يوسف

Yusuf

Joseph · Surah 12 · Ayahs: 111 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

    Open ayah 12:1

    <ITALIC>ALIF LAM RA</ITALIC>. Waɗannan ayoyi ne na Littafi mabayyani.

  2. إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

    Open ayah 12:2

    Lalle Mu Muka saukar da shi Alƙur’ani da (harshen) Larabci don ku hankalta.

  3. نَحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ أَحۡسَنَ ٱلۡقَصَصِ بِمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ وَإِن كُنتَ مِن قَبۡلِهِۦ لَمِنَ ٱلۡغَٰفِلِينَ

    Open ayah 12:3

    Mu ne Muke labarta maka (labari) mafi kyan labartawa ta hanyar yi maka wahayin wannan Alƙur’ani, ko da yake gabaninsa kana cikin marasa sanin(sa). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa kamar yadda ya yi a wasu surori da suka gabata. Babbar hikimar da aka ambata game da waɗannan haruffa ita ce, Allah yana nuni ne da su zuwa ga mu’ujizar Alƙur’ani wanda duk masu fasahar Larabawa suka kasa kawo irinsa duk kuwa da cewa suna magana da irin haruffan da Alƙur’ani ya sauka da su. Wannan yana ƙara tabbatar da cewa Alƙur’ani maganar Allah ce ba ta wani ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa, waɗannan ayoyi da aka saukar cikin wannan Sura suna cikin bayyanannun ayoyin da wannan littafi na Alƙur’ani ya ƙunsa. Sai kuma ya bayyana wa Manzonsa cewa, shi ne ya saukar da Alƙur’ani cikin harshen Larabci domin Larabawa da sauran masu jin wannan harshe su fahimci ma’anonin da ya ƙunsa. Sai kuma ya faɗa masa cewa, shi ne zai ba shi mafi kyan labarai domin ingancinsu da kyakkyawan zubin salonsu da tsarinsu da sauƙin fahimtarsu, ta hanyar saukar masa da Alƙur’ani wanda littafi ne da babu kamarsa. Sai kuma ya tabbatar wa Manzon Allah (ﷺ) cewa, kafin ya saukar masa da wannan littafin yana cikin waɗanda ba su san komai ba game da shari’o’i da kuma ƙissoshin da ya ƙunsa.

  4. إِذۡ قَالَ يُوسُفُ لِأَبِيهِ يَٰٓأَبَتِ إِنِّي رَأَيۡتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوۡكَبٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ رَأَيۡتُهُمۡ لِي سَٰجِدِينَ

    Open ayah 12:4

    (Ka tuna) lokacin da Yusufu ya ce da babansa: “Ya babana, lalle na yi mafarkin taurari goma sha ɗaya da rana da wata, na gan su suna yi min sujjada.”

  5. قَالَ يَٰبُنَيَّ لَا تَقۡصُصۡ رُءۡيَاكَ عَلَىٰٓ إِخۡوَتِكَ فَيَكِيدُواْ لَكَ كَيۡدًاۖ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 12:5

    Ya ce: “Ya ɗana, kada ka labarta mafarkinka ga ‘yan’uwanka, sai su shirya maka makirci; lalle Shaiɗan maƙiyi ne mai bayyana ƙiyayya ga mutum.

  6. وَكَذَٰلِكَ يَجۡتَبِيكَ رَبُّكَ وَيُعَلِّمُكَ مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَعَلَىٰٓ ءَالِ يَعۡقُوبَ كَمَآ أَتَمَّهَا عَلَىٰٓ أَبَوَيۡكَ مِن قَبۡلُ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبَّكَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

    Open ayah 12:6

    “Kamar haka ne kuma Ubangijinka zai zaɓe ka Ya kuma sanar da kai wani abu daga fassarar mafarkai, Ya kuma cika ni’imarsa a gare ka da kuma ga iyalin Ya\'aƙubu kamar yadda tun tuni Ya cika ta ga iyayenka Ibrahimu da Is’haƙa. Lalle Ubangijinka Masani ne Mai hikima.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiga ba wa Annabi (ﷺ) labarin Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ‘yan’uwansa. Ya fara da mafarkin da Annabi Yusufu ya yi, ya kuma faɗa wa mahaifinsa Annabi Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Annabi Yusufu shi ne ɗan Annabi Ya’aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ɗan Annabi Is’haƙa ɗan Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Mai karamci ɗan mai karamci ɗan mai karamci, watau Yusufu ɗan Ya’aƙubu ɗan Is’haƙa ɗan Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).” [Bukhari #3390]. An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: “Wane ne cikin mutane ya fi karamci?” Sai ya ce: “Mafi karamcinsu a wurin Allah shi ne mafi tsoron Allah a cikinsu.” Sai suka ce: “Ba a kan wannan muke tambaya ba.” Sai ya ce: “Mafi karamcin mutane shi ne Yusufu, Annabin Allah ɗan Annabin Allah ɗan Annabin Allah ɗan Badaɗayin Allah….” [Bukhari #4689 da Muslim #2378]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiga ba wa Annabi (ﷺ) labarin mafarkin da Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi na taurari goma sha ɗaya da rana da wata, ya gan su sun faɗi a gabansa suna yi masa sujjada ta gaisuwa da jinjina. Da mahaifinsa ya ji wannan mafarki da ya yi sai ya gargaɗe shi tare da jan kunnensa da cewa, kada ya kuskura ya faɗa wa ‘yan’uwansa wannan mafarki domin za su fahimci abin da ya ƙunsa na fifiko da ɗaukaka da Allah zai ba shi a kansu a nan gaba, har su zo gabansa su zube suna yi masa gaisuwar ban girma. Idan kuwa suka fahimci haka to hassada za ta shiga zukatansu game da shi, sai su shiga yi masa mugun shiri da makirci wanda zai cutar da shi. Domin Shaiɗan zai yi ta zuga su saboda mummunar gabar da ke tsakaninsa da mutane. Malamai sun ambaci cewa, fassarar mafarkin Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ita ce: Taurari goma sha ɗaya yana nufin ‘yan’uwansa su goma sha ɗaya; rana kuwa na nufin mahaifiyarsa; wata kuma yana nufin mahaifinsa Annabi Ya’aƙubu. Kuma mafarkin yana nuna canjin da zai faru nan gaba a rayuwar Annabi Yusufu da zai kai shi ga samun wani babban matsayi da za su zo gabansa su faɗi su yi sujjadar girmamawa da jinjina a gare shi. Annabi Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da faɗa wa ɗansa Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, a nan gaba Allah zai zaɓe shi ya ba shi ilimin fassarar mafarki, ya kuma cika masa ni’imominsa na duniya kamar annabta da mulki da na lahira, watau kyakkyawan sakamako na gidan Aljanna, kamar yadda ya cika wa iyayensa a can baya, watau Annabi Ibrahimu da Annabi Is’haƙa. Ba shakka kuma Ubangijinsa masani ne ga komai na ɓoye da na sarari da abin da yake cikin zukatan bayinsa, mai hikima ne, yana saka komai a muhallinsa yana ba wa kowa matsayinsa. An karɓo daga Abu Ƙatada (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kyakkyawan mafarki daga Allah ne, idan ɗayanku ya yi mafarkin abin da yake so, to kada ya faɗa wa kowa sai masoyinsa; idan kuwa ya ga abin da yake ƙi a mafarki, to ya nemi tsarin Allah daga sharrin wannan mafarkin daga kuma sharrin Shaiɗan, ya yi tofi sau uku, kada kuma ya faɗa wa kowa labarin wannan mafarkin, to ba zai cutar da shi ba.” [Bukhari #7044 da Muslim #2261].

  7. ۞لَّقَدۡ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخۡوَتِهِۦٓ ءَايَٰتٞ لِّلسَّآئِلِينَ

    Open ayah 12:7

    Haƙiƙa akwai ayoyi ga matambaya dangane da (labarin) Yusufu shi da ‘yan’uwansa.

  8. إِذۡ قَالُواْ لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَىٰٓ أَبِينَا مِنَّا وَنَحۡنُ عُصۡبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

    Open ayah 12:8

    (Ka tuna) lokacin da (‘yan’uwan) suka ce: “Lalle Yusufu da ɗan’uwansa babanmu ya fi son su da mu, ga mu kuwa jama’a masu yawa. Lalle babanmu yana cikin kuskure mabayyani.

  9. ٱقۡتُلُواْ يُوسُفَ أَوِ ٱطۡرَحُوهُ أَرۡضٗا يَخۡلُ لَكُمۡ وَجۡهُ أَبِيكُمۡ وَتَكُونُواْ مِنۢ بَعۡدِهِۦ قَوۡمٗا صَٰلِحِينَ

    Open ayah 12:9

    “Ku kashe Yusufu ko kuma ku jefa shi wata ƙasa, (yin haka) zai juyo muku fuskar babanku, sai kuma ku kasance salihai bayansa.”

  10. قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ لَا تَقۡتُلُواْ يُوسُفَ وَأَلۡقُوهُ فِي غَيَٰبَتِ ٱلۡجُبِّ يَلۡتَقِطۡهُ بَعۡضُ ٱلسَّيَّارَةِ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ 

    Open ayah 12:10

    Wani mai magana daga cikinsu ya ce: “Kada ku kashe Yusufu, ku jefa shi cikin duhun kururrumar rijiya, wasu ayarin matafiya za su tsince shi, in har haka za ku yi.” A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, a game da labarin Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ‘yan’uwansa ba shakka akwai ayoyi da darussa masu ɗimbin yawa ga duk wani mai tambaya wanda zai so ya san abin da zai amfane shi ba wanda yake bijire wa gaskiya ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin lokacin da ‘yan’uwan Yusufu suka haɗu don tattaunawa da shawarwari game da lamarin alaƙar mahaifinsu Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Yusufu shi da ɗan’uwansa shaƙiƙi Binyaminu, har suke rantsuwar cewa mahaifinsu ya fi son Yusufu da ɗan’uwansa Binyaminu a kansu tare kuwa da cewa su ne jama’a, watau su suka fi yawa don haka za su fi amfani a wurinsa, amma duk da haka ya fifita son yara ƙanana a kansu, don haka suke ganin lalle mahaifinsu yana tabka babban kuskure cikin wannan lamari. Sai suka fara tunanin hanyar da za su bi wajen kawar da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga idon mahaifinsu don hankalinsa ya dawo kansu; sai wasu suka ce kamata ya yi kawai su kashe shi gaba ɗaya ko su jefar da shi can wata uwa duniya, mahaifinsu ya daina ganin sa gaba ɗaya; idan sun yi haka zai sa hankalin mahaifinsu ya dawo kansu. Su kuma in ya so daga baya sai su tuba su nemi yafiyar Allah. To amma wani daga cikinsu ya tausaya wa Annabi Yusufu, ya nuna maganar kisa ta yi tsauri, don haka maimakon kisa su kai shi su jefa shi cikin wata kururrumar rijiya, idan sun yi haka buƙatarsu ta raba shi da mahaifinsa ta samu ba tare da sun yi kisan kai ba. Ta yiwu wasu ayarin fatake su tsince shi su yi awon gaba da shi zuwa ƙasarsu mai nisa su mayar da shi bawansu, ya gama rayuwarsa a can cikinsu, su kuma su mallake zuciyar mahaifinsu su kaɗai.

  11. قَالُواْ يَٰٓأَبَانَا مَا لَكَ لَا تَأۡمَ۬نَّا عَلَىٰ يُوسُفَ وَإِنَّا لَهُۥ لَنَٰصِحُونَ

    Open ayah 12:11

    Suka ce: “Ya babanmu, me ya sa ne ba ka amince mana game da Yusufu, alhali kuwa lalle mu ba shakka masu kula da shi ne?

  12. أَرۡسِلۡهُ مَعَنَا غَدٗا يَرۡتَعۡ وَيَلۡعَبۡ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ

    Open ayah 12:12

    “Ka tura shi gobe tare da mu ya yi kiwo, ya kuma yi wasa, lalle kuma mu tabbas za Mu kiyaye shi.”

  13. قَالَ إِنِّي لَيَحۡزُنُنِيٓ أَن تَذۡهَبُواْ بِهِۦ وَأَخَافُ أَن يَأۡكُلَهُ ٱلذِّئۡبُ وَأَنتُمۡ عَنۡهُ غَٰفِلُونَ

    Open ayah 12:13

    Ya ce: “Lalle tabbas tafiyarku da shi za ta baƙanta mini rai, ina kuma tsoron kyarkeci ya cinye shi ba da saninku ba.”

  14. قَالُواْ لَئِنۡ أَكَلَهُ ٱلذِّئۡبُ وَنَحۡنُ عُصۡبَةٌ إِنَّآ إِذٗا لَّخَٰسِرُونَ

    Open ayah 12:14

    Suka ce: “Lalle idan kyarkeci ya cinye shi ga mu kuwa muna da yawa kuma majiya ƙarfi to ashe lalle mun taɓe.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da cewa, bayan ‘yan’uwan Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun amince da shawarar a jefa shi kururrumar rijiya, sai suka nufi babansu suka roƙe shi ya ba su dama su fita kiwo tare da Yusufu domin sun fahimci ba ya barin sa ya fita ko’ina tare da su. Suka nuna masa mamakinsu da har ba ya amince musu a kan Yusufu duk kuwa da cewa su masu nuna masa ƙauna ne, suna so masa duk abin da suke so wa kansu na alheri. Don haka suka roƙe shi da ya bar su gobe su fita da shi wurin kiwo shi ma ya shaƙata ya wala kamar yadda mahaifinsa yake ƙaunar ganin sa koyaushe. Suka tabbatar masa cewa lalle za su kula da shi ba za su bari wani abu ya cuce shi ba. Da mahaifinsu Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji wannan zance nasu, sai ya nuna musu cewa, saboda abubuwa biyu ne ba ya son bari su fita kiwo tare da Yusufu: Na ɗaya, zai damu idan ba ya ganin sa kusa da shi; na biyu, yana jin tsoron kada su shagala su manta da kula da shi har kyarkeci ya zo ya cinye shi suna can suna kiwonsu da harbe-harbensu. Suna jin wannan uzuri na biyu sai kawai suka riƙe shi a matsayin abin da za su kafa hujja da shi bayan sun gama aika-aikarsu. Sai ko suka tabbatar masa cewa, babu yadda za a yi su yi sakaci har kyarkeci ya cinye shi alhali ga su da yawa da ƙarfi, suka ce idan kuwa har haka ta faru to lalle sun tabka babbar hasara.

  15. فَلَمَّا ذَهَبُواْ بِهِۦ وَأَجۡمَعُوٓاْ أَن يَجۡعَلُوهُ فِي غَيَٰبَتِ ٱلۡجُبِّۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ لَتُنَبِّئَنَّهُم بِأَمۡرِهِمۡ هَٰذَا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

    Open ayah 12:15

    To lokacin da suka tafi da shi suka kuma haɗu a kan su saka shi cikin duhun kururrumar rijiya. Muka kuma yi masa wahayi (da cewa): “Wallahi (wata rana) za ka ba su labarin wannan al’amari nasu alhali su ba sa jin (haka zai faru).”

  16. وَجَآءُوٓ أَبَاهُمۡ عِشَآءٗ يَبۡكُونَ

    Open ayah 12:16

    Suka kuwa dawo wa babansu da lisha suna kuka.

  17. قَالُواْ يَٰٓأَبَانَآ إِنَّا ذَهَبۡنَا نَسۡتَبِقُ وَتَرَكۡنَا يُوسُفَ عِندَ مَتَٰعِنَا فَأَكَلَهُ ٱلذِّئۡبُۖ وَمَآ أَنتَ بِمُؤۡمِنٖ لَّنَا وَلَوۡ كُنَّا صَٰدِقِينَ

    Open ayah 12:17

    Suka ce: “Ya babanmu, mun tafi muna wasan rige muka kuma bar Yusufu wurin kayanmu, sai kyarkeci ya cinye shi. Ba kuwa za ka gaskanta mu ba ko da muna da gaskiya.”

  18. وَجَآءُو عَلَىٰ قَمِيصِهِۦ بِدَمٖ كَذِبٖۚ قَالَ بَلۡ سَوَّلَتۡ لَكُمۡ أَنفُسُكُمۡ أَمۡرٗاۖ فَصَبۡرٞ جَمِيلٞۖ وَٱللَّهُ ٱلۡمُسۡتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ

    Open ayah 12:18

    Suka kuma zo da jinin ƙarya a rigarsa. (Babansu) ya ce: “Ba haka ba ne, zuciyarku dai ta shirya muku wani abu. Saboda haka (ba ni da wani abin yi) sai haƙuri nagari; Allah kuma Shi ne wanda ake neman taimakonsa a kan abin da kuke sifantawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, Annabi Ya’aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya amince ya bar `ya`yansa sun tafi kiwo tare da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Bayan sun tafi da shi ne sai suka haɗu a kan zartar da shawararsu ta jefa shi cikin duhun kururrumar rijiya. Haka kuwa suka aikata. To bayan sun jefa shi ne Allah ya yi masa wahayi mai ƙunshe da albishir na kuɓutar da rayuwarsa da sake haɗa fuskarsa da ta ‘yan’uwansa, har kuma ya ba da labarin abin da suka ƙulla masa na mugunta da makirci a lokacin da su ba za su iya gane shi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana abin da ‘yan’uwan Yusufu suka yi bayan dawowarsu gida wurin mahaifinsu, suka yi ƙoƙarin ɓoye masa gaskiyar aika-aikar da suka yi wa Yusufu. Da farko sai suka ƙi komawa gida sai a makare bayan isha’i gari ya yi duhu, sannan suka fara kukan alhinin abin da ya sami Yusuf, wai don Annabi Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yarda da su. Daga nan suka faɗa masa uzurin ƙarya na rashin dawowa da Yusufu, watau suka ce masa ai sun bar shi ne ya tsare musu kayayyakinsu su kuma suka tafi suna wasan tsere, ba su ankara ba sai zuwa suka yi suka tarar kyarkeci ya cinye Yusufu. To amma fa a faɗarsu mai yiwuwa ne ya ƙi yarda da su ko da kuwa gaskiya suka faɗa masa, watau domin tsananin son da yake nuna wa Yusufu kuma ga shi tun farko ya nuna musu yana jin tsoron kyarkeci ya cinye shi ba tare da sun kula ba. To suna ganin Annabi Yaƙubu ba zai yarda ya gaskata wannan arashin ba. Domin su tabbatar masa da gaskiyar maganarsu sai suka zo da rigar Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) caɓa-caɓa da jini, wai wannan alama ce da ke nuna gaskiyar maganarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai nutsu da maganarsu ba, domin alamar da suka kawo masa ce ta nuna rashin gaskiyarsu. In ba haka ba, ta yaya dabbar jeji za ta cinye mutum amma ba ta yayyaga rigarsa ba? Don haka sai ya ce musu, zukatansu ne kawai suka shirya musu wani abu, shi kam babu abin da zai iya sai kyakkyawan haƙuri bisa ga wannan jarraba da Allah ya ɗora masa, kuma Allah ne mai taimakon sa a kan wannan bayani nasu marar gamsarwa.

  19. وَجَآءَتۡ سَيَّارَةٞ فَأَرۡسَلُواْ وَارِدَهُمۡ فَأَدۡلَىٰ دَلۡوَهُۥۖ قَالَ يَٰبُشۡرَىٰ هَٰذَا غُلَٰمٞۚ وَأَسَرُّوهُ بِضَٰعَةٗۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 12:19

    Da wasu ayarin matafiya suka zo sai suka tura mai nemo musu ruwa, sai ya zura gugansa (a rijiyar); sai ya ce: “Abin farin ciki ya same ni, wannan yaro ne;” suka kuma ɓoye shi a matsayin kayan kiri. Allah kuwa Masanin abin da suke aikatawa ne.

  20. وَشَرَوۡهُ بِثَمَنِۭ بَخۡسٖ دَرَٰهِمَ مَعۡدُودَةٖ وَكَانُواْ فِيهِ مِنَ ٱلزَّٰهِدِينَ 

    Open ayah 12:20

    Suka kuma sayar da shi araha da ‘yan dirhamai ƙirgaggu, suka zamanto kuma suna masu tsantsami game da shi.

  21. وَقَالَ ٱلَّذِي ٱشۡتَرَىٰهُ مِن مِّصۡرَ لِٱمۡرَأَتِهِۦٓ أَكۡرِمِي مَثۡوَىٰهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوۡ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدٗاۚ وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلِنُعَلِّمَهُۥ مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِۚ وَٱللَّهُ غَالِبٌ عَلَىٰٓ أَمۡرِهِۦ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 12:21

    Wanda ya saye shi kuma daga Masar ya ce da matarsa: “Ki kyautata mazauninsa, muna fatan ya amfane mu, ko kuwa mu riƙe shi a matsayin ɗa.” (Allah Ya ci gaba da cewa): Kamar haka Muka tabbatar da Yusufu a bayan ƙasa don kuma Mu sanar da shi fassarar mafarkai. Allah kuwa Mai rinjaye ne a bisa al’amarinsa, sai dai yawancin mutane ba sa ganewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana abin da ya faru da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bayan ‘yan’uwansa sun jefa shi cikin rijiya sun tafi sun bar shi. Yana ciki ne sai wasu ayarin matafiya zuwa Masar suka iso wurin, sai suka tura mai ɗebo musu ruwan sha, yana isa wurin rijiya sai ya jefa gugansa domin ya janyo ruwa, sai Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya riƙe igiyar gugar mutumin nan ya janyo shi yana tsammanin nauyin ruwa ne. Daga ganin kyakkyawan yaro ya fito daga rijiya sai ya shiga murna yana farin cikin ya yi tsintuwar yaro kyakkyawa. Akwai yiwuwar shekarun Yusufu a lokacin ba su fi shekara goma zuwa sha huɗu ba, amma dai bai balaga ba. Sai mutumin ya nufi ‘yan’uwansa da shi, su kuma suka ɗauke shi suka ɓoye shi a matsayin kadarar fatauci, Allah kuwa yana sane da duk abin da ke faruwa ga Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya bar shi ya ci gaba da faruwa ne saboda wata hikima tasa da ya riga ya ƙaddara. Allah ya ci gaba da bayyana mana cewa, waɗannan ayarin fatake sun isa Masar tare da Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma sun kai shi kasuwar bayi sun sayar da shi a kan ‘yan kuɗi kaɗan, watau dirhamai ƙididdigaggu, domin suna ƙyamar ci gaba da riƙe shi a wurinsu, ƙoƙarinsu dai su rabu da shi saboda sun kula ba ya da kamanni irin na bayi, kuma suna jin tsoron ‘yan’uwansa su gan shi su karɓe shi daga hannunsu. Wannan duk yana cikin rahamar Allah a gare shi, sai bai nufa ya daɗe sosai a hannunsu ba. Allah ya bayyana cewa, wani babban mutum ne a Masar ya sayi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tafi da shi gidansa ya umarci matarsa da ta kyautata masaukinsa, ta hanyar kula da cinsa da shansa da suturarsa, domin wannan mutum ya ga alamar nan gaba Yusufu zai yi musu amfani sosai saboda cikar hankalinsa da ya gani, ko ma su mayar da shi ɗansu domin ba su sami haihuwa ba. Allah ya bayyana cewa, kamar yadda ya kuɓutar da Annabi Yusufu daga kisa, ya fitar da shi daga tsohuwar rijiya, ya kuma kimsa ƙaunarsa a cikin zuciyar wannan babban mutum na Masar, to kamar haka ne ya kafa Yusufu a ƙasar Masar domin ya koyar da shi ilimin fassarar mafarki. Allah kuwa mai rinjaye ne bisa al’amarinsa, duk abin da ya ga dama shi zai wakana, babu mai tilasta shi (Mai tsarki da daukaka), sai dai yawancin mutane kafirai ba su san haka ba.

  22. وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥٓ ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 12:22

    Lokacin kuma da ƙarfinsa ya kawo sai Muka ba shi hikima da ilimi. Kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa.

  23. وَرَٰوَدَتۡهُ ٱلَّتِي هُوَ فِي بَيۡتِهَا عَن نَّفۡسِهِۦ وَغَلَّقَتِ ٱلۡأَبۡوَٰبَ وَقَالَتۡ هَيۡتَ لَكَۚ قَالَ مَعَاذَ ٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ رَبِّيٓ أَحۡسَنَ مَثۡوَايَۖ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّٰلِمُونَ

    Open ayah 12:23

    Wadda kuma yake ɗakinta ta yi ƙoƙarin ya yi lalata da ita, ta kuwa kukkulle ƙofofi, ta kuma ce: “To ka zo mana!” Ya ce: “Allah Ya kiyashe ni! Lalle shi mai gidana ne, ya kyautata mazaunina. Lalle yadda al’amarin yake su azzalumai ba sa rabauta.”

  24. وَلَقَدۡ هَمَّتۡ بِهِۦۖ وَهَمَّ بِهَا لَوۡلَآ أَن رَّءَا بُرۡهَٰنَ رَبِّهِۦۚ كَذَٰلِكَ لِنَصۡرِفَ عَنۡهُ ٱلسُّوٓءَ وَٱلۡفَحۡشَآءَۚ إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُخۡلَصِينَ

    Open ayah 12:24

    Lalle kuma ta yi niyyar ta rarumo shi, shi kuma ya yi niyyar karkata gare ta, ba don ya ga wata hujja ta Ubangijinsa ba. Kamar haka (Muka nuna masa hujjar) don Mu kawar da mummunan aiki da ɓarna daga gare shi. Lalle shi yana daga bayinmu zaɓaɓɓu.

  25. وَٱسۡتَبَقَا ٱلۡبَابَ وَقَدَّتۡ قَمِيصَهُۥ مِن دُبُرٖ وَأَلۡفَيَا سَيِّدَهَا لَدَا ٱلۡبَابِۚ قَالَتۡ مَا جَزَآءُ مَنۡ أَرَادَ بِأَهۡلِكَ سُوٓءًا إِلَّآ أَن يُسۡجَنَ أَوۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 12:25

    Suka kuma yiwo rige wajen ƙofa, sai kuwa ta yaga rigarsa daga baya, kuma suka ci karo da mijinta daf da ƙofar, ta ce: “Ba wani sakamakon da ya cancanta ga wanda ya yi nufin mummunan abu da iyalinka in ban da kawai a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa azaba mai raɗaɗi.”

  26. قَالَ هِيَ رَٰوَدَتۡنِي عَن نَّفۡسِيۚ وَشَهِدَ شَاهِدٞ مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن كَانَ قَمِيصُهُۥ قُدَّ مِن قُبُلٖ فَصَدَقَتۡ وَهُوَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

    Open ayah 12:26

    (Annabi Yusufu) ya ce: “Ita ce ta neme ni”. Wani shaida kuwa daga danginta ya shaida (cewa): “Idan an yaga rigarsa ta gaba, to ta yi gaskiya shi kuwa yana cikin masu ƙarya.

  27. وَإِن كَانَ قَمِيصُهُۥ قُدَّ مِن دُبُرٖ فَكَذَبَتۡ وَهُوَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

    Open ayah 12:27

    “Idan kuwa an yaga rigarsa ta baya, to ta yi ƙarya shi kuwa yana daga masu gaskiya.”

  28. فَلَمَّا رَءَا قَمِيصَهُۥ قُدَّ مِن دُبُرٖ قَالَ إِنَّهُۥ مِن كَيۡدِكُنَّۖ إِنَّ كَيۡدَكُنَّ عَظِيمٞ

    Open ayah 12:28

    To yayin da (mijin nata) ya ga an yaga rigarsa ta baya ne, sai ya ce: “Lalle wannan yana daga irin makircinku; lalle makircinku kuwa yana da girma.”

  29. يُوسُفُ أَعۡرِضۡ عَنۡ هَٰذَاۚ وَٱسۡتَغۡفِرِي لِذَنۢبِكِۖ إِنَّكِ كُنتِ مِنَ ٱلۡخَاطِـِٔينَ

    Open ayah 12:29

    “Kai Yusufu, ka kau da kai daga wannan (magana). Ke kuma ki nemi gafarar laifinki, lalle ke kin zamanto daga masu laifi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata sabuwar jarraba da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fuskanta wadda ta fi ta cikin rijiya hatsari. Watau yayin da Yusufu ya isa ganiyar ƙarfinsa, hankalinsa ya gama cika, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi hukunci da ilimi na annabta daga gare shi, domin yana cikin bayin Allah waɗanda suka kyautata ayyukan ibadarsu ga Allah, kuma irin wannan sakamako Allah yake yi wa irin waɗannan bayi nasa. To a sakamakon wancan matsayi na annabta da ilimi da Allah ya ba wa Yusufu ne wannan jarabawar ta biyo baya. Watau uwar ɗakinsa wadda yake ƙarƙashinta ita ce ta neme shi da yin lalata da ita saboda irin kyan halitta da Allah ya yi masa a lokacin babu wani ɗa namiji da ya sami kamarta. Sai ta kukkulle ƙofofi ta yadda babu ta inda zai gudu, kuma babu wanda zai iya shigowa inda suke, don haka ko mene ne zai faru a nan babu wanda zai sani har ya ɗorar gaba. Sai ko ta shiga kiran sa tana neman ya matso jikinta. Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai yi wata-wata ba ya mayar mata da amsa yana mai neman Allah ya tsare shi daga aikata wannan mummunan aiki, ya nuna mata cewa, yin haka cin amanar mai gidansa ne wanda ya kyautata masa iya kyautatawa, ya ɗauke shi a matsayin ɗansa ya yi masa duk abin da uba yake yi wa ɗansa; to ta yaya shi kuma zai saka masa da cin amanarsa? Idan har ya yi haka to ya tabbata azzalumi, don haka ba zai taɓa rabauta ba, domin azzalumai sam ba sa samun wani rabo. To amma duk da haka ba ta ƙyale shi ba, domin ta riga ta sa shi a ranta, shi ma abin ya fara ɗarsa masa a zuciya, to amma ya ga ayoyin Ubangijinsa waɗanda ba za su taɓa ƙyale shi har ya aikata irin wannan ɗanyen aiki ba. Allah ya kawar da shi daga aikata mummunan aiki da alfasha, saboda shi mutum ne da Allah ya tsarkake masa zuciya shi ma ya tsarkake ibadarsa ga Allah kaɗai. Yayin da Yusufu ya fuskanci yadda matar nan ta dage a kan mummunar buƙatarta sai ya yi ƙoƙarin gudu ya nufi ƙofa a guje, ita kuma ta bi shi tare da ƙoƙarin kawo masa raruma har ta yaga masa riga ta baya. A daf da ƙofa ne suka yi kiciɓis da mijinta zai shigo. To nan da nan sai ta shirya makircin wanke kanta daga tuhuma, ta bayyana wa mijinta wai Yusufu ne ya neme ta da lalata, har ma nan take ta bayyana irin hukuncin da ya wajaba a yi masa, watau a ɗaure shi a kurkuku ko a gana masa mummunar azaba. Amma ba ta ambaci kisa ba domin tsananin son da take wa Yusufu. To a nan ne Annabi Yusufu shi ma ya fito ya kare kansa, ya faɗi gaskiyar abin da ya faru, ya bayyana cewa, ita ce ta neme shi, ba shi ne ya neme ta ba. Daga nan sai mai gidanta ya kasa tantance mai gaskiya a cikinsu, domin ba zai iya tuhumar Annabi Yusufu ba saboda ya san shi ya san kyawawan halayensa tun yana ƙarami. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nufi kawo wanda zai yi shaida daga cikin danginta wanda ya bayyana mai gaskiya a cikinsu, ya ce a duba rigar Yusufu a gani, idan ta gaba ta yage, to wannan alama ce da ke nuna shi ne ya kai mata farmaki ita kuma wajen kare kanta har ta yaga masa riga, don haka ita ce mai gaskiya. Idan kuwa ta baya ne rigar ta yage, to wannan alama ce da ke nuna ita ce ta kai masa cacuma shi kuwa ya juya yana neman tserewa har ta yaga masa riga ta baya, don haka a nan shi ne mai gaskiya. Ana duba rigar Annabi Yusufu kuwa sai aka ga ta baya ne ta yage, sai nan take mai gidan Yusufu ya tabbatar da shi ne mai gaskiya, wannan kawai wani makirci ne matar ta ƙulla masa, sai ya ce mata wannan makircinta ne don ta shirya wa Yusufu ƙazafi, domin mata suna da makirci ba ƙanƙani ba. Daga nan ya roƙi Annabi Yusufu da ya yi watsi da wannan maganar kada ya ɗaga ta ga kowa domin ya rufa wa iyalansa asiri. Ya juya wajen matar ita kuma ya umarce ta da ta tuba ga Allah a kan laifinta na neman Yusufu da ta yi da kuma ƙazafi da ta yi masa, ya ce mata lalle ta tabbata cikin masu laifi.

  30. ۞وَقَالَ نِسۡوَةٞ فِي ٱلۡمَدِينَةِ ٱمۡرَأَتُ ٱلۡعَزِيزِ تُرَٰوِدُ فَتَىٰهَا عَن نَّفۡسِهِۦۖ قَدۡ شَغَفَهَا حُبًّاۖ إِنَّا لَنَرَىٰهَا فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ 

    Open ayah 12:30

    Waɗansu mata kuma a cikin garin suka ce: “Matar Azizu tana neman yaron gidanta; tsananin son sa ya rufe mata zuciya; lalle mu dai muna ganin ta a kan kuskure mabayyani.”

  31. فَلَمَّا سَمِعَتۡ بِمَكۡرِهِنَّ أَرۡسَلَتۡ إِلَيۡهِنَّ وَأَعۡتَدَتۡ لَهُنَّ مُتَّكَـٔٗا وَءَاتَتۡ كُلَّ وَٰحِدَةٖ مِّنۡهُنَّ سِكِّينٗا وَقَالَتِ ٱخۡرُجۡ عَلَيۡهِنَّۖ فَلَمَّا رَأَيۡنَهُۥٓ أَكۡبَرۡنَهُۥ وَقَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّ وَقُلۡنَ حَٰشَ لِلَّهِ مَا هَٰذَا بَشَرًا إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا مَلَكٞ كَرِيمٞ

    Open ayah 12:31

    Lokacin da ta ji irin tsegungumansu, sai ta aika musu (da gayyata), ta kuma tanadar musu wurin zaman cin abinci, kuma ta bai wa kowacce ɗayarsu wuƙa, ta kuma ce (da Annabi Yusufu): “Fita ka gilma ta gabansu.” Lokacin da suka gan shi sai suka girmama shi suka yanyanke hannayensu, suka kuma ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah; ai wannan ba mutum ba ne; wannan babban mala’ika ne kawai!”

  32. قَالَتۡ فَذَٰلِكُنَّ ٱلَّذِي لُمۡتُنَّنِي فِيهِۖ وَلَقَدۡ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفۡسِهِۦ فَٱسۡتَعۡصَمَۖ وَلَئِن لَّمۡ يَفۡعَلۡ مَآ ءَامُرُهُۥ لَيُسۡجَنَنَّ وَلَيَكُونٗا مِّنَ ٱلصَّٰغِرِينَ

    Open ayah 12:32

    Ta ce: “To wannan shi ne wanda kuka zarge ni a kansa. Haƙiƙa kuma na neme shi sai ya ƙi yarda; Wallahi kuwa in bai aikata abin da na umarce shi ba, to za a sa shi kurkuku, kuma lalle zai zamanto cikin wulaƙantattu.”

  33. قَالَ رَبِّ ٱلسِّجۡنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِۖ وَإِلَّا تَصۡرِفۡ عَنِّي كَيۡدَهُنَّ أَصۡبُ إِلَيۡهِنَّ وَأَكُن مِّنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ

    Open ayah 12:33

    (Annabi Yusufu) Ya ce: “Ya Ubangijina, kurkuku shi ya fi soyuwa a gare ni kan abin da suke nema na da shi. Idan kuwa ba Ka ije mini makircinsu ba, to zan karkata gare su kuma in zama cikin jahilai.”

  34. فَٱسۡتَجَابَ لَهُۥ رَبُّهُۥ فَصَرَفَ عَنۡهُ كَيۡدَهُنَّۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

    Open ayah 12:34

    To sai Ubangijinsa Ya amsa masa, sai Ya ije masa makircin nasu. Lalle Shi ne Mai ji kuma Masani.

  35. ثُمَّ بَدَا لَهُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا رَأَوُاْ ٱلۡأٓيَٰتِ لَيَسۡجُنُنَّهُۥ حَتَّىٰ حِينٖ

    Open ayah 12:35

    Sannan bayan duk sun ga ayoyin (da suke wanke Yusufu daga zargi) sai suka ga dai cewa lalle gara su ɗaure shi har zuwa wani lokaci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, labarin Yusufu da matar Azizu ya cika garin Misra har ya kai kunnen matan manyan gari, suka haɗu suna gulmarta, suna mamakin a ce mace mai daraja da matsayi irin nata amma tana neman yaron gidanta; lalle sonsa ya shiga har cikin ƙoƙon zuciyarta, ta kasa danne shi, lalle a faɗarsu, tana kan babban kuskure. Duk kuwa suna wannan tsegunguma ne domin suna so su ma su ga Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), su ga irin kyan halittar da Allah ya yi masa, shi ya sa suka shirya wannan makircin, don labari ya je kunnen matar Azizu, ta ji haushi ta ba su damar su gan shi. To lokacin da ta ji wannan suka da suke yi mata da gulmar da suke yi sai ta aika musu goron gayyata don su zo su ga Yusufu su kuma fahimci hanzarinta. Ta shirya musu wurin zama na alfarma wanda aka cika shi da shimfiɗu da matasan kai iri-iri, sannan ga abinci kala-kala, ciki har da waɗanda sai an yi amfani da wuƙa kafin a ci. Ta ba wa kowace mace wuƙa a hannunta don yanka abinci, sannan ta umarci Yusufu ya fito daga inda ta zaunar da shi ya gilma ta gaban waɗannan matan su ga irin tsananin kyansa da kwarjininsa da sheƙin da yake yi. Ai kuwa yana fitowa suka yi ido huɗu da shi sai suka kiɗime, suka ruɗe, suka shiga yayyanke hannayensu da wuƙaƙe suna tsammanin abinci suke yankawa saboda tsananin kiɗimewa, suka shiga tsarkake Allah mahaliccinsa, suka ce wannan ba mutum ne ba; wani mala’ika ne mai daraja. Ya tabbata a hadisin Mi’irajin Annabi (ﷺ) cewa, ya wuce ta wajen Annabi Yusufu a sama ta uku, ya gan shi an ba shi rabin kyau. [Muslim #162]. Lokacin da suka tantance irin tsananin kyan da Allah ya ba Yusufu, su ma sai tsananin sonsa ya ratsa zukatansu har suka ɗimauce. To a nan ne matar Azizu ta nufi bayyana musu kyan halinsa wanda su ba su sani ba, ta bayyana musu a fili cewa, wannan shi ne yaron da suke zargin ta a kansa, kuma tabbas ita ce ta neme shi tun farko amma ya ƙi yarda da buƙatarta. Sannan a gabansu ta yi masa barazana cewa idan har bai aikata abin da ta nema daga wajensa ba, to tabbas sai an kai shi kurkuku an tsare, kuma sai ya ga wulaƙanci. Daga nan sai waɗannan mata suka shiga roƙon sa da ya amsa wa uwar gidansa ya yi mata abin da take nema. Jin haka ya sa Annabi Yusufu ya shiga addu’a yana neman kariya daga Allah, yana faɗa wa Ubangiji cewa, ya gwammace a kai shi kurkuku a tsare a kan ya amince wa abin da suke roƙo a wajensa, ya roƙe shi da ya kawar masa da makircinsu don gudun kada ya faɗa cikin tarkonsu ya sami kansa cikin jahilai, waɗanda suke fifita jin daɗin duniya a kan na lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ya karɓi addu’ar Yusufu, ya kawar masa da makircinsu, lalle Allah mai jin addu’o’in bayinsa ne, masanin halayen da suke ciki. Bayan Allah ya kuɓutar da Yusufu daga wannan jarrabawar, labarinsa kuma duk ya bazu a cikin garin Misra, sai Azizu da mutanensa suka yanke shawarar su saka Yusufu a kurkuku duk kuwa da sun ga ayoyi da dalilai masu nuna ba shi da laifin komai, saboda kawai su ɓoye abin kunyar da matar Azizu ta tabka, domin idan ba a ganin Yusufu yana yawo to maganar za ta mutu. Sai suka ɗaure shi zuwa wani lokaci da ba su iyakance shi ba.

  36. وَدَخَلَ مَعَهُ ٱلسِّجۡنَ فَتَيَانِۖ قَالَ أَحَدُهُمَآ إِنِّيٓ أَرَىٰنِيٓ أَعۡصِرُ خَمۡرٗاۖ وَقَالَ ٱلۡأٓخَرُ إِنِّيٓ أَرَىٰنِيٓ أَحۡمِلُ فَوۡقَ رَأۡسِي خُبۡزٗا تَأۡكُلُ ٱلطَّيۡرُ مِنۡهُۖ نَبِّئۡنَا بِتَأۡوِيلِهِۦٓۖ إِنَّا نَرَىٰكَ مِنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 12:36

    Wasu samari su biyu kuma suka shiga kurkukun tare da shi; ɗaya daga cikinsu ya ce: “Lalle na yi mafarki ina matsar giya.” Ɗayan kuma ya ce: “Lalle na yi mafarki ina ɗauke da gurasa a kaina, tsuntsaye suna caccakar ta. Ba mu labarin fassararsa; lalle muna ganin ka kana cikin mutane nagari.”

  37. قَالَ لَا يَأۡتِيكُمَا طَعَامٞ تُرۡزَقَانِهِۦٓ إِلَّا نَبَّأۡتُكُمَا بِتَأۡوِيلِهِۦ قَبۡلَ أَن يَأۡتِيَكُمَاۚ ذَٰلِكُمَا مِمَّا عَلَّمَنِي رَبِّيٓۚ إِنِّي تَرَكۡتُ مِلَّةَ قَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ

    Open ayah 12:37

    Ya ce: “Babu wani abinci da za a kawo muku sai na iya ba ku labarinsa tun ma kafin a kawo muku shi. Wannan yana daga abin da Ubangijina Ya sanar da ni; lalle ni na bar hanyar mutanen da ba sa ba da gaskiya da Allah, su kuma suna masu kafircewa da ranar lahira.

  38. وَٱتَّبَعۡتُ مِلَّةَ ءَابَآءِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ مَا كَانَ لَنَآ أَن نُّشۡرِكَ بِٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ عَلَيۡنَا وَعَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ

    Open ayah 12:38

    “Na kuma bi hanyar iyayena Ibrahimu da Is’haƙa da kuma Yaƙubu. Bai kamace mu ba a ce mu tara wani abu da Allah. Wannan yana daga falalar Allah a gare mu da kuma sauran mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa godewa.

  39. يَٰصَٰحِبَيِ ٱلسِّجۡنِ ءَأَرۡبَابٞ مُّتَفَرِّقُونَ خَيۡرٌ أَمِ ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ

    Open ayah 12:39

    “Ya abokaina na kurkuku, yanzu iyayen giji barkatai su suka fi, ko kuwa Allah Ɗaya Mai rinjaye?

  40. مَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ أَسۡمَآءٗ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِ أَمَرَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ 

    Open ayah 12:40

    “Ba komai kuke bauta wa ba- bayan Allah- sai wasu sunaye da kuka ƙaga ku da iyayenku, waɗanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba. Hukunci na Allah ne kawai; Ya yi umarni cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi kaɗai. Wannan shi ne addini miƙaƙƙe, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka).

  41. يَٰصَٰحِبَيِ ٱلسِّجۡنِ أَمَّآ أَحَدُكُمَا فَيَسۡقِي رَبَّهُۥ خَمۡرٗاۖ وَأَمَّا ٱلۡأٓخَرُ فَيُصۡلَبُ فَتَأۡكُلُ ٱلطَّيۡرُ مِن رَّأۡسِهِۦۚ قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ ٱلَّذِي فِيهِ تَسۡتَفۡتِيَانِ

    Open ayah 12:41

    “Ya abokaina na kurkuku, amma ɗaya daga cikinku zai riƙa shayar da mai gidansa giya ne; amma ɗaya kuwa za a tsire shi ne, sannan tsuntsaye su zo su riƙa cakar kansa. An zartar da al’amarin da kuke fatawa game da shi.”

  42. وَقَالَ لِلَّذِي ظَنَّ أَنَّهُۥ نَاجٖ مِّنۡهُمَا ٱذۡكُرۡنِي عِندَ رَبِّكَ فَأَنسَىٰهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ ذِكۡرَ رَبِّهِۦ فَلَبِثَ فِي ٱلسِّجۡنِ بِضۡعَ سِنِينَ

    Open ayah 12:42

    Kuma ya ce wa wanda ya tabbatar da cewa shi zai tsira daga cikinsu: “Ka tuna wa mai gidanka ni;” sai Shaiɗan ya mantar da shi tuna wa mai gidan nasa, sai ya zauna a kurkuku ‘yan shekaru. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) an kai shi kurkuku har kuma ya shahara wurin abokan zamansa a kurkuku da riƙon gaskiya da kyautatawa da amana da ilimin fassarar mafarki. To a kan haka ne wasu samari su biyu waɗanda suka shiga kurkuku tare da shi, har ma sun saba da shi, ɗayansu mai shayar da Sarki giya ne, na biyun kuwa mai dafa masa abinci ne. Sai mai shayar da Sarki ya ce wa Yusufu, shi ya yi mafarki yana matsar inabin giya, ɗayan kuwa ya ce shi ya yi mafarki yana ɗauke da gurasa a kansa, tsuntsaye suna tsattsaga, don haka suka roƙi Yusufu da ya taimaka ya fassara musu mafarkansu saboda sun kula shi mutumin kirki ne. Ganin wannan dama ta samu ta sa Yusufu ya yi amfani da ita wajen kirawo su zuwa ga Tauhidi da barin shirka da Allah. Ya fara yi musu shimfiɗa da ba su labarin ni’imomin da Allah ya yi masa shi da iyayensa, ya nuna musu cewa, ban da sanin fassarar mafarki da ya yi, yana da wata baiwa da Allah ya yi masa, watau duk wani abinci da za a kawo musu, to yana iya ba su labarinsa tun kafin ya iso gare su, ya kuma sanar da su cewa, wannan ilimin nasa daga Allah ne ba tsafi ko duba ba ne. Ya ci gaba da faɗa musu cewa, shi ya bar addinin mutanen da ba sa yin imani da Allah kuma suna kafirce wa ranar lahira, shi kuma ya bi addinin iyayensa ne annabawan Allah, Ibrahimu da Ishaƙa da Yaƙubu, shi ne addinin kaɗaita Allah da bauta, ya tabbatar musu da cewa bai dace a gare su ba su haɗa Allah da wani abu wajen bautarsa ko a siffofinsa, ya ce musu wannan falala ce da Allah ya yi musu, ya sanya su annabawa masu kira zuwa ga addininsa, da kuma mutane ta hanyar aiko musu da manzanni domin su karantar da su addinin gaskiya, to amma yawancin mutane ba sa yi wa Allah godiya a kan wannan babbar ni’ima sai dai su butulce masa su kama hanyar ƙarya. To bayan Annabi Yusufu ya yi musu wannan shimfiɗar sai ya dawo kansu ya kirawo su zuwa ga Tauhidi da watsar da abubuwan da suke bauta wa ba Allah ba, ya kirawo su da abokan zamansa a kurkuku’ domin su ƙara nutsuwa da shi, ya nuna musu cewa, yanzu waɗannan abubuwan bauta barkatai da suka riƙe waɗanda ba za su iya tsinana musu komai a rayuwarsu ba, kuma ba sa cutar da su ba sa iya amfanar su, yanzu su suka fi alheri gare su ko kuma Allah Ɗaya wanda ya siffantu da siffofi na kamala, wanda ba shi da abokin tarayya, kuma mai rinjaye a kan kowa da komai, wanda abin da ya ga dama shi ne yake wakana, wanda bai ga dama ba kuma ba zai wakana ba? Ya ci gaba da bayyana musu cewa, ba komai suke bautawa ba sai wasu sunayen da su ne da iyayensu suka ƙirƙire su, babu wata hujja da suke da ita daga Allah a kan cewa waɗannan abubuwa alloli ne a bauta musu, domin kuwa hukunci na Allah ne shi kaɗai, ba nasu ba, ba kuma na iyayensu ba; shi ne kuma ya umarce su da kada su bauta wa kowa sai shi kaɗai. Annabi Yusufu ya tabbatar musu da cewa, waɗannan bayanai da suke ji daga bakinsa shi ne miƙaƙƙen addini, duk wani addinin da ba shi ba karkatacce ne, sai dai yawancin mutane ba su san haka ba, don haka suke bauta wa wasu ba Allah ba. Bayan Annabi Yusufu ya gama yi musu wannan bayani sai kuma ya juyo kan maganar fassarar mafarkinsu, ya sake kiran su da ‘abokan zamansa a kurkuku’, ya faɗa musu cewa, wanda ya yi mafarki yana matsar inabin giya, to za a fitar da shi daga kurkuku, zai kuma koma aikinsa na shayar da Sarki giya. Amma wanda ya yi mafarkin yana ɗauke da gurasa a kansa tsuntsaye suna caccakar ta, to shi za a yanke masa hukuncin kisa a kuma gicciye shi har ya ruɓe tsuntsaye su riƙa caccakar naman kansa da ƙwaƙwalwarsa. Ya ce musu, wannan ita ce fatawar da suka nema wajensa, haka abin zai faru babu makawa. Daga nan sai Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nemi wanda ya tabbatar shi ne zai kuɓuta ya koma aikinsa na gidan Sarki, idan ya kuɓuta to ya tayar wa da Sarki maganarsa ko zai sake bincike a kai har ya gano gaskiyar lamarin. To amma sai Shaiɗan ya mantar da wannan mutum ya tayar da maganar Annabi Yusufu a wurin Sarki, wannan ya jawo Annabi Yusufu ya ƙara wani adadin shekaru a cikin kurkuku.

  43. وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ إِنِّيٓ أَرَىٰ سَبۡعَ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعَ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖۖ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ أَفۡتُونِي فِي رُءۡيَٰيَ إِن كُنتُمۡ لِلرُّءۡيَا تَعۡبُرُونَ

    Open ayah 12:43

    Sarki kuma ya ce (da jama’arsa): “Lalle na yi mafarkin shanu guda bakwai masu ƙiba da wasu bakwan ƙanjamammu suna cinye su da kuma zangarnu guda bakwai koraye da wasu bakwai busassu. Ya ku manyan malamai, ku sanar da ni fassarar mafarkin nan nawa in kun iya fassara mafarki.”

  44. قَالُوٓاْ أَضۡغَٰثُ أَحۡلَٰمٖۖ وَمَا نَحۡنُ بِتَأۡوِيلِ ٱلۡأَحۡلَٰمِ بِعَٰلِمِينَ

    Open ayah 12:44

    Suka ce: “Ai (wannan) kwashe-kwashen mafarki ne (kawai); mu kuma ba masana fassarar mafarki ne ba.”

  45. وَقَالَ ٱلَّذِي نَجَا مِنۡهُمَا وَٱدَّكَرَ بَعۡدَ أُمَّةٍ أَنَا۠ أُنَبِّئُكُم بِتَأۡوِيلِهِۦ فَأَرۡسِلُونِ

    Open ayah 12:45

    Wanda kuwa ya tsiran nan daga cikinsu, ya kuma tuna bayan zamani mai tsawo, ya ce: “Ni zan ba ku labarin fassararsa; to ku aike ni.”

  46. يُوسُفُ أَيُّهَا ٱلصِّدِّيقُ أَفۡتِنَا فِي سَبۡعِ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعِ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖ لَّعَلِّيٓ أَرۡجِعُ إِلَى ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 12:46

    (Ya zo kurkuku ya ce): “Ya Yusufu, ya mai riƙon gaskiya, ka ba mu fatawar (mafarki) game da shanu bakwai masu ƙiba ga wasu bakwan ƙanjamammu suna cinye su, da kuma zangarnu guda bakwai korayr da wasu bakwai busassu, don in koma wajen mutanen (da suka turo ni) saboda su sani.”

  47. قَالَ تَزۡرَعُونَ سَبۡعَ سِنِينَ دَأَبٗا فَمَا حَصَدتُّمۡ فَذَرُوهُ فِي سُنۢبُلِهِۦٓ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تَأۡكُلُونَ

    Open ayah 12:47

    (Annabi Yusufu) ya ce: “Za ku yi noma shekara bakwai a jere; to abin da kuka girba sai ku bar shi a zangarniyarsa, sai kaɗan daga abin da za ku ci.

  48. ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ سَبۡعٞ شِدَادٞ يَأۡكُلۡنَ مَا قَدَّمۡتُمۡ لَهُنَّ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تُحۡصِنُونَ

    Open ayah 12:48

    “Sannan bayan wannan wasu (shekarun) bakwai masu tsanani za su zo su cinye abin da kuka tanada a cikinsu, sai ɗan kaɗan daga abin da kuke adanawa.

  49. ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ عَامٞ فِيهِ يُغَاثُ ٱلنَّاسُ وَفِيهِ يَعۡصِرُونَ

    Open ayah 12:49

    “Sannan kuma wata shekara za ta zo wadda a cikinta ne mutane za su sami ruwa, a cikinta ne kuma za su tatsi (abubuwan sha).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana fassarar mafarkin da Sarkin Misra ya yi wanda ya zamanto shi ne sanadiyyar fitowar Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga kurkuku, ya kuma zama dalilin ɗaukakarsa a idon Sarki da jama’arsa. Sarkin Misra ya yi mafarkin shanu masu ƙiba guda bakwai da kuma wasu guda bakwai ƙanjamammu, amma kuma su ne suke cinye masu ƙibar. Sannan ya ga wasu zangarnu koraye guda bakwai da wasu bakwai busassu; don haka sai ya tara bokayensa da manyan gari ya nemi su fassara masa wannan mafarkin nasa mai rikitarwa. To amma sai suka nuna masa cewa, wannan kawai kwashe-kwashen mafarkai ne waɗanda ba su da wata fassara, kuma su ma ba su da ilimin fassarar mafarkai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa, saurayin nan wanda ya samu kuɓuta daga kurkuku, watau mai shayar da Sarki sai ya tuna da Annabi Yusufu bayan tsawon lokaci, sai ya je ya sami Sarki ya ce masa shi zai sanar da shi fassarar mafarkinsa bayan ya tambayo Yusufu idan Sarki ya yi masa izinin zuwa wajensa. Sarki ya ba shi izinin zuwa wurin Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya je ya kirawo shi da sunansa ya siffanta shi da mai yawan gaskiya, ya ba shi labarin mafarkin Sarki, ya roƙe shi ya fassara masa shi domin ya koma ya sanar da shi da jama’arsa. Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ba da fassarar mafarkin Sarki tare da bayyana mafita game da matsalar da take tattare da shi, inda ya ce: Mutanen Misra za su yi shekara bakwai a jere suna noma cikin nasara, to duk abin da suka girbe a kowace shekara su bar shi cikin zangarniyarsa don kada ƙwari su lalata shi sai ɗan kaɗan wanda za su yi amfani da shi, shi ne za su sussuke. To bayan wucewar waɗannan shekaru bakwai masu yalwa ne za a kuma samu wasu shekaru bakwai na fari, a cikinsu mutane za su yi ta cinye abin da suka tara a waɗancan shekarun bakwai masu yalwa, ba za su bar komai ba sai abin da za su ɓoye na iri. Bayan waɗannan shekarun na fari kuma sai wata shekara ta zo wadda a cikinta ne mutane za su sami ruwan sama mai yawa, shukokinsu su yi kyau matuƙa, mutane su sami abinci isasshe har ma da wanda za su riƙa tatsewa kamar inabi da zaitun da rake da makamantansu.

  50. وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ ٱئۡتُونِي بِهِۦۖ فَلَمَّا جَآءَهُ ٱلرَّسُولُ قَالَ ٱرۡجِعۡ إِلَىٰ رَبِّكَ فَسۡـَٔلۡهُ مَا بَالُ ٱلنِّسۡوَةِ ٱلَّٰتِي قَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّۚ إِنَّ رَبِّي بِكَيۡدِهِنَّ عَلِيمٞ 

    Open ayah 12:50

    Sarki kuwa ya ce: “Ku zo min da shi.” Lokacin da ɗan aiken ya zo masa (ya ce Sarki na kira), sai ya ce: “Koma wurin mai gidanka ka tambaye shi, mene ne halin matan da suka yanyanke hannayensu? Lalle Ubangijina Yana sane da makircinsu.”

  51. قَالَ مَا خَطۡبُكُنَّ إِذۡ رَٰوَدتُّنَّ يُوسُفَ عَن نَّفۡسِهِۦۚ قُلۡنَ حَٰشَ لِلَّهِ مَا عَلِمۡنَا عَلَيۡهِ مِن سُوٓءٖۚ قَالَتِ ٱمۡرَأَتُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡـَٰٔنَ حَصۡحَصَ ٱلۡحَقُّ أَنَا۠ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفۡسِهِۦ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

    Open ayah 12:51

    (Sarki) ya ce: “Mene ne labarinku lokacin da kuka nemi Yusufu da lalata?” Suka ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah; ba mu san wani mummunan abu game da shi ba.” Matar Azizu ta ce: “Yanzu kam gaskiya ta bayyana; ni ce da kaina na nemi lalata da shi; lalle kuma shi yana cikin masu gaskiya.

  52. ذَٰلِكَ لِيَعۡلَمَ أَنِّي لَمۡ أَخُنۡهُ بِٱلۡغَيۡبِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي كَيۡدَ ٱلۡخَآئِنِينَ

    Open ayah 12:52

    “Wannan kuwa don ya san cewa ni ban ha’ince shi a bayan idonsa, kuma lalle Allah ba Ya shiryar da makircin masu ha’inci.

  53. ۞وَمَآ أُبَرِّئُ نَفۡسِيٓۚ إِنَّ ٱلنَّفۡسَ لَأَمَّارَةُۢ بِٱلسُّوٓءِ إِلَّا مَا رَحِمَ رَبِّيٓۚ إِنَّ رَبِّي غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 12:53

    “Ba kuma wai ina wanke kaina ba ne. Babu shakka ɗabi’ar rai ce ta umarci mutum da yin mummunan abu, sai fa wanda Ubangijina Ya yi wa jin ƙai. Lalle Ubangijina Mai gafara ne Mai jin ƙai.”

  54. وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ ٱئۡتُونِي بِهِۦٓ أَسۡتَخۡلِصۡهُ لِنَفۡسِيۖ فَلَمَّا كَلَّمَهُۥ قَالَ إِنَّكَ ٱلۡيَوۡمَ لَدَيۡنَا مَكِينٌ أَمِينٞ

    Open ayah 12:54

    Sarki kuma ya ce: “Ku zo min da shi in mai da shi ɗan-gaban-goshina.” Lokacin da ya yi magana da shi sai ya ce: “Lalle kai kam a yau kana da matsayi (babba, kuma kai) amintacce ne a wurinmu!”

  55. قَالَ ٱجۡعَلۡنِي عَلَىٰ خَزَآئِنِ ٱلۡأَرۡضِۖ إِنِّي حَفِيظٌ عَلِيمٞ

    Open ayah 12:55

    (Yusufu) Ya ce: “Ka naɗa ni mai kula da taskokin ƙasa, lalle ni mai kiyaye (amana) ne, masani.”

  56. وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَتَبَوَّأُ مِنۡهَا حَيۡثُ يَشَآءُۚ نُصِيبُ بِرَحۡمَتِنَا مَن نَّشَآءُۖ وَلَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 12:56

    Kamar haka ne Muka kafa Yusufu a bayan ƙasa; yana zama a cikinta inda ya ga dama. Muna bayar da rahamarmu ga wanda Muka ga dama, ba kuwa za Mu tozarta ladan masu kyautatawa ba.

  57. وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

    Open ayah 12:57

    Kuma lalle ladan lahira shi ya fi ga waɗanda suka yi imani kuma suka zamanto suna kiyaye dokokin (Allah). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana abin da ya biyo bayan fassarar mafarkin Sarki da Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi. Sarki ya yi matuƙar farin ciki da wannan fassarar har ma ya nemi a je a zo masa da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). To lokacin da ɗan aike ya isar da kiran Sarki ga Annabi Yusufu sai ya nuna ba zai amsa wannan kiran ba har sai Sarki ya nemo matan da suka yi masa sharri har aka ɗaure shi, ya sake bincikar su game da wannan zargin, domin da man makirci ne suka shirya masa tare da goyon bayan matar Azizu, kuma Allah yana sane da wannan makirci nasu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Da ni ne na daɗe a kurkuku kamar yadda Yusufu ya daɗe to da na amsa kiran mai kira.” Watau manzon Sarki. [Bukhari #3372 da Muslim #151]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) daga Manzon Allah (ﷺ) game da faɗar Allah: “Lokacin da ɗan aike ya zo masa sai ya ce: ‘Ka koma wurin mai gidanka ka tambaye shi mene ne halin matan da suka yayyanke hannayensu? Lalle Ubangijina masani ne ga makircinsu.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Da ni ne shi da na amsa kira da gaggawa, da ban nemi yankan hanzari ba.” [Ahmad #8554]. Da aka sanar da Sarki amsar Annabi Yusufu, sai ya sa aka tara masa waɗannan matan ya tambaye su labarinsu game da Yusufu lokacin da suka neme shi domin aikata lalata da shi. Nan take suka wanke Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga zargin da ake yi masa, suka tabbatar wa da Sarki cewa ba su taɓa sanin sa da wani mummunan abu ba. To a nan ne ita ma matar Azizu ta fito ta faɗi gaskiyar abin da ya faru tsakaninta da shi, cewa, ita ce da kanta ta nemi Yusufu, amma shi lalle yana cikin mutane masu gaskiya a duk lamurransa. Ta kuma ce ta yi wannan iƙirari ne a gaban Sarki don Yusufu ya san ba za ta ci amanarsa ba a bayan idonsa, domin Allah ba ya shiryar da makircin maciya amana. Matar Azizu ta ƙara da cewa, wannan magana da take yi ba wai tana wanke kanta ne daga laifukan da ta aikata ba, lalle ta san cewa koyaushe rai yana umartar mutum da mummunan aiki ne, sai fa wanda Allah ya ji ƙan sa ya kuɓutar da shi, lalle kuma Allah Ubangiji mai gafara ne mai jin ƙai. To bayan Sarki ya tabbatar da kuɓutar Annabi Yusufu daga duk wani zargi, ya fahimci cewa mutumin kirki ne mai ilimi da haƙuri, sai ya nemi a zo masa da shi domin ya mayar da shi na kusa da shi a fada. Aka zo da Yusufu gaban Sarki, yayin da ya yi magana da Sarki sai ya fahimci girman matsayinsa sai ya ce: “Lalle kai kam a yau kana da babban matsayi kuma amintacce a wurinmu.” Daga nan Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nemi a ɗora masa wani nauyi na taimakon al’umma, musamman ganin mawuyacin halin da za su faɗa nan gaba na yunwa saboda ƙarancin abinci, sai ya nemi a ba shi matsayin mai kula da taskokin arzikin ƙasar domin zai riƙe amana, kuma yana da ilimin kula da tattalin arziki. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, to kamar yadda ya kuɓutar da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga kurkuku ya wanke shi daga zargin da ake yi masa, hakanan kuma ya kafa shi a cikin ƙasar Misra yana kai-komo a cikinta yadda ya ga dama; wannan kuma wata rahama ce daga Allah da yake yi wa wanda ya ga dama cikin bayinsa a nan duniya, kuma ba ya tozarta ladan masu kyautatawa, yana ba su sakamakonsu cikakke. Kuma lalle sakamakon da ya tanadar musu a lahira ya fi alheri ga waɗanda suka yi imani da Allah kuma suka kiyaye dokokinsa ta hanyar aiki da umarninsa da barin haninsa.

  58. وَجَآءَ إِخۡوَةُ يُوسُفَ فَدَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَعَرَفَهُمۡ وَهُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ

    Open ayah 12:58

    ‘Yan’uwan Yusufu kuma suka zo suka shiga wurinsa sai ya gane su, sai dai su ba su shaida shi ba.

  59. وَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمۡ قَالَ ٱئۡتُونِي بِأَخٖ لَّكُم مِّنۡ أَبِيكُمۡۚ أَلَا تَرَوۡنَ أَنِّيٓ أُوفِي ٱلۡكَيۡلَ وَأَنَا۠ خَيۡرُ ٱلۡمُنزِلِينَ

    Open ayah 12:59

    Lokacin da ya haɗa musu kayan abincinsu, sai ya ce: “Ku zo min da ɗan’uwanku na wajen uba. Ashe ba kwa ganin irin yadda nake cika mudu, kuma ni ne mafi kyautata wa baƙi?

  60. فَإِن لَّمۡ تَأۡتُونِي بِهِۦ فَلَا كَيۡلَ لَكُمۡ عِندِي وَلَا تَقۡرَبُونِ 

    Open ayah 12:60

    “To idan ba ku zo min da shi ba to fa ba ku da wani awo ke nan a wurina (nan gaba), kuma kada ma ku kusanto ni!”

  61. قَالُواْ سَنُرَٰوِدُ عَنۡهُ أَبَاهُ وَإِنَّا لَفَٰعِلُونَ

    Open ayah 12:61

    Suka ce: “To za mu rarrashi babansa game da shi, kuma lalle tabbas za mu aikata (haka).”

  62. وَقَالَ لِفِتۡيَٰنِهِ ٱجۡعَلُواْ بِضَٰعَتَهُمۡ فِي رِحَالِهِمۡ لَعَلَّهُمۡ يَعۡرِفُونَهَآ إِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمۡ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

    Open ayah 12:62

    (Yusufu) Ya ce da yaransa: “Ku sanya hajarsu cikin jakunkunansu don su gan ta lokacin da suka koma ga iyalinsu wataƙila za su dawo.” Lokacin da Yusufu ya karɓi matsayin mai kula da taskokin arzikin ƙasar Misra, ya tafiyar da aikinsa yadda ya kamata: an shuke gonakin ƙasar Misra, an yi noma an sami amfanin gona mai yawa a shekarun nan bakwai masu yalwa, aka kuma cika rumbuna da hatsi domin fuskantar shekaru bakwai na fari. Lokacin da aka fara fari wanda ya shafi kowane yanki har da ƙasar Falasɗinu inda Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ‘ya’yansa suke rayuwa, sai Yaƙubu ya aiko ‘ya’yansa zuwa Misra domin su nemo abinci. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da ‘yan’uwan Yusuf suka shiga wurinsa sai ya gane su, amma su ba su gane shi ba saboda kamanninsa sun canza bayan shekaru da ya kwashe ba ya tare da su, domin sun jefa shi rijiya ne tun yana ƙarami. To lokacin da ya yi musu awo kamar yadda yake yi wa kowa, domin a tsarinsa babu wanda ake ba shi fiye da kayan raƙumi ɗaya, sai ya tambaye su labarin gidansu, sai suka faɗa masa suna da ɗan’uwa na wajen uba, sai ya nemi su zo masa da shi duk sanda za su dawo zai ƙara musu kayan raƙumi ɗaya, ya ce ba su ga yadda yake cika musu mudu ba kuma da irin karɓar baƙin da ya yi musu? Ya kuma tsoratar da su cewa, idan ba su dawo da wannan ɗan’uwan nasu ba, to sun tabbata maƙaryata don haka ba zai ƙara yi musu awo ba, kada ma su matso kusa da inda yake, watau kar su sake shigo masa ƙasa. Sai suka amsa wa Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa za su nemi babansu ya ba su dama su zo da shi, za su kuma yi iya ƙoƙarinsu a kan haka ba za su yi ƙasa a gwiwa ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarci ma’aikatansa da su mayar wa da ‘yan’uwansa hajarsu a cikin kayansu domin idan sun koma ƙasarsu su gan ta su fahimci ba ciniki ya yi da su ba, wannan zai sa su dawo tare da ɗan’uwansu, domin su nuna wa Yusufu cewa lalle su mutane ne masu gaskiya, don haka zai karɓi hajjarsu ya sayar musu da abincin da suka zo nema.

  63. فَلَمَّا رَجَعُوٓاْ إِلَىٰٓ أَبِيهِمۡ قَالُواْ يَٰٓأَبَانَا مُنِعَ مِنَّا ٱلۡكَيۡلُ فَأَرۡسِلۡ مَعَنَآ أَخَانَا نَكۡتَلۡ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ

    Open ayah 12:63

    Lokacin da suka dawo wurin babansu sai suka ce: “Ya babanmu, an hana mu yin awo (nan gaba), sai ka aika mu tare da ɗan’uwanmu mu yiwo awo, lalle kuma mu tabbas za mu kula da shi.”

  64. قَالَ هَلۡ ءَامَنُكُمۡ عَلَيۡهِ إِلَّا كَمَآ أَمِنتُكُمۡ عَلَىٰٓ أَخِيهِ مِن قَبۡلُ فَٱللَّهُ خَيۡرٌ حَٰفِظٗاۖ وَهُوَ أَرۡحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ

    Open ayah 12:64

    Ya ce: “Yanzu anya kuwa na amince muku game da shi, ai sai dai kawai kamar yadda na amince muku game da ɗan’uwansa tun tuni; sai dai Allah ne Fiyayen Mai kiyayewa, kuma Shi ne Fiyayyen masu rahama.”

  65. وَلَمَّا فَتَحُواْ مَتَٰعَهُمۡ وَجَدُواْ بِضَٰعَتَهُمۡ رُدَّتۡ إِلَيۡهِمۡۖ قَالُواْ يَٰٓأَبَانَا مَا نَبۡغِيۖ هَٰذِهِۦ بِضَٰعَتُنَا رُدَّتۡ إِلَيۡنَاۖ وَنَمِيرُ أَهۡلَنَا وَنَحۡفَظُ أَخَانَا وَنَزۡدَادُ كَيۡلَ بَعِيرٖۖ ذَٰلِكَ كَيۡلٞ يَسِيرٞ

    Open ayah 12:65

    Lokacin kuma da suka buɗe jakunkunansu sai suka samu hajarsu an mayar musu da ita, suka ce: “Ya babanmu, me kuma muke nema? Ai wannan hajarmu ce aka dawo mana da ita; (idan muka koma) ai za mu nemo wa iyalinmu abinci kuma mu kula da ɗan’uwanmu, kuma mu ƙara kayan raƙumi (ɗaya). Wannan (kuwa) kaya ne sassauƙa.”

  66. قَالَ لَنۡ أُرۡسِلَهُۥ مَعَكُمۡ حَتَّىٰ تُؤۡتُونِ مَوۡثِقٗا مِّنَ ٱللَّهِ لَتَأۡتُنَّنِي بِهِۦٓ إِلَّآ أَن يُحَاطَ بِكُمۡۖ فَلَمَّآ ءَاتَوۡهُ مَوۡثِقَهُمۡ قَالَ ٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٞ

    Open ayah 12:66

    (Babansu) Ya ce: “Ba zan aika ku tare da shi ba, har sai kun yi min alƙawari tsakaninku da Allah lalle za ku dawo min da shi, sai dai in wata masifa ta rutsa da ku.” Lokacin da suka yi masa alƙawari sai ya ce: “Allah ne Wakili a kan abin da muke faɗa.”

  67. وَقَالَ يَٰبَنِيَّ لَا تَدۡخُلُواْ مِنۢ بَابٖ وَٰحِدٖ وَٱدۡخُلُواْ مِنۡ أَبۡوَٰبٖ مُّتَفَرِّقَةٖۖ وَمَآ أُغۡنِي عَنكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍۖ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَعَلَيۡهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ

    Open ayah 12:67

    Ya kuma ce: “Ya ‘ya’yana, kada ku shiga (Masar) ta ƙofa guda; ku shiga ta ƙofofi daban-daban. Ba zan kare muku komai daga Allah ba; ba wani hukunci sai na Allah; a gare Shi na dogara, kuma a gare Shi ne masu dogaro ya wajaba su dogara.”

  68. وَلَمَّا دَخَلُواْ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَهُمۡ أَبُوهُم مَّا كَانَ يُغۡنِي عَنۡهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍ إِلَّا حَاجَةٗ فِي نَفۡسِ يَعۡقُوبَ قَضَىٰهَاۚ وَإِنَّهُۥ لَذُو عِلۡمٖ لِّمَا عَلَّمۡنَٰهُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 12:68

    To lokacin da suka shiga ta inda babansu ya umarce su, (wannan) ba zai maganta musu komai ba daga Allah, sai dai wata buƙata ce a zuciyar Yakubu da ya samu biyanta. Lalle kuma shi tabbas mai ilimi ne na abin da Muka sanar da shi, sai dai yawancin mutane ba su sani ba. A waɗannan ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da ya faru ne lokacin da ‘yan‘uwan Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka koma wurin babansu, suka ba shi labarin irin karamcin da Yusufu ya yi musu, kuma suka faɗa masa cewa, daga yanzu an ce ba za a ƙara yi musu awo ba idan ba su koma tare da ɗan’uwansu ba, don haka suka roƙi babansu da ya bar shi su tafi tare da shi domin su sami ƙarin awo, kuma suka yi alƙawarin lalle za su kula da shi ba abin da zai same shi har su koma gida. Sai Annabi Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana musu cewa, ba zai taɓa sakin jiki ya amince da maganarsu ba bayan kuwa bai mance da abin da suka yi wa Yusufu a baya ba. Domin kuwa ya amince musu akan Yusufu ne bayan sun yi masa alƙawarin kula da shi, amma ba su cika wancan alƙawari ba, don haka ba zai aminta da su ba, dogaronsa kaɗai ga Allah yake, shi ne Fiyayyen mai kiyayewa kuma Fiyayyen masu rahama. Sai kuma bayan sun buɗe kayayyakinsu sai suka ga hajarsu an dawo musu da ita, watau an ba su kayan abincin ne kyauta ba a karɓi komai daga wajensu ba. Don haka suka ce wa babansu, me kuma za su nema a wajen wannan babban mutum bayan irin wannan goma ta arziki da ya yi musu!? Ga shi dai ya dawo musu da tamanin da suka zo da shi, don haka wannan ya ƙara musu ƙarfin gwiwar lalle su koma masa da ɗan’uwansu domin su sake yin awon abinci ga iyalansu, su kuma kula da ɗan’uwansu, sannan kuma ga ƙarin kayan raƙumi ɗaya na ɗan’uwansu, wannan kuwa abu ne mai sauƙi a wurin Azizu, watau Yusufu, ya yi musu wannan karamci. To amma mahaifinsu Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) har yanzu bai nutsu da maganganun ‘ya’yansa nasa ba, domin bai manta baya ba, sai ya ce ba zai tura dan’uwansu tare da su ba har sai sun ɗauki alƙawari mai ƙarfi tsakaninsu da Allah na cewa za su dawo da shi gida sai dai in wani abu ne ya faru wanda ya fi ƙarfinsu ya hana su dawo da shi. To bayan sun yi masa alƙawari tsakaninsu da Allah a kan haka, sai ya ce, Allah ne wakili a kan abin da suka faɗa. Sai kuma Annabi Yaƙubu ya yi wa ‘ya’yansa wasiyya cewa, idan sun isa ƙasar Misra, to kada su shiga gaba ɗayansu ta ƙofa guda; su shiga ta ƙofofi daban-daban domin kauce wa wata cutarwa da za ta iya fuskantar su, don kada ta same su gaba ɗayansu a lokaci guda. Ya kuma tabbatar musu cewa, ba yana faɗa musu haka ba ne domin ko zai iya kare su daga wani abin cutarwa da Allah ya yi nufin ya same su ba, ko ya jawo musu wani amfani da Allah bai nufe su da shi ba; babu abin da yake faruwa sai abin da Allah ya hukunta faruwarsa. Ya tabbatar musu cewa, shi ma ga Allah kaɗai ya dogara, don haka gare shi kaɗai duk masu dogara za su dogara. Da yawa daga cikin malaman tafsiri sun bayyana cewa, abin da Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake jiye wa ‘ya’yansa tsoro shi ne kambun baka, saboda kasancewarsu dukkansu mazaje ne masu kyan halitta, sannan suna sanye da tufafi iri ɗaya waɗanda ba irin na Misra ba. Kuma da an gan su za a gane baƙi ne. Sai ya ji tsoron kambun baka ya same su, domin ya san kambun baka gaskiya ne (kamar yadda ya zo a hadisi). [Dubi Bukhari #5740 da Muslim #5830].

  69. وَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيۡهِ أَخَاهُۖ قَالَ إِنِّيٓ أَنَا۠ أَخُوكَ فَلَا تَبۡتَئِسۡ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 12:69

    Lokacin kuma da suka shiga wurin Yusufu sai ya janye ɗan’uwansa wajensa ya ce: “Ni fa lalle ɗan’uwanka ne; saboda haka kada ka damu da abin da suke aikatawa.”

  70. فَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمۡ جَعَلَ ٱلسِّقَايَةَ فِي رَحۡلِ أَخِيهِ ثُمَّ أَذَّنَ مُؤَذِّنٌ أَيَّتُهَا ٱلۡعِيرُ إِنَّكُمۡ لَسَٰرِقُونَ 

    Open ayah 12:70

    To lokacin da (Azizu) ya haɗa musu kayayyakinsu sai ya sanya ma’aunin a cikin kayan ɗan’uwansa, sannan mai shela ya yi yekuwa da cewa: “Ya ku waɗannan ayari, lalle ku fa tabbas ɓarayi ne!”

  71. قَالُواْ وَأَقۡبَلُواْ عَلَيۡهِم مَّاذَا تَفۡقِدُونَ

    Open ayah 12:71

    Suka ce: (yayin da) suka juyo wajensu: “Wane abu ne ya ɓace muku?”

  72. قَالُواْ نَفۡقِدُ صُوَاعَ ٱلۡمَلِكِ وَلِمَن جَآءَ بِهِۦ حِمۡلُ بَعِيرٖ وَأَنَا۠ بِهِۦ زَعِيمٞ

    Open ayah 12:72

    Suka ce: “Ma’aunin Sarki ne ba mu gani ba, kuma duk wanda ya zo da shi yana da ladan kayan raƙumi guda, kuma ni ne mai lamuninsa.”

  73. قَالُواْ تَٱللَّهِ لَقَدۡ عَلِمۡتُم مَّا جِئۡنَا لِنُفۡسِدَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا كُنَّا سَٰرِقِينَ

    Open ayah 12:73

    Suka ce: “Wallahi haƙiƙa kun sani ba mu zo don mu yi ɓarna a bayan ƙasa ba, kuma mu ba mu taɓa zama ɓarayi ba.”

  74. قَالُواْ فَمَا جَزَٰٓؤُهُۥٓ إِن كُنتُمۡ كَٰذِبِينَ

    Open ayah 12:74

    (Mutanen Sarki) suka ce: “Mene ne horon da za a yi masa (ɓarawon) idan ƙarya kuke yi?”

  75. قَالُواْ جَزَٰٓؤُهُۥ مَن وُجِدَ فِي رَحۡلِهِۦ فَهُوَ جَزَٰٓؤُهُۥۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 12:75

    Suka ce: “Horonsa shi ne, wanda aka same shi a cikin kayansa, to shi ne horonsa (watau a riƙe shi). Kamar haka muke saka wa azzalumai.”

  76. فَبَدَأَ بِأَوۡعِيَتِهِمۡ قَبۡلَ وِعَآءِ أَخِيهِ ثُمَّ ٱسۡتَخۡرَجَهَا مِن وِعَآءِ أَخِيهِۚ كَذَٰلِكَ كِدۡنَا لِيُوسُفَۖ مَا كَانَ لِيَأۡخُذَ أَخَاهُ فِي دِينِ ٱلۡمَلِكِ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ نَرۡفَعُ دَرَجَٰتٖ مَّن نَّشَآءُۗ وَفَوۡقَ كُلِّ ذِي عِلۡمٍ عَلِيمٞ

    Open ayah 12:76

    Sai ya fara da (binciken) jakunkunansu kafin jakar ɗan’uwansa; sannan ya fito da shi (mudun) daga jakar ɗan’uwansa. Kamar haka Muka shirya wa Yusufu; ba zai yiwu ya riƙe ɗan’uwansa ba a shari’ar Sarkin (Masar), sai dai idan Allah Ya ga dama. Muna ɗaukaka darajojin waɗanda Muka ga dama ne. Kuma duk wani mai ilimi akwai wanda yake samansa a ilimi.

  77. ۞قَالُوٓاْ إِن يَسۡرِقۡ فَقَدۡ سَرَقَ أَخٞ لَّهُۥ مِن قَبۡلُۚ فَأَسَرَّهَا يُوسُفُ فِي نَفۡسِهِۦ وَلَمۡ يُبۡدِهَا لَهُمۡۚ قَالَ أَنتُمۡ شَرّٞ مَّكَانٗاۖ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا تَصِفُونَ

    Open ayah 12:77

    Suka ce: “Idan har ya yi sata, to haƙiƙa ɗan’uwansa ma a da can ya taɓa yin sata.” Sai Yusufu ya ɓoye wannan (maganar) a ransa bai kuma bayyana musu ita ba, yana mai cewa (a ransa): “Ku ne dai masu mummunan matsayi (a wurin Allah). Allah kuwa Shi ne Mafi sanin abin da kuke sifantawa.”

  78. قَالُواْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡعَزِيزُ إِنَّ لَهُۥٓ أَبٗا شَيۡخٗا كَبِيرٗا فَخُذۡ أَحَدَنَا مَكَانَهُۥٓۖ إِنَّا نَرَىٰكَ مِنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 12:78

    Suka ce: “Ya kai wannan Azizu, lalle yana da mahaifi tsoho tukuf, sai ka riƙe ɗayanmu a madadinsa; lalle kuwa muna ganin kana daga masu kyautatawa.”

  79. قَالَ مَعَاذَ ٱللَّهِ أَن نَّأۡخُذَ إِلَّا مَن وَجَدۡنَا مَتَٰعَنَا عِندَهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّظَٰلِمُونَ

    Open ayah 12:79

    Ya ce: “Allah Ya kiyaye mu da riƙe wani ba wanda muka sami kayanmu a wurinsa ba; idan kuwa muka yi haka to lalle mun zama azzalumai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ‘yan’uwan Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun zo masa tare da ɗan’uwansa kamar yadda suka yi masa alƙawari. Da shigarsu sai Yusufu ya yi ƙoƙarin ya janye dan’uwansa shaƙiƙi wajensa ya kuma nuna masa cikin sirri cewa shi ne Yusufu ɗan’uwansa, ya labarta masa duk abin da ya wakana a baya tsakaninsa da ‘yan’uwansa ya umarce shi da kada ya bayyana wannan sirri ga ‘yan’uwansa, kuma kada ya ji wata damuwa ta tsoron ko za su cutar da shi kamar yadda suka yi wa Yusufu a can baya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sa yaransa suka haɗa wa ‘yan’uwansa kayyayakinsu suka ɗora musu a kan raƙumansu, sai ya umarce su da su sanya ma’aunin Sarki wanda ake yin awon da shi cikin kayan ɗan’uwansa shaƙiƙi ba tare da sauran ‘yan’uwansa sun sani ba, da nufin shirya wata dabara da zai riƙe ɗan’uwansa a wurinsa. Bayan sun kama hanya sun tafi, sai Yusufu ya aika mai shela ya bi bayansu yana shelanta dakatar da su domin sun yi sata. Jin an kira su barayi sai abin ya ɗaure musu kai, sai duk suka juyo wajen mai shela suna tambayar sa mene ne ya ɓace musu shi da mutanensa suka fito nema? Sai suka ce, ai ma’aunin Sarki ne ya ɓace ake neman sa, kuma har an sanya lada ga wanda ya gano shi, watau za a ba shi kayan raƙumi guda, kuma shi mai wannan shelar ya ƙara tabbatar musu da cewa, shi ne lamuni a kan haka. Daga nan ‘yan’uwan Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka yi rantsuwa a kan cewa, su ba su zo wannan gari don su yi sata ba, kuma su tun da suke ba su taɓa yin sata ba. Sai mai shela da jama’arsa suka ce musu: “To wane irin horo za a yi wa wanda aka same shi da wannan laifi na sata a yadda yake a shari’ar ƙasarku?” Sai suka ce ai a shari’arsu duk wanda aka gano kayan sata a wurinsa to ana miƙa shi ne ga hannun wanda ya yi wa satar ya mayar da shi bawansa. Haka ne hukuncin ɓarayi a ƙasarsu. Daga nan sai suka mayar da su wajen Yusufu don yin bincike, sai ya fara da binciken jakunkunan ‘yan’uwansa kafin ya binciki jakar ɗan’uwansa shaƙiƙi domin kada su fahimci dabarar da ya shirya musu. Da ya bincika jakar ɗan’uwansa sai ya fito da ma’aunin Sarki daga cikinta. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, kamar yadda ya shirya masa ya sanya ma’aunin Sarki cikin jakar ɗan’uwansa, hakanan ya shirya masa yadda zai hukunta ɗan’uwansa da shari’ar ƙasarsu, kuma ya zamanto su ne da kansu suka yanke wannan hukuncin domin ba su taɓa tsammanin za a sami wannan ma’auni a cikin kayansu ba. Ba don wannan dabarar da Allah ya shirya wa Yusufu ba, to da babu yadda zai iya riƙe ɗan’uwansa a wurinsa, domin ƙasar Misra ba ta tanadi haka ba, sai dai idan Allah ya ga dama ta wata hanyar daban, kuma shi mai iko ne a kan haka. Allah ya bayyana cewa, yana ɗaga matsayin wanda ya ga dama daga cikin bayinsa, kuma komai zurfin ilimin mutum to akwai wanda ya fi shi; ilimin Allah kuwa ya fi na kowa. Ganin abu ya kasance haka, ga su ana ganin su sun fito daga babban gida sai suka nuna wa Yusufu cewa, ai wannan ba abin mamaki ne Binyaminu ya yi sata ba, domin a can baya ma ɗan’uwansa shaƙiƙi, suna nufin Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), shi ma ya taɓa yin sata, don haka wannan halin ‘yan ɗakinsu ne, amma su ba halinsu ne yin sata ba. Annabi Yusufu da ya ji wannan suka da aka yi gare shi da ɗan’uwansa daga bakinsu sai ya ɓoye damuwarsa a ransa, ya danne fushinsa bai nuna musu shi ba ko a fuska ballatana har ya ɗauki wani matakin ramuwar gayya. A ransa kawai ya ce su dai ne masu mummunan matsayi a wurin Allah kuma Allah ne mafi sanin abin da suke siffanta su da shi na sata, domin ya san Annabi Yusufu da ɗan’uwansa ba ɓarayi ne ba. Bayan hukuncin riƙe ɗan’uwansu ya tabbata sai suka shiga lallashin Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suna nuna masa cewa, shi wannan ɗan’uwansu da zai riƙe shi a matsayin bawa babansa tsoho ne tukuf kuma zai shiga damuwar rabuwa da ɗansa da yake matuƙar ƙauna, don haka ya yi musu alfarma ya riƙe ɗaya daga cikinsu a madadinsa, domin sun lura da cewa shi Yusufu mutumin kirki ne. To amma sai Yusufu ya nuna musu cewa bai dace ba ya bar wanda aka sami kaya a wurinsa a riƙe wanda bai yi laifi ba, idan ya yi haka to ya yi zalunci, shi kuwa adalin mai mulki ne ba azzalumi ba. Abin lura a maganar Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ne bai ce: “Wanda ya yi sata ba” sai ya ce: “Wanda muka sami kayanmu a wurinsa” don gudun kada ya yi ƙarya, domin ɗan’uwansa bai yi sata ba.

  80. فَلَمَّا ٱسۡتَيۡـَٔسُواْ مِنۡهُ خَلَصُواْ نَجِيّٗاۖ قَالَ كَبِيرُهُمۡ أَلَمۡ تَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ أَبَاكُمۡ قَدۡ أَخَذَ عَلَيۡكُم مَّوۡثِقٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَمِن قَبۡلُ مَا فَرَّطتُمۡ فِي يُوسُفَۖ فَلَنۡ أَبۡرَحَ ٱلۡأَرۡضَ حَتَّىٰ يَأۡذَنَ لِيٓ أَبِيٓ أَوۡ يَحۡكُمَ ٱللَّهُ لِيۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡحَٰكِمِينَ 

    Open ayah 12:80

    To lokacin da suka fitar da rai daga gare shi, sai suka keɓe suna ganawa. Babbansu ya ce: “Ba ku san cewa babanku ya ɗauki alƙawari daga gare ku tsakaninku da Allah ba, kuma a da can ga irin sakacin da kuka yi game da Yusufu? To ni dai ba zan bar ƙasar (Masar) ba har sai babana ya yi min izini (da komawa), ko kuwa Allah Ya hukunta (abin da Ya ga dama) da ni; Shi ne kuwa Fiyayyen masu hukunci.

  81. ٱرۡجِعُوٓاْ إِلَىٰٓ أَبِيكُمۡ فَقُولُواْ يَٰٓأَبَانَآ إِنَّ ٱبۡنَكَ سَرَقَ وَمَا شَهِدۡنَآ إِلَّا بِمَا عَلِمۡنَا وَمَا كُنَّا لِلۡغَيۡبِ حَٰفِظِينَ

    Open ayah 12:81

    “Sai ku koma wurin babanku ku ce da shi: “Ya babanmu, lalle ɗanka ya yi sata! Ba mu kuwa ba da shaida ba sai da abin da muka sani, ba mu kuma zamanto masu kiyaye gaibu ba.

  82. وَسۡـَٔلِ ٱلۡقَرۡيَةَ ٱلَّتِي كُنَّا فِيهَا وَٱلۡعِيرَ ٱلَّتِيٓ أَقۡبَلۡنَا فِيهَاۖ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ

    Open ayah 12:82

    “Kuma ka tambayi mutanen alƙaryar da muka kasance a cikinta (watau Masar) da kuma ayarin da muka zo cikinsu. Wallahi mu kam lalle masu gaskiya ne.”

  83. قَالَ بَلۡ سَوَّلَتۡ لَكُمۡ أَنفُسُكُمۡ أَمۡرٗاۖ فَصَبۡرٞ جَمِيلٌۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَأۡتِيَنِي بِهِمۡ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 12:83

    Ya ce: “Ba haka ba ne, zuciyarku dai ta shirya muku wani abu. Haƙuri kawai shi ya fi kyau (gare ni). Ina sa tsammani Allah Ya kawo min su gaba ɗaya. Lalle Shi ne Masani, Mai hikima.”

  84. وَتَوَلَّىٰ عَنۡهُمۡ وَقَالَ يَٰٓأَسَفَىٰ عَلَىٰ يُوسُفَ وَٱبۡيَضَّتۡ عَيۡنَاهُ مِنَ ٱلۡحُزۡنِ فَهُوَ كَظِيمٞ

    Open ayah 12:84

    Sai ya kau da kai daga gare su, ya kuma ce: “Wayyo baƙin cikina game da Yusufu!” Idanuwansa kuwa suka yi fari don baƙin ciki, yana cike da ɓacin rai.

  85. قَالُواْ تَٱللَّهِ تَفۡتَؤُاْ تَذۡكُرُ يُوسُفَ حَتَّىٰ تَكُونَ حَرَضًا أَوۡ تَكُونَ مِنَ ٱلۡهَٰلِكِينَ

    Open ayah 12:85

    Suka ce: “Wallahi ba za ka bar tuna Yusufu ba har sai ka tasam ma mutuwa ko sai ka zamanto cikin matattu!”

  86. قَالَ إِنَّمَآ أَشۡكُواْ بَثِّي وَحُزۡنِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَأَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 12:86

    Ya ce: “Ni fa kawai ina bayyana tsananin damuwata ne da baƙin cikina ga Allah, kuma ina sane da abin da ba ku sani ba game da Allah.

  87. يَٰبَنِيَّ ٱذۡهَبُواْ فَتَحَسَّسُواْ مِن يُوسُفَ وَأَخِيهِ وَلَا تَاْيۡـَٔسُواْ مِن رَّوۡحِ ٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ لَا يَاْيۡـَٔسُ مِن رَّوۡحِ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ

    Open ayah 12:87

    “Ya ku ‘ya’yana, ku tafi ku lalubo labarin Yusufu shi da ɗan’uwansa, kada ku ɗebe ƙauna daga rahamar Allah. Lalle ba mai ɗebe ƙauna daga rahamar Allah sai mutane kafirai.” A waɗannan ayoyi Allah ya bayyana cewa, yayin da ‘yan’uwan Yusufu suka ga ya ƙi yarda ya riƙe ɗaya daga cikinsu a madadin ɗan’uwansu Binyaminu sai suka keɓe wuri guda suka shiga shawarar abin da ya kamata su yi, sai babbansu ya tuna musu rantsuwar da suka yi wa mahaifinsu da alƙawarin da suka ɗauka na cewa za su dawo da ɗan’uwansu Binyaminu kuma ba za su bari wani abin ƙi ya same shi ba sai dai abin da ya fi ƙarfinsu. Sannan ya sake tunatar da su abin da suka yi wa Yusufu sanda suka jefa shi rijiya da niyyar ɓatar da shi bayan sun yi wa mahaifinsu alƙawarin za su dawo da shi gida. Don haka shi kam ba zai iya yin arba da mahaifinsa a cikin irin wannan hali ba, shi dai zai ci gaba da zama a ƙasar Misra sai fa idan shi mahaifin nasu ne ya yi masa izinin dawowa, ko kuma Allah ya zartar da hukuncinsa a kansa ya karɓo ɗan’uwansa ko kuma mutuwa ta riske shi a nan. Allah shi ne Fiyayyen masu hukunci, hukuncinsa kuwa adalci ne. Daga nan sai ya shawarce su da su koma wurin mahaifinsu su shaida masa cewa, ɗansa Binyaminu ya yi sata kuma an yanke masa hukuncin zaman bauta a wurin wanda ya yi wa satar, kuma wannan maganar da suke faɗa masa iya gaskiyarsu ke nan, domin a gaban idonsu aka fito da ma’aunin Sarki daga jakar ɗan’uwansu, kuma su ba su san yana sata ba, domin da a ce sun sani to da ba su ɗaukar masa alƙawarin za su dawo da shi ba. Bugu da ƙari kuma suka shaida masa cewa, idan yana shakkar wannan batu nasu, to ya aika a tambayo masa mutanen ƙasar Misra da kuma ayarin fataken da suka kasance tare a can don su tabbatar masa da gaskiyar labarin da ya ji daga bakinsu, domin dai su sun tabbatar suna da gaskiya. Da suka koma ƙasarsu wajen mahaifinsu suka shaida masa abin da ya faru, amma shi bai gamsu ba sai kawai ya zarge su da cewa, zukatansu ne suka ƙawata musu wani makirci kamar yadda suka yi wa ɗan’uwansa Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), don haka babu wani abu da zai iya yi sai dai kyakkyawan haƙuri wanda babu raki a cikinsa ko ya kai kukansa ga wani ba Allah ba. Amma kuma duk da haka bai fitar da rai cewa Allah zai dawo masa da ‘ya’yansa ukun gaba ɗayansu komai daɗewa ba. Ya tabbatar da cewa, abin da yake ƙara masa ƙarfin gwiwar wannan fata nasa shi ne kasancewar Allah masanin komai ne kuma mai hikima ne cikin ayyukansa gaba ɗaya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, daga nan sai Yuƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kawar da kai daga ‘ya’yan nasa, yana mai nuna wa Allah shi kaɗai damuwarsa da baƙin cikinsa game da rasa samun labarin ɗansa Yusufu. Ya yi matsanancin kuka da har ta kai baƙin da yake cikin idanunsa ya koma fari fat kamar ya yi yana, ƙirjinsa yana maƙare da fushi saboda yadda yake ɓoye wa mutane halin damuwar da yake ciki, har ‘ya’yansa suka fara jin tsoron kada wannan damuwar da yake ciki ta zama sanadiyyar halakarsa, suka fara rarrashin sa kan ya rage yawan tunanin Yusufu don ya sawwaƙe wa kansa. To amma sai ya amsa musu da cewa, shi ga Allah kaɗai yake kai kukan tsananin damuwarsa da baƙin cikinsa, kuma ya san abin da su ba su sani ba game da tausayin Allah da luɗufinsa ga bayinsa yayin da suke cikin damuwa idan sun roƙe shi. Daga nan sai ya sake umartar ‘ya’yansa da su tafi su ci gaba da laluben labarin Yusufu da ɗan’uwansa, kada su cire tsammanin samun rahamar Allah da yaye damuwar bayinsa, domin babu wanda yake cire tsammani daga samun rahamar Allah da taimakonsa sai mutane kafirai waɗanda ba su san girman Ƙudurar Allah ba.

  88. فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَيۡهِ قَالُواْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡعَزِيزُ مَسَّنَا وَأَهۡلَنَا ٱلضُّرُّ وَجِئۡنَا بِبِضَٰعَةٖ مُّزۡجَىٰةٖ فَأَوۡفِ لَنَا ٱلۡكَيۡلَ وَتَصَدَّقۡ عَلَيۡنَآۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَجۡزِي ٱلۡمُتَصَدِّقِينَ

    Open ayah 12:88

    Lokacin da suka shiga wurinsa (Annabi Yusufu) sai suka ce: “Ya Azizu, muna fama da yunwa mu mu da iyalanmu, kuma mun zo maka da wata haja marar daraja; to ka cika mana mudu, ka kuma kyautata mana; lalle Allah Yana saka wa masu kyautatawa.”

  89. قَالَ هَلۡ عَلِمۡتُم مَّا فَعَلۡتُم بِيُوسُفَ وَأَخِيهِ إِذۡ أَنتُمۡ جَٰهِلُونَ

    Open ayah 12:89

    Ya ce: “Shin kun kuwa san abin da kuka aikata wa Yusufu shi da ɗan’uwansa a lokacin da kuke jahilai?”

  90. قَالُوٓاْ أَءِنَّكَ لَأَنتَ يُوسُفُۖ قَالَ أَنَا۠ يُوسُفُ وَهَٰذَآ أَخِيۖ قَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَآۖ إِنَّهُۥ مَن يَتَّقِ وَيَصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ 

    Open ayah 12:90

    Suka ce: “Shin kuwa tabbas ko kai ne Yusufu ne?” Ya ce: “Ni ne Yusufu, wannan kuma ɗan’uwana ne; haƙiƙa Allah Ya yi mana baiwa; lalle wanda ya kiyaye dokokin (Allah) ya kuma yi haƙuri, to tabbas Allah ba Ya tozarta sakamakon masu kyautatawa.”

  91. قَالُواْ تَٱللَّهِ لَقَدۡ ءَاثَرَكَ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا وَإِن كُنَّا لَخَٰطِـِٔينَ

    Open ayah 12:91

    Suka ce: “Wallahi haƙiƙa Allah Ya fifita ka a kanmu, mu kuma lalle mun tabbata masu kuskure!”

  92. قَالَ لَا تَثۡرِيبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡيَوۡمَۖ يَغۡفِرُ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَهُوَ أَرۡحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ

    Open ayah 12:92

    Ya ce: “A yau babu wani zargi a kanku; Allah zai yafe muku, Shi ne Mafificin masu rahama.

  93. ٱذۡهَبُواْ بِقَمِيصِي هَٰذَا فَأَلۡقُوهُ عَلَىٰ وَجۡهِ أَبِي يَأۡتِ بَصِيرٗا وَأۡتُونِي بِأَهۡلِكُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 12:93

    “Ku tafi da rigata wannan sannan ku jefa ta a fuskar babana, zai dawo mai gani, ku kuma zo min da iyalanku gaba ɗaya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa, ‘yan’uwan Annabi Yusufu sun fita nemansa shi da ɗan’uwanasa. Lokacin da suka shiga wurin Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai suka sanar da shi cewa, yanzu fa suna cikin wahalar yunwa da fari su da iyalinsu, kuma ga shi ba su da isasshen kuɗin musaya da za su sayi abinci mai yawa da shi wanda zai ishe su har da iyalinsu, suka kuma roƙe shi da ya taimaka musu ya karɓi ɗan abin da yake hannunsu ya cika musu mudu kamar yadda ya saba yi musu a baya, ya ƙara da yi musu sadaka wajen karɓar hajarsu marar daraja, ko kuma ya ƙara musu a kan yadda yake ba su a baya domin Allah yana saka wa masu sadaƙa. To a nan ne fa Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tausaya musu ya bayyana kansa ga ‘yan’uwansa bayan ya ji irin matsanancin halin da suka shiga na fari da yunwa da talauci, ya tambaye su ko sun tuna da makircin da suka ƙulla wa Yusufu shi da ɗan’uwansa da nuna ƙiyayya da hassada lokacin da suke cikin jahilci da rashin sanin abin da aikinsu zai haifar a gaba!? Wannan magana ta Yusufu sai ta ɗaure wa ‘yan’uwansa kai domin ba su taɓa kawowa a tunaninsu ba cewa za su haɗu da Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cikin wannan ɗaukaka da girman matsayi, ga shi tsawon shekara biyu suna mu’amala da shi irin ta mabuƙaci da mai taimaka masa amma ba su gane shi ba, shi kuma bai nuna kansa gare su ba sai yanzu. Don haka cike da mamaki suka tambaye shi wai da gaske shi ne Yusufu? Ya kuma amsa da cewa, lalle shi ne Yusufu, wannan kuma ɗan’uwansa ne, ga shi Allah ya yi musu baiwa ya haɗa fuskokinsu bayan tsawon shekaru da rabuwa da juna. Sannan ya nuna musu cewa, haka sha’anin Allah yake, duk wanda ya tsare dokokin Allah ya yi aiki da umarninsa ya guje wa haninsa, ya kuma yi haƙuri a kan duk wata jarraba, to Allah ba zai taɓa tozarta masa kyawawan ayyukan nan nasa ba, zai kuma kare shi daga duk wani sharri da makirci. To daga nan ne fa ‘yan’uwan Yusufu suka fara ba shi haƙuri da neman afuwa daga wurinsa, suka tabbatar masa tare da rantsuwa da Allah cewa, shi ne gaba da su domin Allah ya fifita shi a kansu da kyawawan ɗabi’unsa ga kuma sarauta da annabci duka Allah ya ba shi, sannan suka fito fili suka yarda da kuskuren da suka tabka a baya na nuna hassada da ƙiyayya gare shi da ɗan’uwansa. To amma da yake Annabi Yusufu mai karamci ne ɗan mai karamci sai ya nuna musu cewa, babu sauran wani zargi a kansu, ya ma roƙa musu gafarar Allah da rahamarsa domin shi ne Fiyayyen masu jin ƙai. To bayan Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana kansa ga ‘yan’uwansa ya kuma sami labarin mahaifinsu da halin da yake ciki na rashin gani, sai ya ba su rigarsa ya umarce su da su koma wajensa su jefa masa ita a fuskarsa ganinsa zai dawo ras, ya kuma nemi da su kwaso duk ilahirin mutanen gidansu gaba ɗaya su zo da su Misra.

  94. وَلَمَّا فَصَلَتِ ٱلۡعِيرُ قَالَ أَبُوهُمۡ إِنِّي لَأَجِدُ رِيحَ يُوسُفَۖ لَوۡلَآ أَن تُفَنِّدُونِ

    Open ayah 12:94

    Lokacin da ayarin ya baro (Masar) sai babansu ya ce: “Lalle ina jin ƙanshin Yusufu; ba don dai kada ku ce na susuce ba!”

  95. قَالُواْ تَٱللَّهِ إِنَّكَ لَفِي ضَلَٰلِكَ ٱلۡقَدِيمِ

    Open ayah 12:95

    Suka ce: “Wallahi mun tabbata ba shakka (har yanzu) kana nan cikin daɗaɗɗiyar rikicewar nan taka!”

  96. فَلَمَّآ أَن جَآءَ ٱلۡبَشِيرُ أَلۡقَىٰهُ عَلَىٰ وَجۡهِهِۦ فَٱرۡتَدَّ بَصِيرٗاۖ قَالَ أَلَمۡ أَقُل لَّكُمۡ إِنِّيٓ أَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 12:96

    To lokacin da mai albishir ya zo masa sai ya jefa ta (rigar) a fuskarsa, sai ya dawo yana gani. Ya ce: “Ban gaya muku ba cewa lalle ni na san abin da ku ba ku sani ba game da Allah?”

  97. قَالُواْ يَٰٓأَبَانَا ٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَآ إِنَّا كُنَّا خَٰطِـِٔينَ

    Open ayah 12:97

    Suka ce: “Ya babanmu, ka nema mana gafarar zunubanmu, lalle mun zamanto masu kuskure!”

  98. قَالَ سَوۡفَ أَسۡتَغۡفِرُ لَكُمۡ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

    Open ayah 12:98

    Ya ce: “Ba da daɗewa ba zan nema muku gafarar Ubangijina; lalle Shi ne Mai yawan gafara, Mai jin ƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta lokacin da ‘yan’uwan Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka baro Misra suka nufo ƙasarsu sai Annabi Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya faɗa wa ‘ya’yansa da waɗanda suke tare da shi cewa, shi fa yana jiyo ƙamshin Yusufu ba don kar su ce ya susuce shi ya sa yake maganganu irin waɗannan ba. Amma wasu daga cikin ‘ya’yansa suka ce da shi, har yanzu dai yana nan cikin daɗaɗɗiyar ɗimuwarsa ta rashin Yusufu. Sai kuwa abin da ya zata shi ne ya faru. To lokacin da mai albishir ya zo wa Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai ya jefa masa rigar Yusufu a fuskarsa, nan take kuwa ganinsa ya dawo, sai ya ce da ‘ya’yan nasa masu cewa ya kiɗime cewa, ba ya faɗa musu cewa ya san luɗufin Allah da tausayinsa ga bayinsa abin da su ba su sani ba? To daga nan fa ‘yan’uwan Yusufu suka fito fili suka tabbatar da laifinsu da suka yi, suka kuma roƙi mahaifinsu ya nema musu gafara wajen Allah don ya yafe musu. Sai ya amsa musu da cewa, zai nema musu gafarar Allah domin ya yafe musu saboda shi mai gafara ne ga bayinsa mai jin ƙansu ne.

  99. فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيۡهِ أَبَوَيۡهِ وَقَالَ ٱدۡخُلُواْ مِصۡرَ إِن شَآءَ ٱللَّهُ ءَامِنِينَ

    Open ayah 12:99

    Lokacin da suka shiga wurin Yusufu sai ya jawo iyayensa ya kuma ce: “Ku shigo Masar in Allah Ya ga dama kuna amintattu.”

  100. وَرَفَعَ أَبَوَيۡهِ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ وَخَرُّواْ لَهُۥ سُجَّدٗاۖ وَقَالَ يَٰٓأَبَتِ هَٰذَا تَأۡوِيلُ رُءۡيَٰيَ مِن قَبۡلُ قَدۡ جَعَلَهَا رَبِّي حَقّٗاۖ وَقَدۡ أَحۡسَنَ بِيٓ إِذۡ أَخۡرَجَنِي مِنَ ٱلسِّجۡنِ وَجَآءَ بِكُم مِّنَ ٱلۡبَدۡوِ مِنۢ بَعۡدِ أَن نَّزَغَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بَيۡنِي وَبَيۡنَ إِخۡوَتِيٓۚ إِنَّ رَبِّي لَطِيفٞ لِّمَا يَشَآءُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ 

    Open ayah 12:100

    Ya kuma ɗora mahaifansa a kan gadon mulki, suka kuma faɗi suna masu gaisuwa a gare shi, ya kuma ce: “Ya babanmu, wannan shi ne fassarar mafarkina na tun tuni. Lalle Ubangijina Ya mai da shi gaskiya; haƙiƙa kuma Ya kyautata min lokacin da Ya fitar da ni daga kurkuku, Ya kuma zo da ku daga ƙauye bayan Shaiɗan ya shiga tsakanina da ‘yan’uwana. Lalle Ubangijina Mai tausasawa ne ga wanda Ya ga dama. Lalle Shi ne Masani, Mai hikima.

  101. ۞رَبِّ قَدۡ ءَاتَيۡتَنِي مِنَ ٱلۡمُلۡكِ وَعَلَّمۡتَنِي مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِۚ فَاطِرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَنتَ وَلِيِّۦ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ تَوَفَّنِي مُسۡلِمٗا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّٰلِحِينَ 

    Open ayah 12:101

    “Ya Ubangijina, haƙiƙa Ka ba ni wani abu na mulki, Ka kuma sanar da ni wani abu daga fassarar mafarki; Ya Mahaliccin sammai da ƙasa, Kai ne Majiɓincina a duniya da lahira; ka karɓi raina ina Musulmi, Ka kuma haɗa ni da (mutane) salihai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ‘yan’uwan Yusufu su goma sha ɗaya da mahaifinsu Yaƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da sauran mutanen gidansu sun bar ƙasarsu ta Falasɗinu sun nufi ƙasar Misra kamar yadda Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nemi su yi. Lokacin da suka isa Misra suka shiga wurin Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai ya jawo iyayensa jikinsa ya yi musu goma ta arziki, ya girmama su matuƙa, ya kuma ce wa ‘yan’uwansa da sauran mutanen gidansu su shigo ƙasar Misra suna amintattu daga duk wani abin ƙi ko sharri, sannan kuma ya ɗora iyayensa a kan karagar mulkinsa. Su kuma sauran ‘yan’uwansa su goma sha ɗaya suka faɗi gabansa suka gaishe shi. To a nan ne Annabi Yusufu ya faɗa wa mahaifinsa cewa, wannan shi ne fassarar mafarkinsa da ya taɓa yi a baya na ganin rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna yi masa sujjada, ga shi a yau Allah ya tabbatar da abin ya faru da gaske. Daga wannan lokacin sai Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga godiya ga Allah bisa ga ni’imomin da ya yi masa masu yawa; daga cikinsu ya ambaci fito da shi daga kurkuku ba tare da an same shi da wani laifi ba da kuma sake haɗa shi da iyayensa da ‘yan’uwansa bayan tsawon shekaru ba sa tare da kuma rabo su da ƙauye su dawo birni da zama tare da shi bayan Shaiɗan ya shiga tsakaninsa da ‘yan’uwansa. Abin lura a nan shi ne, Annabi Yusufu bai ambaci laifin da ‘yan’uwansa suka yi masa ba, sai kawai ma ya nuna Shaiɗan ne ya shiga tsakaninsu, watau duk ya ɗora wa Shaiɗan laifin. Ya yi haka ne kuwa don ya tabbatar musu da cewa ya riga ya yafe musu ya kuma manta da duk abin da ya faru a tsakaninsu a baya. Sai kuma ya tabbatar da cewa, Allah mai tausasawa ne ga bayinsa, mai kai su ne matsayin da ba su yi tsammanin kaiwa gare shi ba, domin cikakken iliminsa da hikimarsa cikin al’amura. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, bayan ni’imar da ya cika wa Annabi Yusufu ta ba shi mulki da sanar da shi fassarar mafarki, sai ya koma ga Allah yana mai sake godiya gare shi tare da roƙon sa ya tabbatar da dugadugansa a kan Musulunci har lokacin mutuwarsa, ya kuma haɗa shi da annabawa salihai daga cikin iyayensa da wasunsu a cikin Aljannar Firdausi. Wannan shi ne ƙarshen labarin Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ‘yan’uwansa wanda Allah ya sanar da Annabinsa Muhammadu (ﷺ); labari ne mai ƙayatarwa wanda yake cike da gargaɗi da darussa.

  102. ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهِ إِلَيۡكَۖ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ أَجۡمَعُوٓاْ أَمۡرَهُمۡ وَهُمۡ يَمۡكُرُونَ 

    Open ayah 12:102

    Wannan yana daga labaran gaibu da Muke yi maka wahayinsa; ba ka kuma tare da su lokacin da suka haɗa al’amarinsu suna ƙulle-ƙullen makirci.

  103. وَمَآ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ وَلَوۡ حَرَصۡتَ بِمُؤۡمِنِينَ 

    Open ayah 12:103

    Yawancin mutane ba za su yi imani ba, komai kwaɗayinka (ga hakan).

  104. وَمَا تَسۡـَٔلُهُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ 

    Open ayah 12:104

    Kuma ba ka tambayar su lada a kansa (wato Alƙur’ani). Shi ba wani abu ne daban ba in ban da gargaɗi ga talikai.

  105. وَكَأَيِّن مِّنۡ ءَايَةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ يَمُرُّونَ عَلَيۡهَا وَهُمۡ عَنۡهَا مُعۡرِضُونَ 

    Open ayah 12:105

    Kuma ayoyi nawa ne a sammai da ƙasa waɗanda (kafirai) suke wucewa ta wajensu, amma suna bijire musu?

  106. وَمَا يُؤۡمِنُ أَكۡثَرُهُم بِٱللَّهِ إِلَّا وَهُم مُّشۡرِكُونَ 

    Open ayah 12:106

    Yawancinsu kuma ba sa yin imani da Allah sai (an same su) suna masu shirka (da Shi).

  107. أَفَأَمِنُوٓاْ أَن تَأۡتِيَهُمۡ غَٰشِيَةٞ مِّنۡ عَذَابِ ٱللَّهِ أَوۡ تَأۡتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ 

    Open ayah 12:107

    Yanzu sun amince ne wata azabar Allah mai lulluɓewa ta zo musu, ko kuwa alƙiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, alhalin su ba su sani ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙarin bayani ne a kan ƙissar Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ta gabata. Ya bayyana cewa, duk abin da aka saurara cikin wannan labari tun daga farkonsa har zuwa ƙarshensa gaibi ne na Allah, ba don ya yi wa Annabi (ﷺ) wahayinsa ba, to da bai san komai a kansa ba, domin kuwa ba ya tare da ‘yan’uwan Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da suka shirya masa makirci har suka jefa shi cikin kururrumar rijiya daga ƙarshe sauran abubuwan da suka biyo baya suka faru. To wannan shi ne cikakken dalili a kan gaskiyar annabcin Annabi Muhammad (ﷺ). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Annabi (ﷺ) cewa yawancin mutane fa ba za su yi imani ba duk kuwa da irin bayyanannun hujjoji da ya zo musu da su, don haka kada ya yawaita damuwa a kansu. Allah kuma ya tabbatar da cewa, Annabi (ﷺ) ba ya karɓar komai daga hannun mutane don ya yi musu wa’azi ballantana su ce abin duniya yake nema, Alƙur’ani da yake karanta musu kuma ba komai ne ba face wa’azi da tunatarwa ga talikai gaba ɗaya, domin su riƙi abin da zai amfane su su kuma guji abin da zai cutar da su. Sannan Allah ya bayyana yadda yawancin mutane suke gafala da ayoyin Allah da ya ajiye a cikin manya-manyan halittu da ya yi na sammai da ƙasa, kamar rana da wata da taurari da duwarwatsu da tekuna da ƙoramu da bishiyoyi da dabbobi na ruwa da na tudu, amma mutane suna ganin su ba sa ɗaukar wata izina daga gare su su fahimci Kaɗaitar Allah da cancantar a bauta masa shi kaɗai. Ya kuma bayyana cewa, ko da an samu wani ɓangare na imani tare da wasu, sun ba da gaskiya da cewa, shi ne mahalicci mai arzutawa, mai kashewa ya raya, duk da haka suna bauta wa wasu gumaka tare da Allah ko kuma suna da’awar yana da ɗa. Tsarki ya tabbata gare shi. Ya tabbata a cikin hadisi daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mushirikai sun kasance suna cewa: “Mun amsa kiranka (Allah) ba ka da wani abokin tarayya.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce musu: “Kaiconku, ya isa haka, ya isa haka!” To amma sai su ƙara da cewa: “Sai dai wani abokin tarayyar da shi naka ne, kai ne ke mallakar sa da abin da ya mallaka.” Suna faɗar haka ne yayin da suke ɗawafi a Ka’aba.” [Muslim #1185] Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara gargaɗin masu bijire wa ayoyinsa suna haɗa shi da wasu wajen bauta cewa, yanzu su sun amince da cewa wata azaba a nan duniya ta zo musu ta lulluɓe su ta ko’ina su rasa mafita daga gare ta? Ko kuma sun yarda alƙiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, alhalin ba su san da zuwanta ba ballantana su yi mata wani tanadi? Wannan shi ne ya hana su yin imani da Kaɗaitakar Allah da gaskiyar Manzonsa?

  108. قُلۡ هَٰذِهِۦ سَبِيلِيٓ أَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا۠ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِيۖ وَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ 

    Open ayah 12:108

    Ka ce: “Wannan ce hanyata, ina yin kira zuwa ga Allah, bisa hujja, ni da wanda ya bi ni. Tsarki kuma ya tabbata ga Allah, ni kuwa ba na cikin masu shirka.”

  109. وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰٓۗ أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۗ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ 

    Open ayah 12:109

    Ba Mu kuma aiko (manzanni) a gabaninka ba sai maza ‘yan birni waɗanda Muke yi wa wahayi. Me ya sa (kafirai) ba za su yi tafiya ba a bayan ƙasa don su ga yadda ƙarshen waɗanda suka rigaye su ya kasance? Lalle kuwa gidan lahira shi ya fi ga waɗanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba?

  110. حَتَّىٰٓ إِذَا ٱسۡتَيۡـَٔسَ ٱلرُّسُلُ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ كُذِبُواْ جَآءَهُمۡ نَصۡرُنَا فَنُجِّيَ مَن نَّشَآءُۖ وَلَا يُرَدُّ بَأۡسُنَا عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ 

    Open ayah 12:110

    Har yayin da manzanni suka ɗebe ƙauna (da imanin mutanensu), su kuma (kafiran) suka yi zaton an faɗa musu ƙarya ne (game da zuwan azabar Allah) sai taimakonmu ya zo musu, sai Muka tserar da wanda Muka ga dama; ba kuwa za a kawar da azabarmu daga mutane masu laifi ba.

  111. لَقَدۡ كَانَ فِي قَصَصِهِمۡ عِبۡرَةٞ لِّأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِۗ مَا كَانَ حَدِيثٗا يُفۡتَرَىٰ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 12:111

    Haƙiƙa akwai izina a cikin labaransu (annabawa) ga ma’abota hankali. (Alƙur’ani) bai zamanto zance ne da ake ƙirƙirar sa ba, sai dai zance ne da yake gaskata abin da ya rigaye shi (na littattafai), da kuma bayanin komai; shiriya ne kuma da rahama ga mutanen da suke yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Manzonsa (ﷺ) ya faɗa wa mutane cewa, wannan tafarkin da yake a kansa shi ne hanyarsa da yake kiran mutane zuwa gare ta a bisa doron hujja bayyananna. Hakanan waɗanda suka bi shi suka karɓi kiransa su ma a kan wannan hanyar tasa suke, suna kuma kira da hujja bayyananna. Sannan ya tabbatar musu cewa, shi ba ya daga cikin masu shirka da Allah, yana cikin masu kaɗaita Allah ne da bauta, tsarki ya tabbata a gare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi ishara da cewa, gabanin Manzon Allah (ﷺ) Annabi Muhammadu bai aiko da wani manzo ba sai daga cikin mazaje ba mata ba, kuma mutum ba aljan ba ba kuma mala’ika ba, ya zama kuma daga cikin mazauna birni ba ɗan ƙauye ba. Saboda haka Ƙuraishawa su bar yin mamakin aiko musu da wani mutum daga cikinsu har ma suna ganin bai fi su da komai ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan al\'ummun da ya aika musu da manzanni suka ƙaryata su kuma ya halaka su a dalilin haka, don haka me zai hana waɗannan masu ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) su yi yawo a bayan ƙasa su ga yadda ƙarshen masu ƙaryata manzannin Allah ya kasance domin su wa’azantu da su? Sai kuma ya ja hankalinsu a kan cewa, ya kamata su fahimci cewa ni’imar gidan lahira ga waɗanda suka kiyaye dokokin Allah a duniya ta fi musu alheri, me ya sa ba sa hankalta su gane abin da ake nuna musu, su bi Allah da Manzonsa su guji saɓa musu? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, manzannin da ya aiko aka ƙaryata su yakan jinkirta azabtar da maƙiyansu na wani ɗan lokaci, har manzannin sukan ɗebe ƙaunar samun nasara a kan maƙiyansu sannan azabar Allah gare su ta yi jinkirin zuwa, har ta kai kafirai suna cewa manzannin nan sun yi musu ƙaryar cewa azabar Allah za ta auko musu idan ba su ba da gaskiya da su ba. To ga shi ba su yi imanin ba kuma har yanzu azabar ba ta zo ba. Ana cikin haka sai nasarar Allah ta zo wa manzanninsa, azabarsa ta sauka ga kafirai, Allah ya tserar da manzannin da mabiyansu, ya halakar da kafirai. To Ƙuraishawa da duk masu ƙaryata Manzo su sani cewa, idan azabar Allah ta zo babu mai iya kawar da ita. Sai kuma daga ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimar bayar da labaran manzanni da al\'ummunsu, kamar labarin Annabi Yusufu da ‘yan’uwansa, cewa ba shakka akwai wa’azi ga mutane masu hankali da lura game da su. Don haka Alƙur’ani wanda ya zo da waɗannan labaran ba za ta yiwu a ce zance ne na ƙarya ba, sai dai shi zance ne da yake gaskata duk littattafan Allah da suka gabace shi, kuma cike yake da bayani filla-filla na hukunce-hukuncen shari’a da duk abin da mutane suke buƙatar sa a rayuwarsu ta duniya da ta lahira, kuma shiriya ce da rahama ga mutanen da suka yi imani, domin su ne kaɗai za su amfana da abin da ya ƙunsa na shiriya da wa’azi.