الأنبياء

Al-Anbiyaa

The Prophets · Surah 21 · Ayahs: 112 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. ٱقۡتَرَبَ لِلنَّاسِ حِسَابُهُمۡ وَهُمۡ فِي غَفۡلَةٖ مُّعۡرِضُونَ

    Open ayah 21:1

    Lokacin yi wa mutane hisabi ya kusanto, alhali suna cikin gafala (suna) masu bijirewa.

  2. مَا يَأۡتِيهِم مِّن ذِكۡرٖ مِّن رَّبِّهِم مُّحۡدَثٍ إِلَّا ٱسۡتَمَعُوهُ وَهُمۡ يَلۡعَبُونَ

    Open ayah 21:2

    Ba wata tunatarwa sabowa (wato Alƙur’ani) da za ta zo musu daga Ubangijinsu face sai sun saurare ta suna masu wasa.

  3. لَاهِيَةٗ قُلُوبُهُمۡۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّجۡوَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ هَلۡ هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡۖ أَفَتَأۡتُونَ ٱلسِّحۡرَ وَأَنتُمۡ تُبۡصِرُونَ

    Open ayah 21:3

    Zukatansu suna cikin gafala. Waɗanda suka yi zalunci kuma suka ɓoye abin da suka tattauna (na cewa): “Wannan ba wani ne in ban da mutum kamarku; yanzu kwa riƙa bin sihiri alhali kuwa ku kuna gani?”

  4. قَالَ رَبِّي يَعۡلَمُ ٱلۡقَوۡلَ فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

    Open ayah 21:4

    Ya ce: “Ubangijina Yana sane da (kowace) magana a cikin sammai da ƙasa; Shi kuwa Mai ji ne, Masani.

  5. بَلۡ قَالُوٓاْ أَضۡغَٰثُ أَحۡلَٰمِۭ بَلِ ٱفۡتَرَىٰهُ بَلۡ هُوَ شَاعِرٞ فَلۡيَأۡتِنَا بِـَٔايَةٖ كَمَآ أُرۡسِلَ ٱلۡأَوَّلُونَ

    Open ayah 21:5

    A’a, cewa dai suka yi: “Ai (shi Alƙur’ani) tarkacen mafarki ne, a’a, shi (Muhammadu) ƙago shi ya yi, a’a, shi mawaƙi dai ne, to sai ya zo mana da wata aya kamar yadda aka aiko wa mutanen farko.”

  6. مَآ ءَامَنَتۡ قَبۡلَهُم مِّن قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَآۖ أَفَهُمۡ يُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 21:6

    Ai babu wata al’umma da ta yi imani a gabaninsu wadda Muka hallaka; shin yanzu su za su yi imani? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da bayanin wani hali mai ban al’ajabi na mutane, watau yadda suka gafala suke bijirewa bayan ga shi ranar yi musu hisabin ayyukansu tana ta ƙara matsowa, watau ranar alƙiyama, amma sun shagala da duniya da ƙyale-ƙyalenta. Sai kuma ya bayyana irin yadda suke bijire wa wa’azi da kiran da ake yi musu, da cewa duk wani abu sabo daga Alƙur’ani da ya sauka daga Ubangijinsu don tunatar da su da gargaɗin su sai su saurare shi sauraro marar amfani, domin za su ɗauke shi ne abin wasa ba na gaske ba. Sukan saurare shi zukatansu suna cike da gafala, ban da duniya babu abin da yake gabansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da kafirai azzalumai suke haɗuwa suna ganawa a kansa, suna tattaunawa da junansu, har ma wasu daga cikinsu suna cewa, wai shi wannan mutum da yake cewa shi Manzon Allah ne ba mutum ne irinsu ba; da me shi ya fi su har da zai yi da’awar manzanci? Sannan su zarge shi da cewa abin da ya zo da shi sihiri ne, sai su ja kunnuwan junansu a kan su nisanci bin sa bayan sun fahimci shi mutum ne kawai kamarsu, kuma sihiri ne ya zo musu da shi ba gaskiya ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya mayar musu da martani a kan waɗannan miyagun maganganu da suke tattaunawa a ɓoye da cewa, Ubangijinsa yana sane da duk wata magana ta sarari da ta ɓoye, a cikin sammai da ƙasa, domin shi mai jin duk maganganun bayinsa ne, kuma masanin duk ayyukansu, don haka zai yi musu sakayya a kansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu irin maganganu na kafirai a kan Manzon Allah (ﷺ) waɗanda suke ƙara tabbatar da rashin gaskiyarsu da kuma rashin wata takamaimiyar hujja da suke dogara a kanta wajen ƙaryata shi. Wasu daga cikinsu suka ce abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da shi wasu kwashe-kwashen mafarki ne wanda ba ya da wata fassara ta gaskiya, wani lokaci kuma sai suka ce ai shi ne yake ƙagar maganganun da kansa waɗanda ba su da wani tushe yana jingina wa Allah. Wani lokaci kuma su ce masa mawaƙi. Wannan tubka-da-warwara tana nuna rashin madafar zancensu, sai shaci-faɗi da son zuciya kawai. Har ma suka ƙalubalance shi da cewa, idan har da gaske shi Manzon Allah ne to ya nuna musu wata mu’ujiza irin ta manzannin farko da Allah ya aiko, kamar sanda ta Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ko taguwar Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su amsa da cewa, duk al\'ummun da suka gabace su waɗanda suka nemi annabawansu da su kawo musu wasu mu’ujizoji, to bayan sun kawo musu su ai bijire musu suka yi ba su yi imani da su ba, daga ƙarshe kuma Allah ya hallaka su. To shin su yanzu waɗannan da suke neman su ma a zo musu da mu’ujiza za su yi imani ne da ita idan ta zo? Watau dai su ma za su yi irin abin da waɗancan suka yi ne, ba za su yi imanin ba.

  7. وَمَآ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِمۡۖ فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّكۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 21:7

    Kuma ba Mu aiko (wasu manzanni) gabaninka ba sai mazaje da Muke yi musu wahayi; to ku tambayi ma’abota sani idan ya zamana ku ba ku sani ba.

  8. وَمَا جَعَلۡنَٰهُمۡ جَسَدٗا لَّا يَأۡكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَمَا كَانُواْ خَٰلِدِينَ

    Open ayah 21:8

    Kuma ba Mu sanya su jiki ne da ba sa cin abinci ba, kuma ba su zamanto masu dawwama ba.

  9. ثُمَّ صَدَقۡنَٰهُمُ ٱلۡوَعۡدَ فَأَنجَيۡنَٰهُمۡ وَمَن نَّشَآءُ وَأَهۡلَكۡنَا ٱلۡمُسۡرِفِينَ

    Open ayah 21:9

    Sannan Muka cika musu alƙawari, sai Muka tserar da su da waɗanda Muke ga damar (tserarwa) kuma Muka hallakar da maɓarnata.

  10. لَقَدۡ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ كِتَٰبٗا فِيهِ ذِكۡرُكُمۡۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ 

    Open ayah 21:10

    Haƙiƙa Mun saukar muku da littafi (wanda) a cikinsa akwai ɗaukakarku; me ya sa ba kwa hankalta? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayar da amsa ne ga maganar kafirai da suka yi ta cewa Allah ba zai aiko mutum ba, sai ya tabbatar musu da cewa bai taɓa aiko da wani manzo ba kafin Annabi (ﷺ) sai mutum namiji wanda ya riƙa yi masa wahayi. Allah bai aiko da mala’ika ba. Don haka ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa kafirai masu waccan magana cewa, su tambayi malaman Ma’abota Littafi za su faɗa masu gaskiyar labarin idan su ba su sani ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar musu da cewa babu wasu manzanni da ya aiko, kuma ya yi su jiki kawai ba sa cin abinci. Su ma suna cin abinci kamar kowa, kuma suna mutuwa idan lokacin mutuwarsu ya zo, ba masu wanzuwa ne ba har abada. Sai kuma ya bayyana cewa ya aiko waɗannan manzanni zuwa ga al\'ummunsu, wasu suka gaskata su, wasu kuma suka ƙaryata su, sai Allah ya cika wa manzannin nan da muminai alƙawarinsa ya kuɓutar da su daga hallaka, ya kuma hallakar da kafirai maɓarnata saboda kafircinsu da ƙetare iyakokinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jawo hankalinsu zuwa ga fahimtar darajar Alƙur’ani da ɗaukakarsa da cewa, ya saukar musu da Alƙur’ani wanda ya ƙunshi ɗaukakarsu kuma abin alfaharinsu, idan har sun yi imani da shi sun yi aiki da karantarwarsa. Yanzu bai kamata su gane hakan ba, su yi gaggawa wajen yin imani da shi da aiki da koyarwarsa?

  11. وَكَمۡ قَصَمۡنَا مِن قَرۡيَةٖ كَانَتۡ ظَالِمَةٗ وَأَنشَأۡنَا بَعۡدَهَا قَوۡمًا ءَاخَرِينَ

    Open ayah 21:11

    Al’ummu nawa ne kuma Muka hallakar (waɗanda) suka kasance azzulumai, Muka kuma halicci wasu mutanen daban bayansu?

  12. فَلَمَّآ أَحَسُّواْ بَأۡسَنَآ إِذَا هُم مِّنۡهَا يَرۡكُضُونَ

    Open ayah 21:12

    Lokacin da suka fara jin azabarmu sai ga su suna guje mata.

  13. لَا تَرۡكُضُواْ وَٱرۡجِعُوٓاْ إِلَىٰ مَآ أُتۡرِفۡتُمۡ فِيهِ وَمَسَٰكِنِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُسۡـَٔلُونَ

    Open ayah 21:13

    (Aka ce da su): “Kada ku gudu, ku dawo zuwa ga abin da aka ni’imta ku da shi, da kuma gidajenku don a yi muku tambayoyi.”

  14. قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ

    Open ayah 21:14

    Suka ce: “Kaiconmu, lallai mu kam mun kasance azzalumai!”

  15. فَمَا زَالَت تِّلۡكَ دَعۡوَىٰهُمۡ حَتَّىٰ جَعَلۡنَٰهُمۡ حَصِيدًا خَٰمِدِينَ

    Open ayah 21:15

    Sannan waccan (maganar tasu) ba su daina faɗar ta ba har Muka mai da su girbabbu, matattu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya hallaka al\'ummu da yawa saboda zaluncinsu da kafircinsu, ya kuma maye gurabensu da wasu al\'ummun daban. Lokacin da azabar Allah ta zo wa waɗannan al\'ummun suka gan ta ƙuru-ƙuru sai suka fice daga gidajensu da garuruwansu suna ƙoƙarin gudu wai su tsira da rayuwarsu. Sai aka riƙa kiran su cikin izgili da tsokana ana faɗa musu cewa su koma gidajensu da garuruwansu inda suka riƙa yin rayuwar tamore da bushasha domin a yi musu tambayoyi a kan rayuwarsu ta duniya. Hakan kuwa ba zai taɓa saɓuwa ba, domin azabar Allah ta riga ta zo musu babu mafaka ko maɓuya. Don haka ne azzalumai za su yi ta kururuwa da nadama marar amfani suna kiran ya kaiconsu, lallai su sun tabbata azzalumai saboda sun kafirce wa Allah da manzanninsa sun ƙi gaskiya. Allah ya bayyana cewa haka za su ci gaba da kururuwa suna surutai na nadama da kaico har sai ya mayar da su kamar girbabbiyar shuka matattu ko shurawa babu mai iya yi.

  16. وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَآءَ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا لَٰعِبِينَ

    Open ayah 21:16

    Kuma ba Mu halicci sama da ƙasa da kuma abin da yake tsakaninsu don wasa ba.

  17. لَوۡ أَرَدۡنَآ أَن نَّتَّخِذَ لَهۡوٗا لَّٱتَّخَذۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّآ إِن كُنَّا فَٰعِلِينَ

    Open ayah 21:17

    In da Mun yi nufin Mu riƙi (abin) da zai shagaltar (mata ko ɗa), to da sai Mu riƙe shi daga waɗanda suke a wurinmu, idan har za Mu yi hakan.

  18. بَلۡ نَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَى ٱلۡبَٰطِلِ فَيَدۡمَغُهُۥ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٞۚ وَلَكُمُ ٱلۡوَيۡلُ مِمَّا تَصِفُونَ

    Open ayah 21:18

    A’a, ba haka ba ne, Muna jefa gaskiya a kan ƙarya, sai ta yi rugu-rugu da ita, sai (ka gan ta) ta ɓace ɓat. Kuma tsananin azaba ya tabbata a gare ku saboda abin da kuke siffanta (Shi da shi).

  19. وَلَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَنۡ عِندَهُۥ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَلَا يَسۡتَحۡسِرُونَ

    Open ayah 21:19

    Duk kuwa waɗanda suke sammai da ƙasa nasa ne, kuma waɗanda suke wurinsa ba sa girman kai game da bauta masa, kuma ba sa gajiya.

  20. يُسَبِّحُونَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ لَا يَفۡتُرُونَ 

    Open ayah 21:20

    Suna tasbihi dare da rana ba sa ƙosawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu dalilai na cikar ikonsa a kan komai da cancantar a bauta masa shi kaɗai. Da cewa bai halicci sama da ƙasa da abin da yake tsakaninsu don wasa ba. Ya halicce su ne don nuna cikar ikonsa da Ƙudurarsa. Ya tabbatar da cewa da a ce yana nufin ya riƙi abin da zai shagaltar da shi kamar mata ko ɗa, to da sai ya riƙe shi daga waɗanda suke tare da shi, a can cikin sammai ba a ƙasa ba, domin girman darajar sama ɗin ne ma Allah ya halicci mafiya yawan masu bauta masa a cikinta. To amma Allah ba zai yi hakan ba, domin ya tsarkaka da a ce ya riƙi ɗa ko mata. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi ne ya ɗauki nauyin ruguza ƙarya a duk inda take, domin da zarar ya yi wa Manzonsa wahayi da gaskiya sai ya jefa wannan gaskiyar a kan ƙaryar kafirai sai ta yi daga-daga da ita, ta wargaje, ta gushe cikin gaggawa, a nemeta a rasa. Sannan Allah ya bayyana cewa tsananin azaba ya tabbata ga azzalumai masu cewa Allah yana da mata ko ɗa, domin wannan siffanta Allah ne da abin da sam bai kamace shi ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi ne mamallakin sammai da ƙasa, don haka shi ba mabuƙaci ne ga komai ba har da zai riƙi mata ko ɗa. Kowa da komai masu buƙata ne a wurinsa. Kuma mala’ikun da suke wajensa waɗanda wasu mushirikai suke cewa ‘ya’yansa ne mata, to wannan shaci-faɗinsu ne; dukkansu bayinsa ne masu bautar sa dare da rana ba sa girman kai wajen bauta masa ba kuma sa gajiya da haka. Suna kuma tsarkake Allah dare da rana ba sa ƙosawa. An karɓo daga Hakim ɗan Hizam (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Annabi (ﷺ) yana zaune tsakiyar sahabbansa sai ya ce musu: “Shin kuwa kuna jin abin da nake ji.” Sai suka ce: “Babu abin da muke ji.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lallai ni ina jin ƙarar sama, kuma ba za a zarge ta ba idan ta yi ƙara, domin babu masaka tsinke a cikinta face akwai wani mala’ika a wurin, yana mai sujjada, ko a tsaye.” [Ibn Abi Hatim, At-Tafsir 1072].

  21. أَمِ ٱتَّخَذُوٓاْ ءَالِهَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ هُمۡ يُنشِرُونَ

    Open ayah 21:21

    Shin ko <b>sun riƙi wasu ababen bauta a nan ƙasa ne waɗanda suke raya matattu?

  22. لَوۡ كَانَ فِيهِمَآ ءَالِهَةٌ إِلَّا ٱللَّهُ لَفَسَدَتَاۚ فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَرۡشِ عَمَّا يَصِفُونَ

    Open ayah 21:22

    Da ya zamana akwai wasu ababen bauta ba Allah ba a cikinsu (wato sammai da ƙasa), to da sun lalace. Sai dai tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi game da abin da suke siffata (Shi da shi).

  23. لَا يُسۡـَٔلُ عَمَّا يَفۡعَلُ وَهُمۡ يُسۡـَٔلُونَ

    Open ayah 21:23

    Ba a tambayar Sa game da abin da yake aikatawa, su dai ne za a tambaye su.

  24. أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗۖ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡۖ هَٰذَا ذِكۡرُ مَن مَّعِيَ وَذِكۡرُ مَن قَبۡلِيۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ ٱلۡحَقَّۖ فَهُم مُّعۡرِضُونَ

    Open ayah 21:24

    Ko kuma sun riƙi wasu ababen bauta ne ba Shi ba? Ka ce (da su): “To ku kawo dalilinku (a kan haka). Ga wa’azin waɗanda suke tare dani (watau Alƙur’ani), ga kuma wa’azin waɗanda suka gabace ni (watau littattafan annabawa sai ku duba).” A’a, yawancinsu dai ba sa sanin gaskiya sannan kuma masu bijire (mata) ne.

  25. وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ

    Open ayah 21:25

    Kuma ba wani manzo da Muka aiko gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Ni; to sai ku bauta min. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya musanta wa mushirikai yadda suka rungumi wasu gumaka suna bauta musu ba Allah ba, kuma su da kansu sun tabbata da cewa waɗannan allolin ba za su iya tayar da matattu bayan mutuwarsu ba, to saboda me suke bautar wasu gajiyayyu marasa ikon komai? Sai kuma ya bayyana dalili na hankali da yake tabbatar da cewa Allah Ɗaya ne ba shi da abokin tarayya, da cewa, da a ce akwai wasu alloli tare da Allah waɗanda su ma suke da iko irin nasa, suke iya aikata abin da suka ga dama, to da tuni tsarin gudanar da sammai da ƙasa ya lalace, sauran halittu ma sun lalace, domin za a sami jayayya tsakanin allolin masu cikakken iko iri guda. To amma wanzuwar sammai da ƙasa a kan tsari guda tutur shi yake tabbatar da Kaɗaitakar Allah. Don haka Allah ya tabbatar da cewa ya tsarkaka daga dukkan abin da suke siffanta shi da shi na yin tarayya da wasu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakken mulkinsa a kan bayinsa, da cewa shi kaɗai ne mai aikata yadda ya ga dama, ya haramta abin da ya so, babu wanda ya isa ya yi masa tambaya a kan duk abin da ya aikata ko hukuncin da ya yanke ya zartar. Shi ne kuma yake da ikon tambayar bayinsa game da duk abin da suka aikata sannan ya yi musu sakayya a kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kore wata hujja ta ilimi wadda masu haɗa shi da wasu wurin bauta suka dogara da ita da cewa suna bauta musu ne kawai ba tare da wani ilimi ba. Ya umarci Annabi (ﷺ) da ya nemi mushirikan da su kawo hujjojinsu masu nuna cancantar gumakansu ga bauta. Ya kuma bayyana musu cewa ga Alƙur’ani nan da aka saukar masa ga kuma littattafan da aka saukar wa sauran annabawa, a cikinsu duka babu wata hujja mai nuna a haɗa Allah da wasu ababe daban a wajen bauta. Don haka ya tabbatar da cewa yawancinsu ba su da wani ilimi da suke dogaro da shi sai ra’ayin riƙau da jahilici da kuma bijire wa gaskiya ba sa son sauraron ta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafa batun bauta masa shi kaɗai da cewa, babu wani manzo da ya aiko gabanin Manzon Allah (ﷺ) sai da ya yi masa wahayi cewa, babu wani abin bautawa da gaskiya sai shi kaɗai, don haka su bauta masa kada su haɗa shi da kowa wajen bauta.

  26. وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۚ بَلۡ عِبَادٞ مُّكۡرَمُونَ

    Open ayah 21:26

    Suka kuma ce wai Allah Ya riƙi ɗa (daga cikin mala’iku)! Tsarki ya tabbata a gare Shi. A’a, su bayi dai ne ababen girmamawa.

  27. لَا يَسۡبِقُونَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ وَهُم بِأَمۡرِهِۦ يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 21:27

    Ba sa rigayar Sa da magana, su kuma da umarninsa suke aiki.

  28. يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ

    Open ayah 21:28

    Yana sane da ayyukansu da suka gabatar da na nan gaba, ba kuma za su yi ceto ba sai ga wanda Ya yarda (daga bayinsa), suna kuwa masu kaffa-kaffa don tsoron Sa.

  29. ۞وَمَن يَقُلۡ مِنۡهُمۡ إِنِّيٓ إِلَٰهٞ مِّن دُونِهِۦ فَذَٰلِكَ نَجۡزِيهِ جَهَنَّمَۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 21:29

    Daga cikinsu kuwa duk wanda ya ce: “Ni abin bauta ne ba shi (Allah) ba,” to wannan za Mu saka masa da (wutar) Jahannama. Kamar haka kuwa Muke saka wa azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana cikakkun dalilai masu nuna tsarkakarsa daga duk wani abokin tarayya, da kuma rusa aƙidar mushirikan Larabawa masu cewa wai mala’iku ‘ya’yan Allah ne mata. Allah ya tsarkake kansa daga wannan mummunan furuci nasu, ya tabbatar musu da cewa mala’iku bayin Allah ne masu girma da daraja a wurinsa amma ba ‘ya’yansa ba. Ya kuma bayyana irin biyayyarsu da ladabinsu gare shi; ba sa rigayar sa da wata magana sai ya umarce su da su faɗi wani abu, sannan kuma idan ya umarce su da aikata wani abu to ba sa saɓa umarninsa ko kaɗan suna bin sa sau da ƙafa. Ya kuma bayyana yadda iliminsa ya kewaye komai nasu ya san duk ayyukansu na baya da waɗanda za su yi a nan gaba, don haka duk abin da suke yi da saninsa suke yin sa. Wannan ya sanya ko da ceto a ranar alƙiyama ba za su yi wa kowa ba sai da izininsa kuma ga wanda ya yarda a ceta, sannan kuma koyaushe suna cike da tsoronsa, don haka ba za su taɓa saɓa ma umarninsa ko haninsa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa, da a ce wani mala’ika zai yi da’awar allanta, watau ya ce shi ma alla ne a bauta masa, to da lallai Allah ya yi masa mummunar azaba a wutar Jahannama, ya dawwama a cikinta har abada. Allah ya bayyana cewa wannan shi ne irin sakamakon da yake yi wa azzalumai masu kafirci da haɗa shi da abokan tarayya.

  30. أَوَلَمۡ يَرَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ كَانَتَا رَتۡقٗا فَفَتَقۡنَٰهُمَاۖ وَجَعَلۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ كُلَّ شَيۡءٍ حَيٍّۚ أَفَلَا يُؤۡمِنُونَ 

    Open ayah 21:30

    Yanzu waɗanda suka kafirta ba sa ganin cewa a da can sammai da ƙasa a haɗe suke, sannan Muka raba su; Muka kuma halicci duk wani abu mai rai daga ruwa? To me ya sa ba za su yi imani ba?

  31. وَجَعَلۡنَا فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِهِمۡ وَجَعَلۡنَا فِيهَا فِجَاجٗا سُبُلٗا لَّعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ

    Open ayah 21:31

    Muka kuma sanya kafaffun duwatsu a ƙasa don kar ta yi tangal-tangal da su, Muka kuma sanya wuraren tafiya a cikinta (su zama) hanyoyi don su gane (inda za su).

  32. وَجَعَلۡنَا ٱلسَّمَآءَ سَقۡفٗا مَّحۡفُوظٗاۖ وَهُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهَا مُعۡرِضُونَ

    Open ayah 21:32

    Muka kuma sanya sama (ta zama) rufi tsararre; su kuwa (duk da haka) masu bijire wa ayoyinta (watau sama) ne.

  33. وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ فِي فَلَكٖ يَسۡبَحُونَ

    Open ayah 21:33

    Shi ne kuma Wanda Ya halicci dare da rana, da kuma rana da wata; kowannensu yana ninƙaya cikin falakinsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin kafirai a kan su yi duba zuwa ga dalilai masu tabbatar da cikar Ƙudurarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai, da cewa yanzu su kafirai ba su san cewa a da sama da ƙasa a manne suke ba sai Allah ya raba su, ya sanya girgije a sama mai zubo da ruwa ya kuma fitar da tsirrai daga cikin ƙasa? Wannan ruwan ne kuma ya mayar da shi madogara ga duk wani abu mai rai, mutum da dabba da sauran halittu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ce: “Ya Manzon Allah, lallai ni duk sanda na gan ka sai in ji daɗi, farin ciki ya lulluɓe ni, ka ba ni labari game da komai.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Komai an halicce shi daga ruwa ne.” [Ahmad #7932]. Allah ya bayyana cewa, yanzu wannan kaɗai bai isa ya sa kafirai su yi imani da Allah ba su bauta masa shi kaɗai? Sai kuma ya ci gaba da lissafa wasu ƙarfafan dalilai game da sama, daga cikinsu akwai duwatsu waɗanda ya kafa su a matsayin turaku waɗanda suke riƙe da ƙasa don kada ta riƙa tangal-tangal da halittun kan doronta. Ya kuma tanadar wa matafiya hanyoyi a bayanta waɗanda suke bi don kai-komonsu da tafiye-tafiyensu. Ya kuma bayyana cewa ya sanya sama ta zama wani amintaccen rufi da ba a tsoron ya faɗo, ga shi kuwa ba ya da wani ginshiƙi da ke riƙe da shi. Kuma ya saka tsaro mai tsanani a cikin sararin samaniya saboda hana shaiɗanu satar sauraro. To amma duk da waɗannan ayoyi da dalilai da Allah yake nuna wa mushirikai sun ci gaba da bijire wa ayoyin nan na samaniya, kamar rana da wata da taurari, ba sa ɗaukar wata izina daga gare su ballantana har su yi imani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da cewa shi ne wanda ya halicci dare domin ya zama lokacin hutawa, ya kuma halicci yini domin ya zamanto lokacin fita neman abinci, ya kuma halicci rana don ta zama alama ce ta yini, wata kuma don ya zamanto shi ne alamar dare, sannan kowannensu ya fitar masa da hanyarsa, watau falaƙinsa wanda yake gudu a cikinsa ba tare da kaucewa ko kuskurewa ba.

  34. وَمَا جَعَلۡنَا لِبَشَرٖ مِّن قَبۡلِكَ ٱلۡخُلۡدَۖ أَفَإِيْن مِّتَّ فَهُمُ ٱلۡخَٰلِدُونَ

    Open ayah 21:34

    Ba Mu kuma sanya wa wani mutum dawwama ba a gabaninka; to yanzu idan ka mutu su ɗin masu dawwama ne?

  35. كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَنَبۡلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلۡخَيۡرِ فِتۡنَةٗۖ وَإِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ

    Open ayah 21:35

    Kowanne rai zai ɗanɗani mutuwa. Muna kuwa jarrabar ku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gare Mu ne za a dawo da ku.

  36. وَإِذَا رَءَاكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَٰذَا ٱلَّذِي يَذۡكُرُ ءَالِهَتَكُمۡ وَهُم بِذِكۡرِ ٱلرَّحۡمَٰنِ هُمۡ كَٰفِرُونَ

    Open ayah 21:36

    Idan kuma waɗanda suka kafirta su ka gan ka, ba abin da suke yi maka sai izgili (suna cewa): “Yanzu wannan shi ne wanda yake aibata allolinku?” Alhali kuwa su suna kafirce wa ambaton (Allah) Mai rahama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a gabanin zuwan Manzon Allah (ﷺ) babu wani ɗan’adam da ya dawwama a bayan ƙasa, don haka fatan mutuwa da mushirikai suke yi wa Manzon Allah (ﷺ) aikin banza ne, ba shi da wani tasiri, don ko ba su yi masa fatan ya mutu ba da man ai zai mutu, yayin da ajalinsa ya zo kwanakinsa na duniya suka ƙare, kamar yadda annabawa da manzannin farko suka rayu kuma suka mutu. Sannan kuma idan Annabi (ﷺ) ya mutu kamar yadda suke jira, shin su za su dawwama ne a raye ba za su mutu ba? Sai kuma ya tabbatar da cewa mutuwa riga ce da kowa sai ya sanya ta a wuyansa; duk wani mahaluƙi sai ya ɗanɗani mutuwa komai daɗewa, sai dai kawai bayi su sani cewa Allah ya yiwo su a duniya, ya umarce su ya kuma hana su; ya jarrabe su da alheri kamar wadata, da kuma sharri kamar talauci, don ya tantance na ƙwarai da wanda ba na ƙwarai ba daga cikinsu. Sannan bayan kowa ya mutu za a koma gaba ɗaya ne zuwa ga Allah don ya yi wa kowa sakamako a kan ayyukansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halayyar kafirai lokacin da suka ga Annabi (ﷺ) yana wa’azi, sai su riƙa yi masa izgili suna nuna shi suna cewa, yanzu wannan ne yake zagin iyayen gijinsu da suke bauta wa? Suna yin wannan izgili tare da kafirce wa Alƙur’ani da Allah ya saukar da kuma butulce wa ni’imomin da ya ba su na rayuwa. Don haka su ne suka fi cancantar a kushe musu ba Manzon Allah ba.

  37. خُلِقَ ٱلۡإِنسَٰنُ مِنۡ عَجَلٖۚ سَأُوْرِيكُمۡ ءَايَٰتِي فَلَا تَسۡتَعۡجِلُونِ

    Open ayah 21:37

    An halicci mutum da son gaggawa. Ba da daɗewa ba zan nuna muku ayoyina, to don haka kada ku nemi gaggauto da (zuwansu).

  38. وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 21:38

    Suna kuma cewa: “Wai yaushe ne wannan alƙawarin (na alƙiyama zai zo) idan kun kasance masu gaskiya?”

  39. لَوۡ يَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ حِينَ لَا يَكُفُّونَ عَن وُجُوهِهِمُ ٱلنَّارَ وَلَا عَن ظُهُورِهِمۡ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

    Open ayah 21:39

    Da waɗanda suka kafirta za su san lokacin da za su kasa kare fuskokinsu daga wuta, da kuma bayansu, ba kuma za a taimake su ba (to da ba su faɗi haka ba).

  40. بَلۡ تَأۡتِيهِم بَغۡتَةٗ فَتَبۡهَتُهُمۡ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ رَدَّهَا وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ 

    Open ayah 21:40

    A’a, za ta zo musu ne ta farat- ɗaya sai ta rikirkita su, ba kuwa za su iya kawar da ita ba, kuma su ba za a saurara musu ba.

  41. وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَحَاقَ بِٱلَّذِينَ سَخِرُواْ مِنۡهُم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

    Open ayah 21:41

    Haƙiƙa kuma an yi izgili ga manzannin da suka gabace ka, sai sakamakon abin da suke yin izgili da shi ya aukar wa masu yin izgilin. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ɗabi’ar jinsin ɗan’adam ta garaje da rashin bin abu a sannu. Wannan ɗabi’ar ce ta sanya kafirai suka riƙa gaggauto da aukuwar azaba a kansu wai idan har Manzon Allah mai gaskiya ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, ba jimawa zai nuna musu azabar tasa wadda suke gaggauto zuwanta, don haka ba ma sai sun nemi gaggauto ta ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai suna ƙaryata ranar alƙiyama har ma suna tambayar muminai cewa in da gaske ne za ta zo to yaushe ne za ta zo idan har muminai gaskiya suke faɗa? A nan ma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar wa kafirai martani da cewa, da a ce sun san lokacin da za su kasa kare fuskokinsu da bayansu daga wuta, kuma ba za su sami mai taimakon su ba wanda zai kare musu azabar, to da ba su riƙa neman a gaggauto da zuwan wannan ranar ba. Sai ya bayyana musu cewa wannan wutar da za a yi musu azaba da ita a wannan ranar ba za su san lokacin zuwanta ba, sai dai ta zo musu kwatsam ba zato ba tsammani, duk ta rikirkita su da tsoro da fargaba, ba kuma za su iya kare kansu daga gare ta ba, kuma ba za a jinkirta musu ba ballantana har su sami damar su tuba Allah ya yi musu rahama. Watau da kafirai masu ja da ranar alƙiyama sun sakankance da wannan rana da ba su gaggauto da azaba ba, da sun kasance cike da tsoro da fargaba a koyaushe, to amma da yake ba su san haka ba shi ne suke irin wannan cika baki. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci abin da Manzon Allah (ﷺ) ya sha fama da shi na izgilin mutanensa gare shi da ƙaryata shi. Allah ya lallashe shi a kan haka, da cewa ba shi kaɗai ne manzon da mutanensa suka yi masa izgili ba; an yi wa manzanni da dama a gabaninsa izgili, to amma daga ƙarshe sai azabar da suke yin izgili game da ita ta auka musu, ta kewaye su ta ko’ina, Allah ya hallaka su gaba ɗayansu. Don haka su ma masu yi wa Manzon Allah izgili su shiga taitayinsu kada irin abin da ya sami waɗancan su ma ya same su.

  42. قُلۡ مَن يَكۡلَؤُكُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ مِنَ ٱلرَّحۡمَٰنِۚ بَلۡ هُمۡ عَن ذِكۡرِ رَبِّهِم مُّعۡرِضُونَ

    Open ayah 21:42

    Ka ce (da su): “Wane ne yake kare ku dare da rana daga (azabar Allah) Mai rahama?” A’a su dai masu bijire wa ambaton Ubangijinsu ne.

  43. أَمۡ لَهُمۡ ءَالِهَةٞ تَمۡنَعُهُم مِّن دُونِنَاۚ لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَ أَنفُسِهِمۡ وَلَا هُم مِّنَّا يُصۡحَبُونَ

    Open ayah 21:43

    Ko kuwa suna da ababen bauta ne da za su kare su (daga azaba) ba Mu ba? Ba za su iya taimakon kansu ba, kuma ba za a kiyaye su (daga azabarmu) ba.

  44. بَلۡ مَتَّعۡنَا هَٰٓؤُلَآءِ وَءَابَآءَهُمۡ حَتَّىٰ طَالَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡعُمُرُۗ أَفَلَا يَرَوۡنَ أَنَّا نَأۡتِي ٱلۡأَرۡضَ نَنقُصُهَا مِنۡ أَطۡرَافِهَآۚ أَفَهُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ

    Open ayah 21:44

    A’a, Mun dai jiyar da waɗannan daɗi ne su da iyayensu, har dai rayuwa ta tsawaita a gare su. Yanzu ba sa ganin cewa Mu Muna zo wa ƙasa Muna cinye iyakokinta da kaɗan-kaɗan? Yanzu su ne masu yin rinjaye?. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana gazawar allolin da kafirai suke haƙilon bauta wa. Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya tambaye su cewa, wane ne zai iya ba su kariya da daddare lokacin da suke cikin gidajensu suna barci, ko da rana lokacin da suka fita hadahadarsu idan Allah mai rahama ya nufi saukar musu da azabar da za ta hallaka su? Tabbas ba su da wasu masu ba su tsaro in ba Allah ba, to amma duk da haka suna bijire wa wa’azozin Ubangijinsu da hujjojin da yake bayyana musu a koyaushe ba sa ɗaukar wa’azi ko izina daga gare su. Sai Allah ya sake tambayar su cewa, shin ko suna da wasu alloli ne da suke bauta wa waɗanda za su kare su daga azabar Allah idan ya yi nufin saukar musu da ita? Allah ya tabbatar musu da cewa su allolin nasu ba za su ma iya taimakon kawunansu ba, su hana wani mummunan abu ya same su, ko su jawo wa kawunansu wani abu mai amfani. To wanda bai amfani kansa ba, bai taimaki kansa ba ta yaya zai amfani wani ko ya taimaka masa?! Ga shi kuma ba waɗanda za su sami kariya ne ba daga Allah idan azabarsa ta zo. Sai kuma ya bayyana dalilin da ya sa kafirai suke ci gaba da kafircinsu yadda suke so, watau ganin yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su jin daɗin rayuwa ya hore musu ni’imominsa su da iyayensu, suna ta wadaƙarsu yadda suke so, ba su san cewa talala ce Allah yake yi musu ba. Suka daɗe cikin rayuwar jin daɗi da morewa har wannan ya ruɗe su suka ci gaba da zama a kan kafircinsu, zukatansu suka ƙeƙashe, amma ba sa la’akari da yadda Allah yake ta tafiyar da rayuwar waɗansu. Wasu ma a gabaninsu ya hallaka su. Ko kuma ba su ga yadda ya riƙa tauye ƙasa ba kaɗan da kaɗan, mutanen cikinta suna ta raguwa saboda mutuwa? Yanzu wannan bai ishe su darasi ba, su ma su ji tsoron aukuwar irin haka gare su? Ko kuma suna tsammanin su sun gagara ne ba za a fi ƙarfinsu ba? Ko kusa! Tabbas za a fi ƙarfinsu, domin ba za su iya guje wa ikon Allah ba ko su hana mutuwa ta riske su.

  45. قُلۡ إِنَّمَآ أُنذِرُكُم بِٱلۡوَحۡيِۚ وَلَا يَسۡمَعُ ٱلصُّمُّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا مَا يُنذَرُونَ

    Open ayah 21:45

    Ka ce (da su): “Ni kawai ina yi muku gargaɗi ne da wahayi.” Kurame kuwa ba za su ji kira ba idan ma ana gargaɗin su.

  46. وَلَئِن مَّسَّتۡهُمۡ نَفۡحَةٞ مِّنۡ عَذَابِ رَبِّكَ لَيَقُولُنَّ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ

    Open ayah 21:46

    Wallahi da wani ɗan furji na azabar Ubangijinka ya shafe su da tabbas za su ce: “Kaiconmu, lalle mu mun tabbata azzalumai.”

  47. وَنَضَعُ ٱلۡمَوَٰزِينَ ٱلۡقِسۡطَ لِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَلَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗاۖ وَإِن كَانَ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٍ أَتَيۡنَا بِهَاۗ وَكَفَىٰ بِنَا حَٰسِبِينَ

    Open ayah 21:47

    Za Mu kuma sanya ma’aunai na adalci a ranar alƙiyama, sannan ba za a zalunci kowanne rai da komai ba, ko da ya zama gwargwadon ƙwayar komayya ne, za Mu zo da shi. Kuma Mun isa Masu hisabi! A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa kafirai cewa shi Manzo ne kawai daga Allah wanda ya zo yana gargaɗin su da wahayin da Ubangijinsa ya yi masa. To amma sanannen abu ne cewa waɗanda kunnuwansu suka doɗe suka zamo kamar kurame ba sa ma sauraron kira da gargaɗin da ake yi musu, balle ya amfane su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa, waɗannan kafiran masu gaggauto da azabar Allah a kansu, da a ce wani ɓangare na azabar zai ɗan shafe su, to da sun fara yin nadama suna kururuwar lallai sun hallaka sun yi hasara, kuma a lokacin za su tabbatar da cewa lallai sun zalunci kansu saboda sun haɗa Allah da wasu wajen bauta, sun ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) da wahayin da ya zo musu da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakken adalcinsa a ranar alƙiyama, da cewa a wannan ranar zai tattara halittun farko da na ƙarshe wuri guda, zai ajiye ma’aunan ayyuka na adalci domin auna ayyukan bayinsa. To babu wani rai da za a zalunce shi a ranar ta hanyar a rage masa kyawawan ayyukansa, ko a ƙara masa laifukan da bai aikata ba. Allah ya tabbatar da cewa a ranar za a yi awo na ƙeƙe-da-ƙeƙe, komai ƙanƙantar aiki ko da bai kai ƙwayar komayya ba, to sai an kawo shi an auna shi a wannan ma’auni na adalci. Allah ya tabbatar da cewa lallai shi ya isa mai hisabi da zai ƙalailaice ayyukan bayinsa gaba ɗaya. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wasu kalmomi biyu marasa nauyi a kan harshe, masu nauyi a kan ma’auni, ababen soyuwa ga Allah mai rahama su ne: Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azim .” [Bukhari #6406 da Muslim #2694]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Asi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah mai girma da buwaya zai waro wani mutum daga cikin al’umma a gaban sauran halittu, sai a buɗe masa kundin takardun ayyukansa guda casa’in da tara, kowane kundi iya ganin mutum, sai Allah ya ce masa: “A nan akwai abin da ba ka san da shi ba? Shin mala’ikun da suke kulawa da kai suna rubuta ayyukanka sun zalunce ka?” Sai ya ce: “A’a ya Ubangijina.” Sai Allah ya ce masa: “To kana da wani hanzari ne ko wani kyakkyawan aiki?” Sai wannan mutum ya ruɗe ya kasa magana, sai kuma ya ce: “A’a ya Ubangijina.” Sai Allah ya ce: “E, kana da wani kyakkyawan aiki guda ɗaya, a yau ba za a zalunce ka ba.” Sai a fito masa da wani kati a cikinsa an rubuta Ash-hadu an la ilaha illallahu wa ashhadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu .” Sai Allah ya ce: “Ku kawo shi.” Sai wannan mutum ya ce: “Ya Ubangijina, me wannan kati zai amfanar tare da waɗannan kundaye?” Sai a ce masa: “Lallai fa kai ba za a zalunce ka ba.” Sai a ɗora waɗannan kundaye a cikin tafin ma’auni guda ɗaya, sai kawai su yi sakayau, wannan kati kuwa sai ya yi nauyi. Babu abin da zai nauyayi sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.” [Ahmad #6994 da Tirmizi #2639 da Ibn Majah #4300].

  48. وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ٱلۡفُرۡقَانَ وَضِيَآءٗ وَذِكۡرٗا لِّلۡمُتَّقِينَ

    Open ayah 21:48

    Haƙiƙa Mun ba wa Musa da Haruna (Attaura) mai rarrabewa (tsakanin ƙarya da gaskiya) da kuma haske da shiriya ga masu taƙawa.

  49. ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ وَهُم مِّنَ ٱلسَّاعَةِ مُشۡفِقُونَ

    Open ayah 21:49

    (Su ne) waɗanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da sun gan Shi ba, kuma su suna masu fargaba game da tashin alƙiyama.

  50. وَهَٰذَا ذِكۡرٞ مُّبَارَكٌ أَنزَلۡنَٰهُۚ أَفَأَنتُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ 

    Open ayah 21:50

    Wannan (Alƙur’ani) kuwa tunatarwa ne mai albarka da Muka saukar da shi. Shin ku yanzu kwa riƙa musun sa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da littafinsa Attaura kamar yadda ya saba ambaton su, tare da ambaton Annabi Muhammadu (ﷺ) da littafin Alƙur’ani. Allah ya ba wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) littafin Attaura mai rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya da tsakanin halal da haram, kuma haske mai shiryarwa ga muminai, mai tunatarwa ga masu taƙawa masu kiyaye dokokin Ubangijinsu. Sai kuma ya bayyana ko su wane ne masu taƙawa, da cewa su ne waɗanda suke jin tsoron Ubangijinsu duk kuwa da ba sa ganin sa da idanuwansu, sannan koyaushe suna tsorace da ranar alƙiyama. Saboda cikakken saninsu ga mahaliccinsu Allah sai suka haɗa tsakanin ihsani da tsoro. Sai kuma ya ambaci falalar Alƙur’ani da amfaninsa a rayuwar muminai, ya tabbatar da cewa shi tunatarwa ce ga dukkan abin da bawa zai so ya sani game da Allah da hukunce-hukuncen addininsa. Kuma mai albarka ne domin ya ƙunshi duk wani alheri na duniya da lahira. To amma duk da wannan matsayi nasa kafirai ba su yarda sun yi imani da shi ba, domin taɓewa da hasara.

  51. ۞وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ إِبۡرَٰهِيمَ رُشۡدَهُۥ مِن قَبۡلُ وَكُنَّا بِهِۦ عَٰلِمِينَ

    Open ayah 21:51

    Haƙiƙa kuma Mun bai wa Ibrahimu shiriyarsa tun da farko, Mun kuma zamanto Muna sane da shi.

  52. إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا هَٰذِهِ ٱلتَّمَاثِيلُ ٱلَّتِيٓ أَنتُمۡ لَهَا عَٰكِفُونَ

    Open ayah 21:52

    (Ka tuna) lokacin da ya ce da babansa da kuma jama’arsa: “Mene ne (amfanin) waɗannan gumakan da kuka duƙufa a bautar su?”

  53. قَالُواْ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا لَهَا عَٰبِدِينَ

    Open ayah 21:53

    Suka ce: “Mun sami iyayenmu suna bauta musu ne.”

  54. قَالَ لَقَدۡ كُنتُمۡ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمۡ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 21:54

    (Ibrahimu) ya ce: “Haƙiƙa ku da iyayen naku kun tabbata a kan ɓata bayyananne.”

  55. قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا بِٱلۡحَقِّ أَمۡ أَنتَ مِنَ ٱللَّٰعِبِينَ

    Open ayah 21:55

    Suka ce: “Yanzu ka zo mana da gaskiya ne ko kuwa kai ma kana cikin masu wasa (da mu) ne?”

  56. قَالَ بَل رَّبُّكُمۡ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ ٱلَّذِي فَطَرَهُنَّ وَأَنَا۠ عَلَىٰ ذَٰلِكُم مِّنَ ٱلشَّٰهِدِينَ

    Open ayah 21:56

    (Ibrahimu) ya ce: “A’a, Ubangijinku dai (Shi ne) Ubangijin sammai da ƙasa, Wanda Ya halicce su, kuma ni ina daga masu shaida a kan wannan. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa tun gabanin ya ba wa Annabi Musa da Haruna (() Attaura ya riga ya ba wa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ilimin sanin hujja mai ƙarfi tun yana ƙaraminsa, domin yana sane da shi da cancantarsa da annabta da zaɓin Ubangiji. Allah ya bayyana yadda Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fara fuskantar mutanensa masu bautar gumaka da wa’azi da jan hankali, yayin da ya tambayi mahaifinsa Azara da mutanensa, game da waɗannan gumakan da suka duƙufa suna bautar su, alhalin ba wani amfani da suke samu a wurinsu? Sai suka amsa masa da cewa su dai sun tashi sun tarar iyayensu suna bauta musu ne don haka su ma suke aikata abin da iyayensu suka aikata. Watau dai wannan ita ce kawai hujjarsu ta bautar gumaka ba tare da wani ilimi daga Allah ba. Sai Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar musu cewa wannan karkatacciyar hanya da suke kai su da iyayensu ɓata ne bayyananne, domin shirka ce da Allah da barin ɗayanta Allah. Sai wannan amsa ta Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ta ba su mamaki ta kuma ɗaure musu kai, sai suke tambayar sa: Wai shin da gaske yake yi kuwa ko kuma yana yi musu wasa ne da zolaya? Sai ya mayar musu da martani cewa, tabbas shi fa da gaske yake, ya ma ƙara tabbatar musu da cewa Ubangijinsu shi ne Ubangijin sammai da ƙasa wanda ya ƙirƙiri halittarsu ba tare da ya kwaikwaya daga wurin wani ba, kuma shi tuni ya shaida da haka ya yi imani da Kaɗaitakar mahaliccinsa, bai yarda da gumakan da suke bauta wa ba.

  57. وَتَٱللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصۡنَٰمَكُم بَعۡدَ أَن تُوَلُّواْ مُدۡبِرِينَ

    Open ayah 21:57

    “Na rantse da Allah tabbas zan shirya wa gumakanku kaidi bayan kun tafi kun ba da baya!

  58. فَجَعَلَهُمۡ جُذَٰذًا إِلَّا كَبِيرٗا لَّهُمۡ لَعَلَّهُمۡ إِلَيۡهِ يَرۡجِعُونَ

    Open ayah 21:58

    Sai ya mayar da su guntu-guntu in ban da babbansu (da ya bari) don ko sa dawo masa (su tambaye shi).

  59. قَالُواْ مَن فَعَلَ هَٰذَا بِـَٔالِهَتِنَآ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 21:59

    Suke ce: “Wane ne ya yi wa ababen bautarmu wannan (aika-aika)? Lallai shi yana daga azzalumai!”

  60. قَالُواْ سَمِعۡنَا فَتٗى يَذۡكُرُهُمۡ يُقَالُ لَهُۥٓ إِبۡرَٰهِيمُ 

    Open ayah 21:60

    (Wasu daga cikinsu) suka ce: “Mun ji wani saurayi yana ambaton su, ana ce da shi Ibrahimu.”

  61. قَالُواْ فَأۡتُواْ بِهِۦ عَلَىٰٓ أَعۡيُنِ ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡهَدُونَ

    Open ayah 21:61

    Suka ce: “(Ku je) ku zo da shi kan idon mutane don su shaidi (abin da ya aikata).”

  62. قَالُوٓاْ ءَأَنتَ فَعَلۡتَ هَٰذَا بِـَٔالِهَتِنَا يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُ

    Open ayah 21:62

    (Da aka kawo shi sai) suka ce: “Yanzu kai ka aikata wannan (irin aiki) ga ababen bautarmu, ya Ibrahimu?”

  63. قَالَ بَلۡ فَعَلَهُۥ كَبِيرُهُمۡ هَٰذَا فَسۡـَٔلُوهُمۡ إِن كَانُواْ يَنطِقُونَ

    Open ayah 21:63

    (Ibrahimu) ya ce: “A’a, wannan babban nasu (shi) ya aikata shi, sai ku tambaye su idan ya zamana suna magana.”

  64. فَرَجَعُوٓاْ إِلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ فَقَالُوٓاْ إِنَّكُمۡ أَنتُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ

    Open ayah 21:64

    Sai suka koma ga (zargin) kawunansu sannan suka ce: “Lallai ku dai ne azzalumai.”

  65. ثُمَّ نُكِسُواْ عَلَىٰ رُءُوسِهِمۡ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَا هَٰٓؤُلَآءِ يَنطِقُونَ

    Open ayah 21:65

    Sannan aka juyo da kawunansu (zuwa kafirci) suka ce (da Ibrahimu): “Mun rantse haƙiƙa ka san cewa su waɗannan ba sa magana.”

  66. قَالَ أَفَتَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يَضُرُّكُمۡ

    Open ayah 21:66

    Ya ce: “To yanzu kwa riƙa bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amfana muku komai ba kuma ba zai cuce ku ba?

  67. أُفّٖ لَّكُمۡ وَلِمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

    Open ayah 21:67

    “Tir da ku, da kuma abin da kuke bauta wa wanda ba Allah ba. To yanzu ba kwa hankalta ba?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana labarin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa, da cewa, bayan ya gama kafa musu hujja ta hanyar wa’azi da jan hankali sai kuma ya ga ya dace ya yi amfani da wata hujjar ta zahiri da kowa zai iya ganin ta ya gane. A wannan karon rantsuwa ya yi a ransa cewa sai ya shirya wa gumakansu wata kutungwila bayan sun watse kowa ya kama gabansa sun shagala da bukukuwansu. Sai ya saɗaɗa ya shiga wurin bautarsu ya farfasa gumakansu ya yi guntu-guntu da su, in ban da babbansu, shi ya ƙyale shi don ya kafa hujja da shi, wataƙila idan sun dawo su tambaye shi wanda ya farfasa musu gumaka. Bayan dawowarsu kuwa suka ga irin ɓarnar da aka yi wa gumakansu, sai suka fara tattaunawa da junansu cewa lallai duk wanda ya rugurguza musu gumakansu haka, ba shakka ya cika azzalumi. Sai nan take wasu suka ce sun taɓa jin wani saurayi mai suna Ibrahimu yana faɗar mummunar magana a kansu yana aibata su, don haka akwai yiwuwar shi ne ya ragargaza su. Sai shugabanninsu suka ba da umarni maza a je a zo da Ibrahimu gaban mutane don kowa ya ji daga bakinsa idan shi ne ya yi musu wannan aika-aika, don a samu kama shi da hujja. Da suka zo da shi suka tambaye shi ko shi ne ya yi wa gumakansu wannan aika-aikar, sai shi kuma ya so ya kama su da hujja don ya nuna musu cewa gumakansu na banza ba su da wani tasiri, sai ya nuna musu ba shi ne ya yi wannan aikin ba; wannan babban gunkin ne da ke tsaye shi ne ya yi fushi ya mammake sauran ƙananan suka dagargaje. To amma ya kamata su tambayi gumakan da kansu idan suna magana ai za su faɗa musu gaskiyar abin da ya faru. Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sani su ma dukkansu sun san gumakan nan ba sa magana, domin ba su taɓa jin su sun yi ba, don haka sai suka koma suna tunani, suka tabbatar da cewa lallai gumakansu ba sa amfanarwa ba sa kuma iya cutarwa, don haka cutar kansu kawai suke yi da har suke bautar su ba Allah ba. To amma sai suka dawo da baya zuwa ga kafircinsu da jayayyarsu, sai suka bayyana wa Annabi Ibrahimu cewa, ai da man ya tabbata cewa waɗannan gumakan ba sa magana, to don me zai umarce su da su tambaye su labarin abin da ya faru? Watau dai suka fassara lamarin da cewa tsokanar su yake yi yana yi musu izgili kawai. Ana zuwa wannan gaɓar sai Annabi Ibrahimu ya shiga yi musu wa’azi yana nuna takaicinsa game da bautar wanin Allah da suke yi, su ma sun tabbatar da cewa gumakan ba za su amfana musu komai ba, ba kuma za su cutar da su da komai ba; sun kasa amfani da hankalin da Allah ya ba su don su gane irin ruɗanin da suke ciki su dawo kan hanya madaidaiciya.

  68. قَالُواْ حَرِّقُوهُ وَٱنصُرُوٓاْ ءَالِهَتَكُمۡ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ

    Open ayah 21:68

    Sai suka ce: “Ku ƙone shi ku kuma taimaki allolinku in kun kasance masu aikata hakan.”

  69. قُلۡنَا يَٰنَارُ كُونِي بَرۡدٗا وَسَلَٰمًا عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ

    Open ayah 21:69

    (Da suka jefa shi cikin wutar sai) Muka ce: “Ke wuta, ki zama sassanya da kuma aminci ga Ibrahimu!”

  70. وَأَرَادُواْ بِهِۦ كَيۡدٗا فَجَعَلۡنَٰهُمُ ٱلۡأَخۡسَرِينَ 

    Open ayah 21:70

    Suka yi nufin shirya masa makirci sai Muka mayar da su taɓaɓɓu.

  71. وَنَجَّيۡنَٰهُ وَلُوطًا إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَا لِلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 21:71

    Muka kuma tserar da shi, shi da Luɗu zuwa ga ƙasar da Muka yi albarka a cikinta ga talikai (watau Sham).

  72. وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ نَافِلَةٗۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا صَٰلِحِينَ

    Open ayah 21:72

    Muka kuma ba shi Is’haƙa da kuma Ya\'aƙubu ƙari (wato jika). Dukkanninsu kuma Mun sanya su salihai.

  73. وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَئِمَّةٗ يَهۡدُونَ بِأَمۡرِنَا وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِمۡ فِعۡلَ ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَإِقَامَ ٱلصَّلَوٰةِ وَإِيتَآءَ ٱلزَّكَوٰةِۖ وَكَانُواْ لَنَا عَٰبِدِينَ

    Open ayah 21:73

    Muka kuma sanya su shugabanni masu shiryarwa da umarninmu, Muka kuma yi musu wahayi na aikata alheri da tsai da salla da ba da zakka, sun kuwa zamanto masu bauta mana ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba mu labarin Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa bayan ya ragargaza gumakansu ya tsayar musu da hujja a aikace game da kasawar gumakan da suke bauta wa ba Allah ba, sun kuma kasa fuskantar sa da wata gamsasshiyar hujja. Don haka sai suka ga bari su yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe shi, sai kawai shugabanninsu suka ba da umarni a jefa shi a cikin wuta a ƙona shi ƙurmus har lahira, don su nuna taimakonsu ga gumakansu da kuma ramuwa a kan abin da ya yi musu. Wannan shi ya fi dacewa idan dai har suna son yi masa wani horo da uƙuba. Sai suka hura wuta ganga-ganga suka jefa Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a cikinta, to amma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira wutar ya ba ta umarni cewa ta juye ta koma sanyi da aminci ga Annabi Ibrahimu. Haka kuwa ya faru, wuta ta ci ta cinye ba tare da ta cutar da shi da komai ba. Allah ya bayyana cewa mutanen Annabi Ibrahimu sun yi niyyar cutar da shi su ƙona shi har lahira, to amma Allah da ikonsa ya mayar da su su ne taɓaɓɓu a duniya da lahira, ya mayar da Ibrahimu shi da mabiyansa su ne maraubauta a duniya da lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haɗa Ibrahimu da ɗan ɗan’uwansa Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya yi imani da shi, ya kuɓutar da su ya fitar da su daga tsakiyar waɗannan azzalumai zuwa ƙasar Sham wadda ya albarkace ta da ɗimbin albarkatu ga mutane ya kuma aiko da annabawa da yawa a cikinta. Haka kuma ya yi wa Annabi Ibrahimu wata baiwar daban, watau ta samun haihuwar ɗansa Is’haƙa ya ƙara masa da jikansa Ya\'aƙubu, kuma dukkansu shi da ɗansa da jikansa Allah ya sanya su masu ɗa’a ne da biyayya ga Allah. Allah kuma ya bayyana wata nagarta tasu, watau yadda ya mayar da su shugabanni masu shiryar da mutane zuwa ga ayyukan alheri da ɗora su a kan hanyar bautar Allah shi kaɗai. Ya kuma yi musu wahayin cewa su dimanci ayyukan alheri su tsayar da salla yadda ya kamata su ba da zakka. Allah ya shaide su da cewa sun kasance masu bautar Allah ne da miƙa wuya a gare shi.

  74. وَلُوطًا ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗا وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَت تَّعۡمَلُ ٱلۡخَبَٰٓئِثَۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمَ سَوۡءٖ فَٰسِقِينَ

    Open ayah 21:74

    Luɗu kuma Muka ba shi hukunci da ilimi, Muka kuma tserar da shi daga alƙaryar nan da (mutanenta) suka zamanto suna aikata munanan ayyuka. Lallai su sun kasance mutanen banza ne fasiƙai.

  75. وَأَدۡخَلۡنَٰهُ فِي رَحۡمَتِنَآۖ إِنَّهُۥ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

    Open ayah 21:75

    Muka kuma shigar da shi cikin rahamarmu; lallai shi yana daga (cikin) mutane na gari. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da yawan ilimi na Shari’a da ya ba shi, da hikimar zartar da hukunce-hukunce na Shari’a a tsakanin mutane yadda ya kamata. Allah ya aika shi zuwa ga mutanensa domin ya kirawo su zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, ya hana su aikata munanan ayyuka na alfasha, musamman mummunan aikin da suka shahara da shi na neman maza. Ya zauna cikinsu tsawon lokaci yana yi musu wa’azi amma suka ƙi amsa kiransa, har sai da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kifar da garinsu ya hallaka su baki ɗaya, domin sun tabbata mutanen banza ne fasiƙai. Shi kuma Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) Allah ya kuɓutar da shi da iyalansa in ban da matarsa. Ya umarce shi da ya bar garin cikin dare, suka fita daga wannan alƙarya suka tsira da taimakon Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya shigar da Annabi Luɗu cikin rahamarsa, ya tserar da shi daga azabar da ta auka wa mutanensa, kuma yana daga cikin mutane na gari masu bin umarnin Allah da hanuwa da haninsa.

  76. وَنُوحًا إِذۡ نَادَىٰ مِن قَبۡلُ فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ

    Open ayah 21:76

    (Ka tuna) lokacin da Nuhu ya roƙi Ubangijinsa tun a da can, sannan Muka amsa masa (roƙonsa) Muka tserar da shi da iyalinsa daga baƙin ciki mai girma.

  77. وَنَصَرۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمَ سَوۡءٖ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 21:77

    Muka kuma taimake shi bisa mutanen da suka ƙaryata ayoyinmu. Lalle su sun kasance mutanen banza, sai Muka nutsar da su gaba ɗaya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabi (ﷺ) labarin Manzonsa na farko a duniya, watau Annabi Nuhu wanda Allah ya aiko shi zuwa ga mutanensa masu bautar wasu ba Allah ba. Sai da ya shekara dubu ba hamsin a cikinsu yana yi musu wa’azi ba dare ba rana, a fili da a ɓoye, to amma suka ƙi karɓar kiransa sai ‘yan kaɗan daga cikinsu. Lokacin da ya tabbatar wa’azinsa ba zai amfane su ba sai ya roƙi Allah da ya hallaka su ƙwansu da ƙwarƙwatarsu, kada ya bar ko da kafiri ɗaya a bayan ƙasa. Sai ko Allah ya amsa masa addu’arsa ya tserar da shi da iyalansa muminai daga baƙin ciki mai girma, lokacin da bala’in ruwan Ɗufana ya ɓarke daga ƙasa da sama, Allah ya taimake shi a kan makircin mutanensa waɗanda suka ƙaryata ayoyin da ya ba shi masu tabbatar da gaskiyarsa. Allah ya bayyana cewa lallai su mutanen banza ne maɓarnata. Allah ya dulmiyar da su baki ɗaya a cikin ruwan Ɗufana duk suka hallaka.

  78. وَدَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ إِذۡ يَحۡكُمَانِ فِي ٱلۡحَرۡثِ إِذۡ نَفَشَتۡ فِيهِ غَنَمُ ٱلۡقَوۡمِ وَكُنَّا لِحُكۡمِهِمۡ شَٰهِدِينَ

    Open ayah 21:78

    (Ka tuna) kuma Dawuda da Sulaimanu lokacin da suke yin hukunci a kan amfanin gona lokacin da dabbobin wasu mutane suka cinye shi da daddare, Mun kuwa zamanto Muna sane da irin hukuncin nasu.

  79. فَفَهَّمۡنَٰهَا سُلَيۡمَٰنَۚ وَكُلًّا ءَاتَيۡنَا حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَسَخَّرۡنَا مَعَ دَاوُۥدَ ٱلۡجِبَالَ يُسَبِّحۡنَ وَٱلطَّيۡرَۚ وَكُنَّا فَٰعِلِينَ

    Open ayah 21:79

    Sai Muka ganar da Sulaimanu shi (hukuncin). Kuma dukkaninsu Mun ba su annabta da ilimi. Muka kuma hore wa Dawuda duwatsu da tsuntsaye, suna tasbihi tare da shi. Mun kuwa kasance Masu aikata (haka).

  80. وَعَلَّمۡنَٰهُ صَنۡعَةَ لَبُوسٖ لَّكُمۡ لِتُحۡصِنَكُم مِّنۢ بَأۡسِكُمۡۖ فَهَلۡ أَنتُمۡ شَٰكِرُونَ 

    Open ayah 21:80

    Muka kuma koya masa yadda ake ƙera silke dominku don ya kare ku lokacin yaƙinku; to shin ku masu godiya ne?

  81. وَلِسُلَيۡمَٰنَ ٱلرِّيحَ عَاصِفَةٗ تَجۡرِي بِأَمۡرِهِۦٓ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَاۚ وَكُنَّا بِكُلِّ شَيۡءٍ عَٰلِمِينَ

    Open ayah 21:81

    Sulaimanu kuwa (Muka hore masa) iska mai ƙarfi tana gudu da umarninsa zuwa ƙasar da Muka yi albarka a cikinta, (watau Sham). Mun kuwa kasance Masana ga kowanne abu.

  82. وَمِنَ ٱلشَّيَٰطِينِ مَن يَغُوصُونَ لَهُۥ وَيَعۡمَلُونَ عَمَلٗا دُونَ ذَٰلِكَۖ وَكُنَّا لَهُمۡ حَٰفِظِينَ

    Open ayah 21:82

    Akwai kuma wasu aljannu da suke nutso don fito masa (da lu’u-lu’u) suna kuma yin wani aikin ban da wannan (kamar gine-gine); Mun zamanto kuma Masu kula da su)). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabi (ﷺ) labarin annabawan Allah guda biyu, watau Dawudu da ɗansa Sulaiman waɗanda sun kasance cikin annabawan Banu Isra’ila. Allah ya ba su ilimi da hikima mai yawa, musamman wadda ta danganci hanyar warware rikice-rikicen Shari’a. Allah ya bai wa Annabi (ﷺ) labarinsu lokacin da suka yanke wani hukunci game da wasu dabbobi da suka shiga gonar wasu manoma suka yi musu mummunar ɓarna. Allah kuma yana sane da irin hukuncin da suka yanke. Yadda kuwa abin ya faru shi ne: Wani manomi ne ya kai ƙara wajen Annabi Dawudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) game da dabbobin wasu mutane da suka shiga gonarsa da daddare ba tare da makiyayansu ba suka cinye masa amfanin gonarsa bayan ya sha wahala a kai. Bayan masu dabbobin sun yarda da laifinsu sai Annabi Dawudu ya yanke hukunci da cewa, manomin nan zai karɓi waɗannan dabbobin a madadin kayan amfanin gonarsa da suka cinye masa bayan ya ƙiyasta ƙimar amfanin gonar daidai take da ta dabbobin. Wannan shi ne horon da ya ga ya dace ya yi wa masu dabbobi bisa ga sakacin da suka yi na rashin kula da dabbobinsu. To amma sai Allah ya ba wa Annabi Sulaiman wata zuzzurfar fahimta dangane da wannan hukunci, sai ya bayyana cewa abin da ya dace a yi a nan shi ne a ɗauki waɗannan dabbobi a damƙa su a hannun manomi ya je da su ya ci gaba da amfani da nononsu da gashinsu, a yayin da su kuma masu dabbobi za su sake noma wa wannan manomi gonarsa har sai ta dawo kamar yadda take da farko kafin dabbobinsu su lalata ta, sannan sai su mayar masa da gonarsa da amfanin cikinta shi kuma ya dawo musu da dabbobinsu. Kowa daga ƙarshe dukiyarsa ta komo hannunsa. Wannan ko shakka babu yana daga cikin cikar hankali da fahimta da Allah ya yi wa Sulaimanu baiwa da su. To amma don Allah ya tabbatar da cewa hukuncin da shi ma Dawudu ya yanke bai saɓa wa Ubangijinsa ba, kuma ya zama abin yabo da hikima da ilimi, sai Allah ya ƙara tabbatar da cewa dukkansu ya ba su annabta da sanin hukunce-hukuncen Shari’a, ba Sulaiman kaɗai ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wata babbar baiwa da ya yi wa Dawudu, watau yadda ya hore masa duwatsu da tsuntsaye waɗanda suke yin tasbihi tare da shi duk lokacin da suka ji muryarsa yana yi. Allah ya tabbatar da cewa wannan aikinsa ne ba na wani ba. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari ya ce Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Ya Aba Musa, haƙiƙa an ba ka sauti mai daɗi irin sautin Dawud.” [Bukhari #5048 da Muslim #793]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata baiwar daban da ya ƙara wa Annabi Dawuda (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), watau yadda ya ba shi ikon sarrafa ƙarfe, yana mulmula shi yadda ya ga dama, ya koyar da shi sana’ar ƙera silke na mayaƙa don kariya daga sara ko suka a fagen daga. Daga wannan lokacin ‘yan’adam suka fahimci wannan sana’a suka riƙe ta a ko’ina. Allah ya bayyana cewa wannan ni’ima ce ga mutane da ya wajaba su gode wa Allah a kanta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi ma Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) akwai wata ƙarin baiwa da ya yi masa baya ga baiwar fahimta. Allah ya hore masa ikon sarrafa iska wadda take tafiya da shi, idan ya ga dama ta yi gudu da ƙarfi idan kuma ya so ya umarce ta ta tafi a sannu gwargwadon buƙatarsa. Takan ɗauke shi da shi da rundunarsa zuwa duk inda ya buƙaci zuwa a faffaɗar masarautarsa mai albarka, watau ƙasar Sham inda babbar cibiyar sarautarsa take. Allah ya tabbatar da cewa ya san komai game da waɗannan annabawa da duk abin da ya ba su na ilimi da hikima da sarauta. Sannan Allah ya bayyana cewa ya kuma hore wa Sulaimanu ikon sarrafa aljannu da sanya su su yi masa hidima irin wadda ya buƙata daga gare su. Daga cikinsu akwai waɗanda aikinsu kawai shi ne nutso a ƙarƙashin ruwa suna fito masa da albarkatu iri daban-daban kamar lu’ulu’u da marjani. Wasu kuma ba su da wani aiki sai yi masa manyan gine-gine da mutum-mutumi da ganuwoyi da makamantansu. Allah ya bayyana cewa shi ne mai tsare da su, yana kuma sane da adadinsu da ayyukansu, babu kuma mai iya guduwa daga cikinsu.

  83. ۞وَأَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلضُّرُّ وَأَنتَ أَرۡحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ

    Open ayah 21:83

    Kuma (ka tuna) Ayyuba lokacin da ya roƙi Ubangijinsa (yana cewa): “Lallai cuta ta same ni, Kai ne kuwa Mafi jin ƙan masu jin ƙai!”

  84. فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ فَكَشَفۡنَا مَا بِهِۦ مِن ضُرّٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ أَهۡلَهُۥ وَمِثۡلَهُم مَّعَهُمۡ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَذِكۡرَىٰ لِلۡعَٰبِدِينَ

    Open ayah 21:84

    Sai Muka amsa masa (roƙonsa) sannan Muka yaye cutar da take tare da shi, Muka kuma ba shi (madadin) iyalinsa (da ya rasa) da kuma kwatankwacinsu tare da su don jin ƙai daga gare Mu da kuma wa’azi ga masu bauta (ga Allah). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tunatar da Annabi (ﷺ) labarin Annabi Ayyuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jarrabe shi da bala’o’i iri-iri na tsananin rashin lafiya da mutuwar iyalansa da lalacewar dukiyarsa. Ya zauna tsawon lokaci cikin wannan jarrabar yana mai haƙuri da dangana da fawwala wa Allah komai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya ɗaga murya ya roƙe shi da cewa cuta ta same shi, don haka ya yaye masa ita, ya tausaya masa domin tausayinsa ya fi na duk wani mai tausayi. Sai ko Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa wa Ayyuba addu’arsa, ya kuma yaye masa cutar da ke tare da shi, sannan ya dawo masa da iyalansa da ya rasa, ya kuma ƙara masa wasu kamarsu. Allah ya tabbatar da cewa ya yi haka ne domin rahama daga wajensa da kuma tunatarwa da wa’azi ga bayinsa masu miƙa wuya gare shi don su ma su koyi haƙuri irin na Annabi Ayyuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Annabin Allah Ayyuba ya zauna cikin bala’i tsawon shekara goma sha takwas. Na kusa da na nesa duk suka guje masa sai wasu ‘yan’uwansa mutum biyu waɗanda suka fi kowa shaƙuwa da shi su ne suke zuwa wajensa safe da yamma. Sai wata rana ɗayansu ya faɗa wa ɗan’uwansa cewa: “Lallai Ayyuba ya yi wani zunubi ne da ba wanda ya taɓa yin irinsa.” Sai ɗan’uwan nasa ya tambaye shi me ya sa ya faɗi wannan maganar tasa? Sai ya amsa masa da cewa: “Idan ka lura za ka ga yau kimanin shekara goma sha takwas ke nan yana cikin wannan bala’in, Allah bai tausaya masa ya yaye masa shi ba.” Da yamma ta yi suka je wajen Ayyuba, wannan mutum bai iya haɗiye wannan maganar ta ɗan’uwansa ba a kan Annabi Ayyuba har sai da ya faɗa masa ita. Ayyuba ya ce: “To ni dai ban san wannan magana da kake faɗa ba. Abin da dai na riga na sani shi ne, ni mutum ne da a duk lokacin da na wuce ta gaban mutum biyu suna jayayya a junansu ɗayansu ya yi rantsuwa da Allah, to idan na dawo gida sai na yi masa kaffara don gudun kada ko ya yi rantsuwan nan ba bisa gaskiya ba.” Ayyuba ya zamanto yana fita bayan gari don biyan buƙatarsa, idan ya gama sai matarsa ta kamo hannunsa (domin su dawo gida). Wata rana sun fita sai matarsa ta ga ya daɗe bai dawo ba, to a lokacin Allah ne ya yi masa wahayi cewa: “Ka hauri ƙasa da ƙafarka, wannan ruwan wanka ne mai sanyi da na sha.” Da matarsa ta jira shi ba ta gan shi ba sai ta bi bayansa, sai ga shi yana tahowa, Allah ya yaye masa cutarsa, ya zamanto ya ma fi da kyau. Da ganin sa sai ta ce: “Bawan Allah, Allah ya yi maka albarka, ko ka ga Annabin Allah ɗin nan marar lafiya? Kai duk da haka ni ban taɓa ganin wani mutum da ya yi kama da shi ba lokacin da yake da lafiya irinka.” Sai ya ce: “Ni ne shi kuwa.” [Ibn Hibban #2898 da Abu Ya’ala #3617].

  85. وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِدۡرِيسَ وَذَا ٱلۡكِفۡلِۖ كُلّٞ مِّنَ ٱلصَّٰبِرِينَ

    Open ayah 21:85

    (Ka tuna) kuma Isma’ila da Idrisa da kuma Zulkifli; dukkansu suna cikin masu haƙuri.

  86. وَأَدۡخَلۡنَٰهُمۡ فِي رَحۡمَتِنَآۖ إِنَّهُم مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

    Open ayah 21:86

    Muka kuma shigar da su cikin rahamarmu; lalle su suna daga bayi na gari. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba wa Annabi (ﷺ) labarin wasu annabawa su uku daga cikin zaɓaɓɓun bayinsa, watau Isma’ila da Idrisa da Zulkifli. Allah ya yabe su da nagarta da haƙuri a kan bin sa da guje wa saɓa masa, ya kuma shigar da su cikin rahamarsa, watau ya ba su annabta sannan ya shigar da su Aljannarsa, domin kasancewarsu bayin Allah na gari waɗanda suka gyara zahirinsu da baɗininsu da kyawawan ayyuka.

  87. وَذَا ٱلنُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَٰضِبٗا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقۡدِرَ عَلَيۡهِ فَنَادَىٰ فِي ٱلظُّلُمَٰتِ أَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبۡحَٰنَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 21:87

    Kuma (ka tuna) ma’abocin kifi (wato Yunusa) lokacin da ya tafi yana cike da fushi, sannan ya zaci cewa ba za Mu ƙuntata masa ba, sai ya kira (Mu) a cikin duffai yana cewa: “Ba wani abin bauta da gaskiya sai Kai (ya Allah), tsarki ya tabbata a gare Ka, lallai ni na kasance cikin azzalumai!”

  88. فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡغَمِّۚ وَكَذَٰلِكَ نُـۨجِي ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 21:88

    Sai Muka amsa masa Muka kuma tserar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka kuwa Muke tserar da muminai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba wa Annabi (ﷺ) labarin Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya ƙaurace wa mutanensa da Allah ya aiko shi wajensu yana cike da fushi, ba tare da samun izini daga Ubangijinsa na ƙaura ce musu ba. Ya ƙaura ce ne saboda sun doge a kan kafirci da saɓon Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai yi zaton cewa Allah zai ƙuntata masa don ya bar jama’arsa kafirai ba. To amma sai Allah ya jarrabe shi da faɗawa cikin ƙunci da tsanani yayin da kifi ya haɗiye shi. To a nan ne fa ya shiga addu’a yana cikin duhu a kan duhu; ga duhun dare ga na kogi ga kuma na cikin kifi, inda yake cewa: “Ya Allah babu abin bauta wa da gaskiya sai kai; tsarki ya tabbata gare ka, lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.” Sai ko Allah ya bayyana cewa ya amsa masa addu’arsa, ya tserar da shi daga tsananin da yake ciki, ya fito da shi daga cikin cikin kifi. Allah kuma ya tabbatar da cewa kamar yadda ya tserar da Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), kamar haka ne yake tserar da muminai yayin da suka faɗa cikin wani tsanani ko musiba. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Addu’ar ma’abocin kifi (Yunus (Amincin Allah ya tabbata a gare shi)) lokacin da ya roƙi Allah yana cikin cikin kifi cewa: ﴾لا إِلهَ إِلّا أَنتَ سُبحانَكَ إِنّي كُنتُ مِنَ الظّالِمينَ﴿ Babu wani Musulmi da zai roƙi Allah da ita game da wata buƙatarsa sai Allah ya amsa masa.” [Ahmad #1462 da Tirmizi #3505].

  89. وَزَكَرِيَّآ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ رَبِّ لَا تَذَرۡنِي فَرۡدٗا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡوَٰرِثِينَ

    Open ayah 21:89

    (Ka tuna) kuma Zakariya’u lokacin da ya roƙi Ubangijinsa (cewa): “Ya Ubangijina, kada Ka bar ni ni kaɗai (ba magaji), Kai ne kuwa Fiyayyen magada.”

  90. فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَوَهَبۡنَا لَهُۥ يَحۡيَىٰ وَأَصۡلَحۡنَا لَهُۥ زَوۡجَهُۥٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَيَدۡعُونَنَا رَغَبٗا وَرَهَبٗاۖ وَكَانُواْ لَنَا خَٰشِعِينَ 

    Open ayah 21:90

    Sai Muka amsa masa Muka ba shi Yahya, Muka kuma gyara masa (mahaifar) matarsa. Lallai su sun kasance suna gaggawa wajen yin alherai, suna kuma roƙon Mu suna masu kwaɗayin (rahamarmu) masu kuma tsoron (azabarmu), sun kuma zamanto masu ƙasƙantar da kai gare Mu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba wa Annabi (ﷺ) labarin Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda shi ma ya faɗa cikin wata damuwa ta rashin samun ɗa magaji wanda zai maye gurbinsa wajen ilmantar da Banu Isra’ila da yi musu wa’azi kamar yadda yake yi, har girma ya riske shi. Bugu da ƙari kuma ga matarsa bakarara ce ba ta haihuwa, ita ma kuma ta manyanta. To amma ganin Maryam Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karrama ta da wasu karamomi na ban mamaki, (Dubi Suratu Ali Imrana, aya ta 37 zuwa ta 41), sai shi ma ya yi addu’a da cewa: “Ya Ubangijina, kada ka bar ni ni kaɗai ba tare da ka ba ni ɗa ba, alhalin kai ne Fiyayyen masu wanzuwa, don haka ka arzuta ni da samun ɗa wanda zai rayu bayana. Sai Allah ya bayyana cewa ya karɓi addu’arsa ya ba shi kyautar ɗa namiji, har ma ya raɗa masa suna Yahya. Bugu da ƙari kuma ya gyara masa matarsa bakarara ta koma mai haihuwa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin yadda wannan gida na Annabi Zakariyya ya kasance, watau shi da matarsa da ɗansa Yahya. Sun zamanto suna gaggawar aikata ayyukan alheri, tare da roƙon Allah da bauta masa, domin fatan samun lada a wajensa da kuma tsoron azabarsa, suna kuma masu ƙasƙantar da kai ga Allah (Mai tsarki da daukaka).

  91. وَٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلۡنَٰهَا وَٱبۡنَهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 21:91

    (Ka tuna) kuma wadda ta tsare matancinta, sai Muka yi busa a cikinta daga Ruhinmu, Muka kuma sanya ta ita da ɗanta aya ga talikai. A wannan ayar kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba wa Annabi (ﷺ) labarin Maryamu da ɗanta Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ita ma da irin karramawar da ya yi mata yayin da ta kame kanta tana ta bautar Allah, sai ya aiko Mala’ika Jibrilu ya yi mata busa ta ɗauki cikin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), [Kamar yadda ya bayyana cikakken labarin a cikin Suratu Maryam daga aya ta 16 zuwa ta 33]. Sai kuma ya bayyana cewa Maryamu da ɗanta Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun zamanto wata alama ce ga mutane wadda take tabbatar da cikakkiyar Ƙudirar Allah (Mai tsarki da daukaka) da nuna cewa babu abin da zai gagare shi, don haka ya halicci Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba tare da uba ba.

  92. إِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُونِ

    Open ayah 21:92

    Lallai wannan addini naku guda ɗaya ne (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, to ku bauta min.

  93. وَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡۖ كُلٌّ إِلَيۡنَا رَٰجِعُونَ

    Open ayah 21:93

    Sannan sai suka rarraba al’amarinsu (na addini) a tsakaninsu; dukkaninsu dai masu komowa ne zuwa gare Mu.

  94. فَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا كُفۡرَانَ لِسَعۡيِهِۦ وَإِنَّا لَهُۥ كَٰتِبُونَ

    Open ayah 21:94

    To duk wanda ya aikata kyawawan ayyuka alhali kuwa shi mumini ne, to babu musantawa ga aikinsa, lallai kuma Mu Masu rubuta masa shi ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, labarun da aka bayar na wasu daga cikin annabawan Allah, bayani ne da ya danganci abu guda, shi ne addinin Allah na Tauhidi, watau kaɗaita Allah da bauta, shi ne kuma Musulunci, addinin da ya zaɓar wa mutane baki ɗaya, ya kuma tabbatar musu da cewa shi ne Ubangijinsu Mahaliccinsu mai kula da duk al’amuransu. Don haka su tsantsanta bauta gare shi shi kaɗai kada su haɗa shi da komai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, duk da irin kiran da annabawa suka yi zuwa ga hanya guda ɗaya ta Tauhidi, to amma duk da haka sai da mutane suka rarrabu, wasu suna ɗayanta Allah wasu kuma suna haɗa shi da wasu abubuwa wajen bauta, watau wasu muminai wasu kuma suka kafirce. Allah kuma ya tabbatar musu da cewa gaba ɗayansu gare shi za su koma ranar alƙiyama ya yi wa kowa sakayya a kan ayyukansa masu kyau da munana. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wanda ya yi kyawawan ayyuka daga cikinsu yana mai imani da Allah da manzanninsa da ranar lahira, to wannan ba za a yi masa runton aikinsa mai kyau ba, za a yi masa kyakkyawar sakayya ne a kai, a kuma ninninka masa ladansa, ya same shi rubuce a cikin littafin ayyukansa ranar alƙiyama, ya yi farin ciki da shi.

  95. وَحَرَٰمٌ عَلَىٰ قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَآ أَنَّهُمۡ لَا يَرۡجِعُونَ

    Open ayah 21:95

    Kuma haramun ne ga (duk) wata al’umma da Muka hallaka cewa za su komo (duniya).

  96. حَتَّىٰٓ إِذَا فُتِحَتۡ يَأۡجُوجُ وَمَأۡجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٖ يَنسِلُونَ

    Open ayah 21:96

    Har sai lokacin da aka buɗe Yajuju da Majuju, su kuwa za su gangaro ne ta kowanne tudu.

  97. وَٱقۡتَرَبَ ٱلۡوَعۡدُ ٱلۡحَقُّ فَإِذَا هِيَ شَٰخِصَةٌ أَبۡصَٰرُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَٰوَيۡلَنَا قَدۡ كُنَّا فِي غَفۡلَةٖ مِّنۡ هَٰذَا بَلۡ كُنَّا ظَٰلِمِينَ

    Open ayah 21:97

    Kuma alƙawarin gaskiya ya gabato, sai ga shi idanuwan waɗanda suka kafirta sun yi zuru-zuru (suna cewa): “Kaiconmu! Haƙiƙa mun kasance cikin gafala game da wannan (ranar); a’a, kai mu dai mun kasance azzalumai ne!” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk mutanen alƙaryar da suka kafirce wa Allah har ya hallaka su, to ba ta yadda za a dawo da su duniya wai don a ba su damar su tuba su gyara kurakuransu, duk kuwa magiyar da za su yi wannan abu sam ba zai taɓa faruwa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa lokaci na nan tafe yayin da za a buɗe wa Yajuju da Majuju ƙofar fitowa daga cikin ganuwar da Zulƙarnaini ya gina don katange tsakaninsu da mutane. Idan kuwa an buɗe ta to za su fito su yi ta kwararowa daga kowane tudu cikin matuƙar sauri don su yaɗa ɓarna a bayan ƙasa. Bayanin Yajuju da Majuju ya gabata a Suratul Kahafi aya, ta 94 zuwa ta 98. An karɓo daga Annawwas ɗan Sam’an (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “....Sannan Allah zai aiko da Yajuju da Majuju (su kuwa za su gangaro ne ta kowanne tudu), sai na farkonsu su wuce ta gaban ƙoramar Ɗabariyya sai su shanye ruwanta, na ƙarshensu kuma su zo wucewa sai su riƙa cewa: “Da fa wurin nan akwai ruwa.” Sai a tsare Annabin Allah Isa da mabiyansa, har ya zamanto kan bijimin sa a wurin ɗayansu a ranar ya fi a ba shi dinari ɗari. Sai Allah ya aiko wa Yajuju da Majuju wasu tsutsotsi su baibaye wuyayensu sai kawai su wayi gari duk a mace kamar mutuwar rai guda. Sannan Annabin Allah Isa da sahabbansa su sauko ƙasa (daga kan duwatsun da suka fake) sai ya zamana babu daidai da wuri ɗani ɗaya a bayan ƙasa face mummunan warin Yajuju da Majuju ya cika shi. Sai Annabi Isa da sahabbansa su roƙi Allah sai Allah ya aiko da wasu tsuntsaye manya-manya kamar wuyan raƙuma su ɗauke gawawwakinsu su jefar da su inda Allah ya ga dama. Sannan sai Allah ya aiko da wani ruwan sama wanda ginin laka ko na gashin dabbobi ba zai iya tare shi ba sai ya wanke bayan ƙasa da shi ta yi haske kamar madubi...” [Muslim #2937]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, bayyanar Yajuju da Majuju alama ce ta kusantowar lokacin alƙiyama, sai abubuwan cikinta na ban tsoro da wahalhalunta su fara bayyana. A ranar ne tsoro zai cika zukatan kafirai, idanuwansu su fito su yi zuru-zuru, daga nan sai su fara kirawo wa kawunansu hallaka, suna nuna nadamar irin rayuwar shagala da gafala da suka yi a duniya, ba su yi wa wannan rana kowane irin tanadi ba, in ban da kafirci da ayyukan saɓon Allah.

  98. إِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمۡ لَهَا وَٰرِدُونَ

    Open ayah 21:98

    (Sai a ce da su): “Lallai ku da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, (duka) makamashin Jahannama ne, kuma ku masu shigar ta ne.”

  99. لَوۡ كَانَ هَٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةٗ مَّا وَرَدُوهَاۖ وَكُلّٞ فِيهَا خَٰلِدُونَ

    Open ayah 21:99

    Da waɗancan (gumakan) sun kasance alloli (na gaske) da ba su shiga cikinta ba, dukkaninsu kuwa madawwama ne a cikinta.

  100. لَهُمۡ فِيهَا زَفِيرٞ وَهُمۡ فِيهَا لَا يَسۡمَعُونَ 

    Open ayah 21:100

    Suna ta ƙaraji a cikinta, alhali kuwa su a cikinta ba sa jin (sautin komai). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai masu bautar wasu ba Allah ba cewa, da su da gumakan ko mutane da aljannun da suke bauta wa dukkansu za su zama makamashin wutar Jahannama a ranar alƙiyama, domin Allah zai tarkata su gaba ɗayansu ya watsa su a cikinta. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, da a ce abubuwan da mushirikan suka bauta wa ba Allah ba gaskiya ne, to da ba su shiga wutar tare da masu bautar su ba. To amma da yake na ƙarya ne dukkansu za su shiga wuta kuma su dawwama a cikinta har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa za su gamu da matsananciyar azaba a wutar Jahannama, wadda za su cika ta da ƙaraji da ihu ta yadda ba za su ji komai ba in ba wannan ife-ifen ba.

  101. إِنَّ ٱلَّذِينَ سَبَقَتۡ لَهُم مِّنَّا ٱلۡحُسۡنَىٰٓ أُوْلَٰٓئِكَ عَنۡهَا مُبۡعَدُونَ 

    Open ayah 21:101

    Lalle waɗanda kalmarmu mafi kyau (ta cewa su ‘yan Aljanna ne) ta riga ta tabbata gare su, waɗannan waɗanda ake nesantawa ne daga gare ta (wutar).

  102. لَا يَسۡمَعُونَ حَسِيسَهَاۖ وَهُمۡ فِي مَا ٱشۡتَهَتۡ أَنفُسُهُمۡ خَٰلِدُونَ 

    Open ayah 21:102

    Ba za su ji hargowarta ba, kuma su masu dawwama ne cikin abin da ransu yake so.

  103. لَا يَحۡزُنُهُمُ ٱلۡفَزَعُ ٱلۡأَكۡبَرُ وَتَتَلَقَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ هَٰذَا يَوۡمُكُمُ ٱلَّذِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ 

    Open ayah 21:103

    Babbar firgitar (wannan ranar) ba ta samun su, kuma mala’iku za su tare su, (suna cewa): “Wannan ita ce ranar taku wadda kuka zamanto ana yi muku alƙawarinta (a duniya).”

  104. يَوۡمَ نَطۡوِي ٱلسَّمَآءَ كَطَيِّ ٱلسِّجِلِّ لِلۡكُتُبِۚ كَمَا بَدَأۡنَآ أَوَّلَ خَلۡقٖ نُّعِيدُهُۥۚ وَعۡدًا عَلَيۡنَآۚ إِنَّا كُنَّا فَٰعِلِينَ 

    Open ayah 21:104

    (Ita ce) ranar da za Mu naɗe sama kamar naɗin marubuci ga takardu. Kamar yadda Muka ƙagi halitta da farko (haka) za Mu mai da ita. Wannan alƙawari ne da Muka ɗauka. Lallai Mun kasance Masu aikata (haka). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa bayinsa waɗanda ya yi wa kyakkyawan sakamako da gidan Aljanna saboda imaninsu da kyawawan ayyukansu, zai nesanta su daga shiga wutar Jahannama, ba ma za su jiyo ɗuriyarta ba, sannan suna cikin ni’imar gidan Aljanna suna more duk abin da suka yi sha’awa na kayan jin daɗi, kuma za su dawwama a cikinta har abada. Babu kuma wani abin tsoro da zai tashi hankalinsu, lokacin da wutar Jahannama za ta mamaye ‘ya’yanta. Mala’iku kuma za su riƙa taryar su da yi musu marhabun, suna jaddada musu cewa, wannan shi ne yinin da aka yi musu alƙawarin zuwansa tun suna duniya, sai su yi musu albishir da kyakkyawan sakamako da za su samu a wannan rana. Wasu daga cikin masana tafsiri, kamar Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) sun bayyana cewa waɗannan ayoyi sun sauka ne don mayar da martani ga mushirikai yayin da suka ce, idan har abubuwan da suke bauta wa ba Allah ba za a shigar da su wuta kamar yadda ya gabata a ayoyin baya, to ke nan har da mala’iku da Annabi Isa da mahaifiyarsa Maryamu da wasu suke bauta musu tare da Allah, su ma duk za su shiga wuta. Sai Allah ya bayyana musu cewa waɗannan duk nagari ne waɗanda suka yi imani da Allah kuma ba su amince da bautar da aka yi musu ba, don haka su ‘yan Aljanna ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta ranar lahira da cewa ita ce ranar da zai naɗe sama kamar yadda ake naɗe takarda da abin da take ɗauke da shi na rubutu. Kuma a ranar ne zai tattara ɗaukacin halittu a cikin yanayin da ya fara halittar su. Ya tabbatar da cewa wannan alƙawari ne da ya yi kuma sai ya cika shi babu makawa, domin ba ya saɓa duk wani alƙawari da ya yi.

  105. وَلَقَدۡ كَتَبۡنَا فِي ٱلزَّبُورِ مِنۢ بَعۡدِ ٱلذِّكۡرِ أَنَّ ٱلۡأَرۡضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ ٱلصَّٰلِحُونَ 

    Open ayah 21:105

    Kuma haƙiƙa Mun rubuta cikin saukakkun littattafai bayan (an rubuta a Lauhul-Mahfuzu) cewa, ita ƙasa bayina na gari ne za su gaje ta.

  106. إِنَّ فِي هَٰذَا لَبَلَٰغٗا لِّقَوۡمٍ عَٰبِدِينَ 

    Open ayah 21:106

    Lallai a cikin wannan (Alƙur’ani) akwai isar da saƙo ga mutane masu bauta.

  107. وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ 

    Open ayah 21:107

    Ba Mu aiko ka ba sai don rahama ga talikai.

  108. قُلۡ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ 

    Open ayah 21:108

    Ka ce (da su): “Abin da kawai ake yiwo min wahayinsa (shi ne) lallai abin bautar ku Allah ne Guda Ɗaya; to shin ko za ku miƙa wuya?”

  109. فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ ءَاذَنتُكُمۡ عَلَىٰ سَوَآءٖۖ وَإِنۡ أَدۡرِيٓ أَقَرِيبٌ أَم بَعِيدٞ مَّا تُوعَدُونَ 

    Open ayah 21:109

    To idan sun ba da baya sai ka ce (da su): “Na sanar da ku cewa ni da ku muna kan abu ɗaya ne (wato ta-ware). Kuma ni ban sani ba, shin abin da ake yi muku alƙawari da shi kusa yake ko kuwa nesa?

  110. إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡتُمُونَ 

    Open ayah 21:110

    “Lalle Shi (Allah) Yana sane da (abin da kuke) bayyanawa na magana Yana kuma sane da abin da kuke ɓoyewa.

  111. وَإِنۡ أَدۡرِي لَعَلَّهُۥ فِتۡنَةٞ لَّكُمۡ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ

    Open ayah 21:111

    “Kuma ban sani ba ko wataƙila shi (jinkirta azabtar da ku) fitina ne a gare ku da kuma jin daɗi zuwa wani ɗan lokaci.

  112. قَٰلَ رَبِّ ٱحۡكُم بِٱلۡحَقِّۗ وَرَبُّنَا ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلۡمُسۡتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ

    Open ayah 21:112

    (Annabi Muhammadu) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka yi hukunci (tsakanina da kafirai) da gaskiya. Ubangijinmu kuwa (Shi ne) Ar-Rahamanu Wanda ake neman taimakonsa a kan abin da kuke siffantawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya riga ya rubuta a cikin littattafan farko da ya saukar wa manzanninsa bayan ya rubuta a cikin Lauhul Mahfuzi cewa bayin Allah na ƙwarai masu biyayya ga Allah da Manzonsa, watau al’ummar Annabi (ﷺ) su ne za su gaje ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa, Alƙur’ani da ya saukar cike yake da wa’azi da tunatarwa kuma isar da saƙo ne ga mutane masu bauta wa Allah bisa ga abin da ya shar’anta musu. Su kaɗai ne kuma za su amfana da shi. Haka kuma bai aiko Manzon Allah (ﷺ) ba sai don ya zama rahama ga duniya baki ɗaya, saboda kwaɗayin ganin sun shiriya, domin su kuɓuta daga azabar Allah ta duniya da ta lahira. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu sun nemi Manzon Allah (ﷺ) ya yi mummunar addu’a ga mushirikai, sai ya ce: “Lallai ni ba a aiko ni don in zama mai yawan la’anta ba; an aiko ni ne kawai don in zamanto rahama.” [Muslim #2559]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ni rahama ce da aka yiwo kyauta da ita.” [As-Shari’ah #1000 da Almustadrak , juzu’i na 1, shafi na 91, Dubi Al-Albani, As-Silsilatus-Sahihah #490]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya sanar da mutane cewa shi fa ana yi masa wahayi ne daga Allah cewa abin bautarsu na gaskiya Ɗaya ne kawai ba shi da wani abokin tarayya, don haka su miƙa wuya gare shi su yi imani da shi su kuma yi masa ɗa’a. Sannan ya sanar da Manzonsa cewa, idan sun bijire masa sun ƙi karɓar abin da ya zo musu da shi na kaɗaita Allah da bauta masa shi kaɗai, to ya sanar da su cewa shi da su suna a kan wani al’amari iri ɗaya, na ta-ware, watau ba shi ba su. Sannan kuma koyaushe suna matsa masa lamba da tambaya a kan sai ya sanar da su yaushe ne azabar Allah za ta sauko musu, kamar yadda Allah yake tsoratar da su? Sai Allah ya umarce shi ya faɗa musu cewa shi ma bai san yaushe ne wannan alƙawarin zai sauka ba, to amma dai su sani cewa duk maganganun da suke yi a bayyane ko a ɓoye Allah yana sane da su babu abin da yake ɓuya a gare shi kuma dukkansu sai ya saka musu a kan ayyukansu ɗaya bayan ɗaya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Manzonsa da ya faɗa musu cewa shi kansa ba shi da wata masaniya game da jinkirta musu azaba da Allah ya yi. Mai yiwuwa ne kuma ya yi haka ne don ya zamo jarraba da talala a gare su, don kuma ya ba su damar jin daɗi na ɗan ƙanƙanin lokaci wanda Allah ya riga ya ƙaddara shi cikin iliminsa, domin su doge a kan kafirci da ɓata. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzon Allah (ﷺ) da ya yi addu’a, ya roƙi Allah Ubangijinsa da ya yi hukunci na gaskiya tsakaninsa da mutanensa waɗanda suka doge a kan kafircinsu, domin a wurin Allah Mai rahama ne kawai yake neman taimako bisa ga duk abin da suke faɗa kuma suke aikatawa na kafirci da ƙaryatawa.