الفرقان

Al-Furqaan

The Criterion · Surah 25 · Ayahs: 77 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. تَبَارَكَ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡفُرۡقَانَ عَلَىٰ عَبۡدِهِۦ لِيَكُونَ لِلۡعَٰلَمِينَ نَذِيرًا

    Open ayah 25:1

    (Allah) Wanda Ya saukar wa Bawansa Alƙur’ani don ya zamo mai gargaɗi ga talikai albarkatunsa sun yawaita.

  2. ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَخَلَقَ كُلَّ شَيۡءٖ فَقَدَّرَهُۥ تَقۡدِيرٗا

    Open ayah 25:2

    (Shi ne) Wanda mulkin sammai da ƙasa nasa ne, kuma bai riƙi wani ɗa ba, ba kuma Shi da wani abokin tarayya a cikin mulkin, Ya kuma halicci kowanne abu, sannan Ya ajiye shi a irin gwargwadon da ya dace da shi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da tabbatar da cewa shi ne wanda alheransa da albarkatunsa suke da yawa; mafi girmansu kuwa shi ne saukar da Alƙur’ani da ya yi ga bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ). Wannan Alƙur’ani kuwa shi ne mai rarrabe tsakanin ƙarya da gaskiya. Ya saukar masa da shi kuma don ya zamanto mai gargaɗi ga talikai mutane da aljannu ya kuma tsoratar da su azabar Allah. Sannan Allah ya bayyana girmansa da yalwar mulkinsa da cewa shi ne kaɗai mamallakin sammai da ƙasa, dukkansu halittarsa ne kuma bayinsa ne kuma a ƙarƙashin ikonsa suke. Kuma ba shi da ɗa ko wani abokin tarayya tare da shi a mulkinsa. Shi ne ya halicci komai ya ƙaddara halittarsu daidai gwargwadon hikimarsa da iliminsa, watau ya ajiye komai inda ya dace da shi.

  3. وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗ لَّا يَخۡلُقُونَ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ وَلَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا وَلَا يَمۡلِكُونَ مَوۡتٗا وَلَا حَيَوٰةٗ وَلَا نُشُورٗا

    Open ayah 25:3

    Kuma suka riƙi ababen bauta ba Shi ba, ba sa halittar komai, alhali kuwa su ake halittawa, kuma ba sa mallakar cuta ko amfani ga kawunansu, ba sa kuma mallakar kashewa ko rayawa ko tashi (bayan mutuwa). A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai sun riƙi wasu abubuwan bauta ba Allah ba, waɗanda suke ɗauke da tawaya ta fuskoki da dama, daga cikinsu ya ambaci huɗu: <b>Na farko </b>, ba sa iya halittar komai komin ƙanƙantarsa. Abin bauta kuwa dole ne ya zama mai ikon halitta. <b>Na biyu </b>, su halittu ne, duk wani mahaluƙi kuwa mabuƙaci ne. Abin bauta kuma dole ne ya zamo mawadaci ba mabuƙaci ba. <b>Na uku </b>, ba sa mallakar wa kawunansu cuta ko amfani ballantana ga wani. Duk mai irin wannan siffar bai dace a bauta masa ba. <b>Na huɗu </b>, ba su da ikon sarrafa komai, domin ba sa iya kashewa ko rayawa ko tayar da matattu bayan mutuwarsu. Don haka ta ƙaƙa za a kirawo su abin bauta?

  4. وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ إِفۡكٌ ٱفۡتَرَىٰهُ وَأَعَانَهُۥ عَلَيۡهِ قَوۡمٌ ءَاخَرُونَۖ فَقَدۡ جَآءُو ظُلۡمٗا وَزُورٗا

    Open ayah 25:4

    Waɗanda kuma suka kafirta suka ce: “Wannan (Alƙur’ani) ba komai ba ne sai ƙarya da ya ƙage ta kuma wasu mutane daban suka taimake shi a kansa.” To haƙiƙa sun zo da zalunci da kuma ƙarya.

  5. وَقَالُوٓاْ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٱكۡتَتَبَهَا فَهِيَ تُمۡلَىٰ عَلَيۡهِ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا

    Open ayah 25:5

    Suka kuma ce: “Tatsuniyoyin mutanen farko ne da ya rubuta su, waɗanda ake masa shiftar su safe da yamma.”

  6. قُلۡ أَنزَلَهُ ٱلَّذِي يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

    Open ayah 25:6

    Ka ce (da su): “Wanda Yake sane da asirin sammai da ƙasa Shi Ya saukar da shi. Lalle Shi Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin ƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafiran Larabawa suka riƙa ƙaryata Alƙur’ani har suna tuhumar Manzon Allah (ﷺ) da cewa shi ne ya ƙirƙiro shi da kansa, wasu mutane wai suka taimaka masa wajen ƙirƙirarsa. Suna nufin Yahudawa ne suka riƙa koya wa Manzon Allah (ﷺ) abin da yake faɗa da sunan Alƙur’ani. Allah ya tabbatar da cewa wannan maganar tasu zalunci ne kuma ƙarya ce kawai suke faɗa. Alƙur’ani maganar Allah ce ba zai yiwu mutum ko aljan su iya kawo kamarsa ba, su ma masu ƙaryatawar sun san hakan. Sannan Allah ya bayyana wata ƙarya ta biyu da suke yi dangane da Alƙur’ani, inda suke cewa, Alƙur’ani tatsuniyoyin mutanen farko ne da ƙarairayin da suka rubuta, shi kuma Annabi (ﷺ) ya riƙa juyar su a rubuce, ana karanta masa su safe da yamma. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗa musu cewa, wanda ya saukar da Alƙur’ani shi ne masanin ɗaukacin abin da yake cikin sammai da ƙasa, don haka duk abin da yake cikin Alƙur’ani gaskiya ne babu ƙarya a ciki. Amma duk da haka sai da ya kwaɗaitar musu da tuba da neman gafarar Allah a kan ƙaryar da suke ƙirawa, ya tabbatar musu da cewa lalle shi mai karɓar tuba ne mai yawan gafara ne mai yawan jin ƙai.

  7. وَقَالُواْ مَالِ هَٰذَا ٱلرَّسُولِ يَأۡكُلُ ٱلطَّعَامَ وَيَمۡشِي فِي ٱلۡأَسۡوَاقِ لَوۡلَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مَلَكٞ فَيَكُونَ مَعَهُۥ نَذِيرًا

    Open ayah 25:7

    Suka kuma ce: “Me ya sa wannan Manzo yake cin abinci kuma yake tafiya cikin kasuwanni? Me ya hana a saukar masa da mala’ika, sai ya zama mai gargaɗi tare da shi?

  8. أَوۡ يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡهِ كَنزٌ أَوۡ تَكُونُ لَهُۥ جَنَّةٞ يَأۡكُلُ مِنۡهَاۚ وَقَالَ ٱلظَّٰلِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلٗا مَّسۡحُورًا

    Open ayah 25:8

    Ko a jefo masa wata taskar dukiya ko ya zama yana da wani lambu wanda <b>daga gare shi zai riƙa ci?” Sai azzalumai suka ce “Ba wanda kuke bi sai wani mutum wanda aka yi wa sihiri!”

  9. ٱنظُرۡ كَيۡفَ ضَرَبُواْ لَكَ ٱلۡأَمۡثَٰلَ فَضَلُّواْ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ سَبِيلٗا

    Open ayah 25:9

    To ka dubi yadda suka riƙa buga maka misali, sai suka ɓata, don haka ba za su iya bin hanyar shiriya ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wautar kafirai a fili yayin da suka kawo wasu siffofi biyar waɗanda suke ganin wai su suka hana su yarda Annabi Muhammadu (ﷺ) Manzon Allah ne, waɗannan siffofi kuwa su ne: <b>Na ɗaya </b>, sun ce me ya sa yana Manzo amma kuma yake cin abinci? Watau dai suna ganin su da shi babu bambanci, domin su ma suna cin abinci suna shan abin sha, shi ma yana ci yana sha. <b>Na biyu </b>, yana fita kasuwa neman abinci. Watau idan haka yake to da me ya fi su kenan? <b>Na uku </b>, me ya hana a saukar masa da mala’ika wanda za su riƙa fita wa’azi tare, idan ya faɗi magana ya gaskata shi, ya kuma mayar da martani ga duk wanda ya nemi ya saɓa masa? <b>Na huɗu </b>, suka ce kuma me ya hana a saukar masa wata taska daga sama wadda za ta ishe shi duk buƙatunsa na yau da kullum, ba sai ya tafi cin kasuwa ba? <b>Na biyar </b>, suka ce kuma me ya hana ya zama yana da wani lambu wanda zai riƙa cin ‘ya’yan itatuwansa da shuke-shukensa, ba sai ya tafi nema a kasuwa ba? Sai kuma suka ce wa muminai da suka yi imani da manzancin Annabi (ﷺ) wai ba Manzo suke bi ba, kawai dai suna bin wani sihirtaccen mutum ne wanda ya rasa hankalinsa a sanadiyyar sihiri da aka yi masa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya duba ya kuma yi mamakin yadda waɗannan kafirai suke ta siffanta shi da siffofi daban-daban, wani lokaci su ce masa mai sihiri wani lokaci kuma su ce mawaƙi ko su ce boka ko mai taɓin hankali. Saboda haka suka ɓata suka kasa gane hanyar shiriya, suka kuma kasa samun hanyar da za su soki gaskiyar Manzo (ﷺ) da amanarsa.

  10. تَبَارَكَ ٱلَّذِيٓ إِن شَآءَ جَعَلَ لَكَ خَيۡرٗا مِّن ذَٰلِكَ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ وَيَجۡعَل لَّكَ قُصُورَۢا 

    Open ayah 25:10

    Albarkatun (Allah) sun yawaita, wanda idan Ya ga dama sai Ya sanya maka alheri fiye da waɗannan: (su ne) gonakai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, Ya kuma sanya maka maka-makan gidaje.

  11. بَلۡ كَذَّبُواْ بِٱلسَّاعَةِۖ وَأَعۡتَدۡنَا لِمَن كَذَّبَ بِٱلسَّاعَةِ سَعِيرًا

    Open ayah 25:11

    Ba haka ba ne, sun dai ƙaryata tashin alƙiyama ne; Mun kuwa tanadi (wutar) Sa’ira ga wanda ya ƙaryata tashin alƙiyama.

  12. إِذَا رَأَتۡهُم مِّن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ سَمِعُواْ لَهَا تَغَيُّظٗا وَزَفِيرٗا

    Open ayah 25:12

    Idan (wutar) ta hango su daga wuri mai nisa sai su ji tafarfasa da gurnaninta.

  13. وَإِذَآ أُلۡقُواْ مِنۡهَا مَكَانٗا ضَيِّقٗا مُّقَرَّنِينَ دَعَوۡاْ هُنَالِكَ ثُبُورٗا

    Open ayah 25:13

    Idan kuwa aka jefa su cikinta a wani wuri ƙuntatacce nata, suna ƙuƙunce, sai su riƙa kiran hallaka a can.

  14. لَّا تَدۡعُواْ ٱلۡيَوۡمَ ثُبُورٗا وَٰحِدٗا وَٱدۡعُواْ ثُبُورٗا كَثِيرٗا

    Open ayah 25:14

    (Sai a ce da su): “A yau kada ku kirawo hallaka ɗaya kawai, ku kirawo hallaka da yawa!”

  15. قُلۡ أَذَٰلِكَ خَيۡرٌ أَمۡ جَنَّةُ ٱلۡخُلۡدِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۚ كَانَتۡ لَهُمۡ جَزَآءٗ وَمَصِيرٗا

    Open ayah 25:15

    Ka ce (da su): “Yanzu wannan ne ya fi alheri, ko kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa masu taƙawa alƙawarinta, ta zama sakamako da makoma a gare su?”

  16. لَّهُمۡ فِيهَا مَا يَشَآءُونَ خَٰلِدِينَۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ وَعۡدٗا مَّسۡـُٔولٗا

    Open ayah 25:16

    Suna da duk abin da suka ga dama a cikinta, masu madawwama ne. (Wannan kuma) ya kasance alƙawari ne abin tambaya a kan Ubangijnka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa cewa, duk waɗannan abubuwa da kafirai suke cewa me ya sa Allah bai yi masa su ba, to su sani cewa, alhairan Allah da albarkatunsa suna da yawa, idan ya ga dama sai ya ba shi abubuwan da suka fi waɗannan alheri, watau a nan duniya sai ya ba shi gonaki waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, kuma ya ba shi maka-makan gidaje waɗanda dukiyarsu ba za ta iya saya musu kamarsu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin da ya jawo suke ƙaryata manzancin Annabi (ﷺ) suke irin waɗancan miyagun maganganu, watau don sun ƙaryata tashin alƙiyama, wannan shi ne abin da ya hana su binciken gaskiya da dalilinta don su bi ta. Allah ya tabbatar musu da cewa ya tanadar wa duk wanda ya ƙaryata ranar alƙiyama azabar wuta mai ruruwa. Sai kuma ya bayyana yanayin wutar da take jiran su da cewa, idan ta hango su ana koro su zuwa gare ta daga wuri mai nisa, sai su riƙa jin tafarfasarta da gurnaninta. Idan aka jefa su cikin wutar Jahannama a wani wuri ƙuntatacce a cikinta an ɗaɗɗaure hannayensu a wuyayensu da sarƙoƙi, sai su riƙa kirawo wa kansu halaka suna tsammanin ko sa kuɓuta. Sai a faɗa musu cewa su daina ma kiran hallaka guda ɗaya, su ma kirawo halaka da yawa, wannan ba zai amfane su da komai ba, domin ba za a saurari kiransu ba, za su yi ta zama ne cikin matsananciyar azaba har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya faɗa musu cewa, yanzu wannan azabar da aka siffanta musu ita ce ta fi alheri ko kuma Aljannar dawwama wadda ni’imominta ba sa yankewa har abada? Ita ce wadda ya yi wa bayinsa muminai masu taƙawa alƙawarinta, don ta zama sakamako da makoma gare su a ranar alƙiyama? Ya bayyana cewa, za su sami duk abin da suka buƙata na ni’ima a cikin gidan Aljanna, wannan alƙawari ne Allah ya yi wa masu taƙawa da za su tambaye shi don ya cika musu shi domin shi ba ya saɓa alƙawari.

  17. وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ فَيَقُولُ ءَأَنتُمۡ أَضۡلَلۡتُمۡ عِبَادِي هَٰٓؤُلَآءِ أَمۡ هُمۡ ضَلُّواْ ٱلسَّبِيلَ

    Open ayah 25:17

    (Ka tuna) kuma ranar da zai tara su da abin da suke bauta wa ba Allah ba, sai Ya ce (da su): “Shin yanzu ku ne kuka ɓatar da bayina waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓace wa hanya don kansu?”

  18. قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ مَا كَانَ يَنۢبَغِي لَنَآ أَن نَّتَّخِذَ مِن دُونِكَ مِنۡ أَوۡلِيَآءَ وَلَٰكِن مَّتَّعۡتَهُمۡ وَءَابَآءَهُمۡ حَتَّىٰ نَسُواْ ٱلذِّكۡرَ وَكَانُواْ قَوۡمَۢا بُورٗا

    Open ayah 25:18

    Suka ce: “Tsarki ya tabbata gare Ka, bai zamanto ya dace da mu ba mu riƙi wasu majiɓinta ba Kai ba, sai dai kuma Ka jiyar da su daɗi ne tare da iyayensu har suka manta tuna Ka, suka kuwa kasance mutane hallakakku.”

  19. فَقَدۡ كَذَّبُوكُم بِمَا تَقُولُونَ فَمَا تَسۡتَطِيعُونَ صَرۡفٗا وَلَا نَصۡرٗاۚ وَمَن يَظۡلِم مِّنكُمۡ نُذِقۡهُ عَذَابٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 25:19

    To haƙiƙa sun ƙaryata ku game da abin da kuke faɗa, to ba za ku samu wata makauta ba, ko kuma wani taimako. Duk wanda kuma ya yi zalunci daga cikinku za Mu ɗanɗana masa azaba mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai masu bautar wasu ba Allah ba, kamar masu bautar mala’iku ko masu bautar annabawa, kamar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ko masu bautar wasu salihan bayi, ya tuna musu ranar da zai tattara su baki ɗaya sai ya tambayi ababen bautar cewa, shin su ne suka ɓatar da waɗannan bayin nasa, suka umarce su da su bauta musu? Ko kuma su bayin ne suka ɓace don kansu? Sai waɗannan ababen bauta su kare kansu a gaban Allah, su tabbatar masa da cewa tsarki ya tabbata a gare shi da a ce yana da wani abokin tarayya, kuma bai dace gare su ba su riƙi wasu masoya da za su jiɓince su ba Allah ba. Don haka ta yaya za su kirawo wasu bayinsa su umarce su su bauta musu? Suka bayyana abin da ya jawo waɗannan suka kafirce da cewa, Allah ne ya hore musu abubuwan jin daɗi na duniya mai yawa su da iyayensu, domin su gode masa su kuma bauta masa shi kaɗai, to amma sai ba su yi haka ba, wannan ni’imar ta zamar musu talala har suka manta da ambaton Allah, suka ci gaba da bautar wasu ba shi ba, suka kuwa kasance mutane halakakku. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai cewa haƙiƙa waɗanda suka bauta wa ba Allah ba ga shi sun ƙaryata su a kan da’awarsu ta cewa su ne suka umarce su da bautar su, kuma ma har za su cece su a wurin Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa a ranar ba za su iya kare kansu daga azabarsa ba, ba kuma za su iya taimakon kawunansu ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa duk wanda ya aikata zalunci daga cikinsu ta hanyar shirka, to zai ɗanɗana masa azaba mai girma kamar dai irin wadda ambatonta ya gabata.

  20. وَمَآ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّآ إِنَّهُمۡ لَيَأۡكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَيَمۡشُونَ فِي ٱلۡأَسۡوَاقِۗ وَجَعَلۡنَا بَعۡضَكُمۡ لِبَعۡضٖ فِتۡنَةً أَتَصۡبِرُونَۗ وَكَانَ رَبُّكَ بَصِيرٗا 

    Open ayah 25:20

    Kuma ba Mu aiko manzanni ba gabaninka sai cewa lalle suna cin abinci kuma suna tafiya cikin kasuwanni. Mun kuwa sanya wasunku su zama fitina ga wasu. Shin za ku yi haƙuri? Ubangijinka kuwa Ya kasance Mai gani ne. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da martani ga kafirai waɗanda suke ganin bai dace a ce manzo yana cin abinci yana zuwa kasuwanni saye da sayarwa ba, da cewa ai babu wani manzo da ya aiko gabanin Manzo (ﷺ) face shi mutum ne mai cin abinci kuma yana tafiya kasuwanni, don haka Manzon Allah (ﷺ) bai zama daban ba a nan. Sai kuma ya bayyana cewa ya sanya wasu mutane su zama fitina ga wasu, don haka manzanni sukan zama fitina ga masu ƙaryata su, masu ɗa’a sukan zama fitina a wurin mai saɓo, masu wadata kuma sukan zama fitina ga marasa wadata. Abin nema ga mutane dai shi ne su yi haƙuri a kan duk wata jarraba da Allah zai yi wa bawansa, sai ya yi masa sakayya idan ya yi haƙuri. Allah ya tabbatar da cewa yana ganin kowa; masu haƙuri da waɗanda ba sa haƙuri; masu biyayya da waɗanda ba sa biyayya.

  21. ۞وَقَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ أَوۡ نَرَىٰ رَبَّنَاۗ لَقَدِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ وَعَتَوۡ عُتُوّٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 25:21

    Waɗanda kuma ba sa tsammanin haɗuwa da Mu suka ce: “Me ya hana a saukar mana da mala’iku ko kuma mu ga Ubangijinmu?” Haƙiƙa lalle sun yi girman kai don (suna) ji da kawunansu, suka kuma yi tsaurin kai babba ƙwarai da gaske.

  22. يَوۡمَ يَرَوۡنَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ لَا بُشۡرَىٰ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُجۡرِمِينَ وَيَقُولُونَ حِجۡرٗا مَّحۡجُورٗا

    Open ayah 25:22

    Ranar da za su ga mala’iku a wannan ranar babu wani farin ciki ga masu laifi, za kuma su riƙa cewa: “(Albishir daga Allah) haramun ne abin haramtawa ne (a gare su)”

  23. وَقَدِمۡنَآ إِلَىٰ مَا عَمِلُواْ مِنۡ عَمَلٖ فَجَعَلۡنَٰهُ هَبَآءٗ مَّنثُورًا

    Open ayah 25:23

    Muka kuma gabato zuwa ga duk wani aiki da suka yi, sai Muka mai da shi ƙura abar ɗaiɗaitawa.

  24. أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ يَوۡمَئِذٍ خَيۡرٞ مُّسۡتَقَرّٗا وَأَحۡسَنُ مَقِيلٗا

    Open ayah 25:24

    ‘Yan Aljanna a wannan ranar su suka fi kyakkyawan mazauni kuma suka fi kyawon wurin barcin ƙailula. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafirai waɗanda ba sa fatan haɗuwa da shi kuma ba sa jin tsoron azabarsa suna izgili na cewa me ya sa Allah bai saukar musu da mala’iku ba waɗanda za su tabbatar musu cewa Annabi mai gaskiya ne game da da’awar manzanci da ya yi, ko kuma me ya hana su ga Allah da kansa ido-da-ido shi ya tabbatar musu da haka da kansa? Allah ya bayyana cewa, lalle waɗannan mutane girman kansu ya kai matuƙa, ya hana su yin imani da har suke nuna tsageranci ga mahaliccinsu suke ganin cewa wai su ne za su zaɓi hanyar da Allah zai isar musu da saƙonsa; idan kuwa bai bi wannan hanyar ba to ba za su yi imani ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa ranar da za su ga mala’iku, watau ranar mutuwarsu ko a cikin ƙaburburansu da ranar da za a kora su domin yi musu hisabi, to a ranar babu sauran wani farin ciki a tare da su. A ranar mala’iku za su riƙa gaya musu cewa babu wani albishir daga Allah sai na matsananciyar azaba. Sannan Allah ya bayyana cewa duk wani kyakkyawan aiki da kafirai suka yi a duniya wanda suke sa ran za su amfana da shi ranar alƙiyama, ya mayar da shi ƙura abar ɗaiɗaitawa, saboda kafircinsu, domin sharaɗin amfanuwa da kyawawan ayyuka shi ne yin imani da Allah da Manzonsa. Sai kuma ya bayyana sakamakon muminai a ranar alƙiyama da cewa, su ne ‘yan Aljanna waɗanda za su fi kowa kyakkyawar matabbata da mafi kyan wurin barcin ƙailula domin samun hutu, saboda sun yi imani da Allah da Manzonsa.

  25. وَيَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلسَّمَآءُ بِٱلۡغَمَٰمِ وَنُزِّلَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ تَنزِيلًا

    Open ayah 25:25

    Kuma (ka tuna) ranar da sama za ta kekkece da girgije, kuma a saukar da mala’iku gungu-gungu.

  26. ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡحَقُّ لِلرَّحۡمَٰنِۚ وَكَانَ يَوۡمًا عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ عَسِيرٗا

    Open ayah 25:26

    Mulki tabbatacce a wannan ranar na (Allah) Mai rahama ne. Kuma ta kasance rana ce mawuyaciya ga kafurai.

  27. وَيَوۡمَ يَعَضُّ ٱلظَّالِمُ عَلَىٰ يَدَيۡهِ يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي ٱتَّخَذۡتُ مَعَ ٱلرَّسُولِ سَبِيلٗا

    Open ayah 25:27

    (Ka tuna) kuma ranar da azzalumi zai riƙa cizon yatsunsa yana cewa: “Ina ma na bi hanya tare da Manzo!

  28. يَٰوَيۡلَتَىٰ لَيۡتَنِي لَمۡ أَتَّخِذۡ فُلَانًا خَلِيلٗا

    Open ayah 25:28

    “Kaicona ina ma da ban riƙi wane aboki ba!

  29. لَّقَدۡ أَضَلَّنِي عَنِ ٱلذِّكۡرِ بَعۡدَ إِذۡ جَآءَنِيۗ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِلۡإِنسَٰنِ خَذُولٗا

    Open ayah 25:29

    “Haƙiƙa ya ɓatar da ni daga bin Alƙur’ani, bayan ya zo mini.” Shaiɗan kuwa ya kasance mai taɓar da mutum ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tuna wa Manzonsa (ﷺ) ranar alƙiyama, ranar da sama za ta kekkece sai kawai a ga wani girgije fari kewaye da mala’iku masu yawa suna ta saukowa domin gudanar da hisabi. Mulki tabbatacce na gaskiya a ranar na Allah ne mai rahama shi kaɗai, kuma rana ce mai tsananin wahala ga kafirai saɓanin muminai waɗanda za ta zo musu da sauƙi. Allah ya bayyana halin kafiri a wannan rana, lokacin da zai riƙa nadama yana cizon ɗan yatsansa yana cewa ina ma da ya bi Manzon Allah ya karɓi gaskiyar da ya zo masa da ita bai ƙaryata shi ba, ya kama hanyar tsira tare da shi. A cikin tsananin nadama da ɓacin rai ya riƙa cewa kaiconsa, ina ma dai bai yi abota da wani kafiri ba wanda ya yi ta yi masa ingiza mai kantu ruwa. A ranar ya tabbatar da cewa wannan aboki nasa fa ya ɓatar da shi daga bin gaskiya bayan Manzon Allah ya zo masa da ita, ya hana shi yarda da Alƙur’ani da aiki da shi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mutum yana kan tafarkin abokinsa ne, don haka ɗayanku ya duba wanda zai yi abota da shi.” [Abu Dawud #4833 da Tirmizi #2378 da Ahmad #8028]. An karɓo daga Abu Musa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Misalin abokin zama na ƙwarai da wanda ba na ƙwarai ba kamar mai ɗauke ne da turaren almiski da mai hura zugazugi; shi mai ɗauke da turaren almiski ko dai ya ‘yam maka ko ka saya daga wajensa, ko kuma ka shaƙi ƙamshinsa. Amma mai hura zugazugi ko dai ya ƙona maka tufafinka ko ka shaƙi warinsa.” [Bukhari #5534 da Muslim #2628]. Sai Allah ya tabbatar da cewa da man shi Shaiɗan ya kasance mai yawan taɓar da mutum ne ya kuma yi banza da shi lokacin da ya faɗa cikin wani bala’i.

  30. وَقَالَ ٱلرَّسُولُ يَٰرَبِّ إِنَّ قَوۡمِي ٱتَّخَذُواْ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ مَهۡجُورٗا 

    Open ayah 25:30

    Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riƙi wannan Alƙur’ani abin ƙaurace wa.”

  31. وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا مِّنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ هَادِيٗا وَنَصِيرٗا

    Open ayah 25:31

    Kamar haka Muka sanya wa kowanne annabi abokan gaba daga masu laifi, kuma Ubangijinka Ya ishe ka Mai shiryarwa Mai taimako. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda Manzon Allah (ﷺ) yake ta kokawa game da halayyar kafirai waɗanda suke bijire wa Alƙur’ani da ya zo yana karanta musu suka riƙa yi masa izgili da ta’annuti iri-iri, duk da cewa wajibi ne a kansu su yi imani da shi su miƙa wuya a gare shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) ya sanar da shi cewa irin wannan cin zarafi da yake fuskanta daga kafirai shi ne abin da sauran annabawa da suka gabace shi suka fuskanta daga kafiran zamaninsu, amma suka yi haƙuri, daga ƙarshe Allah ya ɗora su a kan maƙiyansu. Don haka shi ma ya yi haƙuri, Ubangijinsa ya ishe shi mai shiryarwa zuwa gaskiya kuma mai ba shi nasara a kan maƙiyansa.

  32. وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلۡقُرۡءَانُ جُمۡلَةٗ وَٰحِدَةٗۚ كَذَٰلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِۦ فُؤَادَكَۖ وَرَتَّلۡنَٰهُ تَرۡتِيلٗا

    Open ayah 25:32

    Waɗanda kuma suka kafirta suka ce: “Me ya hana a saukar masa da Alƙur’ani gaba ɗaya, a lokaci guda?” Kamar haka ne (Muke saukar da shi kaɗan-kaɗan) don Mu tabbatar da zuciyarka da shi, Muka kuma karantar (da kai) shi daki-daki.

  33. وَلَا يَأۡتُونَكَ بِمَثَلٍ إِلَّا جِئۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ وَأَحۡسَنَ تَفۡسِيرًا

    Open ayah 25:33

    Kuma ba za su zo maka da wani misali ba (na ƙalu-bale) sai Mun zo maka da gaskiya, kuma da mafi kyan bayani.

  34. ٱلَّذِينَ يُحۡشَرُونَ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ إِلَىٰ جَهَنَّمَ أُوْلَٰٓئِكَ شَرّٞ مَّكَانٗا وَأَضَلُّ سَبِيلٗا

    Open ayah 25:34

    Waɗanda za a tashe su zuwa wutar Jahannama a kan fuskokinsu, waɗannan su suka fi mummunan matsayi kuma mafiya ɓatacciyar hanya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani salo daban na ƙaryata Alƙur’ani da kafirai suka fito wa da Manzon Allah (ﷺ) shi, yayin da suka nuna masa cewa da Alƙur’ani gaskiya ne daga Allah yake to da shi ma an saukar da shi gaba ɗaya kamar yadda aka saukar wa Annabi Musa Attaura da yadda aka saukar wa Annabi Isa Injila. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa ya saukar da Alƙur’ani ne kaɗan-kaɗan domin ya tabbatar da zuciyar Annabi (ﷺ) ya ƙara mata nutsuwa, kuma ya yi haka ne don a sami sauƙin fahimtar sa da haddace shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa babu sanda kafirai za su zo masa da wani misali wanda za su buƙaci amsa daga gare shi face sai Allah ya zo masa da tabbatacciyar amsa ta gaskiya da kuma bayani mafi kyau mai gamsarwa. Sai kuma ya bayyana mummunan sakamakon masu ƙaryata Alƙur’ani da gaskiya a ranar alƙiyama, da cewa su ne waɗanda za a kora su zuwa wutar Jahannama ana jan su a kan fuskokinsu, waɗannan su ne suka fi mummunan matsayi, domin mazauninsu ita ce wutar Jahannama, kuma su ne mafiya nesanta daga hanyar gaskiya, domin hanyar kafirci da ɓata ita ce hanyarsu.

  35. وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَا مَعَهُۥٓ أَخَاهُ هَٰرُونَ وَزِيرٗا

    Open ayah 25:35

    Haƙiƙa kuma Mun bai wa Musa Littafi muka kuma sanya ɗan’uwansa Haruna tare da shi a matsayin Waziri.

  36. فَقُلۡنَا ٱذۡهَبَآ إِلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَدَمَّرۡنَٰهُمۡ تَدۡمِيرٗا

    Open ayah 25:36

    Sai Muka ce: “Ku tafi zuwa ga mutanen da suka ƙaryata ayoyinmu, sai Muka hallaka su hallakarwa mai tsanani!”

  37. وَقَوۡمَ نُوحٖ لَّمَّا كَذَّبُواْ ٱلرُّسُلَ أَغۡرَقۡنَٰهُمۡ وَجَعَلۡنَٰهُمۡ لِلنَّاسِ ءَايَةٗۖ وَأَعۡتَدۡنَا لِلظَّٰلِمِينَ عَذَابًا أَلِيمٗا

    Open ayah 25:37

    Mutanen Nuhu kuma lokacin da suka ƙaryata manzanni sai Muka nutsar da su, Muka kuma sanya su wa’azi ga mutane, kuma Muka tanadi azaba mai raɗaɗi ga azzalumai.

  38. وَعَادٗا وَثَمُودَاْ وَأَصۡحَٰبَ ٱلرَّسِّ وَقُرُونَۢا بَيۡنَ ذَٰلِكَ كَثِيرٗا

    Open ayah 25:38

    Kuma (Muka hallakar da) Adawa da Samudawa da kuma mutanen (rijiyar) Rassu, da kuma wasu al’ummu masu yawa tsakanin hakan.

  39. وَكُلّٗا ضَرَبۡنَا لَهُ ٱلۡأَمۡثَٰلَۖ وَكُلّٗا تَبَّرۡنَا تَتۡبِيرٗا

    Open ayah 25:39

    Kowannensu kuwa Mun ba shi misalai; kuma kowannensu Mun hallaka shi mummunar hallakawa.

  40. وَلَقَدۡ أَتَوۡاْ عَلَى ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِيٓ أُمۡطِرَتۡ مَطَرَ ٱلسَّوۡءِۚ أَفَلَمۡ يَكُونُواْ يَرَوۡنَهَاۚ بَلۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ نُشُورٗا 

    Open ayah 25:40

    Haƙiƙa kuma (su mutanen Makka) sun bi ta alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwan azaba. Shin ba su kasance suna ganin ta ba ne? Ba haka ba ne, sun dai kasance ne ba sa tsammanin tashin alƙiyama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwantar da hankalin Manzonsa tare da lallashin sa game da ƙaryatawar da kafirai suke yi masa da cewa, annabawa da dama da suka gabace shi sun fuskanci ƙalubale daga mutanensu amma daga ƙarshe Allah ya ba su nasara a kansu. Allah ya tunatar masa da Annabi Musa wanda ya ba shi littafin Attaura ya kuma haɗa shi da ɗan’uwansa Annabi Haruna don ya zame masa Waziri da zai taimaka masa isar da saƙo zuwa ga Fir’auna da mutanensa. Allah ya umarce su da su fuskanci Fir’auna da mutanensa waɗanda suka ƙaryata ayoyin Allah masu nuna Kaɗaitakar Allah da Rububiyyarsa. Suka kuwa same su suka kirawo su zuwa ga Tauhidi, to amma sai suka ƙaryata su, Allah kuwa a ƙarshe ya yi musu mummunar halakarwa a kogi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambata masa labarin mutanen Annabi Nuhu waɗanda suka ƙaryata manzanni ta hanyar ƙaryata Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai Allah ya halakar da su baki ɗaya a ruwan Ɗufana, ya kuma sanya hallakarsu ta zama wata babbar aya ga mutane da ke nuna Ƙudurar Allah wajen tunɓuke azzalumai da nuna musu ƙarshensu. Allah kuma ya bayyana cewa ya tanadar wa azzalumai azaba mai raɗaɗi a ranar alƙiyama tana nan tana jiran su. Sannan kuma ya bayyana masa cewa ya hallakar da Adawa mutanen Annabi Hudu da Samudawa mutanen Annabi Salihu, ya kuma hallakar da mutanen rijiyar Rassu da kuma wasu al’ummu masu yawa a tsakanin waɗancan al’ummu guda uku. Allah kuma ya yi masa bayanin yadda ya hallakar da al\'ummun da suka gabace su da dalilan da suka jawo ya hallaka su domin su wa’azantu; dukkansu kuma ya yi musu mummunar hallakarwa ne saboda kafircinsu da tsaurin kansu. Allah kuma ya ambata wa Manzonsa cewa mutanensa Larabawa masu ƙaryata shi suna bi ta alƙaryar mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda aka yi wa ruwan ƙananan duwatsu saboda mummunar alfasha da suka aikata da neman maza. Larabawa a lokacin tafiye-tafiyensu zuwa ƙasar Sham suna bi ta wannan alƙarya mai cike da ababen wa’azantuwa, to shin sun makance ba sa ganin wannan alƙaryar ne? A’a, kawai dai ba sa tsammanin cewa akwai ranar da za a tashe su bayan sun mutu a yi musu hisabi.

  41. وَإِذَا رَأَوۡكَ إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَٰذَا ٱلَّذِي بَعَثَ ٱللَّهُ رَسُولًا

    Open ayah 25:41

    Idan kuma suka gan ka ba sa riƙon ka sai abin yi wa izgili, (suna cewa): “Yanzu wannan ne wanda Allah ya aiko Manzo?

  42. إِن كَادَ لَيُضِلُّنَا عَنۡ ءَالِهَتِنَا لَوۡلَآ أَن صَبَرۡنَا عَلَيۡهَاۚ وَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ حِينَ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ مَنۡ أَضَلُّ سَبِيلًا

    Open ayah 25:42

    “Lalle saura ƙiris ya ɓatar da mu daga ababen bautarmu, ba don mun yi haƙuri a kansu ba.” Ba da daɗewa ba kuwa za su san wanda ya fi ɓatan hanya yayin da za su ga azaba.

  43. أَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ أَفَأَنتَ تَكُونُ عَلَيۡهِ وَكِيلًا

    Open ayah 25:43

    Shin ka ga wanda ya mayar da son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, to yanzu kai za ka zama mai kiyaye shi (daga bin son zuciyarsa)?

  44. أَمۡ تَحۡسَبُ أَنَّ أَكۡثَرَهُمۡ يَسۡمَعُونَ أَوۡ يَعۡقِلُونَۚ إِنۡ هُمۡ إِلَّا كَٱلۡأَنۡعَٰمِ بَلۡ هُمۡ أَضَلُّ سَبِيلًا

    Open ayah 25:44

    Ko kuwa kana tsammanin cewa yawancinsu suna ji ne (na fahimta) ko suna hankalta? Ai su ba wasu ba ne illa kamar dabbobi; a’a su ne ma suka fi (dabbobi) ɓace hanya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin yadda kafirai suka riƙa yi wa Manzon Allah izgili da rashin kunya duk sanda suka haɗu da shi. A cikin izgilinsu suna ce masa; “Yanzu wannan shi ne Manzon da Allah ya aiko mana?” Watau suna ganin bai isa a ba shi manzanci ba domin a lissafinsu shi ba kowa ba ne, ba shi da wani babban matsayin da zai cancanci manzanci a dalilinsa. Wannan yana nuna tsantsar jahilcinsu da rashin sanin wane ne Allah. Don haka sai suke cewa cikin izgili da tsokana cewa wai saura ƙiris ya ɓatar da su domin zai kautar da su daga bautar allolinsu ba don sun yi haƙuri da juriya a kan haka ba, da hujjojinsa sun sanya su sun bi shi sun bar gumakansu. Sai Allah ya bayyana musu cewa yayin da za su ga azaba a ƙaburburansu ko a ranar alƙiyama ai za su gane wanda ya fi ɓace hanya tsakanin su da shi, za su san wane ne ɓatacce a cikinsu, shi ko su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa waɗannan mutane son zuciya kawai suke bi ba hujja ba, har ta kai sun mayar da soye-soyen zukatansu abin bautarsu. Wanda kuwa ya mayar da son zuciyarsa shi ne abin bautarsa, to shi Manzo (ﷺ) ba zai iya kare shi daga bin son zuciyar ba ya dawo da shi zuwa ga imani ya hana shi kafirci. Sai kuma ya tabbatar masa cewa da dama daga cikin waɗanda yake yi musu wa’azi da kiran su zuwa ga Tauhidi ba sa sauraron sa sauraro na karɓa da aiki da abin da suke ji, ba kuma sa hankaltar hujjojin da yake ba su, domin sun zama tamkar dabbobi waɗanda ba sa fahimtar komai ba sa kuma hankaltar wata hujja. Allah ya nuna masa cewa ai su sun ma fi dabbobi ɓata, domin su dabbobi da ma Allah bai ba su guzurin hankali irin na ɗan’adam ba.

  45. أَلَمۡ تَرَ إِلَىٰ رَبِّكَ كَيۡفَ مَدَّ ٱلظِّلَّ وَلَوۡ شَآءَ لَجَعَلَهُۥ سَاكِنٗا ثُمَّ جَعَلۡنَا ٱلشَّمۡسَ عَلَيۡهِ دَلِيلٗا

    Open ayah 25:45

    Shin ba ka ganin (irin aikin) Ubangijinka yadda ya shimfiɗa inuwa, da kuwa ya ga dama da sai ya sanya ta a tsaye cak, sannan Muka sanya rana dalilin samuwarta (inuwar).

  46. ثُمَّ قَبَضۡنَٰهُ إِلَيۡنَا قَبۡضٗا يَسِيرٗا

    Open ayah 25:46

    Sannan Muka riƙa janye ta da kaɗan-kaɗan.

  47. وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِبَاسٗا وَٱلنَّوۡمَ سُبَاتٗا وَجَعَلَ ٱلنَّهَارَ نُشُورٗا

    Open ayah 25:47

    Kuma shi ne wanda ya sanya muku dare ya zama sutura, bacci kuma don hutawa kuma ya sanya rana don watsuwa (wajen neman abinci).

  48. وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ ٱلرِّيَٰحَ بُشۡرَۢا بَيۡنَ يَدَيۡ رَحۡمَتِهِۦۚ وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ طَهُورٗا

    Open ayah 25:48

    Kuma shi ne wanda ya aiko iska don albishir a gabanin (saukar) rahamarsa. Muka kuma saukar da ruwa mai tsarkakewa daga sama.

  49. لِّنُحۡـِۧيَ بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗا وَنُسۡقِيَهُۥ مِمَّا خَلَقۡنَآ أَنۡعَٰمٗا وَأَنَاسِيَّ كَثِيرٗا

    Open ayah 25:49

    Don Mu raya busasshiyar ƙasa da shi, kuma Mu shayar da dabbobi da mutane masu yawa daga abubuwan da Muka halitta.

  50. وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَٰهُ بَيۡنَهُمۡ لِيَذَّكَّرُواْ فَأَبَىٰٓ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورٗا 

    Open ayah 25:50

    Haƙiƙa kuma Mun sarrafa shi a tsakaninsu don su wa’azantu, sai mafi yawan mutane suka ƙi (wa’azantuwa) sai kafirci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu daga cikin ayoyinsa da ni’imominsa waɗanda suke nuna cikar Ƙudurarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin Annabi (ﷺ) da cewa ya duba ya ga yadda Allah ya shimfiɗa inuwa a bayan ƙasa, da ya ga dama da sai ya sanya ta a tsaye cak ba ta motsawa, ya kuma sanya rana ta zama dalilin samuwar inuwar ga abubuwa wadda kuma take ƙaruwa tana raguwa. Sannan kuma ya riƙa janye inuwar da kaɗan-kaɗan tana ta raguwa gwargwadon ɗagawar rana, har ta zamanto ta gushe gaba ɗaya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ni’imar samuwar dare ga ɗan’adam wanda yake a matsayin sutura a wurinsa wadda take suturce shi ta kuma suturce sauran abubuwa. Ya kuma sanya musu bacci don ya zamanto hutu gare su bayan sun yi ayyuka da rana sun gaji. Rana kuma ya sanya musu ita lokacin fitarsu zuwa ayyukansu na yau da gobe. Akwai kuma wata babbar ni’ima da ya yi ga ‘yan’adam mai ƙunshe da dalilan cikar Ƙudurar Allah, watau ita ce lokacin da yake aiko da iska don ta yi albishir da saukar ruwan sama wanda yake rahama ce ga bayin Allah. Ya kuma saukar da ruwa mai tsarki daga sama wanda mutane suke tsarkake jikinsu da tufafinsu da shi. Allah ya bayyana cewa ya yi haka ne don ya raya busasshiyar ƙasa da wannan ruwan sai ta fitar da tsirranta da shuke-shuke iri-iri, kuma ya shayar da mutane da dabbobi da yawa da wannan ruwan. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya sarrafa hujjoji da dalilai daban-daban a cikin Alƙur’ani domin mutane su wa’azantu, to amma yawancinsu suka ƙi wa’azantuwa sai kafirce wa gaskiya da butulce masa.

  51. وَلَوۡ شِئۡنَا لَبَعَثۡنَا فِي كُلِّ قَرۡيَةٖ نَّذِيرٗا

    Open ayah 25:51

    Da kuma Mun ga dama, lalle da mun aiko wani mai gargaɗi cikin kowacce alƙarya.

  52. فَلَا تُطِعِ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَجَٰهِدۡهُم بِهِۦ جِهَادٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 25:52

    To kada ka bi son ran kafirai kuma ka yaƙe su da shi (Alƙur’ani) yaƙi mai girma.

  53. ۞وَهُوَ ٱلَّذِي مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ هَٰذَا عَذۡبٞ فُرَاتٞ وَهَٰذَا مِلۡحٌ أُجَاجٞ وَجَعَلَ بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٗا وَحِجۡرٗا مَّحۡجُورٗا

    Open ayah 25:53

    Shi ne kuma wanda Ya haɗa koguna biyu: wannan mai tsananin daɗi wannan kuma mai tsananin zartsi, Ya kuma sanya shamaki a tsakaninsu da kuma kariya mai karewa.

  54. وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ مِنَ ٱلۡمَآءِ بَشَرٗا فَجَعَلَهُۥ نَسَبٗا وَصِهۡرٗاۗ وَكَانَ رَبُّكَ قَدِيرٗا

    Open ayah 25:54

    Shi ne kuma wanda Ya halicci mutum daga ruwa sannan Ya mayar da shi dangantaka da surukuta. Ubangijinka Ya kasance Mai iko ne.

  55. وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُهُمۡ وَلَا يَضُرُّهُمۡۗ وَكَانَ ٱلۡكَافِرُ عَلَىٰ رَبِّهِۦ ظَهِيرٗا

    Open ayah 25:55

    Kuma suna bauta wa wanin Allah abin da ba zai amfane su ba kuma ba zai cuce su ba. Kafiri kuwa ya kasance mai taimaka wa (Shaiɗan ne) a kan bijire wa Ubangijinsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa da ya ga dama da sai ya rage wa Manzonsa (ﷺ) aiki ya aika wa kowace alƙarya da manzonta mai yi mata gargaɗi, to amma bai ga damar yin haka ba, sai ya aiko Annabi Muhammadu (ﷺ) shi kaɗai zuwa ga talikai baki ɗaya mutum da aljan, don ya ba shi babban matsayi a cikin annabawansa da manzanninsa. Sai kuma ya gargaɗe shi da cewa kada ya yi wa kafirai biyayya a kan abin da suke nema a wajensa na yin sako-sako wajen kiran su zuwa ga Tauhidi, domin shigo-shigo-ba-zurfi ne suke yi masa, sai ya umarce shi da ya yaƙe su da Alƙur’anin da aka saukar masa yaƙi mai girma wanda yake cike da haƙuri da juriya wajen kiran su zuwa ga Allah. Sannan Allah ya ci gaba da ambaton dalilan Ƙudurarsa da cikar ikonsa da cewa shi ne ya haɗa koguna biyu ɗaya mai ruwan daɗi ɗaya kuma mai zartsi, to amma kuma sai ya sanya shamaki a tsakaninsu wanda zai hana su gaurayuwa da juna. Ya kuma bayyana cewa shi ne wanda ya halicci mutum daga ruwan maniyyin namiji da mace ya kuma samar da dangantaka ta jini da ta surukuta tsakanin mutane, don haka Ubangiji mai iko ne a kan komai babu abin da yake gagarar sa. Sai kuma ya bayyana wautar kafirai masu bautar wasu ba Allah ba waɗanda ba za su amfane su da komai ba don sun yi musu biyayya, kuma ba za su cutar da su da komai ba don sun saɓa musu. To amma shi kafiri koyaushe yakan bi Shaiɗan ne a kan abin da zai jawo masa fushin Allah mahaliccinsa.

  56. وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا مُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

    Open ayah 25:56

    Kuma ba Mu aiko ka ba sai kawai don ka zama mai albishir mai gargaɗi gargaɗi.

  57. قُلۡ مَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍ إِلَّا مَن شَآءَ أَن يَتَّخِذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلٗا

    Open ayah 25:57

    Ka ce (da su): “Ba na tambayar ku wani lada a kansa (gargaɗin), sai dai ya rage ga wanda ya ga dama ya riƙi hanya (ta gari) zuwa ga Ubangijinsa.”

  58. وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡحَيِّ ٱلَّذِي لَا يَمُوتُ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِهِۦۚ وَكَفَىٰ بِهِۦ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرًا

    Open ayah 25:58

    Kuma ka dogara ga (Allah) Rayayye Wanda ba zai mutu ba, kuma ka yi tasbihi da godiyar sa, kuma Ya isa Masani ga zunuban bayinsa.

  59. ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَسۡـَٔلۡ بِهِۦ خَبِيرٗا

    Open ayah 25:59

    (Shi ne) wanda Ya halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi. (Shi ne) Arrahmanu, sai ka tambayi Masani game da Shi.

  60. وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱسۡجُدُواْۤ لِلرَّحۡمَٰنِ قَالُواْ وَمَا ٱلرَّحۡمَٰنُ أَنَسۡجُدُ لِمَا تَأۡمُرُنَا وَزَادَهُمۡ نُفُورٗا۩ 

    Open ayah 25:60

    Idan kuwa aka ce da su: “Ku yi sujjada ga Arrahmanu” sai su ce: “Mene ne Arrahmanu? Yanzu ma yi sujjada ga abin da kake umartar mu?” (Wannan umarnin) kuma ya ƙara musu fanɗarewa.

  61. تَبَارَكَ ٱلَّذِي جَعَلَ فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَجَعَلَ فِيهَا سِرَٰجٗا وَقَمَرٗا مُّنِيرٗا

    Open ayah 25:61

    Wanda Ya sanya wuraren saukar taurari cikin sama, Ya kuma sanya mata rana mai haske da wata mai haskakawa, albarkatunsa sun yawaita.

  62. وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ خِلۡفَةٗ لِّمَنۡ أَرَادَ أَن يَذَّكَّرَ أَوۡ أَرَادَ شُكُورٗا

    Open ayah 25:62

    Shi ne kuma wanda Ya sanya dare da rana masu maye wa juna ga wanda ya yi nufin ya wa’azantu ko kuma ya yi nufin godiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa bai aiko shi ba sai don ya zama mai albishir ga wanda ya yi masa ɗa’a da cewa yana da sakamako a wurin Allah na gidan Aljanna, ya kuma zama mai gargaɗi ga wanda ya saɓa masa da cewa yana da azaba ranar alƙiyama. Sannan ya umarce shi da ya sanar da kafirai cewa ba ya neman su biya shi wani lada a kan isar da saƙon da yake yi musu, sai dai wanda ya ga dama ya ciyar da dukiyarsa don Allah domin neman yardarsa. Sai kuma ya umarci Manzonsa da ya dogara ga Allah Rayayye wanda ba zai mutu ba har abada a cikin dukkan al’amuransa, ya kuma tsarkake shi daga duk wata tawaya da kasawa. Ya tabbatar masa cewa ya isa masanin komai game da zunubban bayinsa, babu abin da zai ɓuya gare shi, kuma zai yi musu sakayya a kai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikar ikonsa da cewa shi ne wanda ya halicci sammai da ƙasa da duk halittun da suke tsakaninsu cikin kwana shida, sannan ya daidaita a kan Al’arshi, daidaiton da ya dace da shi, kuma shi ne Allah mai rahama wanda rahamarsa ta yalwaci komai a sammai da ƙasa. Sai kuma ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya tambaye shi, (shi Allah), don ya sanar da shi siffofinsa na kamala da ɗaukaka domin shi ne masanin Zatinsa, babu wanda zai iya siffanta shi kamar yadda shi zai siffanta kansa da kansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kafircin mushirikai da yadda suke ƙaryata siffofin Allah maɗaukaka, da cewa idan aka umarce su da yin sujjada ga Allah mai rahama sai su ce: “Mene ne Arrahmanu ”, watau suna musun a siffanta Allah da sunan ‘Arrahmanu’, suna nuna wai su ba su san shi da wannan sunan ba, har ma su riƙa mamakin yaya za a umarce su da yin sujjada gare shi, alhalin su ba su san wane ne mai wannan sunan ba. Wannan umarni da aka yi musu da kuma ambaton sunan Allah mai rahama sai ya ƙara musu fanɗarewa da guje wa imani da Allah. An karɓo daga Miswar ɗan Makhrama (Allah ya kara masa yarda) cikin bayanin da ya ruwaito a kan Sulhul Hudaibiyya lokacin da Suhailu ɗan Amru ya zo za a rubuta takardar sulhu tsakanin Ƙuraishawa da Manzon Allah (ﷺ), sai Annabi (ﷺ) ya ce wa mai rubutu ya rubuta: “Bismillahir Rahmanir Rahim”, sai Suhailu ya yi farat ya ce:”Amma Arrahman , na rantse da Allah mu ba mu san shi ba, sai dai ya rubuta: “Bismikal Lahumma, kamar yadda kake rubutawa.” Sai Musulmi suka ce: “Wallahi ba zai rubuta haka ba, sai dai ya rubuta: “Bismillahir Rahmanir Rahim.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Rubuta Bismikal Lahumma. ” [Bukhari #2731]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da siffanta kansa da bayanin girman Ƙudurarsa, da cewa shi ne wanda albarkatunsa da alheransa suka yawaita wanda kuma ya sanya masaukan taurari da kuma taurari masu gudu a sararin samaniya, ya kuma sanya rana mai haske a cikinta da kuma wata mai haskakawa wanda yake samun haskensa daga hasken rana. Shi ne kuma Allah wanda ya sanya dare da rana suna maye gurbin juna; idan ɗaya ya tafi sai ɗayan ya zo ya maye gurbinsa. Ya bayyana cewa yana yin wannan aiki ne ga wanda yake nufin ya wa’azantu da ayoyin Allah ya sami shiriya, ko yake nufin gode wa Allah a bisa ɗimbin ni’imominsa.

  63. وَعِبَادُ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلَّذِينَ يَمۡشُونَ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ هَوۡنٗا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ ٱلۡجَٰهِلُونَ قَالُواْ سَلَٰمٗا

    Open ayah 25:63

    Bayin (Allah) Mai rahama kuwa (su ne) waɗanda suke tafiya a bayan ƙasa a natse; idan kuma wawaye sun yi musu magana (sai) su faɗa (musu) magana ta aminci.

  64. وَٱلَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمۡ سُجَّدٗا وَقِيَٰمٗا

    Open ayah 25:64

    (Su ne) kuma waɗanda suke kwana suna masu sujjada da tsayuwa ga Ubangijinsu.

  65. وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱصۡرِفۡ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَۖ إِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا

    Open ayah 25:65

    (Su ne) kuma waɗanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka kawar mana da azabar Jahannama; lalle azabarta ta kasance halaka ce mai ɗorewa.

  66. إِنَّهَا سَآءَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا

    Open ayah 25:66

    “Lalle ita (Jahannama) ta kasance mummunar matabbata kuma mazauna (ga kafirai).”

  67. وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَنفَقُواْ لَمۡ يُسۡرِفُواْ وَلَمۡ يَقۡتُرُواْ وَكَانَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ قَوَامٗا

    Open ayah 25:67

    (Su ne) kuma waɗanda idan suka ciyar ba sa almubazzaranci kuma ba sa yin ƙwauro, (ciyarwarsu) kuwa ta kasance tsaka-tsaki ce.

  68. وَٱلَّذِينَ لَا يَدۡعُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ وَلَا يَقۡتُلُونَ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَا يَزۡنُونَۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ يَلۡقَ أَثَامٗا

    Open ayah 25:68

    (Su ne) kuma waɗanda ba sa bauta wa wani tare da Allah, kuma ba sa kashe ran da Allah Ya hana kashewa sai da haƙƙi, kuma ba sa yin zina. Wanda kuwa ya aikata hakan to zai haɗu da (uƙubar) laifinsa.

  69. يُضَٰعَفۡ لَهُ ٱلۡعَذَابُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَيَخۡلُدۡ فِيهِۦ مُهَانًا

    Open ayah 25:69

    Za a ninninka masa azaba ranar alƙiyama, kuma ya dawwama a cikinta a wulaƙance.

  70. إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ عَمَلٗا صَٰلِحٗا فَأُوْلَٰٓئِكَ يُبَدِّلُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِهِمۡ حَسَنَٰتٖۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا 

    Open ayah 25:70

    Sai dai wanda ya tuba ya kuma yi imani, kuma ya yi aiki na gari, to waɗannan Allah zai musanya munanan ayyukansu da kyawawa. Allah kuwa ya kasance Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

  71. وَمَن تَابَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَإِنَّهُۥ يَتُوبُ إِلَى ٱللَّهِ مَتَابٗا

    Open ayah 25:71

    Wanda kuwa ya tuba ya kuma yi aiki na gari, to lalle shi ne wanda yake tuba na gaskiya zuwa ga Allah.

  72. وَٱلَّذِينَ لَا يَشۡهَدُونَ ٱلزُّورَ وَإِذَا مَرُّواْ بِٱللَّغۡوِ مَرُّواْ كِرَامٗا

    Open ayah 25:72

    (Su ne) kuma waɗanda ba sa halartar wuraren baɗala, idan kuma suka wuce ta wurin aikin assha to sai su wuce suna masu mutunta kansu.

  73. وَٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ لَمۡ يَخِرُّواْ عَلَيۡهَا صُمّٗا وَعُمۡيَانٗا

    Open ayah 25:73

    (Su ne) kuma waɗanda idan aka yi musu wa’azi da ayoyin Ubangijinsu ba sa fuskantar su suna kurame kuma makafi.

  74. وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبۡ لَنَا مِنۡ أَزۡوَٰجِنَا وَذُرِّيَّٰتِنَا قُرَّةَ أَعۡيُنٖ وَٱجۡعَلۡنَا لِلۡمُتَّقِينَ إِمَامًا

    Open ayah 25:74

    (Su ne) kuma waɗanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu masu sanyaya mana zukata daga matayenmu da zuri’armu, kuma Ka sanya mu abin koyi ga masu taƙawa.

  75. أُوْلَٰٓئِكَ يُجۡزَوۡنَ ٱلۡغُرۡفَةَ بِمَا صَبَرُواْ وَيُلَقَّوۡنَ فِيهَا تَحِيَّةٗ وَسَلَٰمًا

    Open ayah 25:75

    Waɗannan su ne ake saka wa da ɗakuna na Aljanna saboda haƙurin da suka yi, za kuma a tare su a cikinta da gaisuwa da sallama.

  76. خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ حَسُنَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا

    Open ayah 25:76

    Suna madawwama a cikinta. Matabbata da mazauni sun kyautata.

  77. قُلۡ مَا يَعۡبَؤُاْ بِكُمۡ رَبِّي لَوۡلَا دُعَآؤُكُمۡۖ فَقَدۡ كَذَّبۡتُمۡ فَسَوۡفَ يَكُونُ لِزَامَۢا

    Open ayah 25:77

    Ka ce: “Ba ruwan Ubangijina da ku in ba don ibadarku ba; to ga shi kun ƙaryata, to wannan (sakamakonsa) zai zama azaba ce mai ɗorewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta bayinsa na gari masu bautar sa da ikhlasi da kyawawan siffofi guda goma tare da bayanin gwaggwaɓan sakamako da ya tanadar musu a ranar alƙiyama. <b>Siffa ta farko </b>, su bayin Allah ne mai rahama. Wannan yana nuna sun sami babban matsayi a wurinsa saboda bautarsu gare shi, domin sifar ‘bawan Allah’ siffa ce ta ƙololuƙar daraja da girmamawa ga bawa. <b>Siffa ta biyu </b>, su ne masu tafiya a bayan ƙasa sannu a hankali, cikin natsuwa, babu girman kai ko ji-ji da kai ko wulaƙanta mutane. An karɓo daga Aliyu ɗan Abu Ɗalibi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan yana tafiya yana yin dama da hagu kamar mai gangarowa daga tudu, tun da nake ban taɓa ganin kamarsa ba.” [Ahmad #746 da Tirmizi #3637]. An karɓo daga Abu Ƙatada (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan za ku tafi salla to kada ku tafi kuna gaggawa; ku tafi cikin nutsuwa, abin da kuka riska sai ku sallata, abin da kuwa ya kuɓuce muku sai ku cikashe.” [Bukhari #635 da Muslim #603]. <b>Siffa ta uku </b>, su ne idan wasu wawaye suka yi musu maganar wauta da rashin hankali to ba sa ramawa sai dai su mayar musu magana mai kyau ta neman zaman lafiya. An karɓo daga Nu’uman ɗan Muƙarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya zagi wani a gaban Manzon Allah, sai wanda aka zaga ya riƙa ce wa mai zagin sa: “Aminci ya tabbata a gare ka.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle akwai wani mala’ika a tsakaninku yana kare ka duk lokacin da wannan yake zagin ka sai ya ce masa: “A’a sai dai kai, kai ne ka fi cancantar wannan zagin.” Idan kuma ɗayan ya ce: “Aminci ya tabbata a gare ka.” sai mala’ikan ya ce: “A’a gare ka dai (ba gare shi ba) kai ne ka fi shi cancantar aminci.” [Ahmad #23745]. <b>Siffa ta huɗu </b>, su ne waɗanda suke kwana suna bautar Allah, suna sallar ƙiyamullaili. <b>Siffa ta biyar </b>, su ne waɗanda suke addu’a suna roƙon Allah da ya kawar musu da azabar Jahannama, saboda azabarta mai lazimta da dawwama ce ga duk wanda ya mutu kafiri bai tuba ba, sannan kuma ita matabbata ce kuma mazauni da ya yi matuƙar muni ga duk wanda zai zauna a cikinsa. <b>Siffa ta shida </b>, su ne waɗanda idan suka ciyar da dukiyarsu ba sa almubazzaranci da bushasha da ita sannan kuma ba sa ƙwauro ga wanda ya wajaba su ba shi daga cikinta, don haka dai suna ciyarwarsu da kashe dukiyarsu tsaka-tsaki ba tare da almubazzaranci ko ƙwauro ba. <b>Siffa ta bakwai </b>, su ne waɗanda ba sa bauta wa wani tare da Allah, watau suna tsantsanta bautarsu ga Allah shi kaɗai ba sa yin shirka. Hakanan ba sa kashe wani rai da Allah ya haramta kashe shi ba da wani haƙƙi ba, kuma ba sa yin zina. Allah ya bayyana cewa duk wanda ya yi shirka ko ya kashe rai ba da haƙƙi ba ko kuma ya yi zina, to zai haɗu da mummunar uƙuba a kan laifin da ya aikata. Kuma za a ninninka masa azaba a ranar alƙiyama ya dawwama a cikinta a wulaƙance. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na tambayi Manzon Allah cewa: “Wane zunubi ne ya fi girma?” Sai ya ce: “Ka sanya wa Allah kishiya alhali shi ya halicce ka.” Sai na ce: “Sai kuma wanne?” Sai ya ce: “Ka kashe ɗanka don gudun ya ci tare da kai.” Na ce: “Sai kuma me?” Sai ya ce: “Ka yi zina da matar maƙocinka.” [Bukhari #4477 da Muslim #86]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hukuncin wanda ya tuba daga aikata waɗancan miyagun laifuffuka, ya yi nadama tare da alƙawarin ba zai koma gare su ba, ya kuma yi imani tare da kyakkyawan aiki wanda zai nuna gaskiyar tubansa, to sai Allah ya tabbatar wa da waɗanda suka yi haka cewa, zai musanya musu munanan ayyukansu da kyawawa, domin Allah ya tabbata mai gafara ne ga duk wanda ya tuba cikin bayinsa mai jin ƙan su ne. Malamai sun ambaci fassara biyu game da canza munanan ayyukansu da kyawawa: <b>Magana ta farko </b>, za a canza su daga aikata munanan aiki zuwa aikata kyakkyawan aiki. Sa’idu ɗan Jubair ya ce: “Allah ya canja su daga masu bautar gumaka zuwa masu bautar Allah mai rahama; ya canza su daga yaƙar Musulmi zuwa yaƙar mushirikai; ya canza su daga masu auren mata mushirikai zuwa ga masu auren mata muminai.” <b>Magana ta biyu </b>, su kansu miyagun ayyukan da suka yi ne a baya Allah zai canja musu su zuwa kyawawa bayan sun tuba, saboda duk sanda ɗayansu ya tuba daga laifin da ya aikata a baya ya yi nadama ya nemi gafarar Allah, to sai wannan laifin ya juye ya koma ɗa’a. Don haka a ranar alƙiyama ko da zai gan shi rubuce a cikin littafinsa, to ba zai cutar da shi ba, kamar yadda bayaninsa zai zo cikin hadisin Abu Zarri (Allah ya kara masa yarda). [Dubi Ibn Kasir, Juzu’i na 6, shafi na 127]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da cewa, duk wanda ya tuba ya nuna ƙwaƙƙwaran dalili a kan gaskiyar tubansa ta hanyar aikata kyawawan ayyuka da barin munana, to lalle wannan tuba ce karɓaɓɓiya a wurin Allah. An karɓo daga Abu Zarri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle ni na san ɗan wuta na ƙarshe da zai fito daga cikinta da na ƙarshen shiga Aljanna. Za a zo da wani mutum gaban Allah sai Allah ya ce: “Ku ajiye manyan laifukansa gefe guda, ku yi masa tambaya a kan ƙananansu.” Sai a ce masa: “A ranar kaza da kaza ka aikata kaza, a rana kaza kuma ka aikata kaza?” Sai ya ce: “E, na aikata.” Ba zai iya musantawa ba. Sai a ce masa: “To kowanne mummunan aiki an musanya maka shi da kyakkyawa.” Sai ya ce: “Ya Allah Ubangijina, na aikata wasu laifuffuka da ni ban gan su ba a nan.” Sai Manzon Allah ya yi dariya har sai da fiƙoƙinsa suka fito. [Muslim #190]. <b>Siffa ta takwas </b>, su ne waɗanda ba sa halartar wuraren baɗala da saɓon Allah, idan kuma suka wuce ta wurin maganganu da ayyukan assha to sai su yi maza su wuce suna masu mutunta kawunansu, ba za su yarda su tsaya a aikata wannan aikin assha tare da su ba ko su tsoma baki cikin maganganun da ba su dace ba. <b>Siffa ta tara </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) su ne waɗanda idan aka tunatar da su da ayoyin Allah ba za su toshe kunnuwansu su ƙi sauraro ba, ba kuma za su rufe idanuwansu su ƙi kallon su ba. <b>Siffa ta goma </b>, su ne waɗanda suke ta addu’a suna roƙon Allah ya nufe su da haihuwar ‘ya’ya na gari masu tsoron Allah waɗanda za su riƙa ganin su suna faranta musu rai saboda nagartar tarbiyyarsu. Hakanan suna roƙon sa ya sanya su su zama abin koyi ga mutane masu taƙawa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗannan bayi nasa na gari da cewa su ne za a saka musu da ɗakuna maɗaukaka a Aljannar Firdausi saboda haƙurin da suka yi wajen ɗa’ar Allah. Mala’iku su tare su da gaisuwa da sallama. Za su kuma dawwama cikin ni’imomin Aljanna har abada. Allah ya bayyana cewa wannan wurin tabbata da wannan mazauni ya yi kyau matuƙa. Sai kuma ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya sanar da kafirai cewa ba ruwan Allah da su in ba domin ɗa’arsu da ibadarsu ba, kuma ko da sun yi ba amfana za su yi da ita ba, hakanan ayyukansu na saɓon Allah ba cutar da shi da komai za su yi ba. Ba domin bayinsa na gari waɗanda suke bauta masa suna roƙon sa ba, da ba ruwansa da su, domin su sun ƙaryata Manzo, don haka sakamakon wannan ƙaryatawar zai zama azaba ce mai ɗorewa a gare su.