فاطر
Faatir
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ جَاعِلِ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ رُسُلًا أُوْلِيٓ أَجۡنِحَةٖ مَّثۡنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَۚ يَزِيدُ فِي ٱلۡخَلۡقِ مَا يَشَآءُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 35:1<b>Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai </b> 1. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Mahaliccin sammai da ƙasa Mai sanya mala’iku manzanni masu fukafukai bibbiyu da masu uku-uku da kuma masu huɗu-huɗu. Yakan kuma ƙara abin da Ya ga dama ga halittar. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da yi wa kansa kirari da yabo, wanda shi ne ya ƙagi halittar sammai da ƙasa ba tare da ya kwaikwayi wani ba. Wannan yana nuna kamalar Ƙudurarsa da yalwar rahamarsa da girman mulkinsa. Shi ne wanda ya sanya mala’iku su zama manzanni masu zartar da duk wani umarni da ya yi musu. Daga cikinsu akwai masu isar wa annabawa wahayinsa. Ya kuma hore musu ƙarfin isar da amanar da ya ɗora musu; cikinsu akwai masu fukafukai bibbiyu, akwai masu uku-uku, akwai kuma masu huɗu-huɗu, waɗanda da su suke tashi domin zartar da duk wani umarni da zai yi musu. Yana kuma ƙara abin da ya ga dama a halittar tasu, don haka akwai mala’iku masu fukafukai fiye da huɗu, ya kuma ƙara wa wanda ya ga dama kyau ko wata gaɓa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Annabi (ﷺ) ya ga Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana da fukafukai ɗari shida.” [Bukhari #3232 da Muslim #174]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi.
مَّا يَفۡتَحِ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ مِن رَّحۡمَةٖ فَلَا مُمۡسِكَ لَهَاۖ وَمَا يُمۡسِكۡ فَلَا مُرۡسِلَ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 35:2Abin da Allah Yake yi wa mutane buɗi da shi na rahama ba mai iya riƙe shi; abin da kuma Yake riƙewa ba mai iya sakin sa bayansa. Shi kuma Mabuwayi ne, Mai hikima. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna kaɗaitarsa da siffar bayarwa ko hanawa; duk wata rahama da ya yi wa mutane buɗi da ita to babu mai iya riƙe ta, duk kuma abin da ya riƙe to babu mai iya sako shi, don haka mabuɗan komai suna hannunsa, shi ne mai ba wa mutane arziki da shiriya da lafiya, shi ne kuma mai hanawa. Shi mabuwayi ne da babu mai iya ja da shi, mai hikima cikin dukkan ayyukansa babu mai cin gyaransa. Abu Sa’id Alkhudri (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito cikin addu’ar da Manzon Allah (ﷺ) yake yi a ruku’u yana cewa: “…Ya Allah babu mai hana abin da ka bayar, babu kuma mai bayar da abin da ka hana, mawadaci wadatarsa ba za ta yi masa amfani ba a wurinka.” [Muslim #477].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ هَلۡ مِنۡ خَٰلِقٍ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ
Open ayah 35:3Ya ku mutane, ku tuna ni’imar Allah a gare ku. Yanzu akwai wani mahalicci ban da Allah wanda zai arzuta ku daga sama da ƙasa? Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. To ta yaya ake karkatar da ku?
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كُذِّبَتۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Open ayah 35:4Idan kuwa suka ƙaryata ka to haƙiƙa an ƙaryata wasu manzannin a gabaninka. Zuwa ga Allah ne kaɗai ake mayar da al’amura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira mutane baki ɗaya da su tuna ni’imar Allah gare su da zukatansu da harasansu da kuma gaɓoɓinsu, su duba su gani shin akwai wani mai ba su arziki daga sama, watau ya saukar musu ruwan sama, ko yake arzuta su daga ƙasa ta hanyar fitar musu da shuke-shuke da kayan marmari iri-iri? Tabbas babu mai yi musu wannan sai Allah, don haka babu wani wanda ya cancanci a bauta masa sai shi kaɗai, to amma duk da haka sai a samu wasu sun kauce wa hanyarsa sun riƙi wasu ababen bauta tare da shi. Wannan abin mamaki ne. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa game da ƙaryata shi da kafirai suke yi, ya sanar da shi cewa ba shi ne farau ba; manzannin da suka gabace shi ma mutanensu sun ƙaryata su, sai suka yi haƙuri Allah kuma ya hallakar da masu ƙaryatawar, ya tserar da manzanninsa da jama’arsu. Makomar al’amura kuma duka zuwa gare shi take, zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ
Open ayah 35:5Ya ku mutane, lalle alƙawarin Allah gaskiya ne, saboda haka kada rayuwar duniya ta ruɗe ku; kada kuma mai ruɗarwa (Shaiɗan) ya ruɗe ku game da Allah.
إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ لَكُمۡ عَدُوّٞ فَٱتَّخِذُوهُ عَدُوًّاۚ إِنَّمَا يَدۡعُواْ حِزۡبَهُۥ لِيَكُونُواْ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ
Open ayah 35:6Lalle Shaiɗan maƙiyinku ne, saboda haka sai ku riƙe shi maƙiyi. Lalle yana kiran mutanensa ne don su zama ‘yan wuta. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo mutane gaba ɗaya don ya tabbatar musu da zuwan ranar alƙiyama da cewa, wannan ranar da duk abubuwan da za su wakana a cikinta gaskiya ne babu tantama a kan haka, don haka sai su yi mata kyakkyawan tanadi tun daga nan duniya, kada su yarda su bari rayuwar duniya da ƙyale-ƙyalenta da sha’awe-sha’awenta su ruɗe su, kuma kada su kuskura su bari Shaiɗan mai ruɗi ya ruɗe su, ya ɗora su a kan hanyar ƙarya ya ƙawata musu ita, ya sanya son rayuwar duniya a zukatansu har su mance da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tunatar da su tsohuwar ƙiyayyar Shaiɗan gare su tun a kan kakansu Annabi Adam, don haka su ci gaba da ɗaukar sa babban maƙiyi wanda za su yi ta yaƙi da shi ba ƙaƙƙautawa. Allah ya yi musu kashedi game da haɗarin miƙa wa Shaiɗan ragama, domin zai ja mabiyansa ne zuwa ga shiga wutar Jahannama mai tsananin ruruwa a ranar alƙiyama.
ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٞ كَبِيرٌ
Open ayah 35:7Waɗanda suka kafirta suna da (sakamakon) azaba mai tsanani; waɗanda kuwa suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to suna da gafara da lada mai girma.
أَفَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ فَرَءَاهُ حَسَنٗاۖ فَإِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۖ فَلَا تَذۡهَبۡ نَفۡسُكَ عَلَيۡهِمۡ حَسَرَٰتٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا يَصۡنَعُونَ
Open ayah 35:8Yanzu wanda aka ƙawata wa mummunan aikinsa ya gan shi kyakkyawa (zai yi daidai da wanda Allah Ya shiryar)? To lalle Allah Yana ɓatar da wanda Ya ga dama Ya shiryi wanda Ya ga dama; saboda haka kada ka halakar da kanka don baƙin ciki game da su. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana makircin Shaiɗan na ɓatar da mabiyansa da jan su zuwa wuta, sai kuma ya bayyana sakamakon waɗanda suka kafirce wa Allah da Manzonsa (ﷺ) suka zaɓi su bi tafarkin Shaiɗan da cewa suna da wata azaba mai tsanani a lahira. Waɗanda kuma suka yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ) suka kuma yi kyawawan ayyuka suka guje wa abubuwan da aka hana su, to waɗannan suna da gafarar zunubansu da kuma lada mai girma, watau gidan Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna bambancin da ke tsakanin waɗannan ɓangarori biyu, ya yi tambaya cewa, yanzu yaya za a yi a daidaita wanda Shaiɗan ya ƙawata masa mummunan aikinsa har ya gan shi kyakkyawa da wanda Allah ya shiryar da shi hanyar gaskiya ya riƙe ta da gaske? Tabbas ba za su zama ɗaya ba. Don haka ba za a taɓa haɗa mabiya Shaiɗan waɗanda suka rungumi kafirci da saɓon Allah da mabiya Allah da Manzonsa waɗanda suka rungumi gaskiya ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa, shiriya da ɓata duka daga Allah ne, shi ne yake ɓatar da wanda ya ga dama, yake kuma shiryar da wanda ya ga dama, don haka ya kwantar wa da Manzo (ﷺ) hankalinsa ya nuna masa kada ya hallaka kansa don baƙin cikin ganin kafirai sun ƙi karɓar gaskiya sun zaɓi ɓata, Allah ya tabbatar masa cewa shi masanin duk abin da suke aikatawa ne, zai kuma yi musu sakayya daidai da ayyukansu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah mai girma da buwaya ya halicci halittarsa a cikin duhu, sannan ya jefa musu wani yanki na haskensa a wannan ranar, to wanda haskensa ya same shi a wannan ranar sai ya shiriya; wanda kuma ya kuskure masa sai ya ɓata.” [Ahmad #6644 da Tirmizi #2642].
وَٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ ٱلرِّيَٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابٗا فَسُقۡنَٰهُ إِلَىٰ بَلَدٖ مَّيِّتٖ فَأَحۡيَيۡنَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ كَذَٰلِكَ ٱلنُّشُورُ
Open ayah 35:9Kuma Allah Shi ne wanda ya aiko da iska sai ta motsa hadari, sai Muka koro shi zuwa ga mataccen gari, sai Muka raya ƙasa da shi bayan mutuwarta. Kamar haka tayar da (matattu) yake. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman Ƙudurarsa da yalwar rahamarsa ga bayinsa tare da yi musu nuni a kan yiwuwar tashin matattu bayan mutuwarsu da cewa, shi ne wanda yake aiko da iska sai ta motsa hadari, sai kuma Allah ya kora wannan hadarin zuwa mataccen gari wanda babu tsirrai a cikinsa, sai ya rayar da busasshiyar ƙasa da ruwansa, ya fito da shuke-shukenta da ‘ya’yan itatuwanta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa kafirai cewa, kamar yadda ya raya wannan matacciyar ƙasa da ruwan sama har tsirranta suka fito, to hakanan zai tashi matattu a ranar alƙiyama ya dawo musu da rayukansu don a yi musu hisabi.
مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعِزَّةَ فَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ جَمِيعًاۚ إِلَيۡهِ يَصۡعَدُ ٱلۡكَلِمُ ٱلطَّيِّبُ وَٱلۡعَمَلُ ٱلصَّٰلِحُ يَرۡفَعُهُۥۚ وَٱلَّذِينَ يَمۡكُرُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۖ وَمَكۡرُ أُوْلَٰٓئِكَ هُوَ يَبُورُ
Open ayah 35:10Wanda ya zamanto yana nufin ɗaukaka, to ɗaukaka gaba ɗayanta ta Allah ce. Daɗaɗan kalmomi zuwa wurinsa suke hawa, kyakkyawan aiki kuwa shi yake ɗaukaka shi. Waɗanda kuwa suke shirya makirci suna da (sakamakon) azaba mai tsanani, kuma makircin waɗannan shi ne yake lalacewa. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa bayinsa hanyar samun ɗaukaka a duniya da lahira da cewa, ɗaukaka gaba ɗayanta tasa ce, don haka duk mai neman ta to ya lizimci ɗa’a ga Allah (Mai tsarki da daukaka), domin shi ne mai ba da ita. Sannan ya ambaci cewa duk wasu kyawawan maganganu kamar Kalmar Shahada da karatun Alƙur’ani da ambaton Allah, to zuwa wurinsa suke hawa, hakanan kuma yana ɗaukaka aiki nagari zuwa gare shi ya yi wa mai shi sakayya ninkin-baninkin. Sai kuma Allah ya ambaci waɗanda suke son samun ɗaukaka ta hanyar kafirce wa Allah da aikata miyagun ayyuka da shirya mummunan makirci na hallaka Manzon Allah (ﷺ) da cewa, an tanadar musu da matsananciyar azaba, kuma makircinsu ba zai taɓa yin nasara ba sai dai ya lalace.
وَٱللَّهُ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ جَعَلَكُمۡ أَزۡوَٰجٗاۚ وَمَا تَحۡمِلُ مِنۡ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلۡمِهِۦۚ وَمَا يُعَمَّرُ مِن مُّعَمَّرٖ وَلَا يُنقَصُ مِنۡ عُمُرِهِۦٓ إِلَّا فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ
Open ayah 35:11Kuma Allah Ya halicce ku ne daga turɓaya sannan daga maniyyi, sannan kuma Ya mayar da ku maza da mata. Kuma mace ba za ta ɗauki ciki ba, ba kuma za ta haifu ba sai da saninsa. Ba kuma wani mai tsawon rai da za a raya shi, ko kuma wani da za a rage tsawon ransa face yana (rubuce) a cikin Lauhul-Mahafuzu. Wannan kuwa a wurin Allah mai sauƙi ne.
وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡبَحۡرَانِ هَٰذَا عَذۡبٞ فُرَاتٞ سَآئِغٞ شَرَابُهُۥ وَهَٰذَا مِلۡحٌ أُجَاجٞۖ وَمِن كُلّٖ تَأۡكُلُونَ لَحۡمٗا طَرِيّٗا وَتَسۡتَخۡرِجُونَ حِلۡيَةٗ تَلۡبَسُونَهَاۖ وَتَرَى ٱلۡفُلۡكَ فِيهِ مَوَاخِرَ لِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 35:12Koguna biyu ba za su daidaita ba, wannan na da daɗin gaske da sauƙin haɗiya, wannan kuma mai zartsin gaske ne, daga kowannensu kuma kuna cin nama sabo (ba bushasshe ba), kuna kuma fito da kayan ado (daga gare su) wanda kuke sawa; kuma kana ganin jiragen ruwa suna keta shi (kogin) don ku nemi falalarsa don kuma ku gode (masa).
يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۚ وَٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ مَا يَمۡلِكُونَ مِن قِطۡمِيرٍ
Open ayah 35:13Yana shigar da dare cikin yini, Yana kuma shigar da yini cikin dare, Ya kuma hore rana da wata kowannensu yana tafiya zuwa ga ajali iyakantacce. (Mai yin wannan kuwa) Shi ne Allah Ubangijinku, mulki (kuwa) nasa ne. Waɗanda kuwa kuke bauta wa ba Shi ba, ba su mallaki ko da rigar ƙwallon dabino ba.
إِن تَدۡعُوهُمۡ لَا يَسۡمَعُواْ دُعَآءَكُمۡ وَلَوۡ سَمِعُواْ مَا ٱسۡتَجَابُواْ لَكُمۡۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكۡفُرُونَ بِشِرۡكِكُمۡۚ وَلَا يُنَبِّئُكَ مِثۡلُ خَبِيرٖ
Open ayah 35:14Idan kuna kiran su, ba sa jin kiranku, ko da ma sun ji, ba za su amsa muku ba; a ranar alƙiyama kuma za su butulce wa shirkarku. Ba kuwa mai ba ka labari kamar cikakken Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci dalilai bakwai na gani a faɗa masu nuna girman Ƙudurarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai. Na farko, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya halicci mutane daga turɓaya, lokacin da ya halicci babansu Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sannan ya halicci sauran ‘yan’adam daga maniyyi, sannan ya sanya su maza da mata suka riƙa auratayya a tsakaninsu suna ci gaba da hayayyafa. Wannan wani babban dalili ne mai tabbatar da cikar Ƙudurar Allah da Ɗayantakarsa. Na biyu, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk abin da mace za ta ɗauki cikinsa da abin da za ta haife yana gudana ne da saninsa; tun farkon ɗaukar cikin har zuwa haihuwarsa yana sane da komai nasa, shi ne kuma mai kulawa da shi. Wannan cikakken ilimi nasa yana nuna cancantar a bauta masa shi kaɗai a yi imani da shi. Na uku, Allah ya bayyana cewa duk wanda zai yi tsawon rai ko mai gajeren kwana, rayuwarsa tana gudana ne yadda Allah ya tsara ta ya kuma rubuta ta a cikin littafin Lauhul Mahfuzu, babu wani wanda ya isa ya canja wani abu in ba shi ba, don haka shi kaɗai ya cancanta a bauta wa. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mazon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda yake son a faranta masa rai a yalwata masa arzikinsa, a kuma jinkirta masa ajalinsa, to ya sadar da zumuncinsa.” [Bukhari #2068 da Muslim #2557]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa wannan aiki ne mai sauƙi a wurinsa, domin cikar iliminsa da kamalar Ƙudurarsa. Na huɗu, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ɗaya daga cikin ayoyinsa ta haɗa koguna guda biyu, ɗaya mai daɗin gaske mai sauƙin kwankwaɗa, ɗayan kuma mai tsananin zartsi wanda ba ya shayuwa, kuma ga su a wuri ɗaya suna gudana, amma ba wanda zai gauraya da wani. Allah kuma ya bayyana cewa waɗannan koguna biyu ba za su taɓa zama daidai ba, amma kuma daga cikin kowannensu ana samun kifaye, ana kuma fito da lu’u-lu’u da murjani waɗanda mutane suke sawa suna yin ado da su. Lalle wannan ma wani babban dalili ne mai nuna girman Ƙudurar Allah ta yin yadda ya ga dama, don haka shi kaɗai ya cancanta a bauta wa. Na biyar, ya janyo hankalin ɗan’adam zuwa ga wata babbar Ƙudurar tasa, watau manyan jiragen ruwa da ya sanya su suna zirga-zirga a cikin ruwa ɗauke da mutane da kaya niƙi-niƙi, amma duk da haka suna keta ruwa suna gudu ba tare da sun nutse ba. Allah ya yi wa ‘yan’adam wannan baiwa ne domin su yi tafiye-tafiyensu gari zuwa gari cikin sauƙi don neman arziki da ɗaukan kayan kasuwancinsu, don kuma su gode masa ta hanyar kaɗaita shi da bauta da bin umarninsa da guje wa haninsa. Na shida, Allah shi ne yake shigar da dare a cikin yini sai ya ƙara tsawo, ya kuma shigar da yini a cikin dare sai shi ma ya ƙara tsawo. Babu wanda ya isa ya yi wannan aikin in ban da shi kaɗai, don haka shi ne ya cancanci a kaɗaita shi da bauta. Na bakwai, Allah shi ne ya hore rana da wata domin buƙatar ɗan’adam ta rayuwarsa da ta dabbobinsa da shuke-shukensa, dukkansu kuma suna gudu har zuwa wani iyakantaccen lokaci, watau ranar alƙiyama, a sannan ne tafiyarsu za ta dakata haskensu ya disashe. To wane ne zai iya yin wannan aikin in ban da Allah? Ashe shi kaɗai ya cancanta a bauta wa ba tare da yi masa shirka ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa mai waɗannan ayyuka duka shi ne Allah Ubangijin dukkan halittu, mulki kuma nasa ne shi kaɗai. Abubuwan da kafirai suke bauta wa kuma ba su mallaki ko da gwargwadon rigar ƙwallon dabino ba, to amma abin mamaki sun dage da bautar su ba ji ba gani, sun bar Allah mai cikakkiyar Ƙudura. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da kafirai kasawar ababen bautarsu, kuma bautar da suke yi musu a banza suke yin ta, domin kuwa idan suna kiran su ba sa jin kiran nasu, saboda daskararrun abubuwa ne marasa rai ballantana su ji kiran. Idan kuwa da a ce ma za su ji kiran nasu, to ba za su iya amsa musu ba. Sannan kuma a ranar alƙiyama za su nesanta kansu da bautar da kafiran suka yi musu, domin su ma a ranar ta kansu suke. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shaida wa Annabi (ﷺ) cewa babu wanda zai ba shi labari na gaskiya kamar Allah mai cikakken sanin komai.
۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ أَنتُمُ ٱلۡفُقَرَآءُ إِلَى ٱللَّهِۖ وَٱللَّهُ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ
Open ayah 35:15Ya ku mutane, ku ne mabuƙata a wurin Allah; Allah kuma Shi ne Mawadaci, Sha-yabo.
إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَأۡتِ بِخَلۡقٖ جَدِيدٖ
Open ayah 35:16Idan Ya ga dama sai Ya tafiyar da ku Ya kawo wata sabuwar halittar.
وَمَا ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ بِعَزِيزٖ
Open ayah 35:17Wannan kuwa ba wani abu ne ba da zai gagari Allah.
وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ وَإِن تَدۡعُ مُثۡقَلَةٌ إِلَىٰ حِمۡلِهَا لَا يُحۡمَلۡ مِنۡهُ شَيۡءٞ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰٓۗ إِنَّمَا تُنذِرُ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَمَن تَزَكَّىٰ فَإِنَّمَا يَتَزَكَّىٰ لِنَفۡسِهِۦۚ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 35:18Kuma wani mai ɗaukar nauyi ba ya ɗaukan laifin wani. Idan kuma wani mai nannauyan zunubi ya yi kira zuwa ɗauke nauyin nasa, ba za a ɗauke masa komai daga nauyin ba, ko da kuwa ɗan’uwa ne makusanci. Kai dai kana mai gargaɗi ne kawai ga waɗanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da ganin Sa ba, suka kuma tsai da salla. Wanda kuwa ya tsarkaka, to ya tsarkaka ne don kansa. Makoma kuma na ga Allah Shi kaɗai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana gajiyawar `yan’adam da buƙatuwarsu a gare shi da kuma cikakkiyar wadatarsa. Watau koyaushe mutane su ne mabuƙata a wurin Allah cikin dukkan al’amuransu, shi kuwa Allah shi ne mai cikakkiyar wadata ba ya da buƙatar komai a wurin kowa. Shi ne sha-yabo a duniya da lahira bisa abin da ya ƙaddara wa bayinsa. Allah kuma ya sanar da su cikar ƙudurarsa da cewa, da ya ga dama da sai ya hallaka su gaba ɗayansu, ya kawo wasu sababbin halittu waɗanda za su bauta masa shi kaɗai ba tare da yi masa shirka ba. Ya kuma tabbatar musu da cewa wannan ba abu ne mai wahala a wurinsa ba da zai gagare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kamalar adalcinsa a ranar alƙiyama, domin babu wanda zai ɗauki nauyin zunuban wani, kowa shi zai ɗauki nauyin laifinsa, da kuwa wani mai nannauyan zunubi zai kira wani ya ɗauke masa wani abu daga zunubansa, to da bai samu mai yi masa haka ba ko da kuwa ɗan’uwansa ne makusanci, domin lahira ba kamar duniya ce ba inda ɗan’uwa yake taimaka wa ɗan’uwansa ko aboki ya taimaki abokinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa game da bijirewar da kafirai suke yi masa da cewa, waɗanda kawai yake yi wa gargaɗi kuma su amfana da gargaɗin nasa su ne waɗanda suke jin tsoron Ubangijinsu duk da cewa ba sa ganin sa, kuma suke tsayar da salla yadda ya kamata, to su ne gargaɗinsa yake amfana, don haka duk wanda ya tsarkake kansa daga shirka da saɓon Allah, to kansa ya yi wa, domin shi ne zai amfana da wannan ba wani ba; Allah ma ba ya da buƙatar ɗa’ar kowa, kowa kuma wurinsa zai koma don ya yi wa kowa sakamako gwargwadon aikinsa.
وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ
Open ayah 35:19Makaho da mai gani ba za su yi daidai ba.
وَلَا ٱلظُّلُمَٰتُ وَلَا ٱلنُّورُ
Open ayah 35:20Da kuma duhu da haske (ba za su yi daidai ba).
وَلَا ٱلظِّلُّ وَلَا ٱلۡحَرُورُ
Open ayah 35:21Da kuma inuwa da zafin (rana) (ba za su yi daidai ba).
وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡأَحۡيَآءُ وَلَا ٱلۡأَمۡوَٰتُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُسۡمِعُ مَن يَشَآءُۖ وَمَآ أَنتَ بِمُسۡمِعٖ مَّن فِي ٱلۡقُبُورِ
Open ayah 35:22Kuma rayayyu da matattu ba za su yi daidai ba. Lalle Allah Yana jiyar da wanda Ya ga dama; kai kuma ba mai iya jiyar da waɗanda suke cikin ƙaburbura ne ba.
إِنۡ أَنتَ إِلَّا نَذِيرٌ
Open ayah 35:23Kai ba kowa ba ne face mai gargaɗi.
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗاۚ وَإِن مِّنۡ أُمَّةٍ إِلَّا خَلَا فِيهَا نَذِيرٞ
Open ayah 35:24Lalle Mu Muka aiko ka da gaskiya kana mai albishir mai kuma gargaɗi. Babu kuma wata al’umma da (ta gabata) sai da wani mai gargaɗi ya zo mata.
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَبِٱلزُّبُرِ وَبِٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُنِيرِ
Open ayah 35:25Idan kuwa sun ƙaryata ka, to haƙiƙa waɗanda suka gabace su ma sun ƙaryata, lokacin da manzanninsu suka zo musu da hujjoji da takardu da kuma littattafai masu hasken (shiriya).
ثُمَّ أَخَذۡتُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ
Open ayah 35:26Sannan Na damƙi waɗanda suka kafirta; to yaya narkona ya kasance? A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana mana rashin daidaituwar abubuwa kishiyoyin juna a wurin Allah da wurin duk wani mai lafiyayyen hankali. Allah ya nuna cewa makaho da mai gani ba za su yi daidai ba; hakanan mumini da kafiri ba za su zama daidai ba. Sannan duhu da haske ba za su yi daidai ba, to hakanan kafirci da imani ba za su zama daidai ba. Inuwa da iska mai zafi kuma ba za su daidaita ba, to hakanan Aljanna da wuta ba za su zama daidai ba. Rayayyu da matattu kuma ba za su yi daidai ba, to hakanan muminai da kafirai ba za su yi daidai ba. Don haka sai mai hankali ya zaɓi abin da ya fi dacewa da shi. Allah kuma ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa shi ne yake jiyar da gargaɗinsa ga wanda ya ga damar shiriyarsa, shi Manzon Allah ba zai iya jiyar da kafirai ba waɗanda suka yi kama da matattun da suke cikin ƙaburburansu; shi kawai mai gargaɗi ne da tsoratarwa game da azabar Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) manufar aiko shi ga mutane, watau domin ya yi albishir ga muminai da sakamakon gidan Aljanna da Allah ya tanadar musu, ya kuma yi gargaɗi ga kafirai game da azabar da ya tanadar musu a lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa babu wata al’umma da ta gabata face sai da manzo mai gargaɗi ya zo mata ya tsayar mata da hujjar Allah. Don haka idan shi Manzo mutanensa sun ƙaryata shi, to ba a kansa aka fara ƙaryata manzanni ba; al’ummun da suka gabata ma sun ƙaryata annabawansu, kamar Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu, manzanninsu sun zo musu da hujjoji bayyanannu masu nuna gaskiyarsu, sun kuma zo musu da takardu da littattafai masu haska wa duk wanda ya karanta su hanyar shiriya. To amma duk da haka sai suka kafirce wa Allah da manzanninsa sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su, ya kuma nuna wa Manzonsa cewa tsananin narkonsa kenan ga waɗanda suka ƙaryata wani daga cikin annabawansa. Don haka su ma masu ƙaryata shi su shiga taitayinsu don kada abin da ya sami kafiran farko su ma ya same su.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ ثَمَرَٰتٖ مُّخۡتَلِفًا أَلۡوَٰنُهَاۚ وَمِنَ ٱلۡجِبَالِ جُدَدُۢ بِيضٞ وَحُمۡرٞ مُّخۡتَلِفٌ أَلۡوَٰنُهَا وَغَرَابِيبُ سُودٞ
Open ayah 35:27Ba ka ganin lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama sai Muka fitar da ‘ya’yan itace iri daban-daban da shi? Daga duwatsu kuma (Ya samar da) hanyoyi farare da jajaye masu launi daban-daban da kuma wasu baƙaƙe ƙirin.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ وَٱلدَّوَآبِّ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ مُخۡتَلِفٌ أَلۡوَٰنُهُۥ كَذَٰلِكَۗ إِنَّمَا يَخۡشَى ٱللَّهَ مِنۡ عِبَادِهِ ٱلۡعُلَمَٰٓؤُاْۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ غَفُورٌ
Open ayah 35:28Daga mutane kuma da dabbobi da kuma dabbobin ni’ima su ma launinsu daban-daban ne kamar waɗancan. Malamai ne kawai suke tsoron Allah daga bayinsa. Lalle Allah Mabuwayi ne Mai gafara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankulan bayinsa zuwa ga lura da la’akari da wasu dalilai masu nuna girman Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa, inda ya nuna cewa su duba su ga yadda ya saukar da ruwa daga sama wanda da shi ne kuma ya fitar da tsirrai da shuke-shuke masu yanayi da ɗanɗano daban-daban. Hakanan kuma ya halicci hanyoyin duwatsu masu launuka daban-daban, wasu farare wasu jajaye wasu kuma baƙaƙe ƙirin. Haka ma mutane da dabbobi su ma ya halicce su da launuka daban-daban. Duk waɗannan dalilai ne masu nuna girman Ƙudurar Allah da cancantar a bauta masa shi kaɗai, don haka ne ma Allah ya tabbatar da cewa malamai waɗanda suka san Allah da shari’arsa su ne kawai suke jin tsoron sa da girmama shi yadda ya kamata a ga girmansa. Lalle shi Allah mabuwayi ne babu mai rinjayar sa, mai gafara ne ga zunubban bayinsa yayin da suka tuba.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَتۡلُونَ كِتَٰبَ ٱللَّهِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ يَرۡجُونَ تِجَٰرَةٗ لَّن تَبُورَ
Open ayah 35:29Lalle waɗanda suke karanta Littafin Allah suka kuma tsai da salla suka kuma ciyar daga abin da Muka arzuta su a ɓoye da sarari, suna burin kasuwancin da ba zai yi tazgaro ba.
لِيُوَفِّيَهُمۡ أُجُورَهُمۡ وَيَزِيدَهُم مِّن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ غَفُورٞ شَكُورٞ
Open ayah 35:30Domin Ya cika musu ladansu Ya kuma ƙara musu daga falalarsa. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai godiya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kyakkyawan sakamako da zai yi wa waɗanda suke karanta littafinsa da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ), watau Alƙur’ani, suka kuma yi aiki da shi, sannan suka tsai da salla yadda ya kamata, suka kuma ciyar daga dukiyar da Allah ya arzuta su da ita ta hanyar fitar da zakka ko ba da sadaka da taimako a fili ko a ɓoye, ba kuma don neman wani suna ba, sai don suna burin ƙulla wani kasuwanci ne da Allah wanda babu tazgaro ko asara a cikinsa, domin kuwa Allah ya ba su ladansu cikakke, ya kuma ƙara musu wani ladan daga falalarsa; lalle kuma Allah mai gafara ne ga zunubansu, mai godiya ne a kan kyawawan ayyukansu.
وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ هُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِعِبَادِهِۦ لَخَبِيرُۢ بَصِيرٞ
Open ayah 35:31Kuma abin da Muka yiwo maka wahayinsa na Littafi shi ne gaskiya, yana gaskata abin da yake gabaninsa (na littattafai). Lalle Allah game da bayinsa Masani ne, Mai gani.
ثُمَّ أَوۡرَثۡنَا ٱلۡكِتَٰبَ ٱلَّذِينَ ٱصۡطَفَيۡنَا مِنۡ عِبَادِنَاۖ فَمِنۡهُمۡ ظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ وَمِنۡهُم مُّقۡتَصِدٞ وَمِنۡهُمۡ سَابِقُۢ بِٱلۡخَيۡرَٰتِ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَضۡلُ ٱلۡكَبِيرُ
Open ayah 35:32Sannan Muka gadar da Littafin ga waɗanda Muka zaɓa cikin bayinmu; to daga cikinsu akwai mai cutar kansa, akwai kuma mai tsakaitawa a cikinsu, kuma akwai wanda ya yi fintinkau a aikata alheri da izinin Allah. Wannan kuwa shi ne falala mai girma.
جَنَّٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَلُؤۡلُؤٗاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِيهَا حَرِيرٞ
Open ayah 35:33(Watau) gidajen Aljanna na dawwama da za su shige su, za a yi musu ado a cikinsu na awarwaron zinare da kuma lu’ulu’u; tufafinsu a cikinsu (gidajen Aljanna) alharini ne.
وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَذۡهَبَ عَنَّا ٱلۡحَزَنَۖ إِنَّ رَبَّنَا لَغَفُورٞ شَكُورٌ
Open ayah 35:34Kuma Su ce: “Yabo ya tabbata ga Allah Wanda Ya yaye mana baƙin ciki; lalle Ubangijinmu Mai gafara ne, Mai godiya.
ٱلَّذِيٓ أَحَلَّنَا دَارَ ٱلۡمُقَامَةِ مِن فَضۡلِهِۦ لَا يَمَسُّنَا فِيهَا نَصَبٞ وَلَا يَمَسُّنَا فِيهَا لُغُوبٞ
Open ayah 35:35“Wanda Ya saukar da mu a gidan dawwama don falalarsa, ba wata wahala da za ta shafe mu a cikinsa, kuma ba wata gajiya da za ta shafe mu a cikinsa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Alƙur’ani wanda ya yi wahayinsa ga Manzonsa (ﷺ) wanda kafirai suke tababa a kansa gaskiya ne ba wata shakka game da shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da shi yana mai gaskata littattafan da suka gabata, domin duk sun ba da labarinsa, yayin da ya sauka yana ƙunshe da abin da suka yi ishara sai gaskiyarsu su ma ta bayyana. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya san komai game da bayinsa kuma mai ganin duk abin da suke aikatawa ne, don haka shi ne ya fi sanin abin da zai dace da su na maslahar rayuwarsu ta duniya da lahira. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya gadar da wannan Alƙur’ani ga al’ummar Annabi (ﷺ) wadda ya zaɓe ta cikin sauran al’ummu. Sai kuma ya kasa wannan zaɓaɓɓiyar al’umma kashi uku: Kashi na farko, su ne waɗanda suka zalunci kansu ta hanyar aikata laifuffukan da ba su kai kafirci ba, watau barin wani abu da ya wajaba, ko aikata wani abu da aka haramta aikata shi. Kashi na biyu, su ne tsaka-tsaki, watau waɗanda suka kula da aikata abubuwan da aka wajabta musu, suka guji abubuwan da aka haramta musu, tare da barin wasu ayyuka na mustahabbi da aikata wasu ayyuka na makaruhi. Kashi na uku, su ne waɗanda suka yi fice wajen aikata ayyukan alheri da izinin Allah da taimakonsa. Su ne waɗanda bayan aikata wajabci ba sa barin mustahabbai kamar nafilfilu na salla da azumi. Sannan bayan sun guje wa haramun, sukan ƙaurace wa makaruhai ma. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan wannan zaɓi da ya yi wa wannan al’umma ya kuma ba ta Alƙur’ani wanda shi me wata babbar falala ce daga Allah da babu irinta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon duk waɗannan kashe-kashe guda uku da cewa dukkansu za su shiga Aljanna inda za su dawwama a cikinta har abada. Za a ni’imta su da ni’imomi iri-iri, daga cikinsu za a yi musu ado da awarwaro na zinari da kuma lu’u-lu’u, sannan tufafin sawarsu na alharini ne mai kauri da shara-shara. To bayan sun sami shiga gidajensu na Aljanna sun sami ni’imomi daban-daban a cikinta sai su yi wa Allah godiya wanda ya tafiyar musu da duk wata damuwa ta tsoron a kai su wuta. Suka ƙara tabbatarwa cewa lalle Allah mai gafarta zunuban bayinsa ne matuƙar sun tuba, mai godiya ne a gare su bisa kyawawan ayyukansu waɗanda ya karɓa ya ninninka musu ladansu, ya ba su abin da yawan ayyukansu ba za su ba su shi ba. Suka kuma ƙara da cewa shi ne wanda ya saukar da su gidan Aljanna da falalarsa ba don ƙoƙarinsu ko dabararsu ba, ya kuma yaye musu duk wata wahala ko gajiya.
وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمۡ نَارُ جَهَنَّمَ لَا يُقۡضَىٰ عَلَيۡهِمۡ فَيَمُوتُواْ وَلَا يُخَفَّفُ عَنۡهُم مِّنۡ عَذَابِهَاۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي كُلَّ كَفُورٖ
Open ayah 35:36Waɗanda kuwa suka kafirta suna da (sakamakon) wutar Jahannama, ba za a karɓi rayukansu ba balle su mutu, ba kuma za a sauƙaƙa musu wani abu daga azabarta ba. Kamar haka Muke saka wa kowanne kafiri.
وَهُمۡ يَصۡطَرِخُونَ فِيهَا رَبَّنَآ أَخۡرِجۡنَا نَعۡمَلۡ صَٰلِحًا غَيۡرَ ٱلَّذِي كُنَّا نَعۡمَلُۚ أَوَلَمۡ نُعَمِّرۡكُم مَّا يَتَذَكَّرُ فِيهِ مَن تَذَكَّرَ وَجَآءَكُمُ ٱلنَّذِيرُۖ فَذُوقُواْ فَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِن نَّصِيرٍ
Open ayah 35:37Su kuwa suna ta kururuwa a cikinta suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka fitar da mu, za mu yi aiki nagari, ba irin wanda muka kasance muna aikatawa ba.” (Sai a ce da su): “Yanzu ba Mu raya ku ba gwargwadon lokacin da mai wa’azantuwa zai wa’azantu, kuma mai gargaɗi ya zo muku? Sai ku ɗanɗani (azaba), sannan azzalumai ba su da wani mataimaki.” A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci sakamakon waɗanda suka kafirce masa, inda ya nuna cewa suna da wutar Jahannama wadda za su dawwama a cikinta har abada, ba za a sake hukunta musu wata mutuwa ba a cikinta ballantana su mutu su huta, sannan kuma ba za a sassauta musu azabarta ba; za su yi ta ɗanɗanar azaba ne ba ƙaƙƙautawa. Allah ya bayyana cewa kamar irin wannan azaba ce yake saka wa kowane kafiri mai butulce wa ni’imomin Allah. Sai kuma ya ƙara bayyana mawuyacin halin da ‘yan wuta za su tsinci kansu a ciki, yayin da za su yi ta kuka suna kururuwa saboda tsananin azabar da ake yi musu suna ta roƙon Ubangiji ya fitar da su daga cikinta, ya sake mayar da su duniya domin su yi aiki nagari, ba irin wanda suka zamanto suna yi ba na saɓon Allah. Sai Allah ya mayar musu da martani da cewa, ashe ba ya raya su gwargwadon lokacin da mai son ya wa’azantu zai wa’azantu ba, ya tuba zuwa ga Allah ya aikata ayyuka nagari, kuma ya aika musu manzo wanda ya zo yana gargaɗin su da azabar Allah? To ba su da wata hujja ko wani hanzari da za su gabatar a gaban Allah. Don haka sai a ce su ɗanɗani azabar wuta domin kuwa azzalumai waɗanda suka cuci kawunansu ta hanyar kafirci da saɓon Allah, ba su da wani mai taimakon su ya kuɓutar da su daga azabar Allah, ko ya sanya a sassauta musu azaba. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah ya yanke uzurin mutumin da ya jinkirta rayuwarsa har ya kai shekara sittin.” [Bukhari #6419].
إِنَّ ٱللَّهَ عَٰلِمُ غَيۡبِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Open ayah 35:38Lalle Allah Masanin gaibin sammai da ƙasa ne. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin zukata ne.
هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَكُمۡ خَلَٰٓئِفَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ فَمَن كَفَرَ فَعَلَيۡهِ كُفۡرُهُۥۖ وَلَا يَزِيدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ كُفۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ إِلَّا مَقۡتٗاۖ وَلَا يَزِيدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ كُفۡرُهُمۡ إِلَّا خَسَارٗا
Open ayah 35:39Shi ne wanda Ya sanya ku halifofi a bayan ƙasa. Saboda haka wanda ya kafirta sakamakon kafircinsa yana kansa, kuma kafircin kafirai ba zai ƙara musu komai ba a wurin Ubangijinsu sai ƙiyayya; kuma kafircin kafirai ba zai ƙara musu komai ba sai hasara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakken iliminsa wanda ya kewaye komai da kowa na fili da na ɓoye, domin shi ne masanin gaibin sammai da ƙasa, babu abin da yake ɓuya gare shi, ya kuma san abin da yake cikin zukatan bayinsa mai kyau ko mummuna, don haka yana yi wa kowa sakayya ne da abin da ya cancanta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da bayinsa cewa, shi ne ya sanya sashinsu yake maye gurbin sashi a bayan ƙasa, don ya jarraba su ya ga irin aikin kowa. Don haka duk wanda ya kafirce wa Allah da abin da manzanninsa suka zo da shi, to sakamakon kafircinsa da zunubinsa yana kansa, ba zai cutar da Allah da komai ba, kuma kafircin kafirai ba zai ƙara musu komai ba a wurin Allah sai matsananciyar ƙiyayya, da hasarar kawunansu da iyalansu da ayyukansu da ma mazaunansu na Aljanna, da a ce sun yi imani.
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ شُرَكَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ أَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ كِتَٰبٗا فَهُمۡ عَلَىٰ بَيِّنَتٖ مِّنۡهُۚ بَلۡ إِن يَعِدُ ٱلظَّٰلِمُونَ بَعۡضُهُم بَعۡضًا إِلَّا غُرُورًا
Open ayah 35:40Ka ce: “Ku ba ni labarin abokan tarayyar naku da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta daga ƙasa, ko kuma suna da wata tarayya ne a cikin (halittar) sammai, ko kuma Mun ba su wani littafi ne, saboda haka suke da wata hujja daga wajensa?” Ba haka ba ne, ba dai abin da azzalumai suke wa juna alƙawari da shi in ban da ruɗi.
۞إِنَّ ٱللَّهَ يُمۡسِكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ أَن تَزُولَاۚ وَلَئِن زَالَتَآ إِنۡ أَمۡسَكَهُمَا مِنۡ أَحَدٖ مِّنۢ بَعۡدِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا
Open ayah 35:41Lalle Allah ne Yake riƙe da sammai da ƙasa don kada su ruguje. Lallai kuwa idan da za su ruguje, to ba wani mai riƙe su in ba Shi ba. Lalle Shi (Allah) Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gafara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da dalilan Kaɗaitakarsa da ruguza hujjar mushirikai ta bauta wa wasu ba Allah ba, yayin da ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ƙalubalanci kafirai da su kawo wani abu ɗaya da allolinsu suka halitta a nan ƙasa, shin sun halicci duwatsunta ne ko ƙoramunta ko dabbobin cikinta? Ko kuma sun yi tarayya ne da Allah wajen halittar sammai? Ko kuma Allah ya ba su wani littafi ne wanda yake ɗauke da hujjar bautar wasu ba Allah ba? Duk waɗannan abubuwa ba ɗaya da ya faru, kafirai dai suna ruɗar junansu da ƙarerayi ne kawai, suna ingiza juna cikin ɓata da bautar wanin Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman Ƙudurarsa wadda da ita ce yake riƙe sammai da kasa don kada su gushe. Kuma da za a ƙaddara cewa za su gushe ɗin, to da babu wanda zai iya riƙe su ya hana su gushewa in ba shi ba. Sai dai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hukunta su yi ta zama kamar yadda ya halicce su tun farko don bayinsa su ci gaba da rayuwa a bayan ƙasa, suna amfana da ni’imominsa na sama da na ƙasa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, domin kuma su fahimci girman Ƙudurarsa, zukatansu su cika da girmama shi da gode masa, su kuma gane haƙurinsa da gafararsa waɗanda suka sanya ba ya gaggauto wa masu laifi azabarsa; yana jinkirta musu ne don su tuba su nemi gafararsa ya kuma gafarta musu.
وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَئِن جَآءَهُمۡ نَذِيرٞ لَّيَكُونُنَّ أَهۡدَىٰ مِنۡ إِحۡدَى ٱلۡأُمَمِۖ فَلَمَّا جَآءَهُمۡ نَذِيرٞ مَّا زَادَهُمۡ إِلَّا نُفُورًا
Open ayah 35:42Suka kuma rantse da Allah iya rantsuwarsu cewa, lallai idan mai gargaɗi ya zo musu, za su zamanto mafiya shiriya daga ɗayan al’ummu; sannan lokacin da mai gargaɗi ya zo musu ba abin da ya ƙara musu sai nisanta (daga shiriya).
ٱسۡتِكۡبَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَكۡرَ ٱلسَّيِّيِٕۚ وَلَا يَحِيقُ ٱلۡمَكۡرُ ٱلسَّيِّئُ إِلَّا بِأَهۡلِهِۦۚ فَهَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا سُنَّتَ ٱلۡأَوَّلِينَۚ فَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَبۡدِيلٗاۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَحۡوِيلًا
Open ayah 35:43Don girman kai a bayan ƙasa da kuma makirci mummuna. (Sakamakon) makirci mummuna kuwa ba ya sauka sai a kan masu shi. Ba abin da suke saurare in ban da sunnar da ta sami mutanen farko. Sannan ba za ka taɓa samun wani canji ba game da sunnar Allah; kuma ba za ka sami wani sauyi ba game da sunnar Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna irin yadda Ƙuraishawa suka riƙa rantsuwa iya rantsuwarsu cewa, idan Allah ya aiko musu da manzo wanda zai gargaɗe su game da azabar Allah kamar yadda ya aiko wa al’ummun da suka gabace su manzanni, to lalle sai sun fi waɗancan al’ummu shiriya da bin gaskiya. To amma bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da Manzonsa Muhammadu (ﷺ) yana gargaɗin su game da azabar Allah, wannan zuwan nasa bai ƙara musu komai ba sai nisantar gaskiya da ƙara ƙanƙame wa ƙaryar da suke kai, suka saɓa alƙawarin da suka yi rantsuwa a kansa, ba don komai ba sai don girman kai a bayan ƙasa da yaudarar mutane da ƙarya. Bugu da ƙari kuma suka shiga ƙulla makirce-makircen yadda za su cutar da Manzon Allah (ﷺ), to amma su sani cewa sakamakon wannan mummunan makirci da suke ƙullawa ba zai sauka a kan kowa ba sai a kansu, domin wannan ita ce sunnar Allah a rayuwa, su kuwa babu abin da suke saurare sai gamuwa da sunnar Allah da ta sami kafiran da suka gabace su, watau Allah ya hallaka su kamar yadda ya hallaka al’ummun da suka gabace su. Allah kuwa ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa, babu wani canji a sunnar Allah wanda zai hana azabar Allah ta sauka a kansu, ba kuma zai kautar da wannan azabar ba zuwa ga wasu daban ba su ba.
أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَكَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعۡجِزَهُۥ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَلِيمٗا قَدِيرٗا
Open ayah 35:44Shin ba su yi tafiya ba ne a cikin ƙasa, sai su ga yaya ƙarshen waɗanda suke gabaninsu ya kasance, alhali kuwa sun zamanto ƙarfafa fiye da su? Ba kuwa wani abu da zai gagari Allah a cikin sammai ko a cikin ƙasa. Lalle Shi Ya kasance Masani ne, Mai iko.
وَلَوۡ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِمَا كَسَبُواْ مَا تَرَكَ عَلَىٰ ظَهۡرِهَا مِن دَآبَّةٖ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِعِبَادِهِۦ بَصِيرَۢا
Open ayah 35:45Idan da Allah Yana (saurin) damƙar mutane saboda laifin da suka aikata, to da bai bar kowane mai rai ba a bayan ƙasa, sai dai kuma Yana saurara musu ne zuwa wani lokaci ƙayyadajje; to idan lokacin nasu ya zo, to lalle Allah Ya kasance Mai ganin bayinsa ne, (zai kuwa saka musu). A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya janyo hankalin kafiran Ƙuraishawa waɗanda suke tafiye-tafiye na kasuwanci zuwa garuruwan Sham da Iraƙi da Yaman da cewa, ba su ga yadda ƙarshen al’ummun da suka gabace su ya kasance ba bayan sun ƙaryata annabawansu? Ai Allah ya hallaka su baki ɗaya, duk kuwa da cewa sun fi su tsananin ƙarfi, amma ba su gagari Allah ba, domin babu abin da zai gagare shi a sammai ko a ƙasa, kuma lalle shi masanin abin da masu ƙaryata manzanninsu suke aikatawa ne, kuma mai ikon ya hallaka su ne idan ya ga dama babu mai iya hana shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa da zai gaggauto uƙubarsa ga mutane saboda miyagun ayyukansu da yawan laifuffukansu, to da ya hallaka duk wata halitta da ke tafiya a bayan ƙasa, to amma Allah yana saurara musu ne zuwa wani ƙayyadajjen lokaci, watau ranar alƙiyama, idan ta zo ne za su tabbatar da cewa lalle Allah mai ganin bayinsa ne da ayyukansu kuma zai yi musu sakayya a kan dukkan ayyukan da suka gabatar.