المؤمنون
Al-Muminoon
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
قَدۡ أَفۡلَحَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Open ayah 23:1Haƙiƙa muminai sun rabauta.
ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي صَلَاتِهِمۡ خَٰشِعُونَ
Open ayah 23:2(Su ne) waɗanda suke masu ƙasƙantar da kai a cikin sallarsu.
وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنِ ٱللَّغۡوِ مُعۡرِضُونَ
Open ayah 23:3Kuma waɗanda suke masu kau da kai daga yasasshiyar magana.
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِلزَّكَوٰةِ فَٰعِلُونَ
Open ayah 23:4Kuma waɗanda suke masu aiwatar da zakka.
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ
Open ayah 23:5Kuma waɗanda suke masu kiyaye farjinsu.
إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ
Open ayah 23:6Sai dai ga matayensu ko kuma ƙwara-ƙwaransu, to lalle su ba abin zargi ba ne.
فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ
Open ayah 23:7Sannan duk wanda ya nemi (wata hanya) ba waɗannan ba, to waɗannan su ne masu ƙetare iyaka.
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ
Open ayah 23:8Kuma waɗanda suke masu kiyaye amanarsu da kuma alƙawarinsu.
وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَوَٰتِهِمۡ يُحَافِظُونَ
Open ayah 23:9Kuma waɗanda suke kiyaye sallolinsu.
أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡوَٰرِثُونَ
Open ayah 23:10Waɗannan su ne magada.
ٱلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡفِرۡدَوۡسَ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 23:11Waɗanda suke gadar (Aljannar) Firdausi, su madawwama ne a cikinta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da muminai samun rabauta a duniya da lahira, watau za su sami abin da suke burin samu na jin daɗin duniya da lahira, za kuma su kuɓuta daga duk wani abin ƙi ko ban tsoro. Bayan babbar sifa ta imani da Allah ya kira muminai da ita, sai kuma ya siffanta su da wasu siffofi guda shida, su ne: <b>Ta farko </b>, su ne masu ƙasƙantar da kai da nutsuwa a cikin sallarsu, gaɓoɓinsu sukan nutsu; ba sa bijiro wa zukatansu da abubuwan da za su shagaltar da su daga sallarsu. <b>Ta biyu </b>, su ne masu kauce wa duk wata maganar banza ko aikin banza waɗanda suke ƙunshe da saɓon Allah, ko kuma marar amfani ga bawa duniya da lahira. <b>Ta uku </b>, su ne masu tsarkake kawunansu daga dukkan wasu miyagun ayyuka, kuma suna tsarkake dukiyoyinsu ta hanyar sadaka ko fitar da zakka. <b>Ta huɗu </b>, su ne masu kiyaye kawunansu daga aikata zina ko luwaɗi; a koyaushe suna tsare mutuncinsu, ba sa kusantar matan da ba su halatta a gare su ba, suna tsayawa ne kaɗai a kan matansu na aure ko saɗakunsu, to su waɗannan ba abin zargi ba ne don sun biya buƙatarsu a wajensu domin Allah ne ya halatta musu kusantar su. Sai Allah ya ƙara tabbatar da cewa duk wanda ya nemi biyan buƙatarsa ta wata hanya ba waɗannan ba, to wannan ya ƙetare iyaka ta Ubangiji. <b>Ta biyar </b>, su ne masu kiyaye amanar da ke tsakaninsu da Allah da wadda take tsakaninsu da ‘yan’uwansu bayin Allah, ba sa cin amanar da take kansu. Hakanan suna kula da duk wata yarjejeniya da za a ƙulla da su, suna sauke nauyinsu ba tare da sun karya ta ba. <b>Ta shida </b>, su ne masu kiyaye sallolinsu na farilla, suna yin su a kai-a kai tare da suna kula da lokutansu da rukunansu da wajibansu har ma da mustahabbai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: Ya Manzon Allah, wanne aiki ne Allah ya fi so? Sai ya ce: “Yin salla a kan lokacinta.” Sai na ce: “Sannan wanne?” Sai ya ce: “Biyayya ga iyaye.” Sai na ce: “Sannan wanne?” Sai ya ce: “Jihadi a tafarkin Allah.” [Bukhari #5970 da Muslim #85]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci sakamakon da ya tanadar wa waɗannan muminai a ranar alƙiyama, da cewa su ne waɗanda za su gaji Aljannar Firdausi wadda ita ce mafi ɗaukakar gidan Aljanna, za su kuma dawwama a cikinta har abada cikin ni’imar da ba ta yankewa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan za ku roƙi Allah Aljanna to ku roƙe shi Aljannar Firdausi domin ita ce mafi ƙololuwar Aljanna, mafi darajar Aljanna; daga cikinta ne ƙoramun Aljanna suke ɓuɓɓugowa, a samanta kuma Al’arshin Allah Mai rahama yake.” [Bukhari #2790]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani daga cikinku face yana da gida biyu; gida a Aljanna da kuma gida a wuta; to idan ya mutu ya shiga wuta sai ‘yan Aljanna su gaje gidansa na Aljanna, wannan ita ce faɗar Allah: “Waɗannan su ne magada.” [Ibn Majah #4341]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Allah (Mai tsarki da daukaka) ya halicci Aljanna da tubalin zinare da na azurfa, ya kuma shuke ta, sannan ya ce mata: “Yi magana.” Sai ta ce: “Haƙiƙa muminai sun rabauta.” Sai mala’iku suka shiga cikinta suka ce: “Kin ji daɗinki, kin zama masaukin sarakuna.” [Albazzar, dubi Kashful Astar #3507].
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن سُلَٰلَةٖ مِّن طِينٖ
Open ayah 23:12Kuma haƙiƙa Mun halicci mutum daga tataccen taɓo.
ثُمَّ جَعَلۡنَٰهُ نُطۡفَةٗ فِي قَرَارٖ مَّكِينٖ
Open ayah 23:13Sannan Muka mai da shi maniyyi cikin wuri amintacce.
ثُمَّ خَلَقۡنَا ٱلنُّطۡفَةَ عَلَقَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡعَلَقَةَ مُضۡغَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡمُضۡغَةَ عِظَٰمٗا فَكَسَوۡنَا ٱلۡعِظَٰمَ لَحۡمٗا ثُمَّ أَنشَأۡنَٰهُ خَلۡقًا ءَاخَرَۚ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ أَحۡسَنُ ٱلۡخَٰلِقِينَ
Open ayah 23:14Sannan Muka mayar da maniyyin ya zama gudan jini, sai gudan jinin ya zama tsoka, sai Muka mai da tsokar ƙasusuwa, sannan Muka lulluɓe ƙasusuwan da nama, sannan kuma Muka mai da shi wata halitta daban. To albarkatun Allah sun yawaita,Wanda Shi ne Mafi gwanintar masu halitta.
ثُمَّ إِنَّكُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ
Open ayah 23:15Sannan kuma lalle tabbas bayan haka za ku mutu.
ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تُبۡعَثُونَ
Open ayah 23:16Sannan kuma haƙiƙa za a tashe ku ranar alƙiyama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana asalin halittar ɗan’adam na farko, watau Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya halicce shi da yumɓu, wanda aka ɗebo tatacciyar ƙasarsa da ta gauraya da ruwa. Sannan kuma Allah ya halicci zurriyyarsa masu hayayyafa ta hanyar ɗigon maniyyi da yake sauka cikin mahaifa ya tabbata cikinta har zuwa lokacin haihuwa. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa daga wannan ɗigon maniyyin ne ya halicci wani gudan jini, sannan ya halicci wata tsokar nama wadda take gwargwadon loma daga wannan gudan jinin, sannan kuma daga wannan tsokar ya halicci ƙasusuwa masu ƙarfi, sai kuma ya lulluɓe waɗannan ƙasusuwa da nama, sannan sai ya mayar da shi wata halitta daban ta hanyar busa masa rai da fito da shi duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa kansa kirari da cewa, albarkatunsa sun yawaita, kuma shi ne mafi gwanintar masu halitta. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah mai gaskiya abin gaskatawa ya faɗa mana cewa: “Lalle ɗayanku ana tattara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwana arba’in (watau yana maniyyi), sannan ya zama jini kwatankwacin haka, sannan ya zama tsoka kamar haka, sannan Allah ya aiko wani mala’ika ya ba shi umarni guda huɗu, a ce masa, rubuta aikinsa da arziƙinsa da ajalinsa, ɗan wuta ne shi ko ɗan Aljanna, sannan a busa masa rai....” [Bukhari #3208 da Muslim #2643]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah mai girma da buwaya ya wakilta wa mahaifa wani mala’ika yana cewa: “Ya Ubangijina maniyyi ne, ya Ubangijina gudan jini ne, ya Ubangijina gudar tsoka ce.” Idan Allah ya nufi ya cika halittarsa, sai mala’ikan ya tambaya cewa: Namiji ne shi ko mace? Ɗan wuta ne shi ko ɗan Aljanna? Kuma mene ne arziƙinsa da ajalinsa? Sai duk a rubuta su yana cikin mahaifiyarsa.” [Bukhari #318 da Muslim #2646]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutane cewa bayan duk sun gama bin waɗannan matakan halitta, to za su kuma mutu yayin da ajalinsu ya zo, sannan kuma bayan mutuwa tabbas za a tashe su daga ƙaburburansu a ranar alƙiyama domin a yi musu hisabi a kan ayyukansu masu kyau da marasa kyau.
وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعَ طَرَآئِقَ وَمَا كُنَّا عَنِ ٱلۡخَلۡقِ غَٰفِلِينَ
Open ayah 23:17Kuma haƙiƙa Mun halicci hanyoyi bakwai a sama da ku, ba Mu kuma zama gafalallu ba game da halittar.
وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَسۡكَنَّٰهُ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابِۭ بِهِۦ لَقَٰدِرُونَ
Open ayah 23:18Muka kuma saukar da ruwa daga sama daidai gwargwado, sai Muka zaunar da shi a cikin ƙasa, kuma lalle Mu Masu iko ne a kan kawar da shi.
فَأَنشَأۡنَا لَكُم بِهِۦ جَنَّٰتٖ مِّن نَّخِيلٖ وَأَعۡنَٰبٖ لَّكُمۡ فِيهَا فَوَٰكِهُ كَثِيرَةٞ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 23:19Sai Muka samar muku gonaki na dabinai da inabai da shi (ruwan), kuna kuma da kayan marmari masu yawa a cikinsu (gonakin), kuma daga gare su kuke ci.
وَشَجَرَةٗ تَخۡرُجُ مِن طُورِ سَيۡنَآءَ تَنۢبُتُ بِٱلدُّهۡنِ وَصِبۡغٖ لِّلۡأٓكِلِينَ
Open ayah 23:20Kuma (Mun halitta muku) wata bishiya da take fitowa a (dutsen) Ɗuri Sina’a, tana fito da man (zaitun) kuma mahaɗin abinci ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu dalilai masu nuna ƙarfin ikonsa da cikar Ƙudurarsa a kan aikata abin da ya ga dama, daga cikinsu har da rayar da matattu. Ya bayyana wa mutane cewa shi ne ya halicci sammai bakwai a samansu, kuma yana sane da komai da ya halitta, bai zama mai gafala game da su ba ko mai mantuwa. Sannan kuma shi ne ya saukar da ruwan sama gwargwadon buƙata, bai yi yawan da zai haddasa ɓarna ba, bai kuma yi kaɗan ba har ya kasa isa, Allah kuma ya tabbatar da shi a kan ƙasa domin mutane su amfana da shi, su sha su shayar da dabbobinsu. Sannan ya tabbatar musu cewa yana da ikon ya tafiyar da shi daga doron ƙasa ba tare da sun amfana da shi ba. Kuma da wannan ruwa ne ya fitar musu da gonaki na itatuwan dabino da na inabi. Baya ga wannan gonakin suna cike da kayan marmari iri-iri kamar ɓaure da rumman da tuffa waɗanda suke ci idan sun yi marmari. Har wa yau da wannan ruwan ne dai ya fitar musu da itaciyar zaitun wadda take fitowa a yankin dutsen Ɗuri Sina’a; a jikinta ake samun man zaitun wanda ake shafawa kuma ana haɗa miyar abinci da shi.
وَإِنَّ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَنۡعَٰمِ لَعِبۡرَةٗۖ نُّسۡقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهَا وَلَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ كَثِيرَةٞ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 23:21Kuma lalle akwai izina a gare ku game da dabbobin ni’ima; Muna shayar da ku daga abin da yake cikinsu, kuma kuna da amfani mai yawa daga gare su, daga gare su kuma kuke ci.
وَعَلَيۡهَا وَعَلَى ٱلۡفُلۡكِ تُحۡمَلُونَ
Open ayah 23:22A kansu da kuma a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana dalilan Ƙudurarsa da cikar ikonsa, da cewa, a tare da dabbobin ni’ima, watau raƙuma da shanu da tumaki da awaki, akwai izina da ƙarfafan dalilai masu nuna ƙarfin Ƙudurar Allah da tausayawarsa gare su, ya kuma bayyana musu cewa yana shayar da su tataccen nono daga abin da yake cikinsu mai daɗin kwankwaɗa ga masu sha, sannan kuma suna samun amfani mai yawa daga waɗannan dabbobi, kamar na hawa da ɗora musu kaya da amfani da gashinsu da fatunsu, sannan kuma su ci namansu. Haka kuma a tafiye-tafiyensu a kan ƙasa suna hawan irin su raƙuma, a ruwa kuwa su hau jiragen ruwa tare da kayayyakinsu na fatauci. Watau dai ya kamata su fahimci cewa wanda ya yi musu waɗannan ni’imomi daban-daban lalle ya cancanci godiya da yabo, ya kuma cancanci a bauta masa shi kaɗai.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 23:23Haƙiƙa kuma Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta in ba Shi ba; me ya sa ne ba za ku yi taƙawa ba.”
فَقَالَ ٱلۡمَلَؤُاْ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ مَا هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُرِيدُ أَن يَتَفَضَّلَ عَلَيۡكُمۡ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَنزَلَ مَلَٰٓئِكَةٗ مَّا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِيٓ ءَابَآئِنَا ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 23:24Sai manya-manyan da suka kafirce daga mutanen nasa suka ce: “Ai wannan ba kowa ba ne face mutum irinku, yana so ne ya samu fifiko a kanku, kuma da Allah Ya ga dama da sai Ya saukar da mala’iku, mu ba mu taɓa jin irin wannan ba daga iyayenmu na farko.
إِنۡ هُوَ إِلَّا رَجُلُۢ بِهِۦ جِنَّةٞ فَتَرَبَّصُواْ بِهِۦ حَتَّىٰ حِينٖ
Open ayah 23:25“Ba kowa ba ne shi in ban da mutum da yake da (taɓin) aljan, sai ku saurara masa har zuwa wani ɗan lokaci.”
قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي بِمَا كَذَّبُونِ
Open ayah 23:26Ya ce: “Ubangijina Ka taimake ni game da abin da suka ƙaryata ni a kansa.”
فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ أَنِ ٱصۡنَعِ ٱلۡفُلۡكَ بِأَعۡيُنِنَا وَوَحۡيِنَا فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ فَٱسۡلُكۡ فِيهَا مِن كُلّٖ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ مِنۡهُمۡۖ وَلَا تُخَٰطِبۡنِي فِي ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِنَّهُم مُّغۡرَقُونَ
Open ayah 23:27Sai Muka yiwo masa wahayi cewa: “Ka sassaƙa jirgin ruwa a ƙarƙashin kulawarmu da umarninmu, sannan idan umarninmu (na hallaka su) ya zo, kuma tanderu ya ɓuɓɓugo da ruwa, sai ka saka ma’aurata guda biyu daga kowane jinsi a cikinsa, da kuma iyalanka, sai wanda kalmar (halaka) ta rigaya a kansa daga cikinsu; kuma kada ka ce min komai game da waɗanda suka kafirta; lalle su waɗanda za a nutsar ne.
فَإِذَا ٱسۡتَوَيۡتَ أَنتَ وَمَن مَّعَكَ عَلَى ٱلۡفُلۡكِ فَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي نَجَّىٰنَا مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 23:28“To idan kai da waɗanda suke tare da kai kuka daidaita a kan jirgin, sai ka ce: “Na gode wa Allah wanda Ya tserar da mu daga mutane azzalumai.”
وَقُل رَّبِّ أَنزِلۡنِي مُنزَلٗا مُّبَارَكٗا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡمُنزِلِينَ
Open ayah 23:29Kuma ka ce: “Ubangijina Ka saukar da ni masauki mai albarka, Kai ne kuwa Fiyayyen masu saukarwa.”
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ وَإِن كُنَّا لَمُبۡتَلِينَ
Open ayah 23:30Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi, Mu kuma haƙiƙa Mun kasance Masu jarrabawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya aika Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa ga mutanensa domin ya kirawo su zuwa ga Allah, ya umarce su da su bauta wa Allah shi kaɗai kuma ba su da wani abin bauta na gaskiya sai shi kaɗai, ya nuna musu cewa yanzu ba sa kiyaye dokokin Allah ba, su bi umarninsa su guji haninsa? Amma sai manya-manyan garin waɗanda suka kafirce wa Allah daga cikin mutanensa suka fito suna hure wa mabiyansu kunne, suna nuna musu cewa Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) fa ba wani ba ne, shi ma mutum ne irinsu, kuma wannan wa’azi da yake yi musu ba wani abu yake so ba illa kawai ya shugabance su ya mayar da su ƙarƙashinsa sai yadda ya ce. Suka nuna musu cewa da Allah ya ga damar aiko da wani manzo to da sai ya aiko da mala’ika ba mutum ba irinsu. Sannan suka nuna musu cewa wannan abu da ya zo da shi ba su taɓa jin labarin wani abu mai kama da shi ba a wajen iyayensu na farko. Ba su tsaya iya nan ba, sai da suka kai ga tuhumar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da hauka da ma rashin sanin abin da yake faɗa. Sannan suka kirawo mutane cewa su zura masa ido har zuwa lokacin da asirinsa zai tonu, ko kuma ya mutu kowa ya huta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ɗaga hannu ya roƙe shi cewa ya kawo masa agaji da taimako a kan mutanensam saboda sun ƙaryata shi, bayan ya ɗauki dogon lokaci yana yi musu wa’azi ba dare ba rana har shekara dubu ba hamsin amma ‘yan kaɗan ne ƙwarai suka yi imani da shi a cikinsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa wahayi da ya sassaƙa jirgin ruwa a ƙarƙashin kulawarsa (Mai tsarki da daukaka) da koyarwarsa gare shi yadda zai yi sassaƙar. Allah kuma ya sanar da shi cewa idan umarninsa na hallaka mutanensa ya zo masa ya kuma ga ruwa ya fara ɓuɓɓugowa daga cikin tanderu, to ya yi hanzari ya ɗauki namiji da mace daga duk wani abu mai rai don su ci gaba da hayayyafa, ya kuma haɗa har iyalansa cikin wannan jirgin in ban da wanda kalmar hallaka ta riga ta tabbata a kansa, watau matarsa da ɗansa. Sannan Allah ya yi masa kashedi da kada ya kuskura ya yi masa magana a kan waɗanda suka kafirta ya nemi a kuɓutar da su. Su waɗannan Allah ya tabbatar masa za a nutsar da su ne a cikin wannan ruwa na Ɗufana. Sai kuma ya koyar da shi abin da zai faɗa shi da waɗanda ya ɗauko a cikin wannan jirgin bayan sun hau sun daidaita a kansa, da cewa: “Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya tserar da mu daga mutane azzalumai.” Sannan ya roƙi Allah Ubangijinsa ya saukar da shi masauki mai albarka a bayan ƙasa, domin Allah shi ne fiyayyen masu ba da masauki. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a cikin wannan aiki nasa na tserar da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da muminai da hallaka kafirai a cikin ruwa lalle akwai hujjoji bayyanannu da suke nuna Ƙudurar Allah wajen taimakon manzanninsa da hallaka masu ƙaryata su. Ya kuma tabbatar da cewa lalle ya jarrabi mutanen Annabi Nuhu da aiko musu shi da ya yi domin a tantance mumini da kafiri, mai biyayya da bijirarre.
ثُمَّ أَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قَرۡنًا ءَاخَرِينَ
Open ayah 23:31Sannan kuma a bayansu Muka halicci wata al’umma daban.
فَأَرۡسَلۡنَا فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 23:32Sai Muka aiko musu wani manzon daga cikinsu da cewa: “Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta in ba Shi ba; me ya sa ne ba za ku yi taƙawa ba?”
وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَتۡرَفۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا مَا هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يَأۡكُلُ مِمَّا تَأۡكُلُونَ مِنۡهُ وَيَشۡرَبُ مِمَّا تَشۡرَبُونَ
Open ayah 23:33Kuma manyan mutane daga cikin mutanensa waɗanda suka kafirce suka kuma ƙaryata haɗuwa da ranar lahira, Muka kuma wadata su a rayuwar duniya, suka ce: “Wannan ba kowa ba ne face mutum kamarku, yana cin irin abin da kuke ci, yana kuma shan irin abin da kuke sha.
وَلَئِنۡ أَطَعۡتُم بَشَرٗا مِّثۡلَكُمۡ إِنَّكُمۡ إِذٗا لَّخَٰسِرُونَ
Open ayah 23:34“Kuma tabbas in har kuka bi mutum kamarku, to lalle tabbas a sannan kun yi asara.
أَيَعِدُكُمۡ أَنَّكُمۡ إِذَا مِتُّمۡ وَكُنتُمۡ تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَنَّكُم مُّخۡرَجُونَ
Open ayah 23:35“Shin yanzu ya riƙa yi muku alƙawarin cewa idan kun mutu kun kuma zama turɓaya da ƙasusuwa cewa lalle za a tashe ku?”
۞هَيۡهَاتَ هَيۡهَاتَ لِمَا تُوعَدُونَ
Open ayah 23:36“Faufau-faufau game da abin da ake yi muku alƙawarinsa!
إِنۡ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا نَمُوتُ وَنَحۡيَا وَمَا نَحۡنُ بِمَبۡعُوثِينَ
Open ayah 23:37“Ba mu da wata (rayuwa) sai rayuwarmu ta duniya; mu mutu kuma mu rayu, ba kuwa za a tashe mu (daga ƙaburburanmu) ba.
إِنۡ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا وَمَا نَحۡنُ لَهُۥ بِمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 23:38“Shi ba kowa ba ne face mutum da ya ƙaga wa Allah ƙarya, mu kuwa ba za mu yi imani da shi ba.”
قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي بِمَا كَذَّبُونِ
Open ayah 23:39Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka taimake ni game da abin da suke ƙaryata ni a kansa.”
قَالَ عَمَّا قَلِيلٖ لَّيُصۡبِحُنَّ نَٰدِمِينَ
Open ayah 23:40Ya ce: “Ba da daɗewa ba tabbas za su wayi gari suna masu nadama.”
فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ بِٱلۡحَقِّ فَجَعَلۡنَٰهُمۡ غُثَآءٗۚ فَبُعۡدٗا لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 23:41Sai tsawa ta far musu bisa cancanta, sai Muka mai da su dudduga. To nisanta (daga rahamar Allah) ta tabbata ga mutane azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan ya hallakar da mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kuma samar da wata al’umma daban, ita ma ya aiko mata da wani manzo wanda ya kirawo su zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, kuma su ji tsoron Allah su kiyaye dokokinsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, manya masu faɗa a ji daga cikin mutanensa waɗanda suka kafirce wa Allah suka ƙaryata zuwan ranar lahira da abin da yake cikinta na sakamako da uƙuba, kuma har ila yau abin da suke rayuwa a cikinsa na jin daɗin duniya da arziƙi da Allah ya ba su ya ƙara musu ɗagawa da girman kai, sai suka fito suna faɗa wa mabiyansu cewa kada su saurari wannan manzon da abin da yake faɗa musu, domin shi ba kowa ba ne face mutum kamarsu, yana cin irin abincin da suke ci yana shan irin abin da suke sha, don haka bai fi su da komai ba balle ma har a ce an naɗa shi manzo an aiko shi wajensu. Suka yi musu kashedi da cewa idan har suka kuskura suka bi shi suka yarda da shi bayan shi mutum ne kamarsu, to lalle sun tabbata hasararru, domin babu wata tsiya da zai tsinana musu, ga shi kuma sun bar bautar allolinsu. Suka ci gaba da nuna wa mabiyansu cewa, wannan da yake cewa shi manzo ne yana faɗa musu abin da hankalinsu ba zai taɓa gamsuwa da shi ba. Ta ƙaƙa zai riƙa yi musu alƙawarin cewa idan sun mutu sun ratattake sun zama ƙasa da ƙasusuwa rududdugaggu, wai za a sake tayar da su da rai? Suka nuna cewa sam-sam wannan batu ba zai taɓa zama gaskiya ba, don haka alƙawarin da yake yi musu ƙanzon kurege ne kawai. Suka hure musu kunnuwa da cewa babu wata rayuwa bayan ta duniya, masu rai daga cikinsu idan sun mutu to ba za a ƙara tashin su ba, waɗanda kuma aka haifa su ne za su ci gaba da rayuwa, kuma ba za a fito da su ba a yi musu hisabi bayan mutuwarsu. Sannan suka tuhume shi da cewa shi kawai mutum ne da ya ƙirƙira wa Allah ƙarya ya ce aiko shi ya yi, alhalin ba haka ne ba, don haka suka tabbatar da cewa su ba za su yi imani da shi ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da lamarin ya kai haka sai wannan manzo ya roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) da ya taimake shi ya hallakar da waɗannan mutane da suka ƙaryata shi. Allah kuwa ya amsa masa da cewa ba da daɗewa ba hallaka za ta zo musu, su wayi gari suna nadama a kan abin da suka aikata lokacin kuma da nadamar ba za ta amfane su da komai ba. Haka kuwa aka yi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da wata tsawa mai tsananin gaske ta hallaka su bisa cancanta, don haka suka wayi gari sun zama kamar duddugar ruwa. Allah ya bayyana cewa nisantar rahama ta tabbata ga waɗannan azzalumai. Wasu malamai sun ce waɗannan mutane su ne Samudawa mutanen Annabi Salihu, domin su ne waɗanda Allah ya hallakar da su da tsawa.
ثُمَّ أَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قُرُونًا ءَاخَرِينَ
Open ayah 23:42Sannan kuma a bayansu Muka halitta wasu al’ummun daban.
مَا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ
Open ayah 23:43Babu wata al’umma da take rigayar ajalinta, babu kuma wadda take jinkiri.
ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا تَتۡرَاۖ كُلَّ مَا جَآءَ أُمَّةٗ رَّسُولُهَا كَذَّبُوهُۖ فَأَتۡبَعۡنَا بَعۡضَهُم بَعۡضٗا وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَۚ فَبُعۡدٗا لِّقَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 23:44Sannan Muka aiko manzanninmu suna biye da juna; duk sanda manzon (kowacce) al’umma ya zo musu sai su ƙaryata shi. Sai Muka hallaka su ɗaya bayan ɗaya, Muka kuma mai da su tarihi. To nisanta (daga rahamar Allah) ta tabbata ga mutanen da ba sa yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan ya hallaka wasu al\'ummu da suka ƙaryata annabawansu, ya sake tayar da wasu al\'ummun daban kamar mutanen Annabi Luɗu da na Annabi Shu’aibu da na Annabi Yunus. A duk waɗannan al’ummu babu wata al’umma da za ta gabaci lokacin hallakarta, watau a hallakar da ita kafin lokacinta ya cika, ko kuma a jinkirta mata bayan wa’adinta ya yi. Watau da zarar lokacin hallaka su ya zo to sai a halaka su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya yi ta aiko manzanni ɗaya bayan ɗaya suna bibiyar juna, to amma abin takaicin duk sa’adda wani manzo ya zo ga mutanensa ya kirawo su zuwa ga kaɗaita Allah da bauta da nisantar bautar wanin Allah, sai wannan al’ummar su ƙaryata shi duk kuwa da irin ayoyi da mu’ujizoji da zai nuna musu. To wannan ya sa Allah ya riƙa hallaka su ɗaya bayan ɗaya har sai da aka wayi gari babu ko ɗaya daga cikinsu dukkansu sun zama tarihi, sai dai a ji labarinsu a bakin mutane, don haka hallaka ta tabbata ga mutanen da suka ƙi yin imani da abin da manzanninsu suka zo musu da shi daga Ubangijinsu.
ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَٰرُونَ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ
Open ayah 23:45Sannan Muka aiko Musa da ɗan’uwansa Haruna da ayoyinmu da kuma hujja bayyananniya.
إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمًا عَالِينَ
Open ayah 23:46Zuwa ga Fir’auna da manyan (\'yan majalisarsa), sai suka yi girman kai kuma suka kasance mutane masu haike wa (jama\'a da zalaunci).
فَقَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لِبَشَرَيۡنِ مِثۡلِنَا وَقَوۡمُهُمَا لَنَا عَٰبِدُونَ
Open ayah 23:47Sai suka ce: “Yanzu ma ba da gaskiya da mutum biyu irinmu, alhali kuwa mutanensu masu yi mana bauta ne?”
فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡلَكِينَ
Open ayah 23:48Sai suka ƙaryata su (wato Musa da Haruna), sannan suka kasance daga waɗanda aka hallaka.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ لَعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ
Open ayah 23:49Haƙiƙa kuma Mun bai wa Musa Littafi (wato Attaura) don su shiriya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya aiko Annabi Musa da Annabi Haruna (() da ayoyi masu nuna gaskiyar manzancinsu; ayoyin su ne: sanda da hannu mai haske da farin ɗango da ƙwarƙwata da kwaɗi da jini da ɗufana da fari da tawayar amfanin gona. Allah kuma ya ba su hujja bayyananna. Allah ya aike su zuwa ga Fir’auna da manyan mutanensa, to amma sai suka yi girman kai suka ƙi ba da gaskiya da su. Allah ya tabbatar da cewa da man can mutane ne masu nuna ɗagawa ga sauran mutane da zalunci da cutarwa. Saboda nuna isarsu ma cewa suka yi, ta yaya ma za su yi imani da wasu mutane biyu, watau Musa da Haruna (() waɗanda su ma kamarsu suke ba su fi su da komai ba, sannan ga mutanensu, watau Banu Isra’ila bayinsu ne a ƙarƙashinsu suke bauta. Don haka sai suka ƙaryata su, hakan kuma ya zama sanadiyyar hallaka su cikin kogi duk suka nutse. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan ya hallaka Fir’auna da rundunarsa ya kuma kuɓutar da Annabi Musa da mutanensa sai kuma ya ba shi littafin Attaura da fatan mutanensa su shiriya da shi su yi aiki da gaskiyar da ya ƙunsa.
وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةٗ وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٖ ذَاتِ قَرَارٖ وَمَعِينٖ
Open ayah 23:50Muka kuma sanya Ɗan Maryamu da mahaifiyarsa (don su zama) aya, Muka kuma zaunar da su a wata jigawa ta hutawa da kuma ruwa mai gudana.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلرُّسُلُ كُلُواْ مِنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَٱعۡمَلُواْ صَٰلِحًاۖ إِنِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ
Open ayah 23:51Ya ku manzanni, ku ci daga halal, kuma ku yi aiki na gari; Lalle Ni ina sane da abin da kuke aikatawa.
وَإِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱتَّقُونِ
Open ayah 23:52Kuma lalle wannan addininku ne, addini guda ɗaya (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, sai ku kiyaye dokokina.
فَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡ زُبُرٗاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ
Open ayah 23:53Sai suka sassaɓa al’amarinsu a tsakaninsu (suka kasu) ƙungiya-ƙungiya; kowacce ƙungiya tana alfahari da nata.
فَذَرۡهُمۡ فِي غَمۡرَتِهِمۡ حَتَّىٰ حِينٍ
Open ayah 23:54Sai ka bar su cikin ɗimuwarsu har zuwa ɗan wani lokaci.
أَيَحۡسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُم بِهِۦ مِن مَّالٖ وَبَنِينَ
Open ayah 23:55Yanzu suna tsammanin cewa abin da Muke ba su na dukiya da ‘ya’yaye (a duniya).
نُسَارِعُ لَهُمۡ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ بَل لَّا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 23:56Muna gaggauto musu sakamakon alheri ne? Ba haka ba ne; su dai ba sa ganewa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya sanya Annabi Isa da mahaifiyarsa Maryamu (() su zama aya wadda take nuna cikar Ƙudurarsa ta ya halicci abin da ya ga dama, a yadda ya ga dama, don haka Nana Maryamu ta ɗauki cikin Annabi Isa ba tare da namiji ba. Allah ya bayyana cewa ya zaunar da Annabi Isa da mahaifiyarsa a kan wata jigawa ma’abociyar wurin hutu da nutsuwa, wadda kuma take da wani idon ruwa mai kwarara koyaushe. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci manzanni da cin halal mai daɗi da kuma yin ayyuka na gari waɗanda suka yi daidai da shari’a, ya kuma tabbatar musu da cewa yana sane da aikin kowa daga cikinsu kuma zai yi wa kowa sakayya a kan ayyukansa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane, lalle Allah tsattsarka ne ba ya karɓar wani aiki sai tsarkakakke, kuma lalle Allah ya umarci muminai da abin da ya umarci manzanni da shi. Allah ya ce: “Ya ku manzanni, ku ci daga tsarkakan abubuwa na halal, kuma ku yi aiki na gari, lalle ni ina sane da abin da kuke aikatawa.” Ya kuma ce: “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku ci daga tsarkakan abubuwa na halal da muka arzuta ku.”… [Muslim #1015]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani annabi da bai yi kiwon dabbobi ba.” Sahabbai suka ce: “Har kai ma ya Manzon Allah?” Ya ce: “Na’am, na kasance ina yi wa mutanen Makka kiwon dabbobi suna biya na wasu ‘yan kuɗaɗe.” [Bukhari #2262]. An karɓo daga Miƙdam (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani wanda zai ci abin da ya fi wanda ya nema ta sana’ar hannunsa, kuma lalle Annabin Allah Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kasance yana cin abincin da ya nema ta sana’ar hannunsa.” [Bukhari #2072]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da manzanni cewa dukkansu addininsu guda ne, watau kira zuwa ga bautar Allah shi kaɗai, kuma Allah ne Ubangijinsu ba su da wani Ubangiji ba shi ba, don haka ya umarce su su kiyaye dokokinsa su aikata abin da ya umarce su da shi su guje wa abin da ya hane su. Allah kuma ya bayyana cewa duk da wannan haɗin kai da ke tsakanin manzannin Allah da gamuwarsu a kan tushen addini, watau Tauhidi, sai ga shi mabiyansu a bayansu sun rarraba a tsakaninsu a kan lamarin addini, sun zama ƙungiya-ƙungiya, kowace ƙungiya tana alfahari da abin da ta kama a matsayin addinin Allah ba ruwanta da abin da sauran suke kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya fita harkarsu gaba ɗaya da abin da suke ciki na jahilci da ruɗu har zuwa lokacin da azaba za ta sauka a kansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya soke wani zaton banza da suke yi wa kansu na ganin cewa abin da ya ba su na dukiya da ‘ya’ya a rayuwar duniya ya gaggauto musu da wani alheri ne wanda suka cancance shi saboda matsayinsu a wurinsa. Allah ya tabbatar musu da cewa wannan zaton nasu ba gaskiya ba ne, Allah dai yana yi musu abin da yake musu ne a matsayin talala, to amma ba sa jin hakan ko a jikinsu, don haka suke wancan banzan zaton. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah ya raba muku halayyarku kamar yadda ya raba muku arzikinku, kuma lalle Allah yana bayar da duniya ga wanda yake so da wanda ma ba ya so, to amma ba ya bayar da imani sai ga wanda yake so.” [Alhakim juzu’i na 1, shafi na 348-349 da Al-Albani, As-Sahiha # 2714].
إِنَّ ٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ خَشۡيَةِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ
Open ayah 23:57Lalle waɗanda su suke cike da tsoron Ubangijinsu.
وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 23:58Kuma waɗanda suke imani da ayoyin Ubangijinsu.
وَٱلَّذِينَ هُم بِرَبِّهِمۡ لَا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 23:59Kuma waɗanda ba sa shirka da Ubangijinsu.
وَٱلَّذِينَ يُؤۡتُونَ مَآ ءَاتَواْ وَّقُلُوبُهُمۡ وَجِلَةٌ أَنَّهُمۡ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ رَٰجِعُونَ
Open ayah 23:60Kuma waɗanda suke ba da abin da suka bayar (na ayyukan kirki), alhali kuwa zukatansu suna tsorace, don kuwa lalle su masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu.
أُوْلَٰٓئِكَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَهُمۡ لَهَا سَٰبِقُونَ
Open ayah 23:61Waɗannan su ne suke gaggawa ga ayyukan alheri, suna kuma masu rige-rige gare su. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffofin bayinsa masu gaggawa wajen ayyukan alheri zaɓaɓɓu a wurinsa, da cewa su ne masu siffofi kamar haka: <b>Na ɗaya </b>, su ne waɗanda suke cike da tsoron Ubangijinsu duk kuwa da cewa sun yi imani da shi sun kuma kyautata ayyukansu. <b>Na biyu </b>, su ne waɗanda suke yin imani da ayoyin littafin Ubangijinsu yayin da suka ji ana karanta musu su. <b>Na uku </b>, su ne waɗanda suke kaɗaita Ubangijinsu ba sa shirka da shi; shirka ta bayyane ko ta ɓoye, ƙarama ko babba. <b>Na huɗu </b>, su ne waɗanda suke matuƙar ƙoƙari wajen aikata alheri suke kusantar Allah da aikata kyawawan ayyuka, to amma suna cike da tsoron ko za a karɓa ko ba za a karɓa ba yayin da suka koma ga Allah ranar alƙiyama. Sai Allah ya tabbatar da cewa waɗannan da suka siffantu da waɗannan kyawawan siffofi su ne waɗanda suke gaggawa wajen ayyukan alheri, suke rigegeniya a junansu kuma su ne suka yi fintinkau babu mai iya cim musu sai wanda zai yi aiki irin nasu.
وَلَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ وَلَدَيۡنَا كِتَٰبٞ يَنطِقُ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 23:62Ba Ma kuwa ɗora wa kowane rai wani abu sai wanda zai iya. Kuma a wurinmu akwai littafi da yake furuci da gaskiya, kuma su ba za a zalunce su ba.
بَلۡ قُلُوبُهُمۡ فِي غَمۡرَةٖ مِّنۡ هَٰذَا وَلَهُمۡ أَعۡمَٰلٞ مِّن دُونِ ذَٰلِكَ هُمۡ لَهَا عَٰمِلُونَ
Open ayah 23:63A’a, ba haka ba ne, zukatansu dai suna cikin gafala daga wannan (littafi mai furta gaskiya), suna kuma da wasu ayyukan ban da waɗannan waɗanda suke aikatawa.
حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذۡنَا مُتۡرَفِيهِم بِٱلۡعَذَابِ إِذَا هُمۡ يَجۡـَٔرُونَ
Open ayah 23:64Har yayin da Muka kama mawadatansu da azaba sai ga su suna kururuwa.
لَا تَجۡـَٔرُواْ ٱلۡيَوۡمَۖ إِنَّكُم مِّنَّا لَا تُنصَرُونَ
Open ayah 23:65(Sai a ce da su): “Kada ku yi kururuwa a yau; lalle ku ba za a kare ku ba daga gare Mu.
قَدۡ كَانَتۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَكُنتُمۡ عَلَىٰٓ أَعۡقَٰبِكُمۡ تَنكِصُونَ
Open ayah 23:66“Haƙiƙa ayoyina sun kasance ana karanta muku su, sai kuka zamanto kuna komawa da baya.
مُسۡتَكۡبِرِينَ بِهِۦ سَٰمِرٗا تَهۡجُرُونَ
Open ayah 23:67“Kuna masu girman kai (na ƙin imani) a wurinsa (Ɗakin Ka’aba), kuna masu hira, kuna ɓata (Alƙur’ani).”
أَفَلَمۡ يَدَّبَّرُواْ ٱلۡقَوۡلَ أَمۡ جَآءَهُم مَّا لَمۡ يَأۡتِ ءَابَآءَهُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 23:68Me ya sa ne ba su yi zuzzurfan tunani ba game da Alƙur’ani, ko kuwa wani abu ne ya zo musu da bai zo wa iyayensu na farko ba?
أَمۡ لَمۡ يَعۡرِفُواْ رَسُولَهُمۡ فَهُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ
Open ayah 23:69Ko kuwa ba su san Manzonsu ba ne, don haka ba su tantance da shi ba?
أَمۡ يَقُولُونَ بِهِۦ جِنَّةُۢۚ بَلۡ جَآءَهُم بِٱلۡحَقِّ وَأَكۡثَرُهُمۡ لِلۡحَقِّ كَٰرِهُونَ
Open ayah 23:70Ko kuwa cewa suke yi ya taɓu? A\'a, ya zo musu ne da gaskiya, sai dai yawancinsu masu ƙin gaskiya ne.
وَلَوِ ٱتَّبَعَ ٱلۡحَقُّ أَهۡوَآءَهُمۡ لَفَسَدَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ بَلۡ أَتَيۡنَٰهُم بِذِكۡرِهِمۡ فَهُمۡ عَن ذِكۡرِهِم مُّعۡرِضُونَ
Open ayah 23:71Da kuma Alƙur’ani ya biye ma son ransu, to da lallai sammai da ƙasa da abin da yake cikinsu duka sun lalace. A’a, Mun dai zo musu ne da abin alfaharinsu, amma kuma suna masu bijire wa abin alfaharin nasu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ba ya ɗora wa wani mutum wani abu sai abin da zai iya ɗauka. Ya tabbatar da cewa a wajensa akwai wani littafi wanda ya tabbatar wa kowa aikinsa, wannan littafi yana furta gaskiyar da babu wani kokwanto game da ita. Kuma za a yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa, babu wanda za a zalunta a kama shi da laifin da bai yi ba ko a yi masa ƙwauron ladansa. Sannan kuma Allah ya bayyana cewa zukatan kafirai suna cikin gafala ba sa tuna wannan littafi mai furta gaskiya, hakanan ba sa tuna littafin da aka saukar musu na shari’a, baya ga kafircinsu suna da wasu miyagun ayyukan da suke aikatawa, don haka kada su yi mamakin yadda Allah ya jinkirta azabtar da su; ya yi musu haka ne domin su ci gaba da aikata sauran ayyukansu miyagu har su cancanci mummunar azabar Allah da take jiran su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin azabar da take jiran su a ranar alƙiyama, lokacin da zai kama masu jin daɗinsu na duniya da azabarsa sai kawai a riƙa jin su suna kururuwa suna neman taimako. Sai a nuna musu cewa su fitar da tsammanin samun tsira daga azabar Allah a wannan rana, don haka su ma daina kururuwa da ihu domin ihunsu duk na banza ne babu wanda zai taimaka musu ya kuɓutar da su daga azabar Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa za a tunatar da su laifukansu na duniya waɗanda suka jefa su cikin wannan mawuyacin hali; da cewa a duniya an riƙa karanta musu ayoyin Allah, to amma sai suka riƙa noƙewa suna juya baya don ba sa son su saurare su. Suna aikata wancan laifi ne tare da nuna wa mutane girman kai da sunan wai su ne masu Masallaci mai alfarma, alhali ba su ne ba, domin ahalin wannan Masallaci su ne masu tsoron Allah. Hasali ma sukan haɗu da daddare a cikin Ka’aba suna hira suna faɗar miyagun maganganu game da Alƙur’ani da Manzo (ﷺ), don haka masu yin wannan mummunan aiki a jikin Ɗakin Ka’aba ai ba su tsarkake shi ba, ba su kuma ga girmansa yadda ya kamata ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa me ya hana waɗannan mushirikai su tsaya su yi dogon tunani dangane da Alƙur’ani irin wanda zai sanya su su yi imani da shi su yi aiki da karantarwarsa. Ko kuma dai wannan wani abu ne ya zo musu wanda bai zo wa iyayensu na farko ba, shi ya sa suka bijire masa suka ƙaryata shi, don su ci gaba da rayuwa a kan abin da iyayensu suka rayu a kai na kafirci da ɓata? Ko kuma abin da ya hana su yin imani shi ne ba su san Manzonsu Annabi Muhammadu (ﷺ) da aka aiko musu ba, don haka ba su tantance ko yana da gaskiya da amana ko ba ya da su? Haƙiƙa kam sun san komai sarai game da shi, su ne ma suke kiran sa mai gaskiya mai amana. Allah (Mai tsarki da daukaka.) ya bayyana muguwar maganar da suke faɗa game da Annabi (ﷺ) cewa wai yana da taɓin hankali. Babu shakka wannan ƙarya ce suke faɗa, su ma kuma sun san haka. Sun san ya zo musu ne da gaskiya wadda babu kokwanto a cikinta, to amma yawancinsu ba sa son gaskiya ne domin hassadar da take cikin zuciyarsu da ra’ayin riƙau a kan ɓarnarsu. Sai Allah ya bayyana cewa da a ce yana gudanar da al’amuransa ne yana tsara su daidai da son zuciyar kafirai, to da sammai da ƙasa duk sun lalace, waɗanda ma suke cikinsu duk sun lalace domin al’amuran za su riƙa wakana ne a bisa jahilci da zalunci, alhali kuma sama da ƙasa ba su tsaya ba sai da adalci da gaskiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa ya saukar musu da Alƙur’ani wanda ya ƙunshi wa’azi da abin da yake ɗaukaka da alfahari ne a gare su, to amma maimakon su riƙe shi su yi aiki da shi su samu ɗaukaka ta duniya da lahira, sai suka bijire masa suka ƙi imani da shi.
أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ خَرۡجٗا فَخَرَاجُ رَبِّكَ خَيۡرٞۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ
Open ayah 23:72Ko kuwa kana neman lada ne a wurinsu, to ladan Ubangijinka shi ya fi alheri; kuma Shi ne Fiyayyen masu arzutawa.
وَإِنَّكَ لَتَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 23:73Kuma lalle kai tabbas kana kiran su ne zuwa ga hanya madaidaiciya.
وَإِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ عَنِ ٱلصِّرَٰطِ لَنَٰكِبُونَ
Open ayah 23:74Lalle kuma waɗanda ba sa yin imani da lahira tabbas su masu bauɗewa ne daga hanya.
۞وَلَوۡ رَحِمۡنَٰهُمۡ وَكَشَفۡنَا مَا بِهِم مِّن ضُرّٖ لَّلَجُّواْ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ
Open ayah 23:75Da kuwa Mun ji ƙan su Mun kuma yaye musu cutar da take tare da su (ta fari), to tabbas da sun zarce cikin shisshiginsu suna fagamniya.
وَلَقَدۡ أَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡعَذَابِ فَمَا ٱسۡتَكَانُواْ لِرَبِّهِمۡ وَمَا يَتَضَرَّعُونَ
Open ayah 23:76Kuma haƙiƙa Mun kama su da azaba amma ba su miƙa wuya ga Ubangijinsu ba, ba sa kuma ƙasƙantar da kai.
حَتَّىٰٓ إِذَا فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابٗا ذَا عَذَابٖ شَدِيدٍ إِذَا هُمۡ فِيهِ مُبۡلِسُونَ
Open ayah 23:77Har dai yayin da Muka buɗe musu ƙofa mai matsananciyar azaba sai ga su cikinta suna masu yanke ƙauna (daga kowace rahama). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa shin ya nemi wani lada ne a wurin kafirai a kan abin da ya zo musu da shi, wanda haka ya sa suka ƙi yin imani da shi? Babu shakka bai taɓa neman wani lada a wurinsu ba. Don haka Allah ya tabbatar masa cewa ladan da Ubangiji zai ba shi ya fi na waɗannan kafiran, domin shi ne fiyayyen mai arzutawa. To me zai sa shi neman wani abu a wurinsu bayan wanda Allah zai ba shi? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Manzonsa kyakkyawar shaida ya tabbatar masa cewa lalle shi yana kiran mutane ne zuwa ga tafarki madaidaici wanda babu wata karkata a cikinsa, watau addinin Musulunci. To amma duk da haka kafirai da ba su yi imani da ranar lahira da sakamako ba, suna kauce wa wannan madaidaiciyar hanya ne wadda take kai duk wanda ya bi ta zuwa ga samun rahamar Ubangiji. Saboda tsananin taurin kan kafirai da dogewarsu a kan kafirci, Allah ya ambaci cewa, da a ce wata cuta ko musiba za ta faɗa musu su roƙi Allah ya yaye musu ita za su yi imani, idan ya yaye musu ita, to tabbas da sun doge a kan shisshiginsu da kafircinsu suna ta ɗimuwa da fagamniya a cikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya jarrabe su da nau’i iri-iri na musibu, to amma wannan bai sanya su sun ƙasƙantar da kansu gaban Allah ba, ba su koma suna bautar da miƙa wuya a gare shi ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Abu Sufyanu ɗan Harbu ya zo wurin Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Ina roƙon ka don Allah don kuma zumunci (watau ya yi musu addu’a Allah ya yaye musu musibar da ta auka musu), domin fa har ta kai yanzu mun shiga cin fatar raƙuma da jini.” Sai Allah ya saukar da wannan ayar ta 76. [Nasa’i, As-Sunanul Kubra #11289 da Ibn Hibban #967]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafirai ba za su bar wannan mummunan halin nasu ba har sai lokacin da zai buɗe musu ƙofar wata azaba mai tsanani wadda idan sun tsinci kawunansu a ciki za su ɗebe ƙauna daga samun kowane irin rangwame da mafita. Don haka su guji aikata abin da zai janyo musu irin wannan azabar wadda idan ta zo babu mai mayar da ita in ba Allah ba.
وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ
Open ayah 23:78Shi ne kuma (Allah) wanda Ya halitta muku ji da gani da kuma zukata. Kaɗan ƙwarai kuke gode wa (masa).
وَهُوَ ٱلَّذِي ذَرَأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
Open ayah 23:79Shi ne kuma wanda Ya halicce ku a bayan ƙasa, kuma zuwa gare Shi za a tattara ku.
وَهُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَلَهُ ٱخۡتِلَٰفُ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 23:80Kuma Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma sassaɓawar dare da rana nasa ne. Me ya sa ba kwa hankalta ne?
بَلۡ قَالُواْ مِثۡلَ مَا قَالَ ٱلۡأَوَّلُونَ
Open ayah 23:81A’a, sun dai faɗi irin abin da (mutanen) farko suka faɗa ne.
قَالُوٓاْ أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
Open ayah 23:82(Wato) sun ce: “Yanzu wai idan mun mutu kuma mun zama turɓaya da ƙasusuwa, anya za a kuwa tashe mu?
لَقَدۡ وُعِدۡنَا نَحۡنُ وَءَابَآؤُنَا هَٰذَا مِن قَبۡلُ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 23:83“Haƙiƙa mu da iyayenmu an yi mana alƙawarin wannan tun tuni, wannan ba wani abu ba ne in ban da tatsuniyoyin mutan da.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa masu ƙaryata tashi ranar alƙiyama cewa shi ne wanda ya halitta musu ji domin su amfana da shi a rayuwarsu ta duniya, su saurari duk abin da ya kamata su saurara da shi. Ya kuma halitta musu gani domin su riƙa gani da shi, ya kuma halitta musu zukata domin su fahimci abubuwa da su. To amma duk da haka ba sa yi wa Allah godiya a kan waɗannan ni’imomi da ya yi musu sai `yar kaɗan. Ya kuma daɗa tabbatar musu da cewa shi ne ya halicci mutane baki ɗaya a bayan ƙasa, kuma gare shi shi kaɗai za a tattara su a ranar alƙiyama don hisabi da sakamako. Kuma shi kaɗai ne yake rayawa yake kashewa kuma babu mai yin haka sai shi. Kuma shi ne kaɗai mai caccanza dare da rana, ya kawo wannan ya tafiyar da wannan, da ya ga dama da sai ya bar dare har abada ko ya bar rana har abada, babu kuma mai iya kawo su sai shi. Don haka ya ja hankalinsu da cewa, yanzu ba za su yi la’akari da wannan Ƙudurar tasa ba da yadda ya kaɗaita da halitta, su fahimci shi mai iko ne a kan komai har da tayar da su bayan sun mutu? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafirai masu ƙaryata zuwan alƙiyama, ba su yi aiki da hankalinsu ba sam-sam, kawai sun riƙa faɗar irin maganganun kafirci waɗanda magabatansu na farko suka riƙa faɗa, domin sun riƙa cewa, yanzu su idan sun mutu sun zama ƙasa da rududdugaggun ƙasusuwa shin lalle za a tashe su da ransu don a yi musu hisabi kamar yadda ake faɗa musu? Suka ce ba yanzu aka fara faɗa musu irin waɗannan maganganu ba, a’a, tun lokacin iyayensu su ma an yi musu alƙawari irin wannan kuma har zuwa yau babu abin da ya tabbata, don haka wannan magana tatsuniyar mutanen farko ce kawai babu ƙanshin gaskiya a cikinta.
قُل لِّمَنِ ٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهَآ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 23:84Ka ce (da su): “Ƙasa da abin da yake cikinta na Wane ne, idan kun kasance kun sani?”
سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 23:85Ai za ka ji sun ce: “Na Allah ne.” Ka ce (da su): “To me ya sa ba kwa wa’azantuwa ne?”
قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلسَّبۡعِ وَرَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 23:86Ka ce (da su): “Wane ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al’arshi mai girma?”
سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 23:87Ai za su ce: “Na Allah ne.” Ka ce (da su): “To me ya sa ba kwa taƙawa?”
قُلۡ مَنۢ بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُوَ يُجِيرُ وَلَا يُجَارُ عَلَيۡهِ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 23:88Ka ce (da su): “Wane ne mulkin komai yake a hannunsa, kuma Shi ne Yake kariya, (Shi) kuma ba a kare wani daga gare Shi, idan kun kasance kun sani?”
سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ فَأَنَّىٰ تُسۡحَرُونَ
Open ayah 23:89Ai za su ce: “Na Allah ne.” Ka ce (da su): “To ta ina ne ake tafiyar muku da hankalinku?”
بَلۡ أَتَيۡنَٰهُم بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 23:90A’a, Mun dai zo musu ne da gaskiya, su kuwa lalle tabbas maƙaryata ne.
مَا ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ مِن وَلَدٖ وَمَا كَانَ مَعَهُۥ مِنۡ إِلَٰهٍۚ إِذٗا لَّذَهَبَ كُلُّ إِلَٰهِۭ بِمَا خَلَقَ وَلَعَلَا بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Open ayah 23:91Allah bai riƙi wani ɗa ba, kuma babu wani abin bauta tare da Shi. (Da ko haka ta faru) to da kowanne abin bauta ya keɓanta da abin da ya halitta, da kuma wani ya yi rinjaye a kan wani. Allah Ya tsarkaka daga abin da suke sifanta (Shi da shi).
عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 23:92Shi ne Masanin ɓoye da sarari, to Ya ɗaukaka daga abin da suke shirka (da Shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tambayi kafirai masu musunta tashin alƙiyama cewa, ƙasa da halittun da suke kanta na wane ne, in sun sani su faɗa? Allah ya tabbatar da cewa za su amsa su ce na Allah ne shi kaɗai. Sai kuma ya umarce shi da ya ce musu me ya sa ba sa wa’azantuwa tun da sun san da haka, su yarda da cewa Allah yana da ikon ya tashe su da rai bayan sun mutu? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar sa da ya tambaye su wane ne Ubangijin sammai bakwai da Al’arshi mai girma wanda babu wata halitta da ta kai girmansa? Allah ya tabbatar da cewa za su amsa su ce dukkansu mulkin Allah ne shi kaɗai. To sai ya umarce shi da ya faɗa musu cewa, tun da sun san da haka me ya sa ba za su kiyaye dokokin Allah ba, su bauta masa kamar yadda ya umarce su, kuma su guji aikata abin da ya hana su? Har wa yau dai ya sake umartar sa da ya tambaye su cewa, wane ne wanda mulkin komai yake a hannunsa shi kaɗai, babu abin da ba ya ƙarƙashin ikonsa, shi ne kuma mai taimaka wa wanda ya ga dama daga cikin bayinsa ya kare shi daga duk abin da zai cutar da shi, amma shi babu wani mai iya ba wani kariya daga azabarsa ko ƙaddararsa? Ya kuma umarce su da su faɗa idan sun san akwai wani mai wannan ikon ban da Allah. Sai ya tabbatar da cewa za su amsa masa da cewa mulkin komai yana hannun Allah. To ya faɗa musu cewa, idan haka ne to ta ina ake karkatar musu da hankalinsu har suka yarda su bauta wa wasu gumaka ba Allah ba, ga shi kuma sun yi imani da cewa mulkin komai nasa ne shi kaɗai? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa al’amarin ba kamar yadda suke riyawa ba ne na cewa Allah ba zai iya tashin matattu ba, ya dai zo musu ne da gaskiyar da babu kokwanto a cikinta, kuma su maƙaryata ne kawai, suna yi wa Allah ƙaryar cewa yana da wani abokin tarayya tare da shi ko yana da ɗa ko mata. Sai ya tabbatar da cewa ba shi da wani ɗa kamar yadda kafirai suke riyawa, kuma babu wani abin bauta na gaskiya tare da shi, da a ce akwai shi kuwa, to da kowane abin bauta ya keɓanta da kasonsa na abin da ya halitta daga cikin halittu, kuma da kowanne ya nemi ya rinjayi ɗan’uwansa, watau ya fi ƙarfinsa ya ƙwace masa mulkinsa, wanda faruwar haka kuwa za ta jawo lalacewar tsarin gudanar duniya gaba ɗaya. To tun da kuwa hakan bai faru ba, wannan ya nuna abin bauta na gaskiya ɗaya ne shi ne Allah Maɗaukakin Sarki. Ya tsarkaka daga abin da mushirikai suke siffanta shi da shi na cewa yana da ɗa ko wani abokin tarayya. Allah ya tabbatar da cewa shi ne kaɗai masanin gaibu da abin da yake sarari, babu abin da yake ɓoye gare shi, don haka ya ɗaukaka daga abin da suke yi masa shirka da shi.
قُل رَّبِّ إِمَّا تُرِيَنِّي مَا يُوعَدُونَ
Open ayah 23:93Ka ce: “Ubangijina, idan Ka nuna min abin da ake yi musu alƙawari da shi (na azaba).
رَبِّ فَلَا تَجۡعَلۡنِي فِي ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 23:94“Ubangijina, kada Ka sanya ni cikin mutane azzalumai.”
وَإِنَّا عَلَىٰٓ أَن نُّرِيَكَ مَا نَعِدُهُمۡ لَقَٰدِرُونَ
Open ayah 23:95Mu kuma lalle Masu iko ne a kan Mu nuna maka abin da Muke musu alkawari.
ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ ٱلسَّيِّئَةَۚ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَصِفُونَ
Open ayah 23:96Ka ingije mummunan abu da wanda ya fi kyau. Mu ne Muka fi sanin abin da suke siffata (ka da shi).
وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنۡ هَمَزَٰتِ ٱلشَّيَٰطِينِ
Open ayah 23:97Kuma ka ce: “Ubangijina, ina neman tsarinka daga waswasin shaiɗanu.
وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحۡضُرُونِ
Open ayah 23:98“Ina kuma neman tsarinka Ubangijina kar su zo min.”
حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ رَبِّ ٱرۡجِعُونِ
Open ayah 23:99Har sai idan da mutuwa ta zo wa ɗayansu zai ce: “Ubangijina, Ku mai da ni (duniya) mana.
لَعَلِّيٓ أَعۡمَلُ صَٰلِحٗا فِيمَا تَرَكۡتُۚ كَلَّآۚ إِنَّهَا كَلِمَةٌ هُوَ قَآئِلُهَاۖ وَمِن وَرَآئِهِم بَرۡزَخٌ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
Open ayah 23:100“Don in yi aiki na gari game da abin da na bari (a rayuwata).” Ina! Lalle wannan kalma ce da yake faɗin ta (da bakinsa). A gabansu kuwa akwai shamaki har zuwa ranar tashinsu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ce, idan har Allah ya nuna masa abin da ya yi wa mushirikai alƙawarin aukuwarsa a kansu na azaba to ya roƙe shi da kada ya sanya shi daga cikin azzalumai, watau kada shi ma azabar ta same shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa yana da ikon ya nuna masa abin da ya yi wa kafirai alƙawarinsa na azaba, kuma babu abin da zai gagare shi. Sannan ya umarci Annabi (ﷺ) da ya mayar wa da wanda ya munana masa da kyakkyawan sakamako, watau ya yafe masa, ya kuma yi haƙuri a bisa cutarwarsa. Allah ya bayyana masa cewa shi ya fi sanin abin da kafirai suke siffanta Allah da shi na shirka da yadda suke ƙaryata shi, da kuma irin abin da suke siffanta Manzon Allah da shi na ce masa marar hankali ko matsafi ko mawaƙi ko boka. Allah kuma ya umarce shi ya nemi tsarin Allah daga waswasin shaiɗanu kuma ya tsare shi da kada su halarci kowane irin al’amarinsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana koyar da mu wasu kalmomi da za mu faɗa lokacin firgici, shi ne mu ce: “Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa da sharrin bayinsa daga kuma waswasin shaiɗanu da kuma kada su halarto ni.” [Abu Dawud #3893 da Tirmizi #3528 da Ahmad #6696]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da mutuwa ta zo ma ɗaya daga cikin mushirikai masu ƙaryata ranar sakamako, ya kuma ga abin da ke shirin faruwa gare shi, to a lokacin ne zai nuna nadamarsa yayin da nadama ba za ta amfane shi da komai ba; zai riƙa roƙon Ubangijinsa Allah cewa ya mayar da shi duniya wai don ya yi aiki na gari idan ya koma. To a nan ne za a tabbatar masa da cewa ya makara, abin da ya nema ba zai samu ba. Kuma wannan maganar yana dai yin ta ne da fatar bakinsa kawai, watau da za a mayar da shi duniya to ba zai cika alƙawarin da ya ɗauka ba na gyara ayyukansa. Sannan Allah ya bayyana cewa waɗanda suka mutu za su ci gaba da zama a cikin shamaki tsakanin rayuwar duniya da ta lahira har lokacin da za a tashe su ya zo, don haka ba za su koma gidan duniya ba don gyara abin da suka ɓata. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan aka sanya mamaci a cikin ƙabarinsa sai wasu mala’iku biyu baƙaƙe masu tsanwayen idanu ana kiran ɗayansu da suna Munkaru, ɗaya kuma Nakiru, sai su ce masa: “Me kake faɗa game da wannan mutumin (watau Annabi Muhammadu (ﷺ)?” Sai ya faɗi abin da ya kasance (a duniya) yana faɗa ya ce: “Shi bawan Allah ne kuma Manzonsa, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa.” Sai su ce: “Da man mun san haka kake faɗa.” Sannan sai a faɗaɗa masa ƙabarinsa zira’i saba’in, sannan a haskaka masa shi, sannan a ce masa: “Kwanta ka yi barcinka.” Sai ya ce: “A bar ni in koma zuwa ga iyalina don in ba su labari.” Sai su ce masa: “Ka yi barci kamar barcin angon da babu mai tashin sa sai mafi soyuwar iyalansa gare shi.” Har lokacin da Allah zai tashe shi daga wannan makwancin nasa. Idan kuma munafuki ne sai ya ce: “Na ji mutane suna faɗa, ni ma na faɗi irin abin da suke faɗa. Ban san komai ba.” Sai su ce: “Lalle mun san haka kake faɗa.” Sai a ce wa ƙasa: “Ki haɗe da shi.” Sai ta matse shi sai ƙasusuwan haƙarƙarinsa sun harhaɗe, ba zai gushe ba cikin azaba har zuwa lokacin da Allah zai tashe shi daga wannan makwancin nasa.” [Tirmizi #1071].
فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَلَآ أَنسَابَ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ وَلَا يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 23:101Sannan idan aka busa ƙaho to fa babu wata dangantaka (mai amfani) a tsakaninsu a wannan ranar, kuma ba za su tambayi juna ba.
فَمَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Open ayah 23:102To waɗanda ma\'aunansu suka yi nauyi waɗannan su ne masu babban rabo.
وَمَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فِي جَهَنَّمَ خَٰلِدُونَ
Open ayah 23:103Waɗanda kuwa ma’aunansu suka yi sakayau waɗannan su ne waɗanda suka yi asarar kawunansu, suna masu dawwama a cikin (wutar) Jahannama.
تَلۡفَحُ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ وَهُمۡ فِيهَا كَٰلِحُونَ
Open ayah 23:104(Wutar) tana ƙona fuskokinsu alhali kuwa suna ciccije haƙoransu a cikinta.
أَلَمۡ تَكُنۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَكُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Open ayah 23:105Yanzu ayoyina ba su zamanto ana karanta muku su ba, sai ya zamana kuna ƙaryata su?
قَالُواْ رَبَّنَا غَلَبَتۡ عَلَيۡنَا شِقۡوَتُنَا وَكُنَّا قَوۡمٗا ضَآلِّينَ
Open ayah 23:106Suka ce: “Ya Ubangijinmu, tsiyarmu ce ta rinjaye mu, mun kuma zamo mutane ɓatattu.
رَبَّنَآ أَخۡرِجۡنَا مِنۡهَا فَإِنۡ عُدۡنَا فَإِنَّا ظَٰلِمُونَ
Open ayah 23:107“Ya Ubangijinmu, Ka fitar da mu daga cikinta, to idan muka sake, to lalle mu azzalumai ne.”
قَالَ ٱخۡسَـُٔواْ فِيهَا وَلَا تُكَلِّمُونِ
Open ayah 23:108Ya ce: “Ku yi min shiru, kada kuwa ku ƙara yi min magana a cikinta.
إِنَّهُۥ كَانَ فَرِيقٞ مِّنۡ عِبَادِي يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّٰحِمِينَ
Open ayah 23:109“Lalle yadda lamarin yake, wata ƙungiya daga bayina sun kasance suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka ji ƙan mu, Kai ne kuwa Fiyayyen masu jin ƙai.
فَٱتَّخَذۡتُمُوهُمۡ سِخۡرِيًّا حَتَّىٰٓ أَنسَوۡكُمۡ ذِكۡرِي وَكُنتُم مِّنۡهُمۡ تَضۡحَكُونَ
Open ayah 23:110“Sai kuka ɗauke su ababen yi wa izgili, har suka mantar da ku ambatona kuka kuma kasance kuna yi musu dariya.
إِنِّي جَزَيۡتُهُمُ ٱلۡيَوۡمَ بِمَا صَبَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
Open ayah 23:111“Lalle Ni Na saka musu a yau saboda haƙurinsu. Lalle kuma su ne marabauta.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu abubuwan na ban tsoro da za su faru a ranar alƙiyama, lokacin da mala’ika Israfilu zai yi busa a ƙaho busa ta biyu yayin da kowa zai fito daga ƙabarinsa, to a wannan ranar babu wata dangantaka da mutane za su yi wa juna alfahari da ita ko ta amfane su, domin a ranar kowa ta kansa yake, babu kuma tambayar juna game da halin da kowa yake ciki, domin wannan ranar ita ce ranar \'kowa tasa ta fisshe shi\'. An karɓo daga Miswaru ɗan Makhrama (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle duk wata dangantaka ta jini a ranar alƙiyama za ta yanke sai dangantaka da ni da alaƙa da ni da surukutaka da ni.” [Ahmad #18907]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk wanda ma’auninsa na aikin alheri a wannan rana ya yi nauyi, to waɗannan su ne masu samun babban rabo a wurin Allah, domin za su sami abin da suke fata, kuma za a nesanta su daga abin da suke ƙi. To amma kuma duk wanda ma’aunan ayyukansa suka yi sakayau, watau munanan ayyukansa suka rinjayi kyawawansu, to waɗannan su ne suka yi asarar kawunansu domin sun aikata abin da ya cutar da su sun yi watsi da abin da zai amfane su da sun aikata shi, kamar imani da Allah da ayyukan ƙwarai, to don haka su ne masu shiga wuta su dawwama a cikinta har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin azabar da za a yi musu da cewa wuta za ta riƙa ƙona fuskokinsu, kuma saboda tsananin raɗaɗin azaba da ɓacin rai za su riƙa ciccije haƙoransu. Sai, a cikin zargi, mala’iku su riƙa tambayar su cewa, ashe ba an riƙa karanta musu ayoyin Alƙur’ani a duniya ba, su kuma suka riƙa ƙaryata su? Sai su kuma su furta cewa: “Ya Ubangiji, tsiyarmu ce wadda ka riga ka rubuta mana ta rinjaye mu, kuma mun kasance mutane ɓatattu.” Sai su ci gaba da roƙon Allah cewa ya fitar da su daga wutar Jahannama suna masu ɗaukar masa alƙawari cewa idan har suka sake komawa cikin kafirci da ɓata, to lalle sun tabbata azzalumai duk abin da ya kama na azaba sai a yi musu. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa musu cewa su yi masa shiru kada wani cikinsu ya sake yi masa wata magana. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci irin mummunan aikinsu da ya kai su ga wannan mawuyacin hali, da cewa lalle a duniya wata jama’a daga cikin bayinsa waɗanda suka yi imani da shi sun kasance suna roƙon sa tare da yin kamun ƙafa da imaninsu da shi cewa ya gafarta musu zunubbansu ya ji ƙan su da rahamarsa, domin shi ne Fiyayyen masu rahama. To amma sai waɗannan kafiran suka mayar da waɗannan muminai abin yi wa izgili, tutur dare da rana ba ƙaƙƙautawa da yi musu ba’a da dariya har hakan ya sa suka manta da ambaton Allah. Sai Allah ya bayyana musu cewa, to fa shi a yau ya saka wa waɗannan muminai da gidan Aljanna saboda haƙurin da suka yi wajen bin Allah da guje wa saɓa masa, da kuma haƙuri da izgili da cin fuskar da kafirai suke yi musu.
قَٰلَ كَمۡ لَبِثۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ عَدَدَ سِنِينَ
Open ayah 23:112Ya ce: “Zaman shekara nawa kuka yi a bayan ƙasa?”
قَالُواْ لَبِثۡنَا يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖ فَسۡـَٔلِ ٱلۡعَآدِّينَ
Open ayah 23:113Suka ce: “Mun zauna ne yini ɗaya ko rabin yini, sai Ka tambayi (mala’iku) masu lissafin (kwanaki).
قَٰلَ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗاۖ لَّوۡ أَنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 23:114Ya ce: “Ai ba ku zauna ba sai ɗan lokaci ƙanƙani (dangane da zaman lahira), da a ce kun kasance kun san da haka.”
أَفَحَسِبۡتُمۡ أَنَّمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ عَبَثٗا وَأَنَّكُمۡ إِلَيۡنَا لَا تُرۡجَعُونَ
Open ayah 23:115(Allah Ya ce da su): “Ko kuna tsammani ne cewa Mun halicce ku ne ba manufa kuma ku ba za a dawo da ku gare Mu ba?”
فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡكَرِيمِ
Open ayah 23:116To Allah Sarki na gaskiya Ya ɗaukaka; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, (Shi ne) Ubangijin Al’arshi mai girma.
وَمَن يَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ لَا بُرۡهَٰنَ لَهُۥ بِهِۦ فَإِنَّمَا حِسَابُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 23:117Duk wanda ya bauta wa wani abin bauta tare da Allah ba da wata hujja ba game da (wannan bautar), to sakamakonsa wajen Ubangijinsa kawai yake. Lalle su dai kafirai ba za su rabauta ba.
وَقُل رَّبِّ ٱغۡفِرۡ وَٱرۡحَمۡ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّٰحِمِينَ
Open ayah 23:118Kuma ka ce: “Ya Ubangijina Ka gafarta (mana) kuma Ka ji ƙan mu, Kai ne kuwa Fiyayyen masu jin ƙai.” To bayan masu laifi sun nemi komawa duniya domin su gyara abin da suka ɓata, sai Allah ya tunatar da su tsawon shekaru da ya ba su a duniya waɗanda za su iya tuba, da sun ga daman haka, to amma ba su yi ba. Ya kuma tambaye su ko shekara nawa suka zauna a bayan ƙasa? Sai suka ba shi amsa da cewa, sun zauna ne yini guda ko ma wani yanki na yini, to amma daga ƙarshe sai suka nemi kawai ya tambayi waɗanda suke kula da lissafin kwanaki da watanni don su faɗa masa haƙiƙanin tsawon lokaci da suka zauna a duniya, domin su a yanzu azabar da suke ciki ta ishe su, ba za su iya tantance haƙiƙanin lissafin ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa zaman da suka yi a duniya ɗan kaɗan ne, idan an kwatanta shi da na lahira marar iyaka, to amma duk da haka ya ishe su su aikata ayyukan alheri da a ce sun sani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa halittunsa gaba ɗaya kashedi da kar su kuskura su yi tsammanin cewa ya halicce su ne don wasa ba tare da wata manufa ba, kuma su daina tunanin cewa ba za su koma gare shi ba don yi musu hisabi da sakamako a kan ayyukansu. Kada ma su kuskura su kawo wannan zaton a zukatansu, domin Allah Sarki na gaskiya ya ɗaukaka a kan yin wani aiki ba tare da manufa ba sai don wasa kawai kuma ya bar bayinsa sasakai ba tare da ya yi musu hisabi a kan ayyuakansu masu kyau da munana ba. Tabbas babu abin bautawa da gaskiya sai shi, shi ne Ubangijin Al’arshi mai girma. Sai kuma ya gargaɗi wanda yake bauta wa wani tare da Allah ba tare da wata hujja ba, da cewa, mummunan sakamakon aikinsa yana wurin Ubangijinsa, shi ne wanda zai yi masa sakayya ta azaba a kansa, domin kafirai ba za su taɓa rabauta ba har abada. Sai kuma a ƙarshen Surar Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gafarta masa zunubbansa ya ji ƙan sa da rahamarsa, domin shi ne fiyayyen masu jin ƙai.