سبإ
Saba
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ
Open ayah 34:1Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Wanda duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa nasa ne, kuma godiya ta tabbata a gare Shi a lahira. Shi kuwa Mai hikima ne, Masani.
يَعۡلَمُ مَا يَلِجُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا يَخۡرُجُ مِنۡهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعۡرُجُ فِيهَاۚ وَهُوَ ٱلرَّحِيمُ ٱلۡغَفُورُ
Open ayah 34:2Yana sane da abin da yake shiga cikin ƙasa da abin da yake fitowa daga cikinta, da kuma abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa cikinta. Kuma Shi Mai rahama ne, Mai gafara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da tabbatar wa da kansa yabo da godiya da kirari da siffofin kamala, kuma duk abin da yake cikin sammai da wanda yake ƙasa halittarsa ne kuma mulkinsa ne, shi ne mai gudanar da su. Hakanan shi ne wanda yake da kyakkyawan yabo a lahira, kuma shi mai hikima ne cikin halittarsa da gudanar da al’amuransa, masanin halayen bayinsa ne, babu abin da yake ɓuya a gare shi. Ya bayyana cewa yana sane da duk abin da yake shiga cikin ƙasa na ruwa da tsirrai, yana kuma sane da duk abin da yake fita daga cikinta na tsirrai da idanuwan ruwa da sauransu. Hakanan yana sane da duk abin da yake sauka daga sama kamar mala’iku da ruwan sama da arziki, yana kuma sane da duk abin da yake hawa sama kamar mala’iku da ayyukan bayinsa da rayukansu. Kuma shi mai rahama ne ga bayinsa muminai, mai gafarta musu zunubansu ne idan sun tuba.
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَأۡتِينَا ٱلسَّاعَةُۖ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتَأۡتِيَنَّكُمۡ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِۖ لَا يَعۡزُبُ عَنۡهُ مِثۡقَالُ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَآ أَصۡغَرُ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكۡبَرُ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٖ
Open ayah 34:3Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: “Ranar alƙiyama ba za ta zo mana ba.” Ka ce: “A’a, na rantse da Ubangijina, tabbas za ta zo muku, (Allah) Shi ne Masanin gaibu; ba abin da yake ɓoye a gare Shi; daidai da ƙwayar zarra a cikin sammai ko a ƙasa, ko wanda ya fi wannan ƙanƙanta ko ya fi girma, face yana nan (a rubuce) a cikin Lauhul-Mahafuzu.
لِّيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ
Open ayah 34:4“Don Ya saka wa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka kyawawa. Waɗannan suna da gafara da arziki na karamci.”
وَٱلَّذِينَ سَعَوۡ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مِّن رِّجۡزٍ أَلِيمٞ
Open ayah 34:5Waɗanda kuwa suka yi ɓarna a cikin ayoyinmu don su nuna gazawarmu, waɗannan suna da mummunar azaba mai raɗaɗi.
وَيَرَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ هُوَ ٱلۡحَقَّ وَيَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
Open ayah 34:6Waɗanda aka bai wa ilimi kuma suna ganin abin da aka saukar maka daga Ubangijinka shi ne gaskiya, kuma yana shiryarwa ne zuwa hanyar (Allah) Mabuwayi, Sha-yabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana inkarin maganar da kafirai suke faɗa ta cewa alƙiyama ba za ta zo musu ba har abada, don a ganinsu ba gaskiya ce ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tabbatar musu da cewa lalle tabbas sai alƙiyama ta zo musu domin ita gaskiya ce sai dai babu wanda ya san lokacin zuwanta sai Allah shi kaɗai, domin shi ne masanin gaibi, babu abin da yake ɓoye masa daidai da ƙwayar zarra a sammai ko a ƙasa, ko wanda ya fi ta ƙanƙanta ko ya fi ta girma, duk suna rubuce a cikin littafin Lauhul Mahfuzu wanda a cikinsa ne Allah ya rubuta duk abubuwan da za su faru har zuwa tashin alƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk abubuwan da aka bayyana a cikin wannan littafi masu tabbata ne, domin ya saka wa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari da kyakkyawan sakamako. Masu irin wannan siffa kuma suna da gafara daga Allah, ba zai kama su da zunubansu ba, suna da kuma wani arziki na karamci, watau gidan Aljanna. Amma waɗanda suka yi ta ƙoƙarin ɓata ayoyin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar, suka riƙa cewa sihiri ne ko bokanci ko waƙa, to waɗannan a ranar alƙiyama suna da mummunar azaba mai raɗaɗi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da shaida a kan cewa malaman sahabbai da malaman ma’abota littafi waɗanda suka yi imani, duka sun ba da shaida kan cewa Alƙur’ani da aka yi wa Manzon Allah wahayinsa gaskiya ne babu wani kokwanto a cikinsa, yana kuma shiryar da mutane ne zuwa ga hanyar Allah mabuwayi wanda babu mai iya ja da shi kuma sha-yabo a duniya da lahira.
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ هَلۡ نَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ رَجُلٖ يُنَبِّئُكُمۡ إِذَا مُزِّقۡتُمۡ كُلَّ مُمَزَّقٍ إِنَّكُمۡ لَفِي خَلۡقٖ جَدِيدٍ
Open ayah 34:7Waɗanda suka kafirta suka ce: “Shin ma nuna muku wani mutum da zai ba ku labarin cewa, idan an yayyaga ku yugu-yugu lallai za ku dawo cikin wata halitta sabuwa?
أَفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَم بِهِۦ جِنَّةُۢۗ بَلِ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ فِي ٱلۡعَذَابِ وَٱلضَّلَٰلِ ٱلۡبَعِيدِ
Open ayah 34:8“Shin ya yi wa Allah ƙarya ne, ko kuma yana da wani taɓin hankali ne?” Ba haka ba ne, waɗanda ba sa yin imani da lahira suna cikin azaba da ɓata mai nisa.
أَفَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَىٰ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِن نَّشَأۡ نَخۡسِفۡ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضَ أَوۡ نُسۡقِطۡ عَلَيۡهِمۡ كِسَفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّكُلِّ عَبۡدٖ مُّنِيبٖ
Open ayah 34:9Ba sa dubawa su ga abin da yake gabansu da abin da yake bayansu na sama da ƙasa? In da Mun ga dama sai Mu nutsar da su cikin ƙasa ko kuma Mu rufto musu da wani yanki daga sama. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga duk wani bawa mai komawa ga Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin izgili da habaici da kafirai masu ƙaryata ranar alƙiyama suke yi wa Manzon Allah (ﷺ), don ya tabbatar musu cewa bayan sun mutu Allah zai sake tashin su ya yi musu hisabi a kan ayyukansu. Sai suka mayar da abin kamar tatsuniya, suka riƙa faɗa wa junansu cewa su zo su ga wani mutum mai ba da labarin cewa idan sun mutu sun rududduge a ƙasa wai za a sake musu sabuwar halitta a dawo musu da ransu; suna ma ganin cewa ko dai ƙarya yake yi wa Allah, ko kuma yana da taɓin hankali ne wanda yake sanya shi yana maganganu irin waɗannan marasa kan gado. Sai aka mayar musu da martani cewa ba haka abin yake ba; su dai waɗanda ba su yi imani da ranar lahira ba an tanadar musu azaba mai tsanani ne a ranar alƙiyama, a nan duniya kuwa da ma suna cikin ɓata ne mai nisa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya janyo hankalinsu a kan su yi duba cikin abin da ke gabansu na halittar ƙasa da abin da yake bayansu na halittar sama waɗanda suke nuna girman Ƙudurar Allah da cikar ikonsa, domin su fahimci cewa idan ya ga dama sai ya nutsar da su cikin ƙasa, ko kuma ya rufto musu da wani yankin sama a kansu lokaci guda ya hallaka su, sai dai kawai yana saurara musu ne. Lalle da za su nutsu su duba wannan da sun ga cewa akwai ayar Allah tabbatacciya ga duk wani bawa mai mayar da al’amarinsa ga Allah; su gane cewa wanda yake da wannan ikon lalle yana iya tashin su bayan mutuwarsu da rududdugewarsu.
۞وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ مِنَّا فَضۡلٗاۖ يَٰجِبَالُ أَوِّبِي مَعَهُۥ وَٱلطَّيۡرَۖ وَأَلَنَّا لَهُ ٱلۡحَدِيدَ
Open ayah 34:10Kuma haƙiƙa Mun bai wa Dawuda falala daga gare Mu; cewa: “Ya ku duwatsu ku riƙa amsa tasbihi tare da shi,” da kuma tsuntsaye; Muka kuma tausasa masa ƙarfe.
أَنِ ٱعۡمَلۡ سَٰبِغَٰتٖ وَقَدِّرۡ فِي ٱلسَّرۡدِۖ وَٱعۡمَلُواْ صَٰلِحًاۖ إِنِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Open ayah 34:11(Muka ce da shi): “Ka riƙa yin cikakken silke, kuma ka kintata wajen yin saƙar; kuma (kai Dawuda da iyalinka) ku yi ayyuka nagari; lalle Ni Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ɗaya daga cikin annabawansa masu mayar da al’amuransu gare shi, watau Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da cewa lalle ya yi masa wata babbar baiwa ta annabci da mulki, ya kuma ba shi murya mai daɗi wadda yake tasbihi yana tsarkake Allah da ita, don haka sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci duwatsu su riƙa amsa tasbihi tare da shi, ya kuma umarci tsuntsaye su ma su riƙa yi tare da shi. Bugu da ƙari kuma Allah ya hore masa baƙin ƙarfe, ya riƙa sarrafa shi kamar laka, ya ƙera abin da ya ga dama na kayan amfani da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa ya riƙa ƙera cikakkun silikai na yaƙi domin amfanin mayaƙansa, ya kuma riƙa saisaita ƙusoshin da yake kafawa a jikinsu kada su yi ƙanƙanta sosai su ƙi biyan buƙata, kada kuma su yi girma da yawa yadda za su kasa shiga. Sai kuma ya umarce shi da yin kyakkyawan aiki, ya kuma tabbatar masa cewa shi mai ganin abin da bayinsa suke aikatawa ne, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan aikinsa.
وَلِسُلَيۡمَٰنَ ٱلرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهۡرٞ وَرَوَاحُهَا شَهۡرٞۖ وَأَسَلۡنَا لَهُۥ عَيۡنَ ٱلۡقِطۡرِۖ وَمِنَ ٱلۡجِنِّ مَن يَعۡمَلُ بَيۡنَ يَدَيۡهِ بِإِذۡنِ رَبِّهِۦۖ وَمَن يَزِغۡ مِنۡهُمۡ عَنۡ أَمۡرِنَا نُذِقۡهُ مِنۡ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ
Open ayah 34:12Kuma (Muka hore wa) Salaimanu iska, tafiyarta ta safe wata guda ce, ta yamma ma kuma wata guda ce; Muka kuma ɓuɓɓugo masa da narkakkiyar tagulla tana gudana. Daga aljannu kuma akwai masu aiki a wajensa da umarnin Ubangijinsa; wanda kuwa ya kauce wa umarninmu daga cikinsu, to za Mu ɗanɗana masa azabar wutar Sa’ira.
يَعۡمَلُونَ لَهُۥ مَا يَشَآءُ مِن مَّحَٰرِيبَ وَتَمَٰثِيلَ وَجِفَانٖ كَٱلۡجَوَابِ وَقُدُورٖ رَّاسِيَٰتٍۚ ٱعۡمَلُوٓاْ ءَالَ دَاوُۥدَ شُكۡرٗاۚ وَقَلِيلٞ مِّنۡ عِبَادِيَ ٱلشَّكُورُ
Open ayah 34:13Suna aikata masa abubuwan da yake bukata na manya-manyan gine-gine da mutum-mutumi da akusa manya-manya kamar tafkuna da kafaffun tukwane. Ya ku iyalin Dawuda, ku yi aikin (ɗa\'a) domin godiya. Masu godiya daga bayina kuwa kaɗan ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana baiwar da ya yi wa Annabi Sulaimanu ɗan Dawud (() ne. Shi ma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi ƙasaitaccen mulki, ya kuma hore masa iska wadda ita ce abin hawansa, wadda takan yi tafiyar wata guda a lokacin safiya, watau rabin yini, ko gwargwadon marece. Sannan kuma ya ɓuɓɓugo masa narkakkiyar tagulla tana gudana a gabansa don ya riƙa sarrafa ta yadda yake so, don ya ƙera abin da ya ga dama da ita. Hakanan kuma Allah ya hore masa aljannu masu yi masa ayyuka daban-daban da biyayya ga umarninsa; duk kuwa daga cikinsu wanda ya tubure ya ƙi yin biyayya to Allah zai ɗanɗana masa azabar wuta mai ƙuna. Allah ya bayyana cewa su waɗannan aljannu suna yi wa Annabi Sulaimanu manya-manyan gine-gine da wuraren ibada da mutum-mutumai da manya-manyan akusa masu kamar manyan tafkunan ruwa da kafaffun tuƙwane waɗanda ba a motsa su daga inda suke saboda girmansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Dawud da iyalansa da yi wa Allah godiya a kan ni’imomin da ya yi musu ta hanyar yin ayyuka nagari ya kuma tabbatar da cewa kaɗan ne daga cikin bayinsa suke gode wa ni’imarsa.
فَلَمَّا قَضَيۡنَا عَلَيۡهِ ٱلۡمَوۡتَ مَا دَلَّهُمۡ عَلَىٰ مَوۡتِهِۦٓ إِلَّا دَآبَّةُ ٱلۡأَرۡضِ تَأۡكُلُ مِنسَأَتَهُۥۖ فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ ٱلۡجِنُّ أَن لَّوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ ٱلۡغَيۡبَ مَا لَبِثُواْ فِي ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ
Open ayah 34:14Sannan lokacin da Muka ƙaddara masa mutuwa ba abin ya nuna musu mutuwarsa sai gara da ta riƙa cin sandarsa; to lokacin da ya faɗi sai aljannu suka gane cewa da sun san gaibu da ba su zauna cikin azabar wulaƙanci ba. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da ajalin Annabi Sulaimanu ya cika, ya mutu yana tsaye ya dogara a kan sandarsa, aljannu suna ta ci gaba da ayyukansu a zatonsu yana nan da ransa yana sa ido a kan ayyukansu. Babu abin da ya nuna musu mutuwarsa sai gara da ta riƙa cin sandarsa a hankali har sandar ta karye, shi kuma ya faɗi ƙasa, to shi ne suka fahimci ashe da ma can ba ya da rai, a nan ne suka dinga cizon yatsa suna cewa ina ma da sun san gaibi kamar yadda ake musu zato, ai da ba su zauna tsawon lokaci ba cikin azaba da wahalar aiki wanda Annabi Sulaimanu ya saka su.
لَقَدۡ كَانَ لِسَبَإٖ فِي مَسۡكَنِهِمۡ ءَايَةٞۖ جَنَّتَانِ عَن يَمِينٖ وَشِمَالٖۖ كُلُواْ مِن رِّزۡقِ رَبِّكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥۚ بَلۡدَةٞ طَيِّبَةٞ وَرَبٌّ غَفُورٞ
Open ayah 34:15Haƙiƙa akwai aya game da gidajen ƙabilar Saba’u (ta ƙasar Yaman); ita ce gonakai guda biyu na lambu a hagu da dama; (aka ce da su): “Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku gode masa. Ƙasa ce mai daɗin zama da kuma Ubangiji mai gafara.
فَأَعۡرَضُواْ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ سَيۡلَ ٱلۡعَرِمِ وَبَدَّلۡنَٰهُم بِجَنَّتَيۡهِمۡ جَنَّتَيۡنِ ذَوَاتَيۡ أُكُلٍ خَمۡطٖ وَأَثۡلٖ وَشَيۡءٖ مِّن سِدۡرٖ قَلِيلٖ
Open ayah 34:16Sai suka bijire, sai Muka aiko musu da ambaliyar madatsar ruwan Arimu , Muka kuma musanya musu gonakin nan nasu biyu da wasu gonakin biyu ma’abota ‘ya’ya masu ɗaci da kuma itacen tsamiya, da wani abu kaɗan na ‘ya’yan magarya.
ذَٰلِكَ جَزَيۡنَٰهُم بِمَا كَفَرُواْۖ وَهَلۡ نُجَٰزِيٓ إِلَّا ٱلۡكَفُورَ
Open ayah 34:17Wannan shi ne Muka saka musu (da shi) saboda kafircinsu; ba kuwa Ma yin sakamako (irin wannan) sai ga mai butulci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin mutanen wani gari waɗanda Allah ya yi musu ni’imomi da dama amma sai suka ƙi gode masa, suka butulce wa ni’imominsa; su ne mutanen Saba’u ta ƙasar Yaman. Allah ya albarkaci wuraren zamansu da maka-makan gonaki guda biyu da suka sanya su a tsakiya, damansu da hagunsu, suna cike da shuke-shuke da kayan marmari iri-iri, ni’ima ta baibaye su ta ko’ina, garinsu ya zama mai daɗin zama, ga kuma Allah mai gafarta zunuban waɗanda suka tuba. Sai aka umarce su da su ci daga arzikin da Allah ya ba su kuma su gode wa ni’imominsa. To amma sai suka bijire wa Allah suka ƙi yin imani da manzanninsa, sai Allah ya yi musu uƙuba, ya canza musu wannan ni’imar da jin daɗin ya kawo musu wani bala’i. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sako musu wata ambaliyar ruwa mai ƙarfi ta hanyar karya madatsar ruwan da suka gina, ruwa ya kwararo ya cinye gonakinsu duk suka lalace, suka dawo suna fitar da wasu ‘ya’yan itatuwa masu ɗaci da itacen tsamiya da wata ‘yar magarya kaɗan. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya yi musu wannan sakayya ne saboda kafircinsu da bijire wa godiya ga Allah, domin ba wanda ya cancanci irin wannan uƙubar sai mutumin da ya kafirce wa Allah ya butulce wa ni’imominsa.
وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُمۡ وَبَيۡنَ ٱلۡقُرَى ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَا قُرٗى ظَٰهِرَةٗ وَقَدَّرۡنَا فِيهَا ٱلسَّيۡرَۖ سِيرُواْ فِيهَا لَيَالِيَ وَأَيَّامًا ءَامِنِينَ
Open ayah 34:18Muka kuma sanya wasu alƙaryu mabayyana a tsakaninsu (mutan Saba’u) da alƙaryar da Muka sa albarka a cikinta (wato ƙasar Sham), Muka kuma taƙaita zangon tafiya a tsakaninsu (alƙaryun; Muka ce): “Ku yi tafiya a cikinsu dare da rana cikin aminci.”
فَقَالُواْ رَبَّنَا بَٰعِدۡ بَيۡنَ أَسۡفَارِنَا وَظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَ وَمَزَّقۡنَٰهُمۡ كُلَّ مُمَزَّقٍۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ
Open ayah 34:19Sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka ƙaddara nisa tsakanin zangunan tafiyarmu,” suka kuwa zalunci kansu, sai Muka mai da su tarihi, Muka kuma warwatsa su wuri-wuri. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga duk wani mai yin haƙuri, mai yin godiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata ni’imar da ya yi wa mutanen Saba’u bayan ni’imar gonaki, watau ni’imar tafiye-tafiyen kasuwanci cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a tsakanin garin Saba’u da ƙasar Sham wadda Allah ya yi wa albarka mai yawa, ya sanya wasu fitattun alƙaryu da matafiya kan iya hango su daga nesa, ya kuma sanya tazara madaidaiciya a tsakaninsu ta yadda idan matafiyi ya bar alƙarya da safe zuwa Azzahar ya isa ta gabanta, idan da yamma ya fito zai iya kwana a alƙaryar da take gaba da ita, har ya isa ƙasar Sham ba tare da ya yi kayan guzurin ruwa ko abinci ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su yi zirga-zirga a tsakanin waɗannan garuruwa dare da rana cikin aminci, ba tare da tsoron yunwa ko ƙishirwa ko maƙiya ba. To amma sai suka butulce wa wannan ni’imar suka fifita Allah ya sanya tazara a tafiye-tafiyensu ya kawar da waɗannan alƙaryu daga kan hanyarsu ta zuwa Sham ta yadda za su buƙaci ababen hawa da ɗaukar guzurin abinci da abin sha, don suna ganin suna da wadata da yalwar arziƙi. Sun manta cewa a cikinsu akwai talakawan da hakan zai zama wahala a gare su. Sai suka zalunci kawunansu yayin da suka bijire wa ni’imar Allah, suka ƙi gode masa, suka yi wa talakawan cikinsu hassada, sai Allah ya mayar da su tarihi har mutane suka riƙa ba da labarinsu, Allah ya tarwatsa su suka warwatsu a garuruwa daban-daban har haɗuwa da junansu ta yi musu wahala. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa a game da wannan al’amari da ya faru ga mutanen Saba’u akwai aya abar lura da izina ga duk wani mai haƙuri a kan ɗa’ar Allah, da barin saɓa masa, mai godiya game da ni’imarsa.
وَلَقَدۡ صَدَّقَ عَلَيۡهِمۡ إِبۡلِيسُ ظَنَّهُۥ فَٱتَّبَعُوهُ إِلَّا فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 34:20Kuma haƙiƙa Iblisu ya tabbatar da zatonsa a kansu gaskiya ne, sai suka bi shi, in ban da wata ƙungiya ta muminai.
وَمَا كَانَ لَهُۥ عَلَيۡهِم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يُؤۡمِنُ بِٱلۡأٓخِرَةِ مِمَّنۡ هُوَ مِنۡهَا فِي شَكّٖۗ وَرَبُّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَفِيظٞ
Open ayah 34:21Shi kuwa ba shi da wani ƙarfi a kansu, sai dai (Mun yi haka ne) don Mu bayyana wanda yake imani da ranar lahira da kuma wanda yake cikin shakka game da ita. Ubangijinka kuwa Mai kiyaye komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa abin da Iblis ya yi zato game da waɗannan kafirai na cewa zai iya ɓatar da su ya raba su da gaskiya ya tabbata, sai suka bi shi a kan kafirci da saɓon Allah, in ban da wata ƙungiya ta muminai waɗanda suka taɓar da zatonsa a kansu, suka ƙi bin tafarkinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi Iblis ba shi da wani ƙarfi da zai iya tursasa su sai sun bi shi, kawai dai ya ƙawata musu ɓata ne su kuma suka amince suka bi shi, kuma Allah ya huwace wa Iblis wannan damar ce, domin ya bayyana wanda ya yi imani da ranar lahira da sakamakon da ke cikinta da wanda yake shakka a kan zuwanta. Sai kuma Allah ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa shi mai kiyaye duk ayyukan bayinsa ne zai kuma yi musu sakayya a kai.
قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا لَهُمۡ فِيهِمَا مِن شِرۡكٖ وَمَا لَهُۥ مِنۡهُم مِّن ظَهِيرٖ
Open ayah 34:22Ka ce: “Ku kirawo waɗanda kuka riya (cewa su ne iyayen giji) ba Allah ba;” ba sa mallakar wani abu daidai da ƙwayar zarra a cikin sammai ko a cikin ƙasa, ba kuma su da wata tarayya a cikinsu, ba Shi kuma da wani mataimaki daga cikinsu.
وَلَا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ عِندَهُۥٓ إِلَّا لِمَنۡ أَذِنَ لَهُۥۚ حَتَّىٰٓ إِذَا فُزِّعَ عَن قُلُوبِهِمۡ قَالُواْ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمۡۖ قَالُواْ ٱلۡحَقَّۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ
Open ayah 34:23Kuma ceto ba ya amfani a wurinsa sai ga wanda Ya yi wa izinin yin sa. Har idan an cire tsoro daga cikin zukatansu, sai su ce: “Me Ubangijinku Ya ce ne?” Suka ce: “Gaskiya Ya faɗa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa wa mushirikai cewa su kirawo allolinsu waɗanda suke da’awar su ne ababen bauta ba Allah ba, domin su amfanar da su ko su yaye musu wata cuta. Tabbas babu abin da za su iya tsinana musu saboda ba su da mallakin wani abu daidai da ƙwayar zarra a cikin sammai ko a ƙasa wanda yake mallakinsu ne su kaɗai, kuma ba su da wata tarayya da Allah a cikin sammai da ƙasa, shi kuma Allah ba shi da wani mai taimakon sa da yake da wata buƙata a wurinsa domin shi mawadaci ne da Zatinsa. Allah kuma ya tabbatar musu da cewa babu wani ceto da zai yi amfani a wurin Allah sai ga wanda ya yi wa izini, shi kuma ba zai ba da izini ga kowa ba sai wanda ya yarda da shi kaɗai. Saboda isar mulkinsa ne ma idan ya yi wata magana a sama mala’iku gaba ɗaya sukan buga fukafukansu suna masu rusunawa ga wannan maganar tasa, har sai lokacin da tsoronsa ya fita daga cikin zukatansu, sai su tambayi Jibrilu abin da Ubangijinsu ya ce. Shi kuma sai ya amsa musu da cewa gaskiya ya faɗa kuma shi ne Maɗaukaki da Zatinsa da siffarsa da ikonsa, mai girma wanda komai tilas ya rusuna masa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan Allah ya hukunta wani al’amari a sama sai mala’iku su buga fukafukansu, suna masu rusunawa da miƙa wuya ga maganarsa, wadda suke jin ƙararta kamar ƙarar saukar sarƙa a kan dutse kamfa, Allah yana isar musu da wannan maganar, to idan an cire tsoro daga zukatansu sai su ce, me Ubangijinku ya faɗa? Sai manyan mala’iku su amsa wa mai tambaya da cewa: “Gaskiya ya faɗa, kuma shi ne Maɗaukaki mai girma.” [Bukhari #4701].
۞قُلۡ مَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ قُلِ ٱللَّهُۖ وَإِنَّآ أَوۡ إِيَّاكُمۡ لَعَلَىٰ هُدًى أَوۡ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 34:24Ka ce: “Wane ne yake arzuta ku daga sammai da ƙasa?” Ka ce: “Allah ne; kuma mu ko ku (ɗaya daga cikinmu) lalle yana a kan shiriya ko kuma yana cikin ɓata mabayyani.”
قُل لَّا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّآ أَجۡرَمۡنَا وَلَا نُسۡـَٔلُ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 34:25Ka ce: “Ba za a tambaye ku ba game da laifin da muka yi, mu ma kuma ba za a tambaye mu ba game da abin da kuke aikatawa.”
قُلۡ يَجۡمَعُ بَيۡنَنَا رَبُّنَا ثُمَّ يَفۡتَحُ بَيۡنَنَا بِٱلۡحَقِّ وَهُوَ ٱلۡفَتَّاحُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 34:26Ka ce: “Ubangijinmu zai tattara mu sannan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya, Shi ne kuwa Mai hukunci, Masani.”
قُلۡ أَرُونِيَ ٱلَّذِينَ أَلۡحَقۡتُم بِهِۦ شُرَكَآءَۖ كَلَّاۚ بَلۡ هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 34:27Ka ce: “Ku nuna min waɗanda kuka riskar da su a matsayin abokan tarayya da Shi; ku bar wannan magana! Shi ne Allah Mabuwayi Mai hikima.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambayi mushirikai masu bautar wasu tare da Allah, su faɗa masa wane ne yake arzuta su daga sammai, ya saukar musu da ruwa, ko daga ƙasa ya fito musu da tsirrai da shuke-shukensu? Ba su da wata amsa face su yarda cewa Allah ne kaɗai yake yi musu duka waɗannan abubuwa. Idan kuma sun ƙi bayar da amsa, to Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) shi ya faɗa musu cewa Allah ne yake arzuta su. Sannan ya nuna musu cewa lalle ko shi Manzo da muminai da ke tare da shi suna kaɗaita Allah, ko kuma su kafirai masu shirka da Allah, to dole ne ɗaya daga cikinsu yana kan hanyar shiriya ko yana cikin ɓata mabayyani. Babu shakka muminai su ne a kan shiriya, mushirikai kuwa suna kan ɓata mabayyani. Sannan Allah ya umarce shi ya bayyana musu cewa a ranar alƙiyama ba za a tambayi mushirikai game da laifukan da muminai suka yi ba, su ma muminai ba za a yi musu tambaya a kan abin da kafirai suka kasance suna aikatawa ba. Don haka kowa shi ne zai ɗauki alhakin aikinsa. Kuma ya faɗa musu cewa komai daɗewa Allah zai tattara su gaba ɗayansu ranar alƙiyama sannan ya yi musu hukunci na adalci, ya bayyana mai gaskiya da marar gaskiya a cikinsu, domin shi ne mai hukunci da adalci kuma masanin abin da yake hukunci da shi. Sai kuma Allah ya sake umartar Annabi (ﷺ) ya nemi mushirikai su nuna masa waɗanda suka mayar abokan tarayya da Allah waɗanda har suka cancanci su bauta musu ba Allah ba da cewa, ba haka lamarin yake ba, babu wanda ya isa ya zama abokin tarayya da Allah, domin ba shi da kini ko tamka, shi ne kaɗai mabuwayi wanda babu mai iya karawa da shi, kuma mai hikima cikin halittarsa da hukuncinsa.
وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا كَآفَّةٗ لِّلنَّاسِ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 34:28Ba Mu kuma aiko ka ba sai ga mutane baki ɗaya kana mai albishir mai kuma gargaɗi, sai dai kuma yawancin mutane ba sa sanin (hakan).
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 34:29Suna kuma cewa: “Yaushe ne wannan alƙawarin (na ranar alƙiyama) zai zo, idan kun kasance masu gaskiya?”
قُل لَّكُم مِّيعَادُ يَوۡمٖ لَّا تَسۡتَـٔۡخِرُونَ عَنۡهُ سَاعَةٗ وَلَا تَسۡتَقۡدِمُونَ
Open ayah 34:30Ka ce: “Kuna da ajiyayyar rana da ba za ku jinkirta ba daga gare ta daidai da sa’a, ba kuma za ku wuce ta ba.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, ya aiko shi ne fa zuwa ga ɗaukacin mutanen duniya ba Larabawa kaɗai ba. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “An ba ni abubuwa biyar da ba a taɓa ba wa wani annabi ba gabanina; an ba ni nasara ta hanyar jefa tsoro (a zukatan abokan gabata) na tafiyar tsawon wata guda; an kuma sanya mini ƙasa ta zamo masallaci da abin tsarki, duk inda salla ta riski mutum daga cikin al’ummata to ya sallace ta a wurin; an halatta mini dukiyoyin ganima, wadda ba a halatta wa wani gabanina ba; an kuma ba ni ceto; kowane annabi ana aiko shi ne ga mutanensa kaɗai, ni kuwa an aiko ni ne zuwa ga dukkan mutane.” [Bukhari #335 da Muslim #521]. Annabi (ﷺ) yana cewa: “An aiko ni zuwa ga baƙaƙen mutane da jajaye.” [Muslim #521]. Allah ya aiko shi ne kuwa domin ya yi wa masu kiyaye dokokinsa albishir da Aljanna, ya gargaɗi kafirai da masu saɓon Allah, ya tsoratar da su wutar Jahannama. Amma duk da haka da yawa daga cikin mutane ba su san haka ba, da a ce sun sani da ba su ƙaryata shi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai suna gaggauto da azabar Allah wadda Manzonsa (ﷺ) yake tsoratar da su ita, har suna cewa yaushe ne wa’adin zuwanta zai kasance, idan har muminai masu gaskiya ne a kan abin da suke riya cewa gaskiya ne? Sai ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya mayar musu da martani da cewa wannan ranar tana nan tafe babu makawa, domin akwai ajiyayyen lokaci da aka sanya musu ranar da zai zo, ba za su yi jinkiri na gwargwadon sa’a ɗaya ba, ba kuma za su gabace ta ba. Wannan ranar kuwa ita ce ranar alƙiyama.
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَن نُّؤۡمِنَ بِهَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ وَلَا بِٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّٰلِمُونَ مَوۡقُوفُونَ عِندَ رَبِّهِمۡ يَرۡجِعُ بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٍ ٱلۡقَوۡلَ يَقُولُ ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ لَوۡلَآ أَنتُمۡ لَكُنَّا مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 34:31Kuma kafirai suka ce: “Ba za mu yi imani da wannan Alƙur’ani ba, haka ma da wanda yake gabaninsa (na saukakkun littattafai).” Da kuwa za ka ga lokacin da za a tsai da azzalumai wajen Ubangijinsu suna mayar wa da juna magana, masu rauninsu (mabiya) suna ce wa masu girman kai (watau shugabanninsu): “Ba don ku ba da mun zamanto muminai.”
قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ لِلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُوٓاْ أَنَحۡنُ صَدَدۡنَٰكُمۡ عَنِ ٱلۡهُدَىٰ بَعۡدَ إِذۡ جَآءَكُمۖ بَلۡ كُنتُم مُّجۡرِمِينَ
Open ayah 34:32Masu girman kan suka ce wa raunanan: “Yanzu mu muka hana ku ku shiriya bayan ta zo muku? Ba haka ba ne, kun dai kasance masu laifi ne.”
وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ بَلۡ مَكۡرُ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ إِذۡ تَأۡمُرُونَنَآ أَن نَّكۡفُرَ بِٱللَّهِ وَنَجۡعَلَ لَهُۥٓ أَندَادٗاۚ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ وَجَعَلۡنَا ٱلۡأَغۡلَٰلَ فِيٓ أَعۡنَاقِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۖ هَلۡ يُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 34:33Raunanan kuma suka ce da manyan masu girman kan: “Ba haka ba ne, makircin dare da na rana ne (da kuke ƙulla mana ya hana mu shiriya), yayin da kuke umartar mu da mu kafirce wa Allah, mu kuma sanya masa abokan tarayya.” Suka kuma bayyana nadama lokacin da suka ga azaba, kuma Muka sanya ƙuƙumi a wuyan waɗanda suka kafirta, ba kuwa za a saka musu da komai ba sai da irin abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana aƙidar Tauhidi, watau kaɗaita shi da bauta, da tabbatar da manzancin Annabinsa (ﷺ) da tabbatar da ranar lahira, sai ya bayyana cewa mushirikai sun riƙa cika baki suna cewa, su ba za su taɓa yin imani da Alƙur’ani ba, kuma ba za su yi imani da sauran littattafan da suka gabace shi ba waɗanda Allah ya saukar wa annabawansa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) irin mummunan halin da waɗannan kafiran za su tsinci kawunansu a ciki a ranar da za a tsayar da su a gabansa cikin wulaƙanci da ƙasƙanci domin yi musu hisabi. A nan ne rigima da cacar baki zai kaure tsakanin mabiya da shugabanninsu, inda za su yi ta tuhumar juna da alhakin jefa su cikin irin wannan mawuyacin hali. Mabiyan za su tuhumi shugabanninsu da cewa su ne suka ɓatar da su suka hana su ba da gaskiya da Allah da Manzonsa (ﷺ). Sai su kuma shugabannin su mayar musu da martani da cewa: ta yaya za su tuhume su da cewa sun hana su yin imani? Yaushe ne ma suka shiga tsakaninsu da shiriya? A’a, da man can su manyan masu laifi ne, watau faɗuwa ce ta zo daidai da zama; sun same su lalatattu sai kawai suka ƙara ingiza su cikin lalata. Sai su mabiyan su sake mayar musu da magana da cewa makircin da suka yi ta ƙullawa dare da rana shi ne ya zama sanadiyyar ɓatansu, yayin da suka riƙa zuga su suna kafirce wa Allah suna bautar wasu ba shi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a nan ne dukkansu suka nuna nadamarsu game da kafircin da suka yi a duniya yayin da suka ga azaba a fili, suka kuma tabbatar sai an azabta su da ita. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ɓangare na azabar wulaƙanci da za a yi musu a ranar lokacin da za a sanya ƙuƙumai a wuyansu sakamakon mummunan aikinsu na bautar wanin Allah da saɓa masa a duniya.
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتۡرَفُوهَآ إِنَّا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ
Open ayah 34:34Ba Mu taɓa aiko wani mai gargaɗi cikin wata alƙarya ba sai mawadatan cikinta sun ce: “Mu dai masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne.”
وَقَالُواْ نَحۡنُ أَكۡثَرُ أَمۡوَٰلٗا وَأَوۡلَٰدٗا وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ
Open ayah 34:35Suka kuma ce: “Mu muka fi kowa yawan dukiya da ‘ya’ya, kuma mu ba waɗanda za a azabtar ba ne.”
قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 34:36Ka ce: “Lalle Ubangijina Yana shimfiɗa arziki ga wanda Ya ga dama, Ya kuma ƙuntata, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka) ba.”
وَمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُكُم بِٱلَّتِي تُقَرِّبُكُمۡ عِندَنَا زُلۡفَىٰٓ إِلَّا مَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ جَزَآءُ ٱلضِّعۡفِ بِمَا عَمِلُواْ وَهُمۡ فِي ٱلۡغُرُفَٰتِ ءَامِنُونَ
Open ayah 34:37Kuma ba dukiyoyinku da ‘ya’yanku ne za su kusantar da ku gare Mu ba, sai wanda ya yi imani ya kuma yi aiki nagari, to waɗannan suna da sakamako ninkin-baninki saboda abin da suka aikata, suna kuma amintattu cikin benaye.
وَٱلَّذِينَ يَسۡعَوۡنَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَٰٓئِكَ فِي ٱلۡعَذَابِ مُحۡضَرُونَ
Open ayah 34:38Waɗanda kuwa suke yin ƙoƙari na ɓata ayoyinmu, don su nuna gazawarmu, waɗannan cikin azaba za a halartar da su.
قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُ لَهُۥۚ وَمَآ أَنفَقۡتُم مِّن شَيۡءٖ فَهُوَ يُخۡلِفُهُۥۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ
Open ayah 34:39Ka ce: “Lalle Ubangijna Yana shimfiɗa arziki ga wanda ya ga dama cikin bayinsa, Yana kuma ƙuntata masa. Kuma duk abin da kuka ciyar (don Allah), to Shi ne zai ba ku madadinsa, Shi ne kuwa Fiyayyen masu arzutawa.” A waɗannan ayoyi kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana shaida wa Manzonsa (ﷺ) cewa ba shi kaɗai ne manyan gari mawadata suka ƙaryata ba; wannan wata tsohuwar al’ada ce, wadda babu sanda Allah zai aiko da wani mai gargaɗi a cikin wata alƙarya sai manyan garin mawadata sun nuna masa cewa, su ba za su yi imani da shi su bar bautar gumakansu ba, har ma su riƙa cika baki da cewa, su masu yawan dukiya ne da yawan ‘ya’ya, don haka zancen yi musu azaba idan sun ƙi yin imani ƙarya ne, don kuwa su ba waɗanda za a azabtar ba ne sai dai ma a lahira, idan gaskiya ce, Allah ya ƙara karrama su a can ya ba su dukiya da ‘ya’ya kamar yadda ya ba su a nan duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya nuna musu cewa yawan dukiya da yawan ‘ya’ya ba shi ne yake nuna girman matsayin wani a wurin Allah ba, domin shi Ubangiji yakan yalwata dukiya ga wanda ya ga dama domin ya jarraba shi ya gani zai yi godiya ko zai butulce. Yakan kuma ƙuntata arziƙi ga wanda ya ga dama, don ya gwada shi ko zai yi haƙuri ko zai bijire masa. Kuma ya tabbatar musu da cewa ita dukiya da ‘ya’ya da suke tinƙaho da su, ba su ne za su kai su ga samun yardar Allah da kusanci da shi ba. Wanda duk ya yi imani da Allah ya yi kyakkyawan aiki, to shi ne wanda dukiyarsa za ta kusantar da shi ga Allah yayin da ya ciyar da ita dominsa. Hakanan su ma ‘ya’ya za su kusantar da shi ga Allah da kyawawan addu’o’insu gare shi. To muminai masu irin wannan siffa su ne suke da lada ninkin-baninkin na kyawawan ayyukansu, suna kuma amintattu a cikin benaye na Aljanna, ba sa tsoron wata azaba ko mutuwa ko yankewar ni’imar da suke ciki. Sannan Allah ya bayyana sakamakon kafirai masu ƙoƙarin hana mutane yin imani da ayoyin Allah domin cim ma mummunar manufarsu da cewa su ne waɗanda suka yi asara a nan duniya sannan a lahira za a halarto da su wuta domin yi musu azaba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Manzonsa (ﷺ) da cewa ya faɗa wa mutane cewa, Ubangijinsa Allah shi ne wanda yake yalwata arziƙi ga wanda ya ga dama daga bayinsa, yake kuma ƙuntata arziƙin wanda ya ga dama, don haka su nemi kusanci gare shi ta hanyar ciyar da dukiyarsu don Allah, domin duk abin da suka ciyar domin shi, to shi ne zai ba su madadinsa a nan duniya, a lahira kuma ya yi musu babban sakamako. Shi ne Fiyayyen mai arzutawa, don haka duk mai neman arziƙi to ya nema a wurinsa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wata rana da bayi za su wayi gari a cikinta face sai wasu mala’iku biyu suna saukowa, ɗayansu yana cewa: ‘Ya Allah ka mayar wa da mai ciyar da dukiyarsa madadin abin da ya ciyar.’ Ɗayan kuma yana cewa: ‘Ya Allah ka lalata dukiyar mai rowa.’” [Bukhari #1442 da Muslim #1010]. An karɓo daga Abu Huraira, har ila yau ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya ce: “Ka ciyar ya kai ɗan’adam zan ciyar da kai.” [Bukhari #5352 da Muslim #993].
وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ يَقُولُ لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ أَهَٰٓؤُلَآءِ إِيَّاكُمۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ
Open ayah 34:40Kuma (ka tuna) ranar da zai tattaro su gaba ɗaya sannan Ya ce da mala’iku: “Ashe yanzu ku ne waɗannan suka kasance suna bauta wa?”
قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِمۖ بَلۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ ٱلۡجِنَّۖ أَكۡثَرُهُم بِهِم مُّؤۡمِنُونَ
Open ayah 34:41Suka ce: “Tsarki ya tabbata a gare Ka, Kai ne Majiɓincinmu ba su ba.” Ba haka ba ne, sun kasance suna bauta wa aljannu ne; mafiya yawansu masu yin imani da su ne.
فَٱلۡيَوۡمَ لَا يَمۡلِكُ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٖ نَّفۡعٗا وَلَا ضَرّٗا وَنَقُولُ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلنَّارِ ٱلَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Open ayah 34:42(Sai Allah Ya ce): “To yau shashinku ba zai mallaki amfani ga wani sashi ba ko cutarwa,” za kuma Mu ce da waɗanda suka kafirta: “Ku ɗanɗani azabar wutar da kuka kasance kuna ƙaryata ta.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin da masu bautar mala’iku za su tsinci kansu a ciki ranar alƙiyama, lokacin da Allah zai tattara su gaba ɗaya su da mala’ikun domin ya kama su da hujja, sai ya tambayi mala’iku cewa waɗannan mushirikan da gaske ne ku suke bauta wa a duniya? Sai mala’iku su nesanta kawunansu daga waɗannan mushirikai, su tsarkake Allah wanda ba shi da abokin tarayya, su tabbatar masa cewa shi ne majiɓincinsu masoyinsu, kuma babu wata soyayya da ta haɗa tsakaninsu da waɗannan mushirikan, kawai su dai suna bauta wa aljannu ne waɗanda suke nuna musu su mala’iku ne alhalin ƙarya suke, sai su umarce su da bautar su ba Allah ba, don haka yawancinsu sun yi imani ne da aljannu. Sai kuma a tabbatar musu da cewa a wannan rana babu wani amfani da ababen bautarsu za su iya tsinana musu ko su cutar da su, domin mulki gaba ɗaya a ranar na Allah ne. Sai Allah ya faɗa wa waɗanda suka zalunci kawunansu da yin shirka da saɓon Allah a duniya cewa su ɗanɗani azabar wuta wadda a duniya suke ƙaryatawa.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّا رَجُلٞ يُرِيدُ أَن يَصُدَّكُمۡ عَمَّا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُكُمۡ وَقَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّآ إِفۡكٞ مُّفۡتَرٗىۚ وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 34:43Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu mabayyana sai su ce: “Wannan ai ba wani ba ne sai wani mutum da yake nufin ya hana ku (bauta wa) abin da iyayenku suka kasance suna bauta wa.” Suka kuma ce: “Wannan ai ba wani abu ba ne in ban da ƙarya da aka ƙirƙira.” Waɗanda kuma suka kafirta suka ce game da gaskiya yayin da ta zo musu: “Wannan ba wani abu ba ne sai sihiri mabayyani.”
وَمَآ ءَاتَيۡنَٰهُم مِّن كُتُبٖ يَدۡرُسُونَهَاۖ وَمَآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمۡ قَبۡلَكَ مِن نَّذِيرٖ
Open ayah 34:44Kuma ba Mu kawo musu wasu littattafai da suke karantawa ba, kuma ba Mu aiko musu da wani mai gargaɗi ba gabaninka.
وَكَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَمَا بَلَغُواْ مِعۡشَارَ مَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ فَكَذَّبُواْ رُسُلِيۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ
Open ayah 34:45Kuma waɗanda suka gabace su sun ƙaryata (annabawa; kafiran Makka) kuwa ba su kai ushurin abin da Muka ba su ba, sai ma sun ƙaryata manzannina; to yaya tsawatarwata ta kasance (gare su)? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana laifin da ya kai kafirai shiga wutar Jahannama da cewa, duk sanda ake karanta musu ayoyin Allah bayyanannu da ya saukar wa Manzonsa domin su ji su yi imani da Kaɗaitakar Allah da manzancin Annabi (ﷺ) sai su bijire har ma su shiga tuhumar Annabi (ﷺ) da cewa shi kawai wani mutum ne da ya zo yake ƙoƙarin ya hana su bautar abin da iyayensu suke bautawa, domin shi ya samu shugabanci da ɗaukaka a cikinsu. Suka kuma zarge shi da cewa shi ne yake ƙirƙirar Alƙur’ani yana cewa daga Allah yake, suka kuma siffanta Alƙur’ani da cewa sihiri ne bayyananne, domin yana raba tsakanin mutum da matarsa da ɗa da ubansa. Don haka suna da’awar cewa addinin da suke bi na iyaye da kakanni shi ne gaskiya. Sai Allah ya mayar musu da martani cewa, ai babu wasu littattafai da ya saukar musu gabanin Alƙur’ani waɗanda suke karantawa suke ganin gaskiyar abin da suke a kai na addini, ko suka ga an bayyana cewa Annabi ne ya ƙirƙiro Alƙur’ani don haka ƙarya ne ba daga Allah yake ba, kuma ba wani manzo da ya aiko musu kafin zuwan Manzon Allah wanda ya riƙa gargaɗin su da azabar Allah, wanda kuma a wajensa suka sami hujjar yin addinin da suke kai, ko suka sami dalilan ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) a cikinsu. A taƙaice dai ba su da wani ilimi na littafi ko na maganar wani manzo da suka dogara da shi sai tatsuniya kawai da molon-ka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗe su da su yi hattara kada azabar da ta samu al’ummun farko waɗanda suka ƙaryata annabawansu su ma ta same su, domin kuwa al’ummu kamar Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu waɗanda Allah ya ba su yawan dukiya da ‘ya’ya da ƙarfin halitta wanda mushirikan Makka ba su sami ushirinsu ba, ba su amfana musu komai ba yayin da suka ƙaryata manzanninsu kuma azabar Allah ta afka musu, dukkansu Allah ya hallaka su saboda ƙaryatawarsu. Don haka su duba su ga yadda tsawatarwar Allah da uƙubarsa ta kasance a gare su.
۞قُلۡ إِنَّمَآ أَعِظُكُم بِوَٰحِدَةٍۖ أَن تَقُومُواْ لِلَّهِ مَثۡنَىٰ وَفُرَٰدَىٰ ثُمَّ تَتَفَكَّرُواْۚ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا نَذِيرٞ لَّكُم بَيۡنَ يَدَيۡ عَذَابٖ شَدِيدٖ
Open ayah 34:46Ka ce: “Ni dai kawai ina yi muku wa’azi ne da abu ɗaya; cewa ku tsaya don Allah; bibbiyu da kuma ɗai-ɗai, sannan ku yi tunani. Ba wata hauka tare da mutuminku, shi ba wani ne ba, sai mai yi muku gargaɗin azaba mai tsanani da take gabanku.”
قُلۡ مَا سَأَلۡتُكُم مِّنۡ أَجۡرٖ فَهُوَ لَكُمۡۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٞ
Open ayah 34:47Ka ce: “Abin da na tambaye ku na wani lada to naku ne; ladana yana wajen Allah kawai; kuma Shi Mai shaida ne a kan komai.”
قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَّٰمُ ٱلۡغُيُوبِ
Open ayah 34:48Ka ce: “Lalle Ubangijina Yana jefo gaskiya (sai ta rushe ƙarya), Masanin gaibu ne.”
قُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَمَا يُبۡدِئُ ٱلۡبَٰطِلُ وَمَا يُعِيدُ
Open ayah 34:49Ka ce: “Gaskiya ta zo ƙarya kuma ba za ta sake faruwa ba, ba kuma za ta dawo ba.”
قُلۡ إِن ضَلَلۡتُ فَإِنَّمَآ أَضِلُّ عَلَىٰ نَفۡسِيۖ وَإِنِ ٱهۡتَدَيۡتُ فَبِمَا يُوحِيٓ إِلَيَّ رَبِّيٓۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٞ قَرِيبٞ
Open ayah 34:50Ka ce: “Idan na ɓata to na ɓata ne a kan kaina; idan kuwa na shiriya to (na shiriya ne) da abin da Ubangijina Yake yi min wahayinsa. Lalle Shi Mai ji ne, Makusanci.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) cewa ya faɗa wa kafirai masu ƙaryata shi suna jifan sa da hauka, ko kuma yana ƙoƙarin biya wa kansa buƙatarsa ne kawai cewa, yana yi musu wa’azi ne da abu ɗaya, watau su tsaya tsakaninsu da Allah; ko mutum bibbiyu ko ɗai-ɗai, kowa ya yi tunani mai zurfi a karan-kansa ya dubi tarihin rayuwar Annabi Muhammadu (ﷺ) da halayen da aka san shi da su na hankali da gaskiya da amana da sanin yakamata, su gane cewa mai waɗannan halaye bai dace da a kira shi mai taɓin hankali ba, su kuma fahimci cewa shi kawai mai yi musu gargaɗi ne game da wata azaba mai raɗaɗi da za ta same su nan gaba idan ba su tuba sun daina shirka da Allah ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Annabi (ﷺ) ya hau kan dutsen Safa sai ya ƙwala kira sai Ƙuraishawa suka taru a wurinsa, sai suka tambaye shi: “Me ya same ka?” Sai ya ce: “Me kuke gani idan da zan ba ku labarin cewa ga mayaƙa nan suna son su kawo muku hari da sassafe ko da yamma, shin za ku gaskata ni?” Suka ce: “Ƙwarai, za mu gaskata ka.” Sai ya ce: “To ni mai yi muku gargaɗin wata azaba ce mai tsanani a gaba gare ku.” Sai Abu Lahab ya ce: “Tir da kai! Da ma don wannan ne ka tara mu?” Sai Allah ya saukar da Surar‘Tabbat Yada Abi Lahabin’. ” [Bukhari #4801]. Allah kuma ya umarce shi da ya tabbatar musu da cewa ba ya buƙatar su biya shi wani lada na kuɗi, ko wani matsayi a kan abin da yake yi musu wa’azi da shi, yake kuma nuna musu na alheri ko sharri. Ko da kuwa a ce ya nemi su ba da wani lada a kan hakan, to wannan nasu ne ba nasa ba, shi sakamakonsa yana wajen Allah shi kaɗai, kuma shi ne shaida a kan komai, ya shaida cewa Manzon Allah ya isar musu da saƙo, kuma yana ganin ayyukan kowa, zai saka wa kowa a kan aikinsa kyakkyawa ko mummuna. Don haka sai ya umarce shi ya shaida musu cewa gaskiyar da yake karantar da su ita ba shi ne ya ƙirƙire ta ba, Ubangijinsa ne yake yi masa wahayinta don ya rushe ƙarya da ita, shi Allah masanin gaibu ne, babu abin da zai iya ɓuya a gare shi. Sannan ya umarce shi ya bayyana musu cewa yanzu gaskiya ta riga ta bayyana da hujjoji masu ƙarfi, ƙarya kuwa ta rushe, ba ita ba alamarta. Kuma idan kafirai sun ci gaba da tuhumarsa da cewa shi ɓatacce ne wai don ya ƙi bin hanyar iyaye da kakanni, to sai Allah ya umarce shi ya faɗa musu cewa idan ma ya ɓata ne to ya ɓata ne don kansa, bai ƙwari kowa ba, kansa ya ƙwara; idan kuwa ya shiryu ne yana bin hanyar gaskiya, to ba shi ne ya shiryar da kansa ba, ya fahimci shiriyar ne daga abin da Allah ya yi masa wahayinsa na Alƙur’ani. Lalle shi Allah mai jin maganganun bayinsa ne, makusanci ne da su.
وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ فَزِعُواْ فَلَا فَوۡتَ وَأُخِذُواْ مِن مَّكَانٖ قَرِيبٖ
Open ayah 34:51Da kuwa za ka ga sanda (kafirai) za su firgita, (da ganin azaba), sannan ba wata makuɓuta, kuma aka damƙo su daga makusancin wuri.
وَقَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦ وَأَنَّىٰ لَهُمُ ٱلتَّنَاوُشُ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ
Open ayah 34:52Suka kuma ce: “Mun yi imani da shi,” yaya kuwa za su iya kamo (wannan imani) daga wuri mai nisa (wato duniya)?
وَقَدۡ كَفَرُواْ بِهِۦ مِن قَبۡلُۖ وَيَقۡذِفُونَ بِٱلۡغَيۡبِ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ
Open ayah 34:53Alhalin kuma haƙiƙa sun riga sun kafirta da shi a da can, kuma suna jifa (da zato) ta wani wuri mai nisa.
وَحِيلَ بَيۡنَهُمۡ وَبَيۡنَ مَا يَشۡتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشۡيَاعِهِم مِّن قَبۡلُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ فِي شَكّٖ مُّرِيبِۭ
Open ayah 34:54Aka kuma kange tsakaninsu da abin da suke sha’awa (na jin daɗin rayuwa ko komawa duniya) kamar yadda aka yi da ire-irensu tun da can. Lalle su sun kasance cikin shakka mai cike da kokwanto. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai za su yi nadama lokacin da ba za ta amfane su ba da cewa, da a ce ya gan su lokacin da za su ga azaba su firgita, kuma babu wurin gudu ko wajen fakewa, a kama su cikin sauƙi ta wuri makusanci, to da lalle ya ga abin mamaki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da suka ga mummunar makomarsu sannan ne za su shelanta imaninsu, to amma ina, lokacin karɓar imaninsu ya riga ya wuce, domin sun baro shi can a baya, watau duniya wadda ita ce gidan aiki, amma lahira gidan sakamako ne babu sauran wani aiki a cikinta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ta yaya a ranar alƙiyama za a karɓi imaninsu alhalin a can duniya sun kafirce wa Allah, sun riƙa jifan Manzo (ﷺ) da zace-zace iri-iri da shaci-faɗi, wani lokaci su kira shi mai sihiri, wani lokaci su ce masa boka ko su kira shi mawaƙi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa za a haramta musu duk abin da suke nema na jin daɗin rayuwa ko tuba daga kafirci da samun tsira daga azabar wuta ko komawa duniya domin su gyara abin da suka ɓata. Wannan shi ne irin abin da aka yi wa al’ummu irinsu a baya yayin da suka ƙaryata manzanninsu, sai azabar Allah ta zo musu, a lokacin suka riƙa ƙoƙarin su tuba amma ba a karɓi tubansu ba, domin kuwa sun kasance cikin shakka game da gaskiyar abin da manzanninsu suka zo musu da shi na Tauhidi da imani da ranar lahira, shakkar da ta mamaye zukatansu har suka ƙi yarda da komai.