طه

Taa-Haa

Taa-Haa · Surah 20 · Ayahs: 135 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. ƊaHa.

  2. مَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لِتَشۡقَىٰٓ

    Open ayah 20:2

    Ba Mu saukar maka da Alƙur’ani don ka wahala ba.

  3. إِلَّا تَذۡكِرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰ

    Open ayah 20:3

    Sai don wa’azi ga wanda zai ji tsoron (haɗuwa da Allah).

  4. تَنزِيلٗا مِّمَّنۡ خَلَقَ ٱلۡأَرۡضَ وَٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلۡعُلَى

    Open ayah 20:4

    Saukakke ne daga wanda Ya halicci ƙasa da sammai masu ɗaukaka.

  5. ٱلرَّحۡمَٰنُ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ ٱسۡتَوَىٰ

    Open ayah 20:5

    (Allah) Mai rahama, Ya daidaita a kan Al’arshi.

  6. لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَمَا تَحۡتَ ٱلثَّرَىٰ

    Open ayah 20:6

    Abin da yake sammai da ƙasa, da abin da yake tsakaninsu da kuma abin da yake ƙarƙashin ƙasa, (duka) nasa ne.

  7. وَإِن تَجۡهَرۡ بِٱلۡقَوۡلِ فَإِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ وَأَخۡفَى

    Open ayah 20:7

    Idan kuma ka ɗaga murya da furuci to lalle Shi Yana sane da sirri da abin da ya fi (sirri) ɓuya.

  8. ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ

    Open ayah 20:8

    Allah (Shi ne wanda) babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi; Yana da sunaye mafiya kyau. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori. Mun yi bayanin manufar buɗe wasu surori da irin waɗannan haruffa a farkon Suratul Baƙara . Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi Muhammad (ﷺ) cewa bai saukar masa da Alƙur’ani ba ne don ya wahalar da shi ta hanyar jefa shi cikin damuwa a kan mutanensa ba su yi imani da shi ba. Allah ya saukar masa da Alƙur’ani ne don ya zama tunatarwa da wa’azi ga masu jin tsoron Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasu siffofi nasa da cewa, ban da saukar da Alƙur’ani, shi ne kuma ya halicci ƙasa da sammai bakwai maɗaukaka, kuma mai iko a kan komai da ke cikinsu. Kuma shi ne Allah mai rahama wanda ya daidaita a kan Al’arshinsa, daidaito wanda ya cancanta da shi. Sannan ya siffanta kansa da cewa duk abin da yake cikin sammai da wanda yake bayan ƙasa da na ƙarƙashin ƙasa duk halittarsa ne shi kaɗai, kuma mulkinsa ne, bayinsa ne. Shi ne yake gudanar da su yadda ya ga dama. Haka kuma ya bayyana faffaɗan iliminsa ga halittunsa inda ya nuna cewa, duk ɗaya ne a wurinsa, ko mutum ya ɗaga muryarsa yayin da yake magana ko ya sirranta ta, to shi Allah yana sane da maganar ta ɓoye da ma wadda ta fi ta ɓoyuwa; domin ya san sirrin da aka furta da ma wanda yake cikin zuciya ba a furta shi ba; hakanan ya san wanda ya ɗarsu a zuciya da ma wanda bai ɗarsu a cikinta ba. Watau dai iliminsa ya yalwaci komai babba da ƙarami na fili da na ɓoye. Sai kuma ya tabbatar da Ɗayantakarsa wajen bauta, domin shi kaɗai ne abin bauta na gaskiya yana da kuma sunaye mafiya kyau da kamala.

  9. وَهَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ

    Open ayah 20:9

    Shin kuwa labarin Musa ya zo maka?

  10. إِذۡ رَءَا نَارٗا فَقَالَ لِأَهۡلِهِ ٱمۡكُثُوٓاْ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا لَّعَلِّيٓ ءَاتِيكُم مِّنۡهَا بِقَبَسٍ أَوۡ أَجِدُ عَلَى ٱلنَّارِ هُدٗى 

    Open ayah 20:10

    Lokacin da ya gano wuta sai ya ce da iyalinsa: “Ku zauna (a nan), lalle ni fa na hangi wuta, (zan je) ko na zo muku da garwashinta ko kuma in sami mai nuna mini (hanya) a wurin wutar.” A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tambayar Annabi (ﷺ) cewa ko labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo masa? Lokacin da Annabi Musa ya baro garin Madyana tare da matarsa domin komawa ƙasar haihuwarsa Masar bayan ya yi gudun hijira daga gare ta tsawon shekaru. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana cikin tafiya ne tare da iyalinsa sai ya ɓace hanya, ga kuma tsananin sanyi babu abin ɗumama jiki tare da su. Sai kawai ya hango wuta tana ci a gefen dutsen Ɗuri, sai ya sanar da iyalansa cewa, ya hango wani hasken wuta, su zauna zai je ya zo musu da garwashinta don ɗumama jiki, ko kuma ya sami wanda zai nuna masa hanya a wurin.

  11. فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِيَ يَٰمُوسَىٰٓ

    Open ayah 20:11

    To lokacin da ya zo wurinta (wato wutar), sai aka kira shi (cewa): “Ya Musa.

  12. إِنِّيٓ أَنَا۠ رَبُّكَ فَٱخۡلَعۡ نَعۡلَيۡكَ إِنَّكَ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوٗى

    Open ayah 20:12

    “Lalle Ni, Ni ne fa Ubangijinka, sai ka tuɓe takalmanka; lalle kana a tsarkakakken kwarin Ɗuwa ne.

  13. وَأَنَا ٱخۡتَرۡتُكَ فَٱسۡتَمِعۡ لِمَا يُوحَىٰٓ

    Open ayah 20:13

    “Kuma Ni Na zaɓe ka (da manzanci), sai ka ji abin da za a yiwo ma wahayi (da shi).

  14. إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ

    Open ayah 20:14

    “Lalle Ni, Ni ne Allah, babu wani abin bauta sai Ni, to ka bauta mini, kuma ka tsai da salla don tuna Ni.

  15. إِنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌ أَكَادُ أُخۡفِيهَا لِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا تَسۡعَىٰ

    Open ayah 20:15

    “Lalle alƙiyama za ta zo, ina nufin ɓoye ta ne don a saka wa kowanne rai da irin abin da yake aikatawa.

  16. فَلَا يَصُدَّنَّكَ عَنۡهَا مَن لَّا يُؤۡمِنُ بِهَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ فَتَرۡدَىٰ

    Open ayah 20:16

    “To kada wanda bai yi imani da ita ba ya kuma bi son ransa ya hana ka gaskata ta, sai ka hallaka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da Annabi Musa ya iso wurin wannan wutar da ya hango sai ya ga ashe wani gagarumin haske ne. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ba ya barci kuma bai kamata ya yi barci ba; yana yin ƙasa da ma’auni kuma yana yin sama da shi, ana ɗaga masa aikin dare kafin aikin rana, da aikin rana kafin na dare. Hijabinsa (shamakinsa) haske ne – a wata ruwayar ya ce ‘wuta ce’ – da ya yaye shi da hasken fuskarsa ya ƙona inda ganinsa ga halitta ya tuƙe.” [Muslim #179]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da Annabi Musa ya iso wajen wannan wutar sai ya ji an kirawo sunansa Musa, a nan ya ji Allah yana tabbatar masa da cewa, shi ne (Allah) Ubangijinsa, don haka ya umarce shi da ya kwaɓe takalmansa domin yana wani kwari ne mai tsarki da ake kira Ɗuwa. Allah ya ci gaba da sanar da Annabinsa cewa ya zaɓe shi a cikin mutane domin ya yi magana da shi ya kuma ba shi manzanci, don haka ya umarce shi da ya saurari abin da za a yi masa wahayi da shi. Allah ya bayyana masa cewa shi ne Allah wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai shi, ya umarce shi da ya bauta masa ya kuma tsayar da salla don ambatonsa da tunawa da shi. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya manta wata salla, to ya sallace ta lokacin da ya tuna ta, ba ta da wata kaffara sai hakan. ‘Kuma ka tsai da salla don tuna ni’.” [Bukhari #597 da Muslim #684]. Allah ya kuma tabbatar masa cewa, lalle alƙiyama gaskiya ce kuma tana nan tafe; ya ɓoye sanin lokacin da za ta zo, babu wanda ya san shi sai shi kaɗai. Kuma ya bayyana hikimar da ke cikin tashin mutane a ranar alƙiyama, shi ne don a yi wa kowa sakamako a kan abin da ya aikata mai kyau da marar kyau. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗe shi da cewa kada ya daka ta duk wani wanda bai yi imani da ranar lahira ba ya kuma bi son zuciyarsa don zai hana shi tunawa da wannan rana da kuma yin aiki domin tanadin zuwanta. Idan kuwa har ya yarda ya bi shi to zai hallaka.

  17. وَمَا تِلۡكَ بِيَمِينِكَ يَٰمُوسَىٰ

    Open ayah 20:17

    “Mene ne kuma wancan yake a hannun damanka ya Musa?”

  18. قَالَ هِيَ عَصَايَ أَتَوَكَّؤُاْ عَلَيۡهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِي وَلِيَ فِيهَا مَـَٔارِبُ أُخۡرَىٰ

    Open ayah 20:18

    (Musa) ya ce: “Ai sandata ce da nake jingina a kanta, ina kuma kaɗo wa dabbobina ganye da ita, ina kuma da sauran wasu buƙatu game da ita.”

  19. قَالَ أَلۡقِهَا يَٰمُوسَىٰ

    Open ayah 20:19

    (Allah) Ya ce: “Jefar da ita ya Musa.”

  20. فَأَلۡقَىٰهَا فَإِذَا هِيَ حَيَّةٞ تَسۡعَىٰ 

    Open ayah 20:20

    Sai ya jefar da ita, sai ga ta ta zama macijiya tana ta sauri.

  21. قَالَ خُذۡهَا وَلَا تَخَفۡۖ سَنُعِيدُهَا سِيرَتَهَا ٱلۡأُولَىٰ

    Open ayah 20:21

    Ya ce: “Kama ta, kuma kada ka ji tsoro; za Mu mai da ita kamar yadda take a da.

  22. وَٱضۡمُمۡ يَدَكَ إِلَىٰ جَنَاحِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٍ ءَايَةً أُخۡرَىٰ

    Open ayah 20:22

    “Kuma ka haɗa hannunka da kwiɓinka zai fito fari sal ba tare da wata cuta ba; (wannan) wata ayar ce daban.

  23. لِنُرِيَكَ مِنۡ ءَايَٰتِنَا ٱلۡكُبۡرَى

    Open ayah 20:23

    “Domin Mu nuna maka irin manya-manyan ayoyinmu.

  24. ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

    Open ayah 20:24

    “Ka tafi wurin Fir’auna don kuwa lalle ya ƙetare iyaka.” A waɗannan ayoyi, bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ginshiƙan imani, watau imani da shi da kuma imani da ranar lahira, sai kuma ya nuna masa wasu ayoyinsa domin zuciyarsa ta ƙara natsuwa, ya ƙara tabbatarwa da cewa shi Manzon Allah ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye shi abin da yake a hannun damarsa, tare da cewa ya fi kowa sanin ko mene ne, don ya jawo hankalinsa ya kuma nuna masa muhimmancin abin da zai nuna masa. Annabi Musa ya amsa wa Allah da cewa sandarsa ce a hannunsa, ya kuma faɗi wasu amfanunnuka guda biyu, amfani na farko ya shafe shi kai-tsaye, watau jingina da ita, na biyu kuwa ya shafi dabbobinsa, shi ne kakkaɓo musu ganyen da suke ci daga itatuwa masu tsawo. Sannan ya ƙara da cewa sandar har ila yau tana da wasu amfanuka na daban ban da waɗanda ya faɗa. Sai Allah ya umarce shi da ya jefar da wannan sandar. Yana jefar da ita kuwa sai nan take ta zama babbar macijiya tana gudu a ƙasa. Ganin haka sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tsorata shi ma ya juya da baya a guje. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya tsaya ya daina gudu ya dawo ya ɗauki sandarsa, ya tabbatar masa cewa zai mayar da ita sanda kamar yadda take a da. Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya miƙa wuya ga umarnin Allah ya kuma ɗauki macijiyan nan, sai ga shi ta koma sanda kamar yadda take da farko. Bayan wannan mu’ujizar kuma sai Allah ya nuna wa Musa wata mu’ujiza ta biyu, ita ce ya umarce shi da ya shigar da hannunsa na dama ta wuyan rigarsa ya haɗa shi da kwiɓinsa sannan ya fito da shi, zai fito yana haske fari ƙal kamar fitila, hasken kuma ba irin na wata cuta ba, kamar cutar albaras. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya yi haka ne don ya nuna masa wasu daga cikin manya-manyan ayoyinsa waɗanda za su ƙara tabbatar masa gaskiyar manzancinsa, ya kuma ƙara samun nutsuwa a zuciyarsa, su kuma zama hujjarsa a gaban Fir’auna da mutanensa. Sai Allah ya umarce shi da ya tafi wurin Fir’auna Sarkin Masar ya kirawo shi zuwa ga gaskiya domin kuwa ya wuce iyaka da kafircinsa da zalunci da ɓarna a bayan ƙasa.

  25. قَالَ رَبِّ ٱشۡرَحۡ لِي صَدۡرِي

    Open ayah 20:25

    (Musa) ya ce: “Ubangijina Ka buɗe mini ƙirjina.

  26. وَيَسِّرۡ لِيٓ أَمۡرِي

    Open ayah 20:26

    “Kuma Ka sauƙaƙa mini lamarina.

  27. وَٱحۡلُلۡ عُقۡدَةٗ مِّن لِّسَانِي

    Open ayah 20:27

    “Ka kuma warware ƙullin da yake a harshena.

  28. يَفۡقَهُواْ قَوۡلِي

    Open ayah 20:28

    “(Don) su fahimci maganata.

  29. وَٱجۡعَل لِّي وَزِيرٗا مِّنۡ أَهۡلِي

    Open ayah 20:29

    “Kuma Ka sanya mini waziri daga dangina.

  30. هَٰرُونَ أَخِي 

    Open ayah 20:30

    “(Watau) ɗau’uwana Haruna.

  31. ٱشۡدُدۡ بِهِۦٓ أَزۡرِي

    Open ayah 20:31

    “Ka ƙarfafa gwiwata da shi.

  32. وَأَشۡرِكۡهُ فِيٓ أَمۡرِي

    Open ayah 20:32

    “Kuma Ka shigar da shi cikin lamarina.

  33. كَيۡ نُسَبِّحَكَ كَثِيرٗا

    Open ayah 20:33

    “Domin mu tsarkake Ka da yawa.

  34. وَنَذۡكُرَكَ كَثِيرًا

    Open ayah 20:34

    “Mu kuma ambace Ka da yawa.

  35. إِنَّكَ كُنتَ بِنَا بَصِيرٗا

    Open ayah 20:35

    “Lalle Kai Ka kasance Kana ganin mu.”

  36. قَالَ قَدۡ أُوتِيتَ سُؤۡلَكَ يَٰمُوسَىٰ

    Open ayah 20:36

    (Allah) Ya ce: “Haƙiƙa an ba ka abin da ka tambaya, ya Musa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi magana da shi ya kuma umarce shi da ya tafi Masar wajen Fir’auna wanda ya yi nisa cikin kafirci, har ma ya yi da’awar shi ubangiji ne abin bauta, sannan kuma ga shi babban azzalumi wanda ba abin da yake yi sai bautar da Banu Isra’ila yana kashe ‘ya’yansu maza yana bautar da matansu. Da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fahimci girman aikin da aka ɗora masa sai ya roƙi Allah wasu buƙatu waɗanda za su taimaka masa ya samu sauke wannan nauyi da Allah ya ɗora masa. <b>Na farko </b>, ya roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yalwata ƙirjinsa, ta yadda zai jure wa duk wani cin-kashi da Fir’auna da mutanensa za su yi masa. Domin har idan ƙirjinsa zai ƙuntata da maganganunsu ko ayyukansu, to zai kasa sauke nauyin da aka ɗora masa. <b>Na biyu </b>, ya roƙe shi ya sauƙaƙa masa lamarinsa, watau ya kawar masa da duk wasu wahalhalu da masibu da ke cikin wannan aiki, ta yadda zai riƙa samun mafita a duk hanyar da ya bi, ya kuma samu karɓuwa a wurin mutanensa cikin sauƙi. <b>Na uku </b>, ya roƙe shi ya warware masa ƙullin da yake kan harshensa, watau ya cire masa in’ina da take damun sa, ta yadda idan yana magana kowa zai fahimce shi cikin sauƙi. <b>Na huɗu </b>, ya roƙe shi ya haɗa shi da wani mataimaki daga cikin danginsa, ya ayyana sunan ɗan’uwansa Haruna a matsayin wanda yake buƙatar a haɗa su tare wajen zartar da wannan babban aiki. Ya bayyana cewa yana son Allah ya ƙarfafa masa gwiwa da wannan ɗan’uwa nasa, ya kuma shigar da shi cikin lamarinsa, watau shi ma ya ba shi annabta ya aika su tare. Sai Annabi Musa ya bayyana amfanin wannan buƙata tasa, da cewa, ya buƙaci haka ne don su haɗu wajen tsarkake Allah da yawa da ambaton sa da yawa, domin Allah yana ganin su ya san kuma halin da suke ciki na rauni da buƙatar duk abubuwan da ya roƙa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa ya amsa duk addu’o’insa, ya biya masa duk buƙatunsa da ya nema.

  37. وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَيۡكَ مَرَّةً أُخۡرَىٰٓ

    Open ayah 20:37

    “Haƙiƙa kuma Mun yi ni’ima a gare ka a wani lokaci.

  38. إِذۡ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ أُمِّكَ مَا يُوحَىٰٓ

    Open ayah 20:38

    “Sanda Muka yiwo wahayi ga mahaifiyarka da abin da ake yin wahayi da shi.

  39. أَنِ ٱقۡذِفِيهِ فِي ٱلتَّابُوتِ فَٱقۡذِفِيهِ فِي ٱلۡيَمِّ فَلۡيُلۡقِهِ ٱلۡيَمُّ بِٱلسَّاحِلِ يَأۡخُذۡهُ عَدُوّٞ لِّي وَعَدُوّٞ لَّهُۥۚ وَأَلۡقَيۡتُ عَلَيۡكَ مَحَبَّةٗ مِّنِّي وَلِتُصۡنَعَ عَلَىٰ عَيۡنِيٓ

    Open ayah 20:39

    “Cewa, ‘ki saka shi (jinjirin) a cikin akwatu, sannan ki jefa shi cikin kogi, to sai kogin ya jefa shi a gaɓa, sai maƙiyina kuma maƙiyinsa ya ɗauke shi.’ Na kuma sanya maka farin jini daga gare Ni, don kuma a yi tarbiyar ka a gaban idona.

  40. إِذۡ تَمۡشِيٓ أُخۡتُكَ فَتَقُولُ هَلۡ أَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ مَن يَكۡفُلُهُۥۖ فَرَجَعۡنَٰكَ إِلَىٰٓ أُمِّكَ كَيۡ تَقَرَّ عَيۡنُهَا وَلَا تَحۡزَنَۚ وَقَتَلۡتَ نَفۡسٗا فَنَجَّيۡنَٰكَ مِنَ ٱلۡغَمِّ وَفَتَنَّٰكَ فُتُونٗاۚ فَلَبِثۡتَ سِنِينَ فِيٓ أَهۡلِ مَدۡيَنَ ثُمَّ جِئۡتَ عَلَىٰ قَدَرٖ يَٰمُوسَىٰ 

    Open ayah 20:40

    “Lokacin da ‘yar’uwarka take tafiya tana cewa (da su): ‘Yanzu ba na haɗa ku da wadda za ta raine shi ba?’ Sai Muka komo da kai zuwa ga mahaifiyarka don zuciyarta ta yi sanyi, kada kuma ta yi baƙin ciki. Kuma ka kashe wani mutum sannan Muka tserar da kai daga uƙuba, Muka kuma jarrabe ka da jarrabobi daban-daban. Sannan ka zauna shekaru a cikin mutanen Madyana, sannan ka zo (nan) daidai lokacin da Na ƙadarta (maka annabta) ya Musa.

  41. وَٱصۡطَنَعۡتُكَ لِنَفۡسِي

    Open ayah 20:41

    “Kuma Na zaɓe ka don kaina. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wasu ni’imomi da ya yi masa a can baya. Ya lissafa ni’imomi takwas a nan: <b>Ta ɗaya, </b> ya tunatar da shi lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi a lokacin Fir’auna yana tsakiyar kashe jarirai maza, don haka ta tsorata matuƙa, sai Allah ya yi mata wahayi da cewa, ta saka shi cikin akwati ta jefa shi cikin ruwa. Sai ta yi hakan, ruwan kuma ya jefo shi a gaɓa, Fir’auna ya ɗauke shi ya rene shi a gidansa har ya zama babban mutum. <b>Ta biyu </b>, Allah ya sanya masa farin jini, kowa ya gan shi sai ya ji yana ƙaunar sa, har Fir’auna da matarsa su ma suka ƙaunace shi, don haka suka ci gaba da kula da shi sosai. <b>Ni’ima ta uku </b>, Allah ya hukunta a gaban idonsa aka rene shi, tare da kulawarsa da kiyayewarsa. <b>Ta huɗu </b>, ita ce lokacin da mahaifiyarsa ta shiga damuwar rashin ganin ɗanta da zamansa a gidan Fir’auna shi kaɗai, har saura ƙiris ta bayyana abin da yake zuciyarta, amma sai Allah ya ɗaure mata zuciyarta ya ba ta juriya. A daidai wannan lokacin sai Allah ya hana shi kama nonon kowace mace, har sai da ‘yar’uwarsa ta je fadar Fir’auna ta faɗa musu cewa akwai mai shayarwa da za ta shayar musu da shi idan suna buƙata. A nan ne aka ba wa mahaifiyarsa dama, ta zo ta ba shi nono ya karɓa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya dawo mata da shi don hankalinta ya kwanta ta daina baƙin cikin rabuwa da shi. <b>Ta biyar </b>, ita ce lokacin da ya girma yana yawo cikin gari sai ya gamu da wani Baƙibɗe yana zaluntar wani Ba’isra’ile, sai ya nemi taimakon Musa. Garin ƙoƙarin kuɓutar da shi sai ya kashe wannan Baƙibɗen, don haka ya ji tsoro ya gudu zuwa garin Madyana. Allah ya tserar da shi daga fushin Fir’auna da uƙubarsa, ya kuma gafarta masa kuskuren kashe rai. <b>Ta shida </b>, ita ce Allah ya yi masa jarrabawa daban-daban; ya haɗu da masifu iri-iri, tun daga cikin mahaifiyarsa har lokacin da ta haife shi ta jefa shi ruwa, mutanen Fir’auna suka tsince shi, ya kuma yi kisan kai ya gudu, duk Allah ya sanya ya haye waɗannan jarrabobin. <b>Ta bakwai </b>, ita ce zamansa a garin Madyana inda ya yi aikin ƙwadago har ya sami yin aure a dalilin haka, sannan ya baro garin daidai lokacin da Allah ya ƙaddara masa samun annabta. Lalle duk waɗannan abubuwa gamon-katari ne daga Allah (Mai tsarki da daukaka). <b>Ta takwas </b>, ita ce zaɓin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa domin ya yi magana da shi, ya ba shi manzanci, ya kuma aike shi zuwa Fir’auna da mutanensa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Annabi Adamu da Annabi Musa sun haɗu sai Musa ya ce wa Adamu: “Shin kai ne wanda ka jefa mutane cikin wahala ka fitar da su daga Aljanna?” Sai Adamu ya ce: “Shin kai ne wanda Allah ya zaɓe ka da manzancinsa, ya zaɓe ka don kansa, ya kuma saukar maka da Attaura?” Sai ya ce: “E.” Sai Adamu ya ce: “Ba ka san abin da ya faru da ni an riga an rubuta mini shi ba tun kafin a halicce shi?” Sai Musa ya ce: “E.” Sai Adamu ya ƙure Musa da hujja.” [Bukhari #4736 da Muslim #2652].

  42. ٱذۡهَبۡ أَنتَ وَأَخُوكَ بِـَٔايَٰتِي وَلَا تَنِيَا فِي ذِكۡرِي

    Open ayah 20:42

    “Ka tafi kai da ɗan’uwanka da ayoyina, kada kuwa ku sassauta game da ambatona.

  43. ٱذۡهَبَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

    Open ayah 20:43

    “Ku tafi wurin Fir’auna, don ko lalle ya wuce iyaka.

  44. فَقُولَا لَهُۥ قَوۡلٗا لَّيِّنٗا لَّعَلَّهُۥ يَتَذَكَّرُ أَوۡ يَخۡشَىٰ

    Open ayah 20:44

    “Sai ku gaya masa magana mai taushi, ko wataƙila zai wa’azantu ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah).”

  45. قَالَا رَبَّنَآ إِنَّنَا نَخَافُ أَن يَفۡرُطَ عَلَيۡنَآ أَوۡ أَن يَطۡغَىٰ

    Open ayah 20:45

    (Musa da Haruna) suka ce: “Ya Ubangijinmu, lalle mu muna tsoron ya far mana ko kuma ya wuce iyaka (wajen yi mana uƙuba).”

  46. قَالَ لَا تَخَافَآۖ إِنَّنِي مَعَكُمَآ أَسۡمَعُ وَأَرَىٰ

    Open ayah 20:46

    Ya ce: “Kada ku ji tsoro; haƙiƙa Ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin (komai). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da ya ba wa Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ɗan’uwansa Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) annabci sai ya umarce su da su tafi zuwa ga Fir’auna wanda ya ƙetare haddi wajen kafirci, har ma ya yi da’awar allantaka, ya kuma gawurta matuƙa wajen zalunci. Allah kuma ya ba wa Musa da ɗan’uwansa Haruna mu’ujizoji waɗanda za su tabbatar wa da Fir’auna da mutanensa gaskiyarsu, ya kuma umarce su da cewa kada su yi rauni wajen ambatonsa a kai-a kai, domin su cika alƙawarin da suka ɗauka na cewa za su ambace shi tare da tsarkake shi da yawa. Allah kuma ya umarce su da su fara bin hanyar hikima wajen kiran Fir’auna; su yi masa magana mai taushi cikin ladabi ba tare da kausasa harshe ba. Ya nuna musu amfanin yin hakan, shi ne don jawo hankalin Fir’auna, wataƙila ya wa’azantu daga abin da za su faɗa masa, ya gane amfaninsa a gare shi, ko kuma ya tsorata ya bar miyagun ayyukansa don jin tsoron abin da zai same shi na azaba idan ya bijire wa wa’azinsu. Sai Annabi Musa da Haruna suka nuna wa Allah (Mai tsarki da daukaka) abin da suke tsoron ya faru lokacin da za su tsaya gaban Fir’auna don su yi masa wa’azi, suka nuna suna jin tsoron ya far musu da cutarwa da uƙuba tun gabanin ma su gama isar masa da saƙon Allah, ko kuma bayan sun isar masa ya ji amma ya yi taurin kai ya bijire. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa musu cewa kada su ji tsoron komai daga Fir’auna, ba zai iya far musu ba, domin Allah yana tare da su yana ba su kariya kuma yana sane da duk abin da yake wakana, yana kuma ganin halin da suke ciki. Daga nan Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna suka sami nutsuwa suka daina jin wani tsoro.

  47. فَأۡتِيَاهُ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولَا رَبِّكَ فَأَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَلَا تُعَذِّبۡهُمۡۖ قَدۡ جِئۡنَٰكَ بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكَۖ وَٱلسَّلَٰمُ عَلَىٰ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلۡهُدَىٰٓ

    Open ayah 20:47

    “Sai ku tafi wajensa sannan ku ce (da shi): “Lalle mu manzannin Ubangijinka ne, sai ka sakar mana Banu-Isra’ila, kada kuma ka azabtar da su; haƙiƙa mun zo maka da aya daga Ubangijinka; aminci kuwa ya tabbata ga wanda ya bi shiriya.

  48. إِنَّا قَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡنَآ أَنَّ ٱلۡعَذَابَ عَلَىٰ مَن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ

    Open ayah 20:48

    “Lalle mu an yi mana wahayi cewa, ita azaba lalle tana nan ga wanda ya ƙaryata ya kuma ba da baya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ɗan’uwansa Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa su tafi wajen Fir’auna su isar masa saƙon da Allah ya aike su da shi. Ya umarce su da abubuwa biyu: Na farko, su kira Fir’auna zuwa ga Musulunci. Na biyu, su ceto Banu Isra’ila daga azaba da bautar da Fir’auna ya jefa su a cikinta shekara da shekaru, domin su ma su sami ‘yanci, ya kuma tsayar musu da Shari’ar Allah. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Abu Sufyana ya faɗa masa cewa lokacin da Hiraƙlu Sarkin Rumawa ya kirawo shi tare da wasu Ƙuraishawa ‘yan kasuwa ya yi umarni a ɗauko wasiƙar da Manzon Allah (ﷺ) ya rubuta masa, a cikinta yana ce masa: “Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai. Daga Muhammadu bawan Allah kuma Manzonsa zuwa ga Hiraƙlu Shugaban Rumawa, aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya...” [Bukhari #6260 da Muslim #1773]. Annabi Musa ya bayyana wa Fir’auna cewa sun zo masa da wasu ayoyi guda biyu, watau mu’ujizar sanda mai zama macijiya da hannu mai haske da Allah ya ba shi. Ya kuma bayyana masa cewa babu mai samun kuɓuta a duniya da lahira sai wanda ya bi Shari’ar Allah ya rungumi shiriya hannu bibbiyu. Suka tabbatar wa da Fir’auna cewa su manzannin Allah ne da ya yi wa wahayi ya aiko su da saƙon cewa duk wanda ya ƙaryata abin da manzanni suka zo da shi daga Allah, ya bijire wa gaskiya, to azaba ta tabbata gare shi.

  49. قَالَ فَمَن رَّبُّكُمَا يَٰمُوسَىٰ

    Open ayah 20:49

    (Fir’auna) ya ce: “Wane ne Ubangijin naku ya Musa?”

  50. قَالَ رَبُّنَا ٱلَّذِيٓ أَعۡطَىٰ كُلَّ شَيۡءٍ خَلۡقَهُۥ ثُمَّ هَدَىٰ 

    Open ayah 20:50

    (Musa) ya ce: “Ubangijinmu (Shi ne) Wanda Ya bai wa kowane abu surar halittarsa sannan Ya shiryar (da shi yadda zai yi tasarrufi).”

  51. قَالَ فَمَا بَالُ ٱلۡقُرُونِ ٱلۡأُولَىٰ

    Open ayah 20:51

    (Fir’auna) ya ce: “To mene ne halin da al’ummun farko suke ciki?”

  52. قَالَ عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّي فِي كِتَٰبٖۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّي وَلَا يَنسَى

    Open ayah 20:52

    (Musa) ya ce: “Saninsu yana wurin Ubangijina a cikin Lauhul-Mahafuzu; Ubangijina kuma ba Ya kuskure (cikin iliminsa) kuma ba Ya mantuwa.

  53. ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَسَلَكَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّن نَّبَاتٖ شَتَّىٰ

    Open ayah 20:53

    “(Shi ne) Wanda Ya sanya muku ƙasa a shimfiɗe, Ya kuma sanya muku hanyoyi na tafiya cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama”, sannan Muka fitar da dangogin shuke-shuke iri-iri da shi (ruwa).

  54. كُلُواْ وَٱرۡعَوۡاْ أَنۡعَٰمَكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ

    Open ayah 20:54

    Ku ci (daga tsirran) kuma ku yi kiwon dabbobinku. Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankula.

  55. ۞مِنۡهَا خَلَقۡنَٰكُمۡ وَفِيهَا نُعِيدُكُمۡ وَمِنۡهَا نُخۡرِجُكُمۡ تَارَةً أُخۡرَىٰ

    Open ayah 20:55

    Daga ita (ƙasar) Muka halicce ku, kuma a cikinta za Mu mayar da ku, daga ita kuma za Mu fito da ku a wani karon. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da labarta abin da ya faru tsakanin Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna da kuma Fir’auna, yayin da suka kira shi ya ba da gaskiya da Allah shi kaɗai, sai ya shiga nuna musu rashin yardarsa da samuwar Allah, har yake tambayar su cewa, wane ne ma Ubangijinsu wanda suke cewa shi ne ya aiko su? Sai Annabi Musa ya amsa masa da cewa, shi ne wanda ya ba wa kowanne abu da ya halitta surar halittarsa da kamanninsa da ya dace da shi, sannan ya shiryar da ɗaukacin halittunsa ga abin da ya halitta dominsu. Da Fir’auna ya tabbatar ba zai iya rushe hujjar Annabi Musa ba, sai nan take ya canja salon tambayarsa ya koma yana kafa hujja da al\'ummun da suka gabata waɗanda suka aikata kafirci cewa, su kuma me suke ciki, tun da ba su bauta wa Allah ba, sun bauta wa wasu abubuwa daban? Sai Annabi Musa ya nuna masa cewa waɗannan al\'ummun, duk da cewa ba su bauta wa Allah ba, to amma Allah ya ƙididdige ayyukansu da suka yi suna nan a wurinsa a rubuce a littafin Lauhul Mahfuzu, babu abin da iliminsa yake kuɓuce masa, ya san komai babba da ƙarami, kuma ba ya manta duk wani abu da ya sani. Sai kuma Annabi Musa ya ci gaba da faɗa wa Fir’auna siffofin Allah, da cewa, Allah shi ne wanda ya halitta musu ƙasa a shimfiɗe domin su ji daɗin rayuwa da tafiya a kanta, ya kuma sanya musu hanyoyin tafiya a kanta zuwa duk inda suke buƙata su je, ya saukar musu da ruwan sama wanda da shi ne ya fitar musu da shuke-shuke iri-iri. Ya umarce su da su ci daga abin da ya fitar musu daga ƙasa na halal masu daɗi, su kuma ciyar da dabbobinsu irin abincinsu. Sai Allah ya bayyana cewa a cikin waɗannan ni’imomi da ya yi musu ba shakka akwai tarin ayoyi da dalilai masu nuna Ƙudurar Allah da Kaɗaitakarsa ga mutane masu hankali. Sai kuma ya ci gaba da cewa, wannan ƙasar dai mai fitar musu da abincinsu da na dabbobinsu, da ita ne ya halicci mutane, halittar asalinsu, watau Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), mutum na farko da Allah ya halicce shi daga ƙasa. Ya kuma bayyana cewa, bayan sun mutu a cikin ƙasar dai za a binne su, sannan idan lokacin tashin alƙiyama ya zo daga cikinta ne za a fito da su domin tattara su a yi musu hisabi a kan ayyukan da suka gabatar a nan duniya.

  56. وَلَقَدۡ أَرَيۡنَٰهُ ءَايَٰتِنَا كُلَّهَا فَكَذَّبَ وَأَبَىٰ

    Open ayah 20:56

    Kuma haƙiƙa Mun nuna masa (Fir’auna) ayoyinmu dukkansu, sai ya ƙaryata kuma ya ƙi (ba da gaskiya).

  57. قَالَ أَجِئۡتَنَا لِتُخۡرِجَنَا مِنۡ أَرۡضِنَا بِسِحۡرِكَ يَٰمُوسَىٰ

    Open ayah 20:57

    (Fir’auna) ya ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka fitar da mu daga ƙasarmu da sihirinka, ya Musa?

  58. فَلَنَأۡتِيَنَّكَ بِسِحۡرٖ مِّثۡلِهِۦ فَٱجۡعَلۡ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكَ مَوۡعِدٗا لَّا نُخۡلِفُهُۥ نَحۡنُ وَلَآ أَنتَ مَكَانٗا سُوٗى

    Open ayah 20:58

    “To lalle kuwa za mu zo maka da wani sihirin irinsa; sai ka sanya lokaci na musamman tsakaninmu da kai wanda mu ba za mu saɓa masa ba, kai ma haka, (ya zama) wuri ne tsaka-tsaki”

  59. قَالَ مَوۡعِدُكُمۡ يَوۡمُ ٱلزِّينَةِ وَأَن يُحۡشَرَ ٱلنَّاسُ ضُحٗى

    Open ayah 20:59

    (Musa) ya ce: “Lokacin (da na sanya) muku shi ne ranar idi, kuma a tattara mutane da hantsi.”

  60. فَتَوَلَّىٰ فِرۡعَوۡنُ فَجَمَعَ كَيۡدَهُۥ ثُمَّ أَتَىٰ 

    Open ayah 20:60

    Sai Fir’auna ya juya, sai ya haɗa makircinsa, sannan ya zo (wurin da aka shirya).

  61. قَالَ لَهُم مُّوسَىٰ وَيۡلَكُمۡ لَا تَفۡتَرُواْ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا فَيُسۡحِتَكُم بِعَذَابٖۖ وَقَدۡ خَابَ مَنِ ٱفۡتَرَىٰ

    Open ayah 20:61

    Musa ya ce da su: “Kaiconku! Kada fa ku ƙirƙira wa Allah ƙarya, sai Ya hallaka ku da azaba; haƙiƙa kuwa wanda ya ƙirƙira (masa ƙarya) to ya taɓe.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya nuna wa Fir’auna ayoyinsa da dama masu nuna Kaɗaitarsa amma wannan bai sa ya miƙa wuya ya ba da gaskiya ba. Sai ya bijire wa umarnin Allah da haninsa, ya ƙaryata hujjoji na gaskiya da ake faɗa masa, ya ƙi yin imani. Maimakon haka ma sai cewa yake yi wai Annabi Musa da man ya zo ne don ya kore su daga ƙasarsu ta Masar domin ya gaje mulkin Fir’auna ta hanyar amfani da tsafi. Har ma ya yi kurarin zai zo masa da wani tsafi irin nasa domin su kara, don haka ya nemi ya ɗan saurara masa, ya ba shi lokaci da wuri na musamman wanda shi da su za su haɗu a cikinsa, babu mai saɓawa, don a ga wanda tsafinsa zai fi tasiri. Sai Annabi Musa ya sanya wa Fir’auna ranar idi ta zamanto ranar haɗuwarsu, ya kuma nemi a gayyato mutane gaba ɗaya su taru lokacin da suke gabatar da bukukuwan idinsu a lokacin hantsi, domin kowa ya gane wa idonsa yadda za ta kaya. Sai nan da nan Fir’auna ya shirya ƙulle-ƙullen makircinsa, ya aika gari-gari aka gayyato masa manyan matsafa masu tarin yawa. Da ranar haɗuwa ta zo sai ya sanya aka yi wa mutane shelar su tattaro su halarci wurin da aka yi alƙawari. Mutane duk suka hallara maza da mata manya da yara daga ko’ina. Annabi Musa ya fara da yi wa matsafan nan wa’azi da cewa, su kiyayi yi wa Allah ƙarya domin kawai su yaudari mutane da tsafi su ɓatar da su. Idan kuwa suka yi haka Allah zai saukar musu da azabarsa wadda za ta hallaka su. Ya kuma tabbatar musu da cewa duk wanda ya ƙaga wa Allah ƙarya to ya taɓe ya yi hasara.

  62. فَتَنَٰزَعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّجۡوَىٰ

    Open ayah 20:62

    Sai suka tattauna al’amarinsu a tsakaninsu, suka kuma gana a asirce.

  63. قَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَٰنِ لَسَٰحِرَٰنِ يُرِيدَانِ أَن يُخۡرِجَاكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِمَا وَيَذۡهَبَا بِطَرِيقَتِكُمُ ٱلۡمُثۡلَىٰ

    Open ayah 20:63

    Suka ce: “Lalle waɗannan biyun (Musa da Haruna) tabbas matsafa ne, suna so ne su fitar da ku daga ƙasarku da tsafinsu, su kuma tafiyar da kyakkyawar hanyarku (ta rayuwa).

  64. فَأَجۡمِعُواْ كَيۡدَكُمۡ ثُمَّ ٱئۡتُواْ صَفّٗاۚ وَقَدۡ أَفۡلَحَ ٱلۡيَوۡمَ مَنِ ٱسۡتَعۡلَىٰ

    Open ayah 20:64

    “Sai ku yiwo shiri haɗaɗɗe sannan ku zo sahu-sahu. Haƙiƙa yau kam wanda ya yi nasara ya rabuta!” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana lokacin da matsafa suka saurari wa’azin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai suka shiga tafka mahawara a tsakaninsu, suka kuma gana da junansu a asirce. Sai wasu matsafan suka faɗa wa ‘yan’uwansu cewa lalle Musa da Haruna su ma matsafa ne, kuma babbar manufarsu ita ce su yi amfani da tsafinsu su fitar da mutane daga ƙasar Masar, sannan su kawar musu da kyakkyawar hanyar rayuwarsu, domin su su tabbatar da tasu hanyar ta hanyar tsafi, daga nan sai su yi suna, su kuma matsafan tauraronsu ya disashe, hanyar cin abincinsu ta toshe. Don haka ne sai suka ƙara tunzura junansu, suka umarci juna da su koma su shirya su inganta lamarinsu na tsafi da makircinsu, sannan su fito sahu-sahu domin razanarwa da ba da tsoro da cika ido. Sai suka shirya sakin kayansu na tsafi a lokaci guda, suka kuma ba wa junansu tabbacin cewa a yau kam wanda ya yi galaba shi ne zai rabauta.

  65. قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلۡقِيَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَنۡ أَلۡقَىٰ

    Open ayah 20:65

    Suka ce: “Ya Musa, ko dai ka jefa (naka) ko kuma mu mu fara jefa (namu).”

  66. قَالَ بَلۡ أَلۡقُواْۖ فَإِذَا حِبَالُهُمۡ وَعِصِيُّهُمۡ يُخَيَّلُ إِلَيۡهِ مِن سِحۡرِهِمۡ أَنَّهَا تَسۡعَىٰ

    Open ayah 20:66

    Ya ce: “A’a, ku (fara) jefawa.” To saboda sihirinsu sai ga igiyoyinsu da sandunansu ana suranta masa cewa su (macizai ne) suna sauri.

  67. فَأَوۡجَسَ فِي نَفۡسِهِۦ خِيفَةٗ مُّوسَىٰ

    Open ayah 20:67

    Sai Musa ya ɓoye (wani abu) na tsoro a ransa.

  68. قُلۡنَا لَا تَخَفۡ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡأَعۡلَىٰ

    Open ayah 20:68

    Muka ce: “Kada ka ji tsoro, lalle kai kake da rinjaye.

  69. وَأَلۡقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلۡقَفۡ مَا صَنَعُوٓاْۖ إِنَّمَا صَنَعُواْ كَيۡدُ سَٰحِرٖۖ وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيۡثُ أَتَىٰ

    Open ayah 20:69

    “Kuma ka jefar da abin da yake hannunka na dama, za ta haɗiye abin da suka aikata; lalle abin da suka aikata makircin matsafi ne; matsafi kuwa ba ya rabauta duk ta inda ya zo.”

  70. فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سُجَّدٗا قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ هَٰرُونَ وَمُوسَىٰ 

    Open ayah 20:70

    Sai matsafan suka faɗi suna sujjada suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin Haruna da Musa!”

  71. قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَۖ فَلَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ فِي جُذُوعِ ٱلنَّخۡلِ وَلَتَعۡلَمُنَّ أَيُّنَآ أَشَدُّ عَذَابٗا وَأَبۡقَىٰ

    Open ayah 20:71

    (Fir’auna) ya ce: “Yanzu kwa yi imani da shi tun kafin in yi muku izini? Lalle shi ne babbanku wanda ya koya muku tsafi; to lalle zan yayyanke hannayenku da ƙafafuwanku a tarnaƙe (wato hannun dama da ƙafar hagu), kuma tabbas zan gicciye ku a kan kututturen dabino, lalle kuma tabbas za ku san wane ne tsakanin ni da shi wanda ya fi tsananin azaba kuma ta fi ɗorewa.

  72. قَالُواْ لَن نُّؤۡثِرَكَ عَلَىٰ مَا جَآءَنَا مِنَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلَّذِي فَطَرَنَاۖ فَٱقۡضِ مَآ أَنتَ قَاضٍۖ إِنَّمَا تَقۡضِي هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَآ

    Open ayah 20:72

    Suka ce: “Ba za mu fifita ka ba a kan abin da ya zo mana na (ayoyi) mabayyana, da kuma a kan wanda Ya halicce mu. Sai ka hukunta duk abin da za ka hukunta; za ka yi hukunci ne kawai a wannnan rayuwar ta duniya.

  73. إِنَّآ ءَامَنَّا بِرَبِّنَا لِيَغۡفِرَ لَنَا خَطَٰيَٰنَا وَمَآ أَكۡرَهۡتَنَا عَلَيۡهِ مِنَ ٱلسِّحۡرِۗ وَٱللَّهُ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓ

    Open ayah 20:73

    “Lalle mu kam mun yi imani da Ubangijinmu don Ya gafarta mana laifukanmu da kuma abin da ka tilasta mu a kansa na tsafi. Allah kuwa Shi ne Mafi alherin (sakamako), kuma Shi ne Mafi dawwamar (azaba).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da siffanta yadda matsafan Fir’auna suka shigo fili kamar yadda suka tsara, sai suka ba wa Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zaɓi, ko dai ya fara jefa sandarsa ko kuma su su fara jefa nasu sandunan da igiyoyi. Sai Annabi Musa ya ba su zaɓi kan su fara jefa nasu. Sai ko matsafan suka jefa sandunansu da igiyoyinsu na tsafi. Saboda sihirinsu sai aka suranta wa Annabi Musa cewa sun zama macizai suna ta sauri. Ganin haka sai Annabi Musa ya tsorata, amma sai ya ɓoye tsoronsa a ransa. Sai Allah ya kwantar masa da hankali da cewa kada ya ji tsoron abin da yake gani na sihirinsu, lalle shi ne zai yi nasara a kansu. Sai kuma ya umarce shi da ya jefar da sandarsa za ta haɗiye dukkan igiyoyinsu da sandunansu waɗanda suka sihirce idanuwan mutane da su; ya tabbatar masa da cewa abin da suka yi makirci ne kawai na matsafa, kuma duk ta inda matsafi ya ɓullo ba zai yi nasara ba. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bi umarnin Ubangijinsa ya jefar da sandarsa, nan take kuwa sai ta juye ta zama macijiya ta kuma bi sandunansu da igiyoyinsu tana ta haɗiyewa. Da ganin haka sai matsafan suka faɗi gaba ɗaya suka yi sujjada domin sun fahimci abin da Musa ya zo da shi tabbas ba tsafi ne ba; wani abu ne daga Allah, suka ce: Mun yi imani da Ubangijin Musa da Haruna, shi ne kuma Ubangijin duk halittu. Sai Fir’auna saboda tsananin kafircinsa ya fara yi wa matsafan nan barazana da gargaɗi mai tsanani da cewa, don me suka yi imani ba tare da sun nemi izininsa ba? A ƙarshe kuma ya wayance ya juya zancen da cewa, ai Musa ne shugabansu, shi ne ma ya koya musu tsafi, don haka yanzu sun haɗa baki ne da shi don su fitar da mutane daga ƙasar Masar su ƙwace mulki. Saboda haka sai ya azabtar da su ta hanyar yanke musu hannayensu da ƙafafunsu a tarnaƙe, watau hannun dama da ƙafar hagu, sannan kuma lalle sai ya gicciye su a kan kututturen dabino; ya yi kurarin cewa tabbas za su fahimci tsakanin shi da Ubangijin Musa wane ne ya fi tsananin azaba kuma mafi ɗorewa? Allah kuma ya bayyana mana cewa, duk wannan kurarin na Fir’auna bai razana matsafan nan ba balle har su janye imanin da suka yi da Allah Ta’ala, sai kawai suka ce masa lalle su kam ba za su fifita binsa a kan bin abin da ya zo musu na ayoyi bayyanannu ba, ba kuma za su fifita shi a kan Allah wanda ya halicce su ba. Suka nuna masa ya yi duk abin da yake ganin zai yi musu, domin ba shi da wani iko a kansu sai a wannan rayuwa ta duniya mai ƙarewa, kuma ikonsa mai gushewa ne ba zai tabbata ba. Suka ƙara tabbatar masa cewa su sun yi imani da Ubangijinsu suna kuma fatan ya yafe musu laifin kafircinsu da sauran laifuffukansu na baya, na tsafin da ya tilasta su su shirya don su yi nasara a kan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Suka bayyana masa cewa, sakamakon da Allah zai yi musu a kan imaninsu ya fi tagomashi a kan abin da shi ya yi musu alƙawarin zai ba su idan sun yi nasarar murƙushe Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Hakanan azabar Allah ta fi ɗorewa da dawwama a kan wadda yake kurarin zai yi musu don sun yi imani.

  74. إِنَّهُۥ مَن يَأۡتِ رَبَّهُۥ مُجۡرِمٗا فَإِنَّ لَهُۥ جَهَنَّمَ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ

    Open ayah 20:74

    Lalle duk wanda ya zo wa Ubangijinsa yana mai babban laifi to lalle yana da (sakamakon) Jahannama, ba zai mutu a cikinta ba, ba kuma zai rayu ba (rayuwa mai daɗi).

  75. وَمَن يَأۡتِهِۦ مُؤۡمِنٗا قَدۡ عَمِلَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلدَّرَجَٰتُ ٱلۡعُلَىٰ

    Open ayah 20:75

    Wanda kuwa ya zo masa yana mumini ya zamana ya yi aiki na gari, to waɗannan suna da (sakamakon samun) darajoji maɗaukaka.

  76. جَنَّٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ مَن تَزَكَّىٰ

    Open ayah 20:76

    (Watau) gidajen Aljanna na dawwama waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, masu dawwama ne a cikinsu. Wannan kuwa shi ne sakamakon wanda ya tsarkaka (daga saɓo). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙarin bayani ne a kan matsayar da matsafa suka ɗauka ta yin imani da Allah da watsi da duk wani aiki na kafirci da sihiri da suke a kai. Allah ya bayyana cewa, lalle yadda lamarin yake dai shi ne, duk wanda ya je wa Ubangijinsa ranar alƙiyama alhali yana kafiri, to tabbas wannan wutar Jahannama ce makomarsa, zai shige ta ya yi ta zama har abada, ba zai mutu ba balle ya huta daga azaba, ba kuma zai yi wata kyakkyawar rayuwa ba. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Amma ‘yan wuta waɗanda su ne ‘yan wuta, to waɗannan ba za su mutu ba a cikinta, ba kuma za su rayu ba...” [Muslim #185]. Sannan kuma Allah ya bayyana cewa wanda ya gamu da shi yana mumini ya kuma yi kyawawan ayyuka, to masu irin waɗannan kyawawan halaye suna da sakamakon waɗansu darajoji maɗaukaka. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle ‘yan Aljanna suna hango ma’abota wasu ɗakuna a samansu kamar yadda kuke hango tauraro mai haske mai shuɗewa a sararin samaniya na gabas ko na yamma, saboda fifikon da ke tsakaninsu.” Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, waɗannan masaukai ne na annabawa, ban da su babu mai kai wa gare su?” Sai ya ce: “Ba haka ne ba, na rantse da wanda raina yake hannunsa, waɗannan wasu mutane ne da suka yi imani da Allah suka kuma gaskata manzanni.” [Bukhari #6555 da Muslim #2831]. Allah ya bayyana cewa wannan shi ne sakamakon duk wanda ya tsarkaka daga kafirci da saɓon Allah, ko dai saboda bai taɓa aikata su ba, ko kuma ya aikata su amma ya tuba ya tsarkake kansa.

  77. وَلَقَدۡ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِي فَٱضۡرِبۡ لَهُمۡ طَرِيقٗا فِي ٱلۡبَحۡرِ يَبَسٗا لَّا تَخَٰفُ دَرَكٗا وَلَا تَخۡشَىٰ

    Open ayah 20:77

    Haƙiƙa kuma Mun yi wa Musa wahayi cewa: “Ka tafi da bayina cikin dare sannan ka keta musu hanya ƙeƙasasshiya a cikin kogi, ba za ka ji tsoron riskar (Fir’auna da jama’arsa) ba, kuma ba za ka ji tsoron (nutsewa) ba.”

  78. فَأَتۡبَعَهُمۡ فِرۡعَوۡنُ بِجُنُودِهِۦ فَغَشِيَهُم مِّنَ ٱلۡيَمِّ مَا غَشِيَهُمۡ

    Open ayah 20:78

    Sai Fir’auna ya bi su shi da rundunarsa sai abin da ya haɗe su na ruwan kogi ya haɗiye su (suka hallaka kakaf)!

  79. وَأَضَلَّ فِرۡعَوۡنُ قَوۡمَهُۥ وَمَا هَدَىٰ

    Open ayah 20:79

    Fir’auna kuma ya ɓatar da mutanensa bai kuma shiryar (da su) ba.

  80. يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ قَدۡ أَنجَيۡنَٰكُم مِّنۡ عَدُوِّكُمۡ وَوَٰعَدۡنَٰكُمۡ جَانِبَ ٱلطُّورِ ٱلۡأَيۡمَنَ وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰ 

    Open ayah 20:80

    Ya ku Banu-Isra’ila, haƙiƙa Mun tserar da ku daga maƙiyinku, (watau Fir’auna) Muka kuma yi muku alƙawarin (ganawa) a ɓarin dama na dutsen Ɗuri, Muka kuma saukar muku da darɓa da kuma (gasassun tsuntsayen) salwa.

  81. كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ وَلَا تَطۡغَوۡاْ فِيهِ فَيَحِلَّ عَلَيۡكُمۡ غَضَبِيۖ وَمَن يَحۡلِلۡ عَلَيۡهِ غَضَبِي فَقَدۡ هَوَىٰ

    Open ayah 20:81

    Ku ci daga daɗaɗan abin da Muka arzuta ku da shi (na halal), kada kuwa ku ƙetare shi (zuwa haramun), sai fushina ya faɗa muku; wanda kuwa fushina ya faɗa masa, to haƙiƙa ya hallaka.

  82. وَإِنِّي لَغَفَّارٞ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا ثُمَّ ٱهۡتَدَىٰ

    Open ayah 20:82

    Lalle Ni kuma Mai yawan gafara ne ga wanda ya tuba kuma ya yi aiki na gari sannan ya (tabbata bisa) shiriya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana umarnin da ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa ya tattara mutanensa Banu Isra’ila waɗanda suka yi imani da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fita da su daga ƙasar Masar cikin dare ba tare da wani ya gan su ba, ya kuma umarce shi da ya keta musu hanya busasshiya ta cikin kogi bayan ya doke shi da sandarsa, wadda za su bi su ratsa ba tare da sun ji tsoron Fir’auna da rundunarsa su cim masu ba, ko su ji tsoron nutsewa a cikin ruwa. Sai Annabi Musa ya aikata abin da Allah ya umarce shi da yi. Bayan sun fita cikin dare sai Fir’auna da rundunarsa suka bi su a baya. Annabi Musa ya doki kogi da sandarsa sai ruwansa ya dare gida biyu, suka ga hanya ɗoɗar suka bi. Shi ma Fir’auna da rundunarsa da suka iso ba da wata-wata ba sai kawai suka bi wannan hanyar. Nan-take kuwa kogin ya haɗe da su gaba ɗaya, suka hallaka, Annabi Musa kuwa da mutanensa suka tsira. Sai Allah ya tabbatar da cewa Fir’auna fa ya ɓatar da mutanensa ne kawai a lamarin addininsu da na rayuwarsu, bai taɓa ɗora su a kan hanyar shiriya ba tun da suke tare da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da zayyana wa Banu Isra’ila irin ni’imomin da ya yi musu da cewa, shi ne ya tserar da su daga babban maƙiyinsu Fir’auna da rundunarsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya iso Madina ya samu Yahudawa suna azumin Ashura sai ya tambaye su, sai suka ce: “Wannan ita ce ranar da Allah ya ba wa Musa nasara a kan Fir’auna a cikinta.” Sai ya ce: “Mun fi su cancantar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), don haka ku yi azumi.” [Bukhari #4737 da Muslim #1130]. Allah kuma ya yi musu alƙawarin ganawa da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a gefen dama na dutsen Ɗuri domin yin magana da shi da ba shi littafin Attaura mai ƙunshe da haske da shiriya da bayanin shari’arsu. Bayan haka kuma ya saukar musu da darɓa da kuma gasassun tsuntsayen salwa masu kama da fakara masu daɗin nama. Allah ya umarce su da su ci daɗaɗan abubuwa na halal da ya arzuta su da su, kada kuma su kuskura su tsallake abin da ya halatta musu zuwa ga abubuwan da ya haramta musu, ko su riƙa yin almubazzaranci da abin da ya arzuta su da shi na halal ko su yi amfani da shi wajen saɓa masa ko su ce za su hana haƙƙoƙi na wajibi da ke kansu. Idan sun yi haka to fushin Allah zai tabbata a kansu; duk kuwa wanda fushin Allah ya tabbata a kansa, to babu shakka ya taɓe duniya da lahira ba zai taɓa rabauta ba har abada. Sai kuma ya tabbatar da cewa shi mai yawan gafara ne ga duk wanda ya tuba tuba na gaskiya, ya kuma yi aiki na ƙwarai, sannan ya tsaya kyam a kan gaskiya har mutuwarsa.

  83. ۞وَمَآ أَعۡجَلَكَ عَن قَوۡمِكَ يَٰمُوسَىٰ

    Open ayah 20:83

    Kuma me ya sa ka gaggawar barin mutanenka, ya Musa?

  84. قَالَ هُمۡ أُوْلَآءِ عَلَىٰٓ أَثَرِي وَعَجِلۡتُ إِلَيۡكَ رَبِّ لِتَرۡضَىٰ

    Open ayah 20:84

    ( <b>Musa) ya ce: “Su waɗannan (mutane nawa) ai za su biyo bayana ne (ba da jimawa ba), na kuwa yi gaggawa ne zuwa gare Ka ya Ubangijina don neman yardarka.”

  85. قَالَ فَإِنَّا قَدۡ فَتَنَّا قَوۡمَكَ مِنۢ بَعۡدِكَ وَأَضَلَّهُمُ ٱلسَّامِرِيُّ

    Open ayah 20:85

    (Allah) ya ce: “To lalle Mun jarrabi mutanenka a bayanka, Samiri kuma ya ɓatar da su.”

  86. فَرَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ غَضۡبَٰنَ أَسِفٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ أَلَمۡ يَعِدۡكُمۡ رَبُّكُمۡ وَعۡدًا حَسَنًاۚ أَفَطَالَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡعَهۡدُ أَمۡ أَرَدتُّمۡ أَن يَحِلَّ عَلَيۡكُمۡ غَضَبٞ مِّن رَّبِّكُمۡ فَأَخۡلَفۡتُم مَّوۡعِدِي

    Open ayah 20:86

    Sai Musa ya komo zuwa ga mutanensa cike da fushi da baƙin ciki. Ya ce: “Ya ku mutanena, yanzu Ubangijinku bai yi muku kyakkyawan alƙawari ba? Ko kuwa lokacin alƙawarin ne ya yi muku tsawo? Ko kuwa kuna so ne fushin Ubangijinku ya saukar muku, shi ne sai kuka saɓa alƙawarin (da muka yi na ku tabbata bisa imani)?”

  87. قَالُواْ مَآ أَخۡلَفۡنَا مَوۡعِدَكَ بِمَلۡكِنَا وَلَٰكِنَّا حُمِّلۡنَآ أَوۡزَارٗا مِّن زِينَةِ ٱلۡقَوۡمِ فَقَذَفۡنَٰهَا فَكَذَٰلِكَ أَلۡقَى ٱلسَّامِرِيُّ

    Open ayah 20:87

    Suka ce: “Ba mu saɓa alƙawarinka da zaɓin kanmu ba, sai dai mu an ɗora mana kayayyakin nauyi ne na ababan adon mutane (Ƙibɗawa), sai muka jefa su (a cikin wuta), sannan Samiri ya jefa (nasa) kamar yadda (muka yi).”

  88. فَأَخۡرَجَ لَهُمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٞ فَقَالُواْ هَٰذَآ إِلَٰهُكُمۡ وَإِلَٰهُ مُوسَىٰ فَنَسِيَ

    Open ayah 20:88

    To sai ya fitar musu da ɗan maraƙi jika-jika mai kuka, sai suka ce: “Wannan ubangijinku ne kuma ubangijin Musa, amma sai ya manta (da yana nan).”

  89. أَفَلَا يَرَوۡنَ أَلَّا يَرۡجِعُ إِلَيۡهِمۡ قَوۡلٗا وَلَا يَمۡلِكُ لَهُمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا

    Open ayah 20:89

    Yanzu ba sa gani cewa (maraƙin) ba ya mayar musu da magana, kuma ba ya mallakar wata cuta ko amfani gare su? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da ya faru bayan ya hallaka Fir’auna da rundunarsa ya kuma tserar da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da jama’arsa, da cewa, ya yi wa Musa alƙawarin ganawa da shi bayan kwana arba’in don ya ba shi littafin Attaura da zai karantar da mutanensa. Lokacin da wa’adin ganawarsu ya yi sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi gaggawa ya je wajen ganawar ba tare da ya tafi tare da wani daga cikin manyan Banu Isra’ila ba, domin yana cike da shauƙi da ɗokin wannan haɗuwa tasa da Ubangijinsa, sai Allah ya tambaye shi cewa, me ya sa ya yi gaggawar barin mutanensa a baya bai zo tare da su ba? Sai Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya faɗi uzurinsa da cewa ya baro su ne a baya domin ba da jimawa ba su ma za su biyo shi; ya kuma yi gaggawar tahowa ne saboda yana cike da ɗokin ganin ya sami yardar Ubangijinsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da shi cewa, bayan barinsa ya jarrabi mutanensa sun auka ga bautar ɗan maraƙi, kuma ba kowa ne ya jefa su a cikin wannan hallaka ba sai Samiri shi ne ya ɓatar da su. Da jin haka sai Musa ya juya cike da fushi da baƙin ciki a kan abin da ya faru ga mutanensa, ya koma ya same su ya ƙalubalance su da cewa, yanzu sun manta ne Allah ya yi musu kyakkyawan alƙawari na cewa zai saukar musu da littafin Attaura ya kuma shigar da su gidan Aljanna idan sun mutu? Shin lokacin ne ya yi musu tsawo har suka manta da abin da ya ɗora su a kai, ko kuma dai kawai sun yi haka ne da gangan domin fushin Allah ya saukar musu, azabarsa ta tabbata a kansu, shi ya sa suka saɓa alƙawarinsa na tabbata a kan ɗa’a har ya dawo? Sai suka amsa wa Musa da cewa, ba da raɗin kansu ne suka saɓa alƙawarinsa ba, su dai an ɗora musu kayan ado na mutanen Fir’auna sun fito da shi, sai suka ga ba za su iya amfani da su ba, sai suka yi rami suka jefa su, shi ma kuma Samiri sai ya kawo wata ƙasa da ya ɗamƙa daga ƙarƙashin kofaton dokin Jibril (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya jefa a cikin ramin nan. To daga waɗannan kayan ado ne Samiri ya fitar musu da wannan ɗan maraƙi jika-jika marar rai amma yana kuka irin na ‘yan maruƙa. Ganin haka sai wasu fitinannu daga cikinsu suka ce: “Wannan shi ne abin bautarku kuma abin bautar Musa, amma ya manta shi a nan ya tafi neman sa cikin duwatsu.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu martani a kan wannan wautar tasu da cewa, shin ba sa ganin wannan ɗan maraƙi ba ya iya magana da su, ba kuma sa iya tattaunawa da shi, sannan ba ya mallakar wata cuta ko wani amfani gare su?

  90. وَلَقَدۡ قَالَ لَهُمۡ هَٰرُونُ مِن قَبۡلُ يَٰقَوۡمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِۦۖ وَإِنَّ رَبَّكُمُ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَٱتَّبِعُونِي وَأَطِيعُوٓاْ أَمۡرِي 

    Open ayah 20:90

    Alhali kuwa haƙiƙa Haruna ya faɗa musu tun da wuri cewa: “Ya ku mutanena, an jarrabe ku da shi ne kawai, kuma lalle Ubangijinku (na gaskiya) Shi ne Arrahamanu, sai ku bi ni kuma ku bi umarnina.”

  91. قَالُواْ لَن نَّبۡرَحَ عَلَيۡهِ عَٰكِفِينَ حَتَّىٰ يَرۡجِعَ إِلَيۡنَا مُوسَىٰ

    Open ayah 20:91

    Suka ce: “Ba za mu gushe muna duƙufa wajen bauta masa ba har sai Musa ya dawo mana.”

  92. قَالَ يَٰهَٰرُونُ مَا مَنَعَكَ إِذۡ رَأَيۡتَهُمۡ ضَلُّوٓاْ

    Open ayah 20:92

    (Musa) ya ce: “Ya Haruna, me ya hana ka lokacin da ka gan su sun ɓace?

  93. أَلَّا تَتَّبِعَنِۖ أَفَعَصَيۡتَ أَمۡرِي

    Open ayah 20:93

    “Ka bi ni (don ka sanar da ni)? Ko kuwa ka saɓa umarnina ne?”

  94. قَالَ يَبۡنَؤُمَّ لَا تَأۡخُذۡ بِلِحۡيَتِي وَلَا بِرَأۡسِيٓۖ إِنِّي خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقۡتَ بَيۡنَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَلَمۡ تَرۡقُبۡ قَوۡلِي

    Open ayah 20:94

    (Haruna) ya ce: “Ya ɗan’ummata, kada ka kama mini gemuna, da kuma (gashin) kaina; lalle ni na ji tsoron ka ce (da ni): ‘Ka rarraba kan Banu-Isra’ila, ba ka kuma kiyaye maganata ba.’”

  95. قَالَ فَمَا خَطۡبُكَ يَٰسَٰمِرِيُّ

    Open ayah 20:95

    (Musa) ya ce: “Mene ne lamarinka, ya Samiri?”

  96. قَالَ بَصُرۡتُ بِمَا لَمۡ يَبۡصُرُواْ بِهِۦ فَقَبَضۡتُ قَبۡضَةٗ مِّنۡ أَثَرِ ٱلرَّسُولِ فَنَبَذۡتُهَا وَكَذَٰلِكَ سَوَّلَتۡ لِي نَفۡسِي

    Open ayah 20:96

    <b> Ya ce: “Na ga abin da ba su gani ba ne, sai na ɗebi danƙi daga gurbin (ƙasar) sawun (goɗiyar) Manzon (wato Jibrilu) sannan na watsa ta (a kan ɗan maraƙin). Kamar haka kuwa raina ya ƙawata mini.”

  97. قَالَ فَٱذۡهَبۡ فَإِنَّ لَكَ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ أَن تَقُولَ لَا مِسَاسَۖ وَإِنَّ لَكَ مَوۡعِدٗا لَّن تُخۡلَفَهُۥۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ إِلَٰهِكَ ٱلَّذِي ظَلۡتَ عَلَيۡهِ عَاكِفٗاۖ لَّنُحَرِّقَنَّهُۥ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّهُۥ فِي ٱلۡيَمِّ نَسۡفًا

    Open ayah 20:97

    (Annabi Musa) ya ce: “To sai ka tafi, amma ka tabbatar cewa (sakamakonka) a rayuwar (da za ka yi) shi ne ka riƙa cewa ‘la misasa ’, (wato ba za ka taɓu ba kuma ba za ka taɓa kowa ba); kuma lalle kana da ƙayyadajjen lokaci wanda ba za a saɓa maka ba; kuma ka dubi ubangijin naka wanda ka duƙufa a kansa kana bauta; lalle za mu ƙona shi sannan tabbas za mu sheƙar da shi cikin kogi.”

  98. إِنَّمَآ إِلَٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَسِعَ كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمٗا

    Open ayah 20:98

    Abin bautarku <b>kawai </b>shi ne <b>Allah wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. Ya yalwaci komai da iliminsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, tun can farko ma Annabi Haruna sai da ya yi wa Banu Isra’ila wa’azi lokacin da ya gan su sun koma bautar ɗan maraƙi, ya tabbatar musu da cewa wannan jarraba ce Allah yake nufin yi musu don gwada ƙarfin imaninsu da shi, ya kuma ware mumini na gaskiya daga cikinsu da kafiri, ya kuma shaida musu cewa Ubangijinsu na gaskiya shi ne Allah mai rahama ba wani wanda ba zai iya mallaka musu amfani ko cuta ba ballantana ma har ya ji ƙan su. Don haka ya kirawo su a kan su dawo su bi shi su bauta wa Allah shi kaɗai su bar bautar ɗan maraƙi. To amma sai fitinannun cikinsu suka mayar masa da amsa cewa su fa ba za su taɓa barin bautar wannan ɗan maraƙi ba har sai Musa ya dawo ya yi musu bayanin cewa ba a kan gaskiya suke ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin yadda Annabi Musa ya nuna wa ɗan’uwansa Haruna ɓacin ransa game da wannan abu da ya faru bayan tafiyarsa, ya zarge shi da cewa, me ya hana shi lokacin da ya ga mutanensa sun saki hanya sun kama bautar ɗan maraƙi ya bi shi can inda yake tare da sauran Banu Isra’ila waɗanda ba su yarda da bautarsa ba don ya sanar da shi? Ko kuma dai ya saɓa wa umarninsa ne lokacin da ya bar shi tare da su don kula da su; ya kuma umarce shi da yin gyara a tsakaninsu kada ya yarda ya bi hanyar maɓarnata?! Sai Musa cikin fushi da ɓacin rai ya kama gemun ɗan’uwansa Haruna da gashin kansa yana ja, sai Haruna ya ce masa, ya daina ja masa gemunsa da gashin kansa; ya bayyana masa hanzarinsa na rashin barinsa ya bi shi da cewa, idan ya tafi ya bar su yana jin tsoron kada Annabi Musa ya zarge shi da cewa ya raba masa kan al’ummarsa kuma bai yi aiki da wasiyyar da ya bar masa ba ta cewa ya yi gyara a cikinsu. Don haka ya zaɓi ya yi haƙuri ya ci gaba da zama tare da su har sanda Musa ya dawo, sai ya ga yadda za a shawo kan matsalar. Bayan Annabi Musa ya ji uzurin ɗan’uwansa Haruna kuma ya gamsu, sai ya juya wajen Samiri ya tambaye shi shi kuma mene ne lamarinsa? Me ya sa shi ya aikata abin da ya aikata ɗin nan? Sai Samiri ya faɗa wa Annabi Musa cewa shi ya ga abin da sauran Banu Isra’ila ba su gani ba, domin ya ga Mala’ika Jibrila a kan dokinsa lokacin da ya zo hallaka Fir’auna da jama’arsa, sai ya damƙi ƙasar ƙafafun dokinsa ya watsa ta cikin narkakken kayan ado bayan ya yi masa ginin surar ɗan maraƙi, sai ya zama wani jika-jikan ɗan maraƙi yana gunji kamar mai rai. Samiri ya ƙara da cewa haka ransa ya ƙawata masa ya aikata kuma ya bi son ransa. Da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji bayanin Samiri da yadda ya shirya hallakar da Banu Isra’ila, yana kuma faɗa cikin gadara da cika baki, sai Annabi Musa ya yi tir da aikinsa kuma ya bayyana masa mummunan sakamakon da yake jiran sa duniya da lahira. A nan duniya ya ce masa ya tafi ya ɓace masa da gani, kuma matsawar dai yana a raye to ba zai iya gauraya da mutane ba, domin duk sanda ya ga wani ya nufo shi zai ce masa: “La misasa ” watau kada a taɓa jikinsa, shi ma kuma ba zai iya taɓa jikin kowa ba. Haka zai yi ta rayuwa cikin wannan azabar har mutuwarsa. A lahira kuwa yana da wani ƙayyadajjen lokaci da yake jiran sa wanda ba zai iya kauce masa ba, a inda Allah zai yi masa hisabi a kan mummunan aikinsa ya gamu da matsananciyar azaba ta har abada. Sai kuma Annabi Musa ya juya wajen ɗan maraƙin da Samiri yake bauta wa don ya tabbatar masa shi da waɗanda suka hallaka tare da shi cewa wannan ba abin bauta ba ne, kuma zai hura wuta ya ƙona shi, bayan ya zama toka kuma zai sheƙar da shi a cikin kogi ta yadda ba wanda zai sake ganin sa har abada. Annabi Musa ya yi haka ne don ya tabbatar da cewa ba abin bauta ba ne; da kuwa abin bauta ne na gaskiya, to da babu mai iya yi masa haka. Sai kuma Annabi Musa ya dawo kan Banu Isra’ila ya ƙara tunatar da su kalmar Tauhidi da bautar Allah shi kaɗai wanda ya siffantu da siffofi na kamala, wanda iliminsa ya kewaye komai, don haka shi kaɗai ne abin bauta da gaskiya, babu wani abin bauta bayan shi.

  99. كَذَٰلِكَ نَقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ مَا قَدۡ سَبَقَۚ وَقَدۡ ءَاتَيۡنَٰكَ مِن لَّدُنَّا ذِكۡرٗا

    Open ayah 20:99

    Kamar haka ne Muke ba ka labari daga labaran abubuwan da suka riga suka wuce. Haƙiƙa kuwa Mun ba ka Alƙur’ani daga wajenmu.

  100. مَّنۡ أَعۡرَضَ عَنۡهُ فَإِنَّهُۥ يَحۡمِلُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وِزۡرًا 

    Open ayah 20:100

    Duk wanda ya bijire masa to lalle zai ɗauki nauyin zunubi a ranar alƙiyama.

  101. خَٰلِدِينَ فِيهِۖ وَسَآءَ لَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ حِمۡلٗا 

    Open ayah 20:101

    (Suna) <b>madawwama a cikinsa (zunubin); kayan (zunubi) kuwa ya munana a gare su ranar alƙiyama.

  102. يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِۚ وَنَحۡشُرُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ زُرۡقٗا 

    Open ayah 20:102

    (Ita ce) ranar da za a busa ƙaho. Kuma Mu tayar da kafirai a wannan ranar idanuwansu jawur.

  103. يَتَخَٰفَتُونَ بَيۡنَهُمۡ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا عَشۡرٗا 

    Open ayah 20:103

    Suna raɗa a tsakaninsu (suna cewa): “Ba ku zauna (a ƙaburburanku) ba face (kwana) goma.”

  104. نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذۡ يَقُولُ أَمۡثَلُهُمۡ طَرِيقَةً إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا يَوۡمٗا 

    Open ayah 20:104

    Mu Muka fi sanin abin da suke faɗi lokacin da wanda ya fi tunani daga cikinsu yake cewa: “Ba ku zauna ba face rana guda.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) babbar manufar da take ƙunshe a cikin labarurrukan Alƙur’ani, da cewa, kamar yadda ya ba shi labarin Annabi Musa da Fir’auna da mutanensa, to hakanan yake ba shi labaran annabawan da suka gabace shi tare da al’ummunsu, domin su zama abin ɗebe kewa a gare shi, kuma Allah yana tabbatar masa da cewa ya saukar masa da Alƙur’ani ne don masu wa’azantuwa su wa’azantu da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi duk wanda zai bijire wa Alƙur’ani ya ƙi imani da shi ko ya ƙi aiki da shi cewa ranar alƙiyama zai zo yana ɗauke da nauyin zunubi mai girma a kansa, sai ya cancanci matsananciyar azaba wadda ita ce wutar Jahannama, zai kuma dawwama har abada a cikinta. Allah kuma ya yi tir da wannan kayan zunubi da zai ɗauka a ranar alƙiyama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta wannan rana ta alƙiyama da cewa rana ce da za a yi busar ƙaho ta biyu inda Allah zai tayar da kafirai a firgice idanuwansu jawur saboda tsananin tsoro da fargaba, ba abin da suke iya yi sai raɗa a tsakaninsu, suna faɗa wa junansu cewa, ai kwana goma kacal suka yi a ƙaburburansu; sun ma kasa tuna kwanakin da suka yi a duniya balle su iya tuna tsawon zamansu na barzahu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi ne ya fi kowa sanin maganganun da suke tattaunawa da junansu cikin raɗa. wanda ya fi kaifin hankali a cikinsu ma shi yake faɗa cewa, kwana ɗaya ne kacal suka yi a barzahu bai ma kai goma ba.

  105. وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡجِبَالِ فَقُلۡ يَنسِفُهَا رَبِّي نَسۡفٗا 

    Open ayah 20:105

    Suna kuma tambayar ka game da duwatsu, to ka ce (da su): “Ubangijina zai niƙe su tilis.

  106. فَيَذَرُهَا قَاعٗا صَفۡصَفٗا 

    Open ayah 20:106

    “Sannan Ya bar ta (wato ƙasar) fili fetal.

  107. لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجٗا وَلَآ أَمۡتٗا 

    Open ayah 20:107

    “Ba za ka ga wani kwari ko tudu a kanta ba.”

  108. يَوۡمَئِذٖ يَتَّبِعُونَ ٱلدَّاعِيَ لَا عِوَجَ لَهُۥۖ وَخَشَعَتِ ٱلۡأَصۡوَاتُ لِلرَّحۡمَٰنِ فَلَا تَسۡمَعُ إِلَّا هَمۡسٗا 

    Open ayah 20:108

    A wannan rana ne za su bi mai kira (zuwa matattara), ba mai bauɗe masa; kuma (duk) muryoyi su yi ƙasa-ƙasa saboda (girman Allah) Mai rahama, sannan ba za ka ji (komai) ba sai raɗa.

  109. يَوۡمَئِذٖ لَّا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَرَضِيَ لَهُۥ قَوۡلٗا 

    Open ayah 20:109

    A wannan ranar ceto ba ya amfani sai ga wanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa izini, kuma Ya yarda da maganarsa.

  110. يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِۦ عِلۡمٗا 

    Open ayah 20:110

    (Allah) Yana sane da abin da yake gaba gare su (na ranar alƙiyama) da kuma abin da yake bayansu (na ayyukan da suka yi a duniya), su kuwa ba za su kewaye da saninsa ba.

  111. ۞وَعَنَتِ ٱلۡوُجُوهُ لِلۡحَيِّ ٱلۡقَيُّومِۖ وَقَدۡ خَابَ مَنۡ حَمَلَ ظُلۡمٗا

    Open ayah 20:111

    Kuma dukkanin fuskoki suka ƙasƙanta ga (Allah) Rayayye, Tsayayye (da Zatinsa). Haƙiƙa kuma duk wanda ya yo dakon zalunci ya taɓe.

  112. وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا يَخَافُ ظُلۡمٗا وَلَا هَضۡمٗا

    Open ayah 20:112

    Duk kuma wanda yake yin aiki na gari alhali kuwa shi mumini ne, to ba zai ji tsoron zalunci ba ko kuma ƙwauro. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta yadda ranar alƙiyama za ta kasance da yadda za ta cika da abubuwan tsoro da tashin hankali. Ya bayyana cewa mushirikai suna tambayar Manzon Allah game da duwatsu; yaya za su kasance a ranar alƙiyama? Sai ya umarce shi da ya ba su amsa da cewa, Ubangijinsa zai tuttunɓuke su daga wurarensu ya kuma niƙe su tilis sannan ya sheƙe ƙurarsu ta bi iska. Ƙasar da take ɗauke da su kuma ta koma fili fetal; ba tudu ba kwari babu sauran wani gini ko tsiro a kanta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wannan rana ne mutane za su bi mai kiran su zuwa ga matattara, kowa da kowa dole ya bi shi, babu mai iya kauce masa. A lokacin tsoro da kwarjini na Allah Mai rahama zai lulluɓe kowa; babu mai iya ɗaga murya ya yi magana mai ƙarfi; muryoyi za su yi tsit babu abin da za ka ji sai dai raɗa can ƙasa wadda ba ma a fahimtar abin da ake cewa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar musu da cewa, a wannan ranar babu wani wanda cetonsa zai yi amfani sai wanda Allah Mai rahama ya ba shi izinin yin ceton, kuma ya yarda ya yi magana a kan haka. Allah kuma yana sane da abin da yake gaban mutane na lamarin lahira, da kuma abin da suka baro a baya na al’amuran duniyarsu, amma bayinsa babu abin da suka sani game da Zatinsa da siffofinsa. Sai kuma ya bayyana yadda mutane a ranar za su kasu gida biyu da sakamakon kowane kashi. Fuskokin bayi za su ƙasƙanta a gaban Allah Rayayye kuma Tsayayye da Zatinsa, wanda rayuwarsa ba ta da farko kuma ba ta da ƙarshe; shi ne mai gudanar da duk lamuran bayinsa. Kason mutane na farko a ranar su ne azzalumai waɗanda suka ƙi yin imani da Allah su yi ayyuka na ƙwarai, suka mutu da tarin zunubai. Allah ya bayyana cewa irin waɗannan mutane sun taɓe a wannan rana domin za su gamu da mummunan sakamakon ayyukansu. Sai kuma kashi na biyu, su ne waɗanda suka yi kyawawan ayyuka bayan sun yi imani da Allah da manzanninsa. To duk wanda ya zamanto cikin wannan kaso, ba zai ji tsoron wani zalunci ba a ranar, watau ba za a azabtar da shi da laifin da bai aikata ba, haka kuma ba zai ji tsoron a yi masa ƙwauron ladansa ba, watau a rage masa wani abu daga kyawawan ayyukansa. A maimakon haka ma sai dai a riɓanya masa ladan kyawawan ayyukansa a kuma gafarta masa kurakuransa.

  113. وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا وَصَرَّفۡنَا فِيهِ مِنَ ٱلۡوَعِيدِ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ أَوۡ يُحۡدِثُ لَهُمۡ ذِكۡرٗا

    Open ayah 20:113

    Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur’ani) Balarabe (watau da harshen Larabci), Muka kuma sarrafa ayoyin gargaɗi a cikinsa don su kiyaye dokokin (Allah) ko kuma ya sa su su wa’azantu.

  114. فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۗ وَلَا تَعۡجَلۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مِن قَبۡلِ أَن يُقۡضَىٰٓ إِلَيۡكَ وَحۡيُهُۥۖ وَقُل رَّبِّ زِدۡنِي عِلۡمٗا

    Open ayah 20:114

    Kuma fa Allah Sarki na gaskiya Ya ɗaukaka (daga maganganun kafirai). Kada kuma ka yi garaje da (karatun) Alƙur’ani tun kafin a gama yi maka wahayinsa, kuma ka ce: “Ubangiji Ka ƙara min ilimi.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda ya saukar da ayoyin da suka yi bayani a kan ranar lahira da tsorace-tsoracenta, to hakanan ya saukar da Alƙur’ani da harshen Larabci mai cike da fasaha da azancin magana, kuma mai ƙunshe da gargaɗi da narko iri-iri don ya sa musu taƙawa da tsoron Allah a zukatansu, su wa’azantu su daina aikata laifuffukan da suke yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tuna musu girmansa da ɗaukakarsa, da cewa ya ɗaukaka ya tsarkaka, shi ne Sarki mamallakin kowa da komai, kuma shi ne gaskiya kuma maganarsa ma gaskiya ce. Ya tsarkaka daga duk wata tawaya da mushirikai suke danganta shi da ita. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nusar da Annabi (ﷺ) yadda ya kamata ya yi wajen sauraron Mala’ika Jibrilu, ya hana shi yin garaje wajen bibiyar duk wata kalma da take fitowa daga Mala’ika Jibrilu idan yana karanta masa Alƙur’ani. Annabi yana gaggawa ne don gudun kada ya manta wani abu na Alƙur’ani, sai Allah ya hana shi yin haka, ya kuma umarce shi da ya yi shiru ya saurara har Mala’ikan ya gama karanta masa, shi kuma Allah shi ne zai tattara masa duk wannan karatu da ya ji a ƙirjinsa ba zai manta ko harafi ɗaya ba har sai ya isar da shi ga al’ummarsa. Allah kuma ya umarce shi da ya ci gaba da roƙon Allah kan ya ƙara masa ilimi. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Ku roƙi Allah ilimi mai amfani, kuma ku nemi tsarinsa daga ilimi marar amfani.” [Ibn Majah #3843 da Ibn Hibban #82].

  115. وَلَقَدۡ عَهِدۡنَآ إِلَىٰٓ ءَادَمَ مِن قَبۡلُ فَنَسِيَ وَلَمۡ نَجِدۡ لَهُۥ عَزۡمٗا

    Open ayah 20:115

    Kuma haƙiƙa Mun yi alƙawari da Adamu tun da farko (cewa kada ya ci itaciyar da aka hana shi), sai ya manta, sai ba Mu same shi da ƙarfin ƙuduri ba.

  116. وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰ

    Open ayah 20:116

    Kuma (ka tuna) lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu” sai suka yi sujjadar sai Iblis ne kawai ya ƙi.

  117. فَقُلۡنَا يَٰٓـَٔادَمُ إِنَّ هَٰذَا عَدُوّٞ لَّكَ وَلِزَوۡجِكَ فَلَا يُخۡرِجَنَّكُمَا مِنَ ٱلۡجَنَّةِ فَتَشۡقَىٰٓ

    Open ayah 20:117

    Sannan Muka ce: “Ya Adamu, lalle wannan maƙiyinka ne kai da matarka, to kada (ku yarda) ya fitar da ku daga Aljanna, sai ka wahala.

  118. إِنَّ لَكَ أَلَّا تَجُوعَ فِيهَا وَلَا تَعۡرَىٰ

    Open ayah 20:118

    “Lalle (Allah) Ya yi maka alƙawarin ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba.

  119. وَأَنَّكَ لَا تَظۡمَؤُاْ فِيهَا وَلَا تَضۡحَىٰ

    Open ayah 20:119

    “Kuma lalle kai ba za ka ji ƙishi ba a cikinta, kuma ba za ka ji zafin rana ba.”

  120. فَوَسۡوَسَ إِلَيۡهِ ٱلشَّيۡطَٰنُ قَالَ يَٰٓـَٔادَمُ هَلۡ أَدُلُّكَ عَلَىٰ شَجَرَةِ ٱلۡخُلۡدِ وَمُلۡكٖ لَّا يَبۡلَىٰ 

    Open ayah 20:120

    Sai Shaiɗan ya yi masa waswasi ya ce: “Ya Adamu, yanzu ba na nuna maka wata bishiya ta dawwama da kuma mulki wanda ba zai ƙare ba?”

  121. فَأَكَلَا مِنۡهَا فَبَدَتۡ لَهُمَا سَوۡءَٰتُهُمَا وَطَفِقَا يَخۡصِفَانِ عَلَيۡهِمَا مِن وَرَقِ ٱلۡجَنَّةِۚ وَعَصَىٰٓ ءَادَمُ رَبَّهُۥ فَغَوَىٰ

    Open ayah 20:121

    Sai suka ci wani abu daga gare ta, sai ga tsiraicinsu ya bayyana gare su, sai suka riƙa lulluɓe (jikinsu) da ganyen Aljanna. Kuma Adamu ya saɓa wa Ubangijinsa ya bar shiriya.

  122. ثُمَّ ٱجۡتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَتَابَ عَلَيۡهِ وَهَدَىٰ

    Open ayah 20:122

    Sannan Ubangijinsa Ya zaɓe shi, sai Ya yafe masa Ya kuma shirye (shi).

  123. قَالَ ٱهۡبِطَا مِنۡهَا جَمِيعَۢاۖ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ فَإِمَّا يَأۡتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدٗى فَمَنِ ٱتَّبَعَ هُدَايَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشۡقَىٰ

    Open ayah 20:123

    (Allah) Ya ce (da Adamu da Hauwa’u): “Ku sauka daga gare ta (Aljannar) gaba ɗayanku, sashinku ya dinga gaba da sashi; sannan idan shiriya ta zo muku daga gare Ni, to duk wanda ya bi shiriyata ba zai taɓe ba, kuma ba zai wahala ba.

  124. وَمَنۡ أَعۡرَضَ عَن ذِكۡرِي فَإِنَّ لَهُۥ مَعِيشَةٗ ضَنكٗا وَنَحۡشُرُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَعۡمَىٰ

    Open ayah 20:124

    “Wanda kuma ya bijire wa Alƙur’ani to lalle zai yi rayuwa mai ƙunci, kuma Mu tashe shi makaho ranar alƙiyama.”

  125. قَالَ رَبِّ لِمَ حَشَرۡتَنِيٓ أَعۡمَىٰ وَقَدۡ كُنتُ بَصِيرٗا

    Open ayah 20:125

    Zai ce: “Ubangijina me ya sa Ka tashe ni makaho, alhali kuwa na kasance mai gani?”

  126. قَالَ كَذَٰلِكَ أَتَتۡكَ ءَايَٰتُنَا فَنَسِيتَهَاۖ وَكَذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمَ تُنسَىٰ

    Open ayah 20:126

    (Allah) Ya ce: “Kamar haka ne ayoyinmu suka zo maka sai ka manta su, to kamar haka kuwa (kai ma) za a manta da kai a yau.”

  127. وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَنۡ أَسۡرَفَ وَلَمۡ يُؤۡمِنۢ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦۚ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَدُّ وَأَبۡقَىٰٓ

    Open ayah 20:127

    Kamar haka Muke saka wa (duk) wanda ya yi ɓarna kuma bai yi imani da ayoyin Ubangijinsa ba. Kuma azabar lahira tabbas ta fi tsanani ta kuma fi dawwama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya labarta mana ƙissar Annabi Adamu da matarsa Hauwa’u da abin da ya faru tsakaninsu da Iblis la’ananne. Allah ya tabbatar da cewa ya yi alƙawari da Adamu tun farko, kuma Annabi Adamu ya ƙuduri aniyar riƙe wannan alƙawari da aiki da shi; to amma daga baya sai ya manta. Allah ya tabbatar da cewa bai sami Adamu da ƙarfin ƙudiri ba, domin mantuwa wadda ɗabi’a ce ta ɗan’adam ita ce ta riske shi, don haka sai ya manta alƙawarin da suka yi da Ubangijinsa, ya faɗa cikin kuskure, amma daga baya ya tuba Allah kuma ya karɓi tubansa, ya sake ɗora kan hanyar shiriya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana abin da ya faru daki-daki da cewa, bayan ya halicci Adamu daga taɓo da hannunsa ya kuma busa masa rai, ya sanar da shi sunayen abubuwan amfaninsa, sai ya umarci mala’iku su girmama shi ta hanyar faɗuwa su yi masa sujjada. Mala’iku gaba ɗaya suka bi umarnin Allah suka faɗi suka yi wa Adamu sujjada in ban da Iblis, wanda shi ma yana cikinsu amma shi aljani ne ba mala’ika ba, sai ya yi girman kai ya ƙi yarda ya yi wa Adamu sujjada, da hujjar cewa shi ya fi shi matsayi, domin shi da wuta aka halicce shi, Adamu kuwa da taɓo Allah ya yi shi. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Adamu da matarsa Hauwa’u cewa, Iblis fa babban maƙiyinsu ne mai yi musu hassada da ni’imar da Allah ya yi musu, don haka kada su yarda ya fitar da su daga gidan Aljanna, za su sha wahala. Sai kuma ya bayyana wa Adamu da Hauwa’u tarin ni’imomin da ya shirya musu a gidan Aljanna, da cewa, ya yi musu tanadin abin da za su ci a cikinta ba za su taɓa jin yunwa ba, da kuma suturar da za su saka ba za su taɓa yin tsiraici ba, da kuma abin sha, don haka ba su ba ƙishi a cikinta, ga kuma inuwa mayalwaciya, ba su babu zafin rana. To sai dai kuma ya haramta musu kusantar wata bishiya guda ɗaya ta cikin Aljannar ya nuna musu illar cin ‘ya’yanta. Amma kuma sai maƙiyinsu Iblis ya saɗaɗo ya shiga yi wa Adamu waswasi a ransa, ya nuna masa cewa zai nuna masa wata bishiya da idan ya ci ‘ya’yanta zai dawwama a Aljanna, kuma ya sami mulki wanda ba zai yanke ba na har abada. Sai ko Adamu ya ruɗu da wannan waswasi na Iblis, domin ya zo masa a matsayin masoyinsa mai faɗa masa gaskiya har da haɗawa da rantsuwa da Allah a kan haka. Sai Adamu da Hauwa’u suka manta wancan alƙawari na farko tsakaninsu da Allah, wanda ya hana su cin wannan itaciya, sai kawai suka ci ‘ya’yanta, nan take kuwa suturar da ke jikinsu ta zube, tsiraicinsu ya bayyana a fili, sai kuma kunyar Allah ta lulluɓe su sai suka fara tsinkar ganyen itatuwan Aljanna suna kare tsiraicinsu da shi. Sai Allah ya tunatar da Adamu cewa ya saɓa wa Ubangijinsa, ya saki hanyar shiriyar da ya ɗora shi a kanta tun farko. To amma sai suka yi gaggawa suka nemi tuba da afuwa daga Allah suka amasa laifinsu, sai kuwa Allah ya karɓi tubansu, ya ma zaɓi Adamu ya kuma sake ba shi shiriya, matsayinsa a wurin Allah ma ya dawo fiye da na farko. Iblis kuma ya juya da makircinsa bai yi nasara ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya umarci Adamu da Hauwa’u kan su sauko daga Aljanna zuwa bayan ƙasa, sannan su da Iblis za su ci gaba da zama abokan gabar juna. Ya kuma sanar da su cewa, idan wani bayani na tafarkin shiriya ya zo musu daga Allah, to su sani duk wanda ya bi wannan tafarkin ya yi aiki da shi bai kauce masa ba, to ba zai taɓe ba, ba kuma zai sha wahala ba a lahira, domin makomarsa Aljanna ce gidan hutu. To amma duk wanda ya kuskura ya bijire wa ayoyin Allah da shiriyarsa ya ƙi karɓar su, to zai fuskanci wata rayuwa mai ƙunci a nan duniya da kuma barzahu (watau a ƙabarinsa). Sannan kuma a ranar lahira a tashe shi don yi masa hisabi yana makaho dunɗum ba ya ganin komai. Anan zai yi ta sallallami yana kururuwa yana tambayar Ubangiji me ya sa ya tashe shi makaho alhali a duniya yana gani tar? Sai Allah ya ba shi amsa da cewa, haka shi ma ya yi a duniya lokacin da ayoyin Allah suka zo masa, an karanta masa dokokin Allah to amma sai ya yi watsi da su. To hakanan shi ma a lahira za a yi watsi da shi. Irin aikinsa ya yi daidai da irin sakamakonsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, irin wannan mummunan sakamakon yake jiran duk wani wanda ya faɗa dumu-dumu cikin aikata laifuka a duniya, ya ƙi yin imani da ayoyin Ubangijinsa bayyanannu. Sai kuma ya ƙara tabbatar da cewa azabar lahira fa ta fi tsanani da muni fiye da rayuwa mai ƙunci ta duniya da barzahu, domin ita ce mai dawwama har abada.

  128. أَفَلَمۡ يَهۡدِ لَهُمۡ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ يَمۡشُونَ فِي مَسَٰكِنِهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ

    Open ayah 20:128

    Yanzu (mutanen Makka) ba su gane cewa al’ummu nawa muka hallaka a gabaninsu ba waɗanda suna wucewa ta gidajensu? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankali.

  129. وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَكَانَ لِزَامٗا وَأَجَلٞ مُّسَمّٗى

    Open ayah 20:129

    Ba don kuwa wata kalma da ta rigaya daga Ubangijinka ba, da kuma wani wa’adi ƙayyadajje, to da (azaba) ta zama dole (a kansu tun a duniya).

  130. فَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ قَبۡلَ طُلُوعِ ٱلشَّمۡسِ وَقَبۡلَ غُرُوبِهَاۖ وَمِنۡ ءَانَآيِٕ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡ وَأَطۡرَافَ ٱلنَّهَارِ لَعَلَّكَ تَرۡضَىٰ 

    Open ayah 20:130

    Sai ka yi haƙuri a kan abin da suke faɗa, kuma ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kafin hudowar rana, da kuma gabanin faɗuwarta; a (wasu) lokatai na dare kuma ka yi tasbihi, da kuma gefukan wuni don (a saka maka da abin da) za ka yarda.

  131. وَلَا تَمُدَّنَّ عَيۡنَيۡكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّنۡهُمۡ زَهۡرَةَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا لِنَفۡتِنَهُمۡ فِيهِۚ وَرِزۡقُ رَبِّكَ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰ

    Open ayah 20:131

    Kada kuma ka zura idanuwanka a kan dangogin daɗin da Muka jiyar da wasu daga cikinsu, na adon rayuwar duniya ne don Mu jarrabe su da shi. Arzikin Ubangijinka kuwa (shi) ya fi alheri ya kuma fi dawwama.

  132. وَأۡمُرۡ أَهۡلَكَ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱصۡطَبِرۡ عَلَيۡهَاۖ لَا نَسۡـَٔلُكَ رِزۡقٗاۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكَۗ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلتَّقۡوَىٰ

    Open ayah 20:132

    Ka kuma umarci iyalinka da (tsai da) salla, kuma ka dawwama a kanta; ba Ma neman ka arzuta (kanka da iyalinka); Mu ne za Mu arzuta ka. Kyakkyawan ƙarshe kuwa yana ga masu taƙawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai abin da za su wa’azantu da shi da a ce sun yi aiki da hankulansu. Wannan kuwa shi ne yawan al\'ummun da Allah ya hallaka gabaninsu waɗanda suna wucewa ta gidajensu suna ganin irin yadda Allah ya yi da su. To amma ba kowa ne zai ɗauki izina da darasi daga hakan ba sai masu lafiyayyun hankula. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Annabi cewa, ba don ya riga ya yi alƙawarin cewa ba zai azabtar da kowa ba har sai ya tsayar masa da hujja, da kuma ajali na rayuwa da ya riga ya ƙayyade wa kowa a duniya ba, to ba don haka ba da ya gaggauto azabarsa ga kafiran nan masu ƙaryata Manzonsa (ﷺ), ya hallaka su kamar yadda ya hallaka kafiran da suka gabace su, domin sun cancanci ya yi musu haka. To amma ba zai yi musu azaba ta gaba ɗaya ba. Sai ya umarci Annabi (ﷺ) da yin haƙuri game da ƙaryatawar da kafirai suke yi masa da miyagun maganganu da munanan siffofin da suke siffanta shi da su. Ya kuma umarce shi da tsarkake Ubangijinsa da gode masa a cikin sallar Asuba gabanin hudowar rana da sallar La’asar kafin faɗuwar rana, da sallar Magariba da Isha’i a cikin sa’o’in dare, da kuma sallar Azahar lokacin da rana ta yi zawali gefen yini na farko da sallar Magariba bayan ƙarewar gefensa na biyu, da fatan ya samu sakamakon ladan da zai yarda da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi Manzonsa da kada ya zura ido ga dangogin kayayyakin jin daɗi na ƙyale-ƙyalen duniya da ya ba wa kafirai masu ƙaryata shi, domin ya jarrabe su da shi, ya sanar da shi cewa, duk abin da ya ba su mai gushewa ne, amma abin da ya yi masa alƙawari na kyakkyawan sakamako shi ne mafi alheri kuma dawwamamme, ba zai yanke ba har abada. Lokacin da Sayyidina Umar (Allah ya kara masa yarda) ya shiga shigifar Manzon Allah (ﷺ) bayan ya ƙaurace wa matansa na tsawon wata guda, ya same shi kwance a kan wata karaunin tabarma. Ban da wata salka ta fata a rataye Umar bai hango komai na jin daɗi a wannan shigifa ta Manzon Allah (ﷺ) ba, sai kawai ya fashe da kuka. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya tambaye shi abin da ya saka shi kuka, sai ya kada baki ya ce: “Ya Ma’aikin Allah, dubi irin rayuwar da Kisra da Ƙaisara suke ciki, ga ka kai kuma zaɓaɓɓen Allah cikin halittunsa, duba ka ga irin yadda kake rayuwa.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kana da wata shakka ne ya ɗan Khaɗɗab? Waɗancan ai su wasu mutane ne da aka gaggauto musu jin daɗinsu tun a nan duniya.” [Bukhari #2468 da Muslim #1479]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) cewa ya umarci iyalansa da tsai da salla, shi ma kuma ya dage wajen kulawa da ita, Allah ya tabbatar masa da cewa ba ya neman sa da ya arzuta kansa ko iyalansa da abinci ko abin sha; Allah ne da kansa ya ɗauke masa wannan nauyin, shi zai hore masa arziƙinsa da na iyalansa. Kuma ya sani cewa kyakkyawan ƙarshe a duniya da lahira yana ga masu tsoron Allah, watau masu aikata umarninsa suna kuma kauce wa haninsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Asi (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku umarci ‘ya’yanku ƙanana da salla idan sun cika shekara bakwai, kuma ku doke su a kan barin ta idan sun cika shekara goma, ku kuma raba tsakanin (mazansu da matansu) a wajen kwanciya.” [Ahmad #6689 da Abu Dawud #496]. An karɓo daga Ma’aƙilu ɗan Yasar (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ubangijinku yana cewa: ‘Ya kai ɗan’adam, ka ba da lokacinka wajen bauta mini zan cika maka zuciya da wadata, zan kuma cika maka hannayenka da arziƙi. Ya kai ɗan’adam, kada ka yi nisa da ni sai in cika maka zuciya da talauci, in kuma cika maka hannaye da shagulgula.’” [Hakim, Al-Mustadrak , Juzu’i na 4, shafi na 326]. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wata rana na yi mafarki da daddare muna zaune a gidan Uƙubatu ɗan Rafi’u sai aka kawo mana dabino lubiya daga dabinon gonar Ibn Ɗab, sai na fassara mafarkin da cewa, mu ne masu ɗaukaka a nan duniya, kuma masu kyakkyawan ƙarshe a lahira, kuma addininmu ya yi kyau.” [Muslim #2270].

  133. وَقَالُواْ لَوۡلَا يَأۡتِينَا بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّهِۦٓۚ أَوَلَمۡ تَأۡتِهِم بَيِّنَةُ مَا فِي ٱلصُّحُفِ ٱلۡأُولَىٰ

    Open ayah 20:133

    Suka kuma ce: “Me ya sa bai zo mana da wata aya daga Ubangijinsa ba?” Yanzu hujjar abin da yake cikin littattafan farko ba ta zo musu ba (wato Alƙur’ani)?

  134. وَلَوۡ أَنَّآ أَهۡلَكۡنَٰهُم بِعَذَابٖ مِّن قَبۡلِهِۦ لَقَالُواْ رَبَّنَا لَوۡلَآ أَرۡسَلۡتَ إِلَيۡنَا رَسُولٗا فَنَتَّبِعَ ءَايَٰتِكَ مِن قَبۡلِ أَن نَّذِلَّ وَنَخۡزَىٰ

    Open ayah 20:134

    In da a ce Mun hallaka su ne da azaba tun gabaninsa (wato Annabi Muhammadu), to da sun ce: “Ubangijinmu, me ya sa ba Ka aiko mana da wani manzo ba sai mu bi ayoyinka tun kafin mu ƙasƙanta mu kuma wulaƙanta?”

  135. قُلۡ كُلّٞ مُّتَرَبِّصٞ فَتَرَبَّصُواْۖ فَسَتَعۡلَمُونَ مَنۡ أَصۡحَٰبُ ٱلصِّرَٰطِ ٱلسَّوِيِّ وَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ

    Open ayah 20:135

    Ka ce (da su): “Kowanne (ni da ku) mai sauraro ne, sai ku saurara; to ba da daɗewa ba za ku san su wane ne ma’abota hanya madaidaiciya, kuma su wane ne suke kan shiriya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin ƙalubalantar da kafirai suka riƙa yi wa Annabi (ﷺ) na cewa, me ya sa bai kawo musu wata hujja mai ƙarfi daga Allah ba wadda za ta tabbatar musu da cewa shi da gaske annabin Allah ne. Sai Allah ya mayar musu da martani cewa, ashe Alƙur’ani bai zo musu ba wanda yake gaskata littattafan da suka gabace shi, watau wannan bai ishe su hujja ba a kan gaskiyar manzancin Annabi (ﷺ)? An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani annabi sai da aka ba shi mu’ujizar da mutane suka yi imani da shi saboda ita. Amma ni mu’ujizar da aka ba ni wahayi ne wanda aka yi min (watau Alƙur’ani), ina fatan in fi su yawan mabiya a ranar alƙiyama.” [Bukhari #4981 da Muslim #231]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa da ya hallaka su da wata azaba kafin ya aiko musu Manzon Allah (ﷺ) ya karanta musu ayoyin Alƙur’ani ya gargaɗe su, to a ranar lahira idan Allah ya titsiye su a gabansa da za su ce, me ya sa bai aiko musu da manzo ba a duniya; ai da ya aiko musu manzo da sun yi imani da shi, sun yarda da abin da ya zo da shi, kafin wannan rana ta lahira ta zo su wulaƙanta su kunyata saboda azabar da za su gamu da ita. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) ya sanar da kafirai cewa shi da su duka suna nan suna sauraron abin da Allah zai yi da su, don haka su ma su ci gaba da sauraro, tabbas ba da jimawa ba za su san su wane ne suke kan miƙaƙƙiyar hanya kuma su wane ne a kan shiriya, Musulmi ko su?