الشعراء
Ash-Shu'araa
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
طسٓمٓ
Open ayah 26:1ƊA SIN MIM.
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ
Open ayah 26:2Waɗannan ayoyi ne na Littafi mabayyani.
لَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:3Ko za ka kashe kanka ne don ba su zama muminai ba?
إِن نَّشَأۡ نُنَزِّلۡ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةٗ فَظَلَّتۡ أَعۡنَٰقُهُمۡ لَهَا خَٰضِعِينَ
Open ayah 26:4Da Mun ga dama da sai Mu saukar musu da aya daga sama sai wuyoyinsu su zamo masu ƙanƙan da kai gare ta.
وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن ذِكۡرٖ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ مُحۡدَثٍ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهُ مُعۡرِضِينَ
Open ayah 26:5Kuma ba wani wa\'azi sabo da zai zo musu daga (Allah) Mai rahama sai sun kasance masu bijire masa.
فَقَدۡ كَذَّبُواْ فَسَيَأۡتِيهِمۡ أَنۢبَٰٓؤُاْ مَا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 26:6To haƙiƙa sun ƙaryata, ba da daɗewa ba labaran aƙibar abin da suke yi wa izgili za su zo musu.
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَمۡ أَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ
Open ayah 26:7Shin ba su yi duba zuwa ga ƙasa ba, (su ga) dangogin tsirrai masu kyau nawa ne Muka tsirar daga cikinta?
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:8Lalle a game da wannan tabbas akwai aya (mai nuna cikar ikon Allah); kuma yawancinsu ba su zamanto masu imani ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:9Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi Mabuwayi ne, Mai rahama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa. Magana a kan irin waɗannan haruffa ta gabata a farkon Suratul Baƙara . Sannan Allah ya bayyana cewa waɗannan ayoyin Alƙur’ani ne mai bayyana ƙarya da gaskiya kuma bayani gamsasshe. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da lallashin Manzonsa game da damuwar da yake ciki ta bijirewar kafirai da ƙin ba da gaskiya da wannan Alƙur’ani da yake karanta musu, duk kuwa da bayyanar hujjarsa a fili. Ya nuna masa cewa ba daidai ne ya kashe kansa ba saboda damuwa don sun ƙi yin imani da Allah da kaɗaita shi. Allah ya tabbatar masa da cewa da ya ga dama da sai ya saukar musu da wata aya daga sama wadda za ta tilasta musu su miƙa wuya gare ta ko da ba sa so, to amma Allah bai yi haka ba, saboda irin wannan imani na dole ba shi da amfani a wurinsa; ya ƙyale su ne don ya jarraba su shin za su yi imani da gaibu ne, watau abin da ba su gan shi ba? Allah kuma ya bayyana cewa su mushirikai babu wata faɗakarwa sabuwa da za ta zo musu daga Allah mai rahama wadda take ƙunshe da hujjoji masu nuna Kaɗaitakarsa da gaskiyar Manzonsa face sai sun bijire wa sauraronta da gaskata ta. Allah ya tabbatar da cewa sun ƙaryata gaskiyar da Manzo (ﷺ) ya zo musu da ita, to amma fa su sani cewa ba da daɗewa ba tabbacin sakamakon abin da suke yi wa izgili zai zo musu, watau azaba za ta auka musu. Sai kuma ya ja hankalinsu a kan su yi tunani da hankalinsu, su dubi ƙasa su ga yadda Allah ya fitar da dangogin tsirrai daga cikinta masu kyau masu kuma amfani. Allah ya tabbatar musu cewa a game da yadda yake fito da tsirrai iri-iri ya raya ƙasa bayan mutuwarta ba shakka akwai bayyanannen dalili a kan Ƙudurar Allah ta sake raya matattu, to amma yawancinsu ba su zamanto masu yin imani ba. Sannan ya tabbatar wa da Manzo cewa Ubangijinsa lalle shi Mabuwayi ne babu abin da zai gagare shi, kuma mai tausayi ne ga bayinsa.
وَإِذۡ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئۡتِ ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 26:10Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka Ya kira Musa cewa: “Ka tafi wajen mutanen nan azzalumai.
قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَۚ أَلَا يَتَّقُونَ
Open ayah 26:11“(Watau) mutanen Fir’auna. Yanzu ba za su kiyaye dokokin Allah ba?”
قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
Open ayah 26:12(Musa) ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni ina tsoron su ƙaryata ni.
وَيَضِيقُ صَدۡرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرۡسِلۡ إِلَىٰ هَٰرُونَ
Open ayah 26:13“Kuma ƙirjina yana ƙuntata, kuma harshena ba ya sakuwa, sai Ka aika zuwa ga (ɗan’uwana) Haruna.
وَلَهُمۡ عَلَيَّ ذَنۢبٞ فَأَخَافُ أَن يَقۡتُلُونِ
Open ayah 26:14“Ni kuma akwai wani laifi da na yi musu, sai nake tsoron su kashe ni.”
قَالَ كَلَّاۖ فَٱذۡهَبَا بِـَٔايَٰتِنَآۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسۡتَمِعُونَ
Open ayah 26:15(Allah) Ya ce: “A’a; (ba abin da zai same ka), sai ku tafi (kai da ɗan’uwanka) da ayoyinmu; lalle Mu masu jin (komai da zai faru) ne tare da ku.
فَأۡتِيَا فِرۡعَوۡنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:16“Ku je wajen Fir’auna sai ku faɗa masa cewa: ‘Lalle mu manzannin Ubangijin talikai ne.
أَنۡ أَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 26:17“‘Cewa, ka sako mana da Banu-Isra’ila’.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin Annabi Musa da Haruna (() lokacin da aka aike su zuwa ga Fir’auna da mutanensa suka ƙaryata su, Allah kuwa ya hallakar da su don su zama izina da darasi ga duk waɗanda za su ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) da ya aiko musu. Allah ya tunatar da Annabi (ﷺ) lokacin da ya umarci Annabi Musa da ya tafi wajen azzaluman mutanen nan waɗanda suka kafirce wa Allah suka bautar da Banu-Isra’ila, watau Fir’auna da mutanensa, ya je ya yi musu wa’azi cikin lalama da tausasa magana cewa, yanzu ba za su yi taƙawa ba, watau su yi aiki da umarnin Allah su kuma guje wa haninsa? Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kawo wa Allah uzurinsa ya nemi ya ƙarfafe shi da mataimaki wanda zai taya shi isar da saƙonsa, saboda yana jin tsoron za su ƙaryata shi, kuma ga ƙirjinsa yana ƙuntata saboda saurin fushi daga abin da suke aikatawa; sannan kuma harshensa ba ya sakuwa ya yi magana yadda ya kamata. Don haka ya roƙi Allah ya aika wa ɗan’uwansa Haruna (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Mala’ika Jibrilu don su haɗu tare su isar da wannan saƙo zuwa ga Fir’auna da mutanensa. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ƙara kawo wani uzurinsa na huɗu, da cewa ya yi wa Fir’auna da mutanensa laifi na kashe wani Baƙibɗe, don haka yana jin tsoron idan sun kama shi za su kashe shi don ɗaukar fansar ɗan’uwansu. To don gudun kada isar da saƙon ya samu tangarɗa idan an kashe shi yake neman su zama su biyu shi da ɗan’uwansa Haruna. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwantar wa da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) hankali, da cewa ba za su kashe shi ba kuma an karɓa masa roƙonsa an haɗa shi da ɗan’uwansa don su isar da wannan manzanci tare, don haka kai-tsaye su tafi da ayoyin da aka ba su masu nuna gaskiyar manzancinsu, kamar sanda da hannunsa mai haske da sauran ayoyi tara da aka ba wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya tabbatar musu da cewa yana tare da su da nasararsa da goyon bayansa, yana kuma jin duk abin da zai gudana tsakaninsu da Fir’auna da mutanensa babu abin da zai kuɓuce masa. Allah ya umarci Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna (() su je wurin Fir’auna su bayyana masa ƙarara cewa su manzanni ne daga Allah Ubangijin talikai, don haka ya sako musu Banu Isra’ila da yake tsare da su yana azabtar da su tare da bautar da su.
قَالَ أَلَمۡ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدٗا وَلَبِثۡتَ فِينَا مِنۡ عُمُرِكَ سِنِينَ
Open ayah 26:18(Fir’auna) ya ce: “Yanzu ba mu muka raine ka a cikinmu tun kana jariri ba, kuma ka zauna ka yi wasu shekaru na rayuwarka a cikinmu?
وَفَعَلۡتَ فَعۡلَتَكَ ٱلَّتِي فَعَلۡتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 26:19“Ka kuma aikata aika-aikarka da ka aikata alhali kuwa kana daga masu butulce wa (ni’imata)?”
قَالَ فَعَلۡتُهَآ إِذٗا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
Open ayah 26:20(Musa) ya ce: “Na aikata haka ne a lokacin ina cikin marasa shiriya (ta rashin wahayi).
فَفَرَرۡتُ مِنكُمۡ لَمَّا خِفۡتُكُمۡ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكۡمٗا وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 26:21“Sannan na guje muku lokacin da na tsorata da ku, sai Ubangijina Ya ba ni kyautar ilimi Ya kuma sanya ni daga manzanni.
وَتِلۡكَ نِعۡمَةٞ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنۡ عَبَّدتَّ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 26:22“Waccen ni’imar kuwa da kake goranta min ita saboda ka bautar da Bani-Isra’ila ne.” Bayan Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna (() sun zama annabawa sai suka tafi fadar Fir’auna suka nemi iso aka yi musu, suka same shi suka isar masa da saƙon da Allah ya umarce su da su isar masa. A nan ne fa sai Fir’auna ya goranta wa Annabi Musa da cewa ba su ne suka raine shi ba tun yana ɗan jariri har ya girma, ya kuma zauna a cikinsu tsawon shekaru suna kula da shi suna kyautata masa, sai kuma kwatsam da rana tsaka ya zo yana cewa wai shi manzo ne daga Allah? Fir’auna kuma ya tuna masa da laifin da ya yi na kashe Baƙibɗe lokacin da suke faɗa da wani Ba’isra’ile yana mai tuhumar sa da butulcin kyautatawar da aka yi masa a gidan Fir’auna. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar wa Fir’auna cewa, haka ne, ya san ya kashe Baƙibɗe, to amma a lokacin da abin ya faru da shi yana cikin halin rashin sani ne domin ba a fara yi masa wahayi ba a lokacin. Don haka sai ya gudu zuwa garin Madyana don tsoron kada shi ma su kashe shi; to a can ne Allah ya ba shi ilimi ya mayar da shi Manzo ya kuma aiko shi zuwa ga mutane. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar wa Fir’auna martanin gorin tarbiyyar da ya yi masa da kuma barin sa da rai bai kuma bautar da shi ba kamar yadda ya yi wa sauran Banu Isra’ila, wannan kulawar da ya ba shi ba za ta hana shi yi masa wa’azi ba da gaya masa gaskiya, domin saƙon Allah ne, dole ya isar da shi.
قَالَ فِرۡعَوۡنُ وَمَا رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:23Fir’auna ya ce: “To wane ne Ubangijin talikai?”
قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Open ayah 26:24(Musa) ya ce: “(Shi ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu, idan har kun kasance masu sakankancewa (da hakan)”.
قَالَ لِمَنۡ حَوۡلَهُۥٓ أَلَا تَسۡتَمِعُونَ
Open ayah 26:25(Fir’auna) ya ce da waɗanda suke kewaye da shi: “Shin ba kwa jin (abin da yake faɗa)?”
قَالَ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 26:26(Musa) ya ce: “Shi ne Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko!”
قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِيٓ أُرۡسِلَ إِلَيۡكُمۡ لَمَجۡنُونٞ
Open ayah 26:27(Fir’auna) ya ce: “Lalle Manzon da aka aiko muku tabbas mai taɓin hankali ne!”
قَالَ رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 26:28(Musa) ya ce: “(Shi ne) Ubangijin mahudar rana da mafaɗarta da kuma abin da yake tsakaninsu; in kun zamanto masu hankalta.”
قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذۡتَ إِلَٰهًا غَيۡرِي لَأَجۡعَلَنَّكَ مِنَ ٱلۡمَسۡجُونِينَ
Open ayah 26:29(Fir’auna) ya ce: “Na rantse in har ka riƙi wani abin bauta ba ni ba, tabbas zan jefa ka cikin ‘yan kurkuku!”
قَالَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكَ بِشَيۡءٖ مُّبِينٖ
Open ayah 26:30(Musa) ya ce: “Ko da na zo maka da wani abu bayyananne?”
قَالَ فَأۡتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 26:31(Fir’auna) ya ce: “To ka zo da shi ɗin in ka kasance daga masu gaskiya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin isgilin da Fir’auna ya fara yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da da’awarsa ta a bauta wa Allah shi kaɗai, inda ya tambayi Annabi Musa wai wane ne ma Ubangijin halittu wanda yake nuna musu shi ya aiko shi, kuma ya ce a bauta masa shi kaɗai? Watau a nan Fir’auna yana nuna masa cewa shi bai yarda da akwai wani Ubangiji in ba shi ba. Sai muhawara ta ci gaba, Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya amsa wa Fir’auna da cewa Ubangijin halittu shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da duk abin da yake tsakaninsu, don haka Fir’auna shi da mutanensa lallai su yi imani da shi su bauta masa shi kaɗai idan har sun kasance masu sakankancewa da haka. Wannan ƙaƙƙarfar amsa ta Annabi Musa da ya ba wa Fir’auna ba ta yi wani tasiri ba; kamar ma ba da shi yake magana ba, sai kawai ya juya wajen fadawansa yana tambayar su wai suna kuwa jin abin da Musa yake faɗa? Sai Annabi Musa ya ƙara tabbatar musu da cewa, Allah shi ne Ubangijinsu kuma Ubangijin iyayensu da kakanninsu na farko. Watau yana tabbatar musu da cewa shi Fir’auna ba ubangijin kowa ba ne, shi ma kansa bawan Allah ne wanda kuma shi ne mahaliccin sammai da ƙasa da duk abin da suka ƙunsa na halittu. Sai Fir’auna ya shiga naɗe tabarmar kunya da hauka, domin ya rasa irin amsar da zai ba wa Annabi Musa, sai kawai ya shiga gaya wa fadawansa wai manzon da aka aiko musu fa mahaukaci ne yana faɗar abin da ba zai taɓa shiga hankali ba. To amma Annabi Musa bai daka ta tasa ba, sai ya ci gaba da faɗa masa gaskiya da hujja mai ƙarfi, da cewa Allah wanda yake kiran su da su bauta masa shi ne Ubangijin mahudar rana kuma Ubangijin mafaɗar rana da abin da yake tsakaninsu, idan har suna da hankali to ya kamata su fahimci haka. Watau ya nuna musu cewa shi ne yake magana ta hankali wadda sai mai hankali zai gane, don haka shi ba mai taɓin hankali ne ba. Yayin da Fir’auna ya ga tusa ta ƙure wa bodari sai ya fara barazana da nuna amfani da ƙarfin mulkinsa da rashin tausayinsa, yana yi wa Annabi Musa barazana da cewa, lalle idan har ya riƙi wani abin bauta ba shi ba, to lalle zai jefa shi gidan kurkuku ya gana masa azaba tare da fursunoni. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) dai bai ji tsoron barazanar Fir’auna ba, sai ma ya jefa masa wata hujja da cewa, yanzu sai ya jefa shi kurkuku ko da kuwa ya zo masa da wata hujja bayyananna wadda take tabbatar da abin da ya zo da shi gaskiya ne daga Allah? To lokacin da Fir’auna ya ji wannan maganar daga Annabi Musa sai ya umarce shi da ya kawo hujjar da take nuna cewa shi mai gaskiya ne, domin ba ya zaton akwai wata mu’ujiza da Annabi Musa zai iya nuna masa.
فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٞ مُّبِينٞ
Open ayah 26:32Sannan (Musa) ya jefa sandarsa sai ga ta (ta zama) kumurci ƙuru-ƙuru.
وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّٰظِرِينَ
Open ayah 26:33Ya kuma zaro hannunsa (daga cikin rigarsa) sai ga shi fari fat ga masu gani.
قَالَ لِلۡمَلَإِ حَوۡلَهُۥٓ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٞ
Open ayah 26:34(Sai Fir’auna) ya ce da manyan mutanen da ke kewaye da shi: “Lalle wannan tabbas mai sihiri ne ƙwararre.
يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِۦ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ
Open ayah 26:35“Yana nufi ne ya fitar da ku daga ƙasarku da sihirinsa, to da me za ku yi umarni?”
قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَٱبۡعَثۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Open ayah 26:36Suka ce: “Ka dakatar da shi tare da ɗan’uwansa, kuma ka aika manzanni cikin birane su tattaro maka (masu sihiri).
يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٖ
Open ayah 26:37“Su zo maka da duk wani mai sihiri ƙwararre.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana yadda Fir’auna ya nemi Annabi Musa ya kawo hujjarsa, shi kuma sai ya jefar da sandarsa ƙasa sai kawai ta zama ƙaton kumurci a fili ƙuru-ƙuru babu wata alamar rufa-ido ko siddabaru. Ya kuma shigar da hannunsa cikin wuyan rigarsa sai ga shi ya fito da shi fari fat yana haske ba kuma irin hasken mai cutar albaras ba, kowa da kowa yana gani. Fir’auna na ganin ayoyin da Annabi Musa ya nuna nan take sai ya ƙaryata shi, ya nuna taurin kansa, kuma ya yi yawo da hankalin `yan majalisarsa da faɗa musu abubuwa uku: <b>Na farko </b>, ya tabbatar musu cewa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ƙwararren mai sihiri ne, don haka kada wannan sihiri nasa ya yaudare su. <b>Na biyu </b>, ya tunzura mutanensa ta hanyar faɗa musu cewa manufar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ita ce ya fitar da su daga ƙasarsu ta hanyar amfani da sihirinsa, ya ja hankalin mutane ya tara mabiya su haɗu su ƙwace ƙasa daga hannunsu. <b>Na uku </b>, ya nemi su ba shi shawarar abin da ya kamata ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da nufin ya ja hankalinsu don su haɗa ƙarfi su yaƙe shi. Amma kuma sanannen abu ne cewa Fir’auna ba ya jin shawarar kowa ballantana har ya nemi a ba shi shawara. Amma duk da haka manyan fadawansa sun ba shi shawarar cewa ya jinkirta da ɗaukan wani mataki a kan Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna, kada ya gaggauta azabtar da su har sai ya aika cikin ilahirin masarautarsa ko’ina da ko’ina an tattaro masa ƙwararrun masu sihiri, domin su yi gaba da gaba da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) su kuma zo masa da dangogin sihiri daban-daban waɗanda za su nuna masa iyakarsa da su.
فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
Open ayah 26:38Sai aka tattara masu sihirin (don su zo) a ƙayyadajjiyar rana sananniya.
وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلۡ أَنتُم مُّجۡتَمِعُونَ
Open ayah 26:39Aka kuma ce da mutane: “Shin za ku tattataro.
لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ
Open ayah 26:40“Don mu goyi bayan masu sihiri idan har sun kasance su ne masu galaba?”
فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُواْ لِفِرۡعَوۡنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ
Open ayah 26:41Sannan lokacin da masu sihirin suka zo sai suka ce da Fir’auna: “Shin muna da wani lada (da za ka ba mu) in har mun zama mu ne masu galaba?”
قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
Open ayah 26:42(Fir’auna) ya ce: “Na’am, kuma ma idan haka ya faru, to tabbas za ku zama daga makusanta.”
قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ
Open ayah 26:43(Sai Musa) ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”
فَأَلۡقَوۡاْ حِبَالَهُمۡ وَعِصِيَّهُمۡ وَقَالُواْ بِعِزَّةِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبُونَ
Open ayah 26:44Sai suka jefa igiyoyinsu da sandunansu suka kuma ce: “Lalle da izzar Fir’auna tabbas mu ne masu galaba.”
فَأَلۡقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ
Open ayah 26:45Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanƙwame duk abin da suke ƙagowa (na sihiri).
فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ
Open ayah 26:46Sai aka durƙusar da masu sihirin suna masu sujjada.
قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:47Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai.
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Open ayah 26:48“Ubangijin Musa da Haruna.”
قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَ فَلَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 26:49(Sai Fir’auna) ya ce: “Yanzu kwa yi imani da shi tun kafin in ba ku izini? Lalle tabbas shi ne babbanku wanda ya koya muku sihiri; to tabbas kuwa kwa sani. Lalle zan yanyanke hannayenku da ƙafafuwanku a tarnaƙe, kuma tabbas zan gicciye ku gaba ɗaya!”
قَالُواْ لَا ضَيۡرَۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
Open ayah 26:50Sai suka ce: “Ai ba damuwa; lalle mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu.
إِنَّا نَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَٰيَٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:51“Lalle mu muna kwaɗayin Ubangijinmu Ya gafarta mana kurakuranmu saboda zamantowarmu farkon muminai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Fir’auna ya karɓi shawarar manyan fadawansa, don haka an tattaro masa ƙwararrun masu sihiri an kuma tsayar da shawarar su haɗu da Annabi Musa a wani wuri da lokaci ƙayyadajje, watau ranar bikin idinsu. Aka kuma yi wa mutane shela aka nuna musu muhimmancin kowa ya halarta domin ya ga yadda za a ƙure sihirin Annabi Musa hujjar masu sihiri ta bayyana ta yi rinjaye, sai a goyi bayansu a ci gaba da zama a kan addinin Fir’auna da bautar sa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da masu sihiri suka iso fadar Fir’auna sai suka gana da shi da farko don su tabbatar zai ba su ladansu idan sun sami galaba a kan Annabi Musa. Shi kuwa Fir’auna ya tabbatar musu da cewa lalle za su sami ladansu, bayan haka ma zai ƙara musu da janyo su kusa da shi a fadarsa don su zama masu ba shi shawara. Daga nan masu sihiri suka hallara wajen taro suka tambayi Annabi Musa cewa su ne za su fara jefa kayan tsafinsu ko kuma shi ne zai fara? Sai ya umarce su da su fara jefa abin da suka yi niyyar jefawa, domin ya tabbatar da cewa shi abin da Allah ya ba shi ba sihiri ne ba mu’ujiza ce. Sai suka jefa igiyoyinsu da sandunansu suka kuma yi rantsuwa da girman Fir’auna cewa su ne za su yi galaba a kan Annabi Musa. Bayan sun gama duk abin da suka so yi sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya jefa sandarsa sai kawai ta zama macijiya ta riƙa bin ƙarairayinsu na sihiri tana ta haɗiyewa. Nan take hujjar Annabi Musa ta bayyana, ƙaryar masu sihiri kuma ta ƙare suka gane cewa ba a kan komai suke ba, nan take kuma suka faɗi suna masu sujjada, suka fito fili suka bayyana cewa su sun yi imani da Ubangijin halittu, watau Allah wanda Fir’auna yake musun samuwarsa, shi ne kuma Ubangijin Musa da Harun. Bayan gaskiya ta bayyana sai Fir’auna ya rikice, ya shiga girman kai yana barazana ga masu sihiri tare da tuhumar su da cewa sun yi imani da Annabi Musa tun kafin ya yi musu izinin hakan. Wannan ya ƙara sa shi ya lalubo wani uzurin da zai faɗa game da imanin masu sihiri, domin ya ruɗi mutane da shi kada su fahimci gaskiya ce ta bayyana gare su har suka yi imani. Watau Fir’auna ya tuhumi masu sihirin da cewa da ma can Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ne shugabansu wanda ya koya musu sihiri, don haka wannan abu da ya faru ba komai ba ne sai haɗin baki a tsakaninsu da shi domin su ƙwace mulkin Masar su fitar da mutanen gari daga garinsu. Don haka sai ya ɗanɗana musu mummunar azaba, ta hanyar yanke hannayensu da ƙafafuwansu a tarnaƙe sannan daga baya ya gicciye su a kan kututturan dabino baki ɗayansu, ba zai bar ko da mutum ɗaya daga cikinsu ba. To amma sai masu sihirin nan suka nuna wa Fir’auna cewa su ba su damu da duk abin da zai yi musu na azaba ba domin sun tabbata su masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu, kuma zai shigar da su cikin rahamarsa madawwamiya. A ƙarshe suka tabbatar masa da cewa su fatansu Ubangijinsu ya gafarta musu laifukansu da suka yi a baya saboda zamantowarsu farkon waɗanda suka yi imani da Annabi Musa suka gaskata shi.
۞وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِيٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Open ayah 26:52Muka kuma yi wa Musa wahayi cewa: “Ka tafi cikin dare tare da bayina, lalle ku za a biyo bayanku.”
فَأَرۡسَلَ فِرۡعَوۡنُ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Open ayah 26:53Sai Fir’auna ya aika zuwa birane don a tattaro (mayaƙa).
إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَشِرۡذِمَةٞ قَلِيلُونَ
Open ayah 26:54(Fir’auna yana cewa): “Lalle waɗannan tabbas ‘yan tsirarin jama’a ne.
وَإِنَّهُمۡ لَنَا لَغَآئِظُونَ
Open ayah 26:55“Kuma haƙiƙa su lalle suna fusata mu.
وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَٰذِرُونَ
Open ayah 26:56“Lalle kuma mu tabbas gaba ɗayanmu masu kwana cikin shiri ne.”
فَأَخۡرَجۡنَٰهُم مِّن جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ
Open ayah 26:57(Allah Ya ce): Sai Muka fitar da su daga gonaki da kuma idandunan ruwa.
وَكُنُوزٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ
Open ayah 26:58Da taskoki da kuma mazauni na alfarma.
كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 26:59Kamar haka ne Muka gadar da su ga Banu-Isra’ila.
فَأَتۡبَعُوهُم مُّشۡرِقِينَ
Open ayah 26:60Sai suka bi bayansu a lokacin fitowar rana.
فَلَمَّا تَرَٰٓءَا ٱلۡجَمۡعَانِ قَالَ أَصۡحَٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدۡرَكُونَ
Open ayah 26:61To lokacin da jama’ar biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce: “Lalle tabbas mu za a cim mana.”
قَالَ كَلَّآۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهۡدِينِ
Open ayah 26:62(Musa) ya ce: “A’a; Ubangijina Yana tare da ni, zai kuwa shiryar da ni (hanyar tsira).”
فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٖ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 26:63Sai Muka yi wahayi ga Musa cewa: “Ka bugi kogin da sandarka;” (da ya buge shi) sai ya dare, kowanne yanki sai ya zama kamar ƙaton dutse.
وَأَزۡلَفۡنَا ثَمَّ ٱلۡأٓخَرِينَ
Open ayah 26:64Muka kuma kusantar da waɗancan (watau mutanen Fir’auna) zuwa can (kusa da kogin).
وَأَنجَيۡنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 26:65Muka kuma tserar da Musa da waɗanda suke tare da shi gaba ɗaya.
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Open ayah 26:66Sannan Muka nutsar da sauran mutanen (watau Fir’auna da mutanensa).
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:67Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:68Kuma lalle Ubangijika tabbas Shi Mabuwayi ne, Mai rahama. Fir’auna da mutanensa sun ci gaba da kafircinsu, Annabi Musa kuma yana ta nuna musu ayoyi iri-iri, duk sanda ya zo musu da wata aya da ta dame su sai su yi masa alƙawarin cewa idan ya roƙi Allah ya yaye musu ita tabbas za su yi imani da shi kuma lalle za su sakar masa da Banu Isra’ila, sai ko Allah ya yaye musu, sai kuma su karya alƙawarin da suka ɗauka. To bayan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fitar da ƙaunar za su yi imani da shi ya sakankance da cewa azabar Allah ta riga ta tabbata a kansu, ya kuma fahimci lokacin tserewa tare da Banu Isra’ila ya matso, sai Allah ya yi masa wahayin cewa ya fita cikin dare tare da Banu Isra’ila kuma lalle Fir’auna da rundunarsa za su biyo bayansu, amma idan har sun biyo su da asuba ne to ba za su iya cim masu ba har su isa kogi, daga nan idan sun shiga su kuma sun biyo su a baya sai kogi ya haɗe da su su hallaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa yayin da Fir’auna ya ji labarin fitar Annabi Musa da mutanensa daga Masar sai ya aika zuwa biranen Masar domin a tattaro masa da rundunar mayaƙa waɗanda za su bi sawun Annabi Musa da jama’arsa su dawo da su Masar don su ɗanɗani kuɗarsu. Aka kuwa tara masa rundunarsa ya kuma ƙarfafi gwiwoyinsu da abubuwa uku: <b>Na farko </b>, ya tabbatar musu da cewa Annabi Musa da mutanensa ‘yan tsiraru ne, don haka dawo da su Masar ba wani abu ne mai wahala ba. <b>Na biyu </b>, ya nuna musu cewa Annabi Musa da jama’arsa da ma can suna muzguna musu da yawan aikata laifuffuka da hana zaman lafiya a gari, ga shi ma sun gudu da kayan aro da suka karɓa daga hannun mutane. <b>Na uku </b>, ya nuna musu cewa su kuma da man kullum cikin shiri suke da sanya idanu a kan Annabi Musa da jama’arsa tun al’amarinsu bai yi girma ba har ya zo ya fi ƙarfinsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya fito da Fir’auna da mutanensa domin su bi sawun Annabi Musa da mutanensa don su hana su fita daga garin Masar, don haka sai suka bar garinsu mai cike da ni’imomi iri-iri, ga gonaki masu cike da shuke-shuke da idanuwan ruwa masu gudana da manya-manyan taskoki cike da dukiya da maka-makan gine-gine na alfarma. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda ya raba Fir’auna da rundunarsa da waɗannan ni’imomi to haka kuma ya gadar wa Banu Isra’ila da wasu ni’imomin irin waɗancan a garuruwan Sham, suka rabu da halin bauta da ƙasƙanci suka koma cikin rayuwa ta jin daɗi da ni’ima da mulki. Sai Fir’auna da manya-manyan mutanensa da rundunarsa mai ƙarfi da yawa suka yi sammako dab da hudowar rana suka bi bayan Annabi Musa da jama’arsa har sai da suka kusa cim musu, suka fara hango junansu, sai sahabban Annabi Musa suka tsorata suna bayyana cewa lalle fa Fir’auna da mutanensa za su cim musu kuma ga shi ba za su iya tunkarar su da yaƙi ba. Sai Annabi Musa ya kwantar musu da hankali ya tabbatar musu da cewa ba za su iya cim musu ba, domin yana tare da Ubangijinsa, kuma shi ya umarce shi da ya fito da su cikin dare, don haka yana tare da shi da nasararsa da taimakonsa, kuma zai nuna masa hanyar tsira. Bayan sun isa dab da Kogin Maliya sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wahayi da cewa ya doki ruwan kogin da sandarsa, nan take kuwa ya doke shi sai suka ga kawai kogin ya tsage ya zama hanyoyi har goma sha biyu, watau adadin ƙabilun Banu-Isra’ila, kowane yanki kuwa na wannan kogi ya zama kamar babban dutse wajen girmansa da tsayuwarsa ta yadda ruwansa ba ya kwarara. Allah ya bayyana cewa ya kusantar da Fir’auna da mutanensa ga wannan kogin har suka shiga ciki suna tsammanin hanyar wucewa ce. Nan ne fa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tserar da Annabi Musa da Banu Isra’ila da ke tare da shi, babu ko mutum guda cikinsu da ya hallaka a ruwa. Allah kuwa ya hallakar da Fir’auna da mutanensa gaba ɗayansu a cikin kogi suka nutse ko mutum ɗaya bai kai labari ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa cikin wannan abu da ya faru na hallaka Fir’auna da mutanensa da tserar da Annabi Musa da mutanensa akwai aya mai nuna cikakkiyar Ƙudurar Allah da gaskiyar manzancin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), to amma yawancinsu ba sa yin imani ko da sun ga irin waɗannan ayoyi. Sannan Allah ya bayyana wa Manzonsa cewa lalle Ubangijinsa mabuwayi ne mai damƙar maƙiyansa da azabarsa, kuma mai rahama ne ga duk wanda ya tuba daga cikinsu.
وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ إِبۡرَٰهِيمَ
Open ayah 26:69Kuma ka karanta musu labarin Ibrahimu?
إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا تَعۡبُدُونَ
Open ayah 26:70Lokacin da ya ce wa babansa da kuma mutanensa: “Me kuke bauta wa?”
قَالُواْ نَعۡبُدُ أَصۡنَامٗا فَنَظَلُّ لَهَا عَٰكِفِينَ
Open ayah 26:71Suka ce: “Muna bauta wa gumaka ne, sai mukan duƙufa wajen bautarsu.”
قَالَ هَلۡ يَسۡمَعُونَكُمۡ إِذۡ تَدۡعُونَ
Open ayah 26:72(Ibrahimu) ya ce: “Shin suna jin ku kuwa lokacin da kuke kiran su?
أَوۡ يَنفَعُونَكُمۡ أَوۡ يَضُرُّونَ
Open ayah 26:73“Ko kuwa suna amfanar ku ne, ko suna cutarwa?”
قَالُواْ بَلۡ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفۡعَلُونَ
Open ayah 26:74Suka ce: “A’a; mun sami iyayenmu ne suna aikata kamar haka.”
قَالَ أَفَرَءَيۡتُم مَّا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ
Open ayah 26:75(Ibrahimu) ya ce: “Yanzu kun ga abin nan da kuka kasance kuna bautawa.
أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلۡأَقۡدَمُونَ
Open ayah 26:76“Ku da iyayenku da suka gabata.
فَإِنَّهُمۡ عَدُوّٞ لِّيٓ إِلَّا رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:77“To lalle su abokan gabata ne sai fa Ubangijin talikai.
ٱلَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهۡدِينِ
Open ayah 26:78“Wanda Ya halicce ni, to Shi ne Yake shiryar da ni.
وَٱلَّذِي هُوَ يُطۡعِمُنِي وَيَسۡقِينِ
Open ayah 26:79“Kuma wanda Shi ne Yake ciyar da ni kuma Yake shayar da ni.
وَإِذَا مَرِضۡتُ فَهُوَ يَشۡفِينِ
Open ayah 26:80<b> “Idan kuma na yi rashin lafiya, to Shi ne zai warkar da ni.
وَٱلَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحۡيِينِ
Open ayah 26:81“Kuma wanda zai kashe ni sannan Ya (sake) raya ni.
وَٱلَّذِيٓ أَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لِي خَطِيٓـَٔتِي يَوۡمَ ٱلدِّينِ
Open ayah 26:82“Wanda kuma nake kwaɗayin Ya gafarta min kurakuraina ranar sakamako.
رَبِّ هَبۡ لِي حُكۡمٗا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 26:83“Ubangijina Ka hore min ilimi, kuma Ka haɗa ni da (bayinka) na gari.
وَٱجۡعَل لِّي لِسَانَ صِدۡقٖ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 26:84“Kuma Ka sanya min abin kyakkyawan ambato cikin ‘yan baya.
وَٱجۡعَلۡنِي مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 26:85“Kuma Ka sanya ni cikin magada Aljannar ni’ima.
وَٱغۡفِرۡ لِأَبِيٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
Open ayah 26:86“Kuma Ka gafarta wa babana, lalle shi ya zamo cikin ɓatattu.
وَلَا تُخۡزِنِي يَوۡمَ يُبۡعَثُونَ
Open ayah 26:87“Kada kuma Ka kunyata ni ranar da za a tashe su.
يَوۡمَ لَا يَنفَعُ مَالٞ وَلَا بَنُونَ
Open ayah 26:88“Ranar da dukiya da ‘ya’yaye ba sa amfani.
إِلَّا مَنۡ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلۡبٖ سَلِيمٖ
Open ayah 26:89“Sai dai wanda ya zo wa Allah da lafiyayyar zuciya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya ba mutanensa labarin Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya tambayi babansa Azaru da mutanensa cewa, mene ne suke bauta wa wanda ba Allah ba? Sai suka amsa masa da cewa suna bauta wa gumaka ne waɗanda su ne suka sassaƙa su da hannayensu. Sai Annabi Ibrahimu ya bayyana musu rashin cancantar su bauta musu, ta hanyar tambayarsu cewa shin gumakan nan suna jin su sa’adda suke yin addu’a, kuma suna amsa musu addu’o’insu? Ko kuma suna yi musu wani amfani idan sun yi musu ɗa’a, ko suna cutar da su ne idan sun saɓa musu? To amma su kansu mutanensa sun tabbatar cewa gumakansu ba sa iya yi musu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, don haka sai suka rasa wata gamsasshiyar amsa da za su ba shi in ban da cewa su dai haka suka tashi suka sami iyayensu suna irin wannan bautar don haka su kawai sun bi sahun iyayensu ne suna koyi da su wajen bauta musu. Sai Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ja hankalinsu da cewa, su sani fa duk abubuwan da suke bauta wa su da iyayensu na farko, gaba ɗayansu maƙiyansa ne domin kuwa su ba allolin gaskiya ba ne, sai Allah kaɗai wanda shi ne Ubangijin halittu. Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da kawo musu siffofin Allah waɗanda da su ne ya cancanci a bauta masa shi kaɗai. <b>Siffar farko ita ce </b>, shi ne wanda ya halicce shi daga babu ya kuma kyautata halittarsa, kuma shi kaɗai ne yake shiryar da shi ga duk wata masalaharsa ta duniya da ta lahira. <b>Ta biyu ita ce </b>, shi ne wanda yake ciyar da shi kuma ya shayar da shi. Watau duk arzikin duniya a hannunsa yake babu mai iya hana abin da ya bayar babu kuma mai bayar da abin da ya hana. <b>Ta uku ita ce </b>, shi ne wanda yake warkar da shi idan ya yi rashin lafiya. Babu wanda waraka take a hannunsa sai Allah shi kaɗai. <b>Ta huɗu ita ce </b>, shi ne wanda zai karɓi ransa yayin da ajalinsa ya zo. Kuma shi ne wanda zai sake raya shi bayan mutuwarsa. Babu mai iya aikata haka sai shi kaɗai. <b>Ta biyar ita ce </b>, shi ne wanda yake kwaɗayi ya gafarta masa kurakuransa a ranar sakamako, watau ranar alƙiyama. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Na ce: “Ya Manzon Allah, Ibn Jud’an mutum ne da ya kasance a zamanin jahiliyya yana sadar da zumunci, yana kuma ciyar da mabuƙata, shin wannan zai yi masa amfani?” Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ba zai amfane shi ba, domin lalle shi babu wata rana da ya taɓa buɗar bakinsa ya ce: “Ya Ubangijina, ka gafarta min kuskurena a ranar sakamako.” [Muslim #214]. Sannan Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya duƙufa ga roƙon Allah kan ya yi masa baiwa da abubuwa shida: <b>Na farko </b>, ya hore masa ilimi na addini domin ya san yadda zai bauta wa Ubangijinsa. <b>Na biyu </b>, ya sada shi da bayinsa na gari, watau annabawan da suka gabace shi ta hanyar ya sanya shi Aljanna tare da su. <b>Na uku </b>, ya sanya masa kyakkyawan ambato a cikin al’ummun da za su zo bayansa. <b>Na huɗu </b>, ya roƙe shi ya sanya shi cikin magada Aljannar ni’ima, watau ya shige ta ya more jin daɗin cikinta kamar yadda mai abu yake more abinsa da ya gada ya zama nasa. <b>Na biyar </b>, ya gafarta wa mahaifinsa Azaru domin ya kasance cikin ɓatattu waɗanda suka rayu a kan bautar gumaka ba Allah ba. Wannan addu’ar ya yi ta ne domin cika wa mahaifinsa alƙawarin da ya yi masa na cewa zai nema masa gafara, amma daga baya ya barranta da shi lokacin da ya tabbatar da cewa shi maƙiyin Allah ne. [Dubi Suratut Tauba aya ta 114]. <b>Na shida </b>, kada Allah ya kunyata shi a ranar alƙiyama, ranar da za a tashi kowa da kowa, ranar da dukiya da ‘ya’ya ba za su yi amfani ba kamar yadda suke yi wa mai su amfani a nan duniya. Sai dai wanda ya zo wa Allah da lafiyayyar zuciya wadda babu shirka babu riya ko munafurci a cikinta, to wannan shi ne zai amfana da dukiyarsa da ya ciyar domin Allah, da kuma ‘ya’yansa da ya bari suka riƙa yi masa kyakkyawar addu’a. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ibrahimu zai haɗu da babansa Azaru ranar alƙiyama fuskarsa ta yi baƙi da ƙura, sai Ibrahimu ya ce masa: “Ban faɗa maka kada ka saɓa mini ba?” Sai babansa ya ce masa: “To a yau ba zan saɓa maka ba.” Sai Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ka yi min alƙawari cewa ba za ka wulaƙanta ni ba a ranar da za a tashe su, to wane wulaƙanci ne ya fi na babana wanda aka nesanta shi daga rahama?” Sai Allah Ta’ala ya ce: “Lalle ni na haramta wa kafirai shiga Aljanna.” Sannan sai a ce masa: “Ya Ibrahimu, mene ne a ƙarƙashin ƙafafunka?” Sai ya duba sai kawai ya ga wani kure kaca-kaca da jini, sai a kama ƙafafunsa (watau kuren) sai a jefa shi cikin wuta.” [Bukhari #3350].
وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 26:90Aka kuma kusantar da Aljanna ga masu taƙawa.
وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِلۡغَاوِينَ
Open ayah 26:91Kuma aka bayyanar da (wutar) Jahima ga ɓatattu.
وَقِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ
Open ayah 26:92Aka kuma ce da su: “Ina abubuwan da kuka kasance kuna bauta wa?
مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلۡ يَنصُرُونَكُمۡ أَوۡ يَنتَصِرُونَ
Open ayah 26:93“Waɗanda ba Allah ba? Shin za su taimake ku, ko za su taimaki kansu?”
فَكُبۡكِبُواْ فِيهَا هُمۡ وَٱلۡغَاوُۥنَ
Open ayah 26:94Sai aka kikkifa su cikinta (wutar) su da ɓatattu.
وَجُنُودُ إِبۡلِيسَ أَجۡمَعُونَ
Open ayah 26:95Da kuma rundunar Iblis gaba ɗaya.
قَالُواْ وَهُمۡ فِيهَا يَخۡتَصِمُونَ
Open ayah 26:96Sai suka ce, alhali suna jayayya da juna a cikinta:
تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ
Open ayah 26:97“Mun rantse da Allah tabbas mun kasance (a duniya) cikin ɓata bayyananne.
إِذۡ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:98“Lokacin da muke daidaita ku da Ubangijin talikai.
وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 26:99“Ba kuwa waɗanda suka ɓatar da mu sai manyan masu laifuka.
فَمَا لَنَا مِن شَٰفِعِينَ
Open ayah 26:100“To a (yau) ba mu da wasu masu ceto.
وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٖ
Open ayah 26:101“Ba kuma wani aboki na ƙut-da-ƙut.
فَلَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:102“To ina ma da za mu samu damar komawa, sai mu zamanto daga muminai!”
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:103Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu, ba su zamanto muminai ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:104Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon bayinsa a ranar alƙiyama masu taƙawa da kuma kafirai. Za a kusanto da Aljanna ga masu kiyaye dokokin Ubangijinsu, suna aikata abin da ya umarce su suna kuma barin abin da ya hana su. Ita kuma wutar Jahannama a bayyanar da ita ga ɓatattu waɗanda suka bijire wa addinin gaskiya a duniya. Sai a tambaye su ina gumakan da suka zamanto suna bauta wa a duniya ba Allah ba? Shin za su taimake su a wannan mawuyacin hali da suke ciki, ko kuma za su taimaki kansu? Ba za su iya ko ɗaya ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa a lokacin za a jefa su cikin wutar Jahannama su da waɗanda suka ɓatar da su wasu kan wasu tare da rundunar Iblis, watau shaiɗanun mutane da aljannu. Daga nan sai jayayya ta kaure tsakanin mushrikai da waɗanda suka bautar da su a duniya, su riƙa rantsuwa cewa wallahi da ma su sun kasance cikin ɓata lokacin da suke daidaita su da Ubangijin halittu, suka riƙa bautar su kamar yadda ake bauta wa Allah. Kuma ba wasu ne suka ɓatar da su ba sai shaiɗanun shuwagabanninsu waɗanda suka ja su zuwa ga bautar wanin Allah. A lokacin ne za su tabbatar da cewa, ba su da wasu masu ceton su daga azabar Allah, kuma ba su da wani aboki amini wanda zai kare su daga azabar Allah ko ya cece su. Daga nan sai su shiga nadama da da-na-sanin cewa ina ma da za su sake samun damar komawa duniya da sun zamo muminai, to amma ina, bakin alƙalami ya riga ya bushe. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a cikin wannan labari da ya gabata da wannan faɗakarwa da ta biyo baya, lallai akwai abin izina da wa’azi ga masu wa’azantuwa, sai dai kuma yawancinsu ba su zamo masu yin imani ba. Sai kuma ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa Ubangijinsa mabuwayi ne, zai azabtar da maƙiyansa, mai rahama ne kuma ga waɗanda suka tuba daga cikinsu suka koma gare shi.
كَذَّبَتۡ قَوۡمُ نُوحٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 26:105Mutanen Nuhu sun ƙaryata mazanni.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 26:106Lokacin da ɗan’uwansu Nuhu ya ce da su: “Yanzu ba za ku kiyaye dokokin Allah ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
Open ayah 26:107“Lalle ni Manzo ne amintacce a gare ku.
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:108“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:109“Ba na kuma tambayar ku wani lada a game da shi (isar da manzancin). Ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai.
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:110“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.”
۞قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلۡأَرۡذَلُونَ
Open ayah 26:111Suka ce: “Yanzu ma yi imani da kai alhali ƙasƙantattu ne mabiyanka?”
قَالَ وَمَا عِلۡمِي بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 26:112Ya ce: “Ba ni da sani game da abin da suka zamanto suna aikatawa.
إِنۡ حِسَابُهُمۡ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّيۖ لَوۡ تَشۡعُرُونَ
Open ayah 26:113“Hisabinsu kawai yana wajen Ubangijina ne; da za ku gane.
وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:114“Ni kuma ba mai korar muminai ba ne.
إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 26:115“Ni kawai mai gargaɗi ne mai bayyanawa.”
قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمَرۡجُومِينَ
Open ayah 26:116Suka ce: “Ya Nuhu, mun rantse idan ba ka daina (faɗar abin da kake faɗa) ba, tabbas za ka zamanto daga cikin jefaffu!”
قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوۡمِي كَذَّبُونِ
Open ayah 26:117Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun ƙaryata ni.
فَٱفۡتَحۡ بَيۡنِي وَبَيۡنَهُمۡ فَتۡحٗا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِيَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:118<b> “Ka yi hukunci tsakanina da su, kuma Ka tserar da ni tare da muminan da suke tare da ni.”
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
Open ayah 26:119Sai Muka tserar da shi da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwan da ke maƙare (da mutane da dabbobi).
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا بَعۡدُ ٱلۡبَاقِينَ
Open ayah 26:120Sannan bayan haka Muka nutsar da sauran.
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:121Lalle <b> a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:122Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Manzonsa labarin Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa mutanensa sun ƙaryata manzannin Allah, saboda sun ƙaryata Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Domin abin da ya zo musu da shi na kaɗaita Allah irinsa ne sauran manzannin Allah suka zo da shi. Annabi Nuhu ya gargaɗe su da cewa su ji tsoron Allah ta hanyar barin bautar gumaka, su bauta wa Allah shi kaɗai, kuma shi Manzon Allah ne da ya aiko zuwa gare su kuma mai amana ne ba zai ƙara komai a kan abin da aka yi masa wahayinsa ba, ba kuma zai rage wani abu ba. Ya sake nanata musu gargaɗin su kiyaye dokokin Allah su aikata abin da ya umarce su su kuma guji abin da ya hana su, kuma su yi masa ɗa’a shi kansa, domin zamantowarsa manzo zuwa gare su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar wa da mutanensa cewa ba ya neman wani lada a wurinsu a kan isar musu da saƙon Ubangijinsu balle ma su ga cewa ya ɗora musu wani nauyi da ba za su iya ɗauka ba. Ya faɗa musu cewa shi ladansa yana wurin Allah ne kawai wanda shi ne Ubangijin halittu duka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Nuhu ya yi ta nanata wa mutanensa cewa su ji tsoron Allah, su kiyaye dokokinsa, su kuma yi masa biyayya, tare da tabbatar musu da hujjojinsa masu nuna gaskiyar manzancinsa da amanarsa da nasiharsa gare su, amma sai mutanensa suka bijire, suka zo da wani dalilin da yake ƙunshe da wauta da rashin hankali da cewa ta yaya za su yi imani da shi su karɓi abin da ya zo musu da shi, alhalin mabiyansa ƙasƙantattun mutane ne, ba ya tare da wasu manyan mutane masu daraja. Sai Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar musu da martani da cewa shi ba shi da wata masaniya game da abin da waɗannan mutane suke aikatawa, watau ba a umarce shi da ya binciki kowa ba kafin ya karɓi imaninsu. Abin da ya sani dai shi ne, sakamakon kowa yana ga Allah wanda shi ne ya san abin da suka ɓoye da abin da suka bayyana a sarari. Da sun gane wannan da ba za su faɗa masa abin da suka faɗa masa ba. To yayin da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fahimci cewa mutanensa suna neman sa ne da ya kori mabiyansa waɗanda suke ganin ƙasƙantattu ne idan har yana son su yi imani da shi, sai ya shaida musu cewa shi ba zai kori muminai daga majalisarsa ba, domin ba abin da suka yi masa da zai sa ya kore su. Shi kawai mai gargaɗi ne a fili mai tsoratar da mutane azabar Allah da fushinsa, don haka babu batun korar wani a hannunsa. Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) dai bai sassauta ba; ya ci gaba da wa’azinsa da nasiharsa ga mutanensa ba dare ba rana tsawon lokaci, su kuma sai ƙara bijire masa suke yi. A ƙarshe ma suka fito fili suka fara yi masa barazana da cewa lalle idan bai daina yi musu wannan wa’azi ba to za su jefe shi da duwatsu har mutuwa. To da Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga kafircin mutanensa ya ƙara tsananta sai ya koma ga Ubangiji ya ɗaga hannu ya roƙe shi yana shaida masa cewa mutanensa fa sun ƙaryata shi, ba shi da sauran wata dabara, yana roƙon sa da ya yi hukunci tsakaninsa da mutanensa, ya hallaka su saboda kafewarsu a kan kafirci, shi kuma ya tserar da shi tare da muminai waɗanda suka yi imani da shi. Sai ko Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karɓi addu’arsa ya tserar da shi har da muminan da suke tare da shi a cikin jirgin ruwa wanda yake cike da mutane da dabbobi. Sannan ya hallaka sauran mutanensa ta hanyar nutsar da su cikin ruwan Ɗufana. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana yin hannunka-mai-sanda da cewa, lalle a cikin wannan labarin na Annabi Nuhu da tserar da shi da hallakar da mutanensa tabbas akwai abin izina ga mutane masu ɗaukar izina. To amma yawancinsu ba sa yin imani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa cewa shi mabuwayi ne yana kuma yin uƙuba ga maƙiyansa, kuma mai rahama ne ga duk wanda ya tuba daga cikinsu ya koma ga Allah.
كَذَّبَتۡ عَادٌ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 26:123Adawa (ma) sun ƙaryata manzanni.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 26:124Lokacin da ɗan’uwansu Hudu ya ce da su: “Yanzu ba kwa riƙa kiyaye dokokin (Allah) ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
Open ayah 26:125“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku.
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:126“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:127“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai.
أَتَبۡنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةٗ تَعۡبَثُونَ
Open ayah 26:128“Yanzu kwa riƙa yin dogayen gine-gine a kan tuddai kuna sharholiya?
وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمۡ تَخۡلُدُونَ
Open ayah 26:129“Kuma ku riƙa gina ganuwoyi da maka-makan gidaje kamar za ku dawwama?
وَإِذَا بَطَشۡتُم بَطَشۡتُمۡ جَبَّارِينَ
Open ayah 26:130“Idan kuma kuka yi damƙa sai kukan yi damƙa da tsanani.
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:131“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.
وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِيٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعۡلَمُونَ
Open ayah 26:132“Kuma ku kiyaye dokokin (Allah) wanda Ya ni’imta ku da abin da kuka sani.
أَمَدَّكُم بِأَنۡعَٰمٖ وَبَنِينَ
Open ayah 26:133“Ya ni’imta ku da dabbobin ni’ima da ‘ya’ya.
وَجَنَّٰتٖ وَعُيُونٍ
Open ayah 26:134“Da kuma gonakai da idanuwan ruwa.
إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 26:135“Lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.”
قَالُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَوَعَظۡتَ أَمۡ لَمۡ تَكُن مِّنَ ٱلۡوَٰعِظِينَ
Open ayah 26:136Suka ce: “Mu duk ɗaya ne a wajenmu; ko ka yi wa’azi ko kuwa kada ka zamanto daga masu wa’azi.
إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 26:137“Wannan ba wani abu ba ne in ban da halayyar mutanen farko.
وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ
Open ayah 26:138“Mu kuma ba waɗanda za a yi wa azaba ba ne.”
فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:139Sai suka ƙaryata shi, sannan Muka hallaka su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:140Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabi (ﷺ) labarin Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da cewa Adawa sun ƙaryata manzanni lokacin da suka ƙaryata Annabi Hudu, yayin da yake yi musu wa’azi yana nuna musu cewa, me ya sa ba za su ji tsoron Allah ba su bar bauta wa gumaka ba Allah ba? Ya bayyana musu cewa shi manzon Allah ne da ya aiko shi zuwa gare su kuma mai amana ne ba zai ƙara wani abu a cikin saƙon Allah ba kuma ba zai rage komai ba. Sai kuma ya umarce su da su kiyaye dokokin Allah, su aikata abin da ya umarce su da aikatawa su guji abin da ya hana su, kuma su yi masa ɗa’a, domin kasancewarsa Manzon Allah ne zuwa gare su. Kuma ya tabbatar musu da cewa ba ya buƙatar wani lada daga wajensu a kan saƙon da yake isar musu daga Allah, ladansa kawai yana wurin Allah Ubangijin talikai ne. Sannan Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tsawata wa mutanensa game da abin da suke ciki na shagalta da rayuwar duniya wadda ta sa ba sa son maganar lahira, ya kuma ja hankalinsu game da manya-manyan gine-gine da suke yi a wurare maɗaukaka domin sharholiya da wasanni kawai ba tare da wani amfani na duniya ko lahira ba. Kuma suna gina ganuwowi da maka-makan gidaje kamar za su dawwama a duniya ba za su mutu ba. Idan kuma za su kai wani farmaki na kisa ko duka to sukan wuce iyaka ne su kai shi da tsattsaurar zuciya wadda babu rahama ko tausayi a cikinta. Sai Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sake umartar su da su kiyaye dokokin Allah; su yi aiki da umarninsa su kuma guje wa haninsa, kuma su yi masa biyayya a kan abin da yake umartar su da shi. Ya ƙara jan hankalinsu a kan su ji tsoron Allah su kiyayi fushinsa, shi ne fa ya ni’imta su da abubuwan jin daɗi na rayuwa, ya ba su dabbobin ni’ima da ‘ya’ya maza da kuma gonaki da idanuwan ruwa masu kwarara. Ya ƙara da cewa yana jiye musu tsoron azabar wani yini mai girma, watau ranar alƙiyama. Bayan duk wannan wa’azin da Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mutanensa da tsoratar da su ranar alƙiyama, amma sai suka bayyana masa cewa duk ɗaya ne a wajensu ya yi musu wa’azi ko kada ya yi, su dai ba za su yi imani da shi ba, ba kuma za su bar abin da suke a kai ba. Abin da suke a kai ba wani sabon abu ne ba, in ban da addinin mutanen farko, watau na iyayensu da kakanninsu kuma shi ne al’adarsu, don haka suna nan a kan bin tafarkin iyayensu, kuma sun tabbatar ba za a azabtar da su a kan haka ba. Sai Allah ya bayyana cewa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ci gaba da ƙaryata shi, sai Allah ya hallakar da su da wata iska mai tsanani. Allah ya bayyana cewa a cikin wannan hallakawar da ya yi musu akwai abin izina ga masu ɗaukar izina, to amma yawancinsu ba masu yin imani ne ba. Ya kuma tabbatar wa Manzonsa cewa shi ne mabuwayi mai iya kama maƙiyansa duk sa’adda ya ga dama, mai rahama ne kuma ga waɗanda suka tuba suka koma gare shi.
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 26:141Samudawa sun ƙaryata manzanni.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 26:142Lokacin da ɗan’uwansu Salihu ya ce da su: “Yanzu ba kwa yi taƙawa ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
Open ayah 26:143“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku.
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:144“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:145“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai.
أَتُتۡرَكُونَ فِي مَا هَٰهُنَآ ءَامِنِينَ
Open ayah 26:146“Yanzu (zatonku) za a bar ku ne cikin abin da yake a nan (duniya) cikin kwanciyar hankali?
فِي جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ
Open ayah 26:147“(Watau) a cikin gonaki da idandunan ruwa?
وَزُرُوعٖ وَنَخۡلٖ طَلۡعُهَا هَضِيمٞ
Open ayah 26:148“Da shuke-shuke da dabinai masu taushin ‘ya’ya?
وَتَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا فَٰرِهِينَ
Open ayah 26:149“Kuma kuna fafe duwatsu kuna yin gidaje kuna masu nuna ƙwarewa?
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:150“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.
وَلَا تُطِيعُوٓاْ أَمۡرَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Open ayah 26:151“Kada kuma ku bi umarnin maɓarnata.
ٱلَّذِينَ يُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا يُصۡلِحُونَ
Open ayah 26:152“Waɗanda suke ɓarna a bayan ƙasa, kuma ba sa gyara.”
قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ
Open ayah 26:153Suka ce: “Lalle kai kana daga waɗanda aka sihirce ne kawai.
مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا فَأۡتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 26:154“Kai ba kowa ba ne sai mutum kamarmu, to ka zo mana da aya idan ka kasance daga masu gaskiya.”
قَالَ هَٰذِهِۦ نَاقَةٞ لَّهَا شِرۡبٞ وَلَكُمۡ شِرۡبُ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
Open ayah 26:155(Salihu) ya ce: “Wannan taguwa ce, tana da (ranar) shanta ku ma kuna da rana sananniya ta shanku.
وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 26:156“Kada kuwa ku shafe ta da mugun abu, sai azabar wani yini mai girma ta kama ku.”
فَعَقَرُوهَا فَأَصۡبَحُواْ نَٰدِمِينَ
Open ayah 26:157Sai suka soke ta, sai kuwa suka wayi gari suna masu nadama.
فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:158Sai azaba ta kama su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:159Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabi (ﷺ) labarin Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yayin da ya aike shi zuwa ga ƙabilarsa Samudawa da cewa sun ƙaryata manzanni saboda sun ƙaryata Annabinsu Salihu wanda ya zo musu da irin saƙon da duk manzannin Allah suka zo da shi na kaɗaita Allah da bauta. Ɗan’uwansu Annabi Salihu ya faɗa musu cewa me ya sa ba za su kiyaye dokokin Allah, su bi umarninsa su guje wa haninsa ba? Ya kuma tabbatar musu cewa shi Manzon Allah ne zuwa gare su kuma mai amana ne ba zai ƙara komai a cikin saƙon da Allah ya yi masa wahayinsa ba, ba kuma zai rage wani abu ba. Shi kuma ba ya neman wani lada a wurinsu na isar musu da saƙon Allah ballantana su ji cewa ya ɗora musu wani harajin da ya fi ƙarfinsu, domin shi ladansa yana wurin Allah Ubangijin talikai, shi kaɗai ne zai biya shi. Sai kuma ya gargaɗe su tare da yi musu wa’azi a kan irin rayuwar da suke yi ta sheƙe-aya; kar su zaci cewa za a bar su cikin ni’imar da suke mora a nan duniya hankalinsu a kwance, a ƙyale su su ci gaba da rayuwa ta jin daɗi a cikin gonaki da idanuwan ruwa masu gudana da shuke-shuke iri-iri da dabinai masu nunannun ‘ya’ya. Sannan su ci gaba da fafe duwatsu suna yin gidajen zama tare da nuna ƙwarewarsu wajen gina su. Ya kuma sake umartar su da su kiyaye dokokin Allah, su bi umarninsa su guji haninsa, sannan su yi masa ɗa’a cikin duk abin da zai umarcesu ko kuma ya hana su, su guji bin umarnin masu ƙetare iyakokin Allah da aikata laifuffuka da yaɗa ɓarna a bayan ƙasa, ba sa ƙoƙarin yin gyara ko kaɗan. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mutanen Annabi Salihu sun yi watsi da duk wani wa’azi da ya yi musu; maimakon su yi imani da shi sai ma suka shiga tuhumar sa da cewa yana cikin mutanen da ake yi wa sihiri a kai-a kai har sihirin ya kawar musu da hankulansu, don haka ba za su yarda da maganganunsa ba. Haka kuma sun soke shi da cewa ai shi mutum ne kamarsu babu abin da ya fi su da shi ballantana har a ba shi manzanci su ba a ba su ba. Kuma idan har da gaske shi Manzon Allah ne to ya nuna musu wata alama da za ta nuna shi mai gaskiya ne. Sai ko Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hore masa taguwa a matsayin mu’ujiza gare shi domin tabbatar da annabcinsa. Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana musu cewa wannan taguwar tana da ranar shan ruwanta su ma mutanen gari suna da ƙayyadajjiyar ranar shan su, don haka kada su shiga ranarta, ita ma ba za ta shiga tasu ranar ba. Ya kuma gargaɗe su da kada su kuskura su shafe ta da wani mugun abu, kamar duka ko kisa sai a dalilin haka wata azaba ta auka musu ta hallaka su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mutanen Annabi Salihu saboda ƙeta da tsaurin kai suka haɗa baki a kan su soke wannan taguwar, sai ko mafi tsagerancin cikinsu ya soke ta. A kan wannan sai suka wayi gari suna nadama bisa ga aika-aikarsu yayin da azabar Allah ta aukar musu. Nadama a lokacin kuwa ba ta yi amfani ba. Azabar kuwa ita ce tsawa da girgizar ƙasa wadda ta hallaka su gaba ɗaya. Allah ya bayyana cewa lalle a game da labarin Annabi Salihu da mutanensa akwai abin izina da darasi ga masu ɗaukar izina da darasi, to amma kuma yawancin mutane ba sa yin imani ko da kuwa an nuna musu ayoyi da mu’ujizoji masu yawa. Allah kuma ya bayyana wa Manzonsa cewa shi mabuwayi ne mai azabtar da maƙiyansa, kuma mai rahama ne, yana kuma karɓar tuban wanda ya tuba ya koma gare shi.
كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 26:160Mutanen Luɗu sun ƙaryata manzanni.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 26:161Lokacin da ɗan’uwansu Luɗu ya ce da su: “Yanzu ba kwa kiyaye dokokin Allah ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
Open ayah 26:162“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku.
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:163“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:164“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai.
أَتَأۡتُونَ ٱلذُّكۡرَانَ مِنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:165“Yanzu kwa riƙa zaike wa maza daga halittu?
وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٌ عَادُونَ
Open ayah 26:166“Kuma ku bar abin da Ubangijinku Ya halitta na matanku dominku? A’a, ku dai mutane ne masu ƙetare iyaka.”
قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُخۡرَجِينَ
Open ayah 26:167Suka ce: “Tabbas Luɗu idan ba ka bar (faɗar abin da kake faɗa ba) haƙiƙa za ka kasance daga korarru (daga garin nan).”
قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلۡقَالِينَ
Open ayah 26:168(Luɗu) ya ce: “Lalle ni ina cikin masu ƙyamar aikin nan naku.
رَبِّ نَجِّنِي وَأَهۡلِي مِمَّا يَعۡمَلُونَ
Open ayah 26:169“Ya Ubangijina, Ka tserar da ni da iyalina daga (sakamakon) abin da suke aikatawa.”
فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 26:170Sai Muka tserar da shi da iyalinsa gaba ɗaya.
إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ
Open ayah 26:171Sai fa wata tsohuwa (watau matarsa) da ta (kasance tana) cikin hallakakku.
ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Open ayah 26:172Sannan Muka hallaka sauran.
وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Open ayah 26:173Muka kuma saukar musu da ruwa na azaba; to ruwan azabar waɗanda aka yi wa gargaɗi ya munana.
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:174Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; yawancinsu kuwa ba su zamanto muminai ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:175Kuma lalle Ubangiijnka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Manzonsa (ﷺ) labarin Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa, lokacin da ya aike shi gare su, sai suka ƙaryata manzanni ta hanyar ƙaryata shi, domin duk manzannin Allah saƙo iri ɗaya suka zo da shi, watau Tauhidi. Allah ya bayyana cewa, ɗan’uwansu Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ja hankalinsu a kan su kiyaye dokokin Allah, watau su bi umarninsa su guje wa haninsa su bar aikata shirka. Ya tabbatar musu cewa shi Manzo ne da Allah ya aiko musu kuma mai amana ne, ba zai ƙara komai cikin saƙon da aka yi masa wahayi ba, ba kuma zai rage komai ba. Sannan kamar sauran manzannin da suka gabace shi ya shaida wa mutanensa cewa ba ya neman wani lada daga wajensu a kan isar musu da saƙon Allah da ya yi ballantana har su ce ya ɗora musu nauyin da ya fi ƙarfinsu. Shi kawai ladansa yana wurin Allah, shi ne zai biya shi ba wani ba. Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo ya sami mutanensa suna aikata wata mummunar alfasha, watau saduwa da maza ta duburarsu, ya nuna musu girman laifinsu, kuma don me suke barin matansu da Allah ya halatta musu domin su biya buƙatar sha’awarsu a wajensu? Annabi Luɗu ya tabbatar musu da cewa lalle su mutane ne da suke ƙetare iyaka. To amma sai mutanensa suka yi watsi da wannan kiran har ta kai suna yi masa barazanar sai sun kore shi daga shi har mabiyansa daga ƙasarsu idan har bai daina yi musu wa’azi a kan wannan batu ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da Annabi Luɗu ya ga mutanensa sun kafe a kan ci gaba da wannan mummunan aiki nasu sai ya bayyana musu cewa lalle shi yana ƙyamar wannan aiki nasu. Ya kuma ɗaga hannu ya yi addu’a yana mai roƙon Allah ya tserar da shi tare da iyalansa daga azabar da za ta auka wa waɗannan maɓarnata saboda mummunan aikinsu. Sai Allah ya amsa addu’arsa ya kuma tserar da shi tare da iyalansa in ban da matarsa wadda take kafira, ita kam tana cikin halakakku. Bayan Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fita daga alƙaryar Sadum tare da iyalansa sai Allah ya hallaka sauran mutanensa mummunar hallakarwa, watau ya yi musu ruwan duwatsu daga sama. Sai Allah ya tabbatar da cewa wannan ruwan azaba ya munana ƙwarai ga mutanen da suka jima ana yi musu gargaɗi ana tsoratar da su azabar Allah amma suka bijire suka ƙi yin imani. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle a cikin wannan labari na Annabi Luɗu da azabar da ya saukar wa mutanensa akwai izina da wa’azi ga mutanen da suke ɗaukar izina. Sai dai yawancinsu ba su zama masu yin imani ba duk kuwa da ayoyin Allah da suka gani. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar wa Manzonsa cewa shi mabuwayi ne mai azabtar da maƙiyansa, mai rahama ne kuma ga waɗanda suka tuba suka koma gare shi.
كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ لۡـَٔيۡكَةِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 26:176Mutanen kurmi sun ƙaryata manzanni.
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ شُعَيۡبٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 26:177Lokacin da Shu’aibu ya ce da su: “Yanzu ba kwa kiyaye dokokin (Allah) ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
Open ayah 26:178“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku.
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 26:179“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni.
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:180“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai.
۞أَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُخۡسِرِينَ
Open ayah 26:181“Ku cika mudu kada kuma ku zamanto daga masu tauye (shi).
وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِ
Open ayah 26:182“Kuma ku riƙa yin awon nauyi da ma’auni na adalci.
وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ
Open ayah 26:183“Kada kuma ku tauye wa mutane kayayyakinsu, kuma kada ku yawaita ɓarna a bayan ƙasa.
وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلۡجِبِلَّةَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 26:184“Kuma ku kiyaye dokokin (Allah) wanda Ya halicce ku da kuma al’ummu na farko.”
قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ
Open ayah 26:185Suka ce: “Kai dai kana daga waɗanda aka sihirce ne kawai.
وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Open ayah 26:186“Kuma kai ba kowa ba ne sai mutum kamarmu, kuma ma lalle muna zaton kana daga maƙaryata!
فَأَسۡقِطۡ عَلَيۡنَا كِسَفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 26:187“Sai ka jeho mana da yankuna (na azaba) daga sama in ka kasance daga masu gaskiya!”
قَالَ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 26:188(Shu’aibu) Ya ce: “Ubangijina Ya fi kowa sanin abin da kuke aikatawa.”
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمِ ٱلظُّلَّةِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ
Open ayah 26:189Sai suka ƙaryata shi, sannan sai azabar yinin girgije (na wuta) ta kama su. Lalle ta kasance azabar wani yini ne mai girma.
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:190Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; sai dai kuma yawancinsu ba su kasance muminai ba.
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 26:191Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai rahama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba wa Manzonsa (ﷺ) labaran annabawa. A nan ya ba shi labarin Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya aike shi zuwa ga mutanen wata alƙarya mai yawan bishiyoyi kusa da Madyana, ya gargaɗe su da cewa me ya hana su su kiyaye dokokin Allah, watau su bi umarninsa su kuma guji haninsa? Ya tabbatar musu da cewa shi Manzon Allah ne da ya aiko shi zuwa gare su, shi kuma mai amana ne ba zai ƙara ko ya rage wani abu cikin wahayin da Allah ya yi masa ba. Ya sake umartar su da su kiyaye dokokin Allah; su bi umarninsa su guji haninsa, shi kuma su yi masa ɗa’a cikin abin da yake faɗa musu. Ya kuma tabbatar musu cewa shi ba ya neman wani lada daga wajensu a kan isar musu da saƙon Allah da shari’arsa ballantana ma su yi zaton cewa ya ɗora musu wani haraji wanda ya fi ƙarfinsu. Don haka ladansa yana wurin Allah Ubangijin halittu ne kawai. Mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) duk da shirkarsu suna kuma tauye mudun awo da sikeli, don haka sai ya umarce su da cewa idan za su sayar wa da mutane kayansu to su cika musu mudu kada su tauye wa mutane mudunsu. Idan kuma awon kayan nauyi ne za su yi wa mutane to su yi musu da sikeli madaidaici. Haka kuma ya hana su tauye wa mutane haƙƙinsu na awon mudu ko na sikeli. Ya kuma hana su yawaita ɓarna a bayan ƙasa ta hanyar saɓon Allah da bijire wa dokokinsa. Kuma lallai su ji tsoron Allah; su aikata umarninsa su guje wa haninsa, Allah shi ne wanda ya halicce su har da al’ummun da suka gabata. To amma sai mutanen Annabi Shu’aibu suka bijire wa wa’azinsa, suka ma tuhumce shi da cewa ana ta yi masa sihiri ne a kai-a kai har hankalinsa ya taɓu, don haka ne yake yi musu irin waɗannan maganganu. Sannan suka nuna masa cewa shi fa bai fi su da komai ba da har Allah zai zaɓe shi ya ba shi manzanci, domin kuwa shi mutum ne kamarsu. Ƙarshe ma suka ce babban zaton da suke yi masa shi maƙaryaci ne yana yi musu ƙaryar manzanci ne, don haka ba za su yi imani da shi ba. Suka ma neme shi da ya jeho musu wani yanki na azaba daga sama idan har da gaske ne shi Manzon Allah ne. Sai Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar musu da martani da cewa Ubangijinsa ya fi kowa sanin laifukan da suke aikatawa na shirka da saɓon Allah da cutar mutane, don haka shi ne zai yanke musu hukuncin saukar musu da azaba idan ya ga dama ya gaggauto musu ita, idan kuma ya ga dama ya saurara musu zuwa wani lokaci na daban. Sai suka ci gaba da ƙaryata Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), a ƙarshe sai wata azaba mai girma ta auka musu, yayin da wani girgije ya yi musu rumfa ya lulluɓe su bayan wani yini mai tsananin zafi, sai aka yi musu ruwan wuta ta ƙone su gaba ɗaya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle ranar hallakar da su wata babbar rana ce mai cike da ban tsoro. Allah ya bayyana cewa lalle a cikin labarin Annabi Shu’aibu da mutanensa da hallakarsu akwai abin izina ga mutane masu ɗaukar izina, amma yawancinsu ba sa yin imani. Ya kuma tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa shi mabuwayi ne ya fi ƙarfin maƙiyansa, kuma mai rahama ne yana karɓar tuban wanda ya tuba ya komo gare shi.
وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 26:192Kuma lalle shi (Alƙur’ani) saukarwa ce ta Ubangijin talikai.
نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلۡأَمِينُ
Open ayah 26:193Ruhi amintacce (watau Jibrilu) ne ya sauko da shi.
عَلَىٰ قَلۡبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ
Open ayah 26:194A bisa zuciyarka don ka zamanto daga masu gargaɗi.
بِلِسَانٍ عَرَبِيّٖ مُّبِينٖ
Open ayah 26:195(Ya saukar da shi) da harshen Larabci mabayyani.
وَإِنَّهُۥ لَفِي زُبُرِ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 26:196Kuma lalle shi yana daga cikin littattafan farko.
أَوَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ ءَايَةً أَن يَعۡلَمَهُۥ عُلَمَٰٓؤُاْ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 26:197Yanzu bai ishe su aya ba cewa, malaman Banu- Isra’ila sun san shi?
وَلَوۡ نَزَّلۡنَٰهُ عَلَىٰ بَعۡضِ ٱلۡأَعۡجَمِينَ
Open ayah 26:198Da kuwa Mun saukar da shi ga wani wanda ba Balarabe ba.
فَقَرَأَهُۥ عَلَيۡهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:199Sannan ya karanta musu shi, to da ba za su yi imani da shi ba.
كَذَٰلِكَ سَلَكۡنَٰهُ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 26:200Kamar haka ne Muka shigar da shi (ƙaryata Annabi) cikin zukatan manyan masu laifi.
لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ
Open ayah 26:201Ba za su yi imani da shi ba har sai sun ga azaba mai raɗaɗi.
فَيَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 26:202Sannan (azabar) za ta zo musu ba zato ba tsammani, ba tare da suna sane ba.
فَيَقُولُواْ هَلۡ نَحۡنُ مُنظَرُونَ
Open ayah 26:203Sai su ce: “Yanzu za a saurara mana?”
أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ
Open ayah 26:204Yanzu azabarmu suke neman gaggautowa?
أَفَرَءَيۡتَ إِن مَّتَّعۡنَٰهُمۡ سِنِينَ
Open ayah 26:205Ka ba Ni labari idan Muka jiyar da su daɗi na tsawon shekaru.
ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُواْ يُوعَدُونَ
Open ayah 26:206Sannan kuma abin da ake yi musu alkawarin narko da shi ya zo musu.
مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يُمَتَّعُونَ
Open ayah 26:207Abin da ake jiyar da su daɗi a da ba zai amfana musu komai ba.
وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ
Open ayah 26:208Ba Mu taɓa hallaka wata al’umma ba face sai ta samu masu yi mata gargaɗi.
ذِكۡرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَٰلِمِينَ
Open ayah 26:209(Wannan) tunatarwa ce (gare su), ba Mu kuwa kasance azzalumai ba.
وَمَا تَنَزَّلَتۡ بِهِ ٱلشَّيَٰطِينُ
Open ayah 26:210Kuma shaiɗanu ba su sauko da shi ba.
وَمَا يَنۢبَغِي لَهُمۡ وَمَا يَسۡتَطِيعُونَ
Open ayah 26:211Kuma bai kamace su ba, ba kuma za su iya ba.
إِنَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّمۡعِ لَمَعۡزُولُونَ
Open ayah 26:212Lalle su ababen kangewa ne daga jin (wahayi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matsayin littafin da ya saukar wa Annabi (ﷺ), da cewa shi Alƙur’ani ne saukakke daga Allah Ubangijin talikai wanda Mala’ika Jibrilu amintaccen Allah ya saukar da shi a bisa zuciyar Manzon Allah (ﷺ) don ya zama ɗaya daga cikin manzannin Allah waɗanda suke gargaɗin mutane suna tsoratar da su azabar Allah. Kuma ya saukar da shi da harshen Larabci bayyananne, don haka Larabawa ba su da wata hujjar ƙaryata shi domin suna fahimtar komai a cikinsa dalla-dalla. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa a cikin littattafan annabawan farko ma an ambaci Alƙur’ani domin dukkansu sun yi albishir da shi. Ya ƙara da cewa, yanzu mushirikai masu ƙaryata Manzon Allah bai isa aya gare su mai tabbatar da gaskiyarsa ba cewa malaman Banu-Isra’ila ma sun san haƙiƙanin abin da Allah ya saukar wa Manzonsa kamar irin su Abdullahi ɗan Salam (Allah ya kara masa yarda) da Salmanul Farisi (Allah ya kara masa yarda)? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin tsaurin kan Ƙuraishawa wajen rashin yin imani da Alƙur’ani, da cewa da a ce ya saukar da shi ga wani mutum Ba’ajame wanda ba ya jin harshen Larabci, ya kuma zo ya karanta musu shi da Larabcinsa mai cike da fasaha al’amarin da zai ba wa kowa mamaki, to tabbas ba za su yi imani da cewa daga Allah yake ba, domin tsananin taurin kansu da ƙin gaskiya. Hakanan da a ce za a saukar da Alƙur’ani da harshen wani wanda ba ya iya magana da Larabci ya karanta musu shi, to a nan ma da sai su ce su fa ba sa fahimtar harshensa, don haka tunda ba sa gane komai daga wannan Alƙur’ani, sai su ƙi yin imani da shi su ƙi gaskata shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kamar yadda za su ƙaryata wancan mutumin Ba’ajame, to hakanan Allah ya shigar da ƙaryata Alƙur’ani da kafirci cikin zukatan kafirai, ba za su taɓa canzawa su bar wannan kafircin nasu ba, kuma ba za su yi imani ba har sai sun ga azaba mai raɗaɗi wadda za ta zo musu ba zato ba tsammani. To a lokacin ne za su tsinci kawunansu cikin tsananin nadama har su riƙa cewa, shin ko za a saurara musu zuwa wani lokaci su tuba zuwa ga Allah? Kafirai sun nace da tambayar Manzon Allah (ﷺ) wai yaushe ne azabar Allah da ake tsoratar da su da ita za ta zo musu? Shi kuma sai ya yi mamaki da cewa yanzu azabar Allah suke neman gaggautowa? Kai wasu ma daga cikinsu suna ƙalubalantar sa da cewa ba za su yi imani da shi ba har sai ya kifo musu da wani yanki na azaba daga sama, alhali kuwa suna da labarin yadda Allah ya hallaka al\'ummun da suka gabata. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa tsawon rai ba ya hana aukuwar azaba ga wanda ya jawo wa kansa ita. Ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa duk wani tsawon rai da za a jiyar da kafirai daɗi da shi komai yawansu sai alƙawarin da aka yi musu na azabar Allah ya zo musu, to wane amfani wannan jin daɗi na duniya zai yi musu? Daga ranar da suka bar duniya ya yanke kenan, sannan wata azaba mai ɗorewa za ta auka musu. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A ranar alƙiyama za a kawo wanda ya fi kowa jin daɗi a duniya daga cikin ‘yan wuta sai a tsoma shi cikin wuta sau ɗaya sai a ce masa, ‘ ya kai ɗan’adam, shin ka taɓa haɗuwa da alheri tunda kake? Shin ka taɓa jin daɗin wata ni’ima tunda Allah ya yi ka? ’ Sai ya ce: “A’a, wallahi ya Ubangijina.” Sai kuma a zo da wanda ya fi kowa shan wahala a duniya daga cikin ‘yan Aljanna, sai a tsoma shi a Aljanna sau ɗaya, sai a ce masa, ‘ ya kai ɗan’adam, shin tunda kake ka taɓa shan wahala? Ka taɓa shiga wani tsanani? ’ Sai ya ce: “A’a, wallahi ya Ubangijina ban taɓa shiga wata wahala ba tunda nake.” [Muslim #2807]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa babu wata al’umma da ya hallakar cikin al’ummun da suka gabata har sai da ya aiko musu da manzanni suka yi musu gargaɗi da wa’azi ya saukar musu da littattafai waɗanda suka ƙunshi shiriya da karantarwa, domin shi Allah ba azzalumi ne ba ballantana ya hallaka su gabanin ya gargaɗe su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da martani ga mushirikai masu cewa wai Annabi Muhammadu (ﷺ) boka ne, kuma Alƙur’ani da yake karanta musu sheɗanu ne suke sauko masa da shi. Allah ya ƙaryata su da cewa ba sheɗanu ne suka saukar masa da shi ba, kuma ma wannan aiki bai dace da sheɗanu ba kuma ba za su iya yin haka ba, domin an riga an katange su a sama ba za su iya sauraron wani wahayi ba ballantana su jiyo shi su kawo wa Annabi (ﷺ).
فَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُعَذَّبِينَ
Open ayah 26:213To kada ka bauta wa wani tare da Allah, sai ka zamanto daga waɗanda za a yi wa azaba.
وَأَنذِرۡ عَشِيرَتَكَ ٱلۡأَقۡرَبِينَ
Open ayah 26:214Kuma ka gargaɗi danginka mafiya kusanci.
وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 26:215Ka kuma tausasa ga wanda ya bi ka daga muminai.
فَإِنۡ عَصَوۡكَ فَقُلۡ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 26:216To idan suka saɓa maka sai ka ce: “Ni lalle ba ruwana da abin da kuke aikatawa.”
وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ
Open ayah 26:217Ka kuma dogara ga Mabuwayi, Mai rahama.
ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ
Open ayah 26:218Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi (don yin salla).
وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّٰجِدِينَ
Open ayah 26:219Da kuma (yayin) jujjuyawarka cikin masu sujjada.
إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 26:220Haƙiƙa Shi Mai ji ne, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana bautar wani abin bauta tare da shi; duk kuwa wanda ya aikata haka to sai Allah ya yi masa azaba. Sai kuma ya umarci Manzon Allah (ﷺ) da ya gargaɗi danginsa na kusa domin kada azabar Allah ta same su idan har suka mutu suna shirka. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yayin da wannan ayar ta sauka: “Kuma ka gargaɗi danginka na kurkusa”, sai Manzon Allah (ﷺ) ya fita ya hau kan Dutsen Safa ya ɗaga muryarsa ya ce: “Ku yi shiri gari ya waye.” Sai suka ce: “Wane ne wannan yake ihu?” Sai suka ce: “Muhammadu ne.” Sai suka taru a gabansa sai ya ce: “Ya Bani wane, ya Bani wane, ya Bani wane, ya Bani Abdi Manafi, ya Bani Abdilmuɗɗalib.” Sai duk suka taru a wajen sai ya ce: “Ku ba ni labari, da zan faɗa muku cewa ga wasu mayaƙa nan za su fito muku ta bayan wannan dutsen shin za ku gaskata ni?” Sai suka ce: “Ba mu taɓa samun ka da ƙarya ba.” Sai ya ce: “To ni lalle mai gargaɗi ne gare ku da wata azaba mai tsanani a nan gaba.” Sai Abu Lahab ya ce: “Tir da kai, yanzu don wannan kawai ka tara mu?” Sai ya tashi ya yi tafiyarsa, sai surar Tabbat Yada Abi Lahabin ta sauka.” [Bukhari #4770 da Muslim #208]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya tausasa magana ko aiki ga muminai waɗanda suka bi shi domin tausaya musu da nuna jin ƙai gare su. Sai kuma ya umarce shi da cewa idan mutanensa suka saɓa masa, suka bijire wa abin da ya zo musu da shi na kaɗaita Allah da yi masa ɗa’a, to ya tabbatar musu da cewa shi ba ruwansa da duk abin da suke aikatawa na shirka da saɓon Allah, aikinsa kawai shi ne ya yi musu wa’azi da nasiha kuma ya yi musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya dogara da shi cikin dukkan al’amuransa domin shi ne Mabuwayi mai yin uƙuba ga maƙiyansa, mai kuma rahama ga duk wanda ya tuba ya koma gare shi. Shi ne kuma wanda yake ganin sa lokacin da yake tsayawa yana salla, yana kuma jujjuyawa daga wani yanayi zuwa wani yanayi a cikin masallata; yana sane da ɗaukacin ayyukansa da sauran ayyukan bayinsa, domin shi mai ji ne kuma masani.
هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ
Open ayah 26:221Shin ba Na ba ku labari ba game da wanda sheɗanu suke saukar masa?
تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ
Open ayah 26:222Suna sauka ne a kan duk wani maƙaryaci mai yawan laifi.
يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ
Open ayah 26:223Suna jefa wa (bokaye) abin da suka sato jinsa, yawancinsu kuwa maƙaryata ne.
وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلۡغَاوُۥنَ
Open ayah 26:224<b> Mawaƙa kuwa ɓatattu ne suke bin su.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّهُمۡ فِي كُلِّ وَادٖ يَهِيمُونَ
Open ayah 26:225Ba ka ga cewa su kutsawa suke yi cikin kowanne kwari ba?
وَأَنَّهُمۡ يَقُولُونَ مَا لَا يَفۡعَلُونَ
Open ayah 26:226Lalle kuma suna faɗar abin da ba sa aikatawa.
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَذَكَرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱنتَصَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَيَّ مُنقَلَبٖ يَنقَلِبُونَ
Open ayah 26:227Sai dai waɗanda suka yi imani kuma suka yi aiki na gari, kuma suka ambaci Allah da yawa, suka kuma yi sakayya bayan an zalunce su. Waɗanda suka yi zalunci kuwa ba da daɗewa ba za su san kowace makomar za su koma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana mayar da martani ne ga kafirai masu cewa sheɗanu ne suka saukar wa da Annabi (ﷺ) Alƙur’ani. Allah ya bayyana musu haƙiƙanin waɗanda sheɗanu suke saukar musu da cewa, sheɗanu suna sauka ne ga duk wani maƙaryaci mai yawan saɓa wa Allah, kamar bokaye da danginsu. Sheɗanu suna hawa sama ta kusa su sato musu jin abin da mala’iku suke tattaunawa a junansu, sai su jefa wa abokansu bokaye abin da suka sato sauraronsa. Allah kuma ya bayyana cewa yawancin bokaye maƙaryata ne, ko da kuwa za su faɗi gaskiya ɗaya to za su gauraya ta da ƙarya ɗari. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan Allah ya zartar da wani al’amari a sama sai mala’iku su buga fukafukansu domin nuna ƙasƙantar da kai ga maganar Allah, sai wani ƙara ya fita kamar an buga sarƙa a kan falalen dutse, har sai an yaye tsoro daga zukatansu sai su ce: “Me Ubangijinku ya ce?” Sai su amsa wa mai wannan tambayar da cewa: “Gaskiya ya faɗa, shi kuma Maɗaukaki ne Mai girma.” Sai masu satar magana su saci wannan maganar. Su kuwa waɗannan sheɗanun sukan hau junansu ne, wasu kan wasu, sai na sama ya kasa kunne ya sato maganar sai ya jefa ta ga na ƙasa da shi, shi ma kuma sai ya jefa wa na ƙasa da shi, haka har ta zo ga matsafi ko boka. Tana yiwuwa tauraro mai wuta ya same shi kafin ya kai ta ga na ƙasa da shi, yana kuma yiwuwa ya jefa maganar kafin tauraron ya cim masa. Sai boka ya gauraya wannan gaskiyar ɗaya da ƙarya ɗari, sai a riƙa cewa, ba a rana kaza ya taɓa faɗar kaza da kaza ba (watau wannan abu kuma ya faru)? Sai a gaskata shi a dalilin wannan kalmar da aka jiyo masa daga sama.” [Bukhari #4800]. Sannan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da martani ga masu kiran Annabi (ﷺ) da mawaƙi har suna iƙirarin cewa abin da ya zo da shi waƙa ce. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mawaƙa, ɓatattu ne suke bin su waɗanda suka kauce wa gaskiya, su ne suke ruwaito waƙoƙinsu ƙarya da gaskiya, Allah ya bayyana irin yadda mawaƙa suke kutsawa cikin kowanne kwazazzabo na waƙe-waƙe, wani lokaci ta hanyar yabo, wani lokaci kuwa ta hanyar zambo, wani lokaci kuma ta hanyar alfahari, wani lokaci kuma ta hanyar habaici, su faɗi ƙarya da gaskiya. Allah ya siffanta su da cewa suna faɗin abin da ba sa aikatawa, su ingiza mutane su yi kyauta su kuma ba sa yi, su kuma nuna a guji rowa su kuma ita suka kama; su ce a yi gaskiya su kuma suna faɗar ƙarya. Amma kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi togaciya ta wasu mawaƙan da suka siffantu da siffofi huɗu: Masu imani da Allah; masu aiki nigari; masu ambaton Allah da yawa; da kuma waɗanda suka yi sakayya ga maƙiya Allah bayan sun zalunce su. Waɗannan mawaƙa su ne irin su Hassan ɗan Sabit (Allah ya kara masa yarda) da Abdullahi ɗan Rawaha (Allah ya kara masa yarda) da Ka’abu ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda). Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗanda suka yi zalunci ta hanyar shirka da saɓon Allah da cutar da jama’a, da sannu za su san irin makomarsu a ranar lahira, ranar da Allah zai yi wa kowa hisabi a kan aikinsa mai kyau da marar kyau.