النحل
An-Nahl
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
أَتَىٰٓ أَمۡرُ ٱللَّهِ فَلَا تَسۡتَعۡجِلُوهُۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 16:1Al’amarin Allah ya zo, don haka kada ku nemi gaggauto shi (watau ranar alƙiyama). Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma ɗaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi).
يُنَزِّلُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ بِٱلرُّوحِ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرُوٓاْ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱتَّقُونِ
Open ayah 16:2Yana saukar da mala’iku da wahayi na umarninsa ga waɗanda Ya ga dama daga bayinsa da cewa,: “Ku yi gargaɗi cewa,, lalle ba wani abin bauta sai Ni, to sai ku kiyaye dokokina.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da tabbatar wa kafirai cewa, ranar alƙiyama da suke yawan tambayar Manzon Allah (ﷺ) game da lokacin zuwanta, to lokacinta ya gabato kuma yana nan zai wakana babu makawa, don haka su daina neman a gaggauto da zuwansa. Sai kuma ya bayyana musu cewa, ya tsarkaka daga duk wani abu da suke yin shirka da shi, watau jingina masa wasu abokan tarayya ko danganta shi ga ‘ya’ya ko mata da duk wani abu da ya saɓa da kamala. Ya kuma bayyana cewa, shi ne yake saukar da mala’iku ɗauke da wahayi mai raya zukatan bayi, wanda yake ƙunshe da hukuncinsa ga wanda ya ga dama cikin bayinsa, su ne manzanninsa, ya kuma umarce su da su gargaɗi mutane game da aikata shirka, su nuna musu cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah kaɗai, don haka su kiyaye dokokinsa, su aikata abin da ya wajabta musu su guji abin da ya hana su.
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۚ تَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 16:3Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi).
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٖ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٞ مُّبِينٞ
Open ayah 16:4Ya halicci mutum daga maniyyi, sai ga shi mai jayayya a fili.
وَٱلۡأَنۡعَٰمَ خَلَقَهَاۖ لَكُمۡ فِيهَا دِفۡءٞ وَمَنَٰفِعُ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 16:5Ya kuma halicci dabbobin ni\'ima. Kuna da (abin) ɗumama jiki tattare da su, da kuma sauran abubuwan amfani; daga gare su ne kuma kuke ci.
وَلَكُمۡ فِيهَا جَمَالٌ حِينَ تُرِيحُونَ وَحِينَ تَسۡرَحُونَ
Open ayah 16:6Kuma kuna da abubuwan ado a tattare da su, lokacin da kuke dawowa (daga kiwo) da kuma lokacin da kuke fita (da safe).
وَتَحۡمِلُ أَثۡقَالَكُمۡ إِلَىٰ بَلَدٖ لَّمۡ تَكُونُواْ بَٰلِغِيهِ إِلَّا بِشِقِّ ٱلۡأَنفُسِۚ إِنَّ رَبَّكُمۡ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 16:7Suna kuma ɗaukar kayayyakinku masu nauyi zuwa garin da ba za ku iya isar sa ba sai da ƙyar. Lalle Ubangijinku tabbas Mai tausayi ne, Mai rahama.
وَٱلۡخَيۡلَ وَٱلۡبِغَالَ وَٱلۡحَمِيرَ لِتَرۡكَبُوهَا وَزِينَةٗۚ وَيَخۡلُقُ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:8Dawakai da kuma alfadarai da jakai (Ya halitta muku su) don ku hau su kuma su zama ado. Zai kuma hallici abin da ma ba ku sani ba.
وَعَلَى ٱللَّهِ قَصۡدُ ٱلسَّبِيلِ وَمِنۡهَا جَآئِرٞۚ وَلَوۡ شَآءَ لَهَدَىٰكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 16:9Kuma bayanin hanya madaidaiciya haƙƙi ne a kan Allah, daga kuma (hanyar) akwai karkatacciya. Da kuma Ya ga dama lalle da Ya shirye ku gaba ɗaya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ɗimbin ni’imominsa ne da ya yi wa bayinsa a sama da ƙasa da tudu da ruwa. Waɗannan ni’imomi kuma dukkansu dalilai ne masu nuna Kaɗaitar Allah a Rububiyyarsa da Uluhiyyarsa. Don haka shi kaɗai ya cancanci bauta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fara da bayanin halittar sammai da abin da yake cikinsu. Hakanan ya halicci ƙasa da abin da take ɗauke da shi, kuma ya yi halittarsu da gaskiya, watau domin su zamanto dalilai masu tabbatar da Kaɗaitakarsa da cancantar a bauta masa ba tare da haɗa komai da shi ba. Sai kuma ya bayyana halittar ɗan’adam wanda shi ne mafi darajar halittunsa gaba ɗaya; ya halicce shi ne daga ɗigon maniyyi wulaƙantacce mai rauni, ya kuma tsara halittarsa mataki-mataki har ya cika daidaitaccen mutum, to amma bayan ya zo duniya sai ya kasance mai yawan jayayya a kan ƙarya don ya kawar da gaskiya, kuma mai bayyana wannan hali a fili maimakon gode wa Allah a kan ni’imomin da ya yi masa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu ni’imomi da ya yi wa ‘yan’adam bayan halittarsu a wannan duniya. Daga cikinsu akwai dabbobin ni’ima, watau raƙuma da shanu da tumakai da awakai; ya halicce su ne don amfanin ‘yan’adam. Suna amfani da gashinsu wajen yin tufafin sawa don ɗumama jiki, da tatsar nononsu domin sha, da kuma cin namansu, har ma suna yin ado da su lokacin da dabbobin suke hutawa da yamma da lokacin da suke fita kiwo da safe. Ya bayyana cewa, da waɗannan dabbobi mutane suke amfani wajen ɗaukar kaya masu nauyi a lokacin tafiye-tafiyensu zuwa wasu garuruwa masu nisan gaske waɗanda ba za su iya kaiwa gare su ba sai da ƙyar da gumin goshi. Don haka ya kamata su sani cewa, lalle Ubangijinsu mai tausayi ne mai jin ƙai; ya hore musu waɗannan dabbobi waɗanda suke da tsananin buƙatarsu a rayuwarsu. Ya ci gaba da bayyana musu ni’imar wasu dabbobin da amfaninsu gare su, su ne dawakai da alfadarai da jakuna. Allah ya halitta musu su ne domin su hau, su ɗaukar musu kaya, kuma su yi ado da su. Baya ga waɗannan dabbobin hawan da ɗaukar kaya kuwa zai ma halicci wasu abubuwan da a wancan lokaci ba su san su ba. Wannan ayar ba ta nuna haramcin cin naman doki ba, domin ta ambaci mafi yawancin amfanin da ake yi da waɗannan dabbobi ne. Sannan kuma an haɗa ambaton dawaki tare da alfadarai da kuma jakuna na gida da aka haramta cin namansu, domin larabawa ba su cika cin nama waɗannan dabbobi ba, domin ba su da yawa a yankinsu, kuma ga shi suna da buƙatar dawakai wajen yaƙe-yaƙensu. Don haka rashin ambaton cin namansu a nan ba ya nuna haramci ko kaɗan. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya hana cin naman jakunan gida, ya ba da izinin cin naman dawakai.” [Bukhari #4219 da Muslim #1941]. An karɓo daga Asma’u ‘yar Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ta ce: “Mun yanka doki mun ci a zamanin Manzon Allah (ﷺ) a Madina.” [Muslim #1942]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi ne ya ɗora wa kansa nauyin bayanin hanya madaidaiciya da za ta kai bayinsa zuwa ga samun yardarsa da kyakkyawan sakamakonsu, watau bayanin addinin Musulunci gare su. Amma akwai wasu karkatattun hanyoyi na Shaiɗan, waɗanda duk wanda ya bi su, to za su raba shi da gaskiya, kamar hanyoyin Yahudu da Nasara da maguzawa da mushirikai. Sannan ya bayyana cewa, duk waɗannan suna wakana ne da ikonsa da ganin damarsa. Da a ce ya ga dama da ya shiryar da mutane gaba ɗaya zuwa ga addinin Musulunci.
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗۖ لَّكُم مِّنۡهُ شَرَابٞ وَمِنۡهُ شَجَرٞ فِيهِ تُسِيمُونَ
Open ayah 16:10Shi ne wanda Ya saukar da ruwa daga sama; daga gare shi ne kuke sha, daga gare shi ne kuma bishiyoyi suke (sha) wanda da su ne kuke kiwon (dabbobinku).
يُنۢبِتُ لَكُم بِهِ ٱلزَّرۡعَ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلنَّخِيلَ وَٱلۡأَعۡنَٰبَ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 16:11Da shi (ruwan) Yake tsiro muku da shuke-shuke da zaitun da dabinai da inabai da kuma kowanne irin ‘ya’yan itace. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke tunani.
وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ وَٱلنُّجُومُ مُسَخَّرَٰتُۢ بِأَمۡرِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Open ayah 16:12Ya kuma hore muku dare da rana da kuma wata; taurari ma ababen horewa ne da umarninsa. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu hankali.
وَمَا ذَرَأَ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُخۡتَلِفًا أَلۡوَٰنُهُۥٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَذَّكَّرُونَ
Open ayah 16:13Da kuma abubuwan da Ya halitta muku a ƙasa masu launi iri daban-daban. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke wa\'azantuwa.
وَهُوَ ٱلَّذِي سَخَّرَ ٱلۡبَحۡرَ لِتَأۡكُلُواْ مِنۡهُ لَحۡمٗا طَرِيّٗا وَتَسۡتَخۡرِجُواْ مِنۡهُ حِلۡيَةٗ تَلۡبَسُونَهَاۖ وَتَرَى ٱلۡفُلۡكَ مَوَاخِرَ فِيهِ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 16:14Shi ne kuma wanda Ya hore muku kogi don ku ci daddaɗan nama mai taushi daga gare shi, ku kuma riƙa fito da kayan ado daga cikinsa waɗanda kuke ɗaurawa, kuma ka ga jiragen ruwa suna keta shi don kuma ku nema daga falalarsa (Ubangiji) don kuma ku riƙa godiya.
وَأَلۡقَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمۡ وَأَنۡهَٰرٗا وَسُبُلٗا لَّعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Open ayah 16:15Ya kuma sanya wa ƙasa turaku don kada ta riƙa tangal-tangal da ku da kuma ƙoramu da hanyoyi don ku riƙa gane (inda kuka dosa).
وَعَلَٰمَٰتٖۚ وَبِٱلنَّجۡمِ هُمۡ يَهۡتَدُونَ
Open ayah 16:16Da kuma alamomin (hanya). Da kuma taurari ne suke gane (inda suka dosa). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana ɗimbin ni’imomin da ya yi wa ‘yan’adam. Ya saukar musu da ruwan sama wanda suke sha suke shayar da dabbobinsu. Da shi ne kuma bishiyoyi suke tsirowa waɗanda dabbobinsu suke ci suna kiwo. Da wannan ruwan sama ne, har ila yau, Allah yake fitar musu da shuke-shukensu na abincinsu da zaitun da inabai da dabinai da kowane irin ‘ya’yan itatuwa. Lalle a cikin halittar waɗannan abubuwa akwai ayoyi masu nuna ikon Allah ga mutanen da suke tunani cikin halittarsa domin kafa dalili da ita a kan cikar Ƙudurarsa da girmansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ni’imarsa ta hore wa ‘yan’adam dare wanda suke hutawa a cikinsa su yi barci, ya kuma hore musu rana domin su fita neman abinci a cikinta. Don haka ya tabbatar musu da cewa, duk kuma manya-manyan halittunsa na sama, kamar rana da wata da taurari, ya hore musu su da umarninsu, su ba su haske su yi amfani da su wajen gane lissafi da kuma tafiyar dare da sauransu. Lalle cikin wannan aiki na Ubangiji akwai ayoyi bayyanannu ga mutane masu hankaltar abubuwa yadda suke. Sannan kuma ya ambaci cewa, daga cikin ni’imominsa na bayan ƙasa akwai abubuwan ban mamaki da ya halitta masu launi iri-iri, kamar dabbobi da ma’adanai da tsirrai da duwatsu masu kamanni daban-daban da amfani iri-iri. Lalle cikin wannan aiki na Allah akwai bayyanannun ayoyi ga mutanen da suke wa’azantuwa da gaskiyar da ake faɗa musu, su gode wa Allah ni’imomin nan da ya yi musu. Sai kuma har wa yau, ya ambaci wasu ni’imomin na halitta da ya yi a ruwa. Wato ya hore wa ‘yan’adam ruwan kogi domin samun amfani iri-iri daga cikinsa. Sukan kamo kifi su ci daddaɗan namansa mai taushi, kuma su riƙa fito da kayan ado daga cikinsa waɗanda suke sawa su da matansu, kamar lu’u-lu’u da murjani. Sannan kuma ga jiragen ruwa manya da ƙanana suna keta ruwa ɗauke da mutane kuma maƙare da kaya, amma ba tare da sun nutse ba. To su sani cewa, Allah ya hore musu waɗannan jirage ne domin su yi amfani da su wajen fita neman arziƙi da kasuwanci kuma domin su gode masa bisa ga waɗannan ni’imomin da ya ba su su kuma kaɗaita shi da bauta. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake ambaton wasu ni’imomin nasa ga ‘yan’adam waɗanda ko su kaɗai ma sun isa su tabbatar musu da cikar Ƙudurarsa da cancantar a kaɗaita shi da bauta. Shi ne wanda ya kafa manya-manyan duwatsu a cikin ƙasa domin su hana ta tangal-tangal da su, ya kuma gudanar da ƙoramu a kanta domin su sami ruwan sha da na shayar da dabbobinsu da shuke-shukensu. Ya kuma fitar musu da hanyoyin tafiye-tafiyensu bai rufe su da duwatsu da ƙoramu ko itatuwa ba. Ya yi musu haka ne domin su sami isa duk inda suke son zuwa. Ya kuma ƙara musu da sanya wasu alamomi bayyanannu a kan ƙasa waɗanda za su taimaka musu wajen gane hanya, kamar duwatsu da tuddai da kwari don su taimaka wa matafiyi wajen tantance inda ya dosa. Da daddare kuwa sai ya sanya musu taurari su ne alamomin da za su yi amfani da su wajen gane hanyoyi don kada su ɓace.
أَفَمَن يَخۡلُقُ كَمَن لَّا يَخۡلُقُۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 16:17Yanzu wanda Yake halitta (zai yi) daidai da wanda ba ya halitta? Yanzo ba kwa wazantu ba?
وَإِن تَعُدُّواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ لَا تُحۡصُوهَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 16:18Idan kuma da za ku ƙirga ni’imar Allah to ba za ku iya ƙididdige ta ba. Lalle Allah tabbas Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعۡلِنُونَ
Open ayah 16:19Allah kuma Ya san abin da kuke ɓoyewa da abin da kuke bayyanawa.
وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَخۡلُقُونَ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ
Open ayah 16:20Waɗannan kuma suke bauta wa ba Allah ba, ba sa iya halittar komai, su ne ma ake halittar su.
أَمۡوَٰتٌ غَيۡرُ أَحۡيَآءٖۖ وَمَا يَشۡعُرُونَ أَيَّانَ يُبۡعَثُونَ
Open ayah 16:21Matattu ne su ba rayayyu ba; ba sa kuma sanin sanda za a tashe su.
إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ فَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٞ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ
Open ayah 16:22Abin bautarku Abin bauta ne Ɗaya, sai dai waɗanda ba sa yin imani da ranar lahira zukatansu masu musun hakan ne, kuma su masu girman kai ne.
لَا جَرَمَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡتَكۡبِرِينَ
Open ayah 16:23Ba shakka, lalle Allah Yana sane da abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanawa. Lalle Shi ba Ya son masu girman kai. A waɗannan ayoyi, bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilai masu nuna samuwarsa da cikar ikonsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai saboda ɗimbin ni’imomin da ya saukar wa bayinsa daga sama da waɗanda ya fitar musu daga ƙasa, ayyukan da babu wani daga cikin allolinsu da zai iya yin ɗaya daga cikinsu, sai kuma ya nuna wa mushirikai ɓacin hanyar da suke kai ta bautar wanin Allah wanda ba ya iya halittar komai suna daidaita shi da Allah mahaliccin komai da kowa. Me ya sanya ba su tuna girman Allah su kaɗaita shi da bauta, kada su yarda su haɗa bautarsa da wani wanda ba zai iya halittar komai ba? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa mutane cewa, ni’imominsa da ya yi musu masu yawa ne ainun, ko sun yi ƙoƙarin lissafa su to ba za su iya ƙididdige su ba saboda matuƙar yawansu da rabe-rabensu. To amma duk da haka yana gafarta wa wanda ya yi sakaci wajen godiyar ni’imar da ya yi masa, yana tausaya masa, ya ci gaba da kwararo masa ni’imominsa duk kuwa da rashin cancantarsa ga hakan. Sannan Allah ya bayyana wasu daga cikin siffofinsa maɗaukaka waɗanda in ba shi ba babu wani abin bauta da ya siffanta da su. Ya tabbatar wa bayinsa cewa, ya san abin da suke ɓoyewa na ayyukansu ya kuma san waɗanda suke bayyanawa, zai kuma yi musu sakayya a kansu gaba ɗaya. To amma waɗanda mushirikai suke bauta wa babu abin da suka iya halitta komai ƙanƙantarsa. Hasali ma dai su masu bauta musu ɗin ne suka ƙera su da hannayensu, don haka wane irin rashin hankali ne ya sa suke bauta wa gumakan da su ne suka sassaƙa ko suka gina su da hannayensu? Sannan kuma wani abin lura har ila yau shi ne, waɗannan gumakan wasu daskararrun abubuwa ne marasa rai balle ilimin sanin wani abu na rayuwa; ba su san lokacin da za a tashe su tare da masu bautar su ba, domin a jefa su cikin wutar Jahannama gaba ɗaya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, daga duk bayanan da suka gabata ya tabbata cewa, abin bautarsu guda ɗaya ne ba shi da abokin tarayya, shi ne Allah. To amma waɗanda ba su yi imani akwai lahira ba zukatansu na cike da musunta Kaɗaitakar Allah saboda rashin tsoron Allah da ya cika su, don haka ba su yi imani da akwai wani hisabi ko uƙuba ba, ga su kuma da ɗan karen girman kai wanda ya hana su karɓar gaskiya, ya hana su miƙa wuya. Sai ya ƙara tabbatar musu da cewa, tabbas yana sane da duk ayyukansu da suke ɓoyewa da waɗanda suke bayyanawa, babu abin da bai sani ba, zai kuma yi musu sakayya a kai, sannan su sani cewa, tabbas shi Allah ba ya son duk wani mai girman kai mai ƙin bautarsa ko miƙa wuya ga umarninsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk wani mai girman kai kwatankwacin ƙwayar zarra a zuciyarsa ba zai shiga Aljanna ba.” Wani mutum ya ce: “Ya Manzon Allah, tabbas mutum yana son tufarsa ta zamanto mai kyau, takalminsa mai kyau.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah mai kyau ne yana son kyakkyawa. Girman kai shi ne ƙin gaskiya da wulaƙanta mutane.” [Muslim #91 da Tirmizi #1999]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Za a tashi masu girman kai a tattaro su ranar alƙiyama suna kamar tururuwa a kamannin mutane, saboda ƙanƙantarsu komai ya kere su, a haka za su shiga wani kurkuku a Jahannama mai suna Bulasu, wuta mai tsananin ƙuna za ta baibaye su, za a kuma shayar da su ruwan mugunyar ‘yan wuta.” [Ahmad #6677 da Tirmizi #2492].
وَإِذَا قِيلَ لَهُم مَّاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمۡ قَالُوٓاْ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 16:24Idan kuma aka ce da su: “Me Ubangijinku Ya saukar?” (Sai) su ce: “Tatsuniyoyin mutanen farko.”
لِيَحۡمِلُوٓاْ أَوۡزَارَهُمۡ كَامِلَةٗ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَمِنۡ أَوۡزَارِ ٱلَّذِينَ يُضِلُّونَهُم بِغَيۡرِ عِلۡمٍۗ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ
Open ayah 16:25(Wannan kuwa) don su ɗauki laifukansu cikakku ranar alƙiyama, da kuma laifukan waɗanda suke ɓatarwa ba da ilimi ba. Ku saurara, abin da suke ɗauka ya munana!
قَدۡ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَأَتَى ٱللَّهُ بُنۡيَٰنَهُم مِّنَ ٱلۡقَوَاعِدِ فَخَرَّ عَلَيۡهِمُ ٱلسَّقۡفُ مِن فَوۡقِهِمۡ وَأَتَىٰهُمُ ٱلۡعَذَابُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 16:26Haƙiƙa waɗanda suka gabace su sun shirya makirci, sai Allah Ya tumɓuke gininsu daga harsashi, sai rufin ya rifto a kansu daga samansu, azaba kuma ta zo musu ta inda ba sa tsammani.
ثُمَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يُخۡزِيهِمۡ وَيَقُولُ أَيۡنَ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تُشَٰٓقُّونَ فِيهِمۡۚ قَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ إِنَّ ٱلۡخِزۡيَ ٱلۡيَوۡمَ وَٱلسُّوٓءَ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 16:27Sannan kuma ranar alƙiyama (Allah) zai kunyata su kuma zai ce: “Ina abokan tarayyar nawa da kuka zamanto kuna jayayya a game da su?” (Sai) waɗanda aka bai wa ilimi su ce: “Lalle a yau wulaƙanci da mummunar azaba sun tabbata a kan kafirai.”
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡۖ فَأَلۡقَوُاْ ٱلسَّلَمَ مَا كُنَّا نَعۡمَلُ مِن سُوٓءِۭۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 16:28Waɗanda mala’iku suke karɓar ransu suna masu zaluntar kawunansu; sai suka ba da kai (suna cewa,): “Ba mu kasance muna yin wani mummunan aiki ba.” A’a, ba haka ba ne, lalle Allah Masanin abin da kuka zamanto kuna aikatawa ne.
فَٱدۡخُلُوٓاْ أَبۡوَٰبَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ فَلَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلۡمُتَكَبِّرِينَ
Open ayah 16:29“Sai ku shiga ƙofofin Jahannama kuna masu dawwama a cikinta; lalle makomar masu girman kai ta munana.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda mushirikai masu musunta Kaɗaitakar Allah da ƙaryata ranar lahira suke kuma ƙaryata Annabi (ﷺ) tare da kafirce wa Alƙur’ani, suke mayar da martani duk sanda za a tambaye su mene ne Allah ya saukar wa Muhammadu (ﷺ)? Sai su amsa da cewa, babu abin da Allah ya saukar masa; duk abin da yake karanta musu ƙarairayinsa ne da tatsuniyoyin mutanen da. Don haka suka kafirce masa suka kuma ja mabiyansu zuwa ga kafirci da ƙaryata Annabi (ﷺ). Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon wannan mummunan aiki nasu ranar alƙiyama, da cewa za su zo suna ɗauke da laifuffukansu cikakku a wannan ranar da kuma laifuffukan mutanen da suka ɓatar suka hana su karɓar Musulunci saboda jahilci da makauniyar biyayyar da suka yi musu. Allah kuma ya yi tir da wannan mummunan laifi da suke dakonsa har lahira. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya, to yana da lada kamar na waɗanda suka bi shi, hakan kuma ba zai rage komai daga nasu ladan ba. Wanda kuma ya yi kira zuwa ga ɓata, to yana da zunubi kamar na waɗanda suka bi shi, hakan kuma ba zai rage komai daga nasu zunubban ba.” [Muslim #2674]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wani makirci da kafirai suke ƙulla wa Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa da addininsa a kansu zai ƙare, domin kafirai a gabaninsu sun yi wa manzanni irin waɗannan ƙulle-ƙullen makirci, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tumɓuke ginin makircinsu daga harsashinsa sai rufinsa ya rufta a kansu, sai kuma ga wata azaba Allah ya aiko musu da ita ta inda ba sa tsammani, domin a zatonsu gine-ginensu za su kare su daga azaba, sai ga shi Allah ya hallakar da su gaba ɗaya da waɗannan gine-gine nasu. Wannan azabar duniya ce, amma a lahira kuwa to Allah zai wulaƙanta su ya ƙasƙantar da su, zai tambaye su ina waɗanda suke bauta wa tare da shi waɗanda a dalilin ƙaunarsu ya sa suke gaba da annabawan Allah da muminai: Me ya hana su kawo musu ɗauki su cece su daga azabar Allah? To amma babu wata amsa da za su iya bayarwa a lokacin, sai malamai masana Allah su amsa da cewa,: Lalle kunyata da wulaƙanci da mummunar azaba a ranar nan sun tabbata a kan kafirai. Sai ya bayyana cewa, waɗanda suka cancanci waccan azaba su ne kafirai waɗanda suka kafe a kan kafirci har zuwa lokacin da mala’ikan mutuwa da mala’iku masu dafa masa suka zo karɓar rayukansu suna cikin kafirci dumu-dumu. To a nan ne za su miƙa wuya suna nuna biyayya, su kuma fito fili su ƙaryata kafircin da suka kasance a kai, su nuna su fa ba su taɓa yin wani mummunan aiki ba; suna zaton wannan gardamar za ta yi musu amfani. To a nan ne za a ƙaryata su a tunatar da su cewa, a rayuwarsu ta duniya su masu munanan ayyuka ne, kuma sun manta Allah masanin duk abin da suka riƙa aikatawa ne na kafirci da saɓon Allah, kuma sai ya yi musu sakayya a kansu ɗaya bayan ɗaya. Domin gaɓoɓinsu ne za su bayar da shaida a kan kafircinsu sai kawai a umarce su da shiga wutar Jahannama ta ƙofar da aka tanada domin masu laifi irin nasu, su yi ta zama a cikinta dindindin babu ranar fitowa. Allah kuma ya yi tir da wannan mummunar makomar ta masu girman kai.
۞وَقِيلَ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ مَاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمۡۚ قَالُواْ خَيۡرٗاۗ لِّلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٞۚ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞۚ وَلَنِعۡمَ دَارُ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 16:30Aka kuma ce da waɗanda suka kiyaye dokokin (Allah): “Me Ubangijinku Ya sauƙar?” Suka ce: “Alheri.” Waɗanda suka kyautata a wannan duniya suna da kyakkyawar (rayuwa). Lalle kuma gidan lahira shi ya fi alheri. Madalla da gidan masu taƙawa.
جَنَّٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ لَهُمۡ فِيهَا مَا يَشَآءُونَۚ كَذَٰلِكَ يَجۡزِي ٱللَّهُ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 16:31Aljannatai ne na jin daɗi za su shige su, ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu; suna da duk abin da suka ga dama cikinsu. Kamar haka Allah Yake saka wa masu taƙawa.
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ طَيِّبِينَ يَقُولُونَ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 16:32Waɗanda mala’iku suke ɗaukar ransu suna tsarkaka, suna cewa: “Aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga Aljanna saboda abin da kuka zamanto kuna aikatawa (a duniya). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffar muminai masu tsoron Allah da kiyaye dokokinsa ta hanyar aiki da umarninsa da barin haninsa. Su kam, duk lokacin da aka tambaye su, mene ne Ubangijinsu ya saukar wa Annabinsu, sai su amsa da cewa,: Ya saukar masa da alheri mai girma. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk waɗanda suka kyautata ibadarsu kuma suka kyautata mu’amalarsu da mutane a wannan rayuwar ta duniya, to suna da kyakkyawan sakamako da zai tanadar musu. Zai ba su yalwar arzuki a nan duniya da nasara a kan abokan gabarsu. Sannan abin da ya tanadar musu na kyakkyawan sakamakon lahira ya fi wannan na duniya, domin sakamakonsu a can gidan Aljanna ne wanda ni’imominsa ba sa yankewa. Tabbas wannan gida madalla da shi. Domin Aljanna ce ta zama har abada, za su shige ta, ƙoramu na gudana ta ƙarƙashin manyan gine-ginenta da bishiyoyinta, za su sami duk wani abin da rayukansu suke sha’awa na abinci da abin sha da tufafi da sauran buƙatunsu, an yi musu tanadinsu. Sai ya bayyana cewa, da irin wannan gwaggwaɓan sakamakon ne zai saka wa masu kiyaye dokokinsa, suna aikata abin da ya umarce su suna kuma barin abin da ya hana su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin waɗannan bayi nasa muminai lokacin da mala’ikun mutuwa za su zo karɓar rayukansu suna tsarkaka babu wata shirka a tare da su; zukatansu sun tsarkaka da sanin Allah da ambatonsa; mala’ikun suna yi musu sallama tare da cewa, a yau ba za su haɗu da wata tawaya ba, suna umartarsu da shiga gidan Aljanna saboda ayyukansu a duniya na riƙo da kyakkyawar aƙida da aiki na ƙwarai.
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ أَوۡ يَأۡتِيَ أَمۡرُ رَبِّكَۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ وَمَا ظَلَمَهُمُ ٱللَّهُ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 16:33Shin akwai abin da (mushrikai) suke sauraro in ban da mala’iku su zo musu, ko kuma umarnin Ubangijinka ya zo? Kamar haka waɗanda ke gabaninsu suka aikata. Allah bai zalunce su ba, sai dai kuma kawunansu suka kasance suna zalunta.
فَأَصَابَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 16:34Sai (sakamakon) mummunan abin da suka aikata ya same su, kuma abin da suke yi wa izgili ya rutsa da su. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, shin mushirikai ba za su ji gargaɗin da ake yi musu ba, su bar miyagun ayyukansu da maganganunsu, har sai lokacin da za su ga mala’ikun mutuwa sun zo karɓar rayukansu, su riƙa dukan fuskokinsu da bayansu. Ko kuma lokacin da Allah zai ba da umarnin a hallaka su tun a nan duniya ba tare da wani daga cikinsu ya kai labari ba? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, miyagun ayyukan da mushirikai suke yi ba su ne farau ba; akwai waɗanda suka gabace su sun yi irin waɗannan miyagun ayyuka Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su, kuma idan ya yi musu hakan ba zaluntar su ya yi ba, su ne dai suka zalunci kawunansu da aikata kafirci wanda ya kai su ga halaka. Sai mummunar uƙubar miyagun ayyukansu ta auka musu, kuma azabar da suke yi wa izgili a duk lokacin da aka tsoratar da su da ita sai ga shi ta kewaye su ta ko’ina ba mafita.
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ لَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا عَبَدۡنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَيۡءٖ نَّحۡنُ وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمۡنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَيۡءٖۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ فَهَلۡ عَلَى ٱلرُّسُلِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 16:35Waɗanda kuma suka yi shirka suka ce: “Da Allah Ya ga dama da ba mu bauta wa komai ba sai Shi, daga mu har iyayenmu, da kuma ba mu haramta komai ba wanda bai haramta ba.” Kamar haka waɗanda suka gabace su suka aikata. Shin akwai abin da yake a kan manzanni in ban da isar da aike a fili?
وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَۖ فَمِنۡهُم مَّنۡ هَدَى ٱللَّهُ وَمِنۡهُم مَّنۡ حَقَّتۡ عَلَيۡهِ ٱلضَّلَٰلَةُۚ فَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 16:36Haƙiƙa kuma Mun aiko manzo a kowacce al’umma cewa,: “Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci Ɗagutu.” To akwai daga cikinsu waɗanda Allah Ya shiryar, akwai kuma daga cikinsu wanda ɓata ya tabbata a kansa. To ku yi tafiya a bayan ƙasa ku ga yadda ƙarshen masu ƙaryatawa ya kasance.
إِن تَحۡرِصۡ عَلَىٰ هُدَىٰهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَن يُضِلُّۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّٰصِرِينَ
Open ayah 16:37Idan ma kana kwaɗayin shiriyarsu ne, to lalle Allah fa ba Ya shiryar da wanda Ya ɓatar; ba su da kuma wasu mataimaka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa mana yadda mushirikai suka riƙa yaudarar kawunansu suna kafa wa Allah hujja da ƙaddara a kan shirkar da suke yi, suna nuna cewa, Allah ne ya ga dama su bauta wa wasu gumaka tare da shi, wai domin da bai ga dama ba da ba su yi haka ba, kuma da sun bauta masa shi kaɗai; ba ma su kaɗai ba har ma iyayensu da ba su yi shirka ba, kuma da ba su haramta wa kansu wani abu wanda Allah bai haramta musu ba. To kuwa tun da har sun aikata waɗannan abubuwa, kuma babu wata azaba da Allah ya yi musu, to wannan a ganinsu yana nuna yardarsa da duka abubuwan da suka yi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, wannan hujjar tasu ta banza ce, domin kafiran da suka gabace su ma sun faɗi irin wannan magana, to amma daga ƙarshe Allah ya hallakar da su da azabarsa. Da a ce hujjarsu gaskiya ce to da Allah bai hallaka kafiran farko ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, nauyin da kawai yake kan manzanni shi ne su isar da saƙon da ya aiko su da shi. Idan sun yi haka to babu wata sauran hujja ga wanda saƙonsu ya je masa, sannan manzanni babu ruwansu da wanda zai kafa hujja da ƙaddara a kan wani mummunan aikinsa. Sai kuma ya bayyana cewa, babu wata al’umma a bayan ƙasa sai da ya aika mata da manzo wanda ya umarci al’ummarsa su bauta wa Allah shi kaɗai, su bar bautar gumaka da shaiɗanu, sai ya zamanto a cikin al’ummarsa akwai wanda Allah ya datar da shi ya yi imani da wannan manzon ya bi shi sau-da-ƙafa. A cikinsu kuma akwai wanda ya kafirce ya bijire wa wannan manzo bai samu gam da katar ba, don haka ɓata ya tabbata a kansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni da tafiya a bayan ƙasa, domin kowa ya gane wa idanunsa makomar masu ƙaryata manzannin Allah, ya ga yadda Allah ya saukar musu da azabarsa ta hallaka su baki ɗaya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Annabi (ﷺ) a kan yadda yake ta ƙoƙari yana kuma damuwa matuƙa wajen ya ga mutanensa duk sun shiriya sun karɓi gaskiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa, duk irin ƙoƙarin da zai yi na ya ga sun shiriya, da duk irin hanyoyin da zai bi don ya fahimtar da su gaskiya, to ya sani cewa, wanda Allah bai so shi da shiriya ba ba zai taɓa shiriya ba, saboda ya riga ya yi wa kansa mummunan zaɓi. Sannan kuma ya bayyana masa cewa, waɗannan mutanen masu ƙaryata shi ba su da mai taimaka musu ya kare su daga azabar Allah sa’adda ta zo musu.
وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَا يَبۡعَثُ ٱللَّهُ مَن يَمُوتُۚ بَلَىٰ وَعۡدًا عَلَيۡهِ حَقّٗا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:38Suka kuma rantse da Allah iya rantsuwarsu, (cewa) Allah ba zai tashi wanda ya mutu ba. A’a, ba haka ba ne, alƙawari ne a kansa na gaskiya, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka).
لِيُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِي يَخۡتَلِفُونَ فِيهِ وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰذِبِينَ
Open ayah 16:39(Zai tashe su) don Ya bayyana musu abin da suke saɓani game da shi, don kuma kafirai su san cewa, su sun tabbata maƙaryata.
إِنَّمَا قَوۡلُنَا لِشَيۡءٍ إِذَآ أَرَدۡنَٰهُ أَن نَّقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Open ayah 16:40Abin da kawai Muke cewa da abu idan Mun nufe shi, sai Mu ce da shi: “Kasance”, sai kawai ya kasance. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ruɗani da mushirikai suka riƙa yaɗawa don nuna cewa, ba sa buƙatar aiko musu wani manzo, domin har rantsuwa suke yi iyakar rantsuwarsu cewa, Allah ba zai tashi wani matacce ba, don haka babu batun wani hisabin ayyukansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa, tabbas Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tashe su, domin wannan alƙawari ne na gaskiya da ya ɗaukar wa kansa, shi kuwa ba ya saɓa alƙawari, sai dai yawancin mutane ba su san haka ba, shi ya sa suke ƙaryatawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, sai ya tashe su gaba ɗayansu domin ya bayyana musu gaskiyar abin da suke saɓawa a kansa, watau sha’anin Tauhidi da Alƙur’ani da annabta, kuma kafirai su tabbatar da cewa, su maƙaryata ne game da sanya wa Allah kishiyoyi da suka yi da ƙaryata batun tashin matattu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cikakken ikonsa a kan aikata duk abin da ya ga dama, babu wani abu da zai gagare shi a sama ko a ƙasa. Idan ya yi nufin raya matattu da tashinsu, to babu abin da zai hana shi aiwatar da haka, domin abin da kawai zai ce da wannan abu shi ne ‘samu’ sai nan take wannan abu ya samu.
وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْ لَنُبَوِّئَنَّهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗۖ وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:41Waɗanda kuma suka yi hijira saboda Allah bayan an zalunce su lalle za Mu shirya musu kyakkyawar (rayuwa) a duniya; ladan lahira kuma ya fi girma da a ce sun kasance suna sane da (haka).
ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Open ayah 16:42Waɗanda suka yi haƙuri kuma ga Ubangijinsu kawai suke dogaro. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka yi imani da shi da duka abin da ya aiko Annabinsa da shi, suka kuma yi hijira daga garuruwansu suka bar dukiyoyinsu da iyalansu don Allah, bayan kafirai sun addabe su da zalunci sun hana su bautar Allah; Allah kuma ya yi musu alƙawarin ba su kyakkyawan masauki a nan duniya da za su rayu a cikin izza da ɗaukaka, sannan ya yi musu tanadin wani sakamako na lahira wanda ya fi na nan duniya, watau gidan Aljanna. Sai kuma ya bayyana girman wannan ladan da cewa, da a ce kowa ya san yadda wannan lada yake to da babu wanda zai zauna bai yi hijira ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana siffofin waɗannan masu hijira da cewa, su ne waɗanda suka yi haƙuri a kan cutarwar da mutanensu suka yi musu; suka haƙura suka bar iyalansu da gidajensu da dukiyoyinsu, suka jure wajen bin Allah da Manzonsa, tare da dogara da Allah shi kaɗai cikin dukkan al’amuransu. To wannan ne ya sa Allah ya ba su wannan gwaggwaɓan ladan mai yawa. An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda), ya kasance idan ya ba wa wani muhajiri haƙƙinsa na dukiyar Baitil Mali sai yakan ce: “Karɓi wannan, Allah ya yi maka albarka, shi ne abin da Allah ya yi maka alƙawarinsa a nan duniya, amma abin da ya ajiye maka a lahira ya fi wannan, da a ce sun sani.” [Ibn Jarir, Tafsir , Juzu’i na 17 shafi na 206].
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِمۡۖ فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّكۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:43Ba Mu taɓa aiko (wasu manzanni) ba a gabaninka sai mazaje waɗanda Muke yi wa wahayi. Don haka ku tambayi ma’abota ilimi idan kun kasance ba ku sani ba.
بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِۗ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلذِّكۡرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 16:44(Mun aiko su) da hujjoji bayyanannu da littattafai. Mun kuma saukar maka da Alƙur’ani don ka yi wa mutane bayanin abin da aka saukar musu ko sa yi tunani.
أَفَأَمِنَ ٱلَّذِينَ مَكَرُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَخۡسِفَ ٱللَّهُ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضَ أَوۡ يَأۡتِيَهُمُ ٱلۡعَذَابُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 16:45Yanzu waɗanda suka shirya mummunan makirci ba sa gudun Allah Ya kife ƙasa da su, ko kuma azaba ta zo musu ta inda ba sa zato?
أَوۡ يَأۡخُذَهُمۡ فِي تَقَلُّبِهِمۡ فَمَا هُم بِمُعۡجِزِينَ
Open ayah 16:46Ko kuwa Ya kama su a cikin kai-kawonsu, ba kuwa za su gagara ba?
أَوۡ يَأۡخُذَهُمۡ عَلَىٰ تَخَوُّفٖ فَإِنَّ رَبَّكُمۡ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٌ
Open ayah 16:47Ko kuma Ya kama su a lokacin da suke cike da tsoron (Sa)? To lalle Ubangijinka Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَىٰ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٖ يَتَفَيَّؤُاْ ظِلَٰلُهُۥ عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَٱلشَّمَآئِلِ سُجَّدٗا لِّلَّهِ وَهُمۡ دَٰخِرُونَ
Open ayah 16:48Shin yanzu ba sa ganin abubuwan da Allah Ya halitta kowane iri ne, inuwowinsa suna bazuwa dama da hagu, suna masu sujjada ga Allah suna kuma masu ƙasƙantar da kai?
وَلِلَّهِۤ يَسۡجُدُۤ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن دَآبَّةٖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ
Open ayah 16:49Abin da yake cikin sammai da abin da yake bayan ƙasa na kowace dabba da mala’iku suna yin sujjada ne ga Allah, su kuma ba sa girman kai.
يَخَافُونَ رَبَّهُم مِّن فَوۡقِهِمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ۩
Open ayah 16:50Suna tsoron Ubangijnsu daga samansu kuma suna aikata abin da ake umartar su da shi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata babbar hujja da mushirikai suka riƙe suke ganin babu kamarta don ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) da ƙin yarda da abin da ya zo musu da shi na shiriya. Watau a ganinsu babu yadda za a yi Allah ya aiko musu da mutum irinsu a matsayin manzo. Da a ce da gaske ne Allah zai aiko wani manzo to da sai ya aiko mala’ika ba mutum ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani a kan haka, ya tabbatar wa da Annabi (ﷺ) cewa, bai taɓa aiko da wasu manzanni a gabaninsa ba sai mazaje daga cikin mutane irinsu waɗanda ya riƙa aika musu da wahayi. Don haka bai taɓa aiko da wani mala’ika a matsayin manzo zuwa ga mutane ba. Wannan shi ne aikin Allah a koyaushe. Idan har suna tantama a kan hakan to su tambayi masana abin da littattafan farko suka ƙunsa na ilimi domin su tabbatar musu da gaskiyar wannan batu, idan har su ba su sani ba. Sannan Allah ya bayyana abin da ya aiko waɗannan manzanni da shi, watau ya aiko su da hujjoji bayyanannu da littattafan da ya saukar musu. Kuma ya tabbatar a cikin dukkan waɗannan littattafai ba a taɓa aiko wa mutane wani manzo mala’ika ba. Sai kuma ya tabbatar da cewa, shi ne ya saukar da Alƙur’ani ga Manzon Allah (ﷺ) domin ya zamanto wa’azi da tunatarwa ga mutane, kuma ya ɗora wa Annabi (ﷺ) nauyin yi musu bayani filla-filla na abubuwan da ya ƙunsa masu buƙatar ƙarin bayani, don mutane su yi tunani su fahimci abin da ya zo da shi su wa’azantu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da waɗannan kafirai masu ƙaryata Annabinsa (ﷺ) da nau’o’in azaba iri-iri da za su iya auka musu idan ba su tuba sun daina kafirci ba, sun kuma daina shirya mummunan makirci don su hana bin hanyar Allah. Ya yi musu kashedi da cewa, yanzu ba sa gudun ya kife ƙasa da su irin yadda ya yi wa Ƙaruna a zamanin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ko ya aiko musu da wata azaba ta inda ba sa zato ba sa tsammani, kuma ya sauko musu da ita a lokacin tafiye-tafiyensu na neman abin duniya ba kuma za su gagare shi ba ko su kuɓuce masa. Ko kuma ya kama su da azaba a lokacin da suke cike da tsoron kamunsa? To Allah mai iya azabtar da su ne a kowane hali suke ciki idan ya ga dama. Sai dai ya ƙyale su bai yi musu hakan ba, saboda shi mai tausayi ne mai rahama, yakan jinkirta wa azzalumi amma duk sa’adda ya damƙe shi to ba zai iya kuɓucewa ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman lamarinsa da cikar ikonsa da yadda komai ya rusuna masa ya miƙa wuya gare shi; duk halittu gaba ɗaya na sama da ƙasa da mala’iku da mutum da aljan duk suna ƙarƙashin gudanarwarsa sai yadda ya yi da su; duk wani abu mai inuwa da inuwarsa take bazuwa dama da hauni, watau safe da yamma to inuwar wannan abin ma tana sujjada ne ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Malamai sun ce: Idan rana ta gushe daga tsakiyar sama to komai yana faɗuwa ya yi sujjada ga Allah (Mai tsarki da daukaka), suna masu ƙasƙantar da kai gare shi. Haka kuma duk abin da yake cikin sammai da duk wani abu mai tafiya a bayan ƙasa mutum ne ko dabba, da dukkan mala’iku suna yi wa Allah sujjada shi kaɗai, ba sa girman kai wajen bautarsa, tare da wannan bautar tasu kuma, suna jin tsoron Ubangijinsu wanda yake sama da su da Zatinsa da ikonsa, suna kuma aikata abin da duk aka umarce su da shi.
۞وَقَالَ ٱللَّهُ لَا تَتَّخِذُوٓاْ إِلَٰهَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِۖ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَإِيَّٰيَ فَٱرۡهَبُونِ
Open ayah 16:51Allah kuma Ya ce: “Kada ku riƙi abubuwan bauta guda biyu. Abin bauta Ɗaya Yake Tilo; to sai ku ji tsoro na Ni kaɗai.”
وَلَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَهُ ٱلدِّينُ وَاصِبًاۚ أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ تَتَّقُونَ
Open ayah 16:52Kuma abin da ke sammai da ƙasa nasa ne, kuma gare Shi ake biyayya tutur. Shin yanzu wanin Allah ne kuke yi wa taƙawa?
وَمَا بِكُم مِّن نِّعۡمَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فَإِلَيۡهِ تَجۡـَٔرُونَ
Open ayah 16:53Kuma duk abin da kuke da shi na ni’ima to daga Allah ne; sannan kuma idan cuta ta same ku to wurinsa kuke kai kuka.
ثُمَّ إِذَا كَشَفَ ٱلضُّرَّ عَنكُمۡ إِذَا فَرِيقٞ مِّنكُم بِرَبِّهِمۡ يُشۡرِكُونَ
Open ayah 16:54Sannan kuma lokacin da Ya yaye muku cutar sai a samu wata ƙungiya daga cikinku suna yin shirka da Ubangijinsu.
لِيَكۡفُرُواْ بِمَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡۚ فَتَمَتَّعُواْ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:55Don su butulce wa abin da Muka ba su. To ku ɗan ji daɗi a (duniya), sai dai ba da daɗewa ba za ku sani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da gargaɗin masu haɗa shi da wasu abubuwa wajen bauta, ya yi kira ga ɗaukacin bayinsa da kada su riƙi abubuwan bauta guda biyu, watau kamar majusawa masu cewa wai akwai allan alheri shi ne haske, akwai kuma na sharri shi ne duhu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, shi kaɗai ne abin bauta na gaskiya babu wani na biyunsa, don haka su tsorace shi shi kaɗai kada su ji tsoron waninsa kamar yadda suke jin tsoronsa. Ya kuma bayyana musu cewa, duk abin da yake cikin sammai da wanda yake ƙasa shi ne mahaliccinsa mamallakinsa mai gudanar da lamuransa shi kaɗai ba tare da wani yana taya shi ba. Don haka su gane cewa, shi kaɗai ake yi wa tabbatacciyar biyayya da tsantsanta bauta da ƙasƙantar da kai gare shi a koyaushe. To yanzu bayan duk sun san waɗannan abubuwa, ta yaya za su ci gaba da tsoron wanin Allah har su riƙa bautarsa ba Allah ba? Suna jin tsoron kada ya raba su da wata ni’ima da suke ciki ne? Sai ya tabbatar musu cewa, duk wata ni’ima da mutane suke ciki ta addini ko ta rayuwa, to daga Allah take shi kaɗai babu mai tarayya da shi a kanta. Sannan idan wata cuta ta same su ta rashin lafiya ko talauci duka gare shi kaɗai suke komawa su yi ta roƙon sa domin ya yaye musu, don sun san babu mai yaye wata cuta sai shi. Don haka wanda shi kaɗai ne mai ba su alheri kuma ya yaye musu sharri ashe ba shi kaɗai ya wajaba su bauta wa ba wani ba? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana butulcin kafirai da cewa, idan ya amsa musu addu’o’insu ya yaye musu damuwarsu, to a maimakon su gode masa sai wasu daga cikinsu su koma su ci gaba da shirka, suna bautar waninsa tare da shi. To yanzu wannan wane irin butulci ne?! Don haka Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da su da cewa, su je su ci gaba da more jin daɗin duniya sai dai ba da daɗewa ba za su sani, lokacin da azabar Allah za ta zo musu a lahira ko ma tun a nan duniya.
وَيَجۡعَلُونَ لِمَا لَا يَعۡلَمُونَ نَصِيبٗا مِّمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡۗ تَٱللَّهِ لَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَفۡتَرُونَ
Open ayah 16:56Suna kuma sanya wani kaso daga abin da Muka arzuta su da shi ga abubuwan da ba su san komai ba. Wallahi tabbas za a tambaye ku game da abin da kuka kasance kuna ƙirƙira.
وَيَجۡعَلُونَ لِلَّهِ ٱلۡبَنَٰتِ سُبۡحَٰنَهُۥ وَلَهُم مَّا يَشۡتَهُونَ
Open ayah 16:57Suna kuma jingina wa Allah ‘ya’ya mata, tsarki ya tabbata a gare Shi, su kuma suna da abin da suke sha\'awa (na ‘ya’ya maza).
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِٱلۡأُنثَىٰ ظَلَّ وَجۡهُهُۥ مُسۡوَدّٗا وَهُوَ كَظِيمٞ
Open ayah 16:58Kuma idan aka yi wa ɗayansu albishir da (‘ya) mace sai fuskarsa ta yi baƙi ƙirin yana cike da tsananin baƙin ciki.
يَتَوَٰرَىٰ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ مِن سُوٓءِ مَا بُشِّرَ بِهِۦٓۚ أَيُمۡسِكُهُۥ عَلَىٰ هُونٍ أَمۡ يَدُسُّهُۥ فِي ٱلتُّرَابِۗ أَلَا سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ
Open ayah 16:59Yana ɓuya daga (idon) mutane saboda munin abin da aka yi masa albishir da shi. Shin zai riƙe shi ne a wulaƙance ko kuwa zai binne shi ne a cikin ƙasa? Ku saurara, abin da suke hukuntawa kam ya munana.
لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ مَثَلُ ٱلسَّوۡءِۖ وَلِلَّهِ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 16:60Waɗanda ba sa imani da ranar lahira suna da mummunar siffa. Allah kuwa Yana da maɗaukakiyar siffa. Kuma Shi ne Mabuwayi Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana jahilcin mushirikai da ƙaryar da suke yi wa Allah, suna zaɓar wasu daga cikin dabbobinsu su ce na gumakansu ne tare da sun san cewa, Allah ne ya halicci waɗannan dabbobi ba gumakansu ba, shi ne ya arzuta su da su, amma maimakon su gode masa sai suke amfani da su wajen yi masa shirka, kamar yadda ya bayyana a Suratul An’am , aya ta 136. Allah ya yi rantsuwa da Zatinsa mai tsarki cewa, lalle sai ya tambaye su game da wannan ƙarya da suke ƙagawa, kuma zai yi musu mummunar uƙuba a kai. Sannan kuma Allah ya ci gaba da bayanin wata kwamacala ta mushirikai da baƙin jahilcin rashin sanin girman Allah, shi ne yadda suka riƙa jingina wa Allah ‘ya’ya mata, suna cewa, mala’iku mata ne kuma ‘ya’yan Allah ne. Suna zaɓa wa Allah abin da su ba sa so wa kawunansu, domin suna ƙyamar haihuwar ‘ya mace. Tsarki ya tabbata ga Allah game da abin da suke jingina masa na ‘ya’ya. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana irin mummunan halin da ɗayansu yake samun kansa a ciki duk lokacin da aka yi masa albishir da haihuwar ‘ya mace, yakan zauna cikin matsananciyar damuwa, fuskarsa ta yi murtuk yana cike da jin haushin abin da aka haifa masa. Don jin halin taskun da ya shiga har yakan ɓuyar wa ‘yan’uwansa don kada su gan shi su yi masa dariya na rashin samun ɗa namiji; daga nan ya shiga halin tararrabi yana tunanin yadda zai ɓullo wa lamarinsa, ko dai ya bar wannan jaririya da rai, idan kuwa ya yi haka zai ci gaba da rayuwa cikin wulaƙanci da ƙasƙanci a tsakanin mutanensa, ko kuma ita ta rayu cikin ƙasƙanci da wulaƙanci saboda ita ‘ya mace ce babu mai ƙaunarta balle ya darajta ta. Ko kuma ya binne ta da rai domin ya kuɓutar da kansa daga wulaƙanci da baƙin ciki, ita ma ta kuɓuta daga wulaƙanci da baƙin ciki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da irin wannan ɗanyen hukunci da suke yi na rashin imani da tausayi da rashin tsoron Allah, musamman yadda suke jingina wa Allah abin da su suke ƙyama a jingina musu, sannan su binne abin da suka haifa da rai wai don tana ‘ya mace. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai waɗanda ba su yi imani da ranar lahira ba su ne masu mummunar siffa, don su ne suke da siffar buƙatuwa zuwa ga ‘ya’ya sannan ga kafirci da jahilci tare da su. Amma Allah (Mai tsarki da daukaka) shi mai cikakkun siffofi ne na kamala maɗaukaka da cikakkiyar wadata da ilimi. Shi ne mabuwayi a mulkinsa, babu wanda zai iya rinjayar sa, mai hikima cikin halittarsa da tsarinsa da shari’arsa.
وَلَوۡ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِظُلۡمِهِم مَّا تَرَكَ عَلَيۡهَا مِن دَآبَّةٖ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ لَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ
Open ayah 16:61Da kuwa Allah Yana kama mutane da laifukansu ne to da bai bar wata dabba (mai tafiya) a bayanta ba (wato ƙasa), sai dai kuma Yana saurara musu ne har zuwa wani lokaci ƙayyadajje. To idan ajalinsu ya zo ba za su jinkirta daidai da sa’a guda ba, kuma ba za su gabata ba.
وَيَجۡعَلُونَ لِلَّهِ مَا يَكۡرَهُونَۚ وَتَصِفُ أَلۡسِنَتُهُمُ ٱلۡكَذِبَ أَنَّ لَهُمُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ لَا جَرَمَ أَنَّ لَهُمُ ٱلنَّارَ وَأَنَّهُم مُّفۡرَطُونَ
Open ayah 16:62Suna kuma sanya wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu suna bayanin ƙaryar cewa, suna da mafi kyan sakamako; ba shakka, lalle suna da (sakamakon) wuta, kuma haƙiƙa su waɗanda za a bar su ne (cikinta har abada).
تَٱللَّهِ لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰٓ أُمَمٖ مِّن قَبۡلِكَ فَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ ٱلۡيَوۡمَ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 16:63Wallahi haƙiƙa Mun aiko (manzanni) zuwa ga al\'ummun da suke gabaninka, sai Shaiɗan ya ƙawata musu ayyukansu, kuma shi ne majiɓincin al’amuransu a yau, kuma suna da azaba mai raɗaɗi.
وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّا لِتُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِي ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 16:64Kuma ba Mu saukar maka da Littafi ba sai don ka yi musu bayanin abin da suka yi saɓani game da shi, kuma shiriya ne da rahama ga mutanen da suke yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin yawan rahamarsa da haƙurinsa ga bayinsa masu yawan aikata laifuffuka. Ya nuna cewa, da a ce zai kama mutane da laifuffukansu na zalunci da kafirci to da bai bar wani ɗan’adam ko wata dabba suna tafiya a bayan ƙasa ba, da tuni ya hallaka su gaba ɗaya. To amma yana haƙuri, yana saurara musu zuwa wani lokaci da ya ƙayyade musu, watau ranar alƙiyama, don haka su shiga taitayinsu tun kafin ajalinsu ya zo musu, domin idan har ajalinsu ya zo to ba za a saurara musu ba daidai da sa’a ɗaya, ba kuma za a gabato musu ba ko da ɗan lokaci ne ƙanƙani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wani ɓangare na zaluncinsu, watau jingina wa Allah ‘ya’ya mata da zaluntar su da suke yi idan su sun same su. Ya bayyana cewa, suna jingina wa Allah abin da su ba sa so, sannan kuma harsunansu suna furta wata babbar ƙarya cewa, wai lalle su a ranar alƙiyama suna da sakamako mafi kyau a wurin Allah, watau Aljanna, idan har da gaske ne za a tashe su bayan mutuwa, domin su ba su ma yarda da alƙiyama ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa, tabbas suna da sakamakon wuta a lahira, kuma idan an jefa su cikinta za a ƙyale su ne har abada babu ranar fita. Sai kuma ya lallashi Manzonsa (ﷺ) game da ƙaryata shi da kafirai suke yi, da cewa, ba shi ne farkon manzo da kafirai suka ƙaryata ba, Allah ya rantse masa da Zatinsa cewa, ya aika wa al\'ummun da suka gabata manzanni don su kirawo su zuwa ga Tauhidi, sai Shaiɗan ya ƙawata musu munanan ayyukansu na shirka da kafirci da saɓon Allah, sai suka ƙaryata manzannin da aka aiko musu, suka ci gaba da riƙe abin da suke kai wanda Shaiɗan ya ƙawata musu, don haka ya zama shi ne majiɓincinsu a nan duniya, suka yi masa biyayya sau da ƙafa. To a lahira sai su nemi taimakonsa ya taimaka musu, domin suna da azaba mai raɗaɗi saboda bijire wa Allah da manzanninsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi (ﷺ) dalilin da ya sanya ya saukar masa da Alƙur’ani, wato don ya bayyana wa mutane abin da suka yi saɓani a kansa na Tauhidi da tashin alƙiyama da hukunce-hukuncen shari’a, kuma Alƙur’ani ya zamanto shiriya da rahama ga muminai, domin su ne masu amfanuwa da shi.
وَٱللَّهُ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ
Open ayah 16:65Allah kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya ƙasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke ji.
وَإِنَّ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَنۡعَٰمِ لَعِبۡرَةٗۖ نُّسۡقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهِۦ مِنۢ بَيۡنِ فَرۡثٖ وَدَمٖ لَّبَنًا خَالِصٗا سَآئِغٗا لِّلشَّٰرِبِينَ
Open ayah 16:66Lalle kuma kuna da wata izina a game da dabbobin ni\'ima; Muna shayar da ku da abin da yake cikin cikkunansu (mai fitowa) ta tsakankanin uwar hanji da jinni; nono tatacce mai daɗin kwankwaɗa ga masu sha.
وَمِن ثَمَرَٰتِ ٱلنَّخِيلِ وَٱلۡأَعۡنَٰبِ تَتَّخِذُونَ مِنۡهُ سَكَرٗا وَرِزۡقًا حَسَنًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Open ayah 16:67Daga kuma ‘ya’yan dabinai da na inabai kuna yin giya da shi, da kuma arziki mai kyau. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke hankalta.
وَأَوۡحَىٰ رَبُّكَ إِلَى ٱلنَّحۡلِ أَنِ ٱتَّخِذِي مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا وَمِنَ ٱلشَّجَرِ وَمِمَّا يَعۡرِشُونَ
Open ayah 16:68Ubangijinka kuma Ya kimsa wa ƙudan zuma cewa,: “Ki gina gidaje a duwatsu da kan bishiyoyi da kuma rufin da (mutane) suke yi”
ثُمَّ كُلِي مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ فَٱسۡلُكِي سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلٗاۚ يَخۡرُجُ مِنۢ بُطُونِهَا شَرَابٞ مُّخۡتَلِفٌ أَلۡوَٰنُهُۥ فِيهِ شِفَآءٞ لِّلنَّاسِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 16:69“Sannan kuma ki ci daga kowanne ‘ya’yan itace, kuma ki shiga hanyoyin Ubangijinki horarru (gare ki).” Abin sha mai launi daban-daban yana fitowa daga cikin cikinta; a cikinsa (kuma) da akwai waraka ga mutane. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutane masu tunani. </b>A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ambaton dalilai na tabbatar da Kaɗaitakarsa wajen bauta. Ya bayyana cewa, shi ne ya saukar da ruwan sama, ya raya ƙasa da shi bayan da ta bushe ta ƙeƙashe, ya fitar da tsirrai daga cikinta. Don haka duk wanda ya yi wannan aiki mai iko ne kan ya sake tayar da matattu bayan mutuwarsu. Lalle cikin wannan akwai aya ga mutanen da suke sauraron wa’azi su fahimci dalilin Kaɗaita Allah da bauta da rashin dacewar a bauta wa wani ba shi ba. Sannan ya ambaci wata hujjar ita ma mai nuna cikakkiyar Ƙudirar Ubangiji da dacewar a bauta masa shi kaɗai, ya tabbatar da cewa, game da dabbobin ni’ima, watau raƙuma da shanu da tumaki da awaki, akwai wata ƙaƙƙarfar hujja ga mutane da take ƙara tabbatar musu da Kaɗaitakar Allah da cancantar a bauta masa shi kaɗai da cikar Ƙudurarsa. Waɗannan dabbobi mutane na amfana da su ta hanyoyi daban-daban; su ci namansu su sha nononsu su ɗora wa wasu kaya ko su hau. Ya bayyana cewa, wani ma abin mamakin da ɗan’adam yake gani a kullum wanda kuma yake cike da nuna Ƙudurar Allah shi ne, tacaccen nono da yake fitowa daga waɗannan dabbobi ta tsakanin abin da yake cikin uwar hanji da jinin da ke gudana a jikinsu, sai wannan nonon ya fito tatacce fari ƙal mai daɗin kwankwaɗa ga masu shan sa. Bayan wannan kuma ga wasu hujjojin da ke tattare da tsirrai na ‘ya’yan dabino da inabi wanda Allah ya arzuta mutane da shi, har ma wasu suke yin abin sa maye da shi suna sha, wanda kuwa yin hakan ba abu ne mai kyau ba, sannan kuma suna yin abin arziki mai kyau da shi. Wannan ayar ta sauka kafin a haramta shan giya. Daga baya Allah ya haramta shan duk wani abu mai gusar da hankali kamar yadda ya zo cikin Suratul Ma’ida , aya ta 90-91. Sannan ya bayyana cewa, lalle cikin wannan aiki na Allah akwai aya ga mutane masu hankalta su fahimci cikakken ikon Allah. Sai kuma ya ci gaba da bayyana wata hujjar ita ma mai cike da al’ajabi wadda ta isa ta nuna Kaɗaitakar Allah Ta’ala, ita ce yadda ya kimsa wa ƙudan zuma cewa, su nufi cikin tsaunuka da bishiyoyi su yi gidajensu a can. Hakanan su yi a cikin amyoyi da mutane suke gina masu su rufa masu su. Sannan ya kimsa masu su je su samu ‘ya’yan itatuwa da furanni da suke sha’awa su ci, su bi hanyoyin da Allah ya hore musu bin su har su komo gidansu ba tare da sun yi ɓatan kai ba ko wani ya shiga wanda ba nasa ba. Sannan daga cikin cikinsu ne zuma iri-iri za ta riƙa fita saboda bambancin ganyaye da furanni da suka tsotsa. Allah ya bayyana cewa, a cikin wannan zumar akwai magani ga mutane mai warkar da cututtuka da dama. Wannan lalle babbar hujja ce mai nuna cikakkiyar Ƙudurar Allah da rahamarsa ga bayinsa, amma ba kowa ne yake gane haka ba sai mutane masu tunani. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ɗan’uwana yana fama da gudawa.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce masa: “Je ka ba shi zuma ya sha.” Sai ya je ya ba shi zuma ya sha, amma sai ga shi kuma ya dawo ya ce: “Ya Manzon Allah, na ba shi zuma ya sha, amma gudawarsa ta ƙaru.” Manzon Allah (ﷺ) ya sake ce masa: “Je ka ka ba shi zuma ya sha.” Ya tafi ya ba shi zuma ya sha, sai kuma ga shi ya sake dawowa ya ce: “Ya Manzon Allah, na ba shi ya sha amma kuma gudawarsa ta daɗa ƙaruwa.” Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya yi gaskiya, cikin ɗan’uwanka kuma ya yi ƙarya, ka sake komawa ka shayar da shi zuma.” Ya sake komawa ya ba shi zuma ya sha sai ya warke.” [Bukhari #5684 da Muslim #2217]. Wasu daga cikin masana magunguna sun ce abin da ya faru game da wannan mutum mai gudawa, cikinsa ne ya kume, to da aka ba shi zuma ya sha sai zumar ta sanya cikin ya saki, domin zuma tana da ɗabi’ar zafi, to sai gudawarsa ta ƙaru, to sai ɗan’uwansa ya zaci ko ta cutar da shi ne, alhalin hakan shi ne maslaha ga ɗan’uwansa. Da ya sake shayar da shi a karo na biyu sai cikin ya ƙara saki, sai gudawar ita ma ta ƙaru, to hakanan da ya sake ba shi ya ci gaba da gudawar har sai da duk abincin da ya ci ya ɓata masa cikin nasa har ya kume ya fita daga jikinsa sai ya samu lafiya. An karɓo daga Nana A’isha, Allah ya yarda da ita ta ce: “Manzon Allah (ﷺ) yana sha’awar abu mai zaƙi da kuma zuma.” [Bukhari#5431 da Muslim#1474]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Akwai magani cikin abubuwa uku: Jarfar ƙaho da shan zuma da lalas da wuta, amma ina hana al’ummata yin lalas.” [Bukhari #5680].
وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ ثُمَّ يَتَوَفَّىٰكُمۡۚ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡ لَا يَعۡلَمَ بَعۡدَ عِلۡمٖ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٞ قَدِيرٞ
Open ayah 16:70Kuma Allah ne Ya halicce ku, sannan kuma Shi zai kashe ku. Daga cikinku akwai wanda zai zama tsoho tukuf don kada ya san komai bayan (da can yana da) sani. Lalle Allah Masani ne, Mai iko.
وَٱللَّهُ فَضَّلَ بَعۡضَكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ فِي ٱلرِّزۡقِۚ فَمَا ٱلَّذِينَ فُضِّلُواْ بِرَآدِّي رِزۡقِهِمۡ عَلَىٰ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَهُمۡ فِيهِ سَوَآءٌۚ أَفَبِنِعۡمَةِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ
Open ayah 16:71Allah kuma Ya fifita sashenku a kan wani sashi a arziki. Waɗanda aka fifita ɗin ba za su ba da arzikin nasu ga bayinsu ba don su zama daidai a cikinsa. Shin da ni’imar Allah ne suke jayayya?
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُم بَنِينَ وَحَفَدَةٗ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِۚ أَفَبِٱلۡبَٰطِلِ يُؤۡمِنُونَ وَبِنِعۡمَتِ ٱللَّهِ هُمۡ يَكۡفُرُونَ
Open ayah 16:72Allah kuma Ya sanya muku matan aure daga jinsinku, Ya kuma sanya muku ‘ya’yaye da jikoki daga matayen naku, Ya kuma arzuta ku da abubuwa tsarkaka. Yanzu da ƙarya suke yin imani kuma suke kafirce wa ni’imar Allah? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matakai daban-daban da mutum yakan keto a rayuwarsa da yawan shekarunsa a duniya. Ya bayyana cewa, shi ne ya halicci mutane bayan babu su, sannan idan lokacin mutuwarsu ya zo shi zai karɓi rayukansu. Ya ƙayyade wa kowa ajalinsa. Daga cikin mutane akwai wanda yake yin tsawon rai har ya tsufa tukuf, gaɓoɓinsa su yi rauni hankalinsa ya riƙa ja da baya har ya sake dawowa kamar ƙaramin yaro, ba ya iya fahimtar komai daga irin abubuwan da yake fahimta lokacin ganiyar ƙuruciyarsa da ƙarfinsa, watau ya koma mai yawan mantuwa. Lalle Allah masanin komai ne, shi kuma yake da sanin hikimar yin halittar ɗan’adam a irin waɗannan matakai. Kuma mai iko ne a kan komai babu abin da yake gagarar sa. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana addu’a yana cewa,: “Ya Allah, ina roƙon ka ka tsare ni daga rowa da kasala da tsufa da zama tsoho takwarkwasasshe da azabar ƙabari da fitinar Dujal da fitinar rayuwa da mutuwa.” [Bukhari #4707]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci fifikon arzuka da ke tsakanin mutane wanda shi ma aikinsa ne shi kaɗai, babu mai tarayya da shi a cikinsa. Allah ya halicci mutane, wasu ya ba su arziki mai yawa, wasu talakawa, wasu sarakuna, wasu kuma waɗanda ake mulka ne. Waɗanda Allah ya ba su arziki ba za su yarda su damƙa wannan arzikin ga bayinsu ba su zama sun yi tarayya da su daidai-wa-daida. To idan haka ne me ya sa su kafirai suka yarda su sanya wa Allah kishiyoyi daga cikin bayinsa, amma su ba su amince bayinsu su yi tarayya da su cikin dukiyoyinsu ba? Wane irin zalunci ne wannan? Wanne butulci ne ya kai wannan? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu ni’imomi na musamman da ya yi wa bayinsa saboda biya musu duk buƙatunsu na rayuwa, inda ya ce, ya halitta wa mutane matan aure daga jinsinsu don su sami nutsuwa da su, sannan ya ba su ‘ya’ya da jikoki daga matayen, ya kuma hore musu arzikin abubuwan da za su ci su sha masu daɗi su da iyalansu. To yanzu duk da irin waɗannan ni’imomi masu yawa da ya yi musu sai kuma su butulce masa, su riƙa yin imani da ƙarya, watau gumakansu da cewa suna amfanarwa suna kuma cutarwa, har ma wai za su cece su a wurin Allah? An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A ranar alƙiyama Allah zai goranta wa bawa ya ce masa: ‘Wane, ashe ba ni ne na karrama ka ba, na ba ka shugabanci; na ba ka aure; na hore maka dawakai da raƙuma; na ƙyale ka kana karɓe ɗaya bisa huɗu na dukiyar ganima?’” [Muslim #2968].
وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَمۡلِكُ لَهُمۡ رِزۡقٗا مِّنَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ شَيۡـٔٗا وَلَا يَسۡتَطِيعُونَ
Open ayah 16:73Suna kuma bauta wa wasu ba Allah ba, waɗanda ba sa mallakar musu wani arziki a sammai da ƙasa, ba za kuma su iya ba.
فَلَا تَضۡرِبُواْ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡثَالَۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:74Kada kuma ku sanya wa Allah abokan tarayya. Lalle Allah Yana sane, ku ne ba ku sani ba.
۞ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا عَبۡدٗا مَّمۡلُوكٗا لَّا يَقۡدِرُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَمَن رَّزَقۡنَٰهُ مِنَّا رِزۡقًا حَسَنٗا فَهُوَ يُنفِقُ مِنۡهُ سِرّٗا وَجَهۡرًاۖ هَلۡ يَسۡتَوُۥنَۚ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:75Allah kuma Ya ba da misali da bawan da aka mallaka, ba shi da iko a kan komai, da kuma wanda Muka bai wa arziki nagari daga gare Mu, to shi kuma yana ciyarwa daga shi (arzikin) a ɓoye da kuma sarari; yanzu za su yi daidai? (Ai ba za su yi daidai ba). To godiya ta tabbata ga Allah. A’a, yawancinsu dai ba su san (haka) ba ne.
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا رَّجُلَيۡنِ أَحَدُهُمَآ أَبۡكَمُ لَا يَقۡدِرُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَهُوَ كَلٌّ عَلَىٰ مَوۡلَىٰهُ أَيۡنَمَا يُوَجِّههُّ لَا يَأۡتِ بِخَيۡرٍ هَلۡ يَسۡتَوِي هُوَ وَمَن يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَهُوَ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 16:76Allah kuma Ya ba da wani misali da mutum biyu, ɗayansu bebe ne ba ya iya yin komai, kuma ya zama nauyi a kan mai gidansa, duk inda ya fuskantar da shi ba zai zo da wani alheri ba. Yanzu shi zai yi daidai da wanda yake umarni da adalci kuma yana bisa tafarki madaidaici?
وَلِلَّهِ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَآ أَمۡرُ ٱلسَّاعَةِ إِلَّا كَلَمۡحِ ٱلۡبَصَرِ أَوۡ هُوَ أَقۡرَبُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 16:77Kuma Allah ne Masanin gaibu na sammai da ƙasa. Al’amarin alƙiyama kuma ba komai ba ne face kamar ƙiftawar ido ko kuma ya fi haka kusa. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana ƙarfafan hujjojin da ke nuna ɓacin aƙidar bautar wanin Allah, inda ya ce, mushirikai suna bautar wasu gumaka ba Allah ba, waɗanda ba su mallaki wani arzuki na sama ko na ƙasa ba da za su ba su, kuma ma ba za su iya hakan ba, saboda daskararrun abubuwa ne, sassaƙaƙƙun itatuwa ne ko kwaɓaɓɓiyar laka babu rai tare da su. Don haka ya yi wa mutane kashedi da cewa, su guji danganta Allah da wasu misalai na gumaka waɗanda ba su da ikon amfanarwa ko cutarwa. Allah ba shi da tamka ballantana a haɗa shi da shi wajen bauta. Allah shi ne ya san haƙiƙanin siffofinsa na kamala da isa; su mushirikai ba su san komai ba, shi ya sa suke aukawa cikin shirka suna kwatanta Allah da gumakansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake bayyana wani misali wanda yake ƙara fito da ɓacin aƙidar bautar wanin Allah da wautar da ke tare da masu yinta. Ya ba da misali na wasu mutane su biyu, ɗayansu bawa ne gajiyayye babu abin da yake iya yi da kansa sai abin da aka sa shi; ɗayan kuwa ɗa ne mai cikakken iko, Allah ya wadata shi da dukiya ta halal yana juya ta yadda ya ga dama, yana yi wa mutane kyauta da ita a sarari da ɓoye. Yanzu ta yaya za a daidaita wannan da wancan bawa na farko? Babu shakka ba za su zama ɗaya ba, duk kuwa da kasancewarsu mutane ne. To idan ya kasance su biyun an halicce su ne, amma ba za su daidaita ba, to ta yaya kafirai za su daidaita wani mahaluƙi da Allah mahalicci mai kowa mai komai? Don haka ne Allah ya yi wa kansa kirari da yabo, ya kuma ya tabbatar da cewa, yawancin mushirikai ba su san haƙiƙanin girman Allah ba ne, da a ce sun sani da sun guji yi masa shirka. Sai kuma ya bayar da misali na biyu domin ya ƙara fito musu da lamarin sararai don su fahimta, inda ya kawo musu misalin wasu mutane su biyu, ɗayansu bebe ne ba ya iya magana ba ya jin komai ba ya fahimtar komai, ba zai iya amfanar kansa ba ballantana ya amfanar da wani. Ya zama kaya mai nauyi a wuyan wanda yake ciyar da shi yake ɗaukar nauyin rayuwarsa. Duk inda ya tura shi don ya samo wani alheri ba zai dawo masa da komai ba, haka zai dawo ziƙau kamar yadda ya tafi. Ɗayan kuwa mutum ne lafiyayye, yana ji yana gani yana magana, yana iya amfanar kansa har ma ya amfanar da wasu; ga shi kuma duk maganganunsa da ayyukansa na adalci ne suna kuma kan hanya miƙaƙƙiya. To shin yanzu za su iya daidaita waɗannan mutane guda biyu? To kamar yadda ba za su daidaita ba, hakanan ma duk wanda aka bauta wa ba Allah ba wanda bai san wani abin amfani ga kansa ba, ba zai iya yi wa kansa komai ba sai abin da Allah ya nufe shi da shi, ta yaya zai zama daidai da Allah mai cikakkun siffofi na kamala, mai iko a kan komai, wanda ba ya faɗar wata magana sai gaskiya, ba ya aikata wani aiki sai wanda za a gode masa a kansa? Sannan ya ƙara bayyana siffarsa da cewa, shi ne kaɗai ya san abin da yake ɓoye a sammai da ƙasa, babu kuma wani da yake tarayya da shi a sanin hakan. Daga cikin abubuwan da suke ɓoye babu wanda ya san lokacin zuwansu akwai ranar alƙiyama, wadda al’amarinta a wurinsa duk lokacin da ya nufi zuwanta kamar ƙiftawar ido ne, ko ma ya fi haka kusa, domin da ya umarce ta ta kasance to za ta kasance. Lalle shi mai iko ne a kan komai babu abin da yake buwayarsa.
وَٱللَّهُ أَخۡرَجَكُم مِّنۢ بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ شَيۡـٔٗا وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 16:78Allah ne kuma Ya fito da ku daga cikkunan iyayenku, ba ku san komai ba, Ya kuma sanya muku ji da gani da kuma zukata don ku gode masa.
أَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ مُسَخَّرَٰتٖ فِي جَوِّ ٱلسَّمَآءِ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱللَّهُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 16:79Yanzu ba sa ganin tsuntsaye da aka lamunce wa (tashi) a sararin sama, ba mai riƙe su sai Allah? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da jan hankali a kan a yi la’akari da wasu ayoyi masu nuna cikar ikonsa, da cewa, shi ne ya fito da mutane suna jarirai daga cikkunan iyayensu mata, suka haifo su ba su san komai ba, amma Allah ya samar musu ji da gani ya saka musu zukata, domin su riƙa jin abin da ake faɗa, su ga abubuwa yadda suke, su kuma fahimci yadda ya kamata su rayu, ya yi musu waɗannan ni’imomi ne duka domin su gode masa ta hanyar bin umarninsa da guje wa haninsa da neman yardarsa. Sannan kuma ya ci gaba da jawo hankalin mushirikai masu bautar wasu gumaka ba Allah ba da cewa, su duba su ga tsuntsaye a sama waɗanda aka hore wa tashi cikin iska saboda fiffike da Allah ya ba su, ya kimsa musu yadda za su riƙa rufe su suna buɗewa babu wani abu a sama da yake riƙe da su, kuma babu wani abu a ƙasa da yake ɗauke da su, babu mai riƙe su sai Allah mai cikakken iko. To lalle a cikin wannan aiki na Ubangiji akwai babbar aya ga mutanen da suka yi imani da Allah, domin su ne masu amfanuwa da irin wannan faɗakarwar.
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنۢ بُيُوتِكُمۡ سَكَنٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّن جُلُودِ ٱلۡأَنۡعَٰمِ بُيُوتٗا تَسۡتَخِفُّونَهَا يَوۡمَ ظَعۡنِكُمۡ وَيَوۡمَ إِقَامَتِكُمۡ وَمِنۡ أَصۡوَافِهَا وَأَوۡبَارِهَا وَأَشۡعَارِهَآ أَثَٰثٗا وَمَتَٰعًا إِلَىٰ حِينٖ
Open ayah 16:80Allah ne kuma Ya sanya muku gidajienku wuraren hutawarku, Ya kuma sanya muku gidaje daga fatun dabbobin ni\'ima, kuna ɗaukar su ba nauyi a ranar tafiyarku da ranar saukarku. Daga kuma gashin (tumaki) da gashin raƙuma da gashin (awaki, Ya sanya muku) kayan shimfiɗa da kuma (kayan) jin daɗi zuwa wani ɗan lokaci.
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّمَّا خَلَقَ ظِلَٰلٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡجِبَالِ أَكۡنَٰنٗا وَجَعَلَ لَكُمۡ سَرَٰبِيلَ تَقِيكُمُ ٱلۡحَرَّ وَسَرَٰبِيلَ تَقِيكُم بَأۡسَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ يُتِمُّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُسۡلِمُونَ
Open ayah 16:81Kuma Allah ne Ya sanya muku inuwoyi daga abin da Ya halitta, Ya kuma sanya muku ɗakuna daga duwatsu, Ya kuma sanya muku riguna da suke kare ku daga zafi, da kuma riguna (na sulke) da suke kare ku (daga makamai) a fagen daga. Kamar haka ne Yake cika muku ni’imarsa don ku miƙa wuya.
فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 16:82To idan suka ba da baya, to kai isar da aike a fili ne kawai a kanka.
يَعۡرِفُونَ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكۡثَرُهُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 16:83Suna sane da ni’imar Allah sannan sai su musanta ta, yawancinsu kuwa kafirai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana wasu ni’imominsa ga ‘yan’adam a halin zaman gidansu ko halin tafiye-tafiyensu. Allah ya kimsa musu yadda za su gina gidaje na duwarwatsu ko na tubala a cikin birane domin hutawarsu. Hakanan ya nuna musu yadda za su yi gidaje na tantuna waɗanda ake yin su da fatun dabbobi kamar na raƙuma da shanu da tumaki, suna kuma iya ɗaukar su saboda rashin nauyinsu suna tafiye-tafiye da su, kamar yadda suke amfani da su a ƙauyukansu. Hakanan kuma ya nuna musu yadda za su yi amfani da gashin waɗannan dabbobi wajen saƙa kayan shimfiɗa a gidajensu da tufafin sawa da na lulluɓa, waɗanda suke morar su na ɗan lokaci. Haka kuma yana daga cikin ni’imomin da Allah ya yi wa ‘yan’adam yadda ya samar musu da inuwoyi na bishiyoyi da gine-gine da suke yi, ya samar musu da ɗakuna a jikin duwarwatsu, watau koguna da ke jikinsu suna kare su daga sanyi da iska da ƙura. Kamar yadda ya ni’imta su da samar musu tufafin sawa na auduga da kittani da ulu waɗanda suke kare su daga zafi. Hakanan ya sanya musu wasu rigunan na silke waɗanda suke amfani da su wajen yaƙe-yaƙensu don kare kai daga sara da suka. Sai kuma ya bayyana musu cewa, kamar yadda ya tanadar musu waɗannan ni’imomi da ya ambata, to hakanan zai cika musu sauran ni’imominsa don ko sa miƙa wuya gare shi shi kaɗai su daina bautar wasu ba Allah ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Manzonsa (ﷺ) tabbacin cewa, idan mushirikan nan suka bijire suka ƙi yin imani bayan duk irin waɗannan bayanai filla-filla da aka yi musu da hujjoji ƙarfafa na sarari, to kada ya damu kansa, domin shi babban aikinsa shi ne isar da saƙon Allah a bayyane, amma shiriyarsu a hannun Allah (Mai tsarki da daukaka) take, yana shiryar da wanda ya ga dama daga cikinsu. Sai kuma ya bayyana cewa, su waɗannan mushirikai masu ƙaryata Annabi (ﷺ) da abin da ya zo musu da shi na bautar Allah shi kaɗai suna yin hakan ne domin kawai girman kai da jayayya, don kuwa sun san duk waɗannan ni’imomin Allah ne da ya yi musu, amma suke musantawa, suna jingina wasunsu ga gumakansu, suna ƙaryata manzancin Annabi (ﷺ). Don haka mafi yawancinsu kafirai ne masu musunta ni’imomin Allah.
وَيَوۡمَ نَبۡعَثُ مِن كُلِّ أُمَّةٖ شَهِيدٗا ثُمَّ لَا يُؤۡذَنُ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ وَلَا هُمۡ يُسۡتَعۡتَبُونَ
Open ayah 16:84Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar da mai shaida daga kowacce al’umma, sannan ba za a yi wa waɗanda suka kafirta izini ba, ba kuwa za a karɓi uzurin nasu ba.
وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلۡعَذَابَ فَلَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ
Open ayah 16:85Idan kuma waɗanda suka kafirta suka ga azaba, to ba za a sauƙaƙa musu ba, ba kuma za a saurara musu ba.
وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ شُرَكَآءَهُمۡ قَالُواْ رَبَّنَا هَٰٓؤُلَآءِ شُرَكَآؤُنَا ٱلَّذِينَ كُنَّا نَدۡعُواْ مِن دُونِكَۖ فَأَلۡقَوۡاْ إِلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلَ إِنَّكُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 16:86Idan kuma waɗanda suka yi tarayya (da Allah) suka ga ababen tarayyarsu (sai) su ce: “Ya Ubangijinmu, waɗannan su ne ababen tarayyarmu waɗanda muka zamanto muna bauta wa ba Kai ba.” Sai su jefa musu magana (cewa,): “Ku dai lalle maƙaryata ne!”
وَأَلۡقَوۡاْ إِلَى ٱللَّهِ يَوۡمَئِذٍ ٱلسَّلَمَۖ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 16:87Kuma a wannan ranar suka miƙa wuya ga Allah; kuma duk abin da suka zamanto suna ƙirƙira ya ɓace musu.
ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ زِدۡنَٰهُمۡ عَذَابٗا فَوۡقَ ٱلۡعَذَابِ بِمَا كَانُواْ يُفۡسِدُونَ
Open ayah 16:88Waɗanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, to Mun ƙara musu azaba a kan azabar (da suka cancance ta) saboda ɓarnar da suka zamanto suna yi.
وَيَوۡمَ نَبۡعَثُ فِي كُلِّ أُمَّةٖ شَهِيدًا عَلَيۡهِم مِّنۡ أَنفُسِهِمۡۖ وَجِئۡنَا بِكَ شَهِيدًا عَلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِۚ وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ تِبۡيَٰنٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 16:89Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waɗannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alƙur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulmi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin da mushirikai za su tsinci kansu a ranar alƙiyama, ranar da zai tashi mai shaida daga kowace al’umma, watau manzon da ya aiko musu, domin ya ba da shaida a kan amsawar da suka yi masa, da waɗanda suka yi imani da waɗanda suka ƙi yin imani. Sannan daga lokacin ba za a ba wa kafirai wata damar gabatar da hanzarinsu game da kafircin da suka yi ba, ba kuma za a sake ba su damar komowa duniya ba don su gyara ɓarnarsu. Lahira kuwa ai gida ne na hisabi ba na aiki ba. Haka kuma ya bayyana cewa, azzalumai za su ga azaba ƙarara, yayin da mala’iku za su zo suna janye da wutar Jahannama da linzami dubu saba’in, kowane linzami mala’ika dubu saba’in ne ke janye da shi. To a ranar ba za a taɓa sassauta musu azaba ba, ba kuma za a saurara musu ba; za su shige ta su kuma dawwama a cikinta har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta cewa, a wannan ranar idan mushirkai suka ga abubuwan da suka bauta wa ba Allah ba, sai su yi farat su faɗa wa Allah cewa, ai su ga waɗanda suka riƙa bauta wa a duniya maimakon su bauta masa. Sun faɗi haka ne kuwa domin su ɗora musu alhakin ɓatansu, wai su kuma a kuɓutar da su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa waɗannan abubuwa da suka bauta wa ikon magana sai su mayar musu da martani cewa, lalle su mushirikai ƙarya suke da har suka mayar da su ababen bauta suka haɗa su da Allah suna bauta musu tare da shi, suka musanta cewa, su ba da umarninsu ko yardarsu suka yi shirkarsu ba. To a nan ne fa dole mushirikai suka saduda suka ƙara miƙa wuya ga Allah shi kaɗai, duk kuma ƙagen da suka dinga yi a duniya na cewa, gumakansu za su cece su a wurin Allah a lokacin ya ɓace musu ɓat. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matakan azabar da wasu kafirai za su haɗu da su a lahira. Watau waɗanda suka kafirce suka kuma hana wasu bin tafarkin Allah, to Allah ya yi alƙawarin ƙara musu azaba ninkin-ba-ninkin saboda ɓarnar da suka tafka ta ɓata da ta ɓatarwa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tuna wa Annabi (ﷺ) ranar da zai tayar wa da kowace al’umma da manzonta domin ya ba da shaida a kan abin da suka aikata na imani ko na kafirci. Wannan manzon daga jinsinsu ne kuma yana magana ne da harshensu, don haka ya fi kowa sanin ayyukan al’ummarsa kuma zai fi kowa adalci da tausayi gare su. Ya bayyana wa Annabi cewa, shi ma a ranar zai zo da shi don gabatar da tasa shaidar ga al’ummarsa tare da sauran al\'ummu gaba ɗaya. Ya kuma tabbatar masa da cewa, ya saukar masa da Alƙur’ani ne don bayanin duk wani abu da yake buƙatar bayaninsa wanda ya shafi haram da halal da sakamakon ayyuka na ƙwarai da waɗanda ba na ƙwarai ba. Ya kuma saukar da shi don ya zama shiriya ga mutane zuwa ga gaskiya, ya kuma zama rahama ga duk wanda ya riƙe shi ya yi aiki da shi, kuma albishir ne ga muminai wanɗanda suka ba da gaskiya da Allah game da kyakkyawan sakamako na Aljanna da yake jiran su a lahira.
۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَٱلۡإِحۡسَٰنِ وَإِيتَآيِٕ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَيَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡبَغۡيِۚ يَعِظُكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Open ayah 16:90Lalle Allah Yana umarni da yin adalci da kyautatawa da kuma bai wa makusanta (taimako), Yana kuma hana alfasha da mummunan aiki da zalunci. Yana gargaɗin ku don ku wa’azantu.
وَأَوۡفُواْ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ إِذَا عَٰهَدتُّمۡ وَلَا تَنقُضُواْ ٱلۡأَيۡمَٰنَ بَعۡدَ تَوۡكِيدِهَا وَقَدۡ جَعَلۡتُمُ ٱللَّهَ عَلَيۡكُمۡ كَفِيلًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا تَفۡعَلُونَ
Open ayah 16:91Ku kuma cika alƙawarin Allah idan kuka ɗauki alƙawari, kada kuma ku warware rantsuwa bayan kun ƙarfafa ta, alhali kuwa kun sanya Allah shaida a kanku. Lalle Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa.
وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّتِي نَقَضَتۡ غَزۡلَهَا مِنۢ بَعۡدِ قُوَّةٍ أَنكَٰثٗا تَتَّخِذُونَ أَيۡمَٰنَكُمۡ دَخَلَۢا بَيۡنَكُمۡ أَن تَكُونَ أُمَّةٌ هِيَ أَرۡبَىٰ مِنۡ أُمَّةٍۚ إِنَّمَا يَبۡلُوكُمُ ٱللَّهُ بِهِۦۚ وَلَيُبَيِّنَنَّ لَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 16:92Kada kuma ku zamanto kamar (mace) wadda ta warware kaɗinta wara-wara bayan ƙarfinsa, kuna ɗaukar rantse-rantsenku yaudara a tsakaninku, don ganin kasancewar wata al’umma ta fi wata yawa da ƙarfi. Allah dai Yana jarabtar ku da shi (cika alƙawari) ne. Don kuma a ranar alƙiyama Ya bayyana muku abin da kuka kasance kuna saɓani a game da shi.
وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَلَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 16:93Da kuwa Allah Ya ga dama da Ya sanya ku al’umma ɗaya (masu addini ɗaya), sai dai kuma Yana ɓatar da wanda Ya ga dama Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama. Kuma tabbas za a tambaye ku game da abin da kuka kasance kuna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu dokokinsa ne waɗanda suke ƙunshe da umarni da hani, waɗanda kuma da su ne rayuwar ɗan’adam a bayan ƙasa za ta kyautata. Allah ya umarci bayinsa da tabbatar da adalci, watau bawa ya ba wa Allah haƙƙoƙinsa yadda ya kamata, hakanan ya ba wa ‘yan’uwansa bayi haƙƙoƙinsu daidai ba tare da ya rage musu ba. Idan kuma zai yi hukunci ne a tsakaninsu to ya yi hukunci da adalci da gaskiya ba tare da nuna son zuciya ba. Sannan ya umarce su da kyautatawa, watau bawa ya bayar da abin da bai zama wajibi a kansa ba wajen ciyarwa ko yin afuwa ga wanda ya munana masa. Ya kuma umarce su da taimaka wa dangi makusanta ta hanyar ba su abin da suke buƙata na rayuwa. Ya kuma hana su aikata duk wani aiki mummuna, kamar zina ko wata mummunar magana. Hakanan ya hana su aikata duk wani abu da shari’a ta hana aikata shi na saɓon Allah. Ya hana su zalunci da nuna wa mutane girman kai da ta’addanci a kan rayukansu da dukiyoyinsu da mutuncinsu. Allah ya bayyana musu cewa, waɗannan bayanai da yake yi musu wa’azi ne yake musu domin su wa’azantu su riƙi abin da suka ji da muhimmanci su amfana a rayuwarsu ta duniya su tsira a lahira. Sai kuma ya umarce su da su cika alƙawurran da suka yi tsakaninsu da Allah da waɗanda suka ɗauka tsakaninsu da junansu. Kuma kada su kuskura su warware rantsuwarsu bayan sun ƙarfafe ta da sunan Allah, sun kuma saka Allah tsakaninsu a matsayin shaida a kan alƙawarin da suka yi da juna cewa, za su cika shi; su tuna cewa, lalle Allah yana sane da duk abin da suke aikatawa, babu abin da yake ɓuya a gare shi, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan aikinsa. Ya sake jan kunnensu da kada su mayar da kansu wawaye marasa hankali ta hanyar warware alƙawarin da suka ɗauka. Watau kar su zama kamar wata sakaryar mata wadda take yini tana wahalar tufkar zare, sai maraice ya yi ta zauna ta yi ta warware abin da ta tufka, daga ƙarshe ta tashi fayau ba abin da ta tsinana wa kanta sai ‘yar karen wahala da ta yini tana sha. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya ja kunnensu da cewa, kada su mayar da rantse-rantsensu wata hanya ta yaudara kawai ba gaskiya a cikinta. Wasu su riƙa amfani da wannan rantsuwar ta ƙarya suna yaudarar wasu, don kawai su riƙa rantse wa mutanen da suka kula sun fi su yawa da ƙarfi domin su nutsu da su, amma idan sun sami damar cin amanarsu sai su ci. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, yana ba su wannan umarni ne na cika alƙawari kowane iri ne don ya jarrabe su ya ga ko za su riƙa cikawar ko ba za su cika ba? Kuma don ya bayyana musu abin da suke saɓani a kansa a duniya ta nuna mai gaskiya da marar gaskiya, mai cika alƙawari da mayaudari. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Tabbas duk wani mayaudari (mai warware alƙawari) za a kafa masa tutarsa kusa da shi ranar alƙiyama sai a yi shela cewa,: ‘Wannan ita ce yaudarar da wane ɗan wane ya yi.’ [Bukhari#6177, 6178 da Muslim#1735] Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da ya ga dama da ya mayar da su al’umma ɗaya a kan addini guda na gaskiya babu wani saɓani a tsakaninsu. To amma ba haka hikimarsa ta gudana ba; ya zamanto yana ɓatar da wanda ya ga dama domin shi ya zaɓi ɓatan, ya kuma shiryar da wanda ya ga dama domin shi ya so shiriyar; ya datar da wanda ya ga dama da falalarsa, ya zamanto mai cika alƙawurran da ya ɗauka. Hakanan kuma lalle a ranar alƙiyama tabbas sai ya yi musu tambayoyi ɗaya bayan ɗaya game da abin da suka aikata a nan duniya.
وَلَا تَتَّخِذُوٓاْ أَيۡمَٰنَكُمۡ دَخَلَۢا بَيۡنَكُمۡ فَتَزِلَّ قَدَمُۢ بَعۡدَ ثُبُوتِهَا وَتَذُوقُواْ ٱلسُّوٓءَ بِمَا صَدَدتُّمۡ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَكُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Open ayah 16:94Kuma kada ku ɗauki rantse-rantsenku yaudara a tsakaninku, sai ƙafafuwanku su zame bayan tabbatarsu, kuma ku ɗanɗani azaba saboda toshe hanyar Allah da kuka yi; kuma (a lahira) kuna da azaba mai girma.
وَلَا تَشۡتَرُواْ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلًاۚ إِنَّمَا عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:95Kada kuma ku sayar da alƙawarin Allah da ɗan kuɗi ƙanƙani. Lalle abin da yake wurin Allah shi ya fi muku alheri in kun kasance kun san (haka).
مَا عِندَكُمۡ يَنفَدُ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ بَاقٖۗ وَلَنَجۡزِيَنَّ ٱلَّذِينَ صَبَرُوٓاْ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 16:96Abin da yake wurinku yana ƙarewa; abin da kuwa yake wurin Allah wanzajje ne. Lalle kuwa tabbas za Mu saka wa waɗanda suka yi haƙuri ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa.
مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 16:97Wanda ya yi kyakkyawan aiki namiji ko mace alhali shi yana mumini, to lalle za Mu raya shi rayuwa mai daɗi, kuma za Mu saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da gargaɗi a kan cin amana da warware rantsuwa da mummunan sakamakon mai aikata hakan. Allah ya hani mutane da mayar da rantse-rantsensu wata hanyar yaudarar juna da bin son zuciya, su riƙa rantsuwa suna kuma warware ta duk sanda suka ga dama. Ya bayyana musu cewa, idan sun ci gaba da aikata haka to dugadugansu za su zame daga kan tafarki madaidaici bayan a da suna tsaye a kansu kyam, sannan kuma a lahira za su ɗanɗani azaba sakamakon ɓacewarsu daga kan hanya da ɓatar da wasu da suka yi. Domin Allah zai ninninka musu azaba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana su karɓar ɗan kuɗi kaɗan na rashawa da cin hanci don su warware alƙawarin da aka yi da su su ƙi cikawa. Ya tabbatar musu cewa, abin da yake wurin Allah na sakamako na nan duniya da na lahira ga wanda ya nemi yardar Allah, ya fi alheri a kan abin da za a ba su na tarkacen duniya mai ƙarewa in sun zamanto sun san da haka. Ya tabbatar musu da cewa, duk abin da mutane suke tarawa na dukiyoyi da jin daɗin duniya komai yawansu mai ƙarewa ne wata rana, amma abin da yake wajen Allah na sakamako wanzajje ne. To mene ne ya sa suke fifita abin da yake gushewa a kan abu mai wanzuwa? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, lalle zai saka wa masu haƙurin kiyaye alƙawuransu da rantsuwarsu da kyakkawan sakamako sabado abin da suka zamanto suna aikatawa na ɗa’a gare shi, domin kuwa a kan duk wani aikin kirki ɗaya zai ninka musu shi har goma zuwa ninki ɗari bakwai, har zuwa ninki barkatai ba iyaka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawari ga duk mutumin da ya yi imani ya yi aiki na ƙwarai, namiji ne shi ko mace, to zai ba shi kyakkyawar rayuwa a nan duniya, a lahira kuwa zai saka masa da mafi kyan abin da ya kasance yana aikatawa na kyawawan ayyuka. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya musulunta kuma aka ba shi abin da zai ishe shi rayuwa, Allah ya sa masa dangana da abin da ya ba shi, to lalle wannan ya sami babban rabo.” [Muslim #1054]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ba ya zaluntar mumini daidai da kyakkyawan aiki ɗaya; a sanadiyyarsa Allah zai ba shi a nan duniya, ya kuma saka masa a lahira a kansa. To amma kafiri za a ciyar da shi da kyawawan ayyukansa a nan duniya, idan kuma ya je lahira to ba shi da wani aikin ƙwarai da za a saka masa da alheri a kansa.” [Muslim #2808].
فَإِذَا قَرَأۡتَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ
Open ayah 16:98To idan za ka karanta Alƙur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan korarre (daga rahamar Allah).
إِنَّهُۥ لَيۡسَ لَهُۥ سُلۡطَٰنٌ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Open ayah 16:99Lalle shi (Shaiɗan) ba shi da iko a kan waɗanda suka yi imani kuma suke dogara da Ubangijinsu.
إِنَّمَا سُلۡطَٰنُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يَتَوَلَّوۡنَهُۥ وَٱلَّذِينَ هُم بِهِۦ مُشۡرِكُونَ
Open ayah 16:100Ikonsa kawai yana kan waɗanda suke jiɓintar sa da kuma waɗanda suke yin tarayya da shi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, idan mutum zai fara karatun Alƙur’ani to ya buɗe shi da neman tsarin Allah daga waswasin Shaiɗan wanda Allah ya kore shi daga rahamarsa. Ya bayyana cewa, Shaiɗan ba shi da wani iko a kan waɗanda suka yi imani da Allah, suke kuma dogara da shi a cikin dukkan al’amuransu na yau da kullum. Inda kawai Shaiɗan yake samun ikonsa shi ne a kan mutanen da suka jiɓince shi suka riƙa yi masa biyayya a kan abin da yake ruɗar su da shi, waɗanda har ta kai suna yin shirka da Allah saboda bin ruɗin Shaiɗan gare su.
وَإِذَا بَدَّلۡنَآ ءَايَةٗ مَّكَانَ ءَايَةٖ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يُنَزِّلُ قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مُفۡتَرِۭۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 16:101Idan kuma Muka musanya wata aya a madadin wata ayar, alhali kuwa Allah ne Mafi sanin abin da Yake saukarwa, sai su ce: “Kai dai mai ƙirƙirar ƙarya ne kawai!” A’a, ba haka ba ne, yawancinsu ba su san (komai) ba ne.
قُلۡ نَزَّلَهُۥ رُوحُ ٱلۡقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِٱلۡحَقِّ لِيُثَبِّتَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 16:102Ka ce: “Ruhul Ƙudusi (wato Mala’ika Jibrilu) ne ya saukar da shi daga Ubangijinka da gaskiya don ya tabbatar da waɗanda suka yi imani (a kan dugadugansu), kuma shiriya ne da albishir ga Musulmai.”
وَلَقَدۡ نَعۡلَمُ أَنَّهُمۡ يَقُولُونَ إِنَّمَا يُعَلِّمُهُۥ بَشَرٞۗ لِّسَانُ ٱلَّذِي يُلۡحِدُونَ إِلَيۡهِ أَعۡجَمِيّٞ وَهَٰذَا لِسَانٌ عَرَبِيّٞ مُّبِينٌ
Open ayah 16:103Kuma haƙiƙa Mun san lalle suna cewa,: “Wani mutun ne kawai yake koya masa shi.” Harshen wanda suke karkata zuwa gare shi ajami ne, wannan kuwa harshe ne na Larabci bayyananne.
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ لَا يَهۡدِيهِمُ ٱللَّهُ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Open ayah 16:104Lalle waɗanda ba sa yin imani da ayoyin Allah, to Allah ba zai shirye su ba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi.
إِنَّمَا يَفۡتَرِي ٱلۡكَذِبَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ
Open ayah 16:105Waɗanda ba sa yin imani da ayoyin Allah su ne kawai suke ƙirƙirar ƙarya; kuma waɗannan su ne maƙaryata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakarcin mushirikai da raunin hankalinsu da ƙarancin fahimtarsu, saboda yadda suka nuna wa Manzon Allah (ﷺ) rashin gaskiyarsu a fili, inda ya ce, duk sanda ya shafe wani hukunci na shari’a ya kawo wani sabo a madadinsa, duba da maslaha da buƙata wadda shi ya fi kowa sanin ta game da hukunce-hukuncen da yake saukarwa ga bayinsa, sai kafirai su riƙa cewa, Annabi (ﷺ) ne yake ƙirƙirar ayoyi yana kuma sake canja su duk sanda ya ga dama, watau ba su yarda aikin Allah ne ba. Allah ya mayar musu da martani cewa, yawancinsu ba su san hikimomin da ke ƙunshe cikin canja wasu hukunce-hukunce da waɗansu ba. Ya kuma umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, Mala’ika Jibrilu shi ne ya sauko da Alƙur’ani da gaskiya daga Ubangiji, babu wani kuskure ko jirkitarwa a cikinsa, kuma ba ƙirƙirarsa ba ce. Ya kuma bayyana musu wasu manufofin saukar da Alƙur’ani da canja wasu hukunce-hukuncensa, shi ne domin ya tabbatar da dugadugan waɗanda suka yi imani da shi, su daɗa samun yaƙini duk lokacin da wani hukunci sabo ya sauko ko aka shafe wani hukunci da wani; don haka su tarbiyyantu da ilimominsa su ɗabi’antu da kyawawan halaye da yake koyarwa. Sannan kuma ya zamanto musu shiriya da gaskiya kuma albishir da lada mai yawa ga Musulmi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin irin ƙaryar da mushirikai suka riƙa yi a kan Annabi (ﷺ). Bayan waccan tuhumar da suka yi masa ta cewa, yana yi wa Allah ƙarya, sai kuma suka sake zuwa da wata tuhumar daban wadda take nuna rashin sanin alƙibla da kame-kamen da suke ciki. Sun zargi Annabi (ﷺ) da cewa wai yana koyo Alƙur’ani ne daga wurin wani bawa matashi ba’ajame, watau wanda ba Balarabe ba. Wannan matashi bawa ne na wasu Ƙuraishawa a garin Makka. Ya kasance yana kasuwancinsa na saye da sayarwa a kusa da dutsen Safa, bai ma iya magana da Larabci ba sai ɗan abin da ba a rasa ba na ya amsa tambaya idan an tambaye shi. To Annabi (ﷺ) ya kasance yana zama wurinsa yana taɗi da shi a wani lokaci, sai mushirikai suka riƙa zargin cewa, wai shi ne yake koya wa Manzon Allah (ﷺ) karatun Alƙur’ani da suke ji daga bakinsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani mai sauƙin fahimta, mai kuma nuna sakarcin waɗannan mutane. Allah ya bayyana cewa, shi wannan bawan fa harshensa da yake magana da shi ajamanci ne ba Larabci ba, shi kuma Alƙur’ani ya sauka ne da harshen Larabci mai cike da fasaha bayyananna, wanda kuka ya gagari kowa, to ta yaya wanda bai iya Larabci ba zai iya koyar da wannan Alƙur’ani? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai su ne manyan maƙaryata, domin su ne ba su yi imani da ayoyin Allah ba, don haka ya ƙi yi musu katarin dacewa da shiriya, kuma za su ci gaba da zama a haka matuƙar sun ci gaba da abin da suke aikatawa, kuma suna da azaba mai raɗaɗi a dalilin kafircinsu da ƙaryata ayoyin Allah. Ya sake tabbatar musu da cewa, Annabi (ﷺ) ba maƙaryaci ne ba dangane da abin da ya zo musu da shi daga Allah. Ashararai su ne maƙaryata waɗanda ba su yi imani da ayoyin Allah ba, domin ba sa tsoron azabarsa, ba sa kuma tunanin samun wani lada daga wajensa; to waɗannan su ne tatattun maƙaryata. Amma Manzon Allah (ﷺ) an san shi kyakkyawan sani; ya fi kowa gaskiya a cikin mutanensa kakaf, babu wani mai kokwanto game da haka, har ta kai suna yi masa laƙabi da ‘Al-Amin’, watau mai amana. Don haka lokacin da Hiraƙlu Sarkin Rumawa ya yi wa Abu Sufyan wasu tambayoyi da suka shafi Annabi (ﷺ), daga cikinsu yana cewa,: Shin kun kasance kuna tuhumar sa da ƙarya ne kafin ya fara faɗar maganganun da yanzu yake faɗa? Abu Sufyan ya amsa masa da cewa: A’a. Sai Hiraƙlu ya ce: “Ba za ta taɓa yiwuwa ba bai yi wa mutane ƙarya ba sannan ya zo yana yi wa Allah ƙarya.” [Bukhari #7].
مَن كَفَرَ بِٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ إِيمَٰنِهِۦٓ إِلَّا مَنۡ أُكۡرِهَ وَقَلۡبُهُۥ مُطۡمَئِنُّۢ بِٱلۡإِيمَٰنِ وَلَٰكِن مَّن شَرَحَ بِٱلۡكُفۡرِ صَدۡرٗا فَعَلَيۡهِمۡ غَضَبٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Open ayah 16:106Wanda ya kafirce wa Allah bayan imaninsa, sai dai wanda aka tilasta wa alhali kuwa zuciyarsa ta cika da imani, amma kuma wanda ya buɗe wa kafirci ƙirjinsa, to (waɗannan) fushin Allah ya tabbata a kansu kuma suna da azaba mai girma.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 16:107Wannan kuwa (ya faru) saboda su sun fi son rayuwar duniya a kan ta lahira, kuma lalle Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai.
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَسَمۡعِهِمۡ وَأَبۡصَٰرِهِمۡۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡغَٰفِلُونَ
Open ayah 16:108Waɗannan su ne waɗanda Allah Ya doɗe zukatansu da jinsu da ganinsu, kuma waɗannan su ne gafalallu.
لَا جَرَمَ أَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 16:109Ba shakka lalle su a lahira su ne taɓaɓɓu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin wasu kaso biyu na mutane a Makka dangane da imaninsu da Musuluncinsu: <b>Kaso na farko, </b> su ne waɗanda aka tilasta musu furta kalmar kafirci ko aikata shi bayan imaninsu, amma zukatansu a natse suke da imani da ƙin kafirci. Kamar yadda ya faru ga Ammar ɗan Yasir (Allah ya kara masa yarda) lokacin da mushirikai suka riƙa yi masa azaba a kan sai ya kafirce wa Annabi (ﷺ), har wahala ta kai shi ga furta kalmar da suka nemi ya furta ta kafirci. Daga bisani ya zo ya shaida wa Annabi (ﷺ) abin da ya faru, Manzon Allah ya karɓi hanzarinsa. <b>Kaso na biyu </b>, su ne waɗanda suka kafirta bayan imaninsu tare da jin gamsuwa da kafircin a zuciyarsu, to waɗannan su ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci azaba nau’i shida da ya tanadar musu: (a) Fushin Allah mai tsanani. (b) Azaba mai girma da take jiran su, saboda sun fifita rayuwar duniya a kan ta lahira, sun amince da yarda da mushirikai ko da kuwa za su fusata Ubangijinsu. (c) Allah ba zai shiryar da su ba, don haka sun rasa gamon katari daga Allah. (d) Allah ya doɗe zukatansu, ba za su taɓa fahimtar wa’azi ba, ya doɗe jinsu ba za su taɓa sauraron abin da zai yi musu amfani ba, hakanan ya doɗe ganinsu ba za su taɓa ganin dalilan da za su sa su yi imani ba. (e) Sun tabbata su ne gafalallu da suka rasa fahimtar hanyoyin da za su kai su ga arziki na har abada ko taɓewa ta har abada. (f) Ya tabbata su ne hasararru waɗanda suka yi hasarar kawunansu a duniya da lahira, suka rasa gidan Aljanna yayin da suka saki imaninsu suka riƙi kafirci.
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا فُتِنُواْ ثُمَّ جَٰهَدُواْ وَصَبَرُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 16:110Sannan lalle Ubangjinka (Mai gafara ne da jin ƙai) ga waɗanda suka yi hijira bayan an fitine su, sannan suka yi jihadi suka kuma yi haƙuri, lalle Ubangijinka, bayansu (waɗannan ayyuka) Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
۞يَوۡمَ تَأۡتِي كُلُّ نَفۡسٖ تُجَٰدِلُ عَن نَّفۡسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 16:111Ranar da kowanne rai zai zo yana kare kansa, kuma a cika wa kowanne rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kason mutane masu rauni a Makka waɗanda mushirikai suka fitine su da kafirci, suka matsa musu har suka furta shi ko suka aikata shi, daga bisani suka samu kuɓuta suka yi hijira zuwa Madina, suka bar danginsu da dukiyoyinsu don neman yardar Allah da gafararsa kaɗai. Suka gauraya da sauran ‘yan’uwansu Musulmi suka yaƙi kafirai tare da su, suka kuma jure wajen bin Allah da Manzonsa da guje wa saɓa wa Allah da haƙuri a kan duk wani abin ƙi da zai same su. To Allah ya tabbatar musu da cewa, ya gafarta musu wancan abin da ya faru a baya na bayyana kafirci da suka yi kuma shi mai jin ƙai ne a ranar lahira, ranar da kowane mutum ta kansa yake, ba ya ta iyayensa ko ‘ya’ya ko mata ko wani ɗan’uwa, a ranar kowane rai za a cika masa sakamon ayyukan da ya yi a duniya kyawawa da munana, babu wanda za a rage masa komai a aikinsa mai kyau ko a ƙara masa wani wanda bai yi ba.
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا قَرۡيَةٗ كَانَتۡ ءَامِنَةٗ مُّطۡمَئِنَّةٗ يَأۡتِيهَا رِزۡقُهَا رَغَدٗا مِّن كُلِّ مَكَانٖ فَكَفَرَتۡ بِأَنۡعُمِ ٱللَّهِ فَأَذَٰقَهَا ٱللَّهُ لِبَاسَ ٱلۡجُوعِ وَٱلۡخَوۡفِ بِمَا كَانُواْ يَصۡنَعُونَ
Open ayah 16:112Allah kuma Ya ba da misali da wata alƙarya wadda ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali, arzikinta yana zo mata a yalwace ta kowanne wuri, sai ta kafirce wa ni’imomin Allah, to sai Allah Ya ɗanɗana mata masifar yunwa da tsoro saboda abin da suka kasance suna aikatawa.
وَلَقَدۡ جَآءَهُمۡ رَسُولٞ مِّنۡهُمۡ فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَهُمۡ ظَٰلِمُونَ
Open ayah 16:113Haƙiƙa kuma Manzo ya zo musu daga cikinsu, sai suka ƙaryata shi, to sai azaba ta afka musu alhali suna azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da misali da garin Makka wanda ya kasance cikin aminci da kwanciyar hankali, ga arzikinsu yana zuwa musu ta ko’ina a yalwace, a lokacin da sauran garuruwa maƙota suka rasa duk waɗannan abubuwa. To amma maimakon mutanen Makka su gode wa Allah game da waɗannan ni’imomi da ya yi musu su yi imani da Manzon da Allah ya aiko musu, sai suka kafirce wa ni’imomin Allah, suka ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) wanda shi ne mafi girman ni’imar da Allah ya ba su. A sakamakon haka Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jarrabe su da wata matsananciyar yunwa, fari ya mamaye su har sai da ta kai mutane suna cin kashin raƙuma haɗe da jininsu. Ya kuma jarrabe su da matsanancin tsoro; domin bayan sun kori Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa sun yi hijira zuwa Madina, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafi Manzonsa da muminai suka zama runduna mai ƙarfin gaske; wannan ya jefa kafiran Ƙuraishawa cikin tsoro da fargabar kada Annabi (ﷺ) ya kawo musu hari har gida. Daga ƙarshe Allah ya ba shi nasara ya cinye garin Makka da yaƙi. Allah ya bayyana cewa, ya yi musu wannan jarrabar ce saboda abin da suka riƙa aikatawa na kafirci da butulci ga ni’imar Allah. Sai kuma ya ƙara bayyana halin Ƙuraishawa wanda ya jawo musu musibar da ta same su, ya tabbatar da cewa, ya aiko musu da Manzo, watau Annabi Muhammadu (ﷺ), wanda sun san amanarsa da gaskiyarsa sarai, amma sai suka ƙaryata shi, suka ƙaryata Alƙur’ani da Allah ya saukar masa, don haka azaba ta auka musu ta yunwa da tsoro, kuma su ne suka zalunci kansu, domin su ne suka kai kawunansu wuraren halaka yayin da suka zaɓi su yi wa Allah shirka, su ƙaryata Manzonsa (ﷺ).
فَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَٱشۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ
Open ayah 16:114To ku ci halal mai daɗi daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma ku gode ni’imomin Allah in kun kasance Shi kaɗai kuke bauta wa.
إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 16:115Abin da kawai Ya haramta muku (shi ne) mushe da jini (mai kwarara) da naman alade da kuma abin da aka yanka da (sunan) wanin Allah; amma wanda ya matsu (ya ci) ba yana mai zalunci ko ƙetare iyaka ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
وَلَا تَقُولُواْ لِمَا تَصِفُ أَلۡسِنَتُكُمُ ٱلۡكَذِبَ هَٰذَا حَلَٰلٞ وَهَٰذَا حَرَامٞ لِّتَفۡتَرُواْ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا يُفۡلِحُونَ
Open ayah 16:116Kuma saboda abin da harsunanku suke bayyanawa na ƙarya kada ku riƙa cewa, wannan halal ne, wannan kuma haram ne, don ku yi wa Allah ƙarya. Lalle waɗanda suke ƙirƙira wa Allah ƙarya ba sa rabauta.
مَتَٰعٞ قَلِيلٞ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 16:117(Wannan) jin daɗi ne ƙanƙani (a duniya), kuma suna da azaba mai raɗaɗi.
وَعَلَى ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا مَا قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ مِن قَبۡلُۖ وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 16:118Kuma Mun haramta wa Yahudawa abin da Muka labarta maka tun tuni; ba Mu kuwa zalunce su ba, sai dai kuma kansu suka zalunta.
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٌ
Open ayah 16:119Sannan lalle Ubangijinka (Mai gafara ne) ga waɗanda suka aikata mummuna a cikin jahilci sannan suka tuba bayan haka suka kuma gyara, lalle Ubagijinka Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da cin abubuwan da suke na halal masu daɗi waɗanda Allah ya arzuta su da su, ya kuma umarce su da gode wa ni’imomin da ya yi musu ta hanyar jingina masa su da sarrafa su a inda ya yarda a saka su, domin shi ne kaɗai wanda ya cancanci a bauta masa; idan haka ne kuwa to dole su bi wannan umarni nasa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu abin da ya haramta musu wanda amfani da shi zai cutar da su a rayuwarsu ta duniya da ta lahira da cewa, ya haramta musu cin naman mushe da jinin da ya kwarara lokacin da aka yanka dabba, da naman alade da duk wata dabba da aka yanka ta ba da sunan Allah ba, ko aka yanka ta don neman kusanci ga wanin Allah. To amma wannan hukunci ya danganci lokacin da mutum yake da zaɓi ne, amma idan ya sami kansa a cikin halin larura ya kuma rasa abin da zai ci ya rayu sai ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan, don haka ya ci ba don yana kwaɗayin cin haram ba, to wannan ko ya ci ba shi da laifi. Lalle Allah zai gafarta masa wannan, kuma shi Allah mai tausayi ne gare shi don haka ne ma ya halatta masa cin abin da ya haramta masa saboda halin larura. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar a kan bin tafarki na mushirikai waɗanda suka riƙa haramta cin naman wasu dabbobi ko hawan su ko ɗora musu kaya da ƙaryar cewa, na gumakansu ne ba tare da wata hujja daga Allah ba. Allah ya tsawatar musu da cewa, kada su ci gaba da ƙirƙirar ƙarya da harsunansu suna jingina ta ga Allah, su ce abu kaza halal ne abu kaza haramun ne, don kawai su ƙaga wa Allah ƙaryar cewa, ya haramta abin da bai haramta ba, ko ya halatta abin da bai halatta ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, duk wanda yake ƙirƙira wa Allah ƙarya ba zai taɓa rabauta ba duniya da lahira. A duniya zai ji ɗan daɗi ne kaɗai ba mai ɗorewa ba, a lahira kuwa zai haɗu da azaba ce mai raɗaɗi wadda ba za ta yanke ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta mana horon da ya yi wa Yahudawa, ya tsananta musu hukuncin wasu abubuwa masu daɗi ya haramta musu amfani da su, saboda yawan laifukansu da taurin kansu ga manzanninsu. Allah ya bayyana cewa, ya yi wa Annabi (ﷺ) bayanin waɗannan abubuwa da ya haramta musu. Watau kamar yadda ya zo cikin Suratul An’am , aya ta 146. Allah ya bayyana cewa, bai zalunce su da wannan hukunci da ya yi musu ba, su ne dai suka zalunci kawunansu da yawan saɓa masa da hana mutane bin hanyarsa. Sai kuma ya bayyana rahamarsa da karamcinsa ga masu saɓonsa cikin jahilci idan sun tuba sun koma gare shi sun gyara aikinsu, ya tabbatar musu cewa, zai yi musu gafara zai kuma ji ƙan su.
إِنَّ إِبۡرَٰهِيمَ كَانَ أُمَّةٗ قَانِتٗا لِّلَّهِ حَنِيفٗا وَلَمۡ يَكُ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 16:120Lalle Ibrahimu ya zama abin koyi ne mai biyayya ga Allah mai kauce wa ɓarna, bai kuma zamanto daga masu shirka ba.
شَاكِرٗا لِّأَنۡعُمِهِۚ ٱجۡتَبَىٰهُ وَهَدَىٰهُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 16:121Mai godiya ne ga ni’imarsa (wato Allah), Ya zaɓe shi, Ya kuma shirye shi zuwa ga tafarki madaidaici.
وَءَاتَيۡنَٰهُ فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗۖ وَإِنَّهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 16:122Mun kuma ba shi kyakkyawa a duniya; lalle kuma shi a lahira tabbas yana daga cikin salihai.
ثُمَّ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ أَنِ ٱتَّبِعۡ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 16:123Sannan Muka yi maka wahayi cewa, ka bi addinin Ibrahimu mai kauce wa ɓarna; bai kuwa zamanto daga masu shirka ba.
إِنَّمَا جُعِلَ ٱلسَّبۡتُ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 16:124An farlanta (girmama ranar) Asabar kawai a kan waɗanda suka yi saɓani game da ita. kuma lalle Ubangijinka tabbas zai yi hukunci tsakaninsu ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna saɓani a game da shi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yabon bawansa kuma manzonsa badaɗayinsa Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda shi ne Limamin mabiya miƙaƙƙiyar hanyar Tauhidi kuma Uban annabawa. Larabawan Ƙuraishawa suna riya cewa, su mabiya addininsa ne, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata su, ya kuma nisanta Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga hanyarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabe shi da cewa shi mutum ne da ya tattara kyawawan halaye wanda ake koyi da halayensa, kuma mai dagewa ne a kan ɗa’ar Allah, ya kauce wa dukkan addinai ya rungumi Musulunci kaɗai, kuma bai taɓa zama daga mushirikai ba. Kuma shi mai godiya ne a kan ni’imomin da Ubangijinsa ya yi masa. Allah ya zaɓe shi ya ba shi annabta ya kuma shiryar da shi zuwa madaidaiciyar hanya, ita ce bauta wa Allah shi kaɗai ba tare da shirka ba. Allah kuma ya bayyana cewa, ya ba Annabi Ibrahimu kyakkyawa a nan duniya, watau annabci da kyakkyawan yabo daga al’umma. Sannan kuma a lahira yana cikin mutanen kirki waɗanda Allah ya tanadar musu gidajen Aljanna. Sannan kuma Allah ya bayyana cewa, ya yi wa Annabi (ﷺ) wahayi da cewa, ya bi addinin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya ƙunshi Tauhidi da nesantar mushirikai da kira zuwa ga Allah da aiki da shari’arsa, ya kuma kauce wa duk wasu addinai in ban da addinin Musulunci kaɗai. Kuma ya ƙara tabbatar masa cewa, Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai taɓa kasancewa, ɗaya daga cikin mushirikai ba; shi mutum ne mai kaɗaita Allah da bauta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya soki tafarkin Yahudawa waɗanda suka sassaɓa a cikin lamarin addinin Allah. Haka kuma ya zaɓa wa kowace al’umma rana ɗaya daga cikin kwanakin mako wadda za su riƙa haɗuwa a cikinta suna bauta wa Allah. Ya bayyana cewa, ya wajabta wa Yahudawa girmama ranar Assabar ne bayan ya ba su damar su zaɓi Juma’a, amma sai suka kauce mata suka zaɓi ranar Assabar wadda suka ce ita ce kaɗai ranar da Allah bai halicci wata halitta a cikinta ba bayan ya gama halittu a ranar Juma’a. Daga lokacin da suka yi wannan zaɓin Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wajabta musu yin aiki da shi a cikin shari’ar littafin Attaura na Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya kuma umarce su da su riƙe shi gam-gam, ya yi musu wasiyyar su bi Annabi Muhammadu (ﷺ) lokacin da Allah zai aiko shi, ya yi kuma alƙawari da su a kan haka. Suka ci gaba da riƙe wannan ranar ta Assabar har zuwa lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). An ce shi ne ya canja musu da ranar Lahadi. Wasu kuma sun ce Annabi Isa ya ci gaba da aiki da shari’ar Annabi Musa wadda ba a goge hukuncinta ba har zuwa lokacin da Allah ya ɗauke shi zuwa sama. To amma Nasara sai suka canja ranar zuwa Lahadi a zamanin Sarkin Rumawa Ƙusɗanɗinu domin su saɓa wa Yahudawa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mu ne na ƙarshe amma kuma na farko a ranar alƙiyama, sai dai kawai an riga ba su littafi. Sannan wannan ranar ta Juma’a ita ce ranar da aka farlanta musu sai suka sassaɓa a kanta, sai mu Allah ya nuna mana ita. Mutane duk bayanmu suke bi, Yahudawa gobe (Assabar) Nasara kuwa jibi (Lahadi).” [Bukhari #876 da Muslim #855]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) da Huzaifa (Allah ya kara masa yarda) suka ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya ɓatar da waɗanda suka gabace mu ba su gano Juma’a ba, Yahudawa suka ɗauki ranar Assabar, Nasara kuwa suka ɗauki ranar Lahadi. Sai mu kuma Allah ya kawo mu ya nuna mana ranar Juma’a. Sai ya jera su kamar haka: Juma’a sai Assabar sai Lahadi. To hakanan ma a lahira suna bayanmu, mu ne na ƙarshen zuwa a duniya, amma kuma na farko a ranar alƙiyama. Kuma mu ne za a fara yi wa hukunci a lahira kafin sauran halittu.” [Muslim #853, 856].
ٱدۡعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلۡحِكۡمَةِ وَٱلۡمَوۡعِظَةِ ٱلۡحَسَنَةِۖ وَجَٰدِلۡهُم بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ
Open ayah 16:125Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangiijnka cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu.
وَإِنۡ عَاقَبۡتُمۡ فَعَاقِبُواْ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبۡتُم بِهِۦۖ وَلَئِن صَبَرۡتُمۡ لَهُوَ خَيۡرٞ لِّلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 16:126Idan za ku yi uƙuba to ku yi uƙuba da kwatankwacin abin da aka yi muku uƙuba da shi. Kuma lalle idan kuka yi haƙuri to tabbas shi ne ya fi alheri ga masu haƙuri.
وَٱصۡبِرۡ وَمَا صَبۡرُكَ إِلَّا بِٱللَّهِۚ وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَلَا تَكُ فِي ضَيۡقٖ مِّمَّا يَمۡكُرُونَ
Open ayah 16:127Kuma ka yi haƙuri, ba kuwa za ka iya haƙurin ba sai da taimakon Allah. Kada ranka ya ɓaci a kansu, kada kuma ka zama cikin ƙunci game da makircin da suke ƙullawa.
إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّٱلَّذِينَ هُم مُّحۡسِنُونَ
Open ayah 16:128Lalle Allah Yana tare da waɗanda suka yi taƙawa da kuma waɗanda suke masu kyautatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya kira mutane zuwa ga addinin Musulunci ta hanyar hikima, watau la’akari da yanayin wanda ake kira da fahimtarsa da matsayinsa, ta hanyar kwaɗaitarwa da tsoratarwa. Ya kuma umarce shi da ya yi jayayya da wanda yake buƙatar sai an yi jayayya da shi amma jayayyar ta kasance ta hanyar da ta fi kyau. To amma shiryar da mutane su karɓi gaskiya wannan ba a hannunsa yake ba, shi abin da ya wajaba a kansa kawai shi ne isar da saƙon Allah. Allah shi ne mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Musulunci, shi ne kuma mafi sanin shiryayyu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni da adalci wajen ɗaukar fansa da neman haƙƙi. Allah ya yi umarni ga wanda zai rama wata uƙuba da aka yi masa, da ya rama daidai da irin yadda aka yi masa, kada ya zaƙe ya ƙara a kan abin da aka yi masa. Amma sai ya nuna cewa, mutane su yi haƙuri su yafe wa wanda ya yi musu ba daidai ba ya fi musu alheri a wurin Allah. An karɓo daga Ubayyu ɗan Ka’abu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: A ranar yaƙin Uhudu an kashe Musulmi sittin mutanen Madina, a mutanen Makka da suka yi hijira kuma an kashe mutum shida, sai sahabban Manzon Allah (ﷺ) suka ce, duk sanda muka sake haɗuwa da mushirikai a rana irin wannan, muka kuma yi nasara a kansu, tabbas sai mun yi musu gunduwa-gunduwa. A ranar Fathu Makka sai wani sahabi ya ce: “Daga yau Ƙuraishawa sai labari.” Sai mai shela ya yi shela yana cewa: Manzon Allah (ﷺ) ya amintar da baƙi da fari sai wane da wane - ya faɗi sunayen wasu mutane – to sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar har zuwa ƙarshenta. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Za mu yi haƙuri ba za mu rama ba.” [Ahmad # da Tirmizi #3129]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi haƙuri a kan cutarwar da mushirikai suke yi masa, ya tabbatar masa cewa, babu mai datar da shi ga yin haƙuri sai Allah, don haka kada ya damu da bijirewar da kafirai suke yi masa, kuma kada ya zama cikin ƙunci saboda ƙulle-ƙullen makirci da suke yi, domin Allah ne mai taimakonsa kuma ya ishe shi komai. Ya kuma tabbatar masa da cewa, lalle yana tare da waɗanda suka kiyaye dokokinsa suka guji saɓa masa, da kuma waɗanda suke masu kyautatawa da yin ayyuka na ƙwarai. Allah zai taimaka musu ya ƙarfafe su cikin dukkan lamarinsu.