هود

Hud

Hud · Surah 11 · Ayahs: 123 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓرۚ كِتَٰبٌ أُحۡكِمَتۡ ءَايَٰتُهُۥ ثُمَّ فُصِّلَتۡ مِن لَّدُنۡ حَكِيمٍ خَبِيرٍ

    Open ayah 11:1

    <b>ALIF LAM RA (Wannan) Littafi ne da aka kyautata ayoyinsa sannan aka bayyana su filla-filla, daga wurin Mai hikima, Masani. </b>

  2. أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَۚ إِنَّنِي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ وَبَشِيرٞ

    Open ayah 11:2

    Da cewa kada ku bauta wa kowa sai Allah. (Ka ce): “Lalle ni mai yi muku gargaɗi ne mai albishir daga gare Shi (Allah).

  3. وَأَنِ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِ يُمَتِّعۡكُم مَّتَٰعًا حَسَنًا إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى وَيُؤۡتِ كُلَّ ذِي فَضۡلٖ فَضۡلَهُۥۖ وَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٖ كَبِيرٍ

    Open ayah 11:3

    “Kuma da cewa, ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare Shi, zai jiyar da ku daɗi, kyakkyawar jiyarwa zuwa wani lokaci ƙayyadadde, Ya kuma bai wa duk wani wanda Ya yi abin kirki (sakamakon) kirkinsa. Idan kuwa kuka ba da baya, to lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.

  4. إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

    Open ayah 11:4

    “Zuwa ga Allah ne makomarku; Shi kuwa Mai iko ne a kan komai.”

  5. أَلَآ إِنَّهُمۡ يَثۡنُونَ صُدُورَهُمۡ لِيَسۡتَخۡفُواْ مِنۡهُۚ أَلَا حِينَ يَسۡتَغۡشُونَ ثِيَابَهُمۡ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

    Open ayah 11:5

    Ku saurara! Lalle su suna karkatar da ƙirazansu don su ɓoye masa (Allah). Ku saurara! Ai lokacin da suke lulluɓa da tufafinsu Yana sane da abin da suke ɓoyewa da kuma abin da suke bayyanawa. Lalle Shi (Allah) Masanin abin da yake cikin zukata ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa, kamar yadda ya saba yi a wasu surori da suka gabace ta, domin tabbatar da mu’ujizar wannan Littafi, watau Alƙur’ani, ya kuma nuna wa Larabawa cewa su kawo wata magana kwatankwacinsa a fasaha da shiriya in har za su iya, kamar yadda wasu malamai suka bayyana. Allah ya bayyana cewa, wannan Alƙur’ani wani babban littafi ne wanda aka kyautata ayoyinsa ta fuskar fasahar zance da adalcin hukunce-hukunce, babu wata tawaya ko giɓi a cikinsa, sannan aka rarrabe bayanin da ke cikin ayoyin daki-daki, komai aka aje shi a muhallinsa, domin ya zo ne daga wurin Allah Gwani mai hikima, masanin sarari da ɓoye. Allah kuma ya bayyana wata babbar hikimar da ke cikinsa, watau ta umartar mutane su bauta wa Allah shi kaɗai ba tare da sun haɗa shi da komai ba. Don haka ya umarci Manzon Allah (ﷺ) ya bayyana wa mutane cewa, shi mai gargaɗi ne daga Allah ga masu saɓa masa game da azabarsa a duniya da lahira, kuma mai yi musu albishir da kyakkyawan sakamako idan sun bi shi sun kaɗaita shi da bauta. Sannan ya umarci Annabi da ya faɗa wa mutane cewa su nemi gafarar zunubansu a wurin Allah, su tuba su yi nadama a kan laifukan da suka yi, su kuma aikata abin da zai sa ya yarda da su; idan sun yi hakan to Allah zai jiyar da su daɗin duniya har zuwa ƙarewar ajalinsu, kuma duk waɗanda suka yi kyawawan ayyukan ɗa’a za a ba su sakamakon aikinsu cikakke babu tawaya; to amma idan suka bijire masa suka bi soye-soyen zukatansu, to ya faɗa musu cewa, yana jiye musu tsoron wata mummunar azaba a lahira da take jiran su. Kuma dukkansu makomarsu zuwa ga Allah ne ranar alƙiyama, kuma shi mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana jahilcin mushirikai da wautarsu, watau yadda suke karkata ƙirazansu wai domin su ɓoye wa Allah abin da suke ciki na shakka da tababa game da addininsa; a zatonsu Allah ba zai san halin da suke ciki ba. Amma Allah ya tabbatar musu cewa, ai ya san duk halin da suke ciki ko da lokacin da suke lulluɓe kawunansu da tufafinsu ne; yana sane da duk abin da kowa yake ɓoyewa da wanda yake bayyanawa. Hasali ma ya san duk abin da yake cikin zukatansu.

  6. ۞وَمَا مِن دَآبَّةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ رِزۡقُهَا وَيَعۡلَمُ مُسۡتَقَرَّهَا وَمُسۡتَوۡدَعَهَاۚ كُلّٞ فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 11:6

    Kuma babu wata dabba a ban ƙasa face arzikinta yana hannun Allah, kuma Yana sane da matabbatarta da ma’ajiyarta. Dukkanin wannan yana nan a cikin littafi mabayyani (shi ne Lauhul Mahafuzu).

  7. وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ وَكَانَ عَرۡشُهُۥ عَلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۗ وَلَئِن قُلۡتَ إِنَّكُم مَّبۡعُوثُونَ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡمَوۡتِ لَيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 11:7

    Shi ne kuma wanda Ya halicci sammai da ƙasa cikin kwana shida, Al’arshinsa kuwa ya kasance a kan ruwa, don Ya jarraba ku a cikinku wa ya fi kyakkyawan aiki. Kuma tabbas idan ka ce (da su): “Lalle za a tashe ku bayan mutuwa,” tabbas kafirai za su ce: “Ai wannan ba wani abu ba ne sai tsafi mabayyani.”

  8. وَلَئِنۡ أَخَّرۡنَا عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابَ إِلَىٰٓ أُمَّةٖ مَّعۡدُودَةٖ لَّيَقُولُنَّ مَا يَحۡبِسُهُۥٓۗ أَلَا يَوۡمَ يَأۡتِيهِمۡ لَيۡسَ مَصۡرُوفًا عَنۡهُمۡ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

    Open ayah 11:8

    Kuma tabbas da Mun jinkirta musu azaba zuwa wani lokaci ƙayyadadde, lalle za su ce: “Me ya tsare ta?” Ku saurara! Ranar da za ta zo musu ba za a kawar da ita daga kansu ba, kuma abin da suke yi wa izgili zai tabbata a kansu.

  9. وَلَئِنۡ أَذَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِنَّا رَحۡمَةٗ ثُمَّ نَزَعۡنَٰهَا مِنۡهُ إِنَّهُۥ لَيَـُٔوسٞ كَفُورٞ

    Open ayah 11:9

    Kuma tabbas idan Muka ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu sannan Muka karɓe ta daga gare shi, lalle shi mai yawan yanke ƙauna ne, mai kuma yawan kafirci.

  10. وَلَئِنۡ أَذَقۡنَٰهُ نَعۡمَآءَ بَعۡدَ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُ لَيَقُولَنَّ ذَهَبَ ٱلسَّيِّـَٔاتُ عَنِّيٓۚ إِنَّهُۥ لَفَرِحٞ فَخُورٌ 

    Open ayah 11:10

    Lalle kuma idan Muka ɗanɗana masa daɗi bayan ya sha wahala da ta same shi, tabbas zai riƙa cewa: “Ai munanan (abubuwa) sun bar ni.” Lalle shi mai farin ciki ne mai yawan alfahari.

  11. إِلَّا ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٞ كَبِيرٞ

    Open ayah 11:11

    Sai dai waɗanda suka yi haƙuri suka kuma yi aiki nagari, waɗannan suna da gafara da kuma lada mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana faffaɗan iliminsa wanda ya haɗe sama da ƙasa da duk abin da suka ƙunsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu wata halitta mai tafiya a bayan ƙasa, mutum ne ko dabba, ta ruwa ko ta tudu, face cinta da shanta yana hannun Allah. Ya kuma san wurin zamansu da wurin tafiye-tafiyensu da kai-kawonsu, ya san inda za su mutu a binne su; duk wannan yana nan a rubuce cikin littafin Lauhul Mahfuzu. Sai kuma ya ba da labarin cewa, shi ne ya halicci sammai da ƙasa cikin kwana shida; ya fara halitta a ranar Lahadi ya ƙare a ranar Juma’a, kuma Al’arshinsa ya kasance a kan ruwa kafin halittar sammai da ƙasa. An karɓo daga Imrana ɗan Husaini (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku Banu Tamim, albishirinku!” Sai suka ce: “Lalle ka yi mana albishir, sai ka ba mu.” Sai ya ce: “Ya ku mutanen Yaman albishirinku!” Sai suka ce: “Mun karɓi albishir, sai ka ba mu labarin farkon wannan al’amari (watau farkon halitta) yaya ya kasance?” Sai ya ce: “Tun kafin halittar komai akwai Allah, kuma Al’arshinsa ya kasance a kan ruwa, ya rubuta ambaton komai a cikin Lauhul Mahfuz.” [Bukhari #7418]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ya ƙaddara abubuwan ƙaddara na halitta tun kafin ya halicci sammai da ƙasa da shekara dubu hamsin, kuma Al’arshinsa ya kasance a kan ruwa.” [Muslim #2653]. Bayan haka sai ya ɗaukaka bisa Al’arshinsa yana gudanar da hukunce-hukuncensa na shari’a da na ƙaddara yadda ya ga dama, domin ya jarraba halittunsa ya bayyana wanda ya fi kyakkyawan aiki, watau wanda ya fi ikhlasi cikin aikinsa da koyi da sunna, ya yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa. Kuma ya bayyana yadda kafirai suke jayayya da Manzon Allah (ﷺ) a kan tashin alƙiyama; duk lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya faɗa musu cewa, lalle za a tashe su daga ƙaburburansu bayan mutuwarsu domin yi musu hisabi a gaban Allah, to sai su riƙa rantsuwa suna cewa, wannan maganar da yake karanta musu a Alƙur’ani ba wani abu ne ba face tsafi bayyananne, don haka sai su ƙaryata shi su ƙi ba da gaskiya. Sannan kuma ya bayyana wani salo da kafirai suka riƙa bi wajen ƙaryata Manzon Allah (ﷺ), shi ne idan ya faɗa musu cewa, Allah na iya saukar musu da azaba idan sun ƙi yin imani da shi. To yayin da Allah ya jinkirta musu wannan azabar sai su kafa hujja da wannan jinkirin su ce da ma Annabi ƙarya yake faɗa musu, wai in ba haka ba me ya hana azabar ta sauko musu? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, ranar da azabar za ta zo musu babu mai iya juyar da wannan ranar ta fasa zuwa, kuma abin da suke izgili da shi na azaba shi ne zai auka musu a wannan ranar. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin halin ɗan’adam yayin da Allah ya ni’imta shi da wasu ni’imomi na dukiya ko lafiya ko ‘ya’ya ko dai wani abu na jin daɗin rayuwar duniya sannan daga baya Allah ya karɓe wannan ni’imar daga hannunsa, to sai ya rikice ya zama mai ɗebe ƙauna gaba ɗaya, ya riƙa ganin babu yadda za a yi wannan ni’imar ta sake dawo masa, ya kuma zama mai yawan kafirci, ya ƙi komawa ga Allah ya nemi taimako da ƙasƙantar da kai a gabansa. Haka kuma idan Allah ya yi masa wata ni’ima bayan wata wahala da yake ciki a da, ba zai tuna cewa Allah ne ya yaye masa wahalar da yake ciki ba, ya ba shi wannan ni’imar, sai dai kawai ya riƙa cewa, wahalhalu sun rabu da shi, ba zai gode wa Allah ba sai dai ya yi ta ji-ji da kai yana fariya da cika baki da ni’imar da yake ciki. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi togaciyar masu haƙuri a kan bin Allah da barin saɓon sa, waɗanda suka yi ayyuka na ƙwarai, to waɗannan ba sa kamuwa da cutar fitar da ƙauna ko kafirce wa ni’imomin Allah ko ji-ji da kai da wulaƙanta mutane. Masu irin wannan hali Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma a ranar lahira.

  12. فَلَعَلَّكَ تَارِكُۢ بَعۡضَ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيۡكَ وَضَآئِقُۢ بِهِۦ صَدۡرُكَ أَن يَقُولُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ كَنزٌ أَوۡ جَآءَ مَعَهُۥ مَلَكٌۚ إِنَّمَآ أَنتَ نَذِيرٞۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٌ

    Open ayah 11:12

    To yanzu za ka bar wani abu daga abin da ake yi maka wahayi da shi, kuma zuciyarka za ta ƙuntata da shi don kawai za su ce: “Me ya hana a saukar masa da wata taska, ko kuma wani mala’ika ya zo tare da shi?” Kai dai mai gargaɗi ne kawai. Allah kuma Wakili ne a kan komai.

  13. أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ فَأۡتُواْ بِعَشۡرِ سُوَرٖ مِّثۡلِهِۦ مُفۡتَرَيَٰتٖ وَٱدۡعُواْ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 11:13

    A’a, ko cewa suka yi: “Ya ƙirƙire shi ne?” Ka ce: “Ku kawo sura goma kamarsa ƙagaggu, kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba (ya taimake ku) in kun kasance masu gaskiya.”

  14. فَإِلَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أُنزِلَ بِعِلۡمِ ٱللَّهِ وَأَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

    Open ayah 11:14

    To idan ba su amsa muku ba, to ku tabbatar cewa lalle an saukar da shi ne (Alƙur’ani) da sanin Allah, kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, To shin yanzu za ku miƙa wuya? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙara lallashin Manzonsa ne game da taurin kai da yake fuskanta na Ƙuraishawa da wasu maganganu na izgili da suke faɗa masa da son su ƙure shi, har suna neman ya canza Alƙur’ani ko wasu ayoyinsa, ya zo musu da abin da bai saɓa wa son zuciyarsu ba; idan ya yi haka to za su yi imani da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa wata tambaya ta kashedi da cewa, yanzu zai iya barin wani abu da Allah ya yi masa wahayin sa ya daina karanta musu shi? Kuma zuciyarsa za ta ƙuntata ne don kawai suna cewa, me ya hana a saukar masa da wata taska ta dukiya daga sama ya zama cikin manyan masu kuɗin Larabawa, ko kuma wani mala’ika ya zo yana yawo tare da shi yana gaskata shi idan yana yi musu wa’azi? Allah a nan yana hana shi ya saurare su a kan waɗannan maganganu nasu na banza, yana nuna masa cewa, shi fa kawai mai gargaɗi ne kuma Allah shi ne wakili a kan komai, shi yake tsare da ayyukansu kuma shi ne mai yi musu sakamako a kansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, maganar da mushirikai suke ta nanatawa koyaushe ita ce, wai Annabi (ﷺ) ne ya ƙirƙiri Alƙur’ani ba wahayi ne daga Allah ba. To in hakan gaskiya ne, wannan ya nuna mutane za su iya kawo kamar Alƙur’ani, to ya ƙalubalance su cewa su ma su kawo ƙirƙirarrun surori goma kamarsa, su kuma nemi duk wanda zai taimaka musu a kan haka ba Allah ba in dai har gaskiya suke faɗi cewa shi ne ya ƙirƙiro Alƙur’ani. To babu shakka ba za su iya amsa wannan ƙalubalen ba. To idan suka kasa, su muminai su san da cewa an saukar da Alƙur’ani ne da ilimin Allah wanda shi ne ya san komai da kowa, kuma ba Annabi ne ya ƙage shi ba, sannan su tabbatar da cewa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah. Anya kuwa za su miƙa wuya su ba da gaskiya bayan bayyanar waɗannan hujjoji?

  15. مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيۡهِمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ فِيهَا وَهُمۡ فِيهَا لَا يُبۡخَسُونَ

    Open ayah 11:15

    Waɗanda suke nufin rayuwar duniya da ƙawace-ƙawacenta, to za Mu ba su cikakken sakamakon ayyukansu a cikinta, kuma ba za a tauye musu (komai ba).

  16. أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَيۡسَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا ٱلنَّارُۖ وَحَبِطَ مَا صَنَعُواْ فِيهَا وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 11:16

    Waɗannan su ne waɗanda ba su da komai a lahira sai wuta; kuma abin da suka aikata a cikinta (duniyar) ya rushe, kuma abin da suke aikatawa ya lalace.

  17. أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّهِۦ وَيَتۡلُوهُ شَاهِدٞ مِّنۡهُ وَمِن قَبۡلِهِۦ كِتَٰبُ مُوسَىٰٓ إِمَامٗا وَرَحۡمَةًۚ أُوْلَٰٓئِكَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ مِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ فَٱلنَّارُ مَوۡعِدُهُۥۚ فَلَا تَكُ فِي مِرۡيَةٖ مِّنۡهُۚ إِنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 11:17

    Shin yanzu wanda yake a kan hujja daga Ubangijinsa, kuma wani mai ba da shaida yana biye da shi (Alƙur’ani); a gabaninsa kuma akwai Littafin (Annabi) Musa (wanda yake) abin koyi ne, kuma rahama ne, (zai yi daidai da wanda ba haka ba)? Waɗannan suna yin imani da shi. Daga sauran ƙungiyoyi kuma duk wanda ya kafirce da shi, to fa wuta ce makomarsa. Don haka kada ka kasance cikin kokwanto game da shi (Alƙur’ani). Lalle shi gaskiya ne daga Ubangijika yake, sai dai kuma yawancin mutane ba sa yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, duk wanda jin daɗin duniya da ƙyale-ƙyalenta yake nufi da aikinsa na ƙwarai ba gidan lahira ne a gabansa ba, to masu wannan niyyar Allah zai cika musu ladansu a nan duniya, ya ba su lafiya da zaman lafiya da dukiya, ba zai rage musu komai ba, to amma fa waɗannan a lahira ba su da wani sakamako sai wuta wadda za su shige ta su dawwama a cikinta har abada, duk wani aikin kirki da suka yi a nan duniya ya rushe, a lahira ba ya da wata ƙima, domin ba su yi shi don Allah ba, babu kuma kyakkyawar niyya tare da su. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ba ya zaluntar mumini a wani aikinsa na lada, zai ba shi sakamakonsa a duniya, kuma ya ba shi a lahira. Amma kafiri sai Allah ya ciyar da shi a duniya a dalilin kyawawan ayyukansa da ya yi don Allah, har sai ya mutu a ranar lahira zai zo ba shi da sauran wani aikin ƙwarai.” [Muslim #2808]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya bai wa Annabi Muhammadu (ﷺ) wata hujja daga gare shi, kuma Mala’ika Jibrilu, ya shaidi haka sannan littafin Attaura da Allah ya saukar wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ma yana yi masa shaida a kan gaskiyar annabcinsa, muminan da suka yi imani da shi ma sun shaida. To ta yaya za a gwada shi da sauran kafirai waɗanda suke fagamniya a cikin ɓata. Muminai su kam sun yi imani da Alƙur’anin da Annabi Muhammadu (ﷺ). Duk kuwa wanda ya kafirce wa Manzon Allah (ﷺ) daga masu bin sauran addinai, to wutar Jahannama ce makomarsa ranar alƙiyama. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, babu wani daga cikin wannan al’umma da zai samu labarina, Bayahude ne shi ko Banasare, sannan ya ƙi yin imani da ni, sai ya shiga wuta <b>.” [ </b>Muslim #153]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Manzonsa (ﷺ) kashedi kada ya ɗarsa wata shakka game da Alƙur’ani ko kuma makomar masu ƙaryata shi, domin wannan gaskiya ce da babu wani kokwanto a cikinta, sai dai kawai mutane ba sa yin imani ne duk kuwa da yawan dalilai da hujjoji gamsassu a kan haka.

  18. وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ يُعۡرَضُونَ عَلَىٰ رَبِّهِمۡ وَيَقُولُ ٱلۡأَشۡهَٰدُ هَٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ كَذَبُواْ عَلَىٰ رَبِّهِمۡۚ أَلَا لَعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 11:18

    Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya ƙirƙira wa Allah ƙarya. Waɗannan za a kawo su a gaban Ubangijinsu, shaidu kuma (wato mala’iku) su ce: “Waɗannan su ne suka yi wa Ubangijinsu ƙarya. Ku saurara, la’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai.

  19. ٱلَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجٗا وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ

    Open ayah 11:19

    “Waɗanda suke hana bin hanyar Allah, suna kuma son ta a karkace; kuma su ne masu kafircewa da ranar lahira.”

  20. أُوْلَٰٓئِكَ لَمۡ يَكُونُواْ مُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا كَانَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِنۡ أَوۡلِيَآءَۘ يُضَٰعَفُ لَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ مَا كَانُواْ يَسۡتَطِيعُونَ ٱلسَّمۡعَ وَمَا كَانُواْ يُبۡصِرُونَ 

    Open ayah 11:20

    Waɗannan ba su zamo masu gagara ba a bayan ƙasa, kuma ba su da masu jiɓintar lamarinsu waɗanda ba Allah ba, (kuma) za a ninka musu azaba. Ba su kasance sun iya jin (gaskiya) ba, ba su kuma zamanto masu iya ganin (ta) ba.

  21. أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

    Open ayah 11:21

    Waɗannan su ne waɗanda suka yi asarar kawunansu. Abin da suke ƙirƙira kuma ya ɓace musu.

  22. لَا جَرَمَ أَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ هُمُ ٱلۡأَخۡسَرُونَ

    Open ayah 11:22

    Ba shakka lalle su ne suka fi asara a lahira.

  23. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَأَخۡبَتُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

    Open ayah 11:23

    Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, suka kuma ƙasƙantar da kansu ga Ubangijinsu to waɗannan su ne ‘yan Aljanna, su masu dawwama ne a cikinta.

  24. ۞مَثَلُ ٱلۡفَرِيقَيۡنِ كَٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡأَصَمِّ وَٱلۡبَصِيرِ وَٱلسَّمِيعِۚ هَلۡ يَسۡتَوِيَانِ مَثَلًاۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

    Open ayah 11:24

    Misalin jama’ar nan guda biyu (mumini da kafiri) kamar makaho ne da kurma da kuma mai gani da mai ji. Shin ga misali za su zama daidai kuwa? To me ya sa ba za ku wa\'azantu ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai maƙaryata za su kunyata a lahira a gaban ɗaukacin halitta, kuma babu azzalumin mutum kamar wanda zai ƙagi ƙarya ya jingina wa Allah, kamar masu jingina masa ɗa ko abokin tarayya; to irin waɗannan mutane za a kawo su gaban Ubangijinsu a ranar alƙiyama domin ya yi musu tambayoyi a kan ayyukansu; to a nan ne mala’iku da manzanni masu bayar da shaida za su ce, waɗannan su ne suka ƙirƙira wa Allah ƙarya. Lalle kuma la’anar Allah, watau kora daga rahamarsa, ta tabbata ga mutane azzalumai waɗanda suka zalunci kawunansu da yi wa Allah ƙarya. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Allah zai matso da mumini kusa da shi sai ya suturta shi ya kuma ce masa: “Shin kana tuna zunubi iri kaza da zunubi iri kaza?” Shi kuma yana cewa: “E, ya Ubangijina.” Har sai ya amsa duk laifukansa, ya kuma tabbatar ya halaka, sai Allah ya ce masa: “Na rufa maka asiri a kansu a duniya, to a yau ma na gafarta maka su.” Sai a ba shi littafin kyawawan ayyukansa. To amma kafirai da munafukai sai masu shaida su ce: “Waɗannan su ne suka yi wa Ubangijinsu ƙarya, to la’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai.” [Bukhari #2441 da Muslim #2768]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin waɗannan azzalumai da cewa, su ne waɗanda suke hana mutane bin hanyar Allah miƙaƙƙiya, suke son koyaushe su gan ta a karkace domin mutane su ƙyamaci bin ta, kuma suna kafirce wa ranar lahira, domin suna ƙaryata zuwanta, to shi ne Allah yake tabbatar musu da cewa ba za su taɓa gagarar sa ba, domin a duk inda suke suna ƙarƙashin mulkinsa ne da gamammen ikonsa, don haka zai iya damƙar su tun a nan duniya kafin a je lahira, domin kuwa ba su da wasu masu taimakon su su kare su daga damƙar Ubangiji. A lahira kuwa za a riɓanya musu azaba ne, saboda bayan kafircewarsu, sun kuma karkatar da wasu daga bin hanyar Allah, domin a nan duniya sun ƙi nutsuwa su saurari gaskiyar da ake faɗa musu, sannan kuma sun ƙi yin tunani cikin ayoyin Allah da ke shimfiɗe a cikin halittunsa domin su ɗauki izina da darasi daga gare su. To waɗannan su ne suka yi asarar kawunansu, suka jefa kansu cikin halaka ta hanyar rungumar wasu gumaka a matsayin ababen tarayya da Allah. To a ranar lahira za su neme su su rasa su; za su ɓace musu ɓat, domin da man na ƙarya ne ba na gaskiya ba. Allah ya sake tabbatar musu da cewa, lalle su ne asararru a ranar alƙiyama, domin sun fifita kafirci a kan imani, sun zaɓi azaba maimakon rahama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ɗaya ɓangaren, watau muminai da cewa, waɗanda suka ba da gaskiya da Allah da shika-shikan imani, kuma suka yi kyawawan ayyuka, suka ƙasƙantar da kansu ga Allah, to waɗannan su ne ‘yan Aljanna masu dawwama a cikinta har abada. Sannan Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da misalin ƙungiyar kafirai da jama’ar Musulmi, inda ya kwatanta su da makahon da yake dinɗim ba ya ganin komai ko kurman da ba ya ji kwata-kwata, ya kuma kwatanta Musulmi da mutumin da yake gani tar kuma yake ji sarai, shin waɗannan jama’u biyu na kafirai da muminai za su taɓa zama daidai? Babu shakka duk mai hankali ya san ba za su daidaita ba. To me ya sa kafirai ba sa wa’azantuwa ne su fahimci bambancin da ke tsakanin imani da kafirci ko mumini da kafiri?

  25. وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦٓ إِنِّي لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٌ

    Open ayah 11:25

    Haƙiƙa kuma Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa (ya ce da su): “Lalle ni mai gargaɗi bayyananne ne a gare ku.

  26. أَن لَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَۖ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ أَلِيمٖ

    Open ayah 11:26

    “Cewa kada ku bauta wa (kowa) sai Allah. Lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wata rana mai raɗaɗi.”

  27. فَقَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ مَا نَرَىٰكَ إِلَّا بَشَرٗا مِّثۡلَنَا وَمَا نَرَىٰكَ ٱتَّبَعَكَ إِلَّا ٱلَّذِينَ هُمۡ أَرَاذِلُنَا بَادِيَ ٱلرَّأۡيِ وَمَا نَرَىٰ لَكُمۡ عَلَيۡنَا مِن فَضۡلِۭ بَلۡ نَظُنُّكُمۡ كَٰذِبِينَ

    Open ayah 11:27

    Sai manya-manya daga cikin mutanensa, waɗanda suka kafirta suka ce (da shi): “Mu fa mun ɗauke ka kawai mutum ne kamarmu, kuma ba ma ganin wani ya bi ka in ban da wulakantattun cikinmu gidadawa. Kuma ba ma ganin ku da wani fifiko a kanmu; kai muna ma tsammanin ku maƙaryata ne.” A waɗannan ayoyi da masu zuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana labarta wa Annabinsa (ﷺ) tarihin Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda shi ne farkon manzo da Allah ya aiko duniya, tare da sauran annabawa don ya lallashe shi ya kwantar masa da hankali game da ƙaryatawar da mutanensa Ƙuraishawa suke yi masa da izgili da tsangwamar sa shi da mabiyansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya aiko Manzonsa Annabi Nuhu zuwa ga mutanensa, waɗanda su ne suka fara bautar gumaka bayan Tauhidi da annabawan da suka riga Annabi Nuhu suka karantar. Babban jigon da’awar Annabi Nuhu shi ne bautar Allah shi kaɗai ba tare da haɗa shi da komai ba, ya nuna musu cewa, idan sun ƙi ba da gaskiya da shi sun ƙi yin watsi da bautar gumakansu, to yana jiye musu tsoron wata azaba mai raɗaɗi da za ta same su daga Allah. To amma maimakon mutanensa su saurare shi su fahimci gaskiyar da yake faɗa musu, sai kawai manyansu masu faɗa a ji suka ƙaryata shi tare da bayyana wasu hujjoji na ƙaryata shi da cewa: (a) Shi mutum ne kamarsu, babu wani dalilin da zai sa su bi wani mutum irin jinsinsu. (b) Mabiyansa wai duk wasu ƙasƙantattun mutane ne marasa galihu cikin jama’a, kuma ga su gidadawa waɗanda ba su yi aiki da tunaninsu ba wajen yarda da shi, kawai sun miƙa masa wuya ne ba tare da wata hujja ba. (c) Su ba su ga wani abu da Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mabiyansa suka fi su da shi ba har da Allah zai fifita su a kansu; su dai ba ƙarfi suka fi su ba, ba yawan dukiya ko ilimi ko ‘ya’ya ba; ba su fi su usuli ba, to saboda me za su yarda su yi imani da irin waɗannan mutane? (d) Su sun fi tsammanin cewa Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da jama’arsa kawai maƙaryata ne babu gaskiya tare da su, don haka me zai sa su yarda da maƙaryata haka kawai? Waɗannan su ne hujjojin bogi da manyan gari suka taka don ƙaryata Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).

  28. قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَءَاتَىٰنِي رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِهِۦ فَعُمِّيَتۡ عَلَيۡكُمۡ أَنُلۡزِمُكُمُوهَا وَأَنتُمۡ لَهَا كَٰرِهُونَ

    Open ayah 11:28

    (Annabi Nuhu) ya ce: “Ya ku mutanena, ku ba ni labari, yanzu idan na zamanto ina riƙe da hujja daga Ubangijina, Ya kuma ba ni wata rahama daga gare Shi, sai aka ɓoye muku ita, yanzu ma tilasta muku ita, alhali kuwa kuna ƙin ta?

  29. وَيَٰقَوۡمِ لَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مَالًاۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۚ وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْۚ إِنَّهُم مُّلَٰقُواْ رَبِّهِمۡ وَلَٰكِنِّيٓ أَرَىٰكُمۡ قَوۡمٗا تَجۡهَلُونَ

    Open ayah 11:29

    “Kuma ya ku mutanena, ba na tambayar ku wata dukiya a kansa (kiran); ladana a wurin Allah kawai yake. Ni kuwa ba zan kori waɗanda suka yi imani ba. Lalle su masu saduwa ne da Ubangijinsu, sai dai ni ina ganin ku mutane ne da kuke jahiltar (gaskiya).”

  30. وَيَٰقَوۡمِ مَن يَنصُرُنِي مِنَ ٱللَّهِ إِن طَرَدتُّهُمۡۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ 

    Open ayah 11:30

    “Ya ku mutanena, wa zai kare ni daga Allah idan na kore su? Me ya sa ne ba kwa wa’azantuwa?

  31. وَلَآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ وَلَآ أَقُولُ إِنِّي مَلَكٞ وَلَآ أَقُولُ لِلَّذِينَ تَزۡدَرِيٓ أَعۡيُنُكُمۡ لَن يُؤۡتِيَهُمُ ٱللَّهُ خَيۡرًاۖ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا فِيٓ أَنفُسِهِمۡ إِنِّيٓ إِذٗا لَّمِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 11:31

    “Ba kuma zan ce da ku ina da taskokin Allah ba, ban kuma san gaibu ba, kuma ba zan ce lalle ni mala’ika ne ba, ba kuma zan ce wa waɗanda idanuwanku suke wulaƙantawa, Allah ba zai ba su wani alheri ba. Allah ne Ya fi sanin abin da yake zukatansu. Idan na yi haka, to lalle na zamanto daga cikin azzalumai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana amsar da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ba wa mutanensa ne da cewa, su faɗa masa, idan har shi yana kan wata hujja daga Ubangijinsa wadda ta tabbatar da cewa annabcinsa daga gare shi ne, ba shi ne ya naɗa kansa ba, watau Allah ne ya so shi da wannan rahamar ta annabta, amma su suka kasa ganin ta saboda jahilcinsu da ruɗuwarsu da duniya, don haka suka ƙi yin imani da shi, ya ce to zai tilasta musu ne sai dole sun yi imani ko da ba sa so? Ba zai iya yi musu dole ba, domin imani dace ne daga Allah ga wanda ya ga dama. Sannan ya bayyana musu cewa, maganar ba ta dukiya ce ba, domin shi kansa da yake tallata musu kiransa, ba nema yake su biya shi wata dukiya ba; shi ladansa yana wurin Allah ne, yana neman su da shiriya ne kawai. Sannan waɗannan talakawan da suke sukan su da cewa gidadawa ne marasa tunani, shi ba zai iya korar su daga majalisarsa ba, domin kuwa sun yi imani, sun kuma san cewa za su koma ga Allah ne ranar alƙiyama inda za a tantance tsakaninsu da su, su wane ne suka fi daraja a wurin Allah. Daga ƙarshe Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) dai ya fahimci cewa mutanensa ba su gama gane haƙiƙanin da’awarsa ba, shi ya sa har suke neman ya kori talakawan da suka yi imani da shi. Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sake kiran mutanensa ya jaddada musu cewa, idan har ya amince ya kori waɗannan matalauta kamar yadda manyan gari suka neme shi bisa zalunci, to wane ne a cikinsu zai kare shi a gaban Allah idan ya yi nufin azabtar da shi? Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nuna musu cewa, yanzu me ya sa ne ba za su wa’azantu ba, su yi tunani su fahimci korar su ba alheri ba ne gare shi har da su ma gaba ɗaya? Idan su matalauta ne, to ai shi ma mai buƙata ne a wurin Allah, don haka ya kore wa kansa abubuwa huɗu: (a) Taskokin Allah ba a hannunsa suke ba, ballantana ya ba wa wasu ya hana wasu. Allah ya aiko shi ne ya tsarkake musu zukata ba ya raba musu arzuki ba. (b) Ya tabbatar musu cewa, shi fa bai san gaibu ba, Allah ne kaɗai ya keɓanta da sanin gaibu, sai dai abin da ya ga dama ya sanar da wanda ya ga dama cikin manzanninsa. (c) Bai taɓa faɗa musu cewa shi mala’ika ne ba; shi mutum ne kamarsu, a gabansu aka haife shi, sun san shi sun kuma san iyayensa. (d) Ya tabbatar musu cewa, ba zai taɓa cewa mutanen da suke yi wa kallon wulaƙanci, Allah ba zai taɓa ba su wani alheri ba, watau ya shiryar da su su fahimci gaskiya, Allah kuma shi ya fi sanin niyyoyinsu. Ya ce, idan har ya kuskura ya yi da’awar waɗannan abubuwa, to lalle ya zama azzalumi wanda ya cancanci azabar Allah.

  32. قَالُواْ يَٰنُوحُ قَدۡ جَٰدَلۡتَنَا فَأَكۡثَرۡتَ جِدَٰلَنَا فَأۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

    Open ayah 11:32

    Suka ce: “Ya Nuhu, haƙiƙa ka ja da mu, ka kuma yawaita jayayya da mu; to sai ka zo mana da abin da kake yi mana alƙawari da shi (na narko) in ka zamo daga masu gaskiya.”

  33. قَالَ إِنَّمَا يَأۡتِيكُم بِهِ ٱللَّهُ إِن شَآءَ وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ

    Open ayah 11:33

    Ya ce: “Ai Allah ne zai zo muku da shi idan Ya ga dama, ku kuma ba za ku gagara ba.

  34. وَلَا يَنفَعُكُمۡ نُصۡحِيٓ إِنۡ أَرَدتُّ أَنۡ أَنصَحَ لَكُمۡ إِن كَانَ ٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يُغۡوِيَكُمۡۚ هُوَ رَبُّكُمۡ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

    Open ayah 11:34

    “Nasihata kuma ba za ta amfane ku ba - ko da na yi nufin yi muku nasihar - idan har da ma can Allah Yana nufin Ya ɓatar da ku. Shi ne Ubangijinku, kuma wurinsa za ku koma.”

  35. أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ إِنِ ٱفۡتَرَيۡتُهُۥ فَعَلَيَّ إِجۡرَامِي وَأَنَا۠ بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُجۡرِمُونَ

    Open ayah 11:35

    A’a, ko dai cewa suke: “Ƙagar sa ya yi?” (wato Alƙur’ani) Ka ce: “Idan ƙagar sa na yi, to alhakin ƙagena yana kaina ne, ni kuma ba ruwana da laifin abin da kuke tabkawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da bayanin ƙissar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa, bayan duk irin hujjoji da ya kawo musu domin ya shawo kansu su ba da gaskiya, sai ƙara zaƙewa suke yi cikin tsaurin kai, suka kira wa’azin da yake musu da sunan ‘jayayya’ suka ma nemi ya sa a saukar musu da azabar da yake cewa yana jiye musu tsoron ta, idan har ya tabbata shi mai gaskiya ne. Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana musu cewa, ai azabar ba a hannunsa take ba, ballantana ya saukar musu da ita kamar yadda suka nema; Allah ne idan ya ga dama sai ya saukar musu da ita a lokacin da ya ga dama, kuma ba za su gagare shi ba ko su kuɓuce masa. Amma shi Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) aikinsa shi ne ya yi musu nasiha ya faɗa musu gaskiya, to amma ya san nasiharsa kaɗai ba za ta amfane su har su gane halakar da suke ciki ba, matuƙar Allah yana nufin ya ɓatar da su, saboda sun nuna sun fi son ɓatan a kan shiriya, domin shi ne Ubangijinsu komai nasu yana wurinsa, kuma wurinsa kaɗai za su koma don ya yi musu hisabi a kan ayyukansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya juyo da akalar magana zuwa ga mushirikan Ƙuraishawa waɗanda idan sun ji Annabi (ﷺ) yana karanta musu irin waɗannan ƙissoshin masu ɗauke da bayanin halayen kafiran farko waɗanda suka yi kama da nasu, sai su ce Manzon Allah (ﷺ) ne yake ƙagar irin waɗannan ƙissoshin. Shi ne a nan Allah yake cewa, ko suna ganin Annabi ne ya ƙagi wannan labarin da yake faɗa musu? To Manzon Allah ya mayar musu da martani cewa, idan shi ne ma ya ƙage su, to ai shi kaɗai zai ɗauki alhakin yi wa Allah ƙarya ba su ba, domin wani rai ba ya ɗaukar laifin wani, kuma shi ma ya faɗa musu cewa ba ruwansa da laifin da suke tabkawa.

  36. وَأُوحِيَ إِلَىٰ نُوحٍ أَنَّهُۥ لَن يُؤۡمِنَ مِن قَوۡمِكَ إِلَّا مَن قَدۡ ءَامَنَ فَلَا تَبۡتَئِسۡ بِمَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ

    Open ayah 11:36

    Aka kuma yi wa Nuhu wahayi cewa: “Ba wanda zai yi imani daga mutanenka sai waɗanda suka riga suka yi. To kada ka yi baƙin ciki game da abin da suke aikatawa.

  37. وَٱصۡنَعِ ٱلۡفُلۡكَ بِأَعۡيُنِنَا وَوَحۡيِنَا وَلَا تُخَٰطِبۡنِي فِي ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِنَّهُم مُّغۡرَقُونَ

    Open ayah 11:37

    “Ka kuma sassaƙa jirgin ruwa a kan idanunmu da koyarwarmu. Kada kuma ka yi Mini maganar komai game da kafirai. Lalle su nutsar da su za a yi.”

  38. وَيَصۡنَعُ ٱلۡفُلۡكَ وَكُلَّمَا مَرَّ عَلَيۡهِ مَلَأٞ مِّن قَوۡمِهِۦ سَخِرُواْ مِنۡهُۚ قَالَ إِن تَسۡخَرُواْ مِنَّا فَإِنَّا نَسۡخَرُ مِنكُمۡ كَمَا تَسۡخَرُونَ

    Open ayah 11:38

    Ya kuma riƙa sassaƙa jirgin, duk sanda kuma wasu manya daga mutanensa suka wuce ta wajensa sai su riƙa yi masa ba’a. Ya ce: “Idan kun yi mana ba’a, to lalle mu ma fa (wata rana) za mu yi muku ba’ar kamar yadda kuke mana (yanzu).

  39. فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن يَأۡتِيهِ عَذَابٞ يُخۡزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيۡهِ عَذَابٞ مُّقِيمٌ

    Open ayah 11:39

    “To ba da daɗewa ba za ku san wanda azaba mai kunyatarwa za ta zo masa, kuma wata azaba madawwamiya ta sauka a kansa.”

  40. حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ قُلۡنَا ٱحۡمِلۡ فِيهَا مِن كُلّٖ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ وَمَنۡ ءَامَنَۚ وَمَآ ءَامَنَ مَعَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلٞ 

    Open ayah 11:40

    Har dai zuwa lokacin da umarninmu ya zo, kuma tanderu ya ɓuɓɓugo da ruwa, Muka ce: “Ka ɗauki ma’aurata bibbiyu daga kowace (halitta) a cikinsa (jirgin) haɗe da iyalanka in ban da wanda maganar (halakar da shi) ta gabata a kansa, kuma (ka ɗauki) waɗanda suka yi imani.” Ba kuwa waɗanda suka yi imani da shi sai ‘yan tsirari.

  41. ۞وَقَالَ ٱرۡكَبُواْ فِيهَا بِسۡمِ ٱللَّهِ مَجۡر۪ىٰهَا وَمُرۡسَىٰهَآۚ إِنَّ رَبِّي لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 11:41

    Ya kuma ce: “Ku shiga cikinsa, da sunan Allah ne tafiyarsa da kuma tsayawarsa. Lalle Ubangijina Mai gafara ne, Mai rahama.”

  42. وَهِيَ تَجۡرِي بِهِمۡ فِي مَوۡجٖ كَٱلۡجِبَالِ وَنَادَىٰ نُوحٌ ٱبۡنَهُۥ وَكَانَ فِي مَعۡزِلٖ يَٰبُنَيَّ ٱرۡكَب مَّعَنَا وَلَا تَكُن مَّعَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 11:42

    Shi kuma (jirgin) yana tafiya da su cikin raƙuman ruwa kamar duwatsu, Nuhu kuwa sai ya kirawo ɗansa alhalin ya kasance a ware waje ɗaya (ya ce): “Kai ɗana, ka hawo mana tare da mu, kada ka zama tare da kafirai.”

  43. قَالَ سَـَٔاوِيٓ إِلَىٰ جَبَلٖ يَعۡصِمُنِي مِنَ ٱلۡمَآءِۚ قَالَ لَا عَاصِمَ ٱلۡيَوۡمَ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِ إِلَّا مَن رَّحِمَۚ وَحَالَ بَيۡنَهُمَا ٱلۡمَوۡجُ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُغۡرَقِينَ

    Open ayah 11:43

    (Ɗan) ya ce: “Ai zan fake a wani dutse wanda zai kare ni daga ruwan.” (Annabi Nuhu) ya ce: “Yau kam babu mai kariya daga al’amarin Allah sai dai wanda Ya yi wa rahama kawai.” Sai raƙumin ruwa ya shiga tsakaninsu, ya zamanto cikin waɗanda aka nutsar (a cikin ruwa).

  44. وَقِيلَ يَٰٓأَرۡضُ ٱبۡلَعِي مَآءَكِ وَيَٰسَمَآءُ أَقۡلِعِي وَغِيضَ ٱلۡمَآءُ وَقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ وَٱسۡتَوَتۡ عَلَى ٱلۡجُودِيِّۖ وَقِيلَ بُعۡدٗا لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 11:44

    Aka ce: “Ke ƙasa, ki haɗiye ruwanki, ke kuma sama ki riƙe ruwanki, aka kuwa ƙafar da ruwan, kuma aka gama al’amarin, (jirgin) kuma ya tsaya a kan (dutsen) Judi ; aka kuma ce: Halaka ta tabbata ga mutane azzalumai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen yi wa mutanensa nasiha, to amma sun ci gaba da yi masa taurin kai da izgili; kaɗan ne ƙwarai suka yi imani, Allah kuma ya sanar da shi cewa, bayan waɗannan ‘yan kaɗan da suka yi imani da shi babu sauran waɗanda za su ƙara yin imani nan gaba, don haka kada ya yi baƙin ciki da abin da suke aikatawa, domin babu abin da ya rage musu sai lokacin saukar azabar Allah a kansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya sassaƙa jirgin ruwa ƙarƙashin kulawarsa da koyarwarsa, ya kuma umarce shi da kada ya kuskura ya nema wa kafirai wani jinkirin azaba domin Allah ya riga ya yanke musu hukuncin nutsarwa a cikin ruwan Ɗufana. To Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya amsa umarnin Allah, ya fara sassaƙa jirgin ruwa, amma kuma mutanensa ba su ƙyale shi ba. Duk sa’adda manyansu suka wuce ta wajensa suka gan shi yana sassaƙar jirgin, sai su riƙa yi masa izgili suna tsokanar sa, har ma suna ganin ya zautu ne, domin me ya kai shi ga sassaƙa jirgin ruwa a garin da ba su da kogi ko ƙoramar da za a shiga da jirgi? Da abin ya ci gaba ba ƙaƙƙautawa sai ya faɗa musu cewa, idan yau suna yi masa izgilin wannan aikin da yake yi na sassaƙa, to ba da jimawa ba shi ma tare da jama’arsa za su yi musu izgili sakamakon abin da zai faru gare su. Kuma idan yau ba su gane dalilin sassaƙawar ba, to nan gaba za su ga wane ne wanda azaba za ta auka masa a nan duniya ta wulaƙanta shi ya kunyata, sannan kuma a lahira ya gamu da wata azaba marar yankewa. Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kammala sassaƙa jirgin ruwa, daga nan sai umarnin Allah ya zo na halakar su, sai kuma ruwa ya fara ɓuɓɓugowa da ƙarfi daga tanderun da suke gasa gurasa, daga nan ruwan Ɗufana ya ɓarke ya fara ambaliya, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya ɗauki aure biyu-biyu daga kowane jinsi na halittu masu rai tare da iyalansa a cikin wannan jirgi, in ban da wanda maganar halakarwa ta tabbata a kansa cewa ruwa zai cinye shi, watau ɗansa da matarsa, ya kuma ɗauki duk wanda ya yi imani da shi daga cikin mutanensa, waɗanda ‘yan kaɗan ne suka yi imani da shi duk tsawon lokacin da ya share a cikinsu yana yi musu wa’azi, watau shekara ɗari tara da hamsin. Sai ya umarci iyalansa da waɗanda suka yi imani daga cikin mutanensa da su hau wannan jirgin, da sunan Allah ne zai gudana a kan ruwa, kuma da sunansa ne zai tsaya. Lalle Allah Ubangijin Annabi Nuhu, mai gafara ne ga bayinsa da suka tuba, kuma mai jin ƙai ne gare su, don haka ne ma ya hore musu abin hawa da suka kuɓuta da shi daga halaka tare da sauran jinsunan halittu daban-daban. To yayin da jirgin ruwan yake tsakiyar tafiya da waɗanda ke cikinsa a tsakiyar raƙuman ruwa masu kamar duwatsu, sai tausayi na uba ya kama Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya kirawo ɗansa kafiri, wanda yake a ware waje guda ya ƙi bin babansa Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa da suka yi imani da shi. Nuhu ya ce masa: “Ya kai ɗan ɗana, zo ka hau jirgin ruwa tare da mu don kai ma ka tsira daga nutsewa cikin ruwa, kada ka zamo cikin kafirai waɗanda ruwa zai halaka su, sai ku halaka tare.” Sai kawai ɗan ya ce masa, ai shi zai fake ne a ƙololuwar dutse inda ruwa ba zai kai gare shi ba. Sai Annabi Nuhu ya ce masa, a yau fa babu wani mai bayar da kariya daga azabar Allah sai wanda Allah ya yi wa rahamarsa kawai. Suna cikin haka sai kawai raƙumin ruwa ya shiga tsakaninsu, nan take kuma ɗan nasa ya tabbata cikin waɗanda ruwa ya cinye saboda kafircinsa. Daga ƙarshe sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci ƙasa ta tsotse ruwanta ita ma sama ya umarce ta da ta riƙe ruwanta ya daina zubowa. Ruwa ya yi ta ja da baya har ya ƙafe, ƙasa ta bushe, Allah ya halaka kafirai, jirgin ruwan nan kuma ya tsaya a kan dutsen Judi , aka kuma ce wa waɗannan halakakkun kafiran, nisan rahama da halaka sun tabbata ga mutane kafirai masu ƙetare iyakokin Allah.

  45. وَنَادَىٰ نُوحٞ رَّبَّهُۥ فَقَالَ رَبِّ إِنَّ ٱبۡنِي مِنۡ أَهۡلِي وَإِنَّ وَعۡدَكَ ٱلۡحَقُّ وَأَنتَ أَحۡكَمُ ٱلۡحَٰكِمِينَ

    Open ayah 11:45

    Nuhu kuma ya kira Ubangijinsa sai ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ɗana yana daga iyalina, lalle kuma alƙawarinka gaskiya ne, kuma Kai ne Ka fi masu hukunci iya hukunci.”

  46. قَالَ يَٰنُوحُ إِنَّهُۥ لَيۡسَ مِنۡ أَهۡلِكَۖ إِنَّهُۥ عَمَلٌ غَيۡرُ صَٰلِحٖۖ فَلَا تَسۡـَٔلۡنِ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۖ إِنِّيٓ أَعِظُكَ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ

    Open ayah 11:46

    (Allah) Ya ce: Ya Nuhu, lalle shi ba ya daga cikin iyalinka, lalle shi aiki ne marar kyau; to kada ka ƙara tambaya Ta abin da ba ka da sani a kansa; lalle Ni Ina gargaɗin ka da kada ka zamanto cikin jahilai.

  47. قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَعُوذُ بِكَ أَنۡ أَسۡـَٔلَكَ مَا لَيۡسَ لِي بِهِۦ عِلۡمٞۖ وَإِلَّا تَغۡفِرۡ لِي وَتَرۡحَمۡنِيٓ أَكُن مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

    Open ayah 11:47

    Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni ina neman tsarinka a kan in tambaye Ka abin da ba ni da sani a kansa, idan kuwa ba Ka yafe mini ba, Ka kuma ji ƙai na, to zan zamo cikin asararru.”

  48. قِيلَ يَٰنُوحُ ٱهۡبِطۡ بِسَلَٰمٖ مِّنَّا وَبَرَكَٰتٍ عَلَيۡكَ وَعَلَىٰٓ أُمَمٖ مِّمَّن مَّعَكَۚ وَأُمَمٞ سَنُمَتِّعُهُمۡ ثُمَّ يَمَسُّهُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 11:48

    Aka ce: Ya Nuhu, ka sauka cikin aminci daga gare Mu da albarka a gare ka da kuma ga al’ummun da suke tare da kai. Wasu al’ummun kuma za Mu jiyar da su daɗi, sannan kuma azaba mai raɗaɗi daga gare Mu ta same su.

  49. تِلۡكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهَآ إِلَيۡكَۖ مَا كُنتَ تَعۡلَمُهَآ أَنتَ وَلَا قَوۡمُكَ مِن قَبۡلِ هَٰذَاۖ فَٱصۡبِرۡۖ إِنَّ ٱلۡعَٰقِبَةَ لِلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 11:49

    Waɗannan suna daga labaran gaibu da muke yi maka wahayinsu, don kai da mutanenka ba ku san su ba kafin wannan (labarin); sai ka yi haƙuri; haƙiƙa kyakkyawan ƙarshe yana ga masu taƙawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana cewa, Annabi Nuhu ya kira Ubangijinsa yana gaya masa cewa, ɗansa mai halaka, shi ma yana cikin iyalansa, ga shi kuma ya yi masa alƙawarin tserar masa da iyalansa, kuma alƙawarin Allah gaskiya ne ba ya saɓawa, ya kuma fi kowa yin hukunci na adalci. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar masa da martani cewa, wannan yaron ba ya cikin iyalansa, dalili kuwa shi ba mutumin ƙwarai ne ba domin kafiri ne, shi kuma Allah ya yi masa alƙawarin tserar da muminai ne kaɗai, don haka wannan roƙon ma da Annabi Nuhu ya yi bai dace ba, don haka Allah ya gargaɗe shi da kada ya sake roƙon abin da ba ya da wani ilimi a kansa, kada ya kuskura ya zama daga cikin jahilai waɗanda ba su san mene ne ya kamata su roƙa, mene ne kuma bai kamata su roƙa ba. Daga nan sai jikin Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi sanyi ya dawo yana neman tsari da Allah a kan kada ya sake roƙon sa abin da ba shi da wani ilimi a kansa, kuma ya tabbatar da cewa idan har Allah bai gafarta masa wannan kuskuren da ya yi ba, ya kuma ji ƙan sa da rahamarsa, to zai zamanto cikin waɗanda suka yi asarar rabonsu na lahira. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce da Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sauka daga jirgin ruwan cikin aminci da kwanciyar hankali da kuma ni’imomi masu yawa gare shi da kuma al\'ummun da suke tare da shi, don su ci gaba da hayayyafa a bayan ƙasa har a samu wasu al\'ummun da za su zo su sami ababen more rayuwa iri-iri. To amma kuma wasu daga cikinsu za su kafirce wa Allah su kuma butulce wa ni’imominsa, sai Allah ya ƙyale su su ɗan ji daɗi kaɗan a rayuwarsu ta duniya, amma in sun mutu za su haɗu da azabar Allah mai tsanani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, wannan labari da ya ba shi na Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana daga cikin labaran gaibu ne, wanda shi Annabi (ﷺ) da mutanensa duk ba su san shi ba, saboda Annabi (ﷺ) tun kafin ma a aiko shi mutum ne ummiyyi ba ya rubutu ba ya karanta rubutu, ballantana a zarge shi da ya karanto ne a littafan Yahudu da Nasara. Hakanan su ma mutanensa Ƙuraishawa ummiyai ne ba su iya rubutu da karatu ba, kuma ba su da wata alaƙa da ma’abota littafi ballantana su sanar da su wani labari irin wannan. To amma ga shi yanzu Allah ya yi masa wahayin sa, don haka ya umarce shi da ya yi haƙuri a kan ƙaryata shi da cutarwar da mutanensa suke yi masa, kamar yadda Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi haƙuri. Lalle kuma nasara da galaba suna tare da masu kiyaye dokokin Allah, masu aikata abin da ya umarce su, su kuma bar abin da ya hane su.

  50. وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمۡ هُودٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۖ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا مُفۡتَرُونَ 

    Open ayah 11:50

    Kuma (Mun aiko wa) Adawa ɗan’uwansu Hudu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta da gaskiya sai shi; ku ba wasu ne ba face masu ƙaga wa (Allah) ƙarya.

  51. يَٰقَوۡمِ لَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًاۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱلَّذِي فَطَرَنِيٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

    Open ayah 11:51

    “Ya ku mutanena, ba na tambayar ku wani lada game da shi (wannan saƙo); ladana dai yana ga wanda ya ƙagi halittata. Yanzu ba za ku hankalta ba?

  52. وَيَٰقَوۡمِ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِ يُرۡسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡكُم مِّدۡرَارٗا وَيَزِدۡكُمۡ قُوَّةً إِلَىٰ قُوَّتِكُمۡ وَلَا تَتَوَلَّوۡاْ مُجۡرِمِينَ

    Open ayah 11:52

    “Kuma ya ku mutanena, ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare Shi, zai sauko muku da mamakon ruwan sama, zai kuma ƙara muku ƙarfi a kan ƙarfinku, kada kuma ku ba da baya kuna masu aikata laifi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin Annabi Hudu ne, wanda ya aika shi zuwa ga Adawa. (Bayanin ƙabilun Adawa ya gabata cikin Suratul A’arafi aya ta 65). Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kirawo mutanensa zuwa ga bautar Allah shi kaɗai ba tare da haɗa shi da komai ba, ya nuna musu cewa, iƙirarinsu na cewa akwai wani abin bauta wa ban da Allah ƙarya ce kawai suke yi. Ya tabbatar musu cewa, ba ya buƙatar wani abu daga dukiyarsu a kan wannan wa’azi da yake yi musu, ladansa yana wajen Allah ne shi kaɗai, don haka me zai hana su hankalta da abin da yake faɗa musu su yi imani da shi? Sannan ya neme su da su roƙi Allah gafara su kuma tuba su daina aikata zunubbai, musamman yin shirka da Allah, idan suka yi haka zai saka musu ta hanyar saukar musu da mamakon ruwan sama, wanda zai ba su damar samun amfanin gona mai yawa, kuma ya ƙara musu ƙarfi da ɗaukaka a kan wanda suke da shi, ya yalwata musu ‘ya’yansu da dukiyoyinsu. Ya kuma gargaɗe su da kada su kuskura su bijire wa kiransa sai su zama masu aikata manyan laifuka.

  53. قَالُواْ يَٰهُودُ مَا جِئۡتَنَا بِبَيِّنَةٖ وَمَا نَحۡنُ بِتَارِكِيٓ ءَالِهَتِنَا عَن قَوۡلِكَ وَمَا نَحۡنُ لَكَ بِمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 11:53

    Suka ce: “Ya kai Hudu ba ka zo mana da wata hujja ba, kuma ba za mu bar abubuwan da muke bauta ba saboda maganarka, ba kuma za mu yi imani da kai ba.

  54. إِن نَّقُولُ إِلَّا ٱعۡتَرَىٰكَ بَعۡضُ ءَالِهَتِنَا بِسُوٓءٖۗ قَالَ إِنِّيٓ أُشۡهِدُ ٱللَّهَ وَٱشۡهَدُوٓاْ أَنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ

    Open ayah 11:54

    “Ba abin da za mu faɗa sai dai kawai (mu ce) wasu abubuwan bautarmu ne suka sa maka taɓuwa.” Ya ce: “Ni lalle ina shaidar da Allah, ku ma kuma ku shaida cewa ni lalle ba ruwana da abin da kuke haɗa (Allah) da shi.

  55. مِن دُونِهِۦۖ فَكِيدُونِي جَمِيعٗا ثُمَّ لَا تُنظِرُونِ

    Open ayah 11:55

    “Wanda ba Shi (Allah) ba; to sai ku shirya min makirci gaba ɗayanku, kar kuma ku saurara mini.

  56. إِنِّي تَوَكَّلۡتُ عَلَى ٱللَّهِ رَبِّي وَرَبِّكُمۚ مَّا مِن دَآبَّةٍ إِلَّا هُوَ ءَاخِذُۢ بِنَاصِيَتِهَآۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

    Open ayah 11:56

    “Lalle ni na dogara ga Allah, Ubangijina kuma Ubangijinku. Babu wata dabba face Shi ne Yake riƙe da makwarkwaɗarta. Lalle Ubangijina a kan tafarki madaidaici Yake.

  57. فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقَدۡ أَبۡلَغۡتُكُم مَّآ أُرۡسِلۡتُ بِهِۦٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَيَسۡتَخۡلِفُ رَبِّي قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ وَلَا تَضُرُّونَهُۥ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَفِيظٞ

    Open ayah 11:57

    “To idan kuka ba da baya, haƙiƙa na isar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijina zai iya musanya wasu mutanen ba ku ba, kuma ba za ku cutar da Shi da komai ba. Lalle Ubangijina Mai kula da komai ne.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana irin mummunan martani da mutanen Annabi Hudu suka mayar masa bayan ya kirawo su da tattausar murya tare da jan hankalinsu zuwa ga bautar Allah shi kaɗai da guje wa shirka. Wasu kausasan maganganu uku suka gaya masa: <b>Na farko </b>: Suka ce wai bai kawo musu wata hujja ba a kan da’awarsa ta manzanci. <b>Na biyu </b>: Suka nuna masa cewa, sam-sam ba za su taɓa barin bautar gumakansu ba saboda wa’azinsa. Wannan yana nuna sun riga sun ɗauki matsayi na kafewa a kan shirkarsu, ba suna neman gaskiya ba ne. <b>Na uku </b>: Suka tabbatar masa cewa ba za su taɓa yin imani da shi ba. Wannan yana ƙara nuna kafewarsu a kan kafirci. Bugu da ƙari kuma suka ci gaba da tuhumar sa da taɓin hankali, suna ganin wai wasu gumakansu ne suka yi fushi da shi har suka haukatar da shi saboda yana sukan su da aibata su da hana a bauta musu. To amma sai Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sake tausasa harshensa wajen ba su amsar waɗannan maganganun, yana cewa, shi kam ya sanya Allah a matsayin mai yi masa shaida, su ma su shaida cewa ya nisanta kansa daga bautar abin da suke bauta wa ba Allah ba. Sannan ya ƙalubalance su da, su shirya masa makirci gaba ɗayansu, kada kuma su saurara masa. Ya tabbatar musu da cewa, shi kam da Allah kaɗai ya dogara ba da wani ba, shi ne Ubangijinsa mai gudanar da lamuran rayuwarsa kuma shi ne Ubangijinsu, babu wani abu mai tafiya a kan ƙasa face yana ƙarƙashin mulkin Allah ne, shi yake riƙe da makwarkwaɗarsa yana sarrafa shi yadda ya ga dama. Don haka Ubangijinsa yana kan hanya miƙaƙƙiya, wadda take cike da adalci, don haka ba zai taɓa ba su damar cutar da shi ba, domin shi ne a kan gaskiya su kuma a kan ɓata. Sannan ya nuna musu cewa, idan suka bijire wa kiransa, to fa shi tabbas ya isar musu da saƙon da aka aiko shi da shi, don haka hujja ta tabbata a kansu, Allah kuwa yana iya hallakar da su gaba ɗayansu, ya zo da wasu mutanen a madadinsu, kuma ba za su cuci Allah da komai ba don sun ƙaryata shi sun bi son zuciyarsu. Allah kuma shi ne mai kula da komai, shi ne mai kare Annabinsa Hudu babu mai iya cutar da shi.

  58. وَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا هُودٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَنَجَّيۡنَٰهُم مِّنۡ عَذَابٍ غَلِيظٖ

    Open ayah 11:58

    Lokacin kuwa da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Hudu shi da waɗanda suka ba da gaskiya da shi, saboda wata rahama daga gare mu, Muka kuma tserar da su daga azaba mai gwaɓi.

  59. وَتِلۡكَ عَادٞۖ جَحَدُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَعَصَوۡاْ رُسُلَهُۥ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَمۡرَ كُلِّ جَبَّارٍ عَنِيدٖ

    Open ayah 11:59

    Waɗancan kuwa su ne Adawa, da suka musanta ayoyin Ubangijinsu, suka kuma saɓa wa manzanninsa, kuma suka bi umarnin duk wani mai girman kai taƙadari.

  60. وَأُتۡبِعُواْ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا لَعۡنَةٗ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَآ إِنَّ عَادٗا كَفَرُواْ رَبَّهُمۡۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّعَادٖ قَوۡمِ هُودٖ 

    Open ayah 11:60

    Aka kuma biyar musu da la’ana a duniya, haka kuma a ranar alƙiyama. Ku saurara! Lalle Adawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu. Ku saurara! Halaka ta tabbata ga Adawa mutanen Hudu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, yayin da mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka dage a kan kafircinsu da ƙaryata shi, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yanke hukuncin hallakar da su, ya kuma tserar da Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka yi imani da shi. Sai ya aiko musu da wata bakararar iska wadda ta riƙa rugurguza duk wani abu da ta biyo ta kansa da izinin Allah cikin tsawon kwana bakwai da yini takwas a jere, ta zubar da Adawa a ƙasa a marmace kamar kututturan dabinai da aka rarake, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Ƙamari , aya ta 18-20. Allah ya tserar da Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka ba da gaskiya da shi daga wata mummunar azaba mai gwaɓi domin rahamar Allah gare shi da jama’arsa. Allah kuma ya bayyana dalilan da suka jawo musu wannan azaba, watau kafirce wa ayoyinsa da suka yi, kuma suka saɓa wa Manzonsa Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), suka yi biyayya ga umarnin duk wani azzalumi mai girman kai kangararre maƙiyin gaskiya. Wannan kuma ya sa la’ana ta yi ta bin su a duniya. Watau duk wani mutumin kirki da ya ji irin mummunan labarinsu sai ya la’ance su, sannan kuma a ranar alƙiyama mala’iku su ci gaba da la’antar su. Haƙiƙa Adawa sun kafirce wa Ubangijinsu, sun butulce wa ni’imomin da ya yi musu, suka ƙaryata Manzonsa Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Don haka nesantar rahamar Allah ta tabbata ga Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).

  61. ۞وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ هُوَ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَٱسۡتَعۡمَرَكُمۡ فِيهَا فَٱسۡتَغۡفِرُوهُ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِۚ إِنَّ رَبِّي قَرِيبٞ مُّجِيبٞ

    Open ayah 11:61

    Haka kuma Muka aiko wa Samudawa ɗan’uwansu Salihu. Ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta ba shi ba; Shi ne Ya halicce ku daga ƙasa, Ya kuma ba ku damar ku raya ta; to ku nemi gafararsa sannan ku tuba gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne, Mai amsawa.”

  62. قَالُواْ يَٰصَٰلِحُ قَدۡ كُنتَ فِينَا مَرۡجُوّٗا قَبۡلَ هَٰذَآۖ أَتَنۡهَىٰنَآ أَن نَّعۡبُدَ مَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا وَإِنَّنَا لَفِي شَكّٖ مِّمَّا تَدۡعُونَآ إِلَيۡهِ مُرِيبٖ

    Open ayah 11:62

    Suka ce: “Ya Salihu, haƙiƙa a da ka kasance a cikinmu abin yi wa (kyakkyawan) fata kafin (ka zo mana da) wannan; yanzu ka riƙa hana mu mu bauta wa abin da iyayenmu suke bauta wa? Lalle mu kam tabbas muna matuƙar shakka game da abin da kake kiran mu gare shi.”

  63. قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَءَاتَىٰنِي مِنۡهُ رَحۡمَةٗ فَمَن يَنصُرُنِي مِنَ ٱللَّهِ إِنۡ عَصَيۡتُهُۥۖ فَمَا تَزِيدُونَنِي غَيۡرَ تَخۡسِيرٖ

    Open ayah 11:63

    Ya ce: “Ya ku mutanena, ku ba ni labari, yanzu idan na kasance a kan bayyananniyar hujja daga Ubangijina, Ya kuma ba ni rahama (ta annabci) to wa zai kare ni daga (azabar) Allah idan na saɓa masa? Don haka babu abin da za ku ƙare ni da shi in ban da taɓewa.”

  64. وَيَٰقَوۡمِ هَٰذِهِۦ نَاقَةُ ٱللَّهِ لَكُمۡ ءَايَةٗۖ فَذَرُوهَا تَأۡكُلۡ فِيٓ أَرۡضِ ٱللَّهِۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابٞ قَرِيبٞ

    Open ayah 11:64

    “Kuma ya ku mutanena, wannan fa taguwar Allah ce a gare ku, sai ku bar ta ta ci a ƙasar Allah, kada ku cutar da ita, sai azaba ta kusa-kusa ta afka muku.”

  65. فَعَقَرُوهَا فَقَالَ تَمَتَّعُواْ فِي دَارِكُمۡ ثَلَٰثَةَ أَيَّامٖۖ ذَٰلِكَ وَعۡدٌ غَيۡرُ مَكۡذُوبٖ

    Open ayah 11:65

    Amma sai suka soke ta, sai ya ce (da su): “Ku ji daɗi cikin gidajenku kwana uku (rak). Wannan alƙawari ne ba abin ƙaryatawa ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba mu labarin Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya aiko shi zuwa ga ƙabilun Samudawa, waɗanda suna daga cikin ƙabilun Larabawa. Sun rayu ne a garin Al-Hijr wanda ke tsakanin Madina da ƙasar Sham. Annabi Salihu ɗan’uwansu ne na jini, ya kirawo su zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, ya nuna musu ba su da wani abin bauta bisa cancanta sai Allah shi kaɗai, kuma shi ne ya halicce su daga ƙasa, domin kuwa shi ya halicci babansu Annabi Adamu, sannan ya saukar da su a bayan ƙasa, ya umarce su da su raya ta da bautar Allah ya kuma ba su damar noma ƙasa da gudanar da sauran sana’o’i da yin gine-gine a bayan ƙasa, don haka su nemi gafarar Allah game da shirkar da suka yi da Allah da kafirci da saɓon Allah, sannan su yi tuba na gaskiya gare shi. Lalle shi Ubangiji makusanci ne ga duk wanda ya tsarkake bauta gare shi, kuma mai karɓar addu’arsa ne. To da jin waɗannan kalamai daga Annabi Salihu sai suka nuna masa cewa, ba za su yarda da shi ba, domin a da suna yi masa kallon mutumin kirki, har ma suna masa fatan alheri, suna sa ran zai zama mai hankali kuma mai faɗa a ji, to amma yanzu da ya zo da waɗannan maganganu, mutuncinsa ya zube a idanunsu. Laifinsa kuwa shi ne, wai yaya zai hana su bauta wa abin da suka tarar da iyayensu suna bauta wa; wannan alama ce da ke nuna yana sukan iyayensu ne, don haka su lalle suna shakkar abin da yake kiran su gare shi na barin bautar gumakansu su dawo ga bautar Allah shi kaɗai, don haka su suna tababar gaskiyarsa, saboda haka ba za su yarda da shi ba. Sai Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar musu da martani cewa, su faɗa masa, shin yanzu idan ya zamanto yana kan wata hujja bayyananna daga Ubangijinsa, sannan kuma Allah ya ba shi annabta daga wajensa, to shi ke nan sai ya yi watsi da wannan hujjar, ya watsar da annabcin da aka ba shi, ya dawo yana bin son zuciyarsu, shi ma ya amince da bautar wanin Allah? Ya kuma tambaye su, wane ne zai kare shi daga azabar Allah idan har ya watsar da isar da saƙon Allah gare su? Don haka ya tabbatar musu da cewa, wannan kira da suke yi masa ba abin da zai ƙara masa a wurin Allah in ban da taɓewa da asara ninki-ba-ninki. Mutanen Annabi Salihu sai suka ƙalubalance shi da cewa, sai ya fito musu da wata taguwa daga wani dutse domin ta zame masa hujjar da take tabbatar da gaskiyar annabcinsa. Allah kuma ya karɓa musu ya yarda zai fitar masa da taguwar amma a kan wasu sharuɗɗa uku da ya gindaya musu, kamar haka: <b>Na farko </b>: Su ƙyale ta ta yi kiwo a bayan ƙasa ta ci abin da take so. <b>Na biyu </b>: Ruwan da suke amfani da shi zai zama na tarayya ne tsakaninsu da ita, watau yau idan sun ɗibi ruwan sha, gobe kuma sai su bar wa wannan taguwar ta sha ita kaɗai. <b>Na uku </b>: Kada su kuskura su cutar da taguwar. Idan sun kiyaye waɗannan sharuɗɗa to za su zauna da wannan taguwa lafiya, idan kuwa suka kuskura suka karya wani sharaɗi daga cikin waɗannan sharuɗɗa to wata azaba ta kusa za ta auka musu. Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi musu wannan gargaɗi amma ba su ɗauki gargaɗinsa a bakin komai ba, don haka sai suka soke wannan taguwar, domin su tabbatar wa da mutane cewa Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) maƙaryaci ne. Ganin haka sai ya sanar da su cewa, su zauna a gidajensu su ji daɗi na tsawon kwana uku rak daga lokacin da suka soke taguwar, sannan azabar Allah za ta auka musu, kuma yana tabbatar musu da cewa wannan alƙawari ne ba na ƙaryatawa ba, kamar yadda su suke tsammani.

  66. فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا صَٰلِحٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَمِنۡ خِزۡيِ يَوۡمِئِذٍۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡعَزِيزُ

    Open ayah 11:66

    To lokacin da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Salihu shi da waɗanda suka yi imani tare da shi saboda wata rahama daga gare mu, kuma (Muka tserar da su) daga kunyatar wannan rana. Lalle Ubangijinka Shi ne Mai ƙarfi Mabuwayi.

  67. وَأَخَذَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلصَّيۡحَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دِيَٰرِهِمۡ جَٰثِمِينَ

    Open ayah 11:67

    Kuma tsawa ta kama waɗanda suka yi zalunci, sai suka wayi gari cikin gidajensu a duddurƙushe (babu rai).

  68. كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَآۗ أَلَآ إِنَّ ثَمُودَاْ كَفَرُواْ رَبَّهُمۡۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّثَمُودَ

    Open ayah 11:68

    Kamar daɗai ba su taɓa zama a cikinsu ba (gidajen). Ku saurara! Lalle Samudawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu. Ku saurara! Halaka ta tabbata ga Samudawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin yadda ya saukar wa Samudawa azabarsa yayin da suka saɓa wa umarnin Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka soke taguwar Allah. Allah ya bayyana cewa, yayin da umarninsa na halakar da su ya zo bayan ƙarewar wa’adin kwana uku da aka ba su, sai ya tserar da Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka yi imani tare da shi da rahamarsa, ya kuma kuɓutar da su daga wulaƙancin wannan ranar. Allah ya tabbatar wa Manzon Allah (ﷺ) cewa lalle Ubangijinsa shi ne ƙaƙƙarfa mabuwayi, babu wanda zai iya karawa da shi har ya yi rinjaye, don haka ne ya iya hallakar da Samudawa duk kuwa da ƙarfin da suke ji da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta nau’in hallakarwar da ya yi musu, watau ya aiko musu da wata tsawa mai tsananin gaske wadda nan da nan ta hallakar da su duk suka mutu saboda zaluncinsu da kafircinsu ga Allah da ƙaryata Manzonsa Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai ga shi sun wayi gari cikin gidajensu a duddurƙushe duk ƙasa ta bice fuskokinsu babu mai sauran motsi, kai ka ce ba su taɓa rayuwa mai daɗi a cikin gidajensu ba. Allah ya ƙara jaddada laifin da Samudawa suka yi har suka cancanci ya yi musu irin wannan halakarwar, watau sun kafirce masa ne, don haka nesanta daga rahamarsa ta tabbata gare su.

  69. وَلَقَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُنَآ إِبۡرَٰهِيمَ بِٱلۡبُشۡرَىٰ قَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞۖ فَمَا لَبِثَ أَن جَآءَ بِعِجۡلٍ حَنِيذٖ

    Open ayah 11:69

    Haƙiƙa kuma mazanninmu sun zo wa Ibrahimu da albishir, suka ce: “Aminci (a gare ku)”, ya ce: “Aminci (a gare ku kuma).” To bai zauna ba sai da ya kawo musu soyayyen ɗan maraƙi.

  70. فَلَمَّا رَءَآ أَيۡدِيَهُمۡ لَا تَصِلُ إِلَيۡهِ نَكِرَهُمۡ وَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۚ قَالُواْ لَا تَخَفۡ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمِ لُوطٖ 

    Open ayah 11:70

    To lokacin da ya ga hannayensu ba sa isa gare shi (soyayyen ɗan maraƙin), sai ya shiga yin ɗari-ɗari da su, kuma ya ɓoye jin tsoronsu a zuciyarsa, suka ce: “Kar ka tsorata; mu an aiko mu ne zuwa ga mutanen Luɗu.”

  71. وَٱمۡرَأَتُهُۥ قَآئِمَةٞ فَضَحِكَتۡ فَبَشَّرۡنَٰهَا بِإِسۡحَٰقَ وَمِن وَرَآءِ إِسۡحَٰقَ يَعۡقُوبَ

    Open ayah 11:71

    Matarsa kuwa tana tsaye sai ta yi dariya, sai Muka yi mata albishir da Is’haƙa, bayan kuma Is’haƙa (sai) Yakubu.

  72. قَالَتۡ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ ءَأَلِدُ وَأَنَا۠ عَجُوزٞ وَهَٰذَا بَعۡلِي شَيۡخًاۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٌ عَجِيبٞ

    Open ayah 11:72

    Ta ce: “Kaicona! Yanzu zan iya haihuwa, ga ni tsohuwa kuma ga mijina nan ma tsoho? Lalle wannan abin mamaki ne!”

  73. قَالُوٓاْ أَتَعۡجَبِينَ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِۖ رَحۡمَتُ ٱللَّهِ وَبَرَكَٰتُهُۥ عَلَيۡكُمۡ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِۚ إِنَّهُۥ حَمِيدٞ مَّجِيدٞ

    Open ayah 11:73

    Suka ce: “Yanzu kya riƙa mamaki game da al’amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarsa su tabbata a gare ku mutanen wannan gidan. Lalle shi (Allah) Sha-yabo ne Mai girma.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin wani ɓangare ne na ƙissar Annabi Ibrahimu da Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kuma ya dunƙule labarinsu wuri guda ne saboda manzancinsu ya kasance a zamani ɗaya ne. Haka kuma shi Annabi Luɗu ya yi imani ne ta hannun baffansa Annabi Ibrahimu. Allah ya zaɓe shi ya kuma aika shi Manzo zuwa ga mutanen alƙaryar Sadum a cikin ƙasar Sham, saboda wani ƙazamin aiki da suka shahara da shi, wanda a gabaninsu ba a taɓa samun mai aikata irinsa ba, wannan aikin kuwa shi ne zaike wa maza ta dubura. Annabi Luɗu ya duƙufa ga yi musu wa’azi amma sun bijire masa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nufi hallakar da su, don haka ya aiko mala’iku don su cika aiki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yayin da mala’ikun nan suka tashi zuwa sai suka fara biyawa ta wurin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a siffar samari don su yi masa albishir da samun ɗa namiji da matarsa Sara da kuma samun jika annabi. Mala’ikun suka fara da yi masa sallama shi kuma ya amsa sallamarsu, nan take bai zauna ba sai ya shiga wajen iyalansa da sauri ya kawo musu liyafa ta gasasshen ɗan maraƙi, don yana tsammanin su mutane ne matafiya suka baƙunce shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yayin da Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga hannayen baƙinsa ba sa isa kan naman da aka kawo musu, sai ya kasa gane manufarsu, tsoronsu kuma ya shige shi, to amma sai ya ɓoye tsoron a zuciyarsa bai nuna musu ba. To amma duk da haka sai mala’ikun suka fahimci halin da yake ciki, sai suka ce masa, kada ya ji tsoron su, su mala’ikun Allah ne, kuma ya aiko su ne zuwa ga mutanen Annabi Luɗu don su halaka su, saboda mummunan laifinsu ya tsananta sosai. A daidai lokacin kuma Saratu matar Annabi Ibrahimu tana tsaye bayan labule tana sauraren tattaunawar mijinta da baƙinsa mala’iku, da jin cewa za a halakar da mutanen Annabi Luɗu, sai farin ciki ya ishe ta har ta fashe da dariya. Sai ita ma suka yi mata albishir na samun haihuwar ɗa namiji, watau Is’haƙa, shi ma kuma zai rayu ya girma har ya haifi ɗa Ya’aƙubu, dukkaninsu kuma annabawa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da cewa, yayin da Saratu ta ji albishirin da aka yi mata na samun haihuwa, sai mamaki ya kama ta matuƙa, sai ta ka da baki ta ce musu, yanzu yaya zai yiwu a ce ta haihu ga ta tsohuwa mijinta ma tsoho? Ta ce babu shakka wannan abin mamaki ne. To amma sai mala’ikun suka amsa mata da cewa, yanzu yaya za ta riƙa mamakin Ƙudirar Allah da ikonsa? Ai ta san Allah mai iko ne a kan komai, kuma rahamarsa da albarkatunsa sun tabbata gare su, su mutanen gidan Annabi Ibrahimu. Lalle kuwa Allah abin yabo ne kuma mai girma. An karɓo daga Ka’abu ɗan Ujrah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mun tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: “Lalle Allah ya koya mana yadda za mu yi muku sallama, to amma yaya za mu yi muku salati ku Ahlul Baiti?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku ce: “Ya Allah ka yi salati ga Muhammadu da kuma iyalan gidan Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga Ibrahimu da iyalan gidan Ibrahimu, lalle kai ne abin yabo mai girma. Ya Allah ka yi albarka ga Muhammadu da kuma iyalan gidan Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimuu da iyalan gidan Ibrahimu, lalle kai ne abin yabo mai girma.” [Bukhari #3370 da Muslim #407]

  74. فَلَمَّا ذَهَبَ عَنۡ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلرَّوۡعُ وَجَآءَتۡهُ ٱلۡبُشۡرَىٰ يُجَٰدِلُنَا فِي قَوۡمِ لُوطٍ

    Open ayah 11:74

    To lokacin da tsoro ya rabu da Ibrahimu, kuma albishir ya zo masa, (sai ya zama) yana muhawara da Mu game da mutanen Luɗu.

  75. إِنَّ إِبۡرَٰهِيمَ لَحَلِيمٌ أَوَّٰهٞ مُّنِيبٞ

    Open ayah 11:75

    Lalle Ibrahimu tabbas mai haƙuri ne mai yawan ambato Allah mai yawan komawa gare Shi.

  76. يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُ أَعۡرِضۡ عَنۡ هَٰذَآۖ إِنَّهُۥ قَدۡ جَآءَ أَمۡرُ رَبِّكَۖ وَإِنَّهُمۡ ءَاتِيهِمۡ عَذَابٌ غَيۡرُ مَرۡدُودٖ

    Open ayah 11:76

    Ya kai Ibrahimu, ka kau da kai daga wannan. Lalle umarnin Ubangijinka ya zo; lalle kuwa azaba wadda ba mai kawar da ita za ta zo musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da mu cewa, yayin da tsoro ya rabu da Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya fahimci cewa waɗannan baƙin ba mutane ne ba mala’iku ne, ya kuma ji daga bakinsu cewa an aiko su ne su je su hallaka mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka ƙi jin gargaɗinsa, sai kuma ya fara jayayya da su game da hallaka mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), yana nema musu alfarmar a ɗan saurara musu zuwa wani ɗan lokaci ko sa tuba su yi imani su bar fajircin da suke yi, domin kuwa shi Annabi Ibrahimu mutum ne mai haƙuri da juriya, kuma mai yawan komawa ga Allah da yawan ambatonsa. To amma sai mala’ikun nan suka amsa masa da cewa, ya kau da kansa daga wannan batu na nema musu jinkiri, domin kuwa umarnin Allah na saukar musu da azaba ya riga ya zo, don haka azaba ce mai girma take tafe a kansu babu kuma mai iya kawar da ita da addu’a ko da jayayya ko da wani abu daban.

  77. وَلَمَّا جَآءَتۡ رُسُلُنَا لُوطٗا سِيٓءَ بِهِمۡ وَضَاقَ بِهِمۡ ذَرۡعٗا وَقَالَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَصِيبٞ

    Open ayah 11:77

    Lokacin kuma da manzanninmu suka zo wa Luɗu, sai aka ɓata masa rai saboda su, kuma zuciyarsa ta yi ƙunci saboda su, ya kuma ce: “Wannan rana ce mawuyaciya!”

  78. وَجَآءَهُۥ قَوۡمُهُۥ يُهۡرَعُونَ إِلَيۡهِ وَمِن قَبۡلُ كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ هَٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِي هُنَّ أَطۡهَرُ لَكُمۡۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُخۡزُونِ فِي ضَيۡفِيٓۖ أَلَيۡسَ مِنكُمۡ رَجُلٞ رَّشِيدٞ

    Open ayah 11:78

    Mutanensa kuwa suka zo masa suna gaggawa, da ma ko can sun zamanto suna yin munanan ayyuka. Ya ce: “Ya ku mutanena, ga ‘ya’yana nan mata, su suka fi tsarkaka a gare ku (ba maza ba), to ku kiyayi Allah, kada ku kunyata ni game da baƙina. Yanzu a cikinku ba wani mutum mai hankali?”

  79. قَالُواْ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَا لَنَا فِي بَنَاتِكَ مِنۡ حَقّٖ وَإِنَّكَ لَتَعۡلَمُ مَا نُرِيدُ

    Open ayah 11:79

    Suka ce: “Haƙiƙa ka sani ba mu da wani haƙƙi (na sha’awa) ga ‘ya’yanka mata, lalle kuma tabbas ka san abin da muke nufi!”

  80. قَالَ لَوۡ أَنَّ لِي بِكُمۡ قُوَّةً أَوۡ ءَاوِيٓ إِلَىٰ رُكۡنٖ شَدِيدٖ 

    Open ayah 11:80

    Ya ce: “Ina ma ina da ƙarfi da zan hana ku, ko kuwa ina da wata ƙaƙƙarfar majingina (da zan dogara da ita)?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba mu labarin abin da ya faru lokacin da baƙin mala’iku suka isa alƙaryar Annabi Luɗu a cikin kamannin mutane kuma samari kyawawa, sai ya shiga damuwa saboda ganin su, ransa ya ɓaci domin ya san mutanensa ba za su ƙyale su ba; ko ta halin ƙaƙa sai sun neme su da aikin alfasha, har ma ya ce: “Wannan rana ce mawuyaciya a gare ni”, domin yana zaton za su fi ƙarfinsa a kansu. Sai kuwa abin da yake gudu ya auku, domin mutanensa sun yo tururuwa cikin gaggawa suna rige-rige da junansu da nufin kowa ya samu rabonsa. Da ma kuma wannan mummunar al’adar ta neman maza don biyan sha’awarsu ta zame musu jiki. Sai Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga ƙoƙarin jawo hankalinsu, yana musu tayin auren ‘ya’yansa mata, su aure su mana domin su suka fi tsarkaka a gare su maimakon neman maza. Ya ƙara gargaɗinsu da su ji tsoron Allah su kiyaye dokokinsa kada su kunyata shi a gaban baƙinsa. Ya ce musu: “Yanzu wai a cikinku babu wani mutum mai hankali?” Watau wanda zai tsawatar musu. To amma ina; hankalinsu ya riga ya ɓace. Sai suka ce masa, ai ya riga ya san cewa su fa ba ruwansu da matan balle su auri ‘ya’yansa ko sauran matan garinsu. Ai shi ya san abin da suke nema, watau buƙatarsu ita ce saduwa da maza kawai. Daga nan sai Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga cikin matsananciyar damuwa, yana tunanin ina ma a ce yana da ƙarfin da zai yi amfani da shi wajen kare baƙinsa, ko kuma yana da dangi a garin waɗanda za su taimaka masa faɗa da waɗannan miyagun mutanen?

  81. قَالُواْ يَٰلُوطُ إِنَّا رُسُلُ رَبِّكَ لَن يَصِلُوٓاْ إِلَيۡكَۖ فَأَسۡرِ بِأَهۡلِكَ بِقِطۡعٖ مِّنَ ٱلَّيۡلِ وَلَا يَلۡتَفِتۡ مِنكُمۡ أَحَدٌ إِلَّا ٱمۡرَأَتَكَۖ إِنَّهُۥ مُصِيبُهَا مَآ أَصَابَهُمۡۚ إِنَّ مَوۡعِدَهُمُ ٱلصُّبۡحُۚ أَلَيۡسَ ٱلصُّبۡحُ بِقَرِيبٖ

    Open ayah 11:81

    (Baƙin) suka ce: “Ya Luɗu, lalle mu manzannin Ubangijinka ne; ba za su iya isowa gare ka ba; don haka sai ka tafi kai da iyalanka cikin wani yanki na dare, kada kuwa ɗaya daga cikinku ya waiwaya, sai matarka kawai. Lalle ita kam abin da ya same su zai same ta. Lalle lokacin da aka ɗebar musu asuba ne kawai; shin asuba ba kurkusa take ba?

  82. فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا جَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهَا حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٖ مَّنضُودٖ

    Open ayah 11:82

    To lokacin da umarninmu ya zo sai Muka mai da samanta ƙasa (wato alƙaryar), Muka kuma yi mata ruwan duwatsu irin na soyayyen yumɓu wasu bayan wasu.

  83. مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَۖ وَمَا هِيَ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ بِبَعِيدٖ

    Open ayah 11:83

    Waɗanda aka yi wa alama daga Ubangijinka. Ba kuwa nesa (dutsen) yake da azzalumai ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ci gaba da bayyana cewa, lokacin da mala’ikun suka ga Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga damuwa sosai da irin yadda mutanensa suka taso haiƙan suna ƙoƙarin sai sun ci mutuncin baƙinsa, sai suka kwantar masa da hankali, suka bayyana masa cewa, su ai mala’iku ne waɗanda Allah ya aiko su don su hallaka mutanensa, don haka babu abin da za su iya yi musu na cutarwa. Suka kuma umarce shi da ya kwashe iyalansa kakaf cikin dare ya bar wannan garin, amma ban da matarsa domin ita ma tana tare da mutanen gari wajen kafirce wa Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Suka umarce shi da kada wani daga cikin iyalinsa ya waiwaya lokacin da suke fita daga garin, in ban da matarsa, ita kam abin da duk zai samu waɗannan mutane ita ma zai same ta. Suka kuma bayyana masa lokacin da Allah ya nufi azabarsa za ta saukar musu, watau lokacin asuba kuma lokaci ne na kurkusa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin azabar da ta auka wa mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da wa’adin da aka ɗeba musu ya zo, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sa mala’ikun nan suka ɓaɓɓako da wannan alƙayar sai da suka ɗaga ta sama, sannan suka mayar da samanta ya koma ƙasa, ƙasa kuma ya koma sama, watau aka kifar da ita, sai kuma ya bi su da ruwan duwarwatsu na wutar Jahannama, kowane dutse kuma yana ɗauke da alamar wanda zai faɗa wa, umarni ne kuma daga Allah. Duwatsun suka yi ta zuba ɗaya bayan ɗaya har sai da suka hallaka su gaba ɗaya. Don haka wannan azaba ba nesa take ba ga duk wanda zai kwaikwayi irin zaluncin waɗannan miyagun mutane, idan Allah ya nufi yi masa azaba irin wannan yana iya yi, domin ba wani abu ne da zai gagare shi ba.

  84. ۞وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ وَلَا تَنقُصُواْ ٱلۡمِكۡيَالَ وَٱلۡمِيزَانَۖ إِنِّيٓ أَرَىٰكُم بِخَيۡرٖ وَإِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٖ مُّحِيطٖ

    Open ayah 11:84

    Kuma Mun aiko wa (mutanen) Madyana ɗan’uwansu Shu’aibu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta ba shi ba, kada kuma ku tauye mudu da sikeli; lalle ni ina ganin ku da alheri (wato wadata), kuma lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wata rana mai kewayewa.

  85. وَيَٰقَوۡمِ أَوۡفُواْ ٱلۡمِكۡيَالَ وَٱلۡمِيزَانَ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ

    Open ayah 11:85

    “Kuma ya ku mutanena, ku cika mudu da sikeli da adalci; kada kuwa ku tauye wa mutane abubuwansu, kada kuma ku yaɗa ɓarna a bayan ƙasa.

  86. بَقِيَّتُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَۚ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِحَفِيظٖ

    Open ayah 11:86

    “Abin da zai wanzu a gare ku na alheri a wurin Allah shi ya fi muku in kun kasance muminai. Ni kuma ba mai tsaron ku ba ne.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiga bayar da labarin Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya aika shi ga mutanen ƙasar Madyana , wadda ta taso tun daga garin Ma’an har ta dangane da Tabuka. Madyanu sunan wata ƙabila ce ta Larabawa da suka zauna a wannan wurin sai ake kiran sunan garin da sunansu. Annabi Shu’aibu ya same su suna bautar gumaka ba Allah ba, sannan suna da ta’adar tauye mudun awo da sikeli na awon nauyi, don haka sai ya fara da kiran su zuwa bautar Allah shi kaɗai, sannan ya yi musu kashedi da tauye mudu da sikeli, ya ankarar da su irin ni’imar arzuki da Allah ya ba su; to kada su bijire masa, domin yana jiye musu tsoron azabar ranar lahira wadda za ta kewaye su ta ko’ina. Annabi Shu’aibu ya umarce su da su cika mudu da adalci yayin da suke yi wa mutane awo, hakanan su yi adalci lokacin da suke tsayar da sikeli; kada su cuci kowa, su ma kada a cuce su, kuma ya tsawatar musu a kan yin ɓarna a bayan ƙasa, ta hanyar fashi da makami, laifin da suka shahara da shi a lokacin. Ya nusar da su cewa, abin da za su samu na halal bayan sun ba wa mutane haƙƙoƙinsu cikakku shi ya fi musu alheri ya kuma fi albarka fiye da ƙwangen da suke yi wa mutane lokacin awo, ko tare mutane suna yi musu fashi da makami, don haka idan har su muminai ne da gaske, to su haƙura da ɗan abin da za su samu na halal. Ya kuma nuna musu cewa, shi ba wanda zai tsaya a kansu yana gadin su ba ne, yana lissafa ayyukansu don ya yi musu hisabi a kai; wannan aikin Allah ne masanin abin da yake ɓoye da na sarari.

  87. قَالُواْ يَٰشُعَيۡبُ أَصَلَوٰتُكَ تَأۡمُرُكَ أَن نَّتۡرُكَ مَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَآ أَوۡ أَن نَّفۡعَلَ فِيٓ أَمۡوَٰلِنَا مَا نَشَٰٓؤُاْۖ إِنَّكَ لَأَنتَ ٱلۡحَلِيمُ ٱلرَّشِيدُ

    Open ayah 11:87

    Suka ce: “Ya kai Shu’aibu, yanzu sallarka ce take umartar ka da (ka sa) mu bar abin da iyayenmu suke bauta wa, kada kuma mu aikata abin da muka ga dama da dukiyoyinmu? Lalle tabbas kai ne mai haƙuri mai hankali!”

  88. قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَرَزَقَنِي مِنۡهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَمَآ أُرِيدُ أَنۡ أُخَالِفَكُمۡ إِلَىٰ مَآ أَنۡهَىٰكُمۡ عَنۡهُۚ إِنۡ أُرِيدُ إِلَّا ٱلۡإِصۡلَٰحَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُۚ وَمَا تَوۡفِيقِيٓ إِلَّا بِٱللَّهِۚ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ أُنِيبُ

    Open ayah 11:88

    Ya ce: “Ya ku mutanena, me kuke gani ne, idan na kasance a kan bayyananniyar hujja daga Ubangijina, Ya kuma arzuta ni da kyakkyawan arziki daga gare Shi. Ba na kuma nufin in aikata abin da nake hana ku aikata shi. Ba komai nake nufi ba sai gyara iyakacin ikona. Kuma dacewata daga Allah kaɗai take. A gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi ne zan koma.

  89. وَيَٰقَوۡمِ لَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شِقَاقِيٓ أَن يُصِيبَكُم مِّثۡلُ مَآ أَصَابَ قَوۡمَ نُوحٍ أَوۡ قَوۡمَ هُودٍ أَوۡ قَوۡمَ صَٰلِحٖۚ وَمَا قَوۡمُ لُوطٖ مِّنكُم بِبَعِيدٖ

    Open ayah 11:89

    “Kuma ya mutanena, kada saɓa mini ya jawo muku irin abin da ya sami mutanen Nuhu ko mutanen Hudu ko kuma mutanen Salihu, ku ma ya same ku. Mutanen Luɗu kuwa ba nesa suke da ku ba.

  90. وَٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِۚ إِنَّ رَبِّي رَحِيمٞ وَدُودٞ 

    Open ayah 11:90

    “Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sannan ku tuba gare Shi. Lalle Ubangijina Mai yawan rahama ne Mai nuna ƙauna.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mutanensa wa’azi da gargaɗi a kan abubuwa biyu, na farko, bautar wani ba Allah ba; na biyu, tauye mudu da sikeli. Su kuma sai suka mayar masa da martani a kan waɗannan abubuwa biyu da yake ƙoƙarin hana su aikatawa, suka ce masa sallarsa ce, watau ibadarsa ta sa shi yake ƙoƙarin raba su da addinin iyayensu na bautar gumaka? Watau dai ba za su daina shirka ba, saboda sun gaje ta ne daga iyayensu. A kan abu na biyu kuma suka nuna masa cewa, dukiyarsu mallakinsu ne, don haka bai isa ya hana su aikata abin da suka ga dama da ita ba, na tauye mudu da sikeli. Cikin izgili da tsokana suka ƙara da ce masa: Lalle kai ne mai haƙuri mai hankali. Watau da har kake iya gane abin da ma ba mu gane ba. Ko kuma suna faɗa masa irin yadda a da suka ɗauke shi kafin ya fara yi musu wa’azi, sun ɗauke shi mutum ne mai haƙuri da juriyar zama da mutane, kuma mai hankali, to mene ne yanzu ya same shi da har ya sa shi irin waɗannan maganganu? Daga nan sai Annabi Shu’aibu ya mayar musu da martani da cewa, yaya za su yi idan har shi yana kan hujja bayyananniya daga Allah Ubangijinsa, kuma ya ba shi arzuki na halal, ya kuma ba shi annabta? Kuma ba yana nufin ya hana su wani mummunan aiki ba kamar tauye mudu da sikeli sannan shi kuma ya saɓa ma wannan ya aikata abin da yake hana su aikatawa ba. Ya tabbatar musu da cewa, buƙatarsa ɗaya ce a wurinsu, ita ce samar da gyara a cikinsu gwargwadon ikonsa, su kuma fahimci Tauhidi su kaɗaita Allah, su daina cutar junansu a mu’amalarsu da juna, kuma Allah ne kaɗai zai yi masa dace cikin wannan aiki da ya ɗora masa, kuma gare shi kaɗai ya dogara, kuma gare shi zai koma. Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da yi wa mutanensa kashedi da su yi hattara kada tsananin gaba da shi ta sa su bijire wa abin da yake gargaɗinsu a kai, daga ƙarshe irin azabar da ta samu mutanen Nuhu da mutanen Hudu da mutanen Salihu su ma ta same su. Mutanen Annabi Luɗu ba nesa suke da su ba, watau garuruwansu ko zamaninsu. Domin Suna da labarin abin da ya same su na azaba yayin da suka saɓa wa annabawansu. Sai kuma ya sake kiran su zuwa ga neman gafarar Ubangijinsu a kan laifuffukan da suke yi, su tuba su gyara ayyukansu, lalle Ubangiji mai rahama ne mai tsananin nuna ƙauna ga masu tuba da neman gafara.

  91. قَالُواْ يَٰشُعَيۡبُ مَا نَفۡقَهُ كَثِيرٗا مِّمَّا تَقُولُ وَإِنَّا لَنَرَىٰكَ فِينَا ضَعِيفٗاۖ وَلَوۡلَا رَهۡطُكَ لَرَجَمۡنَٰكَۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡنَا بِعَزِيزٖ

    Open ayah 11:91

    Suka ce: “Ya kai Shu’aibu, ba ma fahimtar da yawa daga abin da kake faɗa; lalle kuma tabbas muna ganin ka rarrauna a cikinmu, kuma ba don danginka ba da mun jefe ka; ba kuwa za ka gagare mu ba.”

  92. قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَهۡطِيٓ أَعَزُّ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱللَّهِ وَٱتَّخَذۡتُمُوهُ وَرَآءَكُمۡ ظِهۡرِيًّاۖ إِنَّ رَبِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ مُحِيطٞ

    Open ayah 11:92

    Ya ce: “Ya ku mutanena, yanzu dangin nawa ne suka fi Allah girma a wurinku, kuka kuma ɗauke shi abin jefarwa a can bayanku? Lalle Ubangijina a kewaye Yake da (sanin) abin da kuke aikatawa.

  93. وَيَٰقَوۡمِ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنِّي عَٰمِلٞۖ سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن يَأۡتِيهِ عَذَابٞ يُخۡزِيهِ وَمَنۡ هُوَ كَٰذِبٞۖ وَٱرۡتَقِبُوٓاْ إِنِّي مَعَكُمۡ رَقِيبٞ

    Open ayah 11:93

    “Kuma ya ku mutanena, ku yi aiki a kan irin hanyarku; ni ma lalle mai yin aiki ne (a kan tawa). Ba da daɗewa ba za ku san wanda azaba mai wulakantawa za ta zo masa, da kuma wanda yake maƙaryaci. Ku saurara, ni ma lalle mai sauraro ne tare da ku.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana irin jayayyar da mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suke ta yi da shi, har ta kai ga yi masa barazanar kisa idan bai daina yi musu wa’azi ba, har da cewa, su fa ba sa ma fahimtar mafi yawan maganganunsa, kuma su suna yi masa kallon mai rauni ne a cikinsu, watau bai isa a ce shi ne zai riƙa faɗa musu irin maganganun da suke fitowa daga bakinsa ba, domin shi ba kowa ba ne a cikinsu; suna raga masa ne ma saboda alfarmar danginsa waɗanda su suna tare da su a addininsu ba su fita sun bi shi ba; in ba don haka ba da tuni sun jefe shi da duwatsu har mutuwa, domin ba zai gagare su ba. Sai Shu’aibu ya mayar musu da martani cewa, yanzu dangina ne suka fi Allah girma a wurinsu, suka ƙyale shi don su ba don Allah ba, suka yi watsi da Allah da umarninsa, suka kuma ƙi yin imani da Annabinsa? Ya sake tabbatar musu da cewa, Allah yana sane da duk abin da suke aikatawa kuma zai yi musu sakayya a kansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi Shu’aibu ya gane mutanensa sun yi nisa cikin kafirci; lalama da lallashi ba sa ƙara musu komai sai taurin kai, sai ya ɗauki matakin yi musu gargaɗin saukar azabar Allah a kansu da cewa, su ci gaba da bin hanyar da suka zaɓa wa kawunansu ta kafirci da zaluntar juna, shi ma zai ci gaba da bin tasa hanyar wadda Allah ya zaɓa masa, amma kuma su kwana da sanin cewa, ba da jimawa ba za su gane wanda azabar wulaƙanci za ta saukar masa, da wanda yake maƙaryaci tsakanin su da shi. Don haka shi da su duk su saurari hukuncin Allah a kansu.

  94. وَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا شُعَيۡبٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَأَخَذَتِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلصَّيۡحَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دِيَٰرِهِمۡ جَٰثِمِينَ

    Open ayah 11:94

    Lokacin kuwa da umarninmu ya zo Muka tserar da Shu’aibu tare da waɗanda suka yi imani da shi da wata rahama daga gare mu; tsawa kuma ta kama waɗanda suka kafirta, sai suka wayi gari cikin gidajensu a duddurƙushe, (ba rai).

  95. كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَآۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّمَدۡيَنَ كَمَا بَعِدَتۡ ثَمُودُ

    Open ayah 11:95

    Kamar daɗai ba su taɓa zama ba a cikinsu (gidajen) ba. Ku saurara; halaka ta tabbata ga (mutanen) Madyana kamar yadda Samudawa suka halaka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana aukuwar azabar da Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake tsoratar da mutanensa da ita, kuma lokacin da azabar ta zo Allah cikin rahamarsa ya tserar da Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka yi imani tare da shi, su kuma mutanensa azzalumai wata tsawa mai tsanani ta kama su nan da nan suka halaka baki ɗaya, suka wayi gari a yashe matattu a cikin gidajensu kamar daɗai ba su taɓa rayuwa a cikinsu ba. Tabbas mutanen Madyana sun yi nesa daga samun rahamar Allah, kamar yadda Samudawa mutanen Annabi Salihu su ma suka yi nesa daga gare ta.

  96. وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

    Open ayah 11:96

    Haƙiƙa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu da hijjoji bayyanannu.

  97. إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱتَّبَعُوٓاْ أَمۡرَ فِرۡعَوۡنَۖ وَمَآ أَمۡرُ فِرۡعَوۡنَ بِرَشِيدٖ

    Open ayah 11:97

    Zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, sai suka bi umarnin Fir’auna; amma kuma umarnin Fir’auna ba a kan hanya yake ba.

  98. يَقۡدُمُ قَوۡمَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَأَوۡرَدَهُمُ ٱلنَّارَۖ وَبِئۡسَ ٱلۡوِرۡدُ ٱلۡمَوۡرُودُ

    Open ayah 11:98

    Zai jagoranci mutanensa ranar alƙiyama sai ya shigar da su wuta. Kuma tir da shiga wannan mashiga.

  99. وَأُتۡبِعُواْ فِي هَٰذِهِۦ لَعۡنَةٗ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ بِئۡسَ ٱلرِّفۡدُ ٱلۡمَرۡفُودُ

    Open ayah 11:99

    Aka kuma bi su da la’ana a wannan (duniyar) da kuma ranar alƙiyama. Irin wannan kyauta kuwa da aka yi musu ta munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ya aika Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa da hujjoji bayyanannu masu tabbatar da gaskiyar abin da ya zo da shi na kaɗaita Allah da bauta. To amma sai waɗannan fadawa suka biye wa Fir’auna, suka yarda da kafircinsa alhalin al’amarin Fir’auna gaba ɗaya ba a kan daidai yake ba. Don haka sai ya hallakar da su gaba ɗaya duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ranar alƙiyama Fir’auna zai shugabanci mutanensa, yana gaba suna bin sa a baya har sai ya shigar da su wutar Jahannama. Tir da wannan mashiga da zai jefa su cikinta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya bi su da la’ana tun a nan duniya, sun rasa rahamarsa, to hakanan ma a lahira zai bi su da wannan la’anar, ba su babu samun tsira. Tabbas wannan kyauta ta la’ana har iri biyu ta yi matuƙar muni gare su.

  100. ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡقُرَىٰ نَقُصُّهُۥ عَلَيۡكَۖ مِنۡهَا قَآئِمٞ وَحَصِيدٞ 

    Open ayah 11:100

    Waɗannan suna daga labarun alƙaryu da Muke labarta maka su; daga cikinsu akwai waɗanda suke tsaye da waɗanda suke a rushe.

  101. وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡۖ فَمَآ أَغۡنَتۡ عَنۡهُمۡ ءَالِهَتُهُمُ ٱلَّتِي يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ لَّمَّا جَآءَ أَمۡرُ رَبِّكَۖ وَمَا زَادُوهُمۡ غَيۡرَ تَتۡبِيبٖ 

    Open ayah 11:101

    Ba Mu kuwa zalunce su ba, sai dai su ne suka zalunci kansu; allolinsu da suke bauta wa ba Allah ba, ba su maganta musu komai ba, lokacin da umarnin Ubangijinka ya zo; ba su kuwa ƙara musu komai ba in ban da halaka.

  102. وَكَذَٰلِكَ أَخۡذُ رَبِّكَ إِذَآ أَخَذَ ٱلۡقُرَىٰ وَهِيَ ظَٰلِمَةٌۚ إِنَّ أَخۡذَهُۥٓ أَلِيمٞ شَدِيدٌ 

    Open ayah 11:102

    Haka kuwa damƙar Ubangijinka take idan ya damƙi alƙaryu yayin da suka yi zalunci. Haƙiƙa damƙarsa mai raɗaɗi ce mai tsanani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da Annabi (ﷺ) cewa, labaran da yake ba shi a cikin wannan Alƙur’ani duka gaskiya ne. Daga cikin al\'ummu da ya ba shi labarin halakar da su, akwai waɗanda har yanzu sauran kufansu yana nan bai ɓace ba, akwai kuma waɗanda an share su kwata-kwata daga bayan ƙasa, babu sauran wata alamarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, abin da ya auka musu na halaka ya same su ne saboda laifukansu na kafirce wa annabawansa, don haka ba zaluntar su ya yi ba, su ne dai suka zalunci kawunansu, saboda sun riƙi wasu alloli suna bauta musu ba Allah Maɗaukakin Sarki ba, to sai ga shi allolin nasu na ƙarya ba su maganta musu komai ba lokacin da azabar Allah ta abko musu, ba su ƙara musu komai ba sai halaka da hasara. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu mummunan kamu, to haka da man kamun Allah yake, duk sa’adda ya damƙi mutanen wani gari azzalumai a kowane lokaci ne to damƙarsa mai raɗaɗi ce mai tsanani. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah yana saurara wa azzalumi har sai lokacin da ya damƙe shi, to ba zai kuɓuce masa ba.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: “Haka kuma damƙar Ubangijinka take, idan ya damƙi alƙaryu yayin da suka yi zalunci, haƙiƙa damƙarsa mai raɗaɗi ce mai tsanani.” [Bukhari #4686 da Muslim #2583].

  103. إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّمَنۡ خَافَ عَذَابَ ٱلۡأٓخِرَةِۚ ذَٰلِكَ يَوۡمٞ مَّجۡمُوعٞ لَّهُ ٱلنَّاسُ وَذَٰلِكَ يَوۡمٞ مَّشۡهُودٞ 

    Open ayah 11:103

    Lalle game da wannan akwai aya ga wanda ya ji tsoron azabar lahira. Wannan kuwa rana ce da za a tattara mutane a cikinta, kuma wannan rana ce wadda kowa zai halarta.

  104. وَمَا نُؤَخِّرُهُۥٓ إِلَّا لِأَجَلٖ مَّعۡدُودٖ 

    Open ayah 11:104

    Kuma ba ma jinkirta ta sai zuwa lokaci ƙayyadadde.

  105. يَوۡمَ يَأۡتِ لَا تَكَلَّمُ نَفۡسٌ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ فَمِنۡهُمۡ شَقِيّٞ وَسَعِيدٞ 

    Open ayah 11:105

    Ranar da za ta zo ba wani mai rai da zai yi magana sai da izininsa. To daga cikinsu akwai taɓaɓɓe da kuma mai rabauta.

  106. فَأَمَّا ٱلَّذِينَ شَقُواْ فَفِي ٱلنَّارِ لَهُمۡ فِيهَا زَفِيرٞ وَشَهِيقٌ 

    Open ayah 11:106

    To waɗanda suka taɓe suna cikin wuta suna ta kururuwa da ihu a cikinta.

  107. خَٰلِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ إِلَّا مَا شَآءَ رَبُّكَۚ إِنَّ رَبَّكَ فَعَّالٞ لِّمَا يُرِيدُ 

    Open ayah 11:107

    Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa suna nan a dawwame, sai dai abin da Ubangijinka Ya ga dama. Lalle Ubangijinka Mai yawan aikata abin da Yake nufi ne.

  108. ۞وَأَمَّا ٱلَّذِينَ سُعِدُواْ فَفِي ٱلۡجَنَّةِ خَٰلِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ إِلَّا مَا شَآءَ رَبُّكَۖ عَطَآءً غَيۡرَ مَجۡذُوذٖ 

    Open ayah 11:108

    Amma waɗanda aka yi musu dace da rabauta, to suna cikin Aljanna suna masu dawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa suna nan a dawwame, sai dai abin da Ubangijinka Ya ga dama, (wannan) kyauta ce marar yankewa.

  109. فَلَا تَكُ فِي مِرۡيَةٖ مِّمَّا يَعۡبُدُ هَٰٓؤُلَآءِۚ مَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا كَمَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُهُم مِّن قَبۡلُۚ وَإِنَّا لَمُوَفُّوهُمۡ نَصِيبَهُمۡ غَيۡرَ مَنقُوصٖ 

    Open ayah 11:109

    To kada ka zamo cikin kokwanto dangane da abin da waɗannan suke bauta wa. Ba sa bauta sai kamar yadda iyayensu a da can suke bautar. Lalle kuma tabbas za Mu cika musu sakamakonsu ba da tauyewa ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, game da damƙar da ya yi wa alƙaryun da suka yi zalunci da halaka su da ya yi ba shakka akwai aya abin lura game da wannan, amma ga wanda ya ji tsoron azabar ranar lahira. Wannan rana kuwa ita ce ranar da Allah zai tattara mutane gaba ɗaya a cikinta domin yi musu hisabi, don haka dole sai kowa ya halarci wannan taro. Allah kuma ya bayyana cewa, yana jinkirta zuwan wannan rana ce har sai ƙayyadadden lokacin da aka aje mata ya zo. Lokacin da za ta zo kuwa to babu wani rai da zai iya yin wata magana ta kare kai ko ta ceton wani sai idan Allah ya yi masa izini. Mutane kuma za su kasu gida biyu ne a wannan ranar, watau taɓaɓɓu ‘yan wuta, da kuma marabauta ‘yan Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon kowannensu. Su dai taɓaɓɓu su ne za su shiga wutar Jahannama suna ta kururuwa da ihu a cikinta saboda tsananin azabarta. Za su kuma ci gaba da zama a cikinta har abada matuƙar sammai da ƙasa suna nan, sai wanda Allah ya ga damar fitar da shi daga cikin muminai masu laifuka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa (ﷺ) cewa, lalle shi mai aikata abin da ya ga dama ne, babu mai tilasta shi ko ya hana shi. Su kuma marabauta, waɗanda aka yi musu gyaɗar-dogo tun a nan duniya, suka ba da gaskiya suka yi ayyuka na ƙwarai, to su kam za a kai su gidan Aljanna, su kuma dawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa suna nan, sai wanda Allah ya ga damar shigar da shi wuta kafin shigarsa Aljannar saboda zunubinsa, lalle ni’imar Allah ga ‘yan Aljanna marar yankewa ce. Faɗar Allah: “Matuƙar sammai da ƙasa suna nan a dawwame.” wani salon magana ne irin wanda Larabawa suke yi idan suna nufin zartar da wani abu wanda zai ci gaba da wanzuwa har abada, to sai su faɗi haka. Amma da wuta da Aljanna ba za su gushe ba har abada. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Za a zo da mutuwa cikin kamannin wani farin rago mai sofanen baƙi, sai mai shela ya yi shela ya ce: “Ya ku ‘yan Aljanna.” Sai su leƙo su duba, sai ya ce: “Shin kun san wannan?” Sai su ce: “E, mutuwa ce.” Dukkansu sun taɓa ganin ta. Sannan ya yi shela, ya ce: “Ya ku ‘yan wuta.” Sai su leƙo su duba, sai ya ce: “Shin kun san wannan?” Sai su ce: “E, wannan mutuwa ce.” Dukkansu sun taɓa ganin ta. Sai ya yanka shi, Sannan mai shela ya ce: “Ya ku ‘yan Aljanna, ku yi ta zama har abada babu mutuwa, ku ma ‘yan wuta ku yi ta zama har abada babu mutuwa.” [Bukhari #4730 da Muslim #2849]. Bayan Allah ya gama bayanin sakamakon kafirai da muminai a lahira, sai kuma ya ci gaba da tsoratar da mushirikai da irin azabar halakarwar da ta faru ga al\'ummun da suka gabace su, su yi hattara kada su ma ta faru gare su. Allah kuma ya ja hankalin Annabi (ﷺ) cewa, kada ya zamo mai kokwanton ɓacin abin da mushirikai suke bauta wa, ba su da wata hujja ta shari’a ko ta hankali da ke nuna gaskiyar abin da suke kai, abin da kawai ya ja su ga bauta wa wasu ba Allah ba shi ne kwaikwayon iyayensu. Allah kuwa ya yi alƙawari a kan cewa, zai cika musu sakamakonsu na azaba ba tare da ya tauye wani abu daga ciki ba.

  110. وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَٱخۡتُلِفَ فِيهِۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ 

    Open ayah 11:110

    Haƙiƙa kuma Mun bai wa Musa Littafi, sai aka sassaɓa a game da shi. Ba don kuwa wata kalma da ta rigaya daga Ubangijinka ba, to lalle da an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle suna cikin matuƙar kokwanto game da shi (Alƙur\'ani).

  111. وَإِنَّ كُلّٗا لَّمَّا لَيُوَفِّيَنَّهُمۡ رَبُّكَ أَعۡمَٰلَهُمۡۚ إِنَّهُۥ بِمَا يَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

    Open ayah 11:111

    Kuma lalle kowannensu tabbas sai Ubangijinka Ya cika musu sakamakon ayyukansu. Lalle Shi Masanin abin da suke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ya ba wa Annabi Musa littafin Attaura wanda zai sanya Banu Isra’ila su haɗa kansu wajen bin umarninsa da barin haninsa, to amma maimakon haka sai suka shiga saɓani game da wannan, suka rungumi aƙidu mabambanta. To ba don maganar da Allah ya yi ta cewa zai saurara wa masu laifi ba zai gaggauto musu azaba ba, zai bar su sai ranar alƙiyama, to da tuni sun gamu da matsananciyar azaba tun a nan duniya. Allah ya tabbatar da cewa, kafirai na Larabawa da Yahudu da Nasara lalle suna cikin shakka mai sa kokwanto game da lamarin Alƙur’ani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lalle su waɗannan masu jayayya a kan Alƙur’ani suna ƙaryata shi, Allah ba zai ƙyale su hakanan ba, dole ne za su gamu da sakamakonsu cikakke, wanda ya aikata kyakkyawa ya ga kyakkyawa; wanda kuwa ya aikata mummuna shi ma ya ga mummuna. Lalle Allah masanin abin da suke aikatawa ne a sarari da ɓoye.

  112. فَٱسۡتَقِمۡ كَمَآ أُمِرۡتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطۡغَوۡاْۚ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

    Open ayah 11:112

    Don haka sai ka tsaya totar kamar yadda aka umarce ka kai da waɗanda suka tuba tare da kai, kada kuwa ku wuce iyaka. Lalle Shi (Allah) Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.

  113. وَلَا تَرۡكَنُوٓاْ إِلَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ فَتَمَسَّكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِنۡ أَوۡلِيَآءَ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

    Open ayah 11:113

    Kuma kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku, ba ku kuwa da wasu majiɓinta lamura ba Allah ba, sannan ba za a taimake ku ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da muminai da tsayawa kyam a kan umarnin Allah a kan miƙaƙƙiyar hanya ta aikata abin da aka umarce su da barin abin da aka hana su da kuma gaskata duk abin da aka labarta musu, kada su karkata zuwa dama ko hagu, su dawwama a kan haka. Lalle Allah mai ganin abin da suke aikatawa ne, don haka zai yi musu sakamako a kansu. An karɓo daga Sufyanu ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ce: “Ya Manzon Allah, faɗa mini wata magana a Musulunci wanda ban da kai ba zan sake tambayar wani ba game da ita” Sai ya ce: “Ka ce: “Na yi imani da Allah, sannan ka tsaya ƙyam.” [Muslim #38]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗe su da su guji karkata ko ta halin ƙaƙa zuwa ga kafirai azzalumai da sunan kara ko soyayya, sai wuta ta shafe su a dalilin hakan, alhalin ba su da wasu masoya waɗanda za su kuɓutar da su daga wannan azabar, ko su taimaka musu in ba Allah ba.

  114. وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّٰكِرِينَ

    Open ayah 11:114

    Ka kuma tsai da salla farkon rana da ƙarshenta da kuma farkon dare. Lalle kyawawan (ayyuka) suna shafe munana. Wannan tunasarwa ne ga masu tunawa.

  115. وَٱصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 11:115

    Kuma ka yi haƙuri, domin lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa.

  116. فَلَوۡلَا كَانَ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِن قَبۡلِكُمۡ أُوْلُواْ بَقِيَّةٖ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡفَسَادِ فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّنۡ أَنجَيۡنَا مِنۡهُمۡۗ وَٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَآ أُتۡرِفُواْ فِيهِ وَكَانُواْ مُجۡرِمِينَ

    Open ayah 11:116

    Ina ma da a ce an samu mutanen kirki daga tsarekun da suka gabace ku da za su riƙa hana yaɗuwar ɓarna a bayan ƙasa? Sai ‘yan kaɗan kawai (aka samu) daga waɗanda Muka tserar cikinsu. Waɗanda kuma suka yi zalunci sai suka bi abin da aka wadata su da shi, suka kuwa zamanto masu laifi.

  117. وَمَا كَانَ رَبُّكَ لِيُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ بِظُلۡمٖ وَأَهۡلُهَا مُصۡلِحُونَ

    Open ayah 11:117

    Kuma Ubangijinka bai kasance mai hallaka alƙarya ba da zalunci alhali kuwa mutanenta suna masu gyara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da tsayar da salla a farkon rana da ƙarshenta, watau sallar asuba da sallar magariba; wasu malaman suka ce sallar asuba da ta la’asar ne; wasu kuma suna ganin su ne sallar asuba a farkon rana, azahar da la’asar kuma a ƙarshen rana; sai kuma farkon dare, watau sallar isha’i, ko kuma magariba da isha\'i. Wasu malamai suna ganin wataƙila wannan ayar an saukar da ita ne gabanin a farlanta salloli biyar, watau a wannan lokacin salloli biyu kaɗai ake yi, ɗaya kafin hudowar rana, ta biyu kuwa bayan faɗuwar rana, sai kuma ƙiyamullaili da aka farlanta wa Annabi (ﷺ) da al’ummarsa, daga baya aka shafe wajabcinta daga kan al’umma sai Manzo kaɗai. Wasu kuma suka ce shi ma an shafe masa wajabcin. Sannan Allah ya bayyana cewa, ayyukan ƙwarai suna kankare laifin munanan ayyuka da suka gabace su. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya Manzon Allah, na samu wata mace a wani lambu, na yi komai da ita amma ban sadu da ita ba; na sumbace ta, na kuma rungume ta, amma ban da wannan ba abin da na yi da ita; don haka ka yi mini abin da ka ga dama.” Sai Annabi (ﷺ) bai ce masa komai ba. Sai mutumin ya juya ya tafi. Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Allah ya rufa masa asiri shi kuma ya ƙi rufa wa kansa asiri.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya bi shi da kallo sannan ya ce: “Ku dawo mini da shi.” Sai suka dawo da shi wurin Manzon Allah (ﷺ). Sai Annabi ya karanta masa wannan ayar ta 114. Sai Mu’azu ya ce: “Wannan nasa ne shi kaɗai ko na dukkan mutane ne?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A’a, na dukkan mutane ne.” [Muslim #2763]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Salloli biyar da sallar Juma’a zuwa wata sallar Juma’ar da azumin watan Ramadan zuwa wani azumin watan Ramadan, suna kankare laifukan da suke tsakaninsu matuƙar an nisanci manyan laifuka.” [Bukhari #528 da Muslim #667]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da yin haƙuri, ya kuma labarta masa girman ladan masu haƙuri, domin Allah ba ya tozarta ladan masu kyautatawa; yana karɓar kyawawan ayyukansu ya yi musu sakayya da mafi kyan abin da suka aikata. To bayan Allah ya ambaci hallakar al\'ummun da suka gabata a dalilin sun ƙaryata manzanninsu, ya kuma bayyana cewa yawancinsu sun saki hanyar Allah; waɗanda aka ba wa littattafai daga cikinsu ma an samu sun gurɓata littattafan, wanda yin haka zai iya haifar da ɓacewar addinai gaba ɗaya daga doron ƙasa. To amma Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nusantar da cewa saboda samun wasu mutanen kirki daga cikinsu, waɗanda suke kiran mutane zuwa ga kyawawan ayyuka suke hana munana, wannan ya haifar da amfani mai yawa a cikin al\'ummunsu. To da Allah ya tashi hallaka mutanensu kafirai sai su ya tserar da su. Allah ya tabbatar da cewa su waɗannan azzalumai sun yi ta morewarsu ne kawai sun ƙi su fahimci gaskiya su bi ta, don haka suka zamanto masu laifi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzo (ﷺ) cewa, Allah ba zai halaka wata alƙarya ba idan har mutanen cikinta masu gyara ne a bayan ƙasa; yakan hallaka garin da mutanensa suke maɓarnata ne, masu aikata laifuka da zalunci a bayan ƙasa.

  118. وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ لَجَعَلَ ٱلنَّاسَ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗۖ وَلَا يَزَالُونَ مُخۡتَلِفِينَ

    Open ayah 11:118

    Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da lalle Ya yi mutane al’umma ɗaya (a kan addini ɗaya). Ba kuwa za su gushe suna masu saɓawa juna ba.

  119. إِلَّا مَن رَّحِمَ رَبُّكَۚ وَلِذَٰلِكَ خَلَقَهُمۡۗ وَتَمَّتۡ كَلِمَةُ رَبِّكَ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 11:119

    Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama. A kan haka kuwa Ya halicce su; kuma Kalmar Ubangijinka ta tabbata (cewa): Lalle zan cika Jahannama da aljannu da mutane baki ɗaya.

  120. وَكُلّٗا نَّقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلرُّسُلِ مَا نُثَبِّتُ بِهِۦ فُؤَادَكَۚ وَجَآءَكَ فِي هَٰذِهِ ٱلۡحَقُّ وَمَوۡعِظَةٞ وَذِكۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ 

    Open ayah 11:120

    Muna labarta maka kowanne daga labarun manzanni, abin da za Mu kwantar da zuciyarka da shi. Gaskiya kuwa ta zo maka cikin wannan (Surar) da izina da gargaɗi ga muminai.

  121. وَقُل لِّلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنَّا عَٰمِلُونَ

    Open ayah 11:121

    Kuma ka ce da waɗanda ba sa yin imani: “Ku yi aiki a irin hanyarku, mu ma za mu yi aiki (a irin tamu).

  122. وَٱنتَظِرُوٓاْ إِنَّا مُنتَظِرُونَ

    Open ayah 11:122

    “Kuma ku saurara, haƙiƙa (mu ma) masu sauraro ne.”

  123. وَلِلَّهِ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ يُرۡجَعُ ٱلۡأَمۡرُ كُلُّهُۥ فَٱعۡبُدۡهُ وَتَوَكَّلۡ عَلَيۡهِۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 11:123

    Kuma (sanin) gaibu na sammai da na ƙasa na Allah ne, kuma gare Shi ake komar da dukkanin al’amari. To ka bauta masa kuma ka dogara gare Shi. Ubangijinka kuwa ba gafalalle ba ne ga abin da kuke aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cikakkiyar Ƙudurarsa ta cewa da ya ga dama da ya halicci mutane gaba ɗaya a kan manufa ɗaya ko a kan addini ɗaya ko ya halicce su muminai, ko dukkansu kafirai; to amma bai yi hakan ba, shi ya sa mutane suka zamanto koyaushe cikin sassaɓawa a tsakaninsu, saboda bin son zuciya da jahilici, sai fa wanda Ubangiji ya yi masa rahama ya nuna masa gaskiya, ya kuma ba shi ikon bin ta; to waɗannan su ne ba sa saɓawa da junansu a kan sha’anin kaɗaita Allah da bauta da gaskata manzanninsa. Kuma da man Allah ya halicce su ne don wannan jarrabawar, don haka daga cikinsu aka samu mai rabauta ya riƙi gaskiya, aka samu taɓaɓɓe wanda zai riƙi ƙarya da ɓata. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kalmarsa ta riga ta tabbata a kan lalle sai ya cika wutar Jahannama da mabiya Shaiɗan cikin mutane da aljannu. Allah kuma shi ne mai cikakkiyar hikima. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Aljanna da wuta sun yi jayayya, sai Aljanna ta ce: “Me ya sa ni babu masu shiga cikina sai raunanan mutane da marasa matsayin cikinsu?” Ita kuma wuta sai ta ce: “An zaɓa mini masu girman kai da masu nuna isa.” Sai Allah ya ce wa Aljanna: “Ke dai rahamata ce, ina yin rahama da ke ga wanda na ga dama.” Ya ce wa wuta kuma: “Ke kuma azabata ce, ina azabta wanda na ga dama da ke. Kowaccenku kuma zan cika ta.” To amma ita Aljanna sai ya zamana akwai sauran wuri a cikinta, har sai da Allah ya ƙagi wasu halittu ya zaunar da su cikin sauran wurin da bai cika ba a Aljanna. Wuta kuwa sai faɗa take yi cewa: “Shin ko akwai wani ƙari?” Har sai da Ubangiji Mabuwayi ya saka ƙafarsa a cikinta, sai ta ce: “Na rantse da Buwayarka ya isa, ya isa.” [Bukahri #4850 da Muslim #2846]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci hikimar da ke tattare da ba wa Manzon Allah ƙissoshin annabawa da cewa, duk labaran da yake ba shi na manzannin da suka gabace shi tare da al\'ummunsu, da abin da ya gudana a tsakaninsu na jayayya da musu, da juriyar da annabawan suka yi yayin da mutanensu suka ƙaryata su, suka kuma cutar da su, da yadda Allah ya taimaka wa manzanninsa tare da mabiyansu ya tserar da su ya kuma halaka maƙiyansu kafirai, duk Allah yana ambata masa waɗannan ne domin ya tabbatar masa da zuciyarsa a kan gaskiya, ya ƙarfafe ta a kan haƙuri da juriya, don ya zama mai koyi da ‘yan’uwansa annabawa da suka gabace shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar wa Manzonsa cewa, gaskiya ce ta zo masa a cikin wannan Surar wadda ta ƙunshi tarihin annabawa da al\'ummunsu, da yadda ya tserar da annabawa da muminai, ya hallaka maƙiyansu, da kuma wa’azi da tunatarwa ga mumainai da ta ƙunsa, domin su ne masu amfana da tunatarwa. Sai kuma ya umarci Manzonsa ya faɗa wa waɗanda ba su ba da gaskiya da abin da ya zo da shi daga Allah ba cewa, su yi aiki a irin hanyarsu ta kauce wa gaskiya da bijire mata, shi ma tare da waɗanda suka yi imani da shi za su yi aiki a irin hanyarsu ta dagewa a kan gaskiya da kira zuwa ga Allah da haƙuri a kan haka. Ya ƙara da cewa, su saurari abin da zai same su, shi ma tare da sahabbansa za su yi sauraro. Haƙiƙa Allah ya cika wa Manzonsa alƙawarinsa, ya taimake shi ya ba shi nasara a kan maƙiyansa, ya ɗaukaka addininsa a kan kafirci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana a ƙarshen Surar da cewa shi kaɗai ne masanin gaibu na sammai da ƙasa, kuma gare shi ne ake komar da dukkan al’amari ranar alƙiyama, don haka ya umarci Annabinsa da ya bauta masa shi kaɗai, ya dogara gare shi shi kaɗai cikin dukkan lamuransa, shi Allah ba gafalalle ne game da abin da bayinsa suke aikatawa ba, yana sane da komai, kuma zai saka wa kowa a kan ayyukansa kyawawa ko munana.