الكهف
Al-Kahf
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَىٰ عَبۡدِهِ ٱلۡكِتَٰبَ وَلَمۡ يَجۡعَل لَّهُۥ عِوَجَاۜ
Open ayah 18:1Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya saukar wa da Bawansa Littafi, bai kuma sanya masa wata karkata ba.
قَيِّمٗا لِّيُنذِرَ بَأۡسٗا شَدِيدٗا مِّن لَّدُنۡهُ وَيُبَشِّرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرًا حَسَنٗا
Open ayah 18:2Daidaitacce ne, don ya yi gargaɗi game da azaba mai tsanani daga gare Shi (wato Allah), ya kuma yi wa muminai waɗanda suke aiki nagari albishir cewa suna da lada kyakkyawa.
مَّٰكِثِينَ فِيهِ أَبَدٗا
Open ayah 18:3Madawwama a cikinsa har abada.
وَيُنذِرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗا
Open ayah 18:4Ya kuma gargaɗi waɗanda suka ce Allah Yana da ɗa.
مَّا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٖ وَلَا لِأٓبَآئِهِمۡۚ كَبُرَتۡ كَلِمَةٗ تَخۡرُجُ مِنۡ أَفۡوَٰهِهِمۡۚ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِبٗا
Open ayah 18:5Ba su da wani ilimi game da shi (wannan zance) kuma iyayensu ma ba su da (ilimi game da shi). Kalmar da take fitowa daga bakunansu ta yi girma. Ba abin da suke faɗa sai ƙarya.
فَلَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ إِن لَّمۡ يُؤۡمِنُواْ بِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَسَفًا
Open ayah 18:6To ko mai yiwuwa ne za ka kashe kanka da baƙin ciki, in ba su yi imani da wannan zancen ba (watau Alƙur\'ani).
إِنَّا جَعَلۡنَا مَا عَلَى ٱلۡأَرۡضِ زِينَةٗ لَّهَا لِنَبۡلُوَهُمۡ أَيُّهُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗا
Open ayah 18:7Lalle Mu Mun sanya abin da yake bayan ƙasa ya zama ado a gare ta, don (kuma) Mu jarraba su, wane ne daga cikinsu ya fi kyakkyawan aiki?
وَإِنَّا لَجَٰعِلُونَ مَا عَلَيۡهَا صَعِيدٗا جُرُزًا
Open ayah 18:8Lalle kuma Mu za Mu mai da abin da yake kanta (ya zama) turɓaya ƙeƙasasshiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da godiya da yabo da kirari ga Zatinsa don ya tabbatar da cewa, shi ne ya fi kowa cancantar duk wata sifa ta ɗaukaka da kamala. Ya bayyana cewa, shi ne wanda ya saukar wa da bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ) Alƙur’ani wanda ba shi da wata tawaya ta kowace fuska. Ya sanya shi littafi ne daidaitacce wanda babu tufka-da-warwara a cikinsa domin ya tsoratar da kafirai da shi game da wata azaba mai tsanani daga Allah da take jiran su a lahira idan ba su yi imani da Allah da Manzonsa ba. Hakanan kuma ya yi wa muminai waɗanda suka yi ayyuka na ƙwarai albishirin samun wani kyakkyawan sakamako da babu kamarsa, wanda shi ne gidan Aljanna. Za su zauna har abada a cikin wannan sakamako ba zai yanke musu ba. Sannan kuma ya gargaɗi kafirai waɗanda suke cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana da ɗa, su ne Yahudu da Nasara har ma da mushirikan Larabawa masu cewa mala’iku ‘ya’yan Allah ne mata. Ya bayyana cewa masu irin wannan ƙagen ga Allah ba su da wani ilimi ko wani dalili da suka dogara da shi a kan da’awarsu. Kai har ma iyayensu da suke koyi da su ba su da wani ilimi a kan wannan lamari da suke da’awa. Allah ya bayyana cewa, magana mummuna da take fitowa daga bakunansu ta yi matuƙar muni. Ba komai suke furtawa ba kuma sai ƙarya zunzurutunta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da lallashin Manzonsa (ﷺ) wanda rashin yin imanin kafirai yake matuƙar damunsa. Ya nuna masa cewa, kada ya kashe kansa da yawan damuwa da yake sakawa a ransa don mutanensa sun ƙi yin imani da Alƙur’ani, domin shiriyarsu ba a hannunsa take ba. Sai kuma ya bayyana masa cewa, duk wani abu da ya halitta a doron ƙasa ya yi shi ne don jarrabawa don ya tantance waɗanda suka fi kyakkyawan aiki daga cikin bayinsa. Kuma daga ƙarshe duk wani ƙyale-ƙyale da yake bayan ƙasa zai mayar da shi turɓaya ƙeƙasasshiya wadda babu wani tsiro a kanta. Don haka ya daina damuwa da abin da zai gani ko zai ji daga maƙiyansa domin kowa daga ƙarshe zai koma ne ga Allah ya yi wa kowa hisabi a kan abin da ya aikata.
أَمۡ حَسِبۡتَ أَنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡكَهۡفِ وَٱلرَّقِيمِ كَانُواْ مِنۡ ءَايَٰتِنَا عَجَبًا
Open ayah 18:9Shin ka yi tsammanin cewa lalle Mutanen Kogo da Raƙimu sun kasance daga ayoyinmu masu ban mamaki?
إِذۡ أَوَى ٱلۡفِتۡيَةُ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ فَقَالُواْ رَبَّنَآ ءَاتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحۡمَةٗ وَهَيِّئۡ لَنَا مِنۡ أَمۡرِنَا رَشَدٗا
Open ayah 18:10Lokacin da samarin nan suka fake a Kogon, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu rahama daga gare Ka, Ka kuma tanadar mana shiriya cikin lamarinmu.
فَضَرَبۡنَا عَلَىٰٓ ءَاذَانِهِمۡ فِي ٱلۡكَهۡفِ سِنِينَ عَدَدٗا
Open ayah 18:11Sai Muka sanya (shamaki) a kan kunnuwansu (suka yi barci) shekaru masu yawa a cikin Kogon.
ثُمَّ بَعَثۡنَٰهُمۡ لِنَعۡلَمَ أَيُّ ٱلۡحِزۡبَيۡنِ أَحۡصَىٰ لِمَا لَبِثُوٓاْ أَمَدٗا
Open ayah 18:12Sannan Muka tashe su don Mu san wane ne daga ƙungiyoyin nan biyu (masu saɓani game da lamarin samarin) ya fi kiyayewa da tsawon zamaninsu? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yin shimfiɗa ne a kan labarin mutanen kogo, yana tabbatar wa da Annabi (ﷺ) cewa, labarinsu yana ƙunshe da abin mamaki kamar yadda yake zato. Duk kuwa da cewa akwai wasu abubuwa da suka fi shi ban mamaki kamar halittar sammai da ƙasa da sassaɓawar rana da wata. Mutanen kogo wasu samari ne ‘ya’yan sarakunan Rumawa da manyan gari waɗanda suka lura da cewa, abin da mutanensu suke yi na bautar wanin Allah da yin sujjada ga gumaka ɓarna ce ba daidai ne ba, don haka sai suka ware kansu waje guda suka riƙa bautar Allah shi kaɗai ba tare da haɗa shi da komai ba. Suna cikin haka ne wasu suka sami labarinsu sai suka garzaya wajen Sarkinsu suka bayyana masa abin da samarin nan suke ciki. Wannan Sarki mai suna Daƙayanusa wani azzalumin mutum ne. Yayin da ya sami labarinsu sai ya aika aka kawo su gabansa, ya umarce su da lalle su kafirce wa Allah su dawo kan bautar gumakansu, amma waɗannan samari suka taurare masa. Allah kuwa ya ƙara musu ƙarfin imani. Wannan ya sa sarkin ya yi yunƙurin hallaka su gaba ɗayansu, sai suka gudu suka shiga wani kogo suka ɓuya a cikinsa. Suka roƙi Allah da ya ba su wata rahama daga gare shi ya kuma tanadar musu shiriya cikin lamarinsu. To a nan ne Allah ya karɓi roƙonsu ya saka musu wani dogon barci wanda suka share shekaru masu yawa suna yin sa har zuwa wani lokaci da Allah ya ga damar tayar da su don ya tabbatar wa da mutane gaskiyar yiwuwar tashin matattu domin hisabi kuma ya bayyana wane ne a cikin ƙungiyoyi biyu masu saɓani a cikin lamarinsu ya fi kiyaye lissafin shekarun da suka yi suna barci. Game da adadinsu bayani zai zo a aya ta 22, amma game da sunayensu babu wani abin da ya inganta a kan hakan. Sannan sanin sunayensu ba wani abu ne mai muhimmanci ba. <b>Arraƙimu </b> kuwa da Allah ya ambata a nan malamai sun yi saɓani wajen tantance shi: • Wasu sun ce shi ne dutsen da kogon da samarin suka ɓoye yake jiki. • Wasu kuma sun ce shi ne allon da aka rubuta sunayensu a kai. • Amma kuma wasu malamai sun ce Arraƙimu shi ne labarin mutanen nan uku da suka shiga kogon dutse ya rufe da su, kowane ɗaya daga cikinsu ya yi tawassuli da wani aikin ƙwarai da ya taɓa yi don Allah, ya roƙi Allah da shi, har Allah ya buɗe musu ƙofar wannan kogon suka kuɓuta daga halaka. Imamul Bukhari ya zaɓi wannan ra’ayi na ƙarshe. Imamu Ahmad (#18417) da Ɗabarani (Al-Ma’jamu’ul Kabir , juzu’i na 2, shafi na 206) sun ruwaito da kyakkyawan isnadi daga An-Nu’uman ɗan Bashiru (Allah ya kara masa yarda) ya ce, ya ji Manzon Allah (ﷺ) ya ambaci Arraƙimu sai ya ce: “Lalle an sami wasu mutane su uku da suka kasance a cikin kogo sai dutse ya gangaro ya rufe musu ƙofar kogon....” Har zuwa ƙarshen hadisin. Game da addinin da samarin suke bi, wasu malamai sun ce suna bin addinin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne. To amma wannan ra’ayi yana da rauni, domin da a ce addinin Annabi Isa suke bi da Yahudawa ba su ɗauki al’amarinsu da muhimmanci ba. Sai dai sun rayu ne gabanin zuwan Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
نَّحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ نَبَأَهُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّهُمۡ فِتۡيَةٌ ءَامَنُواْ بِرَبِّهِمۡ وَزِدۡنَٰهُمۡ هُدٗى
Open ayah 18:13Mu ne za Mu ba ka labarinsu da gaskiya. Lalle su samari ne da suka yi imani da Ubangijinsu, Muka kuwa ƙara musu shiriya.
وَرَبَطۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ إِذۡ قَامُواْ فَقَالُواْ رَبُّنَا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَن نَّدۡعُوَاْ مِن دُونِهِۦٓ إِلَٰهٗاۖ لَّقَدۡ قُلۡنَآ إِذٗا شَطَطًا
Open ayah 18:14Muka kuma ɗaure zukatansu lokacin da suka tsaya suka ce: “Ubangijinmu Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa; ba za mu bauta wa wani abin bauta ba in ban da Shi; idan muka yi haka kuwa to haƙiƙa mun faɗi ƙarya.
هَٰٓؤُلَآءِ قَوۡمُنَا ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗۖ لَّوۡلَا يَأۡتُونَ عَلَيۡهِم بِسُلۡطَٰنِۭ بَيِّنٖۖ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا
Open ayah 18:15“Waɗannan mutanenmu ne da suka riƙi wasu alloli ba Shi ba; me ya hana ba su zo musu da wata hujja mabayyaniya (kan haka) ba? To ba wanda ya fi zalunci fiye da wanda ya yi wa Allah ƙarya.
وَإِذِ ٱعۡتَزَلۡتُمُوهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ فَأۡوُۥٓاْ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ يَنشُرۡ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَيُهَيِّئۡ لَكُم مِّنۡ أَمۡرِكُم مِّرۡفَقٗا
Open ayah 18:16“Tun da kun ƙaurace musu tare da abin da suke bauta wa sai Allah, to sai ku tare a kogon, Ubangijinku zai yalwata muku rahamarsa ya kuma shirya muku hanyar rayuwa mai sauƙi ga al’amuranku.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shiga fayyace ƙissar mutanen kogo, inda ya bayyana cewa, zai ba wa Annabi (ﷺ) labarinsu da gaskiyar da babu kokwanto a cikinta, da cewa, su samari ne waɗanda suka yi imani da Ubangijinsu suka yarda da shi kaɗai ne abin bauta suka kuma dage da yi masa ɗa’a, sai ya ƙara musu shiriya da tabbata a kan gaskiya. Ya kuma ƙarfafi zukatansu da imani suka samu juriya da haƙuri da rashin tsoro ko fargaba, yayin da suka tsaya gaban sarkinsu kafiri, azzalumi, suka bayyana masa imaninsu da Allah mahaliccin sammai da ƙasa tare da tabbatar masa cewa, ba za su ƙara yarda su bauta wa wani ba shi ba, domin idan har sun yi haka to sun faɗi maganar ƙarya ke nan ba gaskiya ba. A kan haka waɗannan samari suka bar jama’arsu suka koma waje ɗaya suna tattaunawa tsakaninsu da junansu cewa, mutanensu sun riƙi wasu gumaka suna bauta musu ba Allah ba, duk da cewa kuwa ba su da wata hujja bayyananniya a kan haka. Suka tabbatar wa juna cewa babu azzalumi kamar wanda ya ƙaga wa Allah ƙarya ya ce yana da abokin tarayya. Suka zartar da cewa, yanzu kam tun da sun ƙaurace wa mutanensu sun bar abin da suke bauta wa ba Allah ba, to kamata ya yi su gudu su ɓuya a cikin kogo, da fatan Allah zai shimfiɗa musu rahamarsa ya tsare su daga abokan gabarsu, ta yadda ba za su gan su ba, kuma ya shirya musu abin da duk za su buƙata na rayuwa a cikin wannan kogon, su sami hutu da yalwar rayuwa ba tare da sun koma cikin mutanensu ba.
۞وَتَرَى ٱلشَّمۡسَ إِذَا طَلَعَت تَّزَٰوَرُ عَن كَهۡفِهِمۡ ذَاتَ ٱلۡيَمِينِ وَإِذَا غَرَبَت تَّقۡرِضُهُمۡ ذَاتَ ٱلشِّمَالِ وَهُمۡ فِي فَجۡوَةٖ مِّنۡهُۚ ذَٰلِكَ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِۗ مَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ وَلِيّٗا مُّرۡشِدٗا
Open ayah 18:17(Sai) kuma ka ga rana idan za ta ɓullo tana kauce wa kogonsu ta ɓangaren dama, idan kuma za ta faɗi sai ta riƙa kauce musu ta ɓangaren hagu, su kuwa suna tsakiyarsa. Wannan yana daga ayoyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye, wanda kuwa Ya ɓatar to ba za ka sami wani majiɓinci da zai shirye shi ba.
وَتَحۡسَبُهُمۡ أَيۡقَاظٗا وَهُمۡ رُقُودٞۚ وَنُقَلِّبُهُمۡ ذَاتَ ٱلۡيَمِينِ وَذَاتَ ٱلشِّمَالِۖ وَكَلۡبُهُم بَٰسِطٞ ذِرَاعَيۡهِ بِٱلۡوَصِيدِۚ لَوِ ٱطَّلَعۡتَ عَلَيۡهِمۡ لَوَلَّيۡتَ مِنۡهُمۡ فِرَارٗا وَلَمُلِئۡتَ مِنۡهُمۡ رُعۡبٗا
Open ayah 18:18Za kuma ka zaci a farke suke alhali kuwa suna bacci ne. Muka kuma riƙa juya su ta ɓarin dama da kuma ta ɓarin hagu; karensu kuwa ya shimfiɗa ƙafafunsa na gaba a mashigar kogon. Da abin ka leƙa su ne to lalle da ka fita a guje, lalle kuma da ka cika da tsoron su. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana irin tanadin da ya yi wa samarin nan a wannan kogon, ya samar musu wani yanayi da babu abin da zai cutar da su. Rana idan ta fito tana karkace wa kogonsu ta ɓangaren dama, idan kuma ta zo faɗuwa sai ta karkace masa ta ɓangaren hagu. Malam Ibnu Kasir ya ce: “Wannan ya nuna cewa ƙofar shiga kogon tana ɓangaren hagu ne, domin Allah ya bayyana cewa idan rana ta shigo cikinsa lokacin hudowarta tana karkace masa ta ɓangaren dama, watau inuwarsa tana janyewa ta dama, saboda duk sa’adda za ta ƙara yin sama to haskenta yana ƙara raguwa har ya kai lokacin da zai gushe gaba ɗaya yayin da rana ta yi zawali. Don haka ne ma Allah ya ce: ‘Idan ta zo faɗuwa tana kauce musu ta ɓangaren hagu.’ Watau dai rana tana shiga kogonsu ne ta hagun ƙofarsa, watau nahiyar gabas. Wannan ya tabbatar da abin da muka ambata...” Su kuma samarin suna tsakiyar kogon a kwance suna samun iskar shaƙa yadda ya kamata. Da haka Allah ya tsare gangar jikinsu da tufafinsu ba abin da ya same su tsawon shekarun da suka yi suna barci a wannan kogo. Allah ya bayyana cewa duk waɗannan abubuwa da ya yi suna cikin ayoyinsa ne masu nuna cikar ikonsa a kan komai. Don haka duk wanda ya shiryar da shi ga hanyar shiriya shi ne shiryyaye, wanda kuwa ya ɓatar da shi to ba za ka sami wani mai shiryar da shi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata baiwar da ya yi wa waɗannan samari lokacin da suke kwance suna barci a wannan kogo. Watau shi ne yadda idan mutum ya gan su sai ya zaci a farke suke ba barci suke yi ba, domin suna yin barcin zomo ne, idanuwansu duka a buɗe suke. Kuma Allah ya riƙa jujjuya su dama da hagu don kada ƙasa ta ci jikkunansu da tufafinsu. Shi kuma karensu da yake tare da su yana kwance ya shimfiɗa ƙafafunsa a gaban mashigar kogon. A daidai wannan lokaci da a ce mutum zai leƙa su ya yi arba da su to da ya fita a guje ya kuma cika da tsoron su, saboda kwarjini da Allah ya zuba musu, domin ba su ƙarin kariya daga mutane.
وَكَذَٰلِكَ بَعَثۡنَٰهُمۡ لِيَتَسَآءَلُواْ بَيۡنَهُمۡۚ قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ كَمۡ لَبِثۡتُمۡۖ قَالُواْ لَبِثۡنَا يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۚ قَالُواْ رَبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثۡتُمۡ فَٱبۡعَثُوٓاْ أَحَدَكُم بِوَرِقِكُمۡ هَٰذِهِۦٓ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ فَلۡيَنظُرۡ أَيُّهَآ أَزۡكَىٰ طَعَامٗا فَلۡيَأۡتِكُم بِرِزۡقٖ مِّنۡهُ وَلۡيَتَلَطَّفۡ وَلَا يُشۡعِرَنَّ بِكُمۡ أَحَدًا
Open ayah 18:19Kamar haka Muka tashe su don su riƙa tambayar junansu. Wani mai tambaya daga cikinsu ya ce: “Mene ne tsawon zamanku (a nan)?” Suka ce: “Mun yi zaman yini ɗaya ne ko kuma rabin yini.” (Sannan kuma) suka ce: “Ubangijinku ne Ya fi sanin tsawon zaman da kuka yi, sai ku aiki ɗayanku da wannan kuɗin naku cikin gari, sai ya duba ya ga wanne irin abinci ne ya fi tsarki, to sai ya zo muku da abin da za ku ci da shi (kuɗin), kuma ya yi taka-tsantsan kada wani ya shaida ku.
إِنَّهُمۡ إِن يَظۡهَرُواْ عَلَيۡكُمۡ يَرۡجُمُوكُمۡ أَوۡ يُعِيدُوكُمۡ فِي مِلَّتِهِمۡ وَلَن تُفۡلِحُوٓاْ إِذًا أَبَدٗا
Open ayah 18:20“Lalle idan suka yi galaba a kanku to za su jefe ku ko kuma su mai da ku cikin addininsu, to shi ke nan ba za ku rabauta ba har abada.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda ya nuna abubuwan mamakinsa game da waɗannan samari, to hakanan kuma ya tashe su daga dogon barcinsu don su yi wa juna tambaya a kan tsawon lokacin da suka share suna barci. Sai wasu daga cikinsu suka ce, ai sun yi barci ne kawai na yini guda ko ma rabin yini, domin sun shiga wannan kogo ne da safe sai kuma suka farka da yamma. To amma kuma sai wasu daga cikinsu suka ce Allah ne dai kawai ya san tsawon lokacin da suka share suna wannan wuri, don haka su mayar masa da al’amarinsu su dawo da tunaninsu a kan abin da ya fi musu muhimmanci, shi ne nemo abin da za su ci, domin suna cikin matuƙar yunwa. Don haka sai suka yi shawarar su aika ɗaya daga cikinsu ya shiga gari ya nemo musu abinci, suka ba shi kuɗin azurfa da ke tare da su lokacin da suka shiga kogo. Suka kuma jaddada masa cewa, ya tabbatar ya sayo musu abinci na halal, kada ya kawo musu abin da bai halatta ba. Suka kuma ja kunnensa da cewa, ya yi taka-tsantsan wajen shiga wannan garin da wajen fitowa da wajen mu’amalarsa da abokan cinikinsa, kada ya bari wani ya gane inda suka ɓoye, domin idan mutanen garin suka fahimci inda suka ɓoye to za su zo su kama su su je su jefe su har su mutu, ko kuma su tursasa musu komawa ga gurɓataccen addininsu wanda Allah ya so su da shiriya suka bar shi zuwa ga addinin gaskiya. Suka tabbatar wa da juna cewa idan kuwa har suka yarda suka koma tsohon addininsu to ba za su rabauta ba har abada a duniya da lahira. Daga nan wannan ɗan aike ya fita ya nufi hanyar shiga gari; to tun daga nan ya fara ganin canje-canje waɗanda bai san da su ba lokacin da suka fita daga gari. Mamaki ya rufe shi na ganin gagarumin canji. Ta yaya ya faru a ɗan ƙanƙanin lokaci irin wannan? Bai san cewa bayan fitarsu an yi al\'ummu daban-daban sun zo sun shuɗe, komai na garin ya canja daga yadda ya san shi a baya. Yana isowa ƙofar shiga gari kuma ya ga alamun Musulunci a ƙofar garin. Ya sake ruɗewa. Ya shiga kasuwa ya miƙa kuɗinsa domin a ba shi gurasa. Da mai gurasa ya ga wannan tsohon kuɗin sai ya tambaye shi ina ya sami irin wannan kuɗin? Nan take rigima ta kaure tsakaninsu, domin mai gurasa ya zargi wannan saurayi da ya tsinci wata tsohuwar taska ce ta kuɗi, don haka lalle sai ya nuna masa inda ya samo ta. Rigima ta kai su har gaban Sarki, inda daga ƙarshe aka gano cewa, wannan saurayi ɗaya ne daga cikin samarin da tarihi ya nuna sun taɓa fita daga wannan garin sun guje wa wani azzalumin sarki wanda ya nemi sai sun yi kafirci. Daga nan Sarkin ya yi umarni a tasa wannan saurayi gaba har sai ya kai su kogon da ‘yan’uwansa suke ciki. Da suka isa bakin kogo ya roƙi jama’a da kada su shiga domin za su tsoratar da ‘yan’uwansa; su bari shi ya shiga don ya sanar da su abin da ake ciki. Yana shiga kuwa sai suka ji shiru bai sake fitowa ba. Waɗannan samari sun roƙi Allah ya karɓi rayukansu a wannan lokacin. Allah kuwa ya karɓi addu’arsu ya karɓi rayukansu gaba ɗaya. [Dubi, Ibnu Hajar, Taghliƙut Ta’aliƙ , Juzu’i na 4, shafi na 246] Daga Ibnu Abbas (Allah ya kara masa yarda).
وَكَذَٰلِكَ أَعۡثَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ لِيَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَأَنَّ ٱلسَّاعَةَ لَا رَيۡبَ فِيهَآ إِذۡ يَتَنَٰزَعُونَ بَيۡنَهُمۡ أَمۡرَهُمۡۖ فَقَالُواْ ٱبۡنُواْ عَلَيۡهِم بُنۡيَٰنٗاۖ رَّبُّهُمۡ أَعۡلَمُ بِهِمۡۚ قَالَ ٱلَّذِينَ غَلَبُواْ عَلَىٰٓ أَمۡرِهِمۡ لَنَتَّخِذَنَّ عَلَيۡهِم مَّسۡجِدٗا
Open ayah 18:21Kamar haka kuwa Muka nuna wa (mutanen nasu) su don su san cewa lalle alƙawarin Allah gaskiya ne, kuma ita alƙiyama babu kokwanto a cikinta, kuma ka tuna lokacin da su (mutanen) suke ta jayayya a tsakaninsu game da al’amarinsu (watau samarin); sai (wasu daga cikinsu) suka ce: “Ku tayar da gini a kansu (wanda zai toshe ƙofar kogon).” Ubangijinsu Shi Ya fi sanin lamarinsu. Waɗanda suka yi rinjaye kan al’amarinsu suka ce: “Lalle tabbas za mu yi masallaci a kansu (watau a kan ƙabarinsu).” A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda ya nuna abubuwan mamaki game da waɗannan samari har suka share tsawon shekaru suna barci sannan daga ƙarshe ya tashe su, to haka kuma ya nuna su ga mutanen garinsu domin ya nuna musu cewa, ranar alƙiyama gaskiya ce, kuma zai tashi halittu duk, da gangar jikinsu da rayukansu. Sai kuma ya bayyana cewa, mutane sun yi ta saɓani a kan sha’aninsu bayan sun tabbatar da mutuwarsu. Suka shiga tattaunawa da juna a kan abin da ya kamata su yi wa waɗannan bayin Allah. Sai suka kasu gida biyu: Wasu suka ce kawai a gina katanga a ƙofar kogonsu domin ba su kariya da tsaro, a bar al’amarinsu ga Allah, shi ne ya fi kowa sanin halinsu, domin yanayinsu ya nuna su na musamman ne a wurinsa. Sai masu iko a garin suka ce lalle sai sun gina masallaci a wannan wurin domin ibada, su kuma riƙa tunawa da su da girmamawa.
سَيَقُولُونَ ثَلَٰثَةٞ رَّابِعُهُمۡ كَلۡبُهُمۡ وَيَقُولُونَ خَمۡسَةٞ سَادِسُهُمۡ كَلۡبُهُمۡ رَجۡمَۢا بِٱلۡغَيۡبِۖ وَيَقُولُونَ سَبۡعَةٞ وَثَامِنُهُمۡ كَلۡبُهُمۡۚ قُل رَّبِّيٓ أَعۡلَمُ بِعِدَّتِهِم مَّا يَعۡلَمُهُمۡ إِلَّا قَلِيلٞۗ فَلَا تُمَارِ فِيهِمۡ إِلَّا مِرَآءٗ ظَٰهِرٗا وَلَا تَسۡتَفۡتِ فِيهِم مِّنۡهُمۡ أَحَدٗا
Open ayah 18:22(Wasu) suka riƙa cewa su uku ne na huɗunsu shi ne karensu; (wasu) kuma suna cewa biyar ne na shidansu ne karensu don lalube cikin duhu; (wasu) kuma suna cewa su bakwai ne na takwas ɗinsu kuma karensu ne. Ka ce (da su): “Ubangiji Shi Ya fi sanin yawansu, ba wanda ya san lamarinsu sai ‘yan kaɗan.” To kada ka yi jayayya game da (al’amarinsu) sai dai a kan abin da yake a fili, kada kuma ka nemi fatawar ɗaya daga cikinsu game da su (samarin).
وَلَا تَقُولَنَّ لِشَاْيۡءٍ إِنِّي فَاعِلٞ ذَٰلِكَ غَدًا
Open ayah 18:23Kada kuma ka ce da kowane abu: “Lalle zan aikata wannan gobe.”
إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ وَٱذۡكُر رَّبَّكَ إِذَا نَسِيتَ وَقُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَهۡدِيَنِ رَبِّي لِأَقۡرَبَ مِنۡ هَٰذَا رَشَدٗا
Open ayah 18:24Sai dai (tare da cewa): \'In sha Allah \'; ka kuma ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: “Ina fatan Ubangijina Ya nuna mini abin da ya fi wannan zama shiriya.” A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana saɓanin da ma’abota littafi suka yi game da adadin yawan mutanen kogo, inda aka samu wasu suka yi ta faɗar maganganu barkatai ba tare da wani ilimi ba. Sun kasu gida uku: Wasu suka ce su uku ne karensu na huɗu. Wasu kuma suka ce su biyar ne karensu na shida. Allah ya ce duk waɗannan maganganu guda biyu shaci-faɗi ne. Sai kuma ya ambaci kashi na uku masu cewa, adadinsu bakwai ne karensu ne na takwas. Sai ya ƙara da umartar Annabi (ﷺ) ya faɗa wa mutane cewa, Ubangijinsu ne mafi sanin adadinsu, waɗanda suka san adadinsu a cikin mutane kaɗan ne. Don haka jayayya a kan haka ba ta da wani amfani ko maslaha. Saboda haka ya hana Manzonsa ya yi jayayya game da lamarin waɗannan samari, sai fa jayayyar da take bisa hujja da ilimi. Haka kuma ya hana shi neman fatawar wani daga cikin ma’abota littafi a kan sha’anin waɗannan samari. Allah kuma ya sake yin wani hani ga Annabi (ﷺ) har da sauran al’ummarsa da cewa, kada ya furta zai yi wani abu gobe sai ya ce ‘in sha Allah ’, sannan idan ya manta ya ambaci Allah; yin haka zai gusar masa da wannan mantuwar ya tuna masa abin da ya manta; ya kuma umarce shi da ya sa ran zai shiryar da shi hanya mafi kusa ga shiriya a kan wannan lamari. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Annabi Sulaiman ɗan Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce: “Zan kewaya matana su ɗari a wannan dare, kowace ɗaya daga cikinsu za ta haifi yaro wanda zai yi yaƙi don Allah. Sai aka ce masa ya ce ‘in sha Allah’ , sai bai faɗa ba. Sai ya kewaya su gaba ɗayansu, to amma babu wadda ta haihu daga cikinsu sai guda ɗaya wadda ita ma rabin mutum ta haifo (watau ɓari ta yi).” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Da a ce ya ce ‘in sha Allah ’, to da rantsuwarsa ba ta karye ba, da kuma ya cimma buƙatarsa.” [Bukhari #2819 da Muslim #1654]
وَلَبِثُواْ فِي كَهۡفِهِمۡ ثَلَٰثَ مِاْئَةٖ سِنِينَ وَٱزۡدَادُواْ تِسۡعٗا
Open ayah 18:25Sun kuwa zauna cikin kogonsu shekara ɗari uku, suka kuma ƙara tara.
قُلِ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثُواْۖ لَهُۥ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ أَبۡصِرۡ بِهِۦ وَأَسۡمِعۡۚ مَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِيّٖ وَلَا يُشۡرِكُ فِي حُكۡمِهِۦٓ أَحَدٗا
Open ayah 18:26Ka ce: “Allah ne Mafi sanin tsawon zaman da suka yi.” Gaibun da yake sammai da ƙasa nasa ne. Wa ya yi gani irin nasa, wa kuma ya yi ji irin nasa (watau Allah). Ba su da wani majiɓinci in ban da Shi; ba Ya kuma tarayya da wani a cikin hukuncinsa.
وَٱتۡلُ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِن كِتَابِ رَبِّكَۖ لَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَن تَجِدَ مِن دُونِهِۦ مُلۡتَحَدٗا
Open ayah 18:27Kuma ka karanta abin da aka yiwo maka wahayi da shi daga littafin Ubangijinka: Ba mai canja kalmominsa; ba kuma za ka sami wata mafaka ba in ba ta wurinsa ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana adadin shekarun da As’habul Kahfi suka yi suna barci a cikin kogon. Sun zauna a cikinsa tsawon shekara ɗari uku a lissafin shekarar shamsiyya , watau lissafi da fitowar rana da faɗuwarta. Amma a lissafin shekarar ƙamariyya watau a lissafin ganin wata, sun ƙara shekara tara. Duk shekara ɗari a lissafin ƙamariyya tana ƙaruwa da shekara uku ne a kan lissafin shamsiyya . Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tabbatar da cewa, Allah ne ya fi kowa sanin yawan shekarun da samarin suka yi a cikin kogon, domin shi ne ya san gaibun sammai da ƙasa, babu wanda ya kai shi gani da ji; yana ganin komai yana kuma jin komai. Shi ne kuma ya ba da labarin lissafin adadin shekarunsu a kogo don haka ba wanda za a ƙara saurara bayan shi. Kuma ban da Allah babu wani mai jiɓintar al’amarinsu, ba ya haɗa wani a cikin hukuncinsa, shi kaɗai ne ɗaya tilo. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi aiki da Alƙur’anin a aka saukar masa daga Ubangijinsa sau-da-ƙafa, domin duk bayanan da ya ƙunsa da labarai gaskiya ne, haka kuma hukuncinsa adalci ne. Don haka ya riƙe shi ya yi aiki da shi, babu wani mai canza kalmomin Allah ya kawo wasu a madadinsu, kuma ba zai sami wata mafaka ba in ba daga gare shi ba.
وَٱصۡبِرۡ نَفۡسَكَ مَعَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ رَبَّهُم بِٱلۡغَدَوٰةِ وَٱلۡعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجۡهَهُۥۖ وَلَا تَعۡدُ عَيۡنَاكَ عَنۡهُمۡ تُرِيدُ زِينَةَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَا تُطِعۡ مَنۡ أَغۡفَلۡنَا قَلۡبَهُۥ عَن ذِكۡرِنَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ وَكَانَ أَمۡرُهُۥ فُرُطٗا
Open ayah 18:28Ka kuma haƙurƙurtar da kanka (da zama) tare da waɗanda suke bauta wa Ubangijinsu safe da yamma suna neman yardarsa; kar kuma ka kawar da idanuwanka daga gare su kana neman adon rayuwar duniya; kada kuma ka bi wanda Muka shagaltar da zuciyarsa daga ambatonmu ya kuma bi son ransa, wanda kuma al’amarinsa ya zama a sukurkuce.
وَقُلِ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَن شَآءَ فَلۡيُؤۡمِن وَمَن شَآءَ فَلۡيَكۡفُرۡۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلظَّٰلِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمۡ سُرَادِقُهَاۚ وَإِن يَسۡتَغِيثُواْ يُغَاثُواْ بِمَآءٖ كَٱلۡمُهۡلِ يَشۡوِي ٱلۡوُجُوهَۚ بِئۡسَ ٱلشَّرَابُ وَسَآءَتۡ مُرۡتَفَقًا
Open ayah 18:29Kuma ka ce: “Gaskiya daga Ubangijinku take;” to wanda ya ga dama ya yi imani, wanda kuma ya ga dama sai ya kafirta. Lalle kam Mun tanadar wa azzalumai wata wuta wadda katangarta ta kewaye su. Idan kuma suka nemi taimako to za a taimake su ne da ruwa kamar tafasasshen mai da zai riƙa toye fuskoki. Tir da wannan abin shan, makoma kuma ta munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya haƙure wa kansa da zama tare da talakawan sahabbansa waɗanda suke bautar Allah safe da yamma suna masu tsarkake ayyukansu gare shi. Kar ya kuskura idanunsa su ƙetare su su hango wasu waɗanda zai ga dacewar zama tare da su saboda matsayinsu ko wadatarsu. Malamai sun ce wannan ayar ta sauka ne yayin da manyan Ƙuraishawa suka nemi Manzon Allah (ﷺ) ya kori talakawa cikin sahabbansa daga majalisarsa irin su Bilalu da Ammaru da Suhaibu da Khabbabu da Abdullahi ɗan Mas’udu, idan yana son su musulunta su zauna tare da shi su kaɗai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana shi korar su, ya kuma umarce shi da ya yi haƙurin zama tare da su. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mun kasance mu shida tare da Manzon Allah (ﷺ) sai mushirikai suka ce: “Ka kori waɗannan kada su riƙa yi mana rashin kunya.” A lokacin ni ne da Ibnu Mas’ud da wani mutum ɗan ƙabilar Huzailu da Bilalu da wasu mutane biyu da na manta sunayensu. Sai abin da Allah ya ga dama ya ɗarsu a zuciyar Manzon Allah (ﷺ) ya ɗarsu, wani tunani ya zo masa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da aya ta 52 a cikin Suratul An’am .” [Muslim #2413]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana Manzonsa ya yi biyayya ga wanda ya yi watsi da ambaton Allah, wanda har yake umartar Manzo da korar talakawa daga majalisarsa, ya gabatar da bin son zuciyarsa a kan ɗa’ar Ubangijinsa, al’amarinsa kuma duk ya zama a sukurkuce. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗa wa waɗannan gafalallun mutanen masu umartar sa da ya kori Musulmi talakawa, da cewa abin da ya zo musu da shi daga Allah Ubangijinsu shi ne gaskiya, kuma ya jaddada musu cewa, ba zai taɓa korar muminan da suke tare da shi a majalisarsa ba, kamar yadda suke nema a wajensa. Don haka wanda ya ga dama daga cikinsu ya yi imani, zai ga sakamakon imaninsa, wanda kuma ya ga dama ya kafirce, amma ya sani zai ga abin baƙanta rai da yake jiran sa a lahira, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanadar wa azzalumai waɗanda suka zaɓi kafirci wuta mai zafin gaske wadda katangarta ta zagaye su ta ko’ina babu wurin gudu. Idan suka nemi a taimaka musu da ruwa saboda tsananin ƙishi sai a taimake su da wani ruwa mai kama da tafasasshen mai wanda zai riƙa toye fuskokinsu don tsananin zafi. Allah ya bayyana cewa, wannan abin sha nasu ya munana, domin ba zai kashe musu ƙishirwa ba kuma ba zai sanyaya musu fatarsu ba. Hakanan wutar da za a saka su a cikinta ta zamanto musu gidan zama ita ma ta munana matuƙa.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ مَنۡ أَحۡسَنَ عَمَلًا
Open ayah 18:30Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari tabbas Mu ba ma tozarta ladan wanda ya kyautata aiki.
أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ جَنَّٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَيَلۡبَسُونَ ثِيَابًا خُضۡرٗا مِّن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۚ نِعۡمَ ٱلثَّوَابُ وَحَسُنَتۡ مُرۡتَفَقٗا
Open ayah 18:31Waɗannan suna da gidajen Aljanna na dawwama waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, ana yi musu ado a cikinsu (watau gidajen) da awarwaro na zinare, suna kuma sanya tufafi koraye na alharini mai shara-shara da mai kauri, suna kwance a kan gadaje. Madalla (da wannan) lada, wurin hutu kuma ya kyautata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake bayyana kyakkyawan tanadin da ya yi wa muminai a lahira, da cewa su ne waɗanda suka yi imani suka yi kyawawan ayyuka. Allah ya tabbatar da cewa, suna da babban rabo, zai kuma cika musu ladansu cib-cib, domin shi ba ya tozarta ladan wanda ya kyautata aikinsa. Ya bayyana cewa, mutane masu irin waɗannan siffofi a lahira suna da gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su zauna a cikinsu har abada. Za a yi musu ado da awarwaro na zinare, a kuma sanya musu korayen tufafi na alharini mai shara-shara da mai kauri, suna kuma kishingiɗe a cikin gidajen Aljanna a kan wasu karagu waɗanda aka yi musu ado da kyawawan labilaye. Allah ya bayyana cewa, lalle wannan sakamako ya dace da su kuma madalla da shi. Kuma abu ne mai matuƙar kyau a ce gidan Aljanna ya zamo shi ne gidansu na zama har abada. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Adon mumini (a Aljanna) zai kai duk inda alwalarsa ta kai (a jikinsa).” [Muslim #250].
۞وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلٗا رَّجُلَيۡنِ جَعَلۡنَا لِأَحَدِهِمَا جَنَّتَيۡنِ مِنۡ أَعۡنَٰبٖ وَحَفَفۡنَٰهُمَا بِنَخۡلٖ وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُمَا زَرۡعٗا
Open ayah 18:32Ka kuma ba su misali da wasu mutane su biyu da Muka tanadar wa ɗayansu gonakai biyu na inabi, Muka kuma kewaye su da dabinai, Muka kuma sanya wasu shukoki tsakaninsu.
كِلۡتَا ٱلۡجَنَّتَيۡنِ ءَاتَتۡ أُكُلَهَا وَلَمۡ تَظۡلِم مِّنۡهُ شَيۡـٔٗاۚ وَفَجَّرۡنَا خِلَٰلَهُمَا نَهَرٗا
Open ayah 18:33Kowace ɗaya daga gonakin ta ba da ‘ya’yanta kuma ba ta rage komai daga gare su ba. Muka kuma ɓuɓɓugo da ƙorama ta tsakiyarsu.
وَكَانَ لَهُۥ ثَمَرٞ فَقَالَ لِصَٰحِبِهِۦ وَهُوَ يُحَاوِرُهُۥٓ أَنَا۠ أَكۡثَرُ مِنكَ مَالٗا وَأَعَزُّ نَفَرٗا
Open ayah 18:34Ya zamanto yana da ‘ya’yan itace, sai ya ce da abokinsa yayin da yake mahawara da shi: “Ni na fi ka yawan dukiya da ƙarfin jama’a.”
وَدَخَلَ جَنَّتَهُۥ وَهُوَ ظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ قَالَ مَآ أَظُنُّ أَن تَبِيدَ هَٰذِهِۦٓ أَبَدٗا
Open ayah 18:35Ya kuma shiga gonarsa yana kuwa mai zaluntar kansa, ya ce: “Ba na tsammanin cewa wannan za ta ƙare har abada.”
وَمَآ أَظُنُّ ٱلسَّاعَةَ قَآئِمَةٗ وَلَئِن رُّدِدتُّ إِلَىٰ رَبِّي لَأَجِدَنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهَا مُنقَلَبٗا
Open ayah 18:36“Kuma ba na tsammanin alƙiyama za ta tashi, kuma ko da an mayar da ni wurin Ubangijina to lalle zan sami canji fiye ma da ita.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labari na biyu bayan na mutanen kogo. Shi kuma na wasu mutane ne su biyu, su kuma don su zama misali na mutumin da yake godiya ga Allah bisa abin da ya ba shi komai ƙanƙantarsa, da mutumin da zai ba shi ni’ima ta duniya amma ya butulce masa ya kuma kafirce wa ranar alƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ba wa kafirai misali na wasu mutane su biyu, na farkonsu kafiri ne da Allah ya ba shi wasu gonaki biyu na inabi wanda itaciya ce mai matuƙar daraja, sannan ya kewaye masa waɗannan gonaki da itatuwan dabino waɗanda su ma masu daraja ne sosai. Bayan haka ya sanya masa shuke-shuke a tsakiyarsu na sauran amfanin gona, ya kuma keto masa da wata ƙoramar ruwa ta tsakiyar waɗannan gonaki wadda take shayar da su a noman rani. Duk gonakin nan biyu kuwa suka yi matuƙar kyau, son kowa ƙin wanda ya rasa, kuma suka riƙa bayar da ‘ya’yansu da amfaninsu cikakke ba tare da sun rage komai ba. Sai wannan mai gona ya zama yana samun amfanin gona mai matuƙar yawa da kyau, sai duniya ta fara ruɗar sa ya manta da Ubangijinsa, ya ma manta da lahira. Sai wata rana suna mahawara da abokinsa mumini, sai yake nuna masa cewa, shi fa yanzu ba sa’ansa ba ne don ya fi shi yawan dukiya da ƙarfin jama’a masu goyon bayansa da masu yi masa ayyuka da bayi maza da mata da ya mallaka. Sannan bai tsaya da alfaharinsa iya nan ba, sai da ya ƙara da cewa, shi ba ya ma tsammanin akwai tashin alƙiyama; ko ma da a ce za a tashi alƙiyamar shi ya tabbatar yana da makomar da ta fi wannan a wurin Ubangijinsa.
قَالَ لَهُۥ صَاحِبُهُۥ وَهُوَ يُحَاوِرُهُۥٓ أَكَفَرۡتَ بِٱلَّذِي خَلَقَكَ مِن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ سَوَّىٰكَ رَجُلٗا
Open ayah 18:37Abokinsa ya ce da shi yana mai mahawara da shi: “Yanzu ka kafirce wa Wanda Ya halicce ka daga ƙasa, sannan (kuma) daga maniyyi, sannan Ya daidaita ka (ka zama) mutum?
لَّٰكِنَّا۠ هُوَ ٱللَّهُ رَبِّي وَلَآ أُشۡرِكُ بِرَبِّيٓ أَحَدٗا
Open ayah 18:38“Sai dai ni kam Allah Shi ne Ubangijina, ba kuwa zan haɗa wani da Ubangijina ba.
وَلَوۡلَآ إِذۡ دَخَلۡتَ جَنَّتَكَ قُلۡتَ مَا شَآءَ ٱللَّهُ لَا قُوَّةَ إِلَّا بِٱللَّهِۚ إِن تَرَنِ أَنَا۠ أَقَلَّ مِنكَ مَالٗا وَوَلَدٗا
Open ayah 18:39“Kuma mai ya hana ka lokacin da ka shiga gonarka ka ce: ‘Abin da Allah Ya ga dama (shi zai kasance). Babu wani ƙarfi kuma babu dabara sai da Allah.’ Idan kana gani na na fi ka ƙarancin dukiya da ‘ya’ya.
فَعَسَىٰ رَبِّيٓ أَن يُؤۡتِيَنِ خَيۡرٗا مِّن جَنَّتِكَ وَيُرۡسِلَ عَلَيۡهَا حُسۡبَانٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَتُصۡبِحَ صَعِيدٗا زَلَقًا
Open ayah 18:40“To ina fatan Ubangijina Ya ba ni fiye da gonarka, Ya kuma aiko mata (gonarka) da wani bala’i daga sama, sannan ta wayi gari ta zama ƙeƙasasshiyar ƙasa mai santsi.
أَوۡ يُصۡبِحَ مَآؤُهَا غَوۡرٗا فَلَن تَسۡتَطِيعَ لَهُۥ طَلَبٗا
Open ayah 18:41“Ko kuma ruwanta ya zama ya ƙafe ƙarƙaf, ba ko za ka sami hanyar samo shi ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ƙissar mai gonakin nan biyu, da cewa, abokinsa mumini ya yi muhawara da shi yana mai yi masa nasiha yana gargaɗin sa da cewa, yanzu zai kafirce wa Allah wanda ya halicci asalinsa Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga ƙasa, shi kuma ya halicce shi daga maniyyi sannan ya mayar da shi daidaitaccen mutum, ya daidaita masa gaɓoɓinsa har ya zama cikakken mutum; yanzu a ce wanda ya yi masa irin wannan halitta sai ya kasa tashinsa bayan mutuwa? Sai kuma ya nuna masa bambancinsa da shi, ya tabbatar masa cewa, shi ba zai riƙa maganganu irin nasa ba, shi maganarsa ita ce Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne Ubangijinsa wanda ya yi masa ni’imomi masu yawa, don haka ba zai haɗa wani da shi a wajen bautarsa ba. Ya ci gaba da jan hankalinsa a kan ya dawo kan hanyar Allah; idan ya shiga gonarsa ya ga irin baiwar da ya yi masa ya ce: “Ma Sha Allahu La Ƙuwwata Illa Billah .” Watau ya nuna duk abin da ya faru to Allah ne ya ga damar faruwarsa, kuma shi ba shi da wani ƙarfi ko wata dabara sai tare da Allah. Sannan ya sanar da shi cewa, ni’imar imani ita ce ni’ima ta gaske ba yawan dukiya ba; don haka ya daina raina shi don ya gan shi ba ya da yawan dukiya da ‘ya’ya. Shi kansa yana sa ran Allah zai ba shi kyautar da ta fi gonar da ya ba shi, shi kuma da ya kafirce wa Allah akwai yiwuwar Allah ya aiko da wata azaba daga sama ta auka wa gonarsa sai ta wayi gari busasshiyar ƙasa da ba wani tsiro kanta; ƙafafu na zamewa saboda santsinta. Ko kuma ruwanta a wayi gari duk ya ƙafe ƙarƙaf, kuma a rasa hanyar samun sa duk kuwa neman da za a sha. Idan kuwa har gona ta rasa ruwa to ta gama lalacewa ke nan.
وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِۦ فَأَصۡبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيۡهِ عَلَىٰ مَآ أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُشۡرِكۡ بِرَبِّيٓ أَحَدٗا
Open ayah 18:42Aka kuwa hallaka ‘ya’yan itacen nasa, sannan ya wayi gari yana tafa hannayensa kan irin abin da ya ɓatar a kanta, ita kuwa ga ta ta zubo a kan dirkokinta, yana kuma cewa: “Kaicona, ina ma ban haɗa wani da Ubangijina ba!”
وَلَمۡ تَكُن لَّهُۥ فِئَةٞ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مُنتَصِرًا
Open ayah 18:43Ba shi kuwa da wata ƙungiya da za ta taimake shi ban da Allah, kuma bai zamo mai taimaka wa (kansa) ba.
هُنَالِكَ ٱلۡوَلَٰيَةُ لِلَّهِ ٱلۡحَقِّۚ هُوَ خَيۡرٞ ثَوَابٗا وَخَيۡرٌ عُقۡبٗا
Open ayah 18:44A wannan lokacin ne (ya bayyana) cewa taimako na Allah ne Tabbataccen (Sarki). Shi ne Fiyayyen Mai ba da lada kuma Fiyayyen Mai kyautata ƙarshe. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya amsa addu’ar wannan muminin, kuma abin da yake tsammani shi ne ya tabbata, sai ko bala’i ya rutsa da gonakin wannan mutum, duk abin da ke cikinsu ya lalace. Ya wayi gari cikin nadama, yana tafa hannayensa kan yawan dukiyar da ya kashe a waɗannan gonaki nasa da wahalhalun da ya sha wajen lura da su, ga su yau kwance a ƙasa, yana cewa cikin nadama: Ina ma ya yi imani da Allah shi kaɗai bai haɗa kowa da shi ba! Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa,, duk wani abu da mutumin nan yake alfahari da shi a baya yau bai amfane shi da komai ba, ƙarfin jama’arsa bai taimaka masa da wani abu ba ya kare masa bala’in da ya auka masa; shi ma kuma bai iya tsinana wa kansa komai ba. A wannan lokaci ne da Allah ya hallakar da wanda ya kafirce masa ya fifita rayuwar duniya a kan ta lahira, ya kuma bayyana darajar wanda yake masa godiya da babban matsayinsa a wurinsa; a lokacin ne ya tabbata lalle taimako na ga Allah (Mai tsarki da daukaka) tabbataccen Sarki shi kaɗai, shi ne fiyayyen mai saka wa bayinsa muminai, ya kuma ruɓanya musu ladansu, kuma fiyayyen mai kyautata ƙarshensu.
وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ فَأَصۡبَحَ هَشِيمٗا تَذۡرُوهُ ٱلرِّيَٰحُۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقۡتَدِرًا
Open ayah 18:45Kuma ka ba su misalin rayuwar duniya (wadda take) kamar ruwa ne da Muka saukar da shi daga sama, sai tsirran ƙasa suka cakuɗa da shi, sannan ya zama busasshe, iska tana ɗaiɗaita shi. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai.
ٱلۡمَالُ وَٱلۡبَنُونَ زِينَةُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱلۡبَٰقِيَٰتُ ٱلصَّٰلِحَٰتُ خَيۡرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابٗا وَخَيۡرٌ أَمَلٗا
Open ayah 18:46Dukiya da ‘ya’ya adon rayuwar duniya ne; wanzazzun ayyuka nagari kuwa su suka fi lada a wurin Ubangijinka kuma su ne buri mafi alheri. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa masu ruɗuwa da duniya yadda misalinta yake wajen saurin gushewa da ƙarewa, kamar ruwan sama ne da Allah ya saukar da shi ƙasa, tsirran ƙasa suka gauraya da shi suka fito suka yi kyau abin ban sha’awa, amma sai daga ƙarshe su bushe su kakkarye su zama karmami iska tana ɗaukar su har su watse, ƙasa ta koma kamar yadda take tun farko. Allah ya tabbata mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi, yana raya abin da ya ga dama ya hallaka abin da ya ga dama. Sai kuma ya bayyana cewa, dukiya da ‘ya’ya ƙawa ce ta duniya. Dukiya ba za ta amfanar da komai a lahira ba sai abin da mutum ya ciyar na dukiyarsa don neman yardar Allah. Ya kuma tabbatar da cewa, ayyuka da maganganu na ƙwarai su suka fi lada a wurin Ubangiji fiye da duk abin da duniya ta ƙunsa na dukiya da ƙawarta, kuma su ne mafi alherin abin da mutum zai yi burin sa a lahira, domin ƙyale-ƙyalen duniya masu ƙarewa ne, amma ayyuka na ƙwarai wanzazzu ne har abada. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Faɗar: Subahanallahi Wal-Hamdu Lillahi Wa La-Ilaha Illallahu Wal-Lahu Akbar suna daga cikin wanzazzun ayyuka nagari.” [Ibnu Jarir, Jami’ul Bayan , Juzu’i na 18, shafi na 34]. An tambayi Usman (Allah ya kara masa yarda) cewa,: Mene ne wanzazzun ayyuka? Sai ya ce: “Su ne faɗar: La Ilaha Illallahu Wa Subhanallahi Wal-Hamdu Lillahi Wallahu Akbar Wa La Haula Wala Ƙuwwata Illa billahi .” [Ahmad #513].
وَيَوۡمَ نُسَيِّرُ ٱلۡجِبَالَ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ بَارِزَةٗ وَحَشَرۡنَٰهُمۡ فَلَمۡ نُغَادِرۡ مِنۡهُمۡ أَحَدٗا
Open ayah 18:47Kuma ka tuna ranar da za Mu tafiyar da duwatsu kuma ka ga ƙasa a baje (ba tudu ba rafi), Mu kuma tattara su (gaba ɗaya), ba Mu bar ɗaya daga cikinsu ba.
وَعُرِضُواْ عَلَىٰ رَبِّكَ صَفّٗا لَّقَدۡ جِئۡتُمُونَا كَمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةِۭۚ بَلۡ زَعَمۡتُمۡ أَلَّن نَّجۡعَلَ لَكُم مَّوۡعِدٗا
Open ayah 18:48Aka kuma kawo su a gaban Ubangijinka sahu-sahu (a ce da su): “Haƙiƙa kun zo mana kamar yadda tun farko Muka halicce ku. Ba ma haka ba, kun riya cewa ba za Mu sanya muku wani wa’adi ba.”
وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ فَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُشۡفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَٰوَيۡلَتَنَا مَالِ هَٰذَا ٱلۡكِتَٰبِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةٗ وَلَا كَبِيرَةً إِلَّآ أَحۡصَىٰهَاۚ وَوَجَدُواْ مَا عَمِلُواْ حَاضِرٗاۗ وَلَا يَظۡلِمُ رَبُّكَ أَحَدٗا
Open ayah 18:49Aka kuma ajiye littafin (ayyukansu), sannan sai ka ga masu laifi suna cike da tsoron abin da yake cikinsa, suna kuma cewa: “Kaiconmu, me ya sami wannan littafin, ba ya barin (aiki) ƙarami balle babba sai ya ƙididdige su. Suka kuma sami (duk) abubuwan da suka aikata an zo da su. Ubangijinka kuwa ba zai zalunci kowa ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tuna da ranar da Allah (Mai tsarki da daukaka) zai gusar da duwatsu daga wuraren zamansu ya zamanto ƙasa ta fito fili domin an kawar da duk wasu duwatsu da bishiyoyi da gine-gine da suke bayanta. Allah kuma ya tattara halittu wuri guda ba tare da ya bar ko mutum ɗaya ba sai ya tashe shi. Ya bayyana cewa, zai tara ɗaukacin mutane a gaban Ubangiji sahu-sahu domin yi musu hisabi. Sai Ubangiji ya ce da su, ga shi yanzu sun zo masa ɗai-ɗai, kowa a tsirara haihuwar uwarsa, ba takalma a ƙafafunsu kuma ba su da shayi, kamar dai yadda tun farko ya halicce su, bayan a da suna riya cewa, ba za a sake tashin su ba idan sun mutu, kuma babu wani wuri da aka tanada don komawarsu inda za a yi musu hisabi a yi wa kowa sakamako a kan ayyukansa. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Za a tashi mutane a ranar alƙiyama babu takalma a ƙafafunsu tsirara masu loɓa.” Sai A’isha ta ce: “Ya Manzon Allah, duk za a haɗa maza da mata wuri guda suna kallon junansu?” Sai ya ce: “Ya A’isha, abin ya fi ƙarfin su tsaya kallon junansu.” [Bukhari #652 da Muslim #2159]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane, lalle za a tattara ku a gaban Allah tsirararku masu loɓa, (kamar yadda muka fara halitta haka za mu mayar da ita). Ku saurara, farkon wanda za a saka wa tufafi a ranar alƙiyama shi ne Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi)...” [Bukhari #2526 da Muslim #2860]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, za a ajiye littafin ayyuka; wani a ba shi littafinsa a hannun dama, wani a ba shi nasa a hannun hagu. A nan ne za a ga kafirai suna cike da tsoron abin da yake cikin littattafansu, domin sun riga sun san ta’asar da suka aikata a duniya ta kafirci da saɓon Allah. A lokacin ne za su riƙa ihu suna cewa, sun banu sun hallaka, suna mamakin irin wannan littafin da ba zai bar ƙaramin abu da babba na ayyukan da suka yi a duniya ba face sai ya kiyaye su a rubuce. Suka kuwa samu abubuwan da suka aikata a duniya an halarto musu su gaba ɗaya, kuma Allah ba azzalumin kowa ba ne; ba zai kama wani da laifin wani ba, ko ya rage wa wani ladan aikinsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Unaisu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Za a tashi mutane a ranar alƙiyama tsirara masu loɓa babu komai tare da su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo su da wata murya wadda na nesa yake jin ta kamar yadda na kusa yake ji, ya ce: “Ni ne cikakken Sarki, ni ne mai sakamako, bai dace wani ɗan wuta ya shiga wuta ba alhali akwai haƙƙinsa a wurin wani ɗan Aljanna har sai na rama masa, kuma bai dace wani ɗan Aljanna ya shiga Aljanna ba alhalin akwai haƙƙinsa a wurin wani ɗan wuta har sai na karɓo masa, ko na rama masa ko da kuwa mari ne.” Sai sahabbai suka ce: “Ta yaya za a karɓo wannan haƙƙi alhali dukkanmu za mu tashi ba mu da komai?” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Da kyawawan ayyuka da munana.” [Ahmad #16042].
وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ كَانَ مِنَ ٱلۡجِنِّ فَفَسَقَ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِۦٓۗ أَفَتَتَّخِذُونَهُۥ وَذُرِّيَّتَهُۥٓ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِي وَهُمۡ لَكُمۡ عَدُوُّۢۚ بِئۡسَ لِلظَّٰلِمِينَ بَدَلٗا
Open ayah 18:50Kuma ka tuna lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu”, sai suka yi sujjadar in ban da Iblis, ya kasance kuwa daga cikin aljannu, sai ya saɓa wa umarnin Ubangijinsa. Yanzu kwa riƙe shi shi da zurriyarsa masoya ba Ni ba, alhali kuwa su maƙiyanku ne? Wannan canji na azzalumai ya munana.
۞مَّآ أَشۡهَدتُّهُمۡ خَلۡقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَا خَلۡقَ أَنفُسِهِمۡ وَمَا كُنتُ مُتَّخِذَ ٱلۡمُضِلِّينَ عَضُدٗا
Open ayah 18:51Ban halarto da su ba lokacin halittar sammai da ƙasa, ko ma halittar kawunansu, ban kuma kasance Mai riƙon masu ɓatarwa mataimaka ba.
وَيَوۡمَ يَقُولُ نَادُواْ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُم مَّوۡبِقٗا
Open ayah 18:52Kuma (ka tuna) ranar da (Allah) zai ce (da kafirai): “Ku kirawo abokan tarayyar nawa waɗanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku)”, to sai suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, Muka kuma sanya mahallaka a tsakaninsu.
وَرَءَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ ٱلنَّارَ فَظَنُّوٓاْ أَنَّهُم مُّوَاقِعُوهَا وَلَمۡ يَجِدُواْ عَنۡهَا مَصۡرِفٗا
Open ayah 18:53Masu laifi kuma suka ga wuta sai suka tabbatar da cewa lalle za su shige ta ba kuwa za su sami wata makauta ba daga gare ta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin asalin farkon halittar ɗan’adam, yayin da ya halicci Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kuma umarci mala’iku da su yi masa sujjada ta girmamawa da gaisuwa, sai dukkansu suka faɗi suka yi masa sujjada domin cika umarnin Ubangijinsu. To amma shi Iblis sai ya ƙi ya yi biyayya ga wannan umarni na mahaliccinsa. Kuma da ma shi ba mala’ika ne ba, ya kasance ne daga cikin jinsin aljannu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da zurriyyarsa cewa, yanzu sa yarda su ɗauki Iblis da zurriyyarsa su zama masoya da za su jiɓince su ba Allah ba, alhalin ga shi ya tabbata shi maƙiyansu ne? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wadarai da azzalumai waɗanda za su saki Allah su riƙe Iblis da zurriyyarsa masoya. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Iblis yana ajiye karagarsa a kan ruwa, sannan ya baza rundunarsa, wanda ya fi kusanci da matsayi a wurinsa shi ne wanda ya fi fitina daga cikinsu. Ɗaya daga cikinsu zai zo ya ce, na yi kaza da kaza, sai Iblis ya ce: “Tafi can ba ka yi komai ba.” Sai wani kuma ya zo ya ce: “Ban ƙyale shi ba har sai da na raba shi da matarsa.” Sai ya matso da shi kusa da shi ya ce: “Madalla da kai.” Ya kama shi ya rungume shi.” [Muslim #2813]. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk sanda garin Allah ya waye Iblis yana baza rundunarsa yana ce musu: “Duk wanda ya ɓatar da wani Musulmi to zan naɗa masa kambin sarauta.” Sai wani ya fita ya dawo ya ce: “Ban ƙyale shi ba har sai da na ga ya saki matarsa.” Sai Iblis ya ce: “Ba jimawa zai sake wani auren.” Sai kuma ya zo ya ce: “Ban ƙyale shi ba har sai da na ga ya ɓata da iyayensa.” Sai Iblis ya ce: “Ai ba da jimawa ba zai dawo ya sasanta da su, ya ci gaba da yi musu biyayya.” Sai kuma wani ya zo ya ce: “Ban ƙyale shi ba har sai da na ga ya yi zina.” Sai Iblis ya ce: “Babu kamarka.” Wani kuma sai ya zo ya ce: “Ban ƙyale shi ba har sai da na ga ya kashe rai.” Sai Iblis ya ce: “Babu kamarka.” Sai ya naɗa masa kambin sarautarsa.” [Ibn Hibban #6186 da Mustadrak na Hakim, Juzu’i na 4, shafi na 350]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan da suka runguma suna bautar su ba Allah ba su ma bayi ne kamarsu, ba su da wani matsayi na daban a wurin Allah, domin bai zo da su ba ya nuna musu lokacin da yake halittar sammai da ƙasa, hakanan bai zo da su ya nuna wa wani sashinsu sanda ya halicci wani sashe ba. Shi kaɗai ne mai halitta, kuma mai gudanar da abin da ya halitta, kuma bai zamo mai riƙon masu ɓatarwa daga cikin shaiɗanu na mutane ko aljanu su zama mataimakansa ba, domin shi wadatacce ne da Zatinsa ba ya buƙatar taimakon kowa. Sai kuma ya bayyana yadda zai nuna wa masu bautar wasu ba shi ba cewa, ƙarya suke bauta wa ba gaskiya ba. Ya umarci Annabinsa ya tuna ranar alƙiyama sa’adda zai umarci waɗanda suka yi shirka a nan duniya da su kirawo waɗanda suka riƙa da’awar cewa, su ababen tarayya ne na Allah, su kirawo su su ga ko za su taimaka musu da wani abu a wannan ranar. Sai su kirawo su amma ba za su ji sun amsa musu ba ballantana su taimaka musu. Allah ya bayyana cewa, zai sanya wurin hallaka, watau wutar Jahannama, a tsakaninsu, a nan ne za su yi baran-baran da junansu. Sai kuma ya bayyana cewa, bayan an yi hisabi kowa ya san makomarsa, azabar Allah ta wuta ta tabbata ga masu laifi, to a lokacin za su gan ta an zo da ita, su kuma tabbatar da cewa, cikinta za a jefa su, ba kuma za su samu wurin kauce mata ba, dole ne sai sun shige ta ba makawa.
وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٖۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ أَكۡثَرَ شَيۡءٖ جَدَلٗا
Open ayah 18:54Kuma haƙiƙa Mun sassarafa kowane irin misali ga mutane a cikin wannan Alƙur’anin. Mutum kuwa ya kasance wanda ya fi komai yawan musu.
وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰ وَيَسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّهُمۡ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ أَوۡ يَأۡتِيَهُمُ ٱلۡعَذَابُ قُبُلٗا
Open ayah 18:55Ba kuwa abin da ya hana mutane su yi imani lokacin da shiriya ta zo musu, su kuma nemi gafarar Ubangijinsu har sai irin abin da ya zo wa mutanen farko ya zo musu, ko kuwa azaba ta zo musu gaba-da-gaba.
وَمَا نُرۡسِلُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَۚ وَيُجَٰدِلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ لِيُدۡحِضُواْ بِهِ ٱلۡحَقَّۖ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَمَآ أُنذِرُواْ هُزُوٗا
Open ayah 18:56Ba Mu kuma aiko da manzanni ba sai don su zama masu albishir mai gargaɗi. Su kuma waɗanda suka kafirce sai su dinga jayayya da ƙarya don su kawar da gaskiya da ita; suka kuma riƙi ayoyina da kuma abin da aka yi musu gargaɗi da shi a matsayin abin izgili. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa,, ya yi bayanin misalai iri-iri a cikin Alƙur’ani domin mutane su wa’azantu su hankalta, sai dai mutum, musamman kafiri yana da yawan jayayya a kan gaskiyarsa (Alƙur’ani) da take a bayyane ƙarara. An karɓo daga Abu Umamata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu mutanen da za su bar shiriyar da suka kasance a kanta sai an hore musu jayayya.” [Ahmad #22164 da Tirmizi #3253 da Ibn Majah #48]. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mun kasance muna zaune tare da Manzon Allah (ﷺ) sai ya yi dariya, sai ya ce: “Ko kun san dalilin dariyata?” Sai muka ce: “Allah da Manzonsa su ne mafi sani.” Sai ya ce: “Ina dariya ne a kan yadda bawa zai riƙa magana da Ubangijinsa (ranar alƙiyama), ya ce: “Ya Ubangijina, shin ba ka tsare ni daga zalunci ba?” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: “E, haka ne.” Sai bawa ya ce: “To ban yarda wani ya ba da shaida a kaina ba sai dai wata gaɓa ɗaya daga jikina.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: “To kai ma a yau ka isa shaida ga kanka, hakanan su ma mala’iku masu girma marubuta ayyuka sun isa shaidu.” Sai a rufe masa bakinsa, sannan a ce wa gaɓoɓinsa su yi masa shaida. Sai gaɓoɓinsa su yi bayanin duk ayyukan da ya yi (a duniya), sai a kuma ba shi damar ya yi magana, sai ya ce: “Tir da ku, a kanku ne fa nake wannan jayayyar.” [Muslim #2969]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba rashin bayani cikakke ne ya hana kafirai su yi imani da abin da Annabi (ﷺ) ya zo musu da shi daga Allah ba, ko su nemi gafarar zunubansu daga Allah. An yi musu bayani filla-filla tare da ba su misalai iri-iri a cikin Alƙur’ani da kawo musu hujjoji masu ƙarfi. Abin da kawai ya hana su ba da gaskiya shi ne irin gangancin da suke yi na neman cewa su ma a saukar musu da azaba irin wadda aka saukar wa al\'ummun da suka gabace su, idan har abin da Manzo ya zo musu da shi gaskiya ne. Ko kuma su ga azabar da ake tsoratar da su da ita ido-da-ido, a lokacin ne za su yarda abin da Manzo ya zo musu da shi gaskiya ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, ba wasu manzanni da ya aiko sai don su yi albishir ga muminai masu bin Allah da Manzonsa, su kuma yi gargaɗi ga kafirai da masu saɓon Allah. Ba su da ikon tursasa wa mutane sai sun yi imani. Amma duk da haka kafirai suna jayayya da manzannin Allah tare da cewa sai sun nuna musu dalilai a fili, ba don wani abu ba sai don su kawar da gaskiyar da aka saukar wa Manzon Allah (ﷺ) ta hanyar ƙarerayinsu. Kuma suka ɗauki Alƙur’ani da azabar Allah da ake tsoratar da su abin yi wa izgili da dariya.
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ فَأَعۡرَضَ عَنۡهَا وَنَسِيَ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُۚ إِنَّا جَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۖ وَإِن تَدۡعُهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ فَلَن يَهۡتَدُوٓاْ إِذًا أَبَدٗا
Open ayah 18:57Wane ne ya fi zalunci fiye da wanda aka yi masa gargaɗi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya bijire musu, ya kuma manta abin da hannayensa suka gabatar (na mugun aiki). Lalle Mun sanya rufi a zukatansu don kada su fahimce shi (Alƙur’ani), a cikin kunnuwansu kuma (Muka sanya) wani nauyi. Idan kuwa ka kirawo su zuwa ga shiriya to ba za su yi imani ba har abada.
وَرَبُّكَ ٱلۡغَفُورُ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۖ لَوۡ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُواْ لَعَجَّلَ لَهُمُ ٱلۡعَذَابَۚ بَل لَّهُم مَّوۡعِدٞ لَّن يَجِدُواْ مِن دُونِهِۦ مَوۡئِلٗا
Open ayah 18:58Ubangijinka kuwa Mai yawan gafara ne Ma’abocin rahama; da Yana kama su da abin da suka aikata, to da Ya gaggauta musu azaba. A’a, (ba Ya yin haka), sai dai suna da ƙayyadajjen lokaci wanda ba za su sami wata makauta ba daga gare shi.
وَتِلۡكَ ٱلۡقُرَىٰٓ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَعَلۡنَا لِمَهۡلِكِهِم مَّوۡعِدٗا
Open ayah 18:59Kuma waɗancan alƙaryu Mun hallakar da su yayin da suka yi zalunci, Muka kuma sanya ƙayyadajjen lokaci na hallakar da su. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu azzalumi da ya kai mutumin da aka riƙa yi masa wa’azi da ayoyin Allah amma ya yi ko-oho da su, bai damu da abin da ake tsoratar da shi ba na azabar Allah, ya riƙa bijire wa gaskiya duk sanda ya ji ta, ya ma manta da ayyukan kafirci da saɓon Allah da ya riƙa yi a duniya bai tuba ba ya yi nadama a kansu ba. Lalle duk inda wani azzalumi ya kai wannan ya wuce nan. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da yake faruwa ga mutane masu irin wannan hali, da cewa, Allah ya rufe zukatansu ruf sun kasa fahimtar Alƙur’ani, ya mayar da kunnuwansu kurame ba za su saurari Alƙur’ani sauraro na karɓa ba, don haka ko da za a kirawo su zuwa su yi imani ba za su taɓa amsa kiran ba har abada domin zukatansu a rufe suke, kunnuwansu kuma sun kurumce. To don gudun kada Manzon Allah (ﷺ) ya zaci cewa waɗannan kafirai tun da har sun kai ga irin wannan matsayi na bijire wa Allah ba zai ƙyale su haka a duniya ba tare da ya saukar musu da azaba ta hallaka su ba, Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa, ba haka abin zai kasance ba. Shi Allah mai yawan gafarta zunubban bayinsa ne masu tuba, kuma mai rahama ne wanda rahamarsa ta yalwaci komai. Yana kuma daga cikin rahamarsa ya saurara wa masu laifi ko sa tuba ya karɓi tubansu. Ya bayyana cewa, da a ce zai kama waɗannan masu laifin da azabarsa, to da ya gaggauto musu da ita tun a nan duniya, to amma shi mai haƙuri ne, don haka ya bar su domin su tuba. Ya bayyana cewa, akwai lokaci da wuri da ya tanada inda zai yi musu sakayya a kan kafircinsu da zunubansu idan ba su tuba ba, kuma ba za su taɓa samun mafaka da za ta kare su daga gare shi ba. Sai kuma ya bayyana cewa, haka al’adar Allah ta kasance a cikin al\'ummun da suka gabata; yana saurara musu yayin da suka yi kafirci don su tuba su koma gare shi. Idan sun doge a kan kafircinsu sai ya aiko musu da azabarsa idan wa’adin hallaka su ya yi, babu kuma wanda ya isa ya kauce wa wannan wa’adin nasa.
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَىٰهُ لَآ أَبۡرَحُ حَتَّىٰٓ أَبۡلُغَ مَجۡمَعَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ أَوۡ أَمۡضِيَ حُقُبٗا
Open ayah 18:60Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da yaronsa: “Ba zan dakata da (tafiyata) ba har sai na kai mahaɗar kogunan nan biyu, ko kuwa in zarce har tsawon shekaru.”
فَلَمَّا بَلَغَا مَجۡمَعَ بَيۡنِهِمَا نَسِيَا حُوتَهُمَا فَٱتَّخَذَ سَبِيلَهُۥ فِي ٱلۡبَحۡرِ سَرَبٗا
Open ayah 18:61To lokacin da suka isa mahaɗar tasu (watau kogunan) sai suka manta da kifinsu wanda ya kama hanyarsa a cikin kogi kamar ɗakin ƙarƙashin ƙasa. Daga nan har zuwa ƙarshen aya ta 82 Allah ya ba da labarin tafiyar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) neman ilimi wajen Annabi Khadir (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Labarin wannan tafiyar ya zo a cikin hadisin Ubayyu ɗan Ka’ab wanda [Bukhari #122, 2728, 3400, 3401, 4725, 4726, 2727, 6072, 7477 da Muslim #2380] suka ruwaito cewa, wata rana Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tashi a cikin Banu Isra’ila ya yi musu huɗuba ya yi musu wa’azi har mutane suka yi ta yin kuka. Bayan ya gama ya tafi, sai wani mutum ya bi shi ya tambaye shi cewa, wane mutum ne ya fi kowa ilimi? Sai ya ce shi ne ya fi kowa ilimi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɓe shi a kan hakan, domin kamata ya yi ya mayar da ilimi gare shi shi kaɗai. Sai ya yi masa wahayi da cewa, akwai wani bawansa a wata mahaɗar koguna biyu shi ya fi shi ilimi. Sai Annabi Musa ya tambayi Allah ya faɗa masa yadda zai isa inda yake. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya tanadi guzurin kifi tare da shi ya saka shi a cikin kwando, to duk inda ya ga kifin nan ya ɓace to a nan ne wannan bawan Allah yake. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sami mataccen kifi ya sanya a kwando kamar yadda aka umarce shi, ya ɗauki yaronsa mai suna Yusha’u suka tafi, ya gaya masa cewa, ba zai daina tafiya ba har sai ya kai wurin da kogunan nan suka haɗu, ko da kuwa wannan tafiyar za ta ɗauke shi shekaru masu yawa. Wannan mahaɗar kogunan malamai sun yi saɓani wajen tantance ta. Wasu sun ce ita ce mahaɗar kogunan Farisa da Rum; wasu sun ce a Sham take; wasu kuma sun ce a Afrika ce. To amma babu wani ingantaccen nassi da ya nuna wurin da wannan mahaɗar take. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, lokacin da suka kai wurin mahaɗar sai suka manta wannan kifin, wanda shi kuma ya fito daga cikin kwando ya faɗa cikin ruwan ya sami hanya kamar ɗakin ƙarƙashin ƙasa ko bututu ya yi ta tafiya a cikinta. Ya zo a cikin hadisin Ubayyu cewa: Lokacin da Annabi Musa da yaronsa Yusha’u suka isa wurin wani dutse, sai suka sami inuwa suka kwanta daidai wata magudanar ruwa sai barci ya kwashe su. Wannan ruwa da yake kusa da su kuwa ana kiran sa da suna ‘Ruwan rayuwa’ domin duk wani abu da ya taɓa zai rayu ko da kuwa a da ya mutu. Sai kuwa ya taɓa wannan kifin nasu da ke cikin kwando, nan take kuwa ya fara watsal-watsal, ya fito daga kwando ya faɗa kogi, ya kama hanya ya yi tafiyarsa. Allah ya kame masa gudanar ruwa, sai ya yi kamar yana tafiya a cikin wani ɗaki. Annabi Musa yana barci, amma yaronsa ya farka ya ga abin da ya faru, sai kuma bai tashi Annabi Musa daga barci ba da niyyar idan ya farka zai sanar da shi, sai kuma ya manta bai sanar da shi ba.
فَلَمَّا جَاوَزَا قَالَ لِفَتَىٰهُ ءَاتِنَا غَدَآءَنَا لَقَدۡ لَقِينَا مِن سَفَرِنَا هَٰذَا نَصَبٗا
Open ayah 18:62To lokacin da suka wuce (wannan wuri) sai (Musa) ya ce da yaronsa: “Kawo mana abincinmu, haƙiƙa mun haɗu da wahala cikin wannan tafiya tamu.”
قَالَ أَرَءَيۡتَ إِذۡ أَوَيۡنَآ إِلَى ٱلصَّخۡرَةِ فَإِنِّي نَسِيتُ ٱلۡحُوتَ وَمَآ أَنسَىٰنِيهُ إِلَّا ٱلشَّيۡطَٰنُ أَنۡ أَذۡكُرَهُۥۚ وَٱتَّخَذَ سَبِيلَهُۥ فِي ٱلۡبَحۡرِ عَجَبٗا
Open ayah 18:63Sai (yaron) ya ce: “Ba ka gani ba lokacin da muka fake a daidai dutsen nan ai sai na manta da kifin, ba kuwa wani ne ya mantar da ni shi ba sai Shaiɗan, ya hana ni in tuna. Sai kuma ya kama hanyarsa cikin kogi, abin mamaki!”
قَالَ ذَٰلِكَ مَا كُنَّا نَبۡغِۚ فَٱرۡتَدَّا عَلَىٰٓ ءَاثَارِهِمَا قَصَصٗا
Open ayah 18:64(Musa) ya ce: “Wannan da ma shi ne abin da muke nema”, Sai suka koma da baya suna bin sawunsu (ta inda suka fito). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa, Annabi Musa da yaronsa Yusha’u sun bar ƙarƙashin inuwar wannan dutse, sun kama hanya sun ci gaba da tafiya. Ya zo a cikin hadisin Ubayyu cewa: “Sun yi tafiya ta tsawon kwana biyu. Bayan dare ya yi sun kwanta sun yi barci zuwa safiya. Da gari ya waye sai Annabi Musa ya ce wa yaronsa: “Kawo mana karin kumallonmu, haƙiƙa mun haɗu da wahala a cikin wannan tafiya tamu.” Ya zo a cikin wani hadisi cewa, Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai fara jin gajiya ba har sai da ya wuce wurin da aka umarce shi ya je. To a nan ne yaronsa ya tuna abin da ya faru da kifi. Ya tabbatar wa da Annabi Musa cewa, ai lokacin da suna hutawa a ƙarƙashin dutsen nan, ya manta da wannan kifi a wannan wurin, kuma ya tashi ya faɗa cikin kogi ya tafi abinsa. Shi ma dai abin ya ba shi mamaki. Bai gaya masa ba ne domin Shaiɗan ya riga ya mantar da shi ya hana shi tunawa. Da jin haka sai Annabi Musa ya ce, ai wannan abin nema ne ya samu, nan take suka juya suka koma inda suka baro, suna ta bin sawun ƙafafunsu don kada wurin ya ɓace musu.
فَوَجَدَا عَبۡدٗا مِّنۡ عِبَادِنَآ ءَاتَيۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَعَلَّمۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّا عِلۡمٗا
Open ayah 18:65To sai suka sami wani bawa daga bayinmu wanda Muka bai wa rahama daga gare Mu, kuma Muka koyar da shi wani ilimi daga wajenmu.
قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰ هَلۡ أَتَّبِعُكَ عَلَىٰٓ أَن تُعَلِّمَنِ مِمَّا عُلِّمۡتَ رُشۡدٗا
Open ayah 18:66Musa ya ce da shi: “Shin na iya bin ka don ka koyar da ni (wani abu) daga abin da aka koyar da kai na shiriya?”
قَالَ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Open ayah 18:67Ya ce da shi: “Lalle ba za ka iya haƙuri da ni ba.
وَكَيۡفَ تَصۡبِرُ عَلَىٰ مَا لَمۡ تُحِطۡ بِهِۦ خُبۡرٗا
Open ayah 18:68“Ƙaƙa kuwa za ka yi haƙuri kan abin da ba ka kewaye da saninsa ba?”
قَالَ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ صَابِرٗا وَلَآ أَعۡصِي لَكَ أَمۡرٗا
Open ayah 18:69(Musa) ya ce: “Za ka same ni mai haƙuri in sha Allahu , ba kuma zan saɓa wa umarninka ba.”
قَالَ فَإِنِ ٱتَّبَعۡتَنِي فَلَا تَسۡـَٔلۡنِي عَن شَيۡءٍ حَتَّىٰٓ أُحۡدِثَ لَكَ مِنۡهُ ذِكۡرٗا
Open ayah 18:70Ya ce, “To idan ka bi ni kada ka tambaye ni game da kowane abu har sai na ba ka labari game da shi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin labarin Annabi Musa da yaronsa Yusha’u da cewa, sun koma wurin da kifinsu ya ɓace, a nan ne kuma suka sami wani bawan Allah wanda Allah ya ba shi wata rahama daga gare shi, kuma ya sanar da shi wani ilimi na musamman daga wajensa. Hadisin Ubayyu ɗan Ka’ab ya nuna cewa, sun same shi a kan wata koriyar shimfiɗa a tsakiyar kogi ya lulluɓa da tufarsa, ya saka gefen tufar a ƙarƙashin ƙafafuwansa, ɗaya gefen kuma ya saka shi a ƙarƙashin kansa. Da Annabi Musa ya yi masa sallama sai ya buɗe fuskarsa ya ce masa: “Ina aka san sallama a ƙasarka? Wane ne kai?” Ya ce: “Ni ne Musa.” Ya ce: “Musa na Banu Isra’ila?” Ya ce: “E, shi fa.” Wannan mutum, kamar yadda ingantattun hadisai suka nuna, shi ne Khadiru. Amma wannan ba shi ne sunansa na yanka ba, wannan laƙabinsa ne. Yawancin masana sun ce sunansa na yanka shi ne Balya ɗan Malkan. Yawancin malamai suna ganin wannan bawan Allah annabi ne daga cikin annabawan Allah, kuma rahamar da Allah ya ce ya ba shi ita ce annabta da wahayi. Daga nan sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙe shi cikin ladabi da biyayya cewa, ko zai iya bin sa don ya koyar da shi wani abu daga ilimin da Allah ya ba shi? Sai Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya amsa ma Annabi Musa da cewa ba zai iya haƙurin zama da shi ba saboda abin da zai gani na iliminsa wanda ya sha bamban da nashi a zahiri. Ya nuna masa cewa, yana da wuya matuƙa ya yi haƙuri yayin da zai ga wasu abubuwa waɗanda bai gane kansu ba ko hikimar da ke cikinsu. To amma sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ba shi tabbacin cewa, zai same shi mai haƙuri a kan duk abubuwan da zai iya gani, kuma zai yi masa biyayya ba tare da ya saɓa umarninsa ba. Daga nan sai Khadiru ya faɗa masa sharaɗinsa wanda shi ne idan har ya bi shi sun tafi tare to duk abin da ya gan shi yana aikatawa kada ya yi masa wata tambaya a kai har sai shi ya bayyana masa manufar wannan abu.
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا رَكِبَا فِي ٱلسَّفِينَةِ خَرَقَهَاۖ قَالَ أَخَرَقۡتَهَا لِتُغۡرِقَ أَهۡلَهَا لَقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـًٔا إِمۡرٗا
Open ayah 18:71Sai suka tafi, har lokacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, to sai ya huda shi; sai (Musa) ya ce: “Yanzu ka huda shi ne don ka nutsar da waɗanda suke cikinsa? Haƙiƙa ka zo da babban abu.”
قَالَ أَلَمۡ أَقُلۡ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Open ayah 18:72Ya ce: “Ban faɗa maka ba cewa kai ba za ka iya haƙuri da ni ba?”
قَالَ لَا تُؤَاخِذۡنِي بِمَا نَسِيتُ وَلَا تُرۡهِقۡنِي مِنۡ أَمۡرِي عُسۡرٗا
Open ayah 18:73(Musa) ya ce: “Kada ka kama ni da abin da na manta, kada kuma ka ɗora mini abu mai wahala game da al’amarina.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Khadiru. Bayan Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya karɓi buƙatar Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ta zama almajirinsa sai suka tafi. Ya zo a cikin hadisin Ubayyu cewa,, sun tafi da ƙafafunsu har zuwa gaɓar kogi, sai suka ga ƙananan kwale-kwale waɗanda suke sufurin mutane daga wannan gaɓa zuwa ɗaya gaɓar. Sai ga wani jirgin ruwa ya zo wucewa, ta gabansu sai suka roƙi matuƙansa da su ɗauke su, sai suka gane Khadiru sai suka ce: \"Wannan bawan Allah nan ne mutumin kirki\". Sai suka ɗauke su kyauta ba ko kwabo. Ana tsakar tafiya Annabi Musa bai farga ba sai kawai ya ga har Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya cire allon wannan jirgi da gatari. Sai Musa ya ce: “Wane irin abu ne wannan ka aikata? Mutanen nan fa sun ɗauko mu kyauta, amma ka fasa musu jirgin ruwa, kana so ka nutsar da mutanen da ke cikinsa ne? Lalle ka zo da babban abu”. Sai Khadiru ya ce masa: “Ba na faɗi cewa, ba za ka iya haƙuri da ni ba?\" Sai Annabi Musa ya ba shi haƙuri ya roƙe shi da kada ya kama shi da laifin da ya yi da mantuwa; kada kuma ya tsananta masa dangane da tarayya da shi. Ya zo a cikin hadisin Ubayyu cewa, wani tsuntsu ya zo ya sauka a gefen wannan jirgin ruwa nasu ya tsattsago ruwan wannan kogi da bakinsa tsattsaga ɗaya ko biyu, sai Khadiru ya ce: \"Ka san abin da wannan tsuntsun yake cewa?\" Annabi Musa ya ce: “A’a”. Sai ya ce: “Cewa yake: ‘Iliminku ku biyun da kuke da shi idan an kwatanta shi da ilimin Allah bai wuce kamar abin da na raga da bakina daga ruwan wannan kogi ba.”
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا لَقِيَا غُلَٰمٗا فَقَتَلَهُۥ قَالَ أَقَتَلۡتَ نَفۡسٗا زَكِيَّةَۢ بِغَيۡرِ نَفۡسٖ لَّقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـٔٗا نُّكۡرٗا
Open ayah 18:74Sai suka ci gaba da tafiya har dai suka gamu da wani yaro, to sai ya kashe shi, (Musa) ya ce: “Yanzu ka kashe rai tsarkakakke ba tare da (ya kashe) wani rai ba? Haƙiƙa ka zo da wani abu mummuna!”
۞قَالَ أَلَمۡ أَقُل لَّكَ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Open ayah 18:75Ya ce: “Shin ban faɗa maka cewa lalle kai ba za ka iya haƙuri da ni ba?”
قَالَ إِن سَأَلۡتُكَ عَن شَيۡءِۭ بَعۡدَهَا فَلَا تُصَٰحِبۡنِيۖ قَدۡ بَلَغۡتَ مِن لَّدُنِّي عُذۡرٗا
Open ayah 18:76(Musa) ya ce: “Idan na sake tambayar ka wani abu bayansa, to kada ka tafi tare da ni; haƙiƙa ka sami (cikakken) hanzari a kaina.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya karɓi uzurin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) har ma sun ci gaba da tafiya bayan sun fito daga jirgin ruwa. To suna cikin tafiya a kan gaɓar kogi sai Khadiru ya hango wani yaro kafiri mai matuƙar wayo yana wasa cikin yara sai ya kamo shi ya kwantar da shi ya yanka shi da wuƙa ya cire kansa. Sai tsananin kishin addini ya kama Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) na ganin an yi wa yaro ƙarami irin wannan mummunan kisa, ya kasa jurewa sai ya ce masa: Yanzu ka kashe rai tsarkakakke ba tare da ya kashe wani rai ba? Haƙiƙa ka zo da wani abin ƙyama!. Sai Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sake tuna masa da alƙawarinsu da cewa, ai da ma ya gaya masa cewa ba zai iya haƙuri da shi ba. Sai Musa ya ce, yanzu kam in ya sake tambayar sa a nan gaba to ya yarda su rabu daga nan, domin ya yi masa duk wani uzuri da ya kamata ya yi masa, shi kuma ga shi ya saɓa wa umarninsa har sau uku. Ya zo cikin hadisin Ubayyu, Annabi (ﷺ) ya ce: “Allah ya ji ƙan Musa, ba domin ya yi gaggawa ba da ya ga abin mamaki, sai dai ya ji kunyar abokin tafiyarsa ya ce: “Idan na sake tambayar ka wani abu nan gaba, to kada ka tafi tare da ni, haƙiƙa ka sami cikakken hanzari a kaina.” Da ya yi haƙuri da ya sha mamaki.
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَيَآ أَهۡلَ قَرۡيَةٍ ٱسۡتَطۡعَمَآ أَهۡلَهَا فَأَبَوۡاْ أَن يُضَيِّفُوهُمَا فَوَجَدَا فِيهَا جِدَارٗا يُرِيدُ أَن يَنقَضَّ فَأَقَامَهُۥۖ قَالَ لَوۡ شِئۡتَ لَتَّخَذۡتَ عَلَيۡهِ أَجۡرٗا
Open ayah 18:77Sai suka ci gaba da tafiya har suka iso ga mutanen wata alƙarya, sai suka nemi mutanen alƙaryar su ciyar da su, to sai suka ƙi su karɓi baƙuntarsu, sai suka samu wani garu a alƙaryar yana haramar rugujewa sai (Khadiru) ya tashe shi, sai (Musa) ya ce: “Da ka ga dama ai da sai ka karɓi lada a kansa.” (Watau aikin tayarwar).
قَالَ هَٰذَا فِرَاقُ بَيۡنِي وَبَيۡنِكَۚ سَأُنَبِّئُكَ بِتَأۡوِيلِ مَا لَمۡ تَسۡتَطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرًا
Open ayah 18:78Ya ce: “Wannan ita ce rabuwata da kai. Zan ba ka labarin abin da ka kasa haƙuri a kansa.”
أَمَّا ٱلسَّفِينَةُ فَكَانَتۡ لِمَسَٰكِينَ يَعۡمَلُونَ فِي ٱلۡبَحۡرِ فَأَرَدتُّ أَنۡ أَعِيبَهَا وَكَانَ وَرَآءَهُم مَّلِكٞ يَأۡخُذُ كُلَّ سَفِينَةٍ غَصۡبٗا
Open ayah 18:79“To game da shi jirgin ruwan nan ya kasance na wasu miskinai ne da suke aiki a cikin kogi, to sai na yi nufin in lalata shi domin kuwa a gabansu akwai wani sarki da yake ƙwace kowane jirgin ruwa (lafiyayye).
وَأَمَّا ٱلۡغُلَٰمُ فَكَانَ أَبَوَاهُ مُؤۡمِنَيۡنِ فَخَشِينَآ أَن يُرۡهِقَهُمَا طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗا
Open ayah 18:80“To amma kuma game da shi yaron nan, iyayensa sun kasance muminai ne, sai muka ji tsoron kada ya afkar da su cikin shisshigi da kafirci.
فَأَرَدۡنَآ أَن يُبۡدِلَهُمَا رَبُّهُمَا خَيۡرٗا مِّنۡهُ زَكَوٰةٗ وَأَقۡرَبَ رُحۡمٗا
Open ayah 18:81“Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu (wani ɗa) wanda ya fi tsarkaka ya kuma fi shi tausayi.
وَأَمَّا ٱلۡجِدَارُ فَكَانَ لِغُلَٰمَيۡنِ يَتِيمَيۡنِ فِي ٱلۡمَدِينَةِ وَكَانَ تَحۡتَهُۥ كَنزٞ لَّهُمَا وَكَانَ أَبُوهُمَا صَٰلِحٗا فَأَرَادَ رَبُّكَ أَن يَبۡلُغَآ أَشُدَّهُمَا وَيَسۡتَخۡرِجَا كَنزَهُمَا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ وَمَا فَعَلۡتُهُۥ عَنۡ أَمۡرِيۚ ذَٰلِكَ تَأۡوِيلُ مَا لَمۡ تَسۡطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرٗا
Open ayah 18:82“To game da shi garun nan kuwa ya kasance na wasu yara ne marayu a cikin wannan birnin, a ƙarƙashinsa kuwa da akwai wata taska tasu, mahaifinsu kuma ya kasance mutumin kirki ne, to sai Ubangijinka Ya nufi su girma su cika hankalinsu su, kuma fito da taskarsu, don rahama daga Ubangijinka. Ban aikata haka ba ne da raɗin kaina. Wannan shi ne fassarar abin da ka kasa haƙuri a kansa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa sun ci gaba da tafiya har suka iso garin wasu marowatan mutane, suka nemi mutanen garin su ba su abinci, to amma sai mutanen suka ƙi karɓar baƙuncinsu. To sai Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka sami wani garu na garin yana shirin faɗuwa, sai Khadiru ya miƙar da shi, sai Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nuna masa cewa, ai da ya ga dama da ya karɓi lada a kan wannan aiki da ya yi musu, domin sun nemi abinci a wajensu sun hana su, don haka bai dace ya yi musu aiki kyauta ba, sannan ga shi suna buƙatar abin sayen abinci da za su ci. Sai Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce masa, to wannan karon lokacin rabuwarsu ya yi, kuma zai bayyana masa fassarar duk abubuwan da ya kasa haƙuri a kansu har sai da ya yi magana. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fassara ayyukansa ɗaya bayan ɗaya. Jirgin ruwa da ya lalata dai na wasu miskinai ne da suke aiki da shi a wannan ruwan suna samun abin da suke rayuwa da shi, to amma a hanyar da suka biyo akwai wani azzalumin sarki wanda duk inda ya ga lafiyayyen jirgi to zai ƙwace shi; ga shi su kuma raunana ne ba za su iya kare jirginsu ba. Sai Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce, bari ya lalata wani ɓangare na jirgin yadda idan wannan sarki ya gan shi a lalace ba zai yi sha’awarsa ba har ya ƙwace musu. To wannan ita ce hikimarsa ta lalata wannan jirgin. Shi kuma yaron da ya kashe yadda labarinsa yake shi ne, iyayensa muminai ne, shi kuma Allah ya riga ya san kafiri zai taso, sai Khadiru ya ji tsoron idan yaron nan ya girma zai mayar da iyayen nan nasa kafirai masu shisshigi cikin iyakokin Allah saboda tsananin soyayyar da suke yi masa. Kuma ya yi fatan Allah zai canja musu shi da wani ɗan wanda ya fi shi alheri da addini da kirki da tsarkaka daga zunubai da tausaya wa mahaifansa. Dangane da garun da ya miƙar, shi kuma na wasu ƙananan yara ne marayu, mahaifinsu wani mutumin kirki ne a garin. Kafin ya rasu ya binne musu dukiyarsu a ƙarƙashin wannan garun, da nufin idan har Allah ya sa suka girma suka yi hankali sai su tono dukiyarsu. To amma da ya ƙyale garun ya faɗi, da dukiyar ta bayyana kuma da mutanen garin ne za su wawashe ta. To duk wannan tsari rahamar Allah ce gare su. Sai Khadiru (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar wa da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa, duk waɗannan abubuwa da ya ga ya aikata ba gaban kansa ne ya yi su ba, watau da umarnin Allah ya yi su. Ya shaida masa cewa, wannan shi ne fassarar abin da ya kasa haƙuri a kansa.
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَن ذِي ٱلۡقَرۡنَيۡنِۖ قُلۡ سَأَتۡلُواْ عَلَيۡكُم مِّنۡهُ ذِكۡرًا
Open ayah 18:83Suna kuma tambayar ka game da Zulƙarnaini; ka ce (da su): “Ba da daɗewa ba zan ba ku labari a kansa.”
إِنَّا مَكَّنَّا لَهُۥ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَءَاتَيۡنَٰهُ مِن كُلِّ شَيۡءٖ سَبَبٗا
Open ayah 18:84Lalle Mu Muka kafa shi a bayan ƙasa, Muka kuma ba shi hanyar cimma duk wani muradinsa.
فَأَتۡبَعَ سَبَبًا
Open ayah 18:85Sai ya bi hanya. Daga aya ta 83 har zuwa aya ta 98 Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin Zul-Ƙarnaini ne domin amsa tambayar wasu daga cikin kafiran Ƙuraishawa ga Annabi (ﷺ) game da shi, don ya zama tunatarwa da wa’azantarwa gare su. Zul-ƙarnaini dai wani Sarki ne mumini mai Kaɗaita Allah, wanda ya yi imani da ranar lahira. Allah ya ba shi ƙarfin mulki har ya ci garuruwa masu yawa da yaƙi. Allah kuma ya ba shi duk wani abu da mai mulki a zamaninsa yake buƙata don wanzuwar mulkinsa da tabbatar da adalci a bayan ƙasa. Ya kasance mai kira ne zuwa ga Allah, da yaƙi da duk wani mai bautar wani ba Allah ba. Zul-Ƙarnaini ya kewaye duniya da yawo, ya isa yammacin duniya, daga nan ya dawo ya danna gabashinta inda ya isa wurin da ya gina babbar ganuwa tsakanin ƙabilun Yajuju da Majuju da sauran maƙotansu. Yana karɓar umarni ne ta hanyar wahayi da ake yi masa kai-tsaye (idan shi annabi ne), ko ta hanyar wani annabi da ke tare da shi a cikin rundunarsa. Da yawa daga cikin malaman tafsiri suna cewa, Zul-Ƙarnaini shi ne Alexander ɗan Philip mutumin Maƙduniya (Macedon) da ke masarautar Girika (Greek). Kuma babban wazirinsa, suka ce shi ne Aristatalis (Aristotle) shahararren malamin nan na falsafa. Sai dai wannan maganar tasu kuskure ne babba, domin dalilai kamar haka: 1. Zul-Ƙarnaini Sarki ne mumini wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira. Alexander kuwa mushiriki ne mai bautar gumaka da taurari. 2. Alexander ba a kiran sa da suna Zul-Ƙarnaini. 3. Yaƙe-yaƙen Alexander ba su kai ƙasashen Turkawa ba, iyakacinsu ƙasar Farisa. 4. Alexander ba shi ne ya gina babbar ganuwar da ke tsakanin Yajuju da Majuju da sauran ƙabilu maƙotansu ba. 5. Alexander ya rayu ne gabanin haihuwar Annabi Isa da kimanin shekara ɗari uku, yayin da shi kuma Zul-Ƙarnaini ya shuɗe da daɗewa. [Dubi, Ibnu Taimiyya, Al-Jawabus Sahih , Juzu’i na 1, shafi na 346-347]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ban sani ba, shin Tubba’u la’ananne ne ko a’a? Ban kuma sani ba, shin Zul-Ƙarnaini annabi ne ko a’a?....” [Abu Dawud #4674]. An tambayi Sayyidina Aliyyu (Allah ya kara masa yarda) cewa,: Shin Zul-Ƙarnaini annabi ne? Sai ya ce: “Ya kasance bawa ne na ƙwarai, ya so Allah sai shi ma Allah ya so shi, ya yi nasiha don Allah sai shi ma Allah ya yi masa nasiha, sai ya tura shi wajen mutanensa, suka yi masa duka guda biyu a kansa, don haka ne ake kiran sa Zul-Ƙarnaini....” [Ibnu Jarir, Juzu’i na 16, shafi na 16]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ba shi mulki mai ƙarfi a bayan ƙasa, don haka ya riƙi duk wani abu da Allah ya hore masa ya kama hanya don cimma burinsa.
حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ مَغۡرِبَ ٱلشَّمۡسِ وَجَدَهَا تَغۡرُبُ فِي عَيۡنٍ حَمِئَةٖ وَوَجَدَ عِندَهَا قَوۡمٗاۖ قُلۡنَا يَٰذَا ٱلۡقَرۡنَيۡنِ إِمَّآ أَن تُعَذِّبَ وَإِمَّآ أَن تَتَّخِذَ فِيهِمۡ حُسۡنٗا
Open ayah 18:86Har sai da ya isa mafaɗar rana, sai ya same ta tana faɗuwa ne cikin wani marmaro haɗe da baƙin taɓo mai wari, ya kuma sami wasu mutane a wurinta, Muka ce: “Ya Zulƙarnaini, ko dai ka azabtar (da su), ko kuma ka kyautata musu.”
قَالَ أَمَّا مَن ظَلَمَ فَسَوۡفَ نُعَذِّبُهُۥ ثُمَّ يُرَدُّ إِلَىٰ رَبِّهِۦ فَيُعَذِّبُهُۥ عَذَابٗا نُّكۡرٗا
Open ayah 18:87(Zulƙarnaini) ya ce: “Amma wanda ya yi zalunci to za mu azabtar da shi, sannan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa (shi ma) Ya yi masa mummunar azaba.
وَأَمَّا مَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُۥ جَزَآءً ٱلۡحُسۡنَىٰۖ وَسَنَقُولُ لَهُۥ مِنۡ أَمۡرِنَا يُسۡرٗا
Open ayah 18:88“Amma kuma wanda ya yi imani ya kuma yi aiki nagari, to yana da mafi kyan sakamako, kuma za mu faɗa masa tattausar (magana) game da al’amarinmu.”
ثُمَّ أَتۡبَعَ سَبَبًا
Open ayah 18:89Sannan ya kama hanya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Zul-Ƙarnaini ya ci gaba da tafiya a bayan ƙasa da rundunarsa, har ya isa ƙarshen ƙasa ta nahiyar yamma inda ɗan’adam a lokacin ba zai wuce shi ba. Kuma nan ne mafaɗar rana, ya gan ta tana faɗuwa cikin wani marmaro wanda yake cakuɗe da taɓo mai launin baƙi mai wari. A nan ne ya ga wasu mutane kafirai waɗanda suke bautar gumaka ba Allah ba, suna rayuwa kamar dabbobi ba addini. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Zul-Ƙarnaini zaɓi cewa, ko dai ya azabtar da mutanen nan ta hanyar kisa ko waninsa idan sun ƙi yin imani, ko kuma ya bi su ta lalama da kyautatawa. Sai Zul-Ƙarnaini ya bayyana cewa, duk wanda ya yi shirka da Allah ya doge a kan kafirci bayan an yi masa wa’azi an nuna masa gaskiya, to zai yi masa azaba a nan duniya ta hanyar kisa, sannan ya koma ga Ubangijinsa ranar alƙiyama ya yi masa mummunar azaba. Ya kuma bayyana cewa, daga cikinsu duk wanda ya yi imani da Allah ya yi kyakkyawan aiki, to yana da sakamakon gidan Aljanna, sannan zai faɗa masa tattausar magana daga lamarinsa. Sai kuma Zul-Ƙarnaini ya ci gaba da tafiyarsa da sojojinsa bayan ya gama tabbatar da umarnin Allah a kan waɗannan mutanen.
حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ مَطۡلِعَ ٱلشَّمۡسِ وَجَدَهَا تَطۡلُعُ عَلَىٰ قَوۡمٖ لَّمۡ نَجۡعَل لَّهُم مِّن دُونِهَا سِتۡرٗا
Open ayah 18:90Har dai lokacin da ya isa mahudar rana, ya same ta tana ɓullowa ne a kan wasu mutane da ba Mu sanya musu wata kariya ba daga gare ta.
كَذَٰلِكَۖ وَقَدۡ أَحَطۡنَا بِمَا لَدَيۡهِ خُبۡرٗا
Open ayah 18:91Kamar haka (ya yi hukunci watau irin yadda ya yi a mafaɗar rana), haƙiƙa kuma Mun kewaye da sanin (duk) abin da ke tare da shi (Zulƙarnaini). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Zul-Ƙarnaini ya ci gaba da tafiyarsa a bayan ƙasa inda ya dawo kuma ya nufi nahiyar yamma, watau mahudar rana. Ya kuma sami rana tana fitowa a kan wasu mutane waɗanda ba su da wata kariya da za ta kare su daga zafin rana, domin ba su da gidaje kuma inda suke babu bishiyoyi da za su fake a inuwoyinsu, domin a ƙasarsu babu dutse babu bishiya, kuma ƙasar ba za ta ɗauki gine-gine ba. Al-Hasanul Basri ya ce: “Ƙasarsu ta kasance ba ta ɗaukar gini a kanta, sun zamanto duk sa’adda rana ta fito musu sai su gudu su shiga cikin ruwa, idan ta faɗi sai su fito su ci gaba da kiwo a waje kamar dabbobi.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, rayuwar waɗannan mutanen irin rayuwar mutanen nan ne da Zul-Ƙarnaini ya samu a mafaɗar rana, su ma kafirai ne kuma masu aikata laifuffuka da ɓarna a bayan ƙasa. Don haka su ma ya tafiyar da lamarinsu kamar yadda ya yi tare da waɗancan mutanen na farko. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna yana sane da halayen da Zul-Ƙarnaini yake ciki shi da rundunarsa, yana kuma yi musu jagora.
ثُمَّ أَتۡبَعَ سَبَبًا
Open ayah 18:92Sannan ya kama hanya.
حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ بَيۡنَ ٱلسَّدَّيۡنِ وَجَدَ مِن دُونِهِمَا قَوۡمٗا لَّا يَكَادُونَ يَفۡقَهُونَ قَوۡلٗا
Open ayah 18:93Har ya iso (wani gari) tsakanin duwatsu biyu, ya kuma sami wasu mutane a gabansu (watau duwatsun) waɗanda ba sa fahimtar wata magana.
قَالُواْ يَٰذَا ٱلۡقَرۡنَيۡنِ إِنَّ يَأۡجُوجَ وَمَأۡجُوجَ مُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَهَلۡ نَجۡعَلُ لَكَ خَرۡجًا عَلَىٰٓ أَن تَجۡعَلَ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَهُمۡ سَدّٗا
Open ayah 18:94Suka ce: “Ya Zulƙarnaini, lalle Yajuju da Majuju (mutane ne) masu ɓarna a bayan ƙasa, to ko za mu iya biyan ka wata jinga don ka sanya wani shamaki tsakaninmu da su?”
قَالَ مَا مَكَّنِّي فِيهِ رَبِّي خَيۡرٞ فَأَعِينُونِي بِقُوَّةٍ أَجۡعَلۡ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُمۡ رَدۡمًا
Open ayah 18:95Ya ce, “Abin da Ubangijina Ya ba ni ya fi (abin da za ku ba ni), sai dai ku taimake ni da ƙarfi (don) in sanya shamaki tsakaninku da su.
ءَاتُونِي زُبَرَ ٱلۡحَدِيدِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا سَاوَىٰ بَيۡنَ ٱلصَّدَفَيۡنِ قَالَ ٱنفُخُواْۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَعَلَهُۥ نَارٗا قَالَ ءَاتُونِيٓ أُفۡرِغۡ عَلَيۡهِ قِطۡرٗا
Open ayah 18:96“Ku kawo mini guntattakin ƙarafa”; har dai lokacin da ya daidaita (ginin da) duwatsun nan biyu, sai ya ce: “Ku hura wuta da zugazuginku”; har dai yayin da ya mai da shi wuta, sai ya ce: “Ku kawo min narkakkiyar dalma in zuba a kansu.”
فَمَا ٱسۡطَٰعُوٓاْ أَن يَظۡهَرُوهُ وَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ لَهُۥ نَقۡبٗا
Open ayah 18:97Saboda haka ba su samu ikon su haura shi ba, ba su kuma sami ikon huda shi ba.
قَالَ هَٰذَا رَحۡمَةٞ مِّن رَّبِّيۖ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ رَبِّي جَعَلَهُۥ دَكَّآءَۖ وَكَانَ وَعۡدُ رَبِّي حَقّٗا
Open ayah 18:98Ya ce, “Wannan rahama ce daga Ubangijina; sai dai idan alƙawarin Ubangijina ya zo, (watau tashin alƙiyama) to zai mai da shi daga-daga; alƙawarin Ubangijina kuwa ya tabbata gaskiya ne.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Zul-Ƙarnaini ya ci gaba da tafiyarsa tare da sojojinsa har ya kai ga wata hanya tsakanin wasu duwatsu biyu, a kusa da su kuma ya sami wasu mutane waɗanda ba sa fahimtar wani yaren da ba nasu ba. Da suka fahimci cewa, Zul-Ƙarnaini Sarki ne adali sai suka kai masa kukansu na wasu ƙabilu biyu da ake kira Yajuju da Majuju, suka shaida masa cewa, su waɗannan ƙabilu maɓarnata ne a bayan ƙasa, suna kawo wa sauran ƙabilun yankin hare-hare, suna kashe na kashewa su wawashe wa jama’ar gari dukiyoyinsu su lalata musu gonakinsu. Yajuju da Majuju dai suna daga cikin zurriyyar Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Kamannin halittarsu irin ta sauran ‘yan’adam ce babu wani bambanci, suna da yawan gaske da yawan ɓarna da ta’adi a bayan ƙasa. Hakan ya sa ƙabilun suka nemi Zul-Ƙarnaini da ya taimaka musu wajen magance yawan hare-hare da suke kawo musu. Suka tambaye shi cewa, ko zai yarda su ba shi wani lada don ya sanya wani shamaki tsakaninsu da su? Sai Zul-Ƙarnaini ya amsa musu da cewa, abin da Allah ya ba shi na ƙarfin mulki ya fi duk wani abu da za su tara masa, taimakon da kawai yake nema a wajensu shi ne na ma’aikata da kayan aiki na gini da sauran abin da aikin gina ganuwar zai buƙata, shi kuma zai gina musu wannan shamaki a tsakaninsu. Ya umarce su da su kawo masa guntattakin ƙarafa manya-manya, suka kuwa kawo masa, nan take ya fara gina ganuwa tsakanin waɗannan duwatsu guda biyu, har ginin ya kai daidai tsawonsu, sai ya umarci ma’aikatansa da su kunna wa guntattakin ƙarafan nan wuta har sai da suka yi ja jawur, sai ya umarce su su kawo masa narkakkiyar dalma don ya zuba ta a kai. Bayan haka da ta huce ta daskare sai ta zama wani curarren abu guda mai matsanancin ƙarfi wanda ya zama ganuwa tsakanin Yajuju da Majuju da sauran ƙabilu mazauna wannan wuri. Allah ya bayyana cewa, tun bayan gina wannan ganuwa Yajuju da Majuju ba su sami ikon haura ta ba da dawakansu da makamansu domin kai hare-hare, kamar yadda suka saba a baya, haka kuma ba su sami ikon huda ta ta ƙasa da digoginsu ba. An karɓo daga Zainab ‘Yar Jahshin (رضي الله عنها) ta ce: Wata rana Annabi (ﷺ) ya shigo mata a firgice yana cewa,: “La Ilaha Illallahu , Larabawa sun banu daga wani sharri da ya kusanto! A yau an buɗe wata ‘yar ƙofa daga ganuwar Yajuju da Majuju kamar haka.” Sai ya haɗa babban ɗan yatsansa na hannu da mai bi masa ya yi ƙawanya da su. Sai Zainab ta ce: “Ya Manzon Allah, yanzu za a halaka mu alhalin a cikinmu akwai mutanen kirki?” Sai ya ce: “Na’am, idan na banza suka yi yawa.” [Bukhari #3346 da Muslim #2880]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cewa,, yayin da Zul-Ƙarnaini ya dubi aikin wannan ganuwa ya ga ya kammala kamar yadda ya tsara, sai ya bayyana cewa, wannan rahamar Ubangijinsa ce ga mutane da ya tausaya musu, don haka ya tsare su daga sharrin Yajuju da Majuju da wannan ganuwar. To amma fa duk lokacin da wa’adin da Allah ya ajiye na fitowarsu ya zo, watau gabanin tashin alƙiyama, to zai baje wannan ganuwar ya mayar da ita daidai da ƙasa kamar ba a taɓa gina wani abu a wurin ba, kuma tabbas alƙawarin Allah gaskiya ne sai ya tabbata.
۞وَتَرَكۡنَا بَعۡضَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ يَمُوجُ فِي بَعۡضٖۖ وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَجَمَعۡنَٰهُمۡ جَمۡعٗا
Open ayah 18:99Kuma Muka bar sashinsu (mutane) a wannan rana yana cakuɗa da wani sashi; aka kuma busa ƙaho, sannan Muka tattara su gaba ɗaya.
وَعَرَضۡنَا جَهَنَّمَ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡكَٰفِرِينَ عَرۡضًا
Open ayah 18:100Muka kuma bijiro da (wutar) Jahannama a wannan ranar ga kafirai (su gan ta) ƙuru-ƙuru.
ٱلَّذِينَ كَانَتۡ أَعۡيُنُهُمۡ فِي غِطَآءٍ عَن ذِكۡرِي وَكَانُواْ لَا يَسۡتَطِيعُونَ سَمۡعًا
Open ayah 18:101(Su ne) waɗanda idanuwansu suka makance daga ambatona, suka kuma kasance ba sa iya jin (gaskiya).
أَفَحَسِبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن يَتَّخِذُواْ عِبَادِي مِن دُونِيٓ أَوۡلِيَآءَۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا جَهَنَّمَ لِلۡكَٰفِرِينَ نُزُلٗا
Open ayah 18:102Yanzu waɗanda suka kafirta suna tsammanin su riƙi wasu bayina ababen bauta ba Ni ba? Lalle Mun tanadi Jahannama ta zama masauki ga kafirai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, zai bar mutane a wannan ranar suna cakuɗa da junansu. Wannan aya ta 99 za ta iya ɗaukar ma’anar cewa, ranar da Allah (Mai tsarki da daukaka) zai ƙaddara fitowar Yajuju da Majuju bayan ganuwar nan ta fashe, za su fito da yawa suna gauraya da mutane, suna ta ɓarna a kan dukiyoyinsu da lalata musu kayansu. Wannan kuwa zai faru ne kafin tashin alƙiyama. Ayar kuma za ta iya ɗaukar ma’anar cewa, ana nufin ranar alƙiyama da mutane da aljanu za su gauraya da juna wuri ɗaya. Don haka aka bayyana cewa, za a busa ƙaho sai duk matattu su tashi, Allah ya tattara su wuri guda na farkonsu da na ƙarshensu. Shi ya sa ya bayyana cewa, a lokacin ne zai bijiro da Jahannama ga kafirai su gan ta da duk abin da yake cikinta na azaba kafin su shige ta don a ƙara musu baƙin ciki da damuwa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Za a zo da Jahannama a ranar alƙiyama ana janye da ita da linzami dubu saba’in, kowane linzami ɗaya mala’iku dubu saba’in ne suke jan sa.” [Muslim #2842]. Sai kuma ya bayyana halin da kafirai suka kasance a cikinsa wanda ya jawo musu azabar Allah, watau sun makantar da idanunsu da gangan, sun ƙi ganin gaskiya balle su karɓe ta, sannan kuma ba sa iya sauraron gaskiya su yi aiki da ita. Sai kuma ya bayyana cewa, yanzu kafirai za su yi tsammanin su riƙi wasu bayi na Allah su zama majiɓinta al’amarinsu ba Allah ba, suna zaton za su amfane su a ranar alƙiyama, su kare musu azabar Jahannama? Babu shakka wannan zato nasu aikin banza ne. Su sani tun da har sun kafirce wa Allah da manzanninsa sun aikata abin da zukatansu suka ƙawata musu, to lalle kuwa Allah ya tanadar musu Jahannama don ta zamo masauki gare su. Tir da wannan masauki kuwa idan ya zamanto wutar Jahannama ce.
قُلۡ هَلۡ نُنَبِّئُكُم بِٱلۡأَخۡسَرِينَ أَعۡمَٰلًا
Open ayah 18:103Ka ce (da su): “Ba na ba ku labarin waɗanda suka fi asarar ayyukansu ba?
ٱلَّذِينَ ضَلَّ سَعۡيُهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ يُحۡسِنُونَ صُنۡعًا
Open ayah 18:104“(Su ne) waɗanda aikinsu ya ɓace a rayuwarsu ta duniya alhali kuwa su suna tsammanin suna kyautata aiki ne.”
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَلِقَآئِهِۦ فَحَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فَلَا نُقِيمُ لَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَزۡنٗا
Open ayah 18:105Waɗannan (su ne) waɗanda suka kafirce wa ayoyin Ubangijinsu da kuma gamuwa da shi, sai ayyukansu suka lalace, ba za Mu sanya musu wani ma’auni ba a ranar alƙiyama.
ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُمۡ جَهَنَّمُ بِمَا كَفَرُواْ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَرُسُلِي هُزُوًا
Open ayah 18:106Wannan shi ne sakamakonsu, Jahannama, saboda kafircewa da suka yi suka kuma riƙi ayoyina da manzannina abin yi wa izgili. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya ba wa kafirai labarin waɗanda suka fi kowa asarar ayyukansu, watau waɗanda suka yi wahalar banza ba tare da dacewa da wani sakamako ba a wurin Allah, da cewa, su ne waɗanda ayyukansu suka ɓace tun a nan duniya domin sun yi su ba bisa koyarwar Shari’a ba, amma su suna tsammanin suna kyautata aikinsu ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su ne waɗanda suka kafirce wa ayoyin Allah masu tabbatar da Kaɗaitakarsa, suka kuma kafirce wa haɗuwa da shi ranar alƙiyama. Saboda haka ayyukansu suka rushe, Allah ya tabbatar musu da cewa, ba zai sanya musu wani ma’auni ba a ranar alƙiyama, kuma ko da an auna su ba za su yi nauyi a ma’auni ba. Sannan ya bayyana dalilin irin wannan sakamako da ya yi musu da cewa, saboda sun kafirce wa Allah ne, sun kafirce wa ayoyinsa, kuma sun riƙi ayoyin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da manzanninsa abin yi wa izgili.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ كَانَتۡ لَهُمۡ جَنَّٰتُ ٱلۡفِرۡدَوۡسِ نُزُلًا
Open ayah 18:107Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari to Aljannar Firdausi ita ce ta kasance masaukinsu.
خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يَبۡغُونَ عَنۡهَا حِوَلٗا
Open ayah 18:108Suna masu dawwama a cikinta, ba sa neman wani musaya da ita.
قُل لَّوۡ كَانَ ٱلۡبَحۡرُ مِدَادٗا لِّكَلِمَٰتِ رَبِّي لَنَفِدَ ٱلۡبَحۡرُ قَبۡلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَٰتُ رَبِّي وَلَوۡ جِئۡنَا بِمِثۡلِهِۦ مَدَدٗا
Open ayah 18:109Ka ce (da su): “Da kogi zai zamanto tawada don (rubuta) kalmomin Ubangijina, to lalle da kogin ya ƙare kafin kalmomin Ubangijina su ƙare, ko da kuwa Mun zo da ƙarin wasu (koguna) kamarsa.
قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَمَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ رَبِّهِۦ فَلۡيَعۡمَلۡ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَلَا يُشۡرِكۡ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦٓ أَحَدَۢا
Open ayah 18:110Ka ce: “Ni dai mutum ne kawai kamarku da ake yi mini wahayi cewa abin bautarku abin bauta ne Ɗaya; don haka wanda ya kasance yana tsoron gamuwa da Ubangijinsa, to sai ya yi aiki nagari, kada kuma ya tara wani cikin bautar Ubangijinsa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe wannan Sura ne da yi wa muminai masu ayyuka na ƙwarai alƙawarin ba su gidajen Aljannar Firdausi a matsayin masaukinsu ranar alƙiyama. Aljannar Firdausi ita ce ƙololuwar Aljanna kuma mafi daraja. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle a Aljanna akwai daraja ɗari waɗanda Allah ya tanade su don masu jihadi don ɗaukaka addininsa, tazarar da take tsakanin darajoji biyu kamar tazarar da ke tsakanin sama da ƙasa ne. Don haka idan za ku roƙi Allah Aljanna to ku roƙe shi Firdausi, domin ita ce mafi ɗaukakar Aljanna kuma mafi falalarta; daga cikinta ne ƙoramun Aljanna suke ɓuɓɓugowa.” [Bukhari #2790 da Ahmad #8419]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, muminai za su dawwama a cikin wannan Aljannar har abada suna cikin ni’imomin Allah cikakku babu tawaya; ba za su taɓa neman wani musanya da ita ba, saboda ba za su taɓa ƙosawa da ita ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman lamarinsa da yalwar siffofinsa waɗanda sanin bayinsa ba zai iya kewaye su ba. Ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, da a ce za a mayar da ruwan kogi gaba ɗaya ya zama ruwan tawada, a kuma mayar da duk bishiyoyin duniya su zama alƙaluma domin a rubuce kalmomin Ubangiji na Ƙudurarsa da na iliminsa da hikimominsa, to da kogin ya ƙare duk yawansa kuwa ba tare da kalmomin Allah sun ƙare ba, ko da kuwa za a ƙara da wani kogin kamarsa. Sai kuma ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya faɗa wa kafirai cewa, shi mutum ne kamarsu, watau ba mala’ika ne ba, ba kuma aljani ne ba, ba kuma wata halitta ta daban ba. To amma kuma shi Allah ya zaɓe shi ne yana yi masa wahayi cewa, abin bautarsu na gaskiya ɗaya ne ba shi da abokin tarayya, shi ne Allah. To don haka, duk wanda yake jin tsoron haɗuwa da Ubangijinsa, to lalle ya yi aiki na ƙwarai wanda ya dace da Shari’a, kuma ya tsantsanta shi ga Allah shi kaɗai, kada kuma ya haɗa Ubangijinsa da kowa wajen bautarsa.