لقمان
Luqman
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
الٓمٓ
Open ayah 31:1ALIF LAM MIM.
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡحَكِيمِ
Open ayah 31:2Waɗannan ayoyin littafi ne mai hikima.
هُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 31:3Shiriya ne da rahama ga masu kyautatawa.
ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ
Open ayah 31:4Waɗanda suke tsai da salla suke kuma ba da zakka alhali su kuma suna masu sakankancewa da ranar lahira.
أُوْلَٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدٗى مِّن رَّبِّهِمۡۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Open ayah 31:5Waɗannan suna kan shiriya daga Ubangijinsu; waɗannan su ne masu rabauta. </b> Surar ta buɗe da haruffa kamar yadda wasu surori a gabaninta suka buɗe da irin waɗannan haruffa. [Duba farkon Suratul Baƙara don ƙarin bayani a kansu]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗannan ayoyi da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) ayoyi ne na littafin Alƙur’ani wanda yake cike da hikima, kuma shiriya ne ga mutane masu kyautata ayyukansu da sauke haƙƙoƙinsu tsakaninsu da Allah da tsakaninsu da sauran mutane ‘yan’uwansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta waɗannan bayi nasa da cewa su ne masu tsayar da salla yadda ya kamata; suna yin ta a lokutanta da kula da hukunce-hukunceta. Suna kuma fitar da zakka daga cikin dukiyoyinsu, suna ba da ita ga waɗanda suka cancanci su ba su. Sannan kuma sun sakankance da ranar lahira kuma sun yi imani da abin da zai wakana a cikinta na hisabi da kyakkyawan sakamako da mummuna. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa lalle masu waɗannan siffofi su ne suka tabbata a bisa shiriya ta Ubangijinsu, su ne kuma masu samun babban rabo, domin za su samu abin da suke nema na kyakkyawan sakamako, sannan za a tsare su daga duk wani abin ƙi.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشۡتَرِي لَهۡوَ ٱلۡحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّخِذَهَا هُزُوًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ
Open ayah 31:6Daga mutane kuma akwai wanda yake sayen zantuka na sharholiya don ya ɓatar (da mutane) daga hanyar Allah ba tare da wani ilimi ba, yana kuma riƙon ta abar yi wa izgili. (Irin) waɗannan azaba mai wulaƙantarwa ta tabbata gare su.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا وَلَّىٰ مُسۡتَكۡبِرٗا كَأَن لَّمۡ يَسۡمَعۡهَا كَأَنَّ فِيٓ أُذُنَيۡهِ وَقۡرٗاۖ فَبَشِّرۡهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
Open ayah 31:7Idan kuma ana karanta masa ayoyinmu sai ya juya yana mai girman kai kamar bai ji su ba, kamar a ce akwai wani nauyi a cikin kunnuwansa; to ka yi masa albishir da azaba mai raɗaɗi. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci mutanen kirki masu amfanuwa da sauraron Alƙur’ani, sai kuma ya bayyana halayyar wasu marasa imani masu bijire wa sauraronsa da karkata a kan sauraron wasu waƙe-waƙe da sautuka na banza waɗanda Shaiɗan yake ƙawata musu yana ingiza su ciki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa a cikin mutane akwai wanda yake zaɓar maganganu masu shagaltarwa kamar waƙoƙin banza da kaɗe-kaɗe da labaru marasa manufa don ya ɓatar da mutane ya kautar da su daga addinin Allah ba tare da ilimi ba, ya kuma riƙa yin izgili ga ayoyin Allah. Allah ya tabbatar da cewa masu irin wannan hali suna da wata azaba mai wulaƙantarwa a ranar alƙiyama. Da yawa daga cikin magabata na ƙwarai sun bayyana cewa ma’anar ‘zance mai shagaltarwa’ da aka ambata a cikin ayar yana nufin waƙe-waƙe. Daga cikin masu wannan fassara akwai Abdullahi ɗan Mas’ud da Abdullahi ɗan Abbas da Jabir ɗan Abdullahi da Sa’idu ɗan Jubair da Mujahid da Ikrima da sauransu. [Dubi, Mausu’atut Tafsiril Ma’asur , Juzu’i na 17, shafi na 493-500]. Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya kasance yana yin rantsuwa da Allah wanda babu abin bauta da gaskiya sai shi cewa, ‘zance mai shagaltarwa’ ana nufin waƙe-waƙe, har sau uku. [Dubi, Ibni Jarir, Jami’ul Bayan , Juzu’i na 18, shafi na 534 da Al-Baihaƙi, As-Sunanul Kubra , Juzu’i na 10, shafi na 225]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana mummunan halin mai shagalta da wasu maganganu ya yi watsi da Alƙur’ani da cewa, idan ana karanta masa ayoyin Allah sai kawai ya juya baya yana mai girman kai kamar ma bai ji abin da ake karanta masa ba, ya yi kunnen uwar shegu kamar wanda ya kurumce, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi masa albishir da azaba mai raɗaɗi da take jiran sa a ranar alƙiyama.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّٰتُ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 31:8Lalle <b> waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari suna da (sakamakon) gidajen Aljanna na ni’ima.
خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 31:9Suna madawwama a cikinsu; alƙawarin Allah kuwa gaskiya ne. Kuma Shi Mabuwayi ne, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kyakkyawar makoma ta waɗanda suka karɓi ayoyin Allah suka yi aiki da su a nan duniya, da cewa lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, to suna da sakamakon gidajen Aljanna na zama waɗanda Allah ya tanadar musu don su shige su su ji daɗi a cikinsu har abada babu ranar da za a fitar da su daga cikinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa wannan alƙawari ne tabbatacce da ya ɗauka. Kuma shi Allah mabuwayi ne babu mai cin galaba a kansa, mai hikima ne cikin halittarsa da ƙaddararsa da shari’arsa.
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيۡرِ عَمَدٖ تَرَوۡنَهَاۖ وَأَلۡقَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمۡ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٖۚ وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ
Open ayah 31:10Ya halicci sammai ba tare da wani ginshiƙi da kuke ganin sa ba, Ya kuma kafa manya-manyan duwatsu a cikin ƙasa don kada ta riƙa tangal-tangal da ku, Ya kuma yaɗa kowace irin dabba a cikinta. Kuma Mun saukar da ruwa daga sama sai Muka tsirar da kowane irin dangin tsiro mai ƙayatarwa.
هَٰذَا خَلۡقُ ٱللَّهِ فَأَرُونِي مَاذَا خَلَقَ ٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦۚ بَلِ ٱلظَّٰلِمُونَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 31:11Wannan (ita ce) halittar Allah, sai ku nuna min abin da waɗanda ba Shi ba suka halitta. A’a, su dai azzalumai suna cikin ɓata ne mabayyani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikar Ƙudurarsa da kamalar ikonsa waɗanda da su ya cancanci bauta shi kaɗai, da cewa shi ne ya halicci sammai da muke ganin su babu wasu ginshiƙai da suka tallabe su, ya kuma dasa kafaffun duwarwatsu a cikin ƙasa domin kada ta riƙa tangal-tangal da masu rayuwa a bayanta, ya kuma barbaza dangogin dabbobi iri-iri a bayan ƙasa. Sannan ya saukar da ruwan sama wanda a sanadiyyarsa ne ƙasa take tsirar da kowane nau’i na tsirrai masu ban sha’awa da amfani ga mutane da dabbobi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci kafirai masu bautar waninsa cewa ga dai waɗannan manya-manyan halittu da aka ambata duk aikinsa ne halittarsa ne shi kaɗai, su kuma sai su nuna masa abin da allolinsu da suke bauta wa suka halitta. Allah ya tabbatar musu da cewa su dai kawai azzalumai ne da suke cikin ɓata bayyananne yayin da suka zaɓi su riƙa haɗa shi da wasu wajen bauta, alhalin sun san shi kaɗai ne ya yi halitta, gumakansu ba su halicci komai ba tunda su ma sassaƙa su aka yi.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا لُقۡمَٰنَ ٱلۡحِكۡمَةَ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِلَّهِۚ وَمَن يَشۡكُرۡ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٞ
Open ayah 31:12Haƙiƙa kuma Mun bai wa Luƙumanu hikima cewa: “Ka yi godiya ga Allah. Kuma duk wanda yake godewa to yana godewa ne don kansa, wanda kuwa ya kafirta to lalle Allah Mawadaci ne, Sha-yabo.” A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin wani bawansa ne mutumin kirki da ya hore wa ilimi da hikima, mai suna Luƙumanu. Ya ba shi fahimtar addini da gane al’amura yadda suke. Babu wani nassi da ya tabbata game da cewa Luƙumanu annabi ne. Yawancin malamai sun amince da cewa shi wani salihin bawa ne da Allah ya yi masa baiwar hikima da ilimi. Malaman tafsiri da na tarihi sun ambaci cewa ya rayu ne a zamanin Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a cikin garuruwan Banu Isra’ila. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci hikimomin da ya ba shi cewa, ya hore shi a kan ya yi wa Allah godiya bisa wannan ni’ima da ya yi masa, ya kuma tabbatar masa cewa duk wanda ya gode wa Allah to shi ne mai amfana da wannan godiyar, domin Allah ba shi da buƙatar komai daga godiyarsa. Duk kuma wanda ya butulce wa ni’imar da Allah ya yi masa, to ya san da cewa kansa zai cutar ba Allah ba, domin shi Allah mawadaci ne ba ya buƙatar komai a wurin kowa kuma sha-yabo ne a kowane hali.
وَإِذۡ قَالَ لُقۡمَٰنُ لِٱبۡنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَٰبُنَيَّ لَا تُشۡرِكۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ
Open ayah 31:13Kuma (ka tuna) lokacin da Luƙumanu ya ce da ɗansa a yayin da yake yi masa wa’azi: “Ya kai ɗanɗana, kada ka yi shirka da Allah; lalle ita shirka zalunci ne mai girma.
وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ وَهۡنًا عَلَىٰ وَهۡنٖ وَفِصَٰلُهُۥ فِي عَامَيۡنِ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيۡكَ إِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 31:14Kuma Mun yi wa mutum wasiyya game da iyayensa, mahaifiyarsa ta ɗauke shi a cikinta rauni a kan rauni, yaye shi kuwa a cikin shekara biyu ne, saboda haka ka gode min da kuma iyayenka, makoma gare Ni take.
وَإِن جَٰهَدَاكَ عَلَىٰٓ أَن تُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَاۖ وَصَاحِبۡهُمَا فِي ٱلدُّنۡيَا مَعۡرُوفٗاۖ وَٱتَّبِعۡ سَبِيلَ مَنۡ أَنَابَ إِلَيَّۚ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 31:15Idan kuma suka matsa maka kan ka yi tarayya da Ni game da abin da ba ka da wani sani a kansa, to kada ka bi su; kuma ka yi zaman duniya da su ta kyakkyawar hanya; ka kuma bi hanyar wanda ya mayar da al’amarinsa gare Ni. Sannan kuma zuwa gare Ni ne kawai makomarku, sai in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
يَٰبُنَيَّ إِنَّهَآ إِن تَكُ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٖ فَتَكُن فِي صَخۡرَةٍ أَوۡ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ أَوۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَأۡتِ بِهَا ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٞ
Open ayah 31:16(Luƙumanu ya ci gaba da cewa): “Ya kai ɗanɗana, lalle ita (kyakkyawa ko mummuna) in ta kasance daidai da ƙwayar komayya, sannan kuma ta zamanto cikin ƙaton dutse ko kuma cikin sammai ko cikin ƙasa, to Allah zai zo da ita. Lalle Allah Mai tausasawa ne, Masanin (komai).
يَٰبُنَيَّ أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ وَأۡمُرۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَٱنۡهَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَآ أَصَابَكَۖ إِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ
Open ayah 31:17“Ya kai ɗanɗana, ka tsayar da salla kuma ka yi umarni da aikata alheri, ka kuma hana aikata mummunan aiki, kuma ka yi haƙuri bisa duk abin da ya same ka; lalle wannan yana daga manyan al’amura.
وَلَا تُصَعِّرۡ خَدَّكَ لِلنَّاسِ وَلَا تَمۡشِ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَحًاۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخۡتَالٖ فَخُورٖ
Open ayah 31:18“Kada kuma ka riƙa ɗauke wa mutane fuskarka, kuma kada ka yi tafiya a ban ƙasa kana mai taƙama. Lalle Allah ba Ya son duk wani mai taƙama, mai fariya.
وَٱقۡصِدۡ فِي مَشۡيِكَ وَٱغۡضُضۡ مِن صَوۡتِكَۚ إِنَّ أَنكَرَ ٱلۡأَصۡوَٰتِ لَصَوۡتُ ٱلۡحَمِيرِ
Open ayah 31:19“Kuma ka tsakaita tafiyarka, kuma ka yi ƙasa-ƙasa da muryarka. Lalle mafi munin muryoyi ita ce muryar jakai.” A cikin waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wani ɓangare na ilimi da hikima da ya ba wa Luƙumanu yayin da ya zaunar da ɗansa ya yi masa wasu wasiyyoyi guda goma masu matuƙar amfani a rayuwarsa ta duniya da ta lahira. <b>Wasiyya ta farko </b>, ya fara da gargaɗin sa game da haɗa Allah da wani wajen bauta, da cewa yin shirka da Allah zalunci ne mai girman gaske, domin ya ƙunshi ɗaukar haƙƙin Allah mahalicci a ba wa wani mahaluƙi. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lokacin da faɗar Allah ta sauka mai cewa: ‘Waɗanda suka yi imani kuma ba su gauraya imaninsu da zalunci ba, waɗannan su suke da aminci kuma su ne shiryayyu.’ [Al-An’am , aya ta 82] sai wannan ya sa sahabban Manzon Allah (ﷺ) suka damu suka ce: “Wane ne a cikinmu bai zalunci kansa ba?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abin ba kamar yadda kuke zato ba ne; al’amarin ai kamar yadda Luƙumanu ne yake faɗa wa ɗansa cewa: ‘Ya kai ɗana, kada ka yi shirka da Allah, lalle shirka zalunci ne mai girma.’” [Bukhari #6933 da Muslim #124]. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasiyyar farko ta Luƙumanu ga ɗansa sai ya biyo bayanta da bayanin haƙƙin iyaye, domin wannan salo ne na Alƙur’ani ambaton haƙƙin iyaye bayan batun haƙƙin Allah (Mai tsarki da daukaka) a wurare da dama. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya yi wa ɗan’adam wasiyya da ya kyautata wa iyayensa ya yi musu biyayya a duk abin da bai saɓa wa Allah ba. Ya tunatar da shi wahalhalun da mahaifiyarsa ta sha tun daga lokacin da ta sami cikinsa take shiga wahala, wahalar kuma tana ta ƙaruwa; wahala bayan wahala har lokacin haihuwarsa ya zo ta haife shi cikin wahala. Sannan kuma ta shiga cikin wahalar shayar da shi da kula da shi har lokacin yayensa ya yi ta yaye shi cikin shekara biyu. To sai Allah ya umarci mutum da ya gode masa a kan ni’imar da ya yi masa mai tarin yawa sannan kuma ya gode wa iyayensa a kan wahalhalun da suka sha wajen renonsa da tarbiyyarsa har ya zama cikakken mutum mai dogaro da kansa. Ya tunatar da shi cewa zuwa gare shi ne makomarsu gaba ɗaya take, a can ne Allah zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa ɗan’adam kashedi game da yi wa iyayensa biyayya a kan abin da ya saɓa wa shari’a, da cewa kada ya kuskura ya yi wa iyayensa biyayya lokacin da za su yi ta ƙoƙarin tilasa shi da ya yi wa Allah shirka ya bi addininsu wanda ba Musulunci ba saboda kasancewarsu su ba Musulmi ne ba, domin babu biyayya ga wani mahaluƙi wajen saɓa wa mahalicci. To amma kuma duk da haka kada ya bijire wa yi musu biyayya a cikin sauran al’amura na duniya waɗanda ba su saɓa wa addininsa ba; ya ci gaba da kyautata musu da yi musu kyakkyawar mu’amala. Allah ya nuna masa cewa ya bi tafarkin wanda ya mayar da al’amarinsa gare shi ta hanyar kaɗaita shi da bauta da yin ɗa’a gare shi, sannan ya tabbatar masa da cewa makomarsu gaba ɗaya zuwa gare shi take a ranar alƙiyama sannan zai ba su labarin duk abin da suka aikata a nan duniya, ya kuma yi musu sakayya a kai. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wasu ayoyi na Alƙur’ani sun sauka game da ni.” Ya ce: “Mahaifiyar Sa’ad ta rantse ba za ta yi masa magana ba har abada har sai ya kafirce wa addininsa, kuma ba za ta ci ko ta sha komai ba har sai ya bi ta a kan haka. Ta ce masa: ‘Ka riya cewa Allah ya yi maka wasiyya a kan ka bi mahaifanka, ni kuma mahaifiyarka ce kuma ni ce nake ba ka wannan umarnin.’ Ya ce: “Ta zauna a cikin wannan yanayi tsawon kwana uku, saboda wahala har ta riƙa suma. Sai wani ɗanta mai suna Umara ya je ya ba ta ruwa ta sha, sai ta shiga yi wa ɗanta Sa’ad mummunar addu’a, sai Allah ya saukar da waɗannan ayoyin.” [Muslim #1748]. <b>Wasiyya ta biyu </b>, Luƙumanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sake jan hankalin ɗansa, ya sanar da shi cewa, mummunan aiki ko kyakkyawa komai ƙanƙantarsu, ko da kuwa kamar ƙwayar komayya ce a cikin wani babban dutse ko a can wani wuri cikin sammai ko a cikin ƙasa da babu wanda ya san da shi, to ranar alƙiyama Allah zai zo da shi domin ya yi sakayya ga bawa a kansa, lalle Allah mai zuzzurfan sani ne na komai, cikakken masani ne na yadda haƙiƙanin abubuwa suke da inda suke. Wannan wasiyya tana nufin jan hankalin ɗansa a kan ya riƙa tuna cewa Allah yana ganin duk wani motsinsa, don haka ya riƙa kawo shi a ransa a kowane lokaci domin ya kyautata aikinsa iya ƙoƙarinsa. <b>Wasiyya ta uku </b>, Luƙumanu ya sake jawo hankalin ɗansa ya umarce shi da ya tsayar da salla yadda ya kamata, watau ya kula da hukunce-hukuncenta na wajibai da mustahabbai, domin salla ita ce mafi girman ibada da gaɓoɓi suke yi. <b>Wasiyya ta huɗu </b>, ya umarce shi da ya yi umarni da kyakkyawan aiki, wannan kuwa yana buƙatar shi kansa ya san abin da zai yi umarni da shi, ya kuma yi ƙoƙarin aikata shi kafin ya umarci wani da haka. <b>Wasiyya ta biyar </b>, ya umarce shi da ya yi hani ga mummunan aiki, wanda shi ma yana buƙatar ya san mene ne mummuna domin ya guje shi shi kansa. <b>Wasiyya ta shida </b>, ya umarce shi da ya yi haƙuri a kan duk abin da zai same shi lokacin da yake umarni da kyakkyawa ko ya hana mummuna, domin wanda duk ya ɗauki wannan aiki to lalle zai gamu da ƙalubale iri-iri; dole sai ya yi haƙuri sannan ne zai ga amfanin abin da yake yi. Haƙuri a nan ya ƙunshi ya yi haƙuri wajen ɗa’a ga Allah da guje wa saɓon Allah, ya kuma yi haƙuri a kan ƙaddarar Allah marar kyau idan ta same shi. <b>Wasiyya ta bakwai </b>, Luƙumanu ya gargaɗi ɗansa a kan ya guji ɗauke wa mutane fuska domin nuna musu girman kai, watau ya zama mai sakin fuska da haba-haba da jama’a, domin ya samu shiga zukatansu, wa’azinsa a gare su ya yi musu tasiri. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce da ni: “Kada ka raina aikin alheri ko yaya yake, ko da kuwa ka haɗu da ɗan’uwanka ne da sakakkiyar fuska.” [Muslim #2626]. <b>Wasiyya ta takwas </b>, ya ja kunnensa a kan yin tafiya a bayan ƙasa cikin taƙama da ji-ji-da-kai, ya nuna masa cewa lalle Allah ba ya son mai tafiya yana taƙama da ji-ji-da-kai, yana mai alfahari da ni’imar da Allah ya yi masa, yana yi wa mutane girman kai kuma ba ya gode wa Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Wani mutum yana cikin tafiya ya caɓa ado, yana ji-ji da kansa ya taje sumarsa, sai kawai Allah ya nufi ƙasa ta haɗiye shi, yana nan yana ta gangarawa a cikinta har tashin alƙiyama.’” [Bukhari #5789 da Muslim #2088]. <b>Wasiyya ta tara </b>, Luƙumanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarci ɗansa da ya tsakaita tafiyarsa, kada ya riƙa yin ta da sauri sosai, kada kuma ya riƙa tafiya laƙaƙai-laƙaƙai, ya dai yi tafiya cikin nutsuwa baina-baina. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Mutum uku Allah ba ya son su: Mutum mai fariya mai taƙama, domin kuna karantawa a cikin littafin Allah yana cewa: ‘Lalle Allah ba ya son duk wani mai taƙama mai fariya; da marowaci mai yawan gori; da ɗan kasuwa mai yawan rantsuwa....’’” [Ahmad #21530]. <b>Wasiyya ta goma </b>, Luƙumanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarci ɗansa da ya yi ƙasa-ƙasa da muryarsa, kada ya riƙa ɗaga muryarsa ta yadda zai cutar da wani, ya ba shi misali da cewa lalle mafi munin sauti shi ne sautin jaki domin sautinsa ya fi na kowace dabba ƙara mai muni. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Idan kun ji carar zakara to ku roƙi Allah daga falalarsa domin ya ga mala’iku ne, idan kuma kuka ji kukan jaki to ku nemi tsarin Allah daga Shaiɗan domin ya ga Shaiɗan ne.” [Bukhari #3303 da Muslim #2729].
أَلَمۡ تَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَسۡبَغَ عَلَيۡكُمۡ نِعَمَهُۥ ظَٰهِرَةٗ وَبَاطِنَةٗۗ وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ
Open ayah 31:20Yanzu ba kwa gani cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin ƙasa, Ya kuma cika muku ni’imominsa na sarari da na ɓoye? Daga mutane kuma akwai waɗanda suke jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ko wata shiriya ba, ba kuma tare da wani littafi mai haskakawa ba.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَلۡ نَتَّبِعُ مَا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ يَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ
Open ayah 31:21Idan kuma aka ce da su: “Ku bi abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “A’a, mu muna bin abin da muka sami iyayenmu ne a kansa.” Yanzu (sa yi haka) ko da Shaiɗan ya zamanto yana kiran su zuwa ga azaba ta (wuta) mai ruruwa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake janyo hankalin kafirai zuwa ga duba cikin ayoyin Allah na sama da na ƙasa, masu nuna Kaɗaitarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai ba tare da yi masa shirka ba. Allah ya ja hankalin mutane cewa yanzu ba za su duba su ga yadda ya hore musu amfani da duk wani abu da ke cikin sammai na rana da wata da taurari; da abin da yake bayan ƙasa na dabbobi da bishiyoyi da tsirrai da shuke-shuke da ƙoramu da ma’adanai. Ya kuma ba su ni’imominsa cikakku na sarari da suke gani da idanunsu, kamar kyawawan sura ta halitta da ya yi musu, da ni’imominsa na ɓoye kamar hankali da ilimi da ya ba su? To amma abin takaici duk da ganin waɗannan ni’imomi na Allah, sai a sami wani daga cikin mutane yana jayayya da musunta Kaɗaitakar Allah ba tare da wani ilimi na wahayi daga Allah ba, ba kuma tare da wata shiriya ta hankali ko wani saukakken littafi daga Allah ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda masu irin wannan mummunar aƙida suka yi nisa domin kuwa ba hujja suke son ji ba; duk sanda aka ce musu su taho su bi wahayin da Allah ya yi wa Manzonsa (ﷺ), sai su buɗe baki suna mamaki, su ce ba za su bi ba, su kawai za su bi abin da suka tashi suka sami iyayensu da kakanninsu a kai na bautar gumaka. Sai Allah ya tambaye su cewa, shin za su bi iyayen nasu ne ko da kuwa shaiɗan ya kasance yana kiran su ne zuwa faɗawa cikin azabar wutar Jahannama ranar alƙiyama ta hanyar ɓatar da su da ya riƙa yi da bautar gumaka? Kuma su iyayen nasu suka amsa masa gayyatarsa suka zama mabiyansa masu rayuwa cikin ɗimuwa. To yanzu waɗannan ne za su fifita bin su a kan su bi wahayin da aka yi wa Manzo (ﷺ)?
۞وَمَن يُسۡلِمۡ وَجۡهَهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰۗ وَإِلَى ٱللَّهِ عَٰقِبَةُ ٱلۡأُمُورِ
Open ayah 31:22Wanda kuma ya miƙa kansa ga Allah, yana kuma mai kyautatawa, to haƙiƙa ya yi riƙo da igiya ƙwaƙƙwara. Kuma ƙarshen al’amura zuwa ga Allah ne.
وَمَن كَفَرَ فَلَا يَحۡزُنكَ كُفۡرُهُۥٓۚ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ فَنُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Open ayah 31:23Duk kuwa wanda ya kafirta, to kada kafircinsa ya ɓata maka rai. Zuwa gare Mu ne kawai makomarsu take, sai Mu ba su labarin abin da suka aikata. Lalle Allah Masanin abin da yake cikin ƙiraza ne.
نُمَتِّعُهُمۡ قَلِيلٗا ثُمَّ نَضۡطَرُّهُمۡ إِلَىٰ عَذَابٍ غَلِيظٖ
Open ayah 31:24Za Mu jiyar da su daɗi ɗan kaɗan sannan Mu tilasta su zuwa ga azaba mai kauri. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin mutumin da ya miƙa wuyansa ga Allah ya kaɗaita shi da bauta ya kuma kyautata aikinsa, Allah ya tabbatar masa da cewa ya yi riƙo da ƙwaƙƙwarar igiya wadda idan bawa ya riƙe ta to ya kuɓuta, domin ba zai ji tsoron ta tsinke masa ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ƙarshen al’amura zuwa gare shi za su koma, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan aikinsa mai kyau da mummuna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) game da cutarwar da yake ta gamuwa da ita daga mushirikai da tsananin taurin kansu, da cewa duk wanda ya kafirta daga cikinsu to kada kafircinsa ya ɗaga wa Manzon Allah (ﷺ) hankali har ya sa shi cikin damuwa, domin ga Allah ne kawai makomarsu take ranar alƙiyama ya kuma ba su labarin duk munanan ayyukan da suka yi a duniya, ya kuma yi musu sakayya a kansu, ba abin da suka isa su ɓoye masa, domin lalle shi masanin duk abin da yake cikin zukata ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa jin daɗin da ya ba wa kafirai a nan duniya ba wani abin a zo a gani ba ne; ɗan ƙanƙani ne iya rayuwarsu ta duniya; ranar alƙiyama zai tilasta musu shiga cikin azaba matsananciya ta wutar Jahannama.
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 31:25Tabbas kuma in ka tambaye su: “Wane ne ya halicci sammai da ƙasa?” Tabbas za su ce: “Allah ne.” To ka ce: “Alhamdu lillahi .” A’a, yawancinsu dai ba sa sanin (haka).
لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ
Open ayah 31:26Abin da yake cikin sammai da ƙasa na Allah ne. Lalle Allah Shi ne Mawadaci, Sha-yabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai masu bautar gumaka ba Allah ba sun yarda da cewa Allah ne ya halicci sammai da ƙasa, domin idan da Manzon Allah (ﷺ) zai tambaye su game da haka, Allah ya tabbatar masa cewa tabbas za su amsa masa da cewa Allah ne mahaliccinsu. Sai Allah ya umarci Manzonsa ya faɗa musu cewa yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya bayyana hujja a kansu, to amma yawancinsu ba su san wane ne ya cancanci yabo da godiya ba saboda tsantsar jahilcinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk abin da yake cikin sammai da wanda yake a ƙasa nasa ne, domin halittarsa ne mallakarsa ne kuma bayinsa ne, kuma lalle shi mawadaci ne ba ya da buƙatar komai a wajen bayinsa, kuma shi ne sha-yabo a duniya da lahira.
وَلَوۡ أَنَّمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن شَجَرَةٍ أَقۡلَٰمٞ وَٱلۡبَحۡرُ يَمُدُّهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦ سَبۡعَةُ أَبۡحُرٖ مَّا نَفِدَتۡ كَلِمَٰتُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Open ayah 31:27Idan kuwa da a ce, duk bishiyar da take bayan ƙasa alƙaluma ne, kogi kuma (ya zama tawadarsu), bayansa kuma akwai wasu kogunan guda bakwai ƙari a kansa to kalmomin na Allah ba za su ƙare ba. Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.
مَّا خَلۡقُكُمۡ وَلَا بَعۡثُكُمۡ إِلَّا كَنَفۡسٖ وَٰحِدَةٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٌ
Open ayah 31:28Halittarku da tayar da ku bai wuce tamkar na rai ɗaya ba. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yalwa da faɗin iliminsa marar iyaka. Ya buga misali don kusanto da ma’anar zuwa ga ƙwaƙwalen masu sauraro, da cewa, da a ce duk bishiyoyin da suke bayan ƙasa za a yi guntu-guntu da su, a fere su su zama alƙaluman rubutu, sannan duk wani kogi a duniya a mayar da shi tawwada ta rubutu, sannan a ƙara da wasu kogunan bakwai waɗanda su ma za su zama ƙarin tawwadar rubutu, sannan duk a haɗa su a yi ta rubuta kalmomin Allah da su, to da ba su iya ƙare kalmominsa ba, domin ba su da iyaka ko maƙura, sai dai waɗannan alƙaluma da wannan tawwada su ƙare ƙarƙaf. Allah ya tabbatar da cewa lalle shi mabuwayi ne babu mai iya rinjayar sa, mai hikima ne cikin duk maganganunsa da ayyukansa. Sai kuma ya bayyana musu ƙarfin Ƙudurarsa bayan yalwar iliminsa, da cewa halittar mutane gaba ɗayansu da sake tashinsu domin yi musu hisabi a ranar alƙiyama bai wuce gwargwadon halittar rai ɗaya ba a wajen Allah, saboda tsananin sauƙin abin a wurinsa. Lalle Allah mai ji ne mai gani ne, sauraron wani sauti ba zai hana shi sauraron wani ba, hakanan ganin wani abu ba zai hana shi ganin wani ba, don haka halittar wani rai ba zai shagaltar da shi daga halittar wani ran ba ko tashinsa.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِيٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى وَأَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ
Open ayah 31:29Yanzu ba ka gani cewa Allah Yana shigar da dare cikin rana, Yana kuma shigar da rana cikin dare, Ya kuma hore (muku) rana da wata, kowannensu yana tafiya zuwa ga lokaci iyakantacce, kuma lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne?
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ
Open ayah 31:30Wannan kuwa (suna samuwa ne) saboda Allah Shi ne Gaskiya, lalle kuma abin da suke bauta wa ba Shi ba ƙarya ne, lalle kuma Shi Allah Maɗaukaki ne, Mai girma.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱلۡفُلۡكَ تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِنِعۡمَتِ ٱللَّهِ لِيُرِيَكُم مِّنۡ ءَايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ
Open ayah 31:31Ba ka gani cewa jiragen ruwa suna tafiya a cikin kogi da ni’imar Allah, don Ya nuna muku (wasu) daga ayoyinsa? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga duk mai yawan haƙuri, mai yawan godiya.
وَإِذَا غَشِيَهُم مَّوۡجٞ كَٱلظُّلَلِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ فَمِنۡهُم مُّقۡتَصِدٞۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا كُلُّ خَتَّارٖ كَفُورٖ
Open ayah 31:32Idan kuwa wata igiyar ruwa kamar duwatsu ta kere su, sai su roƙi Allah suna tsantsanta addini a gare Shi, to kuma idan Ya tserar da su zuwa gaci, to akan sami tsaka-tsaki daga cikinsu. Kuma babu mai yin jayayya da ayoyinmu sai duk wani mayaudari, mai butulci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana isarsa da Kaɗaitakarsa wajen sarrafa halittunsa na sama da na ƙasa. Allah ya nuna wa ɗan’adam yadda yake shigar da dare cikin yini don tsawonsa ya ragu shi kuma yini ya ƙara tsawo, wani lokaci kuma ya shigar da yini cikin dare, domin tsawonsa ya ragu shi kuma dare ya ƙaru. Haka kuma yadda ya hore tafiyar rana da wata kowannensu yana tafiya a kan hanyarsa har zuwa wani ƙayyadadden lokaci da ya tsara. Allah kuma masanin abin da bayinsa suke aikatawa ne, babu abin da yake ɓuya gare shi na ayyukansu kuma zai yi musu sakayya a kai. Sai kuma ya bayyana cewa wannan gudanar da iko nasa da yadda yake sarrafa halittunsa shi yake tabbatar da cewa, shi ne Allah Ɗaya kuma shi ne tabbas, gaskiya a Zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, kuma ko shakka babu abin da mushirikai suke bauta wa ba shi ba, ƙarya ne marar tushe. Don haka Allah shi ne maɗaukaki da Zatinsa da galabarsa da matsayinsa a kan dukkan halittunsa; babu wani abu sama da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake jawo hankalin mutane don su lura da ayoyin da suke nuna kamalar ikonsa da rahamarsa ga bayinsa, ya nuna wa ɗan’adam yadda jiragen ruwa suke gudu a kan teku cikin luɗufinsa da horewarsa, domin ya nuna wa mutane manya-manyan ayoyinsa masu nuna girman Ƙudurarsa da rahamarsa. Sai kuma ya bayyana cewa lalle a game da waɗannan abubuwa akwai ayoyi ga duk mai yawan haƙuri a kan abin da zai same shi marar daɗi, mai yawan godiya a kan abin da zai same shi na ni’imomin Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan hali na mutane waɗanda ba sa tunawa da Allah sai sun shiga cikin wata musifa da cewa, idan suka shiga jirgin ruwa igiyar ruwa ta taso ta kewaye su kamar manya-manyan duwatsu, suka tabbatar za su hallaka, sai nan take su shiga kiran Allah tare da tsantsanta addu’a gare shi ba tare da sun tuna allolinsu ba, to amma da zarar ya amsa musu addu’o’insu ya tserar da su zuwa tudu sun kuɓuta daga hallakar nutsewa a ruwa, to sai ka samu wani daga cikinsu yana tsaka-tsaki, bai tsaya ya yi wa Allah cikakkiyar godiya da ta wajaba ya yi ba, sai kuma a samu wani daga cikinsu ya shiga jayayya da ni’imar da Allah ya yi masa, amma kuma babu mai jayayya da ayoyin Allah sai wanda yake mayaudari, wanda ya yi wa Allah alƙawarin cewa idan ya kuɓutar da shi zai gode masa, amma kuma sai ya butulce wa ni’imomin da Allah ya yi masa.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡ وَٱخۡشَوۡاْ يَوۡمٗا لَّا يَجۡزِي وَالِدٌ عَن وَلَدِهِۦ وَلَا مَوۡلُودٌ هُوَ جَازٍ عَن وَالِدِهِۦ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ
Open ayah 31:33Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku, kuma ku ji tsoron ranar da mahaifi ba zai amfana wa ɗansa komai ba, kuma ɗan shi ma ba zai amfana wa mahaifinsa komai ba. Lalle alƙawarin Allah gaskiya ne; to kada rayuwar duniya ta ruɗe ku, kuma (Shaiɗan) mai ruɗarwa ya ruɗe ku game da Allah.
إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلسَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ ٱلۡغَيۡثَ وَيَعۡلَمُ مَا فِي ٱلۡأَرۡحَامِۖ وَمَا تَدۡرِي نَفۡسٞ مَّاذَا تَكۡسِبُ غَدٗاۖ وَمَا تَدۡرِي نَفۡسُۢ بِأَيِّ أَرۡضٖ تَمُوتُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرُۢ
Open ayah 31:34Lalle Allah a wurinsa ne (kaɗai) sanin lokacin tashin alƙiyama yake, kuma (Shi) Yake saukar da ruwa, (Shi) kuma Yake sane da abin da yake cikin mahaifu; ba kuwa wani rai da yake sane da abin da zai aikata gobe, ba kuma wani rai da yake sane da ƙasar da zai mutu. Lalle Allah Shi ne Masani, Mai cikakken ilimi. A ayoyi biyu na ƙarshen Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo mutane ya umarce su da yin taƙawa gare shi, ta hanyar kiyaye dokokinsa da bin umarninsa da guje wa haninsa, ya kuma umarce su da su ji tsoron wata rana wadda uba ba zai amfana wa ɗansa komai ba, shi ma kuma ɗan ba zai amfana wa mahaifinsa komai ba; babu ɗaya daga cikinsu da zai ƙara wa ɗaya ladansa ko ya rage masa zunubbansa, kowa daga shi sai aikinsa. Allah ya tabbatar musu da cewa zuwan wannan rana alƙawari ne da Allah ya riga ya yi, kuma shi alƙawarinsa tabbas ne, don haka su shiga taitayinsu kada rayuwar duniya da sha’awace-sha’awacenta su ruɗe su, kada kuma su bari Shaiɗan ya yaudare su, ya nuna musu cewa ai Allah mai haƙuri ne mai gafara, alhali sun bijire wa dokokinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mabuɗan gaibinsa guda biyar waɗanda bai damƙa saninsu a hannun wani mahaluƙi ba, kamar haka: <b>Na farko </b>, sanin lokacin tashin alƙiyama. Wannan ilimi Allah ne kaɗai ya bar wa kansa saninsa; bai sanar da wani mala’ika makusanci ba, ko wani annabi manzo. <b>Na biyu </b>, shi ne mai saukar da ruwan sama sanda ya ga dama a inda ya ga dama, babu wanda ya san haka sai shi. <b>Na uku </b>, shi kaɗai ne ya san abin da yake cikin mahaifu na duk wata halitta mace, mutum ko dabba ko ƙwaro, shi ne ya san komai da ya danganci abin da ke ƙunshe cikin mahaifa, ya san mace ce ko namiji, nagari ne ko ba nagari ba, mai wadata ne ko faƙiri ne, ɗan wuta ne ko ɗan Aljanna. Ya san komai na halittarsa tun daga lokacin shigarta mahaifa har zuwa makomarta ta ƙarshe. Babu wanda ya san wannan sai Allah shi kaɗai. <b>Na huɗu </b>, babu wanda ya san me zai aikata gobe na alheri ko na sharri, na addininsa ko na duniyarsa. Allah ne kaɗai ya san haka. <b>Na biyar </b>, babu wani rai da ya san a wace ƙasa zai mutu; a tudu ne ko a kwari ko a kan dutse ko cikin ruwa; Allah ne kaɗai ya keɓanta da sanin duk waɗannan al’amura. Lalle Allah masanin komai ne cikinsa da wajensa babu abin da yake ɓuya gare shi. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Mabuɗan gaibu biyar ne babu wanda ya san su sai Allah, babu wanda ya san abin da mahaifa take ragewa (na lokaci) sai Allah; babu wanda ya san me zai faru gobe sai Allah; babu wani rai da ya san inda zai mutu sai Allah; kuma babu wanda ya san lokacin tashin alƙiyama sai Allah.’” An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Duk wanda ya riya cewa Annabi (ﷺ) yana ba da labarin abin da zai faru gobe, to lalle ya yi wa Allah ƙarya babba, Allah yana cewa: ‘Ka ce: Waɗanda suke sammai da waɗanda suke ƙasa babu wanda ya san gaibu sai Allah.’” [Muslim #177].