النور
An-Noor
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
سُورَةٌ أَنزَلۡنَٰهَا وَفَرَضۡنَٰهَا وَأَنزَلۡنَا فِيهَآ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖ لَّعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Open ayah 24:1<b>Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai </b> 1. Wannan Sura ce da Muka saukar da ita Muka kuma wajabta (hukunce-hukuncen da suke cikinta), Muka kuma saukar da ayoyi bayyanannu a cikinta don ku wa’azantu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura ne da bayanin cewa ya saukar da ita, ya kuma wajabta aiki da hukunce-hukuncen da suke cikinta, ya kuma saukar da ayoyi bayyanannu a cikinta domin mutane su wa’azantu da abin da ta ƙunsa na hukunce-hukunce su yi aiki da su.
ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِي فَٱجۡلِدُواْ كُلَّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا مِاْئَةَ جَلۡدَةٖۖ وَلَا تَأۡخُذۡكُم بِهِمَا رَأۡفَةٞ فِي دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ وَلۡيَشۡهَدۡ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 24:2Mazinaciya da mazinaci (idan suka yi zina) sai ku yi wa kowanne ɗaya daga cikinsu bulala ɗari, kada kuwa wani tausayi ya kama ku game da (tabbatar da hukuncin) addinin Allah idan kun kasance kuna imani da Allah da ranar lahira; kuma lalle ne wata ƙungiya daga cikin muminai su halarci (wurin) yi musu haddin. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin wadda ba ta taɓa yin aure ba idan ta yi zina ko namijin da bai taɓa aure ba amma ya yi zina. Allah ya yi umarni da a yi wa kowane daga cikinsu bulala ɗari bayan an tabbatar da laifinsa. Ana tabbatar da laifin zina ne ta ɗaya daga cikin waɗannan hayoyi guda uku: 1. Samun shaidu huɗu mazaje waɗanda kowannensu ya ga masu laifin dumu-dumu cikin laifinsu, watau kamar turmi da taɓarya. 2. Iƙirarin mai laifi. 3. Samuwar ciki ga matar da ba ta da miji ko baiwar da ba ta da maigida, kuma babu wasu alamu na tursasawa ko fyaɗe. Za a yi wa kowannensu bulala ɗari ta hanyar duka mai raɗaɗi amma ba mai fasa jiki ba. An karɓo daga Ubadatu ɗan Samit (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku karɓi hukuncin (mazinata) daga gare ni, ku karɓa daga gare ni, Allah ya samar musu mafita; waɗanda ba su taɓa aure ba; mace ko namiji, a yi musu bulala ɗari a kore su (daga garinsu) tsawon shekara ɗaya.” [Muslim #1690]. An karɓo daga Abu Huraira da Zaidu ɗan Khalid, Annabi (ﷺ) ya faɗa wa mutumin da ɗansa ya yi zina da wata mata cewa: “Akwai bulala ɗari a kan ɗanka da kuma raba shi da gari tsawon shekara ɗaya.” [Bukhari #6827, 6828 da Muslim #1697, 1698]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana muminai su ji wani tausayi yayin zartar da hukuncin haddi a kan waɗannan mazinata biyu har wannan tausayi ya kai ga hana su zartar da hukuncin Allah ko ya sa su su sassauta shi daga yadda Allah ya yi umarni idan har sun yi imani da Allah da ranar lahira. Haka kuma ya yi umarni da cewa lalle a sami wata ƙungiya daga cikin muminai da za su halarci lokacin da ake zartar da wannan haddi ga waɗancan mazinata don hakan ya zamo darasi gare su har da wasu ma.
ٱلزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوۡ مُشۡرِكَةٗ وَٱلزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَآ إِلَّا زَانٍ أَوۡ مُشۡرِكٞۚ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 24:3Mazinaci ba ya aure sai da karuwa ko mushirika, karuwa kuma ba ta aure sai da mazinaci ko mushiriki. An kuma haramta wannan ga muminai. Wannan aya malaman tafsiri sun yi saɓani wajen fassararta: Wasu suka ce ma’anar ayar ita ce, wanda ya saba da yin zina ba zai so ya auri wata mata ba sai mazinaciya irinsa ko kuma mushirikar da ba ta guje wa zina, tare da cewa haramun ne a gare shi ya aure ta. Hakanan ita ma mace mazinaciya ba za ta yi sha’awar auren wani ba sai mazinaci irinta ko mushirikin da ba ya guje wa zina tare da haramcin aure tsakaninsu. An kuma haramta wa muminai auren mace mazinaciya ko namiji mazinaci. An ruwaito wannan fassara daga yawancin magabata, kamar su Abdullahi ɗan Abbas da Abdullahi ɗan Umar da Sa’idu ɗan Musayyab da Sa’idu ɗan Jubair da Mujahid da Ƙatada da Zuhri da sauransu. Wannan shi ne ra’ayin Imamu Ahmad da Shaikhul Islam Ibn Taimiyya da sauransu. Wasu malaman kuma suka ce abin da ayar take nufi shi ne, mazinaci ba ya samun abokiyar zina sai mazinaciya irinsa ko mushirika mai halatta zina, hakanan ita ma mazinaciya ba za ta sami abokin zina ba sai irinta mazinaci ko kuma mushiriki mai halatta zina. Daga cikin waɗanda suka yi wannan fassara akwai Abdullahi ɗan Abbas (ra’ayinsa ne na biyu) da Sa’idu ɗan Jubair (shi ma a wani ƙaulin nasa) da Ikrima da Abdurrahman ɗan Zaid ɗan Aslam. Wannan shi ne zaɓin Ibnu Jarir da Ibnu Kasir da wasunsu. Akwai wani ra’ayin ban da wannan. A bisa fassarar malamai na farko suna ganin faɗar Allah cewa: “An kuma haramta wannan ga muminai”, tana nufin haramun ne mumini kamamme ya auri mazinaciya wadda ba ta tuba ta daina zina ba. Hakanan ita ma mumina kamammiya haramun ne ta auri mazinacin da bai tuba ya daina ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Akwai wani mutum sunansa Marsad ɗan Abu Marsad ya kasance yana taimaka wa waɗanda aka tsare su a Makka su sami kuɓuta ya gudu da su zuwa Madina. To yana da wata dadironsa a Makka tun a lokacin jahiliyya. Wani lokaci sai ya tafi Makka domin kuɓutar da wani Musulmi fursuna a hannun kafirai. Bayan ya shiga Makka sai dare ya yi masa, ya sami ƙarƙashin wata katanga ya zauna cikin inuwar farin wata. Yana nan zaune sai ga dadiron nan tasa, watau Anaƙ, ta nufo inda yake zaune, sai ta kula alamar mutum ne a zaune ƙarƙashin katanga. Da ta ƙara matsawa kusa da shi sai ta gane shi, sai ta ce: “Marsad ne?” Sai ya amsa mata da cewa: “E, Marsad ne.” Sai ta yi masa marhabun da lale, ta kuma gayyace shi ya kwana a ɗakinta. Sai ya faɗa mata cewa Allah fa ya haramta zina. Daga jin ya faɗi haka sai kawai ta yi masa kururuwa cewa jama’a su fito ga mai ɗauke musu fursunoninsu ya zo. Kafirai da jin haka sai mutum takwas suka bi shi a baya har cikin dutsen Alkhandama , ya samu ya shiga wani kogon dutse ya ɓoye. Bayan sun gaji da nemansa ba su gan shi ba, sai suka tafi, shi kuma ya fito ya koma wajen wanda ya yi wa alƙawarin kuɓutar da shi ya kwance masa marinsa ya ɗauke shi suka gudu Madina. Daga baya sai ya je ya sami Manzon Allah ya tambaye shi ko zai iya auren wannan matar Anaƙ? Sai Manzon Allah ya yi shiru bai tanka masa ba har sai da wannan ayar ta sauka, sai Manzon Allah ya ce masa: “Ya kai Marsad, mazinaci ba ya auren wata sai mazinaciya ko mushirika, ita ma mazinaciya ba ta auren wani sai mazinaci ko mushiriki, don haka kada ka aure ta.” [Abu dawud #2051 da Tirmizi #3177 da Nasa’i #3228].
وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَأۡتُواْ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَ فَٱجۡلِدُوهُمۡ ثَمَٰنِينَ جَلۡدَةٗ وَلَا تَقۡبَلُواْ لَهُمۡ شَهَٰدَةً أَبَدٗاۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ
Open ayah 24:4Waɗanda kuwa suke jifan mata masu kamun kai sannan ba su kawo shaidu huɗu ba, sai ku yi musu bulala tamanin, kuma kada ku karɓi shaidarsu har abada. Waɗannan kuma su ne fasiƙai.
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 24:5Sai dai waɗanda suka tuba bayan wannan suka kuma kyautata, to haƙiƙa Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin waɗanda za su jefi kamammun mata da aikata laifin zina sannan su kasa kawo shaidu huɗu a kan haka, to sai alƙalai su yi umarni a yi musu bulala tamanin da matsakaiciyar bulala mai raɗaɗi ba mai fasa jiki ba. Sannan Allah ya bayyana cewa kada masu hukunci su sake karɓar shaidarsu har abada, domin sun rabu da biyayya ga Allah. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku nisanci abubuwa bakwai masu hallakarwa.” Sai sahabbai suka ce: “Waɗanne ne ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Shirka da Allah da sihiri da kashe rai da Allah ya haramta kashe shi ba da haƙƙi ba da cin dukiyar maraya da cin riba da tserewa daga fagen daga da jifan mata kamammu gafalallu muminai da zina.” [Bukhari #6857 da Muslim #89]. Amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan sun tuba daga baya sun kyautata, to Allah mai gafara ne mai jin ƙai, don haka zai gafarta musu abin da ya gabata na laifukan da suka yi.
وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ أَزۡوَٰجَهُمۡ وَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ شُهَدَآءُ إِلَّآ أَنفُسُهُمۡ فَشَهَٰدَةُ أَحَدِهِمۡ أَرۡبَعُ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 24:6Waɗanda kuma suke jifan matayensu (da zina) kuma ba su da wasu shaidu sai su kansu, to shaidar ɗayansu ita ce ya rantsuwa da Allah sau huɗu a kan cewa shi lalle yana daga masu gaskiya.
وَٱلۡخَٰمِسَةُ أَنَّ لَعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Open ayah 24:7(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa tsinuwar Allah ta hau kansa in ya kasance daga cikin maƙaryata.
وَيَدۡرَؤُاْ عَنۡهَا ٱلۡعَذَابَ أَن تَشۡهَدَ أَرۡبَعَ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Open ayah 24:8Kuma (abin da) zai kawar mata da azabar haddi shi ne ta yi rantsuwa da Allah sau huɗu kan cewa shi lalle yana daga cikin maƙaryata.
وَٱلۡخَٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَآ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 24:9(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa lalle fushin Allah ya hau kanta idan ya kasance daga masu gaskiya.
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٌ حَكِيمٌ
Open ayah 24:10Ba don falalar Allah gare ku ba da rahamarsa, da kuma cewa Allah Mai karɓar tuba ne, Mai hikima (to da ya kunyata maƙaryaci). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin waɗanda za su jefi matansu na aure da aikata laifin zina sannan ba su da wasu shaidu a kan haka sai su kansu, to hukuncinsu shi ne ya yi rantsuwa huɗu da Allah cewa yana da gaskiya game da laifin da yake zargin matarsa a kai na zina. Sannan a rantsuwarsa ta biyar ya ƙara da yi wa kansa addu’ar la’anar Allah ta tabbata a kansa idan har ƙarya yake yi mata. Ita ma matar Allah ya bayyana cewa ta cancanci a yi mata haddin zina har sai idan ta yi rantsuwa huɗu da Allah cewa ƙarya mijinta ya yi mata da ya zarge ta da laifin aikata zina, sannan a rantsuwa ta biyar ta ƙara da cewa fushin Allah ya tabbata a gare ta idan har gaskiya ya faɗa. Wannan shi ake kira li’ani . An karɓo daga Sahlu ɗan Sa’ad As-Sa’idi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Uwaimir (Allah ya kara masa yarda) ya je wajen shugaban ƙabilarsa Banu Ajlan, watau Asim ɗan Adiyyu ya ce masa: “Me za ku faɗa game da wanda ya sami wani mutum tare da matarsa; shin zai kashe shi ne shi ma a kashe shi ko kuma yaya zai yi? Ka tambaya mini Manzon Allah game da wannan.” Sai Asim ya zo wurin Manzon Allah ya yi masa wannan tambayar, to amma sai Manzon Allah ya nuna masa ba ya son irin waɗannan tambayoyin. Da ya koma sai Uwaimir ya tambaye shi ko ya yi masa tambayarsa. Sai ya faɗa masa cewa ya yi wa Manzon Allah wannan tambayar amma ya nuna masa ba ya son irin waɗannan tambayoyi. Sai Uwaimir ya ce shi sai ya yi wa Manzon Allah wannan tambayar. Ya sami Manzon Allah ya ce masa: “Ya Manzon Allah, mutum ne ya sami wani mutum tare da matarsa, shin zai kashe shi ne ku kuma ku kashe shi, ko kuma yaya zai yi?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya saukar da ayar Alƙur’ani game da lamarinka kai da matarka.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya umarce su da yin li’ani kamar yadda Allah ya ambata a littafinsa, sai Uwaimir ya yi li’ani da matarsa. Sannan sai ya ce: “Ya Manzon Allah, idan har na zauna da ita to haƙiƙa na zalunce ta.” Sai ya sake ta. Sai hakan ya zama hukunci ga ma’auratan da suka yi li’ani . [Bukhari #4745 da Muslim #1492]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Hilalu ɗan Umayya ya zargi matarsa da yin zina da Shariku ɗan Sahma’u, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Ka kawo shaida ko a yi maka bulalar ƙazafi.” Sai Hilalu ya ce: “Ya Manzon Allah, idan ɗayanmu ya ga wani mutum a kan matarsa yanzu sai ya bar shi ya tafi neman shaidu?” Sai Annabi (ﷺ) ya ci gaba da ce masa: “Ko dai ka kawo shaida ko kuma ka sha bulalar ƙazafi.” Sai Hilalu ya ce: “Na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya, lalle ina da gaskiya kuma tabbas sai Allah ya saukar da abin da zai kuɓutar da ni daga haddi.” Sai Jibrilu ya saukar masa waɗannan ayoyin. Sai Annabi (ﷺ) ya aika aka zo da matar Hilalu, sai Hilalu ya yi rantsuwa, shi kuma Manzon Allah yana cewa: “Lalle Allah ya san ɗayanku maƙaryaci ne, shin akwai wanda zai tuba daga cikinku?” Sai ita ma matar ta yi rantsuwa, da ta zo yin rantsuwa ta biyar sai suka dakatar da ita, suka ce mata: “Wannan lalle ita ce za ta wajabta miki hallaka. Sai ta ɗan yi inda-inda ta ɗan ja da baya har sai da aka yi zaton ko ma za ta fasa rantsuwar ne, sai ta ce: “Ba zan taɓa kunyata mutanena ba.” Sai ta ci gaba da rantsuwarta har ta kai ƙarshe....” [Bukhari #4747]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce Manzon Allah (ﷺ) ya yi hukuncin li’ani tsakanin miji da matarsa ya kuma raba tsakaninsu.” [Bukhari #5314 da Muslim #1494]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutane cewa ba don falalarsa da rahamarsa gare su ba da kuma kasancewarsa mai karɓar tuban bayinsa masu tuba da kuma kasancewarsa mai hikima cikin dukkan lamuransa da shari’arsa, to da ya gaggauto musu da azaba ya kuma kunyata su saboda zunubansu.
إِنَّ ٱلَّذِينَ جَآءُو بِٱلۡإِفۡكِ عُصۡبَةٞ مِّنكُمۡۚ لَا تَحۡسَبُوهُ شَرّٗا لَّكُمۖ بَلۡ هُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۚ لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُم مَّا ٱكۡتَسَبَ مِنَ ٱلۡإِثۡمِۚ وَٱلَّذِي تَوَلَّىٰ كِبۡرَهُۥ مِنۡهُمۡ لَهُۥ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Open ayah 24:11Lalle waɗanda suka zo da ƙagaggiyar ƙarya wasu jama’a ne daga cikinku. To kada ku zace shi sharri ne a gare ku; a’a, shi alheri ne a gare ku. Kowanne mutum daga cikinsu yana da sakamakon abin da ya aikata na zunubi. Wanda kuwa ya jiɓinci fara kwaza shi daga cikinsu yana da azaba mai girma.
لَّوۡلَآ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ ظَنَّ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بِأَنفُسِهِمۡ خَيۡرٗا وَقَالُواْ هَٰذَآ إِفۡكٞ مُّبِينٞ
Open ayah 24:12Me ya hana lokacin da kuka ji shi (wato ƙyagen) muminai maza da muminai mata ba su yi wa kawunansu zaton alheri ba suka kuma ce, wannan ai ƙage ne bayyananne?
لَّوۡلَا جَآءُو عَلَيۡهِ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَۚ فَإِذۡ لَمۡ يَأۡتُواْ بِٱلشُّهَدَآءِ فَأُوْلَٰٓئِكَ عِندَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ
Open ayah 24:13Me ya hana su kawo shaidu huɗu game da shi (ƙagen)? To tun da yake ba su kawo shaidun ba, to waɗannan a wurin Allah su ne maƙaryata.
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ لَمَسَّكُمۡ فِي مَآ أَفَضۡتُمۡ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Open ayah 24:14Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba a duniya da lahira, to tabbas da azaba mai girma ta shafe ku game da abin da kuka kutsa cikinsa.
إِذۡ تَلَقَّوۡنَهُۥ بِأَلۡسِنَتِكُمۡ وَتَقُولُونَ بِأَفۡوَاهِكُم مَّا لَيۡسَ لَكُم بِهِۦ عِلۡمٞ وَتَحۡسَبُونَهُۥ هَيِّنٗا وَهُوَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمٞ
Open ayah 24:15Yayin da kuke bayeyeniyarsa (ƙagen) da harsunanku, kuke faɗar abin da ba ku sani ba da bakunanku, kuke kuma tsammaninsa abu ne mai sauƙi, alhali kuwa shi mai girma ne a wurin Allah.
وَلَوۡلَآ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ قُلۡتُم مَّا يَكُونُ لَنَآ أَن نَّتَكَلَّمَ بِهَٰذَا سُبۡحَٰنَكَ هَٰذَا بُهۡتَٰنٌ عَظِيمٞ
Open ayah 24:16Me ya hana yayin da kuka ji shi ku ce: “Bai dace da mu mu yi irin wannan magana ba,” (kuma ku ce:) “Subhanallahi! Ai wannan ƙage ne babba!”
يَعِظُكُمُ ٱللَّهُ أَن تَعُودُواْ لِمِثۡلِهِۦٓ أَبَدًا إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 24:17Allah Yana gargaɗin ku kada ku koma yin irinsa har abada idan kun zamanto muminai.
وَيُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Open ayah 24:18Allah kuma yana bayyana muku ayoyinsa ne, Allah kuwa Masani ne, Mai hikima. Daga nan har zuwa aya ta 26 Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin wani babban abu ne mai tayar da hankali da ya faru mai dangantaka da ƙazafin zina da munafukai suka yi wa Nana A’isha matar Manzon Allah (ﷺ). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi ne don wanke ta daga wannan mummunan zargi maras tushe da gargaɗin muminai game da sakin bakinsu a kan wannan lamari, tare da bayanin mummunan sakamako na waɗanda suka jiɓinci ƙirƙiro wannan ƙazafi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa mutanen da suka ƙiri ƙarya da ƙazafi ga Nana A’isha wata jama’a ce daga cikinsu, su ne munafukai. Allah ya tabbatar musu da cewa kada su zaci wannan abu da suka yi na ƙage sharri ne gare su, su muminai, a’a, alheri ne a gare su saboda abin da za su samu daga Allah na lada da kyakkyawan sakamako idan sun yi haƙuri sun fawwala wa Allah komai. Allah ya bayyana musu cewa duk wani wanda yake da hannu a cikin wannan ƙazamin aiki yana da sakamakon zunubinsa, amma wanda ya ɗauki gabaran kwaza wannan labarin to yana da azaba mai girma a wurin Allah. Malaman hadisi sun ruwaito yadda wannan abin ya faru wanda za mu taƙaita shi kamar haka: A shekara ta 6 ga hijira Annabi (ﷺ) ya shirya fita don yaƙar ƙabilar Banu Musɗaliƙ, ya fita tare da Nana A’isha (Allah ya kara mata yarda) bayan ya yi wa matansa ƙuri’a, ƙuri’arta ta fito. Bayan Annabi (ﷺ) ya gama abin da ya fita yi, sai shi da rundunarsa suka juyo domin dawowa Madina, sai kuma aka yada zango a kan hanya. Da suka tashi ci gaba da tafiyarsu don su ƙarasa Madina sai aka baro ita A’isha a wurin, domin ta fita daga darbukarta ta zagaya don biyan buƙata irin ta ɗan’adam, sai aka ɗauki darbukar aka ɗora a kan raƙumi ana zaton tana ciki, domin ba ta da nauyi saboda ƙuruciyarta da ƙaramin jikinta a lokacin. To da ta dawo sai ta tarar da Annabi da sahabbai sun tafi sai ta dakata a nan wurin don tana tsammanin idan sun isa gida ba su gan ta ba nan ne za su dawo neman ta. To da akwai masu tsayawa a bayan runduna ga ƙa’ida don duba inda aka yada zango ko an bar wani abu mai muhimmanci su taho da shi. Daga cikin masu irin wannan muhimmin aiki akwai Safwanu ɗan Mu’aɗɗil (Allah ya kara masa yarda), yana zuwa wurin sai ya tarar da A’isha har barci ya ɗauke ta; da ta farka ya kuma gane ita ce sai ya durƙusar da raƙuminsa ya kawar da kansa sai ta hau, bai ce mata uffan ba, ita ma kuma ba ta yi masa wata magana ba. Ya ja akalar raƙuminta har suka cimma Annabi da rundunarsa sun kuma ya da zango domin rurrumi. Da isar Safwan wannan wuri sai munafukai da ke tare da shugabansu Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan Salul nan take sai suka fara zunɗen abin da ya haɗa A’isha da Safwan har aka taho aka bar su a baya, sai Ɗan Salul ya fara cewa lalle wani abu ya faru tsakaninsu na lalata. Daga nan ne fa labarin ya bazu cikin garin Madina, munafukai suka yi ta yamaɗiɗi da shi, har ma wasu kaɗan daga cikin Musulmai su ma suka riƙa baza labarin. Wannan abu ya jefa Annabi (ﷺ) da iyalan gidansa da na Sayyadina Abubakar da sauran Musulmi a garin Madina cikin wani mawuyacin hali matuƙa, wanda ta kai har ya daina sakar wa A’isha fuska kamar yadda ya saba yi mata a baya. Ya kuma nemi shawarar wasu daga cikin sahabbansa game da iyalansa waɗanda su kuma suka nuna masa ba su san wani mummunan hali tare da su ba. Bayan kimanin kwana talatin da aka ɗauka cikin wannan hali, A’isha kuwa tana cikin kuka koyaushe ba dare ba rana a gidan iyayenta bayan ta koma can da izinin Manzo (ﷺ), kuma Manzon Allah bai sami wani wahayi ba daga Allah wanda zai bayyana masa gaskiyar al’amarin. Ana tsaka da haka ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyi ya wanke A’isha tatas daga wannan mummunan zargi, ya tabbatar da tsarkinta da nagartarta. [Bukhari #4750 da Muslim #2770]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Musulmi cewa ai wajaba ya yi lokacin da suka ɗauka ana yaɗa wannan mummunan labarin su yi wa junansu kyakkyawan zato, kada su yarda da zargin ɗan’uwansu mumini ba da hujja ba, su ma fito fili su ƙaryata labarin su ce ƙage ne bayyananne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci masu yi wa Nana A’isha ƙage da cewa, me ya hana su kawo shaidu huɗu don tabbatar da gaskiyar abin da suke zargin ta da aikatawa? To tun da yake ba su kawo waɗannan shaidun huɗu ba, to waɗannan a wurin Allah su ne maƙaryata. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalarsa da rahamarsa ga muminai wadda ta hana ya gaggauto musu da uƙuba, ya kuma yafe wa wanda ya tuba; ba don haka ba da wata azaba mai girma ta auka musu saboda kutsawa da suka yi cikin wannan lamari na ƙazafi. Allah ya bayyana irin kutsen da suka yi, watau yayin da suke yayata wannan labari a junansu suna kwaza abin da ba su sani ba da bakunansu suna zaton abu ne mai sauƙi alhalin mai girma ne a wurin Allah, domin abin da ya ƙunsa na danganta wa mumini marar laifi irin wannan babban laifi na zina. Sannan Allah ya koya wa Musulmi ladabi da tarbiyya game da irin wannan lamari idan nan gaba ya faru sun ji ana yaɗa shi, to su fito fili su nuna rashin dacewar faɗar irin wannan ƙazamar magana, su tsarkake Allah su tabbatar da cewa wannan batu ƙage ne babba. Allah kuma ya bayyana musu cewa duk waɗannan batutuwa da yake yi musu yana yi musu wa’azi ne don wannan abu da ya faru ya zamanto shi ne na farko shi ne kuma na ƙarshe ba za su ƙara aikata irinsa ba har abada, matuƙar suna matsayinsu na muminai. Ya tabbatar da cewa yana bayyana musu ayoyinsa ne waɗanda suke ƙunshe da hukunce-hukunce da wa’azozinsa, kuma Allah masanin dukkan ayyukansu ne, babu abin da bai sani ba, zai kuma yi musu sakamako a kai.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ ٱلۡفَٰحِشَةُ فِي ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 24:19Lalle waɗanda suke son yaɗuwar mummunan abu a cikin waɗanda suka yi imani suna da (sakamakon) azaba mai raɗaɗi a duniya da lahira, kuma Allah (Shi) ne Yake sane, ku ba ba ku san komai ba.
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 24:20Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da kuma cewa lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama (da kun faɗa cikin hallaka).
۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ وَمَن يَتَّبِعۡ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَإِنَّهُۥ يَأۡمُرُ بِٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۚ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ مَا زَكَىٰ مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ أَبَدٗا وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُزَكِّي مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 24:21Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin Shaiɗan, wanda kuwa duk ya bi hanyoyin Shaiɗan, to lalle shi (Shaiɗan) umarni yake yi da aikata alfasha da abin ƙyama. Ba don kuma falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da babu ɗaya daga cikinku da zai tsarkaka har abada, sai dai kuma Allah (Shi) Yake tsarkake wanda Ya ga dama, Allah kuwa Mai ji ne, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi masu son ganin munanan laifuka suna yaɗuwa cikin muminai ta hanyar yi musu ƙazafi da yarfe da cewa, lalle suna da azaba mai raɗaɗi a duniya, domin za su haɗu da hukuncin wannan ƙazafi, watau bulala tamanin, a lahira kuma su haɗu da azabar wuta matuƙar sun mutu ba su tuba sun daina wannan mummunan hali ba. Allah ya bayyana cewa yana sane da duk ƙaryar da suke shararawa, kuma shi ne ya san abin da zai zama maslaha ga bayinsa, su ba su san komai a kan hakan ba. An karɓo daga Sauban (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Kada ku cutar da bayin Allah, kada kuma ku kunyata su, kada ku bibiyi al’aurarsu, domin duk wanda ya bibiyi al’aurar ɗan’uwansa Musulmi, to shi ma Allah zai bibiyi al’aurarsa har cikin gidansa ya kunyata shi.” [Ahmad #22402]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rahamarsa ga mutane masu laifi, ya nuna musu cewa ba domin falalarsa da rahamarsa gare su ba, to da ya gaggauto musu da azaba tun a nan duniya a kan abin da suka tafka na ƙarya ga uwar muminai A’isha (Allah ya kara masa yarda), to amma ya jinkirta musu ne domin su tuba ya karɓi tubansu. Sannan ya kirawo muminai waɗanda suka yi imani suke kuma aiki da shari’arsa ya gargaɗe su a kan su guji bin hanyoyin Shaiɗan wanda yake ƙawata musu ƙarya da ƙage, da cewa duk wanda ya bi hanyoyin Shaiɗan, to lalle zai riƙa umartar sa da munanan ayyuka da miyagun maganganu, ya jefa shi cikin aikata abin da sharia’a ta hana. Ya kuma bayyana wa muminai falalarsa da rahamarsa gare su da har ya zamanto yana karɓar tuban wanda ya yi laifi ya tuba, ba don haka ba da ba zai yafe wa wani mai laifi ba har abada ko da ya tuba. To amma yana karɓar tuban wanda ya ga damar ya yafe masa ya kuma tsarkake shi. Ya tabbatar musu cewa shi mai jin duk maganganunsu ne masanin ayyukansu gaba ɗaya, babu abin da yake ɓuya gare shi, don haka zai yi wa kowa sakamako gwargwadon aikinsa mai kyau da mummuna.
وَلَا يَأۡتَلِ أُوْلُواْ ٱلۡفَضۡلِ مِنكُمۡ وَٱلسَّعَةِ أَن يُؤۡتُوٓاْ أُوْلِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ وَلۡيَعۡفُواْ وَلۡيَصۡفَحُوٓاْۗ أَلَا تُحِبُّونَ أَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Open ayah 24:22Kuma kada masu hali da wadata daga cikinku su rantse a kan ƙin ba da (abin hannunsu) ga makusanta da miskinai da masu hijira saboda Allah. Su kuma yi afuwa su yafe. Shin ku ba kwa so ne Allah Ya gafarta muku? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yin kashedi ne ga mutanen kirki masu wadata da su daina yin rantsuwar ba za su taimaka wa danginsu na kusa da mabuƙata da masu hijira don Allah ba, saboda sun yi musu laifi. Allah ya umarce su da su yafe musu su kuma kau da kai daga laifinsu, ya bayyana musu cewa kamar yadda suke son Allah ya gafarta musu idan sun yi masa laifi sun nemi gafararsa, to su ma su yafe wa waɗanda suka yi musu laifi suka kuma tuba. Allah ya tabbatar musu cewa shi mai gafarta wa bayinsa ne da suka tuba, mai jin ƙan su ne, don haka su ma su yi koyi da shi. Wannan ayar ta sauka game da Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ne dangane da abin da ya faru tsakaninsa da ɗan innarsa, watau Misɗahu ɗan Usasa (Allah ya kara masa yarda) wanda Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya kasance yana tallafa masa yana ciyar da shi, domin shi talaka ne ba shi da ƙarfi. To lokacin da munafukai suka jefi Nana A’isha da ɓatanci sai Misɗahu ya zama daga cikin masu kwaza wannan mummunan labari, sai Sayyadina Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya yi fushi da shi har ya rantse da Allah ba zai ƙara taimaka masa ba domin abin da ya yi wa ‘yarsa kuma matar Manzon Allah (ﷺ). To bayan Misɗahu ya tuba an yi masa haddin ƙazafi sai Allah ya saukar da wannan ayar. Yayin da Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya ji Allah yana cewa: “Shin ku ba kwa so Allah ya gafarta muku ne?” Sai ya ce: “Wallahi muna son ka gafarta mana ya Ubangijinmu.” Sai ya koma ya ci gaba da taimakon Misɗahu, ya kuma yi alƙawarin ba zai daina taimaka masa ba har abada. [Duba, Bukhari #2661 da 2770].
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ٱلۡغَٰفِلَٰتِ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ لُعِنُواْ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Open ayah 24:23Lalle waɗanda suke jifan kamammun mata waɗanda ba su san me yake faruwa ba, muminai, (suke jifan su da zina), to an la’ance su duniya da lahira, kuma suna da (sakamakon) azaba mai girma.
يَوۡمَ تَشۡهَدُ عَلَيۡهِمۡ أَلۡسِنَتُهُمۡ وَأَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 24:24A ranar da harsunansu da hannayensu da kuma ƙafafunsu za su ba da shaida a kansu game da abin da suka kasance suna aikatawa.
يَوۡمَئِذٖ يُوَفِّيهِمُ ٱللَّهُ دِينَهُمُ ٱلۡحَقَّ وَيَعۡلَمُونَ أَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 24:25A wannan ranar Allah zai ba su cikakken sakamakonsu na gaskiya kuma za su san cewa lalle Allah Shi ne gaskiya bayyananniya.
ٱلۡخَبِيثَٰتُ لِلۡخَبِيثِينَ وَٱلۡخَبِيثُونَ لِلۡخَبِيثَٰتِۖ وَٱلطَّيِّبَٰتُ لِلطَّيِّبِينَ وَٱلطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَٰتِۚ أُوْلَٰٓئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا يَقُولُونَۖ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ
Open ayah 24:26Miyagun mata da miyagun maganganu sun dace da miyagun maza. Kuma miyagun maza da miyagun maganganu sun dace ne da miyagun mata. Tsarkakan mata da tsarkakan maganganu sun dace da tsarkakan maza. Kuma tsarkakan maza da tsakakan maganganu sun dace da tsarkakan mata. Su waɗannan (tsarkaka) kuwa wankakakku ne daga abin da suke faɗa (na ƙage a kansu), suna da (sakamakon) gafara da arziki mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle masu yin ƙazafi ga kamammun mata muminai waɗanda ba su san abin da ake ciki ba don ɓata musu suna, waɗannan an la’ance su duniya da lahira, bayan abin da yake jiran su na azaba mai girma a lahira. Ranar da harsunansu za su ba da shaida a kansu game da miyagun maganganun da suka yi, hannayensu da ƙafafunsu duk su ba da shaida a kan abin da suka riƙa aikatawa. Allah ya bayyana cewa a ranar ne za a cika musu sakamakon ayyukansu bisa ga adalci, za kuma su gane cewa Allah shi ne gaskiya, duk kuma abin da zai fito daga wajensa na alheri ko na waninsa, na alƙawari lada ko na narko gaskiya ne, a bayyane yake babu tababa a kansa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku nisanci abubuwa bakwai masu hallakarwa.” Sahabbai suka ce: “Waɗanne ne ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Shirka da Allah da sihiri da kashe ran da Allah ya haramta kashewa ba bisa gaskiya ba da cin riba da cin dukiyar maraya da gudowa a ranar yaƙi da yi wa katangaggun mata muminai gafalallu ƙazafi.” [Bukhari #2766 da Muslim #89]. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara masa yarda.H) ta ce: “An jefe ni da abin da aka jefe ni da shi (na ƙazafi) alhalin ni ban san abin da yake faruwa ba, daga baya labari ya zo min.” [Ibn Jarir , juzu’i na 18, shafi na 82]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk wani mai ƙazamin hali namiji da mace ko miyagun maganganu da ayyuka suna dacewa ne da miyagun maza da mata irinsu, hakanan duk wani mai tsarki namiji ko mace ko tsarkakakkun maganganu suna dacewa ne da tsarkaka, Allah ya tabbatar da cewa waɗannan tsarkaka wankakku ne daga abin da waɗannan masu miyagun hali suke tuhumar su da shi, kuma suna da wata gafara daga Allah da wani arziƙi na karamci a gidan Aljanna.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتًا غَيۡرَ بُيُوتِكُمۡ حَتَّىٰ تَسۡتَأۡنِسُواْ وَتُسَلِّمُواْ عَلَىٰٓ أَهۡلِهَاۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Open ayah 24:27Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini, kuma kun yi sallama ga masu su. Wannan kuwa shi ya fi alheri a gare ku don ku wa’azantu.
فَإِن لَّمۡ تَجِدُواْ فِيهَآ أَحَدٗا فَلَا تَدۡخُلُوهَا حَتَّىٰ يُؤۡذَنَ لَكُمۡۖ وَإِن قِيلَ لَكُمُ ٱرۡجِعُواْ فَٱرۡجِعُواْۖ هُوَ أَزۡكَىٰ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ
Open ayah 24:28To idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini; idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma; wannan shi ya fi tsarki a gare ku. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne.
لَّيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَدۡخُلُواْ بُيُوتًا غَيۡرَ مَسۡكُونَةٖ فِيهَا مَتَٰعٞ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُبۡدُونَ وَمَا تَكۡتُمُونَ
Open ayah 24:29Babu wani laifi a kanku ku shiga gidaje waɗanda ba wani zaune a cikinsu, kuma akwai kayanku a cikinsu, kuma Allah Yana sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuke ɓoyewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin wasu hukunce-hukunce ne game da sallama da neman izini yayin shiga gidaje. Allah ya kirawo muminai waɗanda suka yi imani da shi suke kuma aiki da shari’arsa, ya hana su shiga gidajen da ba nasu ba ba tare da sun yi sallama ba sun kuma nemi izinin shiga wajen masu gidan. Ya tabbatar musu da cewa yin hakan shi ne ya fi zama alheri a gare su. Allah ya ba su wannan umarni ne domin su wa’azantu su guji auka wa gidajen da ba nasu ba ba tare da sallama ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya umarce su da cewa idan suka zo gida suka samu ba kowa a gidan, to kada su kuskura su shiga har sai sun sami izini daga wani wanda yake da ikon yi musu izinin shiga. Idan kuwa sun samu da mutane a gidan suka nemi izinin shiga ciki, to amma masu gidan suka nemi su koma kada su shigo musu gida, to su koma su haƙura da shiga wannan gidan, Allah ya tabbatar musu da cewa yin hakan shi ne ya fi musu tsarki a wurin Allah. Allah masanin duk abin da suke aikatawa ne babu abin da yake ɓuya a gare shi, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan ayyukansu. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata rana muna zaune a wata majalisa ta mutanen Madina sai ga Abu Musa Al-Ash’ari ya zo hankalinsa a tashe sai ya ce mana: “Na nemi izinin shiga ne wajen Umar (Allah ya kara masa yarda) har sau uku amma ba a yi min izini ba, sai na juya na tafi abina. Sai Umar ya fito ya ce mini: “Mene ne ya hana ka shigowa?” Na ce: “Na nemi izini sau uku ba a yi mini ba shi ne na tafi, kuma na ji Annabi (ﷺ) ya ce: “Idan ɗayanku ya nemi izini sau uku ba a yi masa ba to ya koma.” Sai Umar ya ce: “Ka kawo hujja a kan wannan maganar ko kuma in doke ka.” Shin a cikinku akwai wanda ya ji wannan daga Annabi (ﷺ)? Sai Ubayyu ɗan Ka’abu ya ce: “Wallahi babu mai tafiya tare da kai sai mafi ƙanƙantar cikinmu.” Abu Sa’id ya ce: “To kuma ni ne mafi ƙanƙantarsu, sai na tashi na je na faɗa wa Umar cewa na ji Annabi (ﷺ) yana faɗin haka.” [Bukhari #6245 da Muslim #2153]. An karɓo daga Anas ko waninsa ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya je gidan Sa’ad ɗan Ubadatu ya nemi izinin shiga ya ce: “Assalamu alaikum wa rahmatullahi.” Sai Sa’ad ya amsa (a ƙasa-ƙasa) ya ce: “Wa alaikumus salam wa rahmatullahi.” Amma Annabi (ﷺ) bai ji shi ba, har sai da ya yi sallama uku, Sa’ad ya amsa masa sau uku, amma bai ji shi ba sai ya tafi. Sai Sa’ad ya bi shi a baya ya ce: “Ya Manzon Allah, mahaifina da mahaifiyata fansa ne a gare ka, duk sallamar da ka yi a kunnena ka yi ta, kuma na mayar maka amma a ƙasa-ƙasa ba ka ji ni ba ne, ina so ne ka yi mini sallama da yawa don in sami albarka.” Sannan ya shigar da shi cikin gidan… [Ahmad #12406]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Busr (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Annabi (ﷺ) ya kasance idan ya zo ƙofar gidan mutane ba ya fuskantar ƙofar da fuskarsa, yakan tsaya ne a gefenta na dama ko na hagu ya ce: “Assalamu alaikum, assalamu alaikum.” A lokacin gidaje ba a sa musu labulaye. [Abu Dawud #5186]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin shiga cikin gidajen da ba su keɓanta da wasu ba, watau wuraren da aka tanada don amfanin kowa da kowa, kamar ɗakunan karatu ko shaguna a kasuwanni, ya nuna cewa babu laifi su shiga cikinsu ba tare da neman izini ba. Ya kuma bayyana cewa ya san abin da suke bayyanawa na halayensu da ayyukansu da wanda suke ɓoyewa, zai kuma yi musu sakayya a kai.
قُل لِّلۡمُؤۡمِنِينَ يَغُضُّواْ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِمۡ وَيَحۡفَظُواْ فُرُوجَهُمۡۚ ذَٰلِكَ أَزۡكَىٰ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا يَصۡنَعُونَ
Open ayah 24:30Ka ce da muminai maza su kame idanuwansu kuma su kiyaye farjinsu. Wannan shi ya fi tsarki a gare su. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne.
وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ وَلۡيَضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّۖ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوۡ ءَابَآئِهِنَّ أَوۡ ءَابَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآئِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ أَخَوَٰتِهِنَّ أَوۡ نِسَآئِهِنَّ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّ أَوِ ٱلتَّٰبِعِينَ غَيۡرِ أُوْلِي ٱلۡإِرۡبَةِ مِنَ ٱلرِّجَالِ أَوِ ٱلطِّفۡلِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يَظۡهَرُواْ عَلَىٰ عَوۡرَٰتِ ٱلنِّسَآءِۖ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِأَرۡجُلِهِنَّ لِيُعۡلَمَ مَا يُخۡفِينَ مِن زِينَتِهِنَّۚ وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Open ayah 24:31Kuma ka ce da muminai mata su kame idanuwansu kuma su kiyaye farjinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi; kuma su sanya lulluɓinsu a kan wuyan rigunansu; kada kuma su fitar da adonsu sai ga mazajensu ko iyayensu ko iyayen mazajensu ko ‘ya’yansu ko ‘ya’yayen mazajensu ko ‘yan’uwansu maza ko kuma ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata ko kuma mata ‘yan’uwansu ko kuma bayinsu ko kuma mazaje masu bin su (don neman abinci) ba kuma masu buƙatar mata ba, ko kuma ƙananan yara waɗanda ba su san sha’awar al’aurar mata ba; kada kuma su buga ƙafafuwansu don a gane abin da suka ɓoye na adon ƙafafunsu (watau mundaye). Kuma ku tuba ga Allah gaba ɗayanku ya ku waɗannan muminai don ku rabauta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa maza muminai cewa su kawar da idanuwansu daga kallon matan da bai halatta su kalle su ba, hakanan da kallon al’aurarsu, su kuma kiyaye farjinsu kada su faɗa cikin aikata haramun kamar zina ko su bayyana tsiraicinsu a fili. Wannan kame idanuwan nasu shi ne ya fi musu tsarki a wurin Allah, lalle Allah masanin abin da suke aikatawa ne zai kuma yi musu sakayya a kai. Sai kuma ya umarce shi da ya faɗa wa su ma mata muminai da su kawar da idanuwansu daga kallon abin da bai halatta su kalla ba, su kuma tsare farjinsu ta hanyar nesantar zina da suturce shi, kada kuma su kuskura su bayyana adonsu ga mazajen da ba muharramansu ba kuma ba mazajen aurensu ba, sai abin da ya fito wanda ba zai yiwu a ɓoye shi ba kamar tufafi. Sannan ya umarce su da su sanya lulluɓinsu su rufe wuyan rigunansu domin a daina ganin gashinsu da wuyansu da adonsu na wuya. Kada kuma su bayyana ɓoyayyen adonsu sai ga mazajensu na aure ko iyayensu ko iyayen mazajensu ko ‘ya’yansu ko ‘ya’yan mazajensu ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu shaƙiƙai ne ko na wajen uba ko na wajen uwa, ko mata ‘yan’uwansu, ko kuma bayin da suka mallaka maza da mata ko kuma maza masu bin su waɗanda sun daina sha’awar mata gaba ɗaya, ko kuma yara waɗanda ba su isa fahimtar al’aurar mata ba saboda ƙanƙantarsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana mata muminai buga ƙafafunsu a ƙasa don a gane abin da suke ɓoyewa na adonsu, kamar mundaye da makamantansu. Sai kuma ya yi kira ga muminai da su tuba gaba ɗayansu ga Allah saboda kuskuren da za su iya yi na kallon abin da bai halatta ba ko wani laifi na daban, domin su sami babban rabo na gidan Aljanna su kuma kuɓuta daga azabar Allah. An karɓo daga Buraida (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa Ali: “Ya kai Ali, kada ka bi kallo da wani kallon; na farko ya halatta gare ka amma na biyu bai halatta gare ka ba.” [Abu Dawud #2149]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku guji zama a kan hanyoyi.” Sai suka ce: “Ya Manzon Allah, ba mu da zaɓi, wuraren zamanmu ne muna hira.” Sai ya ce: “Idan kun ƙi to ku ba wa hanya haƙƙinta.” Sai suka ce: “Mene ne haƙƙin hanya ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Kawar da idanu da kawar da abin da zai cutar da amsa sallama da umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna. [Bukhari #2465 da Muslim #2121].
وَأَنكِحُواْ ٱلۡأَيَٰمَىٰ مِنكُمۡ وَٱلصَّٰلِحِينَ مِنۡ عِبَادِكُمۡ وَإِمَآئِكُمۡۚ إِن يَكُونُواْ فُقَرَآءَ يُغۡنِهِمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 24:32Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku da kuma na gari daga bayinku da kuyanginku. Idan sun zamanto matalauta to Allah zai wadata su daga falalarsa. Allah kuwa Mai yalwa ne, Masani.
وَلۡيَسۡتَعۡفِفِ ٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّىٰ يُغۡنِيَهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَٱلَّذِينَ يَبۡتَغُونَ ٱلۡكِتَٰبَ مِمَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ فَكَاتِبُوهُمۡ إِنۡ عَلِمۡتُمۡ فِيهِمۡ خَيۡرٗاۖ وَءَاتُوهُم مِّن مَّالِ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ ءَاتَىٰكُمۡۚ وَلَا تُكۡرِهُواْ فَتَيَٰتِكُمۡ عَلَى ٱلۡبِغَآءِ إِنۡ أَرَدۡنَ تَحَصُّنٗا لِّتَبۡتَغُواْ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَمَن يُكۡرِههُّنَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ مِنۢ بَعۡدِ إِكۡرَٰهِهِنَّ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 24:33Waɗanda kuma ba su sami wadatar yin aure ba su kame kansu har Allah Ya wadata su daga falalarsa. Waɗanda kuwa suke neman fansar kansu daga bayinku, sai ku ba su damar fansar kansu, idan kun san suna da halin iya biya; kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah da Ya ba ku. Kada kuma ku tilasta wa kuyanginku ‘yan mata a kan yin zina idan sun nemi kame kai, don ku nemi amfanin rayuwar duniya. Wanda duk kuwa ya tilasta su, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai bayan tilastawar da aka yi musu.
وَلَقَدۡ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ ءَايَٰتٖ مُّبَيِّنَٰتٖ وَمَثَلٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 24:34Haƙiƙa kuma Mun saukar muku da ayoyi mabayyana da kuma izina daga waɗanda suka wuce gabaninku, kuma da gargaɗi ga masu taƙawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su aurar da waɗanda suke ƙarƙashinsu marasa aure maza ko mata idan har sun isa auren kuma suna sha’awar sa, to su hanzarta yi musu shi don kada su faɗa wata mummunar hanya a dalilin rashin auren. Hakanan wanda yake da bayi maza ko mata da suka kai munzalin aure, to su ma su taimaka wajen yi musu auren. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku taron samari, duk wanda yake da halin yin aure daga cikinku, to ya yi aure ya fi taimakawa wajen hana kallon haram, ya fi tsare farji daga faɗa wa zina. Wanda kuwa ba zai iya yin auren ba, to sai ya yi azumi domin shi zai karya masa sha’awa.” [Bukhari #5066 da Muslim #1400]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa yin aure yana daga cikin sabubban samun wadata, don haka kada mutum talaucinsa ya hana shi yin aure, Allah ya yi masa alƙawarin wadata shi idan har ya bi umarninsa ya yi aure domin kare kansa daga faɗawa cikin saɓon Allah. Hakanan kuma kada a hana wani matar aure domin talaucinsa, saboda Allah bai yi umarni da shi ba sai domin shi ne ya ɗauki nauyin arzuta su da ci da sha. Allah mai yalwar arziƙi ne domin idan ya wadatar da wani wannan ba zai rage arziƙinsa da komai ba. Yana sane da halin da bayinsa suke ciki don haka yake umartar su da abin da zai amfane su duniya da lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci wanda bai samu ikon yin aure ba saboda ba shi da abin da zai biya sadaki ko abin da zai riƙe matar da shi, kan ya kame kansa har lokacin da Allah zai wadata shi daga yalwatacciyar falalarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da suke da bayi masu sha’awar su fanshi kawunansu daga bauta ta hanyar biyan wani kuɗi da za a yanka musu, Allah ya umarci iyayen gidansu da su ba su wannan damar matuƙar sun fahimci za su iya ɗauka kuma sun ga alamar nagarta tare da su. Sannan ya kwaɗaitar da su kan su ba su wani abu daga dukiyar da Allah ya ba su, watau su rage musu wani abu daga cikin dukiyar da suka ɗora musu da farko don fansar kawunansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu kashedi kan tilasta wa kuyangunsu masu son su tsare mutuncinsu a kan yin zina don su nemo musu dukiya. An tabbatar a cikin ruwayoyi masu dama cewa wannan aya ta sauka ne a kan Abdullahi ɗan Ubayyu ɗan Salul shugaban munafukan Madina. Shi ne yake tilasta wa kuyanginsa fita don yin zina su sama masa dukiya, to amma su ba sa son haka, suna son tsare mutuncinsu da kame kansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar domin jan kunnensa da kuma sauran masu irin halinsa da cewa, su ji tsoron Allah su daina. [Dubi, Ibn Kasir , juzu’i na 6, shafi na 55-56]. Allah ya bayyana cewa masu irin wannan mummunan aiki suna yi ne don neman abin duniya, ya bayyana cewa wanda duk ya tilasta su har suka aikata wannan laifi ba da son ransu ba, to lalle Allah mai gafara ne ga zunubbansu mai jin ƙai ne gare su, domin ya ɗauke zunubi daga kan wanda aka tursasa shi ya aikata laifi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa ya saukar musu da ayoyi bayyanannu waɗanda suke ɗauke da duk hukunce-hukuncen da suke buƙatar saninsu ba tare da wata rikitarwa ba ko shubuha. Hakanan ya saukar musu da misalai da izinoni daga labaran al\'ummun da suka shuɗe na ƙwarai da waɗanda ba na ƙwarai ba, domin su yi koyi da kyawawan ayyukansu su kauce wa munanan ayyukansu. Ya kuma saukar musu wa’azi don masu kiyaye dokokin Allah su wa’azantu da shi, su aikata umarnin Allah su kuma guje wa abin da ya hana.
۞ٱللَّهُ نُورُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ مَثَلُ نُورِهِۦ كَمِشۡكَوٰةٖ فِيهَا مِصۡبَاحٌۖ ٱلۡمِصۡبَاحُ فِي زُجَاجَةٍۖ ٱلزُّجَاجَةُ كَأَنَّهَا كَوۡكَبٞ دُرِّيّٞ يُوقَدُ مِن شَجَرَةٖ مُّبَٰرَكَةٖ زَيۡتُونَةٖ لَّا شَرۡقِيَّةٖ وَلَا غَرۡبِيَّةٖ يَكَادُ زَيۡتُهَا يُضِيٓءُ وَلَوۡ لَمۡ تَمۡسَسۡهُ نَارٞۚ نُّورٌ عَلَىٰ نُورٖۚ يَهۡدِي ٱللَّهُ لِنُورِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَيَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَٰلَ لِلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ
Open ayah 24:35Allah ne hasken sammai da ƙasa. Misalin haskensa tamkar alkuki ne da fitila take a cikinsa; fitilar kuma tana cikin ƙarau; ƙaran kuma tamkar tauraro ne na lu’ulu’u, ana kunna ta da man bishiya mai albarka ta zaitun, ita ba daga mahudar rana take ba kuma ba daga mafaɗarta ba, kuma manta kamar zai kama da kansa ko da wuta ba ta taɓa shi ba. Haske kan haske. Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga haskensa. Kuma Allah yana buga misalai ne ga mutane. Allah kuwa Masanin komai ne. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi ne hasken sammai da ƙasa kuma shi ne mai shiryar da waɗanda suke cikinsu, misalin haskensa (Mai tsarki da daukaka) kuma a zuciyar mumini kamar alkuki ne a jikin bango da fitila take cikinsa; fitilar kuwa tana cikin wani ƙarau mai haske kamar wani tauraro mai haske kai ka ce wani lu’ulu’u ne mai haske. Wannan fitilar ana kunna ta ne daga man wata bishiya mai albarka, ita ce bishiyar zaitun da babu abin da yake kare mata hasken rana safe da yamma. Manta, saboda haskensa da tatuwarsa kamar ya kama wuta da kansa ko da wata wuta ba ta shafe shi ba, to balle kuma ta shafe shi. Hasken wannan fitila a kan hasken wannan ƙaran. To haka hasken zuciyar mumini yake idan hasken shiriya ya haskaka ta. Allah kuma ya tabbatar da cewa yana datar da wanda ya ga dama daga cikin bayinsa ya bi Alƙur’ani, yana kuma bayanin abubuwa daban-daban ga mutane ta hanyar ba su misalai, kuma shi masanin komai ne babu abin da yake ɓoye masa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance idan ya tashi tsayuwar dare yana cewa: “Ya Allah, yabo da godiya da kirari sun tabbata gare ka kai kaɗai, kai ne tsayayye da Zatinka ga sammai da ƙasa da waɗanda suke cikinsu; kuma yabo da godiya da kirari sun tabbata a gare ka kai kaɗai, kai ne hasken sammai da ƙasa da waɗanda suke cikinsu…” [Bukhari #1120 da Muslim #769]. An karɓo daga Abu Musa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya tsaya a cikinmu ya faɗi kalmomi biyar ya ce: “Lalle Allah ba ya barci kuma bai dace shi ya yi barci ba; yana yin ƙasa da ma’aunin adalci yana kuma yin sama da shi, ana kai masa can sama aikin dare kafin na rana da aikin rana kafin na dare. Hijabinsa haske ne, da zai kwaranye shi da lalle hasken fuskarsa ya ƙona duk abin da ganinsa ya kai gare shi na daga halittarsa.” [Muslim #179].
فِي بُيُوتٍ أَذِنَ ٱللَّهُ أَن تُرۡفَعَ وَيُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ يُسَبِّحُ لَهُۥ فِيهَا بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ
Open ayah 24:36(Hasken) yana cikin wasu ɗakuna (watau masallatai) waɗanda Allah Ya yi umarni a ɗaukaka, a kuma ambaci sunansa a cikinsu. (Wasu mazaje) suna tasbihi gare Shi a cikinsu safe da yamma.
رِجَالٞ لَّا تُلۡهِيهِمۡ تِجَٰرَةٞ وَلَا بَيۡعٌ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَإِقَامِ ٱلصَّلَوٰةِ وَإِيتَآءِ ٱلزَّكَوٰةِ يَخَافُونَ يَوۡمٗا تَتَقَلَّبُ فِيهِ ٱلۡقُلُوبُ وَٱلۡأَبۡصَٰرُ
Open ayah 24:37Wasu mazaje ne waɗanda kasuwanci da saye da sayarwa ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka, suna jin tsoron ranar da zukata da idanuwa suke raurawa.
لِيَجۡزِيَهُمُ ٱللَّهُ أَحۡسَنَ مَا عَمِلُواْ وَيَزِيدَهُم مِّن فَضۡلِهِۦۗ وَٱللَّهُ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ
Open ayah 24:38(Suna haka ne) don Allah Ya saka musu da mafi kyan abin da suka aikata, kuma Ya ƙara musu daga falalarsa. Allah kuwa Yana arzuta wanda Ya ga dama ba da iyaka ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wancan haske da ya yi bayaninsa ana samun sa a cikin ɗakunan Allah, watau masallatai waɗanda ya yi umarni a ɗaukaka darajarsu da gine-ginensu, a kuma ambaci sunansa a cikinsu ta hanyar kiran salla da tsai da salla da zikiri. Wasu mazaje suna salla a cikinsu, suna tsarkake Allah domin neman yardarsa safe da yamma. Waɗannan mazaje ne waɗanda harkokin kasuwancinsu da saye da sayarwarsu ba sa shagaltar da su daga ambaton Allah da yin salla yadda ya kamata da bayar da zakka ga masu ita; suna jin tsoron ranar lahira, ranar da zukata suke kaɗuwa suna fatan samun kuɓuta daga azabar Allah, suna kuma jin tsoron ta auka musu. Hakanan idanuwansu suna kaɗuwa domin ba su san ina za su nufa ba don samun tsira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa sun yi haka ne ba don komai ba sai don Allah ya saka musu da mafi kyan ayyukansu, ya kuma ƙara musu daga falalarsa, Allah kuwa yana arzuta wanda ya ga dama ya ba shi sakamako mai ɗimbin yawa ba tare da lissafi ba. An karɓo daga Usman ɗan Affan (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya gina masallaci domin Allah, to Allah zai gina masa kwatankwacinsa a Aljanna.” [Bukhari #450 da Muslim #533]. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Annabi (ﷺ) ya yi umarnin a gina masallatai a unguwanni, kuma a tsaftace su a sa musu turare.” [Ahmad #26386 da Abu Dawud #455 da Tirmizi #594 da Ibn Majah #759].
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَعۡمَٰلُهُمۡ كَسَرَابِۭ بِقِيعَةٖ يَحۡسَبُهُ ٱلظَّمۡـَٔانُ مَآءً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَهُۥ لَمۡ يَجِدۡهُ شَيۡـٔٗا وَوَجَدَ ٱللَّهَ عِندَهُۥ فَوَفَّىٰهُ حِسَابَهُۥۗ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
Open ayah 24:39Waɗanda kuwa suka kafirta ayyukansu kamar kawalwalniya ne a wani faƙo wanda mai jin tsananin ƙishirwa yake zaton ruwa ne, har lokacin da ya zo gare ta ba zai samu komai ba sai ya sami Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisabinsa. Allah kuwa Mai saurin hisabi ne.
أَوۡ كَظُلُمَٰتٖ فِي بَحۡرٖ لُّجِّيّٖ يَغۡشَىٰهُ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ سَحَابٞۚ ظُلُمَٰتُۢ بَعۡضُهَا فَوۡقَ بَعۡضٍ إِذَآ أَخۡرَجَ يَدَهُۥ لَمۡ يَكَدۡ يَرَىٰهَاۗ وَمَن لَّمۡ يَجۡعَلِ ٱللَّهُ لَهُۥ نُورٗا فَمَا لَهُۥ مِن نُّورٍ
Open ayah 24:40Ko kuma kamar duffai a cikin kogi mai zurfi da raƙumin ruwa ya lulluɓe shi, daga samansa kuma akwai wani raƙumin ruwan, daga samansa (kuma) akwai wani hadari. Duffai wasu a kan wasu; idan ya fito da hannunsa ba zai iya ganin sa ba. Wanda kuma Allah bai sanya wa haske ba, to ba shi da wani haske. Bayan Allah ya ambaci halin muminai na kasancewa cikin hasken Allah a duniya wanda da shi ne suke riƙo da kyawawan ayyuka, a lahira kuma su sami babban rabo, sai kuma a nan ya ambaci halayen kafirai da asarar da suka tafka a nan duniya da yadda suka kasance cikin duhu yana dukan duhu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk ayyukan da kafirai suka yi masu kyau a nan duniya ba su da wani lada a kansu ranar alƙiyama, domin za su zama kamar kawalwalniya ne a wata ƙasa mai faƙo wanda mai jin ƙishirwa zai hango ya yi zaton ruwa ne, sai ya kama hanya ya nufi inda yake har sai ya je gare shi sai ya ga babu komai, a nan zai yi ta nadama ya kuma ci gaba da jin ƙishirwa. To kamar haka aikin kafiri yake yana zaton zai amfane shi har sai lokacin da ya mutu aka tashe shi sai ya rasa ladan wannan aiki da ya yi, sai ya haɗu da Ubangijinsa a gabansa, shi kuma ya cika masa hisabin aikinsa ba tare da ya tauye komai ba. Allah mai gaggawar hisabi ne, don haka kafirai su daina ganin nisan zuwan wannan rana, tana tafe ba makawa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayar da misali na biyu na halin da kafirai suke ciki, da cewa ayyukansu kamar duffai ne a cikin wani kogi mai zurfi da raƙumin ruwa ya lulluɓe shi daga samansa, a saman wannan raƙumin ruwan akwai wani ma irinsa, sama kuma girgije ya rufe taurarin da yake gane hanya da su, duffai wani kan wani. To duk wanda yake cikin waɗannan duffai idan ya fito da hannunsa ba zai iya ganin sa ba saboda tsananin duhu. To hakanan kafiri yake a nan duniya, yana cikin duhun jahilci da kafirci da shakka da ɗimuwa da toshewar zuciya. Allah ya tabbatar da cewa duk wanda bai arzuta shi da shiriya ba ya ɗora shi a kan aiki da littafinsa, to ba shi da wata shiriya da zai shiryu da ita ko wani littafi da zai haskaka da shi. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ba ya zaluntar mumini bisa wani kyakkyawan aiki ɗaya, zai yi masa sakayya a kansa a nan duniya, ya kuma saka masa a lahira a kansa. Amma kafiri idan ya aikata kyawawan ayyuka a nan duniya, Allah zai ciyar da shi saboda waɗannan ayyukan, har sai ya je lahira ba zai samu wani aikin lada da za a saka masa a kansa ba.” [Muslim #2808].
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱلطَّيۡرُ صَٰٓفَّٰتٖۖ كُلّٞ قَدۡ عَلِمَ صَلَاتَهُۥ وَتَسۡبِيحَهُۥۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِمَا يَفۡعَلُونَ
Open ayah 24:41Ba ka gani cewa Allah duk abin da yake sammai da ƙasa yana tasbihi ne gare Shi, haka tsuntsaye kuma sun buɗe fukafukansu sun yi sahu, kowanne ɗayansu ya san sallarsa da tasbihinsa? Allah kuwa Masanin abin da suke aikatawa ne.
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 24:42Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne; makoma kuma zuwa ga Allah take. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana nuna wa bayinsa girman ikonsa da kamalarsa, da cewa duk waɗanda suke cikin sammai da waɗanda suke bayan ƙasa suna tsarkake shi. Haka tsuntsaye suna tasbihi da tsarkake shi suna masu buɗe fukafukansu cikin sahu a sararin samaniya. Duk kuwa waɗannan halittun Allah ya san sallar mai yin salla daga cikinsu kamar ɗan’adam da tasbihin mai yin tasbihi daga cikinsu kamar tsuntsaye, kuma Allah masanin abin da suke aikatawa ne, babu wani aiki nasu da bai sani ba. Sannan ya bayyana cewa Allah ne kaɗai ke da mulkin sammai da ƙasa, kuma kowa zuwa gare shi zai koma ranar alƙiyama domin yi masa hisabi.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُزۡجِي سَحَابٗا ثُمَّ يُؤَلِّفُ بَيۡنَهُۥ ثُمَّ يَجۡعَلُهُۥ رُكَامٗا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ يَخۡرُجُ مِنۡ خِلَٰلِهِۦ وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن جِبَالٖ فِيهَا مِنۢ بَرَدٖ فَيُصِيبُ بِهِۦ مَن يَشَآءُ وَيَصۡرِفُهُۥ عَن مَّن يَشَآءُۖ يَكَادُ سَنَا بَرۡقِهِۦ يَذۡهَبُ بِٱلۡأَبۡصَٰرِ
Open ayah 24:43Shin ba ka gani cewa Allah Yana kora gizagizai sannan Ya harhaɗa tsakaninsu sannan Ya mai da su masu hawan juna, sai ka ga ruwan sama yana fitowa ta tsakankaninsa, kuma Yana saukar da wasu kasake (na gizagizai) daga sama waɗanda a cikinsu akwai ƙanƙara, sai Ya sami wanda Ya ga dama da ita (ƙanƙarar) Ya kuma kautar da ita daga wanda Ya ga dama. Hasken walƙiyarsa yana kusa da ya fauce idanu.
يُقَلِّبُ ٱللَّهُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّأُوْلِي ٱلۡأَبۡصَٰرِ
Open ayah 24:44Allah Yana jujjuya dare da yini. Lalle game da wannan tabbas akwai izina ga ma’abota hankula. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin Manzonsa (ﷺ) cewa yanzu bai duba ya ga yadda yake koro giza-gizai a sama ba sannan ya harhaɗa sashinsa da wani sashi, sannan ya mayar da shi wani kan wani, daga nan sai mutum ya ga ruwa yana zubowa daga cikin wannan girgijen. Sannan ya bayyana cewa daga giza-gizan da suka haɗo a sararin samaniya manya-manya kamar duwatsu, yake saukar da ƙanƙarar ruwa ƙanana, sai ya sami wanda ya ga dama cikin bayinsa da wannan ƙanƙarar ya kuma kautar da ita daga wanda ya ga dama daga cikinsu. Hasken walƙiyar wannan girgije yana kusa da ya fauce idanu saboda tsananin haskensa. Ashe yanzu wanda ya samar da wannan giza-gizai ya koro wa bayinsa su suka saukar musu da ruwa lokacin da suke cikin buƙatarsa domin rayuwarsu ta ɗore, ashe ba shi ne ya cancanci su bauta masa ba shi kaɗai ba tare da haɗa shi da komai ba? Sai kuma ya bayyana cewa shi ne yake jujjuya dare da rana; wannan ya zo wannan ya tafi, wani ya fi wani tsawo ko gajarta. Lalle a cikin wannan aiki nasa akwai abin izina ga masu basira, domin abin da suke ɗauke da shi na dalilai masu tabbatar da Rububiyyar Allah da Kaɗaitakarsa wajen bauta.
وَٱللَّهُ خَلَقَ كُلَّ دَآبَّةٖ مِّن مَّآءٖۖ فَمِنۡهُم مَّن يَمۡشِي عَلَىٰ بَطۡنِهِۦ وَمِنۡهُم مَّن يَمۡشِي عَلَىٰ رِجۡلَيۡنِ وَمِنۡهُم مَّن يَمۡشِي عَلَىٰٓ أَرۡبَعٖۚ يَخۡلُقُ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 24:45Kuma Allah Ya halicci kowace dabba daga ruwa; sannan daga cikinsu akwai waɗanda suke jan ciki, kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke tafiya a kan ƙafa biyu, akwai kuma waɗanda suke tafiya a kan ƙafa huɗu. Allah Yana halittar abin da Ya ga dama. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi ne ya halicci duk wani abu mai tafiya a bayan ƙasa daga ruwa, watau ɗigon maniyyi, daga cikinsu akwai waɗanda suke jan ciki kamar macizai, daga cikinsu kuma akwai masu tafiya a kan ƙafafu biyu kamar ɗan’adam da yawancin tsuntsaye, daga cikinsu kuma akwai masu tafiya da ƙafafu huɗu kamar yawancin dabbobi, don haka sassaɓawarsu a nan tare da cewa tushen abin halittarsu ɗaya ne, watau ruwan ɗigon maniyyi, yana nuna cikar Ƙudurar Allah mai yin yadda ya so, don haka ya bayyana cewa yana halittar abin da ya ga dama daga cikin abubuwan da ya ambata a nan da ma waɗanda ba a ambata ba, lalle shi mai iko ne a kan komai babu abin da zai gagare shi.
لَّقَدۡ أَنزَلۡنَآ ءَايَٰتٖ مُّبَيِّنَٰتٖۚ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 24:46Haƙiƙa Mun saukar da ayoyi masu bayyana komai da komai. Allah kuma Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.
وَيَقُولُونَ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلرَّسُولِ وَأَطَعۡنَا ثُمَّ يَتَوَلَّىٰ فَرِيقٞ مِّنۡهُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۚ وَمَآ أُوْلَٰٓئِكَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 24:47Kuma suna cewa: “Mun yi imani da Allah da kuma Manzo kuma mun bi,” sannan wata ƙungiya daga cikinsu takan ba da baya bayan wancan (imanin). Waɗannan kuwa ba muminai ba ne.
وَإِذَا دُعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَهُمۡ إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُم مُّعۡرِضُونَ
Open ayah 24:48Idan kuwa aka yi kiran su zuwa ga Allah da Manzonsa don ya yi hukunci a tsakaninsu sai ka ga wata ƙungiya daga cikinsu suna bijirewa.
وَإِن يَكُن لَّهُمُ ٱلۡحَقُّ يَأۡتُوٓاْ إِلَيۡهِ مُذۡعِنِينَ
Open ayah 24:49Idan kuwa su ne masu gaskiya sai su zo wurinsa suna masu miƙa wuya.
أَفِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَمِ ٱرۡتَابُوٓاْ أَمۡ يَخَافُونَ أَن يَحِيفَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَرَسُولُهُۥۚ بَلۡ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 24:50Shin cuta ce a cikin zukatansu, ko kuwa suna tababa ne, ko kuma suna tsoron Allah da Manzonsa su zalunce su ne? A’a, waɗannan su ne azzalumai.
إِنَّمَا كَانَ قَوۡلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذَا دُعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَهُمۡ أَن يَقُولُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۚ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Open ayah 24:51Muminai ba su da wata magana idan aka kira su zuwa ga Allah da Manzonsa don ya yi hukunci a tsakaninsu sai faɗar: “Mun ji kuma mun bi.” Waɗannan kuwa su ne masu babban rabo.
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَخۡشَ ٱللَّهَ وَيَتَّقۡهِ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
Open ayah 24:52Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinsa, to waɗannan su ne masu rabauta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin rahamar da ya yi wa bayinsa da ya saukar musu da littafi wanda ya ƙunshi ayoyi bayyanannu masu nuna hukunce-hukuncen shari’a da manya-manyan manufofinta da kyawawan ɗabi’u. Ya tabbatar da cewa shi ne mai shiryar da wanda ya ga dama ya ɗora shi a kan tafarki madaidaici miƙaƙƙe ɗoɗar babu karkata a tare da shi, domin ya kai shi zuwa ga shiga gidan Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halayen munafukai waɗanda zukatansu ke cike da shakka da cutar munafurci da ƙarya, su ne masu cewa sun yi imani da Allah da Manzonsa sun kuma bi Allah da Manzonsa, to amma duk wannan magana ce ta fatar baki ba ta shiga zukatansu ba, don haka ne wata ƙungiya daga cikinsu za su ba da baya su bijire wa ɗa’a ga Allah da Manzonsa, su ƙi bin umarninsa su ƙi hanuwa daga abin da suka hana su. Sai Allah ya tabbatar da cewa waɗannan mutane ba muminai ne na gaskiya ba, ko da kuwa suna cika baki cewa sun yi imani, to ƙarya suke yi kawai. Allah ya bayyana abin da yake tabbatar da ƙaryarsu da munafuncinsu, da cewa, idan rigima ta haɗa su da wani sai aka ce musu su zo Allah da Manzonsa su yi musu hukunci sai kawai a ga wasu suna bijire wa hukuncinsu saboda tsabar munafurci da ke cike da zukatansu. Amma fa idan su ne suke da gaskiya sai kawai a gan su da sauri sun zo wurin Manzon Allah (ﷺ) suna ƙasƙantar da kai, ba don suna son hukuncin Allah da Manzonsa ba, sai don hukuncinsu a nan ya dace da buƙatarsu da son zuciyarsu. Don haka wannan ba yabo ne a gare su ba, suka ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da ya jawo musu ƙin amincewa da hukuncin Allah da na Manzonsa da cewa, abin da yake cikin zukatansu na cutar munafurci da ta riga ta kama su da kuma shakkar manzancin Annabi da suke yi na ganin shi ba Manzo ne daga Allah ba, don haka ba za su bi hukuncinsa ba, ko kuma suna jin zai nuna musu irin halinsu ne ya yi musu hukunci na zalunci ba adalci ba, Allah ya tabbatar musu da cewa su ne azzalumai, domin su ne suke guje wa gaskiya da hukunci na adalci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halayen muminai waɗanda suke yarda da hukuncin Allah da Manzonsa ko da kuwa ya saɓa wa son zuciyarsu, da cewa su duk sa’adda aka neme su su zo Allah da Manzonsa su yi musu hukunci a kan wani abu da ya faru a tsakaninsu a nan take sukan amsa su kuma ce sun ji maganar da ake faɗa musu sun kuma bi umarnin da ake ba su. Allah ya tabbatar da cewa masu irin wannan hali su ne masu rabauta duniya da lahira. Duk wanda ya bi Allah da Manzonsa ya miƙa wuya ga hukuncinsu ya ji tsoron abin da saɓon Allah zai jawo masa, ya ji tsoron azabarsa ta hanyar aiki da umarninsa da guje wa haninsa, to waɗannan ne kaɗai masu samun babban rabo a lahira.
۞وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَئِنۡ أَمَرۡتَهُمۡ لَيَخۡرُجُنَّۖ قُل لَّا تُقۡسِمُواْۖ طَاعَةٞ مَّعۡرُوفَةٌۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 24:53Suka kuma rantse da Allah iya iyawarsu cewa lalle idan ka umarce su (da fita) tabbas za su fita. Ka ce (da su): “Ku daina rantse-rantse; biyayya (taku ta ƙarya) sananniya ce. Lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne.”
قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيۡكُم مَّا حُمِّلۡتُمۡۖ وَإِن تُطِيعُوهُ تَهۡتَدُواْۚ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 24:54Ka ce (da su): “Ku bi Allah kuma ku bi Manzo; sannan idan kuka ba da baya, to lalle nauyin abin da aka ɗora masa ne kawai a kansa; kuma nauyin da aka ɗora muku yana kanku, idan kuwa kuka bi shi za ku shiriya. Ba kuwa abin da yake kan Manzo sai isar da aike mabayyani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fallasa halin munafukai da ƙaryarsu yayin da suke yin rantsuwa iyakar rantsuwarsu cewa, idan Manzon Allah (ﷺ) ya umarce su da fita jihadi don Allah, tabbas za su fita. Allah ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa su daina ma rantsuwa, domin kuwa ƙaryarsu sananna ce, hakanan cika bakinsu da sunan biyayya abu ne sananne. Saboda Allah masanin duk abin da suke aikatawa ne, ko da kuwa suna ganin sun yi shi a ɓoye ne, Allah ya sani zai kuma yi musu sakayya a kai. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa wa waɗannan munafukan cewa su yi wa Allah da Manzonsa ɗa’a a zahirinsu da baɗininsu, idan kuwa suka kauce wa abin da aka umarce su da shi, to su sani cewa kawai nauyin da aka ɗora masa shi ne isar musu da saƙon Allah, ya kuma isar, su ma kuma nauyin da yake kansu shi ne su yi masa biyayya, su yi aiki da abin da ya zo musu da shi, to amma sun bijire masa, mummunan halinsu ya bayyana kenan. Idan kuwa suka bi Manzon Allah (ﷺ) to za su shiriya, su kama tafarki madaidaici wanda zai kai su har gidan Aljanna. Don haka zaɓi ya rage nasu. Allah kuwa shi ne mai yi musu hisabi a ranar alƙiyama ba Manzon Allah ba.
وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَيَسۡتَخۡلِفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ كَمَا ٱسۡتَخۡلَفَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمۡ دِينَهُمُ ٱلَّذِي ٱرۡتَضَىٰ لَهُمۡ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّنۢ بَعۡدِ خَوۡفِهِمۡ أَمۡنٗاۚ يَعۡبُدُونَنِي لَا يُشۡرِكُونَ بِي شَيۡـٔٗاۚ وَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ
Open ayah 24:55Allah kuwa Ya yi wa waɗanda suka yi imani daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alƙawarin lalle zai sanya su halifofi a bayan ƙasa kamar yadda Ya sanya waɗanda suke gabaninsu halifofi, kuma lalle zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, tabbas kuma zai dawo musu da zaman lafiya bayan zamantowarsu cikin tsoro. Su bauta mini, ba sa yin shirkar komai da Ni. Wanda kuwa ya kafirta bayan wannan, to waɗannan su ne fasiƙai.
وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Open ayah 24:56Kuma ku tsai da salla ku kuma ba da zakka kuma ku bi Manzo don a ji ƙan ku.
لَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَمَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُۖ وَلَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 24:57Kada kuma ka tsammaci waɗanda suka kafirta za su gagara a bayan ƙasa, kuma makomarsu wuta ce; makoma kuwa ta munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawari ga muminai waɗanda suka yi imani da Allah suka kuma yi ayyuka na gari da cewa zai ba su nasara a kan maƙiyansu, ya mayar da su halifofi a bayan ƙasa kamar yadda ya mayar da muminan farko halifofi, watau kamar mutanen Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bayan hallakar da Fir’auna da rundunarsa. Hakanan ya yi musu alƙawarin zai tabbatar musu da addininsu wanda ya yarje musu, watau Musulunci ya zama addini mai izza da daraja, sannan kuma ya canja musu tsoron da suke rayuwa a cikinsa da zaman lafiya da kwanciyar hankali su yi ta bautar Allah shi kaɗai ba tare da suna haɗa shi da komai ba. Amma kuma ya gargaɗe su da cewa, duk wanda ya kafirce wa waɗannan ni’imomin na Allah daga baya, to waɗannan su ne fasiƙai masu kauce wa ɗa’a ga Allah da yin ɓarna a bayan ƙasa bayan gyaranta. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya umarci muminai da su tsayar da salla yadda ya kamata su kuma bayar da zakkar dukiyoyinsu, sannan su bi Manzon Allah ta hanyar aiki da umarninsa da guje wa haninsa, don da wannan ne kawai za su sami rahamar Allah. Sai kuma ya lallashi Manzonsa da cewa kar ya zaci cewa waɗanda suka kafirce wa Allah, suka riƙa yaƙar sa da mabiyansa, za su gagare shi ko su kuɓuce masa lokacin da ya yi niyyar saukar musu da azabarsa, Allah ba zai ƙyale su haka ba sai ya nuna musu mummunan ƙarshensu, ya kuma tabbatar masa da cewa makomarsu a ranar alƙiyama wutar Jahannama ce, kuma tir da wannan makoma tasu.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِيَسۡتَـٔۡذِنكُمُ ٱلَّذِينَ مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَبۡلُغُواْ ٱلۡحُلُمَ مِنكُمۡ ثَلَٰثَ مَرَّٰتٖۚ مِّن قَبۡلِ صَلَوٰةِ ٱلۡفَجۡرِ وَحِينَ تَضَعُونَ ثِيَابَكُم مِّنَ ٱلظَّهِيرَةِ وَمِنۢ بَعۡدِ صَلَوٰةِ ٱلۡعِشَآءِۚ ثَلَٰثُ عَوۡرَٰتٖ لَّكُمۡۚ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ وَلَا عَلَيۡهِمۡ جُنَاحُۢ بَعۡدَهُنَّۚ طَوَّٰفُونَ عَلَيۡكُم بَعۡضُكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Open ayah 24:58Ya ku waɗanda suka yi imani, bayinku da kuma waɗanda ba su isa mafarki ba a cikinku (watau waɗanda ba su balaga ba) su nemi izininku sau uku. Kafin sallar Asuba da sanda kuke tuɓe tufafinku a lokacin garjin rana da kuma bayan sallar Lisha. Lokatai ne guda uku na tsiraicinku. Babu laifi a kanku ko a kansu bayansu (waɗannan lokatai). Masu shige da fice ne a gare ku sashinku bisa sashi. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyi. Allah kuma Masani ne, Mai hikima.
وَإِذَا بَلَغَ ٱلۡأَطۡفَٰلُ مِنكُمُ ٱلۡحُلُمَ فَلۡيَسۡتَـٔۡذِنُواْ كَمَا ٱسۡتَـٔۡذَنَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Open ayah 24:59Idan kuma yara daga cikinku suka isa mafarki (watau suka balaga) sai su nemi izini kamar yadda waɗanda suke gabaninsu suka riƙa neman izini. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyinsa. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima.
وَٱلۡقَوَٰعِدُ مِنَ ٱلنِّسَآءِ ٱلَّٰتِي لَا يَرۡجُونَ نِكَاحٗا فَلَيۡسَ عَلَيۡهِنَّ جُنَاحٌ أَن يَضَعۡنَ ثِيَابَهُنَّ غَيۡرَ مُتَبَرِّجَٰتِۭ بِزِينَةٖۖ وَأَن يَسۡتَعۡفِفۡنَ خَيۡرٞ لَّهُنَّۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 24:60Tsofaffin mata kuwa waɗanda ba sa tsammanin yin aure to babu laifi a kansu su sauke lulluɓinsu, amma ba masu fitar da adonsu ba; amma kuma su yi lulluɓi shi ya fi zama alheri a gare su. Allah kuwa Mai ji ne, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukunce-hukunce na neman izinin shiga gidaje daga bayi da barori da ƙananan yara waɗanda ba su balaga ba. Allah ya kirawo muminai waɗanda suka yi imani da Allah suke aiki da shari’arsa, ya umarce su da su koya wa bayinsu maza da mata da ‘ya’yansu waɗanda ba su balaga ba cewa, su nemi izinin shiga wurarensu a lokuta guda uku. Na farko, kafin sallar Asuba lokacin da suke canza tufafin barcinsu su sanya tufafin zaman gida. Na biyu, lokacin barcin ƙailula na Azahar yayin da suke cire tufafinsu su sanya na kwanciya domin hutawa. Na uku, bayan sallar Lisha, domin lokaci ne da suke cire tufafinsu su saka tufafin barci. Allah ya bayyana cewa waɗannan lokuta ne guda uku na tsiraicinsu, don haka kada yaran su shiga inda suke sai sun nemi izininsu. Sai kuma ya bayyana cewa sauran lokutan kuma da ba waɗannan ukun ba, babu wani laifi a kansu ko a kan yaran su shiga inda suke ba tare da sun nemi izinin shigowa ba, domin su masu yawan shigi da fici ne gare su, domin buƙatarsu da yi musu hidima. Don haka kallafa musu neman izini yayin shiga wajensu a kowane lokaci akwai matsawa a gare su da ma su magidantan baki ɗaya. Allah ya bayyana cewa kamar yadda ya yi musu bayanin hukunce-hukuncen neman izini, to hakanan yake bayyana musu ayoyinsa masu nuna musu hukunce-hukuncen da ya shar’anta musu. Allah masani ne ga duk wata maslaha da ta danganci bayinsa, mai hikima ne cikin duk abin da ya shar’anta musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da su cewa idan ‘ya’yansu ƙanana suka balaga, to lallai su nemi izninsu duk sanda suka tashi shiga inda suke a kowane lokaci kamar yadda aka yi bayanin wannan hukuncin a baya game da manya. Kamar yadda Allah ya yi wannan bayanin a nan, to hakanan yake bayyana musu ayoyinsa, kuma shi masani ne ga duk wata maslaha ta bayinsa, mai hikima ne cikin hukunce-hukuncensa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin lulluɓin mata tsofaffi tukuf, waɗanda saboda tsufa ma sun daina al’ada balle ɗaukar ciki, waɗanda ba sa tsammanin wani aure, to waɗannan babu laifi a kansu idan sun sassauta lulluɓinsu kamar mayafi ko niƙabi ba kuma tare da sun fito cikin kwalliya ba, to amma dai su yi lulluɓin cikakke shi ne ya fi musu alheri. Allah mai jin komai ne, masanin ayyukan kowa, don haka zai yi wa kowa sakayya daidai aikinsa mai kyau da maras kyau.
لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞ وَلَا عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ أَن تَأۡكُلُواْ مِنۢ بُيُوتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ ءَابَآئِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أُمَّهَٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ إِخۡوَٰنِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَخَوَٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَعۡمَٰمِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ عَمَّٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَخۡوَٰلِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ خَٰلَٰتِكُمۡ أَوۡ مَا مَلَكۡتُم مَّفَاتِحَهُۥٓ أَوۡ صَدِيقِكُمۡۚ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَأۡكُلُواْ جَمِيعًا أَوۡ أَشۡتَاتٗاۚ فَإِذَا دَخَلۡتُم بُيُوتٗا فَسَلِّمُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ تَحِيَّةٗ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ مُبَٰرَكَةٗ طَيِّبَةٗۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 24:61Babu wani laifi a kan makaho, babu kuma wani laifi a kan gurgu, kuma babu wani laifi a kan marar lafiya ko kuma a kanku, kan ku ci a gidajenku ko a gidajen iyayenku maza ko a gidajen iyayenku mata ko a gidajen ‘yan’uwanku maza ko a gidajen ‘yan’uwanku mata ko a gidajen baffanninku ko a gidajen gwaggwanninku ko kuma a gidajen kawunnanku ko kuma a gidajen yagwalgwalanku, ko kuma abin da kuka mallaki mabuɗansa, ko kuma na abokinku. Babu wani laifi a kanku ku ci tare ko kuma daban-daban, sannan idan za ku shiga gidaje sai ku yi wa junanku sallama, (wannan) gaisuwa ce daga wurin Allah mai albarka tsattsarka. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyi don ku hankalta. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin sauƙin da ya yi wa masu larura kan wasu ayyuka na wajibi waɗanda ba za su iya aikatawa ba saboda larurarsu, Allah ya bayyana cewa babu wani laifi a kan makaho da ba ya gani da gurgu da marar lafiya idan sun zamanto ba za su iya wasu ayyuka na wajibi ba kamar jihadi. Sai kuma ya bayyana wa muminai hukuncin cin abinci a wasu gidajen da ba nasu ba, da cewa, babu laifi a kansu su ci abinci a gidansu kamar gidajen ‘ya’yansu, ko su ci a gidan iyayensu maza ko mata ko a gidan ‘yan’uwansu maza da mata ko kuma a gidajen kawunnansu maza da mata ko a gidajen yagwalgwalansu mazansu da matansu ko kuma a cikin gidajen da aka danƙa kula da su a hannunsu, kamar mai gadin lambu. Hakanan babu laifi su ci a gidajen abokansu domin bisa ga al’ada wannan abu ne da babu wata damuwa a cikinsa. Sannan ya bayyana cewa babu laifi ‘yan gida ɗaya su haɗu su ci a kwano ɗaya, ko kuma su rarrabu kowa ya ci a kwanonsa. An karɓo daga Wahshi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya koka wa Manzon Allah (ﷺ) cewa suna cin abinci amma ba sa ƙoshi, sai Manzon Allah ya ce masa: “Wataƙila kuna ci ne daban-daban; ku haɗu tare ku ci abincinku, ku kuma ambaci sunan Allah a kansa, za a sanya muku albarka a cikinsa.” [Ahmad #16078 da Abu Dawuda #3764 da Ibn Majah #3286]. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abincin da Allah ya fi so shi ne wanda hannaye suka yawaita a kansa.” [Abu Ya’ala #2045 da Tabarani, Al-Ausat #7313]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da yin sallama ga junansu a duk lokacin da suka zo shiga gidajensu ko gidajen wasu, watau su ce: “Assalamu Alaikum .” Idan kuwa babu kowa a gidan sai su ce: “Assalamu Alaina Wa Ala Ibadillahis Salihin .” Allah ya nuna musu cewa wannan gaisuwa ce mai albarka daga Allah da ya shar’anta musu ita saboda za ta haifar musu da soyayya da ƙarin danƙon zumunci a junansu, kuma tsarkakakkiya ce da take tsarkake zuciyar duk mai yin ta ko wanda ake yi masa ita. Allah ya ambata musu cewa irin waɗannan bayanai da ya yi musu a wannan Sura, to hakanan yake bayanin ayoyinsa ga mutane domin su fahimce su su yi aiki da su a rayuwarsu.
إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَإِذَا كَانُواْ مَعَهُۥ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ جَامِعٖ لَّمۡ يَذۡهَبُواْ حَتَّىٰ يَسۡتَـٔۡذِنُوهُۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسۡتَـٔۡذِنُونَكَ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ فَإِذَا ٱسۡتَـٔۡذَنُوكَ لِبَعۡضِ شَأۡنِهِمۡ فَأۡذَن لِّمَن شِئۡتَ مِنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمُ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 24:62Muminai na haƙiƙa (su ne) waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, idan kuma suka kasance tare da shi bisa wani al’amari na jama’a, to ba za su tafi ba har sai sun nemi izininsa. Lalle waɗanda suke neman izininka waɗannan (su ne) waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa. To idan sun nemi izininka saboda wani sha’aninsu, sai ka yi izini ga wanda ka ga dama daga cikinsu, kuma ka nema musu gafarar Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama.
لَّا تَجۡعَلُواْ دُعَآءَ ٱلرَّسُولِ بَيۡنَكُمۡ كَدُعَآءِ بَعۡضِكُم بَعۡضٗاۚ قَدۡ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنكُمۡ لِوَاذٗاۚ فَلۡيَحۡذَرِ ٱلَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦٓ أَن تُصِيبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ يُصِيبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Open ayah 24:63Kada ku mayar da kiran Manzo a tsakaninku kamar kiran junanku ga juna. Haƙiƙa Allah Yana sane da waɗanda suke zare jiki daga cikinku a ɓoye. To lalle waɗanda suke saɓa wa umarninsa su ji tsoron kada wata fitina ta shafe su ko kuma wata azaba mai raɗaɗi ta same su.
أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ قَدۡ يَعۡلَمُ مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ وَيَوۡمَ يُرۡجَعُونَ إِلَيۡهِ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُواْۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ
Open ayah 24:64Ku saurara, lalle abin da yake sammai da ƙasa na Allah ne; haƙiƙa Yana sane da abin da ku kuke kansa, da kuma ranar da za a komar da su zuwa gare Shi, sannan Ya ba su labarin abin da suka aikata. Allah Masanin komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai wani ladabin na musamman, watau neman izini lokacin da suka so fita daga wajen taron da suke yi da Manzon Allah (ﷺ), kamar yadda ya bayyana musu ladabin neman izininsa idan sun zo shiga wajensa. Allah ya bayyana cewa muminai na gaskiya su ne waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ); idan kuma suna tare da Manzon Allah a wurin wani taro da ya haɗa su don neman shawara ko tattauna wata maslaha ta addini ko ta al’umma, to kada wani ya bar wurin wannan taro har sai ya nemi izini daga wurin Manzon Allah (ﷺ). Allah ya tabbatar wa Manzonsa cewa waɗannan da suke neman izininsa domin fita daga wurin taro saboda wani uzuri da ya taso musu su ne waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ) imani na haƙiƙa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzon Allah (ﷺ) da cewa idan wani daga cikinsu yana cikin wani uzuri yana buƙatar a yi masa izini don sauke wannan uzurin nasa, to Annabi (ﷺ) ya yi wa wanda ya ga dama daga cikinsu izinin tafiya idan ya fahimci yana da ƙaƙƙarfan uzuri da zai sa ya tafi ya bar taron. Sannan ya umarce shi da ya nema musu gafarar Allah domin akwai yiwuwar samun gazawa cikin uzurin da wasu za su bijiro da shi har Annabi (ﷺ) ya yi musu izini ba tare da sun cancanci hakan ba, Allah yana gafarta zunubban waɗanda suka tuba daga cikin bayinsa, yana jin ƙan su da rahama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai wani haƙƙi na Manzon Allah a kansu wanda yake nuna girmamawa gare shi, da cewa, kada su riƙa kiran sa da tsurar sunansa, watau ɗayansu ya riƙa cewa ‘Ya Muhammadu’ ko ‘Ya Muhammadu ɗan Abdullahi’ ko ‘Ya ɗan Abdullahi’, kamar dai yadda suke kiran junansu. Idan za su kira shi su ce: ‘Ya Manzon Allah’ ko ‘Ya Annabin Allah’. Hakanan idan ya kirawo su wani taro, to kada su ɗauki kiransa da rashin muhimmanci kamar yadda suke ɗaukar kiraye-kirayen junansu. Su gaggauta amsa kiransa. Allah ya tabbatar musu da cewa ya san waɗanda suke zare jiki daga cikinsu su fita daga wurin taro ba tare da sun nemi izinin Manzon Allah (ﷺ) ba, don haka sai ya gargaɗe su da cewa, lalle masu saɓa wa umarnin Manzon Allah (ﷺ) su shiga taitayinsu kada wani bala’i ya auka musu ko kuma wata azaba mai raɗaɗi ta same su a sanadiyyar saɓa umarninsa. Sai kuma Allah (ﷺ) ya rufe Surar da bayyana cewa duk abin da yake cikin sammai da wanda yake bayan ƙasa halittarsa ne, mulkinsa ne, ƙarƙashin gudanarwarsa yake, don haka ya san duk wani hali da bayinsa suke ciki kuma ranar alƙiyama, ranar da za a mayar da su wajensa zai ba su dukkan labaran abin da suka aikata a duniya, domin shi masanin komai ne.