الإسراء

Al-Israa

The Night Journey · Surah 17 · Ayahs: 111 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِيٓ أَسۡرَىٰ بِعَبۡدِهِۦ لَيۡلٗا مِّنَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ إِلَى ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡأَقۡصَا ٱلَّذِي بَٰرَكۡنَا حَوۡلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنۡ ءَايَٰتِنَآۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

    Open ayah 17:1

    <b>Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai </b> 1. Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi Isra’i da bawansa cikin dare daga Masallaci mai alfarma zuwa Masallaci mafi nisa (na Ƙudus) wanda Muka albarkaci kewayensa, don Mu nuna masa wasu daga ayoyinmu. Lalle Shi Mai ji ne, Mai gani. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da tsarkake kansa daga duk wata tawaya ko gajiyawa don ya nuna komai yana ƙarƙashin ikonsa, babu abin da zai gagare shi. Don haka ya yi bayanin tafiyar dare da ya yi da bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ), watau Isra’i daga Masallaci mai alfarma na Makka zuwa Masallacin Baitul Maƙadis, wanda Allah ya albarkaci duk kewayensa da arzikin kayan marmari iri-iri da shuke-shuke da kayan amfanin gona, wanda yake kuma matattara ce ta annabawa. Allah ya yi masa wannan ne domin ya nuna masa manya-manyan ayoyi da shaidu a kan cikar ikonsa. Lalle kuwa Allah mai jin komai ne kuma mai ganin komai. Hadisai da yawa sun tabbata daga Annabi (ﷺ) a kan bayanin wannan tafiya da aka yi da shi daga Masallacin Ka’aba zuwa Masallacin Ƙudus. Bayanin hadisan a dunƙule shi ne: Wata rana Annabi (ﷺ) yana barci da daddare a ɗakin ‘yar’uwarsa Ummu Hani ‘yar Abu Ɗalib sai Mala’ika Jibrilu ya keto rufin ɗakin ya sauko, ya ɗauke shi zuwa Masallacin Ka’aba; a nan ne kuma ya buɗe ƙirjinsa ya wanke masa shi da ruwan Zamzam ya cika masa shi da hikima da imani, sannan ya rufe shi. Ya ɗauke shi zuwa ƙofar Masallaci inda aka zo da Buraƙa. Wata dabba ce fara, ta fi jaki amma ba ta kai alfadari ba, ya hau kanta, ta tafi da shi har sai da ya zo Masallacin Baitul Maƙadis, ya sauko daga kanta ya ɗaure ta a inda annabawa suke ɗaure dabbobinsu na hawa, sannan ya shiga cikin masallacin ya yi salla raka’a biyu. Sai ya fito, Mala’ika Jibrilu kuma ya kawo masa ƙwaryar giya da ta nono sai ya zaɓi ta nono, sai Jibrilu ya ce: “Ka dace da halitta ta asali, watau fiɗra.” Daga nan Mala’ika Jibrilu ya hau da shi zuwa sama ta farko, inda ya haɗu da Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi masa sallama, shi kuma ya amsa masa ya yi masa maraba da ɗa nagari kuma Annabi nagari. Sai suka wuce sama ta biyu inda kuma ya haɗu da Annabi Yahya da Annabi Isa, waɗanda ‘ya’yan inna suke, su ma ya yi musu sallama suka amsa, suka kuma yi masa barka da ɗan’uwa na ƙwarai kuma Annabi na ƙwarai. Sai suka wuce sama ta uku inda suka haɗu da Annabi Yusuf; shi ma suka gaisa, ya yi masa barka da ɗan’uwa na ƙwarai kuma Annabi na ƙwarai. Daga nan suka wuce sama ta huɗu, a nan suka haɗu da Annabi Idris; shi ma suka gaisa, ya yi wa Annabi (ﷺ) barka da zuwa ya yi masa addu’a ta alheri. Sai kuma suka wuce sama ta biyar inda ya haɗu da Annabi Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ma suka gaisa ya yi masa fatan alheri. Sai kuma suka hau sama ta shida inda suka ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka gaisa da Manzon Allah ya yi masa maraba da ɗan’uwa na ƙwarai kuma Annabi na ƙwarai, ya yi masa fatan alheri. Sai suka hau sama ta bakwai inda suka haɗu da Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), shi ma suka gaisa, ya yi masa barka da zuwan ɗa na ƙwarai kuma Annabi na ƙwarai. Ya samu Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana zaune ya jingina da ɗakin Baitul Ma’amuri. Shi wannan ɗaki ne na ibada wanda a kullum mala’iku dubu saba’in ne suke shigar sa, sannan in sun fito ba za su sake komawa ba har abada sai dai wasu sababbi. Sai kuma daga nan Manzon Allah ya wuce zuwa Magaryar tuƙewa (Sidratul Muntaha ). Ita kuma Bishiya ce wadda faɗin ganyenta kamar kunnuwan giwaye suke, ‘ya’yanta kuwa kamar manyan kuloli ne, idan al’amarin Allah ya lulluɓe ta sai ta canja kamanninta nan take, babu mai iya siffanta kyawunta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana da Annabi (ﷺ), a lokacin ne ya ba shi salloli hamsin shi da al’ummarsa. Daga nan Annabi (ﷺ) ya sauko har ya zo wajen Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai ya tambaye shi abin da Allah ya farlanta wa al’ummarsa, sai ya faɗa masa cewa, Allah ya farlanta musu salloli hamsin a kullum. Sai Annabi Musa ya ba shi shawara cewa, ya koma ya nemi sauƙi wurin Allah, domin shi ma ya gwada al’ummarsa Banu Isra’ila amma sun kasa. Annabi (ﷺ) ya karɓi wannan shawarar ya koma wurin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nemi sauƙi. Allah kuwa ya rage masa salloli biyar. Ya sauko har ya zo ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai ya sake ba shi shawarar ya koma wurin Allah ya nemi sauƙi domin al’ummarsa ba za su iya waɗannan salloli a kullum ba. Annabi (ﷺ) ya yarda ya sake komawa wurin Allah (Mai tsarki da daukaka). Allah ya sake rage masa salloli biyar. Ya sake dawowa wurin Annabi Musa. Haka suka yi ta yi da Annabi Musa har sai da sallolin nan suka koma biyar a kullum. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce wa Annabi (ﷺ): “Ya Muhammadu ga su nan salloli ne biyar a kullum dare da rana; kowace salla ɗaya a matsayin goma take, sun zama salloli hamsin ke nan.” Da Annabi (ﷺ) ya sake dawowa wurin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai ya sake ba shi irin waccan shawara ta baya, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na yi ta komawa wurin Ubangijina har na fara jin kunyarsa.” Daga nan sai Annabi (ﷺ) da Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka sauko zuwa Masallacin Baitul Maƙadis inda ya yi wa annabawa limancin salla. Sannan a ƙarshe ya wayi gari a Makka. Daga lokacin ya fara tunanin idan ya ba da labarin tafiyar nan tasa, to kafirai sun samu abin da za su yi ta yi masa izgili da shi suna ƙaryata shi a gaban jama’a. Farkon wanda ya zo wurin Annabi (ﷺ) a wannan safiya daga cikin mushirikai shi ne Abu Jahali, ya tambaye shi, ko akwai wani sabon labari tare da shi? Annabi ya amsa masa cewa, e, akwai. Ya ce mene ne? Annabi ya kwashe duk labarin tafiyar ya faɗa masa. Abu Jahal cikin izgili ya ce wa Manzon Allah: “Baitul Maƙadis aka je da kai sannan kuma ka wayi gari a tsakaninmu?” Sai ya je ya gayyato wa Annabi jama’a don ya faɗa musu wannan labarin. Da Annabi ya zayyana musu duk abin da ya faru gare shi, sai wasu suka ƙaryata shi saboda nisan da suka sani wurin yana da shi. To sai suka nemi ya kwatanta musu wurin yadda yake don su tabbatar in da gaske yake yi ya je, sai kuwa ya siffanta musu shi sosai kamar yadda suka san shi. [Dubi, Bukhari #3207 da Muslim #164 da Ahmad #2819].

  2. وَءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَٰهُ هُدٗى لِّبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُواْ مِن دُونِي وَكِيلٗا

    Open ayah 17:2

    Kuma Mun bai wa Musa Littafi Muka kuma sanya shi ya zama shiriya ga Banu Isra’ila cewa: “Kada ku riƙi wani wakili ba ni ba.”

  3. ذُرِّيَّةَ مَنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٍۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَبۡدٗا شَكُورٗا

    Open ayah 17:3

    (Ya ku) zurriyar waɗanda Muka ɗauko tare da Nuhu (a cikin jirgi). Lalle shi ya zamanto bawa ne mai yawan godiya.

  4. وَقَضَيۡنَآ إِلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ لَتُفۡسِدُنَّ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَّتَيۡنِ وَلَتَعۡلُنَّ عُلُوّٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 17:4

    Muka kuma ƙaddara ga Banu Isra’ila cikin Littafin (Attaura) cewa: “Lalle tabbas za ku yi ɓarna a bayan ƙasa sau biyu, kuma lalle tabbas za ku yi girman kai mai tsanani.

  5. فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ أُولَىٰهُمَا بَعَثۡنَا عَلَيۡكُمۡ عِبَادٗا لَّنَآ أُوْلِي بَأۡسٖ شَدِيدٖ فَجَاسُواْ خِلَٰلَ ٱلدِّيَارِۚ وَكَانَ وَعۡدٗا مَّفۡعُولٗا

    Open ayah 17:5

    “To idan alƙawarin ta farkonsu (ɓarna) ya zo sai Mu aiko muku da bayinmu masu tsananin ƙarfi sai su kutsa tsakiyar gidajen (naku). Kuma (wannan) ya zamanto alƙawari ne mai faruwa.

  6. ثُمَّ رَدَدۡنَا لَكُمُ ٱلۡكَرَّةَ عَلَيۡهِمۡ وَأَمۡدَدۡنَٰكُم بِأَمۡوَٰلٖ وَبَنِينَ وَجَعَلۡنَٰكُمۡ أَكۡثَرَ نَفِيرًا

    Open ayah 17:6

    “Sannan kuma Muka ba ku damar galaba a kansu, Muka kuma ƙare ku da dukiyoyi da ‘ya’ya, Muka kuma sanya ku kuka zama mafi yawan jama’a.

  7. إِنۡ أَحۡسَنتُمۡ أَحۡسَنتُمۡ لِأَنفُسِكُمۡۖ وَإِنۡ أَسَأۡتُمۡ فَلَهَاۚ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ ٱلۡأٓخِرَةِ لِيَسُـُٔواْ وُجُوهَكُمۡ وَلِيَدۡخُلُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ كَمَا دَخَلُوهُ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَلِيُتَبِّرُواْ مَا عَلَوۡاْ تَتۡبِيرًا

    Open ayah 17:7

    “Idan kun kyautata to kanku kuka kyautata wa, idan kuma kuka munana to kanku kuka yi wa. To idan alƙawarin (ɓarnar) ta ƙarshe ya zo (sai maƙiyanku su zo) don su wulaƙanta ku su kuma shiga masallaci (na Baitul Maƙadis) kamar yadda suka shige shi tun farko, kuma za su yi raga-raga da (duk) abin da suka biyo ta kansa.

  8. عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يَرۡحَمَكُمۡۚ وَإِنۡ عُدتُّمۡ عُدۡنَاۚ وَجَعَلۡنَا جَهَنَّمَ لِلۡكَٰفِرِينَ حَصِيرًا

    Open ayah 17:8

    “Mai yiwuwa ne Ubangijinku ya ji ƙan ku. (Amma) kuma idan kuka dawo (kan ɓarnar sai) Mu dawo (da azabtar da ku). Mun kuma sanya Jahannama ta zama shimfiɗa ga kafirai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin baiwar da ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) gabanin Annabi (ﷺ). Allah ya ba shi littafin Attaura wanda ya zamanto a lokacinsa mai shiryar da Banu Isra’ila, yana fitar da su daga duhun kafirci zuwa ga hasken imani. A cikinsa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗe su da kada su riƙi wani abin dogaro wanda za su riƙa mayar da al’amuransu gare shi ban da Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da su cewa, su ne fa zurriyar waɗanda ya kuɓutar a jirgin ruwa tare da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da Ɗufana ya cinye duniya. Don haka ya dace su tuna da wannan ni’imar da ya yi musu, su gode masa ta hanyar bauta masa shi kaɗai da bin umarninsa. Sannan ya umarce su da su yi koyi da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wajen godiya ga Allah, domin shi Nuhu bawa ne na Allah mai yawan godiya gare shi. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah yana yarda da bawan da, idan ya ci abinci ko ya sha ruwa sai ya gode wa Allah ya yabe shi a kan haka.” [Muslim #2734 da Ahmad #11973]. Ya zo a cikin wani dogon hadisin ceto wanda Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito cewa: Annabi (ﷺ) ya ce: “…Mutane za su zo neman ceto wajen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) su ce: “Ya Nuhu, tabbas kai ne farkon manzanni zuwa mutanen duniya, kuma Allah ya sa maka sunan bawa mai godiya.” [Bukhari #4712]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin cewa, Banu Isra’ila ba su yi aiki da nasihar da aka yi musu ba a cikin Attaura. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da su cewa, lalle tabbas za su yi ɓarna a bayan ƙasa har sau biyu, kuma lalle za su yi girman kai matuƙa da gaske wanda zai jefa su cikin zalunci da ta’addanci ga mutane. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan suka yi ɓarna ta farko to zai kawo wasu bayinsa masu tsananin ƙarfi ya ɗora su a kansu su yi ta karkashe su suna tarwatsa su, su kuma yi ta karakaina a tsakiyar gidajensu suna ɓata duk wani abu da suka biyo ta kansa. Allah ya tabbatar musu cewa, wannan alƙawari da ya yi tabbas sai ya faru gare su babu makawa. Sai kuma ya faɗa musu cewa ya dawo musu da daularsu da ƙarfinsu har suka samu yin galaba a kan waɗancan maƙiyan nasu yayin da suka tuba suka koma ga Allah. Ya kuma ƙara musu yawan dukiyoyi bayan an wawashe musu tasu a baya, ya ƙara musu yawan ‘ya’ya bayan an kwashe musu ‘ya’yansu, wasu kuma an mayar da su bayi, ya ba su yawan adadin da ya fi na maƙiyansu. Sannan ya gargaɗe su da cewa, idan sun kyautata sun bi Allah kansu suka yi wa. Idan kuma sun munana sun ɓata ayyukansu to don kansu, ba za su cuci Allah da komai ba. Ya tabbatar musu cewa, idan suka sake yin wata ɓarna a karo na biyu, to zai sake ɗora maƙiyansu a kansu don su sake dawowa cikinsu su wulaƙanta su wulaƙancin da sai ya bayyana a fili a fuskar kowa daga cikinsu, har ma kuma su shiga Baitul Maƙadis su rushe shi kamar yadda suka shige shi a baya suka kuma rushe shi, kuma duk wani gari da suka yi galaba a kan mutanensa za su rushe shi kakaf. Duk da haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna tausayinsa gare su, ya tabbatar musu da cewa, idan sun tuba, to zai ji ƙan su ya tausaya musu. To amma fa idan suka sake komawa ga ɓarna a karo na uku ko fiye da haka, to shi kuwa zai sake dawo musu da uƙubarsa, kuma a lahira ya sanya Jahannama ce makomar kafirai, da ita za a yi musu shimfiɗa.

  9. إِنَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ يَهۡدِي لِلَّتِي هِيَ أَقۡوَمُ وَيُبَشِّرُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 17:9

    Lalle wannan Alƙur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miƙewa, yana kuma yi wa muminai waɗanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma.

  10. وَأَنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا 

    Open ayah 17:10

    Waɗanda kuwa ba su yi imani da ranar lahira ba lalle Mun tanadar musu azaba mai raɗaɗi.

  11. وَيَدۡعُ ٱلۡإِنسَٰنُ بِٱلشَّرِّ دُعَآءَهُۥ بِٱلۡخَيۡرِۖ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ عَجُولٗا

    Open ayah 17:11

    Kuma mutum yakan roƙi sharri kamar yadda yake roƙon alheri; mutum kuwa ya zamanto mai gaggawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalar Alƙur’ani, inda ya ce lalle wannan Alƙur’ani da ya saukar wa Annabinsa Muhammadu (ﷺ) yana nuna wa mutane hanyar da ta fi kowace hanya kyau, ita ce hanyar addinin Musulunci da shari’arsa da koyarwarsa. Yana kuma yin albishir ga muminai waɗanda suka yi kyawawan ayyuka a duniya cewa, suna da wani gagarumin lada daga Allah a lahira. Sannan kuma ya ja kunnen waɗanda ba su yi imani da ranar alƙiyama ba cewa, ya yi musu tanadin mummunar azaba mai raɗaɗi a lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani hali na ɗan’adam wanda yake nuna jahilcinsa da garajensa, da cewa, shi ɗan’adam wani lokaci idan ya yi fushi yakan yi wa kansa ko ‘ya’yansa ko dukiyarsa mummunar addu’a kamar yadda yake yin addu’a ta alheri ga kansa. Da kuwa a ce Allah zai amsa masa addu’arsa ne to da ya hallaka shi ko ya hallakar da dukiyarsa da ‘ya’yansa. Allah ya tabbatar da cewa, shi ɗan’adam mutum ne mai gaggawa sosai. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku yi wa kawunanku mummunar addu’a ko ku yi wa ‘ya’yanku ko ku yi wa hadimanku ko dukiyoyinku, don kada ku yi dace da lokacin da Allah yake baiwarsa ya amsa muku addu’arku.” [Muslim #3009 da Abu Dawud #1532].

  12. وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ ءَايَتَيۡنِۖ فَمَحَوۡنَآ ءَايَةَ ٱلَّيۡلِ وَجَعَلۡنَآ ءَايَةَ ٱلنَّهَارِ مُبۡصِرَةٗ لِّتَبۡتَغُواْ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكُمۡ وَلِتَعۡلَمُواْ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلۡحِسَابَۚ وَكُلَّ شَيۡءٖ فَصَّلۡنَٰهُ تَفۡصِيلٗا

    Open ayah 17:12

    Muka kuma sanya dare da rana su zama ayoyi guda biyu; sai Muka shafe ayar dare (ta zama duhu) Muka kuma sanya ayar rana ta zama mai haskakawa, don ku nemi falala daga Ubangijinku, don kuma ku san yawan shekaru da lissafi. Kowane abu kuwa Mun rarrabe shi filla-filla. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata babbar ni’ima da ya yi wa ɗan’adam kuma wadda take ƙunshe da wasu ayoyi masu nuna Kaɗaitakarsa da cikar Ƙudurarsa. Wannan ni’imar kuwa ita ce jujjuyawar dare da rana da sassaɓawarsu wajen tsawo da gajarta da sanyi da zafi. Ya yi dare mai duhu don ɗan’adam ya huta a cikinsa ya yi barci. Ya kuma sanya rana mai haske domin mutane su fita neman arzikinsu a ciki. Sannan kuma ta hanyar sassaɓawarsu ne mutane za su fahimci lissafin kwanaki da makwanni da watanni da shekaru da lokutan ibadunsu da wa’adin ƙulla mu’amalolinsu da juna. Allah ya bayyana cewa, ya yi bayanin komai filla-filla domin ya tantance mai gaskiya da marar gaskiya ya kuma ware ƙarya da gaskiya.

  13. وَكُلَّ إِنسَٰنٍ أَلۡزَمۡنَٰهُ طَٰٓئِرَهُۥ فِي عُنُقِهِۦۖ وَنُخۡرِجُ لَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ كِتَٰبٗا يَلۡقَىٰهُ مَنشُورًا

    Open ayah 17:13

    Kuma kowane mutum Mun ɗaura masa littafin aikinsa a wuyansa, za kuma Mu fito masa da wani littafi a ranar alƙiyama da zai same shi a buɗe.

  14. ٱقۡرَأۡ كِتَٰبَكَ كَفَىٰ بِنَفۡسِكَ ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكَ حَسِيبٗا

    Open ayah 17:14

    (A ce da shi): “Karanta littafinka; a yau ka isa ka yi wa kanka hukunci da kanka.”

  15. مَّنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۗ وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّىٰ نَبۡعَثَ رَسُولٗا

    Open ayah 17:15

    Wanda ya shiriya to lalle yana shiriya ne don kansa; wanda kuwa ya ɓata to lalle yana ɓata ne don kansa. Ba kuwa wanda zai ɗauki nauyin laifin wani. Kuma ba Mu zamanto Masu azabtarwa ba har sai Mun aiko da manzo.

  16. وَإِذَآ أَرَدۡنَآ أَن نُّهۡلِكَ قَرۡيَةً أَمَرۡنَا مُتۡرَفِيهَا فَفَسَقُواْ فِيهَا فَحَقَّ عَلَيۡهَا ٱلۡقَوۡلُ فَدَمَّرۡنَٰهَا تَدۡمِيرٗا

    Open ayah 17:16

    Idan Muka nufi hallakar da wata alƙarya sai Mu sanya ‘yan ta-moren cikinta su aikata fasiƙanci a cikinta, sai kalmar azaba ta tabbata a kanta (watau alƙaryar) sai Mu rugurguza ta ragaraga.

  17. وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِنۢ بَعۡدِ نُوحٖۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

    Open ayah 17:17

    Al’umma nawa ne Muka hallaka bayan Nuhu? Kuma ai ya isa Ubangijinka Ya zamana Mai cikakken sani ne da gani ga zunuban bayinsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, aikin da duk wani ɗan’adam ya yi a nan duniya yana nan an kiyaye masa shi a littafin ayyukansa wanda mala’iku suke rubutawa da umarnin Allah, alheri ne ko sharri, sannan zai zo da shi rataye a wuyansa a ranar alƙiyama ba zai rabu da shi ba har sai an gama yi masa hisabi. Allah ya tabbatar masa cewa, zai fito masa da wannan littafi mai ƙunshe da duk ayyukansa kyawawa da munana a buɗe masa shi, kuma a umarce shi da ya karanta duk abin da yake ciki da kansa ya yi wa kansa hisabi a ranar. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa, shiriyar kowa da ɓatansa shi kaɗai ta shafa ba wani ba, don babu mai ɗaukar zunuban wani ko ya kawar masa su gwargwadon ƙwayar zarra, domin Allah cikakken adali ne babu wanda yake kamawa da laifi ya yi masa azaba sai bayan ya tsayar masa da hujja ta bakin manzanninsa sannan ya yi jayayya ya ƙaryata su. Amma idan ya miƙa wuya ya yi imani, ko hujjar ba ta je masa ba, to wannan Allah ba ya azabta shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilan da suke sa ya hallakar da wata al’umma ya gusar da ita daga bayan ƙasa, da cewa, duk lokacin da ya nufi hallakar da wata alƙarya saboda zaluncinsu sai ya ƙaddara wa ‘yan ta-moren cikinta su saɓa wa umarninsa su keta dokokinsa, daga nan sai azabar Allah ta tabbata a kan wannan alƙarya, Allah ya rugurguza ta ragaraga. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, irin waɗannan al\'ummun da ya yi wa irin wannan azabar masu yawa ne, kuma duk ya hallaka su, watau kamar mutanen Annabi Nuhu da Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da sauransu; ya hallakar da su ne saboda kafircinsu da zaluncinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa cewa, ya isa ya zamanto mai cikakken sani ne da ganin zunubban da bayinsa suke aikatawa, zai kuma yi musu sakayya a kai.

  18. مَّن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعَاجِلَةَ عَجَّلۡنَا لَهُۥ فِيهَا مَا نَشَآءُ لِمَن نُّرِيدُ ثُمَّ جَعَلۡنَا لَهُۥ جَهَنَّمَ يَصۡلَىٰهَا مَذۡمُومٗا مَّدۡحُورٗا

    Open ayah 17:18

    Wanda ya kasance yana nufin duniya ne (kawai) to za Mu gaggauto masa a cikinta abin da Muka ga dama ga wanda Muka yi nufi; sannan Mu sanya masa Jahannama, ya shige ta (a lahira) yana abin zargi, korarre (daga rahamar Allah).

  19. وَمَنۡ أَرَادَ ٱلۡأٓخِرَةَ وَسَعَىٰ لَهَا سَعۡيَهَا وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ كَانَ سَعۡيُهُم مَّشۡكُورٗا

    Open ayah 17:19

    Wanda kuma ya nufi lahira ya kuma yi aiki irin nata dominta alhalin yana mumini, to waɗannan aikinsu ya zamanto abin godewa ne (a wurin Allah).

  20. كُلّٗا نُّمِدُّ هَٰٓؤُلَآءِ وَهَٰٓؤُلَآءِ مِنۡ عَطَآءِ رَبِّكَۚ وَمَا كَانَ عَطَآءُ رَبِّكَ مَحۡظُورًا 

    Open ayah 17:20

    Dukkansu Muna wadata su ne da baiwar Ubangijinka; waɗannan da kuma waɗancan. Baiwar Ubangijinka kuwa ba ta zamo abar hanawa ba.

  21. ٱنظُرۡ كَيۡفَ فَضَّلۡنَا بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ وَلَلۡأٓخِرَةُ أَكۡبَرُ دَرَجَٰتٖ وَأَكۡبَرُ تَفۡضِيلٗا

    Open ayah 17:21

    Dubi yadda Muka fifita wasunsu a kan wasu. Lalle kuwa lahira ita ta fi girman darajoji, kuma ta fi girman fifiko. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mutane sun kasu gida biyu: <b>Kashi na farko </b>, su ne masu neman duniya da jin daɗinta mai gushewa, suka kuma yi ta aiki tuƙuru domin samun biyan buƙatarsu suka manta da farkonsu da ƙarshensu. To waɗannan Allah yana gaggauto musu da buƙatunsu na duniya gwargwadon yadda ya ga dama, kuma ga wanda ya riga ya rubuta wa hakan tun a Lauhul Mahfuzi. To amma fa wannan ɗan jin daɗi ne ƙanƙani, sannan a lahira Allah ya jefa shi wutar Jahannama yana abin zargi kuma korarre daga rahamar Allah, saboda ya zaɓi duniya ya kafirce wa Allah. <b>Kashi na biyu </b>, su ne waɗanda lahira ce kawai a gabansu suka kuma yi aiki tuƙuru don samun sakamakonta, alhalin sun yi imani da shi. To waɗannan su ne aikinsu yake abin godewa a wurin Allah, zai karɓe shi ya taskace musu ladansa a wurinsa, don ya yi musu kyakkyawar sakayya a kansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk waɗannan kaso guda biyun babu wanda yake hana wa baiwarsa da kyautarsa a nan duniya; kowanne yana ba shi gwargwadon abin da ya riga ya ƙaddara masa zai samu a duniya. Sannan ya nuna yadda ya halicci mutane mabambanta da fifiko a tsakaninsu, watau ya fifita wasu a kan wasu wajen arziki ko ilimi ko martaba. To amma ya nuna cewa, fifikon da ke lahira na ni’imar Aljanna ya fi girman darajoji ya kuma fi falala, don haka kowane mumini lalle ya yi ƙoƙarin samun irin wannan fifikon na lahira ba na duniya ba.

  22. لَّا تَجۡعَلۡ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَقۡعُدَ مَذۡمُومٗا مَّخۡذُولٗا

    Open ayah 17:22

    Kada ka haɗa wani abin bauta daban tare da Allah, sai ka zama abin zargi taɓaɓɓe.

  23. ۞وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنًاۚ إِمَّا يَبۡلُغَنَّ عِندَكَ ٱلۡكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوۡ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفّٖ وَلَا تَنۡهَرۡهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوۡلٗا كَرِيمٗا

    Open ayah 17:23

    Ubangijinka kuwa Ya hukunta cewa, kada ku bauta wa (wani) sai Shi kaɗai, kuma ku kyautatawa iyaye. Ko dai ya zamanto ɗayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkansu, to kada ka nuna ƙosawarka da su, kada kuma ka daka musu tsawa; ka yi musu magana ta girmamawa.

  24. وَٱخۡفِضۡ لَهُمَا جَنَاحَ ٱلذُّلِّ مِنَ ٱلرَّحۡمَةِ وَقُل رَّبِّ ٱرۡحَمۡهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرٗا

    Open ayah 17:24

    Ka kuma ƙasƙantar da kai gare su don tausayawa, ka kuma ce: “Ubangijina Ka ji ƙan su kamar yadda suka raine ni ina ɗan ƙarami.”

  25. رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا فِي نُفُوسِكُمۡۚ إِن تَكُونُواْ صَٰلِحِينَ فَإِنَّهُۥ كَانَ لِلۡأَوَّٰبِينَ غَفُورٗا

    Open ayah 17:25

    Ubangijinku ne Mafi sanin abin da yake zukatanku. Idan kuka zamanto nagari, to lalle Shi Ya tabbata Mai gafara ne ga masu komawa gare Shi da tuba. Daga aya ta 22 har zuwa ta 38 Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kafa wasu dokoki ne guda goma sha biyar waɗanda su ne rukunai na kyakkyawar rayuwa a duniya da samun babban rabo a lahira; kuma su ne za su tabbatar wa da ‘yan’adam kyakkyawar zamantakewa a tsakaninsu. Doka ta farko, ita ce kaɗaita Allah wajen bauta da guje wa bauta wa wani tare da shi a sama ko a ƙasa. Allah ya bayyana cewa, duk wanda ya riƙi wani abin bauta ba shi ba, to zai zama abin zargi daga Allah da mala’ikunsa da manzanninsa da mutanen ƙwarai, kuma zai zama taɓaɓɓe duniya da lahira. Don haka kada wanda ya bauta wa kowa sai shi. Watau a tsarkake shi da bauta shi kaɗai. Sai kuma doka ta biyu, ya umarci mutum ya kyautata wa iyayensa, musamman ma lokacin da suka tsufa ko ɗayansu ya tsufa. Allah ya hana mutum ya yi wa iyayensa kowace irin magana da ke ɗauke da nuna ƙosawa ko gundura game da su, ballantana ma har ya kai ga daka musu tsawa ko ya yi musu baƙar magana. Sannan Allah ya umarce shi da ya yi musu magana ta girmamawa da mutuntawa. Sai kuma ya umarce shi da ƙasƙantar da kai a gabansu tare da tausaya musu koyaushe, sannan ya yi ta yi musu addu’a yana roƙa musu rahamar Allah da gafararsa, suna da rai ne ko bayan sun mutu, saboda kyakkyawar tarbiyya da suka ba shi tun yana ƙarami. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa bayinsa cewa, ya fi kowa sanin abin da yake cikin zukatansu na tsarkake niyya wajen bauta masa ko wani aikin alheri, hakanan da wajen biyayyarsu ga iyaye, musamman idan ya zamanto suna da kyakkyawar niyya a zukatansu dangane da biyayyar da suke yi musu, ba kawai suna yi ne don tsoron su ba ko don kwaɗayin wani abu na maslaha daga gare su, to lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) yana gafarta wa waɗanda suka koma gare shi suka tuba daga duk wani abu na ƙosawa ko gajiyawa da zai fito daga gare su wanda ya danganci ɗa’a ga Allah ko biyayya ga iyayensu. Allah zai gafarta musu ya kuma yafe musu shi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Ya wulaƙanta, sannan ya wulaƙanta, sannan ya wulaƙanta, watau mutumin da ɗaya daga cikin iyayensa biyu ko duka biyun za su tsufa a gabansa, amma bai shiga Aljanna ba.” [Muslim #2551].

  26. وَءَاتِ ذَا ٱلۡقُرۡبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلۡمِسۡكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَلَا تُبَذِّرۡ تَبۡذِيرًا

    Open ayah 17:26

    Kuma ka bai wa makusanci haƙƙinsa, da miskini da matafiyi, kada kuma ka yi kowane irin almubazzaranci.

  27. إِنَّ ٱلۡمُبَذِّرِينَ كَانُوٓاْ إِخۡوَٰنَ ٱلشَّيَٰطِينِۖ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِرَبِّهِۦ كَفُورٗا

    Open ayah 17:27

    Lalle masu almubazzaranci sun tabbata dangin shaiɗanu; Shaiɗan kuwa ya zamanto mai yawan kafirce wa Ubangijinsa ne.

  28. وَإِمَّا تُعۡرِضَنَّ عَنۡهُمُ ٱبۡتِغَآءَ رَحۡمَةٖ مِّن رَّبِّكَ تَرۡجُوهَا فَقُل لَّهُمۡ قَوۡلٗا مَّيۡسُورٗا

    Open ayah 17:28

    Idan kuwa ka kau da kanka daga gare su don neman wata rahama daga Ubangijinka da kake sa ran samun ta, to sai ka yi musu magana mai daɗi.

  29. وَلَا تَجۡعَلۡ يَدَكَ مَغۡلُولَةً إِلَىٰ عُنُقِكَ وَلَا تَبۡسُطۡهَا كُلَّ ٱلۡبَسۡطِ فَتَقۡعُدَ مَلُومٗا مَّحۡسُورًا

    Open ayah 17:29

    Kada kuma ka ƙuƙunce hannunka a wuyanka (ka ƙi yin kyauta), kada kuma ka shimfiɗa shi gaba ɗaya (watau ka saki komai), sai ka wayi gari abin zargi (saboda rowa), mai nadama (saboda almubazaranci).

  30. إِنَّ رَبَّكَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا 

    Open ayah 17:30

    Lalle Ubangijinka Yana shimfiɗa arziki ga wanda Ya ga dama, kuma Yana ƙuntatawa (ga wanda Ya ga dama). Lalle Shi Ya tabbata Masani ne, Mai ganin bayinsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana dokokin shari’arsa waɗanda kulawa da su ne zai lamunce wa ɗan’adam kyakkyawar rayuwa duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasiyya ta uku, watau ba wa dangi makusanta haƙƙinsu na taimako da sada zumunci da girmamawa ga kowanne gwargwadon kusancinsa. Wasiyya ta huɗu ita ce, ba wa mabuƙaci wanda ba ɗan’uwa na jini ba haƙƙinsa, shi ma na taimako da tausayawa daga dukiyar zakka da wadda ba ta zakka ba. Wasiyya ta biyar ita ce, taimakon matafiyi wanda guzurinsa ya yanke masa da abin da zai kai shi garinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kashedi ga yin almubazzaranci da dukiya; wannan ita ce doka ta shida. Almubazzaranci shi ne kashe dukiya inda bai dace ba ko da kuwa kaɗan ce. Allah ya bayyana illar yin haka da cewa, masu almubazzaranci suna kashe dukiyoyinsu wurin saɓon Allah da ta hanyar da ba ta kamata ba, waɗannan ‘yan’uwan shaiɗanu ne, domin su suke yi wa biyayya ba Allah ba. Shaiɗan kuwa da ma shi mai butulci ne ga Ubangijinsa, babu abin da yake aikatawa sai saɓon Allah, ba kuma ya yin umarni da wani abu sai abin da zai fusata Ubangijinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana yadda mutum ya dace ya yi yayin da masu neman wani taimako daga gare shi suka zo, amma kuma ba shi da abin da zai taimaka musu; shi ma yana jiran Allah ya hore masa, to kamata ya yi ya faɗa musu magana mai daɗi, kamar yi musu addu’ar Allah ya hore musu ko kuma yi musu alƙawarin taimaka musu duk lokacin da Allah ya hore. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sifanta yadda mutum ya kamata ya zama tsaka-tsaki wajen sarrafa dukiyarsa, watau kada ya kame hannunsa ya yi rowa da ita, ya ƙi taimaka wa waɗanda ya dace ya taimaka musu; kada kuma ya saki hannunsa wajen kashe dukiyarsa har ya bayar da abin da ya fi ƙarfin dukiyar. Domin kuwa yin rowa zai jawo masa zargi da suka daga mutane; wuce iyaka kuma wajen kashe kuɗi zai haifar masa durƙushewa har ya wayi gari ba abin da zai taimaka da shi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kullum idan gari ya waye mala’iku biyu suna saukowa daga sama, ɗayansu yana cewa,: “Ya Allah, ka mayar wa da mai ciyar da dukiyarsa makwafin abin da ya ciyar.” Ɗayan kuma yana cewa,: “Ya Allah, ka lalata dukiyar wanda ya yi rowa.” [Bukhari #1442 da Muslim #1010]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, arziki yana hannunsa ne yana yalwata shi ga wanda ya ga dama, yana kuma ƙuntata shi ga wanda ya ga dama saboda wata hikima da shi ya fi sanin ta. Lalle Allah mai cikakken sanin bayinsa ne mai ganin duk ayyukansu ne babu abin da yake ɓuya gare shi, don haka yake sarrafa su yadda ya ga dama.

  31. وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 17:31

    Kada kuma ku kashe ‘ya’yayenku don tsoron talauci: Mu ne Muke arzuta su har ma da ku. Lalle kashe su kuskure ne babba.

  32. وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلزِّنَىٰٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَسَآءَ سَبِيلٗا

    Open ayah 17:32

    Kuma kada ku kusanci zina; lalle ita (zina) ta kasance mugun aiki ne, kuma hanya ce wadda ta munana.

  33. وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَمَن قُتِلَ مَظۡلُومٗا فَقَدۡ جَعَلۡنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلۡطَٰنٗا فَلَا يُسۡرِف فِّي ٱلۡقَتۡلِۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورٗا

    Open ayah 17:33

    Kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (kashewa) sai da haƙƙi. Wanda aka kashe ta hanyar zalunci, to lalle Mun bai wa magajinsa dama (ta ramuwa), to (amma) kada ya wuce gona da iri wajen kisa; lalle shi ya zamanto abin dafa wa baya ne.

  34. وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ بِٱلۡعَهۡدِۖ إِنَّ ٱلۡعَهۡدَ كَانَ مَسۡـُٔولٗا

    Open ayah 17:34

    Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai dai ta (hanya) wadda take mafi kyau, har sai ya kawo ƙarfi. Kuma ku cika alƙawari; lalle alƙawari ya kasance abin tambaya ne (a lahira). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana dokokin nan na shari’arsa. Ya ambaci doka ta bakwai, watau hani a kan kashe ‘ya’ya saboda tsoron talauci. Ya tabbatar wa da iyaye cewa, shi ne mai ciyar da su ya shayar da su da sauran buƙatunsu; su ma iyayen shi ne mai arzuta su. Ya yi kashedi da cewa, kashe ‘ya’ya saboda wannan dalili ba ƙaramin laifi ne ba; yana daga cikin manyan laifuka waɗanda suka shafi rashin tausayi da rashin imani, domin babu wani dalilin kashe su sam-sam. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa,: “Wane zunubi ne ya fi girma?” Sai ya ce: “Ka sanya wa Allah kishiya alhalin shi ne ya halicce ka.” Sai na ce: “Sai kuma wanne?” Sai ya ce: “Ka kashe ɗanka don kada ya ci tare da kai.” Na ce: “Sai kuma me?” Sai ya ce: “Ka yi zina da matar maƙocinka.” [Bukhari #4477 da Muslim #86]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci doka ta takwas, ita ce hani a kan kusantar zina, watau nesantar duk wani abu da zai taimaka a kan aukuwar zina. Ya tabbatar da cewa, munin zina ya kai matuƙa sosai, kuma hanya ce mummuna mai kaiwa ga azabar Allah Ta’ala. An karɓo daga Abu Umamata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani matashi ya zo wajen Annabi (ﷺ) ya ce: “Ka ba ni izinin aikata zina.” Sai jama’a suka yiwo kansa suna kwaɓar sa, suna ce masa ya yi shiru kada ya ƙara faɗar wannan ɗanyar maganar. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce da shi: “Matso kusa.” Sai ya matsa dab da Manzon Allah (ﷺ), sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “To zauna.” Sai ya zauna. Sai ya ce masa: “Kana son a yi zina da mahaifiyarka?” Ya ce: “A’a wallahi. Allah ya sanya ni fansa gare ka.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “To mutane ma ba sa son a yi zina da iyayensu mata.” Sai kuma ya ce masa: “Kana so a yi zina da ‘yarka?” Ya ce: “A’a wallahi, ya Manzon Allah. Allah ya sanya ni fansa gare ka.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “To hakanan ma mutane ba sa son a yi da ‘ya’yansu mata.” Sai ya ce masa: “Kana so a yi da gwaggonka?” Sai ya ce: “A’a wallahi. Allah ya sanya ni fansa gare ka.” Sai ya ce masa: “To mutane ma ba sa so a yi zina da gwaggonninsu.” Sai ya ce: “Kana so a yi da innarka?” Sai ya ce: “A’a wallahi. Allah ya sanya ni fansa a gare ka.” Sai Manzon Allah ya ce masa: “To hakanan mutane ma ba sa son a yi da innoninsu.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ɗora masa hannu a jikinsa ya ce: “Ya Allah ka gafarta masa zunubinsa, ka tsarkake zuciyarsa, ka tsare farjinsa.” Daga rannan wannan saurayi bai ƙara waiwayen wani abu irin wannan ba.” [Ahmad, Musnad #22211]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci doka ta tara, ita ce hani a kan kisan wani rai ba tare da haƙƙi ba na ridda ko ƙisasi ko haddin zina. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Jinin mutum Musulmi wanda yake shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah kuma lalle ni Manzon Allah ne, bai halatta ba, sai saboda ɗayan abubuwa uku: Mazinacin da ya taɓa yin aure da wanda ya kashe rai da wanda ya bar addini ya rabu da jama’ar Musulmi.” [Muslim #1676 da Ahmad #3621]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hurumin neman fansa ta ƙisasi ko diyya ga wanda aka kashe ɗan’uwansa na jini bisa zalunci. Allah ya bayyana cewa, ya bai wa ɗan’uwansa hujja ƙarara a hannunsa ta ya nemi sakayya ga ɗan’uwansa, a yi ƙisasi idan kowa ya amince daga dangi, ko ya karɓi diyya. Ya kuma hana ya wuce gona da iri wajen ɗaukar fansa, watau ya kashe wanda ba shi ya yi kisan ba, ko ya yi gunduwa-gunduwa da shi bayan an kashe shi. Shi wannan ɗan’uwa na wanda aka kashe wanda za a taimaka wa ne har ya kai ga cimma burinsa na karɓo haƙƙin jinin ɗan’uwansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana doka ta goma, watau hana cin dukiyar maraya, wanda mahaifinsa ya rasu ya bar shi bai balaga ba. To shi ma haramun ne mutum ya ci dukiyarsa ko ya salwantar masa da ita don an danƙa ta a hannunsa. Sai dai an yarje masa ya haɓaka masa ita ta hanyar kasuwanci da sana’a har lokacin da zai mallaki hankalinsa, sai ya mayar masa da dukiyarsa. Ya zo a cikin [Sahihu Muslim #1826], Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda): “Ya Aba Zarrin, lalle ni na gan ka kai mai rauni ne, kuma ni ina so maka abin da nake so wa kaina, don haka kada ka shugabanci ko da mutum biyu ne, kada kuma ka ɗauki nauyin kula da dukiyar maraya.” Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni da cika alƙawari. Wannan ita ce doka ta sha ɗaya. Alƙawari ya haɗa har da wanda yake tsakanin bawa da Ubangijinsa na bauta masa shi kaɗai ba tare da shirka ba, da kuma wanda yake tsakanin mutum biyu ko fiye. Su cika ba tare da sun rage komai ba ko sun warware shi. Ya kuma gargaɗe su da cewa, tabbas a ranar lahira sai ya tambaye su game da alƙawuransu sun cika ko ba su cika ba?

  35. وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ إِذَا كِلۡتُمۡ وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلٗا

    Open ayah 17:35

    Kuma ku cika mudu idan kuka yi awo, kuma ku auna nauyi da ma’auni na adalci. Wannan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawan ƙarshe.

  36. وَلَا تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا

    Open ayah 17:36

    Kada kuma ka dinga bibiyar abin da ba ka da ilimi a kansa. Lalle ji da gani da kuma tunani duk waɗannan sun zama abin tambaya ne game da su.

  37. وَلَا تَمۡشِ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَحًاۖ إِنَّكَ لَن تَخۡرِقَ ٱلۡأَرۡضَ وَلَن تَبۡلُغَ ٱلۡجِبَالَ طُولٗا

    Open ayah 17:37

    Kada kuma ka yi tafiya a bayan ƙasa kana mai girman kai; lalle kai ba za ka tsaga ƙasa ba (don ƙasaita) kuma ba za ka kai tsawon duwatsu ba.

  38. كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُۥ عِندَ رَبِّكَ مَكۡرُوهٗا

    Open ayah 17:38

    Duk waɗancan abubuwa mummunansu a wurin Ubangijinka abin ƙi ne.

  39. ذَٰلِكَ مِمَّآ أَوۡحَىٰٓ إِلَيۡكَ رَبُّكَ مِنَ ٱلۡحِكۡمَةِۗ وَلَا تَجۡعَلۡ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتُلۡقَىٰ فِي جَهَنَّمَ مَلُومٗا مَّدۡحُورًا

    Open ayah 17:39

    Wannan yana daga cikin abin da Ubangijinka Ya yiwo maka wahayi da shi na hikima. Kada kuma ka sanya wani abin bauta tare da Allah, sai a jefa ka a cikin Jahannama kana abin zargi, korarre (daga rahama). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana dokokinsa da wasiyyoyinsa da ya yi wa bayinsa guda goma sha biyar. A wasiyya ta goma sha biyu da ta sha uku, ya yi wa mutane umarni da cika mudu yayin da suke auna wa wasu, kada su tauye musu komai na haƙƙinsu, ya kuma umarce su da daidaita sikeli bisa gaskiya da adalci, kada su yi dabarar rage wa mutane haƙƙoƙinsu. Ya nuna musu cewa, wannan cika ma’aunin da tsayar da sikelin shi ne alheri gare su duniya da lahira. Sai kuma ya ambaci doka ta sha huɗu wadda ta ƙunshi hani game da kutsawa cikin abin da mutum ba shi da wani ilimi a kansa; ya bi labarin da bai tabbatar da sahihancinsa ba. Allah ya tsoratar da mai aikata haka, ya bayyana cewa sai an titsiye shi ranar alƙiyama an yi masa tambaya game da yadda ya yi amfani da jinsa da ganinsa da zuciyarsa, a alheri ne ya yi amfani da su ko a wajen sharri ne, kuma a yi masa sakayyar da ta dace da aikinsa. Malam Ƙatada ya ce: Ma’anar ayar: “Kada ka ce: Na gani, alhalin ba ka gani ba, ko ka ce: Na ji, alhalin ba ka ji ba, ko ka ce: Na sani, alhalin ba ka sani ba; duk waɗannan sai Allah ya tambaye ka a kansu” [Ibn Kasir, juzi na 5, shafi na 75]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana mumini yin tafiya irin ta ƙasaita da girman kai da taƙama a bayan ƙasa, domin duk inda ya kai ga nuna isa da ƙasaita bai isa ya tsaga ƙasa da tafiyarsa ba, kuma ɗaga kai da tsawonsa ba zai kai na duwatsu ba, don haka bai isa komai ba a wurin Allah. Wannan ita ce doka ta sha biyar. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wani mutum yana cikin tafiya ya caɓa ado yana jiji da kansa ya taje sumarsa sai kawai Allah ya nufi ƙasa ta haɗiye shi, yana nan yana ta gangarawa a cikinta har ranar tashin alƙiyama.” [Bukhari #5789 da Muslim #2088]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk waɗannan munanan ayyuka da aka ambata a ayoyin da suka gabata, Allah (Mai tsarki da daukaka) ba zai taɓa amincewa da ɗaya daga cikinsu ba, sai ya kama duk wanda ya aikata su kuma ya azabtar da shi a kai. Sannan ya nuna cewa, duk abubuwan da ya yi umarni da su da waɗanda ya hana suna daga cikin abubuwan da ya yi wa Manzonsa (ﷺ) wahayinsu na hukunce-hukunce. Sai a ƙarshe ya sake jaddada haninsa ga ɗan’adam da kada ya riƙi wani abin bauta tare da Allah; idan ya yi haka kuwa to ranar alƙiyama za a jefa shi cikin wutar Jahannama yana abin zargi a wurin Allah da bayinsa na ƙwarai, yana kuma korarre daga rahamar Allah.

  40. أَفَأَصۡفَىٰكُمۡ رَبُّكُم بِٱلۡبَنِينَ وَٱتَّخَذَ مِنَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِنَٰثًاۚ إِنَّكُمۡ لَتَقُولُونَ قَوۡلًا عَظِيمٗا 

    Open ayah 17:40

    Shin yanzu kuwa Ubangijinku Ya zaɓar muku ‘ya’ya maza ne (Shi) kuwa Ya ɗauki (‘ya’ya) mata daga mala’iku? Lalle ku tabbas kuna faɗar babbar magana.

  41. وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لِيَذَّكَّرُواْ وَمَا يَزِيدُهُمۡ إِلَّا نُفُورٗا

    Open ayah 17:41

    Haƙiƙa kuma Mun bayyana (hujjoji) a cikin wannan Alƙur’ani don su wa’azantu, (amma) kuma ba abin da yake ƙara musu sai nesanta (daga gaskiya).

  42. قُل لَّوۡ كَانَ مَعَهُۥٓ ءَالِهَةٞ كَمَا يَقُولُونَ إِذٗا لَّٱبۡتَغَوۡاْ إِلَىٰ ذِي ٱلۡعَرۡشِ سَبِيلٗا

    Open ayah 17:42

    Ka ce (da su): “ </b>Da dai akwai wasu alloli tare da shi (Allah), kamar yadda suke da’awa, to kuwa da sun nemi hanyar (yin hamayya) da Mai Al’arshi (watau Allah) <b>.”

  43. سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يَقُولُونَ عُلُوّٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 17:43

    Tsarki ya tabbata gare Shi, kuma Ya ɗaukaka ɗaukaka mai girma game da abin da suke faɗa.

  44. تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ ٱلسَّبۡعُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمۡدِهِۦ وَلَٰكِن لَّا تَفۡقَهُونَ تَسۡبِيحَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا

    Open ayah 17:44

    Sammai bakwai da ƙasa da abin da yake cikinsu (duka) suna tsarkake Shi. Ba wani abu wanda ba ya tasbihi tare da gode masa, sai dai ba kwa fahimtar tasbihinsu. Lalle Shi Ya kasance Mai yawan haƙuri ne, Mai yawan gafara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kakkausar suka ga mushirikai masu cewa wai Allah yana da ‘ya’ya mata su ne mala’iku, ya bayyana cewa, wannan maganar da suke yi ta yi muni matuƙa. Su suna ƙyamar a danganta musu ‘ya’ya mata suna kuma ɗaukan hakan a matsayin tawaya, to ta yaya za a ce, su ya zaɓa musu ‘ya’ya maza, shi kuma ya riƙe ‘ya’ya mata? Wannan maganar tasu babu shakka rashin girmamawa ce ƙarara ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Allah kuma ya bayyana cewa, ya sarrafa wa bayinsa ayoyin Alƙur’ani ta fuskoki daban-daban; ya kawo musu hukunce-hukunce, da wa’azi iri-iri, tare da misalai daban-daban, duka domin su wa’azantu su bi hanya mai amfani gare su duniya da lahira, to amma waɗanda zukatansu sun riga sun lalace, wannan bai ƙara musu komai ba sai nesanta daga gaskiya. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa mushirikai cewa, da a ce akwai wasu abubuwan bauta ba Allah ba, kamar yadda suke riyawa, to da sun nemi hanyar yin galaba da samun nasara a kan Allah (Mai tsarki da daukaka) mai Al’arshi. To amma su da kansu mushirikan sun amince da cewa, allolinsu da suke bauta wa ba sa iya yin komai da kansu kuma ba sa amfanarwa ba sa cutarwa. To idan haka ne me ya sa suke bauta musu ba Allah ba? Ma’ana ta biyu da wasu malamai suka faɗa ta wannan ayar shi ne, da a ce akwai wasu ababen bauta tare da Allah, to da su ma sun riƙa neman kusanci ne ga Allah ta hanyar yi masa ɗa’a da bautarsa, don haka su mushirikai mene ne ya sa suke bauta musu ba za su bauta wa Allah kai-tsaye ba?! Sai kuma ya bayyana cewa, duk wata halitta a sama ko a ƙasa mai bauta ce da tasbihi ga Allah. Sammai bakwai da ƙasa da duk abubuwan da suke cikinsu dukkansu suna tasbihi ne da tsarkake Allah (Mai tsarki da daukaka). Komai ma yana tasbihi ne tare da tsarkake Allah, to amma mutane ba sa fahimtar yadda suke yin tasbihinsu, domin suna yi ne da wani harshe ba irin na mutane ba. Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Haƙiƙa mun kasance muna jin tasbihin abinci yayin da ake cin sa.” [Bukhari #3579]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yawan haƙurinsa ga masu bijire wa umarninsa da ba ya gaggauto musu da uƙuba, yana kuma gafarta musu yayin da suka tuba suka nemi gafararsa.

  45. وَإِذَا قَرَأۡتَ ٱلۡقُرۡءَانَ جَعَلۡنَا بَيۡنَكَ وَبَيۡنَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ حِجَابٗا مَّسۡتُورٗا

    Open ayah 17:45

    Idan ka karanta Alƙur’ani Mukan sanya shamaki mai karewa tsakaninka da waɗanda ba sa imani da lahira.

  46. وَجَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۚ وَإِذَا ذَكَرۡتَ رَبَّكَ فِي ٱلۡقُرۡءَانِ وَحۡدَهُۥ وَلَّوۡاْ عَلَىٰٓ أَدۡبَٰرِهِمۡ نُفُورٗا

    Open ayah 17:46

    Kuma Mukan sanya marufi a kan zukatansu don kada su fahimce shi (Alƙur’anin); a cikin kunnuwansu kuma (Mukan sanya) wani nauyi. Idan kuma ka ambaci Ubangijinka Shi kaɗai a cikin Alƙur’ani sai su ba da baya suna masu bazama.

  47. نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَسۡتَمِعُونَ بِهِۦٓ إِذۡ يَسۡتَمِعُونَ إِلَيۡكَ وَإِذۡ هُمۡ نَجۡوَىٰٓ إِذۡ يَقُولُ ٱلظَّٰلِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلٗا مَّسۡحُورًا

    Open ayah 17:47

    Mu Muka fi kowa sanin irin yadda suke sauraren sa (Alƙur’ani), yayin da suke sauraren ka (kana karanta shi), da kuma sanda suke tattaunawa, yayin da azzalumai suke cewa: “Ai ba wanda kuke bi face wani sihirtaccen mutum.”

  48. ٱنظُرۡ كَيۡفَ ضَرَبُواْ لَكَ ٱلۡأَمۡثَالَ فَضَلُّواْ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ سَبِيلٗا

    Open ayah 17:48

    Duba ka ga yadda suka yi ta ba ka sifofi (iri-iri), sai suka ɓace, ba ko za su sami damar (gane) hanya ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin kafirai lokacin da suke sauraron karatun Alƙur’ani daga Manzon Allah (ﷺ). Watau idan suka ji abin da ya ƙunsa na wa’azuzzuka da tsawatarwa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya wani shamaki tsakaninsa da waɗanda ba su yi imani da ranar lahira ba ya hana su fahimtar haƙiƙanin abin da ake karanta musu, don haka sai su bijire masa, su ƙi miƙa wuya gare shi. Sannan kuma Allah ya saka wasu murafa a kan zukatansu, don haka sai su kasa fahimtar ayoyin Alƙur’ani, ya kuma toshe kunnuwansu da wani nauyi, don haka ba za su taɓa yin sauraro na amfana ba sai dai na tsayuwar hujja a kansu. Don haka ne ma duk sanda Annabi (ﷺ) ya karanta ayoyin Alƙur’ani masu nuna Kaɗaitakar Allah da hana shirka sai su juya baya a guje suna masu watsi da ayoyinsa da suka ji. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin da ya sa ya hana musu fahimtar Alƙur’ani yayin da ake karanta musu shi, da cewa, ya fi kowa sanin mummunar manufarsu lokacin da suke sauraron Alƙur’ani, watau suna sauraro ne da nufin su sami abin da za su kushe shi ne, don haka ba neman gaskiya ne a zukatansu ba, shi ya sa Allah ya toshe musu kafofin fahimtarsa. Haka kuma yana sane da duk abin da suke haɗuwa suna ƙullawa da junansu domin su ƙirƙiri sunan da za su ɓata Manzon Allah (ﷺ) da shi. Azzalumai kuma waɗanda suka cuci kawunansu da kafirci sun fito ƙarara suna faɗa wa mutane cewa, wai idan har suka bi Manzon Allah (ﷺ) to su sani ba wani suke bi ba sai mutumin da aka sihirce shi don haka ya sami taɓin hankali. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabinsa cewa, ya duba ya ga yadda kafirai suka bayar da wani gurɓataccen misali marar tushe da dalili, a kansa, inda suka kira shi matsafi, wasu su ce wanda aka sihirce, wasu kuma su ce mawaƙi wasu kuma boka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, dukkansu sun ɓace ba kuma za su taɓa gane gaskiya ba har abada.

  49. وَقَالُوٓاْ أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا وَرُفَٰتًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ خَلۡقٗا جَدِيدٗا

    Open ayah 17:49

    Kuma suka ce: “Yanzu kuwa idan muka zama ƙasusuwa kuma rududdugaggu, anya kuwa za a tashe mu a sabuwar halitta?”

  50. ۞قُلۡ كُونُواْ حِجَارَةً أَوۡ حَدِيدًا 

    Open ayah 17:50

    Ka ce (da su): “Ku zama dutse ko ƙarfe!

  51. أَوۡ خَلۡقٗا مِّمَّا يَكۡبُرُ فِي صُدُورِكُمۡۚ فَسَيَقُولُونَ مَن يُعِيدُنَاۖ قُلِ ٱلَّذِي فَطَرَكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖۚ فَسَيُنۡغِضُونَ إِلَيۡكَ رُءُوسَهُمۡ وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هُوَۖ قُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَرِيبٗا

    Open ayah 17:51

    “Ko kuma duk wata halitta da ta fi girma a ranku (lalle za a tashe ku).” Sannan za su ce: “To wane ne zai dawo da mu?” Ka ce (da su): “Wanda ya halicce ku tun farko.” Sannan za su girgiza maka kawunansu su kuma ce: “To yaushe ne shi (wannan al’amari zai kasance)?” Ka ce (da su): “Mai yiwuwa ne ya faru ba da daɗewa ba.

  52. يَوۡمَ يَدۡعُوكُمۡ فَتَسۡتَجِيبُونَ بِحَمۡدِهِۦ وَتَظُنُّونَ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 17:52

    “Ranar da zai kira ku sai ku amsa tare da gode masa kuma ku riƙa tsammanin ba ku zauna (a bayan ƙasa ba) sai ɗan lokaci ƙanƙani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai suka riƙa ƙaryata tashi bayan mutuwa, har suna mamakin wai ta yaya za a tashe su bayan sun mutu sun zama ƙasusuwa, jikinsu ya ratattake, suka nuna wai wannan abu sam ba mai yiwuwa ne ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya mayar musu da martani cewa, su rikiɗa su zama dutse ko ƙarfe ko duk wani abu da suke ganin babba ne a idonsu, idan suna zaton in sun yi haka Allah ba zai iya dawo da su yadda suke da farko ba. Lalle duk yadda suka zama ba za su gagari Allah ba. Allah zai dawo da su yadda suke da farko. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk da haka za su riƙa tambaya ta izgili suna cewa, wane ne zai dawo da su da ransu bayan sun mutu? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, wannan dai da ya halicce su lokacin da babu su ba tare da ya kwaikwaya daga kowa ba, shi ne dai zai sake dawo da su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, za su riƙa kaɗa kansu suna izgili da amsar da Manzon Allah (ﷺ) ya ba su. Sai su sake masa wata tambayar don dai su ƙure shi, su ce: To yaushe ne za a tashe su? Allah ya umarce shi da ya faɗa musu cewa, tabbas hakan zai faru ba da jimawa ba. Amma Allah ya bayyana ranar da zai dawo da su gaba ɗayansu, watau ranar da zai kirawo su don su tattaru domin hisabi; nan take kuwa su amsa masa tare da yi masa kirari da miƙa wuya ga umarninsa. A lokacin ne za su yi mamaki su yi tsammanin ‘yan kwanaki kaɗan suka yi a duniya.

  53. وَقُل لِّعِبَادِي يَقُولُواْ ٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ يَنزَغُ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 17:53

    Ka kuma ce da bayina su faɗi (magana) wadda ita ce ta fi kyau. Lalle Shaiɗan yana ɓata tsakaninsu. Lalle Shaiɗan ya tabbata maƙiyi ne mai bayyana (ƙiyayya) ga mutum.

  54. رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِكُمۡۖ إِن يَشَأۡ يَرۡحَمۡكُمۡ أَوۡ إِن يَشَأۡ يُعَذِّبۡكُمۡۚ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا

    Open ayah 17:54

    Ubangijinku (Shi) Ya fi sanin ku; in Ya ga dama sai Ya ji ƙan ku ko kuma in Ya ga dama sai Ya azabtar da ku. Ba Mu kuwa aiko ka ba don ka zama wakili a kansu.

  55. وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِمَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ فَضَّلۡنَا بَعۡضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعۡضٖۖ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

    Open ayah 17:55

    Ubangijinka kuma (Shi ne) Mafi sanin abin da yake cikin sammai da ƙasa. Haƙiƙa kuma Mun fifita wasu annabawa a kan wasu; Muka kuma bai wa Dawuda (littafin) Zabura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya gaya wa muminai su riƙa faɗar kyakkyawar magana a lokacin tattaunawarsu da juna, domin Shaiɗan har koyaushe yana ƙoƙarin ɓata tsakaninsu ne, don haka zai iya haddasa husuma da sharri a tsakaninsu ta hanyar maganar da za su furta wa juna idan ba ta kasance mai kyau ba. Domin shi Shaiɗan maƙiyi ne ga Annabi Adamu da zurriyarsa tun lokacin da ya ƙi yin sujjada ga Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma ƙiyayyarsa a fili take ba a ɓoye ba. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ɗayanku ya nuna ɗan’uwansa da makami domin bai sani ba mai yiwuwa ne Shaiɗan ya kwaɓi hannunsa sai ya jawo masa faɗawa ramin wuta.” [Bukhari #7072 da Muslim #2617]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutane cewa, ya fi su sanin kawunansu, domin babu abin da zai ɓoyu gare shi; ya san wanda ya cancanci shiriya daga cikinsu sai ya ji ƙan sa ya shirye shi idan ya ga dama, ya san kuma wanda bai cancance ta ba sai ya bar shi cikin ɓata don ya yi masa azaba idan ya ga dama. Ya tabbatar wa da Annabi (ﷺ) cewa, bai aiko shi don ya zamanto wakili mai tursasa kafirai sai sun yi imani ko mai ƙididdige ayyukansu ba. Shi kawai mai gargaɗi ne da yin albishir ga mutane. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake sanar da mutane cewa, ya fi kowa sanin halittunsa na sama da na ƙasa, ya kuma san matsayin kowa a wajen ayyukan ƙwarai da waɗanda ba na ƙwarai ba. Kuma shi ne ya fifita wasu annabawa a kan wasu da yawan mabiya da saukar musu da littattafai; shi ne kuma ya ba wa Annabi Dawuda littafin Zabura. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “An sassauta wa Dawuda abin karantawarsa (Zabura); yakan yi umarni a ɗaura wa dabbarsa sirdi, yakan sauke littafinsa kafin a gama sa wa dabbar sirdin.” [Bukhari #4713].

  56. قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمۡلِكُونَ كَشۡفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمۡ وَلَا تَحۡوِيلًا

    Open ayah 17:56

    Ka ce (da su): “Ku kirawo waɗanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku) ba Shi ba, to ba su da ikon yaye muku cuta ko juyar da ita.”

  57. أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ يَبۡتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلۡوَسِيلَةَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ وَيَرۡجُونَ رَحۡمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحۡذُورٗا

    Open ayah 17:57

    Waɗancan da suke bauta wa, su ma suna neman hanya ne zuwa ga Ubangijinsu, a cikinsu wa zai fi kusanci? Suna kuma ƙaunar rahamarsa, kuma suna tsoron azabarsa. Lalle azabar Ubangijinka ta kasance abar tsoro ce.

  58. وَإِن مِّن قَرۡيَةٍ إِلَّا نَحۡنُ مُهۡلِكُوهَا قَبۡلَ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَوۡ مُعَذِّبُوهَا عَذَابٗا شَدِيدٗاۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَسۡطُورٗا

    Open ayah 17:58

    Kuma ba wata alƙarya sai Mu ne masu halaka ta tun kafin ranar alƙiyama, ko kuma Masu azabtar da ita azaba mai tsanani. Wannan ya tabbata a rubuce cikin Littafi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba mu labarin wasu aljannu ne da wasu mushirikai suke bauta musu, sai suka musulunta, su kuma masu bautar su suka ci gaba da bautar su ba tare da sun san cewa, aljannun nan sun musulunta ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) yake umartar Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa mushirikai cewa, su kirawo waɗanda suke bauta wa ba Allah ba, ba za su iya kare su daga wata cuta da za ta same su ba, ba kuma za su iya ɗauke musu ita ba su jefa wa wani domin gajiyawarsu da kasawarsu; duk wani gajiyayye kuwa ba zai taɓa zama abin bauta ba. Sannan ya sanar da su cewa, waɗannan da suke bauta wa daga cikin aljannu da mala’iku da sauran mutanen kirki su kansu suna neman kusanci ne wurin Allah ta hanyar ayyuka na ƙwarai, suna rigegeniya a tsakaninsu wajen yi masa ɗa’a, suna fatan samun rahamarsa suna kuma tsoron azabarsa. Lalle kam azabar Allah abar tsoro ce. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu wata alƙarya da mutanenta suka ƙaryata manzannin Allah sai ya hallaka su ya saukar musu da azaba a nan duniya saboda kafircinsu, ko kuma ya azabtar da su da wata azaba mai tsanani kamar kisa da ɗauri da makamantansu. Wannan hallakarwar wani hukunci ne na Allah da ya riga ya rubuta a cikin littafin Lauhul Mahfuzu.

  59. وَمَا مَنَعَنَآ أَن نُّرۡسِلَ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّآ أَن كَذَّبَ بِهَا ٱلۡأَوَّلُونَۚ وَءَاتَيۡنَا ثَمُودَ ٱلنَّاقَةَ مُبۡصِرَةٗ فَظَلَمُواْ بِهَاۚ وَمَا نُرۡسِلُ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّا تَخۡوِيفٗا

    Open ayah 17:59

    Kuma ba abin da ya hana Mu aiko da ayoyi sai don (al’ummu) na farko sun ƙaryata su; Muka kuma bai wa Samudawa taguwa (don ta zama aya) bayyananniya, sai suka butulce mata. Ba Ma kuwa aiko da ayoyi sai don tsoratarwa.

  60. وَإِذۡ قُلۡنَا لَكَ إِنَّ رَبَّكَ أَحَاطَ بِٱلنَّاسِۚ وَمَا جَعَلۡنَا ٱلرُّءۡيَا ٱلَّتِيٓ أَرَيۡنَٰكَ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلنَّاسِ وَٱلشَّجَرَةَ ٱلۡمَلۡعُونَةَ فِي ٱلۡقُرۡءَانِۚ وَنُخَوِّفُهُمۡ فَمَا يَزِيدُهُمۡ إِلَّا طُغۡيَٰنٗا كَبِيرٗا 

    Open ayah 17:60

    (Ka tuna) kuma lokacin da Muka ce da kai: “Lalle Ubangijinka Ya kewaye mutane (da ikonsa).” Ba Mu kuwa sanya abin da Muka nuna maka ido-da-ido ba (lokacin Isra’i) sai don jarraba ga mutane, da kuma la’ananniyar bishiyar nan (da aka ambata) a cikin Alƙur’ani. Muna kuwa tsoratar da su ne, amma ba abin da yake ƙara musu sai ɗagawa mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rahamar da ya yi wa mutane yayin da ya ƙi amsa kiran mushirikai na ya sauko da wasu mu’ujizoji don tabbatar da gaskiyar manzancin Annabi (ﷺ). Ya nuna cewa, ba abin da ya hana shi sauko da su sai don cewa al\'ummu na farko sun ƙaryata irinsu; don haka idan yanzu ma ya sauko da wasu mushirikai za su ƙaryata su, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gaggauto musu azaba kamar yadda ya yi wa al\'ummun farko bayan sun ƙaryata mu’ujizojin annabawansu. Taguwar Annabi Salihu tana daga cikin manya-manyan ayoyin da Allah ya aiko, amma duk da haka Samudawa suka ƙaryata ta, Allah kuwa ya saukar musu da azaba, kamar yadda ya bayyana a wasu wurare na Alƙur’ani. To haka su ma waɗannan mushrikai da zai aiko musu da wasu manya-manyan ayoyinsa to da sun ƙaryata su sun ƙi yin imani. Domin ba rashin ganin hujja ce ya hana musu yin imani ba; an ba su hujjoji masu yawa amma suka yi watsi da su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yana aiko da ayoyi ne kawai domin tsoratarwa, ba domin tursasawa ba. Sannan Allah ya tunatar da Annabi (ﷺ) lokacin da ya ce da shi, lalle Ƙudurarsa ta kewaye mutane gaba ɗaya, dukkansu suna ƙarƙashin ikonsa, don haka shi ne mai kare Annabinsa daga sharrin duk wani masharranci, har sai ya isar da saƙon Allah ba tare da ya ji tsoron kowa ba. Ya kuma tabbatar masa da cewa, abin nan da ya nuna masa a daren Isra’i, ya gan shi da idonsa ya yi haka ne don ya jarraba mutane, saboda wasu za su gaskata shi, wasu kuma su ƙaryata shi. Hakanan labarin la’ananniyar bishiyar nan ta zaƙƙumi da ya bayar a Alƙur’ani da cewa, tana tsirowa daga ƙarƙashin wutar Jahannama, to ita ma wata jarrabar ce a gare su; wasu za su gaskata su yi imani, wasu kuwa su ƙaryata su kafirce, domin suna ganin ba ta yadda za a yi bishiya ta tsiro a tsakiyar wuta. To idan ba su yi imani da waɗannan ayoyi biyu ba, ba za su taɓa yin imani da wasu ayoyin ba ko da an saukar musu su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yana tsoratar da su da ayoyi amma babu abin da tsoratarwar take ƙara musu sai zaƙewa a kan kafirci da dogewa a cikin ɓata.

  61. وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ قَالَ ءَأَسۡجُدُ لِمَنۡ خَلَقۡتَ طِينٗا

    Open ayah 17:61

    Kuma (ka tuna) lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu.” Sai suka yi sujjadar in ban da Iblis da ya ce: “Yanzu na yi sujjada ga wanda Ka halitta da taɓo?”

  62. قَالَ أَرَءَيۡتَكَ هَٰذَا ٱلَّذِي كَرَّمۡتَ عَلَيَّ لَئِنۡ أَخَّرۡتَنِ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَأَحۡتَنِكَنَّ ذُرِّيَّتَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 17:62

    Ya ce: “Ka gan Ka, wannan da Ka fifita shi a kaina, tabbas idan Ka jinkirta min har zuwa ranar alƙiyama to lalle zan karkatar da zuriyarsa, sai dai kaɗan (daga cikinsu).”

  63. قَالَ ٱذۡهَبۡ فَمَن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ فَإِنَّ جَهَنَّمَ جَزَآؤُكُمۡ جَزَآءٗ مَّوۡفُورٗا

    Open ayah 17:63

    (Allah) Ya ce: “Je ka (an jinkirta maka ɗin), sai dai (duk) wanda ya bi ka daga cikinsu to lalle Jahannama ce sakamakonku, wanda yake sakamako ne cikakke.

  64. وَٱسۡتَفۡزِزۡ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتَ مِنۡهُم بِصَوۡتِكَ وَأَجۡلِبۡ عَلَيۡهِم بِخَيۡلِكَ وَرَجِلِكَ وَشَارِكۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَوۡلَٰدِ وَعِدۡهُمۡۚ وَمَا يَعِدُهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ إِلَّا غُرُورًا

    Open ayah 17:64

    “Ka kuma yi wasa da hankalin wanda ka sami dama daga cikinsu da muryarka ka kuma jawo su da rundunarka mahaya da na ƙasa; ka kuma yi tarayya da su cikin dukiyoyi da ‘ya’yaye; ka kuma yi musu alƙawari.” Shaiɗan kuwa ba wani alƙawari da yake yi musu sai na ruɗi.

  65. إِنَّ عِبَادِي لَيۡسَ لَكَ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٞۚ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ وَكِيلٗا

    Open ayah 17:65

    “Lalle bayina ba ka da iko a kansu.” Kuma Ubangijinka Ya isa zama Wakili. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tuna wa Annabi (ﷺ) hassadar Iblisu ga Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da zurriyyarsa tun lokacin da Allah ya halicci Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarci mala’iku da su faɗi su yi sujjadar gaisuwa gare shi. Duk kuwa suka faɗi suka yi masa sujjada in ban da Iblis shi kaɗai ya ƙi yin sujjada saboda girman kai da hassada. Ya nuna ba zai taɓa yi wa Adamu sujjada ba saboda wai an halicce shi da taɓo shi kuma an yi halittarsa da wuta, don haka yake ganin ya fi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daraja. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Iblis ya fito ƙarara ya nuna hassadarsa da ƙiyayyarsa ga Annabi Adamu da zurriyyarsa, ya faɗa wa Allah a fili cewa, lalle wannan da ya karrama shi a kansa har ya umarce shi da yi masa sujjada, tabbas idan Allah ya jinkirta rayuwarsa zuwa tashin alƙiyama tabbas sai ya hallakar da ‘ya’yansa ya sa sun kauce wa hanya madaidaiciya in ban da ‘yan kaɗan waɗanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zaɓe su saboda ikhlasinsu ya tsare su daga sharrinsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) amshi roƙonsa da cewa, ya je shi da duk waɗanda suka zaɓi su bi shi su bar Allah, wutar Jahannama ce makomarsu, kuma ita ce cikakken sakamakon ayyukansu na saɓon Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Shaiɗan da ya je ya aikata duk abin da zai iya aikatawa wajen ɓatar da mabiyansa a duniya; ya yi wasa da hankalin duk wanda zai iya wasa da hankalinsa da muryarsa mai kira zuwa ga saɓon Allah. Hakanan ya umarce shi da ya tara musu gangaminsa na mayaƙansa barade mahaya dawakai da masu tafiya da ƙafa. Ya kuma umarce shi da ya yi tarayya da su cikin dukiyoyinsu ta hanyar sanya su su yi amfani da su inda ya saɓa wa shari’a, ya kuma yi tarayya da su a cikin ‘ya’yansu ta hanyar samun su ba tare da aure ba, da raɗa musu sunaye na maguzanci. Ya kuma yi ta musu alƙawura na ƙarya. Da man ba abin da Shaiɗan yake yi wa mabiyansa alƙawari da shi sai kawai ruɗi da ƙarairayi. An karɓo daga Iyadh ɗan Himar ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: “Na halicci bayina a bisa hanya miƙaƙƙiya ɗoɗar sai shaiɗanu suka karkatar da su daga kan addininsu, suka haramta musu abin da na halatta musu.” [Muslim #2865]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Da a ce idan ɗayanku zai sadu da iyalansa zai ce: “Ya Allah ka nesantar da mu daga Shaiɗan ka kuma nesantar da Shaiɗan daga abin da za ka arzuta mu.” Idan aka ƙaddara samun ɗa a tsakaninsu to ba zai cutar da shi ba.” [Bukhari #141 da Muslim #1434]. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan mutum ya zo shiga gidansa ya ambaci sunan Allah ko ya zo cin abincinsa ya ambaci sunan Allah, to Shaiɗan zai ce wa ‘yan’uwansa: “Ba ku sami wurin kwana ba, ba ku kuma sami abincin dare ba.” Idan kuwa ya shiga bai ambaci sunan Allah ba sai Shaiɗan ya ce: “Kun sami wurin kwana.” Idan ya zo cin abinci bai ambaci sunan Allah ba sai ya ce: “Kun sami wurin kwana da abincin dare.” [Muslim #2018]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Shaiɗan cewa, ba shi da wani iko na hallaka bayinsa na ƙwarai; shi ne zai kare su daga sharrinsa kuma ya ishe su abin dogaro.

  66. رَّبُّكُمُ ٱلَّذِي يُزۡجِي لَكُمُ ٱلۡفُلۡكَ فِي ٱلۡبَحۡرِ لِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا

    Open ayah 17:66

    Ubangijinku Shi ne wanda Yake tafiyar da jirgi a kan kogi don ku nemi falalarsa. Lalle Shi Ya kasance Mai rahama ne a gare ku.

  67. وَإِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فِي ٱلۡبَحۡرِ ضَلَّ مَن تَدۡعُونَ إِلَّآ إِيَّاهُۖ فَلَمَّا نَجَّىٰكُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ أَعۡرَضۡتُمۡۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ كَفُورًا

    Open ayah 17:67

    Idan kuma bala’i ya same ku a cikin kogi sai duk waɗanda kuke kira su ɓace (muku) sai Shi kawai; sannan lokacin da Ya tserar da ku zuwa sarari sai kuka bijire. Kai mutum ya tabbata butulu!

  68. أَفَأَمِنتُمۡ أَن يَخۡسِفَ بِكُمۡ جَانِبَ ٱلۡبَرِّ أَوۡ يُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ حَاصِبٗا ثُمَّ لَا تَجِدُواْ لَكُمۡ وَكِيلًا

    Open ayah 17:68

    Yanzu kun amince da cewa (Allah) ba zai rufto muku da wani ɓangare na tudu ba, ko kuma Ya aiko muku da jifa ta manya-manyan tsakuwoyi, sannan ba za ku sami wani mai tsaro ba?

  69. أَمۡ أَمِنتُمۡ أَن يُعِيدَكُمۡ فِيهِ تَارَةً أُخۡرَىٰ فَيُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ قَاصِفٗا مِّنَ ٱلرِّيحِ فَيُغۡرِقَكُم بِمَا كَفَرۡتُمۡ ثُمَّ لَا تَجِدُواْ لَكُمۡ عَلَيۡنَا بِهِۦ تَبِيعٗا

    Open ayah 17:69

    Ko kuma kun amince cewa ba zai mai da ku cikinsa ba (kogin) a karo na biyu, sai Ya aiko muku da ƙaƙƙarfar iska, sai Ya nutsar da ku saboda kafircewar da kuka yi, sannan kuma ba za ku sami wani mai nema muku haƙƙinku ba a wajenmu saboda (halakarwar da Muka yi muku)? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rahamar da ya yi wa bayinsa ta hanyar hore musu jiragen ruwa manya da ƙanana da kwale-kwale, ya kimsa musu ilimin ƙera su, ya kuma hore musu kogi wanda za su riƙa tafiya a kansa don su sami sauƙin tafiye-tafiyensu da safarar kayayyakin kasuwancinsu daga gari zuwa gari; daga ƙasa zuwa ƙasa. Wannan ba ƙaramar rahama ya yi wa bayinsa ba, domin shi mai yawan rahama ne gare su a koyaushe. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata rahamar tasa mai nuna Ɗayantakarsa wajen bauta, shi ne idan kafirai suka shiga ruwa suka ga wata halaka ta taso musu gadan-gadan sai su manta da duk wani abin bauta ba Allah ba, su koma suna kiran Allah shi kaɗai suna tsantsanta addu’a gare shi, kai ka ce da man can haka suke yi a rayuwarsu, don sun tabbatar allolinsu ba za su iya tsinana musu komai ba a lokacin. To idan Allah ya yaye musu damuwarsu ya tserar da su zuwa tudu sai su bijire masa, su koma ga halinsu na shirka da Allah da butulce wa ni’imominsa. Allah ya tabbatar da cewa, lalle ɗan’adam ya tabbata butulu ne. Sai kuma ya tunatar da su wani iko nasa da suke mantawa da shi lokacin da suka butulce masa bayan ya tserar da su, da cewa, yanzu ba sa jin tsoron Allah zai iya kifar da wani ɓangare na tudu da su, ko kuma ya aiko musu wasu manyan tsakwankwani daga sama su yi ta jifan su har su hallaka gaba ɗaya? To me ya sa suke zaton sai a ruwa ne kaɗai Allah zai iya hallaka su, don haka suke tsantsanta addu’a a gare shi a yayin da suke cikin ruwa? Me ya sa ba sa tunanin cewa yana da ikon ya hallaka su ta aiko musu azabarsa ta ƙarƙashin ƙasa ko ta sama ya hallaka su idan ya ga dama? Sannan Allah ya nuna musu cewa, idan ma suna zaton sai a ruwa ne kaɗai zai iya hallaka su, to ba sa tunanin cewa wata rana zai iya mayar da su cikin kogin a karo na biyu sai kuma ya aiko musu da wata iska mai tsananin gaske wadda za ta riƙa karya duk wani abu da ta biyo ta kansa, sai ya nutsar da su cikin ruwa da wannan iskar saboda butulcinsu da kafircinsu ba tare da sun sami wani mai tsaya musu ba don ya ƙwato su daga hallaka?

  70. ۞وَلَقَدۡ كَرَّمۡنَا بَنِيٓ ءَادَمَ وَحَمَلۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ كَثِيرٖ مِّمَّنۡ خَلَقۡنَا تَفۡضِيلٗا 

    Open ayah 17:70

    Haƙiƙa Mun girmama ‘yan’dam, Muka kuma ɗauke su (kan ababen hawa) na sarari da na ruwa, Muka kuma arzuta su daga tsarkakan (abubuwa) kuma Muka fifita su a kan wasu da yawa daga abin da Muka halitta nesa ba kusa ba. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falala da girmamawar da ya yi wa ‘yan’adam; ya yi musu kyakkyawar halitta, ya ba su hankali da ilimi, ya ma umarci mala’iku su yi wa ubansu Annabi Adamu sujjadar ban girma. Haka kuma ya hore musu ababen hawa na tudu, kamar dawakai da raƙuma da alfadarai da jakuna, da na ruwa, kamar jiragen ruwa manya da ƙanana. Ya kuma arzuta su da daɗaɗan abubuwan ci da na sha. Bugu da ƙari kuma Allah ya fifita ‘yan’adam a kan sauran halittunsa da dama. Don haka ya wajaba su gode masa bisa ga waɗannan ni’imomi masu yawa da ya yi musu, su guji yi masa butulci da saɓa masa.

  71. يَوۡمَ نَدۡعُواْ كُلَّ أُنَاسِۭ بِإِمَٰمِهِمۡۖ فَمَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَقۡرَءُونَ كِتَٰبَهُمۡ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلٗا

    Open ayah 17:71

    Ranar da za Mu kirawo kowanne (jinsin) mutane da shugabansu, sannan wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama to waɗannan za su karanta littafinsu, sannan ba za a zalunce su ko da gwargwadon zaren ƙwallon dabino ne ba.

  72. وَمَن كَانَ فِي هَٰذِهِۦٓ أَعۡمَىٰ فَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ أَعۡمَىٰ وَأَضَلُّ سَبِيلٗا

    Open ayah 17:72

    To wanda kuwa ya zamanto makaho a wannan (duniya), to shi a lahira ma makaho ne kuma mafi ɓacewa daga hanyar (gaskiya). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin ranar alƙiyama ranar da zai kirawo kowace al’umma da shugabanta wanda shi ne abin koyinsu a duniya. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A ranar alƙiyama mai shela zai yi shela ya ce, kowace al’umma ta bi abin da take bauta wa, sai duk masu bautar wanin Allah (kamar gumaka), su yi ta faɗawa cikin wuta, sai ya zamanto babu waɗanda za su rage sai masu bautar Allah shi kaɗai na kirkinsu da wanda ma ba na kirki ba tare da ɓirɓishin Ahlul Kitabi….” [Bukhari #4581 da Muslim #182]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda aka ba su littafinsu a hannunsu na dama, to za su karanta shi cikin farin ciki da murna, a ba su ladansu cikakke, ba za a tauye musu komai daga sakamakon ayyukansu ba, daidai da zaren cikin ƙwallon dabino. To amma wanda yake mai makantar zuciya ne a nan duniya ya kasa ganin gaskiya ya miƙa wuya, to shi kam a ranar alƙiyama ya fi tsananin makanta, ba zai taɓa gane hanyar shiga Aljanna ba, kamar yadda a duniya yake kasa gane hanyar shiriya.

  73. وَإِن كَادُواْ لَيَفۡتِنُونَكَ عَنِ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ لِتَفۡتَرِيَ عَلَيۡنَا غَيۡرَهُۥۖ وَإِذٗا لَّٱتَّخَذُوكَ خَلِيلٗا

    Open ayah 17:73

    Ba shakka kuwa sun kusa su fitine ka game da abin da Muka yi maka wahayinsa don ka ƙaga mana waninsa; da kuwa haka ta faru, to da lalle sun ɗauke ka masoyi.

  74. وَلَوۡلَآ أَن ثَبَّتۡنَٰكَ لَقَدۡ كِدتَّ تَرۡكَنُ إِلَيۡهِمۡ شَيۡـٔٗا قَلِيلًا

    Open ayah 17:74

    Ba don kuwa Mun tabbatar da kai (a kan umarninmu) ba, haƙiƙa da saura ƙiris ka ɗan karkata gare su.

  75. إِذٗا لَّأَذَقۡنَٰكَ ضِعۡفَ ٱلۡحَيَوٰةِ وَضِعۡفَ ٱلۡمَمَاتِ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ عَلَيۡنَا نَصِيرٗا

    Open ayah 17:75

    To da lalle kuwa Mun ɗanɗana maka ninkin (azabar) rayuwa da kuma ninkin (azabar) mutuwa, sannan ba za ka samu wani mai taimakon ka a kanmu ba.

  76. وَإِن كَادُواْ لَيَسۡتَفِزُّونَكَ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ لِيُخۡرِجُوكَ مِنۡهَاۖ وَإِذٗا لَّا يَلۡبَثُونَ خِلَٰفَكَ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 17:76

    Ba shakka sun kusa su tunzura ka daga ƙasar (ta Makka) don su fitar da kai daga cikinta; da kuwa sun aikata haka to da ba za su zauna (a cikinta) ba bayanka sai ɗan lokaci ƙanƙani.

  77. سُنَّةَ مَن قَدۡ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ مِن رُّسُلِنَاۖ وَلَا تَجِدُ لِسُنَّتِنَا تَحۡوِيلًا

    Open ayah 17:77

    (Wannan ita ce) irin al’adar waɗanda Muka aiko gabaninka daga manzanninmu; ba kuwa za ka sami canji a al’adarmu ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin kariya da kiyayewa da ya bai wa Annabi (ﷺ) lokacin da kafirai suke ta ƙoƙarin su karkatar da shi daga miƙaƙƙiyar hanya. Har su kafirai sun yi kusa su fitini Annabi (ﷺ) su karkatar da shi daga abin da Allah ya saukar masa na Alƙur’ani don ya ƙirƙiri wata magana wadda ta dace da son zuciyarsu ya jingina wa Allah. To Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa cewa, da a ce ya amince ya yi maganar da kafiran suke buƙata su ji daga bakinsa, to da lalle sun ɗauke shi babban masoyi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa, duk da haka ba don ya tabbatar masa da zuciyarsa ya cire masa tsananin kwaɗayin musuluntarsu ba, da ya ɗan karkata gare su ya biya musu wasu daga cikin buƙatunsu saboda tsananin yaudararsu da matuƙar kwaɗayinsa ga musuluntarsu. Allah ya tabbatar masa cewa, da ya kuskura ya yi hakan kuwa to da lalle ya ɗanɗana masa ninkin azaba a duniya, ya kuma yi masa ninkin azaba a lahira, sannan ba zai sami wani mai taimakonsa ba da zai kare shi daga azabar Allah. To amma Allah ya tsare shi ya tabbatar da zuciyarsa a kan gaskiya bai saurari buƙatarsu ya biya musu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafiran Makka suka yi ta tunzura Annabi (ﷺ) suna damun sa da cutarwa iri-iri domin su ga sun kore shi daga garin Makka. Allah ya tabbatar musu cewa, da sun kuskura sun kore shi daga wannan gari, to da su ma tasu ta ƙare, domin bayan sun fitar da shi to ba za su daɗe ba sai ɗan lokaci ƙanƙani, Allah zai aiko musu da azabarsa ta hallaka su. To amma ba su iya korar sa daga Makka ba har zuwa lokacin da Allah ya yi masa izinin ya fita ya yi hijira zuwa Madina. Wasu malaman tafsiri sun ce, kafiran Makka sun fitar da Annabi (ﷺ) daga garin Makka, don haka Allah ya nuna musu abin da ya tsoratar da su da shi na azaba, domin bayan hijirarsa zuwa Madina ba su wuce shekara ɗaya da rabi ba Allah ya kawo yaƙin Badar, suka fita yaƙi aka kashe manya-manyansu a can. Watau dai Allah ya nuna musu ƙarshensu kamar yadda ya yi musu alƙawari. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan ita ce al’adarsa ga manzannin da ya aiko gabanin Annabi (ﷺ). Duk sanda mutanen kowane manzo suka ƙaryata shi suka kore shi daga ƙasarsa, to Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu azabarsa ta hallaka su baki ɗaya. Wannan sunnar Allah ce da ba ta canjawa.

  78. أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمۡسِ إِلَىٰ غَسَقِ ٱلَّيۡلِ وَقُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِۖ إِنَّ قُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِ كَانَ مَشۡهُودٗا

    Open ayah 17:78

    Ka tsayar da salla lokacin zawalin rana zuwa duhun dare, da kuma karatun sallar Asuba. Lalle (lokacin) karatun sallar asuba ya kasance lokacin halartar (mala\'iku).

  79. وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَتَهَجَّدۡ بِهِۦ نَافِلَةٗ لَّكَ عَسَىٰٓ أَن يَبۡعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامٗا مَّحۡمُودٗا

    Open ayah 17:79

    Da daddare kuwa sai ka yi tsayuwar dare da shi (Alƙur’anin) ƙarin (daraja) ne gare ka, tare da ƙaunar Ubangijinka ya tashe ka a matsayin sha-yabo (watau matsayin mai ceto).

  80. وَقُل رَّبِّ أَدۡخِلۡنِي مُدۡخَلَ صِدۡقٖ وَأَخۡرِجۡنِي مُخۡرَجَ صِدۡقٖ وَٱجۡعَل لِّي مِن لَّدُنكَ سُلۡطَٰنٗا نَّصِيرٗا 

    Open ayah 17:80

    Kuma ka ce: “Ubangijina Ka shigar da ni mashiga ta gaskiya, kuma Ka fitar da ni mafita ta gaskiya, kuma Ka ba ni wata hujja mai taimakawa daga gare ka.”

  81. وَقُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَزَهَقَ ٱلۡبَٰطِلُۚ إِنَّ ٱلۡبَٰطِلَ كَانَ زَهُوقٗا

    Open ayah 17:81

    Kuma ka ce: “Gaskiya ta zo, ɓarna kuma ta watse. Lalle da ma can ita ɓarna ai watsattsiya ce.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sanar Annabi (ﷺ) lokutan salloli biyar ne, inda ya umarce shi da ya tsayar da salla lokacin da rana ta yi zawali, watau ta gushe daga tsakiyar samaniya. A nan sallar Azzahar da La’asar sun shiga ke nan. Sannan da lokacin da dare ya lulluɓe da duhunsa; wannan kuma ya ƙunshi sallar Magariba da sallar Isha’i. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci sallar alfijir, watau sallar Asuba. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mala’ikun dare da mala’ikun rana suna haɗuwa a lokacin sallar asuba.” [Bukhari #4717 da Muslim #649]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da tashi cikin wani yanki na dare ya yi sallar nafila. Wannan nafilar a wurinsa ƙarin daraja ce gare shi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ), wacce salla ce ta fi falala bayan sallar farilla? Sai ya ce: “Sallar dare.” [Muslim #1163]. Yin hakan zai sanya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tashi Annabinsa a ranar alƙiyama a matsayin babban mai ceton mutane wanda na farko da na ƙarshe za su gode kuma su yaba masa. Ya tabbata a ingantattun hadisai masu yawa cewa, a ranar alƙiyama bayan an tashi halittu gaba ɗayansu domin yi musu hisabi, za a matso da rana dab da kawunansu, gumi ya kai har wajen kunnuwansu, don haka sai su tafi wurin annabawa ɗaya bayan ɗaya suna neman su cece su daga wannan matsanancin hali, su roƙa musu Allah ya gaggauta yi musu hisabi. Za su fara ne daga Annabi Adamu sannan Annabi Nuhu sannan Annabi Ibrahimu sannan Annabi Musa sannan Annabi Isa; kowanne daga cikinsu zai nuna musu abin ya fi ƙarfinsa, ya gabatar da hanzarinsa, har dai inda za su zo ga Annabi Muhammadu (ﷺ), sai ya faɗa musu cewa wannan matsayi nasa ne, sai ya tafi ya yi sujjada a ƙarƙashin Al’arshi ya yi wa Allah yabo da kirari wanda bai taɓa yi masa irinsa ba. Sai a ce masa ya ɗaga kansa ya roƙi kome yake so, za a ba shi, ya nemi ceton da yake so za a yi masa. Ya ɗago kansa ya ce: “Ya Ubangiji, al’ummata, ya Ubangiji, al’ummata.” Daga nan Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi damar shigar da wasu daga cikin al’ummarsa gidan Aljanna.” [Dubi, Bukhari #3340 da Muslim #194]. Wannan shi ne matsayin na sha-yabo da Allah zai ba shi ranar alƙiyama. Sai kuma ya umarce shi da ya riƙa roƙon Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya shige da ficensa duka su zama ɗa’a ne ga Allah da neman yardarsa. Ya kuma roƙe shi ya ba shi bayyananniyar hujja mai ƙarfi wadda za ta taimaka masa ya ci nasara a kan maƙiyansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya tabbatar wa mushirikai cewa, gaskiya fa ta zo, watau addinin Musulunci, kuma alƙawarin Allah ya tabbata na ba da nasara ga Annabi (ﷺ) da muminai; ƙarya kuma ta watse, watau shirka da kafirci. Lalle tabbas ƙarya kam ba ta da wurin zama sai watsewa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: A lokacin da Annabi (ﷺ) ya shiga Makka (watau ranar Fat\'hu Makka), ya samu gumaka har ɗari uku da sittin a kafe a jikin Ka’aba, sai ya riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya yana zungurin su da sandarsa suna faɗuwa shi kuma ya riƙa karanta wannan ayar: “Gaskiya ta zo, ƙarya kuma ta gushe, lalle da man ƙarya ta tabbata mai gushewa ce;” da kuma faɗar Allah: “Gaskiya ta zo, ƙarya ba za ta iya farar da komai ba kuma ba za ta iya maimaita shi ba.” [ Suratu Saba ’, aya ta 49] [Bukhari #4720 da Muslim #1781].

  82. وَنُنَزِّلُ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِ مَا هُوَ شِفَآءٞ وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَلَا يَزِيدُ ٱلظَّٰلِمِينَ إِلَّا خَسَارٗا

    Open ayah 17:82

    Kuma daga Alƙur’ani Muna saukar da abin da yake shi waraka ne da kuma rahama ga muminai; ba kuma zai ƙari azzalumai (da komai) ba sai taɓewa.

  83. وَإِذَآ أَنۡعَمۡنَا عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ أَعۡرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ كَانَ يَـُٔوسٗا

    Open ayah 17:83

    Kuma idan Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya kuma juya kwiɓinsa; idan kuwa sharri ne ya same shi sai ya zama mai yawan yanke ƙauna.

  84. قُلۡ كُلّٞ يَعۡمَلُ عَلَىٰ شَاكِلَتِهِۦ فَرَبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَنۡ هُوَ أَهۡدَىٰ سَبِيلٗا

    Open ayah 17:84

    Ka ce: “Kowa ya yi aiki bisa hanyarsa sai dai Ubangijinku (Shi ne) Mafi sanin wanda ya fi shiriya a kan madaidaiciyar hanya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falala da albarkar da ke cikin littafinsa Alƙur’ani da cewa, ya ƙunshi waraka ga zukata daga cututtuka irin na kafirci da munafunci da jahilci, kuma waraka ne ga jiki idan an yi ruƙuya da shi. Kuma rahama ne ga muminai masu aiki da koyarwarsa, amma su kafirai babu abin da Alƙur’ani yake ƙara musu sai hallaka da taɓewa, domin sauraron sa yana ƙara baƙanta musu rai, yana nisanta su da shi har su ƙaryata shi su bijire masa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wani mummunan hali na ɗan’adam, shi ne idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa wata ni’ima ta lafiya ko dukiya ko ‘ya’ya, sai ya bijire masa ya ƙi godiya gare shi ta hanyar yi masa ɗa’a, sai ma ya ƙara nisa da Ubangijinsa yana girman kai. Amma kuma da zarar wata rashin lafiya ta same shi ko talauci sai ya zamanto mai tsananin ɗebe ƙauna daga rahamar Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya bayyana cewa, kowane mutum yana aikinsa ne a kan hanyarsa wadda ta yi daidai da halayensa, watau idan yana cikin mutanen ƙwarai sai aikinsa ya kasance ga Allah kaɗai; idan kuwa yana cikin taɓaɓɓu to babu aikin da ya dace da shi sai na taɓaɓɓu irinsa. Allah kuma ya tabbatar da cewa, shi ne ya fi kowa sanin wanda ya fi zamantowa a kan miƙaƙƙiyar hanyar shiriya.

  85. وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنۡ أَمۡرِ رَبِّي وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 17:85

    Suna kuma tambayar ka game da ruhi. Ka ce da su: “Shi ruhi yana daga al’amarin Ubangijina, ba abin da aka ba ku na ilimi sai ɗan kaɗan.”

  86. وَلَئِن شِئۡنَا لَنَذۡهَبَنَّ بِٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ بِهِۦ عَلَيۡنَا وَكِيلًا

    Open ayah 17:86

    Kuma tabbas da Mun ga dama lalle da Mun tafiyar da abin da Muka yo maka wahayi, sannan ba za ka sami wani mataimaki ba a kanmu (game) da shi.

  87. إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّ فَضۡلَهُۥ كَانَ عَلَيۡكَ كَبِيرٗا

    Open ayah 17:87

    Sai dai rahama daga Ubangijinka. Lalle falalarsa gare ka ta zamo mai girma ce.

  88. قُل لَّئِنِ ٱجۡتَمَعَتِ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأۡتُواْ بِمِثۡلِ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لَا يَأۡتُونَ بِمِثۡلِهِۦ وَلَوۡ كَانَ بَعۡضُهُمۡ لِبَعۡضٖ ظَهِيرٗا

    Open ayah 17:88

    Ka ce da su: “Wallahi da mutane da aljannu sun haɗu kan su kawo irin wannan Alƙur’anin, to ba za su zo da irinsa ba, ko da kuwa wasu sun zamanto suna taimaka wa wasu.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana yadda kafirai suka riƙa yi wa Annabi (ﷺ) tambayoyi irin na ƙalubale ba na neman fahimta ba, har ta kai sun tambaye shi mene ne ruhi (watau rai)? Abin da sun san shi ɓoyayyen abu ne wanda babu mai iya siffanta yadda yake. Duk da cewa akwai abubuwa da yawa waɗanda ba su sani ba kuma suna da buƙatar su san su, amma ba su yi tambaya a kansu ba. Ruwayoyi biyu sun tabbata wajen tantance masu yin irin wannan tambayar. <b>Ta farko </b>: An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata rana muna tafiya tare da Manzon Allah (ﷺ) a cikin wata gona a Madina, yana dogarawa da reshen dabino, sai wasu Yahudawa suka zo wucewa, sai wani daga cikinsu ya ce: “Ku yi masa tambaya game da ruhi.” Sai wani ya ce: “Me zai sa ku yi masa tambaya?” Sai wani ya ce: “Kada fa ya fuskance ku da abin da ba zai yi muku daɗi ba.” Sai suka ce: “Ku yi masa tambaya game da ruhi.” Sai suka yi wa Annabi wannan tambayar. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi shiru bai ba su amsa ba.” Ibnu Mas’ud ya ce: “Sai na fahimci wahayi ne ake yi masa, sai na tsaya a inda nake. To lokacin da wahayin ya sauko sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta wannan ayar ta 85.” [Bukhari #4721 da Muslim #2794]. Wannan ruwayar ta nuna ayar ta sauka ne a Madina. <b>Ruwaya ta biyu </b>: An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ƙuraishawa sun ce wa Yahudawa: “Ku ba mu wani abu da za mu tambayi wannan mutumin?” Sai suka ce musu: “Ku tambaye shi game da ruhi.” Sai suka tambayi Annabi (ﷺ) game da shi, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar. Sai Yahudawa suka ce: “Mu an ba mu ilimi mai yawa, domin an ba mu Attaura, wanda kuwa aka ba shi Attaura ai an ba shi alheri mai yawa.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da aya ta 109 a Suratul Kahafi .” [Tirmizi #3140 da Ahmad #2309]. Wannan ruwayar tana nuna an saukar da ayar a Makka ne. Yana yiwuwa kuma an saukar da ayar ne sau biyu. [Dubi, Fathul Bari , juzu’i na 8,shafi na 401]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya bayyana musu cewa, babu wanda ya san haƙiƙanin ruhi sai Allah kaɗai, kuma duk irin yawan ilimin da suke ganin suna da shi to ɗan kaɗan ne idan an kwatanta shi da ilimin Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Ubayyu ɗan Ka’ab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya faɗa a ƙissar Annabi Musa da Khadhir (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa: “…sai wani tsuntsu ya sauka a kan gefen jirgin ruwansu, sai ya tsattsagi ruwa da bakinsa sau ɗaya ko sau biyu, sai Khadhir ya ce: “Ya Musa, ilimina da iliminka idan an kwatanta shi da ilimin Allah to bai wuce kamar abin da tsuntsun nan ya tsattsaga daga kogin nan ba.” [Bukhari #122]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Alƙur’ani da ya yi wahayinsa ga Annabi (ﷺ) wata rahama ce gare shi da kuma bayin Allah. Shi ne kuma mafi girman ni’ima da ya yi masa, domin falalarsa gare shi mai girma ce. Don haka wanda ya yi masa wannan falalar yana da ikon ya gusar masa da ita, sannan ba zai sami mai dawo masa da ita ba, ko wani wakili da zai nema masa alfarmar a dawo masa da ita daga Allah ba. Amma saboda rahamar Allah gare shi bai gusar masa da ita ba, ya ci gaba da tsare ta. Lalle falalar Allah ga Manzonsa mai girma ce da ya zaɓe shi a matsayin Manzonsa kuma cikamakin annabawansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ƙalubalanci Larabawa, da sauran mutane, har da aljannu duka su kawo kwatankwacin Alƙur’ani idan suna iyawa. Allah ya tabbatar da cewa, da a ce duk mutane da aljannu za su haɗu domin su zo da wani abu kamar Alƙur’ani mai balaga da fasaha da kyan zubi da azanci irin nasa, to ba za su iya kawo kamarsa ba har abada, ko da kuwa sashensu zai taimaki sashe a kai.

  89. وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖ فَأَبَىٰٓ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورٗا

    Open ayah 17:89

    Kuma haƙiƙa Mun sarrafa wa mutane kowanne irin misali a cikin wannan Alƙur’ani, sai dai yawancin mutane sun ƙi (komai) sai kafircewa.

  90. وَقَالُواْ لَن نُّؤۡمِنَ لَكَ حَتَّىٰ تَفۡجُرَ لَنَا مِنَ ٱلۡأَرۡضِ يَنۢبُوعًا 

    Open ayah 17:90

    Suka kuma ce: “Ba za mu yi imani da kai ba har sai ka ɓuɓɓugo mana da idon ruwa daga ƙasa.

  91. أَوۡ تَكُونَ لَكَ جَنَّةٞ مِّن نَّخِيلٖ وَعِنَبٖ فَتُفَجِّرَ ٱلۡأَنۡهَٰرَ خِلَٰلَهَا تَفۡجِيرًا

    Open ayah 17:91

    “Ko kuma ya zamana kana da wata gona ta dabinai da inabi, sai kuma ka ɓuɓɓugo da ƙoramu ta tsakiyarta su kwarara sosai.

  92. أَوۡ تُسۡقِطَ ٱلسَّمَآءَ كَمَا زَعَمۡتَ عَلَيۡنَا كِسَفًا أَوۡ تَأۡتِيَ بِٱللَّهِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ قَبِيلًا

    Open ayah 17:92

    “Ko kuma ka rufto da sama a kanmu, kamar yadda ka riya, ta faɗo yanki-yanki, ko kuma ka zo da Allah da kuma mala’iku (mu gan su) ido-da-ido!

  93. أَوۡ يَكُونَ لَكَ بَيۡتٞ مِّن زُخۡرُفٍ أَوۡ تَرۡقَىٰ فِي ٱلسَّمَآءِ وَلَن نُّؤۡمِنَ لِرُقِيِّكَ حَتَّىٰ تُنَزِّلَ عَلَيۡنَا كِتَٰبٗا نَّقۡرَؤُهُۥۗ قُلۡ سُبۡحَانَ رَبِّي هَلۡ كُنتُ إِلَّا بَشَرٗا رَّسُولٗا

    Open ayah 17:93

    “Ko kuma ya zamana kana da wani gida na zinari, ko kuma ka hau sama, ba kuwa za mu amince da hawan naka ba har sai ka saukar mana da wani littafi da za mu karanta shi.” Ka ce (da su): “Tsarki ya tabbata ga Ubangijina, ni ba kowa ba ne face mutum Manzo.”

  94. وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَبَعَثَ ٱللَّهُ بَشَرٗا رَّسُولٗا

    Open ayah 17:94

    Kuma babu abin da ya hana kafirai su yi imani lokacin da shiriya ta zo musu, sai cewar da suka yi: “Yanzu Allah ne zai aiko mutum a matsayin manzo?”

  95. قُل لَّوۡ كَانَ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَلَٰٓئِكَةٞ يَمۡشُونَ مُطۡمَئِنِّينَ لَنَزَّلۡنَا عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَلَكٗا رَّسُولٗا

    Open ayah 17:95

    Ka ce: “Da mala’iku ne suke tafiya a natse a bayan ƙasa, to da lalle Mun aiko musu mala’ika daga sama a matsayin manzo.”

  96. قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

    Open ayah 17:96

    Ka ce: “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku: Lalle Shi ya zamanto Masani ne ga bayinsa, kuma Mai ganin (abin da suke aikatawa) ne.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya sarrafa ayoyin Alƙur’ani ga mutane ta fuskoki daban-daban: Wani lokaci ta hanyar wa’azi; wani lokaci ta hanyar kwaɗaitarwa; wani lokaci kuwa ta hanyar tsoratarwa; wani sa’in ta hanyar ba da misalai da sauran hanyoyin bayani iri-iri da Alƙur’ani ya zo da su. To amma duk da haka yawancin mutane sun ƙi yin imani sai ƙaryata shi da kafirce masa suke yi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta mana irin yadda kafirai suka riƙa bijiro wa Manzon Allah (ﷺ) da wasu buƙatu na mu’ujizoji iri-iri suna son sai ya nuna musu su kafin su yi imani da shi. Sun buƙaci mu’ujizoji har guda shida ne. <b>Ta farko </b>: Suka ce ba za su yi imani da shi ba har sai ya ɓuɓɓugo musu da ruwa daga ƙasar Makka mai cike da duwatsu, ruwan kuma ya riƙa gudana ba ƙafewa. <b>Ta biyu </b>: Ko kuma ya mallaki wani gidan gona mai cike da shuke-shuke kuma ya kwararo da ƙorama a cikinsa mai yawan ruwa wadda za ta shayar da shuke-shuken ciki. <b>Ta uku </b>: Ko ya rufto musu wani yanki na sama kamar yadda yake riyawa cewa, in sun ƙi yin imani azabar Allah za ta same su. <b>Ta huɗu </b>: Ko kuma ya kawo musu Allah da mala’iku su gan su ido-da-ido su kuma ba da shaidar cewa, abin da ya zo musu da shi gaskiya ne. <b>Ta biyar </b>: Ko ya mallaki wani ƙanƙararren gida na zinare. <b>Ta shida </b>: Ko ya tattaka ya hau sama. Suka ce ko da ma ya hau saman ba za su gaskata shi ba har sai ya sauko musu da wani littafi a rubuce daga Allah da za su karanta cewa, shi Manzon Allah ne a cikinsa. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya mayar musu da martani cewa, tsarki ya tabbata ga Allah; shi fa ba wani ba ne face mutum kuma Manzo kamar sauran manzannin Allah, ba shi da ikon ya kawo musu abu ɗaya daga cikin abubuwan nan shida da suka nema. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin da ya hana kafirai su yi imani da Allah da Manzonsa su yi aiki da abin da ya aiko shi da shi wanda kuwa bai wuce cewarsu: Yanzu Allah ne zai aiko mutum a matsayin manzonsa!? Watau me ya hana ya aiko musu mala’ika a matsayin manzonsu? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzon Allah ya mayar musu da martani mai sauƙi na cewa, da a ce mala’iku ne suke tafiya a natse a bayan ƙasa kamar yadda mutane suke tafiya, to da tabbas ya aiko musu da manzo mala’ika irin jinsinsu, domin shi ne zai iya fahimtar da su saƙon da aka aiko shi da shi. A nan ba zai zama da hikima ba a ce ya aiko musu da manzo mutum. To haka lamarin yake game da mutane; ashe mutum ne ya dace ya zamo manzo a gare su ba mala’ika ba. A ƙarshe dai Allah ya sake umartar Annabi (ﷺ) da ya tabbatar wa kafirai cewa, Allah ya isa ya zama shaida tsakaninsa da su don tabbatar da cewa, shi Manzo ne zuwa gare su kuma ya isar musu da saƙon da aka aiko shi da shi, domin Allah mai cikakken sanin halin da bayinsa suke ciki ne kuma yana ganin komai nasu na sarari da na ɓoye.

  97. وَمَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُمۡ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِهِۦۖ وَنَحۡشُرُهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ عُمۡيٗا وَبُكۡمٗا وَصُمّٗاۖ مَّأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ كُلَّمَا خَبَتۡ زِدۡنَٰهُمۡ سَعِيرٗا

    Open ayah 17:97

    Wanda kuwa Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye; wanda kuwa Ya ɓatar to ba za ka sami wani mai taimakon su ba in ban da Shi; za kuma Mu tashe su ranar alƙiyama a kan fuskokinsu suna makafi, kurame, bebaye; makomarsu Jahannama; duk sanda ta lafa sai Mu ƙara musu ƙunarta.

  98. ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُم بِأَنَّهُمۡ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَقَالُوٓاْ أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا وَرُفَٰتًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ خَلۡقٗا جَدِيدًا

    Open ayah 17:98

    Wannan ne sakamakonsu saboda lalle sun kafirce wa ayoyinmu, suka kuma ce: “Yanzu idan muka zama ƙasusuwa kuma rududdugaggu, anya kuwa za a tashe mu a sabuwar halitta?”

  99. ۞أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يَخۡلُقَ مِثۡلَهُمۡ وَجَعَلَ لَهُمۡ أَجَلٗا لَّا رَيۡبَ فِيهِ فَأَبَى ٱلظَّٰلِمُونَ إِلَّا كُفُورٗا

    Open ayah 17:99

    Yanzu ba sa gani cewa Allah wanda Ya halicci sammai da ƙasa Mai iko ne a kan Ya halicci irinsu? Ya kuma sanya musu wani lokaci wanda ba kokwanto a cikinsa, sai azzalumai suka ƙi (yin imani) sai kafircewa.

  100. قُل لَّوۡ أَنتُمۡ تَمۡلِكُونَ خَزَآئِنَ رَحۡمَةِ رَبِّيٓ إِذٗا لَّأَمۡسَكۡتُمۡ خَشۡيَةَ ٱلۡإِنفَاقِۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ قَتُورٗا 

    Open ayah 17:100

    Ka ce da su: “Idan da ku ne kuka mallaki taskokin rahamar Ubangijina to lalle da kun riƙe su ƙam-ƙam don tsoron ciyarwa. Mutum kuwa ya tabbata mai tsananin rowa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shiriya da ɓata duk suna hannunsa; idan ya ga dama ya shiryar da bawansa, to wannan shi ne shiryayye na gaske. Wanda kuwa ya ɓatar da shi, to ban da shi babu mai iya shiryar da shi kuma babu mai iya jiɓintar al’amarinsa ya taimaka masa ya kare shi daga azabar Allah ranar da zai tattaro su ana jan su a kan fuskokinsu ba sa gani, ba sa iya magana, ba sa ji. Makomarsu a ranar wutar Jahannama ce; duk sanda ta lafa Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara rura ta da su, haka za a yi ta azabtar da su ba ƙaƙƙautawa. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya tambayi Annabi (ﷺ) cewa,: “Ya Annabin Allah, ta yaya za a tashi kafiri a kan fuskarsa ranar alƙiyama?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Yanzu ashe wanda ya ba shi damar tafiya a kan ƙafafunsa a duniya ba zai iya tafiyar da shi a kan fuskarsa ba a ranar alƙiyama?” Sai Ƙatadatu mai ruwayar hadisin ya ce: “E, na rantse da Allah zai iya.” [Bukhari #4760 da Muslim #2806]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan sakamako da zai yi wa kafirai bai zalunce su ba; zai yi musu shi ne saboda sun kafirce wa ayoyinsa da manzanninsa sun ƙaryata zuwan ranar alƙiyama wanda duk manzanni suka zo da bayaninsa a littattafai da Allah ya saukar suka kuma ba da labarinsa, amma sai kafirai suka nuna Allah (Mai tsarki da daukaka) ba zai iya tayar da matattu ba, har da cewa, yanzu su idan suka mutu suka zama ƙasusuwa suka ratattake, ta yaya za a sake dawo da halittarsu sabuwa? Suka nuna wannan sam ba zai taɓa faruwa ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, ba sa ganin cewa shi ne ya halicci sammai da ƙasa, waɗanda halittarsu ta fi ta mutane girma? To ta yaya kuma za a ce ba zai iya halittar mutane kamarsu ba? Duk kuwa wanda zai iya halittar babban abu kamar sama da ƙasa, to babu shakka zai iya halittar ƙaramin abu da bai kai shi ba. Kawai dai Allah ya sanya wa faruwar haka wani lokaci ne da babu makawa sai ya faru. To amma duk da waɗannan hujjoji ƙarfafa kuma bayyanannu azzalumai sun ƙi komai sai kafirci saboda zaluncinsu da son zuciya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata mummunar ɗabi’a ta ɗan’adam, watau tsananin rowa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa kafirai cewa, da su ne suke riƙe da taskokin rahamar Allah wadda ba ta ƙarewa, da sun riƙe ta ƙam-ƙam sun hana kowa, don tsoron talauci idan suna bayar da ita. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan ɗabi’a ce ta ɗan’adam, watau tsananin rowa. Sai dai mumini shi ne zai bayar saboda kwaɗayin samun lada a wurin Allah.

  101. وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ تِسۡعَ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۖ فَسۡـَٔلۡ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ إِذۡ جَآءَهُمۡ فَقَالَ لَهُۥ فِرۡعَوۡنُ إِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰمُوسَىٰ مَسۡحُورٗا 

    Open ayah 17:101

    Kuma haƙiƙa Mun bai wa Musa ayoyi tara bayyanannu; to ka tambayi Banu Isra’ila lokacin da ya zo musu, sai Fir’auna ya ce da shi: “Lalle ni fa ina tsammanin kai Musa sihirtacce ne!”

  102. قَالَ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَآ أَنزَلَ هَٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰفِرۡعَوۡنُ مَثۡبُورٗا 

    Open ayah 17:102

    (Musa) ya ce: “Haƙiƙa ka sani ba wanda ya saukar da waɗannan (ayoyin) sai Ubangijin sammai da ƙasa don su zama hujjoji, kuma lalle ina tsammanin kai Fir’auna halakakke ne.”

  103. فَأَرَادَ أَن يَسۡتَفِزَّهُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ فَأَغۡرَقۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ جَمِيعٗا 

    Open ayah 17:103

    Sai ya yi nufin ya girgiza su a ƙasar (ta Masar don ya fitar da su daga ciki), to sai Muka nutsar da shi da duk wanda yake tare da shi gaba ɗaya.

  104. وَقُلۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ لِبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱسۡكُنُواْ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ ٱلۡأٓخِرَةِ جِئۡنَا بِكُمۡ لَفِيفٗا 

    Open ayah 17:104

    Muka kuma ce da Banu Isra’ila: “Ku zauna a ƙasar (ta Falasɗinu), to idan lokacin alƙiyama ya zo za Mu tattaro ku gaba ɗaya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi Muhammadu (ﷺ) ba shi kaɗai ne wanda Allah ya ba wa ayoyi kuma mutanensa suka ƙaryata shi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ayoyi har tara; kowace aya ta isa ta zama hujja a kan manzancinsa. Ayoyin su ne: Sanda da farin hannu da tawayar amfanin gona da ruwa mai kwarara da fari da ƙwarƙwata da kwaɗi da kuma jini. To amma duk da haka mutanensa suka ƙaryata shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da cewa, ya tambayi Yahudawa abin da ya faru lokacin da ya saukar wa kakanninsu da waɗannan ayoyi, amma sai Fir’auna ya ce masa shi fa yana zatonsa wanda aka yi wa sihiri ne. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar masa da martani da cewa, Fir’auna ya tabbatar a ransa cewa, ba wani ne ya saukar da ayoyin nan tara ba sai Ubangijin sammai da ƙasa; ya saukar da su ne domin su zama shaida a kan Kaɗaitakarsa da gaskiyar manzancin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sannan Annabi Musa ya tabbatar wa da Fir’auna cewa, shi halakakke ne hasararre. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Fir’auna ya yi nufin azabtar da Annabi Musa da jama’arsa ya kore su daga ƙasar Masar, amma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka shi tare da sojojinsa gaba ɗaya a cikin ruwa. Sai kuma bayan Allah ya hallaka Fir’auna da rundunarsa, ya umarci Banu Isra’ila cewa, su je su zauna a ƙasar Sham; idan lokacin tashin alƙiyama ya zo zai tara su gaba ɗaya domin yi musu hisabi.

  105. وَبِٱلۡحَقِّ أَنزَلۡنَٰهُ وَبِٱلۡحَقِّ نَزَلَۗ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا مُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا 

    Open ayah 17:105

    Kuma da gaskiya Muka saukar da shi (Alƙur’ani), kuma da gaskiya ya sauko. Ba Mu kuma aiko ka ba sai mai yin albishir,0 mai kuma gargaɗi.

  106. وَقُرۡءَانٗا فَرَقۡنَٰهُ لِتَقۡرَأَهُۥ عَلَى ٱلنَّاسِ عَلَىٰ مُكۡثٖ وَنَزَّلۡنَٰهُ تَنزِيلٗا 

    Open ayah 17:106

    Kuma Mun saukar da Ƙur’ani, Mun bayyana shi don ka karanta wa mutane shi a sannu a hankali, Mun kuma saukar da shi daki-daki.

  107. قُلۡ ءَامِنُواْ بِهِۦٓ أَوۡ لَا تُؤۡمِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهِۦٓ إِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ يَخِرُّونَۤ لِلۡأَذۡقَانِۤ سُجَّدٗاۤ 

    Open ayah 17:107

    Ka ce da su: “Ko ku yi imani da shi ko kada ku yi imani da shi (duk ɗaya ne).” Lalle waɗanda aka bai wa ilimi gabaninsa (Yahudu da Nasara) idan ana karanta musu shi suna faɗuwa da fuskokinsu suna masu sujjada.

  108. وَيَقُولُونَ سُبۡحَٰنَ رَبِّنَآ إِن كَانَ وَعۡدُ رَبِّنَا لَمَفۡعُولٗا 

    Open ayah 17:108

    Suna kuma cewa: “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, lalle alƙawarin Ubangijinmu tabbas ya zamanto abin aikatawa ne.”

  109. وَيَخِرُّونَ لِلۡأَذۡقَانِ يَبۡكُونَ وَيَزِيدُهُمۡ خُشُوعٗا۩ 

    Open ayah 17:109

    Suna kuma faɗuwa da fuskokinsu suna kuka, Yana kuma ƙara musu ƙasƙantar da kai.

  110. قُلِ ٱدۡعُواْ ٱللَّهَ أَوِ ٱدۡعُواْ ٱلرَّحۡمَٰنَۖ أَيّٗا مَّا تَدۡعُواْ فَلَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَلَا تَجۡهَرۡ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتۡ بِهَا وَٱبۡتَغِ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلٗا 

    Open ayah 17:110

    Ka ce: “Ku kira (sunan) Allah ko ku kira (sunan) Arrahaman ; kowanne kuka kira to shi Yana da sunaye ne mafiya kyau.” Kada kuma ka ɗaga muryarka da (karatun) sallarka, kada kuma ka yi shi a ɓoye, ka nemi tsaka-tsakin wannan.

  111. وَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلِيّٞ مِّنَ ٱلذُّلِّۖ وَكَبِّرۡهُ تَكۡبِيرَۢا

    Open ayah 17:111

    Kuma ka ce, “Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗa ba, kuma ba Shi da wani abokin tarayya a cikin mulki, kuma ba Shi da wani mataimaki don kare masa ƙasƙanci.” Kuma ka girmama shi girmamawa ta sosai. A ayoyin ƙarshe na wannan Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya saukar da Alƙur’ani wanda yake ƙunshe da gaskiya, kuma a bisa gaskiya ya sauka, watau Allah ya tsare shi bai bari wata ɓarna ko rashin gaskiya ya gauraya da shi ba, domin mala’ika Jibrilu ne ya sauko da shi. Sannan Allah ya tabbatar da cewa, ya aiko Annabi ne da wannan Alƙur’anin domin ya zama mai albishir da gidan Aljanna ga masu tsoron Allah, mai gargaɗi da wuta ga kafirai da masu saɓon Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, ya saukar da Alƙur’ani zuwa ga Annabi (ﷺ) kaɗan-kaɗan kuma daki-daki don ya karanta wa mutane hukunce-hukuncensa gwargwadon buƙatarsu, a cikin shekara ashirin da uku. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa kafirai cewa, ko su yi imani da Alƙur’ani ko kada su yi imani da shi duka ɗaya ne, domin shi dai Alƙur’ani tabbas gaskiya ne, Allah ya saukar da shi, da ma kuma ya yi nuni game da shi a littattafan da ya saukar a baya, don haka ya bayyana musu cewa, lalle mutanen kirki masu ilimi daga cikin ma’abota littafi waɗanda suke riƙe da littattafansu ba su canja su ba, idan sun ji ana karanta musu Alƙur’ani sukan faɗi ƙasa da fuskokinsu suna sujjada ga Allah, domin godiya gare shi da ya nufe su da riskar zamanin wannan Manzo da aka ba shi Alƙur’ani, watau Annabi Muhammadu (ﷺ). A sujjadarsu suna tsarkake Allah (Mai tsarki da daukaka) daga duk wani abu da mushirikai suke siffanta shi da shi wanda bai dace da shi ba. Suna tabbatar da cewa, duk abin da Allah ya yi alƙawari a kansa ta harshen annabawa da manzanni lalle sai ya tabbata. Suna faɗuwa da fuskokinsu suna kuka domin ƙasƙantar da kansu ga Allah da imani da kuma gaskata littafinsa da Manzonsa (ﷺ). Kuma yana ƙara musu ƙasƙantar da kai da miƙa wuya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa mushirikai waɗanda suka ce ba su yarda da sunan Allah (Arrahman) ba cewa, su kira sunansa (Allah) ko su kira sunansa (Arrahman) duk ɗaya ne babu bambanci a tsakaninsu, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) yana da sunaye mafiya kyau, don haka babu wani sunansa wanda bai dace a kira shi da shi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana Annabi (ﷺ) ya ɗaga muryarsa da ƙarfi lokacin da yake salla yana karanta Alƙur’ani, kada kuma ya ɓoye karatunsa duka ta yadda sahabbansa ba za su iya jin me yake karantawa kwata-kwata ba. Ya umarce shi da yi karatunsa tsakatsaki, bai ɗaga muryarsa da ƙarfi ba, kuma bai ɓoye ta duka ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wannan ayar ta sauka ga Manzon Allah ne lokacin yana ɓuya shi da sahabbansa a Makka. Ya kasance a lokacin idan yana jan sahabbansa salla sai ya ɗaga muryarsa da ƙarfi wajen karatun Alƙur’ani, idan mushirikai suka jiyo shi sai su zagi Alƙur’anin su zagi wanda aka saukarwa da shi su zagi wanda ya sauko da shi, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar.” [Bukhari #4722 da Muslim #446]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi yabo da kirari ga Allah wanda ba shi da wani ɗa kuma ba shi da wani abokin tarayya, a mulkinsa shi kaɗai ne, bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, kuma ba shi da wani kini ko kishiya, don haka shi ba ƙasƙantacce ne ba wanda zai buƙaci mataimaki ko wani waziri ko mai ba shi shawara. Shi ne mahaliccin kowa da komai, mai gudanar da komai shi kaɗai yadda ya ga dama ba tare da abokin tarayya ba. Sannan ya umarce shi ya girmama shi iyakar girmamawa ta hanyar yabonsa da siffanta shi da siffofinsa maɗaukaka da tsarkake shi daga abin da kafirai azzalumai suke siffanta shi da su.