الحجر

Al-Hijr

The Rock · Surah 15 · Ayahs: 99 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ وَقُرۡءَانٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 15:1

    <ITALIC>ALIF LAM RA</ITALIC>. Waɗannan ayoyin Littafi ne, kuma abin karatu ne mabayyani.

  2. رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ كَانُواْ مُسۡلِمِينَ

    Open ayah 15:2

    Waɗanda suka kafirta za su riƙa burin ina ma da sun zama Musulmai.

  3. ذَرۡهُمۡ يَأۡكُلُواْ وَيَتَمَتَّعُواْ وَيُلۡهِهِمُ ٱلۡأَمَلُۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 15:3

    Bar su su ci kuma su ji daɗi, buri kuma ya shagaltar da su ; sai dai ba da daɗewa ba za su sani.

  4. وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٞ مَّعۡلُومٞ

    Open ayah 15:4

    Ba wata alƙarya da Muka hallakar face tana da wani sanannen lokaci (a wurin Allah).

  5. مَّا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ

    Open ayah 15:5

    Ba wata al’umma da za ta riga lokacin da aka iyakance mata ko su jinkirta bayansa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa [Dubi tafsirinmu na Suratul Baƙara don ƙarin bayani game da waɗannan haruffa]. Allah ya bayyana cewa, waɗannan ayoyi masu girman daraja ayoyin littafi ne da ya saukar kuma abin karatu ne da yake bayyana Kaɗaitakar Allah da hukunce-hukuncen shari’a. Sai kuma ya bayyana cewa, kafirai a ranar alƙiyama ko kuma lokacin mutuwa za su yi nadamar ina ma a ce sun kasance su ma Musulmi ne. Domin a lokacin za su gane gaskiyar abin da ake faɗa musu, to amma nadamarsu ba za ta amfane su da komai ba domin lokacinta ya riga ya wuce. Sai kuma ya ja hankalin Manzon Allah (ﷺ) game da abin da kafirai suke yi masa na izgili da cin zarafi cewa, ya ƙyale su, su ci su sha su ji daɗin duniya kamar dabbobi, dogon buri ya shagaltar da su su ƙi yin imani da aiki nagari, amma ba da daɗewa ba za su gane kurensu, za su fahimci irin babbar hasarar da suka tafka ranar alƙiyama. Sannan Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu dalilin jinkirta musu azaba da aka yi ba wani abu ne ya sa haka ba sai domin sunnar Allah ta gabata a baya cewa, babu wata alƙarya da ya hallaka sai bayan da lokacin da ya iyakance musu ya cika. Da lokacin kuwa yayi ba za a ƙara musu ko da sa’a ɗaya ba kamar yadda ba za a rage musu komai ba. Don haka babu wata al’umma da za ta riga lokacin da aka yanke mata, kuma idan lokacinta ya yi ba za a jinkirta mata ba.

  6. وَقَالُواْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِي نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلذِّكۡرُ إِنَّكَ لَمَجۡنُونٞ

    Open ayah 15:6

    Suka kuma ce: “Ya kai wanda aka saukar wa da Alƙur’ani, lalle kai tabbas mahaukaci ne.

  7. لَّوۡ مَا تَأۡتِينَا بِٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

    Open ayah 15:7

    “Me zai hana ka zo mana da mala’iku idan kana daga cikin masu gaskiya?”

  8. مَا نُنَزِّلُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَمَا كَانُوٓاْ إِذٗا مُّنظَرِينَ

    Open ayah 15:8

    (Allah ya ce): “Ba ma saukar da mala’iku sai da gaskiya; inda kuwa haka ya faru, to ba za a saurara musu ba.”

  9. إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا ٱلذِّكۡرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ

    Open ayah 15:9

    Lalle Mu Muka saukar da Alƙur’ani, lalle kuma tabbas Mu za Mu kiyaye shi.

  10. وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي شِيَعِ ٱلۡأَوَّلِينَ 

    Open ayah 15:10

    Haƙiƙa kuma Mun aiko (manzanni) a gabaninka cikin al’ummun farko.

  11. وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

    Open ayah 15:11

    Ba kuwa wani manzo da zai zo musu sai sun zamanto suna yi masa izgili.

  12. كَذَٰلِكَ نَسۡلُكُهُۥ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

    Open ayah 15:12

    Kamar haka ne Muke shigar da shi cikin zukatan kafirai.

  13. لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَقَدۡ خَلَتۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ

    Open ayah 15:13

    Ba za su yi imani da shi ba; haƙiƙa kuma hanyar (sakamakon) mutanen farko ta gabata (wato hallakarwa).

  14. وَلَوۡ فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَظَلُّواْ فِيهِ يَعۡرُجُونَ

    Open ayah 15:14

    Idan da Mun buɗe musu ƙofar sama har suka dinga hawa ta cikinta.

  15. لَقَالُوٓاْ إِنَّمَا سُكِّرَتۡ أَبۡصَٰرُنَا بَلۡ نَحۡنُ قَوۡمٞ مَّسۡحُورُونَ

    Open ayah 15:15

    Tabbas da sun ce: “Ai an yi mana rufa-ido ne kawai; a’a, kai mu dai mutane ne da aka sihirce.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana irin izgili da kafirai suka riƙa yi wa Annabi (ﷺ) suna kiran sa da cewa: “Ya kai wanda aka saukar wa da wa’azi”, watau a riyawarsa ba don sun yarda da cewa Alƙur’ani saukakke ne ba daga Allah. Sun kira shi da wannan ne don su jefe shi da taɓin hankali, suna nufin wai yana aikata abubuwa na marasa hankali. Suka ma ce wai idan har da gaske Allah ne ya aiko shi me ya hana shi zuwa da mala’iku waɗanda za su riƙa ba da shaida a kan abin da yake faɗa? Ko kuma me ya hana ya nemi a hallaka su tun da sun ƙi yin imani da shi, suna kuma aikata kafirci? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa, shi ba ya sauko da mala’iku sai da hikimar da za ta sanya haka. Wato sai lokacin hallaka su ya zo, kuma su sani duk sa’adda mala’iku suka sauko to ta faru ta ƙare, babu sauran a jinkirta musu, za a gaggauto musu da azaba ne nan take. Sannan Allah ya bayyana musu cewa, idan suna neman shaida ne a kan gaskiyar manzancin Annabi (ﷺ), to Alƙur’ani ma ya ishe su shaida, domin shi ne ya saukar masa da shi, yana kuma ɗauke da duk abin da suke buƙatar sani na hukunce-hukunce da tsarin rayuwar ɗan’adam kuma shi ne mai tsare shi daga ƙari ko ragi ko jirkitawa. Sai kuma ya tabbatar wa da Annabi (ﷺ) cewa, ba shi ne manzo na farko da aka taɓa ƙaryatawa ba; gabaninsa ma Allah ya aiko da manzanni da yawa zuwa ga al\'ummu da dama, amma babu wani manzo da ya zo musu sai sun ƙaryata shi sun yi masa izgili, to don haka kamar yadda Allah ya shigar da ɗabi’ar ƙaryatawa cikin zukatan waɗancan al\'ummu to hakan ya shigar da ita cikin zukatan mushirikan Ƙuraishawa, sai suka bijire suka yi taurin kai, don haka mu’amalarsu ga Annabi ta yi kama da mu’amalar kafiran farko ga annabawansu, domin Allah ya tabbatar masa da cewa, ba za su yi imani da wannan Alƙur’ani da ya saukar masa ba. Al’adar Allah ta riga ta gabata ta hallakar da masu ƙaryata manzannin Allah, don haka sai su shiga taitayinsu, su ɗauki izina daga ‘yan baya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, rashin imanin kafirai da ƙaryatawarsu ga Manzo (ﷺ) ba wai don rashin ƙwaƙƙwarar hujja ba ne; taurin kai ne nasu kawai da ƙoƙarin hana mutane su bi gaskiya. Ya kuma tabbatar da cewa, da zai buɗe musu wata ƙofa a sama har su samu suna hawa ta cikinta su leƙo abin da mala’iku suke gudanarwa, to da ba za su yi imani ba, za su tubure ne su ce kawai an yi musu rufa-ido ne, don haka abin da suke gani tasirin tsafi ne amma ba gaskiya ne ba.

  16. وَلَقَدۡ جَعَلۡنَا فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَزَيَّنَّٰهَا لِلنَّٰظِرِينَ

    Open ayah 15:16

    Haƙiƙa kuma Mun sanya taurari a sama, Muka kuma ƙawata ta ga masu gani.

  17. وَحَفِظۡنَٰهَا مِن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٍ

    Open ayah 15:17

    Kuma Muka kiyaye ta daga duk wani shaiɗani la’ananne.

  18. إِلَّا مَنِ ٱسۡتَرَقَ ٱلسَّمۡعَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 15:18

    Sai dai wanda ya yi satar sauraro, sannan sai tauraro mai harshen wuta ya biyo shi.

  19. وَٱلۡأَرۡضَ مَدَدۡنَٰهَا وَأَلۡقَيۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡزُونٖ

    Open ayah 15:19

    Ƙasa kuma Mun shimfiɗa ta Muka sanya manyan duwatsu a cikinta, Muka kuma tsiro da kowane abu a cikinta ƙayyadajje.

  20. وَجَعَلۡنَا لَكُمۡ فِيهَا مَعَٰيِشَ وَمَن لَّسۡتُمۡ لَهُۥ بِرَٰزِقِينَ 

    Open ayah 15:20

    Muka kuma sanya muku kayan rayuwa a cikinta, da kuma wanda ba ku ne kuke arzuta shi ba (wato bayi da dabbobi).

  21. وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا عِندَنَا خَزَآئِنُهُۥ وَمَا نُنَزِّلُهُۥٓ إِلَّا بِقَدَرٖ مَّعۡلُومٖ

    Open ayah 15:21

    Babu wani abu wanda taskokinsa ba a wurinmu suke ba, kuma ba ma saukar da shi sai daidai wani gwargwado sananne.

  22. وَأَرۡسَلۡنَا ٱلرِّيَٰحَ لَوَٰقِحَ فَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَسۡقَيۡنَٰكُمُوهُ وَمَآ أَنتُمۡ لَهُۥ بِخَٰزِنِينَ

    Open ayah 15:22

    Muka kuma aiko da iska mai yin barbara (ga giza-gizai), sai Muka saukar da ruwa daga sama Muka shayar da ku da shi, ba kuma ku ne masu taskance shi ba.

  23. وَإِنَّا لَنَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَنَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثُونَ

    Open ayah 15:23

    Lalle kuma tabbas Mu Muke rayawa kuma Muke kashewa, Mu ne kuma Masu gaje (komai).

  24. وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَقۡدِمِينَ مِنكُمۡ وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَـٔۡخِرِينَ

    Open ayah 15:24

    Haƙiƙa kuma Mun san marigaya daga cikinku kuma haƙiƙa Mun san masu biyowa baya.

  25. وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحۡشُرُهُمۡۚ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٞ

    Open ayah 15:25

    Lalle Ubangijinka kuma Shi zai tattara su. Lalle shi Mai hikima ne, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilai masu tabbatar da gaskiyar abin da Manzo (ﷺ) ya zo da shi na Tauhidi da gaskiyar tashin alƙiyama waɗanda kafirai suke ƙaryata shi a kansu. Allah ya bayyana cewa, ya halicci taurari a sama masu girma waɗanda matafiya suke yin alama da su a tafiye-tafiyensu a kan tudu da ruwa. Kuma ya ƙawata su ga duk wanda zai ɗaga kai ya kalle su. Ya yi haka ne domin su zama dalili ne mai tabbatar da cikakkiyar Ƙudurar Allah. Kuma ya yi wa sama irin wannan nagartacciyar halitta ce domin ta samu cikakken tsaro daga duk wani shaiɗani la’ananne mai ƙoƙarin ya sato labari daga sama ; don haka duk wanda ya yi yunƙurin satar sauraro za a jefe shi da tauraro mai harshen wuta ya ƙona shi ko ya saka shi ya tagayyara. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, cikin dalilan cikar ikonsa akwai ƙasa wadda ya shimfiɗa ta mutane da dabbobi suna yawo a kanta, ya kuma kafa manya-manyan duwarwatsu a cikinta don kada ta riƙa tangal-tangal da su, sannan kuma ya fitar da tsirrai iri daban-daban daga cikinta gwargwadon yadda ya dace da buƙatunsu da kuma hikimarsa. Sannan kuma ya sanya kayan rayuwa a cikinta na abubuwan ci da na sha waɗanda duk wani abu mai rai yake da buƙata. Ya bayyana cewa, shi ne yake arzuta dabbobi da mutanen da ba su da mai ba su sai shi. A taƙaice dai babu wani abu da mutane ko dabbobi suke amfani da shi face Allah ne mai ikon samar da shi da hore musu amfani da shi, kuma yana samar da komai ne gwargwadon hikimarsa da kuma buƙatar masu buƙata. Allah kuma ya ci gaba da bayyana cikakken ikonsa, da cewa, shi ne yake aiko iska wadda take yi wa girgije barbara sai ya cika da ruwa, Allah kuma ya saukar da ruwan sama daga gare shi a wuraren da ya ga dama, sai ya shayar da mutane da dabbobi da shuke-shuke da shi, kuma ya ajiye shi a cikin koguna da ƙoramu da maremari na ruwa da rijiyoyi, kuma babu wani mai iya yin wannan aikin sai Allah shi kaɗai. Kuma daga cikin kamalar ikon Allah (Mai tsarki da daukaka), shi ne yake rayawa yake kuma kashewa, yake tayar da halitta bayan mutuwa, shi kuma wanzajje ne, shi ne mai gaje ƙasa da duk abin da ke cikinta bayan duk wani mai rai ya mutu. Babu abin da bai sani ba; ya san waɗanda za a riga haihuwarsu su riga mutuwa, ya san kuma waɗanda za a haife su daga baya su mutu. Ya tabbatar wa Manzonsa cewa, zai tattara kowa da kowa a ranar alƙiyama domin yi musu hisabi, ya saka wa wanda ya kyautata aikinsa da kyakkyawan sakamako, ya kuma saka wa wanda ya yi mummunan aiki da mummunan sakamako. Shi Allah mai hikima ne cikin dukkan tsare-tsarensa, masanin komai ne babu abin da zai kuɓuce masa.

  26. وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ

    Open ayah 15:26

    Kuma haƙiƙa Mun halicci mutum daga busasshen taɓo mai amo na wani yumɓu mai wari.

  27. وَٱلۡجَآنَّ خَلَقۡنَٰهُ مِن قَبۡلُ مِن نَّارِ ٱلسَّمُومِ

    Open ayah 15:27

    Aljani kuwa Mun halicce shi ne gabanin (halittar mutum) daga wuta mai tsananin zafi.

  28. وَإِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِنِّي خَٰلِقُۢ بَشَرٗا مِّن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ

    Open ayah 15:28

    Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka ya ce da mala’iku: “Lalle Ni zan halicci mutum daga busasshen taɓo mai amo na wani yumɓu mai wari.

  29. فَإِذَا سَوَّيۡتُهُۥ وَنَفَخۡتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُواْ لَهُۥ سَٰجِدِينَ

    Open ayah 15:29

    “To idan Na daidaita shi Na kuma busa masa daga ruhina, to ku faɗi kuna masu sujjada a gare shi.”

  30. فَسَجَدَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ كُلُّهُمۡ أَجۡمَعُونَ 

    Open ayah 15:30

    Sai mala’iku dukkaninsu suka yi sujjada gaba ɗaya.

  31. إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰٓ أَن يَكُونَ مَعَ ٱلسَّٰجِدِينَ

    Open ayah 15:31

    Sai Iblis ya ƙi ya kasance tare da masu yin sujjadar.

  32. قَالَ يَٰٓإِبۡلِيسُ مَا لَكَ أَلَّا تَكُونَ مَعَ ٱلسَّٰجِدِينَ

    Open ayah 15:32

    (Allah) Ya ce: “Ya Iblis, me ka taka da ba za ka kasance tare da masu sujjada ba?”

  33. قَالَ لَمۡ أَكُن لِّأَسۡجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقۡتَهُۥ مِن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ

    Open ayah 15:33

    (Iblis) ya ce: “Ba zai yiwu ba ni in yi sujjada ga wani mutum wanda Ka halitta daga busasshen taɓo mai amo na wani yumɓu mai wari.”

  34. قَالَ فَٱخۡرُجۡ مِنۡهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٞ

    Open ayah 15:34

    (Allah) Ya ce: “To ka fita daga cikinta (Aljannar), lalle kai korarre ne (daga rahamar Allah).

  35. وَإِنَّ عَلَيۡكَ ٱللَّعۡنَةَ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

    Open ayah 15:35

    “Lalle kuma la’ana ta tabbata a kanka har zuwa ranar alƙiyama.”

  36. قَالَ رَبِّ فَأَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ

    Open ayah 15:36

    (Iblis) ya ce: “Ya Ubangijina Ka surara min har zuwa ranar da za a tashe su (watau matattu).”

  37. قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ

    Open ayah 15:37

    (Allah) Ya ce: “To lalle kana daga cikin waɗanda za a saurar musu.

  38. إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡوَقۡتِ ٱلۡمَعۡلُومِ

    Open ayah 15:38

    “Har zuwa rana mai sanannen lokaci.”

  39. قَالَ رَبِّ بِمَآ أَغۡوَيۡتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَأُغۡوِيَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 15:39

    (Iblis) ya ce: “Ubangijina, saboda ɓatar da ni da Ka yi, to lalle kuwa zan ƙawata musu (ɓarna) a bayan ƙasa, kuma tabbas zan ɓatar da su baki ɗaya.

  40. إِلَّا عِبَادَكَ مِنۡهُمُ ٱلۡمُخۡلَصِينَ 

    Open ayah 15:40

    “Sai fa bayinka zaɓaɓɓu daga cikinsu.”

  41. قَالَ هَٰذَا صِرَٰطٌ عَلَيَّ مُسۡتَقِيمٌ

    Open ayah 15:41

    (Allah) Ya ce: “Wannan hanya ce madaidaiciya, mai kaiwa gare Ni.

  42. إِنَّ عِبَادِي لَيۡسَ لَكَ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٌ إِلَّا مَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡغَاوِينَ

    Open ayah 15:42

    “Lalle bayina ba ka da wani iko a kansu, sai dai wanda ya bi ka daga ɓatattu.

  43. وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوۡعِدُهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 15:43

    “Lalle kuma Jahannama tabbas makomarsu ce baki ɗaya.

  44. لَهَا سَبۡعَةُ أَبۡوَٰبٖ لِّكُلِّ بَابٖ مِّنۡهُمۡ جُزۡءٞ مَّقۡسُومٌ

    Open ayah 15:44

    “Tana da ƙofofi bakwai, kowacce ƙofa tana da wani kaso (na kafirai) sananne (da za su shiga ta nan).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin halittar ɗan’adam na farko, watau Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da yadda Iblis ya nuna ƙiyayyarsa da hassadarsa gare shi a gaban mahaliccinsa Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya halicci Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga busasshen taɓo mai amo kuma mai wari saboda daɗewa a ajiye. Ya kuma halicci uban aljannu tun kafin halittar Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi kuma daga wuta mai tsananin zafi. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “An halicci mala’iku daga haske, an kuma halicci aljannu daga harshen wuta, an kuma halicci Adamu daga abin da aka sifanta muku.” [Muslim #2996]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tuna lokacin da Allah ya faɗa wa mala’iku cewa, zai halicci Annabi Adamu daga busasshen yumɓu mai amo, ya kuma umarce su da idan ya gama daidaita halittarsa, to su faɗi gabansa su yi masa sujjada. Sai kuwa suka cika umarnin Allah dukkansu suka faɗi suka yi masa sujjada bayan Allah ya gama halittarsa ya busa masa rai. Iblis wanda yake tare da mala’iku a lokacin ne kaɗai ya ƙi bin wannan umarni don girman kai da hassada. Da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye shi dalilinsa na ƙin yi wa Adamu sujjada bayan ya yi umarni da haka, sai ya amsa cikin nuna girman kai da cewa, ai sam shi bai dace da shi ya yi wa Adamu sujjada ba, saboda an halicce shi da busasshen taɓo mai amo da wari shi kuma an halicce shi da wuta. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Iblis da ya fita daga gidan Aljanna, kuma ya kore shi daga rahamarsa har abada, ya kuma la’ance shi har alƙiyama ta tashi. Sai Iblis ya roƙi Allah da ya saurara masa kada ya karɓi ransa har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Allah kuma ya karɓi roƙonsa ya ce ya saurara masa har lokacin tashin alƙiyama, lokacin da kowa zai mutu ya koma ga Allah, watau lokacin busar ƙaho ta farko. Sai Iblis ya yi alƙawari a gaban Allah, da cewa, tun da har ya ɓatar da shi to sai shi kuma ya ƙawata wa bayinsa hanyoyin saɓonsa a duniya, sai kuma ya ɓatar da su gaba ɗaya daga tafarki madaidaici, amma sai ya togace zaɓaɓɓun bayin Allah masu imani da ikhlasi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa da cewa, zaɓaɓɓun bayinsa kam ba shi da wani iko a kansu ballantana ya yi nasarar ɓatar da su, sai dai kawai ya ɓatar da ɓatattun mutanen da suka bi hanyarsa. Ya kuma tabbatar musu da cewa, Jahannama ce makomarsu gaba ɗayansu daga shi har su. Sannan Allah ya bayyana wannan wuta ta Jahannama da cewa, tana da ƙofofin shigarta har bakwai, kuma kowace ƙofa da akwai wani yanki na mabiya Iblis da za su shiga ta nan.

  45. إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّٰتٖ وَعُيُونٍ

    Open ayah 15:45

    Lalle masu kiyaye dokokin Allah suna cikin gidajen Aljanna da idanuwan (ruwa).

  46. ٱدۡخُلُوهَا بِسَلَٰمٍ ءَامِنِينَ

    Open ayah 15:46

    (A ce da su): “Ku shige ta lafiya lau kuna amintattu.”

  47. وَنَزَعۡنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنۡ غِلٍّ إِخۡوَٰنًا عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ

    Open ayah 15:47

    Muka kuma cire abin da ke cikin zukatansu na ƙullata (suka zama) ‘yan’uwa a kan gadaje suna fuskantar juna.

  48. لَا يَمَسُّهُمۡ فِيهَا نَصَبٞ وَمَا هُم مِّنۡهَا بِمُخۡرَجِينَ

    Open ayah 15:48

    Wata gajiya ba za ta shafe su ba, kuma su ba waɗanda za a fitar ba ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka kiyaye dokokinsa suka guje wa hanyoyin Iblis. Sakamakon shi ne gidajen Aljanna waɗanda suke da idanuwan ruwa masu gudana. Yayin da suka zo shiga gidajensu na Aljanna kuma mala’iku za su riƙa faɗa musu su shiga gidajensu cikin aminci, ba tare da tsoron mutuwa ko rashin lafiya ko wani abin baƙin ciki ba. Allah kuma ya cire duk wata ƙiyayya da ƙullata da take cikin zukatansu, sun zama ‘yan’uwa masu ƙaunar juna. Za su zazzauna a kan kujeru suna fuskantar juna suna hira suna nishaɗi. Ba za su sha wata wahala a cikinta ba, kuma ba za a fito da su daga cikinta ba; za su yi ta zama ne a cikinta har abada. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Muminai za su kuɓuta daga shiga wuta, sai a tsayar da su a kan wata gada da take tsakanin Aljanna da wuta, a karɓar wa sashinsu haƙƙinsa daga sashi, watau zaluncin da suka yi wa juna a duniya, har sai an gama tsarkake su sai a yi musu izinin shiga Aljanna.” [Bukhari #2440]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mala’ika Jibrilu ya zo wurin Annabi (ﷺ) ya ce: “Ya Manzon Allah, ga Khadija nan ta zo maka da ƙwaryar miya a cikinta ko kuma abinci ko abin sha, to idan ta zo gare ka ka isar mata da gaisuwa daga Ubangijinta, ka kuma yi mata albishir da wani gida a Aljanna na dutsen lu’u-lu’u, babu wata hayaniya ko wahala a cikinsa.” [Bukhari #3820 da Muslim #2432]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri da Abu Huraira, daga Annabi (ﷺ) ya ce: “Mai shela zai yi shelar cewa,: ‘Ya ku ‘yan Aljanna, za ku rayu lafiya lau ba za ku yi rashin lafiya ba har abada; kuma za ku rayu har abada ba za ku mutu, za ku ci gaba da zama da ƙuruciya ba za ku tsufa ba har abada; za ku ci gaba da jin daɗi ba za ku wahala ba har abada.’” [Muslim #2837].

  49. ۞نَبِّئۡ عِبَادِيٓ أَنِّيٓ أَنَا ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

    Open ayah 15:49

    Ka bai wa bayina labarin cewa lalle Ni, Ni ne Mai gafara, Mai jin ƙai.

  50. وَأَنَّ عَذَابِي هُوَ ٱلۡعَذَابُ ٱلۡأَلِيمُ 

    Open ayah 15:50

    Kuma lalle azabata ita ce azaba mai raɗaɗi.

  51. وَنَبِّئۡهُمۡ عَن ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ

    Open ayah 15:51

    Kuma ka ba su labari game da baƙin Ibrahimu.

  52. إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗا قَالَ إِنَّا مِنكُمۡ وَجِلُونَ

    Open ayah 15:52

    Lokacin da suka shiga wurinsa suka ce: “Muna yi maka sallama”, ya ce: “Lalle mu a tsorace muke da ku.”

  53. قَالُواْ لَا تَوۡجَلۡ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ

    Open ayah 15:53

    Suka ce: “Kada ka ji tsoro, lalle mu muna yi maka albishir ne da (samun) yaro mai ilimi.”

  54. قَالَ أَبَشَّرۡتُمُونِي عَلَىٰٓ أَن مَّسَّنِيَ ٱلۡكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ

    Open ayah 15:54

    Ya ce: “Yanzu kwa yi mini albishir bayan kuwa ga shi tsufa ya kama ni? To da me kuma za ku yi min albishir?!”

  55. قَالُواْ بَشَّرۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ فَلَا تَكُن مِّنَ ٱلۡقَٰنِطِينَ

    Open ayah 15:55

    Suka ce: “Mun yi maka albishir da gaskiya ne, don haka kada ka zamo daga masu ɗebe ƙauna.”

  56. قَالَ وَمَن يَقۡنَطُ مِن رَّحۡمَةِ رَبِّهِۦٓ إِلَّا ٱلضَّآلُّونَ

    Open ayah 15:56

    Ya ce: “Ba wanda zai ɗebe ƙauna daga rahamar Ubangijinsa, sai ɓatattun (mutane).”

  57. قَالَ فَمَا خَطۡبُكُمۡ أَيُّهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ

    Open ayah 15:57

    Ya ce: “Me yake tafe da ku ya ku waɗannan manzanni?”

  58. قَالُوٓاْ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمٖ مُّجۡرِمِينَ

    Open ayah 15:58

    Suka ce: “Lalle mu an aike mu ne zuwa ga wasu mutane masu laifi (wato mutanen Luɗu).

  59. إِلَّآ ءَالَ لُوطٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 15:59

    “In ban da iyalin Luɗu, lalle tabbas za mu tserar da su baki ɗaya.

  60. إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ قَدَّرۡنَآ إِنَّهَا لَمِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ 

    Open ayah 15:60

    “Sai fa matarsa ita kam mun ƙaddara cewa tabbas za ta zama cikin halakakku.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya sanar da bayinsa cewa, shi mai gafara ne ga duk wanda ya yi laifi ya tuba ya nemi gafara. Kuma azabarsa mai raɗaɗi ce ga duk wanda zai yi laifi ya ƙi tuba zuwa gare shi. Don haka su tuba don su samu gafararsa su kuma kuɓuta daga azabarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartarsa da ya ba su labarin baƙin mala’iku masu daraja da suka ziyarci Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka yi masa albishir da samun haihuwar ɗa da kuma hallaka mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Da suka shiga gare shi suka yi masa sallama shi kuma ya amsa musu da mafi kyan abin da suka yi masa sallama da shi. Ya tashi da gaggawa ya kawo musu soyayyen naman ɗan maraƙi domin su ci, saboda ya zaci cewa, mutane ne kamarsa. To amma sai ya kula sun ƙi cin wannan naman, sai ya tsorata da su ya faɗa musu cewa, shi fa ya tsorata da lamarinsu. To amma sai suka kwantar masa da hankali da cewa su mala’ikun Allah ne, sannan suka yi masa albishir da samun haihuwar ɗa namiji wanda zai zama mai ilimi sosai. Jin wannan albishir nasu ya jefa Annabi Ibrahimu cikin mamaki, ya tambaye su, yanzu sa yi masa albishir irin wannan bayan ga shi tsufa ya kama shi, to wane irin albishir ne wannan suke yi masa?! Sai mala’iku suka amsa masa da cewa, sun yi masa albishir ne da gaskiya, don haka ya daina kokwanto, kuma kada ya cire tsammanin samun haihuwa saboda tsufansa. Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nuna musu cewa, shi bai cire tsammanin samun rahamar Ubangijinsa ba, domin babu mai cire tsammani daga samun rahamar Allah sai ɓatattun mutane da suka saki hanyar Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, bayan hankalin Annabi Ibrahimu ya kwanta ya daina jin tsoro, sai ya shiga tambayar mala’iku labarinsu da dalilin zuwansu. Sai suka faɗa masa cewa, an aiko su ne su hallaka wasu miyagun mutane masu ɓarna, watau mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen neman maza maimakon su riƙa auren ‘ya’ya mata. Mala’ikun suka faɗa masa cewa, ai za su tserar da iyalan Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga hallakarwa in ban da matarsa ita kam za ta kasance cikin halakakku, domin ya tabbata ita kafira ce ba ta yi imani da Annabi Luɗu ba, kuma tana taimaka wa musu ɓarna wajen gudanar da ɓarnarsu.

  61. فَلَمَّا جَآءَ ءَالَ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلُونَ

    Open ayah 15:61

    To lokacin da manzannin suka zo wa iyalin Luɗu.

  62. قَالَ إِنَّكُمۡ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ

    Open ayah 15:62

    Ya ce: “Lalle ku wasu mutane ne da ba a san su ba.”

  63. قَالُواْ بَلۡ جِئۡنَٰكَ بِمَا كَانُواْ فِيهِ يَمۡتَرُونَ

    Open ayah 15:63

    Suka ce: “A’a, mu mun zo maka ne da abin da (mutanenka) suke kokwanto game da shi.

  64. وَأَتَيۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ

    Open ayah 15:64

    “Mun kuma zo maka da dahir, lalle kuma tabbas mu masu gaskiya ne.

  65. فَأَسۡرِ بِأَهۡلِكَ بِقِطۡعٖ مِّنَ ٱلَّيۡلِ وَٱتَّبِعۡ أَدۡبَٰرَهُمۡ وَلَا يَلۡتَفِتۡ مِنكُمۡ أَحَدٞ وَٱمۡضُواْ حَيۡثُ تُؤۡمَرُونَ

    Open ayah 15:65

    “Sai ka tafi da iyalinka cikin wani yankin dare ka kuma riƙa bin su a baya, kada kuwa ɗaya daga cikinku ya waiwaya, kuma ku tafi inda aka umarce ku.”

  66. وَقَضَيۡنَآ إِلَيۡهِ ذَٰلِكَ ٱلۡأَمۡرَ أَنَّ دَابِرَ هَٰٓؤُلَآءِ مَقۡطُوعٞ مُّصۡبِحِينَ

    Open ayah 15:66

    Muka kuwa sanar da shi abin da Muka ƙaddara na wannan al’amari cewa, ƙarshen waɗannan zai yanke ne da asuba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana labarta mana cewa, lokacin da mala’ikun suka bar wajen Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka iso wajen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cikin kamannin mutane, suka yi masa sallama ya amsa musu, sai ya bayyana musu cewa, bai gane ko su wane ne su ba. Da suka ga alamar ya tsorata da su sai suka kwantar masa da hankali da cewa, sun zo ne da niyyar hallaka mutanensa waɗanda suke shakkar aukuwar azaba a kansu, duk kuwa da mummunan laifin da suke tafkawa na neman maza da lalata. Saboda haka mala’ikun suka tabbatar wa Annabi Luɗu cewa, da gaske suke ba da maganar wasa suka zo ba. Sai suka umarce shi da ya kwashe iyalansa cikin dare ya fita daga wannan garin ya bi su a baya, kuma kada wani daga cikinsu ya waiwaya komai suka ji yana faruwa, kawai su yi ta tafiya inda Allah ya umarce su su tafi. Kuma Allah ya sanar da Annabi Luɗu ta hanyar wahayi cewa, ƙarshen mutanensa ya zo, domin da asuba Allah zai hallaka su ƙwansu da ƙwarƙwatarsu, har da matarsa.

  67. وَجَآءَ أَهۡلُ ٱلۡمَدِينَةِ يَسۡتَبۡشِرُونَ

    Open ayah 15:67

    Mutanen garin kuma suka zo suna murna (da ganin baƙin).

  68. قَالَ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ ضَيۡفِي فَلَا تَفۡضَحُونِ

    Open ayah 15:68

    Ya ce: “Lalle waɗannan baƙina ne, kada fa ku kunyata ni.

  69. وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُخۡزُونِ

    Open ayah 15:69

    “Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kada ku tozarta ni.”

  70. قَالُوٓاْ أَوَلَمۡ نَنۡهَكَ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ 

    Open ayah 15:70

    Suka ce: “Ashe ba mu hana ka (ka saukar da) mutane (baƙi ba)?”

  71. قَالَ هَٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِيٓ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ

    Open ayah 15:71

    Ya ce: “Ga ‘ya’yana nan (ku aura) idan kun kasance masu aikata (haka).

  72. لَعَمۡرُكَ إِنَّهُمۡ لَفِي سَكۡرَتِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

    Open ayah 15:72

    “Na rantse da rayuwarka lalle su tabbas suna cikin mayensu suna ta ɗimuwa.”

  73. فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُشۡرِقِينَ

    Open ayah 15:73

    Sai tsawa ta auka musu lokacin hudowar rana.

  74. فَجَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٍ

    Open ayah 15:74

    Sai Muka mayar da samanta ya koma ƙasa, Muka kuma yi musu ruwan duwatsu soyayyu.

  75. إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡمُتَوَسِّمِينَ

    Open ayah 15:75

    Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga masu hangen nesa.

  76. وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٖ مُّقِيمٍ

    Open ayah 15:76

    Lalle kuma ita (alƙaryar) tabbas tana kan wani gwadabe ne miƙaƙƙe.

  77. إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 15:77

    Lalle a game da wannan tabbas akwai izina ga muminai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cewa, lokacin da mutanen alƙaryar Sadum suka sami labarin saukar wasu baƙin samari a gidan Annabi Luɗu sai suka yiwo dafifi suka zo suna murnar sun sami abin da suke nema. Da Annabi Luɗu ya gan su sai ya tare su yana roƙonsu da cewa, waɗannan mutanen fa baƙinsa ce, su ji tsoron Allah kada su kunyata shi a gaban baƙinsa. Yana yi musu magiya su ji tsoron Allah su guji aikata wannan mummunan aiki nasu, kada su tozarta shi. Annabi Luɗu ya yi wannan magana ne kafin ya san cewa waɗannan baƙi nasa mala’ikun Allah ne, kamar yadda yake a [Suratu Hud , aya ta 78-80]. Duk da wannan magiya ta Annabi Luɗu gwiwar mutanensa ba ta yi sanyi ba, sai suka amsa masa da cewa, ashe ba sun yi masa kashedi a kan karɓar baƙuntar mutane ba? Watau shi ne ya jawo wa kansa abin kunya. Sai Annabi Luɗu ya nuna musu `ya`yansu mata da Allah ya halitta musu don su yi auratayya a tsakaninsu, ya umarce su cewa, su je mana su aure su. To amma ina, idonsu ya rufe sun gigice ba su san irin mummunan sakamakon da wannan rashin kunyar zai haifar musu ba, shi ya sa Allah ya yi rantsuwa da rayuwar Annabi Muhammadu (ﷺ) cewa, suna cikin mayen sha’awa suna ɗimuwa da faganniya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana azabar da ta auka wa mutanen Annabi Luɗu da sassafe lokacin da rana take hudowa, sai wata tsawa mai tsanani mai girgiza ƙasa ta auka musu, Allah ya mayar da saman garin ya koma ƙasa, sannan ya bi su da ruwan duwatsu na wutar Jahannama. Allah ya bayyana cewa, a game da wannan hallakarwar da ya yi wa mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lalle akwai ayoyi, watau abubuwan lura ga masu lura da hangen nesa da kyau, domin kufan gidajen waɗannan mutane yana nan a kan hanyar duk masu wucewa ta wannan gari. Lalle a cikin wannan abu da ya faru akwai ayoyi ga muminai.

  78. وَإِن كَانَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأَيۡكَةِ لَظَٰلِمِينَ

    Open ayah 15:78

    Lalle kuma mutanen (alƙaryar) Mai duhuwa tabbas sun zamanto azzalumai.

  79. فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 15:79

    Sai Muka azabtar da su, lalle kuma su biyun suna kan wani gwadabe ne fitacce.

  80. وَلَقَدۡ كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡحِجۡرِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ 

    Open ayah 15:80

    Haƙiƙa kuma mutanen Hijiru (Samudawa) sun ƙaryata manzanni.

  81. وَءَاتَيۡنَٰهُمۡ ءَايَٰتِنَا فَكَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ

    Open ayah 15:81

    Muka kuma kawo musu ayoyinmu, sai suka zamanto masu bijirewa daga gare su.

  82. وَكَانُواْ يَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتًا ءَامِنِينَ

    Open ayah 15:82

    Sun zamanto suna fafe duwatsu suna yin gidaje su zama cikin aminci.

  83. فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُصۡبِحِينَ

    Open ayah 15:83

    Sai tsawa ta auka musu da asuba.

  84. فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

    Open ayah 15:84

    Sai abin da suka zamanto suna aikatawa bai amfane su ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi nuni zuwa ga ƙissar mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka zauna a wata alƙarya mai duhuwa. Sun zalunci kawunansu yayin da suka kafirce wa Allah suka kuma ƙaryata annabawa. Allah ya kama su da azaba mai tsanani ya hallaka su gaba ɗaya. Guraben gidajensu da na mutanen Annabi Luɗu suna nan a fili a kan hanyar matafiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da ƙissar Samudawa mutanen Annabi Salihu, watau mutanen Hijru, wani gari da ke tsakanin Hijaz da Sham. Sun ƙaryata duk manzanni, domin kuwa sun ƙaryata Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya bayyana cewa, ya nuna musu duk wata hujja da dalili da zai tabbatar musu da gaskiyar Annabi Salihu. Daga cikinsu har da taguwar da suka nema a fito masa da ita, amma sai suka bijire wa duk waɗannan hujjoji suka yi watsi da su. Hakanan ba su gode wa Allah a kan ni’imomin da ya yi musu ba, domin ya ba su ƙarfin jiki da lafiya har sun kasance suna fafe duwatsu suna yin gidaje da suke zaune a cikinsu amintattu babu abin da yake ba su tsoro. Ya tabbata a wani hadisi, Annabi (ﷺ) ya wuce ta gidajen Samudawa a Hijru. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku shiga wurin waɗannan da aka saukar wa da azaba sai kuna kuka, idan ba za ku kasance masu kuka ba, to kada ku shiga wurarensu don kada abin da ya same su ku ma ya same ku.” [Bukhari #433 da Muslim #2980]. Allah ya bayyana cewa, saboda wannan butulcin nasu ya hallaka su a lokacin da wata tsawa ta azaba ta afka musu da asuba ba zato ba tsammani. Abin da suka yi ta tarawa na dukiyoyi iri-iri da gidajensu na duwatsu da suka yi ta ginawa ba su kare su daga azabar Allah ba.

  85. وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَإِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞۖ فَٱصۡفَحِ ٱلصَّفۡحَ ٱلۡجَمِيلَ

    Open ayah 15:85

    Ba Mu kuma halicci sammai da ƙasa ba sai da gaskiya. Kuma lalle alƙiyama tabbas mai zuwa ce, sai ka yi afuwa kyakkyawar afuwa.

  86. إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡخَلَّٰقُ ٱلۡعَلِيمُ

    Open ayah 15:86

    Lalle Ubangijinka Shi ne Mai halitta, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna hikimar yin halitta gaba ɗaya da cewa, bai halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakaninsu da abubuwan da suke cikinsu a banza ba; ya yi su ne don wata hikima mai girma, ya halicce su don gaskiya, watau don su nuna cikar ikon mahaliccinsu da yalwar rahamarsa da iliminsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai ba tare da haɗa shi da abokin tarayya ba. Sannan su tabbatar da cewa, alƙiyama gaskiya ce tana nan tafe. Ashe duk wanda ya iya halittar sammai da ƙasa da girmansu, ba zai gagare shi ya sake dawo da halittar mutum ba bayan mutuwa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi afuwa mai kyau, wadda babu cutarwa a cikinta; ya saka da kyakkyawa yayin da aka yi masa mummuna. Lalle Allah shi ne mahaliccin komai da kowa masanin duk wata halitta da ya yi.

  87. وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَٰكَ سَبۡعٗا مِّنَ ٱلۡمَثَانِي وَٱلۡقُرۡءَانَ ٱلۡعَظِيمَ

    Open ayah 15:87

    Haƙiƙa kuma Mun ba ka (ayoyi) bakwai waɗanda ake ta nanatawa (wato Suratul Fatiha ) da kuma Alƙur’ani mai girma.

  88. لَا تَمُدَّنَّ عَيۡنَيۡكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 15:88

    Kada ka zura idanuwanka ga abubuwan jin daɗi da Muka ba wa wasu dangogi daga cikinsu, kada kuma ka yi baƙin ciki a kansu, kuma ka ƙasƙantar da kanka ga muminai.

  89. وَقُلۡ إِنِّيٓ أَنَا ٱلنَّذِيرُ ٱلۡمُبِينُ

    Open ayah 15:89

    Ka kuma ce: “Lalle ni, ni ne mai gargaɗi mabayyani\".

  90. كَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَى ٱلۡمُقۡتَسِمِينَ 

    Open ayah 15:90

    Kamar yadda Muka saukar wa masu rarrabawa (wato ma’abota littafi).

  91. ٱلَّذِينَ جَعَلُواْ ٱلۡقُرۡءَانَ عِضِينَ

    Open ayah 15:91

    (Su ne) waɗanda suka mai da Alƙur’ani kashi-kashi.

  92. فَوَرَبِّكَ لَنَسۡـَٔلَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 15:92

    (Na rantse) da Ubangijinka tabbas za Mu tambaye su gaba ɗaya.

  93. عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 15:93

    Game da abin da suka kasance suna aikatawa.

  94. فَٱصۡدَعۡ بِمَا تُؤۡمَرُ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

    Open ayah 15:94

    To ka tsage gaskiyar abin da aka umarce ka da shi, ka kuma kawar da kanka daga mushirikai.

  95. إِنَّا كَفَيۡنَٰكَ ٱلۡمُسۡتَهۡزِءِينَ

    Open ayah 15:95

    Lalle Mu Mun isar maka (sharrin) masu izgili.

  96. ٱلَّذِينَ يَجۡعَلُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 15:96

    (Su ne) waɗanda suke sanya wani abin bauta tare da Allah. Ba ko da daɗewa ba za su sani.

  97. وَلَقَدۡ نَعۡلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدۡرُكَ بِمَا يَقُولُونَ

    Open ayah 15:97

    Haƙiƙa kuma Muna sane da cewa ƙirjinka yana ƙunci game da abin da suke faɗa.

  98. فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ ٱلسَّٰجِدِينَ

    Open ayah 15:98

    To sai ka yi tasbihi tare da godiyar Ubangijinka, ka kuma zamo cikin masu sujjada.

  99. وَٱعۡبُدۡ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأۡتِيَكَ ٱلۡيَقِينُ

    Open ayah 15:99

    Ka kuma bauta wa Ubangijinka har yaƙini ya zo maka (wato mutuwa). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, ya ba shi wasu ayoyi bakwai waɗanda a koyaushe ake maimaita karatunsu, su ne ayoyin Suratul Fatiha guda bakwai waɗanda kowane mai salla ta farilla ko nafila sai ya maimaita karatunsu a cikin raka’o’in sallarsa. Ya kuma ba shi Alƙur’ani mai girma wanda ya ƙunshi alherin duniya da na lahira, yake kuma bayyana wa ɗan’adam kyakkyawan tsari na rayuwa wanda yake cike da adalci da sanin yakamata. An karɓo daga Abu Sa’id ɗan Al-Mu’alla (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya wuce ni ina salla, sai ya kirawo ni, amma ban amsa masa ba har sai da na gama salla sannan na je wurinsa, sai ya ce: “Me ya hana ka zuwa gare ni?” Sai na ce: “Salla nake yi a lokacin.” Sai ya ce: “Ashe ba Allah ya ce: ‘Ya ku waɗanda suka yi imani, ku amsa kiran Allah, ku amsa wa Manzo idan ya kirawo ku’ ba?” Annabi ya ci gaba da ce masa: “Shin ba na karantar da kai mafi girman sura ba a Alƙur’ani kafin in fita daga wannan masallacin?” Abu Sa’id ya ce: “Sai kuma ya kama hanya zai fita, sai na tuna masa, sai ya ce: “Ita ce (Alhamdu lillahi Rabbil alamin ); su ne ayoyi bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da kuma Alƙur’ani mai girma da aka ba ni.” [Bukhari #4474]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ummul Ƙur’an ita ce ayoyi bakwai da ake maimaita karatunsu da Alƙur’ani mai girma.” [Bukhari #4704]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana Manzonsa ɗaga kai ya kalli ni’imomi na rayuwar duniya iri-iri da Allah ya ba wa kafirai suna fantamawa a cikinsu daidai da son ransu, suna kuma ƙaryata shi da butulce wa Allah. Duk wannan wani ƙyale-ƙyale ne na duniya mai gushewa, don haka kada ya damu da ƙaryata shi ko izgili da suke yi masa, ba wani alheri ko amfani tare da su. Ya mai da hankalinsa ga muminai da suke tare da shi sun ishe shi komai, ya kuma yi tawalu’u gare su. Ya kuma umarce shi da ya dage a kan gargaɗin mutanensa daga azabar Allah, ya kuma bayyana musu cewa, shi mai bayyana gargaɗinsa ne a fili don kowa ya ji ya nutsu. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Misalina da misalin abin da Allah ya aiko ni da shi kamar misalin wani mutum ne da ya zo wa mutanensa ya ce musu: ‘Ya ku mutanena, lalle ni na ga rundunar mahara da idona, kuma ni mai gargaɗi ne gare ku na musamman, don haka ku tsira da kanku, ku tsira da kanku.’ Sai wasu daga cikin mutanensa suka ji maganarsa suka fita a farkon dare suka tafi a natse har suka tsira. Wasu kuma daga mutanensa suka ƙaryata shi, sai kuwa waɗannan mahara suka yi musu sammako suka hallaka su gaba ɗayansu. Wannan shi ne misalin wanda ya yi mini ɗa’a ya bi abin da na zo da shi, da kuma misalin wanda ya saɓa mini ya ƙaryata abin da na zo da shi na gaskiyar.” [Bukhari #7283 da Muslim #2283]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da yi wa mushrikai kashedi da gargaɗi kan su guji abin da zai jawo musu azabarsa kamar yadda ya saukar da ita ga waɗanda suka rarraba littattafansu suka yi imani da wasu suka kafirce wa wasu, ko suka yi imani da wani ɓangare na littafi suka kafirce wa wani ɓangare. Su waɗannan mushrikai kuma siffanta Alƙur’ani suka yi da siffofi iri-iri; wani lokaci su ce tsafi ne, wani lokaci su ce bokanci ne, a wani lokaci kuma su kira shi waƙe. Allah ya yi wa Annabi rantsuwa da Zatinsa cewa, haƙiƙa sai ya yi wa waɗannan mutane gaba ɗayansu tambayoyi game da duk abin da suka aikata a nan duniya na saɓon Allah da kafirci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tsaya ya tsage gaskiya, ya bayyana abin da aka umarce shi da shi na kira zuwa kaɗaita Allah da bauta da ƙaurace wa shirka, kuma kada ya damu da maganganun da mushirikai za su yi ta yi a kai. Kada kuma ya ji tsoron su, Allah (Mai tsarki da daukaka) ne zai tsare shi daga makircin duk wani mai izgili daga cikin shugabannin kafirai na Ƙuraishawa. Allah ya bayyana su da cewa, sun yi nisa wajen rungumar gumaka suna bauta musu tare da Allah, ya kuma tabbatar musu da cewa, za su gane kurensu, don za su ga mummunan sakamakon ayyukansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi cewa, ya san irin damuwar da yake ciki ta ƙaryata shi da kafirai suke yi, tare da yi masa izigili da cin zarafi iri-iri shi da sahabbansa. To sai ya sanar da shi abin da zai riƙa yi don cire wannan damuwar daga ransa, shi ne ya yi ta tsarkake Allah tare da yabon sa da gode masa, watau ya yawaita tasbihi da faɗar ‘Alhamdu lillahi ’, sannan ya shagalta da salloli na farilla da nafila. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Idan Annabi (ﷺ) yana cikin wata damuwa yakan ce: ( <b>لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَرَبُّ الْأَرْضِ وَرَبُّ الْعَرْشِ الْكَرِيم). </b>Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah mai girma mai haƙuri; babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin Al’arshi mai girma; babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin ƙasa kuma Ubangijin Al’arshi mai girma.” [Muslim #7097]. Da waɗannan abubuwa ne zai magance duk wata damuwa da kafirai suka sa shi cikinta. Allah ya umarce shi da ya ci gaba da bautar sa babu ƙaƙƙautawa har ya cim ma dahir, watau mutuwa ta riske shi a kan haka.