مريم
Maryam
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
كٓهيعٓصٓ
Open ayah 19:1KAF HA YA AIN SAD
ذِكۡرُ رَحۡمَتِ رَبِّكَ عَبۡدَهُۥ زَكَرِيَّآ
Open ayah 19:2(Wannan) ambaton rahamar Ubangijinka ne (da Ya yi wa) Bawansa Zakariyya.
إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيّٗا
Open ayah 19:3Lokacin da ya kira Ubangijinsa (ya roƙe Shi) cikin asiri.
قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ ٱلۡعَظۡمُ مِنِّي وَٱشۡتَعَلَ ٱلرَّأۡسُ شَيۡبٗا وَلَمۡ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيّٗا
Open ayah 19:4Ya ce: “Ya Ubangiji lalle ƙasusuwana sun yi rauni, kaina kuma ya yi fari fat da furfura, Ubangijina ban kuma zama mai taɓewa ba game da roƙon Ka.
وَإِنِّي خِفۡتُ ٱلۡمَوَٰلِيَ مِن وَرَآءِي وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا فَهَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا
Open ayah 19:5“Kuma lalle ni na ji tsoron dangina a bayana, matata kuma ga ta bakarara ce, saboda haka Ka yi mini baiwa daga gare Ka ta (ɗa) majiɓinci.
يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنۡ ءَالِ يَعۡقُوبَۖ وَٱجۡعَلۡهُ رَبِّ رَضِيّٗا
Open ayah 19:6“(Wanda) zai gaje ni ya kuma gaji iyalan Ya\'aƙub; Ubangijina kuma Ka sanya shi yardajje (a wurinka).” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori da suka gabace ta. Mun riga mun ambaci bayanin malamai a kansu. [Dubi farkon Suratul Baƙara ]. Allah (Mai tsarki da daukaka) a nan yana ba da labarin bawansa ne Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) game da wata babbar rahama da ya yi masa ta samun haihuwa bayan ya tsufa tukuf bai haihu ba. Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ɗaya ne daga cikin annabawan Banu Isra’ila, yana auren `yar’uwar Maryam (() mahaifiyar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). An karɓo daga Maliku ɗan Sa’asa’a (Allah ya kara masa yarda) a cikin dogon hadisinsa na bayanin Isra’in Annabi (ﷺ) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Sai Jibrilu ya hau da shi har suka iso sama ta biyu, sai ya nemi a buɗe ƙofa, sai aka ce masa: “Wane ne?” Sai ya ce: “Jibrilu ne.” Sai aka ce masa: “Wane ne kuma tare da kai?” Sai ya ce: “Muhammadu ne.” Sai aka ce: “Shin an aika masa ne?” Ya ce: “E.” Ko da na shiga sai na ga Yahya da Isa kuma su biyun ‘ya’yan mata zar suke...” [Dubi Bukhari #3430]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi addu’a cikin dare a ɓoye ya roƙi Allah ya ba shi ɗa. Ya nuna wa Ubangijinsa raunin jikinsa saboda tsufa, ga shi kuma furfura duk ta baibaye kansa, kuma ya tabbata ba zai rasa samun biyan buƙatarsa ta samun ɗa ba duk da halin da yake ciki. Sai kuma ya bayyana dalilinsa na neman haihuwa a wannan yanayi, shi ne yana jin tsoron bayan mutuwarsa danginsa ba za su tsaya su kula da tafiyar da harkokin addini ba kamar yadda yake yi a matsayinsa na Shugaban Limaman Banu Isra’ila a zamaninsa, domin ganin yadda suka shagaltar da kansu da harkokin neman abinci. Ya kuma bayyana cewa matarsa bakarara ce ba ta haihuwa; wannan ya sa yake ta roƙon Allah ya dube shi da rahamarsa ya ba shi ɗa wanda zai taimaka masa, wanda kuma zai gaji annabta da ilimi daga gare shi da kuma iyalan Ya\'aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sannan ya roƙi Allah ya sanya shi ya zama yardadde a addininsa da halayensa da iliminsa a wajensa da wajen sauran jama’a.
يَٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ ٱسۡمُهُۥ يَحۡيَىٰ لَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ مِن قَبۡلُ سَمِيّٗا
Open ayah 19:7(Aka ce): Ya Zakariyya, lalle Muna yi maka albishir da samun ɗa, sunansa Yahya, ba Mu kuwa sanya wa wani sunan ba gabaninsa.
قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا وَقَدۡ بَلَغۡتُ مِنَ ٱلۡكِبَرِ عِتِيّٗا
Open ayah 19:8Ya ce: “Ubangijina ta ƙaƙa zan samu ɗa, alhali kuwa matata ta zamanto bakarara ce, ni kuma ga shi na tsufa tukuf”.
قَالَ كَذَٰلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞ وَقَدۡ خَلَقۡتُكَ مِن قَبۡلُ وَلَمۡ تَكُ شَيۡـٔٗا
Open ayah 19:9Ya ce: “Kamar haka Ubangijinka Ya faɗa (cewa): ‘Shi (wannan) mai sauƙi ne a wurina, don kuwa haƙiƙa Na halicce ka alhalin ba ka zama komai ba.’”
قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَ لَيَالٖ سَوِيّٗا
Open ayah 19:10Ya ce: “Ubangijina Ka sanya mini wata alama.” Sai (Allah) Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana (tsawon) kwana uku daidai.”
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ مِنَ ٱلۡمِحۡرَابِ فَأَوۡحَىٰٓ إِلَيۡهِمۡ أَن سَبِّحُواْ بُكۡرَةٗ وَعَشِيّٗا
Open ayah 19:11<b> Sannan (Zakariyya) ya fito wa mutanensa daga wurin ibada ya yi musu ishara cewa: “Ku yi tasbihi safe da maraice.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya amsa addu’ar Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya kuma yi masa albishir da cewa, zai ba shi ɗa kuma sunansa Yahya, kuma babu wanda aka taɓa sa wa wannan suna gabaninsa. Sai Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana mamakinsa da wannan babbar Ƙudura ta Allah; ta yaya zai sami haihuwa alhalin matarsa bakarara ce ba ta haihuwa, shi kuma ga shi ya tsufa tukuf duk jikinsa ya yi rauni? Shin zai dawo masa da ƙarfinsa ne na jiki ya kuma mayar da matarsa mai haihuwa? Ko kuma wata matar zai aura su haihu da ita?! Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa, yana sane da matarsa ba ta haihuwa kuma shi ya tsufa tukuf ya yi rauni. To amma duk wannan abu ne mai sauƙi a wurin Allah ya ba su ɗa cikin wannan hali. Ya kuma tuna masa cewa, a da shi fa babu shi kwata-kwata amma ya halicce shi; to don haka samar da ɗa daga miji tsoho da mata bakarara ya fi komai sauƙi a wurinsa. Sai Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya buƙaci Allah ya nuna masa wata alama da zai ƙara nutsuwa da ita game da albishir da aka yi masa, wadda kuma za ta nuna masa ya kusa samun wannan albishir. Sai ya bayyana masa cewa alamar da zai gani ita ce, ba zai iya magana da mutane ba har tsawon kwana uku, ba kuma don wani ciwo ba, amma kuma zai iya yin zikiri da tsarkake Ubangijinsa. Sai Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fito daga ɗakin ibadarsa zuwa ga mutanensa waɗanda suke jiran sa a wurin ibada domin ya jagorance su. Ya nuna musu da hannu cewa, su ci gaba da tsarkake Allah safe da yamma.
يَٰيَحۡيَىٰ خُذِ ٱلۡكِتَٰبَ بِقُوَّةٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡحُكۡمَ صَبِيّٗا
Open ayah 19:12(Allah ya ce): “Ya Yahaya, ka riƙi littafin (Attaura) da ƙarfi”; Muka kuma ba shi annabci tun yana ƙarami.
وَحَنَانٗا مِّن لَّدُنَّا وَزَكَوٰةٗۖ وَكَانَ تَقِيّٗا
Open ayah 19:13Kuma (Muka hore masa) tausayi daga gare Mu da tsarkin (zuciya), ya kuma kasance mai kiyaye dokokin Allah ne.
وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَيۡهِ وَلَمۡ يَكُن جَبَّارًا عَصِيّٗا
Open ayah 19:14Kuma mai biyayya ga mahaifansa, bai kuma zamanto mai taurin kai mai saɓa wa (umarnin Allah) ba.
وَسَلَٰمٌ عَلَيۡهِ يَوۡمَ وُلِدَ وَيَوۡمَ يَمُوتُ وَيَوۡمَ يُبۡعَثُ حَيّٗا
Open ayah 19:15Kuma aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da kuma ranar da zai mutu da kuma ranar da za a tashe shi rayayye. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa ya cika wa Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) burinsa, ya ba shi ɗa namiji, watau Yahya, ya raya shi har ya kai munzalin ba shi umarni, don haka ya kira shi ya umarce shi da ya riƙe littafin Attaura hannu biyu-biyu, ya kuma ba shi ilimi da fahimta da ƙoƙari tun yana yaro ƙarami. Ya kuma sanya shi mai tausayin mutane, ga shi kuma tsarkakakke daga aikata laifuka, kuma mai kiyaye dokokin Allah; yana aiki da umarninsa yana kuma guje wa haninsa. Ya kuma sanya shi mai biyayya ne ga iyayensa yana tausaya musu tare da kyautatawa, sannan kuma ba mai saɓa wa umarnin Allah da na iyayensa ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa amincin Allah ya tabbata gare shi tun ranar da aka haife shi da ranar da zai mutu da kuma ranar alƙiyama da za a tashe shi da ransa. Waɗannan lokuta uku su ne waɗanda ɗan’adam ya fi samun kewa a cikinsu; to amma idan har ya sami aminci a cikinsu, wannan yana nuna sauran lokutansa ma zai aminta.
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَرۡيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتۡ مِنۡ أَهۡلِهَا مَكَانٗا شَرۡقِيّٗا
Open ayah 19:16Kuma ka ambaci (labarin) Maryamu a cikin (wannan) Littafi lokacin da ta ƙaurace wa mutanenta zuwa wani wuri a nahiyar gabas.
فَٱتَّخَذَتۡ مِن دُونِهِمۡ حِجَابٗا فَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرٗا سَوِيّٗا
Open ayah 19:17Sai ta saka shamaki tsakaninta da su (mutanen nata), to sai Muka aiko mata da Ruhinmu (shi ne Jibrilu) ya bayyana gare ta da surar daidaitaccen mutum.
قَالَتۡ إِنِّيٓ أَعُوذُ بِٱلرَّحۡمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيّٗا
Open ayah 19:18Ta ce: “Lalle ina neman Allah ya tsare ni daga gare ka idan ka zamanto mai taƙawa ne.”
قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَٰمٗا زَكِيّٗا
Open ayah 19:19Ya ce: “Ni manzo ne kawai na Ubangijinki na zo don in yi miki baiwar ɗa tsarkakakke.”
قَالَتۡ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞ وَلَمۡ أَكُ بَغِيّٗا
Open ayah 19:20Ta ce: “Ta ƙaƙa zan samu ɗa, alhalin kuwa wani namiji bai taɓa shafa ta ba, kuma ni ban zamanto mazinaciya ba?”
قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞۖ وَلِنَجۡعَلَهُۥٓ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِ وَرَحۡمَةٗ مِّنَّاۚ وَكَانَ أَمۡرٗا مَّقۡضِيّٗا
Open ayah 19:21(Mala’ika) ya ce: “Kamar haka ne Ubangijinki Ya faɗa (cewa): “Shi (wannan) mai sauƙi ne a wurina, kuma don Mu mayar da shi aya ga mutane da kuma rahama daga gare Mu, kuma (yin haka) ya zamanto al’amari ne tabbatacce (rubuce a Lauhul-Mahafuzu).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin haihuwar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba tare da uba ba. Ya bayyana cewa mahaifiyarsa Maryam `yar Imrana ta ƙaurace wa `yan’uwanta zuwa nahiyar gabas da Baitul Maƙdis domin samun wurin ibada a keɓance ba tare da hayaniyar mutane ba, ba kuma tare da wani ya san abin da take yi ba, don ta samu sakewa da tsare mutuncinta. Maryam (() ita ce `yar Imrana, ɗaya daga cikin limaman Banu Isra’ila a zamaninsa. Mahaifiyarta mace ce mai yawan bautar Allah da hidimar addini. Wannan ya sa ta roƙi Allah ya ba ta ɗa namiji domin ta sadaukar da shi don hidimta wa ɗakin ibada. To amma sai Allah ya ba ta `ya mace ita ce Maryam ((), sai ta yi wa Allah godiya, ta kuma cika alƙawarinta ta sadaukar da ita ga Allah lokacin da ta girma ta kai munzalin `ya mace. [Dubi, Suratu Ali Imrana, aya ta 32-42]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Maryamu (() ta sanya shamaki tsakaninta da mutanenta don kada su gan ta lokacin da take bautar Ubangijinta. Sai Allah ya aiko mata da Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cikin sura kyakkyawa ya bayyana gare ta, sai ta ji tsoron ko wani ne mai mugun nufi gare ta, sai ta nemi tsarin Allah daga sharrinsa kada ya cutar da ita, idan har shi mutum ne mai taƙawa da tsoron Allah. Sai Jibrilu ya fito ya bayyana mata cewa, shi ba mutum ba ne, shi mala’ika ne da Allah ya aiko shi don ya ba ta wani yaro mai tsarki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Maryamu (() ta nuna tsananin mamaki da jin cewa za ta sami ɗa ba tare da tana da aure ba, ita kuma ba mai neman maza ba. Sai Jibrilu ya tabbatar mata da cewa, a hakan Allah zai ba ta ɗa, domin yin haka ya fi komai sauƙi a wajensa. Ya kuma bayyana mata hikimar da ta sa Ubangiji zai yi hakan, shi ne domin yaron ya zama wata shaida ce mai nuna cikar ikon Allah da Ƙudurarsa, kuma ya zama wata rahamar Allah ce ga mutanen da suka yi imani. Ya ƙara tabbatar mata da cewa, wannan halittar yaro da Allah zai yi wani hukunci ne da ya riga ya zartar da shi a littafin Lauhul Mahfuzu, don haka sai ya faru.
۞فَحَمَلَتۡهُ فَٱنتَبَذَتۡ بِهِۦ مَكَانٗا قَصِيّٗا
Open ayah 19:22Sai ta ɗauki cikinsa sannan ta (tafi) da shi wani wuri mai nisa.
فَأَجَآءَهَا ٱلۡمَخَاضُ إِلَىٰ جِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ قَالَتۡ يَٰلَيۡتَنِي مِتُّ قَبۡلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسۡيٗا مَّنسِيّٗا
Open ayah 19:23Sai ciwon naƙuda ya tilasta mata zuwa ga kututturen dabino, ta ce: “Ina ma na mutu tun kafin wannan (abu ya faru), na kuma kasance yasasshiya, mantacciya!”
فَنَادَىٰهَا مِن تَحۡتِهَآ أَلَّا تَحۡزَنِي قَدۡ جَعَلَ رَبُّكِ تَحۡتَكِ سَرِيّٗا
Open ayah 19:24Sai ya kira ta daga ƙarƙashinta cewa: “Kada ki yi baƙin ciki, haƙiƙa Ubangijinki Ya sanya ƙorama a ƙarƙashinki.
وَهُزِّيٓ إِلَيۡكِ بِجِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ تُسَٰقِطۡ عَلَيۡكِ رُطَبٗا جَنِيّٗا
Open ayah 19:25“Ki kuma girgiza kututturen dabinon nan zai zubo miki da lubiyar dabino nunanniya.
فَكُلِي وَٱشۡرَبِي وَقَرِّي عَيۡنٗاۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلۡبَشَرِ أَحَدٗا فَقُولِيٓ إِنِّي نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَٰنِ صَوۡمٗا فَلَنۡ أُكَلِّمَ ٱلۡيَوۡمَ إِنسِيّٗا
Open ayah 19:26“Don haka ki ci, ki sha, kuma ki kwantar da hankalinki; kuma duk mutumin da kika gani (ya yi magana da ke), sai ki yi nuni da cewa: “Na ɗauki alƙawari ga Allah na kame bakina, ba zan yi magana da wani mutum ba yau.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, bayan Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi busa ga Maryamu (() ta ɗauki cikin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai ta ji tsoron abin kunyar da za ta faɗa cikinsa, sai ta tafi wani wuri mai nisa inda ba mai ganin ta. Yayin da lokacin haihuwarta ya zo sai ta nufi wurin wani kututturen busasshiyar itaciyar dabino, a nan ne ta ji duk abin duniya ya dame ta, ga zafin naƙuda, ga shi kuma ba abinci ko abin sha, sannan ga tunanin maganganun mutane idan sun gan ta da jariri. Waɗannan abubuwa su ne suka sanya ta burin ina ma a ce ta mutu kafin wannan lokaci, an daina maganarta kuma an daina tunawa da ita sam-sam. To a nan sai ta ji Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kirawo ta ta ƙarƙashin ƙafafunta cewa, kada ta yi baƙin ciki, Ubangijinta ya tanadi wata ƙorama ta ƙarƙashinta wadda ruwanta zai amfane ta wajen sha da harkokin haihuwa. Ya kuma umarce ta da ta girgiza kututturen busasshiyar itaciyar dabinon nan, za ta zubo mata da lubiyar nunannen dabino mai daɗi, wadda za ta ci ta kuma sha ruwan wannan ƙoramar. Ya kuma umarce ta da ta kwantar da hankalinta, ta yi farin ciki da ɗanta kamar kowace mace da ta sami haihuwar ɗanta lafiya. Ta ɓangaren maganganun mutane kuwa, sai ya umarce ta da cewa, idan ta gamu da wani ya tambaye ta ina ta sami jariri, to ta nuna masa cewa ta ɗauki alƙawari ga Allah na kame bakinta, don haka babu wanda za ta yi magana da shi.
فَأَتَتۡ بِهِۦ قَوۡمَهَا تَحۡمِلُهُۥۖ قَالُواْ يَٰمَرۡيَمُ لَقَدۡ جِئۡتِ شَيۡـٔٗا فَرِيّٗا
Open ayah 19:27Sai ta zo wa mutanenta da shi tana ɗauke da shi; suka ce: “Ya Maryamu, haƙiƙa kin zo da babban abu!
يَٰٓأُخۡتَ هَٰرُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ ٱمۡرَأَ سَوۡءٖ وَمَا كَانَتۡ أُمُّكِ بَغِيّٗا
Open ayah 19:28“Ya ke ‘yar’uwar Haruna, mahaifinki bai kasance lalataccen mutum ba, mahaifiyarki ma ba mazinaciya ba.”
فَأَشَارَتۡ إِلَيۡهِۖ قَالُواْ كَيۡفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي ٱلۡمَهۡدِ صَبِيّٗا
Open ayah 19:29Sai ta nuna shi; (sai) suka ce: “Ta ƙaƙa za mu yi magana da wanda yake ɗan jariri cikin shimfiɗar jego?”
قَالَ إِنِّي عَبۡدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِيَ ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلَنِي نَبِيّٗا
Open ayah 19:30(Isa) ya ce (da su): “Lalle ni bawan Allah ne, Ya ba ni littafi Ya kuma sanya ni Annabi.
وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا
Open ayah 19:31“Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake, kuma Ya umarce ni da yin salla da kuma ba da zakka matuƙar ina raye.
وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَتِي وَلَمۡ يَجۡعَلۡنِي جَبَّارٗا شَقِيّٗا
Open ayah 19:32“Kuma mai biyayya ga mahaifiyata, bai kuma sanya ni mai girman kai mai saɓo ba.
وَٱلسَّلَٰمُ عَلَيَّ يَوۡمَ وُلِدتُّ وَيَوۡمَ أَمُوتُ وَيَوۡمَ أُبۡعَثُ حَيّٗا
Open ayah 19:33“Amincin (Allah) kuma ya tabbata a gare ni ranar da aka haife ni da ranar da zan mutu da kuma ranar da za a tashe ni rayayye.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin Maryamu (() da cewa ta ɗauko Annabi Isa bayan haihuwarsa ta zo da shi wajen mutanenta, su kuma suna ganin ta ɗauke da jariri sai hankalinsu ya tashi, suka shiga zarginta da cewa lalle ta zo musu da wani lamari da babu mai amincewa da shi, domin yaya za a yi mace ta haihu ba tare da ta sadu da ɗa namiji ba. Sai kuma suka jingina ta ga wani mutum mai ibada da kame kai a lokacin, ana kiran sa Haruna, wasu malamai sun ce ɗan’uwanta ne. An karɓo daga Mughira ɗan Shu’uba (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya aike ni zuwa ga mutanen Najrana sai suka ce da ni: “Me za ka ce, ga shi a cikin littafinku kuna karanta cewa: “Ya `yar’uwar Haruna”, alhalin Annabi Musa ya riga Annabi Isa zuwa da shekaru kaza da kaza?” Sai Mughira ya ce: “Sai na rasa me zan faɗa musu. Lokacin da na dawo wajen Manzon Allah (ﷺ) sai na faɗa masa abin da ya faru, sai ya ce: “Shin ba su sani ba ne cewa suna sanya wa `ya’yansu sunayen annabawansu da mutanen kirkin cikinsu waɗanda suka gabace su?” [Muslim #2135]. Suka kuma faɗa mata cewa, mahaifinta bai zama lalataccen mutum ba kuma mahaifiyarta ma ba a san ta da zina ba. Watau dai suna nufin a dangi ita ce farkon wadda ta fara irin wannan mummunar ɗabi’ar. Sai Maryamu ta nuna musu jaririn da ke tare da ita, tana nufin su yi magana da shi, zai fayyace musu gaskiyar abin da ya faru. Sai suka yi mamakin wannan lamari nata, suka ce ta yaya za su yi magana da jaririn da yake ƙunshe cikin zanin goyo? Lokacin da suka faɗi haka sai Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fara yi musu magana, ya bayyana musu cewa, shi bawan Allah ne, kuma ya riga ya ƙaddara zai ba shi littafin Linjila wadda za su yi hukunci da ita, kuma zai ba shi annabta. Ya kuma mayar da shi mai albarka a duk inda yake a kuma kowane zamani, domin zai zamanto mai koya wa mutane ayyukan alheri yana hana su munanan ayyuka. Sannan duk wanda zai zauna da shi zai sami albarkarsa. Ya ƙara da cewa, Allah ya yi masa wasiyyar kula da salla wadda haƙƙi ne babba daga cikin haƙƙoƙin Ubangijinsa, da kula da zakka wadda ita kuma haƙƙi ne daga cikin haƙƙoƙin jama’a. Ya kuma yi masa wasiyya da ya zama mai biyayya ga mahaifiyarsa domin tana da babban haƙƙi a kansa, bai kuma yi shi mutum mai girman kai ga mutane ba, bai kuma zama marashin rabo duniya da lahira ba. Watau shi mutum ne mai sauƙin kai da tawali’u ga mutane mai babban rabo duniya da lahira. Sannan ya nuna wata falalar Allah (Mai tsarki da daukaka) da ya yi masa ta tabbatar masa da aminci ranar da aka haife shi, Shaiɗan bai samu komai daga gare shi ba, da ranar da zai mutu Allah zai tsare shi daga duk wata azaba da kuma ranar alƙiyama lokacin da za a tashe shi a yi masa hisabi, Allah zai tsare shi daga shiga wuta. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wani ɗan’adam Shaiɗan yana shafar sa lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi in ban da Maryamu da ɗanta.” [Muslim #2366]. A wani lafazin ya ce: “Duk wani ɗan’adam da mahaifiyarsa za ta haife shi, Shaiɗan yana tsikarin sa, sai Maryamu da ɗanta.” An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mutum uku ne kaɗai suka yi magana suna cikin zanin goyo: Isa ɗan Maryamu da sahibin Juraiju... da wani yaro wanda yake shan nonon mahaifiyarsa sai wani mutum ya zo wucewa ta gabansu yana haye a kan wata dabba ta alfarma sanye da kyawawan tufafi, sai mahaifiyar yaron nan ta ce: “Ya Allah ka sanya ɗana ya zama kamar wannan.” Sai yaron ya saki nonon ya juya ya kalli mutumin sai ya ce: “Ya Allah kada ka sanya ni kamarsa”, sai kuma ya ci gaba da shan nononsa. Sai kuma ga mutane sun zo wucewa suna dukan wata yarinya suna cewa, ta yi sata ta yi zina, ita kuma tana cewa: “Hasbiyallahu wa ni’imal wakilu .” Sai mahaifiyar yaron nan ta ce: “Ya Allah kada ka sa ɗana shi ma ya zama kamar wannan.” Sai yaron ya bar shan nonon ya ce: “Ya Allah ka sanya ni in zama kamarta.” Sai uwar yaron nan ta yi mamaki. Sai yaron ya ce mata: “Wannan mutum na farko mutum ne mai girman kai, don haka na roƙi Allah kada ya sa in zama irinsa. Ita kuma wannan yarinya da suke cewa ta yi zina ta yi sata, sharri ne kawai mutane suke yi mata, ba ta yi zina ko sata ba, don haka na roƙi Allah ya sa in zama kamarta.” [Bukhari #3436 da Muslim #2550].
ذَٰلِكَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ قَوۡلَ ٱلۡحَقِّ ٱلَّذِي فِيهِ يَمۡتَرُونَ
Open ayah 19:34Wannan shi ne Isa ɗan Maryamu. Zance na gaskiya wanda a kansa ne suke ta shakka suna jayayya (da junansu).
مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٖۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Open ayah 19:35Ba zai yiwu a ce Allah yana da ɗa ba; tsarki ya tabbata a gare Shi. Idan Ya nufi zartar da wani lamari sai kawai Ya ce masa: “Kasance”, sai ko ya kasance.
وَإِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
Open ayah 19:36“Lalle kuma Allah shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Yahudu da Nasara cewa, wannan da aka ambaci yadda haihuwarsa ta kasance da kalamansa yana jariri shi ne gaskiyar magana game da Isa ɗan Maryamu ((), ba kamar yadda Yahudu suke cin mutuncinsa ba suna cewa ɗan zina ne, ba kuma kamar yadda Nasara suke cewa shi ɗan Allah ne ba. Wannan ita ce maganar gaskiya wadda suka daɗe suna jayayya da shakku a kanta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tabbatarwa cewa ba zai yiwu ba a ce Allah yana da ɗa saboda shi mai cikakkiyar wadata ne ba shi da buƙatar komai, kuma kowa da komai mulkinsa ne kuma bayinsa ne. Ya tsarkaka daga duk wata tawaya ko aibi ko gajiyawa; kuma duk sa’adda ya nufi zartar da wani al’amari babba ko ƙarami sai dai kawai ya ce masa: “Kasance”, sai abin ya tabbata. Don haka ne ma Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ƙara tabbatar wa al’ummarsa cewa, shi bawan Allah ne kuma Allah shi ne Ubangijinsa kuma Ubangijinsu wanda komai nasu yana hannunsa, don haka su bauta masa shi kaɗai; wannan ita ce hanya madaidaiciya mai sadar da bawa ga mahaliccinsa.
فَٱخۡتَلَفَ ٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَيۡنِهِمۡۖ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن مَّشۡهَدِ يَوۡمٍ عَظِيمٍ
Open ayah 19:37Sai ƙungiyoyin suka sassaɓa a tsakaninsu; to bone ya tabbata ga waɗanda suka kafirta daga halartar rana mai girma (ita ce alƙiyama).
أَسۡمِعۡ بِهِمۡ وَأَبۡصِرۡ يَوۡمَ يَأۡتُونَنَا لَٰكِنِ ٱلظَّٰلِمُونَ ٱلۡيَوۡمَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 19:38Ka yi mamakin jinsu da ganinsu a ranar da za su zo mana; sai dai azzalumai a wannan rana suna cikin ɓata mabayyani.
وَأَنذِرۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡحَسۡرَةِ إِذۡ قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ وَهُمۡ فِي غَفۡلَةٖ وَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 19:39Ka kuma gargaɗe su game da ranar nadama, lokacin da aka ƙare hisabi, alhali kuwa su (a duniya) suna cikin rafkana kuma su ba sa yin imani.
إِنَّا نَحۡنُ نَرِثُ ٱلۡأَرۡضَ وَمَنۡ عَلَيۡهَا وَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ
Open ayah 19:40Lalle Mu ne za Mu gaje ƙasa da wanda yake bayanta kuma gare Mu ne za a komar da su. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, an samu saɓani tsakanin ƙungiyoyi daban-daban game da lamarin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), wasu suka wuce gona da iri game da shi, wasu kuma suka ƙasƙantar da shi. Nasara ne suka wuce gona da iri kan batunsa, wasu suka ce ɗan Allah ne, wasu kuma suka ce da shi ɗayan uku ne, watau akwai Allah da ɗansa da kuma ruhi mai tsarki; wasu ma suka ce shi ne Allah. Yahudawa kuwa zagin sa suke yi, suna jifan mahaifiyarsa da aikata zina. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, duk waɗannan maganganun ƙarya ne kuma kafirci ne. Sannan ya yi gargaɗi mai tsanani ga kafirai masu wancan saɓani a kan Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa azaba mai tsanani ta tabbata gare su a ranar alƙiyama, ranar da kowa zai halarce ta, na farko da na ƙarshe, rana mai cike da manya-manyan ababen tsoro da azaba iri-iri. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yahudawa sun karkasu ƙungiya saba’in da ɗaya ko da biyu; Nasara su ma sun karkasu ƙungiya saba’in da ɗaya ko da biyu; al’ummata kuwa za su karkasu ƙungiyoyi saba’in da uku.” [Abu Dawud #4596 da Tirmizi #2640 da Ibn Majah #3991]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai za su zama masu ji da ganin gaskiyar da manzanni suka yi ta faɗa musu ita a duniya suna ƙaryata su, ji da gani na mamaki, a lokacin da hakan ba zai yi musu amfanin komai ba, domin sun kasance a nan duniya suna cikin ɓata mabayyani har suka riƙa ganin Allah yana da ɗa ko ɗayan uku ne, suka riƙa ƙaryata gaskiyar da aka zo musu da ita. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya gargaɗi azzalumai game da ranar alƙiyama, ranar da wasu da dama za su yi nadama a kan miyagun ayyukansu, su ma wasu mutanen kirki su yi nadama a kan rashin yawaita ayyukansu na alheri a duniya, domin a ranar an riga an rufe duk takardun ayyuka da abin da ke cikinsu mai kyau da mummuna, an yi wa kowa hisabi, ‘yan Aljanna sun tafi Aljanna, ‘yan wuta ma sun tafi wuta. Amma kuma ga shi a nan duniya kafirai suna cikin rafkanuwa kuma ba sa ma yin imani da gaskiyar da ake faɗa musu game da ranar alƙiyama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, shi ne kaɗai dawwamamme kowa zai halaka ya bar duniyar nan da abin da ke cikinta, Allah shi kaɗai ne zai gaje ta da duk abin da ta ƙunsa, kuma zuwa gare shi kowa zai koma. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ‘yan Aljanna suka shiga Aljanna, ‘yan wuta suka shiga wuta, za a zo da mutuwa a surar ƙosasshen rago, sai a tsayar da shi tsakanin Aljanna da wuta, sai a ce: “Ya ku ‘yan Aljanna, kun san wannan?” Sai su leƙo su ce: “E, wannan mutuwa ce.” Sai kuma a ce: “Ya ku ‘yan wuta, kun san wannan?” Sai su leƙo su kalle shi su ce: “E, wannan mutuwa ce.” Sai a ba da umarni a yanka shi, sai kuma a ce: “Ya ku ‘yan Aljanna, ku dawwama babu mutuwa. Ya ku ‘yan wuta, ku ma ku dawwama babu mutuwa.” Sannan sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: “Ka kuma gargaɗe su game da ranar nadama, lokacin da aka ƙare hisabi, alhali kuwa (a duniya) suna cikin gafala.” Sai ya yi nuni da hannunsa ya ce: “`Yan duniya suna cikin gafalar duniya.” [Bukhari #4730 da Muslim #4849].
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِبۡرَٰهِيمَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقٗا نَّبِيًّا
Open ayah 19:41Kuma ka ambaci (labarin) Ibrahimu a cikin (wannan) littafi (Alƙur’ani). Lalle shi mutum ne mai yawan gaskiya (kuma) Annabi.
إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ يَٰٓأَبَتِ لِمَ تَعۡبُدُ مَا لَا يَسۡمَعُ وَلَا يُبۡصِرُ وَلَا يُغۡنِي عَنكَ شَيۡـٔٗا
Open ayah 19:42Lokacin da ya ce da Babansa: “Ya Babana, me ya sa kake bauta wa abin da ba ya ji ba kuma ya gani, kuma ba ya yi maka maganin komai?
يَٰٓأَبَتِ إِنِّي قَدۡ جَآءَنِي مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَمۡ يَأۡتِكَ فَٱتَّبِعۡنِيٓ أَهۡدِكَ صِرَٰطٗا سَوِيّٗا
Open ayah 19:43“Ya Babana, Lalle ni haƙiƙa wani ilimi ya zo mini wanda kai bai zo maka ba, to ka bi ni zan shiryar da kai hanya madaidaiciya.
يَٰٓأَبَتِ لَا تَعۡبُدِ ٱلشَّيۡطَٰنَۖ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلرَّحۡمَٰنِ عَصِيّٗا
Open ayah 19:44“Ya Babana, kada ka bauta wa Shaiɗan ; lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓo ne ga (Allah) Mai rahama.
يَٰٓأَبَتِ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يَمَسَّكَ عَذَابٞ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ فَتَكُونَ لِلشَّيۡطَٰنِ وَلِيّٗا
Open ayah 19:45“Ya Babana, lalle ni fa ina tsoron azaba ta shafe ka daga (Allah) Mai rahama, sai ka zama majiɓincin Shaiɗan.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzon Allah (ﷺ) cewa, ya bai wa mutanensa labarin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), waɗanda suke cika bakin cewa su suna bin addininsa ne kuma su zurriyyarsa ne. To ya faɗa musu labarinsa da yadda ya fito ƙarara ya yaƙi bautar gumaka, ya yi kira zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, domin shi Annabi ne mai yawan gaskiya da aiki da ita. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi Ibrahimu ya fito fili ya faɗa wa mahaifinsa Ãzara wanda yake bautar gumaka da ya sassaƙa da hannunsa kamar sauran mutanensa cewa, me ya sa zai riƙa bauta musu alhali ya tabbatar cewa gunki ba ya ji kuma ba ya gani ba kuma zai iya kare masa wata cuta ba, ko ya amfane shi da wani abu? Watau ya nuna masa cewa shi kansa ya fi gunkin da yake bauta wa, domin shi yana ji yana gani, kuma ya san abin da zai cuce shi ko ya amfane shi, to don me zai mayar da kansa ƙasa yana bauta wa wani ƙasƙantacce? Ya sake kiran mahaifinsa cikin girmamawa da ladabi ya tabbatar masa cewa, duk da cewa shi ɗansa ne da ya haifa to amma yanzu yana da wani ilimi na sanin Allah mahalicci wanda shi ba ya da shi, don haka ya bi shi zai nuna masa hanya madaidaiciya wadda za ta kai shi ga samun biyan buƙatarsa, ta tserar da shi daga abin da yake ƙi. Ya sake kiran babansa cikin girmamawa yana hana shi bautar Shaiɗan ta hanyar yi masa biyayya. Ya nuna masa cewa, Shaiɗan ya kasance mai yawan saɓa wa Allah ne mai rahama; tun lokacin da ya umarce shi ya yi wa Adamu sujjada amma ya ƙi ya yi masa. Ya kuma fito ƙarara ya nuna wa mahaifinsa cewa yana jiye masa tsoron azabar Allah, idan har bai tuba ba ya bar wannan ɓata da yake kai, domin idan har ya yarda ya mutu a kansa to za a tashe shi tare da Shaiɗan, a kuma haɗa su wuri guda a cikin azaba.
قَالَ أَرَاغِبٌ أَنتَ عَنۡ ءَالِهَتِي يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُۖ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ لَأَرۡجُمَنَّكَۖ وَٱهۡجُرۡنِي مَلِيّٗا
Open ayah 19:46(Babansa) ya ce: “Yanzu Ibrahimu ƙyamar iyayen gijina kake yi? To tabbas idan ba ka bari ba lalle zan jefe ka; ka ɓace min da gani na tsawon lokaci!”
قَالَ سَلَٰمٌ عَلَيۡكَۖ سَأَسۡتَغۡفِرُ لَكَ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ بِي حَفِيّٗا
Open ayah 19:47(Annabi Ibrahimu) ya ce: “Aminci ya tabbata gare ka; zan nema maka gafarar Ubangijina; don ko lalle Shi ya tabbata Mai haba-haba ne da ni.
وَأَعۡتَزِلُكُمۡ وَمَا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَأَدۡعُواْ رَبِّي عَسَىٰٓ أَلَّآ أَكُونَ بِدُعَآءِ رَبِّي شَقِيّٗا
Open ayah 19:48“Zan kuwa ƙaurace muku ku da abin da kuke bauta wa wanda ba Allah ba, in kuma roƙi Ubangijina, na kuma sa tsammanin cewa ba zan zama taɓaɓɓe ba game da roƙon Ubangijina.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Ãzara mahaifin Annabi Ibrahimu ya mayar masa da martani cikin kakkausan lafazi, ya nuna mamakinsa game da yadda Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake ƙyamar bautar gumaka, har ya gargaɗe shi da cewa, idan bai yi watsi da waɗannan maganganun nasa ba to zai jefe shi har lahira, ko kuma in ba haka ba ya ɓace masa da gani, kada ya sake zuwa inda yake ballantana ya sake yi masa irin wannan wa’azin. Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) dai ya ci gaba da bin hanya ta lalama da tausasa harshe ga mahaifinsa yayin da ya ga yadda ya fusata, ya nuna masa zai rabu da shi rabuwa ta mutunci ba tare da ya cutar da shi ba ko ya yi masa abin da bai dace ɗa ya yi wa mahaifinsa ba, har ma ya yi masa alƙawarin zai nema masa gafarar Allah da shiriya, domin ya tabbatar da cewa Allah mai tausaya masa ne matuƙa. Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ɗauki lokaci yana nema wa mahaifinsa gafarar Allah, har lokacin ma da ya yi hijira zuwa Sham ya gina Ka’aba tare da ɗansa Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), a nan ma ya yi addu’a ga mahaifansa su biyu, kamar yadda ya zo a cikin Suratu Ibrahim aya ta 41. To bayan ya gane cewa mahaifinsa ba zai shiriya ba, zai mutu ne yana gaba da Allah da addininsa, sai ya nesanta kansa da shi ya daina yi masa addu’ar neman gafara, kamar yadda ya zo cikin Suratut Tauba, aya ta 114. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da Annabi Ibrahimu ya fitar da rai daga imanin mahaifinsa da mutanensa sai ya shelanta musu cewa, zai ƙaurace musu har da abubuwan da suke bauta wa ba Allah ba, zai koma inda zai samu damar bauta wa Allah shi kaɗai ba tare da haɗa shi da komai ba, ya yi kuma fatan cewa Allah ba zai hana masa duk abin da ya roƙe shi ba.
فَلَمَّا ٱعۡتَزَلَهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا نَبِيّٗا
Open ayah 19:49To lokacin da ya ƙaurace musu tare da abin da suke bauta wa wanda ba Allah ba, sai Muka yi masa baiwa da Is’haƙa da Ya\'aƙubu; kowannensu kuma Muka ba shi annabta.
وَوَهَبۡنَا لَهُم مِّن رَّحۡمَتِنَا وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ لِسَانَ صِدۡقٍ عَلِيّٗا
Open ayah 19:50Muka kuma yi musu baiwa da rahamarmu, kuma Muka sanya musu kyakkyawan ambato maɗaukaki. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Ibrahimu ya cika ƙudurinsa na ƙaurace wa babansa da mutanensa da abin da suke bauta wa ba Allah ba, ya koma inda ya ci gaba da ibada da roƙon Allah, sai ko Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa baiwar samun ɗa namiji tare da matarsa Saratu wanda suka sa wa suna Is’haƙa; shi ma kuma ɗan nasu ya sami ɗa a lokacin rayuwarsa, aka sa masa suna Ya\'aƙubu. Dukkansu kuma Allah ya ba su annabta a lokacin rayuwar Annabi Ibrahim, don su zama masu ɗebe masa kewar rabuwa da mahaifinsa da mutanensa da ya yi. Sannan kuma Allah ya bayyana cewa ya yi musu baiwa ta alheri mai yawa tare da annabci, ya sa suka zamanto ababen yabo mai ɗorewa a gun kowa.
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مُوسَىٰٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ مُخۡلَصٗا وَكَانَ رَسُولٗا نَّبِيّٗا
Open ayah 19:51Ka kuma ambaci (labarin) Musa cikin (wannan) Littafi (Alƙur’ani). Lalle shi zaɓaɓɓe ne, ya kuma kasance Annabi ne Manzo.
وَنَٰدَيۡنَٰهُ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ ٱلۡأَيۡمَنِ وَقَرَّبۡنَٰهُ نَجِيّٗا
Open ayah 19:52Muka kuma kira shi a gefen dutsen Ɗuri na dama, Muka kuma kusanto shi yana mai ganawa (da Mu).
وَوَهَبۡنَا لَهُۥ مِن رَّحۡمَتِنَآ أَخَاهُ هَٰرُونَ نَبِيّٗا
Open ayah 19:53Kuma cikin rahamarmu Muka yi masa baiwa da ɗan’uwansa Haruna (shi ma) Annabi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya ba da labarin Annabi Musa ɗan Imrana a cikin Alƙur’ani mai girma saboda girman darajarsa da babban matsayi da Allah ya ba shi, saboda ya zaɓe shi ya kuma ba shi annabta da manzanci zuwa Banu Isra’ila. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin babban matsayin da ya yi wa Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), shi ne lokacin da ya kirawo shi ta ɓangaren dama na dutsen Ɗuri a saharar Sina’i, ya kusanto da shi gare shi ya kuma gana da shi, a inda ya ji sautin Ubangijinsa. A nan ne kuma ya ba shi allunan Attaura a rubuce don ya karantar da al’ummarsa Banu Isra’ila. Sannan kuma ya yi masa wata baiwar daga cikin rahamarsa ya ba shi ɗan’uwansa Haruna a matsayin wazirinsa wanda zai taimaka masa wajen isar da saƙonsa yayin da shi Musa ɗin ya roƙi haka wajen Allah (Mai tsarki da daukaka), ya kuma ba Haruna shi ma annabci.
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِسۡمَٰعِيلَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صَادِقَ ٱلۡوَعۡدِ وَكَانَ رَسُولٗا نَّبِيّٗا
Open ayah 19:54Kuma ka ambaci (labarin) Isma’ila a cikin (wannan) Littafi (Alƙur’ani). Lalle shi ya kasance mai gaskiyar alƙawari ne, kuma ya kasance Annabi ne, Manzo.
وَكَانَ يَأۡمُرُ أَهۡلَهُۥ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِۦ مَرۡضِيّٗا
Open ayah 19:55Kuma ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsai da) salla da kuma (ba da) zakka, kuma shi yardajje ne a wurin Ubangijinsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ba da labarin Annabi Isma’ila ɗan Annabi Ibrahimu kuma kakan Shugaban `yan’adam (ﷺ). Allah ya yabe shi da cewa shi mutum ne da yake cika duk wani alƙawari da ya ɗauka, ko dai alƙawarin da yake tsakaninsa da Ubangijinsa ko kuma wanda ya yi da mutane, kamar alƙawarin da ya yi wa mahaifinsa Ibrahim na cewa zai same shi mai haƙuri da miƙa wuya lokacin da aka umarci mahaifin nasa da ya yanka shi, kuma ya cika masa wannan alƙawarin ya miƙa kansa gare shi kafin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fanshe shi da rago mai girma. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya ba wa Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) annabci da manzanci, wannan kuwa ita ce babbar baiwar da Allah zai yi wa bawansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa yana tsayar da umarnin Allah cikin iyalansa, yana umartar su da yin salla wadda ta ƙunshi tsarkake bauta ga Allah shi kaɗai, yana kuma umartar su da ba da zakka wadda ta ƙunshi kyautata wa bayin Allah. Don haka shi Isma’ila ya zamanto yana taimakon kansa ya kuma taimaka wa wasu, musamman iyalansa waɗanda sun fi kowa cancantar da’awarsa da koyarwarsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku umarci ‘ya’yanku da salla tun suna da shekara bakwai, ku kuma doke su a kanta idan sun kai shekara goma, kuma ku raba musu makwanci (watau tsakanin maza da mata).” [Ahmad #6756 da Abu Dawud #495]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi Isma’ila ya kasance yardajje a wurinsa, soboda ya zamanto mai neman yardarsa ne koyaushe, yana kuma aiki da umarninsa.
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِدۡرِيسَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقٗا نَّبِيّٗا
Open ayah 19:56Kuma ka ambaci (labarin) Idrisu a cikin (wannan) Littafi (Alƙur’ani). Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya ne, Annabi.
وَرَفَعۡنَٰهُ مَكَانًا عَلِيًّا
Open ayah 19:57Muka kuma ɗaukaka shi daraja maɗaukakiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ba da labarin Annabi Idris a cikin Alƙur’ani wanda shi ma Annabi ne da Allah ya ba shi yawan gaskiya da aiki da ita. Ya kuma ɗaukaka shi ya ba shi matsayi na annabta ya haɗa masa da ‘Siddiƙiyya’ , wanda shi ma matsayi ne da ya ƙunshi cikakkiyar gaskatawa da cikakken ilimi da tabbataccen yaƙini tare da aiki na gari. Ya zo a cikin hadisin Isra’in Annabi (ﷺ) cewa, ya haɗu da shi a sama ta huɗu. [Dubi, Bukhari #3207 da Muslim #162].
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِن ذُرِّيَّةِ ءَادَمَ وَمِمَّنۡ حَمَلۡنَا مَعَ نُوحٖ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡرَٰٓءِيلَ وَمِمَّنۡ هَدَيۡنَا وَٱجۡتَبَيۡنَآۚ إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُ ٱلرَّحۡمَٰنِ خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَبُكِيّٗا۩
Open ayah 19:58Waɗannan su ne annabawa waɗanda Allah Ya yi ni’ima a gare su, daga zuriyar Adamu, da kuma waɗanda Muka ɗauko (a jirgin ruwa) tare da Nuhu, daga kuma zuriyar Ibrahimu da Isra’ila (watau Ya\'aƙubu), da kuma waɗanda Muka shiryar da su Muka kuma zaɓe su. Idan ana karanta musu ayoyin (Allah) Mai rahama sai su faɗi su yi sujjada suna kuka. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci jinsin annabawa gaba ɗaya bayan ya gabatar da ambaton ɗaiɗaikunsu, da cewa waɗannan annabawa su ne mutanen da Allah ya yi wa ni’ima wadda babu irinta, ya ba su annabta da manzanci ya kuma umarce su da su kira mutane zuwa ga tafarki madaidaici. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci cewa sashin waɗannan annabawa sun fito ne daga zurriyyar Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), wasu kuma sun fito daga zurriyyar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), a yayin da wasunsu kuma sun fito ne daga zurriyar Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da jikansa Ya’aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Waɗannan gidaje su ne mafi darajar gidaje a duniya, Allah ya zaɓe su ya fifita su. Allah kuma ya bayyana wani kyakkyawan halinsu na tsoron Allah da girmama maganarsa, da cewa, idan an karanta musu ayoyin Allah mai rahama suka ji abubuwan da suka ƙunsa na siffofin Allah da batun ranar lahira da sakamakon wuta ko Aljanna, sai su faɗi su yi sujjada suna kuka.
۞فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٌ أَضَاعُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّبَعُواْ ٱلشَّهَوَٰتِۖ فَسَوۡفَ يَلۡقَوۡنَ غَيًّا
Open ayah 19:59Sai wasu suka maye gurbinsu bayansu waɗanda suka tozarta salla suka kuma bi sha’awace-sha’awacen (duniya na saɓo); to ba da daɗewa ba za su haɗu da mummunan sharri (a Jahannama).
إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَأُوْلَٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ شَيۡـٔٗا
Open ayah 19:60Sai dai wanda ya tuba ya yi imani ya kuma yi aiki na gari, to waɗannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a tauye musu komai ba.
جَنَّٰتِ عَدۡنٍ ٱلَّتِي وَعَدَ ٱلرَّحۡمَٰنُ عِبَادَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّهُۥ كَانَ وَعۡدُهُۥ مَأۡتِيّٗا
Open ayah 19:61(Watau) gidajen Aljanna na dindindin waɗanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa bayinsa alƙawari da su alhali ba su gan su ba. Lalle alƙawarinsa kuwa ya tabbata mai zuwa ne.
لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوًا إِلَّا سَلَٰمٗاۖ وَلَهُمۡ رِزۡقُهُمۡ فِيهَا بُكۡرَةٗ وَعَشِيّٗا
Open ayah 19:62Ba za su ji wani zancen banza ba a cikinsu sai sallama (daga mala’iku); kuma arzikinsu na nan tare da su a cikinsu safe da yamma.
تِلۡكَ ٱلۡجَنَّةُ ٱلَّتِي نُورِثُ مِنۡ عِبَادِنَا مَن كَانَ تَقِيّٗا
Open ayah 19:63Waccan ita ce Aljannar da za Mu gadar da ita ga wanda ya zamo mai taƙawa daga cikin bayinmu. A waɗannan ayoyi bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin annabawa masu biyayya ga umarninsa da girmama shi da jin tsoronsa, sai kuma ya kawo bayanin wasu bara-gurbin mutane waɗanda suka maye gurbin waɗanda suka gabace su. Ya bayyana cewa, su waɗannan sun tozarta salla wadda ita ce mafi girman rukunin addinin Musulunci bayan Kalmar Shahada, ba su kiyaye ta ba da yin ta a kan lokacinta tare da sharuɗɗanta, suka bi sha’awace-sha’awacensu na saɓon Allah da tozarta umarninsa. Don haka Allah ya tabbatar musu da cewa, za su gamu da matsananciyar azaba a wutar Jahannama. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abin da yake tsakanin bawa da shirka shi ne barin salla.” [Muslim #82]. An karɓo daga Buraida ɗan Husaibu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Alƙawarin da ke tsakaninmu da su (watau kafirai) ita ce salla, don haka wanda ya bar ta ya kafirta.” [Tirmizi #2621 da Nasa’i #463]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya togace waɗanda suka tuba suka dawo suka kula da sallolinsu kamar yadda ya kamata suka watsar da bin sha’awace-sha’awacensu na duniya suka yi nadama a kan abin da suka aikata da niyyar ba za su ƙara ba nan gaba, suka kuma yi imani da Allah da ranar lahira tare da yin ayyuka na gari waɗanda shari’a ta umarce su da aikatawa. To waɗanan Allah ya yi musu alƙawarin shigar da su gidan Aljanna kuma ba za a tauye musu komai na ladan ayyukansu da suka yi ba, kuma ba za a zarge su da laifukan da ba su aikata ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffofin gidajen Aljanna da zai saka masu bin umarninsa, da cewa su gidajen Aljanna ne waɗanda za a dawwama a cikinsu har abada ba za su gushe ba. Su ne waɗanda Allah mai rahama ya yi wa bayinsa na gari alƙawarin su ba tare da sun gan su ba, amma kuma sun ba da gaskiya da su, sun kuma yi ta yin aiki tuƙuru domin su same su. Allah ya tabbatar musu da cewa alƙawarinsa mai zuwa ne domin ba ya saɓa alƙawari. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) a cikin wani dogon hadisi ya ce: “Allah zai tambayi mala’iku game da bayinsa masu zama suna ambatonsa cewa: “Me suke nema?” Sai su ce: “Suna neman Aljanna ne.” Sai ya ce: “Shin sun taɓa ganin ta?” Sai su ce: “A’a.” Sai ya ce: “To ƙaƙa da a ce sun taɓa ganin ta?” Sai mala’iku su ce: “Ai da sun taɓa ganin ta da sai sun fi haka tsananin kwaɗayin ta da neman ta.” [Bukhari #6408 da Muslim #7424]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ambaton siffofin Aljanna da cewa ‘yan Aljanna ba za su taɓa jin wata maganar banza ba a cikin gidan aljannar sai dai maganar aminci, kamar sallamar mala’iku gare su da ambaton Allah da hirar farin ciki da nishaɗi. Hakanan za a riƙa kawo musu kayayyakin ciye-ciye da shaye-shaye da safe da yamma irin wanda suka nuna suna buƙata. Sai kuma ya bayyana cewa, wannan shi ne gidan Aljanna da yake gadar da shi ga bayinsa masu kiyaye dokokinsa.
وَمَا نَتَنَزَّلُ إِلَّا بِأَمۡرِ رَبِّكَۖ لَهُۥ مَا بَيۡنَ أَيۡدِينَا وَمَا خَلۡفَنَا وَمَا بَيۡنَ ذَٰلِكَۚ وَمَا كَانَ رَبُّكَ نَسِيّٗا
Open ayah 19:64(Mala’ika Jibrilu ya ce): “Ba ma sauka sai da umarnin Ubangijinka; abin da yake gabanmu da wanda yake bayanmu da kuma abin da yake tsakanin waɗannan (duka) nasa ne. Ubangijinka kuma bai zama Mai mantuwa ba.
رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا فَٱعۡبُدۡهُ وَٱصۡطَبِرۡ لِعِبَٰدَتِهِۦۚ هَلۡ تَعۡلَمُ لَهُۥ سَمِيّٗا
Open ayah 19:65“(Shi ne) Ubangijin sammai da ƙasa da kuma abin da yake tsakaninsu, sai ka bauta masa kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin ka san wani tamkarsa?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ne ya umarci Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya ba wa Annabi (ﷺ) amsar tambayar da ya yi masa game da rashin zuwansa na wani ɗan lokaci. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi): “Me yake hana ka ziyartar mu kamar yadda ka saba ziyartar mu?” Sai wannan ayar ta 64 ta sauka. [Bukhari #4731]. A cikin ayar, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mala’ika Jibrilu da ya faɗa wa Manzon Allah (ﷺ) cewa: Su mala’iku ba sa saukowa ƙasa sai da izinin Allah, domin babu abin da suke aikatawa sai da umarninsa. Ya kuma bayyana masa cewa abin da suke tunkara a nan gaba na al’amarin lahira, da wanda suke ba shi baya na duniya, da abin da yake tsakanin duniya da lahira duk na Allah ne, mulkinsa ne sai yadda ya ga dama zai kasance. Ya kuma ƙara tabbatar masa da cewa, Ubangijinsa Allah bai zama mai manta wani abu ba, don haka ba zai manta da shi ba, bai gushe ba yana jiɓintar al’amarinsa yana tsara masa komai yadda ya dace. Sai kuma ya bayyana Rububiyyar Allah ga sammai da ƙasa, watau shi ne wanda ya samar da su daga babu, kuma yake tafiyar da su yadda ya ga dama, don haka kada Manzon Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shagaltar da kansa game da wannan, shi dai ya ci gaba da haƙuri da juriya wajen bautar Allah da watsi da ƙyale-ƙyalen duniya. Sannan ya tabbatar da cewa shi Allah ba ya da mai kama da shi a sunayensa da siffofinsa da ayyukansa, shi kaɗai ne kammalalle ta kowace fuska, don haka shi ne kaɗai ya cancanci a bauta masa.
وَيَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَءِذَا مَا مِتُّ لَسَوۡفَ أُخۡرَجُ حَيًّا
Open ayah 19:66Kuma mutum (watau kafiri) yana cewa: “Yanzu idan na mutu anya kuwa za a ta da ni da rai?”
أَوَلَا يَذۡكُرُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَنَّا خَلَقۡنَٰهُ مِن قَبۡلُ وَلَمۡ يَكُ شَيۡـٔٗا
Open ayah 19:67Yanzu shi kafiri ba zai tuna ba cewa Mu Muka halicce shi tun farko kafin ya zama komai?
فَوَرَبِّكَ لَنَحۡشُرَنَّهُمۡ وَٱلشَّيَٰطِينَ ثُمَّ لَنُحۡضِرَنَّهُمۡ حَوۡلَ جَهَنَّمَ جِثِيّٗا
Open ayah 19:68To na rantse da Ubangijinka lalle za Mu tashe su tare da shaiɗanu, sannan za Mu kawo su a gaban Jahannama suna a duddurƙushe.
ثُمَّ لَنَنزِعَنَّ مِن كُلِّ شِيعَةٍ أَيُّهُمۡ أَشَدُّ عَلَى ٱلرَّحۡمَٰنِ عِتِيّٗا
Open ayah 19:69Sannan daga kowace jama’a lalle za Mu ware waɗanda suka fi tsananin yi wa (Allah) Mai rahama tsaurin kai.
ثُمَّ لَنَحۡنُ أَعۡلَمُ بِٱلَّذِينَ هُمۡ أَوۡلَىٰ بِهَا صِلِيّٗا
Open ayah 19:70Sannan babu shakka Mu Muka fi sanin waɗanda suka fi cancanta da ƙonuwa da ita (watau wuta) A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda mutum kafiri yake ƙaryata tashin mutane da ransu bayan sun mutu domin a yi musu hisabi ranar alƙiyama, yana ganin ta yaya za a iya sake tashin sa da rai bayan ya zama ragargazajjen ƙashi? To sai Allah ya faɗa masa wani dalili mai ƙarfi da kowane mai hankali zai fahimta mai kuma nuna yiwuwar abin da yake ƙaryatawa. Allah ya faɗa masa cewa, yanzu ba zai waiwayi bayansa ba ya tuna cewa Allah ne ya halicce shi bayan a da babu shi; to me zai hana ya iya sake halittar sa a karo na biyu domin yi masa hisabi? Babu shakka wanda ya halicce shi lokacin da babu shi, tabbas yana da ikon sake dawo da halittarsa bayan ya zama ƙasusuwa ratattakakku. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: Allah ya ce: “Ɗan’adam ya ƙaryata ni, bai kuma dace ya ƙaryata ni ba, ya kuma zage ni, bai dace kuma ya zage ni ba. Amma ƙaryata ni da ya yi shi ne ya riya cewa ba zan iya dawo da shi ba kamar yadda yake. Zagi na kuwa da ya yi shi ne faɗar cewa ina da mata da ɗa.” [Bukhari #4482]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da Rububiyyarsa ga masu ƙaryata tashi bayan mutuwa domin yin hisabi, da cewa lalle zai tashe su tare da shaiɗanunsu ya tara su domin yi musu hisabi, ya kuma tabbatar musu cewa lalle zai kawo su gaban Jahannama a duddurƙushe a kan gwiwoyinsu suna cike da tsoro da fargabar azabar da take jiran su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin da zai yi musu a wannan ranar da cewa, lalle zai fito da shugabannin kafirci da zalunci daga kowace ƙungiya ta masu addinin ƙarya da ƙungiyoyin azzalumai domin su jagoranci mabiyansu zuwa azabar da take jiran su. Don haka za a sa su a layi gwargwadon girman kafircin kowa da zaluncinsa. Sai kuma ya bayyana cewa duk zai yi haka ne saboda cikar adalcinsa da yalwar iliminsa, ya tabbatar da cewa ya fi kowa sanin wanda ya fi cancantar shiga wuta, domin ya san ayyukan kowa da gwargwadon irin azabar da ta dace da laifinsa.
وَإِن مِّنكُمۡ إِلَّا وَارِدُهَاۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتۡمٗا مَّقۡضِيّٗا
Open ayah 19:71Ba kuma ɗaya daga cikinku face sai ya bi ta kanta (watau wutar Jahannama). (Wannan) ya kasance tabbataccen abu abin hukuntawa a wurin Ubangijinka.
ثُمَّ نُنَجِّي ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّنَذَرُ ٱلظَّٰلِمِينَ فِيهَا جِثِيّٗا
Open ayah 19:72Sannan kuma za Mu tserar da waɗanda suka kiyaye dokokin Allah Mu kuma bar kafirai a duddurƙushe cikinta.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَيُّ ٱلۡفَرِيقَيۡنِ خَيۡرٞ مَّقَامٗا وَأَحۡسَنُ نَدِيّٗا
Open ayah 19:73Kuma idan ana karanta musu ayoyinmu bayyanannu sai waɗanda suka kafirta su ce da waɗanda suka yi imani: “Wane ne daga cikin ƙungiyoyin nan biyu (watau muminai da kafirai) yake da mafificin matsayi da kuma mafi kyan majalisa?”
وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّن قَرۡنٍ هُمۡ أَحۡسَنُ أَثَٰثٗا وَرِءۡيٗا
Open ayah 19:74Kuma al’umma nawa Muka hallaka a gabanninsu waɗanda suke da mafi kyan abin duniya da kyawun gani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana magana ne da dukkan halittunsa, muminai da kafirai, na kirki da na banza, na farko da na ƙarshe, yana tabbatar musu da cewa, kowa daga cikinsu sai ya bi ta kan Jahannama, watau ta kan Siraɗi da zai shimfiɗa shi a kan doron wutar Jahannama a nemi kowa ya tsallaka ta kansa. Allah ya bayyana cewa wucewa ta kansa tabbataccen abu ne da ya riga ya hukunta sai ya faru. Mutane za su wuce ta kan Siraɗi kowa gwargwadon aikinsa, wasu za su wuce kamar ƙiftawar ido, wasu kuma kamar gudun iska, wasu kuma kamar sukuwar dawakai, akwai kuma masu gudu da ƙafafu, akwai kuma masu tafiya, akwai kuma masu jan ciki, sannan da akwai waɗanda za a finciko su a jefa su wutar Jahannama; kowa dai gwargwadon tsoronsa ga Allah (Mai tsarki da daukaka). wanda ya zo a cikin hadisai masu yawa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa zai tserar da masu taƙawa, waɗanda suka kiyaye dokokin Allah, suka aikata abubuwan da ya umarce su da shi, suka kuma bar waɗanda ya hana su. Sai kuma ya ƙyale azzalumai waɗanda suka cuci kawunansu da kafirci da saɓon Allah, a cikin wutar Jahannama a guggurfane a kan gwiwoyinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin kafirai idan suna jin ana karanta ayoyin Allah bayyanannu masu nuna kaɗaitakar Allah da gaskiyar manzanninsa, sai su ce wa muminai: Mu da ku wane ne ya fi matsayi a duniya na yawan dukiya da yawan ‘ya’ya? Kuma wane ne ya fi kyan majalisa?! Watau suna nuna cewa, da a kan gaskiya suke, su kuma suna kan ƙarya, to da muminai sun fi su jin daɗin duniya, wai saboda Allah mai hikima ne ba zai bar masoyansa cikin wahala da ƙasƙanci ba, ya kuma ba wa maƙiyansa rayuwar jin daɗi da ɗaukaka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani gamsasshe inda ya tabbatar musu cewa ya hallaka al\'ummu da yawa kafin waɗannan kafiran masu alfahari da yawan dukiya da tarin ‘ya’ya da ƙyale-ƙyale na duniya, waɗanda sun fi su tarin dukiya da kyau na gani a faɗa saboda tsadar tufafin da suke sanyawa da hutun da ke tattare da su ya fi na waɗannan kafiran nesa ba kusa ba.
قُلۡ مَن كَانَ فِي ٱلضَّلَٰلَةِ فَلۡيَمۡدُدۡ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ مَدًّاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا رَأَوۡاْ مَا يُوعَدُونَ إِمَّا ٱلۡعَذَابَ وَإِمَّا ٱلسَّاعَةَ فَسَيَعۡلَمُونَ مَنۡ هُوَ شَرّٞ مَّكَانٗا وَأَضۡعَفُ جُندٗا
Open ayah 19:75Ka ce (da su): “Wanda ya zamana yana cikin ɓata to (Allah) Mai rahama zai tsawaita ransa Ya yalwata masa; Har sai sanda suka ga abin da ake yi musu alƙawari da shi ne, ko dai azaba (a duniya) ko kuma tashin alƙiyama, to fa za su san wane ne ya fi mummunan matsayi da kuma (wanda) ya fi raunin mataimaka.”
وَيَزِيدُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ٱهۡتَدَوۡاْ هُدٗىۗ وَٱلۡبَٰقِيَٰتُ ٱلصَّٰلِحَٰتُ خَيۡرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابٗا وَخَيۡرٞ مَّرَدًّا
Open ayah 19:76Kuma Allah Yana ƙara shiryar da waɗanda suka bi hanyar shiriya. Wanzazzun ayyuka na gari kuma su suka fi lada a wurin Ubangijinka, suka kuma fi kyakkyawan ƙarshe. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya bayyana wa kafirai masu alfahari da yawan abin duniya da ƙyale-ƙyalenta cewa, duk wani wanda ya zaɓi ɓata a kan shiriya, to Allah zai ƙara masa ɓata a kan ɓatansa; ya ƙara masa son ɓata don ya zamanto uƙuba gare shi, har sai su masu irin waccan magana sun ga abin da ake yi musu alƙawarinsa, ko dai azaba a nan duniya ta hanyar kisa da kamu ko kuma tashin alƙiyama ranar da za su ga sakamakon ayyukansu, to a nan za su tantance su wane ne tsakanin su da muminai suka fi mummunan matsayi, suka fi kuma raunin mataimaka? Sai kuma ya bayyana cewa, muminai waɗanda suka zaɓi shiriya yana ƙara musu shiriya daga falalarsa da rahamarsa, kuma ayyuka na ƙwarai masu wanzuwa da tabbata sun fi amfani a wurin Allah (Mai tsarki da daukaka) ta wajen samun kyakkyawan sakamako da kuma kyakkyawar makoma.
أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي كَفَرَ بِـَٔايَٰتِنَا وَقَالَ لَأُوتَيَنَّ مَالٗا وَوَلَدًا
Open ayah 19:77Shin kuwa ka ga wanda ya kafirce wa ayoyinmu, ya kuma ce: “Lalle tabbas za a ba ni dukiya da ‘ya’yaye?”
أَطَّلَعَ ٱلۡغَيۡبَ أَمِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحۡمَٰنِ عَهۡدٗا
Open ayah 19:78Shin ko ya san gaibu ne, ko kuwa ya sami alƙawari ne a wurin (Allah) Mai rahama?
كَلَّاۚ سَنَكۡتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُۥ مِنَ ٱلۡعَذَابِ مَدّٗا
Open ayah 19:79A’a, ba haka ba ne. Za Mu rubuta abin da yake faɗa, za Mu kuma ƙara masa azaba ninkin-ba-ninkin.
وَنَرِثُهُۥ مَا يَقُولُ وَيَأۡتِينَا فَرۡدٗا
Open ayah 19:80Kuma Mu gaje abin da yake faɗa ɗin ( na dukiyarsa da ‘ya’yansa), ya kuma zo mana shi kaɗai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin wani kafiri ne wanda baya ga kafircinsa har ma yana yi wa muminai izgili, yana furta cewa, shi fa ko a lahira sai Allah ya ba shi kuɗi da ‘ya’ya. An karɓo daga Khabbab ɗan Arat (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na kasance maƙeri, sai kuma ina bin Al-Asi ɗan Wa’ilu bashi, sai na je wajensa domin ya biya ni bashina, sai ya ce min: “Wallahi ba zan biya ka ba har sai ka kafirce wa Muhammad.” Sai na ce masa: “Wallahi ba zan kafirce wa Muhammad ba (ﷺ) har ka mutu a tashe ka.” Sai ya ce: “To je ka, idan na mutu aka tashe ni sai ka dawo in biya ka, domin ni idan an je can ma ni mai kuɗi ne da ‘ya’ya.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar ta 77-80.” [Bukhari #2091 da Muslim #2795]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Manzonsa cewa, shin ko ya ga mutumin da ya kafirce wa ayoyinsa da hujjojin da ya zo da su, amma kuma yana da’awar shi idan ya mutu an tashe shi to lalle sai an ba shi dukiya da ‘ya’ya? Watau yana nufin shi ɗan Aljanna ne; wannan abu da ban mamaki yake. To sai Allah ya bayyana ƙaryarsa, ya tambaye shi cewa, shin ya san gaibu ne da har ya gano shi ɗan Aljanna ne a lahira, ko kuma sun yi wani alƙawari ne da Allah na cewa zai ba shi dukiya da ‘ya’ya a lahira? Allah ya tabbatar da cewa, babu ko ɗaya daga waɗannan abubuwan, watau dai ƙaryarsa ce kawai yake sharawa. To sai Allah ya yi masa alƙawarin narko mai tsanani da cewa, zai rubuta duk waɗannan ƙazaman maganganu da yake furtawa domin yi masa hisabi a kansu, kuma ya ƙara masa azaba a Jahannama ninkin-ba-ninkin saboda hauhawar kafircinsa a nan duniya. Sannan Allah ya bayyana cewa zai ɗauke shi kacokam ya raba shi da dukiyar da ‘ya’yan da yake taƙama da su, ya koma gare shi shi kaɗai tinƙinsa babu ko sutura a jikinsa, a inda zai ga mummunar azabar da take jiran sa.
وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لِّيَكُونُواْ لَهُمۡ عِزّٗا
Open ayah 19:81(Kafirai) kuma suka riƙi wasu abubuwan bauta ba Allah ba don su zama mataimaka a gare su.
كَلَّاۚ سَيَكۡفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمۡ وَيَكُونُونَ عَلَيۡهِمۡ ضِدًّا
Open ayah 19:82A’a, ba haka ba ne. Ba da daɗewa ba za su kafirce wa bautar da suke yi musu, su kuma zama abokan gaba a gare su.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّآ أَرۡسَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ تَؤُزُّهُمۡ أَزّٗا
Open ayah 19:83Shin ba ka san Mu Muka ɗora shaiɗanu a kan kafirai ba suna ingiza su (cikin ɓata) ingizawa?
فَلَا تَعۡجَلۡ عَلَيۡهِمۡۖ إِنَّمَا نَعُدُّ لَهُمۡ عَدّٗا
Open ayah 19:84To kada ka yi gaggawa a kansu; kawai dai Muna ƙididdige musu (kwanakinsu) ɗai da ɗai.
يَوۡمَ نَحۡشُرُ ٱلۡمُتَّقِينَ إِلَى ٱلرَّحۡمَٰنِ وَفۡدٗا
Open ayah 19:85Ranar da za Mu tayar da masu taƙawa zuwa ga (Allah) Mai rahama a matsayin manyan baƙi.
وَنَسُوقُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ إِلَىٰ جَهَنَّمَ وِرۡدٗا
Open ayah 19:86Mu kuma kora kafirai zuwa Jahannama cikin tsananin ƙishirwa.
لَّا يَمۡلِكُونَ ٱلشَّفَٰعَةَ إِلَّا مَنِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحۡمَٰنِ عَهۡدٗا
Open ayah 19:87Ba wani mai ikon yin ceto sai wanda yake da alƙawari a wurin (Allah) Mai rahama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai waɗanda suka saki Allah suka kafirce wa manzanninsa sun riƙi wasu abubuwan bauta ba Allah ba don su zame musu mataimaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa ba za su sami wata biyan buƙata a wajensu ba, kuma babu wani taimako da za su yi musu, hasali ma za su kafirce wa bautar da suke yi musu ranar alƙiyama, su yi baram-baram da juna suna la’antar juna, su zama abokan gabar juna. Sai kuma ya bayyana cewa ya ɗora shaiɗanu a kan kafirai suna ingiza su cikin ayyukan kafirci da saɓon Allah da katange hanyarsa. Sai Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da kada ya nemi gaggauto da hallakarsu, domin Allah yana ƙididdige kwanakin rayuwarsu, idan kwanakinsu suka ƙare ajalinsu ya yi to azabar Allah za ta riske su duk inda suke. Sai kuma ya umarce shi da ya tuna ranar alƙiyama sanda Allah zai tattara muminai masu kiyaye dokokinsa, waɗanda suka aikata abin da ya umarce su suka bar abin da ya hana su, a matsayin manyan baƙi masu daraja ya karrama su. Su kuma kafirai ya kora su zuwa Jahannama suna cikin matsananciyar ƙishirwa, suna neman masu taimaka musu sun rasa, domin a ranar a cikinsu babu wani mai ikon yin ceto, domin ceto duka na Allah ne shi kaɗai, sai ga wanda ya sami izini daga Allah mai rahama saboda ya riƙe alƙawarin da ya yi na imani da Allah da manzanninsa.
وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗا
Open ayah 19:88Suka kuma ce: “(Allah) Mai rahama (wai) yana da ɗa.
لَّقَدۡ جِئۡتُمۡ شَيۡـًٔا إِدّٗا
Open ayah 19:89Haƙiƙa kun zo da babban abu (marar daɗin ji).
تَكَادُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ يَتَفَطَّرۡنَ مِنۡهُ وَتَنشَقُّ ٱلۡأَرۡضُ وَتَخِرُّ ٱلۡجِبَالُ هَدًّا
Open ayah 19:90Sama ta kusa ta kece saboda shi (mummunan furucin), ƙasa kuma ta tsage, duwatsu kuma su zube su yi rugu-rugu.
أَن دَعَوۡاْ لِلرَّحۡمَٰنِ وَلَدٗا
Open ayah 19:91Saboda sun yi da’awar Allah Yana da ɗa!
وَمَا يَنۢبَغِي لِلرَّحۡمَٰنِ أَن يَتَّخِذَ وَلَدًا
Open ayah 19:92Bai kuwa dace da (Allah) Mai rahama Ya zama Yana da ɗa ba.
إِن كُلُّ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ إِلَّآ ءَاتِي ٱلرَّحۡمَٰنِ عَبۡدٗا
Open ayah 19:93Ba wani abu da yake cikin sammai da ƙasa face ya zo wa (Allah) Mai rahama a matsayin bawa.
لَّقَدۡ أَحۡصَىٰهُمۡ وَعَدَّهُمۡ عَدّٗا
Open ayah 19:94Lalle Ya kiyaye da su Ya kuma ƙididdige su sosai.
وَكُلُّهُمۡ ءَاتِيهِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَرۡدًا
Open ayah 19:95Kuma dukkansu kowa zai zo masa a ranar alƙiyama shi kaɗai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wasu Yahudu da Nasara da ma wasu mushirikai sun yi da’awar cewa yana da ɗa. Allah ya nuna cewa masu irin wannan mummunar magana sun zo da wani babban abu wanda girman muninsa ya kusa ya sanya sammai su kekkece ƙasa kuma ta tsattsage duwatsu kuma su zube ƙasa su yi rugu-rugu, saboda sun jingina wa Allah ɗa alhali bai dace ba ko kaɗan Allah mai rahama ya zamana yana da ɗa. Shi ɗa yana nuna buƙatuwa ne, Allah kuma mai cikakkiyar wadata ne ba ya da buƙata a wajen kowa, duk mala’ikun da suke sammai da halittun da suke ƙasa na mutane da aljannu da wasunsu za su je wa Allah mai rahama a matsayin bayi ranar alƙiyama suna masu ƙasƙantar da kawunansu ga Allah mahaliccinsu, dukkansu suna ƙarƙashin ikonsa. Ya tabbatar da cewa, iliminsa ya kewaye su baki ɗaya kuma a lissafe suke a wurinsa ɗaya bayan ɗaya. Kuma dukkansu kowa shi kaɗai zai je wa Allah ranar alƙiyama babu kowa babu komai tare da shi sai ayyukansa. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wanda ya kai Allah haƙurin sauraron mummunan furuci; suna cewa wai Allah yana da ɗa amma duk da haka yana ba su lafiya yana arzuta su.” [Bukhari #6099 da Muslim #2804].
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ سَيَجۡعَلُ لَهُمُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وُدّٗا
Open ayah 19:96Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, to (Allah) Mai rahama zai sanya musu ƙauna.
فَإِنَّمَا يَسَّرۡنَٰهُ بِلِسَانِكَ لِتُبَشِّرَ بِهِ ٱلۡمُتَّقِينَ وَتُنذِرَ بِهِۦ قَوۡمٗا لُّدّٗا
Open ayah 19:97To Mun dai sauƙaƙe shi (Alƙur’ani) da harshenka ne don kawai ka yi wa masu taƙawa albishir da shi, ka kuma gargaɗi mutane masu tsananin jayayya da shi.
وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّن قَرۡنٍ هَلۡ تُحِسُّ مِنۡهُم مِّنۡ أَحَدٍ أَوۡ تَسۡمَعُ لَهُمۡ رِكۡزَۢا
Open ayah 19:98Al’umma nawa Muka hallaka a gabaninsu, shin kana jin ɗuriyar wani daga cikinsu, ko kuwa kana jin ‘yar muryarsu? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana rufe wannan Sura ne da bayyana tanadin ni’imarsa da ya yi wa waɗanda suka yi imani suka yi aiki na ƙwarai, ya yi musu alƙawarin zai sa farin jininsu a zukatan muminai masoyansa a sama da ƙasa, dukkanin bayinsa na gari su so su su ƙaunace su a zukatansu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan Allah yana son bawa sai ya kirawo Jibrilu ya ce masa: “Allah yana son wane, don haka kai ma ka so shi.” Sai Jibrilu shi ma ya yi shela a cikin mala’iku da ke sama ya ce: “Lalle Allah yana son wane don haka ku ma ku so shi”. Sai mala’iku a sama dukkansu su so shi sannan sai a ba shi karɓuwa a bayan ƙasa.” [Bukhari #3209 da Muslim #2637]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata babbar ni’imarsa ga bayinsa, watau yadda ya sauƙaƙe Alƙur’ani da harshen Manzonsa (ﷺ) don ya yi wa mutane wa’azi da shi, ya yi wa masu bin dokokin Allah sau-da-ƙafa albishir na samun babban rabo da gwaggwaɓan sakamako a wurin Allah, ya kuma gargaɗi mutanen da suka yi ƙaurin suna a kafirci da saɓon Allah da shi Alƙur’ani, ya kuma tsayar musu hujja bayyananniya. Sannan Allah ya tsoratar da kafirai ta hanyar bayyana musu yadda ya hallaka al\'ummu da yawa da suka gabace su saboda kafircinsu da ƙaryata manzanninsu, kamar mutanen Annabi Nuhu da Adawa da Samudawa da Fir’auna da mutanensa, waɗanda dukkansu a yanzu babu wanda ake iya jin ɗuriyarsa sai dai a labarai da karatun tarihi. To wannan kaɗai ya isa ya zama wa’azi a gare su.