النمل

An-Naml

The Ant · Surah 27 · Ayahs: 93 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. طسٓۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡقُرۡءَانِ وَكِتَابٖ مُّبِينٍ

    Open ayah 27:1

    ƊA SIN. Waɗannan ayoyin Alƙur’ani ne kuma Littafi mabayyani.

  2. هُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 27:2

    (Kuma) shiriya da albishir ne ga muminai.

  3. ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ

    Open ayah 27:3

    Waɗanda suke tsai da salla, suke kuma ba da zakka suna masu sakankancewa da ranar lahira. Surar ta buɗe da wasu haruffa waɗanda muka yi bayanin irinsu a baya. (Dubi Suratul Baƙara , aya ta 1). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan ayoyi ne da ya saukar na Alƙur’ani wanda shi kuma littafi ne bayyananne babu wata rikitarwa a cikinsa. Duk wanda ya tsaya ya karance shi cikin tsanaki, to zai fahimci lallai daga Allah yake. Sai ya bayyana cewa masu shiryuwa da ayoyin Alƙur’ani su ne muminai waɗanda suka yi imani da Allah. A gare su ayoyin Alƙur’ani shiriya ne da albishir da samun sakamakon Ubangijinsu Allah, watau gidan Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasu muhimman siffofi na waɗannan muminan guda uku. <b>Ta ɗaya </b>, tsayar da salla, watau yin ta kamar yadda aka yi umarni a yi ta, da kuma kiyaye lokutanta da sharuɗɗanta. <b>Ta biyu </b>, bayar da dukiya sadaka ga mabuƙata domin tallafa musu da tsarkake dukiyar. <b>Ta uku </b>, sakankancewa da zuwan ranar lahira, wanda zai haifar da kyawawan ayyuka da guje wa munanansu.

  4. إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ زَيَّنَّا لَهُمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَهُمۡ يَعۡمَهُونَ

    Open ayah 27:4

    Lalle waɗanda ba sa imani da ranar lahira Mun ƙawata musu ayyukansu, don haka suke ɗimuwa.

  5. أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَهُمۡ سُوٓءُ ٱلۡعَذَابِ وَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ هُمُ ٱلۡأَخۡسَرُونَ

    Open ayah 27:5

    Waɗannan su ne waɗanda suke da mummunar azaba, kuma su ne suka fi hasara a lahira. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda ba su yi imani da ranar lahira ba, da cewa shi ne ya ƙawata musu miyagun ayyukansu har suka riƙa ganin su kyawawa, sakamakon ƙaryata shi da suka yi da ƙaryata manzanninsa, don haka suka doge a kan aikata munanan ayyuka, suka ci gaba da zama cikin ɗimuwa da kasa gane gaskiya. Ya bayyana cewa mutane masu irin waɗannan siffofi za su gamu da mummunar azaba a nan duniya ta hanyar karkashe su a wurin yaƙi, ko kama su a matsayin fursunonin yaƙi, a lahira kuma su ne suka fi kowa hasara, domin za su yi hasarar kawunansu da iyalansu, su kuma shiga wutar Jahannama su dawwama a cikinta har abada.

  6. وَإِنَّكَ لَتُلَقَّى ٱلۡقُرۡءَانَ مِن لَّدُنۡ حَكِيمٍ عَلِيمٍ

    Open ayah 27:6

    Lalle kuma kai tabbas ana yi maka wahayin Alƙur’ani ne daga wajen (Allah) Mai hikima, Masani.

  7. إِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِأَهۡلِهِۦٓ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا سَـَٔاتِيكُم مِّنۡهَا بِخَبَرٍ أَوۡ ءَاتِيكُم بِشِهَابٖ قَبَسٖ لَّعَلَّكُمۡ تَصۡطَلُونَ

    Open ayah 27:7

    Ka tuna lokacin da Musa ya ce da iyalinsa: “Lalle ni na hango wata wuta, to (zan je) in zo muku da labari, ko kuma in zo muku da ɗosanen garwashi don ku ji ɗumi.”

  8. فَلَمَّا جَآءَهَا نُودِيَ أَنۢ بُورِكَ مَن فِي ٱلنَّارِ وَمَنۡ حَوۡلَهَا وَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 27:8

    To lokacin da ya zo mata (wutar) sai aka kira shi cewa, an tsarkake wanda yake cikin wutar da waɗanda suke daura da ita (wato mala’iku), kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

  9. يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّهُۥٓ أَنَا ٱللَّهُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 27:9

    Ya Musa, lalle lamarin dai, Ni ne Allah Mabuwayi, Mai hikima.

  10. وَأَلۡقِ عَصَاكَۚ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهۡتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنّٞ وَلَّىٰ مُدۡبِرٗا وَلَمۡ يُعَقِّبۡۚ يَٰمُوسَىٰ لَا تَخَفۡ إِنِّي لَا يَخَافُ لَدَيَّ ٱلۡمُرۡسَلُونَ 

    Open ayah 27:10

    Kuma ka jefar da sandarka. To lokacin da ya gan ta tana jujjuyawa kamar macijiya, sai ya juya da baya a guje bai dawo ba. (Allah ya ce): Ya Musa, kada ka ji tsoro, lalle Ni manzanni ba sa jin tsoro a wurina.

  11. إِلَّا مَن ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسۡنَۢا بَعۡدَ سُوٓءٖ فَإِنِّي غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 27:11

    Sai dai wanda ya zalunci (kansa), sannan ya musanya kyakkyawa bayan mummuna, to lalle Ni Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

  12. وَأَدۡخِلۡ يَدَكَ فِي جَيۡبِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٖۖ فِي تِسۡعِ ءَايَٰتٍ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَقَوۡمِهِۦٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ

    Open ayah 27:12

    Kuma ka saka hannunka cikin wuyan rigarka, zai fito fari fat ba na cuta ba; (wannan aya ce) daga cikin ayoyi tara zuwa ga Fir’auna da mutanensa. Lalle su sun kasance mutane ne fasiƙai.

  13. فَلَمَّا جَآءَتۡهُمۡ ءَايَٰتُنَا مُبۡصِرَةٗ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 27:13

    To lokacin da ayoyinmu waɗanda suke a sarari suka zo musu, sai suka ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.”

  14. وَجَحَدُواْ بِهَا وَٱسۡتَيۡقَنَتۡهَآ أَنفُسُهُمۡ ظُلۡمٗا وَعُلُوّٗاۚ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

    Open ayah 27:14

    Suka kuma musanta su don zalunci da girman kai, alhali kuwa zukatansu sun sakankance da su. To sai ka duba ka ga yadda ƙarshen maɓarnata ya kasance. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fara yin magana da Manzonsa inda ya tabbatar masa da cewa lalle wannan Alƙur’ani ne wanda aka saukar masa shi daga Allah mai hikima wajen gudanar da al’amuran bayinsa, kuma mai cikakken sani game da halayen bayinsa da abin da suke ciki, don haka duk hukuncinsa adalci ne, duk wani labarinsa kuma gaskiya ne. Sai Allah ya umarci Manzonsa da ya gaya wa mutanensa labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya baro garin Madyana tare da iyalansa. Yana cikin tafiya tsakiyar saharar Sina’a sai ya ɓace hanya cikin dare mai duhu ga kuma tsananin sanyi, inda ya hango wata wuta tana ci daga nesa, kusa da wani dutsi da ake kiran sa Dutsen Ɗuri. Sai ya umarci iyalansa da su sami wuri su zauna, shi zai tafi wajen wannan wutar don ya zo musu da labarin hanyar da za su bi ta kai su Masar daga masu hura wutar, ko kuma ya zo musu da wani garwashin wuta domin su ji ɗumi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya isa wurin wannan wutar sai kawai ya ji ana kiran sa cewa, an yi albarka da tsarkakewa ga wanda yake cikin wannan wutar da waɗanda suke gefenta, watau mala’iku. Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu gaba ɗaya. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya tsaya a cikinmu ya ambata mana wasu kalmomi biyar ya ce: “Lalle Allah mai girma da buwaya ba ya barci, kuma ba ya dacewa a gare shi ya yi barci; yana ƙasa-ƙasa da mizanin adalci yana kuma yin sama da shi; ana kuma ɗaukaka masa ayyukan dare kafin na rana da ayyukan rana kafin na dare; shamakinsa haske ne – a ruwayar Abubakar ya ce wuta ce – da a ce zai yaye shi da hasken fuskarsa ya ƙone dukkan abin da ganinsa ya tuƙe gare shi na halittarsa.” [Muslim #179]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a nan ne ya kira Annabi Musa da sunansa, ya tabbatar masa da cewa shi ne Allah Gagara-badau Mabuwayi wanda ya fi ƙarfin kowa, kuma mai hikima cikin dukkan lamuransa na halitta da ƙaddara da shari’a. Sai ya umarce shi da ya jefar da sandar da take hannunsa, nan take Annabi Musa ya jefar da ita, sai kuwa ta zama wata ƙatuwar macijiya tana jujjuyawa tana tafiya da sauri. Sai tsoro ya kama Annabi Musa ya juya a guje bai dawo ba, sai Allah ya umarce shi da ya dawo ya kuma daina jin wani tsoro, domin shi Manzonsa ne kuma a gabansa yake, manzanni kuwa a gaban Allah ba sa jin tsoron komai. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi albishir ga duk wanda ya zalunci kansa ta hanyar aikata mummunan aiki sannan ya tuba ya nemi gafarar Allah, to Allah yana tabbatar masa da cewa shi mai gafara ne gare shi mai jin ƙan sa ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya shigar da hannunsa a cikin rigarsa, ya haɗa shi da kwiɓin jikinsa, to hannun zai fito fari yana haske kamar fitila ba kuma tare da wata cuta ba kamar albaras. Wannan yana daga cikin ayoyi guda tara masu tabbatar da gaskiyar manzancinsa, waɗanda suka haɗa da shekarun fari da tawayar kayan amfanin gona da ruwan Ɗufana da fari da ƙwarƙwata da kwaɗi da jini. Duk waɗannan mu’ujizoji ne ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa Fir’auna da mutanensa, saboda sun tabbata mutane ne fasiƙai waɗanda suka kauce wa ɗa’a ga Allah suka zaɓi hanyar kafirci. Bayan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya je wa Fir’auna da jama’arsa da waɗannan hujjoji bayyanannu waɗanda suka gani da idanuwansa, sai kawai suka zarge shi da cewa ya zo musu da sihiri ne a fili. Allah ya tabbatar da cewa Fir’auna da mutanensa jayayya kawai suke yi da ayoyin Allah bayyanannu, suna nuna rashin yardarsu da su bayan kuma sun tabbatar da cewa daga Allah waɗannan ayoyin suke, saboda zaluncinsu da girman kansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya duba ya ga yadda ƙarshen maɓarnata ya zama, watau yadda Allah ya hallakar da su baki ɗaya kamar ma ba a taɓa yin su a doron ƙasa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nutsar da Fir’auna da rundunarsa cikin ruwa suka hallaka, ya kuma tserar da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Banu Isra’ila daga mummunan makircinsu.

  15. وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ عِلۡمٗاۖ وَقَالَا ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي فَضَّلَنَا عَلَىٰ كَثِيرٖ مِّنۡ عِبَادِهِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 27:15

    Haƙiƙa kuma Mun bai wa Dawuda da Sulaimana ilimi; suka kuma ce: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya fifita mu a kan masu yawa daga bayinsa muminai.”

  16. وَوَرِثَ سُلَيۡمَٰنُ دَاوُۥدَۖ وَقَالَ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ عُلِّمۡنَا مَنطِقَ ٱلطَّيۡرِ وَأُوتِينَا مِن كُلِّ شَيۡءٍۖ إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡفَضۡلُ ٱلۡمُبِينُ

    Open ayah 27:16

    Sulaimanu kuma ya gaji Dawuda; ya kuma ce: “Ya ku waɗannan mutane, (wato Yahudawa), an sanar da mu zancen tsuntsaye, kuma an ba mu daga kowane abu (na tafiyar da mulki); lalle wannan tabbas ita ce bayyananniyar falala.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayar da wani ɓangare na labarin Annabi Dawud da Annabi Sulaiman ((), biyu daga cikin annabawan Banu Isra’ila. Allah ya tabbatar da cewa ya ba su wani ilimi mai girma, daga ciki har da ilimin fahimtar maganar tsuntsaye, kamar yadda ya koyar da Annabi Dawud sana’ar ƙira, sai suka bayyana godiyarsu ga Allah wanda ya fifita su a kan muminai da dama, ya kuma ba su matsayi na annabci, ya hore wa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sarrafa aljannu da shaiɗanu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya gaji mahaifinsa Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), gadon ilimi da annabta da Allah ya ba shi, kamar yadda kuma ya gaji mulkinsa wanda Allah ya faɗaɗa masa shi, watau ya ninka masa ƙarfinsa, saboda haka ne Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana ni’imomin da Allah ya yi musu ga mutane da cewa Allah ya hore musu hanyoyin fahimtar maganar tsuntsaye, ya kuma hore musu dukkan abin da ake bai wa annabawa da sarakuna, sai kuma ya tabbatar musu da cewa wannan ita ce falala ta zahiri da Allah ya yi musu.

  17. وَحُشِرَ لِسُلَيۡمَٰنَ جُنُودُهُۥ مِنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ وَٱلطَّيۡرِ فَهُمۡ يُوزَعُونَ

    Open ayah 27:17

    Aka kuma tattara wa Sulaimanu rundunoninsa na aljannu da mutane da kuma tsuntsaye, sai aka riƙa turo su sahu-sahu.

  18. حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَوۡاْ عَلَىٰ وَادِ ٱلنَّمۡلِ قَالَتۡ نَمۡلَةٞ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّمۡلُ ٱدۡخُلُواْ مَسَٰكِنَكُمۡ لَا يَحۡطِمَنَّكُمۡ سُلَيۡمَٰنُ وَجُنُودُهُۥ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

    Open ayah 27:18

    Har dai zuwa lokacin da suka iso kwarin tururuwa, sai wata tururuwa ta ce: “Ya ku waɗannan taron tururuwa, ku shige gidajenku kada Sulaimanu da rundunoninsa su tattake ku alhali kuwa ba da saninsu ba.”

  19. فَتَبَسَّمَ ضَاحِكٗا مِّن قَوۡلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَدۡخِلۡنِي بِرَحۡمَتِكَ فِي عِبَادِكَ ٱلصَّٰلِحِينَ

    Open ayah 27:19

    Sai ya yi murmushi yana mai dariya saboda maganarta, ya kuma ce: “Ubangijina Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imar da Ka yi min ni da mahaifana, da kuma yadda zan yi aiki na gari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka shigar da ni don rahamarka cikin bayinka na gari.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kaɗan daga cikin ni’imomin da ya yi wa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da cewa an tattaro masa da rundunoninsa daga aljannu da mutane da tsuntsaye, sai aka riƙa turo su cikin wani tsari mai ban sha’awa. Suka yi ta tafiya cikin tsari sahu-sahu har sai da suka iso kwarin tururuwa, wani wuri ne a ƙasar Sham, sai wata tururuwa ta kira sauran ‘yan’uwanta taron tururuwa ta ba su umarni da su koma cikin gidajensu don kada Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da rundunar sojojinsa su tattake su su mutu ba tare da sun sani ba. Yayin da Annabi Sulaimanu ya ji maganar wannan tururuwa sai ya yi murmushi yana dariya, saboda farin cikin jin wannan magana tata, sannan ya roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kimsa masa gode wa ni’imar da ya yi masa da ya ba shi ikon fahimtar maganganun tsuntsaye da ƙwari da kuma ni’imar da ya yi wa iyayensa. Ya kuma roƙe shi ya ba shi ikon yin aiki na ƙwarai wanda zai yarda da shi, watau wanda ya dace da umarnin Allah tare da yin ikhlasi a cikinsa, kuma ya roƙi shi ya sanya shi cikin jimillar bayinsa na gari da tsantsar rahamarsa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wata tururuwa ta ciji wani daga cikin annabawa sai ya ba da umarni a ƙone alƙaryar tururuwar gaba ɗaya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa wahayi cewa: “Don kawai wata tururuwa ta cije ka sai ka hallakar da al’umma guda wadda take yi wa Allah tasbihi?” [Bukhari #3019 da Muslim #224].

  20. وَتَفَقَّدَ ٱلطَّيۡرَ فَقَالَ مَا لِيَ لَآ أَرَى ٱلۡهُدۡهُدَ أَمۡ كَانَ مِنَ ٱلۡغَآئِبِينَ

    Open ayah 27:20

    Kuma ya bincika tsuntsaye, sai ya ce: “Me ya sa ba na ganin Alhudahuda, ko kuwa yana cikin waɗanda ba sa nan ne?

  21. لَأُعَذِّبَنَّهُۥ عَذَابٗا شَدِيدًا أَوۡ لَأَاْذۡبَحَنَّهُۥٓ أَوۡ لَيَأۡتِيَنِّي بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 27:21

    “Na rantse zan yi masa azaba mai tsanani, ko kuma tabbas zan yanka shi, ko kuma lalle ya zo min da hujja bayyananna.”

  22. فَمَكَثَ غَيۡرَ بَعِيدٖ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمۡ تُحِطۡ بِهِۦ وَجِئۡتُكَ مِن سَبَإِۭ بِنَبَإٖ يَقِينٍ

    Open ayah 27:22

    Sai ko ba da daɗewa ba ya dawo, sannan (bayan an tambaye shi) ya ce: “Ni fa na gano abin da ba ka sani ba, na kuma zo maka da tabbataccen labari daga birnin Saba’u.

  23. إِنِّي وَجَدتُّ ٱمۡرَأَةٗ تَمۡلِكُهُمۡ وَأُوتِيَتۡ مِن كُلِّ شَيۡءٖ وَلَهَا عَرۡشٌ عَظِيمٞ

    Open ayah 27:23

    “(Shi ne ) lalle na sami wata mace tana mulkar su, an kuma ba ta daga kowane abu (na mulki), tana kuma da gadon sarauta mai girma.

  24. وَجَدتُّهَا وَقَوۡمَهَا يَسۡجُدُونَ لِلشَّمۡسِ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَصَدَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّبِيلِ فَهُمۡ لَا يَهۡتَدُونَ

    Open ayah 27:24

    “Na same ta ita da mutanenta suna sujjada ga rana ba Allah ba. Shaiɗan kuma ya ƙawata musu ayyukansu, sai ya kange su daga bin hanya ta gaskiya, don haka su ba sa kan shiriya.

  25. أَلَّاۤ يَسۡجُدُواْۤ لِلَّهِ ٱلَّذِي يُخۡرِجُ ٱلۡخَبۡءَ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَيَعۡلَمُ مَا تُخۡفُونَ وَمَا تُعۡلِنُونَ

    Open ayah 27:25

    “Don kada su yi sujjada ga Allah wanda Yake fito da abin da yake ɓoye a cikin sammai da ƙasa, kuma Yake sane da abin da kuke ɓoyewa da abin da kuke bayyanawa.

  26. ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ۩

    Open ayah 27:26

    “(Shi ne) Allah Wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, Ubangijin Al’arshi mai girma.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wata rana Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana bibiyar rundunoninsa na aljannu da mutane da tsuntsaye, lokacin da ya zo kan tsuntsaye sai bai ga Alhudahuda a cikinsu ba. Sai ya yi tambaya cewa, me ya sa bai ga Alhudahuda ba? Watau shi ne bai gan shi ba yana cikin ribibi ko kuma dai ba ya wurin ne? Sai aka sanar da shi cewa ba ya nan. Sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi barazanar cewa lalle idan ya dawo sai ya yi masa azaba mai tsanani, ko ya yanka shi sakamakon rashin ganin sa da ya yi, ko kuma ya zo masa da wata bayyananniyar hujja karɓaɓɓiya wadda za ta nuna uzurinsa a fili. Ba a jima ba kuma sai ga Alhudahuda ya dawo, ya bayyana wa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) uzurinsa na rashin halarta a kan kari, da cewa ya gano masa wani abu da shi bai san da shi ba, domin ya zo masa da wani sahihin labari wanda babu kokwanto a cikinsa daga birnin Saba’u na ƙasar Yaman. Watau ya samu mutanen wannan birnin wata mata ce take mulkinsu, kuma an ba ta duk wani abu da mulkinta yake buƙata na ƙarfin mayaƙa da tattalin arziki, sannan kuma tana da wani gadon sarauta mai girman gaske wanda takan hau shi don gudanar da sha’anin mulkinta. Alhudahuda ya ci gaba da bayyana wa Annabi Sulaimanu abin da ya gano a birnin Saba’u, da cewa ya sami wannan mata mai mulki da mutanenta suna bautar rana ne ba Allah ba, kuma Shaiɗan ne ya ƙawata musu ayyukan shirka da saɓon Allah da suke yi, ya kuma hana su bin hanyar gaskiya, don haka suka kasa shiryuwa su bauta wa Allah shi kaɗai wanda yake fito musu da ruwan da yake ɓoye a sama, da tsirran da suke cikin ƙasa, kuma yake sane da ayyukansu da suke ɓoyewa da waɗanda suke bayyanawa. Shi ne Allah wanda babu abin bauta da gaskiya sai shi Ubangijin Al’arshi mai girma.

  27. ۞قَالَ سَنَنظُرُ أَصَدَقۡتَ أَمۡ كُنتَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

    Open ayah 27:27

    Sai (Sulaimana) ya ce: “To za mu duba ko ka yi gaskiya ko kuwa ka zama cikin maƙaryata.

  28. ٱذۡهَب بِّكِتَٰبِي هَٰذَا فَأَلۡقِهۡ إِلَيۡهِمۡ ثُمَّ تَوَلَّ عَنۡهُمۡ فَٱنظُرۡ مَاذَا يَرۡجِعُونَ

    Open ayah 27:28

    “Ka tafi da wannan wasiƙar tawa sai ka jefa musu ita sannan ka ja da baya kaɗan, sai ka ga da me za su mayar da martani?”

  29. قَالَتۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ إِنِّيٓ أُلۡقِيَ إِلَيَّ كِتَٰبٞ كَرِيمٌ

    Open ayah 27:29

    Sai ta ce: “Ya ku manyan fada, lalle an jefo min wata wasiƙa mai daraja.

  30. إِنَّهُۥ مِن سُلَيۡمَٰنَ وَإِنَّهُۥ بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ 

    Open ayah 27:30

    “(Mai cewa): Lalle wannan (wasiƙar) daga Sulaimana ne kuma lalle ina farawa da Bismillahi Arrahamani Arrahim .

  31. أَلَّا تَعۡلُواْ عَلَيَّ وَأۡتُونِي مُسۡلِمِينَ

    Open ayah 27:31

    “Kada ku yi min girman kai, ku zo min kuna masu miƙa wuya!” A waɗannan ayoyi, bayan Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ji duk bayanan Alhudahuda, sai ya bayyana masa cewa za su duba su yi bincike don tabbatar da gaskiyar labarinsa ko ƙaryarsa, watau kafin su san irin matakin da za su ɗauka a kai. Daga nan sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fara ɗaukar matakin bincike, ya rubuta taƙaitacciyar wasiƙa ya ba Alhudahuda don ya isar da ita ga Sarauniyar Saba’u, ya umarce shi da ya je garin ya jefa musu wannan wasiƙar, sai ya ɗan ja da baya kaɗan ya tsaya inda zai ji abin da Sarauniya da fadawanta za su tattauna a kansa da kuma irin martanin da za su dawo da shi. Bayan Alhudahuda ya aikata abin da aka umarce shi da shi, wasiƙa ta je hannun Sarauniyar Saba’u, ta kuma karanta ta ga abin da yake ciki, sai ta tara manyan gari a fadarta ta faɗa musu cewa an fa jefo mata wasiƙa mai girma. Abin da ta ƙunsa kuwa shi ne, “Wannan wasiƙa daga Sulaimanu take” kuma an buɗe ta da Bismilla, watau “Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai”. Sannan wasiƙar ta ce: “Lalle kada ku yi min girman kai, ku zo min kuna masu miƙa wuya”. Watau dai yana sanar da su cewa kada su bijire masa, su zo suna masu miƙa wuya ga abin da yake kiran su a kai na kaɗaita Allah da barin shirkar da suke kai ta bautar rana.

  32. قَالَتۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ أَفۡتُونِي فِيٓ أَمۡرِي مَا كُنتُ قَاطِعَةً أَمۡرًا حَتَّىٰ تَشۡهَدُونِ

    Open ayah 27:32

    (Sai Sarauniyar) ta ce: “Ya ku manyan fada, ku ba ni shawara game da al’amarina, (domin) ni ba zan yanke (shawarar) wani al’amari ba sai kuna nan.”

  33. قَالُواْ نَحۡنُ أُوْلُواْ قُوَّةٖ وَأُوْلُواْ بَأۡسٖ شَدِيدٖ وَٱلۡأَمۡرُ إِلَيۡكِ فَٱنظُرِي مَاذَا تَأۡمُرِينَ

    Open ayah 27:33

    Sai suka ce: “Mu dai ƙarfafa ne kuma mayaƙa sosai, al’amarin kuwa yana hannunki, sai ki duba abin da za ki yi umarni.”

  34. قَالَتۡ إِنَّ ٱلۡمُلُوكَ إِذَا دَخَلُواْ قَرۡيَةً أَفۡسَدُوهَا وَجَعَلُوٓاْ أَعِزَّةَ أَهۡلِهَآ أَذِلَّةٗۚ وَكَذَٰلِكَ يَفۡعَلُونَ

    Open ayah 27:34

    Sai ta ce: “Lalle sarakuna idan suka shigo wata alƙarya sai su yi kaca-kaca da ita, kuma su mayar da manyanta ƙasƙantattu; kuma haka suke aikatawa.

  35. وَإِنِّي مُرۡسِلَةٌ إِلَيۡهِم بِهَدِيَّةٖ فَنَاظِرَةُۢ بِمَ يَرۡجِعُ ٱلۡمُرۡسَلُونَ

    Open ayah 27:35

    “Ni kam lalle zan aika musu ne da wata kyauta sannan in saurari abin da manzanni za su dawo da shi.”

  36. فَلَمَّا جَآءَ سُلَيۡمَٰنَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَالٖ فَمَآ ءَاتَىٰنِۦَ ٱللَّهُ خَيۡرٞ مِّمَّآ ءَاتَىٰكُمۚ بَلۡ أَنتُم بِهَدِيَّتِكُمۡ تَفۡرَحُونَ

    Open ayah 27:36

    To lokacin da (manzo) ya zo wa Sulaimanu sai ya ce: “Yanzu kwa ƙare ni da wata dukiya, alhali abin da Allah Ya ba ni ya fi wanda Ya ba ku? A’a, ku ne kuke farin ciki da kyautarku.

  37. ٱرۡجِعۡ إِلَيۡهِمۡ فَلَنَأۡتِيَنَّهُم بِجُنُودٖ لَّا قِبَلَ لَهُم بِهَا وَلَنُخۡرِجَنَّهُم مِّنۡهَآ أَذِلَّةٗ وَهُمۡ صَٰغِرُونَ

    Open ayah 27:37

    “Koma musu (da kyautarsu) sannan (ka gaya musu) lalle za mu zo musu da runduna wadda ba za su iya tunkarar ta ba, kuma lalle za mu fitar da su daga cikinta (alƙaryar) a wulaƙance suna ƙasƙantattu!” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Sarauniyar birnin Saba’u ta tara manyan gari ta nemi shawararsu, ta kuma tabbatar musu da cewa ba za ta yanke komai ba a kan wannan al’amari har sai ta saurari ra’ayinsu. Sai suka mayar mata da jawabi da cewa, su mutane ne ƙarfafa kuma jaruman mayaƙa, saboda haka ko da ta bijire wa Annabi Sulaimanu ta ƙi yarda da shi, to su a shirye suke su fafata yaƙi a kan haka, amma dai sai suka mayar da magana gare ta domin sun yarda da cewa ita mace ce mai zurfin hankali, don haka ba za ta yanke abin da bai dace ba, kuma a shirye suke su zartar da duk abin da ta umarce su. Sai Sarauniya ta bayyana musu illar yaƙi da sarakuna masu ƙarfi da cewa, idan har suka yi nasarar kama wata alƙarya, to fa sai sun yi babbar ɓarna a cikinta, sun yi kashe-kashe sun wawashe dukiyar al’umma, sun kama manyan garin sun mayar da su wulaƙantattu sun bautar da su. Ta kuma tabbatar musu cewa koyaushe haka halin sarakunan yake. A ƙarshe dai ta zartar da nata tunani da cewa, za ta fito musu ta hanyar lalama, ta aika masa da kyauta ta alfarma, don ta ga ko wannan zai canza masa ra’ayinsa ko kuma a’a. Sai ta aika wasu manyan fadawanta da kyauta zuwa ga Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Yayin da suka isa gare shi suka ƙaddamar masa da kyautar Sarauniya sai ya ƙi karɓar kyautarsu, ya kuma mayar musu da martani mai zafi da cewa, suna zato za su ƙare shi ne da wata dukiya don su canza masa tunaninsa ya fasa aikata abin da ya yi niyya? Don haka ya tabbatar musu da cewa abin da Allah ya ba shi ya zarce abin da suke taƙama da shi, domin shi Allah ya ba shi ƙasaitaccen mulkin da bai taɓa ba wa wani mahaluƙi irinsa ba, bugu da ƙari kuma ga shi Annabin Allah. Sai ya soke su da cewa su ne wannan kyautar za ta raɗa su da ƙasa har su yi ta farin ciki da ita, saboda son duniya da ke zukatansu da kuma ƙarancin abin da suka mallaka, idan an kwatanta shi da abin da shi ya mallaka. Daga nan ne fa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarci wannan manzon na Sarauniya da ‘yan rakiyarsa su koma su mayar mata da kyautarta sannan su isar mata da saƙonsa na cewa, tabbas ba makawa zai zo musu da rundunarsa da ba za su iya tunkarar ta ba, kuma lalle sai ya fitar da su daga garin Saba’u cikin wulaƙanci da ƙasƙanci matuƙar ba su sallama kansu gare shi ba.

  38. قَالَ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ أَيُّكُمۡ يَأۡتِينِي بِعَرۡشِهَا قَبۡلَ أَن يَأۡتُونِي مُسۡلِمِينَ

    Open ayah 27:38

    Sai (Sulaimanu) ya ce: “Ya ku manyan fada, wane ne daga cikinku zai zo min da gadon mulkinta tun kafin su zo min suna masu miƙa wuya?”

  39. قَالَ عِفۡرِيتٞ مِّنَ ٱلۡجِنِّ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن تَقُومَ مِن مَّقَامِكَۖ وَإِنِّي عَلَيۡهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٞ

    Open ayah 27:39

    Sai wani ifritu daga cikin aljannu ya ce: “Ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga majalisarka; lalle ni kuma mai ƙarfi ne amintacce game da (kawo) shi.”

  40. قَالَ ٱلَّذِي عِندَهُۥ عِلۡمٞ مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن يَرۡتَدَّ إِلَيۡكَ طَرۡفُكَۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسۡتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَٰذَا مِن فَضۡلِ رَبِّي لِيَبۡلُوَنِيٓ ءَأَشۡكُرُ أَمۡ أَكۡفُرُۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيّٞ كَرِيمٞ 

    Open ayah 27:40

    Sai wani (mutum) wanda yake da ilimin Littafi (na Attaura) ya ce: “Ni zan kawo maka shi kafin ka ƙifta idonka!” To lokacin da (Sulaimanu) ya gan shi ga shi nan a gabansa sai ya ce: “Wannan yana daga falalar Ubangijina don Ya jarraba ni (Ya gani) shin zan gode ne ko zan butulce; to duk wanda ya gode kansa ya yi wa; wanda kuwa ya butulce, to lalle Ubangijina Mawadaci ne, Mai karamci.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan manzannin Sarauniya sun koma domin isar da saƙon Annabi Sulaimanu zuwa gare ta sai ya tabbatar wa fadawansa cewa Sarauniya da mutanenta za su miƙa wuya gare shi, amma duk da haka sai ya tambayi fadawan da suke gabansa na mutane da aljannu cewa wane ne a cikinsu zai iya kawo masa gadon sarautarta tun kafin su zo su sallama kansu? Da jin wannan tambaya sai wani ƙaƙƙarfan aljani ya bayyana cewa shi zai iya kawo wa Annabi Sulaimanu wannan gadon kafin ya tashi daga majalisarsa. Ya kuma tabbatar masa da cewa shi ƙaƙƙarfa ne don haka ɗaukar wannan gado ba zai gagare shi ba, sannan kuma shi mai amana ne, ba zai taɓa komai daga jikin wannan gado ba. Sai kuma wani salihin malami mai ilimin littafi da ke zaune a gaban Annabi Sulaimanu ya bayyana masa cewa shi zai iya kawo masa gadon kafin ma ya ƙifta idonsa. Faɗar wannan ke da wuya sai kawai Annabi Sulaimanu ya ga gado gingirin a gabansa. Sai ya ce tabbas wannan lamari ba komai ba ne sai falalar Ubangijinsa a gare shi, kuma ya yi masa haka ne don ya jarrabe shi ya ga shin zai gode wa Allah kan ɗimbin ni’imomin da ya yi masa ko zai butulce? Sannan ya bayyana cewa duk wanda ya gode wa Allah kansa ya yi wa, domin shi ne zai ga amfanin godiyar. Hakanan duk wanda ya butulce to don kansa, domin shi Allah mawadaci ne ba shi da buƙatar komai a wurin kowa, kuma mai karamci ne don haka ne ma yake ƙara wa bayi masu yi masa godiya a kullum.

  41. قَالَ نَكِّرُواْ لَهَا عَرۡشَهَا نَنظُرۡ أَتَهۡتَدِيٓ أَمۡ تَكُونُ مِنَ ٱلَّذِينَ لَا يَهۡتَدُونَ

    Open ayah 27:41

    (Sai Sulaimanu) ya ce: “Ku sauya kamannin gadon nata mu gani za ta gane (shi) ko kuwa za ta zamanto cikin waɗanda ba sa ganewa?”

  42. فَلَمَّا جَآءَتۡ قِيلَ أَهَٰكَذَا عَرۡشُكِۖ قَالَتۡ كَأَنَّهُۥ هُوَۚ وَأُوتِينَا ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهَا وَكُنَّا مُسۡلِمِينَ

    Open ayah 27:42

    To lokacin da ta zo, sai aka ce (da ita): “Shin haka kuwa gadonki yake?” Sai ta ce: “Sai ka ce shi.” (Sulaimanu ya ce): “An kuwa ba mu ilimi tun gabaninta, kuma mun kasance Musulmi.

  43. وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعۡبُدُ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ إِنَّهَا كَانَتۡ مِن قَوۡمٖ كَٰفِرِينَ

    Open ayah 27:43

    “Kuma abin da ta kasance tana bauta wa ba Allah ba, shi ya hana ta (yin imani); lalle ita ta kasance cikin mutane kafurai.”

  44. قِيلَ لَهَا ٱدۡخُلِي ٱلصَّرۡحَۖ فَلَمَّا رَأَتۡهُ حَسِبَتۡهُ لُجَّةٗ وَكَشَفَتۡ عَن سَاقَيۡهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ صَرۡحٞ مُّمَرَّدٞ مِّن قَوَارِيرَۗ قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي وَأَسۡلَمۡتُ مَعَ سُلَيۡمَٰنَ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 27:44

    Aka ce da ita: “Ki shiga fadar;” to lokacin da ta gan ta sai ta zace ta ruwa ne mai zurfi, sai kuwa ta yaye ƙwaurinta. Sai (Sulaimanu) ya ce: “Ai ita fada ce da aka gina da gogaggun kasaken ƙarau (ruwa yake gudana ta ƙarƙashinsu).” Ta ce: “Ya Ubangijina, haƙiƙa na zalunci kaina, na kuma miƙa wuya ga Allah Ubangijin talikai tare da Sulaimanu.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga gadon Sarauniya a gabansa, sai ya umarci masu gudanar da lamarin fada da cewa su sauya kamannin gadon ta hanyar ƙara masa wasu abubuwa da ba ya da shi ko rage masa wasu domin yana so ne ya auna kaifin basirarta ya ga cewa za ta gane nata ne ko ba za ta iya ganewa ba. Bayan isowar Sarauniya fadar Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai ta ga gadon sarauta a gabanta wanda ya yi kama da nata, to amma a iya saninta ta baro nata a ƙasarta, daga nan sai aka tambaye ta cewa shin gadonta kamar wannan yake? Sai ta amsa da cewa: “Kamar dai shi.” Da Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ga kaifin basirarta da zurfin hankalinta sai ya bayyana girman ni’imar da Allah ya yi masa wadda ta zarce irin abin da Allah ya ba ta na hankali da ganewa. Ya bayyana cewa Allah ya ba shi ilimi tun gabanin a ba ta wanda kuma ya fi nata, domin nasa ilimin annabta ne, sannan kuma ga shi Musulmi ne tun da farko, ita kuma kafira mai bautar rana ba Allah ba, bautar da ta hana ta ita da mutanenta su yi imani da Allah su bauta masa shi kaɗai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi niyyar ya nuna wa Sarauniya ƙasaitaccen mulkin da Allah ya ba shi, don haka ya kirawo ta don ya nuna mata fadarsa, aka yi mata iso ta shigo sai ta ga ai wani wuri ne kamar ruwa mai zurfi za ta shiga, sai kawai ta yaye ƙwaurinta don kada tufafinta su jiƙe da ruwa. Sai Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sanar da ita cewa wannan da take gani ba ruwa ne a kwance ba; fada ce da aka gina ta da gogaggun kasaken ƙarau waɗanda ruwa yake gudana ta ƙarƙashinsu, don haka ba sai ta yaye ƙwaurinta ba. To lokacin da ta ga abin da ta gani na mamaki da girman mulki da ƙasaitar iko, ta kuma fahimci cewa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba wai sarki ne ba kawai; annabin Allah ne, sai ta bayyana tubanta ga Allah ta kuma musulunta a hannun Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).

  45. وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ فَإِذَا هُمۡ فَرِيقَانِ يَخۡتَصِمُونَ

    Open ayah 27:45

    Haƙiƙa kuma Mun aiko wa Samudawa ɗan’uwansu Salihu da cewa: “Ku bauta wa Allah,” sai ga su sun rabu ƙungiyoyi biyu suna jayayya.

  46. قَالَ يَٰقَوۡمِ لِمَ تَسۡتَعۡجِلُونَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبۡلَ ٱلۡحَسَنَةِۖ لَوۡلَا تَسۡتَغۡفِرُونَ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

    Open ayah 27:46

    Ya ce: “Ya ku mutanena, don me kuke neman gaggautowar mummunan sakamako tun gabanin kyakkyawa? Don me ba za ku nemi gafarar Allah ba don a ji ƙan ku.”

  47. قَالُواْ ٱطَّيَّرۡنَا بِكَ وَبِمَن مَّعَكَۚ قَالَ طَٰٓئِرُكُمۡ عِندَ ٱللَّهِۖ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ تُفۡتَنُونَ

    Open ayah 27:47

    Sai suka ce: “Mu mun camfa ka kai da waɗanda suke tare da kai.” Sai ya ce: “Camfinku na ga Allah. A’a, ku dai mutane ne da ake jarraba ku.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo wani ɓangare na labarin Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yayin da ya aike shi zuwa ga ƙabilarsa Samudawa waɗanda suke bautar gumaka ba Allah ba. Ya umarce su da su bauta wa Allah shi kaɗai su bar bautar gumaka, sai ga shi sun kasu ƙungiya biyu; • Ƙungiya ta farko su ne waɗanda suka ba da gaskiya da Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka yarda su bauta wa Allah shi kaɗai. • Ƙungiya ta biyu su ne waɗanda suka ƙaryata Annabi Salihu suka kafirce wa Allah. Waɗannan kuma su ne suka fi yawa. Ƙungiyoyin biyu suka shiga jayayya da juna, kowa yana cewa shi ne a kan gaskiya. Annabi Salihu ya yi ta bin Samudawa da lalama tare da nuna musu haɗarin abin da suke kai na shirka da Allah wanda zai iya jawo musu hallaka kamar yadda aka hallakar da waɗanda suka gabace su kamar Adawa. To amma wannan bai sa sun saurare shi ba, sai ma tsaurin kansu ne ya ƙaru har suka fara nemansa da ya kawo musu azabar da yake ta tsoratar da su da ita idan har shi mai gaskiya ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da jan hankalin mutanensa da cewa bai dace su riƙa gaggauto wa kawunansu uƙubar Allah ba wadda idan har ta sauka ba za ta yi musu kyau ba, a maimakon su nemi rahamar Allah ta hanyar yin imani da aikata kyawawan ayyuka, su nemi gafarar Allah su tuba su bar abin da suke a kai na shirka da saɓon Allah, don Allah ya ji ƙan su ya yafe musu laifukansu na baya da suka yi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mutanen Annabi Salihu sun bijire wa wannan nasiha da wa’azi da ya yi musu har ma sai suka shiga zargin sa shi da waɗanda suka ba da gaskiya da shi suna camfa su da cewa su ne sanadiyyar faruwar wasu matsaloli na rayuwa da suke fuskanta. Sai Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya amsa musu da cewa duk wani camfi da za su yi a kan musibun da suke samun su Allah yana sane da haka, kuma wannan wata jarraba ce daga Allah saboda zunubansu da kafircinsu.

  48. وَكَانَ فِي ٱلۡمَدِينَةِ تِسۡعَةُ رَهۡطٖ يُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا يُصۡلِحُونَ

    Open ayah 27:48

    A cikin birnin kuma akwai wani gungu na mutum tara waɗanda suke ɓarna a bayan ƙasa kuma ba sa gyara.

  49. قَالُواْ تَقَاسَمُواْ بِٱللَّهِ لَنُبَيِّتَنَّهُۥ وَأَهۡلَهُۥ ثُمَّ لَنَقُولَنَّ لِوَلِيِّهِۦ مَا شَهِدۡنَا مَهۡلِكَ أَهۡلِهِۦ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ

    Open ayah 27:49

    Sai suka ce: “Mun rantse da Allah a junanmu cewa lalle za mu kashe shi cikin dare shi da iyalinsa, sannan za mu faɗa wa mai neman jininsa cewa, ba mu halarci wurin kashe iyalinsa ba, kuma lalle mu masu gaskiya ne.”

  50. وَمَكَرُواْ مَكۡرٗا وَمَكَرۡنَا مَكۡرٗا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ 

    Open ayah 27:50

    Kuma suka shirya makirci, Mu kuma Muka shirya rusa makircinsu alhali kuwa su ba su sani ba.

  51. فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ مَكۡرِهِمۡ أَنَّا دَمَّرۡنَٰهُمۡ وَقَوۡمَهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 27:51

    Sai ka duba ka ga yadda ƙarshen makircinsu ya zama, watau Mun hallakar da su tare da mutanensu baki ɗaya.

  52. فَتِلۡكَ بُيُوتُهُمۡ خَاوِيَةَۢ بِمَا ظَلَمُوٓاْۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 27:52

    To ga gidajensu can a rugurguje babu kowa saboda zaluncinsu. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke ganewa.

  53. وَأَنجَيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

    Open ayah 27:53

    Muka kuma tserar da waɗanda suka yi imani, suka kuma kasance suna kiyaye dokokin Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da mu cewa a garin Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), watau Hijiru akwai gungun wasu mazaje su tara waɗanda in ban da ɓarna a bayan ƙasa babu abin da suka sa a gaba. Ko kaɗan ba su da niyyar kawo gyara ko goyon bayansa. Sai suka ɗaura ɗamarar yaƙi da Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da da’awarsa da addininsa. Waɗannan mutane sun haɗu sun tattauna suka kuma yi rantsuwa a junansu cewa lallai za su far ma Annabi Salihu cikin dare su kashe shi tare da iyalansa. Sannan idan masu bin kadin jininsa sun fito suna neman a ɗaukar musu fansa, to za su fito su ƙeƙasa ƙasa su rantse cewa su ba su ma san wanda ya yi kisan ba, kuma ba shakka su iya gaskiyarsu suke faɗa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa sun shirya makircinsu na kashe Annabi Salihu da iyalansa a ɓoye ko da mutanensu kafirai ba su faɗa wa ba, to amma shi ma Allah ya shirya yadda zai ruguza makircinsu ya kare Annabi Salihu da iyalansa har da mabiyansa ya kuma hallaka maƙiyansa kafirai ba tare da sun san da haka ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa ya duba ya ga yadda ƙarshen makircin waɗancan maɓarnata ‘yan ta’adda ya zamo, watau shin sun yi nasara ko kuma Allah ya wargaza lamarinsu? Allah ya bayyana cewa tabbas ya hallakar da su gaba ɗaya, domin ya sauko musu da wata tsawa ta azaba wadda ta gama da su baki ɗaya. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya nuna cewa ga gidajensu can a rugurguje, katangunsu sun faɗi, rufinsu ya ɗauke, fayau babu kowa a cikinsu saboda zaluncinsu da shirkarsu da Allah. Lalle a cikin hallakar da waɗannan kafirai akwai izina ga mutane masu gane haƙiƙanin al’amura yadda suke. Allah kuma ya tabbatar da cewa ya tserar da mutanen da suka yi imani da Allah da Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma suka zamanto suna kiyaye dokokin Allah (Mai tsarki da daukaka).

  54. وَلُوطًا إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَتَأۡتُونَ ٱلۡفَٰحِشَةَ وَأَنتُمۡ تُبۡصِرُونَ

    Open ayah 27:54

    Kuma ka (ambaci) Luɗu lokacin da ya ce da mutanensa: “Yanzu kwa riƙa zaike wa alfasha alhali kuwa kuna gani?

  55. أَئِنَّكُمۡ لَتَأۡتُونَ ٱلرِّجَالَ شَهۡوَةٗ مِّن دُونِ ٱلنِّسَآءِۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ تَجۡهَلُونَ

    Open ayah 27:55

    “Yanzu kwa riƙa zaike wa maza don sha’awa ba mata ba? A’a, ku dai wasu irin mutane ne da kuke da jahilci”.

  56. ۞فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوۡمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَخۡرِجُوٓاْ ءَالَ لُوطٖ مِّن قَرۡيَتِكُمۡۖ إِنَّهُمۡ أُنَاسٞ يَتَطَهَّرُونَ

    Open ayah 27:56

    To babu wata amsa da ta fito daga bakin mutanensa sai kawai suka ce: “Ku fitar da Luɗu shi da iyalinsa daga alƙaryarku; lalle su mutane ne da suke nuna su masu tsarki ne.”

  57. فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ قَدَّرۡنَٰهَا مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ

    Open ayah 27:57

    Sai Muka tserar da shi tare da iyalinsa in ban da matarsa da Muka ƙaddara ta cikin hallakakku.

  58. وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ

    Open ayah 27:58

    Muka kuma yi musu ruwan azaba; to ruwan azabar waɗanda aka yi wa gargaɗi ya munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya aike shi zuwa ga alƙaryar Sadum inda mutanen garin suka shahara da wata mummunar al’ada ta neman maza da sha’awa, mugun aikin da ba a taɓa samun masu yin irinsa ba gabaninsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ja hankalinsu da cewa, yanzu sa riƙa aikata wannan mummunan aiki alhalin suna ganin muninsa a zahiri kuma suna sane, amma toshewar basira ta sa sun ƙi dainawa? Ya fito ƙarara ya bayyana musu abin da yake nufi da maganarsa, watau neman maza da sha’awa maimakon mata da Allah ya halatta musu su neme su ta hanyar aure amma suka tubure su sai dai maza. Ya tabbatar da cewa su mutane ne da jahilci ya yi wa katutu, don haka ba su san komai daga abin da ya wajaba a kansu na imani da tsarkaka daga saɓon Allah ba. Bayan Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya gargaɗi mutanensa ya yi musu nasiha sun ƙi ba shi wata amsa da ke nuna sun yarda da wa’azinsa sun karɓi nasiharsa, sai ma kawai suka shiga kiraye-kirayen junansu cewa su haɗu su kori Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da iyalansa da mabiyansa daga garinsu, domin wai su mutane ne da suke tsarkake kansu daga neman maza. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tserar da Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da iyalansa, in ban da matarsa da Allah ya riga ya ƙaddara tana cikin halakakku. Amma bai halakar da su ba sai da ya aiki mala’iku suka zo wurin Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cikin kamanni na wasu baƙi. Da mutanen gari suka ji labarin zuwansu, sai suka yo tururuwa zuwa gidan Annabi Luɗu da niyyar aikata mummunan aiki da baƙinsa. Annabi Luɗu ya ƙulle ƙofar gidansa, al’amari ya tsananta gare shi. Amma mala’ikun nan suka sanar da shi cewa su ba mutane ba ne, mala’iku ne, sun zo da nufin tserar da shi da iyalansa daga wannan gari, domin asuba na yi za su hallaka mutanen alƙaryar baki ɗaya. Suka umarce shi ya fita tare da iyalansa cikin dare, amma matarsa ita ma tana daga cikin waɗanda za a hallakar, domin tana tare da mutanen gari a kan kafirci, ba ta yi imani da shi ba. Annabi Luɗu da iyalansa kuwa suka fita cikin dare suka tsira, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mala’ikun nan suka ɓaɓɓake wannan gari kacokam da duk abin da yake cikinsa suka ɗaga shi can ƙololuwar sama sannan suka kifar da shi, samansa ta koma ƙasa, sannan aka bi su da ruwan duwatsu na azaba. Allah ya tabbatar da cewa ruwan azabar da aka yi wa waɗanda aka yi wa gargaɗi suka ƙi ji ya munana.

  59. قُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ وَسَلَٰمٌ عَلَىٰ عِبَادِهِ ٱلَّذِينَ ٱصۡطَفَىٰٓۗ ءَآللَّهُ خَيۡرٌ أَمَّا يُشۡرِكُونَ

    Open ayah 27:59

    Ka ce: “Yabo ya tabbata ga Allah, kuma aminci ya tabbata ga bayinsa waɗanda Ya zaɓa.” Yanzu Allah ne Ya fi ko kuwa abin da suke tarawa (da Shi)?

  60. أَمَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَنۢبَتۡنَا بِهِۦ حَدَآئِقَ ذَاتَ بَهۡجَةٖ مَّا كَانَ لَكُمۡ أَن تُنۢبِتُواْ شَجَرَهَآۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٞ يَعۡدِلُونَ 

    Open ayah 27:60

    Ko kuwa wane ne ya halicci sammai da ƙasa, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan Muka tsirar da (shukokin) gonaki masu ƙayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba? Shin akwai wani abin bauta na gaskiya tare da Allah? A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa gaskiya.

  61. أَمَّن جَعَلَ ٱلۡأَرۡضَ قَرَارٗا وَجَعَلَ خِلَٰلَهَآ أَنۡهَٰرٗا وَجَعَلَ لَهَا رَوَٰسِيَ وَجَعَلَ بَيۡنَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ حَاجِزًاۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 27:61

    Ko kuwa wane ne ya sanya ƙasa wurin zama, ya kuma sanya ƙoramu a tsattsakinta, kuma ya sanya mata turaku, kana kuma ya sanya shamaki tsakanin kogunan nan biyu (na ruwan daɗi da na ruwan zartsi)? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? A’a, yawancinsu dai ba sa ganewa.

  62. أَمَّن يُجِيبُ ٱلۡمُضۡطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكۡشِفُ ٱلسُّوٓءَ وَيَجۡعَلُكُمۡ خُلَفَآءَ ٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ

    Open ayah 27:62

    Ko kuwa wane ne yake amsa wa wanda yake cikin matsuwa lokacin da ya roƙe shi, yake kuma yaye duk wani bala’i, yake kuma sanya ku halifofi a bayan ƙasa? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? Kaɗan ne ƙwarai kuke wa’azantuwa.

  63. أَمَّن يَهۡدِيكُمۡ فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ وَمَن يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ بُشۡرَۢا بَيۡنَ يَدَيۡ رَحۡمَتِهِۦٓۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ تَعَٰلَى ٱللَّهُ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

    Open ayah 27:63

    Ko kuwa wane ne yake shiryar da ku a cikin duffan tudu da na kogi, kuma wane ne yake sako iska tana mai bushara gabanin (saukar) rahamarsa? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah? Allah Ya ɗaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi).

  64. أَمَّن يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَمَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 27:64

    Ko kuwa wane ne yake ƙagar halitta sannan ya dawo da ita (bayan mutuwa), kuma wane ne yake arzuta ku ta sama da ƙasa? Shin akwai wani abin bauta da gaskiya tare da Allah?” Ka ce (da su): “Ku kawo dalilinku idan kun kasance masu gaskiya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tabbatar masa dukkan siffofi na yabo da godiya bisa ni’imominsa ga bayinsa, da kuma amincin da ya ba wa bayinsa waɗanda ya zaɓa ya kuɓutar da su daga azabar duniya wadda ya halakar da maƙiyansa da ita. Sannan ya ƙalubalance su da cewa yanzu Allah ne ya fi ko kuwa abin da suke shirka da shi wanda ba ya tsinana musu wani amfani ko ya magance musu wata cuta? Allah kuma ya yi bayanin wasu ayyukansa waɗanda ya keɓanta da su masu nuna cikar Ƙudurarsa da ƙarfin ikonsa don tabbatar da Kaɗaitarsa wajen bauta. Allah ya ci gaba da tambayar mushirikai masu bautar waninsa da cewa, wane ne ya halicci sammai da ƙasa ba tare da ya kwaikwaya daga wurin wani ba, ya kuma saukar wa da mutane ruwa daga sama ya fitar musu da shukokin gonaki masu kyau da ban sha’awa da shi, yayin da su mutane ba za su iya fitar da bishiyoyin waɗannan gonaki ba domin gazawarsu, amma kuma sun san Allah ne ya yi musu wannan baiwa? To shin akwai wani abin bauta tare da Allah wanda shi ma zai iya waɗannan ayyuka har ya cancanci a bauta masa tare da Allah? Allah ya tabbatar da cewa babu, su dai mushirikai kawai mutane ne da suke kauce wa gaskiya, suke kuma daidaita wasu da Allah ba tare da wata hujja ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar su cewa, wane ne ya sanya ƙasa ta zama mazauni ga bayinsa, su gina gidajen zama a kanta su kuma yi shuke-shuke da kai-komonsu a kanta ba tare da tana tangal-tangal da su ba, ya kuma sanya ƙoramu suna gudana a tsakankaninta domin mutane da dabbobi su amfana, ya kuma kafa duwarwatsu a kanta don zama turaku masu hana ta motsi, ya kuma sanya shamaki tsakanin koguna guda biyu, na ruwan daɗi da na ruwan zartsi, ta yadda ba za su gauraya da juna ba, ruwan da mutane za su sha ya lalace su rasa ruwan sha? Ya tambaye su cewa, shin akwai wani abin bauta na gaskiya tare da Allah wanda zai iya yin waɗannan ayyuka da har za a daidaita shi da Allah a bauta masa tare da shi? Sai Allah ya tabbatar da cewa babu, yawancinsu ba su da sani ne, suna dai bin iyayensu ne da shugabanninsu ido rufe. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake tambayar su cewa, wane ne yake amsa addu’ar wanda ya shiga wata matsuwa idan ya roƙe shi, ya yaye masa duk wani mummunan abu da zai same shi na rashin lafiya da talauci da makamantansu? An karɓo daga wani mutum daga ƙabilar Balhujaim ya ce: Na ce: “Ya Manzon Allah zuwa ga me kake kira?” Ya ce: “Ina kira ne zuwa ga Allah shi kaɗai wanda idan wata cuta ta same ka ka roƙe shi sai ya yaye maka, wanda kuma idan ka ɓace a ƙungurmin jeji ka roƙe shi sai ya dawo da kai hanya, wanda kuma idan fari ya same ka ka roƙe shi sai ya fito maka da shuka.” Mutumin nan ya ce: Sai na ce: “To yi mini wasiyya.” Sai ya ce: “Kada ka kuskura ka zagi wani, kada kuma ka guje wa aikin alheri ko da kuwa ka haɗu da ɗan’uwanka ne kana yi masa fara’a, ko da kuwa ka zuba ruwa ne daga gugarka a cikin ƙoƙon mai neman ruwan sha, ka kuma sanya kwarjallenka zuwa rabin ƙwauri, idan ka ƙi to zuwa idanuwan ƙafa. Ka guji sakin kwarjallenka yana jan ƙasa, domin barin kwarjalle yana jan ƙasa yana daga cikin girman kai, Allah kuwa ba ya son girman kai.” [Ahmad #20636]. Wane ne kuma yake mayar da mutane halifofi a bayan ƙasa; wasu su shuɗe wasu su zo su gaje su, tsareku bayan tsareku? Allah ya tambaye su cewa, shin akwai wani abin bauta tare da Allah da yake tarayya da shi a kan waɗannan ayyuka? Sam babu shi. Allah ya tabbatar da cewa kaɗan ne ƙwarai suke wa’azantuwa ko suke ɗaukan izina, Sai kuma har wa yau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tambayar su cewa, wane ne yake shiryar da su ya nuna musu hanya lokacin da suke tafiya a cikin duffan tudu da na kogi ta hanyar alamu da taurari da ya sanya musu har su samu su tsira daga hallaka? Wane ne kuma yake aiko musu da iska don ta zama albishir gabanin ya saukar musu da rahamarsa, watau ruwan sama wanda rahamar Allah ne ga bayinsa? Allah ya tambaye su cewa, yanzu akwai wani abin bauta tare da Allah wanda yake yi musu waɗannan ayyuka da har ya cancanci su bauta masa? Allah ya ɗaukaka ya kuma tsarkaka daga duk abin da suke yi masa shirka da shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake tambayar mushirikai cewa, wane ne yake ƙirƙirar halitta, ya ƙage ta daga babu, sannan kuma ya dawo da ita bayan mutuwa domin hisabi? Kuma wane ne yake arzuta mutane daga sama da ƙasa ta hanyar saukar musu da ruwan sama ya fitar musu da tsirrai daga ƙasa? Shin akwai wani abin bauta tare da Allah wanda zai iya yin waɗannan abubuwan da aka ambata? Sai kuma ya neme su da su kawo hujjojinsu da dalilansu a kan abin da suke faɗa na tarayyar ababen bautar tare da Allah, in dai har suna da gaskiya, domin ita gaskiya ana tabbatar da ita ne ta hanyar hujja da dalili ba ta hanyar da’awar baka kaɗai ba.

  65. قُل لَّا يَعۡلَمُ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ ٱلۡغَيۡبَ إِلَّا ٱللَّهُۚ وَمَا يَشۡعُرُونَ أَيَّانَ يُبۡعَثُونَ

    Open ayah 27:65

    Ka ce (da su): “Duk wanda yake cikin sammai da ƙasa in ba Allah ba ba wanda ya san gaibu. Su kuma ba su san lokacin da za a tashe su ba.”

  66. بَلِ ٱدَّٰرَكَ عِلۡمُهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ مِّنۡهَاۖ بَلۡ هُم مِّنۡهَا عَمُونَ

    Open ayah 27:66

    A’a, iliminsu game da ranar lahira ya bibiyi na junansu ne. Ba ma wannan kaɗai ba, hakanan suna cikin kokwanto ne game da ita. Ban da hakan ma, su dai makafi ne game da ita. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tabbatar da cewa babu wani a cikin sammai da ƙasa da ya san gaibu sai Allah shi kaɗai. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Duk wanda ya riya cewa Annabi (ﷺ) ya san abin da zai kasance gobe, to haƙiƙa ya yi wa Allah ƙarya babba, Allah yana cewa: “Ka ce: “Duk wanda yake cikin sammai da ƙasa in ban da Allah babu wanda ya san gaibu.” [Muslim #177]. Hakanan duk waɗanda suke sama da ƙasa babu wanda ya san yaushe ne za a tashi mutane domin hisabi da sakamako sai Allah kaɗai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da jahilcin mushirikai masu ƙaryata ranar lahira game da ita, ya bayyana cewa iliminsu game da sha’anin lahira ya bibiyi na junansu ne, watau sun sami iliminsu game da ita daga iyayensu, su ma daga nasu iyayen, watau abin da ya shahara a wajensu na ƙaryata ranar alƙiyama. Allah ya nuna ba wannan kaɗai ba ma, a’a suna ma cikin shakku da ruɗu game da lahirar, kai haƙiƙa idanunsu ma sun makance ne ba sa ganin kowace irin hujja da take tabbatar da zuwan ranar lahira.

  67. وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَءِذَا كُنَّا تُرَٰبٗا وَءَابَآؤُنَآ أَئِنَّا لَمُخۡرَجُونَ

    Open ayah 27:67

    Waɗanda suka kafirta, kuma suka ce: “Yanzu bayan mun zama ƙasa mu da iyayenmu, ashe lalle za a (sake) fito da mu?

  68. لَقَدۡ وُعِدۡنَا هَٰذَا نَحۡنُ وَءَابَآؤُنَا مِن قَبۡلُ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

    Open ayah 27:68

    “Haƙiƙa an yi mana alƙawarin wannan mu da iyayenmu tun a da can, wannan ba komai ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko.”

  69. قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

    Open ayah 27:69

    Ka ce (da su): “Ku yi tafiya a bayan ƙasa za ku ga yadda ƙarshen kafurai ya kasance.”

  70. وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَلَا تَكُن فِي ضَيۡقٖ مِّمَّا يَمۡكُرُونَ 

    Open ayah 27:70

    Kuma kada ranka ya ɓaci game da su, kada kuma ka zama cikin ƙuncin zuciya game da makircin da suke ƙullawa.

  71. وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 27:71

    Suna kuma cewa: “Yaushe ne lokacin wannan wa’adin idan kun kasance masu gaskiya?”

  72. قُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ رَدِفَ لَكُم بَعۡضُ ٱلَّذِي تَسۡتَعۡجِلُونَ

    Open ayah 27:72

    Ka ce (da su): “Lalle sashin abin da kuke gaggauto da zuwansa (na azaba) ya kusanto.”

  73. وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَشۡكُرُونَ

    Open ayah 27:73

    Kuma lalle Ubangijinka Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa.

  74. وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَعۡلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمۡ وَمَا يُعۡلِنُونَ

    Open ayah 27:74

    Lalle kuma Ubangijinka tabbas Yana sane da abin da zukatansu suke ɓoyewa, da kuma abin da suke bayyanawa.

  75. وَمَا مِنۡ غَآئِبَةٖ فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٍ

    Open ayah 27:75

    Kuma babu wani abu da yake ɓoye a cikin sammai da ƙasa face yana cikin littafi mabayyani (watau Lauhul-Mahafuzu). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai suke jayayya a kan tabbatar ranar alƙiyama har ma suke cewa babu yadda za a yi a tashe su ballantana iyayensu da rai bayan sun mutu sun zama ƙasa, kuma da man can an daɗe ana yi musu wannan alƙawari su da iyayensu, ga shi an kawo yanzu abin da ake faɗa musu bai auku ba, saboda haka ne wai suka tabbatar da cewa duk maganganun da ake faɗa musu game da zuwan ranar alƙiyama ba komai ba ne in ban da tatsuniyoyin mutanen da. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya faɗa musu cewa su yawata ko’ina a bayan ƙasa su ga yadda ƙarshen masu manyan laifuffuka irin nasu ya kasance, watau duk Allah ya hallakar da su saboda ƙaryata annabawansu da suke yi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Manzonsa (ﷺ) nasiha da ya daina ɓata ransa a kansu don ganin sun bijire wa da’awarsa; kada ya nuna damuwarsa a kan haka, Allah zai taimake shi a kansu, ya mayar da makircinsu ya koma musu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tambayar da mushirikai suke yi wa Manzon Allah (ﷺ) game da tashin alƙiyama da cewa, wai yaushe ne ranar za ta zo idan har yana da gaskiya? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya mayar musu da martani cewa su daina wani zumuɗi domin wani ɓangare na azabar da suke sauraron zuwanta ya kusanto. Sannan Allah ya tabbatar wa da Annabi cewa shi mai falala ne a kan mutane saboda haka ne ba ya gaggauto musu da azaba duk kuwa da kafircinsu da saɓon Allah da suke ta tafkawa dare da rana. To amma yawancin mutane ba sa gode wa ni’imomin da yake yi musu. Ya kuma bayyana masa cewa lalle ya san ɗaukacin abubuwan da zukatan bayinsa suke ɓoyewa da wanda suke bayyanawa, babu abin da yake ɓoye a gare shi, zai saka musu kuma a kan dukkan ayyukansu. Kuma ya tabbatar da cewa babu wani abu da yake ɓoye a sama da ƙasa wanda mutane ba su san da zamansa ba face yana rubuce a cikin littafi mabayyani, watau Lauhul-Mahfuzu.

  76. إِنَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ يَقُصُّ عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ أَكۡثَرَ ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

    Open ayah 27:76

    Lalle <b> wannan Alƙur’anin yana labarta wa Banu-Isra’ila mafi yawan abin da suke saɓani a kansa.

  77. وَإِنَّهُۥ لَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 27:77

    Lalle kuma shi (Alƙur’ani) tabbas shiriya ne kuma rahama ce ga muminai.

  78. إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُم بِحُكۡمِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡعَلِيمُ

    Open ayah 27:78

    Lalle Ubangijinka zai yi shari’a a tsakaninsu da hukuncinsa. Shi kuwa Mabuwayi ne, Masani.

  79. فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۖ إِنَّكَ عَلَى ٱلۡحَقِّ ٱلۡمُبِينِ

    Open ayah 27:79

    To ka dogara ga Allah; lalle kai kana kan gaskiya mabayyaniya.

  80. إِنَّكَ لَا تُسۡمِعُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَلَا تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا وَلَّوۡاْ مُدۡبِرِينَ 

    Open ayah 27:80

    Lalle kai ba ka iya jiyar da matattu, ba kuma ka iya jiyar da kurame kira lokacin da suka juya suna masu ba da baya.

  81. وَمَآ أَنتَ بِهَٰدِي ٱلۡعُمۡيِ عَن ضَلَٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ

    Open ayah 27:81

    Kuma sannan kai ba za ka iya shiryar da makafi daga ɓatansu ba; ba wanda kake iya jiyarwa sai wanda ya yi imani da ayoyinmu, to waɗannan su ne Musulmi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da gaskiyar Alƙur’ani wanda ya saukar wa Manzonsa (ﷺ), da cewa yana ba wa Banu Isra’ila labarin mafi yawan abin da suke saɓani a cikinsa tare da yi musu bayanin wuraren da suka kauce wa gaskiya. Kuma lalle shi Alƙur’ani shiriya ce da rahama ga muminai masu aiki da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa tabbas shi ne zai yi hukunci na adalci ranar alƙiyama a tsakanin muminai da kafirai da ma’abota littafi, inda zai ji ƙan muminai ya kuma azabta kafirai. Shi ne Mabuwayi gagara badau wanda babu mai iya rinjayar sa kuma Masani wanda yake tantance tsakanin mai gaskiya da maƙaryaci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya dogara gare shi cikin dukkan al’amuransa, ya kuma tabbatar masa cewa yana kan gaskiya bayyananna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Manzo (ﷺ) cewa idan har ya sauke nauyin da aka ɗora masa na isar da saƙon Allah ya kuma dogara da Allah a kan haka, to ɓacewar duk wanda ya ɓace ba za ta cutar da shi ba, domin shi ba zai iya jiyar da matattu komai ba, su ne waɗanda zukatansu suka mutu saboda kafirci, hakanan ba zai iya jiyar da kurame kira ba idan sun juya masa baya. Kuma ba zai iya shiryar da makafi waɗanda basirarsu ta toshe suka makance su dawo daga ɓatan da suke kai ba, don haka ya daina damuwa yana baƙin ciki saboda su. Ya bayyana masa cewa masu imani da Allah waɗanda suke miƙa wuya ga umarninsa ne kaɗai zai iya jiyar da su da’awarsa kuma su saurare shi su amfana da abin da yake karanta musu.

  82. ۞وَإِذَا وَقَعَ ٱلۡقَوۡلُ عَلَيۡهِمۡ أَخۡرَجۡنَا لَهُمۡ دَآبَّةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ تُكَلِّمُهُمۡ أَنَّ ٱلنَّاسَ كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا لَا يُوقِنُونَ

    Open ayah 27:82

    Kuma idan lokacin da aka alƙawarta musu ya cika, to za Mu fito musu da wata dabba daga ƙasa da za ta riƙa faɗa musu cewa: “Lalle mutane sun zamanto ba sa sakankancewa da ayoyinmu.”

  83. وَيَوۡمَ نَحۡشُرُ مِن كُلِّ أُمَّةٖ فَوۡجٗا مِّمَّن يُكَذِّبُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُمۡ يُوزَعُونَ

    Open ayah 27:83

    Kuma ka tuna ranar da za Mu tattara jama’a na kowacce al’umma, daga cikin waɗanda suke ƙaryata ayoyinmu ana koro su na farko da na ƙarshe.

  84. حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُو قَالَ أَكَذَّبۡتُم بِـَٔايَٰتِي وَلَمۡ تُحِيطُواْ بِهَا عِلۡمًا أَمَّاذَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 27:84

    Har yayin da suka zo (sannan Allah) Ya ce da su: “Yanzu ku kuka ƙaryata ayoyina, alhali kuwa ba ku tantance da saninsu ba? Ko kuwa me kuka zamanto kuna aikatawa ne (a duniya)?”

  85. وَوَقَعَ ٱلۡقَوۡلُ عَلَيۡهِم بِمَا ظَلَمُواْ فَهُمۡ لَا يَنطِقُونَ

    Open ayah 27:85

    Kuma abin da aka alƙawarta musu na azaba ya tabbata a kansu saboda kafircinsu, to su ba za su iya furta komai ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin wata alama daga cikin manyan alamomin tashin alƙiyama ya kuma bayyana wasu abubuwa da za su kasance a ranar hisabi. Watau idan lokacin saukar azabarsa ya tabbata zai fito wa da mutane wata dabba daga ƙasa da za ta riƙa yi musu magana cewa lalle mutane sun kasance ba sa sakankancewa da ayoyin Allah, watau imaninsu ya yi rauni matuƙa da gaske. Lokacin da wannan dabba za ta bayyana imanin wanda zai yi imani a lokacin ba zai amfane shi ba. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abubuwa uku idan suka bayyana to imanin wani rai wanda bai yi imani da can ba, ko kuma bai yi aiki na gari ba, ba zai yi masa amfani ba, hudowar rana daga mafaɗarta da bayyanar Dujal da fitowar dabba daga ƙasa.” [Muslim #417]. Sannan Allah ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tuna ranar da zai tattara jama’ar manyan mutane daga cikin kowace al’umma na farko da na ƙarshe wuri guda waɗanda suka ƙaryata ayoyinsa sai a gargaɗa su zuwa ga hisabi. Har sai sun iso wajen yi musu hisabi, a nan ne Allah zai tambaye su hujjarsu ta ƙaryata ayoyinsa masu nuna Kaɗaitakarsa suka kuma ƙunshi shari’arsa, alhalin ba wani ilimi ne suka samu ba wanda ya nuna waɗannan ayoyin ƙarya ne. Sannan ya tambaye su abin da suka kasance suna aikatawa a rayuwarsu ta duniya. A nan ne za su tabbatar da kuskuren da suka tafka a duniya, su yi nadamar da ba za ta amfane su da komai ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa azabarsa za ta tabbata a kansu saboda zaluncin da suka yi na kafirce wa Allah da ƙaryata manzanninsa, kuma a wannan ranar ba za su iya buɗa baki su kare kansu ba, kuma ba su da wata hujjar da za su bayar don kuɓutar da kansu daga azaba.

  86. أَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا جَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِيَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 27:86

    Yanzu ba sa gani cewa Mu Muka samar da dare don su nutsu a cikinsa, da kuma rana mai haskakawa (don su yi harka)? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin imani.

  87. وَيَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَفَزِعَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُۚ وَكُلٌّ أَتَوۡهُ دَٰخِرِينَ

    Open ayah 27:87

    (Ka tuna) kuma ranar da za a busa ƙaho sai duk mahaluƙin da yake cikin sammai da ƙasa ya firgita, sai dai wanda Allah Ya toge. Kuma gaba ɗayansu za su zo masa suna masu miƙa wuya.

  88. وَتَرَى ٱلۡجِبَالَ تَحۡسَبُهَا جَامِدَةٗ وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ ٱلسَّحَابِۚ صُنۡعَ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ أَتۡقَنَ كُلَّ شَيۡءٍۚ إِنَّهُۥ خَبِيرُۢ بِمَا تَفۡعَلُونَ

    Open ayah 27:88

    Kuma za ka ga duwatsu ka zaci a tsaye suke cak, alhali kuwa su suna tafiya ne irin tafiyar gizagizai. Aikin Allah kenan wanda Ya kyautata halittar kowane irin abu. Lalle Shi Masanin abin da kuke aikatawa ne.

  89. مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَا وَهُم مِّن فَزَعٖ يَوۡمَئِذٍ ءَامِنُونَ

    Open ayah 27:89

    Duk waɗanda suka zo da kyakkyawan (aiki), to suna da (lada) fiye da shi, kuma su amintattu ne daga firgitar wannan ranar.

  90. وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَكُبَّتۡ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ هَلۡ تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ 

    Open ayah 27:90

    Waɗanda kuwa suka zo da mummunan (aiki), to an kifar da fuskokinsu cikin wuta, to ba za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jawo hankalin masu ƙaryata tashi bayan mutuwa da cewa ba sa duban barcin da suke yi su farka, shi kansa yana nuna musu yiwuwar tashi bayan mutuwa? Ya kuma bayyana cewa yanzu ba su ga yadda ya samar da dare ba, domin su yi barci su samu natsuwa da hutu, ya kuma sanya rana mai haskawa domin su sami damar gani a cikin yini, su fita su yi harkokinsu na yau-da-kullum? Ya tabbatar musu cewa, a cikin wannan barci da suke yi kullum mai kama da mutuwa da kuma farkawar da suke yi mai kama da tashi bayan mutuwa, lalle akwai ayoyi bayyanannu ga mutane masu imani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da cewa ya tuna ranar da Mala’ika Israfilu, wanda shi ne aka wakilta shi ya busa ƙaho domin tashin alƙiyama, zai yi busa ta biyu sai duk mahaluƙin da yake cikin sammai da wanda yake bayan ƙasa su firgita, sashinsu ya gauraya da sashi saboda tsoron abin da zai biyo bayan busar, watau hisabi da sakamako, sai fa waɗanda Allah ya ga dama ya toge su daga wannan firgicin domin nuna wata falalarsa gare su. Dukkan halittu a wannan rana za su zo wa Allah suna masu miƙa wuya, masu ɗa’a gare shi. Sannan a ranar mutum zai ga duwatsu ya yi zaton a tsaye suke cak ba sa motsi alhalin kuwa gudu suke sheƙawa kamar girgije a sama, saboda tsananin tsoro. Wannan aikin Allah kenan wanda ya kyauta halittar komai, shi ne wanda yake tafiyar da waɗannan duwatsu kamar haka. Allah ya tabbatar da cewa lalle shi masanin abin da bayinsa suke aikatawa ne, kuma zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda sakamakonsa yake na adalci da falala, da cewa duk wanda ya zo a ranar alƙiyama da imani da aiki na ƙwarai, to yana da sakamakon Aljanna. Wannan falala ce ta Allah gare shi. Kuma masu irin wannan matsayi su amintattu ne daga firgitar wannan ranar. Wanda kuwa ya zo da kafirci da saɓon Allah to sakamakon waɗannan wutar Jahannama ce. Za a riƙa yi musu tambaya irin ta wulaƙanci da ƙasƙanci, da cewa shin za a saka musu da wani abu ne in ba da abin da suka kasance suna aikatawa ba na kafirci da saɓon Allah?

  91. إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ رَبَّ هَٰذِهِ ٱلۡبَلۡدَةِ ٱلَّذِي حَرَّمَهَا وَلَهُۥ كُلُّ شَيۡءٖۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

    Open ayah 27:91

    (Ka ce da su): “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Ubangijin wannan garin (Makka) wanda Ya mayar da shi mai alfarma, kuma komai nasa ne; kuma an umarce ni da in zama cikin Musulmi.

  92. وَأَنۡ أَتۡلُوَاْ ٱلۡقُرۡءَانَۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَقُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ

    Open ayah 27:92

    “An kuma (umarce ni) da in karanta Alƙur’ani; don haka duk wanda ya shiriya, to ya shiriya ne don amfanin kansa; wanda kuwa ya ɓace sai ka ce (da shi): ‘Da ma ni ina cikin masu gargaɗi ne kawai’”.

  93. وَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ سَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ فَتَعۡرِفُونَهَاۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 27:93

    Ka kuma ce: “Dukkan yabo ya tabbata ga Allah; ba da daɗewa ba zai nuna muku ayoyinsa, za kuma ku san su. Ubangijinka kuma ba rafkananne ba ne game da abin da kuke aikatawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa wa mushirikai cewa shi fa an umarce shi ne ya bauta wa Ubangijin wannan gari na Makka wanda ya mayar da shi mai alfarma, don haka ya haramta zubar da jini a cikinsa, ko a zalunci wani ko a kashe dabbar farauta a cikinsa ko a sare bishiyarsa. Mulkin komai nasa ne. Ya kuma umarci Manzonsa ya zama cikin Musulmi masu miƙa wuya ga Allah da yi masa biyayya. Sannan ya faɗa musu cewa ya umarce shi ya karanta wa mutane Alƙur’ani, duk wanda ya karɓi shiriyarsa ya yi aiki da karantarwarsa to don amfanin kansa ne, wanda kuwa ya ɓace ya bijire wa karantarwarsa ya ƙi aiki da shi ko ma ya ƙaryata shi, to ya sanar da su cewa shi da ma yana cikin masu yi wa mutane gargaɗin azabar Allah ne kawai, amma shiriyarsu ba a hannunsa take ba. Sai kuma a ayar ƙarshe ta wannan Sura Allah ya umarce shi da ya nuna godiyarsa da kirarinsa ga Allah bisa ga ɗimbin ni’imominsa da ba za su lissafu ba; ya tabbatar masa cewa zai nuna musu ayoyinsa a karan kansu da kuma ayoyin da suke sama da na ƙasa da ma waɗanda suke tattare da abin da ya arzuta su da shi, duk su gane su, su san su sanin da zai yi musu jagora zuwa ga sallama wa gaskiya, domin wanda zai shiryu ya shiryu a kan hujja, wanda kuma zai ɓace ya ɓace bayan hujja ta tsayu a kansa. Allah ya tabbatar da cewa shi ba rafkananne ba ne daga abin da mutane suke aikatawa, yana sane da komai kuma zai saka wa kowa a kan aikinsa.