الرعد

Ar-Ra'd

The Thunder · Surah 13 · Ayahs: 43 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓمٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِۗ وَٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 13:1

    <ITALIC>ALIF LAM MIM RA</ITALIC>. Waɗannan ayoyi ne na Littafi (wato Alƙur’ani). Wanda kuma aka saukar maka daga Ubangijinka gaskiya ne, sai dai lalle yawancin mutane ba sa yin imani.

  2. ٱللَّهُ ٱلَّذِي رَفَعَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيۡرِ عَمَدٖ تَرَوۡنَهَاۖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَ يُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُم بِلِقَآءِ رَبِّكُمۡ تُوقِنُونَ

    Open ayah 13:2

    Allah Wanda Ya ɗaukaka sammai ba tare da wasu ginshiƙai da kuke ganinsu ba; sannan Ya daidaita bisa Al’arshi; Ya kuma hore muku rana da wata; kowannensu yana gudu zuwa wani lokaci ƙayyadadde. Yana shirya al’amari, Yana bayyana ayoyi don ku sakankance da haɗuwarku da Ubangijinku.

  3. وَهُوَ ٱلَّذِي مَدَّ ٱلۡأَرۡضَ وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۡهَٰرٗاۖ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ جَعَلَ فِيهَا زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

    Open ayah 13:3

    Shi ne kuma Wanda Ya shimfiɗa ƙasa Ya kuma sanya turaku (na duwatsu) a cikinta da ƙoramu; kuma daga kowaɗanne ‘ya’yan itace Ya sanya ma’aura biyu (mace da namiji); dare yana rufe rana. Lalle a game da waɗannan abubuwan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani.

  4. وَفِي ٱلۡأَرۡضِ قِطَعٞ مُّتَجَٰوِرَٰتٞ وَجَنَّٰتٞ مِّنۡ أَعۡنَٰبٖ وَزَرۡعٞ وَنَخِيلٞ صِنۡوَانٞ وَغَيۡرُ صِنۡوَانٖ يُسۡقَىٰ بِمَآءٖ وَٰحِدٖ وَنُفَضِّلُ بَعۡضَهَا عَلَىٰ بَعۡضٖ فِي ٱلۡأُكُلِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

    Open ayah 13:4

    A cikin ƙasa kuma da akwai yankuna masu maƙotaka da juna, da gonakai na inabai da shuke-shuke da dabinai masu tushiya ɗaya da kuma waɗanda suke kowane tushiyarsa daban, ana shayar da su da ruwa ɗaya, Muna kuma fifita wasunsu a kan wasu wajen ɗanɗano. Haƙiƙa a game da wannan da akwai ayoyi ga mutanen da suke da hankali. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori da suka gabace ta. Kamar yadda muka riga muka ambata cewa, malamai sun yi maganganu mabambanta game da manufar waɗannan haruffa, sai dai ana iya cewa, haruffan suna nuni ne zuwa ga mu’ujizar Alƙur’ani, watau duk da kasancewarsa magana ce da ta gudana da waɗannan haruffa waɗanda Larabawa ma da su suke magana, amma kuma sun kasa kawo wani abu kwatankwacin Alƙur’ani, wanda hakan yake tabbatar da cewa, shi maganar Allah ne ba ta wani mutum ba. Don haka ya bayyana cewa, waɗannan ayoyin da wannan Surar ta ƙunsa ayoyin Alƙur’ani ne wanda littafi ne da ya ƙunshi duk abin da ɗan’adam yake buƙatar sanin sa da ya danganci aƙida ko shari’a. Shi ne abin da Allah ya saukar wa Manzonsa wanda yake gaskiya ne babu wani kokwanto a cikinsa, to amma mutane da dama taurin kai da jayayya sun hana su ba da gakiya da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk halittun da suke sama da ƙasa suna nuna cikakken ikonsa ne da cancantar a bauta masa shi kaɗai, kuma shi ne ya halicci sammai; wata a saman wata, ba tare da ginshiƙai da suke riƙe da su waɗanda kuke iya ganinsu da idanunku ba. Sannan cikin cikar ɗaukakarsa ya daidaita a kan Al’arshinsa daidaitar da ta dace da kamalar Zatinsa. Haka kuma ya hore rana da wata domin amfanin halittunsa; rana da wata kowannensu yana gudu a cikin magudanarsa zuwa wani ƙayyadadden lokaci da Allah ne kaɗai ya san shi. Yana kuma gudanar da al’amuran da ya ga dama a cikin sammai da ƙasa babu mai hana shi. Wannan bayani ne na ayoyin Allah da yake yi wa mutane domin su tabbatar cewa, akwai ranar alƙiyama tana nan tafe, su tashi su yi tanadin aiki na ƙwarai don haɗuwa da Ubangijinsu a wannan rana. Sannan Allah ya ci gaba da bayyana dalilai na gani da ido masu tabbatar da Ɗayantakarsa da cikar Ƙudurarsa. Daga cikin ayoyi da suke nuna haka akwai duwatsu waɗanda suka zama turaku ga ƙasa don su hana ta motsi da mutanen da ke kanta. Kuma ya halicci ‘ya’yan itatuwa iri-iri kowannensu ya yi shi aure biyu, kamar yadda ya yi ɗan’adam da dabbobi mace da namiji. Haka kuma yana rufe hasken rana da duhun dare sai ko’ina ya zama duhu ƙirin. Ya bayyana cewa, duk waɗannan ayoyi ne, watau hujjoji ga mutane masu tunani game da ayyukan Allah (Mai tsarki da daukaka) don su fahimce su su ɗauki izina daga gare su sai hakan ya amfane su wajen gane girman Allah da kaɗaitakarsa. Ya kuma ci gaba da bayyana wasu dalilan na gani da ido masu tabbatar da cikakkiyar Ƙudurarsa, watau yadda ya halicci ƙasa iri daban-daban masu maƙotaka da juna waɗanda ake shuka abubuwa daban-daban a cikinsu kamar kayan marmari da hatsi da itatuwan dabino waɗanda suke da tushe ɗaya da waɗanda suke da tushe daban-daban, kuma ana shayar da su ruwa ɗaya, to amma sai su fito mabambanta a kamanni da ɗanɗano da girma duk kuwa da cewa, an shuka dukansu a ƙasa ɗaya kuma sun sha ruwa ɗaya. Lalle wannan yana nuna cikar Ƙudurar Allah wanda yake aikata abin da ba wani wanda zai iya aikata irinsa. Babu kuwa waɗanda suke fuskantar waɗannan ayoyi na Allah su fahimce su sai mutane masu hankali.

  5. ۞وَإِن تَعۡجَبۡ فَعَجَبٞ قَوۡلُهُمۡ أَءِذَا كُنَّا تُرَٰبًا أَءِنَّا لَفِي خَلۡقٖ جَدِيدٍۗ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ ٱلۡأَغۡلَٰلُ فِيٓ أَعۡنَاقِهِمۡۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

    Open ayah 13:5

    Idan kuwa kana mamakin (ƙaryata ka da suke yi), to ai abin mamaki shi ne faɗarsu (cewa): “Yanzu idan muka zama turɓaya anya kuwa za a sake halittarmu?” Waɗannan su ne waɗanda suka kafirce wa Ubangijinsu, waɗannan kuma akwai ƙuƙumi (da za a sa musu) a wuyoyinsu. Waɗannan kuwa su ne ‘yan wuta madawwama a cikinta.

  6. وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبۡلَ ٱلۡحَسَنَةِ وَقَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِمُ ٱلۡمَثُلَٰتُۗ وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغۡفِرَةٖ لِّلنَّاسِ عَلَىٰ ظُلۡمِهِمۡۖ وَإِنَّ رَبَّكَ لَشَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

    Open ayah 13:6

    Suna kuma nemanka da gaggauto musu da azaba tun kafin (su nemi) kyakkyawa (wato rahamar Allah), alhali kuwa haƙiƙa misalai (na waɗanda aka halakar) a gabansu sun wuce. Lalle kuma Ubangijinka Ma’abocin gafara ne ga mutane a kan laifuffukansu, kuma lalle Ubangijinka tabbas Mai tsananin azaba ne.

  7. وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦٓۗ إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرٞۖ وَلِكُلِّ قَوۡمٍ هَادٍ

    Open ayah 13:7

    Waɗanda suka kafirta suna cewa: “Me ya hana a saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa?” Lalle kai mai gargaɗi ne kawai; kowaɗanne mutane kuwa suna da mai shiryawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, idan akwai wani abin mamaki game da maganganun kafirai babu kamar ƙaryata ranar alƙiyama da suke yi, har suna tababa da cewa, yanzu ashe idan sun mutu sun zama ƙasa Allah zai iya sabunta halittarsu? Allah ya bayyana cewa, waɗannan masu wannan maganar su ne suka ƙaryata dawo da rai bayan mutuwa suka kafirce wa Allah Ubangijinsu domin sun nuna kasawar Ƙudurarsa ta tashin matacce bayan mutuwa. Don haka mummunan sakamakon da za su haɗu da shi ranar alƙiyama shi ne, za a sanya musu sarƙoƙin wuta a wuyansu, za kuma su zama ma’abotan wutar Jahannama masu zama a cikinta har abada ba za su mutu ba kuma azaba ba za ta yanke musu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci yadda waɗannan kafirai suke ƙaryata Annabi (ﷺ) game da kashedin da yake yi musu na azabar da za ta iya auka musu tun a nan duniya sakamakon kafircinsu, don isgili har suna neman sa da ya gaggauto musu da ita maimakon su roƙi rahamar Allah. Wannan yana nuna kafewarsu a kan kafircinsu da rashin yarda da gargaɗi da tsoratarwa da ake yi musu, alhali suna da labaran irin dangogin azaba da Allah ya saukar wa al\'ummun da suka gabace su waɗanda suka yi ayyukan kafirci irin nasu, to amma ba sa ɗaukan wani wa’azi ko izina daga gare su. Amma Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi cewa, lalle yana yin gafara ga mutane duk kuwa da laifuffukan da suke tafkawa, ya saurara musu don su tuba ya kuma karɓi tubansu, amma idan har suka doge a kan kafircinsu da miyagun halayensu to su sani cewa, shi fa mai tsananin azaba ne ga masu taurin kai su ƙi tuba, kuma yana iya gaggauto musu wani ɓangare na azabarsa tun a nan duniya kafin ta lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai suka riƙa ƙaryata annabcin Manzon Allah (ﷺ) kamar yadda suka ƙaryata zuwan ranar alƙiyama. Suka riƙa ƙalubalantar sa da ya nuna musu mu’ujiza irin ta annabawan da suka gabace shi kamar Annabi Musa da sandarsa ko Annabi Isa da yake raya matattu, to shi ma me ya sa ba a saukar masa tasa mu’ujizar ba wadda za su gani su yi imani da shi? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa, shi fa ba wani ba ne sai mai gargaɗi mai tsoratar da mutane azabar Allah, watau shi ba shi da wata mu’ujiza sai wadda Allah ya ba shi, kuma shi aiko shi aka yi zuwa ga mutane ya nuna musu gaskiya domin su bi ta, kuma kowace al’umma da aka taɓa yi a baya suna da annabinsu da Allah ya aiko shi gare su don ya nuna musu hanyar shiriya. Don haka wanda ya shiryu cikinsu don kansa, wanda kuma ya zaɓi ɓata kansa ya cutar ba wani ba.

  8. ٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تَحۡمِلُ كُلُّ أُنثَىٰ وَمَا تَغِيضُ ٱلۡأَرۡحَامُ وَمَا تَزۡدَادُۚ وَكُلُّ شَيۡءٍ عِندَهُۥ بِمِقۡدَارٍ

    Open ayah 13:8

    Allah Yana sane da abin da (mahaifar) kowace mace take ɗauke da shi da kuma abin da mahaifa take ragewa da wanda take ƙarawa; kowane abu kuma a wurinsa yana da gwargwado.

  9. عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ ٱلۡكَبِيرُ ٱلۡمُتَعَالِ

    Open ayah 13:9

    (Shi) Masanin abin da ke ɓoye da na sarari ne, Mai girma, Mai cikar ɗaukaka.

  10. سَوَآءٞ مِّنكُم مَّنۡ أَسَرَّ ٱلۡقَوۡلَ وَمَن جَهَرَ بِهِۦ وَمَنۡ هُوَ مُسۡتَخۡفِۭ بِٱلَّيۡلِ وَسَارِبُۢ بِٱلنَّهَارِ 

    Open ayah 13:10

    Duka ɗaya ne (a wurin Allah) wanda ya ɓoye magana daga cikinku da wanda ya bayyana ta da wanda yake ɓuya da daddare da mai bayyana da rana.

  11. لَهُۥ مُعَقِّبَٰتٞ مِّنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦ يَحۡفَظُونَهُۥ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوۡمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنفُسِهِمۡۗ وَإِذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِقَوۡمٖ سُوٓءٗا فَلَا مَرَدَّ لَهُۥۚ وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَالٍ

    Open ayah 13:11

    (Kowanensu) yana da (mala’iku) masu take masa baya a gabansa da kuma bayansa suna kiyaye shi da umarnin Allah. Lalle Allah ba Ya canja abin da mutane suke ciki har sai sun canja halayensu. Idan kuma Allah Ya yi nufin wata azaba ga mutane, to ba mai juyar da ita, ba su kuwa da wani mai jiɓintar su wanda ba Shi ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cikakkiyar Ƙudurarsa a kan ɗan’adam tun daga halittarsa a cikin mahaifiyarsa har zuwa fitowarsa duniya da rayuwarsa a bayan ƙasa. Allah ya bayyana cewa, yana sane da abin da kowace mace take ɗauke da shi a cikinta, ya san komai game da shi, ya san namiji ne ko mace, mai kyau ko mummuna, mumini ko kafiri, mutumin kirki ko na banza, wanda zai yi tsawon rai ko wanda ba zai yi ba, mai ilimi ko jahili. Yana sane da abin da yake ƙaruwa a mahaifa da abin da yake raguwa na lokacin haihuwarta, ko dai ta haihu kafin cikar wata tara ko ta haihu bayan cikar muddar cikinta, ko ɗan ya zo cikakke da ƙoshin lafiya ko kuma ya zo da wata nakasa ko rashin lafiya, komai a wurin Allah yana da gwargwadon yadda ya tsara shi ba zai ƙaru ba a kan haka ba kuma zai ragu ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah yana haɗa halittar ɗayanku a cikin mahaifiyarsa kwana arba’in yana ɗigon maniyyi; sannan ya zama gudan jini kwatankwacin haka; sannan ya zama tsoka kwatankwacin haka, sannan a aiko masa da mala’ika ya busa masa rai, a kuma umarce shi da abubuwa huɗu, da rubuta arzikinsa da ajalinsa da aikinsa da kuma shi ɗan wuta ne ko ɗan Aljanna.” [Bukhari #3208 da Muslim #6893]. Sannan Allah ya bayyana cewa, shi ne masanin duk wani gaibi wanda babu wanda ya san shi, kuma shi ne masanin duk wani abu na sarari da kowa zai iya gani. Shi ne mai girma a siffofinsa da sunayensa da ayyukansa, shi ne kuma maɗaukaki wanda yake sama da duk wani mahaluƙi da Zatinsa da siffofinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi masanin komai ne babu abin da yake ɓuya gare shi, domin kuwa duk ɗaya ne a wurinsa babu bambanci tsakanin wanda ya bayyana maganarsa a fili aka ji da wanda ya ɓoye ta a ransa bai furta ba, da wanda ya ɓoye kansa cikin dare da wanda ya fito fili rana tsaka, kuma babu wanda Allah bai san abin da yake aikatawa ko yake faɗa ba mai kyau ko mummuna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda yake tsaron kowane ɗan’adam ta hanyar sanya masa mala’iku a gabansa da bayansa, na rana daban na yamma daban, suna musanyan aiki a tsakaninsu, suna tsaron sa da umarnin Allah daga duk abin da zai cutar da shi wanda Allah ya umarce su su kare shi daga gare shi. Hakanan suna rubuta ayyukansa da maganganunsa ba sa barin komai. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mala’iku suna karɓa-karɓar aikin sa-ido a kanku, wasu da daddare wasu kuma da rana, suna haɗuwa a lokacin sallar asuba da sallar la’asar, sannan waɗanda suka kwana daga cikinsu sai su koma sama, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su, alhalin ya fi su sanin komai: “A wane hali kuka baro bayina?” Sai su ce: “Mun baro su suna salla, mun kuma same su suna salla.” [Bukhari #556 da Muslim #1464]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa bayinsa cewa, ba ya canja wani hali da mutane suke ciki na ni’ima da walwala har sai sun canja halayensu masu kyau sun koma ga marasa kyau. Kamar yadda ba zai canja musu wani mummunan hali da suka shiga ba har sai sun canja munanan halayensu sun riƙi kyawawa. Sannan ya tabbatar musu da cewa, idan ya nufi bayinsa da wata azaba saboda miyagun halayensu na kafirci da saɓon Allah, to babu wanda ya isa ya kawar musu da wannan azabar, ba kuma su da wanda zai jiɓinci al’amuransu ya samar musu abin da suke so, ya kare su daga abin da suke ƙi wanda ba Allah ba. Don haka su guji aikata abin da zai jawo musu fushin Allah da azabarsa, ko kuma su rasa mai kare su.

  12. هُوَ ٱلَّذِي يُرِيكُمُ ٱلۡبَرۡقَ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَيُنشِئُ ٱلسَّحَابَ ٱلثِّقَالَ

    Open ayah 13:12

    Shi ne Wanda Yake nuna muku walƙiya don tsoratarwa da kuma kwaɗaitarwa, Yake kuma haɗo hadari mai nauyi (ɗauke da ruwa).

  13. وَيُسَبِّحُ ٱلرَّعۡدُ بِحَمۡدِهِۦ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ مِنۡ خِيفَتِهِۦ وَيُرۡسِلُ ٱلصَّوَٰعِقَ فَيُصِيبُ بِهَا مَن يَشَآءُ وَهُمۡ يُجَٰدِلُونَ فِي ٱللَّهِ وَهُوَ شَدِيدُ ٱلۡمِحَالِ

    Open ayah 13:13

    Tsawa tana tsarkake (Shi) tare da gode masa, mala’iku ma (suna tasbihi) saboda tsoron Sa, Yana kuma aiko da tsawawwaki sai Ya sami wanda Ya ga dama da su, kuma su (waɗannan kafirai) ga su suna jayayya game da (sha’anin) Allah. Shi kuwa Mai tsananin ƙarfi ne.

  14. لَهُۥ دَعۡوَةُ ٱلۡحَقِّۚ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَجِيبُونَ لَهُم بِشَيۡءٍ إِلَّا كَبَٰسِطِ كَفَّيۡهِ إِلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَٰلِغِهِۦۚ وَمَا دُعَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ

    Open ayah 13:14

    Gare Shi (Shi kaɗai) kira na gaske yake; waɗanda kuwa suke bauta wa wasu ba Shi ba, to ba sa amsa musu da komai illa tamkar wanda ya shimfiɗa tafukansa ga ruwa don ya isa bakinsa, ba kuwa zai isa gare shi ba. Addu’ar kafirai kuma ba a komai take ba illa a cikin ɓata.

  15. وَلِلَّهِۤ يَسۡجُدُۤ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ طَوۡعٗا وَكَرۡهٗا وَظِلَٰلُهُم بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ۩

    Open ayah 13:15

    Waɗanda kuma suke sammai da ƙasa (duka) ga Allah suke sujjada sun so ko sun ƙi, haka kuma inuwoyinsu, safe da maraice. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ƙarin wasu ayyukansa masu nuna cikar Ƙudurarsa da buƙatuwar bayinsa gare shi da cancantar a bauta masa shi kaɗai da rashin cancantar a bauta wa wasu ba shi ba. Ya bayyana cewa, shi ne yake nuna wa mutane walƙiya yayin da hadari ya haɗo don tsoratarwa ga wasu kamar matafiya a hanya ko wanda ya yi shanyar kayansa domin busar da su, ko kuma domin kwaɗaitarwa ga wasu kamar manoma masu jiran ruwa domin amfanin gonakinsu ya yi kyau, yana kuma haɗo da hadari mai nauyi wanda yake ɗauke da ruwa. Daga cikin cikar Ƙudurarsa tsawa ma tana tsarkake shi da yin tasbihi tare da gode masa. Hakanan su ma mala’iku koyaushe cikin yi masa tasbihi suke suna cike da tsoronsa da girmama shi. Tare da waccan walƙiya mai ba da tsoro da kwaɗaitarwa, har ila yau, yana aiko da tsawa, watau aradu, ɗauke da wuta, ya jefa ta a kan wanda ya ga dama daga cikin bayinsa ya halaka shi da ita. An karɓo daga Abdullahi ɗan Zubairu (Allah ya kara masa yarda) ya kasance idan ya ji rugugin tsawa (aradu) sai ya yi shiru ya bar maganar da yake yi ya ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda tsawa ke tsarkake shi tare da gode masa, mala’iku ma suke masa tasbihi tare da tsoron sa.” [Bukhari, Al-adabul Mufrad #723 da Malik, Muwaɗɗa #1822]. Abdullahi ɗan Abbas ya kasance idan ya ji rugugin tsawa yakan ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda tsawa (aradu) ta yi masa tasbihi.” [Bukhari, Al-adabul Mufrad #722]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai suna jayayya a kan kaɗaita shi da bauta, alhalin shi mai tsananin ƙarfi ne ga duk mai saɓa masa. Sannan ya bayyana cewa, shi ne kaɗai ya cancanci kira na gaskiya, wato kira zuwa ga Tauhidi, kuma shi ne kaɗai mai amsa addu’a na gaskiya, amma duk sauran abubuwan da mushirikai suke bauta wa tare da shi ba za su iya tsinana musu komai ba, domin ko roƙon su da suke yi ba za su iya amsa musu shi ba, hasali ma sun zama kamar mai jin ƙishirwa ne da zai riƙa miƙa hannunsa ga ruwa yana jiran ya taso ya kai bakinsa sannan ya sha, to da zai shekara ɗari a haka ba ranar da wannan ruwan zai taso da kansa ya shiga bakinsa. Don haka abin da yake yi aikin wofi ne marar amfani. To haka bautar duk wani mai bautar wanin Allah take; mai roƙon sa da neman agaji a wurinsa ba zai taɓa samun biyan buƙatarsa ba sai dai ya yi ta shan wahalar banza. Don haka Allah ya tabbatar da cewa, addu’ar kafirai ga gumakansu a banza da wofi take tafiya ba za ta amfane su da komai ba sai tsabar wahala. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wata halitta da ke sammai da wadda take ƙasa tana rusuna wa Allah da sujjada, sun so ko sun ƙi. Mumini shi ne wanda yake miƙa wuyansa ga Allah da zaɓinsa, kafiri kuwa shi ne wanda yake rusuna wa Allah ba da sonsa ba, sai dai don ya zama dole ya bi dokokin Allah na halittarsa, gaɓoɓinsa su gudanar da aikinsu kamar yadda Allah ya nufe su su yi, shi ma kansa ya buƙatu ga duk wani abu da Allah ya sanya rayuwarsa ba za ta yiwu ba sai da shi, kamar ci da sha da barci da makamantansu. Hakanan duk inuwowin halittu na sammai da ƙasa suna sujjada ga Allah safe da maraice. Wannan kuwa babbar aya ce mai tabbatar da cewa, Allah ne kaɗai ya cancanci a bauta masa; duk wani abin bauta ba shi ba ƙarya ne.

  16. قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ قُلِ ٱللَّهُۚ قُلۡ أَفَٱتَّخَذۡتُم مِّن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ لَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ نَفۡعٗا وَلَا ضَرّٗاۚ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ أَمۡ هَلۡ تَسۡتَوِي ٱلظُّلُمَٰتُ وَٱلنُّورُۗ أَمۡ جَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ خَلَقُواْ كَخَلۡقِهِۦ فَتَشَٰبَهَ ٱلۡخَلۡقُ عَلَيۡهِمۡۚ قُلِ ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُوَ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّٰرُ

    Open ayah 13:16

    Ka ce (da su): “Wane ne Ubangijin sammai da ƙasa?” Ka ce: “Allah ne”. Ka ce (da su): “Amma yaya kuka riƙi wasu iyayen giji ba Shi ba su zama majiɓinta (gare ku), ba sa mallakar wani amfani ko cuta ga kansu?” Ka ce: “Shin makaho da mai gani za su yi daidai, ko kuwa shin duhu da haske za su yi daidai? Ko sun sanya wa Allah wasu abokan tarayya ne waɗanda suka yi halitta kamar halittarsa, sai halittar ta yi musu kama da juna?” Ka ce: “Allah ne Mahaliccin komai, kuma Shi ne Makaɗaici, Mai rinjaye.”

  17. أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَسَالَتۡ أَوۡدِيَةُۢ بِقَدَرِهَا فَٱحۡتَمَلَ ٱلسَّيۡلُ زَبَدٗا رَّابِيٗاۖ وَمِمَّا يُوقِدُونَ عَلَيۡهِ فِي ٱلنَّارِ ٱبۡتِغَآءَ حِلۡيَةٍ أَوۡ مَتَٰعٖ زَبَدٞ مِّثۡلُهُۥۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ وَٱلۡبَٰطِلَۚ فَأَمَّا ٱلزَّبَدُ فَيَذۡهَبُ جُفَآءٗۖ وَأَمَّا مَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ فَيَمۡكُثُ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَالَ

    Open ayah 13:17

    Ya saukar da ruwa daga sama, sai magudanai suka kwarara daidai gwargwadon abin da za su iya ɗauka, sai (shi ruwan) mai kwarara ya ɗauko kumfa a samansa. Akwai kuma wata kumfar kamarta daga abin da kuke narkawa a wuta don samun abin ado ko kuwa (ƙera) abin jin daɗi. Kamar haka ne Allah Yake ba da misalin gaskiya da ɓarna. To amma kumfar sai ta tafi ta bi iska; amma kuma abin da zai amfani mutane sai ya zauna a ƙasa. Kamar haka ne Allah Yake ba da misali. A waɗannan ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Larabawa sun yi imani da cewa, Allah shi ne mahaliccin sammai da ƙasa babu wani gunki daga cikin gumakan da suke bauta wa da ya halicce su, amma duk da haka sun nace a kan bautar gumaka ba Allah ba, saboda haka Allah ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambaye su, wane ne ya halicci sammai da ƙasa? Ya kuma umarce shi da ya ba su amsar cewa, Allah ne mahaliccinsu mai kuma gudanar da su yadda ya ga dama, babu kuma mai musun haka. To amma kuma yaya aka yi suka rungumi wasu abubuwa waɗanda ba za su iya amfanar kansu da komai ba, ba kuma za su iya kare kansu daga wata cuta ba ballantana har su yi wa wani haka, suka mayar da su majiɓinta al’amuransu ba Allah ba? Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ƙalubalance su da wasu tambayoyi waɗanda suke nuna tufka da warwara cikin aƙidunsu, inda ya ce, shin yanzu kafiri mai makauniyar basira da mumini mai ganin shiriyar Allah za su yi daidai? Ko kuma kafirci, wanda duhu ne, da imani, wanda shi kuma haske ne, za su yi daidai? Ko kuma suna ganin akwai wasu abokan tarayya da Allah waɗanda su ma suka yi halitta kamar yadda ya yi, don haka sai halittun nasa da nasu suka gauraya su kuma suka kasa tantance na kowa, don haka suka zaɓi su bauta musu tare da shi? Babu shakka amsoshin waɗannan tambayoyi duka a fili suke, saboda dalilan da suka gabata masu tabbatar da Kaɗaitakar Allah a cikin siffofinsa da ayyukansa. Don haka ya umarci Annabi (ﷺ) ya tabbatar musu cewa, Allah ne mahaliccin komai, babu wanda ya yi tarayya da shi cikin halittarsa kuma shi ne kaɗai abin bauta mai rinjaye a kan kowa da komai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayar da wasu misalai guda biyu masu nuna rugujewar ƙarya da gaggawa, da kuma wanzuwar gaskiya da tabbatarta har abada. <b>Misalin farko </b> shi ne ruwan da ya sauka daga sama, ya kwarara cikin rafuka har suka cika taf suna gudu har suka haifar da wata gagarumar kumfa wadda daga ƙarshe za ta baje ta bi iska. A nan Allah ya kwatanta gaskiya da wannan ruwan wanda shi ne zai ci gaba da zama a ƙasa mutane su amfana da shi wajen shansu da shayar da dabbobinsu da shuke-shukensu. Ya kuma kwatanta ƙarya da wannan kumfar da ta taso saman ruwan, ga ta da fari da ɗaukar hankali, amma ba ta da wani amfani ga kowa, daga ƙarshe ma sai ta gushe a neme ta a rasa. <b>Misali na biyu </b> kuwa shi ne wajen dahuwar tama ko ma’adanan ƙasa da mutane kan yi, yayin da wata kumfa takan taso wadda ita ma takan gushe da gaggawa da zarar wutar dahuwar ta lafa ko an kashe ta, a ƙarshe sai ruwan waɗannan ma’adanan ko tamar shi ne zai wanzu mutane su amfana da shi wajen ƙere-ƙerensu na kayan ado. To duk waɗannan misalan biyu suna nuna cewa, gaskiya ita ce mai tabbata, mai amfani ga mutane, ƙarya kuwa mai gushewa ce ba za ta amfani kowa ba. Da waɗannan misalan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake bayyana misalin gaskiya da ƙarya. Ƙarya kamar sharar ruwa ce da kumfarsa mai yawo a kansa, kuma ta yi kama da dattin da yake fita da tsatsa daga ƙarafan ma’adanai yayin da suka sha wuta. Gaskiya kuwa ita ce kamar tataccen ruwa wanda ake sha, yake fitar da tsirrai da ‘ya’yan itatuwa da ciyawar dabbobi. Haka kuma ta yi kama da abin da yake wanzuwa na ma’adanai bayan an narka shi da wuta, wanda da shi ne, mutane suke amfani wajen ƙere-ƙerensu. To irin waɗannan misalan ne Allah yake ba wa mutane domin su bambance tsakanin ƙarya da gaskiya. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Misalin abin da Allah ya aiko ni da shi na shiriya da ilimi kamar misalin mamakon ruwa ne da ya sauka a wata ƙasa, wani ɓangare nata ƙasa ce mai kyau ta sha ruwan ta fitar da abincin dabbobi da ingirici mai yawa, wani ɓangarenta kuwa tsandauri ne don haka ta riƙe ruwa, Allah ya amfanar da mutane da ita, suka sha ruwan kanta suka shayar da dabbobinsu suka kuma yi shuke-shuke. Sannan ruwan ya sauka wani ɓangare na ƙasa wadda ƙeƙuwa ce ba ta riƙe ruwa ba kuma ta fitar da abincin dabbobi. To wannan shi ne misalin wanda ya fahimci addinin Allah, abin da Allah ya aiko ni da shi ya amfane shi, ya koya ya koyar. Da kuma misalin mutumin da bai damu da hakan ba, bai kuma karɓi shiriyar da Allah ya aiko ni da ita ba.” [Bukhari #79 da Muslim #2282].

  18. لِلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِرَبِّهِمُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُۥ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦٓۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ سُوٓءُ ٱلۡحِسَابِ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

    Open ayah 13:18

    Waɗanda suka amsa (kiran) Ubangijinsu suna da kyakkyawar (makoma). Waɗanda kuwa ba su amsa ba, da a ce duk abin da ke ƙasa gaba ɗaya tare kuma da wani kwatankwacinsa duka nasu ne, to da lalle sun fanshi kansu da shi (ranar alƙiyama). Waɗannan suna da mummunan hisabi, kuma Jahannama ce makomarsu, kuma tir da wannan shimfiɗa.

  19. ۞أَفَمَن يَعۡلَمُ أَنَّمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ كَمَنۡ هُوَ أَعۡمَىٰٓۚ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

    Open ayah 13:19

    Yanzu wanda ya san cewa abin da aka saukar maka daga Ubangijinka gaskiya ne (zai zama) kamar wanda yake shi makaho ne? Lalle ma’abota hankali ne kaɗai ke wa’azantuwa.

  20. ٱلَّذِينَ يُوفُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَلَا يَنقُضُونَ ٱلۡمِيثَٰقَ 

    Open ayah 13:20

    (Su ne) waɗanda suke cika alƙawarin Allah kuma ba sa warware alƙawarin.

  21. وَٱلَّذِينَ يَصِلُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ وَيَخَافُونَ سُوٓءَ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 13:21

    Waɗanda kuma suke sadar da abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (na zumunci), suke kuma tsoron Ubangijinsu, kuma suke tsoron mummunan hisabi.

  22. وَٱلَّذِينَ صَبَرُواْ ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ

    Open ayah 13:22

    Waɗanda kuma suka yi haƙuri don neman yardar Ubangijnsu, suka kuma tsai da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi a ɓoye da sarari, suke kuma ingije mummunan aiki da kyakkyawa, waɗannan suna da (kyakkyawar) makoma ta gidan (Aljanna).

  23. جَنَّٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَدۡخُلُونَ عَلَيۡهِم مِّن كُلِّ بَابٖ

    Open ayah 13:23

    Gidajen Aljanna na dawwama, za su shiga su da waɗanda suka kyautata (aiki) daga iyayensu da matansu da kuma zuriyarsu; mala’iku kuma za su riƙa shigowa wurinsu ta kowace ƙofa.

  24. سَلَٰمٌ عَلَيۡكُم بِمَا صَبَرۡتُمۡۚ فَنِعۡمَ عُقۡبَى ٱلدَّارِ

    Open ayah 13:24

    (Suna ce musu): “Aminci ya tabbata a gare ku saboda haƙurin da kuka yi. To madalla da gida na ƙarshe (watau Aljanna)”.

  25. وَٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهۡدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مِيثَٰقِهِۦ وَيَقۡطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ

    Open ayah 13:25

    Waɗanda kuma suke warware alƙawarin Allah bayan sun ƙulla shi, suke kuma yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi, kuma suke ɓarna a bayan ƙasa, waɗannan la’ana ta tabbata a gare su kuma suna da (sakamakon) mummunan gida (shi ne Jahannama). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kasuwar mutane gida biyu: <b>Na farko </b>, waɗanda suka amsa kiran Ubangijinsu na kaɗaita shi da bauta da ɗa’a ga Manzonsa (ﷺ), to waɗannan ya yi musu tanadin sakamako mafi kyau, watau Aljanna. <b>Na biyu </b> kuwa, su ne mutanen da suka ƙi karɓar kiran Allah na kaɗaita shi da bauta, suka kuma ƙi biyayya ga Manzonsa (ﷺ), to waɗannan suna da sakamakon mummunar azaba. Saboda tsammaninta da sun san za a ba su fansar kawunansu idan sun bayar da duk dukiyoyin da suka mallaka da sun yarda sun bayar don su fanshi kawunansu, to amma Allah ya bayyana musu cewa, da a ce za su mallaki duk dukiyar da take bayan ƙasa, a kuma haɗa da wata kamarta su bayar da ita gaba ɗaya wajen fansar kawunansu daga wannan azabar, to ba za a karɓe ta daga wurinsu ba a ba su fansa. Allah ya tabbatar da cewa, za su gamu da mummunan bincike game da munanan ayyukansu, sannan daga ƙarshe mazauninsu shi ne wutar Jahannama wadda za a yi musu shimfiɗa da ita. Lalle kuwa wannan shimfiɗa ta yi matuƙar muni. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwatanta kashi na farko waɗanda su ne suka yi ilimi mai amfani suka kuma yi aiki da iliminsu suka yarda da abin da Allah ya saukar wa Annabi (ﷺ) gaskiya ce da babu wani kokwanto a cikinta, ya kwatanta su da mutum mai gani tar. Sannan ya kwatanta kashi na biyu, watau waɗanda suka ƙi karɓar kira zuwa ga kaɗaita Allah da bauta, suka ƙi yin imani da Alƙur’ani, ya kwatanta su da mutum makaho wanda ba ya ganin komai da ke gabansa balle ya nufi inda yake da lafiya, ya kauce wa abin da zai cutar da shi. Allah ya tabbatar da cewa, waɗannan nau’in mutane biyu ba za su taɓa zama daidai ba, amma ba kowa ne yake ɗaukar wa’azi ya fahimci misalan da Allah ke bayarwa ba sai mutane masu lafiyayyen hankali kaɗai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffofi takwas na mutanen da suka karɓi kiran Allah da Manzonsa, waɗanda su ne kamar haka: 1. Su ne masu cika alƙawarin da suka ɗauka tsakaninsu da Allah ko tsakaninsu da mutane, ba sa yarda su warware su. 2. Su ne waɗanda suke sada zumuncin da ke tsakaninsu da Allah na bautar sa shi kaɗai da bin umarninsa da barin haninsa, da kuma zumuncin da ke tsakaninsu da junansu na ‘yan’uwantaka, ba sa yanke shi. 3. Su ne masu tsoron Ubangijinsu don haka suke aikata abin da ya wajabta musu suke barin abin da ya hana su. 4. Su ne masu tsoron ranar hisabi ranar alƙiyama, domin sun yi imani da cewa, duk wanda aka yi masa hisabi na ƙeƙe da ƙeƙe to ya halaka. 5. Su ne masu haƙuri a kan bin Allah da haƙuri a kan abin da ya same su na ƙaddara marar daɗi, da haƙuri a kan kauce wa saɓon Allah, ba don wani abu ba sai domin neman yardar Allah (Mai tsarki da daukaka). 6. Su ne masu tsayar da salla a lokutanta da sharuɗɗanta yadda ya kamata ba tare da sakaci ba. 7. Su ne masu fitar da haƙƙoƙin da ke cikin dukiyoyinsu su bayar a ɓoye don guje wa riya, ko a sarari don a gani a yi koyi da su. 8. Su ne masu saka mummuna da kyakkyawa, watau ba sa ramuwar gayya ko da an cutar da su, sukan kyautata wa wanda ya munana musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, sakamakon waɗannan mutane masu irin waɗannan kyawawan siffofin ita ce Aljanna, gidan da za su shige shi su zauna har abada babu mai fitar da su. Yana daga cikin cikar ni’imar da Allah zai yi musu a Aljanna shi ne ya haɗa su wuri ɗaya da ‘yan’uwansu waɗanda suka cancanci shiga Aljanna da kyawawan ayyukansu. Daga cikinsu akwai iyayensu maza da mata da matansu na aure da ‘ya’yansu domin ya ɗebe musu duk wata kewa. Baya ga wannan kuma mala’iku suna kawo musu ziyara suna shigowa ta ƙofofi daban-daban suna gaishe su da sallama, suna faɗa musu cewa, aminci ya tabbata gare su a kan haƙurin da suka yi a duniya. Madalla da wannan gidan na ƙarshe, watau Aljanna. Bayan Allah ya ambaci siffofin waɗanda suka amsa kiransa da sakamakonsu, sai kuma ya ambaci siffofin waɗanda suka ƙi amsa kiransa suka kafe a kan bautar waninsa. Su kuma siffofinsu guda uku ne: <b>Na farko </b>, warware alƙawarinsu tsakaninsu da Allah na su bauta masa shi kaɗai ba tare da abokin tarayya ba, sai suke yin shirka da shi. <b>Na biyu </b>, yanke zumuntar da Allah ya yi umarni a sadar da ita. <b>Na uku </b>, yaɗa ɓarna a bayan ƙasa ta hanyar kafirci da saɓon Allah da zaluntar bayin Allah da hana mutane karɓar gaskiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗannan da cewa, sun cancanci la’anar Allah da ta mala’ikunsa da bayinsa muminai, don haka sun yi nisa daga samun rahamar Allah, makomarsu ita ce mummunar azaba ta wutar Jahannama. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Alamomin munafuki uku ne: Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya; idan ya yi alƙawari sai ya saɓa; idan kuma aka amince masa to zai ci amana.” [Bukhari #33 da Muslim #59]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya halicci halitta, bayan ya gama halittar sai zumunta ta tashi ta ce: “Wannan wurin tsayuwa ne na mai neman tsarinka daga yanke zumunci.” Sai Allah ya ce: “E, haka ne. Shin ba za ki yarda in sadar da wanda ya sadar da ke ba, in kuma yanke duk wanda ya yanke ki?” Zumunta ta ce: “E, na yarda!” Allah ya ce: “To na ba ki wannan.” [Bukhari #4830 da Muslim #2554].

  26. ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ وَفَرِحُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا مَتَٰعٞ

    Open ayah 13:26

    Allah ne Yake shimfiɗa arziki ga wanda Ya ga dama, Yake kuma ƙuntatawa (ga wanda Ya ga dama. (Kafirai) kuma sun yi farin ciki da rayuwar duniya, rayuwar duniya kuwa ba komai ba ce illa ɗan jin daɗi kaɗan dangane da na lahira.

  27. وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَنۡ أَنَابَ

    Open ayah 13:27

    Waɗanda suka kafirta kuma suna cewa: “Me ya hana a saukar masa da aya daga Ubangijinsa?” Ka ce: “Lalle Allah Yana ɓatar da wanda Ya ga dama, Yana kuma shiryar da wanda ya koma gare Shi.

  28. ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَطۡمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكۡرِ ٱللَّهِۗ أَلَا بِذِكۡرِ ٱللَّهِ تَطۡمَئِنُّ ٱلۡقُلُوبُ

    Open ayah 13:28

    “(Su ne) waɗanda suka yi imani , zukatansu kuma suna nutsuwa da ambaton Allah. Ku saurara, da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa.

  29. ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ طُوبَىٰ لَهُمۡ وَحُسۡنُ مَـَٔابٖ

    Open ayah 13:29

    “Waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to farin ciki ya tabbata a gare su da kuma kyakkyawar makoma.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, arziki duka yana hannunsa ne, shi ne wanda yake rabon sa yadda ya ga dama, ya yalwata wa wanda ya ga dama cikin bayinsa, ya ƙuntata wa wanda ya ga dama gwargwadon hikimarsa da adalcinsa. Don haka ba wa wani arziki ba ya nufin Allah ya fifita shi ko ya zaɓe shi a kan wanda bai ba wa arzuki ba, hakanan wanda ya ƙuntata masa arzikinsa ba yana nufin ba ya son sa ba ne. To amma su kafirai suna farin cikin sun samu jin daɗin duniya, don haka suka maida hankalinsu a kanta ba sa tunanin lahira ko kaɗan, sun manta da cewa, ita rayuwar duniya idan an kwatanta ta da rayuwar lahira ai ɗan jin daɗi ne ɗan kaɗan mai gajeren lokaci zai zo ya wuce kamar ba a yi ba. An karɓo daga Al-Mustaurid (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duniya idan an kwatanta ta da lahira ba wani abu ba ce sai kamar ɗayanku ne da zai sa ɗan yatsansa a cikin teku, ya duba ya ga abin da zai fito da shi (na ruwan wannan tekun).” [Muslim #2858]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin abin da kafirai suke ƙalubalantar Manzon Allah (ﷺ) da shi, suna cewa, me ya hana Allah ya saukar masa da wata mu’ujiza wadda za su gani da idanunsu su yarda cewa, da gaske Allah ne ya aiko shi, kuma abin da yake karanta musu na Alƙur’ani gaskiya ne? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa, Allah shi ne wanda yake ɓatar da wanda ya ga dama da adalcinsa, ya shiryi wanda ya ga damar shiriyarsa da falalarsa, don haka su sani cewa, abin ba a hannunsu yake ba ballantana su danganta shi da saukar wata mu’ujiza daga sama, domin ko da Allah ya saukar da mu’ujizar idan bai ga damar su shiriya ba to ba za su shiryu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffar waɗanda suke shiryuwa da shiriyarsa da cewa, su ne waɗanda suka yi imani da shi a matsayin Allah Ɗaya abin bauta ba tare da shirka ba, kuma zukatansu suke samun nutsuwa da ambaton Allah da karatun littafinsa Alƙur’ani da sauraronsa. Lalle kuwa da ambaton Allah ne kaɗai zukata kan samu natsuwa da gushewar kewa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ambaton siffofin waɗannan bayi nasa nagari da cewa, su ne waɗanda suka yi imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar lahira sannan ayyukansu na ƙwarai suka gaskata imaninsu. Allah kuma ya tabbatar musu da samun gwaggwaɓan sakamako a lahira domin za su gamu da farin ciki mai ɗorewa a gidan Aljanna.

  30. كَذَٰلِكَ أَرۡسَلۡنَٰكَ فِيٓ أُمَّةٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهَآ أُمَمٞ لِّتَتۡلُوَاْ عَلَيۡهِمُ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَهُمۡ يَكۡفُرُونَ بِٱلرَّحۡمَٰنِۚ قُلۡ هُوَ رَبِّي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ مَتَابِ 

    Open ayah 13:30

    Kamar haka Muka aiko ka cikin al’umma wadda tuni wasu al’ummun sun wuce kafinta, don ka karanta musu abin da Muka yi maka wahayinsa, alhali kuwa su suna kafirce wa Arrahamanu . Ka ce: “Shi ne Ubangijina, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, gare Shi kawai na dogara, kuma gare Shi kawai tubata take.”

  31. وَلَوۡ أَنَّ قُرۡءَانٗا سُيِّرَتۡ بِهِ ٱلۡجِبَالُ أَوۡ قُطِّعَتۡ بِهِ ٱلۡأَرۡضُ أَوۡ كُلِّمَ بِهِ ٱلۡمَوۡتَىٰۗ بَل لِّلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ جَمِيعًاۗ أَفَلَمۡ يَاْيۡـَٔسِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن لَّوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَهَدَى ٱلنَّاسَ جَمِيعٗاۗ وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ تُصِيبُهُم بِمَا صَنَعُواْ قَارِعَةٌ أَوۡ تَحُلُّ قَرِيبٗا مِّن دَارِهِمۡ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ وَعۡدُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ

    Open ayah 13:31

    Da a ce akwai wani abin karantawa da za a gusar da duwatsu da shi, ko kuma a keta ƙasa da shi, ko kuma a yi magana da matattu da shi, (to da wannan Alƙur’anin ne). Bari dai, dukkanin al’amari gaba ɗaya na Allah ne. Shin waɗanda suka yi imani ba su san da cewa da Allah Ya ga dama da Ya shiryi mutane gaba ɗaya ba? Kafirai kuwa azaba ba za ta daina samun su ba saboda abin da suka aikata, ko kuwa ta faɗo kusa da gidajensu har sai alƙawarin Allah ya zo. Lalle Allah ba Ya saɓa alƙawari.

  32. وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَأَمۡلَيۡتُ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ عِقَابِ

    Open ayah 13:32

    Haƙiƙa an yi wa manzannin da suka gabace ka izgili, sai Na yi wa waɗanda suka kafirta talala, sannan Na damƙe su. To yaya uƙubata ta kasance (a gare su)? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wa Annabi (ﷺ) cewa, ba shi ne farau ba a cikin manzanni; gabaninsa Allah ya aiko da wasu annabawa da yawa zuwa ga al\'ummunsu. Don haka shi ma ya aiko shi ne zuwa ga wannan al’umma domin ya karanta musu Alƙur’ani da aka yi masa wahayinsa wanda ya isa ya zama dalili mai nuna gaskiyarsa, da a ce kafirai za su nutsu su saurare shi su yi tunani a kai, to amma abin takaicin shi ne suna jayayya da musu ne a kan haka, domin ta kai su har suna kafirce wa sunan Allah mai rahama baya ga shirka da shi da suke yi. Kafiran Ƙuraishawa sun kasance suna ƙyamar su siffanta Allah da Mai rahama, domin haka ne a lokacin sulhun Hudaibiyya da Manzon Allah (ﷺ) ya yi umarni da rubuta ‘Bismillahir Rahmanir Rahim ’ a takardar sulhu suka ƙi amincewa, suka ce su sam ba su san haka ba. [Dubi, Bukhari #2731, 2732]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: Lalle sunayen da Allah ya fi so su ne Abdullahi da Abdurrahman.” [Muslim #2132]. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa kafirai cewa, shi mai wannan suna Arrahmanu wanda suke kafirce wa, shi ne Ubangijinsa abin bautarsa na gaskiya, wanda kuma da shi ya dogara cikin duk al’amuransa, kuma gare shi yake tuba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da kasancewar Alƙur’ani shi ne mafi girman mu’ujizar Annabi (ﷺ) kuma ba a taɓa samun wata mu’ujiza ta wani annabi da ta kai tasa ba. Allah ya bayyana cewa, da akwai wani littafi daga littattafan da ya saukar wanda duwatsu za su riƙa barin wurarensu saboda shi, ko kuma a tsattsage ƙasa da shi, ta koma gaba ɗayanta ta zama ƙoramu da marmaro na ruwa, ko kuma a karanta shi ga matattu su sake rayuwa, to da kuwa wannan Alƙur’anin ne da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Manzonsa Muhammadu (ﷺ), watau shi ne zai zamanto da irin wannan matsayi a cikin sauran littattafan da Allah ya saukar, domin shi hujja ce bayyananniya mai matuƙar tasiri ga zukata, da a ce su waɗannan kafiran suna da zukata masu tsoron Allah, to amma ina! Sun kasance kawai masu jayayya ne da ƙaryatawa, ba su san cewa, duk wani al’amari na Allah ne ba, daga ciki har da batun saukar da wata mu’ujiza wadda suke nema. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin muminai da cewa, ba su san da cewa idan da Allah ya ga damar ya shiryar da mutane gaba ɗaya, ba tare da saukar da wata mu’ujiza ba, ai da ya aikata haka, domin babu wani abu da zai gagare shi, to amma kuma ba haka ya ga dama ba. Sannan Allah ya tsoratar da kafirai da irin azabar da za ta same su idan suka ci gaba da ƙaryata gaskiya da jayayya da Annabi (ﷺ), ya tabbartar musu da cewa, ba za su gushe ba wata matsananciyar musiba mai ƙwanƙwasa tana auka musu saboda kafircinsu da yawan saɓon Allah da suke yi, ko kuma wata azaba ta sauko kusa da gidajensu, watau Annabi (ﷺ) da sahabbansa su kai musu farmaki har gida su ci su da yaƙi. Sannan azabar duniya ta ci gaba da samun su har lokacin da alƙawarin Allah zai zo, shi ne tashin alƙiyama a lokacin da za su gamu da azaba marar yankewa, kuma wannan abu ne tabbatacce domin Allah ba ya saɓa alƙawari. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) da cewa, ya yi haƙuri a kan abin da yake gani na izgili da gallazawa da kafirai suke yi masa; ba a kansa aka fara yin haka ba, kafiran da suka gabata sun yi wa manzanninsu irin wannan izgilin da cin zarafi, kuma Allah ya saurara musu na wani ɗan lokaci har suka fara zaton ko manzanninsu ƙarya suke faɗa musu, kuma ma babu abin da zai same su, sai kawai Allah ya damƙe su mummunar damƙa, ya saukar musu da azabarsa iri-iri wadda idan mutum ya gan ta zai ga irin tsananinta, to don haka su ma waɗannan kafiran kada su ruɗu da jinkirtawar da ake musu, duk ranar da Allah zai damƙe su ba za su ji da daɗi ba.

  33. أَفَمَنۡ هُوَ قَآئِمٌ عَلَىٰ كُلِّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۗ وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ قُلۡ سَمُّوهُمۡۚ أَمۡ تُنَبِّـُٔونَهُۥ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَم بِظَٰهِرٖ مِّنَ ٱلۡقَوۡلِۗ بَلۡ زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ مَكۡرُهُمۡ وَصُدُّواْ عَنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ

    Open ayah 13:33

    Yanzu wanda Yake tsaye a kan kula da kowane rai game da abin da ya aikata, (zai zama daidai da wanda ba haka ba?) Sun kuma sanya wa Allah abokan tarayya. Ka ce: (da su) “Ku faɗa min sunayensu. Ko kuwa kuna ba Shi labarin abin da bai sani ba ne a bayan ƙasa, ko kuma dai kun riƙe wata ɓatacciyar magana ce?” Bari dai; an dai ƙawata wa kafirai makircinsu ne kawai, aka kuma toshe musu hanyar (Allah). Wanda kuwa Allah Ya ɓatar to ba shi da wani mai shiryarwa.

  34. لَّهُمۡ عَذَابٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَقُّۖ وَمَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ

    Open ayah 13:34

    Suna da wata azaba a rayuwar duniya; kuma lalle azabar lahira ita ta fi tsanani; ba su kuwa da wani mai kare su daga (azabar) Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana rashin hankalin kafirai masu barin bautar Allah su kama bautar wasu gumaka marasa amfani, da cewa, yanzu Allah wanda yake tsaye da kula da arzikin duk halittunsa, yake kallon abin da kowane rai yake aikatawa, wanda zai yi masa sakayya a kansa, shi ne ya dace a bauta wa, ko kuwa waɗannan gumakan nasu waɗanda ba su san komai ba, ba kuma sa tsinana musu komai? To amma kafirai saboda rashin tunaninsu sai suka sanya wa Allah kishiyoyi suna bautar su ba Allah ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambaye su su yi masa bayanin su wane ne waɗannan ababen bautar nasu, idan har suna da gaskiya a kan da’awar da suke yi na allantakarsa; ko kuma suna faɗa wa Allah abin da bai san da shi ba ne a bayan ƙasa na wasu abokan tarayya da shi? Tabbas, Allah shi ne masanin komai na sarari da na ɓoye, da a ce yana da wani abokin tarayya to da ya san da shi ya kuma ba da labarinsa; ko kuma dai suna faɗa wa Allah wata ɓatacciyar magana ce wadda babu gaskiya a cikinta sai zato da shaci-faɗi? Sai a ƙarshe dai Allah ya tabbatar da cewa, kafirai ba su da wata hujja da suke riƙe da ita ta yin watsi da bautar Allah shi kaɗai su kama wasu abubuwan bauta marasa amfani; Shaiɗan ne dai kawai ya ƙawata musu makircinsu sai suka kafirce wa Allah, daga nan ya raba su da hanyar shiriya. Duk kuwa wanda Allah ya ɓatar da shi daga hanyar shiriya to babu wanda zai iya shiryar da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗannan kafirai wanda shi ne azabar duniya ta kisa a fagen yaƙi da faɗawa hannun muminai a matsayin fursunonin yaƙi. Sannan kuma azabar lahira wadda take jiran su ta fi ta duniya tsanani, saboda azaba ce mai bala’in raɗaɗi kuma ba mai yankewa ba. Ga shi kuma ba su da mai kare su daga wannan azabar.

  35. ۞مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ أُكُلُهَا دَآئِمٞ وَظِلُّهَاۚ تِلۡكَ عُقۡبَى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْۚ وَّعُقۡبَى ٱلۡكَٰفِرِينَ ٱلنَّارُ

    Open ayah 13:35

    Misalin Aljannar nan da aka yi wa masu taƙawa alƙawari da ita; ƙoramu ne suke gudana ta ƙarƙashinta; abincinta kuma mai dawwama ne da kuma inuwarta. Wannan shi ne makomar waɗanda suka kiyaye dokokin Allah; makomar kafirai kuma ita ce wuta.

  36. وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَۖ وَمِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ مَن يُنكِرُ بَعۡضَهُۥۚ قُلۡ إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ وَلَآ أُشۡرِكَ بِهِۦٓۚ إِلَيۡهِ أَدۡعُواْ وَإِلَيۡهِ مَـَٔابِ

    Open ayah 13:36

    Waɗanda kuwa Muka bai wa littafi (muminansu) suna farin ciki da abin da aka saukar maka; akwai kuma wasu daga ƙungiyoyi waɗanda suke musun wani sashi nasa. Ka ce: “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Allah, kada kuma in tara wani abu da Shi. Kuma zuwa gare Shi kawai nake kira, wurinsa ne kawai kuma makomata.”

  37. وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ حُكۡمًا عَرَبِيّٗاۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَمَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا وَاقٖ

    Open ayah 13:37

    Kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur’ani), ya zama hukunci, da harshen Larabci. Lalle kuma idan ka bi son ransu bayan abin da ya zo maka na ilimi, to ba ka da wani majiɓinci ko mai kariya daga (azabar) Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka kiyaye dokokinsa, suka aikata abin da ya wajabta musu suka bar wanda ya haramta musu, da cewa, suna da gidan Aljanna wadda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashin gidajenta da bishiyoyinta, ga kayan marmarin cikinta ba sa yankewa, hakanan inuwarta ba ta gushewa ba ta kuma raguwa. Amma waɗanda suka kafirce wa Allah kuwa sakamakonsu wutar Jahannama ce za su zauna cikinta ba fita har abada. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Sahabbai sun ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Ya Ma’aikin Allah, yaya muka ga ka miƙa hannu daga inda kake tsaye (watau cikin sallar kusufi) ka kamo wani abu, sai kuma muka ga ka dawo da baya?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Tabbas na ga Aljanna ne, sai na kamo wata hantsar kayan marmari daga cikinta, da na ɗauko muku shi da kun yi ta cin sa har ƙarshen rayuwar duniya.” [Bukhari #1052 da Muslim #907]. An karɓo daga Sahlu ɗan Sa’ad (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle a cikin Aljanna akwai wata bishiya da mahayin abin hawa zai yi tafiyar tsawon shekara ɗari a ƙarƙashin inuwarta bai kai ƙarshenta ba.” A ruwayar Abu Sa’id Al-Khudri ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle a cikin Aljanna akwai wata bishiya da mahayin ingarman doki mai gudu zai yi gudu tsawon shekara ɗari a cikin inuwarta bai kai ƙarshenta ba.” [Bukhari #6552, 6553 da Muslim #2827]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Yahudawa da Nasara waɗanda Allah ya ba su littattafai, suna farin ciki da Alƙur’ani yayin da suka ji ya yi daidai da abin da ya zo a littattafansu, to amma kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke ƙaryata wasu ayoyi na Alƙur’ani waɗanda suka saɓa wa son zuciyarsu, ko kuma ayoyin da suke ɗauke da bayanin canja littattafan Allah da suka yi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya sanar da su cewa, shi Allah ya umarce shi ne kawai da ya bauta masa shi kaɗai ba tare da ya haɗa komai da shi ba, kuma zuwa gare shi kaɗai yake kira kuma makomarsa gare shi kaɗai take, kuma da wannan koyarwar ce Attaura da Linjila suka sauka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda ya aiko da manzanni gabanin Manzon Allah (ﷺ) ya kuma saukar musu da littattafai daga sama, to hakanan ya saukar wa da Annabi (ﷺ) littafin Alƙur’ani wanda yake bayani ne dalla-dalla babu wata sarƙaƙiya a cikinsa kuma a cikin harshen Larabci mai cike da fasaha da azanci, Allah kuma ya ɗaukaka darajar Annabinsa da wannan Alƙur’ani a kan sauran annabawa, don haka sai ya gargaɗe shi da cewa, idan har ya kuskura ya amince da son zuciya irin ta Yahudu da Nasara masu neman sa da ya shafe abin da ya saɓa wa soye-soyen zukatansu daga Alƙur’ani bayan abin da ya zo masa na ilimin da Allah ya sanar da shi, to ya sani cewa, ba shi da wani majiɓincin al’amarinsa in ba Allah ba wanda zai taimaka masa a kan abokan gabarsa, haka kuma ba shi da wanda zai kare shi daga azabar Allah.

  38. وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَذُرِّيَّةٗۚ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ لِكُلِّ أَجَلٖ كِتَابٞ

    Open ayah 13:38

    Haƙiƙa kuma Mun aiko manzanni a gabaninka, Muka kuma ba su matan aure da zurriya. Bai kuma kamata ba ga wani annabi ya zo da wata aya (da za a neme shi da ya kawo ta) sai da izinin Allah. Kuma kowane lokaci yana nan a rubuce.

  39. يَمۡحُواْ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ وَيُثۡبِتُۖ وَعِندَهُۥٓ أُمُّ ٱلۡكِتَٰبِ

    Open ayah 13:39

    Allah Yana shafe abin da ya ga dama, Yana kuma tabbatar (da abin da ya ga dama); kuma a wurinsa asalin littafi yake.

  40. وَإِن مَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ وَعَلَيۡنَا ٱلۡحِسَابُ 

    Open ayah 13:40

    Ko dai Mu nuna maka irin sashin abin da Muke yi musu gargaɗi da aukuwarsa, ko kuma Mu karɓi ranka (kafin lokacin), abin da yake kanka kawai shi ne isar da aike, Mu kuma hisabi yana a kanmu.

  41. أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا نَأۡتِي ٱلۡأَرۡضَ نَنقُصُهَا مِنۡ أَطۡرَافِهَاۚ وَٱللَّهُ يَحۡكُمُ لَا مُعَقِّبَ لِحُكۡمِهِۦۚ وَهُوَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 13:41

    Yanzu ba sa ganin cewa Muna zaike wa ƙasa Muna ta cinye iyakokinta? Allah ne Mai yin hukunci, babu kuma mai yin gyara ga hukuncinsa. Shi ne kuma Mai saurin yin hisabi.

  42. وَقَدۡ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَلِلَّهِ ٱلۡمَكۡرُ جَمِيعٗاۖ يَعۡلَمُ مَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٖۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلۡكُفَّٰرُ لِمَنۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ

    Open ayah 13:42

    Haƙiƙa kuma waɗanda suke gabaninsu sun ƙulla makirci, (sakamakon) ƙulle-ƙulle dukkaninsa ga Allah yake; Yana sane da abin da kowane rai yake aikatawa. Ba da daɗewa ba kuma kafirai za su san wane ne mai kyakkyawan gidan (ƙarshe).

  43. وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَسۡتَ مُرۡسَلٗاۚ قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡ وَمَنۡ عِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡكِتَٰبِ

    Open ayah 13:43

    Kafirai kuma suna cewa: “Kai ba manzo ba ne.” Ka ce (da su): “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku, da kuma wanda yake da ilimin Littafi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi (ﷺ) ba shi ne farau a cikin manzanni ba wanda ya kasance mutum mai aure ya hayayyafa; an aiko manzanni da yawa gabaninsa kuma sun auri mata har sun samu ‘ya’ya da jikoki, wannan bai zama abin suka ga manzancinsu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da martani ga kafirai masu neman sai Annabi (ﷺ) ya zo musu da wata mu’ujiza sannan ne za su yi imani da shi, Allah ya tabbatar musu da cewa, wannan abin da suke nema daga Annabi (ﷺ) ba a hannunsa yake ba, domin kuwa babu wani manzo da zai zo da wata mu’ujiza sai da izinin Allah. Sai kuma ya bayyana musu cewa, komai da suke gani ya wakana, to da ma Allah ya riga ya ƙaddara samuwarsa a wannan lokacin, ba zai rage lokacinsa ba ba kuma zai ƙara ba, don haka su daina ganin abin da Annabi (ﷺ) yake tsoratar da su na azaba bai zo ba, har su yi tsammanin ko ba gaskiya yake faɗa musu ba; lokacinsa ne bai zo ba, idan ya zo to babu mai kawar da shi. Sannan kuma wani abu da ba su sani ba shi ne, Allah (Mai tsarki da daukaka) yana shafe abin da ya ga dama na alheri ko na sharri, na rabauta ko na taɓewa, ko shari’a da hukunce-hukunce, yana kuma tabbatar da wanda ya ga dama, domin Lauhul Mahafuzu kacokam yana wurinsa, komai kuma yana nan tattare a cikinsa, duk abin da ya bayyana na shafe wani abu ko tabbatar da shi yana yin daidai ne da abin da yake cikin Lauhul Mahafuzu ba ya saɓawa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Annabi (ﷺ) cewa, aikinsa kawai shi ne isar da saƙo, amma me zai faru ga waɗanda suka bijire wa kiransa kuma mene ne sakamakonsu wannan ba aikinsa ba ne, idan Allah ya ga dama yana iya nuna masa wani nau’i na azabar da ya yi musu tanadi tun a nan duniya, idan kuma ya ga dama yana iya karɓar ransa ba tare da ya ga irin azabar da za ta same su ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya faɗakar da kafirai da cewa, shin ba su ga yadda Allah yake ba wa Musulmi nasara a kansu ba, suna ta cinye garuruwansu da yaƙi, Musulunci kuma yana ta ƙara ƙarfi da yawa a garuruwansu? Allah ne mai yin hukunci tsakanin bayinsa da abin da ya ga dama, babu kuma mai warware hukuncin ko ya canja masa shi, kuma shi mai saurin yin hisabi ne ga mutanen farko da na ƙarshe a yini ɗaya kacal. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rarrashi Annabi (ﷺ) da cewa, kada ya damu da irin makirci da ƙulle-ƙullen da kafirai suke yi masa, ba za su taɓa yin nasara ba, domin kafiran da suka gabace su su ma sun ƙulla makirci ga annabawansu sun ƙaryata su, amma wannan bai yi wani tasiri ba ko kaɗan, domin makirci mai tasiri na ga Allah shi kaɗai, hakanan shi kaɗai ne ya san abin da suke aikatawa kuma zai yi musu sakayya a kai, a lokacin za su gane irin babban kuren da suka tabka na rashin ba da gaskiya da suka yi, za su gane lalle muminai su ne masu gaskiya, su ne kuma masu rabauta da gidan Aljanna. Sai kuma a ayar ƙarshe ta wannan surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci maganar da kafirai suke faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, shi ba Manzon Allah ba ne, watau suna ƙaryata da’awarsa ta manzanci. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa, Allah ya isa shaida tsakaninsa da su a kan cewa, shi Manzonsa ne, domin kuwa ya yi masa wahayi da yake tabbatar da haka, ya kuma ba shi goyon baya da nasara a kan abokan gabarsa, sannan ya tabbatar da da’awarsa bai ƙaryata shi ba. Hakanan kuma ga shaidar waɗanda suke da ilimin littattafan da Allah ya saukar, watau cikin malaman ma’abota littafi waɗanda suka musulunta, sun shaida da manzancinsa har ma sun yi imani da shi. Waɗanda kuwa suka ƙaryata shi daga cikin malaman Yahudu da Nasara sun yi haka ne saboda girman kai amma a zuciyarsu sun san shi Manzon Allah ne.