العنكبوت
Al-Ankaboot
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
الٓمٓ
Open ayah 29:1ALIF LAM MIM.
أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ
Open ayah 29:2Yanzu mutane suna tsammanin za a ƙyale su ne saboda suna cewa: “Mun yi imani,” kuma ba za a fitine su ba?
وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Open ayah 29:3Haƙiƙa kuwa Mun fitini waɗanda suke gabaninsu; to tabbas kuwa Allah zai bayyana waɗanda suka yi gaskiya, lalle kuma zai bayyana maƙaryata.
أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَسۡبِقُونَاۚ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ
Open ayah 29:4Ko kuma waɗanda suke aikata munanan ayyuka suna tsammanin za su gagare Mu ne? Abin da suke hukuntawa ya munana. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da haruffa kamar yadda ya yi a wasu surori da suka gabace ta [Dubi farkon Suratul Baƙara a wannan tafsirin domin ƙarin bayani]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yanzu mutane za su yi tsammani a bar su hakanan ba a jarrabi gaskiyar imaninsu ba don kawai sun furta da baki cewa sun yi imani? Watau abin ba haka yake ba, lalle sai an jarraba su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya jarrabi al\'ummun da suka gabaci wannan al’umma, kuma yana yin haka ne domin ya rarrabe tsakanin masu gaskiya cikin da’awar imaninsu a fili a san su, da kuma maƙaryata. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na tambayi Manzon Allahا (ﷺ) cewa: Waɗanne mutane ne jarrabawarsu ta fi tsanani?” Sai ya ce: “Annabawa ne, sannan waɗanda suka fi kwatanta irin ayyukansu sannan masu biye da su. Akan jarrabi mutum gwargwadon addininsa, to idan addininsa mai ƙarfi ne sai jarrabawarsa ta fi tsananta, idan kuwa akwai sakaci a cikin addininsa sai a jarrabe shi gwargwadon ƙarfin addininsa. Jarraba ba za ta rabu da bawa ba har sai ta sanya shi yana tafiya a bayan ƙasa ba tare da wani zunubi a kansa ba.” [Tirmizi #2398 da Ahmad #1481]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kashedi ga masu miyagun ayyuka na kafirci da saɓon Allah, masu zaton za su gagare shi, ya nuna musu cewa wannan zaton banza da wofi ne suke yi kuma mummunan hukunci suke yanke wa kawunansu, domin suna jayayya ne da ikon Allah da cikakkiyar Ƙudurarsa a kan komai.
مَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ ٱللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ لَأٓتٖۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 29:5Wanda ya zama yana fatan haɗuwa da Allah, to lalle lokacin (haɗuwa da) Allah tabbas mai zuwa ne. Kuma Shi ne mai ji, Masani.
وَمَن جَٰهَدَ فَإِنَّمَا يُجَٰهِدُ لِنَفۡسِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَنِيٌّ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 29:6Duk wanda kuwa ya yi jihadi, to yana jihadin ne don kansa. Lalle Allah tabbas Mawadaci ne daga talikai.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَحۡسَنَ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 29:7Waɗanda kuma suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, tabbas za Mu kankare musu munanan ayyukansu, kuma tabbas za Mu saka musu mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk wanda ya yi imani da ranar lahira yake fatan haɗuwa da Allah a wannan rana domin ya yi masa kyakkyawan sakamako bisa kyawawan ayyukansa, to ya sani Allah ba zai tozarta masa aikinsa ba, kuma lokacin da ya ajiye na zuwan wannan rana yana nan tafe ba da jimawa ba. Allah ya tabbatar da cewa shi mai jin maganganun bayinsa ne kuma masanin ayyukansu, ba abin da zai kuɓuce masa daga ciki kuma zai yi musu sakayya a kai. Sai kuma Allah ya bayyana cewa abin da ya ɗora wa bayinsa na ayyuka ba don amfaninsa ba ne sai don amfanin kansu, don haka duk wanda ya yaƙi zuciyarsa ya yi wa Allah ɗa’a, ya kuma guje wa saɓa masa, to ya sani ya yi ne don kansa, domin kuwa shi zai ci moriyar aikinsa, Allah ba ya buƙatar komai daga halittunsa; biyayyarsu ba za ta ƙare shi da komai ba, hakanan saɓawarsu ba za ta rage shi da wani abu ba. Sannan ya bayyana yalwar rahamarsa da kyautatawarsa ga halittunsa duk kuwa da kasancewarsa ba ya amfana daga gare su da komai, ya kuma tabbatar da cewa bayinsa waɗanda suka yi imani suka yi haƙuri a kan jarrabawarsa gare su suka kuma yi ayyuka nagari, to lalle zai shafe musu zunubbansu kuma a lahira zai yi musu sakayya fiye da abin da suka kasance suna aikatawa a duniya, domin zai riɓanya musu ladan ayyukansu tun daga ninki goma har zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa adadi ba iyaka.
وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حُسۡنٗاۖ وَإِن جَٰهَدَاكَ لِتُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَآۚ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 29:8Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa iyayensa; idan kuma suka yaƙe ka kan ka yi shirka da Ni game da abin da ba ka da sani a kansa, to kada ka bi su. Wurina ne makomarku take kawai, sannan zan ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَنُدۡخِلَنَّهُمۡ فِي ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 29:9Waɗanda kuma suka yi imani suka yi ayyuka nagari tabbas za Mu shigar da su cikin salihai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa ɗan’adam wasiyyar kyautata wa iyayensa da suka haife shi, lallai ya yi musu magana mai daɗi kuma ya kyautata musu a aikace. To amma yayin da za su matsa masa a kan sai ya haɗa Allah da wani abu wajen bauta wanda ba shi da wani ilimi ko wata hujja a kansa, to kada ya yi musu biyayya a kan haka, domin babu biyayya ga wani mahaluƙi a kan saɓa wa mahalicci. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abi Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mahaifiyata ta ce mini: “Ba zan ƙara cin abinci ko in sha abin sha ba har sai ka kafirce wa Muhammad.” Sai ta daina cin komai ta daina shan komai har sai da ta kai sai sun buɗe bakinta da sanda sun ɗura mata abinci ko abin sha. Sai wannan ayar ta sauka.” [Ahmad #1614]. Sai kuma Allah ya bayyana cewa makomar kowa zuwa gare shi ne shi kaɗai, watau ranar alƙiyama sannan zai ba kowa labarin abin da ya aikata a nan duniya kuma zai saka masa gwargwadon aikinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka yi imani da shi suka kuma yi ayyuka nagari, da cewa zai shigar da su cikin mutanen ƙwarai a ranar alƙiyama, ya tashe su tare, ya ba su lada irin nasu.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ فَإِذَآ أُوذِيَ فِي ٱللَّهِ جَعَلَ فِتۡنَةَ ٱلنَّاسِ كَعَذَابِ ٱللَّهِۖ وَلَئِن جَآءَ نَصۡرٞ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمۡۚ أَوَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 29:10Kuma cikin mutane akwai mai cewa: “Mun yi imani da Allah,” to idan aka cuce shi a kan hanyar Allah sai yakan ɗauki fitinar mutane kamar azabar Allah, lalle kuwa idan wata nasara ta zo daga Ubangijinka, tabbas zai riƙa cewa: “Lalle mu mun kasance tare da ku.” Yanzu Allah ba Shi Ya fi kowa sanin abin da ke cikin zukatan talikai ba?
وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ
Open ayah 29:11Tabbas kuma Allah zai bayyana waɗanda suka yi imani, kuma tabbas zai bayyana munafukai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ɓangare na siffofin munafukai masu yin imani da fatar baki kawai amma zukatansu ba su rabu da kafirci ba. Allah ya nuna cewa munafuki zai yi ta cika baki da faɗar ya yi imani, to amma idan wata jarraba ta same shi ta tsangwama da cutarwa daga kafirai sai ya kasa jurewa, har ma ya ɗauki azabar kafirai a gare shi kamar azabar Allah, sai kawai ya yi ridda ya koma ga kafirci. To amma yayin da nasarar Ubangiji ta zo wa Manzonsa da muminai suka samu galaba a kan kafirai, sai ya dawo yana tabbatar wa muminai cewa shi ma yana tare da su, yana nan da imaninsa bai yi ridda ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗakar da shi cewa, shin ya manta ne Allah yana sane da duk abin da mutane suke ɓoyewa a zukatansu? Tabbas babu abin da yake ɓuya ga Allah (Mai tsarki da daukaka) na kafirci ko na imani, to ta yaya za su ce su za su ba wa Allah labarin abin da yake zukatansu bayan ya fi su sanin komai? Sai Allah ya tabbatar da cewa lalle sai ya jarraba mutane ta kowace fuska, abu mai daɗi da marar daɗi domin ya bambance tsakanin muminai na gaskiya da kuma maƙaryata munafukai, ya kuma saka wa kowa daidai da aikinsa.
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّبِعُواْ سَبِيلَنَا وَلۡنَحۡمِلۡ خَطَٰيَٰكُمۡ وَمَا هُم بِحَٰمِلِينَ مِنۡ خَطَٰيَٰهُم مِّن شَيۡءٍۖ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 29:12Kuma waɗanda suka kafirta suka ce da waɗanda suka yi imani: “Ku bi tafarkinmu, (mu) lalle za mu ɗauke muku kurakuranku,” alhali kuwa su ba za su iya ɗauke wani abu na kurakuransu ba; lalle su dai tabbas maƙaryata ne.
وَلَيَحۡمِلُنَّ أَثۡقَالَهُمۡ وَأَثۡقَالٗا مَّعَ أَثۡقَالِهِمۡۖ وَلَيُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَمَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 29:13Tabbas kuma za su ɗauki zunubansu da kuma wasu zunuban tare da zunubansu; kuma tabbas za a tambaye su a ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna ƙirƙira. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafiran Ƙuraishawa suna zolayar muminai da cewa su zo su bi addininsu su ci gaba da ayyuka irin nasu, idan an je lahira wai su za su ɗauke musu zunubansu, don haka idan an zo yin uƙuba su za a yi wa ba muminai da suka bi su ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani ya tabbatar da ƙaryarsu da cewa ba za su ɗauke wa muminai wani abu na zunubansu ba idan har suka kuskura suka bi su, domin kuma tabbas su kafirai maƙaryata ne. Sai kuma Allah ya tabbatar da cewa su waɗannan kafirai masu ƙoƙarin su yi wa Musulmi shigo-shigo-ba-zurfi ba zai ƙyale su hakanan ba tare da ya ƙara musu wani nauyin zunubi a kan nasu na da ba. Ya tabbatar musu cewa lalle sai sun ɗauki nauyin zunubansu waɗanda suka aikata tare da zunuban waɗanda suka bi kiraye-kirayensu na kafirci, ba kuma tare da sun rage wa mabiyansu wani abu daga cikin zunubansu ba. Ya ƙara tabbatar musu cewa ranar alƙiyama lallai sai an tambaye su game da ƙarairayin da suka riƙa ƙirƙira a duniya. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya yi kira zuwa ga shiriya, to yana da lada kwatankwacin ladan waɗanda suka bi shi, kuma wannan ba zai tauye wani abu na ladansu ba. Duk kuma wanda ya yi kira zuwa ga ɓata, to yana da zunubi kwatankwacin zunuban waɗanda suka bi shi, kuma wannan ba zai rage wani abu daga zunubansu ba.” [Muslim #2674].
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَلَبِثَ فِيهِمۡ أَلۡفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمۡسِينَ عَامٗا فَأَخَذَهُمُ ٱلطُّوفَانُ وَهُمۡ ظَٰلِمُونَ
Open ayah 29:14Kuma haƙiƙa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna cikinsu shekara dubu ba hamsin, sai (ruwan) Ɗufana ya ci su, alhalin suna azzalumai.
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَصۡحَٰبَ ٱلسَّفِينَةِ وَجَعَلۡنَٰهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 29:15Sai Muka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa, Muka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wani ɓangare na ƙissar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda shi ne farkon manzannin Allah. Ya bayyana cewa ya aiko shi zuwa ga mutanensa masu shirka da Allah domin ya kirawo su zuwa ga kaɗaita Allah; ya zauna a cikinsu yana yi musu wa’azi yana kiran su zuwa kaɗaita Allah da bauta har tsawon shekara ɗari tara da hamsin, amma sai suka ƙaryata shi suka doge a kan kafircinsu da shirkarsu; mutane ƙalilan ne suka yi imani da shi. Sai ya roƙi Allah ya aiko musu da ruwan Ɗufana don ya hallaka su suna kan zaluncinsu da kafircinsu ba su bari ba. Allah kuma ya bayyana cewa ya karɓi roƙonsa ya hallaka kafirai gaba ɗaya kuma ya kuɓutar da Annabi Nuhu da muminan da suke tare da shi a cikin jirgin ruwa daga hallakar nutsewa cikin ruwa, ya kuma bar wannan jirgin ruwa don ya zama abin izina ga mutane.
وَإِبۡرَٰهِيمَ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُۖ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 29:16Kuma (ka tuna) Ibrahimu lokacin da ya ce da mutanensa: “Ku bauta wa Allah, kuma ku kiyaye dokokinsa, wannan shi ya fi muku alheri in kun kasance kun san (haka).
إِنَّمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا وَتَخۡلُقُونَ إِفۡكًاۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ لَكُمۡ رِزۡقٗا فَٱبۡتَغُواْ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزۡقَ وَٱعۡبُدُوهُ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥٓۖ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 29:17Lalle abin da kuke bauta wa ba Allah ba gumaka ne kawai, kuna kuma ƙirƙirar ƙarya ne. Lalle waɗanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba su mallaki wani arziki ba gare ku , sai ku nemi arziki a wurin Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa; gare Shi ne kawai za a mayar da ku.
وَإِن تُكَذِّبُواْ فَقَدۡ كَذَّبَ أُمَمٞ مِّن قَبۡلِكُمۡۖ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 29:18Idan kuma kuka ƙaryata, to haƙiƙa da ma wasu al’ummun da suke gabaninku sun ƙaryata; ba abin da yake kan Manzo sai isar da saƙo mabayyani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya aika manzonsa Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa ga mutanensa don ya kirawo su zuwa ga kaɗaita Allah (Mai tsarki da daukaka), sai ya umarce su da su ji tsoron Allah su kiyaye dokokinsa ta hanyar aikata umarninsa da guje wa haninsa. Yin haka ya fi musu alheri in sun kasance sun san haka. Sannan ya nuna musu kyawun abin da yake kiran su a kansa da kuma munin abin da suke a kai na yin shirka da Allah. Abin da suke bauta wa ba komai ba ne face gumaka waɗanda ba za su amfane su da komai ba, ba kuma za su kare su daga wata cuta ba. Ya tabbatar musu da cewa ƙarya ce kawai suke ƙirƙira da kansu, domin su ne suke sassaƙa su da hannayensu suke kuma sanya musu sunaye sannan daga bisani su riƙa bauta musu. Allah kuma ya sake jan hankalinsu a kan su lura cewa waɗannan gumakan nasu ba su cancanci bauta ba, domin ba su mallaki komai na arziki da za su arzuta su da shi ba. Sai su nemi arziki a wurin Allah domin shi kaɗai ne mai arzutawa, su kuma bauta masa shi kaɗai, su gode masa bisa ni’imar arziki iri-iri da ya yi musu, kuma su sani gare shi kaɗai za su koma a ranar alƙiyama don ya yi musu hisabi da sakamako a kan ayyukansu. Gumakansu kuma ba su da wani abu daga cikin waɗannan. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunanar da mushirikai cewa idan sun ƙaryata abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da shi, to ba su ne farau ba a kan haka, akwai al’ummu da dama da suka gabace su, kamar mutanen Annabi Nuhu da Adawa da Samudawa, dukkansu sun ƙaryata manzanninsu, Allah kuma ya hallaka su. Shi kuma Manzo babu abin da yake kansa sai isar da saƙo a sarari, wanda ya gaskata ya tsira, wanda kuwa ya ƙaryata to don kansa. Shi kam Manzon Allah ya isar musu da duk abin da Allah ya umarce shi ya isar gare su.
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ كَيۡفَ يُبۡدِئُ ٱللَّهُ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥٓۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ
Open ayah 29:19Yanzu ba su ga yadda Allah Yake farar halitta ba, sannan Shi ne kuma zai mayar da ita? Lalle wannan mai sauƙi ne a wurin Allah.
قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ بَدَأَ ٱلۡخَلۡقَۚ ثُمَّ ٱللَّهُ يُنشِئُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأٓخِرَةَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 29:20Ka ce: “Ku yi tafiya a bayan ƙasa sai ku duba ku ga yadda Allah Ya fari halittu. Sannan Allah ne zai sake samar da su samarwar ƙarshe. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai.
يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَرۡحَمُ مَن يَشَآءُۖ وَإِلَيۡهِ تُقۡلَبُونَ
Open ayah 29:21“Yana azabtar da wanda Ya ga dama, Yana kuma jin ƙan wanda Ya ga dama; kuma wurinsa kawai za a mayar da ku.
وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ
Open ayah 29:22“Kuma ku ba za ku gagara ba a ƙasa ko kuma a sama; kuma ba ku da wani majiɓinci ko mataimaki in ba Allah ba.”
وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَلِقَآئِهِۦٓ أُوْلَٰٓئِكَ يَئِسُواْ مِن رَّحۡمَتِي وَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 29:23Waɗanda kuma suka kafirce wa ayoyin Allah da kuma gamuwa da Shi, waɗannan sun ɗebe ƙauna daga rahamata, kuma waɗannan suna da azaba mai raɗaɗi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya juyo a kan kafiran Makka waɗanda suke ƙaryata tashi bayan mutuwa da hisabi ranar alƙiyama, ya bayyana musu cewa ba su ga yadda Allah ya fari halitta ba daga babu? Sannan kuma shi ne zai sake dawo da ita bayan gushewarta, wannan kuma abu ne mai sauƙi ƙwarai a gunsa don babu abin da yake gagarar sa. Sannan ya umarci Manzon Allah (ﷺ) ya umarci waɗannan mushirikan su yi tafiya a bayan ƙasa su duba su ga yadda Allah ya fari halittar mutane da dabbobi da tsirrai da itatuwa, sannan da yadda suke mutuwa kaɗan-kaɗan. Kuma shi ne wanda zai sake raya su a karo na biyu bayan mutuwarsu don yi musu hisabi da sakamakon ayyukansu masu kyau da marasa kyau. Lalle Allah mai iko ne a kan komai babu abin da zai gagare shi, watau kamar yadda fara halittarsu ba ta gagare shi ba, to hakanan sake tashinsu bayan mutuwarsu ba zai gagare shi ba. Sai kum Allah ya bayyana adalcinsa da falalarsa a ranar alƙiyama inda zai azabtar da wanda ya ga dama da adalcinsa, ya kuma ji ƙan wanda ya ga dama da falalarsa, kuma wajensa ne shi kaɗai za a mayar da su a ranar alƙiyama domin hisabi a kan ayyukansu. Kuma su waɗannan kafirai masu ƙaryata tashi bayan mutuwa da zuwan ranar alƙiyama su sani ba za su iya gagarar Allah ba har su tsere masa a sama ko a ƙasa, duk inda za su shiga suna cikin damƙarsa. Ya kuma tabbatar musu cewa babu wani wanda ya isa ya taimaka musu ya kare su daga azabar Allah a sama ko a ƙasa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin da kafirai masu ƙaryata zuwan lahira da cewa su ne waɗanda suka kafirce wa ayoyin Allah da haɗuwa da shi a ranar alƙiyama, to waɗannan su ne waɗanda suke ɗebe ƙauna daga samun rahamar Allah, domin ba su yi wani aiki mai kyau da zai sa su yi tsammanin samunta ba, don haka har abada ba su ba shiga Aljanna saboda kafircinsu. Waɗannan suna da azaba mai raɗaɗi tana jiran su a ranar alƙiyama.
فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوۡمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُواْ ٱقۡتُلُوهُ أَوۡ حَرِّقُوهُ فَأَنجَىٰهُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلنَّارِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 29:24To ba wani jawabi da ya fito daga bakin mutanensa sai cewa da suka yi: “Ku kashe shi ko kuma ku ƙone shi!” Sai Allah Ya tserar da shi daga wutar. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suka yi imani.
وَقَالَ إِنَّمَا ٱتَّخَذۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا مَّوَدَّةَ بَيۡنِكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ ثُمَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكۡفُرُ بَعۡضُكُم بِبَعۡضٖ وَيَلۡعَنُ بَعۡضُكُم بَعۡضٗا وَمَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّٰصِرِينَ
Open ayah 29:25Kuma ya ce (da su): “Lalle ba abin da kuka riƙa wanin Allah sai gumaka kawai don ƙauna da take tsakaninku a rayuwar duniya; sannan ranar alƙiyama wasunku za su kafirce wa wasu, kuma wasunku za su la’anci wasu, makomarku kuma wuta ce, ba ku da kuwa wasu mataimaka.”
۞فَـَٔامَنَ لَهُۥ لُوطٞۘ وَقَالَ إِنِّي مُهَاجِرٌ إِلَىٰ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 29:26Sai Luɗu ya yi imani da shi. (Sai Ibrahimu) kuma ya ce: “Lalle ni mai yin hijira ne zuwa ga Ubangijina; lalle Shi Mabuwayi ne, Mai hikima.”
وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَجَعَلۡنَا فِي ذُرِّيَّتِهِ ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلۡكِتَٰبَ وَءَاتَيۡنَٰهُ أَجۡرَهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَإِنَّهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 29:27Muka kuma yi masa baiwa da (ɗansa) Is’haƙa da kuma (jikansa) Ya\'aƙubu, Muka kuma sanya annabta da littafi a cikin zuriyarsa, Muka kuma ba shi ladansa a duniya; kuma lalle shi a lahira tabbas yana cikin salihai. Waɗannan ayoyi ci gaba ne da labarin Annabi Ibrahimu da mutanensa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kira mutanensa zuwa ga kaɗaita Allah da bauta da watsi da bautar wanin Allah cikin hikima da ilimi, amma sai mutanensa suka mayar masa da mummunan martani ta hanyar umartar junansu da cewa su kashe Annabi Ibrahimu ko ma su jefa shi cikin wuta ya ƙone ƙurmus domin su taimaka wa gumakansu. Haka kuwa suka yi suka jefa shi wuta, amma sai Allah ya kuɓutar da shi. Allah kuma ya tabbatar da cewa lalle a game da abin da ya faru na jefa Annabi Ibrahimu cikin wuta da kuɓutar da shi ba shakka akwai ayoyi masu ɗauke da izina da darussa ga muminai, domin su ne masu ɗaukar izina daga abin da manzanni suka zo da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu nasihohin da Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya riƙa yi wa mutanensa da cewa, sun riƙi gumaka ne suna bauta musu ba Allah ba domin kawai su ƙarfafa soyayyar da ke tsakaninsu da junansu a nan duniya, to amma su sani cewa a lahira wannan soyayyar za ta yanke, za su yi baram-baram da junansu lokacin da za su ga azaba ƙuru-ƙuru, su yi ta tsine wa junansu, daga ƙarshe matabbatarsu ita ce wutar Jahannama, ba su da kuwa wasu mataimaka da za su kare su daga aukawa cikin azabar Allah; gumakansu ba za su tsinana musu komai ba a wannan rana. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ci gaba da da’awarsa yana ta kiran mutanensa zuwa ga Tauhidi har lokacin da ɗan’uwansa Annabi Luɗu ya yi imani da shi, mutanensa kuma suka bijire wa kiransa, wa’azinsa bai amfane su da komai ba, daga nan sai ya yanke shawarar yin hijira zuwa ƙasar Sham mai albarka don ya ci gaba da bautar Ubangijinsa a can domin Allah shi ne mabuwayi, babu mai iya rinjayar sa, kuma duk wanda ya yi hijira zuwa gare shi ba zai ƙasƙanta ba, kuma mai hikima ne cikin duk abin da ya ƙaddara ya kuma tsara. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan Annabi Ibrahimu ya yi hijira zuwa Sham sai ya yi masa kyautar Is’haƙa da ɗansa Ya’aƙub, ya kuma ƙara yi masa wata baiwar mai girma ta sanya annabta a cikin ‘ya’yansa ya saukar musu da littattafai, ya kuma ba shi ladan haƙuri da juriyar da ya yi a kan gaskiya a nan duniya, ya gyara masa ‘ya’yansa ya sanya masa kyakkyawan ambato cikin mutane, sannan kuma lalle a lahira za a yi masa sakamako irin wanda ake yi wa mutanen kirki; abin da aka ba shi a nan duniya kuma ba zai sa a rage masa abin da zai samu a lahira ba.
وَلُوطًا إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ إِنَّكُمۡ لَتَأۡتُونَ ٱلۡفَٰحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنۡ أَحَدٖ مِّنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 29:28Kuma (ka tuna) Luɗu lokacin da ya ce da mutanensa: “Lalle ku kuna zaike wa mummunan aiki wanda ba wani mutum guda daga talikai da ya rigaye ku (aikata) shi.
أَئِنَّكُمۡ لَتَأۡتُونَ ٱلرِّجَالَ وَتَقۡطَعُونَ ٱلسَّبِيلَ وَتَأۡتُونَ فِي نَادِيكُمُ ٱلۡمُنكَرَۖ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوۡمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُواْ ٱئۡتِنَا بِعَذَابِ ٱللَّهِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 29:29“Yanzu kwa riƙa zaike wa maza, ku kuma riƙa tsare hanya (kuna yin fashi), kuma kuna aikata abin ƙi a cikin majalisarku?” Ba wani jawabi da ya fito daga bakin mutanensa sai cewa suka yi: “To ka zo mana da azabar Allah idan ka kasance cikin masu gaskiya.”
قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Open ayah 29:30(Sai Luɗu) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka taimake ni kan mutanen nan maɓarnata.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya aiko da Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa ga mutanen Sadum waɗanda suka shahara da wata mummunar al’ada ta neman maza domin biyan buƙatar sha’awarsu. Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya gargaɗe su a kan wannan mummunan aiki da suke yi wanda ba a taɓa samun wasu suna aikata irinsa ba gabaninsu; su ne farkon waɗanda suka tsiri wannan mummunan laifi wanda duk wani mai lafiyayyen hankali zai ƙyamace shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mutanensa kashedi game da munanan ayyukan da suke yi, inda suka riƙa biyan buƙatar sha’awarsu da maza, sannan su riƙa tsare hanya suna yi wa matafiya fashi, mutane kuma suna jin tsoron bin hanyoyinsu domin gudun su tsare su su yi lalata da su. Sannan suna aikata miyagun ayyuka a majalisunsu, kamar nuna tsiraici da cutar da masu wucewa a hanya da maganganunsu ko da ayyukansu. Sai Allah ya nuna cewa a maimakon su karɓi nasihar da Annabi Luɗu ya yi musu sai ya zamanto babu abin da ya fito daga bakinsu sai cewa suka yi ya sauko musu azabar Allah da yake razana su da ita, idan har abin da yake faɗa musu gaskiya ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ganin irin yadda mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka nuna taurin kansu da neman ya saukar musu da azaba, sai ya roƙi Allah ya taimake shi a kan waɗannan mutane maɓarnata masu yaɗa kafirci da fitsara a bainar jama’a.
وَلَمَّا جَآءَتۡ رُسُلُنَآ إِبۡرَٰهِيمَ بِٱلۡبُشۡرَىٰ قَالُوٓاْ إِنَّا مُهۡلِكُوٓاْ أَهۡلِ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةِۖ إِنَّ أَهۡلَهَا كَانُواْ ظَٰلِمِينَ
Open ayah 29:31Lokacin kuwa da manzanninmu suka zo wa Ibarahimu da albishir, sai suka ce: “Lalle mu masu hallaka mutanen wannan alƙaryar ne, lalle mutanenta sun kasance azzalumai.”
قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطٗاۚ قَالُواْ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَن فِيهَاۖ لَنُنَجِّيَنَّهُۥ وَأَهۡلَهُۥٓ إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ كَانَتۡ مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ
Open ayah 29:32Sai (Ibrahimu) ya ce: “Lalle Luɗu yana cikinta”. Sai suka ce: “Mu muka fi sanin waɗanda suke cikinta; tabbas za mu tserar da shi tare da iyalinsa, sai matarsa kawai da ta kasance cikin waɗanda za su yi saura (a hallaka su tare)”.
وَلَمَّآ أَن جَآءَتۡ رُسُلُنَا لُوطٗا سِيٓءَ بِهِمۡ وَضَاقَ بِهِمۡ ذَرۡعٗاۖ وَقَالُواْ لَا تَخَفۡ وَلَا تَحۡزَنۡ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهۡلَكَ إِلَّا ٱمۡرَأَتَكَ كَانَتۡ مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ
Open ayah 29:33Lokacin kuma da manzanninmu suka zo wa Luɗu, sai ya yi baƙin ciki da zuwansu, zuciyarsa kuma ta ƙuntata saboda su, sai suka ce da shi: “Kada ka ji tsoro, kuma kada ka damu; lalle mu masu tserar da kai ne tare da iyalinka, sai matarka kawai da ta kasance cikin waɗanda za su yi saura (a hallaka su tare).
إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَىٰٓ أَهۡلِ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةِ رِجۡزٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ
Open ayah 29:34“Lalle mu masu saukar da azaba ce daga sama a kan mutanen wannan alƙaryar saboda abin da suka kasance suna aikatawa na fasiƙanci.”
وَلَقَد تَّرَكۡنَا مِنۡهَآ ءَايَةَۢ بَيِّنَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Open ayah 29:35Kuma haƙiƙa Mu mun bar aya bayyananniya game da ita (alƙaryar) ga mutanen da suke hankalta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya karɓi addu’ar Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya aiko da mala’iku domin hallaka mutanensa. Sai mala’ikun nan suka fara biyawa ta wajen Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don su yi masa albishir da samun haihuwar ɗansa Is’haƙa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kuma jikansa Ya’aƙub (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sai Annabi Ibrahim ya so ya san inda suka nufa daga wajensa, sai suka bayyana masa cewa za su je ne su hallaka mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) domin sun tabbata mutane ne azzalumai saboda aikata alfasha da suke yi. Daga nan sai Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga tattaunawa da su a kan haka, ya nuna musu a wannan alƙarya da za su hallakar akwai Annabi Luɗu wanda shi ba azzalumi ne irinsu ba. Sai mala’ikun suka amsa masa da cewa su ne suka fi shi sanin waɗanda suke cikin wannan alƙarya ta Sadum, suka kuma tabbatar masa da cewa lalle za su tserar da Annabi Luɗu da iyalansa daga wannan azabar in ban da matarsa, ita kam tana cikin waɗanda za a hallakar. Sai mala’ikun suka nufi alƙaryar mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da isarsu gidansa aka kuma sanar da shi ya yi baƙi, sai ya yi baƙin ciki da zuwansu, ya shiga matsananciyar damuwa domin jiye musu tsoron mugun halin mutanensa, musamman saboda mala’ikun sun zo a cikin kamanni na mutane maza, su kuma mutanensa sun jarrabu da neman maza da lalata. Bayan mala’ikun sun fahimci damuwarsa sai suka kwantar masa da hankali suka nuna masa kada ya ji tsoro, mutanensa ba za su iya cutar da shi ba, kuma su mala’iku ne, sun zo ne don su hallaka mutanensa kuma za su tserar da shi tare da iyalansa duka in ban da matarsa, ita kam za ta yi saura a cikin mutanensa, don haka za ta hallaka tare da su. Suka kuma yi masa bayanin irin azabar da aka umarce su da su saukar wa mutanensa, watau azabar ruwan duwatsu na wuta daga sama bayan an ɗaga garin sama an kifar da shi saboda fasiƙancin da suke aikatawa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle ya bar bayyananniyar aya ga mutanen da suke da hankali masu ɗaukar izina da darasi daga ayoyin Allah.
وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗا فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱرۡجُواْ ٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ
Open ayah 29:36Mun kuma (aika wa mutanen) Madyana ɗan’uwansu Shu’aibu, sai ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, kuma ku yi fatan (kyakkyawan samakon) ranar lahira, kada kuma ku riƙa yaɗa ɓarna a bayan ƙasa.”
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دَارِهِمۡ جَٰثِمِينَ
Open ayah 29:37Sai suka ƙaryata shi, sai girgizar ƙasa ta kama su, suka wayi gari duddurƙushe (matattu) cikin gidajensu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya aika wa mutanen Madyana ɗan’uwansu na jini Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai ya umarce su da su bauta wa Allah shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, kuma su yi kwaɗayin kyakkyawan sakamakon ranar lahira, da bautar da za su yi wa Allah, ya kuma hana su yaɗa ɓarna a bayan ƙasa ta hanyar kafirci da saɓon Allah. Daga cikin ɓarnar da suke yaɗawa a bayan ƙasa akwai tauye wa mutane haƙƙoƙinsu na awo da tsare hanyoyi suna yi wa mutane fashi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mutanen Annabi Shu’aibu sun ƙaryata shi, sai azabar girgizar ƙasa ta auka musu, sai suka wayi gari a duddurƙushe a gidajensu duk sun hallaka babu mai sauran motsi.
وَعَادٗا وَثَمُودَاْ وَقَد تَّبَيَّنَ لَكُم مِّن مَّسَٰكِنِهِمۡۖ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَصَدَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّبِيلِ وَكَانُواْ مُسۡتَبۡصِرِينَ
Open ayah 29:38Kuma (Mun hallaka) Adawa da Samudawa, haƙiƙa (abin da ya faru a gare su) ya bayyana gare ku a fili a gidajensu; kuma Shaiɗan ya ƙawata musu ayyukansu, sai ya kange su daga hanya (madaidaiciya), sun kuma kasance masu gani da basirarsu (amma suka zaɓi ɓata).
وَقَٰرُونَ وَفِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَۖ وَلَقَدۡ جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا كَانُواْ سَٰبِقِينَ
Open ayah 29:39Kuma (Mun hallaka) Ƙaruna da Fir’auna da Hamana; haƙiƙa kuma Musa ya zo musu da hujjoji bayyanannu, sai suka yi girman kai a bayan ƙasa, kuma ba su kasance masu guje wa (azaba) ba.
فَكُلًّا أَخَذۡنَا بِذَنۢبِهِۦۖ فَمِنۡهُم مَّنۡ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِ حَاصِبٗا وَمِنۡهُم مَّنۡ أَخَذَتۡهُ ٱلصَّيۡحَةُ وَمِنۡهُم مَّنۡ خَسَفۡنَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ وَمِنۡهُم مَّنۡ أَغۡرَقۡنَاۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Open ayah 29:40Kowanne (cikin al’ummun da suka gabata) Mun kama shi da laifinsa; daga cikinsu akwai waɗanda Muka aiko wa da duwatsu, akwai kuma waɗanda tsawa ta kama su, kuma daga cikinsu akwai waɗanda Muka kifar da su cikin ƙasa, akwai kuma daga cikinsu waɗanda Muka nutsar a ruwa. Allah kuma bai kasance Yana zaluntar su ba, sai dai kawai kawunansu suke zalunta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci Adawa mutanen Annabi Hudu da Samudawa mutanen Annabi Salihu don ya ƙara tabbatar wa Ƙuraishawa cewa ya hallaka su yayin da suka kafirce wa annabawansu, kuma abin da ya faru da su na hallakarwa kafiran Ƙuraishawa sun gan shi a fili a mazaunan Adawa da Samudawa, domin suna kan hanyoyinsu na tafiya fatauci zuwa Yaman da Sham. Suna ganin kufaifan gidajensu babu kowa a cikinsu. Shaiɗan ne ya ƙawata musu miyagun ayyukansu na kafirci da saɓon Allah sai suka riƙa ɗauka wani abu ne mai kyau suke aikatawa, Shaiɗan ya raba su da tafarki madaidaici, alhali manzanninsu sun zo musu da ayoyi bayyanannu waɗanda suke cike da basira da hankali da za su samu damar bambance tsakanin ƙarya da gaskiya da kuma ɓata da shiriya. To amma sai suka zaɓi su bi son zuciyarsu a maimakon shiriya, don haka ba su da wani hanzari a wurin Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci cewa ya hallaka Ƙaruna yayin da ya nuna zaluncinsa ga mutanensa a fili, ya kifar da shi har da gidansa suka nutse cikin ƙasa. Haka kuma ya hallaka Fir’auna da wazirinsa Hamana lokacin da ya aika musu Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ayoyi bayyanannu masu nuna gaskiyar manzancinsa, amma sai suka nuna girman kai a ƙasar Masar, suka ƙi yin imani da Annabi Musa, don haka ba su iya kuɓuce wa azaba ba yayin da ta zo musu, sai Allah ya nutsar da su a cikin ruwa suka hallaka gaba ɗayansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin hanyoyin da ya hallaka dukkan waɗancan al’ummu da suka ƙaryata manzanninsu a dunƙule. Daga cikinsu akwai mutanen Annabi Luɗu waɗanda Allah ya aiko musu ruwan duwatsu irin na soyayyen yumɓu. Daga cikinsu akwai mutanen Annabi Salihu da mutanen Annabi Shu’aibu waɗanda Allah ya hallaka su da tsawa. Daga cikinsu akwai Ƙaruna wanda Allah ya nutsar da shi a cikin ƙasa daga shi har dukiyarsa da gidansa. Daga cikinsu kuma akwai mutanen Annabi Nuhu da Fir’auna da Hamana waɗanda Allah ya nutsar da su a ruwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ba zai yiwu haka kawai ya zalunce su ya hallakar da su ba laifin zaune ba na tsaye ba, sai dai kawai su ne suka zalunci kawunansu ta hanyar kafirci da ayyukan saɓon Allah, don haka suka cancanci azabarsa.
مَثَلُ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡلِيَآءَ كَمَثَلِ ٱلۡعَنكَبُوتِ ٱتَّخَذَتۡ بَيۡتٗاۖ وَإِنَّ أَوۡهَنَ ٱلۡبُيُوتِ لَبَيۡتُ ٱلۡعَنكَبُوتِۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 29:41Misalin waɗanda suka riƙi wasu iyayen giji ba Allah ba, kamar misalin gizogizo ne da ya saƙa gida; haƙiƙa kuwa lalle gidan gizogizo shi ya fi kowanne gida rauni, da sun kasance suna sanin (haka).
إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ مِن شَيۡءٖۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 29:42Lalle Allah Yana sane da kowane abu da suke bauta wa wanda ba Shi ba. Kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima.
وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِۖ وَمَا يَعۡقِلُهَآ إِلَّا ٱلۡعَٰلِمُونَ
Open ayah 29:43Waɗancan misalan Muna ba da su ne ga mutane; ba kuwa wanda yake hankaltar su sai malamai kawai.
خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 29:44Allah Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga muminai.
ٱتۡلُ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَۖ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ تَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۗ وَلَذِكۡرُ ٱللَّهِ أَكۡبَرُۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تَصۡنَعُونَ
Open ayah 29:45Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alƙur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin ƙi. Kuma tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da misalin waɗanda suka riƙi wasu ababen bauta ba Allah ba suna tsammanin za su sami wata kariya ko wani amfani daga gare su. Allah ya kwatanta misalinsu da gizogizo wanda yakan saƙa gidansa da nufin ya kare masa sanyi ko zafi ko iska ko ruwan sama, ko ya kare shi daga wanda zai kai masa harin ta’addanci, to amma daga ƙarshe ba zai samu kariya daga waɗannan abubuwan ba, domin duk a cikin gidajen ƙwari da na dabbobi babu wanda rauninsa ya kai na gidan gizogizo. To hakanan su ma mushirikai, ababen shirkarsu ba za su amfane su da komai ba, da a ce sun san haka da ba su riƙe su ababen bauta ba Allah ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yana sane da duk wani abu da suke bauta wa ba shi ba, babu abin da yake ɓuya a gare shi, kuma shi ne mabuwayi da babu mai gagararsa ko ya rinjaye shi, kuma mai hikima ne cikin ayyukansa da tsarinsa. Sai kuma Allah ya bayyana cewa irin waɗannan misalan da yake bayarwa a Alƙur’ani domin jan hankali da faɗakarwa da tabbatar da gaskiya da rushe ɓarna, babu mai fahimtar su yadda ya dace har su amfane shi sai mutanen da Allah ya ba su ilimin sanin shari’arsa da hikimarsa cikin halittunsa. Sai kuma Allah ya bayyana wata hikimar tasa ta halittar sammai da ƙasa ya tabbatar da cewa ya halicce su ne da gaskiya, watau bai halicce su don wasa ba ko kuma ba don wani amfani ba. Ya tabbatar da cewa lalle a cikin halittarsu da ya yi akwai ayoyi bayyanannu masu nuna girman Ƙudurarsa da isar ikonsa ga mutane muminai, domin su ne suke kafa hujja a kan samuwar mahalicci da halittarsa. Amma kafirai sai dai su yi ta ganin halittun Allah a sama da ƙasa da kawunansu amma ba sa ɗaukar wata izina ko wani darasi daga gare su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya karanta wa mutane Alƙur’ani da ya yi masa wahayinsa, ya kuma tsayar da salla yadda ya kamata da rukunanta da sharuɗanta da mustahabbanta, kuma lalle ita salla idan ana yin ta yadda ya dace to tana hana mai yin ta faɗawa cikin saɓon Allah da munanan ayyuka, domin tana samar da wani haske a cikin zukata wanda yake tsare bawa daga aikata saɓon Allah, yake kuma ƙarfafa masa yin ayyuka na ƙwarai. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle wani yana yin sallar dare amma idan gari ya waye sai ya riƙa yin sata.” Sai Manzon Allah ya ce: “Lalle da sannu abin da kake faɗa (watau sallarsa cikin dare) za ta hana shi (sata).” [Ahmad #9778 da Ibn Hibban #2560]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle ambaton Allah shi ne ya fi komai girma. Kuma Allah ya san abin da mutane suke aikatawa, zai kuma saka wa kowa a kan ayyukansa kyawawa da munana.
۞وَلَا تُجَٰدِلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡۖ وَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَأُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَإِلَٰهُنَا وَإِلَٰهُكُمۡ وَٰحِدٞ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ
Open ayah 29:46Kuma kada ku yi jayayya da ma’abota littafi (Yahudu da Nasara) sai ta hanyar da ta fi kyau, sai dai waɗanda suka yi zalunci daga cikinsu; kuma ku ce: “Mun yi imani da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar muku, kuma Abin bautarmu da Abin bautarku Ɗaya ne, kuma mu masu miƙa wuya ne gare Shi.”
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَۚ فَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۖ وَمِنۡ هَٰٓؤُلَآءِ مَن يُؤۡمِنُ بِهِۦۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 29:47Kamar haka kuma Muka saukar maka da Alƙur’ani. To waɗanda Muka bai wa littafi (a gabaninka) suna imani da shi; daga waɗannan kuma (wato mutanen Makka) akwai wanda yake imani da shi. Ba kuwa mai musun ayoyinmu sai kafirai.
وَمَا كُنتَ تَتۡلُواْ مِن قَبۡلِهِۦ مِن كِتَٰبٖ وَلَا تَخُطُّهُۥ بِيَمِينِكَۖ إِذٗا لَّٱرۡتَابَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ
Open ayah 29:48Ba ka zamanto kuma kana karanta wani littafi kafinsa ba (wato Alkur’ani), kuma ba ka rubuta shi da hannun damanka; da kuwa haka ya faru, to da sai masu ƙaryatawa su shiga kokwanto.
بَلۡ هُوَ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ فِي صُدُورِ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 29:49A’a, shi dai (Alƙur’ani) ayoyi ne bayyanannu (da suke) cikin zukatan waɗanda aka bai wa ilimi. Ba kuwa mai yin musun ayoyinmu sai azzalumai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗakar da Musulmi kan yadda ya kamata su tattauna da ma’abota littafi, musamman bayan sun yi hijira zuwa Madina inda suka haɗu da Yahudawa mazauna birnin Madina. Allah ya nusantar da muminai da su yi jayayya da su ta hanya mafi kyau, watau wa’azi cikin hikima da tausasa harshe da bayanin hujjoji masu gamsarwa yayin da suka fahimci suna so ne su gane gaskiya. Amma azzalumai daga cikinsu masu taurin kai da ƙoƙarin tayar da fitina ko shirin yaƙar Musulmi, to waɗannan sai a tafiyar da su ta hanyar da ta dace. Idan sun shelanta yaƙi to a yaƙe su har sai sun musulunta ko sun miƙa wuya sun zauna da Musulmi lafiya, sun biya jiziyar da take kansu. Sai kuma Allah ya nuna wa Musulmi wasu hanyoyi da za su bi na tattaunawa da ma’abota littafi masu son su fahimci gaskiya, ya ce su nuna musu cewa sun yi imani da abin da Allah ya saukar musu, watau Alƙur’ani, sun kuma yi imani da abin da su ma ya saukar musu, watau Attaura da Linjila. Sannan su sanar da su cewa dukkansu abin bautarsu ɗaya ne ba shi da abokin tarayya a bautarsa ko siffofinsa da ayyukansa. Don haka su tabbatar musu da cewa su sun miƙa wuya gare shi shi kaɗai. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ma’abota littafi suna karanta Attaura da harshen Ibraniyanci suna fassara wa Musulmi da Larabci, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku gaskata ma’abota littafi, kada kuma ku ƙaryata su, ku ce: ‘Mun yi imani da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar muku, kuma abin bautarmu da abin bautarku ɗaya ne, kuma mu masu miƙa wuya ne gare shi.’” [Bukhari #4485, 7362]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzo (ﷺ) cewa kamar yadda ya saukar wa annabawan da suka gabace shi littattafai hakanan shi ma ya saukar masa Alƙur’ani. To wasu daga cikin ma’abota littafi masu karanta Attaura, irin su Abdullahi ɗan Salam suna yin imani da Annabi (ﷺ) saboda sun karanta siffofinsa a littattafansu. Daga cikin mushirikai ma akwai waɗanda suke yin imani da shi, to amma babu masu musun ayoyin Allah sai tsantsar kafirai masu girman kai masu ƙyamar gaskiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hujjar da take ƙara tabbatar da cewa Alƙur’ani saukakke ne daga Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ƙirƙirar Manzon Allah ne ba, ya bayyana wa mushirikai abin da suka riga suka sani na halayensa tun kafin a aiko shi, da cewa ai bai zamanto yana karanta wani littafi ba kafin a saukar masa Alƙur’ani ballantana a ce a ciki ya koya, kuma bai zamanto yana rubuta wani abu da hannunsa ba, domin shi ummiyyi ne ba ya karatu ba ya rubutu. Ashe ba don haka ba da sai jahilai su riƙa shakka game da annabcinsa su fake da cewa Alƙur’anin da yake karanta musu ya samo shi ne daga littattafan magabata. Sai kuma Allah ya tabbatar da cewa shi Alƙur’ani ayoyi ne bayyanannu a zukatan muminai waɗanda aka ba su ilimi, watau waɗannan su ya kamata a saurari maganarsu ba jahilai ba waɗanda ba su san komai daga ayoyinsa ba, waɗannan maganganunsu ba su da wani tasiri. Ya bayyana cewa babu masu jayayya da ayoyin Allah sai azzalumai waɗanda suka cuci kawunansu da shirka da saɓon Allah. An karɓo daga Iyadh ɗan Himar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah (Mai tsarki da daukaka) yana cewa: “Ni mai jarrabar ka ne mai kuma jarrabar wasu ta sanadiyyarka ne, mai saukar maka da wani littafi ne wanda ruwa ba zai wanke shi ba, za ka riƙa karanta shi kana barci ko kana farke.” [Muslim # 2865]. Yana nufin da za a rubuta Alƙur’ani sannan daga baya a wanke shi, to hakan ba zai sa a rasa shi ba, domin yana nan a haddace a zukatan muminai.
وَقَالُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَٰتٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّمَا ٱلۡأٓيَٰتُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٞ مُّبِينٌ
Open ayah 29:50Suka kuma ce: “Me ya hana a saukar masa da wasu ayoyi daga Ubangijinsa?” Ka ce (da su): “Ayoyi suna wurin Allah ne kawai, ni kuma ba kowa ba ne face mai gargaɗi, mai bayyana (gargaɗin).”
أَوَلَمۡ يَكۡفِهِمۡ أَنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَرَحۡمَةٗ وَذِكۡرَىٰ لِقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 29:51Yanzu bai ishe su ba cewa, Mun saukar maka da Littafi da ake karanta musu shi? Lalle a game da wannan tabbas akwai rahama da kuma tunatarwa ga mutanen da suke yin imani.
قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡ شَهِيدٗاۖ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ وَكَفَرُواْ بِٱللَّهِ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 29:52Ka ce (da su): “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku; Yana sane da abin da yake cikin sammai da ƙasa. Waɗanda kuwa suka yi imani da ƙarya suka kuma kafirce wa Allah, waɗannan su ne asararru.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk da ƙarfafan hujjoji da suka tabbatar da gaskiyar Manzo (ﷺ) kafirai sun nace da neman ya kawo musu wasu mu’ujizoji daban waɗanda su suka ambata, suna ganin in da gaske ne shi Manzon Allah ne me zai hana Ubangijinsa ya saukar masa da waɗannan ayoyi? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya faɗa musu cewa shi fa ba a hannunsa saukar da wata aya yake ba; wannan yana wurin Allah ne kawai, shi aikin da Allah ya ɗora masa shi ne ya yi gargaɗi ga mutane dangane da azabar Allah in ba su yi imani ba. Sannan ya sanar da su cewa, yanzu Alƙur’ani da ya saukar masa bai ishe su aya ba? Allah ya nuna girman Alƙur’ani ta hanyar siffanta shi da wasu manyan siffofi kamar haka: <b>Siffa ta farko </b>, littafi ne da ake karanta musu shi, wannan ya nuna yaɗuwarsa ko’ina a kowane zamani, bai taƙaita ga wasu mutane ban da wasu ba, ga shi kuma ya ƙunshi ƙalubale na a kwaikwaye shi idan an isa, amma hakan bai yiwu ba. <b>Ta biyu </b>, kasancewar ana karanta shi a koyaushe kuma a ko’ina ya nuna ya fi sauran mu’ujizoji da Allah ya ba wa sauran annabawa, kamar sandar Annabi Musa ko taguwar Annabi Salihu ko warkar da makaho da tayar da matacce da izinin Allah da aka ba wa Annabi Isa. Waɗannan mu’ujizojinsu na gani ne da ido kawai, sun kuma taƙaita a zamaninsu. Amma mu’ujizar Alƙur’ani ta danganci aiki na ƙwaƙwalwa da tunani na hankali wanda ba mai taƙaita ne ba a wani zamani ban da wani ba; yana ɗorewa ne har zuwa tashin ƙiyama. <b>Ta uku </b>, Alƙur’ani rahama ne, domin ya ƙunshi shari’a wadda take rahama ce ga halittu a kowane lokaci kuma a ko’ina. <b>Ta huɗu </b>, kuma tunatarwa ne, domin ya ƙunshi wa’azi da nasihu iri-iri da jan hankali game da rayuwar lahira; wannan ya ba shi fifiko a kan sauran mu’ujizoji na annabawa. <b>Ta biyar </b>, an danganta rahamar Alƙur’ani da tunatarwarsa ga mutane muminai, domin a nuna cewa amfanin da ke cikinsa babu mai morar sa sai wanda ya yi imani da Manzo Allah (ﷺ), domin shi ne zai gaskata shi ya kuma yi aiki da koyarwarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzo (ﷺ) ya bayyana musu wata ƙaƙƙarfar hujja da ke nuna cewa shi Manzon Allah ne da gaske, watau shaidar da Allah ya yi masa da ta nuna gaskiyarsa ta kuma tabbatar da ƙaryarsu, domin Allah ne wanda ya san abin da yake cikin sammai da ƙasa, ba abin da yake ɓuya a gare shi. Da a ce Manzon Allah (ﷺ) ƙarya yake yi masa da ya fallasa shi, ba zai ƙarfafe shi da ayoyi ba, ba kuma zai yi ta cin nasara ba a kan magabtansa a tsawon rayuwarsa. Sai dai kuma duk da wannan bayani mutanen da suka riga suka yi imani da ƙarya suka rungumi wasu ababen bauta ba Allah ba suka kafirce wa Allah, to waɗannan asararru ne ba za su ci riba ba ko kaɗan, tunda sun fifita kafirci a kan imani da Allah da Manzonsa.
وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَلَوۡلَآ أَجَلٞ مُّسَمّٗى لَّجَآءَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ وَلَيَأۡتِيَنَّهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 29:53Suna kuma neman ka da ka gaggauto musu da azaba. Ba don kuwa akwai lokaci na musamman (da aka tanada) ba, tabbas da azabar ta zo musu, kuma tabbas da za ta zo musu ne ba zato ba tsammani, alhali ba su sani ba.
يَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةُۢ بِٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 29:54Suna (kuma) neman ka da ka gaggauto musu da azaba, alhali kuwa Jahannama tabbas mai kewaye kafirai ce.
يَوۡمَ يَغۡشَىٰهُمُ ٱلۡعَذَابُ مِن فَوۡقِهِمۡ وَمِن تَحۡتِ أَرۡجُلِهِمۡ وَيَقُولُ ذُوقُواْ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 29:55A ranar da azaba za ta lulluɓe su ta samansu da ta ƙarƙashin ƙafafuwansu, kuma (Allah) Ya ce (da su): “Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kuna aikatawa.” Bayan Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya mayar wa da kafirai martani a kan neman a saukar masa da wasu mu’ujizoji don su yarda da manzancinsa, sai suka ci gaba da ƙaryata abin da yake yi musu gargaɗi a kansa na uƙubar Allah idan sun ƙi yin imani, har ma suna neman sa da ya gaggauto musu da azabar in da gaske ne abin da yake faɗa, kada ya jira har sai an je lahira, domin su ba su ma yarda akwai ranar alƙiyama ba ballantana a yi musu hisabi. Sai Allah ya amsa musu da cewa ba abu ne da zai gagare shi ba ya saukar musu da azabar da suke nema, sai dai kawai komai ya sanya masa lokaci wanda ba ya gaggauto shi kafin ya zo kuma ba ya jinkirta shi idan ya zo, amma su san da cewa lalle azabar nan sai ta auko musu ba zato ba tsammani. Ya kuma bayyana musu cewa su daina wata gaggawa don ganin wata gamammiyar azaba ba ta sauka a kansu a nan duniya ba, su sani akwai azabar lahira tana nan tana jiran su, domin lalle Jahannama a kewaye take da su ta ko’ina, ba wurin gudu ko tsere mata. Ya kuma tabbatar musu da cewa wannan azabar ta lahira matsananciya ce, kuma za ta same su ta lulluɓe su ta samansu ta yi musu rumfa, ta ƙasansu kuwa ta zame musu shimfiɗa, Allah kuma ya riƙa ce musu: “Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kuna aikatawa”, watau babu wanda ya zalunce su, su dai ne suka zalunci kawunansu da kafirci da aikata shirka.
يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ أَرۡضِي وَٰسِعَةٞ فَإِيَّٰيَ فَٱعۡبُدُونِ
Open ayah 29:56Ya ku bayina waɗanda suka yi imani, lalle ƙasata yalwatacciya ce, to Ni kaɗai sai ku bauta Mini.
كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۖ ثُمَّ إِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ
Open ayah 29:57Kowanne rai zai ɗanɗani mutuwa; sannan wurinmu za a mayar da ku.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَنُبَوِّئَنَّهُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ غُرَفٗا تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ نِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ
Open ayah 29:58Waɗanda kuma suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, lallai za Mu zaunar da su cikin manya-manyan gidaje a Aljanna (waɗanda) ƙoramu za su riƙa gudana ta ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu. Madalla da ladan masu aiki (nagari).
ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Open ayah 29:59(Su ne) waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu kawai suka dogara.
وَكَأَيِّن مِّن دَآبَّةٖ لَّا تَحۡمِلُ رِزۡقَهَا ٱللَّهُ يَرۡزُقُهَا وَإِيَّاكُمۡۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 29:60Sau tari ga dabba nan da ba za ta iya ɗaukar arzikinta ba, Allah ne Yake arzuta ta har da ku. Shi ne Mai ji, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira bayinsa waɗanda suka yi imani da shi, suka kuma yi imani da Manzonsa (ﷺ) amma suna zaune a cikin kafirai suna tsangwamar su a kan addininsu har ma suna ƙoƙarin su hana su bautar Allah shi kaɗai, to sai ya umarce su da yin hijira zuwa inda za su sami ‘yancin bautar Allah shi kaɗai ba tare da tsangwama ba domin ƙasarsa mai yalwa ce. Sai kuma ya nuna musu cewa, kada tsoron mutuwa ya hana su yin hijira da gujewa su tsira da addininsu, domin ita mutuwa rigar kowa ce, duk wani mai rai sai ya ɗanɗane ta, sannan daga ƙarshe duk za a mayar da su ne zuwa ga Allah (Mai tsarki da daukaka) ranar alƙiyama don a yi musu hisabi a kan ayyukansu, a bayyana sakamakon waɗanda suka yi imani tare da ayyuka nagari, a shigar da su ɗakunan Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, su zauna a cikinsu zama na har abada babu mutuwa. Allah kuma ya yi musu sam-barka a kan wannan kyakkyawan sakamako da zai ba wa waɗanda suka yi ayyukan ɗa’a gare shi. Allah ya siffanta waɗannan bayi nasa masu rabauta da wannan gwaggwaɓan sakamako da cewa su ne waɗanda suka yi haƙuri a kan yi masa biyayya da kauce wa saɓa masa, da haƙuri game da cutarwar mushirikai a gare su. Su ne kuma masu dogaro ga Allah shi kaɗai cikin dukkan al’amuransu. Sai kuma Allah ya ƙara jan hankalin muminai a kan kada tsoron talauci ko yunwa ya hana su yin hijira zuwa inda za su bauta masa shi kaɗai, ya bayyana musu cewa da yawa daga cikin dabbobi waɗanda ba za su iya ciyar da kansu ba ko su tara wa kansu arziki, Allah ne yake ciyar da su, kuma su ma mutanen shi ne yake ciyar da su, don haka ba su da wani hanzari na ƙin yin hijira don tsoron talauci ko yunwa. Sannan ya tabbatar musu da cewa shi mai jin duk maganganun da suke furtawa ne, masanin niyyoyinsu da ayyukansu ne, zai kuma yi musu sakayya a kan haka.
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۖ فَأَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ
Open ayah 29:61Tabbas da za ka tambaye su: “Wane ne ya halicci sammai da ƙasa, ya kuma hore rana da wata?” To tabbas za su ce: “Allah ne.” To ta yaya ake karkatar da su (daga kaɗaita Shi)?
ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُ لَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ
Open ayah 29:62Allah Yana shimfiɗa arziki ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, Ya kuma ƙuntata masa. Lalle Allah Masanin komai ne.
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّن نَّزَّلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ مِنۢ بَعۡدِ مَوۡتِهَا لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 29:63Kuma tabbas da za ka tambaye su: “Wane ne ya saukar da ruwa daga sama, sai ya raya ƙasa da shi bayan mutuwarta?” Lalle za su ce: “Allah ne.” Ka ce (da su): “Alhamdu Lillahi .” A’a, yawancinsu dai ba sa hankalta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda mushirikan Larabawa suka riƙa tufka da warwara game da Tauhidi. Domin idan da Manzon Allah (ﷺ) zai tambaye su wane ne ya halicci sammai da ƙasa, ya kuma hore rana da wata suna maye gurbin juna? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa za su amsa masa da cewa Allah ne ya halicce su. To in haka ne me ya sa ake karkatar da su daga yin imani da Kaɗaitakarsa, har suke bauta wa wasu iyayen giji ba shi ba? Sai ya tabbatar musu da cewa shi ne yake yalwata arzikinsa ga wanda ya ga dama daga bayinsa, yake kuma ƙuntata wa wanda ya ga dama saboda wata hikima da shi kaɗai ya san ta, saboda lalle shi masanin komai ne dangane da hanyoyin gudanar da al’amuran bayinsa yadda ya dace da rayuwarsu a bayan ƙasa, babu abin da ya gagare shi. Sai kuma ya bayyana cewa da Manzon Allah (ﷺ) zai tambaye su cewa wane ne ya saukar da ruwa daga sama wanda da shi ne ya fitar da tsirrai daga ƙasa bayan ta bushe ƙayau? Allah ya tabbatar masa da cewa lalle amsarsu ita ce, Allah ne ya yi hakan. Sai ya umarci Manzonsa da ya yabi Ubangiji ya gode masa game da hujja mabayyaniya da ya ba shi a kansu, ya kuma bayyana masa cewa yawancinsu ba sa hankalta, ba don haka ba da ba su riƙa bautar gumaka tare da Allah ba alhalin suna ganin ba sa amfanar su da komai, kuma ba sa iya cutar da su da komai ballantana su ji tsoron su su bauta musu.
وَمَا هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا لَهۡوٞ وَلَعِبٞۚ وَإِنَّ ٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَ لَهِيَ ٱلۡحَيَوَانُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 29:64Kuma wannan rayuwar duniya ba komai ba ce face sharholiya da wasa. Kuma lalle (rayuwar) gidan lahira ita ce rayuwa, in da sun kasance sun sani.
فَإِذَا رَكِبُواْ فِي ٱلۡفُلۡكِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ إِذَا هُمۡ يُشۡرِكُونَ
Open ayah 29:65To idan suka hau jiragen ruwa sukan roƙi Allah suna masu tsantsanta addini a gare Shi; to lokacin da Ya tserar da su zuwa tudu sai ga su suna yin shirka.
لِيَكۡفُرُواْ بِمَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ وَلِيَتَمَتَّعُواْۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 29:66Don su kafirce wa abin da Muka ba su, kuma don su ji daɗi; to da sannu za su sani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matsayin rayuwar duniya da zamantowarta ba komai ba idan an kwatanta ta da rayuwar lahira. Ya siffanta rayuwar duniya da cewa ita sharholiya ce kawai da wasa, saboda abin da ke cikinta na sha’awace-sha’awace da ƙyale-ƙyale masu ɗaukan hankali da ruɗi. Rayuwa ta haƙiƙa ita ce rayuwar lahira wadda ba ta da ƙarshe. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa da kafirai sun san zaɓen tumun daren da suka yi da ba su fifita rayuwar duniya a kan ta lahira ba; da ba su ɗauki mai gushewa ba sun bar mai dawwama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata tufka da warwara ta mushirikan Ƙuraishawa game da kaɗaita Allah da ikhlasi wajen roƙon sa da cewa, idan suka shiga jirgin ruwa ya fara tangal-tangal da su, suka hango hallaka a fili, sai su kira Allah shi kaɗai suna masu tsantsanta addu’arsu a gare shi, domin ya tserar da su daga nutsewa a ruwa, sai su manta da allolinsu. Amma da zarar ya kuɓutar da su daga hallaka sun haye tudu, sai su koma su ci gaba da bautar gumakansu, suna kuma yin haka ne don su butulce wa ni’imomin da Allah ya yi musu. Sai Allah ya yi musu talala da cewa su je su yi ta more abin da aka ba su na jin daɗin duniya, ba da jimawa ba za su gane babban kuskuren da suka tafka a rayuwarsu lokacin da mutuwa ta zo musu.
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا جَعَلۡنَا حَرَمًا ءَامِنٗا وَيُتَخَطَّفُ ٱلنَّاسُ مِنۡ حَوۡلِهِمۡۚ أَفَبِٱلۡبَٰطِلِ يُؤۡمِنُونَ وَبِنِعۡمَةِ ٱللَّهِ يَكۡفُرُونَ
Open ayah 29:67Yanzu ba su ga cewa, Mu Muka sanya musu Harami amintacce ba, alhali kuwa ana ta fauce mutane a kewayensu? Shin yanzu sa riƙa yin imani da ƙarya su kuma riƙa kafirce wa ni’imar Allah?
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُۥٓۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 29:68Wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya ƙaga wa Allah ƙarya ko kuma ya ƙaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu ashe babu mazaunar kafirai a cikin Jahannama?
وَٱلَّذِينَ جَٰهَدُواْ فِينَا لَنَهۡدِيَنَّهُمۡ سُبُلَنَاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَمَعَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 29:69Waɗanda kuma suka yi jihadi saboda Mu to tabbas za Mu shiryar da su hanyoyinmu, kuma lalle Allah Yana tare da masu kyautatawa. A ayoyin ƙarshe na wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata babbar ni’ima da ya yi wa Ƙuraishawa amma suke butulce masa suna kafirce wa Manzonsa (ﷺ). Allah ya tunatar da su ni’imar zaman lafiya da ya yi musu a garin Makka, babu mai zubar da jininsu ko ya ƙwace musu dukiyarsu, a yayin da sauran garuruwa ake ta kai musu hare-hare ana kashe su ana kama su ribatattun yaƙi, ana kuma kama matansu da ‘ya’yansu a matsayin bayi, sannan a wawashe musu dukiyoyinsu. Amma duk wannan ni’imar ba sa ganin ta, sun rungumi allolin ƙarya suna imani da su suna bautar su suna kuma butulce wa ni’imar Allah ba sa gode masa ko kaɗan. Sai kuma Allah ya bayyana cewa babu azzalumin da ya kai wanda zai ƙirƙiri ƙarya ya jingina wa Allah, ya ce wai Allah yana da abokin tarayya ko yana da ɗa, ko kuma ya ƙaryata gaskiyar da Manzon Allah (ﷺ) ya zo masa da ita. Allah ya tabbattar musu da cewa lalle a Jahannama akwai mazaunar kafirai da makamantansu. Sai kuma Allah ya bayyana makomar muminai da sakamakonsu da cewa, duk waɗanda suka yi gwagwarmaya saboda shi, suka bar garuruwansu na haihuwa, suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu, tabbas zai shiryar da su hanyoyinsa na alheri, su dace da bin tafarki madaidaici, kuma lalle shi yana tare da masu kyautatawa da taimakonsa da nasararsa.