السجدة
As-Sajda
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
الٓمٓ
Open ayah 32:1ALIF LAM MIM.
تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 32:2Saukar da Littafin da babu kokwanto a cikinsa daga Ubangijin talikai ne.
أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۚ بَلۡ هُوَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أَتَىٰهُم مِّن نَّذِيرٖ مِّن قَبۡلِكَ لَعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ
Open ayah 32:3Ko kuwa suna cewa (Annabi Muhammadu) ƙirƙirar sa ya yi?” Ba haka ne ba, shi dai (Alƙur’ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake, don ka gargaɗi mutanen da wani mai gargaɗi bai zo musu gabaninka ba, don su shiriya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori gabaninta da haruffa makamantansu. [Duba farkon tafsirinmu na Suratul Baƙara don ƙarin bayani]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan Alƙur’ani da Manzonsa Muhammadu (ﷺ) ya zo da shi saukakke ne daga gare shi, kuma babu wani kokwanto a kansa. Ya kuma bayyana cewa kafirai waɗanda suka ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) suna da’awar cewa wai Annabi (ﷺ) shi ne ya ƙirƙiri Alƙur’ani ya danganta shi ga Allah, wanda ba haka al’amarin yake ba. Shi Alƙur’ani gaskiya ne da babu kokwanto a kansa, saukakke ne daga Allah wanda shi ne Ubangijin Manzon Allah, kuma ya saukar masa da shi ne domin ya gargaɗi wasu mutane, watau Larabawa da babu wani manzo gabaninsa da ya zo ya gargaɗe su da azabar Allah (Mai tsarki da daukaka), domin su shiriya su kama gaskiya su yi aiki da ita.
ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ مَا لَكُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِيّٖ وَلَا شَفِيعٍۚ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 32:4Allah ne Wanda Ya halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida sannan Ya daidaita bisa Al’arshi; ba ku da wani majiɓincin al’amari ko mai ceto bayansa. Yanzu me ya sa ba kwa wa’azantuwa?
يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ يَعۡرُجُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥٓ أَلۡفَ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ
Open ayah 32:5Yana shirya al’amari daga sama zuwa ƙasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke ƙirgawa.
ذَٰلِكَ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 32:6Wannan (Shi ne) Masanin ɓoye da sarari, Mabuwayi, Mai rahama.
ٱلَّذِيٓ أَحۡسَنَ كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥۖ وَبَدَأَ خَلۡقَ ٱلۡإِنسَٰنِ مِن طِينٖ
Open ayah 32:7Wanda Ya kyautata kowane abu da ya halicce shi; kuma Ya fari halittar mutum daga taɓo.
ثُمَّ جَعَلَ نَسۡلَهُۥ مِن سُلَٰلَةٖ مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ
Open ayah 32:8Sannan Ya sanya zuriyarsa daga tataccen ruwa wulaƙantacce.
ثُمَّ سَوَّىٰهُ وَنَفَخَ فِيهِ مِن رُّوحِهِۦۖ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ
Open ayah 32:9Sannan Ya daidaita shi, Ya kuma busa masa daga ruhinsa; kuma Ya sanya muku ji da gani da zukata. Kaɗan ne ƙwarai kuke godewa. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da ingancin manzancin Annabi Muhammadu (ﷺ), sai kuma ya bayyana dalilai masu tabbatar da Kaɗaitakar Allah (Mai tsarki da daukaka) da cancantar a bauta masa shi kaɗai, da cewa shi ne wanda ya halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida, waɗanda suka fara daga Lahadi zuwa Juma’a, duk kuwa da kasancewar shi mai iko ne ya halicce su cikin lokacin da ke ƙasa da ƙiftawar ido. Sannan ya daidaita a kan Al’arshi daidaito wanda ya dace da shi. Ya tabbatar wa da mutane cewa ba su da wani wanda zai jiɓinci al’amuransu in ba shi ba, ko kuma wanda zai iya ceton su a wajen Ubangijinsu, ya kuɓutar da su daga azabarsa idan ya yi niyyar azabtar da su. Sai kuma ya ja hankalinsu da cewa me ya sa ba za su yi tunani ba su fahimci cewa wanda ya halicci sammai da ƙasa da abin da ke tsakaninsu ya kuma daidaita a kan Al’arshinsa shi ne kaɗai ya cancanci su bauta wa ba wani ba? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa shi ne yake tsara al’amuran dukkan halittu na cikin sammai da ƙasa, sannan wannan al’amarin ya hau zuwa gare shi a cikin wani yini da gwargwadon tsawonsa yake shekara dubu ne daga irin lissafin mutane na duniya. Ya tabbatar musu cewa mai tsara waɗannan al’amura duka shi ne wanda ya san abin da yake ɓoye da na sarari, shi ne kuma Mabuwayi da babu mai iya ja da shi wanda yake azabtar da maƙiyansa, shi ne kuma mai rahama wanda yake jin ƙan bayinsa muminai. Shi ne kuma wanda ya kyautata duk wani abu da ya halitta, ya yi masa halittar da ta dace da shi, ta kuma dace da hikimar halittarsa. Sai kuma ya bayyana cewa ya fara halittar mutum na farko daga taɓo ba tare da ya kwaikwaya a wurin wani ba. mutum na farko shi ne Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya sanya halittar zurriyar Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a bayansa daga ruwa wulaƙantacce, watau maniyyi wanda yake fita daga jikin shi ɗan’adam, sannan ya cika halittarsa ya yi shi daidaitaccen mutum, ya busa masa ruhinsa, ta hanyar aiko masa mala’ika wanda ya wakilta masa busa rayuka, tun daga lokacin da ɗan’adam ya zama mutum mai rai a jikinsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutane wasu ni’imomin da ya yi musu a halittarsu yayin da ya sanya musu ji da gani ya kuma ba su zukata waɗanda za su yi tunani da su. Duk waɗannan ni’imomi manya-manya da ya yi wa mutane domin su gode masa ne ta hanyar bauta masa shi kaɗai ba tare da sun yi masa shirka ba, to amma sai ya zamanto kaɗan ne ƙwarai suke gode masa a kan waɗannan ni’imomi.
وَقَالُوٓاْ أَءِذَا ضَلَلۡنَا فِي ٱلۡأَرۡضِ أَءِنَّا لَفِي خَلۡقٖ جَدِيدِۭۚ بَلۡ هُم بِلِقَآءِ رَبِّهِمۡ كَٰفِرُونَ
Open ayah 32:10Suka kuma ce: “Yanzu idan muka zagwanye a cikin ƙasa, ashe za a sake sabunta halittarmu?” A’a, su dai suna kafircewa ne da saduwa da Ubangijinsu.
۞قُلۡ يَتَوَفَّىٰكُم مَّلَكُ ٱلۡمَوۡتِ ٱلَّذِي وُكِّلَ بِكُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 32:11Ka ce (da su): “Mala’ikan mutuwa ne wanda aka wakilta muku zai karɓi ranku sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kafirci da wautar mushirikai masu ƙaryata tashi bayan mutuwa, domin su a ganinsu ta yaya bayan sun mutu an binne su a cikin ƙasa sun ɓace a cikinta, sun zama turɓaya sannan kuma a ce za a sake tayar da su a yi musu sabuwar halitta? Suna ganin wannan wata magana ce da hankalinsu ba zai iya ɗaukan ta ba. Sai Allah ya nuna musu cewa suna faɗar wannan batu ne kawai domin da ma can sun kafirce wa haɗuwa da Ubangijinsu, ba su yi imani da tashi bayan mutuwa ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya mayar musu da martani cewa mala’ikan mutuwa wanda aka wakilta shi ya karɓi rayukansu shi ne zai karɓi rayukansu idan ajalinsu ya yi, sannan zuwa ga Allah ne kaɗai za a mayar da su ranar alƙiyama domin ya yi musu hisabi ya saka wa kowa a kan aikinsa.
وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلۡمُجۡرِمُونَ نَاكِسُواْ رُءُوسِهِمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ رَبَّنَآ أَبۡصَرۡنَا وَسَمِعۡنَا فَٱرۡجِعۡنَا نَعۡمَلۡ صَٰلِحًا إِنَّا مُوقِنُونَ
Open ayah 32:12Da kuwa za ka ga lokacin da masu manyan laifuka suke sunkuye da kawunansu a wurin Ubangiijnsu (suna cewa): “Ya Ubangijinmu, mun gani, mun kuma ji, to Ka mayar da mu (duniya), za mu yi aiki nagari, haƙiƙa mu masu sakankancewa ne.”
وَلَوۡ شِئۡنَا لَأٓتَيۡنَا كُلَّ نَفۡسٍ هُدَىٰهَا وَلَٰكِنۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ مِنِّي لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 32:13Idan kuwa da Mun ga dama, tabbas da Mun bai wa kowane rai shiriyarsa, sai dai kuma maganata ta tabbata cewa, tabbas zan cike Jahannama da aljannu da mutane gaba ɗaya.
فَذُوقُواْ بِمَا نَسِيتُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَآ إِنَّا نَسِينَٰكُمۡۖ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡخُلۡدِ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 32:14Sai (a ce da su): “Ku ɗanɗani (azaba) saboda mancewa da kuka yi da saduwa da wannan ranar taku, lalle Mu ma Mun yi watsi da ku; kuma ku ɗanɗani azaba mai ɗorewa saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa waɗannan kafiran masu ƙaryata ranar alƙiyama za su bayyana a wannan ranar a gaban Allah cikin halin ƙasƙanci, suna sunkuyar da kawunansu a wulaƙance suna nadama, suna tabbatar wa Ubangiji cewa yanzu kam sun yarda da akwai tashi bayan mutuwa, domin sun gane wa idanuwansu, sun kuma ji maganar gaskiya da aka yi ta faɗa musu ita tun a duniya suna ƙaryatawa. Sai su shiga roƙon Allah cewa ya mayar da su duniya domin su gyara abin da suka ɓata, su yi aiki na ƙwarai, domin su yanzu sun ga dahir; sun tabbatar da gaskiyar abin da manzanninsu suka riƙa gaya musu a duniya. Allah ya bayyana wa Manzonsa cewa da zai ga waɗannan masu manya-manyan laifuffuka a cikin irin wannan hali na ƙasƙanci da nadama to da ya ga babban al’amari mai ban al’ajabi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa komai yana gudana ne da hukuncinsa da ƙaddararsa da cewa, da ya ga dama da lalle kowane rai ya tanadar masa shiriyarsa ya ɗora shi a kan daidaitacciyar hanya, sai dai maganarsa ta riga ta tabbata cewa sai ya cika wutar Jahannama da kafirai na mutane da aljannu, domin sun zaɓi hanyar kafirci da ɓata a kan hanyar imani da nagarta. Wannan kuwa adalci ne na Allah da gudanar da komai a bisa hikima da dacewa. Sai kuma ya bayyana cewa za a riƙa faɗa wa su waɗannan ‘yan wuta cewa su ɗanɗani azaba saboda sun manta da haɗuwa da Allah a wannan rana, sun gafala game da ita, don haka Allah zai sanar da su cewa shi ma a wannan rana zai bar su cikin azaba ba tare da ya kula su ba; ya ce da su su ɗanɗani azabar wuta ta dindindin ba mai yankewa ba, saboda abin da suka kasance suna aikatawa a duniya na kafirci da saɓon Allah.
إِنَّمَا يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِهَا خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَسَبَّحُواْ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ۩
Open ayah 32:15Lalle kawai masu imani da ayoyinmu su ne waɗanda idan aka yi musu wa’azi da su za su faɗi suna masu sujjada su kuma yi tasbihi tare da yabon Ubangijinsu, kuma su ba sa yin girman kai.
تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمۡ عَنِ ٱلۡمَضَاجِعِ يَدۡعُونَ رَبَّهُمۡ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Open ayah 32:16Kuyaɓunsu suna nesantar wuraren kwanciya, suna bauta wa Ubangijinsu cikin halin tsoro da kuma kwaɗayi, kuma suna ciyarwa daga abin da Muka arzuta su.
فَلَا تَعۡلَمُ نَفۡسٞ مَّآ أُخۡفِيَ لَهُم مِّن قُرَّةِ أَعۡيُنٖ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 32:17Kuma ba wani rai da zai san abin da aka ɓoye musu na faranta rai, don sakamako game da abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka yi imani da shi da manzanninsa da cewa, masu yin imani da ayoyinsa da ya saukar wa Manzonsa su ne kawai waɗanda idan aka karanta musu waɗannan ayoyi aka yi musu wa’azi da su, sukan faɗi ƙasa suna masu sujjada, su kuma yi tasbihi da yabon Ubangijinsu, ba sa girman kai wajen bautar sa ko yi masa sujjada. Allah ya bayyana siffofinsu da cewa, suna ƙaurace wa wuraren kwanciya da jikinsu; su haƙura da bacci, su nufi wurin bautar Allah, su tsaya suna salla suna roƙon sa a sallolinsu, suna masu tsoron azabarsa kuma masu kwaɗayin rahamarsa. Suna kuma sadaukar da dukiyoyin da Ubangijinsu ya ba su wajen ɗaukaka addininsa ko taimakon bayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa babu wani rai da zai san abin da aka tanada musu na sakamako wanda zai faranta musu rai, saboda kyawawan ayyukan da suka aikata a duniya. Sakamako ne da babu wanda ya san iyakar girmansa sai Allah (Mai tsarki da daukaka). An karɓo daga Mu’azu ɗan Jabal (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na yi tafiya tare da Manzon Allah (ﷺ) sai wata rana na wayi gari kusa da shi muna tafiya sai na ce: “Ya Manzon Allah, ka faɗa mini aikin da zai shigar da ni Aljanna, ya nisanta ni daga wuta.” Sai ya ce: “Lalle ka yi tambaya game da wani babban abu, amma kuma mai sauƙi ne ga wanda Allah ya sawwaƙe masa: Ka bauta wa Allah kada ka haɗa komai da shi, ka kuma tsayar da salla, ka kuma bayar da zakka, ka yi azumin Ramadana, ka je hajjin Ɗakin Allah.” Sannan ya ce: “Yanzu ba na nuna maka ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka kuma tana bice zunubi, da sallar mutum a cikin tsakiyar dare.” Sai ya karanta aya ta 16 har zuwa ta 17…” [Ahmad #22016 da Tirmizi #2616 da Ibn Majah #3973]. An karɓo daga Sahlu ɗan Sa’ad As-Sa’idi ya ce: Na halarci wani majilisi na Manzon Allah (ﷺ) inda ya siffanta Aljanna har ya gama maganarsa. A ƙarshen zancensa sai ya ce: “A cikinta akwai abin da ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, bai kuma taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani mutum ba.” Sai ya karanta wannan ayar ta 16 zuwa ta 17. [Muslim #2825].
أَفَمَن كَانَ مُؤۡمِنٗا كَمَن كَانَ فَاسِقٗاۚ لَّا يَسۡتَوُۥنَ
Open ayah 32:18Yanzu wanda ya zamanto mumini ya zama kamar wanda ya kasance fasiƙi? Ai ba za su zama daidai ba.
أَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ جَنَّٰتُ ٱلۡمَأۡوَىٰ نُزُلَۢا بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 32:19Amma waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, to suna da gidajen Aljanna na makoma, (wannan) liyafa ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa.
وَأَمَّا ٱلَّذِينَ فَسَقُواْ فَمَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُۖ كُلَّمَآ أَرَادُوٓاْ أَن يَخۡرُجُواْ مِنۡهَآ أُعِيدُواْ فِيهَا وَقِيلَ لَهُمۡ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلنَّارِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 32:20Amma kuma waɗanda suka fice daga biyayyar Allah, to makomarsu wuta ce; ko da yaushe suka yi niyyar fitowa daga gare ta sai a mayar da su a cikinta a kuma ce da su: “Ku ɗanɗani azabar wuta wadda kuka kasance kuna ƙaryatawa.”
وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَدۡنَىٰ دُونَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَكۡبَرِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Open ayah 32:21Kuma tabbas lalle za Mu ɗanɗana musu (wani abu) daga azabar da ta fi ƙanƙanta (ta duniya) kafin azabar da ta fi girma (ta lahira) don su dawo (daga ɓata).
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ ثُمَّ أَعۡرَضَ عَنۡهَآۚ إِنَّا مِنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُنتَقِمُونَ
Open ayah 32:22Wane ne kuma mafi zalunci fiye da wanda aka yi wa wa’azi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya bijire musu? Lalle Mu Masu saka wa masu manyan laifuka ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babban bambanci da tazara da ke tsakanin mumini da fasiƙi mai bijire wa biyayyar Allah da cewa, babu yadda za a daidaita tsakanin wanda ya yi imani da Allah, ya yi kyawawan ayyuka ya bar abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana da mutumin da ya kauce wa hanyar Allah, ya zaɓi saɓon Allah. Sakamakonsu a wurin Allah ba zai taɓa zama irin ɗaya ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka yi imani da Allah suka yi ayyuka nagari da cewa an tanadar musu Aljanna da za su zauna cikinta cikin karramawa ta Allah gare su, sakamakon kyawawan ayyukan da suka kasance suna yi a duniya. Sannan kuma ya bayyana sakamakon waɗanda suka kauce wa ɗa’ar Allah suka zaɓi kafirci da saɓon Allah; to su wutar Jahannama ce matabbatarsu da aka tanadar musu a ranar alƙiyama. Duk kuwa lokacin da suka yunƙuro domin su fita daga cikinta sai a mayar da su cikinta, a daka musu tsawa cewa, su ɗanɗani azabar wutar da suka kasance suna ƙaryatawa a duniya lokacin da manzanninsu suke tsorata su da ita. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa waɗannan kafirai cewa, zai ɗanɗana musu azabar duniya ta hanyar jarraba iri-iri da fitintinu da zai saukar musu, kafin su kai ga mafi girman azaba ta lahira idan har suka mutu ba su tuba ba. Ya bayyana cewa yana ɗanɗana musu azabar duniya ne domin ko sa dawo ga ɗa’a ga Allah su tuba su bar abin da suke yi na kafirci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa babu mafi zalunci kamar wanda aka yi masa wa’azi da ayoyin Allah amma kuma sai ya bijire musu ya yi watsi da su. Sai Allah ya tabbatar da cewa, lalle sai ya yi sakamakon azaba ga masu bijire masa suna aikata kafirci da ayyukan saɓon Allah.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَلَا تَكُن فِي مِرۡيَةٖ مِّن لِّقَآئِهِۦۖ وَجَعَلۡنَٰهُ هُدٗى لِّبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 32:23Haƙiƙa kuma Mu Mun bai wa Musa Littafi, to kada ka kasance (kai Manzo) cikin kokwanto na saduwa da shi (Musan). Kuma Mun sanya shi ya zamanto shiriya ga Banu-Isra’ila.
وَجَعَلۡنَا مِنۡهُمۡ أَئِمَّةٗ يَهۡدُونَ بِأَمۡرِنَا لَمَّا صَبَرُواْۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يُوقِنُونَ
Open ayah 32:24Muka kuma sanya shugabanni daga cikinsu waɗanda suke shiryarwa da umarninmu yayin da suka yi haƙuri, suka kuma kasance suna sakankancewa da ayoyinmu.
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَفۡصِلُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 32:25Lalle Ubangijinka Shi ne zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna sassaɓawa a kansa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci cewa ya ba wa Annabi Musa littafin Attaura, sai kuma ya faɗakar da Manzonsa (ﷺ) cewa, kada ya yi wani kokwanto game da haɗuwarsu da shi Annabi Musa a daren Isra’i da Mi’iraji. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A daren da aka yi Isra’i da ni na ga Musa ɗan Imrana, wani mutum ne wankan tarwaɗa, dogo mai cibbiri-cibbirin gashin kai kamar dai shi ɗaya ne daga cikin mazajen ƙabilar Shanu’a…” [Bukhari #3239 da Muslim #165]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya sanya littafin Attaura da ya ba wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zama shiriya ne ga Banu Isra’ila, wanda ya ƙunshi shari’ar da ta dace da zamaninsu; saɓanin Alƙur’ani, shi Allah ya sanya shi shiriya ne ga mutanen duniya baki ɗaya a kowane zamani. Sai kuma Allah ya yaba wa wasu daga cikin Banu Isra’ila, da cewa ya mayar da su shugabanni masu gaskiya waɗanda mutane za su yi koyi da su, suna kuma nuna gaskiya a ayyukansu, saboda haƙurin da suka yi wajen aiki da umarninsa da guje wa haninsa da kuma juriya wajen isar da saƙonsa, sannan kuma suna ba da gaskiya matuƙa sosai da ayoyin da Allah ya saukar wa manzanninsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Manzonsa (ﷺ) cewa shi ne zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alƙiyama game da abin da suka kasance a nan duniya suna saɓani a kansa, sai ya bayyana mai gaskiya da marar gaskiya a tsakaninsu ya kuma yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa.
أَوَلَمۡ يَهۡدِ لَهُمۡ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ يَمۡشُونَ فِي مَسَٰكِنِهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٍۚ أَفَلَا يَسۡمَعُونَ
Open ayah 32:26Yanzu ba su gane wa idanunsu ba al’ummu nawa Muka hallakar a gabaninsu waɗanda suke ta zirga-zirga tsakankanin gidajensu? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi; to me ya sa ba sa sauraro ne?
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا نَسُوقُ ٱلۡمَآءَ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡجُرُزِ فَنُخۡرِجُ بِهِۦ زَرۡعٗا تَأۡكُلُ مِنۡهُ أَنۡعَٰمُهُمۡ وَأَنفُسُهُمۡۚ أَفَلَا يُبۡصِرُونَ
Open ayah 32:27Ko kuwa ba sa gani cewa Mu Muke koro ruwa zuwa ga ƙeƙasasshiyar ƙasa, sai Mu fitar da tsirrai da shi, waɗanda dabbobinsu da su kansu suke ci daga gare shi? To me ya sa ba sa lura ne? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin kafirai a kan cewa yanzu ba su gane wa idanuwansu ba irin yadda Allah ya hallaka al’ummun da suka gabace su waɗanda suka ƙaryata manzanninsu? Ga su kuwa a kullum suna ta zirga-zirga a tsakankanin gidajensu da suke zaune a ciki kafin a hallaka su, amma ba su wa’azantu da wannan ba. Allah ya bayyana cewa lalle a cikin abin da ya faru ga waɗannan al’ummu na hallaka saboda kafircinsu da miyagun ayyukansu akwai abin izina da wa’azi da shaidar da ta tabbatar da cewa manzanninsu masu gaskiya ne, Allah ne kuma ya aiko su. To yanzu su waɗannan kafiran ba za su tsaya su yi sauraro na fahimta da wa’azantuwa ba? Sannan Allah ya sake jan hankalinsu game da ƙaryata tashi bayan mutuwa da suke yi da cewa, ba sa ganin yadda yake aiko da ruwan sama zuwa ga ƙeƙasasshiyar ƙasa wadda ba ta fitar da komai sai ya raya ta da wannan ruwan saman sai ka ga ta fitar da tsirranta wanda suke ci su da dabbobinsu? Yanzu ashe ba za su dubi wannan aiki na Allah ba su gane cewa wanda ya iya raya ƙeƙasasshiyar ƙasa zai iya raya matattu?
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡفَتۡحُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 32:28Suna kuma cewa: “Yaushe ne (ranar) wannan hukuncin idan kun kasance masu gaskiya?
قُلۡ يَوۡمَ ٱلۡفَتۡحِ لَا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِيمَٰنُهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ
Open ayah 32:29Ka ce: “Ranar hukuncin, waɗanda suka kafirce, imaninsu ba zai amfane su ba, kuma ba ma za a saurara musu ba.”
فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَٱنتَظِرۡ إِنَّهُم مُّنتَظِرُونَ
Open ayah 32:30To ka rabu da su, ka kuma saurara, lalle su ma masu sauraro ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai suke neman gaggauto da azabar Allah da fushinsa a kansu, domin su nuna rashin imaninsu da Allah har ma suna cewa yaushe ne hukuncin Allah zai zo wanda muminai suke ta faɗa musu cewa yana zuwa, kuma a ranar ne Allah zai yanke hukuncinsa a tsakaninsu ya kai ɗan wuta cikin wuta, ɗan Aljanna ya tafi Aljanna? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) cewa ya faɗa musu, idan ranar hukuncin ta zo, to su sani waɗanda suka kafirce wa Allah a nan duniya, imaninsu ba zai yi musu amfani ba a can yayin da suka yi ido biyu da azabar Allah, kuma ba za a jinkirta musu ba har su tuba a karɓi tubansu. Sai kuma ya umarci Manzo (ﷺ) cewa ya kau da kansa daga waɗannan kafirai, domin sun riga sun yi zurfi a cikin kafircinsu da ɓatarsu, ya saurari abin da zai auka musu na azaba su ma suna sauraro ne.