القصص
Al-Qasas
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
طسٓمٓ
Open ayah 28:1ƊA SIN MIM.
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ
Open ayah 28:2Waɗannan ayoyi ne na Littafi mabayyani.
نَتۡلُواْ عَلَيۡكَ مِن نَّبَإِ مُوسَىٰ وَفِرۡعَوۡنَ بِٱلۡحَقِّ لِقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 28:3Muna karanta maka labarin Musa da Fir’auna da gaskiya don mutane da suke yin imani.
إِنَّ فِرۡعَوۡنَ عَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَجَعَلَ أَهۡلَهَا شِيَعٗا يَسۡتَضۡعِفُ طَآئِفَةٗ مِّنۡهُمۡ يُذَبِّحُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَيَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 28:4Lalle Fir’auna ya yi ɗagawa a cikin ƙasar (Masar) ya kuma mayar da mutanenta ƙungiyoyi daban-daban, yana bautar da wata ƙungiyar daga cikinsu, yana yanka ‘ya’yayensu maza, yana kuma ƙyale matansu da rai. Lalle shi ya kasance cikin maɓarnata.
وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَنَجۡعَلَهُمۡ أَئِمَّةٗ وَنَجۡعَلَهُمُ ٱلۡوَٰرِثِينَ
Open ayah 28:5Muna kuma nufin za Mu yi baiwa ga waɗanda aka wulaƙanta a cikin ƙasar (Masar) Mu kuma mayar da su shugabanni, kuma Mu mayar da su magadan (mulkin Fir’auna).
وَنُمَكِّنَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَنُرِيَ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَجُنُودَهُمَا مِنۡهُم مَّا كَانُواْ يَحۡذَرُونَ
Open ayah 28:6Mu kuma kafa su a ƙasar, kuma Mu nuna wa Fir’auna da Hamana da rundunoninsu gaba ɗayansu abin da suke jin tsoro game da su (Banu Isra’ila). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da wasu haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori da suka gabace ta. Dubi farkon Suratul Baƙara don ganin bayani a kansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗannan ayoyi da za su zo cikin wannan Sura ayoyi ne na littafi mai bayanin duk wasu buƙatu da bayi suke buƙatar saninsu. Allah ya tabbatar wa Manzonsa cewa shi ne yake karanta masa labarin Annabi Musa da Fir’auna bisa gaskiya domin mutanen da suka yi imani, saboda su ne kaɗai za su amfana da shi. Allah ya fara da ba shi labarin Fir’auna wanda ya yi ɗagawa a ƙasar Masar ya yi wa mutanen cikinta mulkin kama-karya ya mayar da su ƙungiyoyi daban-daban yana nuna bambanci tsakaninsu, yana kuma bautar da wata ƙungiyar daga cikinsu su ne Banu Isra’ila, yana yanka ‘ya’yansu maza yana ƙyale matansu domin su riƙa yi masa bauta a gidajensa duk dai domin ya ƙasƙantar da su ya wulaƙanta su. Allah ya bayyana cewa lalle Fir’auna ya tabbata cikin maɓarnatan mutane waɗanda ba su da wani alheri duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sanar da cewa a lokacin da Fir’auna yake waccan aika-aika a kan Banu Isra’ila shi kuma yana nufin ya yi baiwa ga su Banu Isra’ila waɗanda ake wulaƙantawa a ƙasar Masar, ta hanyar hallaka Fir’auna babban maƙiyinsu da kawar musu da yanayin ƙasƙanci da suke rayuwa a cikinsa, ya kuma mayar da su shugabanni waɗanda za a riƙa koyi da su wajen gaskiya da ayyukan alheri, sannan ya gadar musu da ƙasar Sham mai albarka bayan hallaka Fir’auna, sannan kuma ya kafa su a bayan ƙasa ya ba su mulki. Shi kuma Fir’auna da babban Wazirinsa mai taimaka masa wajen zalunci da ɓarna a bayan ƙasa, watau Hamana, tare da rundunarsu masu taimaka musu a harkokin mulkinsu na zalunci Allah ya nuna musu abin da suke tsoron aukuwarsa na gushewar mulkinsu da rushewar masarautarsu a hannun yaron da za a haifa daga ƙabilar Banu Isra’ila.
وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ أُمِّ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَرۡضِعِيهِۖ فَإِذَا خِفۡتِ عَلَيۡهِ فَأَلۡقِيهِ فِي ٱلۡيَمِّ وَلَا تَخَافِي وَلَا تَحۡزَنِيٓۖ إِنَّا رَآدُّوهُ إِلَيۡكِ وَجَاعِلُوهُ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 28:7Muka kuma yi wa mahaifiyar Musa wahayi da cewa: “Ki shayar da shi; to yayin da kika ji masa tsoro, sai ki jefa shi a cikin kogi, kada kuma ki ji tsoro, kuma kada ki yi baƙin ciki; lalle Mu Masu dawo miki da shi ne, kuma Masu sanya shi ne cikin manzanni.”
فَٱلۡتَقَطَهُۥٓ ءَالُ فِرۡعَوۡنَ لِيَكُونَ لَهُمۡ عَدُوّٗا وَحَزَنًاۗ إِنَّ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَجُنُودَهُمَا كَانُواْ خَٰطِـِٔينَ
Open ayah 28:8Sai mutanen Fir’auna suka tsince shi domin (daga baya) ya zama abokin gaba da kuma baƙin ciki a gare su. Lalle Fir’auna da Hamana da rundunoninsu sun kasance masu laifi.
وَقَالَتِ ٱمۡرَأَتُ فِرۡعَوۡنَ قُرَّتُ عَيۡنٖ لِّي وَلَكَۖ لَا تَقۡتُلُوهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوۡ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدٗا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 28:9Matar Fir’auna kuma ta ce: “(Shi) farin ciki ne a gare ni har da kai; kada ku kashe shi, muna fatan ya amfane mu ko kuma mu ɗauke shi a matsayin ɗa,” alhali kuwa su ba su san (abin da zai faru ba). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci yadda mulkin Fir’auna zai zama nan gaba da kuma yadda zai ɗaukaka sha’anin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanensa ya kafa su a bayan ƙasa. Allah ya ambaci yadda Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya taso a gidan Fir’auna ƙarƙashin kulawarsa har zuwa lokacin da ya aiko shi zuwa ga Fir’auna da rundunarsa. Bayan mahaifiyar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ta haife shi sai Allah ya yi mata wahayi yayin da ta shiga jin tsoron abin da zai faru gare shi idan har Fir’auna da zabaniyawansa suka sami labarin haihuwarsa. Allah ya umarce ta da ta shayar da shi, amma idan har ta ji tsoron Fir’auna game da shi to ta sanya shi cikin akwati ta jefa shi ruwa, watau ƙoramar Nil, kar kuma ta ji tsoron nutsewarsa a cikin ruwa ko Fir’auna ya hallaka shi, kuma kada ta yi baƙin cikin rabuwa da shi. Allah ya yi mata alƙawarin zai dawo mata da shi domin ta ci gaba da shayar da shi. Hasali ma ya tabbatar mata da cewa zai sanya shi cikin manzanninsa waɗanda yake aikowa zuwa ga bayinsa. Wannan kuwa ita ce mafi girman bushara ga mahaifiyar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). To mahaifiyar Annabi Musa dai hankalinta bai kwanta ba, don haka ta aikata abin da aka umarce ta da shi, ta saka shi cikin akwati ta rufe ta jefa shi cikin ƙoramar Nil. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma da ikonsa ya sanya ruwa ya ja akwatin Annabi Musa har zuwa gaɓar da mutanen Fir’auna suke shaƙatawa, a nan ne suka tsince shi suka kai shi gidan Fir’auna domin daga baya ya zame musu babban maƙiyi kuma abin baƙin cikinsu wanda a ƙarshe zai jawo musu halaka shi da jama’arsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da cewa Fir’auna da Wazirinsa da rundunoninsu masu taimaka musu sun kasance masu aikata babban laifi saboda kafircinsu da zaluncinsu da ɓarnarsu a bayan ƙasa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar cewa yayin da Fir’auna ya ga jariri, watau Annabi Musa a gabansa sai bai nutsu da shi ba, har ma ya yi yunƙurin hallaka shi kamar yadda ya saba kashe jarirai maza, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jefa ƙaunar Musa a zuciyar matar Fir’auna Asiya sai nan take ta roƙi Fir’auna da kada ya kashe shi, domin tana ganin zai zama abin farin ciki a gare su nan gaba ko kuma ya amfane su ko ma su ɗauke shi a matsayin ɗansu. Allah ya bayyana cewa duk suna wannan hasashe ne bisa rashin sanin abin da zai kasance a hannun wannan jariri na rushewar mulkin Fir’auna.
وَأَصۡبَحَ فُؤَادُ أُمِّ مُوسَىٰ فَٰرِغًاۖ إِن كَادَتۡ لَتُبۡدِي بِهِۦ لَوۡلَآ أَن رَّبَطۡنَا عَلَىٰ قَلۡبِهَا لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 28:10Zuciyar mahaifiyar Musa kuma ta wayi gari ba komai a cikinta (sai tunaninsa); ba shakka sauran ƙiris ta bayyana shi, ba don Mun ɗaure zuciyarta ba don ta zama cikin muminai.
وَقَالَتۡ لِأُخۡتِهِۦ قُصِّيهِۖ فَبَصُرَتۡ بِهِۦ عَن جُنُبٖ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 28:11Ta kuma ce da ‘yar’uwarsa: “Ki bi sawunsa”; sai ta hango shi daga nesa, su kuwa ba su gane ita (‘yar’uwarsa ba ce).
۞وَحَرَّمۡنَا عَلَيۡهِ ٱلۡمَرَاضِعَ مِن قَبۡلُ فَقَالَتۡ هَلۡ أَدُلُّكُمۡ عَلَىٰٓ أَهۡلِ بَيۡتٖ يَكۡفُلُونَهُۥ لَكُمۡ وَهُمۡ لَهُۥ نَٰصِحُونَ
Open ayah 28:12Da ma kuma can Mun haramta masa (nonon) masu shayarwa, sai (‘yar’uwar tasa) ta ce: “Yanzu ba na nuna muku mutanen wani gida da za su shayar muku da shi ba, su kuma za su kyautata masa?”
فَرَدَدۡنَٰهُ إِلَىٰٓ أُمِّهِۦ كَيۡ تَقَرَّ عَيۡنُهَا وَلَا تَحۡزَنَ وَلِتَعۡلَمَ أَنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 28:13Sai Muka dawo da shi wurin mahaifiyarsa don hankalinta ya kwanta kuma don kada ta yi baƙin ciki, don kuma ta san cewa alƙawarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancinsu ba sa fahimtar (haka). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin da mahaifiyar Annabi Musa ta shiga bayan jin cewa ya faɗa hannun babban maƙiyinsa Fir’auna wanda a koyaushe daga wannan lokacin zai iya hallaka shi kamar yadda ya saba yi ga ‘ya’yan Banu Isra’ila maza. Sai ta wayi gari zuciyarta fayau ba komai a cikinta na al’amarin duniya in ban da tunanin ɗanta Annabi Musa, har saura ƙiris ta fito ta bayyana cewa ɗanta ne fa saboda tsananin shaƙuwarta da shi, ba don an yi sa’a Allah ya danne mata zuciyarta ba ya sa mata dauriya da haƙuri don ta zama daga cikin bayinsa muminai masu dogara ga Allah, masu haƙuri a kan abin da ya hukunta. Bayan mahaifiyar Annabi Musa ta jefa shi a cikin ƙoramar Nilu sai ta aika ‘yar’uwarsa cewa ta bi sawunsa ba tare da ta yarda wani ya gane ita ‘yar’uwarsa ce ba. Sai ta bi sawunsa ta yadda take hango shi daga nesa kamar babu ruwanta da shi, ta zo wucewa ne kawai, Fir’auna da mutanensa ba su san abin da take ciki ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) cikin cikar Ƙudurarsa sai ya tsara wa Annabi Musa cewa ba zai karɓi nonon duk wata mai shayarwa ba da aka kawo masa don su shayar da shi a gidan Fir’auna. To lokacin da ‘yar’uwarsa ta fuskanci yadda suka damu da sai sun samar masa mai shayarwa, sai ta tambaye su ko suna son ta nuna musu mutanen wani gida waɗanda za su shayar musu da shi su kula da shi sosai su kyautata masa? Da man kuwa wannan ita ce babbar buƙatarsu saboda tsananin ƙaunar Annabi Musa da ta mamaye zukatansu. Nan take suka amsa mata, ita kuma ta nuna musu mutanen gidansu inda mahaifiyarsu take. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya dawo wa da mahaifiyar Annabi Musa ɗanta don ta yi farin cikin ganin sa a kusa da ita, ta kuma daina baƙin cikin rabuwa da shi, har ila yau kuma ta tabbatar da cewa alƙawarin da Allah ya yi mata na dawo mata da shi gaskiya ne babu wani kokwanto a cikinsa. Sai dai yawancin mutane ba su san da wannan alƙawarin ba sannan kuma ba su san cewa ita uwarsa ce ba.
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسۡتَوَىٰٓ ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 28:14Lokacin kuma da ya kai ganiyar ƙarfinsa ya kuma kammala, sai Muka ba shi hukunci da ilimi. Kamar haka kuwa Muke saka wa masu kyautatawa.
وَدَخَلَ ٱلۡمَدِينَةَ عَلَىٰ حِينِ غَفۡلَةٖ مِّنۡ أَهۡلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيۡنِ يَقۡتَتِلَانِ هَٰذَا مِن شِيعَتِهِۦ وَهَٰذَا مِنۡ عَدُوِّهِۦۖ فَٱسۡتَغَٰثَهُ ٱلَّذِي مِن شِيعَتِهِۦ عَلَى ٱلَّذِي مِنۡ عَدُوِّهِۦ فَوَكَزَهُۥ مُوسَىٰ فَقَضَىٰ عَلَيۡهِۖ قَالَ هَٰذَا مِنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِۖ إِنَّهُۥ عَدُوّٞ مُّضِلّٞ مُّبِينٞ
Open ayah 28:15Sai ya shiga cikin birnin a lokacin hutawar mutanensa, sai ya sami mutum biyu a cikinsa suna faɗa; wannan ɗan ƙabilarsa ne, wannan kuma daga maƙiyansa, sai ɗan ƙabilar tasa ya nemi taimakonsa a kan wanda yake daga maƙiyansa; to sai Musa ya naushe shi, sai kuwa ya kashe shi; (da ya ga haka sai) ya ce: “Wannan yana daga aikin Shaiɗan, lalle shi kuwa maƙiyi ne mai ɓatarwa na fili.”
قَالَ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي فَٱغۡفِرۡ لِي فَغَفَرَ لَهُۥٓۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 28:16Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na zalunci kaina, sai Ka yi min gafara,” sai ko Ya yi masa gafara. Lalle Shi kuwa Mai gafara ne, Mai jin ƙai.
قَالَ رَبِّ بِمَآ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ فَلَنۡ أَكُونَ ظَهِيرٗا لِّلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 28:17Ya ce: “Ya Ubangijina, saboda ni’imar da Ka yi min, ba zan taɓa zama mai taimakon masu laifi ba.” Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da rayuwa a gidan Fir’auna ƙarƙashin kulawar mahaifiyarsa da renonta, yana sanya tufafi irin na mutanen gidan Fir’auna, yana hawan abin hawa irin nasu, mahaifiyarsa kuwa hankalinta a kwance, domin tana tare da ɗanta a koyaushe, babu wata fargaba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana cewa yayin da Annabi Musa ya kai shekarun cikar ƙarfinsa sai ya ba shi fahimta da ilimin sanin addinin Banu Isra’ila tun gabanin a ba shi annabta. Allah ya tabbatar da cewa kamar yadda ya yi wa Annabi Musa irin wannan kyakkyawan sakamako saboda kyautatawarsa to hakanan yake saka wa duk wasu masu kyautatawa a kowane zamani a kuma kowane wuri. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da cewa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga cikin birnin Masar a lokacin da mutane suke gidajensu suna hutawa, sai ya ci karo da wasu mutane su biyu suna faɗa da doke-doke, ɗayansu daga ƙabilarsa ne Banu Isra’ila, ɗayan kuwa daga ƙabilar Ƙibɗawa mutanen Fir’auna abokan gabar Annabi Musa da jama’arsa ne. Sai ɗan ƙabilar Annabi Musa ya nemi taimakonsa a kan Baƙibɗe maƙiyinsu, sai Annabi Musa ya naushe shi da hannunsa sai ko wannan naushin ya yi sanadin mutuwarsa, sai Annabi Musa ya yi nadama da faruwar wannan abu, ya ce lallai wannan aikin Shaiɗan ne, maƙiyi mai ɓatarwa, mai bayyana adawarsa a fili ga mutane. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙi Ubangijinsa yana mai iƙirari da laifinsa a gabansa cewa lallai shi ya zalunci kansa da ya kashe wannan Baƙibɗe, don haka yana roƙon Allah ya gafarta masa zunubinsa. Allah kuwa ya tabbatar mana cewa ya gafarta wa Annabi Musa, lallai kuma shi mai gafara ne ga wanda ya tuba daga cikin bayinsa, mai jin ƙan su ne. Sannan Annabi Musa ya sake tabbatar wa da Allah cewa saboda ni’imar da ya yi masa ya ba shi ƙarfi da ilimi da hikima, ya yi alƙawarin ba zai taɓa zama mai taimakon masu aikata laifi ba.
فَأَصۡبَحَ فِي ٱلۡمَدِينَةِ خَآئِفٗا يَتَرَقَّبُ فَإِذَا ٱلَّذِي ٱسۡتَنصَرَهُۥ بِٱلۡأَمۡسِ يَسۡتَصۡرِخُهُۥۚ قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰٓ إِنَّكَ لَغَوِيّٞ مُّبِينٞ
Open ayah 28:18Sai ya wayi gari a cikin birnin a tsorace yana ɗar-ɗar, sai ga wanda ya nemi taimakon nan nasa a jiya yana sake neman taimakonsa, (sai) Musa ya ce da shi: “Lalle kai dai ɓatacce ne a fili!”
فَلَمَّآ أَنۡ أَرَادَ أَن يَبۡطِشَ بِٱلَّذِي هُوَ عَدُوّٞ لَّهُمَا قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ أَتُرِيدُ أَن تَقۡتُلَنِي كَمَا قَتَلۡتَ نَفۡسَۢا بِٱلۡأَمۡسِۖ إِن تُرِيدُ إِلَّآ أَن تَكُونَ جَبَّارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا تُرِيدُ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلۡمُصۡلِحِينَ
Open ayah 28:19To lokacin da ya nufi wawurar abokin gabar tasu (sai mai neman taimakon) ya ce: “Ya Musa, shin yanzu nufi kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe rai a jiya? Ba abin da kake nufi sai ka zama mai tsaurin rai a bayan ƙasa; ba ka kuma nufin ka zama cikin masu kawo gyara.”
وَجَآءَ رَجُلٞ مِّنۡ أَقۡصَا ٱلۡمَدِينَةِ يَسۡعَىٰ قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّ ٱلۡمَلَأَ يَأۡتَمِرُونَ بِكَ لِيَقۡتُلُوكَ فَٱخۡرُجۡ إِنِّي لَكَ مِنَ ٱلنَّٰصِحِينَ
Open ayah 28:20Sai wani mutum (mumini daga mutanen Fir’auna) ya zo daga can ƙarshen birnin yana gaggawa, ya ce: “Ya Musa, lalle manyan gari (suna can) suna shawara a kanka don su kashe ka, to ka fita (daga birnin nan), lalle ni ina cikin masu yi maka nasiha.”
فَخَرَجَ مِنۡهَا خَآئِفٗا يَتَرَقَّبُۖ قَالَ رَبِّ نَجِّنِي مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 28:21Sai ya fita daga cikinsa (wato birnin) a tsorace yana ta ɗar-ɗar, ya ce: “Ya Ubangijina, Ka tserar da ni daga azzaluman mutanen nan.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan abin da ya faru na kashe Baƙibɗe sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya wayi gari a cikin birnin Masar a tsorace yana zuba idon ya ga abin da zai biyo baya, sai kuma ga mutumin nan da ya nemi taimakonsa jiya a kan Baƙibɗe yau ma yana rigima da wani Baƙibɗen daban yana kuma neman taimakonsa, sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zarge shi da cewa lalle shi mutum ne ɓatacce matuƙa. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yunƙura zai rarumi wannan Baƙibɗe, sai Ba’isra’ilen ya zaci shi za a raruma, sai ya zargi Annabi Musa da cewa, yana son shi ma ya kashe shi ne kamar yadda ya kashe wani rai jiya? Ya ƙara da cewa lallai Annabi Musa yana nufin zama mutum mai tsaurin kai azzalumi a bayan ƙasa mai kashe mutane ba gaira ba dalili, kuma ba ya nufin ya zama mai kawo gyara a gari sai dai ya yi ɓarna. Daga nan fa sai labarin abin da Annabi Musa ya aikata ya bazu ya cika gari har ya kai kunnen Fir’auna da jama’arsa, nan da nan suka fara tattaunawa a asirce a kan za su kashe Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) amma kuma sai Allah ya ƙaddara wani mutum daga can ƙarshen birni ya ji abin da suke ƙulla wa Annabi Musa ya yi gaggawa ya zo wurinsa ya zayyana masa bayanin shawarar da manyan gari suka yanke na kashe shi, don haka ya yi masa nasihar cewa lalle ya fita daga wannan gari na Masar domin ya tsira da ransa. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya karɓi wannan nasihar ya kuma fita a tsorace yana tunanin abin da zai faru da shi, ya ɗaga hannu ya roƙi Allah ya tserar da shi daga azzaluman mutane masu nufin cutar da shi.
وَلَمَّا تَوَجَّهَ تِلۡقَآءَ مَدۡيَنَ قَالَ عَسَىٰ رَبِّيٓ أَن يَهۡدِيَنِي سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ
Open ayah 28:22Yayin da kuma ya sa gaba ya nufi wajen (birnin) Madyana, sai ya ce: “Ina fatan Ubangijina Ya shiryar da ni hanyar da ta fi dacewa.”
وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدۡيَنَ وَجَدَ عَلَيۡهِ أُمَّةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسۡقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمۡرَأَتَيۡنِ تَذُودَانِۖ قَالَ مَا خَطۡبُكُمَاۖ قَالَتَا لَا نَسۡقِي حَتَّىٰ يُصۡدِرَ ٱلرِّعَآءُۖ وَأَبُونَا شَيۡخٞ كَبِيرٞ
Open ayah 28:23Lokacin da kuma ya iso mashayar ruwa ta Madyana sai ya sami wani gungun mutane suna shayar (da dabbobinsu), ya kuma sami wasu mata su biyu a gefensu suna kare (dabbobinsu); sai ya ce (da su): “Me ya same ku ne?” Sai suka ce: “Mu ai ba ma shayarwa har sai duk makiyaya sun watse, kuma mahaifinmu tsoho ne tukub.”
فَسَقَىٰ لَهُمَا ثُمَّ تَوَلَّىٰٓ إِلَى ٱلظِّلِّ فَقَالَ رَبِّ إِنِّي لِمَآ أَنزَلۡتَ إِلَيَّ مِنۡ خَيۡرٖ فَقِيرٞ
Open ayah 28:24To sai ya shayar musu (da dabbobin nasu), sannan ya koma wurin wata inuwa ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni mabuƙacin duk wani alhairi ne da za ka hore mini!”
فَجَآءَتۡهُ إِحۡدَىٰهُمَا تَمۡشِي عَلَى ٱسۡتِحۡيَآءٖ قَالَتۡ إِنَّ أَبِي يَدۡعُوكَ لِيَجۡزِيَكَ أَجۡرَ مَا سَقَيۡتَ لَنَاۚ فَلَمَّا جَآءَهُۥ وَقَصَّ عَلَيۡهِ ٱلۡقَصَصَ قَالَ لَا تَخَفۡۖ نَجَوۡتَ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 28:25Sai ɗayarsu ta zo masa tana tafiya cikin jin kunya ta ce: “Babana yana kiran ka don ya saka maka ladan shayarwar da ka yi mana.” To lokacin da ya zo wurinsa ya kuma ba shi labarin(sa) sai ya ce da shi: “Kada ka ji tsoro, ka tsira daga azzaluman mutane.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fita daga Masar ya kama hanyar Madyana sai ya roƙi Allah Ubangijinsa cewa ya shiryar da shi hanyar da ta fi dacewa domin samun kuɓuta daga azzalumai. Allah ya ci gaba da cewa, lokacin da Annabi Musa ya isa garin Madyana ya nufi wata rijiya inda ya sami mutanen garin suna shayar da dabbobinsu, a gefe guda kuma sai ya hango wasu mata su biyu zaune suna tsare da dabbobinsu ba su gauraya da sauran mutane ba, sai ya matsa kusa ya tambaye su ko me ya sa ba su shiga tare da mutane su shayar da dabbobinsu ba? Sai suka amsa masa da cewa ai sun saba da man haka suke yi, ba sa shayar da dabbobinsu har sai kowa ya watse don gudun cakuɗuwa da maza. Sannan suka faɗi uzurin mahaifinsu da yake aiko su suna mata shi ba ya zuwa da kansa da cewa, mahaifinsu tsoho ne tukub ba zai iya aikin shayar da dabbobi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Musa ya tausaya wa ‘yan matan nan, ya shayar musu da dabbobinsu ba tare da ya nemi wani lada a wajensu ba, daga nan ya koma wata inuwa domin ya huta saboda tsananin zafin rana da ake yi a lokacin. A nan ne ya roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) da ya hore masa abincin da zai ci domin yana cikin matsananciyar buƙata. To waɗannan ‘yan mata kuwa sai suka koma gida suka ba wa mahaifinsu labarin duk abin da ya faru tsakaninsu da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sai ya aika ɗaya daga cikinsu zuwa gare shi domin ta kirawo masa shi, sai ta zo masa tana tafiya cikin jin kunya ta gaya masa cewa mahaifinta yana kiran sa don ya biya shi ladan shayar musu da dabbobi da ya yi. Annabi Musa ya amsa wannan kira nasa ya kuma je ya ba shi labarinsa gaba ɗaya, sai wannan tsoho mutumin kirki ya kwantar wa da Annabi Musa hankali ya nuna masa kada ya ji wani tsoro, ya tabbatar masa cewa ya tsira daga azzaluman mutane, watau Fir’auna da rundunarsa domin ba su da wani iko da garin Madyana, don haka ba za su iya cutar da shi ba.
قَالَتۡ إِحۡدَىٰهُمَا يَٰٓأَبَتِ ٱسۡتَـٔۡجِرۡهُۖ إِنَّ خَيۡرَ مَنِ ٱسۡتَـٔۡجَرۡتَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡأَمِينُ
Open ayah 28:26Sai ɗayarsu ta ce: “Babana, ka ɗauke shi aiki mana; don kuwa lalle ba wanda ya fi dacewa ka ɗauka aiki sai ƙaƙƙarfa, amintacce.”
قَالَ إِنِّيٓ أُرِيدُ أَنۡ أُنكِحَكَ إِحۡدَى ٱبۡنَتَيَّ هَٰتَيۡنِ عَلَىٰٓ أَن تَأۡجُرَنِي ثَمَٰنِيَ حِجَجٖۖ فَإِنۡ أَتۡمَمۡتَ عَشۡرٗا فَمِنۡ عِندِكَۖ وَمَآ أُرِيدُ أَنۡ أَشُقَّ عَلَيۡكَۚ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 28:27Sai ya ce da (Musa): “Ina so in aura maka ɗaya daga ‘ya’yayen nan nawa guda biyu, a kan ka yi min aiki na shekara takwas; to amma idan ka cika goma to wannan raɗin kanka ne; ba na kuwa nufin in ƙuntata maka. Za ka same ni kuwa in Allah Ya yarda daga cikin nagartattun mutane.”
قَالَ ذَٰلِكَ بَيۡنِي وَبَيۡنَكَۖ أَيَّمَا ٱلۡأَجَلَيۡنِ قَضَيۡتُ فَلَا عُدۡوَٰنَ عَلَيَّۖ وَٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٞ
Open ayah 28:28(Musa) ya ce: “Wannan tsakanina da kai ne; kowanne ɗayan lokatan biyu na cika to kada a ƙware ni; Allah kuwa shaida ne game da abin da muke faɗa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ɗaya daga ‘yan matan nan biyu ta roƙi mahaifinta da ya ɗauki Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) aiki don ya riƙa yi musu kiwon dabbobinsu, domin tana ganin lalle ya cancanci ya yi wannan aiki saboda shi mutum ne da ya haɗa ƙarfi na jiki da kuma amana. Da ƙarfinsa zai yi duk abin da aka buƙaci ya yi, sannan kuma da amanarsa zai tsare musu dukiyarsu ba zai ha’ince su ba. Sai mahaifinta ya amince da wannan shawara da ‘yarsa ta ba shi, ya sanar da Annabi Musa cewa yana da niyyar zai aura masa ɗaya daga ‘ya’yan nasa, amma sadakinta shi ne ya yi masa kiwon dabbobinsa na tsawon shekara takwas, sai dai in ya ga dama bisa raɗin kansa ya cike shekarun suka kai goma to wannan zaɓinsa ne kuma kyautatawa ce daga wurinsa ba dole ba ne, kuma shi ba ya son ya ƙuntata masa. Sannan ya tabbatar masa da cewa lalle zai same shi daga cikin mutane nagari masu cika alƙawari idan sun ɗauka. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ba shi amsa da cewa wannan tsakaninsa ne da shi, ya kuma amince da sharaɗinsa, kuma duk ɗayan lokutan biyu da ya ga dama ya ɗauka, shekara takwas ko goma, to ya sauke nauyin da ke kansa, kada kuma a nemi ƙarin wani lokaci a wurinsa ko a ƙware shi. Shi ma ya tabbatar masa da cewa lalle Allah ne wakili a kan duk wata yarjejeniya da za su ƙulla a tsakaninsu.
۞فَلَمَّا قَضَىٰ مُوسَى ٱلۡأَجَلَ وَسَارَ بِأَهۡلِهِۦٓ ءَانَسَ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ نَارٗاۖ قَالَ لِأَهۡلِهِ ٱمۡكُثُوٓاْ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا لَّعَلِّيٓ ءَاتِيكُم مِّنۡهَا بِخَبَرٍ أَوۡ جَذۡوَةٖ مِّنَ ٱلنَّارِ لَعَلَّكُمۡ تَصۡطَلُونَ
Open ayah 28:29To yayin da Musa ya cika lokacinsa ya kuma tafi da iyalinsa, sai ya hango wuta daga gefen (dutsen) Ɗuri, ya ce: “Lalle na hango wuta, (zan je don) in zo muku da labari daga wurinta ko kuma (in samo muku) wani garwashi na wutar don ku ji ɗumi.”
فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِيَ مِن شَٰطِيِٕ ٱلۡوَادِ ٱلۡأَيۡمَنِ فِي ٱلۡبُقۡعَةِ ٱلۡمُبَٰرَكَةِ مِنَ ٱلشَّجَرَةِ أَن يَٰمُوسَىٰٓ إِنِّيٓ أَنَا ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 28:30To lokacin da ya zo wurinta sai aka yi kira daga gefen kwari na damarsa a wani wuri mai albarka na bishiya, cewa: “Ya Musa, lalle Ni ne Allah Ubangijin talikai!
وَأَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۚ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهۡتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنّٞ وَلَّىٰ مُدۡبِرٗا وَلَمۡ يُعَقِّبۡۚ يَٰمُوسَىٰٓ أَقۡبِلۡ وَلَا تَخَفۡۖ إِنَّكَ مِنَ ٱلۡأٓمِنِينَ
Open ayah 28:31“Kuma ka jefar da sandarka;” to lokacin da ya gan ta tana girgiza kamar maciji sai ya ba da baya a guje, bai ko waiwaya ba. (Aka ce da shi): “Ya Musa dawo, kada ka ji tsoro; lalle kai kana cikin amintattu.
ٱسۡلُكۡ يَدَكَ فِي جَيۡبِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٖ وَٱضۡمُمۡ إِلَيۡكَ جَنَاحَكَ مِنَ ٱلرَّهۡبِۖ فَذَٰنِكَ بُرۡهَٰنَانِ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Open ayah 28:32“Ka sanya hannunka a cikin wuyan rigarka, zai fito fari fat ba tare da wata cuta ba, kuma ka haɗe hannunka da kwiɓinka saboda tsoron (farinta); to biyu ɗin nan hujjoji ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir’auna da mutanensa. Lalle su sun kasance mutane ne fasiƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya cika lokacin da suka yi yarjejeniya a kansa da wannan tsoho mutumin kirki. Bisa ga kyakkyawan zato ga Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi masa aiki ne na shekara goma don kyautata masa. Daga baya Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tuna gida, don haka begen danginsa ya kama shi sai ya ɗauki iyalansa daga Madyana ya nufi komawa da su ƙasar Masar, domin a zatonsa cewa tsawon lokacin da ya ɗauka ba ya ƙasar zai sa su manta da duk wani abu da ya faru a baya. Yana tsakiyar tafiya ne a cikin sahara cikin wani dare mai sanyi sai ya hango wuta a kusa da dutsen Ɗuri. Sai ya umarci iyalansa da su zauna nan inda suke domin ya tafi ya duba wannan wuta da ya hango, wataƙila ya samo musu labarin hanyar da za ta kai su Masar ko kuma ya zo musu da garwashin wuta wanda za su ɗumama jikinsu saboda sanyi. To lokacin da Annabi Musa ya iso wajen wannan wuta sai Ubangijinsa (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo shi daga gefen kwari na dama a wannan wuri mai bishiya da Allah ya yi wa albarka da magana da shi, ya kuma kirawo shi da sunansa Musa, ya kuma tabbatar masa cewa shi ne Allah Ubangijin halittu. A nan ne ya umarce shi da ya jefar da sandar da take a hannunsa, nan take ya bi umarnin Allah ya jefar da ita ƙasa, sai kawai ya ga ta rikiɗe ta zama macijiya tana motsi tana gudu da sauri. Ganin haka sai ya tsorata ya juya baya da gudu bai dawo ba har sai da Ubangijinsa ya kirawo shi da cewa ya dawo kada kuma ya ji wani tsoro, domin lalle yana cikin amintattu waɗanda Allah yake ba su kariya. Sannan kuma Allah ya umarce shi da ya shigar da hannunsa a cikin wuyan rigarsa zai ga hannun ya fito fari fat ba tare da wata cuta ba kamar albaras. Nan take kuwa sai ya sanya hannunsa a cikin wuyan rigarsa, da ya fito da shi sai ya gan shi fari sol kamar ƙanƙara. Daga nan sai Allah ya umarce shi da ya haɗa hannunsa da gefen jikinsa domin ya daina jin tsoro da faɗuwar gaba. Allah ya tabbatar masa cewa waɗannan abubuwa biyu da ya ba shi, watau rikiɗewar sanda ta zama macijiya da kuma hannu mai haske kamar fitila, wasu hujjoji ne guda biyu daga Ubangijinsa da zai tafi da su wajen Fir’auna da jama’arsa, ya tabbatar masa cewa lalle Fir’auna da manyan fadawansa sun tabbata mutane ne fasiƙai waɗanda suka kangare wa Allah ta hanyar kafirci da yawan saɓonsa.
قَالَ رَبِّ إِنِّي قَتَلۡتُ مِنۡهُمۡ نَفۡسٗا فَأَخَافُ أَن يَقۡتُلُونِ
Open ayah 28:33(Musa) ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na kashe musu wani mutum, to ina tsoron su kashe ni.
وَأَخِي هَٰرُونُ هُوَ أَفۡصَحُ مِنِّي لِسَانٗا فَأَرۡسِلۡهُ مَعِيَ رِدۡءٗا يُصَدِّقُنِيٓۖ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
Open ayah 28:34“Kuma ɗan’uwana Haruna shi ya fi ni fasahar harshe, sai Ka aike shi tare da ni ya zama mataimakina yana gaskata ni; lalle ni ina jin tsoron su ƙaryata ni.”
قَالَ سَنَشُدُّ عَضُدَكَ بِأَخِيكَ وَنَجۡعَلُ لَكُمَا سُلۡطَٰنٗا فَلَا يَصِلُونَ إِلَيۡكُمَا بِـَٔايَٰتِنَآۚ أَنتُمَا وَمَنِ ٱتَّبَعَكُمَا ٱلۡغَٰلِبُونَ
Open ayah 28:35(Sai Allah) Ya ce: “Za Mu ƙarfafa dantsenka da ɗan’uwanka kuma za Mu sanya muku wata hujja, don haka ba za su isa gare ku (da cuta) ba. Da ayoyinmu - ku da waɗanda suka bi ku - ku ne masu yin galaba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya fahimci nauyin da Allah ya ɗora masa, sai kuma ya nemi wasu buƙatu daga Ubangijinsa. Da farko ya koka masa cewa a can baya fa ya taɓa kashe musu mutum, don haka yanzu yana tsoron idan ya je isar musu da saƙon Allah za su iya kashe shi. Abu na biyu ya nemi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafe shi da ɗan’uwansa Haruna saboda ya fi shi fasahar harshe, don haka ya buƙaci ya aika su tare don ya riƙa gaskata maganarsa idan Fir’auna da mutanensa sun ƙaryata shi. Ya kuma nanata tsoronsa na cewa Fir’auna da mutanensa za su ƙaryata shi, domin wannan ita ce al’adar al’ummun da Allah ya aika wa annabawa a gabaninsa, watau ƙaryata manzanninsu. Sai ko Allah ya amsa masa roƙonsa, ya tabbatar masa da cewa zai ƙara masa ƙarfi ta hanyar haɗa ɗan’uwansa tare da shi, kuma zai ba su wata hujja mai ƙarfi, don haka Fir’auna da fadawansa ba za su iya isa gare su ba balle su cutar da su. Sannan a dalilin waɗannan ayoyi da Allah ya aiko su da su, su ne da mabiyansu za su yi rinjaye su sami nasara a kan maƙiyansu.
فَلَمَّا جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا بَيِّنَٰتٖ قَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّفۡتَرٗى وَمَا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِيٓ ءَابَآئِنَا ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 28:36To lokacin da Musa ya zo musu da ayoyinmu mabayyana sai suka ce: “Ai wannan ba wani abu ba ne face ƙagaggen sihiri, mu kuma ba mu taɓa jin wannan ba a wurin iyayenmu na farko.”
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ مِنۡ عِندِهِۦ وَمَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 28:37Musa kuma ya ce: “Ubangijina (Shi ne) Ya fi sanin wanda ya zo da shiriya daga wurinsa, da kuma wanda kyakkyawan ƙarshe zai kasance a gare shi; lalle yadda al\'amarin yake, azzalumai ba sa rabauta.”
وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ مَا عَلِمۡتُ لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرِي فَأَوۡقِدۡ لِي يَٰهَٰمَٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجۡعَل لِّي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Open ayah 28:38Fir’auna kuma ya ce: “Ya ku manyan gari, ban san kuna da wani abin bauta ba in ba ni ba, kai ko Hamana, shirya min ƙonannen taɓo sannan ka yi min dogon gini don in hango abin bautar Musa, lalle ni ina tsammanin cewa shi yana cikin maƙaryata.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da Annabi Musa ya zo wa Fir’auna da mutanensa tare da hujjoji bayyanannu sai suka ƙaryata shi suka zarge shi da cewa abin da ya zo da shi wani sihiri ne da shi ya ƙirƙira da kansa, kuma ma su ba su taɓa jin irin wannan maganar ta Annabi Musa a wurin iyayensu na farko ba, watau su dai ba su taɓa jin an ce abin bauta ɗaya ne ba tunda suke, don haka Annabi Musa ƙarya kawai yake shara musu. Sai Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar musu da martani inda ya tabbatar musu da cewa Allah Ubangijinsa shi ne ya fi sanin wanda ya zo da shiriya daga wurinsa, ya kuma fi sanin wanda zai yi kyakkyawan ƙarshe a lahira, amma ko shakka babu su azzaluman mutane ba za su taɓa rabauta ba ta samun biyan buƙatarsu kuma su kuɓuta daga abin da suke tsoro. To amma maimakon waɗannan maganganu na hankali da Fir’auna ya ji daga Annabi Musa su sanya jikinsa ya yi sanyi, sai girman kansa da rashin kunyarsa ga mahaliccinsa suka ƙaru, ya kira manyan fadawansa ya ƙara jaddada musu cewa shi fa bai san suna da wani abin bauta ba wanda ba shi ba. Sannan ya kirawo babban wazirinsa Hamana ya umarce shi da ya shirya ƙanannun tubala masu ƙarfi domin ya gina masa doguwar hasumiya da zai hau kanta wataƙila ya samu hango abin bautar Annabi Musa. Daga ƙarshe ma ya nuna cewa shi a zatonsa Annabi Musa maƙaryaci ne kawai yake da’awar cewa Allah ne ya aiko shi zuwa gare su shi da mutanensa.
وَٱسۡتَكۡبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُۥ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ إِلَيۡنَا لَا يُرۡجَعُونَ
Open ayah 28:39Ya kuma yi girman kai shi da rundunoninsa a ƙasar (Masar) ba da gaskiya ba, suka kuma yi tsammanin cewa su ba za a komar da su zuwa gare Mu ba.
فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 28:40Sai Muka kama shi da rundunoninsa, sannan Muka watsa su a cikin kogi; to ka duba ka ga yadda ƙarshen azzalumai ya kasance.
وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَئِمَّةٗ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلنَّارِۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا يُنصَرُونَ
Open ayah 28:41Muka kuma mayar da su shugabanni masu kira zuwa ga wuta; ranar alƙiyama kuma ba za a taimake su ba.
وَأَتۡبَعۡنَٰهُمۡ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا لَعۡنَةٗۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ هُم مِّنَ ٱلۡمَقۡبُوحِينَ
Open ayah 28:42Muka kuma bi su da la’anta a wannan duniyar; ranar alƙiyama kuma suna cikin waɗanda za a jefa cikin mummunan hali. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa girman kan Fir’auna da rundunarsa ya ƙara tsananta a ƙasar Masar ba tare da wata hujja ta gaskiya ba, suka kuma musanta tashi bayan mutuwa, suka yi tsammani cewa babu ranar alƙiyama ballantana a yi musu hisabi ko uƙuba a kan aika-aikar da suke yi a nan duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya damƙi Fir’auna da rundunoninsa ya watsa su a cikin kogi gaba ɗayansu suka hallaka. Daga nan ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya duba ya ga yadda ƙarshen azzalumai ya kasance, domin a fahimci cewa wannan ita ce sunnar Allah ga duk wanda yake ƙaryata manzanninsa da ayoyinsa. Allah kuma ya bayyana cewa ya ƙaddara Fir’auna shi da manyan mataimakansa su kasance jagorori ababen koyi ga sauran ɓatattu da azzalumai, masu kiran mutane zuwa ga wuta ta hanyar abin da suke yaɗawa na kafirci da saɓon Allah a bayan ƙasa. Sannan kuma idan sun je lahira ba su da masu taimakon su don su kuɓutar da su daga azabar Allah, sai dai ma a ƙara ninninka musu mummunar azaba saboda munanan ayyuka da aƙidu da suka shuka a bayan ƙasa suka kuma riƙa jan mutane cikinsu. To a kan haka za a rubuta musu mummunan sakamakonsu da kuma sakamakon waɗanda suka yi koyi da su wajen aiki irin nasu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya bi su da la’anta da wulaƙanci tun a nan duniya, a ranar alƙiyama kuma suna daga cikin waɗanda za su fuskanci mummunan hali da nesantawa daga rahamar Allah.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ مِنۢ بَعۡدِ مَآ أَهۡلَكۡنَا ٱلۡقُرُونَ ٱلۡأُولَىٰ بَصَآئِرَ لِلنَّاسِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لَّعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 28:43Haƙiƙa kuma Mun bai wa Musa littafin (Attaura) bayan Mun hallaka al’ummu na farko don izina ga mutane da shiriya da rahama ko sa wa’azantu.
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلۡغَرۡبِيِّ إِذۡ قَضَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَى ٱلۡأَمۡرَ وَمَا كُنتَ مِنَ ٱلشَّٰهِدِينَ
Open ayah 28:44Kai kuma ba ka kasance a gefen (dutsen Ɗuri) na yamma ba lokacin da Muka yo wahayin manzanci zuwa ga Musa, ba ka kuma kasance cikin mahalarta wurin ba.
وَلَٰكِنَّآ أَنشَأۡنَا قُرُونٗا فَتَطَاوَلَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡعُمُرُۚ وَمَا كُنتَ ثَاوِيٗا فِيٓ أَهۡلِ مَدۡيَنَ تَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِنَا وَلَٰكِنَّا كُنَّا مُرۡسِلِينَ
Open ayah 28:45Sai dai cewa Mu Mun halicci al’ummu, sai nisan zamani ya tsawaita a gare su. Kuma ba ka kasance a zaune cikin mutanen Madyana ba kana karanta musu ayoyinmu, sai dai kuma Mu Mun kasance Masu aiko da (manzanni).
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلطُّورِ إِذۡ نَادَيۡنَا وَلَٰكِن رَّحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أَتَىٰهُم مِّن نَّذِيرٖ مِّن قَبۡلِكَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 28:46Kuma ba ka kasance a gefen (dutsen) Ɗuri ba, lokacin da Muka kirawo (Musa), sai dai wata rahama daga Ubangijinka, don ka gargaɗi wasu mutane da mai gargaɗi bai zo musu ba gabaninka ko sa wa’azantu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimar da ta sa aka bai wa Annabi Musa littafin Attaura aka kuma aika shi zuwa ga Banu Isra’ila. Hikimar ita ce ya ba shi Attaura ne bayan ya aika manzanni daban-daban zuwa ga al’ummun da suka gabace shi amma suka ƙaryata su sai Allah ya hallaka su. A cikin littafin Attaura an bayyana wa mutane duk abin da zai amfane su don su riƙe shi da abin da zai cutar da su don su guje shi, sannan kuma rahama ne wanda ya ƙunshi alherin duniya da lahira gare su, domin su wa’azantu su riƙa tuntuntuni game da ni’imomin Allah gare su su kuma gode masa su yi imani da shi. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah bai hallaka wasu mutane ko wata al’umma da wata azaba daga sama ba tun bayan da ya saukar da Attaura a bayan ƙasa in ban da mutanen alƙaryar da aka mayar da su birrai. Shin ba ka ga faɗar Allah ba da yake cewa: “Haƙiƙa Mun bai wa Musa littafin (Attaura) bayan Mun hallaka al’ummu na farko don ya zama izina ga mutane da shiriya da rahama don su wa’azantu?” [Al-Hakim, Al-Mustadrak , Juzu’i na 2, Shafi na 408]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Manzonsa cewa bai kasance a gefen dutsen Ɗuri da ke yamma da Annabi Musa ba lokacin da ya yi masa wahayin manzanci zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa; watau ba ya wurin ballantana har ya san wannan labarin ya kuma bayar da shi ga mutane, sai dai abin da duk yake faɗa musu wahayi ne Allah ya yi masa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa buƙata ce ta kama kan aiko da manzo domin Allah ya halicci al’ummu da yawa bayan Annabi Musa sai lokaci ya tsawaita a gare su har suka manta da alƙawuran da suka yi tsakaninsu da Allah; ilimi ya yi ƙaranci sosai; buƙatar aiko da wani manzo ta tsananta, don haka Allah ya aiko da Annabi Muhammad (ﷺ) ya saukar masa da wahayi. Allah kuma ya bayyana wa Manzonsa cewa bai kasance yana zaune a cikin mutanen Madyana yana karantar da su ayoyin Allah ba, sai dai ya aiko shi ne daga wurinsa ya kuma yi masa wahayin labarin Annabi Musa da zamansa a garin Madyana, shi kuma ya sanar da mutane wannan labari da aka yi masa wahayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake jaddada wa Manzonsa (ﷺ) cewa bai kasance a gefen dutsen Ɗuri ba lokacin da Allah ya kirawo Annabi Musa ya yi masa wahayinsa a lokacin ballantana ya riƙa ba wa mutane labarin abin da ya faru, sai dai ya aiko shi don ya zama rahama daga gare shi zuwa ga mutane, ya kuma yi masa wahayin duk abubuwan da suka faru da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don ya gargaɗi wasu mutane waɗanda mai gargaɗi bai zo musu ba gabaninsa, watau Ƙuraishawa da kuma Larabawa domin su wa’azantu da abin da za su ji daga wajensa.
وَلَوۡلَآ أَن تُصِيبَهُم مُّصِيبَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ فَيَقُولُواْ رَبَّنَا لَوۡلَآ أَرۡسَلۡتَ إِلَيۡنَا رَسُولٗا فَنَتَّبِعَ ءَايَٰتِكَ وَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 28:47Kuma ba don kada wata masifa ta same su ba saboda abin da suka aikata da kansu sai su riƙa cewa: “Ya Ubangijinmu, ina ma da Ka aiko mana da wani manzo, da sai mu bi ayoyinka mu kuma kasance cikin muminai?”
فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ مِنۡ عِندِنَا قَالُواْ لَوۡلَآ أُوتِيَ مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ مُوسَىٰٓۚ أَوَلَمۡ يَكۡفُرُواْ بِمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ مِن قَبۡلُۖ قَالُواْ سِحۡرَانِ تَظَٰهَرَا وَقَالُوٓاْ إِنَّا بِكُلّٖ كَٰفِرُونَ
Open ayah 28:48To lokacin da gaskiya ta zo musu daga wajenmu sai suka ce: “Ina ma da an ba shi irin abin da aka bai wa Musa?” Yanzu ashe tun da can ba su kafirce da abin da aka bai wa Musa ba; suka ce: “Su biyun sihiri ne (wato Alƙur’ani da Attaura) da suke taimakon juna?” Suka kuma ce: “Lalle mu mun kafirce da su gaba ɗaya.”
قُلۡ فَأۡتُواْ بِكِتَٰبٖ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ هُوَ أَهۡدَىٰ مِنۡهُمَآ أَتَّبِعۡهُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 28:49Ka ce (da su): “To ku zo da wani littafi daga wajen Allah wanda ya fi su nuna hanyar shiriya (wato Alƙur’ani da Attaura), zan bi shi idan kun kasance masu gaskiya.”
فَإِن لَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكَ فَٱعۡلَمۡ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيۡرِ هُدٗى مِّنَ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 28:50To idan ba su amsa maka ba, to ka sani cewa ba abin da suke bi sai soye-soyen zukatansu kawai. Ba kuwa wanda ya fi ɓacewa kamar wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da wata shiriya daga Allah ba. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.
۞وَلَقَدۡ وَصَّلۡنَا لَهُمُ ٱلۡقَوۡلَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 28:51Haƙiƙa kuma Mun saukar musu da Alƙur’ani (guntu-guntu) don su wa’azantu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimar aiko Manzon Allah (ﷺ), watau don yanke hanzarin kafirai. Domin da a ce wata azaba ta sauka a kansu saboda kafircinsu da yawan saɓon Allah da suke yi, to da sai su ce me ya sa Allah bai aiko musu da wani manzo ba wanda zai gargaɗe su ya tsoratar da su azabar Allah? Ai da haka ya faru da sun bi ayoyin da ya zo musu da su sun yi aiki da su sun kuma kasance daga cikin muminai masu bin umarnin Ubangijinsu. To ba don wannan ba da ya gaggauto musu azaba ya hallaka su, to amma ya jinkirta musu har sai da ya aiko musu da manzo daga cikinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo wa Ƙuraishawa da saƙo daga Allah, sai suka tambayi Yahudawa game da shi, su kuma sai suka nuna musu hanyar da za su ƙalubalance shi da ita, watau su tambaye shi cewa ko shi an ba shi irin mu’ujizojin da aka ba wa Annabi Musa, kamar sandarsa mai rikiɗewa ta zama macijiya da hannunsa mai haske kamar fitila ba tare da wata cuta ba? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya mayar musu da martani da cewa, ashe a baya can ba sun kafirce wa Attaura da aka ba wa Annabi Musa ba? Kuma yayin da Annabi ya zo musu da Alƙur’ani shi ma ai watsi suka yi da shi, har ma suka ce wai Attaura da Alƙur’anin ai dukkansu sihiri ne masu taimaka wa juna, don haka su ba su yi Imani da ko ɗaya daga cikinsu ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya neme su da su kawo wani littafin daga Allah wanda ya fi Attaura da Alƙur’ani nuna hanyar shiriya; idan kuwa har sun zo da shi to shi ma Manzon Allah (ﷺ) zai bi shi ya yi imani da shi, idan har su masu gaskiya ne a kan maganar da suke faɗa game da su, watau Attaura da Alƙur’ani. Sai kuma ya bayyana musu cewa idan har sun kasa amsa wannan ƙalubale da ya yi musu, watau sun gaza kawo wani littafi wanda ya fi Attaura da Alƙur’ani shiriya, to ya tabbatar da cewa ba su da wani dalili na ƙaryata shi in ban da bin son zuciya kawai, kuma lalle su sani cewa babu ɓataccen mutum da ya kai ga mai bin son zuciyarsa ya bar shiriya ta Allah da ta zo masa. Lalle kuma Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai waɗanda suka cuci kansu da kafirci da saɓon Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimar saukar da Alƙur’ani guntu-guntu har ya cika ya haɗu da juna, da cewa, ya yi musu haka ne don su wa’azantu da abin da yake cikinsa su yi imani da shi.
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 28:52Waɗanda Muka bai wa littafi a gabaninsa (Alƙur’ani) (suka tsaya a kansa) su suna yin imani da shi (Alƙur’ani).
وَإِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلِهِۦ مُسۡلِمِينَ
Open ayah 28:53Idan kuma ana karanta musu (Alƙur’anin) sai su ce: “Mun yi imani da shi, lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinmu, lalle mu mun kasance Musulmi tun gabaninsa.”
أُوْلَٰٓئِكَ يُؤۡتَوۡنَ أَجۡرَهُم مَّرَّتَيۡنِ بِمَا صَبَرُواْ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Open ayah 28:54Waɗannan (su ne) za a ba su ladansu ninki biyu saboda haƙurin da suka yi. Kuma suna kawar da mummunan aiki da kyakkyawa, suna kuma ciyarwa daga abin da Muka arzuta su (da shi).
وَإِذَا سَمِعُواْ ٱللَّغۡوَ أَعۡرَضُواْ عَنۡهُ وَقَالُواْ لَنَآ أَعۡمَٰلُنَا وَلَكُمۡ أَعۡمَٰلُكُمۡ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡ لَا نَبۡتَغِي ٱلۡجَٰهِلِينَ
Open ayah 28:55Idan kuma suka ji maganar banza sai su kau da kai daga gare ta, sai kuma su ce: “(Sakamakon) ayyukanmu yana gare mu, ku kuma na ayyukanku yana gare ku, kun kuɓuta daga gare mu, ba ruwanmu da wawaye!” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wasu daga ma’abota littafi, watau Yahudawa waɗanda suka ci gaba da riƙo da Attaura suna yin imani da gaskiya tun gabanin a saukar da Alƙur’ani; to su waɗannan suna yin imani da abin da suka gani a littafinsu na labarin Manzon Allah da Alƙur’ani da siffofinsa. Kuma idan ana karanta musu Alƙur’ani sai su nuna cewa su lalle sun yi imani da shi, kuma lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinsa, kuma su tun da ma can sun kasance Musulmi ne, domin sun riga sun yi imani da duk abin da manzanni suka zo musu da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗannan masu irin wannan siffar zai ninka musu ladan aikinsu sau biyu, na farko saboda haƙurin da suka yi na tsayawa kyam a kan imaninsu da duk abin da ya zo musu a cikin littafinsu; na biyu kuma saboda imanin da suka yi da Annabi (ﷺ) da Alƙur’ani bayan an aiko shi da shi. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mutum uku ana ba su ladansu sau biyu: Mutum daga cikin ma’abota littafi wanda ya yi imani da annabinsa ya kuma yi imani da ni; da bawan da ya bayar da haƙƙin Allah ya kuma bayar da haƙƙin iyayen gidansa; da kuma mutumin da yake da baiwa sai ya yi mata kyakkyawar tarbiyya sannan ya ‘yanta ta ya kuma aure ta.” [Bukhari #97 da Muslim #154]. An karɓo daga Abu Umama Al-Bahili ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya musulunta daga cikin ma’abota littattafai biyu (Attaura da Linjila), to yana da ladansa sau biyu, yana da abin da muke da shi na haƙƙoƙi, kuma abin da ya wajaba kanmu shi ma ya wajaba a kansa, kuma duk wanda ya musulunta daga cikin mushirikai, to yana da ladansa, yana da abin da muke da shi na haƙƙoƙi, kuma abin da ya wajaba a kanmu shi ma ya wajaba a kansa.” [Ahmad #22234]. Sai kuma ya nuna sifarsu da cewa suna kawar da laifuffukan da suka yi ta hanyar aikata kyawawan ayyuka, kuma suna ciyar da abin da Allah ya arzuta su da shi a wajen ayyukan alheri. Sannan Allah ya ci gaba da faɗar kyawawan halayen waɗannan mutane da cewa, su ne waɗanda idan suka ji maganar banza sukan kau da kai daga gare ta ba za su tanka ba ko su rama; sukan faɗa wa masu irin wannan maganar cewa kowa ya je da halinsa; su ayyukansu da suka aikata a kansu ne za a saka musu, su ma a kan ayyukansu za a yi musu sakayya; babu wanda za a ba shi ladan wani ko a yi masa uƙuba saboda laifin wani. Suka kuma nuna musu cewa sun kuɓuta daga gare su; ba za su zage su ba ba za su cuce su ba, kuma su ba sa neman su yi abota da jahilai, domin yin haka zai cutar da su a rayuwarsu ta duniya da ta addini.
إِنَّكَ لَا تَهۡدِي مَنۡ أَحۡبَبۡتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ
Open ayah 28:56Lalle kai ba ka iya shiryar da wanda ka so, sai dai Allah ne Yana shiryar da wanda Ya ga dama. Shi kuma ne Ya san masu shiryuwa.
وَقَالُوٓاْ إِن نَّتَّبِعِ ٱلۡهُدَىٰ مَعَكَ نُتَخَطَّفۡ مِنۡ أَرۡضِنَآۚ أَوَلَمۡ نُمَكِّن لَّهُمۡ حَرَمًا ءَامِنٗا يُجۡبَىٰٓ إِلَيۡهِ ثَمَرَٰتُ كُلِّ شَيۡءٖ رِّزۡقٗا مِّن لَّدُنَّا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 28:57Suka kuma ce: “Idan har Muka bi shiriya tare da kai, to za a kame mu (ribatattu) daga ƙasarmu”. (Ka ce da su): “Yanzu ashe ba Mu ne Muka ba su ikon Harami amintacce ba da ake kawo kowanne irin (nau’i) na ‘ya’yan itace gare shi don arzutawa daga gare Mu?” Sai dai kuma yawancinsu ba sa sanin (haka). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Manzonsa cewa shi ba zai iya shiryar da wanda yake so ba ya sanya shi ya yi imani da Allah da abin da aka aiko shi da shi na gaskiya; Allah ne kaɗai yake iya shiryar da wanda ya ga dama, sai ya datar da shi ya karɓi shiriyarsa, kuma shi ne ya fi kowa sanin masu shiryuwa daga cikin bayinsa. An karɓo daga Al-Musayyab ɗan Hazn Al-Makhzumi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da Abu Ɗalib ya zo mutuwa sai Manzon Allah (ﷺ) ya je wurinsa sai ya iske Abu Jahal ɗan Hisham da Abdullahi ɗan Abu Umayya ɗan Mughira a wurinsa, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya kai Baffana, ka faɗi ‘La ilaha illallahu’, kalmar da zan yi maka shaida da ita a gaban Allah.” Sai Abu Jahal da Abdullahi ɗan Abu Umayya suka ce masa: “Yanzu kai za ka watsar da addinin Abdulmuɗɗalib kenan?” Annabi bai gushe ba yana ta bijirar masa da wannan kalma, su kuma suna ta maimaita masa waccan magana tasu, har dai daga ƙarshe ya ce shi yana nan a kan addinin Abdulmuɗɗalib, ya ƙi amincewa ya furta Kalmar Shahada. Sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Lalle tabbas zan nema maka gafara matuƙar ba a hana ni ba.” Sai ayar ta 113 a Suratut Tauba ta sauka, da kuma wannan ayar ta 56. [Bukhari #1360 da Muslim #24]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana uzurin da mushirikan Makka suka riƙa ba wa Manzon Allah (ﷺ) a kan rashin yin imani da shi, da cewa in sun amince sun bi shiriya tare da shi sun yi imani da abin da ya zo musu da shi, to za a fincike su daga ƙasarsu Makka su zama ribatattun yaƙi a hannun maƙiyansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa, ashe ba shi ne ya ba su iko da Harami amintacce ba, watau Makka wadda aka haramta zubar da jini da zalunci a cikinta fiye da ko’ina, suna kuma samun aminci a cikinta babu mai iya kawo musu hari, sannan kuma ana kawo musu kayan marmari iri-iri daga ko’ina don Allah ya arzuta su daga arziƙinsa, to amma yawancinsu ba su san girman ni’imar da Allah ya yi musu ba ballantana su gode masa.
وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةِۭ بَطِرَتۡ مَعِيشَتَهَاۖ فَتِلۡكَ مَسَٰكِنُهُمۡ لَمۡ تُسۡكَن مِّنۢ بَعۡدِهِمۡ إِلَّا قَلِيلٗاۖ وَكُنَّا نَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثِينَ
Open ayah 28:58Kuma al’umma nawa ce Muka hallakar wadda ta butulce wa rayuwarta? To ga gidajensu can ba a zaune su ba a bayansu sai kaɗan; Mu ne Muka kasance magadan.
وَمَا كَانَ رَبُّكَ مُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ حَتَّىٰ يَبۡعَثَ فِيٓ أُمِّهَا رَسُولٗا يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِنَاۚ وَمَا كُنَّا مُهۡلِكِي ٱلۡقُرَىٰٓ إِلَّا وَأَهۡلُهَا ظَٰلِمُونَ
Open ayah 28:59Kuma Ubangijinka bai zamanto Mai hallakar da alƙaryu ba har sai Ya aiko da manzo a cikin manyan biranensu, yana karanta musu ayoyinmu. Kuma ba Mu kasance Masu hallaka alƙaryu ba sai idan mutanensu sun zama azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dangogin azaba da hallakarwar da suka sami al’ummun da suka ƙaryata annabawa da cewa ya hallakar da alƙaryu da dama saboda sun kafirce wa ni’imar da ya yi musu sun zarme cikin saɓon sa. Kuma Larabawa su ne shaida, domin suna ganin gidajensu bayan an hallakar da su babu kowa zaune a cikinsu sai wasu ‘yan tsirarun mutane matafiya da sukan ya da zango su zauna na ɗan lokaci. Allah kuma ya tabbatar da cewa shi ne mai gadon waɗannan gidajen nasu kuma mai gadon sama da ƙasa da duk abin da yake cikinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzo (ﷺ) cewa ba zai taɓa hallakar da wata al’umma ba har sai ya aika mata da manzonsa, kamar yadda ya aiko da Manzo (ﷺ) zuwa ga uwar alƙaryu, watau Makka, ya yanke wa mutanenta duk wani hanzari da uzuri, amma suka bijire. Kuma ba zai taɓa hallakar da mutanen kowace alƙarya ba idan suna kan gaskiya suna bin tafarki madaidaci, sai dai idan sun kasance azzalumai masu aikata kafirci da saɓon Allah.
وَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَيۡءٖ فَمَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتُهَاۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 28:60Kuma duk irin abin da aka ba ku, to jin daɗin rayuwar duniya ne da adonta. Abin da yake wurin Allah kuwa (shi) ya fi alhairi ya fi kuma wanzuwa. Yanzu ba kwa hankalta ba?
أَفَمَن وَعَدۡنَٰهُ وَعۡدًا حَسَنٗا فَهُوَ لَٰقِيهِ كَمَن مَّتَّعۡنَٰهُ مَتَٰعَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا ثُمَّ هُوَ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ
Open ayah 28:61Yanzu wanda Muka yi wa alƙawari kyakkyawa da zai same shi, zai zama kamar wanda Muka jiyar da shi daɗin rayuwar duniya, sannan kuma shi yana daga waɗanda za a kai su wuta a ranar alƙiyama? Bayan da mushirikai suka ba da hanzarinsu na rashin karɓar Musulunci da cewa suna jin tsoron kada maƙiyansu su haɗu a kansu su yaƙe su ko kuma su yanke alaƙar kasuwanci da su, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa duk wani abu da zai ba su, to abu ne da za su more shi a nan duniya su yi ado da shi sannan daga ƙarshe ya gushe ko ya ƙare. To amma tanadin da ya yi musu a lahira na kyakkyawan sakamako shi ne ya fi musu alheri da wanzuwa a kan duk wani ƙyale-ƙyale na duniya. Sai kuma ya tabbatar da haka ta hanyar jan hankalin masu hankali da su duba su gani, wane ne ya fi morewa da samun alheri tsakanin wanda ya yi wa kyakkyawan alƙawarin gidan Aljanna da ni’imominta waɗanda ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, zuciya kuma ba ta taɓa tunanin su ba, matuƙar ya yi wa Allah ɗa’a ya yi aiki nagari, idan an haɗa shi da wanda Allah ya jiyar da shi daɗin rayuwar duniya ya manta da aiki nagari bai miƙa wuya ga abin da manzanni suka zo da shi ba har ya mutu a kan haka, sannan a ranar alƙiyama ya tsinci kansa cikin waɗanda za a kai su wutar Jahannama?! An karɓo daga Al-Mustaurid ɗan Shaddad (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na rantse da Allah, duniya idan aka kwatanta ta da lahira ba komai ba ce face kamar ɗayanku ne ya tsoma ɗan yatsansa a cikin kogi, to sai ya duba ya ga me zai fito da shi?” [Muslim #2858].
وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ أَيۡنَ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Open ayah 28:62Kuma ka tuna ranar da (Allah) zai kirawo su sai Ya ce: “Ina abokan tarayyar nawa waɗanda kuka kasance kuna riyawa?”
قَالَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ رَبَّنَا هَٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَغۡوَيۡنَآ أَغۡوَيۡنَٰهُمۡ كَمَا غَوَيۡنَاۖ تَبَرَّأۡنَآ إِلَيۡكَۖ مَا كَانُوٓاْ إِيَّانَا يَعۡبُدُونَ
Open ayah 28:63Sai waɗanda alƙawarin Allah (na azaba) ya tabbata a kansu su ce: “Ya Ubangijinmu, waɗannan da muka ɓatar, mun ɓatar da su ne kamar yadda mu ma muka ɓata; ba ruwanmu da kowa sai kai; don kuwa ba su kasance mu suke bauta wa ba.”
وَقِيلَ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ لَوۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ يَهۡتَدُونَ
Open ayah 28:64Kuma aka ce: “Ku kirawo abokan tarayyar naku”, sannan suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, suka kuma ga azaba. (Suka riƙa burin) ina ma sun kasance shiryayyu!
وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ مَاذَآ أَجَبۡتُمُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 28:65(Ka tuna) kuma ranar da (Allah) zai kirawo su sannan Ya ce: “Me kuka amsa wa manzanni (da shi?)”
فَعَمِيَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَنۢبَآءُ يَوۡمَئِذٖ فَهُمۡ لَا يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 28:66Sai abubuwan da za su faɗa suka ɓace musu a wannan ranar, don haka su ba za su iya tambayar junansu ba.
فَأَمَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَعَسَىٰٓ أَن يَكُونَ مِنَ ٱلۡمُفۡلِحِينَ
Open ayah 28:67To amma wanda ya tuba ya kuma yi imani ya kuma yi aiki nagari, to ana fatan ya zama cikin masu samun babban rabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin wulaƙancin da zai sami kafirai a ranar alƙiyama lokacin da zai kirawo su ya tambaye su, ina ababen tarayyarsa da suka riƙa bauta musu a duniya suna riya cewa su ababen tarayya ne ga Allah, me ya sa a yau ba za su amfane su da komai ba? Sai shugabannin kafirai waɗanda azaba ta tabbata a kansu su kirawo Ubangiji su nuna mabiyansu su ce waɗannan ne suka ɓatar kamar yadda su ma suka dulmiya cikin ɓata. Sai su nesanta kansu daga mabiyansu, su nuna su allambaran ba su suke bauta wa ba, suna dai bauta wa shaiɗanu ne kawai. Sai a umarci mushirikai da su kirawo ababen tarayyarsu waɗanda suke cewa za su cece su a lahira, sai su kirawo su domin su cece su daga azabar Allah da wulaƙancin da suke ciki, to amma sai su ji shiru ba su amsa musu kiran su ba, to a nan ne za su ga azabar Allah muraran sai su riƙa burin ina ma a duniya sun kasance shiryayyu? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a wannan rana za a tambaye su me suka amsa wa manzanni da shi lokacin da Allah ya aiko su zuwa gare su? To sai abubuwan da za su faɗa don tsayar da hujja da kare kai suka ɓace musu, suka kasa furta komai, suka kuma kasa tambayar junansu saboda tsananin rikicewa da jin tabbas ba makawa sai sun tafi wuta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci halin da muminai suke ciki a wannan rana, da cewa duk wanda ya tuba ya bar haɗa Allah da wani ya yi imani da Allah da manzanninsa, ya kuma yi kyakkyawan aiki, to wannan tabbas yana daga cikin masu rabauta da samun abin da suke nema, masu tsira daga duk wani abin ban tsoro.
وَرَبُّكَ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخۡتَارُۗ مَا كَانَ لَهُمُ ٱلۡخِيَرَةُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 28:68Kuma Ubangijinka Yana halittar abin da Ya ga dama Yana kuma zaɓar (abin da Ya ga dama). Ba su suke da zaɓi ba. Tsarki ya tabbata ga Allah kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yin shirka (da shi).
وَرَبُّكَ يَعۡلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمۡ وَمَا يُعۡلِنُونَ
Open ayah 28:69Kuma Ubangijinka Ya san abin da zukatansu suke ɓoyewa da kuma abin da suke bayyanawa.
وَهُوَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلۡأُولَىٰ وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 28:70Kuma Shi ne Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; yabo ya tabbata a gare Shi a duniya da lahira; hukunci kuma nasa ne, kuma zuwa gare Shi ne kawai za a mayar da ku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa cewa shi ne yake halittar abin da ya ga dama yake kuma zaɓar wanda ya ga dama ya datar da shi ga yi masa ɗa’a, kuma ya zaɓi wanda ya ga dama ya ba shi annabta. Su kuma mushirikai ba su da wani zaɓi nasu na kansu ballantana ma su yi wa Allah shisshigi cikin abin da ya zaɓa, ko kuma su zaɓo masa kishiyoyi suna bauta musu, alhali kuwa Allah bai ba wa wani mahaluƙi wannan haƙƙi ba. Don haka Allah ya tsarkaka ya kuma ɗaukaka daga duk wani abu da kafirai suke tara shi da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa yana sane da duk abin da zukatan bayinsa suke ɓoyewa da abin da suke bayyanawa, babu abin da yake ɓoyuwa a gare shi, kuma zai yi wa kowa sakayyar da ta dace da shi. Sai ya tabbatar da cewa shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi. Yabo da godiya da kirari kuma sun tabbata a gare shi a nan duniya da kuma lahira. Shi ne kuma wanda idan ya zartar da hukunci to ya zauna babu mai iya ja da shi a kansa, kuma duk halittu zuwa gare shi za a mayar da su ranar alƙiyama don ya yi wa kowa hukunci a kan ayyukansa masu kyau ko munana.
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمُ ٱلَّيۡلَ سَرۡمَدًا إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَنۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَأۡتِيكُم بِضِيَآءٍۚ أَفَلَا تَسۡمَعُونَ
Open ayah 28:71Ka ce: “Ku ba ni labari, (yanzu) idan Allah Ya sanya muku dare tutur har zuwa ranar alƙiyama, wane abin bauta ne ba Allah ba zai zo muku da wani haske? To me ya sa ba kwa ji?”
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمُ ٱلنَّهَارَ سَرۡمَدًا إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَنۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَأۡتِيكُم بِلَيۡلٖ تَسۡكُنُونَ فِيهِۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ
Open ayah 28:72Ka ce: “Ku ba ni labari, (yanzu) idan Allah Ya sanya muku rana tutur har zuwa ranar alƙiyama, wane abin bauta ne ba Allah ba zai zo muku da dare da za ku samu nutsuwa a cikinsa? To me ya sa ba kwa gani?”
وَمِن رَّحۡمَتِهِۦ جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 28:73Daga rahamarsa ne kuma Ya sanya muku dare da rana don ku samu nutsuwa a cikinsa (wato dare) kuma don ku nema daga falalarsa (da rana), don kuma ku riƙa yin godiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu daga cikin ni’imominsa ga bayinsa waɗanda ya wajaba su kalle su, su kuma gode masa a kansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa ya faɗa wa mushirikai cewa su ba shi labari cewa, idan Allah ya mayar musu da dare tutur har zuwa ranar alƙiyama ba tare da yankewa ba, to wane abin bauta ne ba Allah ba wanda zai kawo musu wani haske kamar na rana? Ya kuma tambaye su cewa me ya sa ba sa sauraron waɗannan hujjoji da ake kawo musu su fahimci cewa babu wani abin bauta da zai iya kawo musu waɗannan abubuwa? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Manzonsa (ﷺ) ya tambaye su su ba shi labari, idan ya mayar musu da yini tutur, watau rana diman-da’iman har zuwa ranar alƙiyama ba tare da yankewa ba, wane abin bauta ne ba Allah ba da zai zo musu da wani dare wanda za su samu nutsuwa a cikinsa su huta daga wahalhalun aiki da suka yi fama da shi da rana? Ya kuma tambaye su cewa me ya sa ba za su dubi waɗannan ayoyi ba su gane cewa babu wani abin bauta da zai iya kawo musu waɗannan in ba Allah ba? Sai ya tabbatar musu da cewa daga cikin rahamarsa ne ga mutane ya halitta musu dare mai duhu don su samu su huta a cikinsa bayan sun sha wahalhalun aiki da rana, ya kuma halitta musu yini mai haske domin su fita neman arziki a cikinsa, don kuma su gode wa ni’imomin Allah a gare su, su guje wa butulce masa.
وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ أَيۡنَ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Open ayah 28:74Ka kuma (tuna) ranar da (Allah) zai kirawo su, sai Ya ce: “Ina abokan tarayyar nawa waɗanda kuka kasance kuna riyawa?”
وَنَزَعۡنَا مِن كُلِّ أُمَّةٖ شَهِيدٗا فَقُلۡنَا هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ فَعَلِمُوٓاْ أَنَّ ٱلۡحَقَّ لِلَّهِ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 28:75Muka kuma ware wani shaida daga kowacce al’umma (wato annabinsu) sai Muka ce: “To ku kawo dalilinku (na yin tarayya da Allah).” Sai suka san cewa lalle gaskiya tana ga Allah, kuma abin da suka kasance suna ƙirƙira ya ɓace musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake nuna wa mushirikai cewa bautar wanin Allah da suke yi son zuciya ne ƙarara amma ba wani dalili suke da shi mai ƙarfi ba. Allah ya tunatar da su ranar alƙiyama ranar da zai kirawo su ya tambaye su, ina abubuwan da suke bauta wa a duniya suna riya cewa abokanan tarayyarsa ne, sai su zo su kuɓutar da su daga azabar Allah a gare su a wannan ranar. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan an halarto da kowace al’umma da abubuwan da suka bauta wa ba Allah ba, sai ya ware wani mai ba da shaida daga cikin kowace al’umma, watau annabinsu da Allah ya aika musu, domin ya ba da shaida a kan kafircinsu da ƙaryata manzanni da suka yi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya neme su da su kawo hujjarsu ta bautar wasu ba Allah ba da kuma hujjarsu ta ƙaryata manzanninsa. To a nan ne za su tabbatar da cewa Allah ne mai gaskiya shi kaɗai, sai kuma su nemi abubuwan da suka ƙirƙira suna bauta musu su rasa su, domin sun ɓace musu ɓat ba ɗuriyarsu.
۞إِنَّ قَٰرُونَ كَانَ مِن قَوۡمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيۡهِمۡۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلۡعُصۡبَةِ أُوْلِي ٱلۡقُوَّةِ إِذۡ قَالَ لَهُۥ قَوۡمُهُۥ لَا تَفۡرَحۡۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡفَرِحِينَ
Open ayah 28:76Lalle Ƙaruna yana daga mutanen Musa, sai ya yi musu girman kai, Muka kuma ba shi taskokin (dukiya) wadda lalle makullansu suna yi wa tarin jama’a ƙarfafa nauyin (ɗauka), yayin da mutanensa suka ce da shi: “Kada ka yi fariya, lalle Allah ba Ya son masu fariya.
وَٱبۡتَغِ فِيمَآ ءَاتَىٰكَ ٱللَّهُ ٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَۖ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ ٱلدُّنۡيَاۖ وَأَحۡسِن كَمَآ أَحۡسَنَ ٱللَّهُ إِلَيۡكَۖ وَلَا تَبۡغِ ٱلۡفَسَادَ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 28:77“Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka; kada kuma ka manta rabonka na duniya; kuma ka kyautata kamar yadda Allah Ya kyautata maka, kada kuma ka nemi yin ɓarna a bayan ƙasa. Lalle Allah ba Ya son masu ɓarna.”
قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمٍ عِندِيٓۚ أَوَلَمۡ يَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَهۡلَكَ مِن قَبۡلِهِۦ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مَنۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُ قُوَّةٗ وَأَكۡثَرُ جَمۡعٗاۚ وَلَا يُسۡـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 28:78Ya ce: “Ai ni an ba ni ita (wato dukiyar) ta hanyar ilimin da nake da shi ne.” Shin yanzu bai sani ba ne cewa haƙiƙa Allah Ya hallaka wasu al’ummun da suke a gabaninsa waɗanda suka fi shi ƙarfi da kuma yawan tarin (dukiya)? Ba kuwa za a tambayi masu laifi game da laifukansu ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin wani ƙasurgumin kafiri da ya yi zamani da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ana kiran sa Ƙaruna, wanda yana daga cikin mutanen Annabi Musa, watau Banu Isra’ila, sai dai da alama yana da ƙaƙƙarfar alaƙa da fadar Fir’auna da jama’arsa, don haka suka buɗa masa damammaki na tara ƙazamar dukiya wadda shi ma kansa bai san iyakar yawanta ba, sai ya riƙa taskace ta a wurare da gine-gine daban-daban, ya kuma tanadi makullai yana kulle waɗannan taskoki nasa. Watau saboda yawan waɗannan makullai sai an tara ƙatti majiya ƙarfi suke iya ɗaukar su, amma fa da kyar saboda tsananin nauyinsu da yawansu. Ganin irin wannan maɗuɗuwar dukiya da Allah ya mallaka wa Ƙaruna sai ta sanya shi ya shiga nuna wa mutanensa ɗagawa da girman kai, yana wulaƙanta su yana cutar da su. Wannan ya sa masu hankali daga cikin jama’arsa suka shirya haɗuwa da shi don su yi masa nasiha, su ja hankalinsa game da haɗarin da yake ƙoƙarin jefa kansa ciki. Sun yi masa nasihohi har guda biyar: <b>Nasiha ta farko </b>, sun ja kunnensa da yi masa gargaɗi a kan ya daina yi wa mutane fariya da homa saboda yawan dukiya da ya tara, domin kuwa Allah ba ya son masu irin wannan hali nasa, don haka ya guji janyo wa kansa fushin Allah da uƙubarsa. <b>Nasiha ta biyu </b>, suka nuna masa ya nemi lada a wurin Allah da wannan dukiya da ya ba shi, domin sakamakon lahira shi ne mai ɗorewa har abada. <b>Nasiha ta uku </b>, suka nuna masa cewa kada ya fahimci kamar suna umartar sa ne da ya kashe dukiyarsa duka wajen neman lahira; sai dai ya biya buƙatunsa na duniya ta hanyar amfani da dukiyarsa cikin abin da Allah ya halatta masa. <b>Nasiha ta huɗu </b>, suka yi kira gare shi da ya kyautata wa mutane ta hanyar taimaka wa mabuƙata ya yawaita aikin alheri kamar yadda Allah ya kyautata masa ya ba shi wannan tarin dukiyar. <b>Nasiha ta biyar </b>, suka kuma ja kunnensa da yi masa gargaɗi a kan ya daina yaɗa ɓarna a bayan ƙasa ta hanyar saɓon Allah da zalunci da wulaƙanta mutane, domin Allah ba ya son ɓarna, don haka ya guji jawo wa kansa fushin Allah da uƙubarsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan Ƙaruna ya ji duk waɗannan nasihohi daga bakin jama’arsa sai ya fara cika baki yana cewa, ai shi wannan dukiyar ba kowa ne ya ba shi ita ba sai iliminsa, watau saninsa da ƙwarewa da harkokin kasuwanci da neman kuɗi su suka ba shi damar ya tara dukiyarsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar masa da martani da cewa, yanzu shi Ƙaruna duk ilimin da yake tutiya da shi bai san cewa a baya can an yi wasu al’ummu waɗanda suka fi shi ƙarfi da tara dukiya ba, amma da suka yi ɗagawa da butulce wa Ubangijinsu sai Allah ya hallaka su, yanzu ko ɗuriyarsu ma ba a ji? Lokacin kuma da Allah ya yi niyyar hallaka su, ya gama da su ne kawai ba tare da ya tsaya yi musu wasu tambayoyi a kan laifuffukansu ba balle ma ya saurari hanzarinsu.
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ فِي زِينَتِهِۦۖ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا يَٰلَيۡتَ لَنَا مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ قَٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٖ
Open ayah 28:79Sai ya fito wa mutanensa a cikin adonsa; sai waɗanda suke burin rayuwar duniya suka ce: “Ina ma da za mu mallaki irin abin da aka bai wa Ƙaruna? Lalle shi mai babban rabo ne.”
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَيۡلَكُمۡ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّمَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗاۚ وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّٰبِرُونَ
Open ayah 28:80Waɗanda kuwa aka bai wa ilimi sai suka ce: “Kaiconku, ai ladan Allah shi ya fi alheri ga wanda ya yi imani, ya kuma yi aiki na gari. Ba kuwa wanda ake yi wa katari da shi sai masu haƙuri.”
فَخَسَفۡنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلۡأَرۡضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٖ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُنتَصِرِينَ
Open ayah 28:81Sannan muka kifar da shi (Ƙaruna) tare da gidansa cikin ƙasa, kuma ba shi da wata jama’a da za su taimake shi ba Allah ba, kuma bai kasance daga masu taimaka wa kawunansu ba.
وَأَصۡبَحَ ٱلَّذِينَ تَمَنَّوۡاْ مَكَانَهُۥ بِٱلۡأَمۡسِ يَقُولُونَ وَيۡكَأَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُۖ لَوۡلَآ أَن مَّنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا لَخَسَفَ بِنَاۖ وَيۡكَأَنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 28:82Kuma waɗanda suka yi burin matsayinsa a jiya suka wayi gari suna cewa: “Wai, yau mun ga abin al’ajabi! Allah Yana yalwata arziki ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, Yana kuma ƙuntatawa ga wanda Ya ga dama; ba don Allah Ya ba mu sa’a ba da mu ma Ya kifar da mu. Wai, abin mamaki, lalle kafurai ba sa rabauta!”
تِلۡكَ ٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ نَجۡعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوّٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فَسَادٗاۚ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 28:83Wancan gida na lahira Muna ba da shi ga waɗanda ba sa nufin girman kai da ɓarna a bayan ƙasa. Kyakkyawan ƙarshe kuma yana ga masu kiyaye dokokin Allah ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Ƙaruna ya yi watsi da nasihohin da aka yi masa, ya ci gaba da ɗagawarsa da sheƙe ayarsa. Wata rana ya shirya fita rangadi cikin jama’arsa, ya fita tare da jama’arsa cikin kwalliya ta ƙasaita har ya ja hankalin Banu Isra’ila suka kasu gida biyu: Kashi na farko, su ne gama-garin mutane marasa ilimi waɗanda suka kiɗime da ganin irin wannan sheƙe-aya da Ƙaruna yake yi da dukiyarsa, suka fara burin ina ma su ma su samu dukiya mai yawa irin tasa, domin suna ganin shi kam ya dace da babban rabo a duniya. Kashi na biyu kuwa su ne masu ilimin cikinsu masu hankali da hangen nesa; su kam sun fahimci cewa duk wannan abu da Ƙaruna yake yi ba komai ba ne sai ruɗin Shaiɗan, kuma jin daɗin duniya komai yawansa mai ƙarewa ne. Suka kuma yi Allah wadarai da abin da jahilai suke faɗa, suka nuna musu cewa sakamakon da Allah zai bayar a lahira da jin daɗin da ya tanada a can ga duk wanda ya yi imani ya kuma yi aiki nagari ya fi duk wani ƙyale-ƙyale na duniya da aka ba wa Ƙaruna yake bushasha a cikinsa. Amma ba kowa yake samun dacen faɗar irin wannan magana ba ko ya yi aiki da ita sai waɗanda suka yi haƙuri suka fifita sakamakon da ke wurin Allah a kan duk wani jin daɗi na nan duniya. Yayin da Ƙaruna yake tsakiyar sheƙe ayarsa ya kuma ruɗi wasu daga cikin mutanensa Banu Isra’ila har suka bi shi, sai kwatsam azabar Allah ta auka masa ba zato ba tsammani, Allah ya nutsar da shi har da gidansa da dukiyarsa a cikin ƙasa, kuma aka rasa waɗanda za su taimaka masa cikin jama’arsa da suke yi masa kanzagi da bayinsa masu tsaron sa, su kare shi daga azabar Allah, kuma shi kansa ba zai iya taimaka wa kansa da komai ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ganin irin wannan mummunan ƙarshe da Ƙaruna ya faɗa ya sanya jahilan can da suka ruɗu da shi da farko suka dawo cikin hankalinsu, suka shiga sallallami da mamakin cewa ashe Allah ne yake ba da arziki ga wanda ya ga dama daga cikin bayinsa, ya kuma ƙuntata wa wanda ya ga dama. Suka gane cewa ba don Allah ya yi musu baiwa da afuwarsa ba bai kama su da laifin maganganun da suka yi ba, to da su ma tuni ƙasa ta haɗiye su tare da Ƙaruna. Suka yi mamaki matuƙa da yadda masu kafirce wa Allah ba sa rabauta a duniya ko a lahira, domin ga shi dai yadda Ƙaruna ya zamanto aya a gare su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yana bayar da sakamakon gidan lahira da jin daɗinta ne kawai ga mutanen da ba sa yin girman kai da bijire wa imani da Allah da bin gaskiya a bayan ƙasa, kuma ba sa nufin ɓarna a cikinta; kyakkyawan ƙarshe kuma yana ga masu kiyaye dokokin Allah, domin su ne kaɗai za su rabauta da ni’imar Aljanna da kuma samun yardar Allah (Mai tsarki da daukaka). Sannan Allah ya tabbatar da cewa duk wanda ya zo masa ranar alƙiyama da kyakkyawan aiki, kamar salla da zakka da azumi da sadaka, to yana da sakamakon da ya fi wannan kyakkyawan aikin nasa, domin za a ninka masa shi goma zuwa ɗari bakwai zuwa ninkin ba-iyaka. Duk kuma wanda ya zo da mummunan aiki kamar kafirci da shirka da bidi’a da zina da sauransu, to ba za a saka wa mai mummunan aiki ba sai da kwatankwacin abin da ya aikata ba ƙari ba ragi.
مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 28:84Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waɗanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa.
إِنَّ ٱلَّذِي فَرَضَ عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٖۚ قُل رَّبِّيٓ أَعۡلَمُ مَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ وَمَنۡ هُوَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 28:85Lalle Wanda Ya saukar maka da Alƙur’ani tabbas zai mayar da kai zuwa makoma. Ka ce: “Ubangijina Shi Ya san wanda ya zo da shiriya da kuma wanda yake cikin ɓata mabayyani.”
وَمَا كُنتَ تَرۡجُوٓاْ أَن يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبُ إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرٗا لِّلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 28:86Kuma ba ka kasance kana fatan a saukar maka da littafi ba, sai dai (an yi haka ne) don rahama daga Ubangijinka; to don haka kada ka zamanto mai taimakon kafirai.
وَلَا يَصُدُّنَّكَ عَنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بَعۡدَ إِذۡ أُنزِلَتۡ إِلَيۡكَۖ وَٱدۡعُ إِلَىٰ رَبِّكَۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Open ayah 28:87Kuma lallai kada su hana ka (isar da) ayoyin Allah bayan an riga an saukar maka da su; kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka; kuma lallai kada ka zamanto daga mushrikai.
وَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۘ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ كُلُّ شَيۡءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجۡهَهُۥۚ لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 28:88Kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Kowane abu mai halaka ne sai Fuskarsa kawai. Hukunci (duk) nasa ne, zuwa gare Shi kuma za a mayar da ku. A ayoyin ƙarshe na wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, Ubangijinsa wanda ya saukar masa da Alƙur’ani ya kuma ɗora masa nauyin karantar da shi da aiki da hukunce-hukuncensa, lalle zai mayar da shi mahaifarsa, watau Makka. Idan mun dubi wannan Sura a matsayinta na kasancewarta Makkiyya gaba ɗayanta, wannan kamar nuni ne Allah yake yi wa Manzonsa (ﷺ) cewa za a fitar da shi daga garin Makka zuwa inda zai yi hijira, amma kuma Allah zai dawo da shi zuwa mahaifarsa. Hasali ma shi kansa Annabi an nuna masa a mafarki garin da zai yi hijirar zuwa gare shi cewa, gari ne mai bishiyoyin dabino, kamar yadda ya zo a cikin Sahihul Bukhari [#3905] da Muslim [#2473]. Sannan kuma Waraƙatu ɗan Naufal ya sanar da shi cewa, mutanen Makka za su fitar da shi daga mahaifarsa. [Dubi Bukhari #3 da Muslim #160]. Annabi (ﷺ) kuma bai manta da wannan ba. Wasu malaman tafsiri sun fassara ayar da cewa Allah yana sanar da Manzonsa (ﷺ) cewa kamar yadda ya saukar masa da Alƙur’ani hakanan kuma zai mayar da shi makomarsa ta ƙarshe, watau Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗa wa mushirkai masu ganin sa a kan ɓata cewa, Ubangijinsa shi ya fi sanin wanda ya zo da shiriya da kuma wanda yake cikin ɓata bayyananne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da shi irin falala da ni’ima da ya yi masa wadda ba ya tsammaninta, watau saukar masa da Alƙur’ani. Allah ya yi masa haka ne domin nuna masa rahamarsa a gare shi, don haka ya gargaɗe shi da cewa kada ya kuskura ya zamanto mai taimaka wa kafirai a kan ɓatansu, kuma kada ya yarda mushirkai su hana shi isar da saƙon ayoyin da aka riga aka saukar masa, ya tashi ya ci gaba da kira zuwa ga Ubangijinsa da yin imani da shi da aiki da shari’arsa. Kuma kada ya zamanto daga cikin masu shirka da Allah; ya kasance tare da muminai masu kaɗaita Allah da bauta. Sai kuma ya sake yi masa wani hani a kan kiran wani da bauta masa tare da Allah, saboda babu wani abin bauta na gaskiya sai Allah shi kaɗai, kuma komai na duniyar nan zai hallaka ya gushe sai Allah kaɗai shi ne mai wanzuwa; rayayye wanda da ba zai mutu ba har abada. Hukunci kuma duk nasa ne a duniya da lahira, kuma zuwa gare shi ake komar da kowa da komai domin ya yi wa bayinsa hisabi a kan ayyukan da suka aikata masu kyau da munana.