يس
Yaseen
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
يسٓ
Open ayah 36:1YA SIIN.
وَٱلۡقُرۡءَانِ ٱلۡحَكِيمِ
Open ayah 36:2Na rantse da Alƙur’ani mai hikima.
إِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 36:3Lalle kai (Manzon Allah) tabbas kana daga cikin manzanni.
عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 36:4(Kana) a kan tafarki madaidaici.
تَنزِيلَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ
Open ayah 36:5(Alƙur’ani) saukarwar (Allah) Mabuwayi Mai jin ƙai ne.
لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أُنذِرَ ءَابَآؤُهُمۡ فَهُمۡ غَٰفِلُونَ
Open ayah 36:6Don ka gargaɗi mutanen da ba a yi wa iyayensu gargaɗi ba, don haka kuwa suna cikin gafala.
لَقَدۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ عَلَىٰٓ أَكۡثَرِهِمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 36:7Haƙiƙa hukuncin Allah (na azaba) ya wajaba a kan mafiya yawansu, don ba za su yi imani ba.
إِنَّا جَعَلۡنَا فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ أَغۡلَٰلٗا فَهِيَ إِلَى ٱلۡأَذۡقَانِ فَهُم مُّقۡمَحُونَ
Open ayah 36:8Lalle Mun sanya ƙuƙumai a wuyoyinsu har zuwa haɓoɓinsu, don haka kawunansu a ɗage suke.
وَجَعَلۡنَا مِنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ سَدّٗا وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ سَدّٗا فَأَغۡشَيۡنَٰهُمۡ فَهُمۡ لَا يُبۡصِرُونَ
Open ayah 36:9Muka kuma sanya wani shamaki a gabansu da kuma shamaki a bayansu, sai Muka lulluɓe musu (idanuwa), don haka ba sa gani.
وَسَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ ءَأَنذَرۡتَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تُنذِرۡهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 36:10Kuma duk ɗaya ne a wurinsu ko ka yi musu gargaɗi ko ba ka yi musu gargaɗi ba, ba za su yi imani ba.
إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلذِّكۡرَ وَخَشِيَ ٱلرَّحۡمَٰنَ بِٱلۡغَيۡبِۖ فَبَشِّرۡهُ بِمَغۡفِرَةٖ وَأَجۡرٖ كَرِيمٍ
Open ayah 36:11Kana yin gargaɗi ne kawai ga wanda ya bi umarnin Alƙur’ani, ya kuma ji tsoron Allah ba tare da ya gan Shi ba; sai ka yi masa albishir da samun gafara da lada na karamci.
إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَنَكۡتُبُ مَا قَدَّمُواْ وَءَاثَٰرَهُمۡۚ وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ فِيٓ إِمَامٖ مُّبِينٖ
Open ayah 36:12Lalle Mu ne za Mu raya matattu, Muke kuma rubuta irin abubuwan da suka gabatar (a rayuwarsu) da kuma abin da suka bari a bayansu (bayan mutuwa). Kowane abu kuma Mun ƙididdige shi a cikin Lauhul-Mahafuzu. </b> Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da haruffa guda biyu, watau ‘Ya\' da ‘Sin’, waɗanda suke ishara zuwa ga mu’ujizar Alƙur’ani. [Duba tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara ]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da Alƙur’ani wanda ayoyinsa suke cike da hikima da zubi mai matuƙar tsari da azanci, wanda ƙarya ba ta zuwa masa ta gabansa ko ta bayansa. Sai kuma Allah ya tabbatar da manzancin Annabi (ﷺ) da cewa lalle shi yana ɗaya daga cikin manzannin da Allah ya aiko zuwa ga bayinsa don su umarce su da bautar sa shi kaɗai ba tare da haɗa shi da wani ba, don haka ba shi ne farau cikin manzanni ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa Manzonsa (ﷺ) yana kan tafarki madaidaici, yana bin miƙaƙƙiyar hanyar shari’a, kuma ita wannan hanyar saukakkiya ce daga Allah Mabuwayin Sarki wanda babu mai iya karawa da shi, mai rahama ga bayinsa muminai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa manufar saukar masa da waccan shari’ar da ba shi Alƙur’ani mai girma ita ce, don ya yi wa Larabawa gargaɗi da shi, waɗanda wani annabi bai zo wa iyayensu ba, ya gargaɗe su a kan abin da suke aikatawa na shirka, don haka suna cikin gafala da ɗimuwa ta rashin sanin Tauhidi da imani. Kuma haka abin ya kasance game da duk wata al’umma wadda ta rasa mai yi mata gargaɗi, don haka takan zama cikin tsananin buƙatar aika mata da manzo domin nuna mata tafarki madaidaici. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa yawancin waɗanda ya aika wa manzanninsa suke kiran su zuwa bauta masa shi kaɗai da ƙaurace wa shirka, sun kafirce wa kiran annabawansu, sai azabar Allah ta tabbata a kansu, domin ba za su yi imani da Allah da Manzonsa ba, ba kuma za su yi aiki da gaskiyar da ta zo musu ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwatanta su da mutanen da aka sanya ƙuƙumi a wuyoyinsu aka haɗa hannayensu a ƙarƙashin haɓoɓinsu aka ɗaure tamau, sai ya zamanto dole ne su ɗaga kawunansu sama don ba za su iya yin ƙasa-ƙasa da su ba. To waɗannan mutane da aka ci galaba ne a kansu ba za su iya yin imani ba, kuma ba za su miƙa wuya ga Allah ba, kuma ba za su iya rusuna kawunansu gare shi ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara da bayyana cewa, ya sanya shamaki tsakaninsu a gabansu da kuma bayansu wanda ya katange su daga ba da gaskiya da amsa kiran Allah, ya kuma rufe idanunsu ba sa ganin gaskiya su amfana da ita. Wannan kuwa ya faru ne gare su bayan taurin kansu da dogewarsu a kan kafirci da bushewar zukatansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa, waɗannan kafiran ko ya yi musu gargaɗi ko kar ya yi musu gargaɗi duka ɗaya ne a gare su ba za su yi imani da gaskiyar da ya zo musu da ita daga Allah ba. Waɗanda kawai za su amfana da gargaɗinsa su ne waɗanda suka gaskata Alƙur’ani, suka kuma ji tsoron Allah ba tare da suna ganin sa ba, ko lokacin da suka kaɗaita babu mai ganin su sai Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya yi wa duk wani mai irin wannan siffa albishir da samun gafara daga Allah da kuma wani babban lada wanda yake jiran sa a lahira, watau shiga Aljanna. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa zai tashi matattu don yi musu sakayya a kan ayyukansu, kuma shi ne yake rubuta duk abin da suka aikata a rayuwarsu ta duniya mai kyau ko mummuna, har ma da ayyukan da suka bar gurabensu masu kyau a bayan mutuwarsu, kamar sadaka mai gudana, ko marasa kyau kamar aikin kafirci, kuma ya ƙididdige komai a cikin littafin Lauhul Mahfuzu, ba abin da yake ɓuya gare shi. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An samu ƙarin filayen da babu kowa a kusa da Masallacin Annabi (ﷺ) sai ƙabilar Banu Salima suka yi nufin dawowa kusa da Masallacin. Da labari ya kai ga Manzon Allah (ﷺ) sai ya ce musu: “Labari ya zo mini cewa kuna son ku dawo kusa da Masallaci?” Sai suka ce: “E, haka ne, mun so mu yi haka ya Manzon Allah.” Sai ya ce: “Ya ku Banu Salima, ku yi zamanku a unguwanninku za a rubuta muku ladan tattakinku (watau na zuwa Masallaci).” [Muslim #665].
وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلًا أَصۡحَٰبَ ٱلۡقَرۡيَةِ إِذۡ جَآءَهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Open ayah 36:13Kuma ka ba su misali da mutanen wata alƙarya lokacin da manzannin suka zo mata.
إِذۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمُ ٱثۡنَيۡنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزۡنَا بِثَالِثٖ فَقَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَيۡكُم مُّرۡسَلُونَ
Open ayah 36:14A yayin da Muka aika musu (manzanni) biyu sai suka ƙaryata su, sannan Muka ƙarfafe su da na uku, sai suka ce: “Lalle mu manzanni ne zuwa gare ku.”
قَالُواْ مَآ أَنتُمۡ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا وَمَآ أَنزَلَ ٱلرَّحۡمَٰنُ مِن شَيۡءٍ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا تَكۡذِبُونَ
Open ayah 36:15Suka ce: “Ku ai ba kowa ba ne face mutane kamarmu, kuma (Allah) Mai rahama bai saukar da komai ba, ku dai ba abin da kuke yi sai ƙarya.”
قَالُواْ رَبُّنَا يَعۡلَمُ إِنَّآ إِلَيۡكُمۡ لَمُرۡسَلُونَ
Open ayah 36:16Suka ce: “Ubangijinmu Yana sane da cewa mu lalle tabbas manzanni ne zuwa gare ku.
وَمَا عَلَيۡنَآ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 36:17“Kuma babu wani abu a kanmu sai isar da aike bayyananne.”
قَالُوٓاْ إِنَّا تَطَيَّرۡنَا بِكُمۡۖ لَئِن لَّمۡ تَنتَهُواْ لَنَرۡجُمَنَّكُمۡ وَلَيَمَسَّنَّكُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 36:18Suka ce: “Mu dai lalle mun camfa ku, tabbas idan ba ku bari ba to za mu jefe ku, kuma tabbas za ku gamu da azaba mai raɗaɗi daga gare mu.”
قَالُواْ طَٰٓئِرُكُم مَّعَكُمۡ أَئِن ذُكِّرۡتُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ مُّسۡرِفُونَ
Open ayah 36:19Suka ce: “Camfinku ya ƙare a kanku. Yanzu don an yi muku gargaɗi ne (za ku faɗi haka?) A’a, ku dai mutane ne maɓarnata.” </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ba wa kafirai masu ƙaryata shi labarin mutanen wata alƙarya da su ma suka ƙaryata manzannin da Allah ya aika musu suka yi jayayya da su, daga ƙarshe aka hallaka su baki ɗaya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya fara aika musu da manzanni biyu ne domin su kirawo su zuwa ga kaɗaita Allah da bauta, to amma sai suka ƙaryata su suka ƙi yin imani da su. Sai Allah ya ƙarfafe su da wani manzo na uku ko wannan zai taimaka su yi imani. Waɗannan manzanni uku suka shaida wa mutanen alƙaryar cewa, lalle su manzannin Allah ne da ya aiko su don su kirawo su zuwa kaɗaita Allah da bauta da bin dokokinsa. To amma duk da haka sai mutanen alƙaryar suka ce, su fa ba za su yi imani da su ba, domin su ba su yarda an aiko su ba, saboda suna ganin su ma mutane ne kamarsu, ba su fi su da komai ba. Hasali ma dai ba su yarda cewa Allah ya saukar da wani wahayi daga sama ba, don haka su sun ɗauke su a matsayin masu yi wa Allah ƙarya suna cewa wai ya aiko su zuwa gare su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mana martanin da manzannin nan uku suka mayar wa mutanen wannan alƙaryar yayin da suka tabbatar musu da cewa lalle Allah wanda ya aiko su ya san su manzanninsa ne, domin da ƙarya suke yi masa to da ya tona asirinsu ya kuma kunyata su. Don haka wannan ma kaɗai ya isa hujja a kan gaskiyar manzancinsu. Sannan suka nuna musu cewa su ba wani abu suka zo nema a wurinsu ba, su kawai buƙatarsu ita ce su isar da saƙon Allah mabayyani a gare su, amma ba su ne masu kimsa shiriya a zukatan mutane ba, wannan aikin Allah ne shi kaɗai. To amma maimakon mutanen alƙaryar su yi murna da wannan alheri da ya zo musu su miƙa wuya, sai kawai suka shiga tuhumar waɗannan manzanni uku da cewa sun jawo musu masifa da sharri, domin kuwa sun camfa su. Suka fara razana su da cewa, lalle idan ba su daina wannan wa’azin nasu na cewa a bauta wa Allah shi kaɗai ba a kuma yarda da manzancinsu, tabbas za su jefe su da duwatsu har lahira, kuma za su ɗanɗana musu azaba mai raɗaɗi. Sai manzannin nan suka ba su amsa da cewa camfinsu a kansu zai ƙare, saboda kafircinsu da rashin imani da manzannin Allah da suka yi. Suka kuma nuna mamakinsu game da wannan furuci na kafirai, domin babu dalilin da zai sa su riƙa camfa mutanen da suke tunatar da su Allah suna gargaɗin su game da azabarsa. To amma ba komai ya jawo musu hakan ba sai zarmewa da suka yi wajen kafirci da saɓon Allah.
وَجَآءَ مِنۡ أَقۡصَا ٱلۡمَدِينَةِ رَجُلٞ يَسۡعَىٰ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُواْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 36:20Wani mutum kuma ya zo daga can ƙarshen gari yana sauri ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi waɗannan manzannin.
ٱتَّبِعُواْ مَن لَّا يَسۡـَٔلُكُمۡ أَجۡرٗا وَهُم مُّهۡتَدُونَ
Open ayah 36:21“Ku bi waɗanda ba sa tambayar ku wani lada, ga su kuma shiryayyu.
وَمَا لِيَ لَآ أَعۡبُدُ ٱلَّذِي فَطَرَنِي وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 36:22“Ni kuma me zai hana ni in bauta wa wanda Ya halicce ni, kuma gare Shi ne za a komar da ku?
ءَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً إِن يُرِدۡنِ ٱلرَّحۡمَٰنُ بِضُرّٖ لَّا تُغۡنِ عَنِّي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يُنقِذُونِ
Open ayah 36:23“Yanzu na riƙi wasu ababen bauta ba Shi ba, alhali kuwa idan (Allah) Mai rahama Ya nufe ni da wata cuta, cetonsu ba zai amfana min komai ba, kuma ba za su iya tsamo ni ba?
إِنِّيٓ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ
Open ayah 36:24“Lalle ni idan na yi haka to tabbas na zama cikin ɓata mabayyani.
إِنِّيٓ ءَامَنتُ بِرَبِّكُمۡ فَٱسۡمَعُونِ
Open ayah 36:25“Lalle ni na yi imani da Ubangijinku, sai ku saurare ni.”
قِيلَ ٱدۡخُلِ ٱلۡجَنَّةَۖ قَالَ يَٰلَيۡتَ قَوۡمِي يَعۡلَمُونَ
Open ayah 36:26Aka ce (da shi): “Shiga Aljanna.” Ya ce: “Kaicon mutanena, ina ma da suna sane?
بِمَا غَفَرَ لِي رَبِّي وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ
Open ayah 36:27“Da gafarar da Ubangijina Ya yi min, Ya kuma sanya ni cikin waɗanda aka karrama?”
۞وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ مِنۢ بَعۡدِهِۦ مِن جُندٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا كُنَّا مُنزِلِينَ
Open ayah 36:28Ba Mu kuma saukar da wata runduna (ta mala’iku) a kan mutanensa daga sama ba a bayansa, ba Mu kuma saba saukarwa ba.
إِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَإِذَا هُمۡ خَٰمِدُونَ
Open ayah 36:29Ba abin da ya kasance sai tsawa guda ɗaya, sai ga su matattu. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wani mutum daga wani wuri mai nisa na wannan birni wanda ya sami labarin da’awar waɗannan manzanni uku da yadda mutanensu suka ƙaryata su, ya zo don yi musu nasiha yana umartar su da su bi abin da waɗannan manzanni suka zo musu da shi. Ya tabbatar musu da cewa ba wani lada suke nema a wajensu ba, sun zo ne kawai don su isar musu da saƙon Allah, kuma su mutane ne shiryayyu masu bin tafarkin gaskiya, don haka ya dace su bi abin da suke kiran su a kai. To amma duk da wannan nasiha da ya yi wa mutanensa, wannan bai sa sun yi imani ba, sai ma suka riƙa zargin sa da sukan sa game da bin waɗannan manzannin. Sai shi kuma ya mayar musu da martani cewa, me zai hana shi ya bauta wa Allah wanda ya ƙaga halittarsa, ya wadata shi da buƙatunsa, su ma kuma me zai hana su bauta wa Allah wanda ya halicce su kuma wurinsa ne gaba ɗaya za a mayar da su don ya yi musu hisabi a kan ayyukansu? Ya nuna musu rashin yardarsa da bautar wani ba Allah ba da cewa, yanzu ta yaya zai riƙi wasu abubuwan bauta ba Allah ba yana bauta musu? Waɗannan ababen bauta kuma ba su da wani amfani ko kaɗan, domin idan Allah mai rahama ya nufe shi da wani mummunan abu ba za su iya kare shi ba, domin cetonsu ba zai wadatar da shi da komai ba, ba kuma za su iya kuɓutar da shi daga azabar Allah ba idan har ya mutu a kan kafirci bai tuba ba. Don haka idan ya tsaya a kan bautar su ba Allah ba to lalle ya yi babban ganganci, domin ya bar wanda ya cancanci bauta ya kama wanda bai cancanta ba. Ya ma fito fili ya faɗa musu shi fa ya yi imani da Ubangijinsa kuma su ma shi ne Ubangijinsu, don haka su saurari nasiharsa su yi aiki da ita, kuma barazanar kisa da suke yi masa shi ba ta dame shi ba. To amma sai suka kashe shi domin ganin ya matsa musu da nasiha, nan take bayan ya yi shahada sai aka ce masa ya shiga Aljanna. To yayin da ya shiga cikinta ya ga irin karamcin da aka yi masa da ɗimbin ni’imomi da aka tanadar masa sai ya yi burin ina ma a ce mutanensa waɗanda suka ƙaryata shi suka kuma kashe shi sun ga irin garaɓasar da yake ciki da gafarar zunubansa da ya samu da karamcin Ubangijinsa a gare shi, don su ma su yi imani su sami irin sakamakon da ya samu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya hallakar da waɗannan kafirai da suka ƙaryata manzanninsa uku, suka kuma kashe mutumin da ya yi musu nasiha da cewa, bai buƙaci saukar da mala’iku daga sama ba don halaka su, domin a wurinsa al’amarin mai matuƙar sauƙi ne, sai kawai Allah ya ƙaddara hallakarsu ta zamanto tsawa guda ɗaya ce daga sama, kawai sai ga su a mace ba rai, kamar wutar da take ci balbal sai kawai a ga ta mutu murus ba ita ba alamarta.
يَٰحَسۡرَةً عَلَى ٱلۡعِبَادِۚ مَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 36:30Nadama ta tabbata ga bayi (masu ƙaryatawa), <b>ba wani manzo da zai zo musu sai sun zamanto suna yi masa izgili.
أَلَمۡ يَرَوۡاْ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ أَنَّهُمۡ إِلَيۡهِمۡ لَا يَرۡجِعُونَ
Open ayah 36:31Shin ba sa gani ne, al’ummu nawa ne Muka hallaka kafin su, cewa lalle kuwa ba sa dawowa zuwa gare su?
وَإِن كُلّٞ لَّمَّا جَمِيعٞ لَّدَيۡنَا مُحۡضَرُونَ
Open ayah 36:32Kuma duk gaba ɗayansu wurinmu za a tattara su. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matsayin kafiran da suke ƙaryata manzanninsa suke yi musu izgili da cewa, matsayi ne mai ban takaici da ban haushi, domin kuwa nadamarsu za ta yi tsawo a ranar alƙiyama inda ba za ta yi musu wani amfani ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara jan hankalinsu da cewa shin ba su ga abin izina ba game da al’ummun da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallakar gabaninsu, kuma sun riga sun mutu ba za su ƙara dawowa duniya ba, sun je sun tarar da ayyukansu da suka gabatar waɗanda Allah zai yi musu sakamako a kansu? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa duk al’ummu gaba ɗayansu za a tattaro su a gabansa, domin ya yi musu hukunci na adalci ba tare da an zalunci kowa da komai ba.
وَءَايَةٞ لَّهُمُ ٱلۡأَرۡضُ ٱلۡمَيۡتَةُ أَحۡيَيۡنَٰهَا وَأَخۡرَجۡنَا مِنۡهَا حَبّٗا فَمِنۡهُ يَأۡكُلُونَ
Open ayah 36:33Kuma wata aya ce a gare su (ganin) matacciyar ƙasar da Muka raya ta Muka fitar da ƙwaya daga gare ta, wadda kuma ita ce suke ci.
وَجَعَلۡنَا فِيهَا جَنَّٰتٖ مِّن نَّخِيلٖ وَأَعۡنَٰبٖ وَفَجَّرۡنَا فِيهَا مِنَ ٱلۡعُيُونِ
Open ayah 36:34Muka kuma sanya gonaki na dabinai da na inabai a cikinta (ƙasar), Muka kuma ɓuɓɓugo da idanuwan ruwa daga gare ta.
لِيَأۡكُلُواْ مِن ثَمَرِهِۦ وَمَا عَمِلَتۡهُ أَيۡدِيهِمۡۚ أَفَلَا يَشۡكُرُونَ
Open ayah 36:35Don su ci daga ‘ya’yan (itacenta) da kuma abin da hannanyensu suka aikata. Me ya sa ba za su riƙa godiya ba?
سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَزۡوَٰجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ وَمِنۡ أَنفُسِهِمۡ وَمِمَّا لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 36:36Tsarki ya tabbata ga wanda Ya halicci dangogin komai na maza da mata daga abin da ƙasa take tsirowa, kuma daga su kansu, da ma daga abin da ba su sani ba. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu manyan dalilai masu nuna cikar Ƙudurarsa ta iya tayar da matattu ya yi musu hisabi a ranar alƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya nuna musu wata ayarsa game da ƙasar da ta riga ta ƙeƙashe, amma sai ya saukar mata ruwan sama ya raya ta da shi, ya fitar wa bayinsa dangogin tsirrai da shuke-shuke iri-iri wanda za su ci da wanda dabbobinsu za su ci. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sanya gonakin dabino da na inabi a cikin wannan ƙasar da ya raya da ruwan sama, sannan kuma ya ɓuɓɓugo da idanuwan ruwa daga cikinta wanda za a shayar da shuke-shuke da shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu haka ne don su ci ‘ya’yan itatuwan da ya ni’imta su da su, ba don ƙarfinsu ko ƙwarewarsu ba, to me ya hana su gode wa Allah a kan wannan gagarumar ni’ima da ya yi musu, su bauta masa shi kaɗai ba tare da haɗa shi da abokan tarayya ba, su kuma yi imani da manzanninsa? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata hikima tasa da cewa, shi ne wanda ya halicci kowane jinsin abu bibiyu namiji da mace na tsirrai da shuke-shuke da ma su kansu mutane, ya kuma yi su maza da mata jinsi daban-daban, har ma da sauran wasu halittu da ba su sani ba, na kan tudu da na cikin ruwa. Babu shakka duk wanda yake da ikon yin irin wannan aiki, tabbas mai iko ne a kan tayar da matacce bayan mutuwarsa, kuma shi ne kaɗai ya cancanta a bauta masa ba tare da shirka ba.
وَءَايَةٞ لَّهُمُ ٱلَّيۡلُ نَسۡلَخُ مِنۡهُ ٱلنَّهَارَ فَإِذَا هُم مُّظۡلِمُونَ
Open ayah 36:37Dare ma aya ne a gare su, wanda Muka saɓule yini daga gare shi, sai ga su cikin duhu.
وَٱلشَّمۡسُ تَجۡرِي لِمُسۡتَقَرّٖ لَّهَاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ
Open ayah 36:38Rana kuma tana gudu zuwa wurin da aka iyakance mata. Wannan tsari ne na (Allah) Mabuwayi, Masani.
وَٱلۡقَمَرَ قَدَّرۡنَٰهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَٱلۡعُرۡجُونِ ٱلۡقَدِيمِ
Open ayah 36:39Wata kuma Mun ƙaddara masa masaukai, har ya koma kamar tsohuwar zarbar dabino.
لَا ٱلشَّمۡسُ يَنۢبَغِي لَهَآ أَن تُدۡرِكَ ٱلۡقَمَرَ وَلَا ٱلَّيۡلُ سَابِقُ ٱلنَّهَارِۚ وَكُلّٞ فِي فَلَكٖ يَسۡبَحُونَ
Open ayah 36:40Ba zai yiwu rana ta riski wata ba, dare kuma ba zai riga yini ba. Kowanne kuwa yana iyo ne a cikin falaki. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana manyan ayoyinsa masu nuna cikar Ƙudurarsa da girman ikonsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa kafirai cewa, dare ma wata aya ce a gare su da ke tabbatar da yiwuwar tashi bayan mutuwa, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) yana gusar da rana daga dare sai kawai mutane su gan su a cikin duhu. Hakanan ma yakan kawar da wannan duhun na dare wanda ya game ko’ina da ina, sai kawai a ga rana ta fito ta haskaka sasannin ƙasa, kowa kuma sai ya fita neman abincinsa. Don haka ita rana haka take tutur tana gudu ne zuwa matabbatarta inda aka iyakance mata ba ta ƙetare shi, ba ta yin gaban kanta. Wannan gudu da take yi kuwa tsari ne na Allah mabuwayi cikin mulkinsa masanin ɗaukacin halittunsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya ƙaddara wa wata nasa masaukai, a kowane dare yana da nasa masauki har sanda girmansa ya cika, sannan ya dawo yana ƙanƙancewa har ya zama siriri sosai kamar zarbar dabino wadda saboda daɗewa ta sirance ta tanƙware ta zama kamar baka. Wannan ita ce alamar ƙarshen kwanakin kowane wata. Sannan Allah ya tabbatar da cewa waɗannan ayoyi na rana da wata da dare da yini duka suna gudana ne a kan tsarin da ya ajiye su a kai, babu mai wuce iyakarsa, watau ba zai yiwu rana ta riski wata ba har ta canza masa hanyar tafiyarsa ko ta tafiyar da haskensa; hakanan ba zai yiwu dare ya riga yini har ya shiga cikinsa kafin ƙarewar lokacinsa ba. Duk waɗannan halittu da sauran manyan taurari kowanne cikinsu yana da hanyarsa ta musamman wadda aka tsara masa yake tafiya a kanta koyaushe da izinin Allah. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na kasance a masallaci tare da Manzon Allah (ﷺ) lokacin faɗuwar rana sai ya ce: “Ya kai Abu Zarrin, ka kuwa san inda rana take faɗuwa?” Sai na ce: “Allah da Manzonsa ne mafi sani.” Sai ya ce: “Lalle tana tafiya ne har sai ta yi sujjada a ƙarƙashin Al-Arshi, wannan shi ne faɗin Allah: “Rana kuma tana gudu zuwa matabbatarta, wannan tsari ne na Mabuwayi, Masani.” [Bukhari #4802 da Muslim #159].
وَءَايَةٞ لَّهُمۡ أَنَّا حَمَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُمۡ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
Open ayah 36:41Kuma wata aya ce a gare su cewa Mu Muka ɗauki iyayensu a cikin jirgin ruwa wanda aka maƙare.
وَخَلَقۡنَا لَهُم مِّن مِّثۡلِهِۦ مَا يَرۡكَبُونَ
Open ayah 36:42Muka kuma halitta musu abin da suke hawa kwatankwacinsa.
وَإِن نَّشَأۡ نُغۡرِقۡهُمۡ فَلَا صَرِيخَ لَهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنقَذُونَ
Open ayah 36:43Idan kuwa da Mun ga dama, sai Mu nutsar da su, don haka babu wani mai taimakon su, ba kuma za a kuɓutar da su ba.
إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّنَّا وَمَتَٰعًا إِلَىٰ حِينٖ
Open ayah 36:44Sai dai rahama daga gare Mu da kuma jin daɗi zuwa wani lokaci. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya daɗa bayyana wata ayar ce mai nuna girman Ƙudurarsa da kuma rahamarsa ga bayinsa da cewa, shi ne ya tserar da zurriyar Annabi Adamu a zamanin Annabi Nuhu bayan ɓarkewar ruwan Ɗufana, a cikin jirgin ruwa wanda yake maƙare da halittun Allah daban-daban, kamar mutane da dabbobi da tsuntsaye waɗanda Allah ya umarci Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ɗauka a cikin jirgin; daga kowane jinsi kuma ya ɗauki namiji da mace. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wata ayarsa mai tabbatar da Kaɗaitakarsa da ni’imarsa ga bayinsa da cewa, shi ne ya halitta musu wasu ababen hawan daban bayan jirgin ruwa waɗanda suke hawa domin zirga-zirgarsu a tudu ko a ruwa. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda yake yalwata musu falalarsa a koyaushe, domin da ya ga dama da sai ya nutsar da su a cikin ruwan babu kuma mai iya taimaka musu ya hana shi abin da ya yi niyyar aikatawa ko ya tserar da su yayin da ya nutsar da su, sai dai idan shi ne ya nufe su da rahama sai ya kuɓutar da su su dawo su ci gaba da more rayuwar duniya zuwa ƙarshen taƙaitaccen lokacin da aka ƙayyade musu. Ya kuwa yi musu haka ne domin su ɗauki darasi da izina.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّقُواْ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيكُمۡ وَمَا خَلۡفَكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Open ayah 36:45Idan kuwa aka ce da su: “Ku kiyayi abin da yake gabanku da abin da yake bayanku, don a ji ƙan ku”, (sai su bijire).
وَمَا تَأۡتِيهِم مِّنۡ ءَايَةٖ مِّنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِمۡ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ
Open ayah 36:46Babu wata aya daga ayoyin Ubangijinsu da za ta zo musu sai sun kasance masu bijire mata.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ أَنفِقُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنُطۡعِمُ مَن لَّوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ أَطۡعَمَهُۥٓ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 36:47Idan kuma aka ce da su: “Ku ciyar daga abin da Allah Ya arzuta ku,” sai waɗanda suka kafirta su ce wa waɗanda suka yi imani: “Yanzu ma ciyar da wanda, da Allah Ya ga dama da ya ciyar da shi? Ba abin da kuke ciki in ban da ɓata mabayyani.” </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai suka yi ta bijire wa Allah duk da ayoyin da yake nuna musu da tsoratarwar da yake yi musu da cewa, duk sanda aka gargaɗe su game da ranar lahira wadda suke fuskanta da abubuwan ban tsoro da ke cikinta, aka kuma yi musu kashedi game da duniya wadda suke ba ta baya, domin fatan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu baiwa da rahamarsa, sai su ƙi sauraron abin da ake gaya musu, su yi watsi da duk wani gargaɗi da ake yi musu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk lokacin da ayoyin Allah suka zo musu masu ɗauke da dalilai a kan Tauhidi da bayanin bautar Allah shi kaɗai, sai su bijire musu su ƙi tsayawa su wa’azantu da su. Sannan kuma idan an neme su da su taimaki talakawa da mabuƙata da dukiyar da Allah ya arzuta su da ita sai su yi ƙememe, har ma su riƙa faɗin wai don me za a ce su taimaka wa wasu, ai tunda aka gan su a cikin talauci da rashi, to da ma haka Allah yake son ya gan su, domin da ya ga dama ai shi ne zai ciyar da su ba su ba, don haka wai su ba za su yarda su saɓa wa muradin Allah ba. Suka kuma nuna wa muminai cewa umarnin da suke yi musu na ciyar da wasu kuskure ne ƙarara, kuma ba gaskiya ne ba.
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 36:48Suna kuma cewa: “Yaushe ne wannan alƙawarin, idan kun kasance masu gaskiya?”
مَا يَنظُرُونَ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ تَأۡخُذُهُمۡ وَهُمۡ يَخِصِّمُونَ
Open ayah 36:49Ba abin da suke sauraro sai tsawa guda ɗaya da za ta far musu, a yayin da suke cikin hayaniyar rayuwa.
فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ تَوۡصِيَةٗ وَلَآ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمۡ يَرۡجِعُونَ
Open ayah 36:50Don haka ba za su sami damar yin wata wasiyya ba, kuma za su iya koma wa wajen iyalinsu ba.
وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَإِذَا هُم مِّنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ يَنسِلُونَ
Open ayah 36:51Aka kuma busa ƙaho, sai ga su suna fitowa daga ƙaburbura zuwa wurin Ubangijinsu.
قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا مَنۢ بَعَثَنَا مِن مَّرۡقَدِنَاۜۗ هَٰذَا مَا وَعَدَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَصَدَقَ ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Open ayah 36:52Suka ce: “Kaiconmu, wane ne ya tashe mu daga makwancinmu?” (Sai a ce da su): “Ai wannnan shi ne abin da (Allah) Mai rahama Ya yi alƙawarinsa, manzanni kuma sun yi gaskiya.”
إِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَإِذَا هُمۡ جَمِيعٞ لَّدَيۡنَا مُحۡضَرُونَ
Open ayah 36:53Ba abin da zai kasance sai tsawa guda ɗaya, sai ga su gaba ɗaya an tattaro su gabanmu.
فَٱلۡيَوۡمَ لَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗا وَلَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 36:54To a yau fa ba za a zalunci wani rai da komai ba, ba kuma za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin yadda kafirai suke ƙaryata zuwan ranar alƙiyama, suna ganin ba gaskiya muminai suke faɗa musu ba yayin da suke gargaɗin su game da zuwan wannan rana, da abubuwan tsoro da ta ƙunsa, har ma suna yi musu izgili da cewa yaushe ne ma ranar za ta zo, domin an daɗe ana yi musu alƙawarin zuwanta amma su har yanzu shiru suke ji. Sai aka mayar musu da martani cewa, ba abin da suke sauraro sai busar ƙaho ta farko da mala’ika zai yi, sai kwatsam ba zato ba tsammani suna tsaka da hayaniyarsu ta rayuwa, kamar ciniki ko noma ko kiwo da sauransu, sai ta auko musu ba shiri. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da wannan busar ƙahon ta shammace su, to ba za su sami damar ko da yin wasiyya ga junansu ba, ba ma za su iya komawa gidajensu wajen iyalansu ba, a nan take za su mutu. Daga nan kuma sai a yi busa ta biyu domin tashi, to a nan ne mutane za su riƙa fitowa daga ƙaburburansu cikin gaggawa a firgice domin yi musu hisabi da sakamako. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a wannan ranar kafirai masu ƙaryata tashin alƙiyama za su shiga cikin takaici da nadama, har ma suna tambayar cewa, wane ne ya tashe su daga ƙaburburansu? To sai a amsa musu da cewa, ai da ma wannan shi ne abin da Allah ya yi alƙawarin aukuwarsa, ga shi kuwa ya auku, kuma manzannin Allah sun yi gaskiya a kan duk abin da suka isar na saƙon Ubangijinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da cewa al’amarin tashin halittu da ransu daga ƙaburbura ba wani abu ne mai wahalarwa ko ɗaukan wani lokaci a wajensa ba; kawai busa ce ta biyu za a yi a ƙaho sai duk halittu gaba ɗaya su tattara gaban Allah domin yi musu hisabi. A wannan ranar kuma hukunci za a yi na adalci ga kowa da kowa, ba wani da za a zalunce shi ko a tauye wa masu haƙƙi haƙƙinsu, ba kuma za a ƙara wa wani laifin da bai aikata ba; kowa za a saka masa da abin da ya aikata a duniya na alheri ko na sharri.
إِنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ ٱلۡيَوۡمَ فِي شُغُلٖ فَٰكِهُونَ
Open ayah 36:55Lalle ‘yan Aljanna a yau suna cikin shagali, suna masu farin ciki.
هُمۡ وَأَزۡوَٰجُهُمۡ فِي ظِلَٰلٍ عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ مُتَّكِـُٔونَ
Open ayah 36:56Su da matansu suna cikin inuwoyi kishingiɗe a kan gadaje.
لَهُمۡ فِيهَا فَٰكِهَةٞ وَلَهُم مَّا يَدَّعُونَ
Open ayah 36:57Suna da kayan marmari a cikinta, suna kuma da duk irin abin da suke nema.
سَلَٰمٞ قَوۡلٗا مِّن رَّبّٖ رَّحِيمٖ
Open ayah 36:58Sallama (za a riƙa yi musu), <b> magana ce daga Ubangiji Mai rahama. </b> A waɗannan ayoyi kuwa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon muminai ne a lahira, inda ya nuna cewa ‘yan Aljanna a ranar za su zamanto cikin shagali na ni’ima, babu tunanin wasu abubuwa a gabansu, saboda ni’imomin da aka tanadar musu na Aljanna da babban rabo da za su samu, don haka a ranar cike suke da murna da jin daɗi, suna kishingiɗe tare da matansu a kan karagu na alfarma cikin inuwoyin Aljanna. Wannan yana nuna kamalar hutu da nutsuwa da jin daɗi marar iyaka da za su samu a wannan ranar. Bugu da ƙari kuma za a tanadar musu kayan marmari iri-iri, kamar inabi da rumman da ɓaure. Duk wani abu da za su buƙata na jin daɗi da morewa, za su same shi ba tare da wata wahala ko ɓata lokaci ba. Sannan abin da ya fi komai daɗi da za su dace da shi a wannan rana shi ne, sallama daga Allah Ubangijinsu. Da zarar sun samu kai wa ga wannan, to sun sami duk wani aminci da jin daɗin da babu kamarsa, domin sun dace da gaisuwar da babu abin da ya kai ta daraja da ɗaukaka.
وَٱمۡتَٰزُواْ ٱلۡيَوۡمَ أَيُّهَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Open ayah 36:59Kuma (za a ce): “Ku ware a yau, ya ku waɗannan masu manyan laifuka.”
۞أَلَمۡ أَعۡهَدۡ إِلَيۡكُمۡ يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ أَن لَّا تَعۡبُدُواْ ٱلشَّيۡطَٰنَۖ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Open ayah 36:60Yanzu ban umarce ku ba, ya ku ‘yan’adam, da cewa kada ku bauta wa Shaiɗan; lalle shi maƙiyi ne mai bayyana (ƙiyayya)?
وَأَنِ ٱعۡبُدُونِيۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
Open ayah 36:61Kuma ku bauta min. Wannan shi ne tafarki madaidaici.
وَلَقَدۡ أَضَلَّ مِنكُمۡ جِبِلّٗا كَثِيرًاۖ أَفَلَمۡ تَكُونُواْ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 36:62Haƙiƙa kuma (Shaiɗan) ya ɓatar da halittu masu yawa; shin ba za ku hankalta ba?
هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ
Open ayah 36:63Wannan ita ce Jahannamar da ta kasance ana yi muku alƙawarinta.
ٱصۡلَوۡهَا ٱلۡيَوۡمَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ
Open ayah 36:64Ku shige ta a yau saboda kafircin da kuke yi.
ٱلۡيَوۡمَ نَخۡتِمُ عَلَىٰٓ أَفۡوَٰهِهِمۡ وَتُكَلِّمُنَآ أَيۡدِيهِمۡ وَتَشۡهَدُ أَرۡجُلُهُم بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 36:65A yau za Mu toshe bakunansu, hannayensu su yi mana magana, ƙafafuwansu kuma su ba da shaidar irin abin da suka kasance suna aikatawa.
وَلَوۡ نَشَآءُ لَطَمَسۡنَا عَلَىٰٓ أَعۡيُنِهِمۡ فَٱسۡتَبَقُواْ ٱلصِّرَٰطَ فَأَنَّىٰ يُبۡصِرُونَ
Open ayah 36:66Da kuma Mun ga dama da sai Mu shafe idanuwansu su riƙa rige-rigen hawan siraɗi, to ta yaya za su iya gani (a wannan lokaci)?
وَلَوۡ نَشَآءُ لَمَسَخۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ مَكَانَتِهِمۡ فَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ مُضِيّٗا وَلَا يَرۡجِعُونَ
Open ayah 36:67Da kuma Mun ga dama da sai Mu jirkita halittarsu a inda suke, saboda haka ba za su iya ci gaba da tafiya ba, ba kuma za su iya dawowa ba.
وَمَن نُّعَمِّرۡهُ نُنَكِّسۡهُ فِي ٱلۡخَلۡقِۚ أَفَلَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 36:68Wanda kuma Muka tsawaita rayuwarsa, za Mu mayar da halittarsa baya; me ya sa ne ba sa hankalta? </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon kafirai waɗanda suka ƙaryata manzanninsa da ranar alƙiyama da cewa, a ranar ne za a umarce su da su ware daga cikin muminai domin bai dace da su su cakuɗu da bayin Allah na gari ba, domin sakamakonsu daban-daban ne, kamar yadda ayyukansu suke daban-daban. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zarge su da bijire masa da bin Shaiɗan. Ya tunatar da su wasiyyar da ya yi musu ta hanyar manzanninsa da cewa kada su kuskura su bi Shaiɗan su riƙa aikata kafirci da ayyukan saɓo, domin shi Shaiɗan babban maƙiyinsu ne mai bayyana ƙiyayyarsa gare su a fili. To ina hankalinsu ya tafi da har suka rungume shi suna yi masa biyayya? Sannan ya tabbatar musu cewa, ya umarce su da su bauta masa shi kaɗai kada su haɗa kowa da bautarsa, domin bautarsa da yi masa biyayya ita ce hanya miƙaƙƙiya wadda za ta kai su ga shiga Aljanna da samun yardar Allah. To amma sai suka yi watsi da wannan wasiyya ta Ubangiji suka saɓa masa, suka kuma bi Shaiɗan maƙiyinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗakar da su cewa Shaiɗan fa ya ɓatar da mutane masu yawa, wanda hakan abin mamaki ne, domin ina hankulansu suke da ba za su gane cewa kamata ya yi su bauta wa Allah shi kaɗai ba su guji biyayya ga Shaiɗan babban maƙiyinsu? To tunda sun kafirce wa Allah sun ƙi kaɗaita shi da bauta sun zaɓi su bi Shaiɗan to a ranar alƙiyama za a nuna musu wutar Jahannama wadda aka yi ta yi musu gargaɗi a kanta a duniya suna ƙaryatawa. Hujjarsu wai don ba su gan ta ba; to a yau ga ta ga su suna ganin ta ƙuru-ƙuru. Sai a umarce su da su shiga cikinta su ƙuna da tsananin zafinta saboda kafircin da suka yi a duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a ranar ne zai toshe bakunansu ba za su iya musanta abin da suka aikata na kafirci da saɓon Allah ba. Hannayensu da sauran gaɓɓansu ne za su riƙa magana suna ba da shaidar duk abin da suka aikata a duniya. An karɓo daga Anas ɗan Malik ya ce: “Mun kasance a wurin Manzon Allah (ﷺ) sai ya yi dariya, sai ya ce: “Shin ko kun san me nake yi wa dariya?” Sai muka ce: “Allah da Manzonsa ne mafi sani.” Sai ya ce: “Ina dariya ne a kan yadda bawa zai magana da Ubangijinsa, zai ce: “Ya Ubangijina, ashe ba ka kare ni daga zalunci ba?” Sai Allah ya ce: “E, haka ne, na kare ka.” Sai bawa ya ce: “To ni ban yarda wani ya ba da shaida a kaina ba sai wani ɓangare na jikina.” Sai Allah ya ce: “Kai kanka a yau ka isa mai shaida a kanka, hakanan mala’iku masu girma marubuta su ma sun isa shaidu.” Annabi (ﷺ) ya ce: “Sai a toshe bakinsa sai a ce wa gaɓoɓinsa: “Ku yi magana.” Sai su yi magana su ba da labarin ayyukansa, sai kuma a ba shi damar yin magana, sai ya ce: “Tir da ku, dominku ne nake wannan fafutukar.” [Muslim #2969]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa da ya ga dama da sai ya shafe idanuwansu kamar yadda ya toshe bakunansu, sai su daina ganin komai, sannan ya umarce su da su yi rige-rigen hawan siraɗi domin su ƙetara zuwa Aljanna, amma ina! Ba za su iya ba bayan an shafe idanunsu. Sannan Allah ya bayyana cewa, da ya ga dama da ya jirkita halittarsu ya mayar da su sandararru ta yadda ba za su iya barin inda suke ba, ba kuma za su iya gaba ko baya ba domin su guje wa faɗawa wutar Jahannama. Abin nufi a nan shi ne, su dai waɗannan kafirai azabar Allah ta riga ta tabbata a kansu, dole ne su gamu da mummunan sakamakonsu. A wurin da suke kuwa babu komai sai wutar da aka fito musu da ita a fili ƙarara suka gan ta. Babu kuma mai iya kuɓuta daga faɗawa cikinta sai dai ta hanyar tsallake siraɗi, hakan kuwa ba zai samu ba sai ga muminai waɗanda za su riƙa tafiya a cikin haskensu. Amma su kafirai babu wata dama da Allah (Mai tsarki da daukaka) zai ba su ta samun kuɓuta daga wuta. To idan Allah ya ga dama sai ma ya shafe idanunsu, ya kuma dankwafar da su su kasa motsawa nan da can, ba za su iya gane inda siraɗin yake ba ballantana su tsallaka shi su wuce zuwa Aljanna, ba kuma za su iya yin gaba ko baya ba ballantana su tsere wa azabar wuta, don haka babu makawa sai sun shige ta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da ɗan’adam cewa tsawon rai ba shi ne zai hana shi mutuwa ba, wanda ma Allah ya ba shi tsawon rai, to zai mayar da halittarsa baya ne, ya koma ya yi rauni na jiki da na ƙwaƙwalwa, don haka me ya hana waɗannan kafiran su yi tunani su gane cewa duniya ba matabbata ce ba; gida na har abada shi ne gidan lahira?
وَمَا عَلَّمۡنَٰهُ ٱلشِّعۡرَ وَمَا يَنۢبَغِي لَهُۥٓۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ وَقُرۡءَانٞ مُّبِينٞ
Open ayah 36:69Ba Mu kuma koyar da shi (Muhammadu) waƙa ba, kuma ba za ta yiwu ba gare shi. (Abin da ya zo da shi) ba wani abu ba ne sai wa’azi da kuma Alƙur’ani mabayyani.
لِّيُنذِرَ مَن كَانَ حَيّٗا وَيَحِقَّ ٱلۡقَوۡلُ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 36:70Don ya gargaɗi wanda ya kasance rayayye (wato mumini), azaba kuma ta tabbata a kan kafirai. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar wa da mushirikai martani a kan tuhumar da suka yi wa Alƙur’ani ne cewa waƙa ce, wai shi kuma Manzon Allah mawaƙi ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi bai koya wa Manzonsa waƙa ba, kuma waƙa ma ba ta dace da shi ba, domin yawancin mawaƙa taɓaɓɓu ne kuma sai taɓaɓɓu ne suke bin su; shi kuwa shiryayye ne mai cikakken hankali, don haka yanayinsa ma bai yi kama da na mawaƙa ba ballantana har a ce masa mawaƙi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa abin da yake koyarwa ba wani abu ba ne face wa’azi da kuma Alƙur’ani mabayyani ga duk wanda yake da hankali na lura da haka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa an saukar wa Manzo (ﷺ) Alƙur’ani ne domin ya gargaɗi duk wani mai rayayyar zuciya mai hasken basira, domin shi kaɗai ne zai amfana da shi, su kuma kafirai azabar Allah ce za ta tabbata a kansu bayan an tsayar musu da hujja da saukar da Alƙur’ani, don haka ba su da sauran wani hanzari a wurin Allah.
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا خَلَقۡنَا لَهُم مِّمَّا عَمِلَتۡ أَيۡدِينَآ أَنۡعَٰمٗا فَهُمۡ لَهَا مَٰلِكُونَ
Open ayah 36:71Yanzu ba sa gani ne cewa Mu Muka halitta musu dabbobin ni’ima daga abin da hannanyenmu suka aikata, sai ga su suna mallakar su?
وَذَلَّلۡنَٰهَا لَهُمۡ فَمِنۡهَا رَكُوبُهُمۡ وَمِنۡهَا يَأۡكُلُونَ
Open ayah 36:72Muka kuma hore musu su, don haka ababen hawansu daga cikinsu ne, kuma daga gare su suke ci.
وَلَهُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ وَمَشَارِبُۚ أَفَلَا يَشۡكُرُونَ
Open ayah 36:73Suna kuma da wata moriya da abin sha daga gare su. Yanzu ba za su riƙa godiya ba? </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya janyo hankalin kafirai masu bautar waninsa da su duba su ga dabbobin ni’ima da ya halitta musu, waɗanda suka mallaki damar sarrafa su yadda suke buƙata ba tare da wata wahala ba. Ya kuma hore musu waɗannan dabbobi suna miƙa wuya gare su, suna sarrafa su yadda suka ga dama, su hau wasu su ɗora wa wasu kayansu masu nauyi, su yanka wasu daga cikinsu su ci namansu. Bayan wannan kuma sukan ci moriyarsu ta fuskoki daban-daban, kamar amfani da gashin raƙuma da na tumakai da fatunsu, domin shimfiɗa da kayan sawa. Hakanan sukan sayar da su su mori dukiyoyinsu. Sannan kuma sukan samu abin sha a tattare da su kamar nonon shanu ko na raƙuma ko na ƙananan dabbobi. To amma me ya hana su gode wa Allah wanda ya albarkace su da waɗannan ni’imomi masu ɗimbin yawa?
وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لَّعَلَّهُمۡ يُنصَرُونَ
Open ayah 36:74Suka kuma riƙi wasu ababen bauta ba Allah ba, don a taimaka musu.
لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَهُمۡ وَهُمۡ لَهُمۡ جُندٞ مُّحۡضَرُونَ
Open ayah 36:75Ba za su iya taimakon su ba, su da gumakan nasu duka ababen tattarawa ne (cikin wuta).
فَلَا يَحۡزُنكَ قَوۡلُهُمۡۘ إِنَّا نَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَ
Open ayah 36:76To kada maganarsu ta baƙanta maka. Lalle Mu Muna sane da abin da suke ɓoyewa da kuma abin da suke bayyanawa. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana butulcin kafirai ne waɗanda suka rungumi wasu abubuwan bauta ba Allah ba, suna kuma bauta musu tuƙuru sun yi watsi da kaɗaita Allah da bauta. A tsammaninsu waɗannan alloli za su taimaka musu su kuɓutar da su daga azabar Allah idan ya yi nufin azabtar da su. Sun jahilci cewa waɗannan allolin ba sa iya taimaka wa kawunansu ma ballantana su taimaka wa wani; a ƙarshe ma da su da allolin duk za a tattaro su ne zuwa wuta, a lokacin da suke nesanta kansu da juna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) ya kwantar masa da hankali game da ƙaryata shi da kafirai suke yi suna cewa, shi ba Manzon Allah ne ba, ko kuma shi mawaƙi ne da sauran tuhumce-tuhumce da suke yi masa. Allah ya gaya masa cewa kada maganganunsu su baƙanta masa rai; yana sane da duk abin da suke ɓoyewa da wanda suke bayyanawa, kuma lalle zai yi musu sakayya a kansu.
أَوَلَمۡ يَرَ ٱلۡإِنسَٰنُ أَنَّا خَلَقۡنَٰهُ مِن نُّطۡفَةٖ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٞ مُّبِينٞ
Open ayah 36:77Yanzu mutum ba ya gani cewa Mu Muka halicce shi daga maniyyi, sai ga shi ya zama mai jayayya a fili?
وَضَرَبَ لَنَا مَثَلٗا وَنَسِيَ خَلۡقَهُۥۖ قَالَ مَن يُحۡيِ ٱلۡعِظَٰمَ وَهِيَ رَمِيمٞ
Open ayah 36:78Ya kuma buga mana misali, kuma ya manta da halittarsa (yayin da) ya ce: “Wane ne zai raya ƙasusuwa, alhali kuma sun rududduge?
قُلۡ يُحۡيِيهَا ٱلَّذِيٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلۡقٍ عَلِيمٌ
Open ayah 36:79Ka ce: “Wannan da Ya fare su tun farko Shi ne zai raya su; Shi kuwa Masanin kowacce irin halitta ne.
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلشَّجَرِ ٱلۡأَخۡضَرِ نَارٗا فَإِذَآ أَنتُم مِّنۡهُ تُوقِدُونَ
Open ayah 36:80“Wanda kuma Ya samar muku wuta daga koriyar bishiya, sai ga shi kuna hura wuta daga gare ta.”
أَوَلَيۡسَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يَخۡلُقَ مِثۡلَهُمۚ بَلَىٰ وَهُوَ ٱلۡخَلَّٰقُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 36:81Yanzu wanda Ya halacci sammai da ƙasa ba zai zama Mai ikon halitta irinsu ba? Ai tabbas zai iya, kuma Shi ne Mai yawan yin halitta, Masani.
إِنَّمَآ أَمۡرُهُۥٓ إِذَآ أَرَادَ شَيۡـًٔا أَن يَقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Open ayah 36:82Umarninsa kawai idan Ya yi nufin wani abu sai Ya ce da shi: “Kasance”, sai ya kasance.
فَسُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 36:83To tsarki ya tabbata ga wanda mulkin kowane abu yake a hannunsa, kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku. </b> A ayoyi na ƙarshen wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar da martani ne ga masu jayayya a kan Ƙudurar Allah ta sake tayar da matattu cikin wata sabuwar halitta, kuma ya ja hankalin ɗan’adam cewa ya duba ya ga yadda asalin halittarsa take. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya halicce shi ne daga ɗigon ruwan maniyyi wulaƙantacce, wanda ya bi mataki daban-daban wasu bayan wasu har ya zama mutum daidaitacce, aka busa masa rai, har aka haife shi ya taso tun yana ƙarami har ya girma, sai kuma ga shi yanzu ya zama mai yawan jayayya da mahaliccinsa. Me zai hana shi ya dubi irin tazarar da take tsakanin yanayinsa na farko lokacin da yake maniyyi da kuma yadda ya koma daga ƙarshe? Ashe wannan bai isa ya zama dalili mai nuna cikar Ƙudurar Allah a kan sake dawo da shi bayan mutuwa ba? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafircin ɗan’adam ya kai shi ga manta wannan ƙwaƙƙwaran dalili har ta kai shi ga kafa hujja da rududdugaggun ƙasusuwa na matattu cewa, wai wane ne zai dawo da su su koma masu rai. Ya manta da ikon wanda ya ƙirƙire su daga babu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya amsa musu da cewa, wanda ya halicci waɗannan rududdugaggun ƙasusuwa da farko, shi ne kuma wanda zai sake raya su, domin kuwa wanda ya halicce su a karon farko ba zai gagare shi ya dawo musu da ransu ba. Wannan <b>hujja ta farko </b>kenan. <b>Hujja ta biyu </b>, shi Allah (Mai tsarki da daukaka) masanin kowacce irin halitta ne, dangane da yanayi da kuma lokacin kowace halitta. Don haka mai cikakken ilimi na halitta irin haka yaya zai gagare shi ya dawo wa da matacce ransa duk sanda ya ga dama? <b>Hujja ta uku </b>, shi ne wanda ya samar da wuta daga ɗanyar bishiya, watau ya haɗa abubuwa biyu kishiyoyin juna a wuri guda, ga lemar da ke jikin ɗanyar bishiya ya kuma nufi wuta ta kama a jikinta. Babu shakka wanda yake da ikon yin haka, tabbas yana da cikakken ikon da zai raya matattu. <b>Hujja ta huɗu </b>, shi ne wanda ya halicci sammai da ƙasa da duk abin da ke cikinsu duk kuwa da girmansu da yalwarsu. Yanzu yaya za a ce ba zai zama mai ikon raya matattu ba bayan mutuwarsu? Lalle shi kaɗai ne mai wannan ikon. Hasali ma halittar ɗan’adam ta fi sauƙi gare shi a kan halittar sammai da ƙasa. <b>Hujja ta biyar </b>, Allah shi ne mahaliccin dukkan halittu manya da ƙanana; babu wani mahaluƙi da halittarsa za ta gagare shi, kuma shi masanin komai ne babu abin da yake ɓuya a gare shi. To ta yaya zai kasa tayar da matattu? <b>Hujja ta shida </b>, shi kaɗai ne ya kaɗaita da ikon cewa, idan ya yi nufin samar da kowane abu sai kawai ya ce masa ‘ya samu’, sai kuwa ya samu kamar yadda Allah yake nufinsa. Don haka raya matacce ma yana ƙarƙashin wannan iko nasa, saboda haka wannan ba zai gagare shi ba. <b>Hujja ta bakwai </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkaka daga duk wata nakasa ko aibi da mushirikai suke danganta shi da shi, kamar gajiyawa ko kasawa, domin kuwa shi ne mamallakin komai, shi yake sarrafa komai yadda yake so, makullan komai suna hannunsa, komai a ƙarƙashin ikonsa yake, saboda haka dawo wa da matattu rayukansu abu ne mai matuƙar sauƙi a wurinsa, kuma dukkansu zuwa gare shi za a mayar da su domin yi musu hisabi da sakamako.