ابراهيم

Ibrahim

Abraham · Surah 14 · Ayahs: 52 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓرۚ كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ لِتُخۡرِجَ ٱلنَّاسَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ

    Open ayah 14:1

    ALIF LAM RA. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya.

  2. ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡكَٰفِرِينَ مِنۡ عَذَابٖ شَدِيدٍ

    Open ayah 14:2

    (Watau) Allah, Wanda abin da yake cikin sammai da na cikin ƙasa duka nasa ne. Bone na wata azaba mai tsanani kuma ya tabbatta ga kafirai.

  3. ٱلَّذِينَ يَسۡتَحِبُّونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٖ

    Open ayah 14:3

    Waɗanda suke fifita son rayuwar duniya a kan lahira, suke kuma hanawa (a bi) hanyar Allah, kuma suke neman ta zama karkatacciya. To waɗannan suna cikin ɓata mai nisa.

  4. وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا بِلِسَانِ قَوۡمِهِۦ لِيُبَيِّنَ لَهُمۡۖ فَيُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 14:4

    Ba Mu taɓa aiko wani manzo ba kuwa sai da harshen mutanensa don ya yi musu bayani; sannan Allah Yana ɓatar da wanda ya ga dama, ya kuma shiryar da wanda ya ga dama. Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da haruffa irin yadda ya buɗe wasu surorin da suka gabata. Mun yi bayani a kansu. [Duba farkon Suratul Baƙara ]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya saukar da wannan Littafi Alƙur’ani ga Manzonsa (ﷺ) domin ya fitar da mutane daga duhun kafirci da na jahilci da ɓata zuwa ga hasken imani da ilimi da shiriya. Watau zuwa ga addinin Musulunci wanda shi ne hanyar Allah mabuwayi wanda babu mai rinjayarsa, sha-yabo a kan duk ayyukansa da maganganunsa da shari’arsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da kafirai waɗanda suka ƙi miƙa wuya ga umarninsa, ya tabbatar musu da cewa, shi ne kaɗai Allah mamallakin abin da yake bayan ƙasa, don haka shi kaɗai ya cancanta a bauta wa, kada a haɗa shi da komai. Saboda haka tsananin azaba ya tabbata ga kafirai waɗanda ba sa ganin girman Allah ba sa bin umarninsa, suna kuma fifita rayuwar duniya mai gushewa a kan ta lahira mai ɗorewa. Ba su tsaya nan ba; sun kuma riƙa kautar da mutane daga hanyar Allah, kuma suna ƙoƙarin su gan ta a karkace don su jefa tsanarta a zukatan mutane har ya zamanto babu mai son bin ta ko riƙo da ita. Allah ya bayyana cewa, duk waɗanda suka siffantu da waɗannan siffofi to suna cikin wani ɓata mai nisa da gaskiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin rahama da baiwa da ya yi wa bayinsa wajen aiko musu da manzanni, su kuma ya aiko su da harshen mutanensu don su samu sauƙin yi musu bayanin abin da Allah ya aiko su da shi. Su ma kuma mutanen su ji sauƙin fahimtar su, don kuma hujjar Allah ta tsaya a kansu, don haka Allah ya ɓatar da wanda ya ga dama da adalcinsa, ya kuma shiryar da wanda ya ga damar shiryar da shi da falalarsa. Shi ne kuma mabuwayi wanda babu mai iya rinjayar sa a kan halittarsa ko tsarinsa.

  5. وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ أَنۡ أَخۡرِجۡ قَوۡمَكَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ وَذَكِّرۡهُم بِأَيَّىٰمِ ٱللَّهِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ

    Open ayah 14:5

    Haƙiƙa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu cewa: “Ka fitar da mutananka daga duffai zuwa ga haske, kuma ka tunatar da su ni’imomin Allah (da ya yi musu).” Lalle game da wannan da akwai ayoyi ga duk wani mai yawan haƙuri, mai yawan godiya.

  6. وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ أَنجَىٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ وَيُذَبِّحُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ

    Open ayah 14:6

    Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa: “Ku tuna ni’imar Allah a gare ku lokacin da Ya tserar da ku daga mutanen Fir’auna, suna gana muku azaba, suna kuma yanyanka ‘ya’yanku, kuma suna raya matayenku. A game da wannan da akwai bala’i mai girma daga Ubangijinku.

  7. وَإِذۡ تَأَذَّنَ رَبُّكُمۡ لَئِن شَكَرۡتُمۡ لَأَزِيدَنَّكُمۡۖ وَلَئِن كَفَرۡتُمۡ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٞ

    Open ayah 14:7

    “Kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar da ku: “Lalle idan kuka gode wa (ni’imata) tabbas zan ƙara muku; idan kuwa kuka butulce, to lalle azabata tabbas mai tsanani ce.”

  8. وَقَالَ مُوسَىٰٓ إِن تَكۡفُرُوٓاْ أَنتُمۡ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا فَإِنَّ ٱللَّهَ لَغَنِيٌّ حَمِيدٌ

    Open ayah 14:8

    Musa kuma ya ce: “Idan kuka kafirce, ku da waɗanda suke a bayan ƙasa baki ɗaya, to lalle Allah tabbas Mawadaci ne, Sha-yabo.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya aiko Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kuma ƙarfafe shi da wasu mu’ujizoji waɗanda suke tabbatar da gaskiyar manzancinsa, kuma ya umarce shi da ya fitar da mutanensa daga duhun kafirci da jahilci da ɓata zuwa ga hasken imani da ilimi da shiriya. Hakanan ya tunatar da Banu Isra’ila game da wasu kwanaki da suka shuɗe a rayuwarsu da Allah ya yi musu ni’imomi masu yawa a cikinsu. A cikin waɗannan tabbas kwanakin akwai ƙwararan dalilai masu nuna Ɗayantakar Allah da girman ikonsa da ni’imominsa ga muminai. Waɗannan duka ayoyi ne ga duk wani mai yawan haƙuri bisa ɗa’a ga Allah da juriya a kan abin da zai same shi na ɓacin rai da tashin hankali, mai yawan godiya game da ni’imomin Allah gare shi. An karɓo daga Suhaibu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Akwai abin mamaki ga al’amarin mumini, al’amarinsa duka alheri ne, babu kuma mai samun haka sai mumini. Idan wani abin farin ciki ya same shi sai ya gode, sai ya zama alheri gare shi; idan kuma wata cuta ta same shi sai ya yi haƙuri sai ya zama alheri gare shi.” [Muslim #2999]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa cewa, ya tuna lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bi umarnin Allah, ya tunatar da mutanensa ni’imomin da Allah ya yi musu a tarihin rayuwarsu, lokacin da ya kuɓutar da su daga sharrin Fir’auna da jama’arsa, lokacin da suke ɗanɗana musu azaba iri-iri suna nuna musu wulaƙanci daban-daban wanda ya kai har suna yanka ‘ya’yansu maza jarirai don gudun kada a haifo wanda zai ƙwace wa Fir’auna mulkinsa. Sai kuma su ƙyale ‘ya’yansu mata domin su riƙa yi musu bauta a gidajensu, suna saka su ayyukan ƙasƙanci da tozartawa. Allah ya bayyana cewa, a cikin wannan yanayi da Banu Isra’ila suka tsinci kansu a mulkin Fir’auna lalle akwai babbar jarrabawa gare su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kuɓutar da su sakamakon haƙurin da suka yi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana mana cewa, Annabi Musa ya shelanta wa mutanensa da babbar murya don kowa ya ji cewa,, idan suka yi wa Allah godiya a kan ni’imomin can da ya yi musu, to lalle tabbas zai ƙara musu ni’imominsa da falalarsa, amma idan suka butulce wa ni’imominsa suka ƙi godiya, to su sani cewa, lalle azabarsa mai tsanani ce. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya bayyana wa mutanensa cewa,, idan da a ce za su kafirce wa Allah tare da duk waɗanda suke bayan ƙasa, to kawunansu suka cuta ba Allah ba, domin shi mawadaci ne da Zatinsa ba ya da buƙatar komai a wurin kowa, kuma sha-yabo ne saboda kyawawan ayyukansa; don haka imanin masu imani ba zai ƙare shi da komai ba, hakanan kafircin kafirai ba zai cuce shi da komai ba. An karɓo daga Abu Zarrin Al-Ghifari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: Allah ya ce: “Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljannunku; zukatansu za su zamanto kamar zuciyar wanda ya fi kowa taƙawa daga cikinku (shi ne Annabi Muhammadu), wannan ba zai ƙara komai a cikin mulkina ba. Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljannunku; zukatansu za su zamanto kamar zuciyar wanda ya fi kowa fajirci daga cikinku (shi ne Iblis), to wannan ba zai tauye komai daga cikin mulkina ba…” [Muslim #2577].

  9. أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ نَبَؤُاْ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ قَوۡمِ نُوحٖ وَعَادٖ وَثَمُودَ وَٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ لَا يَعۡلَمُهُمۡ إِلَّا ٱللَّهُۚ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَرَدُّوٓاْ أَيۡدِيَهُمۡ فِيٓ أَفۡوَٰهِهِمۡ وَقَالُوٓاْ إِنَّا كَفَرۡنَا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ وَإِنَّا لَفِي شَكّٖ مِّمَّا تَدۡعُونَنَآ إِلَيۡهِ مُرِيبٖ

    Open ayah 14:9

    Wai yanzu labarin waɗanda suka gabace ku bai zo muku ba na mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa da waɗanda (suka zo) daga bayansu? Ba wanda ya san iyakarsu sai Allah. Manzanninsu sun zo musu da hujjoji bayyanannu, amma sai suka riƙa cizon hannayensu (saboda haushi), suka kuma ce: “Lalle mu kam mun kafirta da abin da aka aiko ku da shi, lalle kuma muna cikin matuƙar shakka game abin da kuke kiran mu zuwa gare shi.”

  10. ۞قَالَتۡ رُسُلُهُمۡ أَفِي ٱللَّهِ شَكّٞ فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يَدۡعُوكُمۡ لِيَغۡفِرَ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمۡ وَيُؤَخِّرَكُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ قَالُوٓاْ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا تُرِيدُونَ أَن تَصُدُّونَا عَمَّا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا فَأۡتُونَا بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ 

    Open ayah 14:10

    Mazanninsu suka ce: “Yanzu kuwa ashe akwai wata shakka game da Allah, Maƙagin sammai da ƙasa? Yana kiran ku ne don ya gafarta muku zunubanku kuma ya saurara muku har zuwa wani lokaci ƙayyadajje.” Suka ce: “Ku ba wasu ba ne daban in ban da mutane kamar mu, kuna so ne ku hana mu bin abin da iyanenmu suka kasance suna bauta wa, to sai ku kawo mana hujjoji bayyanannu.”

  11. قَالَتۡ لَهُمۡ رُسُلُهُمۡ إِن نَّحۡنُ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَمُنُّ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَمَا كَانَ لَنَآ أَن نَّأۡتِيَكُم بِسُلۡطَٰنٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 14:11

    Manzanninsu suka ce: “Mu ba kowa ba ne in ban da mutane kamarku, sai dai Allah Yana yin baiwa ga wanda Ya ga dama ne daga bayinsa, kuma ba zai yiwu ba a gare mu mu zo muku da wata hujja sai dai da izinin Allah. Muminai kuwa lalle su dogara ga Allah kawai.

  12. وَمَا لَنَآ أَلَّا نَتَوَكَّلَ عَلَى ٱللَّهِ وَقَدۡ هَدَىٰنَا سُبُلَنَاۚ وَلَنَصۡبِرَنَّ عَلَىٰ مَآ ءَاذَيۡتُمُونَاۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ

    Open ayah 14:12

    “Kuma me zai hana mu mu dogara ga Allah, alhali kuwa haƙiƙa Ya shiryar da mu hanyoyinmu? Lalle kuwa tabbas za mu yi haƙuri bisa irin cutar mu da kuka yi. Masu dogaro kuma sai su dogara ga Allah kaɗai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tambayar kafiran Ƙuraishawa da ire-irensu cewa,, ba su samu labarin al\'ummun da suka gabace su ba waɗanda suka ƙaryata manzanninsu, kamar mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da na Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Samudawa mutanen Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ma wasu al\'ummu masu yawan da babu wanda ya san adadinsu sai Allah. Dukkansu manzanninsu sun zo musu da hujjoji bayyanannu, to amma sai suka riƙa sanya hannayensu suna rufe bakunansu, watau suna cizon yatsunsu saboda haushin manzanninsu da ya cika musu zukata. Kai sun ma fito fili suna sanar da manzanninsu cewa, su fa sun kafirce wa duk abin da aka aiko su da shi, suna kuma shakkar abin da suke kiran su zuwa gare shi. Sai manzanninsu suka amsa musu da cewa,, yanzu akwai abin da za su yi shakkarsa dangane da sha’anin kaɗaita Allah da bauta, duk da hujjoji masu yawa da ke kewaye da su a kan cancantarsa ga hakan? Cikinsu akwai cewa shi ne wanda ya ƙirƙiri halittar sammai da ƙasa ba tare da wani ya riga shi ba, sannan kuma abin mamaki, har ila-yau, shi ne sun riƙa shakka game da abin da manzannin nan suka zo musu da shi duk da cewa, abu ne mai matuƙar amfani gare su, watau kiran su zuwa ga yin imani da Allah domin ya gafarta musu zunuban da suka yi, kuma ya jinkirta musu har zuwa ƙarshen lokacin da aka yanka musu na rayuwarsu ta duniya. To amma duk da wannan jawabin da manzannin suka yi musu, sai mushirikai suka sake fito da wata maganar marar tushe, suka soki manzannin da cewa, ai su mutane ne kamarsu ba su da wani abin da suka fi su da shi da har zai sa Allah ya zaɓe su ya aiko su, kawai dai suna so ne su raba su da bautar abin da iyayensu suka kasance suna bauta wa. Kuma suka nemi manzannin nan su kawo musu wata hujja da za su gamsu da ita ta cewar su manzannin Allah ne na gaskiya. Sai waɗannan manzanni suka yarda cewa, su mutane ne kamarsu a halitta, sai dai hakan ba yana nuna sun yi kama da su ne ta kowace nahiya ba, domin su kansu su san cewa, Allah yana keɓe wanda ya ga dama da wata ni’ima tasa ta musamman, don haka ne ya zaɓo su daga cikin mutane ya ba su manzanci. To amma batun hujja kuwa, su kafirai suna nufin irin mu’ujizoji da suke neman sai an nuna musu kafin su yarda da gaskiyar manzanninsu, sai manzannin suka faɗa musu cewa, aikata haka ba ya hannunsu; yana hannun Allah ne, kuma da izininsa za su iya nuna musu wannan hujjar da suke buƙata. Don haka muminai suna dogaro ga Allah ne shi kaɗai cikin duk wani lamarinsu. Suka sake jaddada musu cewa, ba su da wani uzuri da zai hana su dogaro da Allah, alhali shi ne ya ɗora su a kan miƙaƙƙiyar hanyar da suka bi. Sannan sun tabbata da cewa kafirai ba za su ƙyale su ba, za su ci gaba da cutar da su da yi musu izgili da ƙaryata su, to su a shirye suke su yi haƙuri a kan duk waɗannan abubuwa. Kuma gare shi za su ci gaba da dogaro, domin da man gare shi masu dogaro suke dogara cikin duk lamarinsu.

  13. وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِرُسُلِهِمۡ لَنُخۡرِجَنَّكُم مِّنۡ أَرۡضِنَآ أَوۡ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَاۖ فَأَوۡحَىٰٓ إِلَيۡهِمۡ رَبُّهُمۡ لَنُهۡلِكَنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 14:13

    Waɗanda suka kafirta kuma suka ce da manzanninsu: “Lalle ba makawa za mu fitar da ku daga ƙasarmu, ko kuwa lalle ku komo cikin addininmu. Sai Ubangijinsu ya aiko musu cewa: “Lalle za Mu hallaka azzalumai.

  14. وَلَنُسۡكِنَنَّكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَافَ مَقَامِي وَخَافَ وَعِيدِ

    Open ayah 14:14

    “Kuma tabbas za mu zaunar da ku ƙasar (tasu) a bayansu. Wannan kuwa sai ga wanda ya ji tsoron tsayuwa a gabana ya kuma ji tsoron narkona.”

  15. وَٱسۡتَفۡتَحُواْ وَخَابَ كُلُّ جَبَّارٍ عَنِيدٖ

    Open ayah 14:15

    Sai kuma (manzannin) suka nemi nasarar (Allah), kuma (a ƙarshenta) duk wani mai nuna isa mai taurin kai ya hallaka.

  16. مِّن وَرَآئِهِۦ جَهَنَّمُ وَيُسۡقَىٰ مِن مَّآءٖ صَدِيدٖ

    Open ayah 14:16

    A gabansa Jahannama ce (take jiran sa), za a kuma shayar da shi ruwan mugunya.

  17. يَتَجَرَّعُهُۥ وَلَا يَكَادُ يُسِيغُهُۥ وَيَأۡتِيهِ ٱلۡمَوۡتُ مِن كُلِّ مَكَانٖ وَمَا هُوَ بِمَيِّتٖۖ وَمِن وَرَآئِهِۦ عَذَابٌ غَلِيظٞ

    Open ayah 14:17

    Yana kwankwaɗar sa, ba kuwa zai ji daɗin haɗiyarsa ba, mutuwa kuma za ta zo masa ko ta ina, ba kuwa zai mutu ba; kuma a gabansa ga azaba mai kauri. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani irin mummunan mataki da kafirai suka shirya ɗauka a kan manzanninsu bayan sun kasa bayyana musu wani ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa suka kafirce wa Allah (Mai tsarki da daukaka) suka ƙaryata su. Sai kafiran suka yi barazanar korar manzannin daga ƙasarsu, in ba haka ba kuwa su manzannin su dawo cikin addinin waɗannan kafirai. To amma Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafi manzannin ta hanyar yi musu wahayi da cewa, lalle zai hallaka waɗannan kafirai saboda zaluncinsu na yi wa Allah shirka da ƙaryata manzanninsa da cutar da su, ya kuma yi wa manzannin alƙawarin mallaka musu wannan ƙasar don ci gaba da zama a cikinta su da mabiyansu bayan ya hallaka kafirai. To amma sai da ya bayyana sharuɗɗan zartar da wannan alƙawari da cewa, guda biyu ne: Na farko, halarto da girman Allah da tsoron tsayawa a gabansa. Na biyu; tsoron narkon azabarsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa,, manzanni sun nemi taimakon Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya ba su nasara a kan abokan gabarsu. Allah kuma ya nufi duk wani kafiri mai nuna isa da mai taurin kai ya yi hasara duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana mafi munin hasara da taɓewa da kafiri zai gamu da ita ranar alƙiyama, domin kuwa Jahannama ce take jiran sa, sannan a shayar da shi mugunyar ‘yan wuta, watau ruwan da yake fitowa daga gyambonsu. Shi za su yi ta kwankwaɗa ba tare da yana kashe musu ƙishi ba, kuma za su ci gaba da zama cikin azabar ƙishirwa da wasu dangogin azaba daban-daban. Mutuwa kuma ta yi ta zo masa ta ko’ina, saboda tsananin azabar da yake ɗanɗana, to amma ba zai samu ya mutu ba ballantana ya huta da azabar. Bayan wannan azabar kuma a gabansa akwai wata matsananciyar azabar tana jiran sa.

  18. مَّثَلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡۖ أَعۡمَٰلُهُمۡ كَرَمَادٍ ٱشۡتَدَّتۡ بِهِ ٱلرِّيحُ فِي يَوۡمٍ عَاصِفٖۖ لَّا يَقۡدِرُونَ مِمَّا كَسَبُواْ عَلَىٰ شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ

    Open ayah 14:18

    Misalin waɗanda suka kafirce wa Ubangijnsu; ayyukansu sun yi kama da toka wadda iska mai tsananin ƙarfi ta kwasa a wata rana mai guguwa; ba za su sami iko a kan komai ba dangane da abin da suka aikata (na kirki). Wannan shi ne ɓata mai nisa.

  19. أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۚ إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَأۡتِ بِخَلۡقٖ جَدِيدٖ

    Open ayah 14:19

    Ashe ba ka ga cewa, lalle Allah Ya halicci sammai da ƙasa kan gaskiya ba? Idan Ya ga dama sai Ya hallakar da ku Ya kuma zo da wata halitta sabuwa.

  20. وَمَا ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ بِعَزِيزٖ 

    Open ayah 14:20

    Wannan kuwa ba abin da zai gagari Allah ba ne. A waɗannan ayoyi, bayan Allah ya bayyana irin mummunar azabar da take jiran kafirai, sai kuma ya bayyana cewa, duk yawan kyawawan ayyuka da za su yi a nan duniya ba za su amfane su da komai a ranar alƙiyama ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwatanta ayyukansu da toka wadda wata guguwa za ta taso da ƙarfi ta kwashe ta ta ɗaiɗaita ta a cikin iska ta warwatse a ko’ina, babu mai iya harhaɗo ta wuri guda don ta yi wani amfani. To haka kyawawan ayyukan kafirai za su kasance a ranar alƙiyama, ba za su ga komai ba daga cikinsu ballantana su amfana da su. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Na ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Ya Manzon Allah, Ibnu Jud’an ya kasance a zamanin jahiliyya yana sada zumunci yana ciyar da mabuƙata, shin wannan zai amfane shi?” Sai Manzon Allah ya ce: “A’a, ba zai amfane shi ba, domin babu wata rana da ya taɓa cewa,: “Ya Allah ka gafarta mini kurakuraina a ranar sakamako.” [Muslim #214]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan ranar, watau alƙiyama, tana nan tafe babu makawa, domin kuwa duk wanda ya ƙagi halittar sammai da ƙasa ba tare da wani ya taimaka masa ba, to yana da cikakken ikon da zai hallaka su ya ƙagi wasu halittun daban, wannan ba wani aiki ne da zai gagare shi ba sam sam.

  21. وَبَرَزُواْ لِلَّهِ جَمِيعٗا فَقَالَ ٱلضُّعَفَٰٓؤُاْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُنَّا لَكُمۡ تَبَعٗا فَهَلۡ أَنتُم مُّغۡنُونَ عَنَّا مِنۡ عَذَابِ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۚ قَالُواْ لَوۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ لَهَدَيۡنَٰكُمۡۖ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَجَزِعۡنَآ أَمۡ صَبَرۡنَا مَا لَنَا مِن مَّحِيصٖ

    Open ayah 14:21

    Suka kuma fito gaba ɗaya a gaban Allah (ranar alƙiyama), sai raunanan suka ce da waɗanda suka yi girman kai: “Lalle mu mun zamanto mabiya a gare ku, to ko za ku maganta mana wani abu daga azabar Allah?” Suka ce: “Da Allah Ya shirye mu da lalle mun shiryar da ku; duka ɗaya ne gare mu ko mun yi raki ko mun yi haƙuri (duka dai) ba mu da wata maguda.”

  22. وَقَالَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَمَّا قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ إِنَّ ٱللَّهَ وَعَدَكُمۡ وَعۡدَ ٱلۡحَقِّ وَوَعَدتُّكُمۡ فَأَخۡلَفۡتُكُمۡۖ وَمَا كَانَ لِيَ عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّآ أَن دَعَوۡتُكُمۡ فَٱسۡتَجَبۡتُمۡ لِيۖ فَلَا تَلُومُونِي وَلُومُوٓاْ أَنفُسَكُمۖ مَّآ أَنَا۠ بِمُصۡرِخِكُمۡ وَمَآ أَنتُم بِمُصۡرِخِيَّ إِنِّي كَفَرۡتُ بِمَآ أَشۡرَكۡتُمُونِ مِن قَبۡلُۗ إِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 14:22

    Shaiɗan kuma lokacin da aka gama hukunci ya ce: “Lalle Allah Ya yi muku alƙawari na gaskiya, ni kuma na yi muku alƙawari sai na saɓa muku. To ba ni da wani ƙarfi da na nuna muku, sai dai na yi kiran ku ne sai kuka amsa mini; to kada ku zarge ni, ku zargi kanku; ni ba zan taimake ku ba, ku kuma ba za ku taimake ni ba. Lalle ni na riga na kafirta da abin da kuka yi tarayya da ni a kansa tun a da can. Lalle azzalumai suna da (sakamakon) azaba mai raɗaɗi.”

  23. وَأُدۡخِلَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡۖ تَحِيَّتُهُمۡ فِيهَا سَلَٰمٌ

    Open ayah 14:23

    Aka kuma shigar da waɗanda suka yi imani, suka kuma yi aiki nagari gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu da izinin Ubangijinsu; gaisuwarsu a cikinsu ita ce: “Aminci (ya tabbata a gare ku).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar da mutane lokacin da za su fito gaba ɗaya daga ƙaburburansu, don ya yi musu hisabi, a kai kowa gidansa, a nan ne mabiya da shugabanninsu za su shiga musayar magana da junansu a wutar Jahannama. Mabiya su zargi shugabanninsu da cewa, su a duniya suna yi musu biyayya, suna aiki da umarninsu suna hanuwa da haninsu, to yau ga shi duk an haɗa su a wuta, shin yanzu za su iya ɗauke musu wannan azabar da suke ciki? Sai shugabannin su amsa musu da cewa, ai da Allah ya shiryar da su to da sun shiryu sun bi gaskiya gaba ɗaya sun kuɓuta daga azaba, to amma sai suka ɓace, don haka suka ɓatar da mabiyansu. Suka ƙara musu da cewa, a yanzu kam bayan an gama hisabi har an saka su wutar Jahannama to duk wani raki da za su yi ko su yi haƙuri su jure wa azabar wuta, hakan ba shi da wani amfani a gare su, domin kuwa babu sauran wata maguda ko maɓoya da ta rage musu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, a nan ne Iblis zai miƙe shi kuma ya yi tasa huɗubar ga duk ‘yan wuta, ya fito fili ya tabbatar musu cewa ba a kan gaskiya ya ɗora su ba, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu alƙawarin gaskiya yayin da ya aiko musu da manzanni ya yi umarni da su bi su domin su sami tsira, amma sai suka ƙi imani da su, shi kuma sai ya yi musu alƙawarin ƙarya, ya nuna musu su bi shi za su rabauta. To a yau ga yadda al’amarin ya kwaɓe musu, domin ba su samu abin da ya yi musu alƙawari da shi ba. Ya bayyana musu cewa, shi fa a lokacin da yake kiran su zuwa ga ɓata ba wani ƙarfi yake nuna musu ba don su yi masa biyayya a kan kafirci da ɓata, kawai ya kira su ne zuwa kafirci, ya ƙawata musu saɓon Allah sai suka bi shi a kan haka; don haka a yau su daina zargin sa da ya ɓatar da su, su zargi kawunansu. Sannan ya tabbatar musu da cewa, shi ba zai iya taimakon su ya kare su daga azaba ba, su ma kuma ba za su iya taimaka masa da komai ba. Ya ƙara da cewa, shi lalle ya kafirce wa bautar da suka yi masa, yayin da suka sanya shi abokin tarayya da Allah a duniya, domin kuwa ya san azzalumai da suka haɗa Allah da wani wajen bauta suna da azaba mai raɗaɗi sakamakon aikinsu. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana makomar kafirai a ranar alƙiyama, sai kuma ya bayyana makomar muminai waɗanda suka yi imani kuma suka yi kyawawan ayyuka da cewa, za a shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su zauna a cikinsu zama na har abada da izinin Ubangijinsu. Za su riƙa gai da junansu, mala’iku ma za su riƙa yi musu gaisuwa da sallama, watau amincin Allah ya tabbata a gare su.

  24. أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا كَلِمَةٗ طَيِّبَةٗ كَشَجَرَةٖ طَيِّبَةٍ أَصۡلُهَا ثَابِتٞ وَفَرۡعُهَا فِي ٱلسَّمَآءِ

    Open ayah 14:24

    Shin ba ka ga yadda Allah Ya ba da misali ba? Daddaɗar kalma kamar daddaɗar bishiya ce wadda tushenta kafaffe ne (a ƙasa) reshenta kuma yana sama.

  25. تُؤۡتِيٓ أُكُلَهَا كُلَّ حِينِۭ بِإِذۡنِ رَبِّهَاۗ وَيَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَالَ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ

    Open ayah 14:25

    Tana bayar da ‘ya’yanta ko da yaushe da izinin Ubangijinta. Allah kuwa Yana ba da misalai ne ga mutane don su wa’azantu.

  26. وَمَثَلُ كَلِمَةٍ خَبِيثَةٖ كَشَجَرَةٍ خَبِيثَةٍ ٱجۡتُثَّتۡ مِن فَوۡقِ ٱلۡأَرۡضِ مَا لَهَا مِن قَرَارٖ

    Open ayah 14:26

    Misalin kuma mummunar kalma kamar mummunar bishiya ce da aka tumɓuke daga kan ƙasa, ba ta da wata matabbata.

  27. يُثَبِّتُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلۡقَوۡلِ ٱلثَّابِتِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَيُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلظَّٰلِمِينَۚ وَيَفۡعَلُ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ

    Open ayah 14:27

    Allah Yana tabbatar da waɗanda suka yi imani a kan magana tabbatacciya a rayuwar duniya da kuma a lahira; Yana kuma ɓatar da azzalumai. Allah kuma Yana aikata abin da Ya ga dama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwatanta Kalmar Shahada da wata bishiya wadda saiwoyinta suka kama ƙasa sosai, ressanta kuma suna sama, tana fitar da ‘ya’ya masu daɗi a ko da yaushe. Wannan ita ce shiriya lokacin da za ta shiga zuciyar mumini sannan ta yi naso ta kwarara a kan sauran gaɓoɓinsa, ta kuma cika wasu zukata masu yawa, ta haskaka su da haskenta, ta zama kamar bishiyar da take fitar da ‘ya’yanta masu daɗi kuma marasa yankewa ga kowa da kowa. Da yawa daga cikin magabata na ƙwarai sun ce wannan kalma ita ce Kalmar Shahada, watau shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Bishiyar kuwa ita ce mumini. Kalmar Shahada tana kafa tushenta a cikin zuciyar mumini, da ita kuma ake ɗaukaka kyakkyawan aikinsa zuwa sama. An ruwaito cewa, wannan bishiyar mai kyau ita ce bishiyar dabino. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana muna zaune gaban Manzon Allah (ﷺ) sai ya ce: “Ku faɗa mini wacce bishiya ce mai kama da Musulmi wadda ganyenta ba ya kakkaɓewa a lokacin sanyi ko zafi, kuma take bayar da ‘ya’yanta ko da yaushe da izinin Ubangijinta?” Ɗan Umar ya ce: “Sai na ji a raina cewa, ita ce bishiyar dabino, to amma sai na ga Abubakar da Umar ba su ce komai ba, sai na ƙi yin magana tun da su ma ba su ce wa Manzon Allah komai ba.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ita ce bishiyar dabino.” [Bukhari #4689 da Muslim #2811]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwatanta kalmar kafirci da wata mummunar bishiya mai ‘ya’ya marasa daɗin ci, kuma marar amfani. An siffanta ta gunar shanu wadda aka tumɓuke ta daga kan ƙasa, watau ba ta da wasu saiwoyi a ƙasa da ke riƙe da ita, kuma ga shi ba ta da wasu ‘ya’ya masu daɗi ko amfani sai ‘ya’ya munana masu tsananin ɗaci. To kamar haka ita ma kalmar kafirci take a zuciya, ba ta da wani tushe tabbatacce, ba ta haifar da wani aiki ko magana mai kyau sai dai abin da zai cutar da mai ita, abin da ba shi da wani amfani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, zai tabbatar da muminai a kan kalmar Tauhidi a nan rayuwarsu ta duniya har su mutu a kanta. Hakanan da lokacin kwanciyarsu a cikin ƙabari da lokacin yi musu tambayar ƙabari, ya kuma tashe su da ita a ranar alƙiyama domin yi musu sakamako a kanta. To amma waɗanda suka zaɓi ɓata a kan shiriya, suka yarda da kafirci da shirka, suka zalunci kawunansu, to su Allah yana ɓatar da su, ya hana musu dace a rayuwar duniya da ta bayan mutuwa, domin Allah yana yin abin da ya ga dama, ya shiryar da wanda ya ga dama da falalarsa, ya kuma ɓatar da wanda ya ga dama da adalcinsa.

  28. ۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ بَدَّلُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ كُفۡرٗا وَأَحَلُّواْ قَوۡمَهُمۡ دَارَ ٱلۡبَوَارِ

    Open ayah 14:28

    Shin ba ka ga waɗanda suka musanya ni’imar Allah da kafirci ba, suka kuma jefa mutanensu gidan hallaka?

  29. جَهَنَّمَ يَصۡلَوۡنَهَاۖ وَبِئۡسَ ٱلۡقَرَارُ

    Open ayah 14:29

    (Watau) Jahannama, za su shige ta; makoma kuwa ta munana.

  30. وَجَعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلُّواْ عَن سَبِيلِهِۦۗ قُلۡ تَمَتَّعُواْ فَإِنَّ مَصِيرَكُمۡ إِلَى ٱلنَّارِ 

    Open ayah 14:30

    Sun sanya wa Allah abokan tarayya don su ɓatar (da mutane) daga hanyarsa. Ka ce: “Ku ji daɗi (kaɗan a duniya), to lalle makomarku wuta ce!”

  31. قُل لِّعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا بَيۡعٞ فِيهِ وَلَا خِلَٰلٌ

    Open ayah 14:31

    Ka ce da bayina waɗanda suka yi imani, su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi, a ɓoye da sarari tun kafin zuwan ranar da babu ciniki a cikinta, kuma babu abota. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar wa Annabi (ﷺ) abin da ya sani game da kafiran Ƙuraishawa na butulce wa ni’imar da Allah ya yi musu ya, ba su zaman lafiya a garuruwansu yayin da wasu garuruwan suke cikin tashin hankali da hargitsi, sannan ya yi musu wata babbar ni’ima wadda ta zarce kowace irin ni’ima da ya taɓa yi musu, watau shi ne ya aiko musu da Annabi daga cikin jinsinsu, to amma maimakon su gode wa Allah sai suka butulce masa ta hanyar kafirci da ƙaryata Manzonsa, da haka suka jefa mabiyansu cikin gidan halaka, watau gidan wutar Jahannama wadda za su shige ta su kuma ɗanɗani azabarta. Tir da wannan makoma. Sannan Allah ya bayyana irin mummunan ɓatan da suka faɗa ciki, kuma suka yi sanadiyyar ɓatan sauran mabiyansu, ya bayyana cewa, sun riƙi gumaka abokan tarayya da Allah suna bauta musu ba Allah ba, sannan suna ɓatar da wasu ta hanyarsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, su ji daɗi ɗan kaɗan na duniya da bin soye-soyen zukatansu da yaɗa ɓarna a bayan ƙasa, to amma su sani cewa, ƙarshen makomarsu ranar alƙiyama ita ce wutar Jahannama ba su da wata makoma ba wannan ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya umarci muminai su tsayar da sallolinsu cikakku kamar yadda aka umarce su, su kuma taimaka da dukiyoyinsu ga mabuƙata; taimako na wajibi, kamar zakka da makamanciyarta, ko na mustahabbi. Suna iya yin haka a ɓoye don gudun riya, suna kuma iya yin haka a bayyane don a yi koyi da su kafin ranar alƙiyama ta zo, ranar da dukiya ko abota ba za su amfani kowa ba, ba za a karɓi fansa daga wani ba domin kuɓutar da shi daga azaba, aboki ba zai iya ceton abokinsa ba sai da izinin Allah ga wanda ya yarda da shi.

  32. ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡفُلۡكَ لِتَجۡرِيَ فِي ٱلۡبَحۡرِ بِأَمۡرِهِۦۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡأَنۡهَٰرَ

    Open ayah 14:32

    Allah ne Wanda Ya halicci sammai da ƙasa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya fitar da ‘ya’yan itace don arzuta ku; Ya kuma hore muku jiragen ruwa don ku yi tafiya a cikin kogi da umarninsa, Ya kuma hore muku ƙoramu.

  33. وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ دَآئِبَيۡنِۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ

    Open ayah 14:33

    Ya kuma hore muku rana da wata tutur; Ya kuma hore muku dare da rana.

  34. وَءَاتَىٰكُم مِّن كُلِّ مَا سَأَلۡتُمُوهُۚ وَإِن تَعُدُّواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ لَا تُحۡصُوهَآۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَظَلُومٞ كَفَّارٞ

    Open ayah 14:34

    Ya kuma ba ku daga duk abin da kuka roƙe Shi. In da za ku ƙirga ni’imomin Allah to ba za ku iya ƙididdige su ba. Lalle mutum mai yawan zalunci ne mai yawan butulci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kaɗan daga cikin ɗimbin ni’imomi da ya yi wa ɗan’adam amma yake nuna butulcinsa, har ma yake ƙaryata annabawansa. Daga cikin waɗannan ni’imomi akwai halittar sammai da ƙasa wadda Allah ya yi ba tare da kwaikwayon kowa ba, ba kuma tare da wani ya taimaka masa ba, sannan ya saukar da ruwan sama wanda ya fitar da tsirrai da abinci da kayan marmari iri-iri da shi domin amfanin ‘yan’adam, sannan kuma ya hore musu jiragen ruwa domin sufuri da ɗaukan kaya masu nauyi suna gudu a kan teku cikin ikon Allah. Bayan haka kuma ya samar musu da ƙoramu na ruwan sha, su sha su kuma shayar da dabbobinsu da shuke-shukensu. Daga cikin waɗannan ni’imominsa kuma akwai halittar rana da wata waɗanda ya hore wa ɗan’adam amfani da haskensu da zafin rana, ga su suna gudana a sama ko da yaushe ba yankewa. Sannan kuma ya hore musu dare da yini waɗanda suke bibiyar juna, ya sanya dare ya zama lokacin hutawa da barci, ya sanya yini ya zama lokacin kujuba-kujuba da neman abinci. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya dunƙule waɗannan ni’imomi da cewa, ya ba wa ‘yan’adam duk wani abu da suka roƙe shi na buƙatarsu da ma wanda ba su roƙe shi ba, domin idan da mutane za su lissafa ni’momin Allah a gare su, to ba za su iya ƙididdige su ba saboda yawansu. Waɗannan da aka ambata ma misalai ne aka bayar, to amma sau da yawa mutum yakan mance da waɗannan ni’imomin ya ƙi godiya ga Allah, ya ma butulce masa ya yi ta yin kafirci da saɓo iri-iri. Da ma wannan shi ne halin ɗan’adam idan bai samu tarbiyya ta annabawa ba.

  35. وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا ٱلۡبَلَدَ ءَامِنٗا وَٱجۡنُبۡنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعۡبُدَ ٱلۡأَصۡنَامَ

    Open ayah 14:35

    (Ka tuna) kuma lokacin da Ibrahimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya wannan gari (Makka) ya zama amintacce, kuma Ka nesantar da ni da ‘ya’yana daga bauta wa gumaka.

  36. رَبِّ إِنَّهُنَّ أَضۡلَلۡنَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِۖ فَمَن تَبِعَنِي فَإِنَّهُۥ مِنِّيۖ وَمَنۡ عَصَانِي فَإِنَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 14:36

    “Ya Ubangijina, lalle su (gumakan) sun ɓatar da mutane masu yawa; wanda kuwa ya bi ni to lalle shi yana tare da ni; wanda kuma ya saɓa mini to lalle Kai Mai gafara ne, Mai jin ƙai.”

  37. رَّبَّنَآ إِنِّيٓ أَسۡكَنتُ مِن ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيۡرِ ذِي زَرۡعٍ عِندَ بَيۡتِكَ ٱلۡمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱجۡعَلۡ أَفۡـِٔدَةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ تَهۡوِيٓ إِلَيۡهِمۡ وَٱرۡزُقۡهُم مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡكُرُونَ

    Open ayah 14:37

    “Ya Ubangijinmu, lalle ni na zaunar da wasu daga zuriyata a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa kusa da Ɗakinka mai alfarma; ya Ubangijinmu don su tsai da salla, to Ka sanya zukatan mutane su riƙa karkatowa zuwa gare su, kuma Ka arzuta su da ‘ya’yan itace don su gode (maka).

  38. رَبَّنَآ إِنَّكَ تَعۡلَمُ مَا نُخۡفِي وَمَا نُعۡلِنُۗ وَمَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ

    Open ayah 14:38

    “Ya Ubangijinmu, lalle Kai Ka san abin da muke ɓoyewa da abin da muke bayyanawa. Babu wani abu a cikin ƙasa ko a cikin sama da zai ɓuya ga Allah.

  39. ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي وَهَبَ لِي عَلَى ٱلۡكِبَرِ إِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

    Open ayah 14:39

    “Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya ba ni Isma’ila da Is’haƙa a cikin halin tsufa. Lalle Ubangijina tabbas Mai jin roƙo ne.

  40. رَبِّ ٱجۡعَلۡنِي مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِيۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلۡ دُعَآءِ 

    Open ayah 14:40

    “Ya Ubangijina, Ka sanya ni in zama mai tsayar da salla da kuma zuriyata. Ya Ubangijinmu, Ka karɓi addu’ata.

  41. رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيَّ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ يَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡحِسَابُ

    Open ayah 14:41

    “Ya Ubangijinmu Ka gafarta mini, ni da iyayena da kuma muminai ranar da hisabi zai kankama.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ɓangare na labarin Baban annabawa, Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da yadda ya yi kira zuwa ga bautar Allah shi kaɗai da ƙaurace wa bautar gumaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tuna lokacin da Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ɗauko kuyangarsa Hajara tare da ɗanta Annabi Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kawo su kwarin Makka ya ajiye su ya tafi ya bar su da umarnin Allah (Mai tsarki da daukaka). Ya ɗaga hannu ya yi musu addu’a da cewa, Allah ya mayar da wannan wuri ya zama gari mai aminci da zaman lafiya, ba za a zubar da jinin wani ko zaluntar wani a cikinsa ba. Ya kuma roƙe shi ya nesanta shi tare da ‘ya’yansa daga bautar gumaka. Sannan ya ambaci abin da ya sa shi tsoron shi ko ‘ya’yansa wani ya faɗa cikin shirka, da cewa, su waɗannan gumaka sun ɓatar da mutane da dama domin sun ɗauki cewa, za su cece su a lahira, don haka suke bauta musu ba Allah ba. Ya tabbatar da cewa, duk wanda ya bi shi daga cikin mutane ya kaɗaita Allah da bauta, to ya tabbata cikin mabiyansa kuma cikin jama’arsa. Duk kuwa wanda ya saɓa masa ya rungumi bautar wanin Allah, ya ƙi yi wa Allah biyayya, to Allah shi mai gafara ne ga wanda ya ga dama ya gafarta masa, mai jin ƙai ne ga wanda ya nufe shi da jin ƙansa. Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da faɗa wa Allah cewa, ya zaunar da wasu daga zurriyarsa, su ne ɗansa Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mahaifiyarsa Hajara, sai kuma jikokinsa ‘ya’yan Isma’ilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya zaunar da su a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa, babu ko ruwan sha kusa da Ɗakin Ka’aba, watau garin Makka. Ya bayyana cewa, ya saukar da su ne a wannan wuri don su tsayar da salla, domin ita ce ginshiƙin addini bayan Kalmar Shahada, don haka duk wanda ya tsayar da ita ya kula da ita, to zai kula da sauran ibadunsa. Ya kuma roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karkato da zukatan mutane zuwa gare su, su riƙa marmarin ziyarar wannan gari koyaushe. Ya kuma arzuta su da kayan marmari iri-iri da za a riƙa shigo musu da su daga ko’ina a duniya, domin su gode wa Allah game da ni’imominsa da ya yi musu. Sannan ya ƙara tabbatar da cikakken sanin Allah ga komai, ya san abin da mutane suke ɓoyewa da abin da suke bayyanawa; babu abin da yake ɓuya gare shi a sama yake ko a ƙasa. Haka kuma ya san duk irin buƙatar da Annabi Ibrahimu da zurriyyarsa suke da ita kuma zai taimaka musu ya biya musu ita. Sai kuma ya yi yabo da godiya da kirari ga Allah wanda ya amsa masa addu’arsa ya yi masa baiwa da Isma’ila da Is’haƙa bayan ya tsufa tukuf har ya fitar da rai daga samun haihuwa. Lalle Allah mai amsa addu’ar duk wanda ya roƙe shi ne. Daga nan sai Annabi Ibrahimu ya roƙi Allah ya sanya shi ya zama mai tsayar da salla da sharuɗɗanta yadda ya kamata, hakanan su ma zurriyyarsa su zamo masu kula da salla kamar yadda ya dace, yana mai fatan Allah ya karɓa masa addu’arsa. Sai kuma ya yi wa mahaifansa addu’ar Allah ya gafarta musu, tare da sauran muminai maza da mata, ya yafe musu zunubbansu a ranar da za a tsayar da su a gabansa domin yi musu hisabi. Da ma Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mahaifinsa alƙawarin nema masa gafara wurin Allah, kamar yadda ya zo a cikin [Suratu Maryam , aya ta 47], to shi ne a nan ya cika alƙawarinsa. Daga baya ne kuma Allah ya sanar da shi cewa, mahaifinsa ba zai yi imani ba, zai mutu a cikin kafirci, sai ya dakatar da yi masa addu’ar neman gafara, kamar yadda [aya ta 114 a cikin Suratut Tauba ] ta bayyana.

  42. وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ غَٰفِلًا عَمَّا يَعۡمَلُ ٱلظَّٰلِمُونَۚ إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمۡ لِيَوۡمٖ تَشۡخَصُ فِيهِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ

    Open ayah 14:42

    Kada ka yi tsammanin Allah ba Shi da masaniyar abin da azzalumai suke aikatawa. Yana dai saurara musu ne kawai zuwa ranar da idanuwa za su fito zuru-zuru.

  43. مُهۡطِعِينَ مُقۡنِعِي رُءُوسِهِمۡ لَا يَرۡتَدُّ إِلَيۡهِمۡ طَرۡفُهُمۡۖ وَأَفۡـِٔدَتُهُمۡ هَوَآءٞ

    Open ayah 14:43

    Suna masu gaggawa masu ɗage da kawunansu sama ba sa ƙiftawa; zukatansu kuma fanko ne (don tsananin firgita).

  44. وَأَنذِرِ ٱلنَّاسَ يَوۡمَ يَأۡتِيهِمُ ٱلۡعَذَابُ فَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ رَبَّنَآ أَخِّرۡنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖ نُّجِبۡ دَعۡوَتَكَ وَنَتَّبِعِ ٱلرُّسُلَۗ أَوَلَمۡ تَكُونُوٓاْ أَقۡسَمۡتُم مِّن قَبۡلُ مَا لَكُم مِّن زَوَالٖ

    Open ayah 14:44

    Kuma ka gargaɗi mutane game da ranar da azaba za ta zo musu, sai waɗanda suka yi kafirci su ce: “Ya Ubangijinmu, Ka saurara mana zuwa ɗan lokaci ƙanƙani, za mu amsa kiranka kuma mu bi manzanni.” (Sai a ce da su): “A da ba ku ne kuka yi rantsuwa ba cewa ba za ku gushe ba?

  45. وَسَكَنتُمۡ فِي مَسَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَتَبَيَّنَ لَكُمۡ كَيۡفَ فَعَلۡنَا بِهِمۡ وَضَرَبۡنَا لَكُمُ ٱلۡأَمۡثَالَ

    Open ayah 14:45

    “Kuka kuma zauna a gidajen waɗanda suka zalunci kawunansu, kuma irin yadda Muka yi musu ya bayyana a gare ku, Muka kuma ba ku misalai!”

  46. وَقَدۡ مَكَرُواْ مَكۡرَهُمۡ وَعِندَ ٱللَّهِ مَكۡرُهُمۡ وَإِن كَانَ مَكۡرُهُمۡ لِتَزُولَ مِنۡهُ ٱلۡجِبَالُ

    Open ayah 14:46

    Haƙiƙa kuma sun shirya makircinsu, sakamakon makircinsu kuma yana wurin Allah, ko da kuwa duwatsu za su gushe don makircinsu.

  47. فَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ مُخۡلِفَ وَعۡدِهِۦ رُسُلَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٖ

    Open ayah 14:47

    To kada ka yi tsammanin Allah Mai saɓa wa manzanninsa alƙawarinsa ne. Lalle Allah Mabuwayi ne Ma’abocin uƙuba.

  48. يَوۡمَ تُبَدَّلُ ٱلۡأَرۡضُ غَيۡرَ ٱلۡأَرۡضِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُۖ وَبَرَزُواْ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ

    Open ayah 14:48

    (Ka tuna) ranar da za a sake ƙasa ba (wannan) ƙasar ba, da kuma sammai (ba waɗannan samman ba. Halittu) kuma suka fito (daga cikin ƙasa) a gaban Allah Makaɗaici, Mai rinjaye.

  49. وَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ مُّقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ

    Open ayah 14:49

    Kuma za ka ga masu laifi a wannan ranar a ƙuƙumce cikin maruruwa.

  50. سَرَابِيلُهُم مِّن قَطِرَانٖ وَتَغۡشَىٰ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ 

    Open ayah 14:50

    Rigunansu na (tafasasshen) man ƙaɗiran ne, kuma wuta za ta lulluɓe fuskokinsu.

  51. لِيَجۡزِيَ ٱللَّهُ كُلَّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 14:51

    (An yi musu haka ne) don Allah Ya saka wa kowanne rai da gwargwadon abin da ya aikata. Lalle Allah Mai saurin hisabi ne.

  52. هَٰذَا بَلَٰغٞ لِّلنَّاسِ وَلِيُنذَرُواْ بِهِۦ وَلِيَعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَلِيَذَّكَّرَ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

    Open ayah 14:52

    Wannan (Alƙur’ani) saƙo ne ga mutane don kuma a gargaɗe su da shi, kuma su san cewa Shi Allah Ɗaya ne, don kuma ma’abota hankali su wa’azantu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, kada ya yi tsammanin wai don Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jinkirta sauko da azabarsa ga azzalumai ya sha’afa ne daga miyagun ayyukansu na ƙaryata Allah da Manzonsa da hana mutane karɓar gaskiya da sauran miyagun ayyukansu. A’a, Allah ya san duk waɗannan abubuwa da suke aikatawa, domin babu abin da yake ɓuya gare shi. Yana dai jinkirta musu ne kawai har zuwa ranar alƙiyama, ranar da idanuwa za su fito zuru-zuru saboda tsananin fargaba da tsoron abin da za su gani. Lokacin da mutane za su fito daga cikin ƙaburburansu suna gaggawa wajen amsa kiran mai kiran su. Duk kowa ya ɗaga kansa sama yana kallon sararin samaniya a cike da fargaba da tsoro, ba mai iya dawo da ganinsa ƙasa sai dai su ci gaba da zare idanuwansu sama domin tsananin razani da suke ciki. Zukatansu kuma sun zama fanko ba sa iya fahimtar komai don tsananin firgita. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tsoratar da al’ummarsa azabar ranar alƙiyama, ranar da mutanen da suka zalunci kansu da aikata kafirci da shirka da Allah da saɓon Allah za su riƙa roƙon Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jinkirta musu azaba, ya ma mayar da su duniya ko da na ɗan lokaci ƙanƙani ne domin su sami wata dama su yi imani da shi su bi manzannin da ya aiko musu. Sai a mayar musu da martani cikin zargi da cewa, ba su ne a duniya suka rantse a kan cewa, ba za su rabo da rayuwarsu ta duniya zuwa ta lahira ba, domin ba su yarda da akwai tashi bayan mutuwa ba? Har ila yau a faɗa musu cewa, ba su ne suka zauna a gidajen al\'ummun da suka gabace su ba, waɗanda suka zalunci kawunansu da kafirci da ƙaryata annabawa kamar Adawa da Samudawa da sauransu, kuma sun ga irin yadda Allah ya hallaka su, kuma ya yi ta ba su misalai iri-iri don su wa’azantu su gyara halayensu amma hakan bai amfane su ba? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan azzalumai da suka zauni gidajen al\'ummun da suka gabace su sun shirya makirce-makirce iri-iri na yadda za su ga ƙarshen gaskiya da masu kira zuwa gare ta. Daga cikinsu har da waɗanda suka shirya kashe Manzon Allah (ﷺ), amma Allah yana sane da duk ƙulle-ƙullensu na makirci, kuma makircinsu a wurinsa bai taka kara ya karya ba, domin kuwa ai ba zai iya gusar da duwatsu daga mahallansu ba, saɓanin shirin Allah wanda babu mai iya tunkarar sa komai ƙarfinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara kwantar wa da Manzonsa hankali ya tabbatar masa cewa, ba zai saɓa alƙawarin nasara da ya yi masa ba, domin bai taɓa saɓa wa manzanninsa alƙawarin da ya yi musu ba, domin shi mabuwayi ne babu abin da ya fi ƙarfinsa, kuma zai ɗaukaka masoyansa ya ba su izza, kuma shi ma’abocin sakayyar uƙuba ne ga maƙiyansa kuma maƙiyan manzanninsa. Sai ya bayyana inda sakamakon wannan azabar zai faru, shi ne ranar alƙiyama, ranar da za a canja wannan ƙasar da wata ƙasar fara ƙal, sammai ma a canja su da wasu sammai daban. A lokacin duk mutane za su fito daga ƙaburburansu ɗauke da ayyukansu domin tsayuwa gaban Allah wanda shi kaɗai ne mai mulki da isa a wannan ranar. An karɓo daga Sahlu ɗan Sa’ad (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Za a tattara mutane a ranar alƙiyama a kan wata ƙasa fara ƙal kamar gurasar farin gari mai tsafta, babu wata alama ta wani ɗan’adam a kanta.” [Bukhari #6521 da Muslim #2790]. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara masa yarda) ta ce: “Ni ce farkon wadda ta tambayi Manzon Allah (ﷺ) game da wannan ayar [aya ta 48] na ce: “Ina mutane suke a wannan ranar ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Suna kan siraɗi.” [Muslim #2791]. Hakanan lokacin da wani Bayahude ya tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa,: “Ina mutane za su kasance ranar da za a canja wannan ƙasar da wata ƙasar, a kuma canja sammai su ma?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya amsa masa da cewa,: “Suna cikin wani duhu kafin a hau gadar siraɗi.” [Muslim #315]. Daga Saubanu (Allah ya kara masa yarda). Baihaƙi ya fassara hadisin A’isha (Allah ya kara masa yarda) da wannan hadisin, watau faɗar “Suna kan siraɗi” yana nufin suna cikin wani duhu kafin hawan siraɗi wanda za su tsallaka ta kansa. [Dubi, Ibn Hajar, Fat’hul Bari , Juzu’i na 11, shafi na 376]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin azabar da za a yi wa kafirai a wannan rana. Ya bayyana abubuwa uku da za a yi musu azaba da su: <b>Na farko </b>: za a haɗa sashinsu da sashe a ɗaure a mari. Za a dubi masu kafirci da laifuka iri ɗaya a haɗa su a ɗaure wuri guda. <b>Na biyu </b>: za a yi musu tufafi da man ƙaɗiran , wani baƙin mai ne kamar kwalta yana da saurin kamawa da wuta, ga shi kuma da ɗan karen wari. Idan an shafe jikinsu da wannan mai za su yi baƙi ƙirin, su riƙa wani mummunan wari, sannan wuta ta riƙa saurin cinye fatunsu ana canja musu wasu. <b>Na uku </b> : wuta za ta riƙa lulluɓe fuskokinsu, su ƙone ƙurmus. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu haka ne don ya saka wa kowane rai da sakamakon irin aikinsa, wanda ya yi aiki mai kyau ya ga sakamako mai kyau, watau gidan Aljanna, wanda kuwa ya yi aiki mummuna ya ga mummunan sakamako, watau wutar Jahannama. Lalle Allah mai saurin yi wa mutane hisabi ne a kan ayyukansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe wannan Surar da bayyana manufar saukar da Alƙur’ani ga mutane, watau don ya zamanto isar da saƙo ne gare su, a kuma gargaɗe su da abin da ya ƙunsa na tsoratarwa da narkon azaba, don kuma su san cewa, Allah shi kaɗai ne abin bautarsu, don haka su bauta masa kada su haɗa shi da kowa wajen bauta, kuma don masu hankali su wa’azantu da abin da yake cikinsa na darussa daban-daban.