الروم

Ar-Room

The Romans · Surah 30 · Ayahs: 60 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓمٓ

    Open ayah 30:1

    ALIF LAM MIM.

  2. غُلِبَتِ ٱلرُّومُ

    Open ayah 30:2

    An yi galaba a kan Rumawa.

  3. فِيٓ أَدۡنَى ٱلۡأَرۡضِ وَهُم مِّنۢ بَعۡدِ غَلَبِهِمۡ سَيَغۡلِبُونَ

    Open ayah 30:3

    A ƙasa mafi kusa (da su), su kuma da sannu za su yi galaba (a kan Farisa) bayan galabar da aka yi a kansu.

  4. فِي بِضۡعِ سِنِينَۗ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ مِن قَبۡلُ وَمِنۢ بَعۡدُۚ وَيَوۡمَئِذٖ يَفۡرَحُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 30:4

    A cikin ‘yan tsirarun shekarun (da ba su kai goma ba). Al’amari a da can da nan gaba na Allah ne. A wannan ranar ne muminai za su yi farin ciki.

  5. بِنَصۡرِ ٱللَّهِۚ يَنصُرُ مَن يَشَآءُۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

    Open ayah 30:5

    Da samun nasar Allah (a kan Farisa). Shi Yake taimakon wanda Ya ga dama; domin kuwa Shi ne Mabuwayi, Mai rahama.

  6. وَعۡدَ ٱللَّهِۖ لَا يُخۡلِفُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 30:6

    (Wannan ya kasance) alƙawarin Allah ne; Allah ba Ya saɓa alƙawarinsa, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka) ba.

  7. يَعۡلَمُونَ ظَٰهِرٗا مِّنَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ عَنِ ٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ غَٰفِلُونَ

    Open ayah 30:7

    Suna sanin abin da yake a sarari na rayuwar duniya ne, alhali kuwa su gafalallu ne game da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da wasu haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori a baya da irin waɗannan haruffa. [Duba bayaninsu a farkon Suratul Baƙara ]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin galabar da Farisawa suka samu a kan Rumawa a mafi kusancin lardin Sham da ƙasar Farisa, amma kuma ya tabbatar da cewa daga baya Rumawa su ne za su yi galaba a kan Farisawa a cikin ‘yan shekaru waɗanda ba za su kasa uku ba, ba kuma za su wuce tara ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa dukkan al’amura nasa ne, kafin su ci nasara da kuma bayan sun yi nasara. Sai kuma ya bayyana cewa ranar da Rumawa za su yi nasara a kan Farisawa abokan faɗansu, a wannan ranar Musulmi za su cika da farin ciki domin ganin cewa Rumawa ma’abota littafi ne kamarsu, watau mabiya addinin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah ya tabbatar da cewa shi ne yake ba da nasara ga wanda ya ga dama a kan wanda ya ga dama. Shi kuma mabuwayi ne babu mai iyawa da shi, mai rahama ne ga bayinsa muminai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan nasara da zai ba wa Rumawa alƙawari ne da ya ɗaukar wa kansa, kuma duk sanda wannan alƙawari ya tabbata, to farin cikin muminai zai ƙaru da yaƙininsu game da gaskiyar alƙawarinsa, to amma duk da haka yawancin mutane saboda kafircinsu ba sa fahimtar haka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yawancinsu ba sa yin imani da hukunce-hukuncen shari’a. Abin da kawai suka sani shi ne yadda za su shirya wa kawunansu rayuwar duniya da gina ta da samar da abubuwan more rayuwa, amma kuma dangane da rayuwar lahira wadda ita ce rayuwa ta haƙiƙa mai ɗorewa masu bijirewa ne, wannan rayuwar ba ta gabansu.

  8. أَوَلَمۡ يَتَفَكَّرُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۗ مَّا خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ بِلِقَآيِٕ رَبِّهِمۡ لَكَٰفِرُونَ

    Open ayah 30:8

    Yanzu ba su yi tunani a kan kansu ba? Allah bai halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu ba sai da gaskiya kuma (ya yi su zuwa) lokaci ƙayyadajje. Lalle mafi yawan mutane masu kafircewa ne da haɗuwa da Ubangijinsu.

  9. أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَأَثَارُواْ ٱلۡأَرۡضَ وَعَمَرُوهَآ أَكۡثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

    Open ayah 30:9

    Shin ba za su yi tafiya a bayan ƙasa ba su ga yadda ƙarshen waɗanda suka gabace su ya zama? Sun kasance sun fi su tsananin ƙarfi, sun kuma tona ƙasa suka kuma raya ta fiye da yadda su (mutanen Makka) suka raya ta, kuma manzanninsu sun zo musu da (ayoyi) bayyanannu; to Allah bai kasance Mai zaluntar su ba, sai dai su ne suka kansance suna zaluntar kawunansu.

  10. ثُمَّ كَانَ عَٰقِبَةَ ٱلَّذِينَ أَسَٰٓـُٔواْ ٱلسُّوٓأَىٰٓ أَن كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ بِهَا يَسۡتَهۡزِءُونَ 

    Open ayah 30:10

    Sannan kuma ƙarshen waɗanda suka munana (ayyukansu) ya kasance mummunan (sakamako), don sun ƙaryata ayoyin Allah, kuma sun kasance suna yin izgili gare su. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin mushirikai cewa me zai hana su nutsuwa su yi tunani a kan kawunansu, su ga irin halittar da ya yi musu, ya daidaita musu ita ta hanya mai ban mamaki, sannan su fahimci cewa Allah bai halicci sammai da ƙasa don wasa ba, ya halicce su ne da gaskiya don a bauta masa shi kaɗai, ya kuma sanya musu ƙayyadajjen lokaci na wanzuwarsu a duniya; idan lokacin gushewarsu ya yi Allah zai tafiyar da su ya canja su da wasu domin yin hisabi. Sai kuma Allah ya nuna cewa yawancin mutane suna kafirce wa haɗuwarsu da Ubangijinsu ranar alƙiyama, wannan ne ya hana su yin wani kazar-kazar domin tanadin zuwan wannan rana ta hanyar yin imani da ayyuka nagari. Sai kuma Allah ya bayyana cewa, me ya sa su waɗannan masu ƙaryata Manzonsa (ﷺ) ba za su yi yawo a ƙasashen duniya ba, domin su samo darussa na al’ummun da suka gabace su waɗanda suka ƙaryata annabawansu, su ga yadda ƙarshensu ya zama. Allah ya bayyana musu cewa waɗancan al’ummun da aka yi a baya sun fi su tsananin ƙarfi na jiki, domin mutane ne da suka tona ƙasa suka yi noma da gine-gine a kanta, suka raya ta da abubuwan more rayuwa fiye da yadda su mushirikai masu ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) suka yi. Amma kuma yayin da manzanninsu suka zo musu da hujjoji bayyanannu masu nuna Kaɗaitakar Allah sai suka ƙaryata su, sai ko Allah ya hallaka su, ya kuma tabbatar musu da cewa bai zalunce su da komai ba, su ne dai suka zalunci kawunansu ta hanyar kafirce wa Allah da manzanninsa da aikata ayyuka na saɓon Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ƙarshen dai mutanen da suka munana ayyukansu da aikata shirka da saɓon Allah ƙarshe ne da ya yi matuƙar muni a gare su, saboda sun ƙaryata ayoyin Allah sun riƙa izgili da su.

  11. ٱللَّهُ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

    Open ayah 30:11

    Allah ne Yake farar halitta sannan Ya dawo da ita (bayan mutuwa), sannan kuma gare Shi za a komar da ku.

  12. وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُبۡلِسُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

    Open ayah 30:12

    Kuma ranar da alƙiyama za ta tashi, a wannan ranar ne masu manyan laifuka (kafirai) za su yanke ƙauna daga rahama.

  13. وَلَمۡ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَآئِهِمۡ شُفَعَٰٓؤُاْ وَكَانُواْ بِشُرَكَآئِهِمۡ كَٰفِرِينَ

    Open ayah 30:13

    Daga abokan tarayyar tasu kuwa ba su da wasu masu ceton su, za su ma kasance masu kafirce wa abokan tarayyar tasu.

  14. وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوۡمَئِذٖ يَتَفَرَّقُونَ

    Open ayah 30:14

    Kuma ranar da alƙiyama za ta tashi, a wannan ranar ne (mutane) za su rarrabu.

  15. فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَهُمۡ فِي رَوۡضَةٖ يُحۡبَرُونَ

    Open ayah 30:15

    To amma waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to su kam suna cikin dausayin (Aljanna) ana faranta musu rai.

  16. وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَلِقَآيِٕ ٱلۡأٓخِرَةِ فَأُوْلَٰٓئِكَ فِي ٱلۡعَذَابِ مُحۡضَرُونَ

    Open ayah 30:16

    Amma kuma waɗanda suka kafirta suka kuma ƙaryata ayoyinmu da haɗuwa da ranar lahira, to waɗannan za a halartar da su cikin azaba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da kawo dalilai masu tabbatar da tashin alƙiyama wanda mushirikai suke ƙaryatawa. Allah ya bayyana cewa shi ne mai ƙirƙirar halitta ba tare da ya gani a wurin wani ya kwaikwaya ba, sannan zai kashe abin da ya halitta idan lokacin mutuwarsa ya zo, sannan zai sake dawo da shi da ransa, sannan zuwa wajensa ne za a mayar da kowa domin yin hisabi da sakamakon ayyuka a ranar alƙiyama. Sai kuma Allah ya bayyana halin da kowa zai tsinci kansa a ciki a wannan ranar da cewa, masu manyan laifuka, watau kafirai, za su fitar da tsammanin samun rahamar Allah, domin a ranar duk wata hujjarsu ta yin kafirci za ta zo ƙarshe, kuma daga duk gumakan da suka riƙa bautar su a nan duniya tare da Allah su rasa samun waɗanda za su cece su daga azabar Allah kamar yadda suke riyawa a duniya, sai ma a wannan rana za su zamanto masu kafirce musu ne, su nesantar da kansu daga shirkar da suka yi wa Allah da su, domin dukkansu za su yi tarayya cikin hallaka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rarrabuwar mutane kashi biyu a ranar. <b>Kashi na farko </b>, su ne muminai waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to waɗannan za a saka su gidajen Aljanna a kuma yi ta faranta musu rai ta hanyar tanadar musu ni’ima ta har abada ba mai yankewa ba. <b>Kashi na biyu </b>, su ne waɗanda suka kafirce wa Allah suka kuma ƙaryata ayoyin da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ), suka kuma ƙaryata tashi bayan mutuwa da ranar hisabi, to waɗannan su ne za a jefa su cikin azabar wutar Jahannama inda za su yi ta zama har abada.

  17. فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمۡسُونَ وَحِينَ تُصۡبِحُونَ

    Open ayah 30:17

    To tsarki ya tabbata ga Allah yayin kuka shiga lokacin maraice, da kuma yayin da kuka wayi gari.

  18. وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَعَشِيّٗا وَحِينَ تُظۡهِرُونَ

    Open ayah 30:18

    Yabo kuma nasa ne a cikin sammai da ƙasa, da kuma yayin da kuka yi yammaci da kuma shigowarku lokacin azahar.

  19. يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَيُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ

    Open ayah 30:19

    Yana fitar da rayayye daga matacce, Yana kuma fitar da matacce daga rayayye, kuma Yana raya ƙasa bayan mutuwarta. Kamar haka ne ku ma za a fito da ku (daga ƙaburburanku). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da tsarkakarsa daga duk wata tawaya ko wani aibi ko nakasa, kuma babu wani abu mai kama da shi a cikin halittunsa kakaf, don haka ya umarci bayinsa da su yi masa tasbihi, su tsarkake shi yayin da suka shiga lokacin maraice, watau lokutan sallar magariba da isha’i. Hakanan su yi masa tasbihi su tsarkake shi lokacin da suka wayi gari, watau lokacin sallar asuba. Sannan ya tabbatar wa da kansa dukkan siffofin yabo da kirari, a sammai mala’iku suna yabon sa, a ƙasa kuma sauran halittunsa suna yabon sa. Sai kuma ya umarci bayinsa da su yi masa tasbihi, su tsarkake shi yayin da suka shiga yammaci, watau lokacin sallar magariba da isha\'i, da kuma yayin shigarsu lokacin asuba, watau sallar asuba. Kuma ya bayyana cewa shi ne kaɗai wanda cikakke yabo da kirari ya tabbata a gare shi a cikin sammai da ƙasa. Duk halittunsa suna gode masa tare da yabon sa, don haka ya umarci bayaninsa su tsarkake shi lokacin shigar marece, watau sallar la\'asar, su kuma tsarkake shi lokacin azahar, watau lokacin sallar azahar. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakkiyar Ƙudurarsa da ikonsa, ta fitar da rayayye daga matacce, kamar fito da mutum daga ɗigon maniyyi, da fitar da ɗan tsako daga ƙwan kaza. Hakanan yake fitar da matacce daga cikin rayayye, kamar fitar da maniyyi daga mutum ko fitar da ƙwai daga kaza. Shi ne kuma mai raya ƙasa bayan ta bushe saboda rashin ruwa, sai ya saukar mata da ruwa daga nan sai ta fitar da tsirranta. To wannan cikakkiyar Ƙudura ta Allah ita take tabbatar da cewa zai fito da matattu daga ƙaburburansu bayan mutuwa domin yi musu hisabi a ranar alƙiyama.

  20. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ إِذَآ أَنتُم بَشَرٞ تَنتَشِرُونَ 

    Open ayah 30:20

    Yana daga ayoyinsa cewa Ya halicce ku daga turɓaya, sannan kuma sai ga ku mutane kun warwatsu (a ko’ina).

  21. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا لِّتَسۡكُنُوٓاْ إِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُم مَّوَدَّةٗ وَرَحۡمَةًۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

    Open ayah 30:21

    Yana kuma daga ayoyinsa cewa Ya halitta muku mata daga jinsinku don ku samu nutsuwa gare su, Ya kuma sanya soyayya da jin ƙai tsakaninku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu manyan dalilai masu tabbatar da cikar Ƙudurarsa da cancantar ɗayanta shi da bauta, da kuma tashi bayan mutuwa. <b>Na farko </b>, halittar mutum ta farko daga yumɓu, yayin da ya halicci asalin ubansu Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga yumɓu. Sai kuma daga nan mutane suka ci gaba da yaɗuwa ta hanyar hayayyafa, suka kuma warwatsu a ko’ina a bayan ƙasa. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah Ta’ala ya halicci Adamu daga damƙa ta ƙasa da ya ɗebo ta daga dukkanin dangogin ƙasa, sai ‘ya’yan Adamu suka zo gwargwadon launukan wannan ƙasar, daga cikinsu akwai ja akwai fari akwai baƙi akwai tsaka-tsaki; akwai mai sauƙin kai akwai kuma mai wuyar sha’ani; akwai nagari akwai kuma mugu.” [Abu Dawud #4693 da Tirmizi #2955]. Wannan aya ce mai nuna cewa wanda ya halicce ku daga asali guda, watau turɓaya, sannan ya yaɗa ku ko’ina a bayan ƙasa shi ne Ubangiji Ɗaya wanda zai iya dawo da ku bayan mutuwa. <b>Na biyu </b>, halitta wa maza matansu na aure daga jinsinsu domin su samu nutsuwa da junansu, sannan ya sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu. Allah ya tabbatar da cewa lalle a cikin wannan aiki nasa akwai dalilai bayyanannu ga mutane masu tunani masu amfani da hankalin da Allah ya ba su.

  22. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡعَٰلِمِينَ

    Open ayah 30:22

    Yana kuma daga cikin ayoyinsa <b>halittar sammai da ƙasa da kuma sassaɓawar harsunanku da launukanku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga ma’abota ilimi.

  23. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبۡتِغَآؤُكُم مِّن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ

    Open ayah 30:23

    Yana kuma daga cikin ayoyinsa <b>baccinku da daddare da kuma rana da neman falalarsa da kuke yi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga masu ji (na lura). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana ayoyinsa masu nuna cikakken ikonsa da Kaɗaitakarsa da Ƙudurarsa. <b>Na uku </b>, akwai halittar sammai da ƙasa. Daga cikin abubuwan da Allah ya ajiye a bayan ƙasa kuma akwai ‘yan’adam waɗanda ya yi su da harsuna iri-iri da launuka daban-daban, duk kuwa da kasancewarsu sun samo asali daga mutum guda ne, watau Annabi Adamu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa lalle a cikin wannan aiki nasa akwai ayoyi ga mutane masu ilimi da basira. <b>Na huɗu </b>, barci da mutane suke yi da daddare ko da rana domin samun hutu daga wasu ayyukan gajiya. Hakanan akwai watsuwa da suke yi da rana domin neman arziki daga Allah (Mai tsarki da daukaka); Allah ya tabbatar da cewa lalle a cikin wannan aiki nasa akwai hujjoji da dalilai ga mutane masu ji na lura da sauraro na fahimta da karɓa.

  24. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ يُرِيكُمُ ٱلۡبَرۡقَ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَيُحۡيِۦ بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

    Open ayah 30:24

    Yana kuma daga cikin ayoyinsa nuna muku walƙiya da Yake yi don tsoratarwa da kwaɗaitarwa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya ƙasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane da suke hankalta.

  25. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَن تَقُومَ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ بِأَمۡرِهِۦۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمۡ دَعۡوَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ إِذَآ أَنتُمۡ تَخۡرُجُونَ

    Open ayah 30:25

    Yana k <b>uma daga cikin ayoyinsa sama da ƙasa su tsaya da umarninsa. Sannan kuma yayin da Ya kira ku (don ku tashi) daga ƙasa sai ga ku kuna fitowa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ambaton ayoyinsa masu nuna cikar Ƙudurarsa: <b>Na biyar </b>, akwai walƙiya da yake nuna wa bayinsa gabanin saukar ruwan sama. Sai walƙiyar ta kasance tare da tsawa mai tsoratarwa, tare da sanya musu rai ga samun ruwan sama. Sai ko Allah ya saukar da ruwan sama wanda zai raya ƙasa bayan bushewarta ya fitar da tsirrai a kanta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa lalle a cikin wannan aiki nasa akwai dalilai masu ƙarfi ga mutane masu hankali. Wannan ya isa ya zama hujja a kan yiwuwar tashi bayan mutuwa domin hisabi da sakamako. <b>Na shida </b>, akwai tsayuwar sama ba tare da wani ginshiƙi da ya tokare ta ba ya hana ta faɗowa, da kuma tsayuwar ƙasa da izininsa (Mai tsarki da daukaka) ba tare da tana tangal-tangal ba. To mai wannan Ƙudura da zai riƙe sammai da ƙasa da ita tabbas yana da iko idan ya kira halittarsa domin tashi daga ƙaburburansu sai kawai a gan su suna ta fitowa daga cikin ƙasa.

  26. وَلَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ كُلّٞ لَّهُۥ قَٰنِتُونَ

    Open ayah 30:26

    Kuma duk waɗanda suke cikin sammai da ƙasa nasa ne; dukkaninsu masu biyayya ne gare Shi.

  27. وَهُوَ ٱلَّذِي يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَهُوَ أَهۡوَنُ عَلَيۡهِۚ وَلَهُ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 30:27

    Shi ne wanda Yake farar halittu, sannan Ya dawo da su (bayan mutuwa. Yin haka) kuwa shi ya fi sauƙi a gare Shi. Kuma siffofi mafiya ɗaukaka sun tabbata gare Shi a cikin sammai da ƙasa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk abin da yake cikin sammai da ƙasa halittarsa ne, mulkinsa ne kuma bayinsa ne, dukkansu masu ƙasƙantar da kai ne da miƙa wuya a gare shi. Sai kuma ya ambaci cewa shi ne wanda ya ƙagi halitta ba tare da ya gani ya kwaikwaya ba, sannan shi ne zai dawo da abin da ya halitta bayan mutuwarsa, kuma dawo da shi ma ya fi sauƙi a gare shi a bisa ƙiyasin ɗan’adam, domin ƙagar abu daga babu ya fi maimaita yinsa a karo na biyu wuya, amma a wurin Allah duk ɗaya ne wajen sauƙi, domin shi idan yana nufin aikata wani abu cewa kawai yake da shi ‘kasance’, sai abin ya kasance. Sai kuma Allah ya tabbatar da cewa shi ne wanda yake da siffofi mafiya ɗaukaka da kamala a sammai da ƙasa, shi kuma ne mabuwayi wanda ya fi ƙarfin kowa, kuma mai hikima ne a cikin duk ayyukansa. An karɓo daga Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah yana cewa: “Ɗan’adam ya ƙaryata ni, bai kuma dace ya yi min haka ba. Ya kuma zage ni, bai kuma dace da shi ya yi min haka ba. Amma ƙaryatawar da ya yi mini cewarsa: ‘Ba zai dawo da ni ba kamar yadda ya fare ni’, alhalin ƙirƙirar halittar da farko ba ta fi min dawo da ita sauƙi ba. Amma zagi na kuwa da ya yi cewa da yake yi: ‘Allah ya riƙi ɗa’, alhalin ni ne Ɗaya tilo wanda ake nufi da buƙata, wanda bai haifa ba ba a kuma haife shi ba, kuma ba ya da wanda yake daidai da shi.” [Bukhari #4974].

  28. ضَرَبَ لَكُم مَّثَلٗا مِّنۡ أَنفُسِكُمۡۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُم مِّن شُرَكَآءَ فِي مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ فَأَنتُمۡ فِيهِ سَوَآءٞ تَخَافُونَهُمۡ كَخِيفَتِكُمۡ أَنفُسَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

    Open ayah 30:28

    Ya ba ku misali daga kawunanku; shin kuna da wasu abokan tarayya daga bayinku da kuka mallaka a kan da abin da Muka arzuta ku (da shi), ku da su ku zama daidai kuke game da wannan; kuna ma jin tsoron su kamar yanda kuke tsoron junanku? Kamar haka Muke rarrabe ayoyin (filla-filla) ga mutanen da suke hankalta.

  29. بَلِ ٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَهۡوَآءَهُم بِغَيۡرِ عِلۡمٖۖ فَمَن يَهۡدِي مَنۡ أَضَلَّ ٱللَّهُۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّٰصِرِينَ

    Open ayah 30:29

    Ba haka ba ne, waɗanda suka yi zalunci dai sun bi son ransu ne ba tare da wani ilimi ba; to wane ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar? Kuma ba su da wasu mataimaka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da misalin munin shirka ta hanyar amfani da rayuwar mushirikai don su yi tunani su gane munin aƙidar bautar wanin Allah. Ya bayyana cewa, yanzu shin cikinsu su mushirikai za a iya samun waɗanda suka mallaki bayi da barori waɗanda za su yi tarayya da su a cikin dukiyoyinsu da duk abin da suka mallaka har bayin nan su riƙa sarrafa dukiyarsu yadda suke so ba tare da neman izininsu ba, har ta kai suna jin tsoron kada bayin nasu su kwashe musu duk abin da suka mallaka, kamar yadda idan ‘ya’ya sun haɗa tarayya ta dukiya da wasu ‘ya’yan suke jin tsoron junansu kada sashensu ya hau kan dukiyar sashe? Tabbas babu wani mushiriki da zai yarda da wannan ga kansa, to amma me ya sa suke riya cewa Allah mahaliccin talikai yana da wasu ababen tarayya daga cikin abin da ya halitta da kansa a matsayin bayinsa kuma mulkinsa? Me ya sa suka yarda da cewa waɗannan ababen tarayya da suka riƙa suna iya yin tasarrufi a cikin sha’anin Ubangiji kamar yadda yake yi? Babu shakka wannan misali ne Allah ya ba da shi domin kawo musu gaskiya kusa da hankulansu, ta yadda duk mai hankali zai gane. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai ba sun ɓata ne saboda rashin samun gamsasshiyar hujja a kan ɓacin abin da suke kai ba, a’a, sun saki gaskiya ne domin bin son zuciya da kuma makauniyar biyayya ga iyayensu waɗanda suka samu a kan ɓata. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa waɗannan mutane sun riga sun ɓata ba su da wani uzuri da za su kawo a gabansa. To shin ko akwai wani wanda zai iya shiryar da wanda Allah ya riga ya ɓatar? Babu shakka babu mai iya yin haka. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa a ranar alƙiyama ba su da wasu mataimaka da za su kare su dag azabar Allah.

  30. فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗاۚ فِطۡرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَيۡهَاۚ لَا تَبۡدِيلَ لِخَلۡقِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ 

    Open ayah 30:30

    To sai ka tsayar da fuskarka ga addini mai kauce wa ɓarna. (Shi ne) asalin halittar da Allah Ya halicci mutane a kanta. Ba wani canji ga halittar Allah. Wannan shi ne miƙaƙƙen addinin, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka ba).

  31. ۞مُنِيبِينَ إِلَيۡهِ وَٱتَّقُوهُ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

    Open ayah 30:31

    ( <b>Kuma) kuna masu komawa zuwa gare Shi (wato Allah) kuma ku kiyaye dokokinsa ku kuma tsai da salla kuma kada ku zamanto cikin mushirikai.

  32. مِنَ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمۡ وَكَانُواْ شِيَعٗاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ

    Open ayah 30:32

    Irin waɗanda suka rarraba addininsu suka kuma zamanto ƙungiya-ƙungiya; kowacce ƙungiya tana mai farin ciki da abin da yake nata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ma duk wanda ya yi imani da shi cewa ya tsayar da fuskarsa kyam ga addini miƙaƙƙe wanda ya ɗora shi a kansa ya umarce shi da ya bi shi, yana mai karkace wa duk wasu gurɓatattun addinai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa Musulunci shi ne addinin da ya dace da halittar Allah ta asali wadda ya halicci mutane a kanta, kuma babu wani canji ga halittar tasa. Sai ya sake tabbatar masa da cewa wannan umarni da ya ba shi shi ne addini miƙaƙƙe wanda babu karkata a cikinsa, sai dai yawancin mutane ba su san haka ba. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Babu wani yaro da za a haifa sai a kan halittarsa ta asali (watau fiɗira ) sai dai daga baya ne iyayensa suke mayar da shi Bayahude ko su mayar da shi Banasare ko Bamajuse. Kamar yadda ake haifar dabba mai cikakkiyar halitta, shin kukan gan ta da yagaggen kunne?” Sannan sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta wannan ayar.” [Bukhari #4775 da Muslim #2658]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su koma ga Allah tare da yin tuba daga zunubbansu su kuma kiyaye dokokinsa ta hanyar aikata abin da ya wajabta musu da guje wa abin da ya haramta musu, kuma su tsayar da salla kamar yadda ya dace. Ya kuma gargaɗe su da kada su kasance daga cikin mushirikai waɗanda suka gurɓata halittunsu na asal,i suka haɗa Allah da wasu a wajen bauta, ko kuma su zama cikin mushirikai waɗanda suka yi wa addininsu a-yaga, watau suka yi imani da wani sashe nasa suka kafirce wa wani sashe, sai suka rarraba ƙungiya-ƙungiya, kowace ƙungiya suna farin ciki da ɓarnar da suke kai, domin suna ganin su kaɗai ne a kan gaskiya, duk sauran a kan ɓata suke.

  33. وَإِذَا مَسَّ ٱلنَّاسَ ضُرّٞ دَعَوۡاْ رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَآ أَذَاقَهُم مِّنۡهُ رَحۡمَةً إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُم بِرَبِّهِمۡ يُشۡرِكُونَ

    Open ayah 30:33

    Idan kuma wani matsi ya sami mutane sai su roƙi Ubangijinsu suna masu komawa gare Shi, sannan kuma idan Ya ɗanɗana musu rahama daga gare Shi sai ka ga wata ƙungiyar daga cikinsu suna tarayya da Ubangijinsu.

  34. لِيَكۡفُرُواْ بِمَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡۚ فَتَمَتَّعُواْ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 30:34

    Don su kafirce wa abin da Muka ba su. To ku ji daɗi, da sannu za ku sani.

  35. أَمۡ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٗا فَهُوَ يَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُواْ بِهِۦ يُشۡرِكُونَ

    Open ayah 30:35

    Ko kuma Mun saukar musu da wani littafi ne wanda shi ne yake magana da abin da suka kasance suna shirka da shi?

  36. وَإِذَآ أَذَقۡنَا ٱلنَّاسَ رَحۡمَةٗ فَرِحُواْ بِهَاۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ إِذَا هُمۡ يَقۡنَطُونَ

    Open ayah 30:36

    Idan kuma Muka ɗanɗana wa mutane rahama sai su yi farin ciki da ita; idan kuwa wata masifa ta same su saboda abin da hannayensu suka gabatar sai ka gan su suna ɗebe ƙauna.

  37. أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

    Open ayah 30:37

    Yanzu ba su gani ba cewa Allah Yana shimfiɗa arziki ga wanda Ya ga dama, Yana kuma ƙuntatawa (ga wanda ya ga dama)? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin wasu mutane mushirikai masu butulce wa ni’imomin da yake yi musu a kai-a kai, da cewa akwai wasu mutane waɗanda idan wani tsanani ya same su, kamar rashin lafiya ko talauci ko fari, sai su marairaice wa Allah suna roƙon sa shi kaɗai domin ya yaye musu masifarsu. Sai idan ya ji ƙan su ya raba su da masifar da suke ciki, sai kawai a samu wasu daga cikinsu sun koma sun ci gaba da shirkar da suke yi wa Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan hali nasu shi ne ya kai su ga kafirce wa ni’imomin da ya ba su, don haka ya yi musu talala da cewa su ci gaba da jin daɗin rayuwarsu ta duniya, da sannu za su gani da idanunsu a ranar alƙiyama su tabbatar da cewa sun kasance a kan ɓata mabayyani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci mushirikai a kan hujjarsu ta yin shirka da shi. Shin ya saukar musu da wani littafi ne wanda suke kafa hujja da shi a kan shirkarsu? Ba shakka a fili yake cewa babu wani littafi saukakke tare da su wanda yake goyon bayan shirkar da suke yi da Allah, ko wani aikin kafirci ko na saɓo. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wata mummunar ɗabi’a ta mutane, sai dai waɗanda Allah ya tsare, da cewa idan ya ba su wata ni’ima daga cikin ni’imominsa, kamar lafiya ko arziki sai su riƙa farin ciki na girman kai da wannan ni’imar, amma idan wani mummunan abu ne ya same su, kamar rashin lafiya ko talauci sakamakon laifuffukansu, sai kawai a gan su suna ɗebe ƙauna daga samun rahamar Allah, ko su fitar da rai cewa Allah zai iya yaye musu abin da yake damun su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jawo hankalinsu da cewa, yanzu ba sa ganin Allah ne yake yalwata arzikinsa ga wanda ya ga dama daga bayinsa don ya jarrabe shi ya ga ko zai gode masa ko kuma zai butulce masa? Yake kuma ƙuntata wa wanda ya ga dama daga cikinsu don ya jarrabe shi ya ga ko zai yi haƙuri ba zai yi raki ba? Allah ya tabbatar da cewa a cikin wannan aiki nasa lallai akwai ayoyi masu nuna cikar rahamarsa da luɗufinsa ga mutane muminai.

  38. فَـَٔاتِ ذَا ٱلۡقُرۡبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلۡمِسۡكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يُرِيدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

    Open ayah 30:38

    Sannan ka bai wa (ɗan’uwa) makusanci haƙƙinsa da miskini da matafiyi. Wannan shi ya fi alheri ga waɗanda suke nufin Fuskar Allah; kuma waɗannan su ne masu rabauta.

  39. وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن رِّبٗا لِّيَرۡبُوَاْ فِيٓ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ فَلَا يَرۡبُواْ عِندَ ٱللَّهِۖ وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن زَكَوٰةٖ تُرِيدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُضۡعِفُونَ

    Open ayah 30:39

    Kuma abin da kuka bayar na riba don ya ƙaru a cikin dukiyoyin mutane, to ba ya ƙaruwa a wurin Allah; abin kuma da kuka bayar na zakka kuna masu nufin Fuskar Allah, to waɗannan su ne masu ninninka (ladansu).

  40. ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ ثُمَّ رَزَقَكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡۖ هَلۡ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَفۡعَلُ مِن ذَٰلِكُم مِّن شَيۡءٖۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ 

    Open ayah 30:40

    Allah (Shi ne) Wanda Ya halicce ku sannan Ya arzuta ku sannan Shi zai kashe ku sannan Ya raya ku; shin a cikin abokan tarayyarku akwai wanda zai aikata wani abu daga wannan? Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma ɗaukaka daga abin da suke tarawa (da Shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Musulmi da ya ba wa ɗan’uwansa makusanci haƙƙinsa yayin da yake cikin wata buƙata domin kyautata masa da kuma sada zumunci da ke tsakaninsu; da kuma miskini mabuƙaci shi ma ya ba shi abin da zai biya masa buƙatarsa gwargwadon halinsa. Hakanan ya taimaka wa matafiyin da guzurinsa ya yanke don ya sami abin da zai mayar da shi garinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa irin wannan taimako da yake umarni da shi shi ne mafi alheri ga mutanen da suke fuskantar Allah don neman yardarsa, kuma masu ba da irin wannan taimako lalle su ne masu samun babban rabo, watau gidan Aljanna da kuɓuta daga azabar Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana aikin da wasu mutane suke yi ba don Allah ba sai don nufin tara abin duniya wanda ba zai kai su ko’ina ba. Irin wannan aiki shi ne bayar da dukiyarsu bashi ga wasu mutane don su dawo musu da ita tare da ƙari, watau kuɗin riba. To wannan aiki nasu ba zai ƙare su da komai ba a wurin Allah, sai dai ya rushe duk wata albarka daga cikin dukiyarsu, kuma ba su da wani lada a wurin Allah, domin aikinsu ya rasa ikhlasi wanda sharaɗi ne na karɓar ayyukan bayi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) Ya tabbatar da cewa duk wani abu da za su bayar na dukiyarsu don Allah ga wani, don ya yi maganin buƙatarsa, ba don neman wani matsayi ko yabo daga mutane ba, to waɗannan su ne ake riɓanya musu ladansu a wurin Allah. Malaman tafsiri da dama daga cikin magabata da ‘yan baya sun fassara wannan ayar da cewa, a nan Allah yana hana su bayar da kyauta ne don tsammanin a rama musu da mafi yawan abin da suka bayar. Ya nuna musu cewa irin wannan kyautar ba ta da lada a wurin Allah, domin ba don shi aka yi ta ba, an yi ta ne domin a sami ƙari. Sai kuma Allah ya bayyana musu irin kyautar da za su yi su sami ninkin ladanta a wurinsa, ita ce wadda za su yi dominsa shi kaɗai. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Wanda ya yi sadaka da kwatankwacin ƙwayar dabinuwa ɗaya ta kuɗin halal, domin Allah ba ya karɓa sai abin da yake halal ne, to Allah zai karɓi (sadakarsa) da hannunsa na dama, sannan ya yi masa renonta kamar yadda ɗayanku yake renon ɗan duƙushin dokinsa, har sai ta koma kamar dutse babba.” [Bukhari #1410 da Muslim #1014]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi kaɗai ne ya keɓanta da yin halitta da arzutawa da kashewa sannan da rayawa bayan mutuwa domin yin hisabi ranar alƙiyama. Ya tabbatar da cewa babu wani abu da masu shirka suke yin shirka da shi da zai iya yin ɗaya daga cikin waɗannan ayyukan, ko ya yi tarayya da shi a cikinsu. Sai kuma ya tsarkake kansa daga duk abin da suke yin shirka da shi. Abin da kuma suke yin shirka ba zai cutar da shi da komai ba sai dai su su cuci kawunansu.

  41. ظَهَرَ ٱلۡفَسَادُ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ بِمَا كَسَبَتۡ أَيۡدِي ٱلنَّاسِ لِيُذِيقَهُم بَعۡضَ ٱلَّذِي عَمِلُواْ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

    Open ayah 30:41

    Ɓarna ta bayyana a kan tudu da kuma (cikin) ruwa saboda abubuwan da hannayen mutane suka aikata don a ɗanɗana musu sashin abin da suka aikata, ko wataƙila sa juyo.

  42. قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلُۚ كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّشۡرِكِينَ

    Open ayah 30:42

    Ka ce (da su): “Ku yi tafiya mana a bayan ƙasa sannan ku duba ku ga yadda ƙarshen waɗanda suke gabaninku ya zama. Yawancinsu sun kasance mushirikai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ɓarna da fasadi suka bayyana a bayan ƙasa suka watsu a ko’ina, mutane da yawa kuma suna shirka da Allah, wasu suna zaluntar bayin Allah da aikata laifuffuka iri daban-daban, wanda hakan ya haifar da lalacewar rayuwa a tudu da ruwa, cututtuka suka yawaita a bainar jama’a, aka rasa samun zaman lafiya, sai yaƙe-yaƙe da fitintinu, duk kuwa wannan ‘yan’adam ne suka jawo wa kawunansu shi saboda munanan ayyukansu, domin Allah ya ɗanɗana musu wani sashi na sakamakon ayyukansu tun a nan duniya domin fatan su koma gare shi su tuba su gyara halayensu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Manzonsa (ﷺ) cewa ya umarci mushirikai su yi tafiya a bayan ƙasa don su gane wa idanuwansu yadda al’ummun da suka gabace su suka ƙaryata manzanninsu suka yi mummunan ƙarshe. Yawancinsu shirka suka yi wa Allah suna bautar wasu ba shi ba, sai ya hallaka su saboda hakan.

  43. فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ ٱلۡقَيِّمِ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۖ يَوۡمَئِذٖ يَصَّدَّعُونَ

    Open ayah 30:43

    To sai ka tsai da fuskarka ga addini madaidaici tun kafin ranar nan da ba ta da makawa ta zo daga Allah; a wannan ranar ne (mutane) za su rarraba.

  44. مَن كَفَرَ فَعَلَيۡهِ كُفۡرُهُۥۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا فَلِأَنفُسِهِمۡ يَمۡهَدُونَ

    Open ayah 30:44

    Wanda ya kafirta to zunubin kafircinsa yana kansa; waɗanda kuwa suka yi aiki kyakkyawa, to kansu suke yi wa shimfiɗa (ta alheri).

  45. لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 30:45

    Don (Allah) Ya saka wa waɗanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari daga falalarsa. Lalle Shi (Allah) ba Ya son kafirai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya tsayar da fuskarsa kyam ga addinin Musulunci wanda yake miƙaƙƙe ne babu wata karkata a cikinsa, ta hanyar tsantsanta bauta ga Allah da bin umarninsa da guje wa haninsa a zahiri da baɗini cikin rayuwarsa ta nan duniya tun gabanin zuwan ranar da ba ta da makawa daga Allah, watau ranar alƙiyama wadda ba za a jinkirta wa mutane ba idan ta zo don su yi wani aiki, ba abin da zai kasance a ranar sai sakamako. A wannan ranar mutane za su rarrabu; wasu a nufi gidan Aljanna da su a sanya su cikin ni’imominta; wasu kuma a nufi gidan wutar Jahannama da su a jefa su cikin azabarta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk abin da ya sami wani a wannan ranar to sakamakon aikinsa ne na nan duniya ya gani, don haka wanda ya kafirce wa Allah kansa ya cuta, domin zai dawwama ne a cikin wutar Jahannama; wanda kuwa ya yi kyakkyawan aiki don Allah, to shi ma kansa yake yi wa shimfiɗa ta alheri wadda za ta kai shi ga shiga Aljanna ya zauna a cikin ni’imominta har abada. Sai kuma ya bayyana dalilin rarrabuwarsu ƙungiyoyi biyu a lahira, da cewa ya yi haka ne domin ya saka wa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari da kyakkyawan sakamako fiye da aikinsu. Su kuma waɗanda suka kafirce masa da manzanninsa Allah ya tabbatar da cewa ba ya son kafirai, don haka za su gamu da fushinsa da azabarsa a ranar alƙiyama.

  46. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَن يُرۡسِلَ ٱلرِّيَاحَ مُبَشِّرَٰتٖ وَلِيُذِيقَكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَلِتَجۡرِيَ ٱلۡفُلۡكُ بِأَمۡرِهِۦ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

    Open ayah 30:46

    Yana kuma daga ayoyinsa cewa Yana aiko iska tana mai yin albishir (da ruwa) kuma don Ya ɗanɗana muku rahamarsa, don kuma jiragen ruwa su riƙa gudana da umarninsa, kuma don ku nema daga falalarsa ko kwa gode. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake bayanin cikar Ƙudurarsa da gamammiyar rahamarsa ga bayinsa, da cewa daga cikin manya-manyan ayoyinsa masu nuna cikar Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa shi ne yana aiko da iska mai yi wa bayinsa albishir na saukar ruwan sama, daga nan sai ya saukar musu da ruwa don ya ɗanɗana musu rahamarsa su sami yalwar ruwan sama amfanin gonakinsu ya yi kyau, don kuma jiragen ruwansu su riƙa gudana a kan koguna ɗauke da su da kayayyakinsu da izininsa, don kuma su nemi falalarsa ta hanyar yin kasuwanci a cikin ruwa. Duk Allah ya yi musu waɗannan abubuwa ne domin su gode masa, shi kuma ya ƙara musu.

  47. وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ رُسُلًا إِلَىٰ قَوۡمِهِمۡ فَجَآءُوهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَٱنتَقَمۡنَا مِنَ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْۖ وَكَانَ حَقًّا عَلَيۡنَا نَصۡرُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

    Open ayah 30:47

    Haƙiƙa kuma Mun aiko wasu manzanni gabaninka zuwa ga mutanensu, sai suka zo musu da hujjoji bayyanannu, sai Muka azabtar da waɗanda suka kafirce, kuma taimakon muminai ya zama haƙƙi ne a kanmu. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ba yanzu ne ya fara aiko da manzo ba. Ya aiko da manzanni tun gabanin Manzo (ﷺ) zuwa ga al\'ummunsu masu aikata shirka da kafirci a bayan ƙasa. Manzannin suka je musu da hujjoji da dalilai masu ƙarfi masu tabbatar da gaskiyarsu, to amma sai suka ƙaryata abin da manzanninsu suka je musu da shi, sai Allah ya saukar da azabarsa ga waɗanda suka kafirce masa suka ƙaryata manzanninsa, ya hallaka su baki ɗaya, ya kuma kuɓutar da manzanninsa da waɗanda suka yi imani daga hallaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa ya wajabta wa kansa taimakon waɗanda suka yi imani a koyaushe.

  48. ٱللَّهُ ٱلَّذِي يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابٗا فَيَبۡسُطُهُۥ فِي ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ يَشَآءُ وَيَجۡعَلُهُۥ كِسَفٗا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ يَخۡرُجُ مِنۡ خِلَٰلِهِۦۖ فَإِذَآ أَصَابَ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ إِذَا هُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ

    Open ayah 30:48

    Allah (Shi ne) wanda Yake aiko da iska sai ta motsa girgije, sai Ya shimfiɗa shi a (sararin) sama yadda Ya ga dama, Ya kuma sanya shi yanki-yanki, sai ka ga ruwa yana fitowa ta tsakaninsa, to idan Ya saukar da shi ga waɗanda Ya ga dama daga bayinsa sai ka gan su suna ta murna.

  49. وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلِ أَن يُنَزَّلَ عَلَيۡهِم مِّن قَبۡلِهِۦ لَمُبۡلِسِينَ

    Open ayah 30:49

    Ko da yake da can kafin a saukar musu shi tabbas sun kasance masu ɗebe ƙauna.

  50. فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ 

    Open ayah 30:50

    To sai ka yi duba ga guraben rahamar Allah (ka ga) yadda Yake raya ƙasa bayan mutuwarta. Lalle wannan tabbas Mai raya matattu ne, kuma Mai iko ne a kan komai.

  51. وَلَئِنۡ أَرۡسَلۡنَا رِيحٗا فَرَأَوۡهُ مُصۡفَرّٗا لَّظَلُّواْ مِنۢ بَعۡدِهِۦ يَكۡفُرُونَ

    Open ayah 30:51

    Tabbas kuma in da za Mu aiko da iska su gan shi (wato amfanin gonarsu) ya yi fatsi-fatsi da sai su ci gaba da kafirce wa (Allah) bayan haka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana dalilai da hujjoji masu nuna Ƙudurarsa da ikonsa a kan tayar da matattu bayan mutuwa da kuma cikakkiyar rahamarsa da ta yalwaci komai, da cewa shi ne wanda yake aiko da iska iri daban-daban sai ta haɗo hadari sannan ta motsa shi, sai Allah ya shimfiɗa shi a sararin sama yadda ya ga dama, kaɗan ko mai yawa, sannan ya mayar da shi yanki-yanki, sai a riƙa ganin ruwa yana saukowa daga tsakaninsa; to duk waɗanda suka yi dace wannan ruwa ya sauka gare su da yardar Allah sai su cika da farin ciki game da rahamar Allah da ta sauka gare su, sai gonakinsu su yi kyau su sami abincinsu da na dabbobinsu da ruwan shansu da na dabbobinsu. Allah ya bayyana halin da suke ciki kafin saukar wannan ruwan, watau har sun kasance sun ɗebe ƙaunar saukarsa domin ganin ya yi jinkirin zuwa, don haka ganinsa ya saka su cikin farin ciki mai yawa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) cewa ya duba ya ga guraben saukar wannan ruwa ya ga yadda ya cika da rahamar Allah ga bayinsa, ta yadda yake raya ƙasa da dangogin tsirrai iri-iri bayan ƙeƙashewarta na wani tsawon lokaci. Allah ya tabbatar da cewa lalle wanda ya iya raya wannan ƙeƙasasshiyar ƙasa tabbas zai iya dawo da matattu da ransu bayan mutuwa, domin shi mai iko ne a kan komai babu abin da zai gagare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara fito da butulcin masu kafirce wa ni’imomin Allah da mantawa da rahamar da yake yi musu. Ya rantse cewa da zai aiko wa da gonakinsu wata iska wadda za ta lalata musu shuke-shukensu su yi fatsi-fatsi su lalace bayan da farko sun yi kore shar, to da sun koma suna kafirce wa duk ni’imomin da ya yi musu a baya ba tare da sun duba yawan rahamarsa da ya yi musu ba a can baya, watau maimakon su gode masa a kan ni’imominsa da ya yi musu marasa iyaka, su kuma yi haƙuri su dogara gare shi idan wani abin ƙi ya same su daga baya, to amma sai suka juyar da al’amarin, ba su gode masa ba a can baya sannan kuma suka dawo suka butulce masa.

  52. فَإِنَّكَ لَا تُسۡمِعُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَلَا تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا وَلَّوۡاْ مُدۡبِرِينَ

    Open ayah 30:52

    To lalle kai ba ka iya jiyar da matattu, kuma ba ka iya jiyar da kurame kira lokacin da suka juya suna masu ba da baya.

  53. وَمَآ أَنتَ بِهَٰدِ ٱلۡعُمۡيِ عَن ضَلَٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ

    Open ayah 30:53

    Kuma kai ba mai iya shiryar da makafi (wato ɓatattu) ba ne daga ɓatansu; ba waɗanda kake iya jiyarwa sai waɗanda suka yi imani da ayoyinmu don haka suna masu miƙa wuya. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ƙwararan dalilai da hujjoji masu nuna Kaɗaitakarsa da cikakkiyar Ƙudurarsa a kan tayar da matattu da tashin alƙiyama domin hisabi, babu abin da kafirai suke ƙara yi sai bijirewa da kafircewa, sai Allah ya nuna wa Manzonsa cewa waɗannan kafirai sun zama kamar matattu ne ko kurame. To kamar yadda ba zai iya jiyar da matattu ko ya jiyar da kurame ba, hakanan ba zai iya jiyar da waɗanda suka bijire suka ƙi yarda su amfana da hujjojin da ake kawo musu ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa waɗannan ɓatattun da suka ƙi bin hanyar shiriya madaidaiciya ba zai iya dawo da su kan hanya ba, domin sun riga sun makance ba sa ganin gaskiya.

  54. ۞ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن ضَعۡفٖ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعۡدِ ضَعۡفٖ قُوَّةٗ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعۡدِ قُوَّةٖ ضَعۡفٗا وَشَيۡبَةٗۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡقَدِيرُ

    Open ayah 30:54

    Allah (Shi ne) Wanda Ya halicce ku daga rauni, sannan kuma Ya sanya ƙarfi bayan raunin, sannan kuma Ya sanya rauni da furfura bayan ƙarfi. Yana halittar abin da Ya ga dama; Shi ne kuwa Masani, Mai iko. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu daga cikin ayoyin da ke tattare da halittar ɗan’adam da matakai daban-daban da yake bi ta kansu a rayuwarsa, masu nuna cikar Ƙudurar Allah da yalwar iliminsa da hikimarsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi ne ya halicci mutane suka fara daga rauni, watau lokacin da suke jarirai, har zuwa girmansu, sannan ya ba su ƙarfi bayan rauni, watau lokacin da suka kai ganiyar ƙarfinsu, sannan ya sake sanya musu rauni bayan ƙarfinsu, watau lokacin da tsufa ya cim musu. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) yake halittar abin da ya ga dama, ya sanya masa rauni ko ya sanya masa ƙarfi, shi ne masanin komai, babu abin da yake ɓuya a gare shi, kuma mai iko ne a kan komai, babu abin da yake gagararsa.

  55. وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُقۡسِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ مَا لَبِثُواْ غَيۡرَ سَاعَةٖۚ كَذَٰلِكَ كَانُواْ يُؤۡفَكُونَ

    Open ayah 30:55

    Kuma a ranar da alƙiyama za ta tashi masu manyan laifuka za su rantse (kan) ba su zauna ba (a ƙaburburansu) fiye da sa’a ɗaya. Kamar haka suka kasance ana karkatar da su (daga gaskiya).

  56. وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَٱلۡإِيمَٰنَ لَقَدۡ لَبِثۡتُمۡ فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡبَعۡثِۖ فَهَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡبَعۡثِ وَلَٰكِنَّكُمۡ كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 30:56

    Waɗanda kuwa aka bai wa ilimi da imani sai suka ce: “Haƙiƙa kun zauna ne gwargwadon yadda Allah Ya rubuta muku a littafinsa har zuwa ranar tashi; to wannan kuma ita ce ranar tashin, sai dai kuma ku kun kasance ba ku san (haka) ba.”

  57. فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَعۡذِرَتُهُمۡ وَلَا هُمۡ يُسۡتَعۡتَبُونَ

    Open ayah 30:57

    To a wannan ranar waɗanda suka yi zalunci hanzarinsu ba zai amfane su ba, kuma ba za a nemi su kawo wani uzuri ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ƙwararan hujjoji a kan tashi bayan mutuwa domin hisabi, sai kuma ya bayyana wani abu da zai faru a ranar alƙiyama tsakanin kafirai masu ƙaryata ta da muminai waɗanda suka yi imani da zuwanta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa ranar da alƙiyama za ta tsaya, masu manyan laifuka, watau kafirai, za su riƙa rantsuwa a kan cewa ba su zauna a ƙaburburansu ba sai wani ɗan lokaci kaɗan. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata su ya tabbatar da cewa, kamar yadda suka kasa gane tsawon lokacin zamansu a ƙaburburansu, hakanan suka kasance a duniya ana karkatar da su daga bin gaskiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara da cewa, waɗanda Allah ya ba wa ilimi da imani za su mayar musu da martani da cewa lalle sun zauna gwargwadon abin da Allah ya riga ya rubuta musu za su zauna tun daga lokacin halittarsu har zuwa ranar da aka tashe su daga ƙaburburansu, watau ranar alƙiyama, kuma wannan ita ce ranar tashin da suka ƙaryata a duniya, ga ta sun gan ta da idanuwansu, to amma a da sun kasance ba su san haka ba don haka ne suka kafirce wa ranar. Sai kuma Allah ya tabbatar musu da cewa a wannan ranar da zai tayar da halittu gaba ɗaya, domin hisabi da ba da sakamakon ayyuka, duk wani hanzari da azzalumai za su ƙirƙiro su faɗa ba zai amfane su ba, kuma ba za a ba su wata dama ta su tuba a karɓi tubansu ba, domin lokacinta ya riga ya wuce.

  58. وَلَقَدۡ ضَرَبۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖۚ وَلَئِن جِئۡتَهُم بِـَٔايَةٖ لَّيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا مُبۡطِلُونَ

    Open ayah 30:58

    Kuma haƙiƙa Mun ba wa mutane kowane irin misali a cikin wannan Alƙur’anin. Kuma tabbas idan da za ka zo musu da wata aya lallai da waɗanda suka kafirce sun ce: “Ai ku maɓarnata ne kawai.”

  59. كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 30:59

    Kamar haka ne Allah Yake toshe zukatan waɗanda ba sa sanin (gaskiya).

  60. فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ وَلَا يَسۡتَخِفَّنَّكَ ٱلَّذِينَ لَا يُوقِنُونَ 

    Open ayah 30:60

    Sai ka yi haƙuri, lalle alƙawarin Allah gaskiya ne; kada kuma waɗanda ba sa sakankancewa (da alƙiyama) su ingiza ka (har ka kasa haƙuri). A waɗannan ayoyi na ƙarshen Surar, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa bayan ya bayyana duk wasu dalilai masu gamsarwa a kan Ɗayantakarsa da kuma tashin alƙiyama, duk da haka yawancin kafirai sun ci gaba da ƙaryatawa, don haka babu wani dalili ko hujja da ta yi saura wadda za su gani su yi imani. Allah kuma ya bayyana cewa ya buga wa mutane kowane irin misali a cikin Alƙur’ani domin su bambance tsakanin ƙarya da gaskiya, amma yawancinsu sun bijire mata, to da Manzon Allah (ﷺ) zai zo musu da wata ayar daban mai nuna gaskiyarsa, tabbas da sai sun faɗa masa shi da muminai cewa, ba a kan komai suke ba sai ƙarya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa yadda ya toshe zukatan waɗannan kafiran har suka kasa fahimtar gaskiya, to kamar haka ne yake toshe zukatan duk waɗanda ba su san cewa abin da ya zo da shi gaskiya ne ba. Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi haƙuri a kan ƙaryata shi da mutanensa suke yi, ya tabbatar masa cewa alƙawarin da ya yi masa na samun nasara da kafuwa a bayan ƙasa gaskiya ne, kuma mai tabbata ne babu makawa. Ya kuma gargaɗe shi da cewa kada ya yarda waɗanda ba su sakankance da tashinsu ranar alƙiyama ba su ingiza shi ya kasa haƙuri, har ya nemi a gaggauto da abin da suke son a gaggauto musu da shi.