّا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنۡ عَاصِمٖۖ كَأَنَّمَآ أُغۡشِيَتۡ وُجُوهُهُمۡ قِطَعٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مُظۡلِمًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 10:27Waɗanda kuma suka yi mummunan aiki, to sakamakon mummunan aiki irinsa ne, kuma ƙasƙanci zai lulluɓe su; ba su da wani mai kare su daga (azabar) Allah; kamar dai an lulluɓe fuskokinsu ne da wani yanki na dare mai duhu ƙirin. Waɗannan su ne ‘yan wuta; su kuma masu dawwama ne a cikinta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, lalle waɗanda suka kyautata ayyukansu a duniya suna da sakamakon gidan Aljanna a lahira da ma ƙari a kan hakan. Mafi girman ƙarin sakamako da Allah zai yi wa ‘yan Aljanna shi ne ya ba su damar ganin fuskarsa mai daraja kamar yadda ayoyi na 22 da 23 na cikin Suratul Ƙiyama suka nuna. An karɓo daga Suhaibu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Idan ‘yan Aljanna suka shiga gidan Aljanna sai Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ce: “Kuna son ƙarin wani abu in ƙara muku?” Sai su ce: “Ashe ba ka haskaka mana fuskokinmu ba? Ashe ba ka shigar da mu gidan Aljanna ba, ka kuma tserar da mu daga wuta?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Sai Allah ya yaye shamaki; to babu wani abu da aka ba su da ya fi soyuwa a wurinsu kamar ganin Ubangijinsu mai girma da buwaya.” Sannan ya karanta wannan ayar.” [Muslim #181]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗin sakamakon ‘yan Aljanna bayan sun shige ta, yana cewa wani ƙunci ko wulaƙanci da ƙasƙanci ba zai rufe musu fuskokinsu ba. Waɗannan su ne ‘yan Aljanna masu zama a cikinta har abada. Sannan kuma Allah ya bayyana sakamakon waɗanda suka yi mummunan aiki a duniya suka kafirce wa Allah da Manzonsa, to su kam suna da wani mummunan sakamako, kowa gwargwadon munin aikinsa na duniya, wulaƙanci da ƙasƙanci da taɓewa za su lulluɓe su a wannan ranar, ba za su samu wanda zai kare su daga fushin Allah da azabarsa ba, za su zamanto tamkar an lulluɓe fuskokinsu ne da wani yanki na dare mai tsananin duhu, saboda duhun fuskokinsu. Waɗannan su ne ‘yan wuta masu zama a cikinta har abada.
وَيَوۡمَ نَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ مَكَانَكُمۡ أَنتُمۡ وَشُرَكَآؤُكُمۡۚ فَزَيَّلۡنَا بَيۡنَهُمۡۖ وَقَالَ شُرَكَآؤُهُم مَّا كُنتُمۡ إِيَّانَا تَعۡبُدُونَ
Open ayah 10:28(Ka tuna) ranar da za mu tara su ga baki ɗaya, sannan mu ce da waɗanda suka yi shirka: “Ku tsaya cak a wurarenku ku da abokan tarayyarku”. Sai kuma mu raba tsakaninsu; sai abokan tarayyarsu kuma su ce: “Ba mu ne kuka kasance kuna bauta wa ba.
فَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ إِن كُنَّا عَنۡ عِبَادَتِكُمۡ لَغَٰفِلِينَ
Open ayah 10:29“To kuma Allah Ya isa shaida tsakaninmu da ku: mu kam lalle mun kasance ba mu ma san kuna bautar mu ba.”
هُنَالِكَ تَبۡلُواْ كُلُّ نَفۡسٖ مَّآ أَسۡلَفَتۡۚ وَرُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۖ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 10:30A can ne kowane rai zai samu sakamakon abin da ya gabatar (a duniya). An kuma mayar da su zuwa ga Allah Majiɓincinsu na gaskiya; abin da kuma suka kansance suna ƙirƙira ya ɓace musu. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabi (ﷺ) ranar ƙiyama ne lokacin da Allah zai tattara halittunsa wuri ɗaya don yi musu hisabi, sannan ya kira waɗanda suka yi shirka ya umarce su da cewa, su tsaya cak a wurarensu su da abokan tarayyarsu, sai kuma ya raba tsakaninsu da abokan tarayyarsu, sai su abokan tarayyar su faɗa wa masu bauta musu cewa, su fa a gaskiya ba su suke bauta wa ba; suna bauta wa soye-soyen zukatansu ne kawai tare da shaiɗanunsu waɗanda suka umarce su da su bauta musu. Suka ce Allah ne shaida a tsakaninsu, kuma su ba su ma san da bautar da suka kasance suna yi musu ba. Allah ya bayyana cewa, a wannan wuri ne a ranar alƙiyama kowane rai zai san abin da ya aikata na alheri ko na sharri, domin zai gan shi rubuce a gabansa kuma a yi masa hisabi a kansa. Kuma an mayar da mushirikai zuwa ga Ubangijinsu na gaskiya don ya yi musu sakayya da adalci, duk kuma abin da suka ƙirƙira na ƙarya ga Allah ya ɓace musu.
قُلۡ مَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أَمَّن يَمۡلِكُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَمَن يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَمَن يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۚ فَسَيَقُولُونَ ٱللَّهُۚ فَقُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 10:31Ka ce: “Wane ne yake arzuta ku ta sama da ƙasa? Ko kuma wane ne mamallakin ji da gani? Kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wane ne kuma yake tsara al’amura?” To ai za su ce: “Allah ne.” To ka ce: “Yanzu ba za ku kiyaye dokokinsa ba?”
فَذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَاذَا بَعۡدَ ٱلۡحَقِّ إِلَّا ٱلضَّلَٰلُۖ فَأَنَّىٰ تُصۡرَفُونَ
Open ayah 10:32To wannan Shi ne Allah Ubangijinku na gaskiya. Bayan gaskiya kuwa babu wani abu sai ɓata. To yaya ake karkatar da ku?
كَذَٰلِكَ حَقَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى ٱلَّذِينَ فَسَقُوٓاْ أَنَّهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 10:33Kamar haka ne kalmar Ubangijinka ta tabbata a kan waɗanda suka yi fasiƙanci cewa su ba za su yi imani ba. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya tambayi mushirikai cewa, wane ne yake arzuta su ta sama da ta ƙasa? Ko kuma wane ne ya mallaki ji da gani? Wane ne kuma da girman ikonsa yake fitar da abu mai rai daga matacce, yake kuma fitar da matacce daga mai rai? Wane ne yake gudanar da al’amuran dukkan halittu, yake sarrafa komai a sama da ƙasa yadda ya ga dama? To duka dai mushirikai za su ce: Ai Allah ne shi kaɗai yake yin duk waɗannan abubuwa. To sai Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, idan haka ne me ya hana su kiyaye dokokinsa su kuma ji tsoron azabarsa? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, to mai yin waɗannan ayyuka shi ne kaɗai wanda ya cancanci a bauta masa, shi ne kuma Ubangijinsu na gaskiya wanda babu shakka dangane da shi. To mene ne kuma bayan gaskiya ta bayyana in ba ɓata ba? Don haka ta ƙaƙa ake juyar da su ba sa fahimtar gaskiya? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda aka karkatar da mushirikai daga kan gaskiya suka ci gaba da aikata shirka, to haka kalmar Allah ta azaba ta tabbata a kan waɗanda suka yi fasiƙanci cewa ba za su yi imani ba.
قُلۡ هَلۡ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥۚ قُلِ ٱللَّهُ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ
Open ayah 10:34Ka ce: “Shin daga cikin abokan tarayyarku ko akwai wanda yake ƙaga halitta, sannan ya maimaita ta?” Ka ce: “Allah Shi ne Wanda Yake ƙaga halitta sannan Ya maimaita ta. To ta yaya ake kautar da ku?”
قُلۡ هَلۡ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّۚ قُلِ ٱللَّهُ يَهۡدِي لِلۡحَقِّۗ أَفَمَن يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لَّا يَهِدِّيٓ إِلَّآ أَن يُهۡدَىٰۖ فَمَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ
Open ayah 10:35Ka ce: “Shin daga abokan tarayyarku ko akwai wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya?” Ka ce: “Allah Shi ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. To yanzu wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya shi ya fi cancanta a bi, ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai dai a shiryar da shi? To me ya same ku ne? Yaya kuke wannan hukuncin?
وَمَا يَتَّبِعُ أَكۡثَرُهُمۡ إِلَّا ظَنًّاۚ إِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا يَفۡعَلُونَ
Open ayah 10:36Yawancinsu kuma ba abin da suke bi sai zato. Lalle zato ba ya wadatar da komai game da gaskiya. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya tambayi mushirikai masu bautar wasu ba Allah ba cewa, a cikin abubuwan da suke bauta wa ko akwai wanda zai iya ƙagar halittar wani abu, sannan idan wannan abin ya mutu ya sake dawo masa da ransa? To idan ba su da wata amsar da za su iya bayarwa, to shi Annabi (ﷺ) ya amsa musu da cewa, Allah ne kaɗai yake iya ƙagar halitta sannan ya sake dawo mata da rai bayan mutuwa, to amma duk da sun san Allah ne kaɗai zai iya yin hakan gumakansu kuma ba za su iya yi ba, me ya same su ne ba za su bi gaskiya ba? Ta yaya ne kuma ake kawar da su daga gaskiya suka kama ɓata? Allah kuma ya sake umartar Annabi (ﷺ) da ya tambaye su cewa, shin cikin allolin da suke bauta wa ko akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya? Idan ba su da amsa, to shi ya amsa musu da cewa, Allah ne kaɗai mai shiryarwa zuwa ga gaskiya. To yanzu ashe wanda yake mai shiryarwa zuwa ga gaskiya, watau Allah, shi ne ya fi cancantar a bauta masa ko kuma allolinsu waɗanda ba sa iya shiryar da kowa zuwa ga gaskiya sai dai su a shiryar da su, su ne suka kamata a bauta musu ba Allah ba? Me ya samu mushirikai ne, yaya suke irin wannan ɗanyen hukunci? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su dai waɗannan mushirikai ba komai suke bi ba wajen shirkarsu da Allah sai zunzurutun zato marar tushe kuma marar tabbas; shi kuwa zato ba ya wadatar da komai game da tabbatar da gaskiya. Lalle Allah masanin duk abin da suke aikatawa ne, kuma zai yi musu sakayya a kai.
وَمَا كَانَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ أَن يُفۡتَرَىٰ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 10:37Wannan Alƙur’ani bai yiwuwa a ƙage shi daga (tunanin) wani wanda ba Allah ba, sai dai (shi) gaskatawa ne ga abin da ya gabace shi (na littattafan da aka saukar), kuma bayani ne dalla-dalla na hukunce-hukuncen (da Allah ya saukar); babu kokwanto a cikinsa cewa daga Ubangijin talikai yake.
أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ فَأۡتُواْ بِسُورَةٖ مِّثۡلِهِۦ وَٱدۡعُواْ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 10:38Ko kuma cewa suke yi: “Ƙagar sa ya yi ne?” Ka ce: “To ku kawo sura (ɗaya tal) irinsa, kuma ku kirawo wanda duk za ku iya (ya taimaka muku) wanda ba Allah ba idan kun kasance masu gaskiya!”
بَلۡ كَذَّبُواْ بِمَا لَمۡ يُحِيطُواْ بِعِلۡمِهِۦ وَلَمَّا يَأۡتِهِمۡ تَأۡوِيلُهُۥۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 10:39A’a, ba haka ba ne, sun dai ƙaryata abin da ba su da iliminsa ne, kuma har yanzu haƙiƙanin fassararsa ba ta zo musu ba. Kamar haka ne waɗanda suka gabace su suka ƙaryata. To duba ka ga yadda ƙarshen azzalumai ya zama.
وَمِنۡهُم مَّن يُؤۡمِنُ بِهِۦ وَمِنۡهُم مَّن لَّا يُؤۡمِنُ بِهِۦۚ وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 10:40Daga cikinsu kuma akwai wanda yake yin imani da shi (Alƙur’ani), akwai kuma wanda ba ya yin imani da shi. Ubangijinka kuma Shi ne Mafi sanin maɓarnata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ba zai yiwu a ce wannan Alƙur’anin ƙarya ne, wani ne ya ƙago shi ba Allah ba. A’a, Alƙur’ani littafi ne da Allah ya saukar, wanda kuma yake gaskata duk littattafan da suka gabace shi waɗanda Allah ya saukar ga annabawansa, sannan yana bayanin abin da Allah ya wajabta wa wannan al’umma na aƙida da hukunce-hukunce da bayanin labarai daban-daban, wanda babu shakka a cikinsa, saukakke ne daga Ubangijin talikai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da cewa; su mushirikai cewa suke yi wai Annabi Muhammadu (ﷺ) shi ne ya ƙagi Alƙur’ani, to idan haka ne, shi Annabi (ﷺ) ya neme su, su ma su ƙago ko da sura ɗaya ce tal kamar ta Alƙur’ani, domin ai su ma Larabawa ne ƙwararru masu magana da harshen Larabci kamarsa, su yi hakan idan har suna da gaskiya a kan cewa shi ne ya ƙago Alƙur’ani. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce, abin ba kamar yadda suke riyawa ba ne, kawai dai sun ƙaryata Alƙur’ani ne don ba su laƙanci abin da ya ƙunsa na ilimi ba, kuma suna ganin har yanzu kashedin da Allah (Mai tsarki da daukaka) yake yi musu na saukar azaba saboda ƙaryata Alƙur’ani da suka yi, bai same su ba. To kamar haka ne waɗanda suka gabace su cikin kafirai suka ƙaryata annabawansu. Allah kuma ya umarci Annabi (ﷺ) ya duba ya ga yadda ƙarshen azzalumai masu ƙaryata ayoyin Allah cikin al\'ummun da suka gabata ya zama. Sai kuma ya bayyana cewa, daga cikin su waɗannan mushirikan akwai wanda zai yi imani nan gaba ya tuba ya bar shirka, akwai kuma wanda ba zai yi imani ya tuba ba, zai yi ta zama a kan kafircinsa har mutuwa. Allah ya tabbatar da cewa, shi ya fi kowa sanin maɓarnata kuma zai yi maganin su duniya da lahira.
وَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل لِّي عَمَلِي وَلَكُمۡ عَمَلُكُمۡۖ أَنتُم بَرِيٓـُٔونَ مِمَّآ أَعۡمَلُ وَأَنَا۠ بَرِيٓءٞ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 10:41Idan kuwa suka ƙaryata ka, to ka ce: “Aikina nawa ne ku ma aikinku naku ne. Ku babu ruwanku da abin da nake aikatawa, ni ma kuma babu ruwana da abin da kuke aikatawa.”
وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُونَ إِلَيۡكَۚ أَفَأَنتَ تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ وَلَوۡ كَانُواْ لَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 10:42Daga cikinsu akwai waɗanda suke sauraron ka. Yanzu kai za ka iya jiyar da kurame ko da ba su da hankali?
وَمِنۡهُم مَّن يَنظُرُ إِلَيۡكَۚ أَفَأَنتَ تَهۡدِي ٱلۡعُمۡيَ وَلَوۡ كَانُواْ لَا يُبۡصِرُونَ
Open ayah 10:43Daga cikinsu kuma akwai wanda yake ƙura maka ido. Yanzu kai za ka iya shiryar da makafi ko da ba sa gani?
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظۡلِمُ ٱلنَّاسَ شَيۡـٔٗا وَلَٰكِنَّ ٱلنَّاسَ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 10:44Lalle Allah ba Ya zaluntar mutane da komai, sai dai mutane kawunansu kawai suke zalunta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, idan mushirikai suka ƙaryata shi, suka kuma ƙi yin imani da abin da ya zo musu da shi na gaskiya, to ya faɗa musu cewa, aikinsa nasa ne ba za a kama su da laifinsa ba; su ma kuma ayyukansu nasu ne, ba za a kama shi da laifukansu ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, daga cikin kafirai akwai masu sauraron sa yayin da yake karanta Alƙur’ani ko yake magana da su, to amma zukatansu a rufe suke, a lokacin ba sa amfana da komai cikin abin da suke sauraro, su da kurame a lokacin ɗaya suke babu bambanci, to shin Annabi (ﷺ) zai iya jiyar da wanda yake kurma wani abu, musamman idan kurumcin ya haɗu da rashin hankali? Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya ƙara da cewa, cikinsu har ila yau akwai waɗanda suke ƙura masa idanu idan yana bayani kamar suna ganin hasken gaskiya da ke tare da shi, to amma fa da su da makafi a lokacin ɗaya suke babu bambanci. To shin Annabi (ﷺ) zai iya shiryar da makafi ya nuna musu hanya ko da kuwa ba sa ganin komai kuma babu wata basira tare da su? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lalle shi ba ya zaluntar bayinsa da komai, sai dai su mutane su ne suke zaluntar kawunansu da kafirci da saɓon Allah da suke tafkawa, don haka suka cancanci azabar Allah.
وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ كَأَن لَّمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا سَاعَةٗ مِّنَ ٱلنَّهَارِ يَتَعَارَفُونَ بَيۡنَهُمۡۚ قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱللَّهِ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ
Open ayah 10:45Ranar da zai tattara su kuwa (za su ga) kamar ba su zauna ba sai wani ɗan lokaci na rana da suke gane junansu (a cikinsa). Haƙiƙa waɗanda suka ƙaryata gamuwa da Allah sun taɓe, ba su kuma zamanto shiryayyu ba.
وَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ ثُمَّ ٱللَّهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ
Open ayah 10:46Ko dai Mu nuna maka sashin abin da Muke musu alkawarinsa ko kuma Mu karɓi ranka, to makomarsu dai gare Mu take, sannan Allah Yana sane da abin da suke aikatawa.
وَلِكُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولٞۖ فَإِذَا جَآءَ رَسُولُهُمۡ قُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 10:47Kowacce al’umma kuma tana da manzo. To idan manzonsu ya zo (suka ƙaryata shi) to sai a yi hukunci a tsakaninsu da adalci, su kuma ba za a zalunce su ba. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, a ranar da zai tattara kafirai gaba ɗaya a wuri guda domin yi musu hisabi, za su ga kamar ba su taɓa zama a duniya ba sai ɗan lokaci na yini. A ranar za su riƙa gane junansu kamar yadda suke yi a duniya. Don haka waɗanda suka ƙaryata haɗuwa da Allah sun yi hasarar ladansu da gidan Aljanna, kuma ba su zamanto shiryayyu ba. Sannan Allah ya bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, ko dai ya gaggauto wa da kafirai uƙubarsu tun a duniya domin ya nuna masa wani ɓangare na alƙawarinsa da yake musu na azaba, ko kuma ya karɓi ransa kafin ya nuna masa hakan, to dai ko ma mene ne, makomarsu gaba ɗaya zuwa ga Allah ne, kuma Allah yana ganin abin da suke aikatawa a nan duniya, don haka zai yi musu sakayya a kansa gobe ƙiyama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kowace al’umma tana da manzon da ya zo mata daga Allah yana kiran ta zuwa ga yin imani da bautar Allah shi kaɗai. To idan wannan manzon ya zo wa wannan al’umma a ranar alƙiyama domin ya ba da shaida a kansu, a lokacin Ubangiji zai yi musu hukunci na adalci ba tare da ya zalunce su ba.
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 10:48Suna kuma cewa: “To yaushe ne wannan alƙawari (zai zo) idan kun kasance masu gaskiya?”
قُل لَّآ أَمۡلِكُ لِنَفۡسِي ضَرّٗا وَلَا نَفۡعًا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۗ لِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌۚ إِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ فَلَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ
Open ayah 10:49Ka ce: “Ba na mallakar wata cuta, ko wani amfani ga kaina sai dai abin da Allah Ya ga dama. Kowacce al’umma tana da lokacin (da aka iyakance mata). Idan lokacin nasu ya yi, to ba za su yi jinkiri na sa’a guda ba, kuma ba za su gaggauto ba.”
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَتَىٰكُمۡ عَذَابُهُۥ بَيَٰتًا أَوۡ نَهَارٗا مَّاذَا يَسۡتَعۡجِلُ مِنۡهُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 10:50Ka ce: “Yanzu ku ba ni labari (yadda za ku yi) idan azabar Allah ta zo muku da daddare ko da rana; mene ne masu laifi suke yi wa gaggawar zuwansa?
أَثُمَّ إِذَا مَا وَقَعَ ءَامَنتُم بِهِۦٓۚ ءَآلۡـَٰٔنَ وَقَدۡ كُنتُم بِهِۦ تَسۡتَعۡجِلُونَ
Open ayah 10:51“Shin sai idan (azabar) ta afka (muku) ne za ku yi imani da Shi (Allah)? Sai yanzu ne, alhali kuwa da can kun kasance kuna neman gaggautowarta?”
ثُمَّ قِيلَ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡخُلۡدِ هَلۡ تُجۡزَوۡنَ إِلَّا بِمَا كُنتُمۡ تَكۡسِبُونَ
Open ayah 10:52Sannan aka ce da waɗanda suka yi zalunci: “Ku ɗanɗani azaba mai dawwama; shin za a saka muku (da wani abu ne) in ban da abin da kuka kasance kuna aikatawa?.”
۞وَيَسۡتَنۢبِـُٔونَكَ أَحَقٌّ هُوَۖ قُلۡ إِي وَرَبِّيٓ إِنَّهُۥ لَحَقّٞۖ وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ
Open ayah 10:53Suna kuma tambayar ka cewa: “Yanzu (batun azabar nan) gaskiya ne kuwa?” Ka ce: “I mana, na ko ranste da Allah lalle shi gaskiya ne; ba kuma za ku kuɓuce ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin tambayar da mushirikai suke yi wa Annabi (ﷺ) da mabiyansa cewa, yaushe ne azabar Allah da suke yi musu alƙawarinta za ta zo musu idan sun kasance masu gaskiya? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ba su amsa cewa, shi a matsayinsa na Annabi ba shi da ikon ya cutar da kansa ko ya amfanar da kansa da komai sai abin da Allah ya ga dama ya ƙaddara masa, kuma ba shi da ikon ya zo musu da azabar da suke neman ya zo musu da ita, sai dai su sani cewa, kowacce al’umma tana da lokacin da aka iyakance mata na rayuwarta; idan wannan lokacin ya yi to ba za a jinkirta musu ba daidai da sa’a guda kuma ba za a gabato musu da ajalinsu ba kafin lokacinsa. Ya kuma umarce shi ya faɗa musu cewa, yanzu idan azabar Allah ta zo musu da daddare ko da rana, mene ne waɗannan masu laifi za su amfana da gaggauto da zuwanta in ban da sharri wanda kuma ba za su iya kauce masa ba idan ya zo? Kuma shin wai sai idan azabar ta auka musu ne sannan za su yi imani lokacin da imani ba zai yi musu amfani ba? Sai yanzu ne za su yi imani alhalin a da suna nema a gaggauto da azabar wadda suke ƙaryatawa? Sannan Allah ya bayyana cewa, a ranar alƙiyama za a faɗa wa waɗanda suka zalunci kawunansu cewa, su ɗanɗani azaba ta har abada, domin ai ba za a saka musu da komai ba sai da abin da suka kasance suna aikatawa a nan duniya. Sannan Allah ya bayyana cewa, mushirikai suna tambayar Annabi (ﷺ) cewa, azabar da aka yi musu alƙawarin zuwanta gaskiya ne kuwa? To Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya ba su amsa da \"I mana, na ko ranste da Allah lalle shi gaskiya ne, ba kuma za ku kuɓuce ba”. Watau idan ya zo.
وَلَوۡ أَنَّ لِكُلِّ نَفۡسٖ ظَلَمَتۡ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لَٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۖ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 10:54Da a ce kowane rai da ya yi zalunci ya mallaki duk abin da yake bayan ƙasa, to lalle da ya fanshi kansa da shi. Suka kuwa ɓoye nadama a lokacin da suka ga azaba; an kuma yi hukunci tsakaninsu na adalci; ba kuma za a zalunce su ba.
أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 10:55A saurara, lalle duk abin da yake sammai da ƙasa na Allah ne. A saurara, lalle alƙwarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancin mutane ba su sani ba.
هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 10:56Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma wurinsa za a mai da ku. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayani cewa, da a ce kowane rai da ya aikata kafirci ko shirka da Allah ya mallaki duk abin da yake bayan ƙasa, to da ya bayar da shi gaba ɗaya ranar alƙiyama a matsayin dukiyar fansar kansa daga azabar Allah, da ya san za a karɓa daga wajensa. Kafirai kuma za su riƙa ɓoye nadamarsu da takaicinsu a kan kafircinsu lokacin da suka ga azabar Allah ranar alƙiyama, suka tabbatar sai ta auka musu. Allah kuma ya yi hukunci a tsakaninsu da adalci ba tare da ya zalunce su ba da komai. Sai ya bayyana cewa, duk abin da yake cikin sammai da wanda yake bayan ƙasa haƙiƙa duk nasa ne, kuma lalle alƙawarinsa gaskiya ne yana nan tafe ba makawa, sai dai yawancin waɗannan mushirikan ba su sani ba. Shi ne kuma Ubangiji Allah Ɗaya tal mai kashewa mai rayawa, kuma zuwa gare shi kaɗai ɗaukacin mutane makomarsu take, don haka zai yi musu sakayya a ranar alƙiyama a kan ayyukansu.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَتۡكُم مَّوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَشِفَآءٞ لِّمَا فِي ٱلصُّدُورِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 10:57Ya ku mutane, haƙiƙa gargaɗi ya zo muku daga Ubangijinku da kuma waraka ga abin da yake cikin zukatanku, kuma shiriya ne da rahama ga muminai.
قُلۡ بِفَضۡلِ ٱللَّهِ وَبِرَحۡمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلۡيَفۡرَحُواْ هُوَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ
Open ayah 10:58Ka ce: “Da falalar Allah da rahamarsa, sai su yi farin ciki da wannan; shi ya fi alheri daga abin da suke tarawa (na dukiya).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ne ga mutane baki ɗaya domin sanar da su cewa, Alƙur’ani ya zo musu daga Ubangijinsu wanda yake ƙunshe da wa’azi da umarni da hani, kuma shi ne waraka ga cututtukan zukata irin su sha’awa da ƙullaci da hassada, kuma shiriya ne ga duk wanda ya yi riƙo da shi, zai kuma kuɓutar da shi daga halaka. Haka kuma shi rahama ce ga muminai domin shi ne zai tabbatar musu da duk wani alheri da amfani a rayuwar duniya da ta lahira. Sannan Allah ya umarci Annabi (ﷺ) da ya umarci muminai su yi farin ciki da murna a bisa falalar Allah, watau imani da Alƙur’ani ba da wani jin daɗi na duniya mai ƙarewa ba, wannan shi ne ya fi musu alheri fiye da abin da suke tarawa na ƙyale-ƙyalen duniya.
قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ لَكُم مِّن رِّزۡقٖ فَجَعَلۡتُم مِّنۡهُ حَرَامٗا وَحَلَٰلٗا قُلۡ ءَآللَّهُ أَذِنَ لَكُمۡۖ أَمۡ عَلَى ٱللَّهِ تَفۡتَرُونَ
Open ayah 10:59Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin abin da Allah Ya saukar muku na arziki, sannan kuka mayar da wani haram wani kuma halal”. Ka ce: “Yanzu Allah ne Ya yi muku izinin (yin haka), ko kuwa Allah kuke yi wa ƙage ne?”
وَمَا ظَنُّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَشۡكُرُونَ
Open ayah 10:60Mene ne kuma tsammanin waɗanda suke yi wa Allah ƙagen ƙarya a ranar alƙiyama? Lalle Allah Ma’abocin falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tambayi mushirikai game da arziƙin da Allah ya ba su na dabbobi da kayan amfanin gona, amma kuma sai suka ware wasu suka halatta wa kawunansu, suka kuma haramta wasu ga kawunansu. To wai shin Allah ne ya ba su damar su halatta waɗanda suka halatta, su kuma haramta waɗanda suka haramta, ko kuwa dai ƙarya ce suke ƙaga wa Allah? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin tsananin narkonsa gare su a kan ƙaryar da suke ƙaga masa da cewa, me suke tsammanin zai yi musu a ranar alƙiyama, shin suna zaton zai ƙyale su ne hakanan ba tare da ya azabtar da su ba? A’a, ba haka ne ba, uƙubarsu a ranar mai tsananin gaske ce saboda ƙaryar da suke yi wa Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, falalarsa ga mutane mai yawa ce, daga cikin falalarsa akwai hore wa bayinsa ni’imomi masu yawa a duniya, yake kuma saurara wa masu laifi ba tare da ya gaggauto yi musu azaba ba; sai dai yawancin mutane ba sa gode wa waɗannan ni’imomi da ya yi musu.
وَمَا تَكُونُ فِي شَأۡنٖ وَمَا تَتۡلُواْ مِنۡهُ مِن قُرۡءَانٖ وَلَا تَعۡمَلُونَ مِنۡ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيۡكُمۡ شُهُودًا إِذۡ تُفِيضُونَ فِيهِۚ وَمَا يَعۡزُبُ عَن رَّبِّكَ مِن مِّثۡقَالِ ذَرَّةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَلَآ أَصۡغَرَ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكۡبَرَ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٍ
Open ayah 10:61Kuma babu wani al’amari da (kai Annabi) kake zamantowa cikinsa, babu kuma wani abu na Alƙur’ani da kake karantawa, kuma babu wani abu da kuke aikatawa (kai da al’ummarka), sai Mun zamanto Muna kallon ku lokacin da kuke kutsawa cikinsa. Kuma babu wani abu da yake ɓoye wa Ubangijinka daidai da ƙwayar komayya, a ƙasa ko a sama ko kuma mafi ƙanƙanta ko mafi girma daga wancan (abin) sai fa yana cikin litttafi mabayyani (Lauhul-Mahafuzu).
أَلَآ إِنَّ أَوۡلِيَآءَ ٱللَّهِ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 10:62A saurara, lalle waliyyan Allah babu wani tsoro a gare su, kuma ba za su yi wani baƙin ciki ba.
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ
Open ayah 10:63(Su ne) waɗanda suka yi imani kuma suka kasance masu kiyaye dokokin Allah.
لَهُمُ ٱلۡبُشۡرَىٰ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ لَا تَبۡدِيلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 10:64Suna da albishir a rayuwar duniya da kuma ta lahira. Babu wani sauyi ga kalmomin Allah. Wannan shi ne babban rabo. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da Annabi (ﷺ) cewa, babu wani aiki da zai zamanto a cikinsa, ko wata sura ta Alƙur’ani da zai karanta, ko abin da mutane za su aikata na alheri ko na sharri, babba ko ƙarami mai yawa ko kaɗan, face Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ganin duk abin da yake gudana lokacin da suke aiwatar da shi, kuma zai kiyaye musu shi, ya yi musu sakayya a kai. Hakanan babu abin da yake ɓoye wa Allah komai ƙanƙantarsa, ko da ƙwayar komayya ne, a sama ko a ƙasa, ko ma abin da bai kai haka ba ko ya fi hakan, face duk wannan abu yana nan rubuce a cikin Lauhul-Mahfuzu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ko su wane ne waliyyansa, watau masoyansa, waɗanda yake son su yake taimakon su a koyaushe, ya bayyana cewa waɗannan bayin Allah na ƙwarai babu wani tsoro a tare da su game da abin da za su iske ranar alƙiyama, kuma ba za su yi wani baƙin ciki ba dangane da abin da za su bari nan duniya. Sai ya bayyana siffofin waɗannan waliyyai da abin da suka yi suka cancanci wannan babban matsayi a wurinsa. Ya ce su ne waɗanda suka yi imani da duk abin da ya wajaba a kansu su yi imani da shi, kuma suka zamanto masu kiyaye dokokin Allah, ta hanyar aikata umarninsa da kauce wa haninsa. Sannan ya bayyana sakamakonsu da cewa, suna da albishir daga Allah a rayuwarsu ta duniya da kuma rayuwarsu ta lahira. Babu kuma wani sauyi daga maganar Allah, kuma babu saɓa wa alƙawari a wurinsa. Wannan shi ne babban rabo.
وَلَا يَحۡزُنكَ قَوۡلُهُمۡۘ إِنَّ ٱلۡعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًاۚ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 10:65Kada kuma wata maganarsu ta baƙanta maka rai. Lalle girma gaba ɗayansa na Allah ne. Shi Mai ji ne, Masani.
أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَمَا يَتَّبِعُ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُرَكَآءَۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنۡ هُمۡ إِلَّا يَخۡرُصُونَ
Open ayah 10:66Ku saurara, lalle duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa na Allah ne. Waɗanda suke bauta wa wani ba Allah ba, ba ababen tarayya (na gaskiya) suke bi ba. Ba abin da suke bi sai mummunan zato, kuma ba abin da suke yi sai shaci-faɗi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana lallashin Annabi (ﷺ) ne dangane da abin da kafirai suke faɗa masa na baƙaƙen maganganu da ƙaryata shi a kan saƙon da ya zo musu da shi. Allah yana cewa, kada maganarsu da izgilinsu su baƙanta masa rai, domin girma da ɗaukaka duka na Allah ne shi kaɗai a duniya da lahira; shi ne mai kare shi daga duk wata cuta da makircinsu, kuma shi mai jin duk abin da yake fita daga bakunansu ne, masani ne game da duk ayyukansu, don haka zai yi musu sakayya a kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakken ikonsa mai nuna zai iya yin duk abin da ya ga dama, watau kasancewar duk abin da yake sammai da wanda yake ƙasa nasa ne shi kaɗai ba ya da abokin tarayya a ciki. Kuma su masu bautar wasu abubuwan tarayya ba Allah ba me suke bi ne? Ba komai suke bi ba sai zato ba tare da wani dalili ba, kuma ba komai suke faɗa ba sai ƙarya suna jingina wa Allah.
هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ
Open ayah 10:67Shi ne Wanda Ya sanya muku dare don ku samu nutsuwa, rana kuma don haskakawa. Lalle a game da wannan ba tabbas akwai ayoyi ga mutane masu ji.
قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۖ هُوَ ٱلۡغَنِيُّۖ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ إِنۡ عِندَكُم مِّن سُلۡطَٰنِۭ بِهَٰذَآۚ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 10:68Suke ce Allah Yana da ɗa! Tsarki ya tabbata gare Shi. Shi Mawadaci ne. Abin da yake cikin sammai da abin da yake ƙasa nasa ne. Ko kuna da wata hujja ne game da wannan? Yanzu kwa riƙa faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?
قُلۡ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا يُفۡلِحُونَ
Open ayah 10:69Ka ce: “Lalle waɗanda suke ƙaga wa Allah ƙarya ba za su rabauta ba.”
مَتَٰعٞ فِي ٱلدُّنۡيَا ثُمَّ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ ثُمَّ نُذِيقُهُمُ ٱلۡعَذَابَ ٱلشَّدِيدَ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ
Open ayah 10:70Jin daɗi ne kawai a cikin duniya, sannan kuma gare Mu ne makomarsu take, sannan Mu ɗanɗana musu azaba mai tsanani saboda abin da suka zamanto suna yi na kafirci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wasu ni’imominsa ne ga ɗan’adam. Ya ambaci cewa shi ne wanda ya halitta musu dare domin su samu hutu a cikinsa bayan sun yi aiki sun gaji, kuma ya samar musu da yini mai haske domin su fita neman abincinsu a cikinsa da biyan buƙatunsu na rayuwa. Lalle game da waɗannan ayyuka na Allah akwai ayoyi masu nuna kaɗaitakarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai ga mutane masu sauraron ayoyin Allah suna ɗaukar izina daga gare su. Sai kuma ya bayyana cewa, mushirikan Larabawa sun riya cewa wai Allah yana da ɗa, tsarki ya tabbata a gare shi, Allah mawadaci ne ba ya buƙatar mata ko ɗa, kai ba ya da buƙata wajen kowa da komai, sammai da ƙasa duk nasa ne. Don haka ta yaya zai riƙi ɗa daga abin da shi ne ya halicce shi kuma mallakarsa ne? Waɗannan mushirikai masu da’awar cewa Allah yana da ɗa ba su da wata hujja a kan wannan mummunar maganar tasu. To me ya sa za su riƙa maganar da ba su da ilimi a kanta suna jingina ta ga Allah? Sannan ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tabbatar wa duk masu yi wa Allah ƙarya cewa, ba za su rabauta ba har abada a duniya ko a lahira. A nan duniya za su ji ɗan ji daɗi kaɗan; daga ƙarshe makomarsu zuwa ga Allah ne sannan ya ɗanɗana musu azaba mai raɗaɗi saboda kafircinsu.
۞وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ نُوحٍ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيۡكُم مَّقَامِي وَتَذۡكِيرِي بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَعَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡتُ فَأَجۡمِعُوٓاْ أَمۡرَكُمۡ وَشُرَكَآءَكُمۡ ثُمَّ لَا يَكُنۡ أَمۡرُكُمۡ عَلَيۡكُمۡ غُمَّةٗ ثُمَّ ٱقۡضُوٓاْ إِلَيَّ وَلَا تُنظِرُونِ
Open ayah 10:71Ka kuma karanta musu labarin (Annabi) Nuhu, a lokacin da ya ce da mutanensa: “Ya ku mutanena, idan zamana a cikinku da kuma wa’azin da nake muku da ayoyin Allah sun dame ku, to ni fa ga Allah ne kawai na dogara, sai ku tattara al’amarinku ku kuma (ku kira) abokan tarayyarku, sannan kada al’amarin naku ya zama a ɓoye, sannan ku zartar (da shi) a gare ni, kada kuma ku saurara mini.
فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَمَا سَأَلۡتُكُم مِّنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 10:72“To idan kuka ba da baya, to ban tambaye ku wani lada ba; ladana yana ga Allah; an kuwa umarce ni da in kasance cikin Musulmai.”
فَكَذَّبُوهُ فَنَجَّيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ وَجَعَلۡنَٰهُمۡ خَلَٰٓئِفَ وَأَغۡرَقۡنَا ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Open ayah 10:73Sai suka ƙaryata shi, sai Muka tserar da shi da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwa, Muka kuma mayar da su masu maye gurbin (waɗanda suka gabace su), Muka kuma nutsar da waɗanda suka ƙaryata ayoyinmu. To duba ka ga yadda ƙarshen waɗanda aka yi wa gargaɗi ya kasance. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasu dalilai a kan kaɗaitakarsa da abin da ya gudana tsakanin Manzon Allah (ﷺ) da kafirai, sai kuma ya kawo wasu ƙissoshi na wasu annabawa tare da mutanensu don su zama lallashi ga Annabi (ﷺ) a kan abin da mutanensa suke yi masa na tsangwama da cutarwa. Allah ya fara da labarin Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) inda ya umarci Annabi (ﷺ) da ya karanta wa kafirai labarinsa a lokacin da yake faɗa wa mutanensa cewa, idan zamansa a cikinsu da gargaɗi da yake yi musu da hujjoji masu ƙarfi sun dame su, har suna shirin su auka masa, su cuce shi, to yana shaida musu cewa, shi da Allah kaɗai ya dogara, shi ne wanda zai taimake shi ya kare shi daga sharrinsu. Don haka su gama shirinsu gaba ɗaya na cutar da shi, su ma nemo waɗanda za su taimaka musu, sannan kada su gudanar da al’amarinsu a ɓoye; su zartar da duk abin da suka gama saƙawa a ransu, kada su saurara masa. Sannan Allah ya bayyana cewa, idan sun bijire wa da’awarsa, to shi fa da man ba yana neman wani lada ne daga wurinsu ba, ladansa yana wurin Allah, shi ne kuma ya umarce shi ya zamanto farkon masu miƙa wuya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin mutanen Annabi Nuhu cewa, sun ƙaryata shi, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tserar da shi da waɗanda suka yi imani da shi a cikin jirgin ruwa, su kuma waɗanda suka kafirce masa, Allah ya nutsar da su a cikin ruwan Ɗufana. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi tunani da duba na tsanaki game da yadda ƙarshen al’amarin mutanen da manzonsu ya yi musu gargaɗin azabar Allah ya kasance.
ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ رُسُلًا إِلَىٰ قَوۡمِهِمۡ فَجَآءُوهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُواْ بِمَا كَذَّبُواْ بِهِۦ مِن قَبۡلُۚ كَذَٰلِكَ نَطۡبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلۡمُعۡتَدِينَ
Open ayah 10:74Sannan a bayansa (Annabi Nuhu) Muka aika manzanni zuwa ga mutanensu suka zo musu da (ayoyi) mabayyana, ba su zamanto suna gaskata abin da a da can suke ƙaryata shi ba. Kamar haka ne Muke tushe zukatan masu shisshigi.
ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ وَهَٰرُونَ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ بِـَٔايَٰتِنَا فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ
Open ayah 10:75Sannan daga bayansu Muka aiko Musa da Haruna zuwa ga Fir’auna shi da jama’arsa da ayoyinmu, sai suka yi girman kai suka kuwa zamanto mutane masu laifi.
فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ مِنۡ عِندِنَا قَالُوٓاْ إِنَّ هَٰذَا لَسِحۡرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 10:76To lokacin da gaskiya ta zo musu daga wurinmu sai suka ce: “Lalle wannan tabbas tsafi ne bayyananne.”
قَالَ مُوسَىٰٓ أَتَقُولُونَ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَكُمۡۖ أَسِحۡرٌ هَٰذَا وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّٰحِرُونَ
Open ayah 10:77Musa ya ce: “Yanzu kwa riƙa ce wa gaskiya (tsafi) lokacin da ta zo muku? Yanzu wannan ne tsafin, alhali kuwa matsafa ba sa cin nasara?”
قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَلۡفِتَنَا عَمَّا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا نَحۡنُ لَكُمَا بِمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 10:78Suka ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka raba mu da abin da muka sami iyayenmu a kansa, ku kuma (kai da Haruna) ku zamanto ku ne masu girma a bayan ƙasa? Mu kam ba za mu yi imani da ku ba!” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin ya aiko da wasu manzannin bayan wucewar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya ba su mu’ijizoji masu tabbatar da ingancin manzancinsu ga mutanensu, to amma sai waɗanda suka rungumi kafirci daga cikin mutanensu suka ƙi yarda su ba da gaskiya da su, to Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe zukatansu domin sun ƙi yin imani. To kamar haka ne Allah yake rufe zukatan masu shisshigi. Bayan wucewar waɗannan manzanni Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko da Annabi Musa da Haruna zuwa ga Fir’auna da jama’arsa, ya ba su mu’ujizoji masu tabbatar da gaskiyarsu, to amma sai mutanen Fir’auna suka yi girman kai suka ƙi karɓar gaskiya suka kuma zamanto mutane masu laifi. Yayin da Annabi Musa ya zo wa Fir’auna da saƙo na gaskiya sai shi da mutanensa suka bijire suka ce wai abin da Musa ya zo da shi tsafi ne bayyananne. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tsawatar musu da cewa, yanzu gaskiyar da ta zo musu suke gani da idanunsu ita ce za su kira tsafi? Matsafa ai ba sa rabauta a duniya da lahira. Jin wannan ya sa Fir’auna da manyan fadawansa suka tambayi Annabi Musa cewa, yanzu ya zo ne don ya raba su da bautar abin da suka sami iyayensu suna bauta wa, su kuma Annabi Musa da Haruna girma da sarauta su zama nasu? To su kam ba za su yi imani da su ba.
وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ٱئۡتُونِي بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ
Open ayah 10:79Fir’auna kuma ya ce: “Ku zo mini da duk wani ƙwararren matsafi.”
فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ
Open ayah 10:80To lokacin da matsafan suka zo, sai Musa ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”
فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئۡتُم بِهِ ٱلسِّحۡرُۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبۡطِلُهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصۡلِحُ عَمَلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 10:81To lokacin da suka jefa (kayan tsafinsu), sai Musa ya ce: “Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne; lalle ko Allah zai ɓata shi. Lalle Allah ba Ya gyara aikin maɓarnata.
وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 10:82“Allah zai tabbatar da gaskiya da ikonsa ko da kuwa masu manyan laifuka sun ƙi.” Lokacin da Fir’auna da fadawansa suka zargi Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa shi matsafi ne, sai kuma suka shiga laluben abin da za su kafa hujja da shi a kan wannan zargin nasu. Allah ya ba da labarin cewa yayin da Fir’auna da mutanensa suka ga dagewar Annabi Musa a kan da’awarsa zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, sai Fir’auna ya yi shela da a gayyato masa duk wani gwanin tsafi daga ko’ina a ƙasar. Yayin da suka hallara, sai Annabi Musa ya umarce da su jefar da igiyoyinsu da sandunansu a ƙasa; da suka jefar sai igiyoyin da sandunan suka riƙa gudu a ƙasa, sai Annabi Musa ya ce, wannan abu da suka kawo shi ne tsafi, kuma Allah zai rushe shi, kuma Allah ba ya gyara aikin maɓarnata, kuma shi zai tabbatar da gaskiyar da Annabi Musa ya zo da ita ko da kuwa masu laifi sun ƙi.
فَمَآ ءَامَنَ لِمُوسَىٰٓ إِلَّا ذُرِّيَّةٞ مِّن قَوۡمِهِۦ عَلَىٰ خَوۡفٖ مِّن فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِمۡ أَن يَفۡتِنَهُمۡۚ وَإِنَّ فِرۡعَوۡنَ لَعَالٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Open ayah 10:83To ba wanda ya yi imani da Musa sai wasu ‘yan samari daga mutanensa don tsoron kada Fir’auna da mutanensa su azabtar da su. Kuma lalle Fir’auna ya tabbata mai girman kai ne a bayan ƙasa. Lalle kuma shi yana cikin maɓarnata.
وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰقَوۡمِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ فَعَلَيۡهِ تَوَكَّلُوٓاْ إِن كُنتُم مُّسۡلِمِينَ
Open ayah 10:84Musa kuma ya ce: “Ya ku mutanena, idan har kun yi imani da Allah, to a gare Shi kawai za ku dogara in kun kasance Musulmai.
فَقَالُواْ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡنَا رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا فِتۡنَةٗ لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 10:85Sai suka ce: “Ga Allah kaɗai muka dogara. Ya Ubangijinmu, kada ka sanya mu zama fitina ga mutane azzalumai.
وَنَجِّنَا بِرَحۡمَتِكَ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 10:86“Ka kuma tserar da mu da rahamarka daga mutane kafirai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, duk da irin ƙarfafan hujjoji da Annabi Musa ya nuna wa mutanensa, babu wanda ya yi imani da shi sai wasu samari kaɗan daga cikin mutanen Fir’auna saboda tsoron fitinarsa da ta mutanensa. Kuma lalle Fir’auna babban mai girman kai ne da zalunci a bayan ƙasa, sannan kuma ya yi nisa sosai cikin kafirci da ɓarna. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi ta lallashin mutanensa waɗanda suka yi imani da shi yana kwantar musu da hankali da cewa, su dogara ga Allah shi kaɗai su miƙa wuya gare shi matuƙar dai sun kasance Musulmi. Jin haka Banu Isra’ila suka ce sun dogara ga Allah shi kaɗai, kuma suka roƙe shi da kada ya sanya su zama fitina ga kafirai, watau kada ya ba kafirai nasara a kansu har su riƙa zaton ko su ne a kan gaskiya, muminai kuma a kan ƙarya. Suka kuma roƙe shi da ya tserar da su da rahamarsa daga mutane kafirai, watau Fir’auna da jama’arsa.
وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوۡمِكُمَا بِمِصۡرَ بُيُوتٗا وَٱجۡعَلُواْ بُيُوتَكُمۡ قِبۡلَةٗ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 10:87Kuma Muka yi wa Musa wahayi shi da ɗan’uwansa cewa: “Ku tanadar wa mutanenku gidaje a Masar, ku kuma sanya gidajenku wurin salla.” Ka kuma yi wa muminai albishir (da samun nasara).
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبَّنَآ إِنَّكَ ءَاتَيۡتَ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَأَهُۥ زِينَةٗ وَأَمۡوَٰلٗا فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا رَبَّنَا لِيُضِلُّواْ عَن سَبِيلِكَۖ رَبَّنَا ٱطۡمِسۡ عَلَىٰٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ وَٱشۡدُدۡ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُواْ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ
Open ayah 10:88Musa kuma ya ce: “Ya Ubangijinmu, lalle Ka bai wa Fir’auna da mutanensa kayan ado da kuma dukiyoyi a rayuwar duniya; ya Ubangijimu, don su ɓatar (da jama’a) daga hanyarka; ya Ubangijimu, Ka shafe dukiyoyinsu Ka kuma ƙeƙasar da zukatansu ba za su yi imani ba har sai sun ga azaba mai raɗaɗi.”
قَالَ قَدۡ أُجِيبَت دَّعۡوَتُكُمَا فَٱسۡتَقِيمَا وَلَا تَتَّبِعَآنِّ سَبِيلَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 10:89(Allah) Ya ce: “Haƙiƙa an amsa addu’arku, sai ku tsaya ƙyam (a kan tafarkinku), kada kuwa ku bi hanyar waɗanda ba sa sanin (gaskiya).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa ya yi wa Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna wahayi cewa, su tanadar wa mutanensu gidajen zama a garin Masar, sannan su mayar da su wuraren sallolinsu, su kuma yi sallolinsu na farilla a kan lokaci, kuma ya ya umarci Annabi Musa da ya yi wa muminai albishir da samun nasara da lada daga Allah. Sai kuma Annabi Musa ya yi addu’a ga Fir’auna da azzaluman mutanensa yana mai faɗa wa Allah cewa, ga shi dai ya ba wa Fir’auna da manyan fadawansa kayan ado na more rayuwar duniya da dukiya mai yawa domin ta zama fitina a gare su, su yi amfani da ita don su ɓatar da mutane, hakan kuma ya zame musu uƙuba gare su. Don haka ya roƙe shi da ya lalata dukiyoyinsu ta yadda ba za su more su ba, sannan ya doɗe musu zukatansu don kuwa ya tabbata cewa ba za su yi imani ba har sai sun ga azaba mai raɗaɗi ta afka musu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Musa da Haruna cewa, ya amsa musu addu’arsu, don haka su ci gaba da tsayawa ƙyam a kan addininsu, su ci gaba da da’awarsu da wa’azinsu ga Fir’auna da mutanensa, kada su bi hanyar waɗanda ba su san komai dangane da gaskiyar alƙawarinsa ba, da kuma cewar shi ba ya saɓa alƙawarinsa.
۞وَجَٰوَزۡنَا بِبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱلۡبَحۡرَ فَأَتۡبَعَهُمۡ فِرۡعَوۡنُ وَجُنُودُهُۥ بَغۡيٗا وَعَدۡوًاۖ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَدۡرَكَهُ ٱلۡغَرَقُ قَالَ ءَامَنتُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱلَّذِيٓ ءَامَنَتۡ بِهِۦ بَنُوٓاْ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَأَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 10:90Muka kuma ƙetarar da Banu Isra’ila kogi, sai Fir’auna ya bi su shi da rundunarsa don zalunci da ta’addanci, har sai lokacin da nutsewa ta riske shi sai ya ce: “Na yi imani cewa babu wani abin bauta sai wanda Banu Isra’ila suka yi imani da shi, kuma ni ina cikin Musulmai.”
ءَآلۡـَٰٔنَ وَقَدۡ عَصَيۡتَ قَبۡلُ وَكُنتَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 10:91Sai yanzu kuma, bayan da can ka yi ta saɓo, ka kuma kasance cikin masu ɓarna?
فَٱلۡيَوۡمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنۡ خَلۡفَكَ ءَايَةٗۚ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ عَنۡ ءَايَٰتِنَا لَغَٰفِلُونَ
Open ayah 10:92To a yau kam za Mu tserar da gangar jikinka don ka zamanto aya ga na bayanka. Lalle kuwa yawancin mutane masu gafala ne ga lura da ayoyinmu. A nan Allah yana bayanin cewa ya ƙetarar da Banu Isra’ila kogi. Fir’auna kuma da rundunarsa ta zalunci suka bi su da niyyar dawo da su ga azaba da wulaƙanci, to amma sai ruwa ya haɗiye su. Lokacin da Fir’auna ya ga halaka ne, ruwa zai ci shi, sannan ne ya ce ya yi imani babu wani abin bauta sai wanda Banu Isra’ila suka yi imani da shi kuma yana cikin masu miƙa wuya, watau dai zai yi biyayya ga Annabi Musa da abin da ya zo da shi na gaskiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar masa da martani cewa, sai yanzu ne zai ce ya yi imani, alhalin a baya kafin ya ga wannan halaka ya saɓa masa ya tabbata cikin maɓarnata masu hana a bi gaskiya? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa, to a wannan lokaci zai fito da gawarsa fili a kan tudu domin duk wanda zai ƙaryata halakarsa ya ga gawarsa da idonsa, kuma ya zama darasi ga ‘yan bayansa, domin yawancin mutane gafalallu ne ga lura da ayoyin Allah ba sa ɗaukar izina.
وَلَقَدۡ بَوَّأۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ مُبَوَّأَ صِدۡقٖ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ فَمَا ٱخۡتَلَفُواْ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 10:93Haƙiƙa Mun sanya Banu Isra’ila a kyakkyawan matsayi na gaskiya, Muka kuma arzuta su da abubuwa daɗaɗa na halal, to kawunansu ba su tashi rabuwa ba har sai lokacin da ilimi ya zo musu. Lalle Ubangijinka zai yi hukunci tsakaninsu ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna saɓani a kansa.
فَإِن كُنتَ فِي شَكّٖ مِّمَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ فَسۡـَٔلِ ٱلَّذِينَ يَقۡرَءُونَ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكَۚ لَقَدۡ جَآءَكَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ
Open ayah 10:94To idan kana tababa game da abin da Muka saukar maka to sai ka tambayi waɗanda suke karanta littafi gabaninka. Haƙiƙa gaskiya ta zo maka daga Ubangijinka; to kada ka zama daga cikin masu kokwanto.
وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Open ayah 10:95Lalle kuma kada ka kasance daga cikin waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah, sai ka zamo daga asararru. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana irin ni’imomin da ya yi wa Banu Isra’ila, ya saukar da su kyawawan gidaje masu nagarta, ya kuma arzuta su da daɗaɗan abubuwa na halal na ƙasa mai albarka. Ba su yi saɓani a kan gaskiyar aiko Manzon Allah (ﷺ) ba har sai da Alƙur’ani ya sauko da bayanin gaskiyar manzancinsa da addininsa, a lokacin ne yawancinsu suka ƙaryata. Ya bayyana wa Manzon Allah (ﷺ) cewa Ubangijinsa zai yi musu hukunci a ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna saɓani a kansa na al’amarin manzancinsa, sai ya shigar da masu ƙaryatawa gidan wuta, ya shigar da muminai Aljanna. Sai kuma ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa idan yana tababa game da abin da Allah ya saukar masa, to ya tambayi waɗanda suke karanta littafin da Allah ya saukar gabanin Alƙur’ani, watau Attaura da Linjila, wannan batun da yake faɗa masa yana nan tabbace a cikin littattafansu. A nan babu abin da ya nuna Annabi (ﷺ) ya yi tababa ko shakka game da wahayi da Allah ya yi masa, sai dai ana nufin ne a tsayar wa da ma’abota littafi hujjar gaskiyar annabcin Manzon Allah (ﷺ), a nuna musu cewa hakan yana nan a rubuce a cikin littattafansu a wurin malamansu, idan aka tambaye su, in za su faɗi gaskiya, to za su bayyana hakan. Hakanan waɗanda suka yi imani daga cikin ma’abota littafi, kamar Abdullahi ɗan Salam da jama’arsa, sun tabbatar da hakan. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi Annabi (ﷺ) da kada ya zamanto daga cikin masu shakka, kuma kada ya zamanto cikin waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah sai ya zamo cikin hasararru waɗanda Allah ya yi fushi da su.
إِنَّ ٱلَّذِينَ حَقَّتۡ عَلَيۡهِمۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 10:96Lalle waɗanda kalmar Ubangijinka ta tabbata a kansu (ta zamansu ‘yan wuta) ba za su yi imani ba.
وَلَوۡ جَآءَتۡهُمۡ كُلُّ ءَايَةٍ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ
Open ayah 10:97Ko da kuwa dukkanin ayoyi sun zo musu har sai sun ga azaba mai raɗaɗi.
فَلَوۡلَا كَانَتۡ قَرۡيَةٌ ءَامَنَتۡ فَنَفَعَهَآ إِيمَٰنُهَآ إِلَّا قَوۡمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُواْ كَشَفۡنَا عَنۡهُمۡ عَذَابَ ٱلۡخِزۡيِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ
Open ayah 10:98Babu wasu mutane na wata alƙarya da suka yi imani, sannan imaninsu ya amfane su, sai fa mutanen Yunusa, lokacin da suka yi imani sai Muka yaye musu azabar wulaƙanci a rayuwar duniya, Muka kuma jiyar da su daɗi har zuwa wani lokaci (iyakantacce).
وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ لَأٓمَنَ مَن فِي ٱلۡأَرۡضِ كُلُّهُمۡ جَمِيعًاۚ أَفَأَنتَ تُكۡرِهُ ٱلنَّاسَ حَتَّىٰ يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 10:99Da Ubangijinka Ya ga dama lalle da duk waɗanda suke bayan ƙasa sun yi imani gaba ɗayansu. Shin kai ne za ka tilasa wa mutane har su zama muminai?
وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تُؤۡمِنَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَجۡعَلُ ٱلرِّجۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 10:100Ba zai yiwu wani rai ya yi imani ba sai da izinin Allah. Yana kuma sanya azaba ne a kan waɗanda ba sa hankalta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, waɗanda kalmar Allah ta tabbata a kansu cewa za su mutu a kan kafirci, ba za su rabauta da rahamar Allah ba, don haka waɗannan ba za su taɓa yin imanin da zai yi musu amfani ba kafin mutuwarsu, ko da kuwa dukkan wasu ayoyi da hujjoji sun zo musu, har sai sun ga azaba mai raɗaɗi ƙarara ta zo musu, to a lokacin ne za su ce sun yi imani, imanin da ba zai yi musu amfani ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin mutanen alƙaryar Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka yi imani bayan sun tabbatar da azaba za ta zo musu a halaka su gaba ɗaya, sai kuma imaninsu ya amfane su, Allah ya tserar da su ya janye musu azabar. Allah ya bayyana cewa, babu wata alƙarya da ya taɓa halakar wa a baya da aka yi musu irin wannan alfarmar sai mutanen Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya bar su suka ci gaba da more rayuwarsu har zuwa lokutan mutuwarsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, da ya ga dama da waɗanda suke a doron ƙasa sun yi imani gaba ɗayansu da abin da ya zo musu da shi, sai dai Allah yana da hikimarsa a nan, yana shiryar da wanda ya ga dama, ya ɓatar da wanda ya ga dama bisa hikimarsa, don haka shi Manzon Allah (ﷺ) ba zai iya tilasta wa mutane sai sun yi imani ba. Kuma ma babu wani rai da zai yi imani sai da ganin damar Allah da ƙaddarawarsa, don haka kada Manzon Allah ya wahalar da kansa a kan wannan, domin al’amarinsu duka yana hannun Allah ne, don haka yana sanya fushinsa da azabarsa a kan mutanen da ba sa hankaltar umarninsa da haninsa.
قُلِ ٱنظُرُواْ مَاذَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَا تُغۡنِي ٱلۡأٓيَٰتُ وَٱلنُّذُرُ عَن قَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 10:101Ka ce: “Ku yi tunanin abubuwan da suke cikin sammai da ƙasa.” Ayoyi kuwa da masu gargaɗi ba sa wadatar da mutanen da ba sa yin imani.
فَهَلۡ يَنتَظِرُونَ إِلَّا مِثۡلَ أَيَّامِ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِهِمۡۚ قُلۡ فَٱنتَظِرُوٓاْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُنتَظِرِينَ
Open ayah 10:102Ai ba abin da suke saurare sai irin azabar da ta sami waɗanda suka wuce gabaninsu. Ka ce: “Sai ku saurara, lalle ni ma ina tare da ku cikin masu sauraro.”
ثُمَّ نُنَجِّي رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ كَذَٰلِكَ حَقًّا عَلَيۡنَا نُنجِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 10:103Sannan Muka riƙa tserar da manzanninmu da waɗanda suka yi imani da su. Kamar haka ne ya zama lalle a kanmu Mu tserar da muminai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa mushirikai masu neman wasu mu’ujizoji daga gare shi cewa, su yi duba da tunani game da abin da yake cikin sammai da ƙasa na ayoyin Allah bayyanannu, su kaɗai sun ishe su ba sai sun nemi wasu ayoyi daban ba. Ayoyin Allah da wa’azuzzuka da manzanni masu gargaɗin bayi game da azabar Allah ba za su amfani mutanen da ba su yi imani da su ba, saboda tsaurin kansu da bijirewarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara da cewa, to yanzu shin waɗannan mutane akwai abin da suke jira ne in ban da irin abin da ya sami kafiran da suka gabace su na azabar Allah ya same su? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi ya faɗa musu cewa, su jira lokacin zuwan azabar Allah gare su, shi ma yana tare da su yana jiran hakan. Idan kuma azabar ta zo to Allah yakan tserar da manzanninsa da waɗanda suka yi imani tare da su, to haka shi ma Manzon Allah (ﷺ), Allah zai kuɓutar da shi da waɗanda suka yi imani da shi da rahamarsa da falalarsa.
قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي شَكّٖ مِّن دِينِي فَلَآ أَعۡبُدُ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِنۡ أَعۡبُدُ ٱللَّهَ ٱلَّذِي يَتَوَفَّىٰكُمۡۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 10:104Ka ce: “Ya ku mutane, idan kun kasance cikin kokwanto game da addinina, to ba zan bauta wa waɗanda kuke bauta wa ba Allah ba, sai dai ni zan bauta wa Allah ne wanda Yake karɓar rayukanku, an kuma umarce ni da in zama cikin muminai.
وَأَنۡ أَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 10:105“Kuma (an umarce ni) da cewa: ‘Ka tsai da fuskarka ga addinin Allah wanda ya karkace wa ɓarna, kada kuma ka kasance cikin mushirikai.
وَلَا تَدۡعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَۖ فَإِن فَعَلۡتَ فَإِنَّكَ إِذٗا مِّنَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 10:106“Kada kuma ka bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai amfane ka ba, ba kuma zai cuce ka ba; to idan kuwa ka aikata haka to lalle daga sannan ka zama cikin azzalumai.’”
وَإِن يَمۡسَسۡكَ ٱللَّهُ بِضُرّٖ فَلَا كَاشِفَ لَهُۥٓ إِلَّا هُوَۖ وَإِن يُرِدۡكَ بِخَيۡرٖ فَلَا رَآدَّ لِفَضۡلِهِۦۚ يُصِيبُ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 10:107Idan Allah Ya ɗora maka wata cuta to ba mai yaye maka ita sai shi; idan kuma Ya nufe ka da alheri to ba mai juyar da falalarsa. Yana bayar da shi ga waɗanda Ya ga dama daga bayinsa. Shi ne kuma Mai gafara, Mai jin ƙai.
قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُمُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِوَكِيلٖ
Open ayah 10:108Ka ce: “Ya ku mutane, haƙiƙa gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku; duk wanda ya shiriya to ya shiriya ne don kansa; wanda kuma ya ɓace to lalle ya ɓace don kansa ne; ni kuwa ba wakili ne a kanku ba.”
وَٱتَّبِعۡ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيۡكَ وَٱصۡبِرۡ حَتَّىٰ يَحۡكُمَ ٱللَّهُۚ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡحَٰكِمِينَ
Open ayah 10:109Kuma ka bi abin da aka yi maka wahayinsa, ka kuma yi haƙuri har sai Allah Ya yi hukunci. Shi ne kuwa Fiyayyen masu hukunci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) ya faɗa wa mushirikai cewa, idan su suna shakkar addinin da ya kawo musu, watau Musulunci, to shi fa ba zai taɓa amincewa ya bauta wa gumakansu da suke bauta wa ba; shi Allah kaɗai yake bauta wa, shi ne kuma mai karɓar rayukansu idan lokacin mutuwarsu ya zo; ya kuma shaida musu Allah ya umarce shi ya kasance daga muminai. Kuma ya sanar da su cewa, Allah ya umarce shi da ya tsaya ƙyam a kan addinin Musulunci ya kauce wa duk wata ɓarna, kada kuma ya kuskura ya zama cikin masu haɗa Allah da wasu kishiyoyi cikin bauta. Idan kuwa har ya yi hakan, to zai zama cikin halakakku. Kuma Allah ya hane shi da bauta wa duk wani abu da ba zai amfane shi da komai ba, ba kuma zai cutar da shi da komai ba, idan kuwa har ya yi haka, to ya tabbata cikin azzalumai masu shirka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ƙarfafa masa cewa, idan Allah ya nufe shi da samun wata cuta ko wani bala’i, to babu mai yaye masa su sai Allah, idan kuwa ya nufe shi da wani alhairi ko wata ni’ima, to babu wanda ya isa ya hana masa samun su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ne yake nufin bayinsa da samun abin da ya ga dama mai daɗi ko marar daɗi, shi ne kuma yake gafarta wa wanda ya tuba daga zunubansa, yake jin ƙan wanda ya yi imani da shi ya yi masa ɗa’a. Haka kuma ya umarce shi da ya faɗa wa mutane cewa, Alƙur’ani da ya zo musu da shi cike yake da shiriya da gaskiya daga Ubangijinsu mahalicci, don haka wanda ya karɓi shiriyarsa to kansa ya yi wa kyakkyawan tanadi, wanda kuwa ya bijire masa, ya doge a kan ɓata, to shi ma wannan kansa kaɗai ya cuta. Annabi (ﷺ) ba mai gadin kowa ne ba, da zai tsaya a kan mutum dole sai ya yi imani; shi ma yana bin umarni na wahayin da aka yi masa ne daga Allah; an kuma umarce shi da ya yi aiki da shi sau-da-ƙafa, ya kuma yi haƙuri a kan biyayyar Allah da jurewa a kan masu cutar da shi, har ya samu ya isar da saƙon Allah (Mai tsarki da daukaka), a ƙarshe kuma Allah zai yi hukunci a tsakaninsa da su, domin shi ne Fiyayyen masu hukunci, kuma hukuncinsa cike yake da adalci.