الأحزاب

Al-Ahzaab

The Clans · Surah 33 · Ayahs: 73 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ ٱتَّقِ ٱللَّهَ وَلَا تُطِعِ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا

    Open ayah 33:1

    Ya kai wannan Annabi, ka kiyaye dokokin Allah, kada ka yi wa kafirai da munafukai ɗa\'a. Lalle Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima.

  2. وَٱتَّبِعۡ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا

    Open ayah 33:2

    Kuma ka bi abin da ake yi maka wahayinsa daga Ubangijinka. Lalle Allah Ya kasance Masanin abin da kuke aikatawa ne.

  3. وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا

    Open ayah 33:3

    Ka kuma dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa wakili. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da kira ga Annabi (ﷺ) da umartar sa a kan ya dawwama a kan aiki da umarninsa da guje wa haninsa. Ya kuma hana shi yin biyayya ga kafirai da munafukai a kan abin da zukatansu suke so wanda ya saɓa wa shari’ar Allah. Allah ya tabbatar da cewa shi masanin duk abin da kafirai da munafukai suke ƙullawa ne, mai hikima ne a halittarsa da tsare-tsarensa da shari’arsa. Sannan Allah ya umarce shi da bin abin da ya saukar masa na wahayi shi da al’ummarsa, ya tabbatar musu cewa shi masanin duk abin da suke aikatawa ne kuma zai yi musu sakayya a kan ayyukansu baki ɗaya. Sai kuma ya umarce shi da ya dogara ga Allah shi kaɗai cikin dukkan al’amuransa, domin kuwa shi Allah ya isa ya zamanto wakili mai tsare bayinsa waɗanda suka dogara da shi.

  4. مَّا جَعَلَ ٱللَّهُ لِرَجُلٖ مِّن قَلۡبَيۡنِ فِي جَوۡفِهِۦۚ وَمَا جَعَلَ أَزۡوَٰجَكُمُ ٱلَّٰٓـِٔي تُظَٰهِرُونَ مِنۡهُنَّ أُمَّهَٰتِكُمۡۚ وَمَا جَعَلَ أَدۡعِيَآءَكُمۡ أَبۡنَآءَكُمۡۚ ذَٰلِكُمۡ قَوۡلُكُم بِأَفۡوَٰهِكُمۡۖ وَٱللَّهُ يَقُولُ ٱلۡحَقَّ وَهُوَ يَهۡدِي ٱلسَّبِيلَ

    Open ayah 33:4

    Allah bai sanya wa wani mutum zuciya biyu ba a cikinsa. Kuma bai sanya matanku waɗanda kuke yi musu zihari (su zama) iyayenku ba. Bai kuma sanya ‘ya’yan riƙonku (su zama) ‘ya’yanku ba. Wannan magana ce da kuke yi da bakunanku; Allah kuwa Yana faɗar gaskiya ne, kuma Shi ne Yake shiryarwa ga hanya (ta gaskiya).

  5. ٱدۡعُوهُمۡ لِأٓبَآئِهِمۡ هُوَ أَقۡسَطُ عِندَ ٱللَّهِۚ فَإِن لَّمۡ تَعۡلَمُوٓاْ ءَابَآءَهُمۡ فَإِخۡوَٰنُكُمۡ فِي ٱلدِّينِ وَمَوَٰلِيكُمۡۚ وَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٞ فِيمَآ أَخۡطَأۡتُم بِهِۦ وَلَٰكِن مَّا تَعَمَّدَتۡ قُلُوبُكُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمًا

    Open ayah 33:5

    Ku danganta su (‘ya’yan riƙo) ga iyayensu maza shi ne adalci a wurin Allah. Amma idan ba ku san iyayensu maza ba, to ‘yan’uwanku ne a addini, kuma bararrun bayinku ne. Babu kuma laifi a kanku game da abin da kuka yi kuskuren yin sa, sai dai abin da zukatanku suka yi gangancin (aikatawa). Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda aka riga aka sani cewa, babu wani mutum da Allah ya halicce shi da zuciya biyu a jikinsa; kowane mahaluƙi da zuciya ɗaya aka san shi. Don haka ba yadda za a yi matar mutum ta zama mahaifiyarsa; kowa a duniya mahaifiya ɗaya gare shi, ita ce wadda ta tsuguna ta haife shi. To duk wanda ya haramta wa kansa matarsa saboda ya mayar da ita a matsayin mahaifiyarsa, wannan ya zo da ƙarya da mummunar magana. Hakanan kuma ‘ya’yan riƙo da suke ƙarƙashin wasu ba za su taɓa zama ‘ya’yansu na cikinsu ba, su zama daidai wajen hukunce-hukuncen shari’a, domin ɗan mutum na haƙiƙa shi ne wanda ya haife shi daga tsatsonsa. Da wannan bayani ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rushe al’adar nan ta Larabawa ta jahiliyya da mutum yake haramta wa kansa matarsa ta hanyar kwatanta ta da mahaifiyarsa. Hakanan kuma al’adarsu ta mayar da ‘ya’yan riƙo daidai da ‘ya’yan da suka haifa wajen hukunce-hukuncen auratayya da gado. Allah ya tabbatar musu da cewa wannan magana ce kawai da suke faɗa da bakunansu, amma ko kaɗan ba gaskiya ce ba. Allah shi ne mai faɗar gaskiya don bayinsa su ji su yi aiki da ita, kuma shi ne yake shiryar da su zuwa ga hanyar gaskiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su danganta ‘ya’yan riƙo ga iyayensu maza na haƙiƙa, domin yin haka ne kaɗai adalci a wurin Allah. Idan kuwa ba su san iyayensu maza ba, to su riƙe su a matsayin ‘yan’uwansu ne a addini. Kuma ‘yantattun bayinsu, su ce da ɗayansu: Ya ɗan’uwana, wannan babu laifi a cikinsa. Hakanan idan sun yi kuskure wajen danganta wani zuwa wanda ba mahaifinsa ba, to a nan ma ba su da laifi. Amma za a kama su da laifi yayin da suka yi gangancin danganta wani zuwa wanda ba shi ya haife shi ba. Idan bawa ya yi laifi sannan ya tuba to lalle Allah mai gafara ne zai karɓi tubarsa, mai jin ƙai ne, shi ya sa ba zai kama mutum da laifin kuskure ba. Wannan ayar ta shafe abin da yake a farkon Musulunci na halaccin dangata ‘ya’yan riƙo zuwa ga waɗanda suke riƙon su. Allah ya yi umarni da cewa, lalle kowa a danganta shi da mahaifinsa na asali, yin haka kuma shi ne adalci a wurinsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: A da can Zaidu ɗan Harisa ba ma kiran sa da wani suna sai Zaidu ɗan Muhammad saboda shi ne ya ‘yanta shi, har sai da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: ‘Ku danganta su ga iyayensu maza shi ya fi adalci a wurin Allah.’ [Bukhari #4782 da Muslim #2425]. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Abu Huzaifa ɗan Utbatu ɗan Rabi’a sahabi ne da ya halarci yaƙin Badar, ya mayar da ɗan riƙonsa Salim ɗansa, ya kuma aura masa ‘yar ɗan’uwansa, watau Hindatu ‘yar Walidu ɗan Utbatu, alhalin shi Salim bararren bawa ne na wata mace daga cikin mutanen Madina. Hakanan Manzon Allah (ﷺ) ya mayar da Zaidu ɗansa. Yadda kuma abin yake tun a zamanin jahiliyya, idan mutum ya mayar da ɗan riƙonsa ɗansa sai mutane su danganta masa shi, idan ya mutu kuma sai wannan ɗan riƙo ya ci gadonsa, har lokacin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar. Sai aka danganta su zuwa iyayensu maza na asali; wanda kuwa ba a san ubansa ba sai akan ɗauke shi ɗan’uwa ko bararren bawa…” [Bukhari #4000]. Babu laifi don wani ya kira ɗan wani da cewa ‘ya ɗana’ da nufin nuna ƙauna da soyayya a gare shi. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce mini: ‘Ya ɗana.’” [Muslim #2151]. An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya danganta kansa ga wanda ba babansa ba alhali yana sane da cewa ba shi ne babansa ba, to Aljanna ta haramta gare shi.” [Bukhari #6766 da Muslim #63]. An karɓo daga Aliyyu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: ‘Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “…wanda ya danganta kansa ga wanda ba babansa ba; ko ya dangantu ga waɗanda ba su ne suka ‘yanta shi ba, to la’anar Allah da ta mala’iku da mutane gaba ɗaya ta tabbata a kansa, Allah ba zai karɓi farillarsa ko nafila ba.” [Muslim #1370]

  6. ٱلنَّبِيُّ أَوۡلَىٰ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ مِنۡ أَنفُسِهِمۡۖ وَأَزۡوَٰجُهُۥٓ أُمَّهَٰتُهُمۡۗ وَأُوْلُواْ ٱلۡأَرۡحَامِ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلَىٰ بِبَعۡضٖ فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ إِلَّآ أَن تَفۡعَلُوٓاْ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِكُم مَّعۡرُوفٗاۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَسۡطُورٗا

    Open ayah 33:6

    Annabi shi ya fi cancanta ga muminai fiye da kansu; matansa kuma iyayensu ne. Dangi na zumunta kuma shashinsu ya fi kusanci daga wani shashi a cikin Littafin Allah daga kusancin muminai da masu hijira, sai dai idan za ku aikata wani alheri ne ga masoyanku (muminai). Wannan ya kasance a rubuce a cikin Lauhul Mahafuzu. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa Annabi Muhammadu (ﷺ) shi ne ya fi cancantar su yi wa biyayya, su nuna masa ƙauna a fili fiye da kawunansu, su kuma fifita abin da ya umarce su da shi a kan abin da zukatansu suke sha’awa. Matansa kuwa a matsayin iyayen muminai suke a wajen girmamawa da darajtawa, don haka haramun ne ga wani mumini ya auri ɗaya daga cikinsu bayan rasuwarsa (ﷺ). An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani mumini face ni na fi kowa cancantar ya yi mini biyayya a duniya da lahira. Ku karanta wannan ayar in kun ga dama: ‘Annabi shi ya fi cancanta da muminai (su yi masa biyayya) fiye da kawunansu.’ Duk muminin da ya mutu ya bar dukiya to magadansa su gaje shi ko su wane ne. Idan kuwa ya bar bashi ko iyali mabuƙata, to waliyyinsa ya zo wurina ni ne majiɓincin al’amarinsa.” [Bukhari #2399]. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ni ne na fi cancanta ga kowane mumini fiye da kansa, duk mutumin da ya mutu ya bar bashi, to a zo wurina, wanda kuwa ya bar dukiya to ta magadansa ce.” [Muslim #867]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Hisham (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na kasance tare da Annabi (ﷺ) yana riƙe da hannun Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) sai Umar ya ce masa: ‘Ya Manzon Allah, lalle na fi son ka fiye da komai in ban da raina.’ Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce da shi: “A’a, na rantse da wanda raina yake hannunsa, har sai ka fi so na fiye da ranka.” Sai Umar ya ce da shi: “To lalle kam yanzu wallahi na fi son ka fiye da raina.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: ‘Sai yanzu ne ya Umar.’” [Bukhari #6632]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kuma bayyana wa muminai cewa dangi na zumunci su ne suka fi cancanta su ci gadon junansu a cikin hukuncin da Allah ya zartar, fiye da sauran muminai da waɗanda suka yi hijira don Allah. Waɗanda a farkon Musulunci suke cin gadon junansu ta wannan hanyar, sai aka soke gado a tsakaninsu daga baya. Sai kuma Allah ya nuna musu cewa suna iya su kyautata wa ‘yan’uwansu muminai waɗanda ba za su ci gadonsu ba, ta hanyar wasiyya ko kyauta; yin haka abu ne mai kyau. Ya tabbatar musu da cewa wannan hukunci da ya bayyana musu haka yake a rubuce a cikin Lauhul Mahfuzu, don haka aiki da shi ya zama wajibi.

  7. وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِيثَٰقَهُمۡ وَمِنكَ وَمِن نُّوحٖ وَإِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۖ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

    Open ayah 33:7

    Kuma (ka tuna) lokacin da Muka riƙi alƙawura daga annabawa (na isar da aike), kuma daga gare ka, kuma daga Nuhu da Ibrahimu da Musa da Isa ɗan Maryamu; Muka kuma riƙi alƙawari mai kauri daga gare su.

  8. لِّيَسۡـَٔلَ ٱلصَّٰدِقِينَ عَن صِدۡقِهِمۡۚ وَأَعَدَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابًا أَلِيمٗا

    Open ayah 33:8

    Don (Allah) Ya tambayi masu gaskiya game da gaskiyarsu, Ya kuma tanadi azaba mai raɗaɗi ga kafirai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya tuna alƙawari mai ƙarfi da ya yi da annabawa na cewa su bauta masa shi kaɗai kada su haɗa shi da komai, kuma su isar wa al’ummunsu wahayin da ya yi musu. Sai kuma Allah ya ware manyansu waɗanda suka fi himma wajen isar da saƙonsa, ya tuna musu alƙawarinsa a gare su, waɗannan kuwa su ne: Shi kansa Manzon Allah (ﷺ) da kuma Annabi Nuhu wanda shi ne farkon manzannin Allah a bayan ƙasa, sai kuma Annabi Ibrahim Badaɗayin Allah mai rahama, uban annabawa, sannan Annabi Musa abokin zancen Allah (Mai tsarki da daukaka), sannan Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) mai yawan albarka. Allah ya tabbatar wa da Annabi (ﷺ) shugaban talikai duka, cewa ya yi alƙawari mai ƙarfi da waɗannan annabawa duka. Ya yi wannan alƙawari ne da su domin ya tambayi masu gaskiya game da gaskiyarsu, ya kuma tambayi annabawan ko sun isar da saƙon da ya aike su da shi, domin ya yi kyakkyawar sakayya ga waɗanda suka ba da gaskiya da su suka bi su; su kuma waɗanda suka kafirce musu suka ƙaryata saƙon da ya aiko su da shi ya yi musu tanadin wata azaba mai raɗaɗi ta wutar Jahannama a ranar alƙiyama.

  9. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ جَآءَتۡكُمۡ جُنُودٞ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا وَجُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرًا

    Open ayah 33:9

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku tuna ni’imar Allah a gare ku lokacin da wasu rundunoni (na gangankon kafurai) suka zo muku, sai Muka aiko musu iska da wasu rundunoni da ba ku gan su ba. Allah kuwa Ya kasance Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.

  10. إِذۡ جَآءُوكُم مِّن فَوۡقِكُمۡ وَمِنۡ أَسۡفَلَ مِنكُمۡ وَإِذۡ زَاغَتِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَبَلَغَتِ ٱلۡقُلُوبُ ٱلۡحَنَاجِرَ وَتَظُنُّونَ بِٱللَّهِ ٱلظُّنُونَا۠ 

    Open ayah 33:10

    A lokacin da suka zo muku ta samanku da ƙasanku, da kuma yayin da idanuwa suka kauce wa (ganin komai sai maƙiya), zukatanku kuma suka cika da tsoro kuka riƙa zace-zace game da Allah.

  11. هُنَالِكَ ٱبۡتُلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَزُلۡزِلُواْ زِلۡزَالٗا شَدِيدٗا

    Open ayah 33:11

    A nan ne fa aka jarrabi muminai, aka kuma girgiza su girgizawa mai tsanani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin wata babbar ni’ima da ya yi wa Musulmi ta ba su kariya da nasara a kan gangamin abokan gabarsu, ya kuma ja hankalinsu zuwa ga yi masa godiya a kan wannan ni’imar. Kafiran Ƙuraishawa sun yi ta kwafsa yaƙi da Musulmi amma ba su sami wata nasara ba, sun jefa kansu cikin matsaloli da dama har ta kai kasuwancinsu ya shiga matsala, domin sun rasa hanyoyinsu na tafiya ƙasar Sham fatauci. Hakanan su ma Yahudawan Madina sun gwada yaƙar Manzon Allah (ﷺ) ta hanyoyin makirce-makirce amma ba su yi nasara ba, har Annabi (ﷺ) ya kori wasu daga cikinsu daga Madina. Wannan ya sa suka shiga zuga mushirikai a kan su haɗa ƙarfi su yaƙi Musulmi don su karya su su huta. A shekara ta biyar bayan hijira suka haɗa runduna ta mayaƙa dubu goma suka nufo Madina don rushe da’awar Annabi (ﷺ) da kawo ƙarshen Musulunci. Da Annabi (ﷺ) ya samu labarin kafirai za su zo yaƙar sa, sai ya yi shawara da sahabbansa a kan abin da ya kamata su yi don fuskantar wannan babbar matsala, sai suka yanke shawara a kan su haƙa rami babba, watau Gwalalo a kan iyakokin Madina domin hana rundunonin kafirai shigowa cikinta, saboda sun yi yawan da Musulmi ba za su iya tunkarar su da yaƙi ba. To a nan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake tunatar da Musulmi game da ni’imar da ya yi musu, da cewa rundunonin kafirai sun zo Madina domin yaƙar su inda Yahudawan Madina da munafukai suka taimaka wa kafiran, to amma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da wata iska mai ƙarfi wadda ta tuttunɓuke tantunansu, ta kifar da tukwanen girke-girkensu, ta kashe musu wutacen da suka hura, kuma guguwa mai ƙarfi ta taso ta turbuɗe musu kayayyakinsu, nan take duk suka tarwatse suka ɗaiɗaice cikin hasara da wulaƙanci. Allah kuma ya aiko musu da wata runduna ta mala’iku waɗanda babu mai ganin su, Allah kuma ya kasance mai ganin abin da bayinsa suke aikatawa ne, kuma zai yi musu sakayya a kan ayyukansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin tsananin tsoro da Musulmi suka shiga yayin da kafirai suka zo musu ta saman kwazazzabo da ƙasansa, watau ta gabas da yamma, a lokacin idanu suka kauce wa ganin komai in ban da maƙiyansu, zukata suka cika da tsoro da razani har wasu daga cikin Musulmi suka yi ta yin zace-zace iri-iri game da Allah; wani lokaci su yi zaton samun nasara, wani lokaci kuma su riƙa zaton ba za su yi nasara ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a wannan lokaci ne aka jarrabi muminai da ganin wannan gangami na maƙiya, aka kuma girgiza su da tsananin tsoro matuƙar girgizawa, a lokacin ne aka gane mumini na gaskiya da munafuki mai ƙaryar imani.

  12. وَإِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ مَّا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ إِلَّا غُرُورٗا

    Open ayah 33:12

    Kuma (ka tuna) lokacin da munafukai da waɗanda suke da cuta a zukatansu suke cewa: “Allah da Manzonsa ba wani alƙawarin da suka yi mana sai na ruɗi.”

  13. وَإِذۡ قَالَت طَّآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ يَٰٓأَهۡلَ يَثۡرِبَ لَا مُقَامَ لَكُمۡ فَٱرۡجِعُواْۚ وَيَسۡتَـٔۡذِنُ فَرِيقٞ مِّنۡهُمُ ٱلنَّبِيَّ يَقُولُونَ إِنَّ بُيُوتَنَا عَوۡرَةٞ وَمَا هِيَ بِعَوۡرَةٍۖ إِن يُرِيدُونَ إِلَّا فِرَارٗا

    Open ayah 33:13

    Kuma (ka tuna) lokacin da wata jama’a daga cikinsu ta ce: “Ya ku mutanen Yasriba, ba ku da wurin zama, sai ku koma.” Wata ƙungiya kuma daga cikinsu tana neman izinin Annabi da cewa: “Lalle gidajenmu tsirara tuƙwi suke,” alhali kuwa ba tsirara tuƙwi suke ba; ba abin da suke nufi sai gudu.

  14. وَلَوۡ دُخِلَتۡ عَلَيۡهِم مِّنۡ أَقۡطَارِهَا ثُمَّ سُئِلُواْ ٱلۡفِتۡنَةَ لَأٓتَوۡهَا وَمَا تَلَبَّثُواْ بِهَآ إِلَّا يَسِيرٗا

    Open ayah 33:14

    Da kuwa za a shigo musu ta kowane ɓangare sannan a neme su da yin fitinar (komawa ga kafirci), to Wallahi da sun aikata (hakan) ba kuwa za su jinkirta da shi ba (wato kafircin) sai ɗan lokacin ƙanƙani.

  15. وَلَقَدۡ كَانُواْ عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ مِن قَبۡلُ لَا يُوَلُّونَ ٱلۡأَدۡبَٰرَۚ وَكَانَ عَهۡدُ ٱللَّهِ مَسۡـُٔولٗا

    Open ayah 33:15

    Tun da can kuwa haƙiƙa sun yi wa Allah alƙawarin (cewa) ba za su ba da baya ba. Alƙawarin Allah kuwa ya kasance abin tambaya ne.

  16. قُل لَّن يَنفَعَكُمُ ٱلۡفِرَارُ إِن فَرَرۡتُم مِّنَ ٱلۡمَوۡتِ أَوِ ٱلۡقَتۡلِ وَإِذٗا لَّا تُمَتَّعُونَ إِلَّا قَلِيلٗا

    Open ayah 33:16

    Ka ce: “In kuna guje wa mutuwa ne ko kisa, to gudun ba zai amfane ku ba, a yayin nan kuwa ba za a jiyar da ku wani daɗi ba sai ɗan kaɗan.”

  17. قُلۡ مَن ذَا ٱلَّذِي يَعۡصِمُكُم مِّنَ ٱللَّهِ إِنۡ أَرَادَ بِكُمۡ سُوٓءًا أَوۡ أَرَادَ بِكُمۡ رَحۡمَةٗۚ وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

    Open ayah 33:17

    Ka ce: “Wane ne zai kare ku daga Allah idan Ya nufe ku da wani mummunan abu ko kuma Ya nufe ku da wata rahama?” Ba kuma za su sama wa kansu wani majiɓinci ko mai taimako ba in ba Allah ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin da munafukai suka riƙa nuna wa Musulmi yayin da suka ga yanayin da Musulmi suke ciki, inda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tuna sanda munafukai da wasu masu raunin imani masu shakka a zukatansu suke da’awar cewa duk alƙawarin nasara a kan maƙiya wanda Allah da Manzonsa suka yi musu ba komai ne ba sai ruɗi kawai, watau ruɗar su kawai ake yi ba a gaya musu gaskiyar al’amari. An ruwaito cewa wani daga cikin munafukai har cewa yake yi: “Muhammadu yana yi mana alƙawarin cewa za mu mallake taskokin dukiyar Kisra da Ƙaisara, alhalin ga shi ɗayanmu ba ya iya fita bayan gari don biyan buƙatarsa.” [Dubi, Ɗabarani Al-Mu’jamul Kabir #3017]. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Manzonsa (ﷺ) da cewa ya tuna lokacin da wata ƙungiya ta munafukai suka riƙa kiran muminai mutanen Madina da sunan ‘Mutanen Yasriba’, watau tsohon sunan Madina tun gabanin Musulunci, suna cewa ba su da wurin zama a inda suka tsaya, watau daidai dutsen Sal’u a kusa da Gwalalon da suka haƙa, suna umartar su da su koma gidajensu cikin ƙuryar Madina, suna kuwa faɗa musu haka ne domin su daƙile su su hana su yaƙi tare da Manzon Allah (ﷺ) da sauran Musulmi mutanen Makka. Sai kuma wata ƙungiyar daban ta munafukai waɗanda su kuma suka riƙa neman izinin Annabi (ﷺ) a kan ya ba su dama su koma gidajensu, suna da’awar cewa sun baro gidajensu fayau babu wani tsaro, don haka suna jin tsoron kada abokan gabarsu su auka wa iyalansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata su ya tabbatar wa Manzon Allah cewa gidajensu ba fayau suke ba kamar yadda suka faɗa; manufarsu kawai ita ce su gudu su bar fagen yaƙi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara fito da halin waɗannan munafukai fili da cewa, da a ce kafirai za su sami shigo musu cikin Madina ta kowace nahiya sannan su neme su da su bar Musulunci su koma cikin kafirci da shirka da Allah, ba shakka da sun yarda sun ba wa maƙiyansu wannan dama sun yi ridda sun koma cikin shirka, ba tare da sun jinkirta aikata hakan ba sai jinkiri na ɗan lokaci kaɗan, domin da man addinin bai ratsa zukatansu ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara da cewa da can su waɗannan munafukai bayan gudowar ranar yaƙin Uhudu sun yi wa Allah alƙawari ba za su sake gudu daga fagen yaƙi ba domin tsoro ko karya alƙawari, to sai ga shi yanzu sun karya wannan alƙawarin sun manta da cewa sai Allah ya tambayi bawansa a kan alƙawarin da ya ɗauka, shin ya cika koko a’a? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa wa munafukai cewa gudu daga fagen daga don tsoron yaƙi ko tsoron mutuwa ba zai yi musu wani amfani ba, domin Allah ya riga ya yanka wa kowa ajalinsa, don haka ko da sun gudu amma ajalinsu bai yi ba, to fa ba za su ji daɗin rayuwarsu ba sai na ɗan lokaci kaɗan. Sai Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya tambaye su cewa wane ne ya isa ya kare su daga Allah idan ya nufe su da wani mummunan abu kamar mutuwa ko kisa, ko kuma ya nufe su da wata rahama kamar kuɓuta daga kisa ko samun wani alheri, wane ne zai iya hana ɗayan waɗannan ya same su? Don haka gudunsu daga fagen yaƙi ba zai tsinana musu komai ba, kuma ba za su iya sama wa kansu wani majiɓincin al’amarinsu ko mataimaki ba wanda zai kare su daga azabar Allah in ba Allah shi kaɗai ba.

  18. ۞قَدۡ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ ٱلۡمُعَوِّقِينَ مِنكُمۡ وَٱلۡقَآئِلِينَ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ هَلُمَّ إِلَيۡنَاۖ وَلَا يَأۡتُونَ ٱلۡبَأۡسَ إِلَّا قَلِيلًا

    Open ayah 33:18

    Haƙiƙa Allah Yana sane da masu hana ruwa gudu daga cikinku, da masu ce wa ‘yan’uwansu: “Ku zo wurinmu,” kuma ba sa zuwa yaƙi sai kaɗan.

  19. أَشِحَّةً عَلَيۡكُمۡۖ فَإِذَا جَآءَ ٱلۡخَوۡفُ رَأَيۡتَهُمۡ يَنظُرُونَ إِلَيۡكَ تَدُورُ أَعۡيُنُهُمۡ كَٱلَّذِي يُغۡشَىٰ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡمَوۡتِۖ فَإِذَا ذَهَبَ ٱلۡخَوۡفُ سَلَقُوكُم بِأَلۡسِنَةٍ حِدَادٍ أَشِحَّةً عَلَى ٱلۡخَيۡرِۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَمۡ يُؤۡمِنُواْ فَأَحۡبَطَ ٱللَّهُ أَعۡمَٰلَهُمۡۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٗا

    Open ayah 33:19

    (Su ne) masu yi muku rowar (taimako); sannan idan (abin) tsoro ya zo, sai ka gan su suna duban ka idanuwansu suna jujjuyawa kamar wanda yake suman mutuwa; sannan idan tsoron ya yaye, sai su riƙa cutar da ku da harsuna kaifafa, suna masu rowar alheri. Waɗannan ba su yi imani ba, don haka Allah Ya lalata ayyukansu. Wannan kuwa ya kasance abu ne mai sauƙi a wurin Allah.

  20. يَحۡسَبُونَ ٱلۡأَحۡزَابَ لَمۡ يَذۡهَبُواْۖ وَإِن يَأۡتِ ٱلۡأَحۡزَابُ يَوَدُّواْ لَوۡ أَنَّهُم بَادُونَ فِي ٱلۡأَعۡرَابِ يَسۡـَٔلُونَ عَنۡ أَنۢبَآئِكُمۡۖ وَلَوۡ كَانُواْ فِيكُم مَّا قَٰتَلُوٓاْ إِلَّا قَلِيلٗا 

    Open ayah 33:20

    Suna zaton rundunonin gangami ba su tafi ba; da a ce kuwa rundunonin na gangami za su sake dawowa to da sai su riƙa burin ina ma suna can tare da mutanen ƙauye suna tambayar labaranku; ko ma da za su kasance a cikinku to da ba za su yi yaƙi ba sai ɗan kaɗan. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tabbatar da cewa yana sane da duk abin da munafukai suke yi na daƙile Musulmai da karya musu gwiwa wajen fita yaƙi, yana kuma sane da masu cewa ‘yan’uwansu su dawo wurinsu su bar fagen yaƙi domin babu wata nasara da za su samu a can, kuma suna jiye musu tsoron a kashe su. Allah ya bayyana cewa waɗannan masu sage wa ‘yan’uwansu gwiwa mutane ne da ba kasafai suke fita yaƙi tare da Musulmi ba sai wasu ‘yan lokuta kaɗan, domin kawai guje wa abin kunya ba don su taimaka wa Allah da Manzonsa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wani mummunan hali da aka san munafukai da shi na tsananin rowa da dukiyarsu ba sa ciyar da ita don Allah, kuma masu rowa da kawunansu ba sa fita yaƙi tare da Musulmi sannan ba sa nuna wa Musulmi ƙauna ko kaɗan. Sannan kuma ya bayyana tsananin tsoro da ke tare da su da zarar sun ga wani abin tsoro, kamar abokan gaba sun tunkaro su sai a gan su sun yi zuru-zuru da idanuwansu suna jujjuya su kamar wanda yake cikin magagin mutuwa yana suma. To amma da zarar tsoron ya kau, hankulansu sun dawo jikinsu sai su shiga cutar da muminai da kausasan maganganu masu ciwo. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya siffanta su da tsananin rowar alheri idan an buƙaci hakan daga gare su. Allah ya tabbatar da cewa waɗannan mutane alal-haƙiƙa ba su yi imani ba, don haka ya lalata sakamakon ayyukansu, yin haka kuwa a wurinsa abu ne mai sauƙi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗannan munafukai ba su yi tsammanin gangamin rundunonin maƙiya za su bar Madina ba tare da sun shigo cikinta sun yi kaca-kaca da ita ba. To Allah (Mai tsarki da daukaka) ya taɓar da zatonsu ya fatattaki kafirai. Ya kuma bayyana cewa da a ce waɗannan rundunoni za su sake dawowa karo na biyu, to da sai waɗannan munafukai sun riƙa fatan su gudu su koma ƙauyuka tare da mutanen ƙauye suna tambayar labarin halin da Musulmi a Madina suke ciki, watau suna nan ko kuma kafirai sun gama da su? Sannan ya tabbatar wa muminai cewa ai in da ma za su tsaya su fita yaƙi tare da su, to ba za su taɓuka komai ba na a-zo-a-gani, don haka kada muminai su damu da su ko su yi baƙin cikin rabuwarsu da su.

  21. لَّقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِي رَسُولِ ٱللَّهِ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَذَكَرَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا

    Open ayah 33:21

    Haƙiƙa kuna da kyakkyawan abin koyi tare da Manzon Allah, ga wanda yake yin kyakkyawan fata game da Allah da ranar lahira, ya kuma ambaci Allah da yawa.

  22. وَلَمَّا رَءَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلۡأَحۡزَابَ قَالُواْ هَٰذَا مَا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَصَدَقَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥۚ وَمَا زَادَهُمۡ إِلَّآ إِيمَٰنٗا وَتَسۡلِيمٗا

    Open ayah 33:22

    Lokacin kuwa da muminai suka ga rundunonin gangami sai suka ce: “Wannan shi ne abin da Allah da Manzonsa suka yi mana alƙawari, Allah kuwa da Manzonsa sun yi gaskiya. Ba kuwa abin da (wannan) ya ƙara musu sai imani da miƙa wuya.

  23. مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ رِجَالٞ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيۡهِۖ فَمِنۡهُم مَّن قَضَىٰ نَحۡبَهُۥ وَمِنۡهُم مَّن يَنتَظِرُۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبۡدِيلٗا

    Open ayah 33:23

    <b> Akwai wasu mazaje daga muminai da suka cika abin da suka yi wa Allah alƙawari da shi; akwai daga cikinsu wanda ya haɗu da ajalinsa, akwai kuma daga cikinsu wanda yake sauraron (ajalin); kuma ba su yi kowace irin saɓawa ba (game da alƙawarin).

  24. لِّيَجۡزِيَ ٱللَّهُ ٱلصَّٰدِقِينَ بِصِدۡقِهِمۡ وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ إِن شَآءَ أَوۡ يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

    Open ayah 33:24

    Don Allah Ya saka wa masu gaskiya a kan gaskiyarsu, Ya kuma azabtar da munafukai idan Ya ga dama, ko kuma Ya karɓi tubarsu. Lalle Allah Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa suna da kyakkyawan abin koyi a tare da Manzon Allah (ﷺ) daga maganganunsa da ayyukansa, kamar yadda yake fita da kansa wurin yaƙi, ya sadaukar da dukiyarsa da kansa domin ɗaukaka addinin Allah. To saboda me sauran Musulmi ba za su yi koyi da shi a nan ba? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa babu wanda zai yi koyi da Manzon Allah (ﷺ) sai mutumin da yake yin kyakkyawan fata game da Allah da kuma ranar lahira na samun kyakkyawan sakamako a can, yake kuma aiki domin haka, ya kuma ambaci Allah ambato mai yawa. Amma duk wanda ba haka yake ba to ba zai zama mai koyi da shi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halayen muminai da suka bambanta da halayen munafukai, da cewa lokacin da muminai suka ga gangamin rundunar kafirai sun nufo su domin yaƙar su sai suka tabbatar da cewa wannan shi ne abin da Allah da Manzonsa suka yi musu alƙawarin faruwarsa, domin Allah da Manzonsa sun tabbatar musu da cewa sai an jarrabe su da bala’o’i iri-iri kafin nasarar Allah ta zo musu, suka nuna gaskatawarsu ga Allah da Manzonsa domin abin da suka sanar da su ga shi ya tabbata. Allah ya yi musu shaida da cewa ganinsu ga wannan rundunonin kafirai ba abin da ya ƙara musu sai imani da miƙa wuya ga Allah da umarninsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi wasu jajirtattun muminai waɗanda suka yi wa Allah alƙawari na gaskiya suka kuma cika shi, yayin da suka dage suka yi haƙuri wajen yaƙi da kafirai. Daga cikinsu akwai waɗanda suka rasu ko aka kashe su suka yi shahada; akwai kuma waɗanda suke jiran shahadar ta zo musu, ba su canza komai daga alƙawarin da suka yi wa Allah ba, kamar yadda munafukai suka canja. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Baffana wanda aka yi masa takwara da ni (watau Anas ɗan An-Nadhru) bai sami fita yaƙin Badar tare da Manzon Allah (ﷺ) ba sai abin yake damun sa ainun, har yana cewa: ‘Yanzu a ce yaƙin farko da Manzon Allah (ﷺ) ya halarta ni ban sami halartar sa ba. Idan har Allah ya nuna mini lokacin da zan halarci wani yaƙi tare da Manzon Allah (ﷺ) to Allah zai ga abin da zan aikata.’ Sai ya ji nauyin ya yi wata maganar ban da wannan. Sai ya sami halartar yaƙin Uhudu tare da Manzon Allah (ﷺ). Sai Sa’adu ɗan Mu’azu ya haɗu da shi sai Anas ya tambaye shi ya ce: ‘Ya Baban Amru ina zuwa ne?’ Sannan ya ce: ‘Wayyo ina jiyo ƙanshin Aljanna kafin in ƙarasa dutsen Uhudu!’ Nan take ya shiga yaƙar kafirai har sai da aka kashe shi, aka sami gurbin suka da sara da harbi har tamanin da ɗoriya a jikinsa. Sai ‘yar’uwarsa Rubayyi’u ‘yar Nadhru (Allah ya kara mata yarda) ta ce: ‘Ban gane gawar ɗan’uwana ba sai ta hanyar zanen ‘yan yatsunsa.’ Sai wannan ayar ta 23 ta sauka. Sahabbai suna ganin a kansa ne da sauran abokansa wannan ayar ta sauka.” [Muslim #1903]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin da ya sanya yake jarrabar muminai a nan duniya, watau domin ya saka wa masu gaskiya waɗanda suka cika wa Allah alƙawarin da suka ɗaukar masa. Su kuma munafukai ya azabtar da su saboda karya alƙawarinsu; idan ya ga damar yi musu haka sai ya karɓi ransu tun gabanin su tuba su bar kafirci. Idan kuma ya ga dama sai ya datar da su su tuba su koma gare shi, domin shi ya tabbata mai gafara ne ga wanda ya tuba mai rahama ne gare shi.

  25. وَرَدَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِغَيۡظِهِمۡ لَمۡ يَنَالُواْ خَيۡرٗاۚ وَكَفَى ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلۡقِتَالَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ قَوِيًّا عَزِيزٗا

    Open ayah 33:25

    Allah kuma Ya komar da waɗanda suka kafirta da fushinsu ba su sami wani alheri ba. Allah kuma Ya ɗauke wa muminai yin yaƙi. Domin kuwa Allah Ya kasance Mai ƙarfi ne, Mabuwayi.

  26. وَأَنزَلَ ٱلَّذِينَ ظَٰهَرُوهُم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مِن صَيَاصِيهِمۡ وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلرُّعۡبَ فَرِيقٗا تَقۡتُلُونَ وَتَأۡسِرُونَ فَرِيقٗا

    Open ayah 33:26

    Ya kuma sauko da waɗanda suka taimake su daga ma’abota littafi daga ganuwoyinsu Ya kuma jefa tsoro a zukatansu, wasu jama’ar kuke kashe su kuna kuma ribace wasu jama’ar.

  27. وَأَوۡرَثَكُمۡ أَرۡضَهُمۡ وَدِيَٰرَهُمۡ وَأَمۡوَٰلَهُمۡ وَأَرۡضٗا لَّمۡ تَطَـُٔوهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٗا

    Open ayah 33:27

    Ya kuma gadar muku ƙasarsu da gidajensu da dukiyoyinsu, da kuma wata ƙasa ma da ba ku taɓa taka ta ba. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya murƙushe gangamin rundunonin kafiran Ƙuraishawa da ƙabilar Gaɗafanu da waɗanda suke tare da su ya sanya su cikin baƙin ciki da damuwar rashin cim ma burinsu na cin muminai da yaƙi. Allah kuma ya ɗauke wa muminai wannan yaƙin ya aiko wa da kafirai wata guguwa mai ƙarfi ya kuma saukar da mala’iku ya fatattaki rundunar kafirai da su. Allah ya tabbatar da cewa shi mai ƙarfi ne mabuwayi, babu mai iya ja da shi ko ya yi nasara a kansa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan yana dawowa daga wurin yaƙi ko hajji ko umara yakan fara yin kabarbari uku sannan ya ce: “Babu abin bauta da gaskiya sai Allah ba shi da abokin tarayya, mulki da yabo nasa ne, shi kuma mai iko ne a kan komai. Mu masu dawowa ne, masu tuba ne, masu bauta ne, masu sujjada ne ga Ubangijinmu, masu godiya ne. Allah ya gaskata alƙawarinsa ya taimaki bawansa ya karya rundunoni shi kaɗai.” [Bukhari #4116 da Muslim #1344]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abu Aufa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya yi mummunar addu’a ga rundunonin kafirci ya ce: “Ya Allah, ya wanda ya saukar da littafi, mai gaggawar hisabi, ka karya gangamin rundunonin kafirai. Ya Allah, ka karya su, ka girgiza su.” [Bukhari #2933 da Muslim #1744]. An karɓo daga Sulaimanu ɗan Surad (Allah ya kara masa yarda) ya ce: A ranar yaƙin Gwalalo Annabi (ﷺ) ya ce: “Nan gaba mu ne za mu fita yaƙar su ba su ne za su fito yaƙar mu ba.” [Bukhari #4109]. Watau bayan an fatattake su a wannan yaƙin. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya azabtar da Yahudawan da suka mara wa kafirai baya, watau Yahudawan Banu Ƙuraiza, da cewa ya sauko da su daga ganuwoyinsu waɗanda suka tanada domin kare kawunansu daga maƙiyansu. Allah kuma ya jefa tsoro a zukatansu suka kasa yin fito-na-fito da Musulmi suka miƙa wuya a gare su cikin wulaƙanci, Allah ya ɗora muminai a kansu suka riƙa kashe mazajensu waɗanda za su iya yin yaƙi suka kuma ribace mata da ƙananan yara. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan ya hallaka Yahudawa ya mallaka wa Musulmi gonakinsu na dabino da shuke-shuke, ya kuma mallaka musu gidajensu da sauran dukiyoyinsu, sai kuma ya yi wa Musulmi albishir da cewa ya mallaka musu wata ƙasa da ba su taɓa taka ta da ƙafafunsu ba, ita ce ƙasar Khaibar wadda Musulmi suka same ta bayan shekara bakwai da hijirar Annabi (ﷺ), bayan kuma shekara biyu da gama yaƙin Gwalalo. Tabbas Allah kuwa mai iko ne a kan komai, babu abin da yake gagarar sa. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Yayin da Manzon Allah (ﷺ) ya dawo daga yaƙin Gwalalo, ya ajiye makamansa ya yi wanka sai Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo masa ya ce: “Shin ka ajiye makamanka ne? Mu dai mala’iku wallahi har zuwa yanzu ba mu ajiye namu ba. Don haka ka fita zuwa gare su.” Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Zuwa ina?” Ya ce: “Nan nan kusa.” Sai ya nuna ɓangaren Yahudawan Banu Ƙuraiza. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya fita zuwa gare su. [Bukhari #2413 da Muslim #1769]. Annabi (ﷺ) ya yi musu ƙawanya har tsawon kwana ashirin da biyar, shugaban Yahudawa Ka’abu ɗan Asad ya yi wa jama\'arsa Yahudawa tayin su zaɓi ɗaya daga cikin abubuwa uku: 1. Ko dai su musulunta; 2. Ko kuma su kashe ‘ya’yansu da matansu da hannuwansu sannan su zare takubbansu su fita su yaƙi Musulmi ko su yi nasara ko a kashe su; 3. Ko kuma su bari sai ranar Assabar su shammaci Musulmi su auka musu, domin ba za su yi zaton za su yaƙe su a ranar Assabar ba. Amma ‘yan’uwansu Yahudawa suka shure duk waɗannan abubuwan uku. Sai daga ƙarshe suka yarda da duk wani hukuncin da Sa’ad ɗan Mu’azu zai yanke a kansu, domin suna ganin sun ƙulla ƙawance da shi a zamanin jahiliyya. Sai Annabi (ﷺ) ya sa aka je aka zo da shi a kan jaki ba shi da lafiya, sai shi kuma ya yanke hukuncin cewa a kashe duk mazajensu waɗanda za su iya yaƙi, a kama ‘ya’yansu da matansu a matsayin ribar yaƙi. [Dubi, Bukhari #4121 da Muslim #1768].

  28. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ إِن كُنتُنَّ تُرِدۡنَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتَهَا فَتَعَالَيۡنَ أُمَتِّعۡكُنَّ وَأُسَرِّحۡكُنَّ سَرَاحٗا جَمِيلٗا

    Open ayah 33:28

    Ya kai wannan Annabi, ka gaya wa matanka: “Idan kun kasance kuna son rayuwar duniya ne da kuma adonta, to sai ku zo in jiyar da ku daɗi, in kuma sake ku kyakkyawan saki.

  29. وَإِن كُنتُنَّ تُرِدۡنَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَ فَإِنَّ ٱللَّهَ أَعَدَّ لِلۡمُحۡسِنَٰتِ مِنكُنَّ أَجۡرًا عَظِيمٗا

    Open ayah 33:29

    “Idan kuwa kun kasance kuna ƙaunar Allah ne da Manzonsa da kuma ranar lahira, to haƙiƙa Allah Ya tanadi lada mai girma ga masu kyautatawa daga cikinku.

  30. يَٰنِسَآءَ ٱلنَّبِيِّ مَن يَأۡتِ مِنكُنَّ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖ يُضَٰعَفۡ لَهَا ٱلۡعَذَابُ ضِعۡفَيۡنِۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٗا 

    Open ayah 33:30

    Ya ku matan Annabi, duk wadda ta zo da wani abin ƙi na sarari daga cikinku to za a ninninka mata azaba ninki biyu. Yin wannan kuma ya kasance abu ne mai sauƙi ga Allah.

  31. ۞وَمَن يَقۡنُتۡ مِنكُنَّ لِلَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتَعۡمَلۡ صَٰلِحٗا نُّؤۡتِهَآ أَجۡرَهَا مَرَّتَيۡنِ وَأَعۡتَدۡنَا لَهَا رِزۡقٗا كَرِيمٗا

    Open ayah 33:31

    Duk kuwa wadda ta yi biyayya ga Allah da Manzonsa daga cikinku ta kuma yi aiki nagari, to za Mu ba ta ladanta sau biyu, kuma Mun tanadar mata arziki mai girma. Waɗannan ayoyi sun sauka ne lokacin da matan Annabi (ﷺ) suka haɗa baki suka same shi, suna neman sa da ya ƙara musu a kan abin da yake yi musu na ciyarwa da tufatarwa, suka nemi abin da ya fi ƙarfinsa. To sai abin ya dame shi sosai har ta kai ya yi rantsuwar ba zai sake shiga ɗakin kowa ce daga cikinsu ba har tsawon wata guda. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi nufin kawo masa sauƙi cikin lamarin ya kuma yi nufin ɗaukaka darajar matansa, ya tsarkake su daga duk wani abu da zai zubar musu mutuncinsu. Sai ya umarce shi da ya ba su zaɓin cewa, idan sun kasance rayuwar duniya suke so da kuma ƙyale-ƙyalen da ke cikinta, to su zo ya ba su ɗan abin more rayuwa da ake ba wa matan da aka saki, sannan sai ya sake su kyakkyawan saki wanda babu cutarwa a cikinsa. Idan kuwa sun kasance suna neman yardar Allah da Manzonsa ne, suna ƙaunar gidan Aljanna a lahira, to su yi haƙuri da rayuwar da suke ciki kuma lalle Allah ya tanadi lada mai girma ga duk wadda ta kyautata zamantakewarta da Manzon Allah ta yi haƙuri da rayuwar da take ciki. An karɓo daga A’isha matar Manzon Allah (ﷺ) ta ce: “Yayin da aka umarci Manzon Allah (ﷺ) cewa ya ba wa matansa zaɓi sai ya fara da ni ya ce mini: ‘Lalle zan faɗa miki wani al’amari, to amma kada ki yi gaggawa har sai kin nemi shawarar mahaifanki.’ Ta ce: “Annabi (ﷺ) ya riga ya san mahaifana ba za su taɓa ba ni shawarar rabuwa da shi ba. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta waɗannan ayoyi na 28-29”. Sai A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “A kan wanne abu ne a nan da har sai na yi shawara da mahaifana, lalle ni ina ƙaunar Allah da Manzonsa da gidan lahira.” Ta ce: “Sauran matayen Manzon Allah (ﷺ) su ma suka yi irin yadda na yi.” [Bukhari #4786 da Muslim #1475]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara jan kunnensu da yi musu albishir idan sun kyautata ayyukansu, ya kira su da ‘matan Annabi’ domin su fahimci girman matsayinsu, ya tabbatar musu da cewa duk wadda ta zo da wani saɓon Allah a sarari, to za a ninka mata azabarta ninki biyu a ranar alƙiyama saboda matsayinta da ba da kariya ga mutuncin Manzon Allah. Allah kuma ya nuna wannan riɓanya azabar a wurinsa abu ne mai sauƙi. Sannan ya nuna musu cewa wadda kuma ta ɗore a kan biyar Allah da Manzonsa, ta kuma yi aiki nagari, to ita ma Allah zai ninka mata ladanta har sau biyu, kuma a lahira Allah ya tanadar mata wani lada na karamci, watau gidan Aljanna.

  32. يَٰنِسَآءَ ٱلنَّبِيِّ لَسۡتُنَّ كَأَحَدٖ مِّنَ ٱلنِّسَآءِ إِنِ ٱتَّقَيۡتُنَّۚ فَلَا تَخۡضَعۡنَ بِٱلۡقَوۡلِ فَيَطۡمَعَ ٱلَّذِي فِي قَلۡبِهِۦ مَرَضٞ وَقُلۡنَ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

    Open ayah 33:32

    Ya ku matan Annabi, ku fa ba kamar sauran mata kuke ba. Idan kun kiyaye dokokin Allah, to kada ku tausasa murya har yadda wani mai raunin imani a zuciyarsa zai yi kwaɗayin (wani abu), kuma ku yi Magana irin maganar da ta dace da shari’a.

  33. وَقَرۡنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجۡنَ تَبَرُّجَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ ٱلۡأُولَىٰۖ وَأَقِمۡنَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتِينَ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِعۡنَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُذۡهِبَ عَنكُمُ ٱلرِّجۡسَ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِ وَيُطَهِّرَكُمۡ تَطۡهِيرٗا

    Open ayah 33:33

    Ku kuma zauna a cikin gidajenku, kada kuma ku riƙa fita (da bayyana ado) irin ta jahiliyyar farko; ku kuma tsayar da salla, ku ba da zakka, ku kuma bi Allah da Manzonsa. Abin da Allah Yake nufi kawai shi ne Ya kawar muku da duk wata ƙazanta, ya ku iyalin gidan Annabi, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa.

  34. وَٱذۡكُرۡنَ مَا يُتۡلَىٰ فِي بُيُوتِكُنَّ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ وَٱلۡحِكۡمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا

    Open ayah 33:34

    Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin gidajenku na ayoyin Allah da kuma hikima. Lalle Allah Ya kasance Mai tausayawa ne, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa matan Annabi (ﷺ) cewa su sani su fa ba kamar sauran mata suke ba wajen daraja da ɗaukaka da matsayi; su Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fifita darajarsu a kan ta sauran mata matuƙar za su kiyaye dokokin Allah su ji tsoron sa. Sai kuma Allah ya hana su tausasa murya idan suna magana da mazajen da ba muharramansu ba, domin yin haka zai sanya wanda yake da wata cuta ta munafurci ko sha’awa ta haram ya yi kwaɗayin wani abu tare da su. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya umarce su da su yi maganar da ta dace da gwargwadon buƙata wadda ba za ta ja hankali ba. Sannan kuma ya umarce su da su zauna a cikin gidajensu kada su riƙa fita yawo sai da buƙata, kada kuma su riƙa bayyana adonsu irin yadda mata suke yi a zamanin jahiliyya kafin zuwan Musulunci, yadda suke fito da kwalliyarsu don su ja hankulan mazaje. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku hana bayin Allah mata fita zuwa masallatan Allah, su kuma su fita ba cikin kwalliya ba.” [Abu Dawud #565]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mace al’aura ce, idan ta fita daga gidanta sai Shaiɗan ya sanya idanunsa a kanta, lokacin da ta fi kusanci da Ubangijinta shi ne lokacin da take zaune ƙuryar gidanta.” [Ɗabarani, Al-Mu’ujamul Ausaɗ #2890]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da tsayar da salla yadda ya dace, su kuma fitar da zakkar dukiyoyinsu, kuma su bi Allah da Manzonsa, ya nuna musu cewa ya umarce su da waɗannan abubuwa ne ba don komai ba sai don yana nufin gusar musu da duk wata ƙazanta ya tsarkake musu zukatansu, ya yi musu kwalliya da kyawawan ɗabi’u ya raba su da munana domin su Ahalin gidan Annabi ne (ﷺ). Haka kuma ya umarce su da su riƙa tuna ayoyin Allah da aka saukar wa Manzon Allah (ﷺ) waɗanda ake karanta su a gidajensu da kuma sunnar Manzo (ﷺ) wadda suke samu daga wurinsa, ya tabbatar musu cewa shi mai tausasawa ne gare su yayin da ya yi musu tagomashin kasancewa matan Manzonsa (ﷺ), kuma masani ne mai cikakken sani a lokacin da ya zaɓe su a matsayin matan Manzonsa (ﷺ), ya kuma mayar da su iyayen muminai. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda), ta ce: Wata rana Annabi (ﷺ) ya fito da safe sanye da wani mayafi mai zanen sirdin raƙuma a jikinsa, sai Hasan ɗan Aliyyu ya zo sai Manzon Allah (ﷺ) ya shigar da shi cikinsa, sai kuma Husaini shi ma ya zo, sai Manzo (ﷺ) ya shigar da shi cikin wannan mayafi, sai Faɗima ta zo ita ma ya shigar da ita ciki, sannan sai Aliyyu ya zo shi ma Manzon Allah (ﷺ) ya shigar da shi ciki, sannan sai ya ce: “Abin da Allah yake nufi kawai shi ne ya kawar muku da duk wata ƙazanta, ya ku Ahalin gidan Annabi, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa.” [Muslim #2424]. An karɓo daga Umar ɗan Abu Salama (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da wannan aya ta sauka ga Annabi (ﷺ) yana gidan Ummu Salama (Allah ya kara mata yarda), sai ya kirawo Faɗima da Hasan da Husaini sai ya lulluɓe su a cikin mayafi, Aliyyu kuma yana bayansa shi ma ya lulluɓe shi, sannan ya ce: “Ya Allah, waɗannan Ahalin gidana ne, ka gusar musu da ƙazanta, ka kuma tsarkake su tsarkakewa sosai.” Ummu Salama ta ce: “Ni ma ina tare da su ya Annabin Allah?” Sai ya ce: “Ke kina nan a kan matsayinki, kina kuma tattare da alheri.” [Tirmizi #3205].

  35. إِنَّ ٱلۡمُسۡلِمِينَ وَٱلۡمُسۡلِمَٰتِ وَٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ وَٱلۡقَٰنِتِينَ وَٱلۡقَٰنِتَٰتِ وَٱلصَّٰدِقِينَ وَٱلصَّٰدِقَٰتِ وَٱلصَّٰبِرِينَ وَٱلصَّٰبِرَٰتِ وَٱلۡخَٰشِعِينَ وَٱلۡخَٰشِعَٰتِ وَٱلۡمُتَصَدِّقِينَ وَٱلۡمُتَصَدِّقَٰتِ وَٱلصَّٰٓئِمِينَ وَٱلصَّٰٓئِمَٰتِ وَٱلۡحَٰفِظِينَ فُرُوجَهُمۡ وَٱلۡحَٰفِظَٰتِ وَٱلذَّٰكِرِينَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱلذَّٰكِرَٰتِ أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمٗا

    Open ayah 33:35

    Lalle Musulmi maza da Musulmi mata, da muminai maza da muminai mata, da masu biyayya maza da masu biyayya mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haƙuri maza da masu haƙuri mata, da masu ƙasƙantar da kai maza da masu ƙasƙantar da kai mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da maza masu kiyaye farjinsu da mata masu kiyaye farjinsu, da maza masu ambaton Allah da yawa da mata masu ambaton Allah (da yawa, dukkaninsu) Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da daidaiton jinsin maza da na mata dangane da bautar Allah da imani da shi da kuma aikata kyawawan ayyuka da cancantar samun kyakkyawan sakamako a lahira. Allah ya siffanta maza da mata da kyawawan siffofi goma, su ne: Na farko, Musulunci, watau miƙa wuya ga Allah ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi da barin abin da ya hana. Na biyu, imani, wanda yake nufin ƙudurce duk wani abu da Allah ya nemi Musulmi ya gaskata shi. Na uku, dawwama a kan biyayyar Allah cikin natsuwa. Na huɗu, gaskiya a cikin maganganu da ayyuka. Na biyar, haƙuri a kan ɗa’a ga Allah da guje wa abin da ya hana, da haƙuri a kan abin da Allah zai ƙaddara wa bawa marar daɗi. Na shida, ƙasƙantar da kai da tawalu’u ga Allah (Mai tsarki da daukaka). Na bakwai, sadaka da dukiya da taimaka wa mabuƙata. Na takwas, azumi wanda ya ƙunshi na farilla da na nafila. Na tara, kiyaye mutunci daga aukawa cikin laifin zina da abubuwan da suke jawowa a faɗa cikinta. Na goma, ambaton Allah da yawa da harsuna da zukata. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk waɗanda suka haɗa waɗannan siffofi to ya yi musu tanadin gafara da lada mai girma, watau gidan Aljanna.

  36. وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٖ وَلَا مُؤۡمِنَةٍ إِذَا قَضَى ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ أَمۡرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ ٱلۡخِيَرَةُ مِنۡ أَمۡرِهِمۡۗ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 33:36

    Bai kamata ga wani mumini ko wata mumina ba, idan Allah da Manzonsa suka yi hukunci a kan wani al’amari su zama suna da wani zaɓi game da al’amarinsu. Wanda kuwa ya saɓa wa Allah da Manzonsa, to haƙiƙa ya ɓata, bayyanannen ɓata.

  37. وَإِذۡ تَقُولُ لِلَّذِيٓ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ وَأَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِ أَمۡسِكۡ عَلَيۡكَ زَوۡجَكَ وَٱتَّقِ ٱللَّهَ وَتُخۡفِي فِي نَفۡسِكَ مَا ٱللَّهُ مُبۡدِيهِ وَتَخۡشَى ٱلنَّاسَ وَٱللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخۡشَىٰهُۖ فَلَمَّا قَضَىٰ زَيۡدٞ مِّنۡهَا وَطَرٗا زَوَّجۡنَٰكَهَا لِكَيۡ لَا يَكُونَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ حَرَجٞ فِيٓ أَزۡوَٰجِ أَدۡعِيَآئِهِمۡ إِذَا قَضَوۡاْ مِنۡهُنَّ وَطَرٗاۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ مَفۡعُولٗا

    Open ayah 33:37

    (Ka tuna) lokacin da kake ce wa wannan da Allah Ya yi wa ni’ima, kai ma ka yi masa ni’ima: “Riƙe matarka, kuma ka kiyaye dokokin Allah”, alhali kuwa kana ɓoyewa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kana kuma tsoron mutane, alhali kuma Allah ne Ya fi cancanta ka ji tsoron Sa; to lokacin da Zaidu ya gama buƙatarsa da ita (matarsa Zainab), Mun aurar maka ita, don saboda kada ya zama akwai ƙuntatawa ga muminai game da (auren) matan ‘ya’yansu na riƙo lokacin da suka gama bukata da su. Al’amarin Allah kuwa ya kasance abin zartarwa ne.

  38. مَّا كَانَ عَلَى ٱلنَّبِيِّ مِنۡ حَرَجٖ فِيمَا فَرَضَ ٱللَّهُ لَهُۥۖ سُنَّةَ ٱللَّهِ فِي ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلُۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ قَدَرٗا مَّقۡدُورًا

    Open ayah 33:38

    Babu wani laifi a kan Annabi game da abin da Allah Ya halatta masa; (wannan kuwa) Sunnar Allah ce ga waɗanda suka gabace ka (daga annabawa). Al’amarin Allah kuwa ya kasance mai tabbata ne ba makawa.

  39. ٱلَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَٰلَٰتِ ٱللَّهِ وَيَخۡشَوۡنَهُۥ وَلَا يَخۡشَوۡنَ أَحَدًا إِلَّا ٱللَّهَۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ حَسِيبٗا

    Open ayah 33:39

    Waɗanda suke isar da saƙon Allah suke kuma tsoron Sa, ba sa kuwa tsoron kowa sai Allah. Allah kuwa Ya isa Mai yin hisabi.

  40. مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا 

    Open ayah 33:40

    (Annabi) Muhammadu bai kasance uban ɗaya daga cikin mazajenku ba, sai dai (shi) ya kasance Manzon Allah ne kuma cikamakin annabawa. Allah kuma Ya kasance Masanin komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ba ya dacewa ga mumini namiji ko mace idan Allah da Manzonsa (ﷺ) sun yanke wani hukunci ya zamanto suna da wani zaɓi nasu na kansu; a kan su karɓi wannan hukunci ko su yi watsi da shi. Dole ne su yarda da abin da Allah da Manzonsa suka zartar ko da kuwa ya saɓa wa son zuciyarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana hukuncin wanda ya saɓa masa ko ya saɓa wa Manzonsa (ﷺ) da cewa ya ɓata ɓata mabayyani, domin ya saki hanyar da za ta kai shi ga samun yardar Allah, ya kama hanyar faɗawa cikin azabar wutar Jahannama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci ƙissar Zaidu ɗan Harisa (Allah ya kara masa yarda) da umarnin da ya yi wa Manzonsa (ﷺ) na auren matar Zaidu (Allah ya kara masa yarda) bayan ya sake ta. Dalilin saukar waɗannan ayoyi shi ne, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi nufin rushe wata al’ada ta jahiliyya ne dangane da ‘ya’yan riƙo waɗanda ba daidai suke da ‘ya’yan cikin mutum ba. Gabanin wannan hukunci da Allah ya zartar, Larabawa sun yarda da cewa idan mutum yana riƙon wani a matsayin ɗansa, to haramun ne a kansa ya auri matar da ya saki, domin a wurinsu kamar ya auri matar ɗan da ya haifa ne bayan ya sake ta. Annabi (ﷺ) ya riƙi Zaidu ɗan Harisa (Allah ya kara masa yarda) kamar ɗansa, har ma ana kiran sa Zaidu ɗan Muhammad, sai bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana a danganta kowa in ba ga mahaifinsa ba, shi ne aka dawo ana kiran sa da Zaidu ɗan Harisa (Allah ya kara masa yarda). Annabi (ﷺ) yana matuƙar ƙaunar Zaidu (Allah ya kara masa yarda), har ma ana kiran sa da ɗan lelen Manzon Allah. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya aura masa Zainab ‘yar Jahshi wadda ita kuma ‘yar gwaggon Manzon Allah ce Umaimatu ‘yar Abdulmuɗɗalib. Ya zauna da ita tsawon shekara guda, daga baya zamansu ya fara samun matsala, shi kuma Zaidu (Allah ya kara masa yarda) ya riƙa kawo ƙarar ta wajen Manzon Allah (ﷺ), shi kuma yana lallashin sa yana faɗa masa ya ji tsoron Allah ya riƙe matarsa. To da yake Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi nufin rushe waccan al’ada ta jahiliyya sai ya sanar da Manzonsa cewa Zaidu (Allah ya kara masa yarda) zai saki matarsa Zainab shi kuma zai aure ta bisa umarnin Allah. Wannan lamari ya yi wa Manzon Allah (ﷺ) girma a ransa ainun, domin tsoron abin da mutane za su riƙa faɗa na cewa ya auri matar ɗansa na riƙo. Don haka sai ya ɓoye wannan al’amari a zuciyarsa bai faɗa wa kowa ba, Allah kuwa ya nuna masa bai dace gare shi ya ji tsoron mutane ba, shi kaɗai ya kamata ya ji tsoro. Da zama ya ƙi yiwuwa tsakanin Zaidu da matarsa Zainab sai ya sake ta, Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ya aurar da ita ga Manzonsa (ﷺ). Daga wannan lokaci kuma Allah Ya rushe waccan al’adar ta jahiliyya, ya saukar da waɗannan ayoyi yana umartar Annabi (ﷺ) ya tuna sanda yake umartar Zaidu wanda Allah ya yi masa ni’imar Musulunci da imani da biyayya ga Manzonsa (ﷺ), shi kuma ya yi masa ni’imar ‘yanta shi daga bauta, Annabi kuma yake umartar sa da ya riƙe matarsa Zainab, ya ji tsoron Allah ta hanyar bin umarninsa da barin abin da ya hana shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zargi Annabi da cewa yana ɓoye wani abu a ransa, watau wahayin da Allah ya yi masa na auren Zainab da zai yi don jin tsoron mutane. Allah kuwa sai ya bayyana wannan lamari, don haka Allah ya kamata Annabi ya ji tsoro ba mutane ba. Yayin da zaman auren Zaidu da Zainab ya zo ƙarshe sai Allah ya aura masa ita, domin ya tabbatar babu wani laifi ga muminai su auri matan ‘ya’yansu na riƙo bayan sun sake su sun kammala iddarsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya daɗa tabbatar da cewa al’amarinsa abin zartarwa ne babu wanda ya isa ya hana faruwarsa. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lokacin da iddar Zainab ta ƙare, Annabi (ﷺ) ya ce wa Zaidu: ‘Ka je ka yi mata maganata.’ Sai Zaidu (Allah ya kara masa yarda) ya tafi ya same ta tana kwaɓin garinta, Zaidu ya ce: “Yayin da na gan ta sai ta yi mini kwarjini har na kasa ci gaba da kallon ta, saboda na ga Manzon Allah (ﷺ) ya yi maganar aurenta, don haka sai na juya mata baya na koma da baya-baya na ce: “Albishirinki Zainab, Manzon Allah (ﷺ) ya yi maganar aurenki.” Sai ta ce: ‘Ni ba abin da zan iya yi yanzu har sai na nemi zaɓin Ubangijina (watau ta yi istikhara ).’ Sai ta tsaya a wurin sallarta ta yi salla ta yi addu’a. Sai Alƙur’ani ya sauko. Annabi (ﷺ) ya zo ya shiga wurinta ba tare da ya nemi izinin shiga ba....” [Muslim #1428]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Zainab ‘yar Jahshi ta kasance tana yi wa matan Annabi (ﷺ) alfahari da cewa: ‘Dukkanku iyayenku ne suka aurar da ku, ni kuwa Allah ne ya aurar da ni daga can saman sammai bakwai.’” [Bukhari #4721]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzo (ﷺ) cewa ba wani laifi da zai samu ko takuruwa game da auren abin da Allah ya halatta masa ya aura wadda ɗan riƙonsa ya taɓa aura ya saki, domin a wajen aiki da umarnin Allah ba shi ne farau ba, annabawa da suka gabace shi haka su ma suka yi. Wannan kuwa wani al’amari ne da Allah ya riga ya ƙaddara sai ya faru, saboda ba zaɓin Ma’aiki ne ba ko ra’ayinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffofin waɗannan manzanni da suka gabata da cewa su ne masu isar da saƙonnin da Allah ya aiko su da su zuwa ga al\'ummunsu, kuma ba sa tsoron kowa sai Allah, don haka ba sa waiwayen abin da mutane suke faɗa yayin da suke aikata abin da Allah ya halatta musu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi kaɗai ya isa ya kiyaye ayyukan bayinsa, domin ya yi musu hisabi a kansu, ya saka wa kowa gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna. Daga nan kuma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dangantakar Manzonsa (ﷺ) da matsayinsa a cikin al’ummarsa da cewa, shi Annabi Muhammadu (ﷺ) bai kasance uban ɗaya daga cikin mazajen wannan al’umma ba, don haka ba shi ne mahaifin Zaidu ba ballantana auren matar da Zaidu ya saka ya haramta a gare shi. Sai dai matsayinsa a cikin wannan al’umma shi Manzon Allah ne zuwa ga mutane gaba ɗaya, kuma cikamakin annabawa, babu wani annabi da zai zo a bayansa, kuma Allah masanin komai ne. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Banu Isra’ila sun kasance annabawansu ne suke shugabantar su, duk sanda wani annabi ya rasu sai wani annabin ya maye gurbinsa, amma lalle ni babu wani annabi a bayana.” [Bukhari #3455 da Muslim #1842]. An karɓo daga Sauban (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle za a yi wasu manyan maƙaryata talatin a cikin al’ummata kowannensu yana riya cewa lalle shi annabi ne, to kuma ni ne cikamakin annabawa, a bayana babu wani annabi da zai zo....” [Abu Dawud #4252 da Tirmizi #2219]. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya faɗa wa Ali cewa: “Kai matsayinka a wurina kamar matsayin Haruna ne a wurin Musa, sai dai ni babu wani annabi a bayana.” [Tirmizi #3730].

  41. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ ذِكۡرٗا كَثِيرٗا

    Open ayah 33:41

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa.

  42. وَسَبِّحُوهُ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلًا

    Open ayah 33:42

    Kuma ku yi tasbihi a gare Shi safe da yamma.

  43. هُوَ ٱلَّذِي يُصَلِّي عَلَيۡكُمۡ وَمَلَٰٓئِكَتُهُۥ لِيُخۡرِجَكُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَكَانَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ رَحِيمٗا

    Open ayah 33:43

    Shi ne wanda Yake yi muku salati da mala’ikunsa don Ya fitar da ku daga duffai zuwa haske, Allah kuwa Ya kasance Mai rahama ga muminai.

  44. تَحِيَّتُهُمۡ يَوۡمَ يَلۡقَوۡنَهُۥ سَلَٰمٞۚ وَأَعَدَّ لَهُمۡ أَجۡرٗا كَرِيمٗا

    Open ayah 33:44

    Gaisuwarsu a ranar da za su haɗu da Shi (ita ce) ‘Salamun Alaikum ’. Ya kuma tanadar musu da lada na karamci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su yawaita ambaton Allah da harsunansu da zukatansu da gaɓoɓinsu, su kuma tsarkake shi daga dukkan tawaya da aibi ta hanyar yin tasbihi da hailala safe da yamma. An karɓo daga Abud-Darda (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yanzu ba na faɗa muku mafi alherin ayyukanku ba, mafi tsarkakarsu a wurin mamallakinku (Allah), mafi ɗaukakawa ga darajojinku, mafi alheri a kan bayar da sadakar zinari da azurfa, mafi alheri a kan ku haɗu da maƙiyanku ku sari wuyayensu su ma su sari wuyayenku?” Sahabbai suka ce: “Mene ne wannan aikin ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Ambaton Allah mai girma da buwaya.” [Ahmad #21702 da Tirmizi #3377]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Busur (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Ya Manzon Allah, hukunce-hukuncen Musulunci sun yi mini yawa, ka umarce ni da wani abu da zan ƙanƙame shi.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Kada harshenka ya gushe yana ɗanye shatab da ambaton Allah.” [Ahmad #17680 da 2329]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wata rahama da falala da ya yi wa muminai, da cewa shi ne yake yi musu salati, watau yake yin rahama da yabo gare su. Mala’ikunsa ma suna yi musu addu’a da nema musu gafarar Allah, domin Allah ya fitar da su daga duffan kafirci zuwa hasken imani. Allah ya tabbatar wa muminai cewa, shi mai rahama ne a gare su, don haka ba zai yi musu azaba ba idan har sun yi masa ɗa’a, sun yi aiki da umarninsa. Sannan ya bayyana rahamarsa gare su a lahira yayin da zai shigar da su Aljanna; gaisuwarsu a ranar da za su haɗu da Ubangijinsu kuma ita ce ‘Salamun Alaikum ’, watau samun aminci da kuɓuta daga duk wani abin ƙi. Kuma Allah ya tanadar musu wani lada mai karamci, wannan sakamako ne a kan biyayyar da suka yi gare shi da nisantar saɓa masa.

  45. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ شَٰهِدٗا وَمُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

    Open ayah 33:45

    Ya kai wannan Annabi, lalle Mu Mun aiko ka kana mai shaida, kuma mai albishir kuma mai gargaɗi.

  46. وَدَاعِيًا إِلَى ٱللَّهِ بِإِذۡنِهِۦ وَسِرَاجٗا مُّنِيرٗا

    Open ayah 33:46

    Kuma mai kira zuwa ga Allah da izininsa, kuma fitila mai haskakawa.

  47. وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ بِأَنَّ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ فَضۡلٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 33:47

    Ka kuma yi wa muminai albishir cewa, suna da wata falala mai girma daga wurin Allah.

  48. وَلَا تُطِعِ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَدَعۡ أَذَىٰهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا

    Open ayah 33:48

    Kada kuma ka yi wa kafirai da munafukai ɗa\'a, ka kuma bar cutarsu (da suke yi maka), ka kuma dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa Ya zama abin dogara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira Annabi (ﷺ) ya tunatar da shi nauyin da ya ɗora masa na manzanci zuwa ga mutane baki ɗaya, don ya zama mai shaida a kansu game da saƙon da ya isar musu, mai albishir ga muminai da tanadin da Allah ya yi musu na gidan Aljanna, mai kuma tsoratar da kafirai game da wuta wadda aka tanade ta domin waɗanda suka kafirce wa Allah da manzanninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa ya aiko shi don ya zama mai kira zuwa ga kaɗaita Allah da bauta da izininsa, ya kuma zama fitila mai haske da za ta haskaka wa mutane hanyar shiriya. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wallahi an siffanta Annabi Muhammadu (ﷺ) a Attaura da wasu siffofinsa da suka zo a Alƙur’ani, an kirawo shi: ‘Ya kai wannan Annabi, lalle mu mun aiko ka don ka zama mai shaida mai albishir kuma mai gargaɗi, ka zamo kariya ga Larabawa ummiyyai. Kai bawana ne kuma manzona, na raɗa maka suna Al-Mutawakkilu (watau mai dogaro ga Allah).’ Shi ba mai kakkausan hali ba ne, ba mai ƙeƙasasshiyar zuciya ba, ba mai hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mugunta da mugunta, sai dai ya yi afuwa, ya yi gafara. Allah ba zai karɓi ransa ba har sai ya miƙar da karkataccen addini da shi, watau su ce: [Babu abin bauta da gaskiya sai Allah], ya kuma buɗe makafin idanuwa da kuramen kunnuwa da rufaffun zukata da wannan Kalma ta Shahada.” [Bukhari #4838]. Allah kuma ya umarce shi da ya faɗa wa muminai waɗanda suka yi imani da Allah suka kuma yi kyawawan ayyuka, ya kuma yi musu albishir cewa suna da wata falala daga Allah mai girma wadda ta ƙunshi samun nasara a nan duniya da rabauta da gidan Aljanna a lahira. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi Manzonsa (ﷺ) a kan kada ya biye wa ta kafirai da munafukai game da abin da suke buƙata wanda ya saɓa wa shari’a, ya kuma umarce shi da ya kau da kansa daga gare su, wataƙila yin haka ya sanya su yi imani da abin da ya zo musu da shi na Musulunci. Ya kuma dogara ga Allah a cikin dukkan al’amuransa don Allah ya ba shi nasara a kan abokan gabarsa. Ya tabbatar masa cewa ya isa ya zama abin dogaro ga bayinsa cikin duk al’amuransu na duniya da na lahira.

  49. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نَكَحۡتُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمۡ عَلَيۡهِنَّ مِنۡ عِدَّةٖ تَعۡتَدُّونَهَاۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحٗا جَمِيلٗا

    Open ayah 33:49

    Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka auri mata muminai, sannan kuka sake su tun kafin ku sadu da su, to babu wata idda taku a kansu da za ku nemi cikar adadin (kwanakinta); to ku jiyar da su daɗi, kuma ku sake su kyakkyawan saki. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai wani hukunci ne da ya shafi aure da saki da iddar mata, watau idan sun auri muminai mata sai suka sake su tun kafin su sadu da su, to waɗannan mata babu idda a kansu da za su yi wa waɗannan mazaje da suka sake su; suna iya yin aurensu duk sanda suka ga dama. Wannan hukunci bai shafi matar da mijinta ya mutu ba bayan an ɗaura musu aure bai sadu da ita ba; ita wannan malamai sun haɗu a kan cewa za ta yi masa iddar takaba, watau zaman wata huɗu da kwana goma kafin ta yi wani aure. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mazajen da su ba su abin da zai daɗaɗa musu rai don su rage musu raɗaɗin sakin da aka yi musu, sannan su ƙyale su su koma ga iyayensu ba tare da sun cutar da su ba. An karɓo daga Sahal ɗan Sa’ad da Abu Usaid (Allah ya kara masa yarda) cewa: “Lalle Annabi (ﷺ) ya auri Umaimatu ‘yar Shurahilu, da ya shiga wurinta ya miƙa hannunsa gare ta sai ta nuna masa ba ta so, sai ya umarci Abu Usaid da ya shirya mata kayanta, ya kuma ba ta rigunan sawa biyu na farin kittani, (ya mayar da ita wurin iyayenta)”. [Bukhari #5256].

  50. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِنَّآ أَحۡلَلۡنَا لَكَ أَزۡوَٰجَكَ ٱلَّٰتِيٓ ءَاتَيۡتَ أُجُورَهُنَّ وَمَا مَلَكَتۡ يَمِينُكَ مِمَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَيۡكَ وَبَنَاتِ عَمِّكَ وَبَنَاتِ عَمَّٰتِكَ وَبَنَاتِ خَالِكَ وَبَنَاتِ خَٰلَٰتِكَ ٱلَّٰتِي هَاجَرۡنَ مَعَكَ وَٱمۡرَأَةٗ مُّؤۡمِنَةً إِن وَهَبَتۡ نَفۡسَهَا لِلنَّبِيِّ إِنۡ أَرَادَ ٱلنَّبِيُّ أَن يَسۡتَنكِحَهَا خَالِصَةٗ لَّكَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۗ قَدۡ عَلِمۡنَا مَا فَرَضۡنَا عَلَيۡهِمۡ فِيٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ وَمَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ لِكَيۡلَا يَكُونَ عَلَيۡكَ حَرَجٞۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا 

    Open ayah 33:50

    Ya kai wannan Annabi, lalle Mun halatta maka matanka waɗanda ka ba da sadakinsu, da kuma kuyanginka daga abin da Allah Ya ba ka na ganima, da ‘ya’yan baffanka mata da ‘ya’yan gwaggwaninka mata da ‘ya’yan kawunka mata, da ‘ya’yan yagwalgwalanka mata waɗanda suka yi hijira tare da kai, da kuma duk wata mace mumina, idan ta ba da kanta ga Annabi (shi) Annabin kuwa yana nufin ya aure ta, (wannan) keɓantacce ne a gare ka, ban da sauran muminai. Haƙiƙa Mun san abin da Muka ɗora musu game da matansu da kuma kuyanginsu, don kada a samu wata ƙuntatawa a kanka. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Annabinsa (ﷺ) nau’in matan da ya halatta masa ya aura da ƙwaraƙwarai da suka halatta a gare shi. A cikin abubuwan da aka yi bayani akwai waɗanda sauran muminai suka yi tarayya da shi a cikinsu, akwai kuma abin da shi kaɗai ya keɓanta da shi. Allah ya fara da cewa, ya halatta masa auren matansa waɗanda ya ba su sadakinsu. Wannan ya shafi duk wani Musulmi, yana iya auren wadda ya biya sadakinta. Sannan da ƙwaraƙwaran da ya mallaka yana iya saɗaka da su idan yana so. Wannan ma sauran muminai sun yi tarayya da shi a ciki, watau su ma suna iya yin saɗaka da kuyanginsu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa ya halatta masa auren ‘ya’yan baffanninsa maza da na gwaggwanninsa mata da ‘ya’yan kawunnansa maza da na innoninsa mata waɗanda suka yi hijira zuwa Madina tare da shi. Sauran muminai ma sun yi tarayya da shi a wannan hukunci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa, ya halatta masa auren duk wata mace mumina wadda za ta ba da kanta kyauta gare shi, idan yana son aurenta to zai iya auren ta ba tare da sadaki ko waliyyi ko shaidu ba. Wannan hukunci ya keɓanta da shi ne shi kaɗai ban da sauran muminai, su kam dole ne aurensu sai da sadaki da waliyyi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya san abin da ya wajabta wa muminai game da adadin matan da kowannensu ya halatta ya aura, watau ya ƙayyade musu auren iya mata huɗu kada su wuce su. Ya kuma san abin da ya shar’anta musu dangane da kuyanginsu, za su iya saɗaka da ko guda nawa ne ba tare da ƙayyadewar adadi ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa dalilin da ya sanya ya halatta masa abubuwan da ya ambata, watau ya yi haka ne don kada ya ƙuntata masa ko ya wahalar da shi, Allah kuma ya tabbata mai gafara ne ga wanda ya tuba daga cikin bayinsa, mai rahama ne gare su.

  51. ۞تُرۡجِي مَن تَشَآءُ مِنۡهُنَّ وَتُـٔۡوِيٓ إِلَيۡكَ مَن تَشَآءُۖ وَمَنِ ٱبۡتَغَيۡتَ مِمَّنۡ عَزَلۡتَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكَۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن تَقَرَّ أَعۡيُنُهُنَّ وَلَا يَحۡزَنَّ وَيَرۡضَيۡنَ بِمَآ ءَاتَيۡتَهُنَّ كُلُّهُنَّۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا فِي قُلُوبِكُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَلِيمٗا

    Open ayah 33:51

    Ka dakatar da duk wadda ka ga dama daga cikinsu, ka kuma jawo duk wadda ka ga dama; (duk) wadda kuwa ka nema daga waɗanda ka dakatar, to babu wani laifi a kanka. (Yin) wannan kuwa shi ya fi kusantar da kwanciyar ransu da kuma rashin yin baƙin ciki, su kuma yarda da duk abin da ka ba su dukkaninsu. Allah kuwa Yana sane da abin da yake cikin zukatanku. Allah kuwa Ya kasance Masani ne, Mai haƙuri. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya keɓance Annabi (ﷺ) da wani hukunci dangane da zamantakewarsa ta aure da matansa, watau ya ba shi damar ya gudanar da mu’amalar aure da su ba tare da wajabta masa rabon kwana a tsakanninsu ba, kamar yadda ya wajabta wa al’ummarsa. Ya halatta masa ya dakatar da kwanan wadda ya ga dama daga cikin matansa, ya jawo wadda ya ga dama; idan kuma ya so ya jawo kwanan wadda ya dakatar to yana iya yin hakan babu wani laifi a kansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ba shi wannan zaɓi ne don shi ne zai kwantar wa matansa hankali, kuma su yarda da abin da ya ba wa kowace ɗaya daga cikinsu, domin sun tabbatar ba zai hana musu haƙƙoƙinsu ba ko ya ƙi yi musu adalci. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara masa yarda) ta ce: “Bayan wannan ayar ta (51) ta sauka, Annabi (ﷺ) ya kasance yana neman izinin ɗaya daga cikinmu a ranar kwananta (watau ta bar wa ‘yar’uwarta).” Sai Mu’azatu ta tambayi A’isha cewa: “To ke me kike faɗa masa?” Sai ta ce: “Nakan ce masa: Ni ba zan so in fifita wata a kaina dangane da kai ba, ya Manzon Allah.” [Bukhari #4789]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya san abin da yake cikin zukatan mazaje na karkata ga wasu matan su bar wasu, domin ya san abin da yake cikin zukatan bayinsa, shi kuma mai haƙuri ne ba ya gaggauto da uƙuba ga wanda ya saɓa masa, yakan ba shi damar tuba domin ya yafe masa.

  52. لَّا يَحِلُّ لَكَ ٱلنِّسَآءُ مِنۢ بَعۡدُ وَلَآ أَن تَبَدَّلَ بِهِنَّ مِنۡ أَزۡوَٰجٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَكَ حُسۡنُهُنَّ إِلَّا مَا مَلَكَتۡ يَمِينُكَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ رَّقِيبٗا

    Open ayah 33:52

    Bayan (waɗannan) wasu mata ba su halatta gare ka ba, ko kuma ka musanya waɗansu (matan) da su, ko da kuwa kyansu ya ƙayatar da kai, sai dai abin da ka mallaka na kuyangi. Allah kuwa Ya kasance Mai lura ne da komai. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tagomashin da ya yi wa matan Manzon Allah (ﷺ) bayan an ba su zaɓi tsakanin zama da shi da kuma ƙyale-ƙyalen duniya, sun zaɓi Allah da Manzonsa da gidan lahira. To sai Allah ya faɗa wa Manzo (ﷺ) cewa bai halatta ba gare shi ya sake auren wasu mata ban da waɗannan da suke tare da shi, kuma bai halatta ya saki wasu daga cikinsu ba domin ya auro wasu matan ya cike gurbi da su, ko da kuwa ya ga wadda kyanta ya ƙayatar da shi ya yi nufin auren ta, Allah bai ba shi izini ba. Amma ya halatta gare shi ya riƙi ƙwaraƙwarai daga cikin kuyangin da yake mallaka ba tare da an ƙayyade masa wani adadi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi mai lura ne da komai.

  53. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتَ ٱلنَّبِيِّ إِلَّآ أَن يُؤۡذَنَ لَكُمۡ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيۡرَ نَٰظِرِينَ إِنَىٰهُ وَلَٰكِنۡ إِذَا دُعِيتُمۡ فَٱدۡخُلُواْ فَإِذَا طَعِمۡتُمۡ فَٱنتَشِرُواْ وَلَا مُسۡتَـٔۡنِسِينَ لِحَدِيثٍۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ يُؤۡذِي ٱلنَّبِيَّ فَيَسۡتَحۡيِۦ مِنكُمۡۖ وَٱللَّهُ لَا يَسۡتَحۡيِۦ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ وَإِذَا سَأَلۡتُمُوهُنَّ مَتَٰعٗا فَسۡـَٔلُوهُنَّ مِن وَرَآءِ حِجَابٖۚ ذَٰلِكُمۡ أَطۡهَرُ لِقُلُوبِكُمۡ وَقُلُوبِهِنَّۚ وَمَا كَانَ لَكُمۡ أَن تُؤۡذُواْ رَسُولَ ٱللَّهِ وَلَآ أَن تَنكِحُوٓاْ أَزۡوَٰجَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦٓ أَبَدًاۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمًا

    Open ayah 33:53

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen Annabi sai idan an yi muku izini zuwa (cin) abinci, alhali ba tare da kuna jiran dahuwarsa ba, sai dai kuma idan aka kira ku, to ku shiga, sannan idan kuka ci sai ku fice, ba tare da yin wata hira ta ɗebe kewa ba. Lalle wannan ya kasance yana cutar Annabi, sai yakan ji kunyar ku; Allah kuwa ba Ya jin kunyar (faɗar) gaskiya. Idan kuma za ku tambaye su (wato matan Annabi) wani abu na amfani, sai ku tambaye su ta bayan shamaki. Yin wannan shi ya fi tsarki ga zukatanku da kuma zukatansu. Kuma bai kamace ku ba ku cuci Manzon Allah ko kuma ku auri matansa a bayansa har abada. Lalle (yin) wannan ya kasance abu mai girma a wurin Allah.

  54. إِن تُبۡدُواْ شَيۡـًٔا أَوۡ تُخۡفُوهُ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا

    Open ayah 33:54

    Idan kuma kuka bayyana wani abu ko kuka ɓoye shi, to Allah Ya kasance Masanin komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana koya wa muminai ladabin shiga gidan Manzon Allah da kuma ladabin da za su yi wurin magana da matansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana su shiga gidan Manzon Allah (ﷺ) sai bayan an yi musu izinin shiga domin su ci abinci, ya kuma hana su zama suna jiran dahuwar abincin. Amma idan Manzon Allah (ﷺ) ne ya kirawo su cin abinci a gidansa to suna iya shiga, kuma da zarar sun gama cin abinci sai su watse kowa ya kama gabansa, kada su zauna su dasa hirar daɓe ko da a tsakaninsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana dalilin wannan hani da ya yi musu da cewa zamansu su daɗe a gidansa suna jiran dahuwar abinci, ko bayan sun ci su zauna suna hira, al’amari ne da yake cutar da Annabi (ﷺ), domin yana hana shi walwala da sakewa a gidansa tare da iyalansa, shi kuma yana jin kunyar ya yi magana a kai, Allah kuwa ba ya jin kunyar faɗar gaskiya ga kowane ne. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lokacin da Annabi (ﷺ) ya auri Zainab ‘yar Jahshi, ya gayyaci mutane ya shirya musu abinci suka ci, to bayan sun gama sai suka zauna suna ta hira, sai Annabi (ﷺ) ya yunƙura kamar zai tashi don su gani su ma su tashi, amma sai suka ƙi tashi. Lokacin da ya ga haka sai shi ya tashi, to ganin haka sai wasu daga cikinsu suka tashi suka fita, amma sai mutum uku suka ci gaba da zama suna hira, sai Annabi (ﷺ) ya zo don ya shiga wurin matarsa Zainab sai ya sami waɗannan mutane zaune suna ta hira, (sai ya koma) sannan su kuma suka tashi suka fita. Sai na je na faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa mutanen nan fa sun tafi, sai ya zo ya shiga wurin matarsa, ya saki shamaki tsakanina da shi, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da wannan ayar.” [Bukhari #4791 da Muslim #1428]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya koya wa muminai yadda za su yi magana da matan Annabi (ﷺ) idan za su buƙaci wani abin a wurinsu, da cewa, idan suna buƙatar wani abin amfani a wurinsu to su tambaye su ta bayan shamaki, kada su nemi ganin su ido-da-ido, don tsare mutuncin Annabi (ﷺ). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa dalilin kafa musu wannan doka shi ne su sami tsarkin zuciya su da matan gaba ɗaya, don haka Shaiɗan ba zai sami wata kafa ya sanya wani mummunan wasiwasi a zukatansu ba. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Umar ya ce wa Annabi (ﷺ): “Ya Manzon Allah, muminan ƙwarai da waɗanda ba na ƙwarai ba duk suna shiga gidanka, da a ce ka umarci (matanka) iyayen muminai su sanya shamaki, (watau tsakaninsu da maza).” sai wannan ayar ta sauka.” [Bukhari #4790]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa bai kamace su ba ko kaɗan su riƙa aikata abin da zai cutar da Annabi (ﷺ), kamar daɗewa a gidansa suna hira. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haramta musu auren matansa (ﷺ) bayan rasuwarsa, domin su matansa ne na Aljanna, sannan iyayen muminai ne, mutum kuwa ba zai auri uwarsa ba. Allah ya ƙara tabbatar musu da cewa cutar da Annabi (ﷺ) ko auren wata daga cikin matansa bayan rasuwarsa babban lamari ne a wurin Allah, domin zunubinsa yana da girma ainun. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi bayinsa da cewa, duk abin da suka bayyana na ayyukansu ko suka ɓoye a zukatansu, to Allah masanin komai ne, babu abin da zai ɓuya a wajensa, zai kuma yi musu sakayya a kai.

  55. لَّا جُنَاحَ عَلَيۡهِنَّ فِيٓ ءَابَآئِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآئِهِنَّ وَلَآ إِخۡوَٰنِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآءِ إِخۡوَٰنِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآءِ أَخَوَٰتِهِنَّ وَلَا نِسَآئِهِنَّ وَلَا مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّۗ وَٱتَّقِينَ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدًا

    Open ayah 33:55

    Babu laifi a kansu (matan) game da iyayensu maza (su gan su kuma su yi magana da su ba tare da shamaki ba) da kuma ‘ya’yansu maza da ‘ya’uwansu da ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza da ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata, da kuma matansu da bayinsu. Ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Ya kasance Mai ganin komai ne. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai mata waɗanda za su iya magana da su ba tare da wani shamaki a tsakaninsu ba da cewa, babu laifi ga iyayensu maza su gan su ko su yi magana da su, hakanan ‘ya’yansu maza da ‘yan’uwansu maza da ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza da ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata waɗanda suka haɗa dangantaka da su ta haihuwa ko ta shayarwa, da mata muminai ‘yan’uwansu, da bayinsu maza waɗanda suka mallake su cikakkiyar mallaka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su kiyaye dokokin Allah a koyaushe a kuma kowane hali, domin shi mai ganin duk ayyukansu ne na sarari da na ɓoye, zai kuma yi musu sakayya a kansu.

  56. إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِيِّۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ صَلُّواْ عَلَيۡهِ وَسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا

    Open ayah 33:56

    Lalle Allah da mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama mai yawa. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman darajar Manzonsa (ﷺ) a wajensa da sauran mala’ikunsa, da cewa shi kansa Allah yana yi masa salati, watau yana yabon sa a cikin mala’ikunsa domin ƙaunar sa da yake yi, hakanan su ma mala’iku duka suna yi wa Manzon Allah (ﷺ) salati, watau suna yi masa kyakkyawar addu’a da roƙa masa ƙarin daraja a wurin Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su ma su yi masa salati da sallama mai yawa, domin koyi da Allah da mala’ikunsa, su kuma ba shi wani ɓangare na haƙƙinsa a kansu. An karɓo daga Ka’abu ɗan Ujra (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Sahabbai sun ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Ya Manzon Allah, mun san yadda za mu yi maka sallama, to amma yaya za mu yi maka salati?” Sai ya ce: “Ku ce: “Ya Allah ka yi salati ga Muhammadu da iyalan Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga iyalan Ibrahimu, lalle kai sha yabo ne mai girma. Ya Allah ka yi wa Muhammadu albarka da iyalan Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga iyalan Ibrahimu, lalle kai sha yabo ne mai girma.” [Bukhari #4797]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya yi mini salati ɗaya, to Allah zai yi masa salati goma.” [Muslim #408].

  57. إِنَّ ٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَأَعَدَّ لَهُمۡ عَذَابٗا مُّهِينٗا

    Open ayah 33:57

    Lalle waɗanda suke cutar Allah da Manzonsa, to Allah Ya la’ance su a duniya da lahira, Ya kuma tanadar musu azaba mai wulaƙantarwa.

  58. وَٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ بِغَيۡرِ مَا ٱكۡتَسَبُواْ فَقَدِ ٱحۡتَمَلُواْ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا

    Open ayah 33:58

    Waɗanda suke cutar muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi laifi ba, to haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage da kuma zunubi bayyananne. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman martabar Annabi (ﷺ) sai kuma ya yi gargaɗi mai tsanani ga waɗanda suke cutar da shi da miyagun maganganunsu ko da ayyukansu, da cewa lalle waɗanda suke cutar da Allah da Manzonsa (ﷺ), to ya la’ance su a duniya da lahira, watau ba su babu samun rahamarsa, ya kuma tanadar musu azabar wulaƙanci a lahira. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su ma masu cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi musu wani laifi ba, to su sani cewa sun ɗaukar wa kansu laifin wani ƙage da zunubi bayyananne. An karɓo daga Sa’idu ɗan Zaid (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mafi munin riba, mutum ya ci mutuncin ɗan’uwansa Musulmi ba tare da wani haƙƙi ba.” [As-Shashi, Al-Musnad #208]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Shin ko kun san abin da ake ce wa giba (yi da mutum)?” Sai suka ce: “Allah da Manzonsa ne suka fi sani.” Sai ya ce: “Ka ambaci ɗan’uwanka da abin da yake ƙi.” Sai aka ce: “Idan yana da abin da muke faɗa fa?” Sai ya ce: “Idan yana da abin da kake faɗa a kansa, to ka yi gibar sa, idan kuwa ba ya da shi, to ka yi masa ƙage.” [Muslim #2589].

  59. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَآءِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ يُدۡنِينَ عَلَيۡهِنَّ مِن جَلَٰبِيبِهِنَّۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن يُعۡرَفۡنَ فَلَا يُؤۡذَيۡنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

    Open ayah 33:59

    Ya kai wannan Annabi, faɗa wa matanka da ‘ya’yanka mata da kuma matan muminai (cewa) su sanya lulluɓinsu. Wannan shi ya fi sanya wa a gane su, don kada a cuce su. Allah kuma Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nemi Annabinsa (ﷺ) da ya umarci matansa da ‘ya’yansa mata da matan muminai su saki lulluɓinsu a jikinsu lokacin da suka fito daga gidajensu, domin a tantance tsakaninsu da mata marasa kamun kai, don kada a cutar da su kamar yadda akan yi wa marasa kamun kai. Allah ya tabbatar masa da cewa shi mai gafara ne ga bayinsa masu laifi idan sun tuba, mai jin ƙan su ne. An karɓo daga Ummu Salama (Allah ya kara masa yarda) ta ce: “Lokacin da wannan ayar ta sauka matan mutanen Madina sukan fita kai ka ce hankaku ne a kan kawunansu saboda nutsuwa, suna lulluɓe da baƙaƙen lulluɓi.” [Abu Dawud #410].

  60. ۞لَّئِن لَّمۡ يَنتَهِ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡمُرۡجِفُونَ فِي ٱلۡمَدِينَةِ لَنُغۡرِيَنَّكَ بِهِمۡ ثُمَّ لَا يُجَاوِرُونَكَ فِيهَآ إِلَّا قَلِيلٗا 

    Open ayah 33:60

    Tabbas munafukai da waɗanda suke da raunin imani a zukatansu da kuma masu yaɗa ƙarairayi a Madina, idan ba su bari ba, lalle za Mu cuna ka a kansu (don ka hukunta su), sannan kuma ba za su zauna da kai a cikinta ba sai ɗan lokaci ƙanƙani.

  61. مَّلۡعُونِينَۖ أَيۡنَمَا ثُقِفُوٓاْ أُخِذُواْ وَقُتِّلُواْ تَقۡتِيلٗا

    Open ayah 33:61

    (Su) la’anannu ne; duk inda aka gamu da su a kama su, kuma a yi musu mummunan kisa.

  62. سُنَّةَ ٱللَّهِ فِي ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلُۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّةِ ٱللَّهِ تَبۡدِيلٗا

    Open ayah 33:62

    (Wannan) Sunnar Allah ce ga waɗanda suka gabata a da; ba kuma za ka sami wani canji ba game da sunnar Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi munafukai waɗanda suke cike da hassada da ƙiyayya ga muminai, da waɗanda zukatansu suke ɗauke da cutar sha’awa da waɗanda suke baza labaran ƙarya a Madina don su raba kan muminai, Allah ya ja kunnuwansu da cewa idan ba su daina miyagun halayensu ba, to lalle zai umarci Annabi (ﷺ) da ya hukunta su, zai kuma ɗora shi a kansu har ya fi ƙarfinsu. Daga wannan ranar kuwa zaman garin Madina zai yi musu wuya sai na ɗan lokaci kaɗan, domin za a kore su daga wannan gari saboda yawaitar ɓarnarsu da sharrinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa su la’anannu ne waɗanda ba su ba rahamar Allah, kuma duk inda aka gamu da su sai a kama su a yi musu mummunan kisa saboda munafuncinsu da yaɗa ɓarna da suke yi a bayan ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan sunnarsa ce mai gudana a kan munafukai duk sanda suka bayyana munafuncinsu a fili, sunnar Allah kuwa tabbatacciya ce ba za ka sami wani canji ba game da ita.

  63. يَسۡـَٔلُكَ ٱلنَّاسُ عَنِ ٱلسَّاعَةِۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ ٱللَّهِۚ وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّ ٱلسَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبًا

    Open ayah 33:63

    Mutane suna tambayar ka game da (ranar) alƙiyama; ka ce (da su): “Saninta a wajen Allah kawai yake.” Ba ka sani ba ko watakila alƙiyamar za ta kasance kusa.

  64. إِنَّ ٱللَّهَ لَعَنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمۡ سَعِيرًا

    Open ayah 33:64

    Lalle Allah Ya la’anci kafirai Ya kuma tanadar musu da (wutar) Sa’ira.

  65. خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّا يَجِدُونَ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

    Open ayah 33:65

    Masu dawwama ne a cikinta har abada; ba kuma za su sami wani majiɓinci ko mataimaki ba.

  66. يَوۡمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ يَقُولُونَ يَٰلَيۡتَنَآ أَطَعۡنَا ٱللَّهَ وَأَطَعۡنَا ٱلرَّسُولَا۠

    Open ayah 33:66

    A ranar da za a riƙa jujjuya fuskokinsu cikin wuta, suna cewa: “Kaiconmu, ina ma da mun bi Allah mun bi Manzo!”

  67. وَقَالُواْ رَبَّنَآ إِنَّآ أَطَعۡنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَآءَنَا فَأَضَلُّونَا ٱلسَّبِيلَا۠

    Open ayah 33:67

    Suka kuma ce: “Ya Ubangijinmu, lalle mu mun bi shugabanninmu da manyanmu sai suka ɓatar da mu hanya.

  68. رَبَّنَآ ءَاتِهِمۡ ضِعۡفَيۡنِ مِنَ ٱلۡعَذَابِ وَٱلۡعَنۡهُمۡ لَعۡنٗا كَبِيرٗا

    Open ayah 33:68

    “Ya Ubangijinmu, Ka ba su azaba riɓi biyu, Ka kuma la’ance su babbar la’ana.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai sun riƙa yi wa Annabi (ﷺ) tambayar cewa ya faɗa musu yaushe ne ranar alƙiyama za ta zo, domin su nuna cewa ƙarya yake yi da ya ce akwai ranar alƙiyama. Su ma Yahudawa sun matsa wa Annabi lamba kan sai ya faɗa musu lokacin, don kawai su ce sun ƙure shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya faɗa musu cewa, shi ba shi da wata masaniya game da lokacin zuwanta, wannan ilimi yana ga Allah shi kaɗai, shi ya bar wa kansa sani, kuma tana yiwuwa ma alƙiyamar ta kusa zuwa. Sannan Allah ya la’anci kafirai, ya nesanta su daga rahamarsa, ya kuma yi musu tanadin wutar Jahannama mai tsananin ƙuna a lahira wadda za su dawwama har abada a cikinta kuma ba za su sami wani majiɓinci ko mataimaki ba wanda zai fito da su daga wannan mummunar azabar. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mawuyacin halin da za su shiga a wannan ranar, domin a nan za a riƙa jujjuya fuskokinsu a cikin wuta kamar ana dahuwar nama a cikin tukunya, su kuma suna ta ihu suna nadama, suna cewa ina ma dai sun bi Allah sun aikata abin da ya umarce su, sun guje wa abin da ya hane su, kuma sun bi Manzon Allah a kan abin da ya zo musu da shi daga Allah. Daga nan sai su fara neman hujjar da za su ba wa Allah don ya tserar da su daga wannan azaba da suke ciki, to amma hujjar da suka kawo mai matuƙar rauni ce, domin cewa suke yi su fa sun bi shugabanninsu ne da manyansu sai suka jefa su cikin ɓata. Don haka sai su roƙi Allah ya azabtar da shugabanninsu ninki biyu, watau azabar ɓatan da suka yi da kuma ɓatar da wasu da suka yi, kuma ya la’ance su ya nesanta su daga rahamarsa la’ana mai girma.

  69. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ ءَاذَوۡاْ مُوسَىٰ فَبَرَّأَهُ ٱللَّهُ مِمَّا قَالُواْۚ وَكَانَ عِندَ ٱللَّهِ وَجِيهٗا

    Open ayah 33:69

    Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku zamanto kamar waɗanda suka cuci Musa sai Allah Ya wanke shi daga abin da suka faɗa (a kansa). Ya kuma kasance mai alfarma ne a wurin Allah. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira muminai ya gargaɗe su da kada su yi koyi da Yahudawa waɗanda suka riƙa cutar da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da yi masa miyagun maganganu iri-iri, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wanke shi daga aibata shi da suka yi, domin ya kasance mai daraja ne a wurinsa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Banu Isra’ila sun kasance suna taruwa suna yin wanka tsirara suna kallon junansu, amma shi Musa sai ya zamanto yana yin wankansa shi kaɗai. Sai suka ce: ‘Babu abin da yake hana shi wanka tare da mu sai don yana da gwaiwa.” Sai wata rana ya tafi yana wanka, ya ɗora tufafinsa a kan wani dutse, sai dutsen ya gudu da tufafinsa, sai Musa ya fita ya bi shi yana cewa: ‘Kai dutse tufafina! kai dutse tufafina!!.’ Yana cikin haka sai Banu Isra’ila suka gan shi, nan take suka ce: ‘Wallahi Musa ba ya da wata cuta tare da shi.’ Sai dutse ya tsaya Musa ya ɗauki tufafinsa sai ya riƙa dukan wannan dutsen.” [Bukhari #3404 da Muslim #339]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Annabi (ﷺ) ya yi wani rabo sai wani mutum ya ce: “Wannan rabon ba a nufi Allah da shi ba.” Sai Abdullahi ɗan Mas’ud ya garzayo ya faɗa wa Annabi (ﷺ) abin da mutumin nan ya faɗa, sai Annabi (ﷺ) ya yi fushi har sai da fushin ya bayyana a fuskarsa sannan ya ce: “Allah ya ji ƙan Musa, haƙiƙa an cutar da shi fiye da haka amma ya yi haƙuri.” [Bukhari #3405 da Muslim #1062].

  70. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَقُولُواْ قَوۡلٗا سَدِيدٗا 

    Open ayah 33:70

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku faɗi Magana wadda take daidai ce.

  71. يُصۡلِحۡ لَكُمۡ أَعۡمَٰلَكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ فَازَ فَوۡزًا عَظِيمًا

    Open ayah 33:71

    Zai kyautata muku ayyukanku, Ya kuma gafarta muku zunubanku. Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa, to haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su kiyaye dokokinsa ta hanyar bin umarninsa da guje wa haninsa, su kuma riƙa magana wadda take kan hanya ta gaskiya. Ya tabbatar musu cewa idan sun yi haka, to zai gyara musu ayyukansu ya karɓe su kuma ya ba su lada, ya kuma gafarta musu zunubansu ya yafe musu. Ya bayyana cewa duk wanda ya bi Allah da Manzonsa (ﷺ) to ya sami babban rabo da babu wanda ya fi shi, domin zai sami gidan Aljanna da dacewa da yardar Allah (Mai tsarki da daukaka).

  72. إِنَّا عَرَضۡنَا ٱلۡأَمَانَةَ عَلَى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱلۡجِبَالِ فَأَبَيۡنَ أَن يَحۡمِلۡنَهَا وَأَشۡفَقۡنَ مِنۡهَا وَحَمَلَهَا ٱلۡإِنسَٰنُۖ إِنَّهُۥ كَانَ ظَلُومٗا جَهُولٗا

    Open ayah 33:72

    Lalle Mun bijiro da amana ga sammai da ƙasa da duwatsu sai suka ƙi ɗaukar ta suka ji tsoron ta, sai kuwa mutum ya ɗauke ta; lalle shi (mutum) ya kasance mai yawan zalunci ne, mai yawan jahilci.

  73. لِّيُعَذِّبَ ٱللَّهُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ وَيَتُوبَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمَۢا

    Open ayah 33:73

    Don Allah Ya azabtar da munafukai maza da munafukai mata, da mushirikai maza da mushirikai mata, Ya kuma karɓi tubar muminai maza da muminai mata. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A ayoyin ƙarshe na wannan Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman sha’anin amanar da ya ɗora wa bayinsa wadda ita ce su bi umarninsa su guje wa haninsa a sarari ko a ɓoye da cewa, ya bijiro da wannan amana ga manya-manyan halittunsa, watau sammai da ƙasa da duwatsu, ya ba su zaɓi su ɗauka ko su bari, idan sun ɗauka sun kiyaye ta to suna da kyakkyawan sakamako a wurinsa, idan kuwa sun kasa kiyaye ta to za su haɗu da uƙubarsa, sai suka ƙi yarda su ɗauki wannan amana, suka ji tsoron kada su kasa sauke nauyinta bayan sun ɗauka. Sai kuma Allah ya bijiro da ita amanar ga mutum bisa wancan sharaɗi sai ko ya ɗauke ta. Allah ya bayyana cewa lalle mutum ya tabbata mai yawan zalunci ne ga kansa, mai yawan jahiltar abin da zai kai ya komo. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa mutane sun kasu kashi uku dangane da wannan amanar: Kashi na farko, su ne munafukai waɗanda a fili suna nuna suna kula da wannan amanar, suna kiyaye ta, amma a zukatansu ba haka ne ba. Kashi na biyu, su ne mushirikai waɗanda suka yi watsi da amanar a fili da ɓoye. Kashi na uku, su ne muminai waɗanda suka kiyaye wannan amanar, suka ba da haƙƙoƙinta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa zai azabtar da munafukai mazansu da matansu, da mushirikai mazansu da matansu, saboda munafuncinsu da shirkarsu, sannan kuma zai karɓi tuban muminai mazansu da matansu, domin sun kiyaye amanar da suka ɗauka, sun yi aiki da umarnin Allah sun guji haninsa. Allah ya kasance mai gafara ne ga zunuban bayinsa idan suka tuba, kuma mai rahama ne gare su.