الحج

Al-Hajj

The Pilgrimage · Surah 22 · Ayahs: 78 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ

    Open ayah 22:1

    Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku. Lalle girgizar (ranar) alƙiyama abu ne mai girma.

  2. يَوۡمَ تَرَوۡنَهَا تَذۡهَلُ كُلُّ مُرۡضِعَةٍ عَمَّآ أَرۡضَعَتۡ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمۡلٍ حَمۡلَهَا وَتَرَى ٱلنَّاسَ سُكَٰرَىٰ وَمَا هُم بِسُكَٰرَىٰ وَلَٰكِنَّ عَذَابَ ٱللَّهِ شَدِيدٞ

    Open ayah 22:2

    Ranar da za ku gan ta, (don tsananin firgita) kowacce mai shayarwa za ta manta da abin da ta shayar, kuma kowacce mai ciki ta zubar da cikinta, ka ga kuma mutane suna tangaɗi, alhali kuwa ba bugaggu ba ne, sai dai azabar Allah ce mai tsanani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da kiran mutane gaba ɗaya ya umarce su da su kiyaye dokokin Ubangijinsu, su aikata abin da ya wajabta musu su kuma guji abin da ya hana su. Ya kuma tsoratar da su da cewa, ranar alƙiyama cike take da manya-manyan abubuwan ban tsoro. Daga cikinsu akwai wata babbar girgizar ƙasa mai tayar da hankali. Don haka wajibi ne mutane su yi tanadin kyawawan ayyuka domin zuwan wannan rana da ba ta da makawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana yadda mutane za su ruɗe su ɗimauce sakamakon firgicin wannan ranar, domin kuwa saboda tsananin tsoro mace mai shayarwa za ta manta da jaririn da take shayarwa, sannan mai ciki za ta yi ɓarin cikinta, hankalin kowa duk ya ɓace su zamo kamar masu mayen giya, alhalin kuwa ba giya suka sha ba; tsananin azabar Allah ne kawai ya sanya su suka rasa hankulansu. An karɓo daga Imran ɗan Husain (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata rana a cikin ɗaya daga tafiye-tafiyen Manzon Allah (ﷺ) ya kula da cewa wasu sahabbansa sun yi wa sauran nisa sai ya ɗaga muryarsa ya karanta waɗannan ayoyi guda biyu. Yayin da sahabbansa suka ji haka sai suka ƙara sauri, suka kuma fahimci cewa yana so ne ya faɗa musu wata magana. Lokacin da suka taru a gabansa sai ya ce: “Shin ko kun san wacce rana ce waccan? (Watau wadda Allah yake magana a kanta cikin ayoyi biyu da ya karanta.)” Sai ya ce: “Ita ce ranar da Allah zai kirawo Adamu ya ce masa: “Ya kai Adamu, ka fito da waɗanda za a aika wuta.” Sai ya ce: “Ya Ubangiji, su wane ne ‘yan wuta?” Sai ya ce: “Daga cikin kowane dubu ka fitar da ɗari tara da tis’in da tara ka tura su zuwa wuta, ɗayan kuwa ka tura shi Aljanna.” Sahabbai suna jin wannan magana sai duk suka ruɗe ba wanda aka gan shi ya yi dariya. Da Annabi (ﷺ) ya ga haka sai ya ce: “Ku yi aiki, kuma albishirinku! Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, a tare da ku akwai wasu halittu guda biyu, a duk inda suke sai sun fi komai yawa, su ne Yajuju da Majuju da waɗanda suka hallaka daga cikin ‘ya’yan Adamu da kuma ‘ya’yan Iblis.” Da jin haka sai hankalin sahabbai ya kwanta....” [Ahmad #19901 da Tirmizi #3169].

  3. وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيۡطَٰنٖ مَّرِيدٖ

    Open ayah 22:3

    Daga mutane kuma akwai wanda yake jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ba, kuma yake bin kowanne shaiɗani mai tsaurin kai.

  4. كُتِبَ عَلَيۡهِ أَنَّهُۥ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُۥ يُضِلُّهُۥ وَيَهۡدِيهِ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

    Open ayah 22:4

    An ƙaddara masa (wato Shaiɗan) cewa duk wanda ya rungume shi to haƙiƙa zai ɓatar da shi kuma ya ja shi zuwa ga azaba ta (wutar) Sa’ira. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana mayar da martani ne ga waɗanda suke musanta tashi bayan mutuwa da zuwan ranar alƙiyama, da cewa a cikin mutane akwai wanda yake jayayya game da Ƙudurar Allah ba tare da wani ilimi ko wata hujja ba, har yana ganin wai Allah ba zai iya tayar da matattu bayan mutuwarsu ba. Ba wanda yake koyi da shi wajen riƙo da wannan mummunar aƙida in ban da duk wani shaiɗani mai tsaurin kai mai bijire wa Allah Ubangijinsa daga shaiɗanun aljannu ko na mutane shuwagabannin ɓata. Su waɗannan an riga an rubuta musu cewa duk wanda ya bi ɗaya daga cikinsu ya gaskata abin da yake saƙa masa a zuciya, to tabbas zai ɓatar da shi ne daga kan hanyar gaskiya, ya kuma ja shi zuwa ga azabar wuta, saboda kafirci da saɓon Allah da yake jan sa zuwa gare shi.

  5. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّنَ ٱلۡبَعۡثِ فَإِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ مِن مُّضۡغَةٖ مُّخَلَّقَةٖ وَغَيۡرِ مُخَلَّقَةٖ لِّنُبَيِّنَ لَكُمۡۚ وَنُقِرُّ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ مَا نَشَآءُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ نُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡلَا يَعۡلَمَ مِنۢ بَعۡدِ عِلۡمٖ شَيۡـٔٗاۚ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ هَامِدَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡ وَأَنۢبَتَتۡ مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ

    Open ayah 22:5

    Ya ku mutane, idan kun zamanto cikin kokwanton tashi (bayan mutuwa), to lalle Mu Muka halicce ku daga ƙasa, sannan daga maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan daga tsoka, mai cikakkiyar halitta da kuma wadda ba cikakkiya ba, don Mu bayyana muku (Ikonmu). Kuma Muna tabbatar da abin da Muka ga dama a cikin mahaifa har zuwa wani lokaci ƙayyadajje, sannan kuma Mu fito da ku kuna jarirai, sannan kuma don ku kai cikar ƙarfinku; daga cikinku akwai wanda za a karɓi ransa, akwai kuma wanda za a bari har zuwa mafi ƙasƙantar rayuwa don ya kai ga halin da ba zai san komai ba bayan kuwa da can ya sani. Za ka kuma ga ƙasa a ƙeƙashe, sannan idan Muka saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura kuma ta fitar da kowanne irin tsiro mai ƙayatarwa.

  6. ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّهُۥ يُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَأَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 22:6

    Wannan (kuwa) saboda lalle Allah Shi ne gaskiya, kuma lalle Shi ne Yake raya matattu, kuma lalle Mai iko ne a kan komai.

  7. وَأَنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٞ لَّا رَيۡبَ فِيهَا وَأَنَّ ٱللَّهَ يَبۡعَثُ مَن فِي ٱلۡقُبُورِ

    Open ayah 22:7

    Kuma lalle alƙiyama za ta zo babu kokwanto game da ita, kuma lalle Allah zai tashi waɗanda suke cikin ƙaburbura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da ƙarfafan dalilai biyu game da tashin matattu da aukuwar ranar alƙiyama. Dalili na farko shi ne halittar ɗan’adam bayan a da babu shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ne ya fari halittar Annabi Adamu uban mutane daga ƙasa, sannan ya halicci zurriyyarsa daga ruwan maniyyin namiji da na mace bayan ya shiga mahaifa. Daga maniyyi kuma ya koma daskararren jini, sannan ya zama tsokar nama wadda ba ta fi lomar mutum ba, sannan ta rikiɗa ta zama daidaitacciyar halitta ta mutum a cikin wannan mahaifar har zuwa lokacin haihuwa. Daga nan sai a haifi mutum mai rai, ko kuma wannan tsokar ta zama wata halitta wadda ba cikakken mutum ba, daga bisani a yi ɓarinsa. Allah ya bayyana cewa yana yin wannan ne duka domin ya ankarar da mutane cikakken ikonsa na halittar ɗan’adam zango bayan zango. Kuma shi yake da ikon raya jariran da ya ga damar raya su a cikin mahaifar iyayensu har zuwa lokacin haihuwarsu, watau cikin wata tara, sannan ya fitar da su ‘yan ƙanana daga cikin cikkunan iyayensu mata. Su rayu bayan haka har ƙarfinsu ya kawo, hankalinsu kuma ya cika. To daga cikinsu akwai wanda zai mutu tun gabanin ya kai wannan lokacin, akwai kuma wanda zai yi tsawon rai har ya tsufa tukuf ƙarfinsa ya ƙare gaba ɗaya, hankalinsa ya yi rauni har ma wani lokaci ya fi yaro ƙarami taɓarɓarewa, ya manta da duk abin da a da ya sani. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle ana haɗa halittar ɗayanku a cikin cikin mahaifiyarsa, yana maniyyi kwana arba’in, sannan ya zama gudan jini kamar haka, sannan ya zama gudar tsoka kamar haka, sannan a aiko masa da mala’aika, a umarce shi da abubuwa guda huɗu: Ya rubuta aikinsa da arzikinsa da ajalinsa; ɗan wuta ne ko ɗan Aljanna. Sannan a umarce shi ya busa masa rai.” [Bukhari #3205 da Muslim #2643]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana addu’a yana cewa: “Ya Allah, ina roƙon ka ka tsare ni daga rowa da kasala da tsufa da zama tsoho takwarkwasasshe da azabar ƙabari da fitinar Dujal da fitinar rayuwa da ta mutuwa.” [Bukhari #4707]. Dalili na biyu shi ne raya ƙasa da ruwan sama bayan ƙeƙashewarta. Allah ya bayyana cewa za a ga ƙasa ta bushe babu wani tsiro a kanta, amma da zarar ruwan sama ya sauka a kanta sai a ga ta girgiza ta fitar da tsirranta, ta kumburo saboda tsirran da suka fito daga cikinta, ta fitar da kowane irin tsiro mai ban sha’awa da ƙayatarwa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗannan ƙarfafan dalilan biyu suna nuna abubuwa biyar: <b>Abu na farko </b>, Allah shi ne abin bauta na gaskiya wanda babu shakka a cikin samuwarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai. <b>Na biyu </b>, shi ne mai tayar da matattu bayan mutuwarsu kamar yadda ya halicce su a karon farko ya kuma raya ƙasa da ruwan sama bayan bushewarta. <b>Na uku </b>, shi mai iko ne a kan komai, babu abin da yake gagarar sa. <b>Na huɗu </b>, tabbatar da zuwan ranar alƙiyama wadda babu wani kokwanto a kan zuwanta. <b>Na biyar </b>, lalle Allah zai tayar da waɗanda suke cikin ƙaburbura domin yi musu hisabi a kan ayyukansu masu kyau da munana.

  8. وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ

    Open ayah 22:8

    Daga mutane kuma akwai wanda yake jayayya game da (al’amarin) Allah ba tare da ilimi ba ko shiriya ko kuma wani littafi mai haske.

  9. ثَانِيَ عِطۡفِهِۦ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۖ لَهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞۖ وَنُذِيقُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

    Open ayah 22:9

    Yana juyar da kansa don ya ɓatar da (mutane) daga hanyar Allah; yana da wulaƙanci a duniya; kuma ranar alƙiyama Mu ɗanɗana masa azabar ƙuna.

  10. ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ يَدَاكَ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ 

    Open ayah 22:10

    (Za a ce da shi): “Wannan (kuwa) saboda abin da hannayenka suka aikata ne, kuma lalle Allah ba Mai zaluntar bayi ba ne.” Bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci waɗanda suka kauce hanyar shiriya saboda makauniyar biyayya ga wasu ɓatattu a aya ta 3, sai kuma a nan ya ambaci waɗanda su ne shugabannin ɓatan, da cewa, a cikin kafirai da akwai waɗanda suke yin jayayya game da Kaɗaitakar Allah ba tare da wani ilimi ba ko wata ingantacciyar hujja, ba kuma tare da bin wata shiriya ba da za ta shiryar da shi zuwa ga gaskiya, ba kuma tare da riƙo da wani littafi mai haske wanda Allah ya saukar domin shiriyarsu ba. Allah ya bayyana mummunar ɗabi’ar wannan kafiri mai yawan jayayya, wanda yake karkatar da kansa domin girman kai da ƙoƙarin kautar da mutane daga yin imani da shiga addinin Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk mai irin wannan mummunan hali yana tare da ƙasƙanci da wulaƙanci a nan duniya saboda Allah zai kunyata shi tun kafin ya je lahira. Sannan bayan ya je lahira Allah ya ɗanɗana masa azabar wuta mai tsananin ƙuna. Kuma a sanar da shi cewa wannan azabar da yake ɗanɗana saboda abin da ya aikata ne a duniya kuma Allah ba azzalumin kowa ba ne, domin ba wanda zai azabtar sai mai laifi.

  11. وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَعۡبُدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ حَرۡفٖۖ فَإِنۡ أَصَابَهُۥ خَيۡرٌ ٱطۡمَأَنَّ بِهِۦۖ وَإِنۡ أَصَابَتۡهُ فِتۡنَةٌ ٱنقَلَبَ عَلَىٰ وَجۡهِهِۦ خَسِرَ ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةَۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡخُسۡرَانُ ٱلۡمُبِينُ

    Open ayah 22:11

    Daga mutane kuma akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gaɓa; to idan alheri ya same shi sai ya nutsu da shi, idan kuwa wata masifa ta same shi sai ya juya a kan fuskarsa; to ya yi hasarar duniya da lahira. Wannan (kuwa) ita ce hasara bayyananniya.

  12. يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُۥ وَمَا لَا يَنفَعُهُۥۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ

    Open ayah 22:12

    Yana bauta wa wanin Allah, abin da ba zai cuce shi ba kuma ba zai amfane shi ba. Wannan kuwa shi ne ɓata mai nisa.

  13. يَدۡعُواْ لَمَن ضَرُّهُۥٓ أَقۡرَبُ مِن نَّفۡعِهِۦۚ لَبِئۡسَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَلَبِئۡسَ ٱلۡعَشِيرُ

    Open ayah 22:13

    Yana bauta wa abin da cutarsa ta fi kusa fiye da amfaninsa. Tabbas mataimaki ya munana, kuma tabbas aboki ya munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halayyar wasu mutane waɗanda imani bai ratsa zukatansu ba, da cewa, a cikin mutane akwai wanda ya rasa alƙibla guda ɗaya, ya zamanto yana bautar Allah ne rabi da rabi, watau a cikin shakku. Idan ya yi imani ya ga yana samun alheri kamar wadata da ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali, to sai ya ɗore a kan imaninsa da bautar Allah. Amma idan ya ga yana gamuwa ne da wata jarraba ta talauci ko rashin lafiya ko wani abu makamancin wannan, to sai ya riƙa ganin addininsa ne ya jawo masa haka. Don haka sai ya yi ridda ya koma kafirci. Allah ya bayyana cewa, tabbas wannan mutum ya yi asarar duniyarsa, domin kafircinsa ba zai ƙara masa wani abu a cikin rabonsa na duniya da aka riga aka rubuta masa ba, kuma ba zai yaye masa wata damuwar da yake ciki wadda Allah bai yi nufin yaye masa ita ba. Hakanan ya yi asarar lahirarsa, domin azabar Allah ce take jiran sa a can. Babu ko shakka wannan ita ce babbar asara a fili ƙarara. Allah ya ci gaba da bayanin halin wannan mutum bayan ya yi ridda ya kafirce masa, da cewa zai ci gaba da kiran wasu ababen bauta ba Allah ba waɗanda ba za su iya cutar da shi komai ba, ba kuma za su amfane shi da komai ba. Wannan shi ne ɓata mai nisa tsakaninsa da gaskiya, domin ya kauce wa bautar wanda zai amfane shi ya kama wanda ba zai yi masa amfani ba. Hasali ma cutarwarsa gare shi ta fi zama tabbas a kan amfaninsa, wanda babu shi ma kwata-kwata. Allah ya yi tir da wannan abin bauta ba Allah ba da sunan mataimaki ko aboki.

  14. إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ

    Open ayah 22:14

    Lalle Allah Yana shigar da waɗanda suka yi imani kuma suka yi aiki na gari gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Lalle Allah Yana aikata abin da Ya ga dama. Bayan Allah ya ambaci halin kafiri da mummunan sakamakonsa, sai kuma ya bayyana halin muminai da sakamakonsu, inda yake cewa, zai shigar da waɗanda suka yi imani kuma suka yi kyawawan ayyuka gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Ya tabbatar da cewa yana aikata abin da ya yi nufi, don haka yana jin ƙan duk wanda ya nufi jin ƙansa, ya kuma azabtar da wanda ya nufi yi masa azaba, babu wanda ya isa ya hana shi.

  15. مَن كَانَ يَظُنُّ أَن لَّن يَنصُرَهُ ٱللَّهُ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ فَلۡيَمۡدُدۡ بِسَبَبٍ إِلَى ٱلسَّمَآءِ ثُمَّ لۡيَقۡطَعۡ فَلۡيَنظُرۡ هَلۡ يُذۡهِبَنَّ كَيۡدُهُۥ مَا يَغِيظُ

    Open ayah 22:15

    Wanda ya zamanto yana tsammanin cewa Allah ba zai taimake shi ba, (wato Annabinsa) a duniya da lahira, to sai ya hau sama da igiya, sannan ya yanke ta, ya duba shin wannan mugun tanadi nasa zai kawar da abin da yake cike da haushinsa?

  16. وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖ وَأَنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يُرِيدُ

    Open ayah 22:16

    Kamar haka kuwa Muka saukar da shi (Alƙur’ani) ayoyi mabayyana, kuma lalle Allah Yana shiryar da wanda Yake nufin (shiryar da shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk wani mai tsammanin Allah ba zai taimaki Manzonsa (ﷺ) da addinin da ya zo da shi ba a duniya da lahira, yake kuma jiran ya ga addinin ya rushe, to ya sani wannan nasarar daga sama wurin Allah take sauka, don haka idan yana jin haushi to sai ya samu igiya ya kama ya hau sama sannan ya yanke igiyar ya faɗo ƙasa ya gani wannan zai kawar masa haushinsa? Allah dai zai ci gaba da taimakon Manzonsa da addininsa ko mutum yana so ko ba ya so. Sannan Allah ya bayyana cewa kamar yadda ya bayyana hujjoji a kan tashin matattu da kuma tashin alƙiyama, to haka ya saukar wa Annabi Muhammadu (ﷺ) Alƙur’ani wanda ya ƙunshi ayoyi bayyanannu, kuma yana shiryar da wanda ya ga damar shiriyarsa ya nuna masa gaskiya ya kuma ba shi ikon bin ta.

  17. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلصَّٰبِـِٔينَ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلۡمَجُوسَ وَٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡصِلُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

    Open ayah 22:17

    Lalle waɗanda suka yi imani da waɗanda suka zama Yahudawa da Sabi\'awa da waɗanda suka zama Majusawa da kuma waɗanda suka yi shirka, lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alƙiyama. Lalle Allah Mai ganin kowane abu ne. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle waɗanda suka yi imani daga al’ummar Musulmi da kuma Yahudawa da Sabi’awa da Nasara da Majusawa masu bautar wuta da masu shirka, duk gaba ɗayansu Allah zai yi musu hukunci a ranar alƙiyama ya shigar da muminai gidan Aljanna ya kuma shigar da sauran wuta. Lalle Allah yana ganin duk ayyukan bayinsa da maganganunsu, babu abin da yake ɓuya daga gare shi kuma zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa. (Dubi Suratul Baƙara, aya ta 62).

  18. أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَسۡجُدُۤ لَهُۥۤ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ وَٱلنُّجُومُ وَٱلۡجِبَالُ وَٱلشَّجَرُ وَٱلدَّوَآبُّ وَكَثِيرٞ مِّنَ ٱلنَّاسِۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيۡهِ ٱلۡعَذَابُۗ وَمَن يُهِنِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن مُّكۡرِمٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ۩

    Open ayah 22:18

    Shin ba ka san cewa duk abin da yake cikin sammai da ƙasa suna yin sujjada ne ga Allah ba, (haka ma) rana da wata da taurari da duwatsu da bishiyoyi da dabbobi da kuma mutane masu yawa; da yawa kuma azaba ta tabbata a kansu? Duk kuwa wanda Allah Ya wulaƙanta, to ba shi da wani mai girmama shi. Lalle Allah Yana aikata abin da Ya ga dama. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Manzonsa cewa ɗaukacin mala’ikun da suke cikin sammai da muminai mutane da aljannu da suke bayan ƙasa suna yi masa sujjada domin ɗa’a a gare shi. Hakanan rana da wata da taurari a sama da duwatsu da bishiyoyi da dabbobi a ƙasa gaba ɗayansu suna yi masa sujjadar miƙa wuya gare shi. Haka kuma mutane masu yawa a bayan ƙasa suna yi masa sujjadar ɗa’a, da yawa kuma sun ƙi su yi masa sujjada, don haka azabarsa ta tabbata a kansu saboda kafircinsu. Duk kuma wanda Allah ya hukunta masa ƙasƙanci da wulaƙanci saboda kafircinsa to babu wanda ya isa ya girmama shi. Allah kuma yana aikata abin da ya ga dama ne babu mai tilasta shi. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya tambaye ni ya ce: “Shin ka san inda wannan ranar take tafiya?” Sai na ce: “Allah da Manzonsa ne suka fi sani.” Sai ya ce: “To lalle tana tafiya ne ta yi sujjada a ƙarƙashin Al’arshi, sannan ta nemi izinin sake fitowa. To lokaci ya kusa zuwa da za a ce mata: ‘Ki koma ta inda kika zo’.” [Bukhari #3199 da Muslim #159].

  19. ۞هَٰذَانِ خَصۡمَانِ ٱخۡتَصَمُواْ فِي رَبِّهِمۡۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قُطِّعَتۡ لَهُمۡ ثِيَابٞ مِّن نَّارٖ يُصَبُّ مِن فَوۡقِ رُءُوسِهِمُ ٱلۡحَمِيمُ

    Open ayah 22:19

    Biyu ɗin nan (muminai da kafirai) masu jayayya ne da suka yi jayayya game da Ubangijinsu (wato addininsu); waɗanda suka kafirce sai aka ɗinka musu tufafi na wuta, kuma ana zuba musu tafasasshen ruwa ta saman kawunansu.

  20. يُصۡهَرُ بِهِۦ مَا فِي بُطُونِهِمۡ وَٱلۡجُلُودُ 

    Open ayah 22:20

    Ana narka abin da yake cikinsu da shi (tafasasshen ruwan) da kuma fatu.

  21. وَلَهُم مَّقَٰمِعُ مِنۡ حَدِيدٖ

    Open ayah 22:21

    Suna kuma (shan duka) da gudumomi na baƙin ƙarfe.

  22. كُلَّمَآ أَرَادُوٓاْ أَن يَخۡرُجُواْ مِنۡهَا مِنۡ غَمٍّ أُعِيدُواْ فِيهَا وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

    Open ayah 22:22

    Duk sanda suka yi nufin fita daga cikinta (wutar) saboda baƙin ciki sai a sake mayar da su cikinta, (a ce da su): “Ku ɗanɗani azabar gobara.”

  23. إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَلُؤۡلُؤٗاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِيهَا حَرِيرٞ

    Open ayah 22:23

    Lalle Allah Yana shigar da waɗanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, ana yi musu ado a cikinsu da awarwaro na zinare da kuma lu’ulu’u; tufafinsu kuwa a cikinsu alharini ne.

  24. وَهُدُوٓاْ إِلَى ٱلطَّيِّبِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَهُدُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡحَمِيدِ

    Open ayah 22:24

    Kuma an shiryar da su zuwa ga magana mai daɗi (a duniya, wato Kalmar Shahada), an kuma shiryar da su zuwa ga tafarkin (Allah) Sha-yabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana makomar ƙungiyoyi guda biyu, watau muminai da suka yi aiki da dokokinsa, da kuma waɗanda suka kafirce masa suka bijire wa manzanninsa. Waɗannan ƙungiyoyi biyu suna jayayya ne game da Ubangiji, ƙungiyar kafirai za su gamu da matsananciyar azaba domin kuwa za a ɗinka musu tufafi na wuta waɗanda za su rufe jikinsu ta ko’ina, a kuma riƙa kwararo musu da tafasasshen ruwa ta saman kawunansu, wanda da shi ne za a riƙa narka kayan cikinsu, da fatunsu ya sa duk su zagwanye. Bugu da ƙari kuma mala’iku za su yi ta dukan su a kawunansu da gudumomi na baƙin ƙarfe. Duk kuma sa’adda suka yi yunƙurin fitowa daga cikin wannan matsananciyar azaba sai a mayar da su cikinta, a ce da su: “Ku ɗanɗani azabar gobara.” An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda), ya kasance yana rantsuwa da Allah cewa wannan aya ta 19 ta sauka ne game da Hamza da abokansa su biyu, da Utba da abokansa su biyu, ranar da suka yi fito-na-fito a yaƙin Badar. [Bukhari #3966 da Muslim #3033]. An karɓo daga Aliyyu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ni ne farkon wanda zai gurfana a gaban Allah mai rahama domin husuma a ranar alƙiyama.” Ƙaisu ya ce: A kansu wannan ayar ta sauka: (Waɗannan biyun su ne suka yi jayayya game da Ubangijinsu). Ya ce: “Su ne waɗanda suka yi fito-na-fito a ranar yaƙin Badar, watau su ne: Aliyyu da Hamza da Ubaida (ɓangaren muminai) da Shaibatu ɗan Rabi’a da Utbatu ɗan Rabi’a da Alwalidu ɗan Utbatu (ɓangaren kafirai).” [Bukhari #4744]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci sakamakon ƙungiyar muminai, da cewa waɗannan su ne waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki na ƙwarai, to su Allah zai shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Ana kuma yi musu ado da awarwaro na zinare da lu’u-lu’u, sannan kuma tufafinsu na sawa na alhariri ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa tun suna duniya ya shiryar da su game da faɗar daddaɗar magana, ita ce Kalmar Shahada da kabbara da kirari ga Allah, kuma ya shiryar da su zuwa ga hanyar Musulunci abin yabo.

  25. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ ٱلَّذِي جَعَلۡنَٰهُ لِلنَّاسِ سَوَآءً ٱلۡعَٰكِفُ فِيهِ وَٱلۡبَادِۚ وَمَن يُرِدۡ فِيهِ بِإِلۡحَادِۭ بِظُلۡمٖ نُّذِقۡهُ مِنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ

    Open ayah 22:25

    Lalle waɗanda suka kafirta suke kuma toshe hanyar Allah da kuma Masallacin Harami wanda Muka sanya shi bai-ɗaya ga mutane, mazaunin cikinsa da kuma mai zuwa (daga waje). Wanda kuwa ya nufe shi da wata fanɗara da zalunci to za Mu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan halin da mushirikai suke ciki na kafirce wa Allah da hana mutane karɓar addinin Musulunci, da kuma kange su daga shiga Masallaci mai alfarma na Makka, kamar yadda suka hana Manzon Allah da sahabbansa yayin da suka je don yin Umra a shekarar Hudaibiyya, watau shekara ta shida bayan hijira. Waɗannan kafirai za su gamu da azabar Allah mai tsanani idan har suka mutu ba su tuba ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya sanya wannan Masallacin na Harami ya zamanto alƙibla ce ga dukkan Musulmi lokacin sallolinsu a duk inda suke, kuma wuri ne na yin aikin Hajji da Umara. Kuma mazaunin garin Makka da baƙo wanda ya zo daga wajenta duka ɗaya suke a cikin wannan Haramin, babu wanda zai nuna ya fi wani haƙƙi a cikinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kashedi ga duk wani wanda zuciyarsa za ta riya masa yin wani aikin assha a cikinsa na zalunci ko na saɓon Allah, to lalle Allah zai ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi.

  26. وَإِذۡ بَوَّأۡنَا لِإِبۡرَٰهِيمَ مَكَانَ ٱلۡبَيۡتِ أَن لَّا تُشۡرِكۡ بِي شَيۡـٔٗا وَطَهِّرۡ بَيۡتِيَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلۡقَآئِمِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ

    Open ayah 22:26

    Kuma (ka tuna) lokacin da Muka nuna wa Ibrahimu gurbin Ɗakin (Ka’aba, Muka ce da shi): “Kada ka haɗa komai da Ni (wajen bauta), kuma ka tsarkake Ɗakina ga masu ɗawafi da masu zama a cikinsa da kuma masu ruku’i masu sujjada.

  27. وَأَذِّن فِي ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَجِّ يَأۡتُوكَ رِجَالٗا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٖ يَأۡتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٖ

    Open ayah 22:27

    Kuma ka yi shela cikin mutane saboda yin Hajji, za su zo maka matafiya a ƙasa da kuma kan kowanne raƙumi mai ɗamammen ciki, za su zo maka daga kowane lungu mai nisa.

  28. لِّيَشۡهَدُواْ مَنَٰفِعَ لَهُمۡ وَيَذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡلُومَٰتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلۡأَنۡعَٰمِۖ فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡبَآئِسَ ٱلۡفَقِيرَ

    Open ayah 22:28

    Don su halarci amfanin da za su samu, kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sanannu a kan abin da Muka arzuta su da shi na dabbobin ni’ima (watau raƙuma da tumaki da awakai da shanu); sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galaɓaitaccen matalauci.

  29. ثُمَّ لۡيَقۡضُواْ تَفَثَهُمۡ وَلۡيُوفُواْ نُذُورَهُمۡ وَلۡيَطَّوَّفُواْ بِٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ

    Open ayah 22:29

    Sannan su gusar da ƙazantarsu (kamar yin aski da yanke farce), kuma su cika alƙawarinsu (na yin hadaya da layya), kuma su yi ɗawafi a \'yantaccen Ɗaki (na Ka’aba). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman darajar Ɗakinsa mai alfarma da kuma darajar wanda ya gina shi, watau Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya umarci Annabi (ﷺ) ya tuna lokacin da ya nuna wa Annabi Ibrahimu gurbin Ɗakin Ka’aba da iyakokinsa wanda a da bai taɓa saninsa ba. Ya kuma yi masa wahayi da cewa kada ya yi shirka wajen bautar Allah, ya bauta wa Allah shi kaɗai, ya kuma tsarkake Ɗakinsa daga dukkan najasa ta zahiri da ta baɗini domin amfanin masu ɗawafi da masallata a cikinsa. Ya kuma umarci Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya yi shela a cikin mutane ya kira su zuwa ga wannan Ɗakin domin aikin Hajji, Allah ya tabbatar masa da cewa mutane za su riƙa yin tururuwa zuwa gare shi, wasu a ƙafa wasu haye a kan ramammun raƙuma saboda wahalar tafiya, za su ɗauko su da guzirinsu daga kowace hanya mai nisa. Za su zo domin su halarci abubuwa masu yawa da za su amfane su, kamar samun gafarar Allah da gwaggwaɓan lada da haɗin kai tsakanin muminai da makamantansu. Kuma domin su ambaci sunan Allah lokacin da za su yanka dabbobin hadayarsu, ta raƙuma da shanu da tumaki a cikin kwanakin yanka na aikin Hajji, watau ranar goma ga watan Zulhijja da kwana uku bayansa. Duk wannan domin su nuna godiyarsu ga Allah da ya arzuta su da waɗannan dabbobi. Allah kuma ya umarce su da su ci daga naman hadayarsu su kuma ciyar da mabuƙata da matalauta daga ciki. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wasu kwanaki da aikin ƙwarai ya fi falala a cikinsu kamar waɗannan kwanakin (goma na farkon Zulhijja).” Sahabbai suka ce: “Har ma da jihadi?” Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Har ma da jihadi, sai dai mutumin da ya fita yaƙi da ransa da dukiyarsa bai kuma dawo da komai ba.” [Bukhari #969 da Ahmad #1968]. An karɓo daga Abu Ƙatada (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) game da azumin ranar Arfa sai ya ce: “Ina tsammanin zai kankare zunubin shekara mai wucewa da mai zuwa.” [Muslim #1162]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mahajjata da su kammala ayyukansu na Hajji su yi aski da yanke farce da kawar da duk wata ƙazanta daga jikinsu su cire haraminsu. Ya kuma umarce su da su cika alƙawarin da suka ɗaukar wa kansu na bakance da yin Hajji ko Umara ko hadaya, su kuma yi ɗawafin a Ɗakin da Allah ya ‘yanta shi daga duk wani azzalumi tun lokacin da aka gina shi.

  30. ذَٰلِكَۖ وَمَن يُعَظِّمۡ حُرُمَٰتِ ٱللَّهِ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّهُۥ عِندَ رَبِّهِۦۗ وَأُحِلَّتۡ لَكُمُ ٱلۡأَنۡعَٰمُ إِلَّا مَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱجۡتَنِبُواْ ٱلرِّجۡسَ مِنَ ٱلۡأَوۡثَٰنِ وَٱجۡتَنِبُواْ قَوۡلَ ٱلزُّورِ 

    Open ayah 22:30

    Wannan (umarni da aka yi muku) kuwa, duk wanda ya girmama abubuwan da Allah Ya hana (a Hajji) to shi ya fi masa alheri a wurin Ubangijinsa. An kuma halatta muku dabbobin ni’ima, in ban da waɗanda aka karanta muku (haramcinsu). To sai ku nisanci ƙazanta ta bauta wa gumaka, kuma ku nisanci faɗar shaidar zur.

  31. حُنَفَآءَ لِلَّهِ غَيۡرَ مُشۡرِكِينَ بِهِۦۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَكَأَنَّمَا خَرَّ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَتَخۡطَفُهُ ٱلطَّيۡرُ أَوۡ تَهۡوِي بِهِ ٱلرِّيحُ فِي مَكَانٖ سَحِيقٖ

    Open ayah 22:31

    Kuna masu kauce wa ɓarna don Allah, ba masu haɗa shi da wasu ba. Duk wanda kuwa ya haɗa Allah da wani, to kamar ya faɗo ne daga sama, sai tsuntsaye suka fauce shi, (suka yagalgala shi) ko kuma iska ta jefa shi cikin wani wuri mai zurfi (ta rugurguza shi).

  32. ذَٰلِكَۖ وَمَن يُعَظِّمۡ شَعَٰٓئِرَ ٱللَّهِ فَإِنَّهَا مِن تَقۡوَى ٱلۡقُلُوبِ

    Open ayah 22:32

    Wannan kuwa (haka yake), duk wanda ya girmama wuraren ibadar (Hajji) na Allah to lalle wannan yana daga taƙawar zukata.

  33. لَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ مَحِلُّهَآ إِلَى ٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ

    Open ayah 22:33

    Kuna da wata moriya game da su (dabbobin) har zuwa wani lokaci ƙayyadajje (shi ne lokacin yanka su), sannan kuma wurin yankansu zuwa ga Ɗaki ne \'yantacce (wato Harami baki ɗayansa). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa hukunce-hukunce na aikin Hajji da suka gabata abubuwa ne da ya yi umarni da su ya kuma wajabta su ga muminai, don haka lalle su girmama abin da ya wajabta musu. Allah ya bayyana cewa duk wanda ya nisanci abin da aka hana mai ihrami aikatawa domin girmama iyakokin Allah da kauce wa keta su da kuma kiyaye alfarmar abubuwa masu alfarma, to wannan shi ya fi musa alheri a wajen Ubangijinsa duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar wa da mutane cewa ya halatta musu cin naman dabbobin ni’ima, watau raƙuma da shanu da tumaki, babu wani nau’i nasu da aka haramta cin namansu ko amfani da su, kamar yadda mushirikan Larabawa suka riƙa yi a Jahiliyya. Idan ma akwai, to sai fa abin da Allah ya bayyana haramcinsa a wasu ayoyin Alƙur’ani, kamar mushe da jini mai kwarara da makamantansu, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Ma’ida, aya ta 3. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni ga mutane da su nisanci duk wata ƙazanta ta gumaka da duk wata maganar ƙarya ga Allah ko ga wani daga cikin bayinsa. An karɓo daga Abu Bakra (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Shin ba na faɗa muku mafi girman zunubi ba?” Sahabbai suka ce: “E, a faɗa mana ya Ma’aikin Allah.” Sai ya ce: “Shirka da Allah da saɓa wa iyaye.” Yana kishingiɗe sai ya tashi zaune ya ce: “Ku saurara, da maganar ƙarya, ku saurara, da shaidar zur.” Annabi ya yi ta maimaita wannan maganar har sai da sahabbai suka ce ina ma ya yi shiru. [Bukhari #2654 da Muslim #87]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su tsarkake ibadarsu gare shi shi kaɗai su kauce wa duk wani addini ba Musulunci ba, kada kuma su haɗa komai da shi wajen bauta. Ya kamanta duk wanda ya haɗa Allah da wani cikin bauta, da cewa ya yi kama da wanda ya faɗo daga sama, ko dai tsuntsaye su fauce shi su yagalgala namansa da ƙasusuwansa, ko kuma iska ta jefa shi cikin wani rami mai zurfi inda zai kakkarye ya hallaka. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk waɗannan abubuwa da ya yi umarni da su na kaɗaita shi da tsantsanta bauta gare shi da nisantar gumaka da maganar ƙarya, duk suna cikin dokokin da ya wajabta wa Musulmi su kiyaye su. Kma duk wanda ya girmama alamomin addini, kamar hadaya da sauran ayyukan Hajji, to wannan alama ce ta taƙawar zukata. Ya bayyana cewa cikin hadayar da mahajjata suke yankawa yayin gama aikin hajjinsu akwai wasu abubuwa masu amfani gare su, kamar hawansu da amfani da gashinsu da nononsu da sauransu har zuwa lokacin yankansu yayin da suka iso Ɗakin Allah mai dogon tarihi.

  34. وَلِكُلِّ أُمَّةٖ جَعَلۡنَا مَنسَكٗا لِّيَذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلۡأَنۡعَٰمِۗ فَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَلَهُۥٓ أَسۡلِمُواْۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُخۡبِتِينَ

    Open ayah 22:34

    Kowacce al’umma kuma Mun sanya musu (irin) bautar (da za su yi) don su ambaci sunan Allah bisa abin da Ya arzuta su da shi na dabbobin ni’ima. Sannan abin bautarku abin bauta ne guda Ɗaya, to gare Shi kawai za ku miƙa wuya. Kuma ka yi albishir ga masu ƙasƙantar da kai.

  35. ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَٱلصَّٰبِرِينَ عَلَىٰ مَآ أَصَابَهُمۡ وَٱلۡمُقِيمِي ٱلصَّلَوٰةِ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

    Open ayah 22:35

    (Su ne kuwa) waɗanda, idan aka ambaci Allah sai zukatansu su raurawa, kuma masu haƙuri bisa abin da ya same su, kuma masu tsai da salla, kuma masu ciyarwa daga abin da Allah Ya arzuta su (da shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kowace al’umma da ta gabata ya tanadar mata hanyar da za ta bauta masa ta hanyar zubar da jinin abin yanka domin neman kusanci gare shi. Kuma ambaton sunan Allah lokacin da za su yanka abin da za su kusanci Allah da yankansa. Yin haka ya zama godiya ne ga Allah bisa ga abin da ya arzuta su da shi na dabbobin ni’ima, watau raƙuma da shanu da tumaki. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya yi layya da raguna biyu masu launin baƙi-baƙi, sai na ga ya danne wuyansu da ƙafarsa ya yi Bismilla ya yi kabbara ya yanka su da hannunsa.” [Bukhari #5558 da Muslim #1966]. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na halarci sallar layya tare da Annabi (ﷺ) a filin idi, lokacin da ya gama huɗubarsa ya sauko daga kan minbari sai aka zo masa da rago sai ya yanka shi da hannunsa, ya ce: “Bismillahi Wallahu Akbar , wannan nawa ne da kuma wanda bai sami damar yin layya ba daga cikin al’ummata.” [Abu Dawud #2810 da Tirmizi #1521]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da mutane cewa abin bautarsu Ɗaya ne ba shi da abokin tarayya, don haka su miƙa wuya a gare shi su yi masa biyayya. Ya kuma umarci Manzon Allah (ﷺ) cewa ya yi albishir ga masu ƙasƙantar da kai ga Allah da ikhlasi, ya kuma faɗa musu abin da zai faranta musu rai. Sai ya bayyana wasu siffofi huɗu na masu ƙasƙantar da kansu ga Allah: <b>Siffa ta farko </b>, su ne waɗanda idan an ambaci Allah sai zukatansu su raurawa saboda tsoron uƙubarsa. <b>Ta biyu </b>, su ne masu haƙuri a kan duk abin da ya same su marar daɗi, watau ba sa raki ko nuna hushi game da ƙaddarar Allah. <b>Ta uku </b>, su ne masu tsayar da salla yadda aka umarce su da kula da lokutanta da rukunanta da wajibanta da mustahabbanta. <b>Ta huɗu </b>, su ne masu ciyarwa daga dukiyar da Allah ya arzuta su da ita; ciyarwa ta wajibi kamar zakka da ta sadaka da sauran ayyukan alheri.

  36. وَٱلۡبُدۡنَ جَعَلۡنَٰهَا لَكُم مِّن شَعَٰٓئِرِ ٱللَّهِ لَكُمۡ فِيهَا خَيۡرٞۖ فَٱذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَا صَوَآفَّۖ فَإِذَا وَجَبَتۡ جُنُوبُهَا فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡقَانِعَ وَٱلۡمُعۡتَرَّۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرۡنَٰهَا لَكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

    Open ayah 22:36

    (Raƙuma) kuma masu ƙiba Mun sanya muku su alamomi ne na bautar Allah; kuna da amfani game da su (na rayuwarku). To sai ku ambaci sunan Allah a kansu suna tsaye a kan ƙafa uku (lokacin soke su). To idan ransu ya fita bayan sun faɗi, sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da mai wadatar zuci da kuma mai bara. Kamar haka Muka hore muku su don ku yi godiya.

  37. لَن يَنَالَ ٱللَّهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَآؤُهَا وَلَٰكِن يَنَالُهُ ٱلتَّقۡوَىٰ مِنكُمۡۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرَهَا لَكُمۡ لِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

    Open ayah 22:37

    Namansu da jininsu ba sa zuwa wajen Allah, sai dai taƙawarku ce za ta isa gare Shi. Kamar haka Ya hore muku su don ku girmama Allah bisa shiryarwar da Ya yi muku (da addininsa). Kuma ka yi albishir ga masu kyautatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci raƙuma da shanu waɗanda ya hore wa mutane su don su zama abin da za su riƙa yankawa a hadayarsu da layyarsu, ya sanya su alamomi ne na addininsa, ya kuma tabbatar da cewa a tare da su akwai abubuwan amfani masu yawa ga Musulmi, na duniya da na lahira. Haka kuma ya umarce su da ambaton sunan Allah idan sun zo soke su, musamman raƙuma bayan sun tsaya da ƙafafunsu uku an ɗaure ɗayar domin kada su fizge su gudu. To idan sun faɗi bayan an soke an gyara su sun zama daidai a ci, sai ya umarce su da su ci wani kaso daga gare su, sannan su yi kyauta da wani kaso ga mabuƙacin da ya kame kansa ba ya roƙo, da ma wanda yake roƙo shi ma a ba shi. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda), ya ga wani mutum ya gurfanar da raƙumarsa zai soke ta, sai ya ce masa: “Tashe ta tsaye a kan ƙafafuwanta, ka dabaibaye su, wannan ita ce sunnar Baban Ƙasimu (ﷺ).” [Bukhari #1713 da Muslim #1320]. Dangane da ni’imomin da Allah ya yi wa mutane a kan waɗannan dabbobi kuma ya bayyana cewa, ya hore musu su don su hau su ɗora musu kaya, kuma su yanka ko su soke domin neman kusanci ga Allah. Allah ya yi wa mutane wannan ne don su gode masa a kan ni’imominsa su yi masa biyayya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa masu layya ko hadaya cewa ba ruwansa da namansu ko jininsu; abin da kawai Allah yake la’akari da shi, yake kuma sakayya a kansa shi ne taƙawa, watau masu layya ko hadaya su yi don Allah kawai ba don fariya ko riya ba. Sannan Allah ya ƙara tabbatar da ni’imar da ya yi wa mutane na hore musu waɗannan dabbobi domin su yi wa Allah kabbara su kuma gode masa bisa ga dacen bin hanyar gaskiya da ya yi musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi albishir ga masu kyautata ibadarsu da mu’amalolinsu da mutane.

  38. ۞إِنَّ ٱللَّهَ يُدَٰفِعُ عَنِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ خَوَّانٖ كَفُورٍ

    Open ayah 22:38

    Haƙiƙa Allah Yana bayar da kariya ga waɗanda suka yi imani. Lalle Allah ba Ya son duk mai ha’inci, butulu.

  39. أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُمۡ ظُلِمُواْۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصۡرِهِمۡ لَقَدِيرٌ

    Open ayah 22:39

    An yi izini (na yin yaƙi) ga waɗanda ake yaƙa don ko lalle an zalunce su. Lalle kuma Allah Mai iko ne bisa taimakon su.

  40. ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بِغَيۡرِ حَقٍّ إِلَّآ أَن يَقُولُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّهُدِّمَتۡ صَوَٰمِعُ وَبِيَعٞ وَصَلَوَٰتٞ وَمَسَٰجِدُ يُذۡكَرُ فِيهَا ٱسۡمُ ٱللَّهِ كَثِيرٗاۗ وَلَيَنصُرَنَّ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ 

    Open ayah 22:40

    (Su ne) waɗanda aka fitar da su daga gidajensu ba da wani laifi ba, sai don kawai sun ce: “Allah ne Ubangijinmu”. Kuma ba don kariyar Allah ga wasu mutane ta hanyar wasu ba, to da lalle an rusa wuraren bauta (na Nasara da suka ƙaurace wa ‘yan’uwansu), da coci-coci da wuraren bautar Yahudawa da masallatai (na Musulmi) waɗanda ake ambaton sunan Allah da yawa a cikinsu. Kuma tabbas Allah zai taimaki mai taimakon Sa. Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwayi.

  41. ٱلَّذِينَ إِن مَّكَّنَّٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَمَرُواْ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَنَهَوۡاْ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۗ وَلِلَّهِ عَٰقِبَةُ ٱلۡأُمُورِ

    Open ayah 22:41

    (Su ne) waɗanda, idan Muka kafa su a bayan ƙasa sai su tsai da salla su kuma ba da zakka kuma su yi umarni da aikin alheri su kuma yi hani daga mummunan aiki. Ƙarshen al’amura kuwa na Allah ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi ne yake kare muminai daga sharrin maƙiyansu saboda imaninsu, amma kuma ba ya son duk wani mai cin amanar Allah da ta bayinsa, mai butulce wa ni’imomin Allah ba ya gode masa a kansu. Allah kuma ya sanar da muminai cewa ya yi musu izinin su tashi su yaƙi azzalumai don kare kansu daga waɗanda suka zalunce su, suka cutar da su., lokacin da Musulmi suke a Makka kafin su yi hijira zuwa Madina. Kafiran Ƙuraishawa sun takura wa Annabi (ﷺ) da sahabbansa, sun yi ta cutar da su da zagi da duka da duk wani salo na ƙunci wulaƙanci da cin mutunci. Amma Allah (Mai tsarki da daukaka) bai ba wa Musulmi izini su yi yaƙi ba a lokacin, ya umarce su ne da su ci gaba da haƙuri da afuwa da kawar da kai. Bayan sun yi hijira sun kafa Daularsu a Madina sun yi ƙarfi sai Allah ya umarce shi da su tashi su kare kansu su yaƙi waɗanda suke zaluntar su, ya kuma yi musu alƙawarin ba su nasara a kan maƙiyansu domin shi Allah mai iko ne a kan komai. Sai kuma ya ambaci irin zaluncin da kafirai suka riƙa yi wa Musulmi, na fitar da su daga gidajensu ba tare da sun yi musu laifin komai ba, sai don zalunci da kuma cewa sun yi imani Allah ne Ubangijinsu abin bautar su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ba domin ya shar’anta wa annabawa da muminai su tashi su kare kansu da wuraren ibadarsu daga ta’addancin kafirai ba, to ba shakka da sun aiwatar da ta’addancinsu a kan wuraren bauta masu yawa, da sun rushe wuraren bauta na Nasara da suke ƙaurace wa mutane suna bautar Allah a cikinsu, da kuma coci-coci na Nasara da wuraren bautar Yahudawa da masallatan Musulmi waɗanda aka tanade su domin salla, kuma Musulmi suke ambaton Allah da yawa a cikinsu. Sannan Allah ya ƙara tabbatar da cewa lalle ya yi alƙawarin sai ya taimaki duk mai taimakon addininsa, lalle kuma shi mai ƙarfi ne Mabuwayi, babu mai iya ja da shi ya yi nasara. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Yayin da aka fitar da Annabi (ﷺ) daga Makka sai Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Sun kori Annabinsu! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un , tabbas kuwa za su hallaka, sai Allah ya saukar da wannan ayar ta 39.” Ibnu Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Daga lokacin aka fahimci sai an yi yaƙi (watau tsakanin Musulmi da kafirai).” Ibnu Abbas ya ƙara da cewa: “Wannan ita ce farkon ayar da ta sauka game da yaƙi.” [Ahmad #1865 da Tirmizi #3171]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗannan muminai da ya yi musu alƙawarin ba su nasara su ne waɗanda, idan ya kafa su a bayan ƙasa ya ba su iko da galaba a kan abokan gabarsu, to lalle za su tsayar da salla kamar yadda ya kamata, kuma za su fitar da zakkar dukiyoyinsu, za kuma su yi umarni da kyakkyawan aiki wanda shari’a ta yi umarni da shi, za su kuma hana aikata abin da aka hana. Sannan ya ƙara tabbatar da cewa ƙarshen al’amura duka gare shi za su koma, don haka shi ne mai bayar da lada shi ne kuma mai yin uƙuba.

  42. وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَعَادٞ وَثَمُودُ

    Open ayah 22:42

    Idan kuwa suka ƙaryata ka, to haƙiƙa mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa sun ƙaryata (manzanni) kafin su.

  43. وَقَوۡمُ إِبۡرَٰهِيمَ وَقَوۡمُ لُوطٖ

    Open ayah 22:43

    Da mutanen Ibrahimu da mutanen Luɗu (su ma sun ƙaryata).

  44. وَأَصۡحَٰبُ مَدۡيَنَۖ وَكُذِّبَ مُوسَىٰۖ فَأَمۡلَيۡتُ لِلۡكَٰفِرِينَ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

    Open ayah 22:44

    Da ma mutanen Madyana (su ma sun ƙaryata); an kuma ƙaryata Musa, sai Na jinkirta wa kafurai, sannan Na kama su (da azabata); to ƙaƙa (ƙarshen) kashedina (a gare su) ya kasance?

  45. فَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَا وَهِيَ ظَالِمَةٞ فَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَبِئۡرٖ مُّعَطَّلَةٖ وَقَصۡرٖ مَّشِيدٍ

    Open ayah 22:45

    Sannan alƙarya nawa muka hallaka su alhalin suna azzalumai, sai ga su suna rugurguje a kan rufinsu sun zama kufai, da kuma rijiyoyin da aka watsar da amfani da su, da manya-manyan gine-gine da aka ɗaukaka su?

  46. أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَتَكُونَ لَهُمۡ قُلُوبٞ يَعۡقِلُونَ بِهَآ أَوۡ ءَاذَانٞ يَسۡمَعُونَ بِهَاۖ فَإِنَّهَا لَا تَعۡمَى ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَلَٰكِن تَعۡمَى ٱلۡقُلُوبُ ٱلَّتِي فِي ٱلصُّدُورِ

    Open ayah 22:46

    Yanzu ba za su yi tafiya a bayan ƙasa ba don su samu zukata da za su riƙa tunani da su, ko kuwa kunnuwa da za su riƙa ji da su? To lalle yadda lamarin yake ba idanduna ba ne suke makancewa sai dai zukatan da suke cikin ƙiraza su ne suke makancewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Annabi (ﷺ) game da ƙaryatawar da mutanensa suke yi masa, da cewa, idan har sun ci gaba da ƙaryata shi to ya yi haƙuri, ba shi ne farkon annabin da mutanensa suka ƙaryata ba; mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙaryata shi; Adawa sun ƙaryata Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), su ma Samudawa sun ƙaryata Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Hakanan mutanen Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙaryata shi; mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ma sun ƙaryata shi, mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙaryata Annabi Shu’aibu, Fir’auna da mutanensa sun ƙaryata Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). To amma dukkansu Allah ya jinkirta azabtar da su, daga ƙarshe ya kama su mummunan kamu. Allah ya ja hankalin Annabi (ﷺ) da cewa ya duba ya ga yadda ƙarshen kashedin da ya yi musu ya zamanto a gare su, domin kuwa dukkansu ya hallaka su saboda kafircinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ba waɗancan al’ummu ne kawai ya hallaka ba, ya hallaka al’ummu masu yawa yayin da suka yi zalunci da kafirci da shirka da ƙaryata manzanni, ya yi rugurugu da alƙaryunsu suka wayi gari babu wasu mazauna a cikinsu; rijiyoyinsu aka yi watsi da su da manya-manyan gine-gine na alfarma waɗanda suka kasa kare su daga azabar Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga kafirai idan har suna tababa game da wannan batu, to me zai hana su yi tattaki su ziyarci waɗannan alƙaryu su ga yadda Allah ya hallaka mazauna cikinsu ya bar su kufai babu kowa a wurin, sai su yi tunani da hankulansu don su wa’azantu, su kuma buɗe kunnuwansu su saurari labaransu sauraro na fahimta da aiki, domin makanta ta haƙiƙa ba ita ce rasa idanu ba; haƙiƙanin makanta mai hallakarwa ita ce makantar zuci wadda take hana mutane karɓar gaskiya da aiki da ita.

  47. وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥۚ وَإِنَّ يَوۡمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلۡفِ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ

    Open ayah 22:47

    Kuma suna neman ka da gaggauto musu da azaba, Allah kuwa ba Ya saɓa alƙawarinsa. Lalle kuma yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shekara dubu ne daga irin waɗanda kuke ƙirgawa.

  48. وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ أَمۡلَيۡتُ لَهَا وَهِيَ ظَالِمَةٞ ثُمَّ أَخَذۡتُهَا وَإِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 22:48

    Kuma alƙaryu nawa ne Na saurara musu, alhali kuwa suna kafirai, sannan (daga baya) Na kama su? Makoma kuma zuwa gare Ni ne.

  49. قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَآ أَنَا۠ لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 22:49

    Ka ce: “Ya ku mutane, ni dai kawai mai gargarɗi ne a gare ku mai bayyana (gargaɗi).”

  50. فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ 

    Open ayah 22:50

    To waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, suna da gafara da kuma arziki mai girma.

  51. وَٱلَّذِينَ سَعَوۡاْ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

    Open ayah 22:51

    Waɗanda kuwa suka yi iya ƙoƙarinsu game da ɓata ayoyinmu suna ganin za su gagare Mu, to waɗannan su ne ma’abota (wutar) Jahima. A waɗannan ayoyi bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) a kan ƙuntatawar da mushirikai suke yi masa, sai kuma ya bayyana wani izgili da kafirai suke yi masa na neman ya gaggauto musu da azaba wadda yake yi musu barazana da ita ta duniya da ma ta lahira. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa su daina garaje domin wannan alƙawari ne na Allah kuma ba zai taɓa saɓa alƙawarinsa ba, domin ya fara gaggauto musu da wata azaba ta kisa a yaƙin Badar lokacin da aka kashe wasu manyan shugabannin Ƙuraishawa a wannan yaƙin. Bugu da ƙari kuma akwai ranar alƙiyama tana nan tafe wadda a cikinta ne za su gamu da mummunan sakamakon da yake jiran su. Kuma yini ɗaya na azabar wannan ranar kamar tsawon shekara dubu yake a lissafin shekarunsu na duniya saboda tsananin azabar da ke cikinsa. Wannan ya nuna cewa su ne suke ganin tsawon lokacin da aka ɗauka ba a zo musu da azabar da ake yi musu kashedinta ba. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Talakawan Musulmi za su riga masu wadatarsu shiga Aljanna da rabin yini, watau shi ne shekara ɗari biyar.” [Ahmad #8521 da Tirmizi #1354 da Ibn Majah #4122]. Sai kuma ya bayyana musu cewa jinkirin da yake yi musu ba saɓa alƙawari ne ba, talala ce yake yi musu, zai kama su a nan gaba, domin akwai al’ummu masu yawa a gabaninsu da suka yi zalunci na kafirci da saɓon Allah da cutar da junansu amma Allah bai gaggauto musu da azaba ba, ya yi musu talala har sai da lokacin kama su ya zo sai ya yi musu mummunan kamu, ya hallaka su baki ɗaya. Makomarsu gaba ɗayansu kuma zuwa gare shi take, watau ranar alƙiyama a nan ne zai yi musu sakamako da azabar wuta ta har abada saboda kafircinsu. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya sanar da su cewa shi Manzo ne mai gargaɗi bayyananne a gare su, don haka gaggauto da azaba ba a hannunsa take ba tana hannun Allah ne; idan ya ga dama ya gaggauto ta, idan kuma ya ga dama ya yafe wa wanda ya tuba ya koma gare shi. Sai kuma ya bayyana cewa waɗanda suka yi imani da Allah kuma suka yi kyawawan ayyuka, Allah ya tanadar musu gafara ga zunubansu da wani arzuki na karamci mai ɗorewa a gidan Aljanna. Amma waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah suna tsammanin ko za su gagari Allah su kuɓuce wa azabarsa, to waɗannan su ne ma’abota wutar Jahannama; za su shige ta su yi ta zama a cikinta har abada.

  52. وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٖ وَلَا نَبِيٍّ إِلَّآ إِذَا تَمَنَّىٰٓ أَلۡقَى ٱلشَّيۡطَٰنُ فِيٓ أُمۡنِيَّتِهِۦ فَيَنسَخُ ٱللَّهُ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ ثُمَّ يُحۡكِمُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

    Open ayah 22:52

    Kuma babu wani manzo ko wani annabi da Muka aiko a gabaninka face idan ya yi karatu sai Shaiɗan ya jefa (ruɗu da wasiwasi) cikin karatunsa; sannan Allah Yakan ɓata abin da shi Shaiɗan yake jefawa, sannan Allah Ya tabbatar da ayoyinsa. Allah kuwa Masani ne Mai hikima.

  53. لِّيَجۡعَلَ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡقَاسِيَةِ قُلُوبُهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَفِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ

    Open ayah 22:53

    (Yakan yi haka ne) don Ya sanya abin da Shaiɗan yake jefawa ya zama fitina ga waɗanda suke da cuta a cikin zukatansu, da kuma masu ƙeƙasassun zukata. Lalle kuma azzalumai tabbas suna cikin saɓani mai nisa.

  54. وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَيُؤۡمِنُواْ بِهِۦ فَتُخۡبِتَ لَهُۥ قُلُوبُهُمۡۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

    Open ayah 22:54

    Don kuma waɗanda aka bai wa ilimi su san cewa shi (Alƙur’ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake, sai su yi imani da shi sai zukatansu su nutsu da shi. Kuma lalle Allah tabbas Mai shiryar da waɗanda suka yi imani ne zuwa ga tafarki madaidaici. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Annabi (ﷺ) ne game da ƙaryata shi da mutanensa suka yi, da cewa babu wani manzo ko annabi da ya aiko gabaninsa face idan ya fito yana karanta wa mutane littafin Allah sai Shaiɗan ya yi ƙoƙarin jefa ruɗu da wasiwasi a cikin zukatan masu sauraron wannan karatun nasa domin ya hana su yin imani da abin da ake karanta musu, kamar yadda idan Annabi (ﷺ) yana karanta wa mushirikai Alƙur’ani Shaiɗan yakan jefa ruɗani a cikin zukatansu sai su riƙa kiran Annabi (ﷺ) da matsafi ko mawaƙi ko boka da sauran sunaye na banza, to amma sai Allah ya shafe wannan ruɗun da wasiwasin na Shaiɗan ya tabbatar da ayoyinsa na gaskiya, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) masanin komai ne mai hikima ne cikin ayyukansa gaba ɗaya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kasa mutane gida uku dangane da ruɗun da Shaiɗan yake kawowa lokacin da Annabi yake karanta ayoyin Allah: <b>Kashi na farko </b>, su ne munafukai masu cutar munafurci a zukatansu, sai wannan ya zame musu wata jarraba, sai munafurcinsu ya ƙaru, cutar zukatansu ta daɗa hauhawa. <b>Kashi na biyu </b>, su ne mushirikai waɗanda zukatansu suka ƙeƙashe suka mutu murus, to sai su yi amfani da wannan ruɗin na Shaiɗan su riƙa hana mutane yin imani da gaskiya. To duk waɗannan kaso biyun azzalumai ne masu nuna adawa ga Allah da Manzonsa (ﷺ) don haka sun yi nisa da gaskiya da shiriya. <b>Kashi na uku </b>, su ne muminai waɗanda Allah ya ba su ilimi, to waɗannan za su san cewa lalle Alƙur’ani gaskiya ne kuma saukakke ne daga Allah Ubangijinsu, don haka sai su yi imani da shi, zukatansu kuma su nutsu da shi su miƙa wuya gare shi. Allah kuma ya tabbatar da cewa lalle zai shiryar da muminai zuwa ga hanyar gaskiya miƙaƙƙiya ɗoɗar wadda babu karkata a cikinta, sakamakon miƙa wuya da suka yi ga wahayin Ubangijinsu.

  55. وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي مِرۡيَةٖ مِّنۡهُ حَتَّىٰ تَأۡتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةً أَوۡ يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَقِيمٍ

    Open ayah 22:55

    Waɗanda kuwa suka kafirce ba za su daina kokwanton sa ba (watau Alƙur’ani) har sai alƙiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, ko kuma azabar rana bakarara ta zo musu.

  56. ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ

    Open ayah 22:56

    Mulki a wannan ranar na Allah ne, zai yi hukunci a tsakaninsu. To waɗanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, suna cikin gidajen Aljanna na ni’ima.

  57. وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

    Open ayah 22:57

    Waɗanda kuwa suka kafirta suka kuma ƙaryata ayoyinmu, to waɗannan suna da azaba mai wulaƙantawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafirai ba za su daina halinsu na yin shakka game da Alƙur’ani ba, za su doge a kan haka har sai ranar alƙiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, ko kuma azabar wannan ranar ta zo musu. A wannan ranar kafirai ba za su gamu da wata rahama ko wani alheri ba; za su yi ta nadamar da ba za ta yi musu amfani ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa mulki gaba ɗaya a wannan ranar a hannunsa yake, nasa ne shi kaɗai babu mai ja da shi. Shi ne zai yi hukunci tsakanin muminai da kafirai, kowanne ya yanke masa hukuncin da ya cancance shi. Waɗanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari, to waɗannan suna da babban sakamako na gidajen Aljannar ni’ima wadda ba ta yankewa. Waɗanda kuwa suka kafirta suka kuma ƙaryata ayoyin da Allah ya saukar wa Manzonsa, to waɗannan suna da azaba mai wulaƙantarwa ta wutar Jahannama.

  58. وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ قُتِلُوٓاْ أَوۡ مَاتُواْ لَيَرۡزُقَنَّهُمُ ٱللَّهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ

    Open ayah 22:58

    Waɗanda kuwa suka yi hijira saboda Allah sannan aka kashe su ko kuma suka mutu, to lalle Allah tabbas zai arzuta su da kyakkyawan arziki. Kuma lalle Allah tabbas Shi ne Fiyayyen masu arzutawa.

  59. لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ

    Open ayah 22:59

    Lalle tabbas Zai shigar da su wata mashiga da za su yarda da ita. Kuma lalle Allah tabbas Masani ne, Mai hakuri.

  60. ۞ذَٰلِكَۖ وَمَنۡ عَاقَبَ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبَ بِهِۦ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيۡهِ لَيَنصُرَنَّهُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ 

    Open ayah 22:60

    Wannan (abu da aka ambata haka yake), duk wanda ya yi uƙuba da irin abin da aka yi masa uƙuba da shi, sannan aka daɗa yi masa ta’addanci, to lalle Allah tabbas zai taimake shi. Lalle Allah tabbas Mai afuwa ne, Mai gafara.

  61. ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

    Open ayah 22:61

    Wannan (taimakon kuwa zai kasance ne) saboda lalle Allah Shi Yake shigar da dare cikin rana, Yake kuma shigar da rana cikin dare, kuma lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.

  62. ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ

    Open ayah 22:62

    Wannan kuwa saboda lalle Allah Shi ne (abin bauta) na gaskiya, kuma lalle abin da suke bauta wa wanda ba Shi ba shi na ƙarya ne, kuma lalle Allah Shi ne Maɗaukaki, Mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi babban albishir ga waɗanda suka yi hijira don Allah suka bar garuruwansu da gidajensu domin neman yardar Allah da yaɗa addininsa, suka kuma fita jihadi aka kashe su a can, to waɗannan Allah ya yi musu alƙawarin tabbas zai arzuta su a gidan Aljanna da kyakkyawan arziki wanda ba zai yanke ba har abada, domin Allah shi ne fiyayyen masu arzutawa. Zai shigar da su wani wurin da za su yarda da shi, watau gidan Aljanna. Lalle Allah yana sane da ayyukansu da niyyoyinsu, kuma shi mai haƙuri ne, shi ya sanya ba ya gaggauto da uƙuba ga bayinsa da suka yi laifi, yana jinkirta musu ne domin su tuba ya yafe musu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk wanda aka cuce shi ko aka zalunce shi, to ya halatta a gare shi ya rama zaluncin da aka yi masa daidai da abin da aka yi masa; yin haka ba laifi ba ne. Idan kuma bayan ya rama gwargwadon abin da aka yi masa, sai kuma aka sake yi masa wani ta’addancin don ramuwar da ya yi, to lalle tabbas Allah zai taimaka masa a kan wanda ya yi masa ta’addanci. Kuma Allah ya tabbatar da cewa shi mai afuwa ne ga muminai masu laifi, mai gafara ne gare su. Sai kuma ya tabbatar da cikakkiyar Ƙudurarsa ta aikata abin da ya ga dama ga halittarsa, domin shi ne mai ikon shigar da lokutan dare a cikin na rana, ya kuma shigar da lokutan rana a cikin na dare ta hanyar ƙara tsawon ɗaya ya rage na ɗayan. Kuma shi ne wanda yake jin duk maganganun bayinsa yake kuma sane da ayyukansu, babu abin da yake ɓuya gare shi, kuma zai yi musu sakayya a kai. Sai kuma ya tabbatar da cewa shi ne Allah wanda yake zartar da waɗannan ayyuka, wanda kuma ya siffantu da siffofin kamala. Don haka shi ne abin bauta na gaskiya, duk wani abu da wasu suke bauta wa ba Allah ba ƙarya ne wanda ba shi da wani tushe ko tabbas. Allah shi kaɗai ne wanda yake da ɗaukaka ta zati da siffa da iko, kuma shi ne mai girma wanda kowa a ƙasa da shi yake.

  63. أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَتُصۡبِحُ ٱلۡأَرۡضُ مُخۡضَرَّةًۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٞ

    Open ayah 22:63

    Shin ba ka ga cewa Allah ne Ya saukar da ruwa daga sama ba, sai ƙasa ta zama koriya shar? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Masani.

  64. لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

    Open ayah 22:64

    Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa nasa ne. Kuma lalle Allah tabbas Shi ne Mawadaci, Sha-Yabo.

  65. أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱلۡفُلۡكَ تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِأَمۡرِهِۦ وَيُمۡسِكُ ٱلسَّمَآءَ أَن تَقَعَ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 22:65

    Shin ba ka ga cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin ƙasa, da kuma jiragen ruwa da suke gudu a cikin kogi da umarninsa, kuma Yake riƙe sama don kada ta faɗo a kan ƙasa, sai da izininsa? Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama ga mutane.

  66. وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَكَفُورٞ

    Open ayah 22:66

    Shi ne kuma Wanda Ya raya ku sannan zai kashe ku sannan Ya (sake) raya ku. Lalle mutum tabbas mai yawan butulci ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana wa Manzonsa isar mulkinsa da cikakkiyar Ƙudurarsa ta aikata abin da ya ga dama, da cewa shi ne ya saukar da ruwan sama sai ƙasa ta wayi gari ta zama koriya shar saboda tsirran da suka fito daga cikinta. Allah kuma ya yi haka ne saboda tausayawarsa ga bayinsa ya samar musu abincin da za su ci su rayu, domin ya fi kowa sanin abin da zai zama maslaha da amfani a gare su, kuma babu abin da yake ɓuya a gare shi. Sannan ya tabbatar musu da cewa duk abin da yake cikin sammai da wanda yake cikin ƙasa mallakarsa ne, kuma shi lalle Mawadaci ne ba shi da buƙata a wurin wani mahaluƙi kowane ne. Abin gode wa ne wanda kowa yake yi masa kirari da Sha-yabo. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzon (ﷺ) wasu dalilai na cikar ikonsa da kamalar Ƙudurarsa, da kuma ni’imominsa ga mutane, da cewa, shi ne ya hore musu duk abin da yake bayan ƙasa na dabbobi da sauran daskararrun abubuwa, kamar duwatsu da bishiyoyi da sauransu domin amfaninsu da biyan buƙatunsu na rayuwa. Hakanan kuma ya hore musu jiragen ruwa waɗanda suke kai-komo a cikin koguna daga gari zuwa gari ɗauke da mutane da kayayyakinsu. Shi ne kuma yake riƙe da sama domin kada ta faɗo a kan ƙasa sai da izininsa. Ba don rahamarsa da cikakkiyar Ƙudurarsa ba da sai ta faɗo a kan mutane duk ta hallaka su, to amma Allah shi mai tausayin mutane ne mai rahama gare su, wannan ya sa ya hore musu duk waɗannan abubuwa da aka ambata da ma wasu daban. Sannan Allah ya ci gaba da lissafa ni’imominsa da dalilan ikonsa, da cewa shi ne ya halicci mutane daga babu ya hura musu rai; sannan bayan cikar ajalinsu shi ne zai karɓi rayukansu, sannan bayan mutuwarsu zai sake raya su domin ya yi musu hisabi a kan ayyukansu ya saka wa kowa da irin abin da ya cancanta, to amma duk da waɗannan ni’imomin na Ubangiji sai ga ɗan’adam yana jayayya wajen bautar sa, ko ya yi jayayya a kan cewa zai iya tashin matattu bayan mutuwarsu.

  67. لِّكُلِّ أُمَّةٖ جَعَلۡنَا مَنسَكًا هُمۡ نَاسِكُوهُۖ فَلَا يُنَٰزِعُنَّكَ فِي ٱلۡأَمۡرِۚ وَٱدۡعُ إِلَىٰ رَبِّكَۖ إِنَّكَ لَعَلَىٰ هُدٗى مُّسۡتَقِيمٖ

    Open ayah 22:67

    Kowacce al’umma Mun sanya mata hanyar (shari’a) da za su yi aiki da ita; to lalle kada su yi jayayya da kai game da lamarin (addini). Kuma ka yi kira zuwa ga (addinin) Ubangijinka; lalle kai tabbas kana bisa shiriya madaidaiciya.

  68. وَإِن جَٰدَلُوكَ فَقُلِ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 22:68

    Idan kuwa suka yi maka jayayya, sai ka ce: “Allah ne Ya fi sanin abin da kuke aikatawa.”

  69. ٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

    Open ayah 22:69

    Allah zai yi hukunci a tsakaninku ranar alƙiyama game da abin da kuka kasance kuna sassaɓawa a kansa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kowace al’umma ya tanadar musu tasu shari’ar da za su yi aiki da ita, don haka shi ma Manzo (ﷺ) Allah ya ba shi tasa shari’ar da yake aiki da ita. Saboda haka bai dace mushirikai da mabiya sauran addinai su yi jayayya da shi game da tasa shari’ar ba, domin shi ne a kan gaskiya, su kam suna rayuwa ne a kan ɓata. Sai ya umarci Annabi (ﷺ) ya ci gaba da yi musu wa’azi, ya kira su zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, domin shi ne a kan tafarki madaidaici wanda ba shi da wata karkata sam-sam. Sai kuma ya bayyana masa cewa, idan waɗannan kafirai sun dage a kan ci gaba da jayayya da shi bayan hujja ta bayyana gare su a fili, to ya mayar da al’amarinsa ga Allah ya fito fili ya faɗa musu cewa, Allah ne ya fi kowa sanin abin da suke aikatawa, don haka su jira za su ga sakamakon abin da suke aikatawa. Kuma su kwana da sanin cewa a ranar alƙiyama Allah zai yi hukunci na adalci tsakanin bayinsa muminai da kafirai game da abubuwan da suka yi saɓani a kansu na batutuwan addini da na rayuwa.

  70. أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ 

    Open ayah 22:70

    Shin ba ka sani ba cewa lalle Allah Yana sane da abin da yake cikin sama da wanda yake ƙasa? Lalle wannan yana cikin littafi (wato Lauhul-Mahafuzu). Lalle wannan mai sauƙi ne a wurin Allah.

  71. وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ سُلۡطَٰنٗا وَمَا لَيۡسَ لَهُم بِهِۦ عِلۡمٞۗ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِن نَّصِيرٖ

    Open ayah 22:71

    Suna kuma bauta wa wanda ba Allah ba, abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi, da kuma abin da ba su da ilimi game da shi. Azzalumai kuwa ba su da wani mataimaki.

  72. وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ تَعۡرِفُ فِي وُجُوهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡمُنكَرَۖ يَكَادُونَ يَسۡطُونَ بِٱلَّذِينَ يَتۡلُونَ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِنَاۗ قُلۡ أَفَأُنَبِّئُكُم بِشَرّٖ مِّن ذَٰلِكُمُۚ ٱلنَّارُ وَعَدَهَا ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 22:72

    Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu bayyanannu, to za ka ga alamar musantawa a fuskokin waɗanda suka kafirta, suna kamar za su auka wa waɗanda suke karanta musu ayoyinmu. To ka ce: “Shin ba na ba ku labarin abin da ya fi wannan muni ba? Wuta ce da Allah Ya yi alƙawari ga waɗanda suka kafirta; makoma kuwa ta munana.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Annabi (ﷺ) cewa yana sane da duk abin da yake cikin sama da duk abin da yake a bayan ƙasa; domin kuwa komai yana nan a rubuce a cikin Lauhul Mahfuzu, don haka sanin komai abu ne mai matuƙar sauƙi a wurinsa. Sai kuma ya bayyana cewa duk da kasancewar Allah ne mai wannan faffaɗan ilimi, mushirikai sun bijire a kan bautar sa shi kaɗai, sun ci gaba da bauta wa wasu gumaka waɗanda Allah bai taɓa saukar da wata hujja a cikin wani littafinsa kan cewa a bauta musu ba, su kansu masu bautar ba su da wani dalili da suka dogara da shi na bauta wa wani tare da Allah, wanda ya wuce cewa, suna bin abin da suka sami iyayensu ne a kai ido rufe. Wannan shirka da suke yi wa Allah tabbas babu zaluncin da ya kai shi. Don haka idan azabar Allah ta sauko musu ba su da wani wanda zai iya taimaka musu ya kare su daga gare ta. Sai kuma ya bayyana irin taurin kansu da bijirewarsu yayin da suka ji ana karanta musu ayoyin Allah bayyanannu masu kira zuwa ga kaɗaita Allah da bauta, lokacin ne za a ga alamar fushi da musuntawa da bijirewa ta bayyana a fuskokinsu, har ma saboda tsananin fushi sai su yi kamar za su auka wa waɗanda suke karanta musu ayoyin. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, idan suna ganin munin abin da yake karanta musu, hakan kuma yana ɗaga musu hankali, to ya yi musu albishir da wani abu da ya fi wannan muni a gare su, watau wutar Jahannama da Allah ya yi musu tanadinta kuma lalle zai shigar da su cikinta. Wannan makoma ta wutar Jahannama kuwa ta yi matuƙar muni.

  73. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ضُرِبَ مَثَلٞ فَٱسۡتَمِعُواْ لَهُۥٓۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَن يَخۡلُقُواْ ذُبَابٗا وَلَوِ ٱجۡتَمَعُواْ لَهُۥۖ وَإِن يَسۡلُبۡهُمُ ٱلذُّبَابُ شَيۡـٔٗا لَّا يَسۡتَنقِذُوهُ مِنۡهُۚ ضَعُفَ ٱلطَّالِبُ وَٱلۡمَطۡلُوبُ

    Open ayah 22:73

    Ya ku mutane, an ba da misali, to sai ku saurare shi. Lalle waɗanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba za su taɓa iya halittar ƙuda ba, ko da sun taru domin (halitta) shi; idan kuma da ƙudan zai cire musu (su gumakan) wani abu, to ba za su iya ƙwato shi ba daga wurinsa. Wanda yake nema da wanda ake nema (duka) sun yi rauni!

  74. مَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

    Open ayah 22:74

    Ba su girmama Allah ba kamar yadda ya kamata su girmama Shi. Lalle Allah tabbas Ƙaƙƙarfa ne, Mabuwayi.

  75. ٱللَّهُ يَصۡطَفِي مِنَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ رُسُلٗا وَمِنَ ٱلنَّاسِۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

    Open ayah 22:75

    Allah Yana zaɓar manzanni daga mala’iku kuma daga mutane. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.

  76. يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ

    Open ayah 22:76

    Yana sane da abin da yake gabansu da abin da yake bayansu. Zuwa ga Allah ne kawai ake komar da al’amura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ƙaƙƙarfar hujja ta rashin cancantar bautar da kafirai suke yi wa abin bautarsu da cewa, ba sa iya tsinana wa kansu wani abu, ko su kare kansu daga wata cuta balle har su kare wani. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo wa mushirikai wani sassauƙan misali wanda za su saurara ko ya zame musu abin izina, da cewa, abin da suke bauta wa wanda ba Allah ba, ba zai iya halittar ko da ƙuda ba saboda kasawarsa, ko da kuwa za su yi taron dangi don wannan aikin. Hasali ma, da abin a ce ƙuda zai sauka a kan gumakan ya ɗauke musu wani abu, kamar turaren da ake saka musu a jiki, to fa ba za su iya ƙwato shi ba. To idan har ba za su iya halittar ƙanƙanin abu kamar ƙuda ba, ba kuma za su iya ƙwato wani abu daga wajensa ba, to ta yaya za a yi tsammanin za su iya halittar abin da ya fi ƙuda girma? To amma duk da haka saboda ɓata suna bauta musu ba Allah ba. Sai Allah ya tabbatar da cewa shi mai neman, watau gunkinsu, da wanda ake nema, watau ƙudan, duk sun tabbata masu rauni ne; wanda ya fi su rauni kuma shi ne wanda zai rungumi abu mai rauni a matsayin abin bauta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafirai ba su ba wa Allah girman da ya kamata su ba shi ba, domin sun bauta wa wasu tare da shi. Lalle Allah ƙaƙƙarfa ne, mabuwayi. Yana daga cikin ƙarfinsa da buwayarsa ikon halittar sammai da ƙasa da abin da yake cikinsu, kuma babu mai iya rinjayar sa a komai, saɓanin tarkacen da mushirikai suke bauta wa, waɗanda suke ƙasƙantattu ne ba sa ma iya yi wa kansu komai balle su yi wa wani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimarsa da cewa shi ne yake zaɓar manzanni daga cikin mala’iku da kuma mutane. Yakan aiko wasu mala’ikunsa zuwa ga annabawa, kamar yadda ya riƙa aiko Mala’ika Jibrilu zuwa ga manzanni daga cikin mutane; su kuma manzanni ya aika su zuwa ga mutane. Ya tabbatar da cewa yana jin duk abin da mushirkai suke faɗa dangane da manzanninsa mutane. Ya kuma san halin da dukkanin manzanni na mala’iku da na mutane suke ciki gabanin halittarsu da bayan mutuwarsu. Ya tabbatar musu da cewa makomar dukkan al’amura tana gare shi shi kaɗai ranar alƙiyama, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan abin da ya aikata.

  77. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱرۡكَعُواْ وَٱسۡجُدُواْۤ وَٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمۡ وَٱفۡعَلُواْ ٱلۡخَيۡرَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ۩

    Open ayah 22:77

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi ruku’i kuma ku yi sujjada, ku kuma bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alheri don ku rabauta.

  78. وَجَٰهِدُواْ فِي ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦۚ هُوَ ٱجۡتَبَىٰكُمۡ وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمۡ إِبۡرَٰهِيمَۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ

    Open ayah 22:78

    Kuma ku yi jihadi wajen (ɗaukaka addinin) Allah iyakar iyawarku. Shi ne Ya zaɓe ku, bai kuma sanya muku wani ƙunci ba cikin addini. Addinin Babanku ne Ibrahimu. (Allah) Shi ne Ya kira ku Musulmi tuntuni, da kuma cikin wannan (Alƙur’ani) don Manzo ya zama shaida a gare ku, ku kuma ku zama shaida ga (sauran) mutane. To sai ku tsai da salla kuma ku ba da zakka, ku kuma yi riƙo da (addinin) Allah, Shi ne Majiɓincin al’amarinku; to madalla da Majiɓinci, kuma madalla da Mataimaki. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga muminai waɗanda suka yi imani da Allah suka kuma yi ayyuka na ƙwarai, ya umarce su da yin ruku’u da sujjada a cikin sallolinsu ga Allah shi kaɗai. Sannan ya umarce su da aikata alheri ga mutane, kamar sadaka da taimako da sada zumunci domin su sami babban rabo kuma su kuɓuta daga duk wani abin ƙi. Allah kuma ya umarce su da yin jihadi domin shi, ya tabbatar musu cewa shi ne ya zaɓa musu addini mai sauƙi wanda babu ƙunci ko tsanani a cikinsa, kuma shi ne addinin babansu Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya tura shi Yaman tare da Mu’azu ɗan Jabal (Allah ya kara masa yarda) ya ce musu: “Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi wa mutane albishir kada ku kore su; ku haɗa kawunanku kada ku saɓa.” [Bukhari #3038 da Muslim #1733]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle wannan addini ne mai sauƙi babu wanda zai ɗora wa kansa abin da ya fi ƙarfinsa na addini sai ya rinjaye shi…” [Bukhari #39]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) wane addini ne Allah ya fi so, sai ya ce: “Addinin Annabi Ibrahimu mai sauƙi.” [Ahmad #2107]. Sannan kuma Allah ya tabbatar musu da cewa shi ne ya sa musu suna ‘Musulmi’ a cikin littattafan da suka gabata da kuma cikin Alƙur’ani, domin Manzo ya zama mai shaida a gare ku cewa ya isar muku da saƙon Allah, ku kuma ku zama masu shaida a kan sauran al\'ummun da suka gabace ku cewa manzanninsu sun isar musu da saƙo. [Duba Tafsirin aya ta 143 cikin Suratul Baƙara ]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su tsayar da salla yadda ya kamata, su kuma ba da zakkar dukiyoyinsu, su kuma yi riƙo da hanyar Allah, su dogara da shi cikin dukkan lamuransu, domin Allah shi ne majiɓincin al’amuransu; madalla da majiɓinci kuma madalla da mai taimakon wanda ya nemi taimakonsa daga cikin muminai. Don haka kowa ya nemi taimakonsa zai taimaka muku.