الصافات
As-Saaffaat
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلصَّٰٓفَّٰتِ صَفّٗا
Open ayah 37:1Ina rantsuwa da mala’iku masu yin sahu-sahu.
فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجۡرٗا
Open ayah 37:2Sannan da masu yi wa girgije tsawa.
فَٱلتَّٰلِيَٰتِ ذِكۡرًا
Open ayah 37:3Da masu karanta maganar Allah.
إِنَّ إِلَٰهَكُمۡ لَوَٰحِدٞ
Open ayah 37:4Lalle Ubangiijnku tabbas Ɗaya ne.
رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَرَبُّ ٱلۡمَشَٰرِقِ
Open ayah 37:5Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu, kuma Ubangijin wuraren hudowar rana. </b> Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da yin rantsuwa da mala’ikunsa masu tsayawa sahu-sahu suna bautar sa. An karɓo daga Jabiru ɗan Samura (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yanzu ba za ku riƙa tsai da sahunku kamar yadda mala’iku suke tsai da sahu a wajen Ubangijinsu ba?” Sai muka ce: “Yaya mala’iku suke tsai da sahu a wajen Ubangijinsu?” Sai ya ce: “Suna cika sahu-sahu na farko, sannan suna daidaita a cikin sahu.” [Muslim #430 da Abu Dawud #661 da Nasa’i #816 da Ibn Majah #992]. An karɓo daga Huzaifa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “An fifita mu a kan sauran mutane da abu uku: An sanya tsayuwar sahunmu kamar tsayuwar sahun mala’iku; an sanya mana bayan ƙasa gaba ɗayanta ta zama masallaci; an kuma sanya mana turɓayarta ta zama abin tsarki idan mun rasa ruwa.” [Muslim #522]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da rantsuwa da mala’iku masu yi wa girgije tsawa su kora shi zuwa inda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ga damar ya saukar da ruwansa. Ya kuma rantse da mala’iku masu karanta maganar Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin waɗannan rantse-rantse da ya yi da cewa lalle abin bautar mutane ɗaya ne, shi ne Allah Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu, kuma Ubangijin rana da wuraren hudowarta da faɗuwarta a tsawon shekara, ba shi da abokin tarayya wajen halittar waɗannan abubuwa da sarrafa su da gudanar da su.
إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِزِينَةٍ ٱلۡكَوَاكِبِ
Open ayah 37:6Lalle Mun ƙawata sama ta kusa da ado na taurari.
وَحِفۡظٗا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ مَّارِدٖ
Open ayah 37:7Da kuma tsaro daga dukkan wani shaiɗan mai tsaurin kai.
لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٖ
Open ayah 37:8Ba kuma za su iya jiyowa ba (daga asirin) mala’iku na sama, sai a yi ta jifan su ta kowane ɓangare.
دُحُورٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ وَاصِبٌ
Open ayah 37:9Don kora; suna kuma da wata azaba dawwamamma.
إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ ثَاقِبٞ
Open ayah 37:10Sai dai wanda ya yi fautowar jin, to sai wani tauraro mai haske da ƙuna ya biyo shi. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya ƙawata sama ta kusa da ƙasa da ado na taurari masu matuƙar haske da sheƙi kamar gwalagwalai. Ya kuma bayyana wani muhimmanci na waɗannan taurarin bayan ado da suka yi wa sama, domin da su ne Allah yake tsare saman daga duk wani shaiɗani mai taurin kai da bijire wa ɗa’ar Allah, da su ne ake jifan irin wannan shaiɗanu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa su waɗannan shaiɗanu masu taurin kai ba za su iya jiyo maganar mala’iku ba a sama yayin da suke ambaton wani wahayi da Allah ya yi musu wanda ya danganci shari’arsa ko ƙaddararsa, za a yi ta jifan su ne da garwashin wuta ta kowane ɓangare don a kore su a hana su sauraron maganar mala’iku, sannan kuma a lahira suna da wata azaba mai raɗaɗi ta dindindin. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi togaciya ta wani daga cikin shaiɗanun wanda zai samu damar waftar wata kalma daga cikin tattaunawar mala’iku a kan wani abu da ba wani mahaluƙi a ƙasa da yake da masaniya a kansa, to shi ma bai tsira ba sai wani gargwashi mai haske da ƙuna ya bi shi domin ƙona shi. Tana yiwuwa ya samu damar jefa wa ‘yan’uwansa shaiɗanu wannan kalmar kafin garwashin ya cim masa ya ƙona shi, su kuma su isar wa bokaye wannan batu, daga nan su kuma bokaye su gauraya shi da ƙarairayi ɗari su gaya wa mutanensu.
فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَهُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَم مَّنۡ خَلَقۡنَآۚ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّن طِينٖ لَّازِبِۭ
Open ayah 37:11Ka tambaye su cewa, yanzu su suka fi ƙarfin halitta ko kuwa waɗanda a da Muka halitta? Lalle Mu Mun halicce su daga wani taɓo mai danƙo.
بَلۡ عَجِبۡتَ وَيَسۡخَرُونَ
Open ayah 37:12A’a, kai dai ka yi mamakin (ikon Allah da ƙaryatawarsu) ne, su kuma suna yin izgili.
وَإِذَا ذُكِّرُواْ لَا يَذۡكُرُونَ
Open ayah 37:13Idan kuma aka yi musu wa’azi ba sa wa’azantuwa.
وَإِذَا رَأَوۡاْ ءَايَةٗ يَسۡتَسۡخِرُونَ
Open ayah 37:14Idan kuma suka ga wata aya sai su tsananta ba’a.
وَقَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٌ
Open ayah 37:15Su kuma ce: “Wannan ba wani abu ba ne in ban da sihiri mabayyani.
أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
Open ayah 37:16“Yanzu idan muka mutu muka zama ƙasa da ƙasusuwa shin da gaske za a tashe mu?
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ
Open ayah 37:17“Haka ma da iyayenmu na farko?”
قُلۡ نَعَمۡ وَأَنتُمۡ دَٰخِرُونَ
Open ayah 37:18Ka ce: “Na’am, (za a tashe ku) kuna kuwa ƙasƙantattu.”
فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ فَإِذَا هُمۡ يَنظُرُونَ
Open ayah 37:19To (wannan) ba wani abu ba ne sai kawai tsawa guda ɗaya, sai ga su suna sauraron (abin da zai faru). </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) ya tambayi mushirikai masu ƙaryata tashi bayan mutuwa, shin yanzu halittarsu ce ta fi ƙarfi ko kuma jikinsu da gaɓoɓinsu ne suka fi sauran abubuwan da Allah ya halitta ƙarfi, kamar sammai da ƙasa da mala’iku da taurari da sauran manya-manyan halittun Allah? Su kansu mushirikan sun tabbata ba za a taɓa gwada halittarsu da ta waɗancan ba, domin su Allah ya halicce su ne daga wani taɓo mai danƙo, to me ya sa za su riƙa ƙaryata tashi bayan mutuwa alhali ga shi daga irin abin da aka halicce su mai rauni da laushi? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Manzonsa (ﷺ) cewa ba ma sai ya tambaye su ba domin su mutane ne masu taurin kan tsiya, wannan tambayar ma ba amfanar su za ta yi ba, don ba sa yin duba zuwa ga dalilan da suke nuna cikar ikon Allah da kamalar Ƙudurarsa har su yi mamakin wannan dalilai. Allah ya bayyana cewa Manzonsa ne zai yi mamakin Ƙudurarsa da yadda yake gudanar da al’amuran halittarsa, kuma shi ne yake mamakin yadda mushirikai suke ƙaryata tashi bayan mutuwa, saboda zaƙewarsu wajen ƙaryata hakan, har suke haɗawa da yin izgili. Idan ma an yi musu wa’azi a kan haka to ba sa amfana da duk gargaɗin da ake yi musu saboda zukatansu sun riga sun ƙeƙashe. Wannan ya sa duk wata ayar da za su gani daga cikin ayoyin da suke tabbatar da gaskiyar Manzon Allah sai su daɗa sa ƙaimi wajen izgili da ba’a, har ma suna nuna mamakinsu a kan haka, suna cewa Annabi Muhammadu (ﷺ) bai zo musu da komai ba in ban da sihiri bayyananne. Suna kuma mamakin wai a ce yanzu idan sun mutu sun zama ƙasa da rududdugaggun ƙasusuwa wai a ce za a sake tayar da su da ransu; suna ganin wannan ba abu ne da zai yiwu ba. Kuma ma abin da yake ƙara ba su mamaki shi ne wai a ce har iyayensu ma da suka mutu shekaru aru-aru su ma za a tashe su? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya tabbatar musu da cewa, tabbas za a tashe su ko da kuwa sun mutu sun zama ƙasa da ƙasusuwa rududdugaggu, kuma za a tashe su ne suna ƙasƙantattu a ranar alƙiyama, domin kuwa tashinsu da rai ba abu ne mai wata wahala ba; kawai busa ɗaya ce Mala’ika Israfilu zai yi a cikin ƙaho, watau busa ta biyu, sai su tashi gaba ɗayansu suna kallon abubuwan ban tsoro na wannan ranar, suna kuma sauraron abin da Allah zai yi da su.
وَقَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا هَٰذَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Open ayah 37:20Sai su ce: “Kaitonmu!” (Sai a ce da su): “Wannan ita ce ranar sakamako.
هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 37:21“Wannan ita ce ranar hukunci wadda kuka kasance kuna ƙaryatawa.”
۞ٱحۡشُرُواْ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَأَزۡوَٰجَهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَعۡبُدُونَ
Open ayah 37:22(Za a ce da mala’iku): “Ku tattaro waɗanda suka yi zalunci su da abokan haɗinsu (shaiɗanu) da kuma abin da suka kasance suna bauta wa.
مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهۡدُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:23Waɗanda ba Allah ba, sai ku nuna musu hanyar zuwa wutar Jahima.
وَقِفُوهُمۡۖ إِنَّهُم مَّسۡـُٔولُونَ
Open ayah 37:24“Kuma ku tsayar da su; don lalle za a tambaye su.
مَا لَكُمۡ لَا تَنَاصَرُونَ
Open ayah 37:25“Cewa: ‘Me ya sa ba kwa taimakon juna ne?’”
بَلۡ هُمُ ٱلۡيَوۡمَ مُسۡتَسۡلِمُونَ
Open ayah 37:26Ba haka ba ne, su dai a yau masu miƙa wuya ne. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ranar alƙiyama kafirai masu ƙaryata wannan rana za su shiga nadama marar amfani, da takaici su tabbatar da cewa wannan fa ita ce ranar sakamako wadda Allah yake saka wa bayinsa a kan duk wani aiki da suka gabatar a rayuwarsu ta duniya. Sai a ƙara tabbatar musu da cewa wannan ita ce ranar hukunci tsakanin bayi wadda suke ƙaryata zuwanta. Sannan kuma a wannan ranar ne za a umarci mala’iku da su tattara azzalumai waɗanda suka yi wa Allah shirka da duk wasu masu kama da su da masu ƙaryatawa a haɗa su tare da gumakan da suke bauta wa, sai a nuna musu hanyar shiga wuta. Amma kafin su kora su zuwa cikinta sai sun tsare su, domin a yi musu hisabi, game da kafircinsu da duk laifukan da suka aikata a duniya. Daga nan sai a daka musu tsawa a ce da su me ya sa a nan ba sa taimakon junansu kamar yadda suka riƙa riyawa a duniya, suna cika bakin cewa gumakansu ne za su taimake su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa a ranar babu maganar su taimaki juna; dukkansu za su miƙa wuya ne ga Allah su sallama, domin ba su da sauran wata dabara ko ƙarfi.
وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 37:27Shashinsu kuma ya fuskanci shashi suna tambayar juna.
قَالُوٓاْ إِنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَأۡتُونَنَا عَنِ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 37:28Suka ce: “Lalle kun kasance kuna zo mana ta damanmu (don mu amince muku).”
قَالُواْ بَل لَّمۡ تَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:29Suka ce: “A’a, ba ku dai kasance muminai ba ne.
وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنِۭۖ بَلۡ كُنتُمۡ قَوۡمٗا طَٰغِينَ
Open ayah 37:30“Kuma mu ba mu da wani iko a kanku; ku dai kawai kun kasance mutane ne masu ɗagawa.
فَحَقَّ عَلَيۡنَا قَوۡلُ رَبِّنَآۖ إِنَّا لَذَآئِقُونَ
Open ayah 37:31“Saboda haka faɗar Ubangijinmu (ta azaba) ta tabbata a kanmu; (cewa) lalle tabbas za mu ɗanɗana kuɗarmu.
فَأَغۡوَيۡنَٰكُمۡ إِنَّا كُنَّا غَٰوِينَ
Open ayah 37:32“Don haka muka ɓatar da ku, domin mu ma lalle mun kasance ɓatattu ne.”
فَإِنَّهُمۡ يَوۡمَئِذٖ فِي ٱلۡعَذَابِ مُشۡتَرِكُونَ
Open ayah 37:33Saboda haka su a wannan ranar, masu tarayya ne a cikin azaba.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 37:34Lalle Mu kamar haka Muke yi wa masu manyan laifuka.
إِنَّهُمۡ كَانُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسۡتَكۡبِرُونَ
Open ayah 37:35Lalle sun kasance idan aka ce da su: “Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah,” sai su yi girman kai.
وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓاْ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٖ مَّجۡنُونِۭ
Open ayah 37:36Su kuma riƙa cewa: “Yanzu ma bar allolinmu don wani mawaƙi mai taɓin hankali?”
بَلۡ جَآءَ بِٱلۡحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:37Ba haka ba ne, ya dai zo ne da gaskiya, ya kuma gaskata manzanni. </b> A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da za a tattara mushirikai shugabanni da mabiya a cikin wutar Jahannama, za su fuskanci juna ne, rigima da zargi su kaure a tsakaninsu. Mabiya ne za su zargi shugabanninsu da cewa a duniya sun riƙa yaudarar su da daɗin baki, suna ɓullo musu ta fuskar addini da nuna cewa su masu gaskiya ne, suna ƙawata musu shirka da saɓon Allah, suka kuma hana su bin gaskiya da yarda da abin da manzanni suka zo musu da shi daga Allah. To su ma shugabannin sai su mayar musu da martini, su ƙaryata su, su nuna ba haka lamarin yake ba; su da ma suna kan ɓata da kafirci ne, ba su taɓa yin imani ba sai dai su ƙaryata manzanninsu. Kuma su ba wani ƙarfi suka nuna musu ba, suka sa su kafirta dole; kawai dai su mabiyan mutane ne masu zaƙewa cikin kafirci da ɓata da saɓon Allah, don haka, \'za mu ce ta tarar da mu je mu\'. Don haka sai suka tabbatar wa da mabiyansu cewa duk gaba ɗayansu maganar Allah ce ta azaba ta tabbata a kansu, saboda haka za su ɗanɗani azaba tare ba makawa, domin da su shuwagabannin da mabiyansu duka ɓatattu ne, kuma abin da ya cancanta da su ke nan. Suka nuna musu cewa, waɗannan su ne dalilansu da suka sanya suka ɓatar da su, suka riƙa kiran su zuwa ga kafirci da ɓata, domin su ma da man ɓatattu ne ba sa kan tafarkin shiriya, don haka marar abu ba ya bayar da shi ga wani. Watau sai su daina zargin su su zargi kansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa gaba ɗayansu shugabannin da mabiyan nasu za su yi tarayya a cikin azaba ranar alƙiyama, kamar yadda a duniya suka haɗu a kan kafirci da shirka da Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa, kamar yadda ya yi wa waɗannan irin wannan sakamakon azaba, haka zai yi wa duk wasu masu manyan laifuka na kafirci da haɗa shi da wasu wajen bauta. Allah kuma ya bayyana mummunan laifin da suka aikata wanda ya jawo musu wannan sakamako, watau tun a duniya idan aka neme su da yin Kalmar Shahada su ce: ‘La ilaha illal Lahu ’ kuma su yi aiki da ita su watsar da bautar duk wani abu ba Allah ba, sai su yi watsi da wannan kira saboda girman kai na ƙin gaskiya, suna ma cewa, ta yaya wai za su bar bautar allolinsu su kama maganar wani mawaƙi mai taɓin hankali? Suna nufin Manzon Allah (ﷺ). Sai Allah ya mayar musu da martani cewa shi Annabi Muhammadu (ﷺ) ba mawaƙi ne ba kuma ba mai taɓin hankali ba; Annabin Allah ne da ya zo musu da Alƙur’ani wanda yake kiran su zuwa ga kaɗaita Allah da bin Manzonsa, kuma ya gaskata sauran manzanni a kan saƙon da suka zo da shi daga Allah na Tauhidi da tabbatar da ranar alƙiyama kuma bai saɓa musu da komai ba.
إِنَّكُمۡ لَذَآئِقُواْ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَلِيمِ
Open ayah 37:38Lalle ku tabbas za ku ɗanɗani azaba mai tsanani.
وَمَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 37:39Ba kuwa za a saka muku ba sai da irin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:40Sai dai bayin Allah waɗanda aka tsarkake.
أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ رِزۡقٞ مَّعۡلُومٞ
Open ayah 37:41Waɗannan suna da arziki sananne.
فَوَٰكِهُ وَهُم مُّكۡرَمُونَ
Open ayah 37:42(Shi ne) kayan marmari; su kuma ababen karramawa ne.
فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 37:43A cikin gidajen Aljanna na ni’ima.
عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ
Open ayah 37:44A kan gadaje suna fuskantar juna.
يُطَافُ عَلَيۡهِم بِكَأۡسٖ مِّن مَّعِينِۭ
Open ayah 37:45Ana zagaya su da kofuna na giya.
بَيۡضَآءَ لَذَّةٖ لِّلشَّٰرِبِينَ
Open ayah 37:46Fara fat, ga kuma daɗi ga masu sha.
لَا فِيهَا غَوۡلٞ وَلَا هُمۡ عَنۡهَا يُنزَفُونَ
Open ayah 37:47Babu sa ciwon kai a gare ta, kuma ba za a bugar da su da ita ba.
وَعِندَهُمۡ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ عِينٞ
Open ayah 37:48A wurinsu kuma akwai mataye masu taƙaita kallonsu ga mazajensu, masu ƙwala-ƙwalan ido.
كَأَنَّهُنَّ بَيۡضٞ مَّكۡنُونٞ
Open ayah 37:49Kai ka ce su wani ƙwai ne a cikin kwasfa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai waɗanda suka zaɓi zama cikin bautar wanin Allah da ƙaryata Manzo (ﷺ) za su ɗanɗani azaba mai raɗaɗi ranar alƙiyama sakamakon munanan ayyukansu, domin kuwa ba za a saka musu da komai ba sai da abin da suka kasance suna aikatawa a duniya na kafirci da saɓon Allah. A ɗaya ɓangaren kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon muminai waɗanda suka tsantsanta bautarsu gare shi, kuma ya tsarkake su, to su waɗannan Allah ya tserar da su daga azaba, suna kuma da arzikinsu sananne da Allah ya tanadar musu, wanda ya ƙunshi kayan marmari iri-iri waɗanda ba su taɓa gani ko cin abu mai daɗi irinsu ba, sannan kuma a karrama su da babban matsayi a gidajensu na Aljanna, har ma a datar da su da ganin Allah (Mai tsarki da daukaka). Wannan tagomashi kuma za su same shi ne a gidajen Aljannar ni’ima madawwamiya wadda ba za ta yanke ba har abada. Allah kuma ya ambaci wasu dangogin ni’imomin da za a tanadar musu a Aljanna. Daga ciki akwai gadaje na alfarma da za su kishingiɗa a kansu suna fuskantar junansu, watau sun yi da’ira babu wanda zai juya wa ɗan’uwansa baya suna cike da farin ciki, ana kuma zagaya su da kofuna na giya tatacciya garai-garai kamar wani idanun ruwa mai kwarara, kuma ga ta fara fat, duk wanda ya sha ta zai samu cikakken jin daɗi da annashawa, domin ita ba kamar giyar duniya ce ba, ba ta gusar da hankali ba kuma ta sanya ciwon kai, sai dai ta ƙara wa mai shan ta lafiyar hankali da ta jiki. Sannan kuma za a ba su `yan mata kyawawa masu kamun kai waɗanda ba sa kallon wasu maza in ba nasu ba, masu kuma kyawawan idanu, ga su kuma farare ƙal, idan mutum ya kalle su zai ga kamar ƙwan tsuntsaye ne da yake cikin kwasfarsa, a killace kuma babu wani hannu da ya taɓa shafar su.
فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 37:50Sannan sashinsu ya fuskanci shashi suna tambayar juna.
قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٞ
Open ayah 37:51Wani daga cikinsu ya ce: “Lalle a da can ina da wani aboki.
يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُصَدِّقِينَ
Open ayah 37:52“Da yake cewa: ‘Yanzu kai kana cikin masu ba da gaskiya?
أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ
Open ayah 37:53“’Yanzu idan muka mutu muka zama ƙasa da ƙasusuwa shin ko za a iya yi mana wani sakamako?’”
قَالَ هَلۡ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ
Open ayah 37:54Ya ce: “Shin ko za ku leƙa ne?”
فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِي سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:55Sai shi ya leƙa, sai kuwa ya gan shi a tsakiyar wuta.
قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرۡدِينِ
Open ayah 37:56Ya ce: “Wallahi ka kusa ka hallakar da ni.
وَلَوۡلَا نِعۡمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ
Open ayah 37:57“Ba don rahamar Ubangijina ba, da lalle ni ma na zama cikin ‘yan wuta.”
أَفَمَا نَحۡنُ بِمَيِّتِينَ
Open ayah 37:58(Sai ‘yan Aljanna su ce da juna): “Ashe yanzu ba za mu sake mutuwa ba?
إِلَّا مَوۡتَتَنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ
Open ayah 37:59“Sai fa mutuwarmu ta farko, ba kuma za a azabtar da mu ba?”
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 37:60Lalle wannan shi ne babban rabo.
لِمِثۡلِ هَٰذَا فَلۡيَعۡمَلِ ٱلۡعَٰمِلُونَ
Open ayah 37:61Don samun irin wannan lalle masu (kyakkyawan) aiki su yi aiki. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci ‘yan Aljanna da cikar farin cikinsu da ni’imomin da ya ba su, sai kuma ya bayyana irin hirar da suke yi a cikin Aljanna da junansu a kan abubuwan da suka faru a rayuwarsu ta duniya, har wani daga cikinsu yake faɗa wa ‘yan’uwansa cewa, yana da wani aboki a duniya wanda bai yarda da ranar lahira ba, har ta kai yake yi wa abokinsa mumini izgili da cewa, yanzu shi yana cikin masu gaskata tashi bayan mutuwa; bayan mutane sun mutu sun zama ƙasa da ƙasusuwa rududdugaggu, kuma a ce wai za a sake tashin su da ransu a yi musu hisabi a kan ayyukansu na duniya? Yana ganin wautarsa da har ya amince da haka. Bayan wannan mumini ɗan Aljanna ya gama ba wa abokansa labarinsa shi da abokinsa mai ƙaryata tashi bayan mutuwa, sai ya nemi abokansa da su raka shi ya je ya leƙa wuta don ya ga halin da wancan kafirin abokin nasa yake ciki domin su ƙara gode wa Allah a kan ni’imar da ya yi musu. Da suka je suka leƙa wutar Jahannama sai kuwa ya tsinkayo abokin nan nasa a tsakiyar wutar Jahannama, nan take ya tuna babbar ni’imar da Allah ya yi masa da ya tsare shi, abokinsa bai ja shi zuwa kafirci ba. Ya rantse masa da Allah cewa saura ƙiris ya hallaka shi, ya sa shi ma ya kafirce wa Allah da ranar alƙiyama. Ya ƙara da cewa, ba don ni’imar da Allah Ubangijinsa ya yi masa ba, da yanzu shi ma yana cikin wuta tare da wannan aboki nasa kafiri. Don haka sai farin ciki ya ƙara rufe shi har yake faɗa wa ‘yan’uwansa ‘yan Aljanna cewa daga yanzu kam babu sauran wata mutuwa a gare su in ban da mutuwarsu ta farko da suka yi aka tashe su, ba kuma za a yi musu azaba ba, sai dai a dawwamar da su a cikin gidan Aljanna har abada. Suka tabbatar da cewa wannan sakamako da Allah ya yi musu shi ne babban rabo da babu kamarsa. Sai kuma Allah ya kwaɗaitar da bayinsa a kan aikin alheri tuƙuru. domin samun rabo mai girma irin wannan, domin wannan shi ne kasuwanci mai cikakkiyar riba da babu tazgaro a cikinsa.
أَذَٰلِكَ خَيۡرٞ نُّزُلًا أَمۡ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ
Open ayah 37:62Shin wannan liyafa ita ce ta fi alheri ko kuwa bishiyar Zaƙƙum?
إِنَّا جَعَلۡنَٰهَا فِتۡنَةٗ لِّلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 37:63Lalle Mu Mun sanya ta don ta zama fitina ga azzalumai.
إِنَّهَا شَجَرَةٞ تَخۡرُجُ فِيٓ أَصۡلِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:64Lalle ita wata bishiya ce da take fitowa a tsakiyar wutar Jahima.
طَلۡعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَٰطِينِ
Open ayah 37:65‘Ya’yanta kai ka ce kawunan shaiɗanu ne.
فَإِنَّهُمۡ لَأٓكِلُونَ مِنۡهَا فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ
Open ayah 37:66To su lalle za su ci daga gare ta, za su kuma cika cikkuna da ita.
ثُمَّ إِنَّ لَهُمۡ عَلَيۡهَا لَشَوۡبٗا مِّنۡ حَمِيمٖ
Open ayah 37:67Sannan kuma suna da wani gauraye na tafasasshen ruwa a kanta.
ثُمَّ إِنَّ مَرۡجِعَهُمۡ لَإِلَى ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:68Sannan kuma lalle makomarsu wutar Jahima ce.
إِنَّهُمۡ أَلۡفَوۡاْ ءَابَآءَهُمۡ ضَآلِّينَ
Open ayah 37:69Lalle su sun sami iyayensu ɓatattu.
فَهُمۡ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ يُهۡرَعُونَ
Open ayah 37:70Sai suka riƙa gaggawar bin sawunsu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana tambayar mutane cewa, shin waɗancan ni’imomi na gidan Aljanna da aka ambata su ne suka fi alheri da karamci ko kuma bishiyar Zaƙƙumi wadda aka la’ance ta a cikin Alƙur’ani, wadda kuma ita ce abincin kafirai wanda ba ya sa ƙiba ba ya kuma maganin yunwa. Allah ya bayyana cewa ya sanya wannan bishiyar don ta zama fitina ga kafirai azzalumai, domin lokacin da suka ji an ambaci cewa bishiya ce a tsakiyar wuta, sai suka ƙaryata hakan suka nuna cewa ai babu yadda za a yi bishiya ta tsiro a cikin wuta, domin wuta takan cinye duk wani itace da tsiro, ba zai yiwu ba kuma a ce har ya fito a cikinta. Sai kuma ya siffanta ta da cewa wata mummunar bishiya ce wadda take fitowa a can ƙarƙashin Jahannama, kuma ‘ya’yanta ba su da kyan gani sai ka ce kawunan shaiɗanu ne. Wannan kuma yana nuna tsananin munin ɗanɗanonta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa kafirai ba makawa za su ci ‘ya’yan wannan itaciya mai matuƙar ɗaci, har sai sun cika cikkunansu da ita, sannan su bi ta da tafasasshen ruwa, kuma makomarsu bayan haka zuwa wutar Jahimu ce, inda za a riƙa kwasar su daga wannan azabar zuwa wata. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana abin da ya jawo musu wannan mummunan hali da suka shiga, watau bin hanyar da iyayensu ɓatattu suke a kai da kauce wa hanyar shiriya, ba bisa ga wata hujja da suke da ita ba, suka bijire wa hanyar manzannin Allah da shiriyar da suka zo da ita.
وَلَقَدۡ ضَلَّ قَبۡلَهُمۡ أَكۡثَرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 37:71Haƙiƙa kafin su mafi yawan mutanen farko sun ɓata.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ
Open ayah 37:72Kuma haƙiƙa Mun aiko masu gargaɗi a cikinsu.
فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Open ayah 37:73To ka dubi yadda ƙarshen waɗanda aka yi wa gargaɗi ya kasance.
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:74Sai dai bayin Allah waɗanda aka tsarkake. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzon Allah cewa ba mutanensa ne kaɗai suka ɓace ba, yawancin al’ummun da suka gabace su sun zama ɓatattu, duk kuwa da cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aika musu da manzanni masu yi musu gargaɗi suna kuma tsoratar da su azabar Allah, to amma sai suka kafirce, don haka Allah ya hallaka su. Sai Allah ya tuna wa Manzonsa (ﷺ) cewa ya duba ya ga yadda ƙarshen waɗannan mutane da aka yi wa gargaɗi suka bijire ya kasance. Ƙarshensu shi ne shiga wutar Jahannama su kuma dawwama a cikinta har abada, saboda kafircinsu da saɓon Allah da suka yi. Sai kuma Allah ya bayyana cewa akwai kaɗan daga cikinsu waɗanda ya tsarkake su da Imani, to waɗannan zai kuɓutar da su daga mummunan ƙarshe wanda ya sami kafirai.
وَلَقَدۡ نَادَىٰنَا نُوحٞ فَلَنِعۡمَ ٱلۡمُجِيبُونَ
Open ayah 37:75Kuma <b>haƙiƙa Nuhu ya roƙe Mu, to madalla da Masu amsawa.
وَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 37:76Muka kuma tserar da shi tare da iyalinsa daga baƙin ciki mai girma.
وَجَعَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلۡبَاقِينَ
Open ayah 37:77Muka kuma sanya zuriyarsa su ne suka wanzu.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:78Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga \'yan baya.
سَلَٰمٌ عَلَىٰ نُوحٖ فِي ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 37:79Aminci ya tabbata ga Nuhu a cikin talikai.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:80Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa.
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:81Lalle shi yana daga bayinmu muminai.
ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Open ayah 37:82Sannan Muka nutsar da sauran. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya karɓi addu’ar Annabinsa Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya yi wa mutanensa addu’a bayan ya shekara dubu ba hamsin a cikinsu yana yi musu wa’azi amma suka ƙaryata shi. Dalili kenan ya sa ya roƙi Allah ya hallaka su gaba ɗayansu. Bayan Allah ya karɓi addu’ar Annabi Nuhu, sai kuma ya yabi kansa da gaggauta amsa addu’ar bayinsa nagari da yake yi yayin da suka roƙe shi. Haka kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kuɓutar da Annabinsa Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da iyalan gidansa da waɗanda suka yi imani da shi daga cutarwar mutanensa, da kuma azabar nutsewa a ruwan Ɗufana wanda ya hallaka su da shi baki ɗaya. Babu wanda ya yi saura a bayan ƙasa sai zurriyarsa, ya kuma zama abin yabo a cikin al’ummun da suka zo daga baya. Sannan Allah ya tabbatar masa da aminci da kuɓuta daga duk wata mummunar magana da za a faɗa a kansa, sai dai a yi ta ambaton sa da alheri ana yabon sa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa irin wannan kyakkyawan sakamako da ya yi wa Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) irinsa ne yake yi wa bayinsa masu kyautata ibadarsu da yi masa ɗa’a. Kuma shi Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana cikin manyan bayinsa muminai masu biyayya gare shi, kuma sauran al’ummarsa gaba ɗaya da suka bijire ya nutsar da su cikin ruwan Ɗufana wanda ya aiko musu.
۞وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبۡرَٰهِيمَ
Open ayah 37:83Lalle kuma Ibrahimu yana daga mabiya addininsa.
إِذۡ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلۡبٖ سَلِيمٍ
Open ayah 37:84A yayin da ya zo wa Ubangijinsa da lafiyayyar zuciya.
إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَاذَا تَعۡبُدُونَ
Open ayah 37:85Lokacin da ya ce da babansa da kuma mutanensa: “Me kuke bauta wa ne?
أَئِفۡكًا ءَالِهَةٗ دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ
Open ayah 37:86“Yanzu iyayen giji na ƙarya ba Allah ba kuke nufi?
فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 37:87“To mene ne tsammaninku game da Ubangijin talikai?”
فَنَظَرَ نَظۡرَةٗ فِي ٱلنُّجُومِ
Open ayah 37:88Sai ya yi duba a cikin taurari, duba na tunani.
فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٞ
Open ayah 37:89Sannan ya ce: “Lalle ni fa ba ni da lafiya.”
فَتَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ مُدۡبِرِينَ
Open ayah 37:90Sai suka juya daga wurinsa suna masu ba da baya.
فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمۡ فَقَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 37:91Sai ya saɗaɗa zuwa ga gumakansu ya ce (da su): “Yanzu ba za ku ci (abincin da ke gabanku) ba?
مَا لَكُمۡ لَا تَنطِقُونَ
Open ayah 37:92“Me ya sa ba kwa yin magana ne?”
فَرَاغَ عَلَيۡهِمۡ ضَرۡبَۢا بِٱلۡيَمِينِ
Open ayah 37:93Sai ya yi kansu yana duka da hannunsa na dama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa yana daga cikin mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka rungumi Tauhidi da kiran mutane zuwa ga Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tuna lokacin da Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya je wa Ubangijinsa da lafiyayyar zuciya wadda babu shirka a cikinta, ya kuma zamanto mai nasiha ga mutanensa, har da mahaifinsa lokacin da ya zarge su da bautar wani ba Allah ba. Ya ƙalubalance su da cewa ta yaya za su yarda su riƙa bauta wa allolin ƙarya su bar Ubangijinsu Allah (Mai tsarki da daukaka)? Kuma me suke zato ne daga Allah Ubangijin talikai idan har suka haɗu da shi suna kan bauta wa wasu ba shi ba? Me suke tsammanin zai saka musu da shi?! Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga tunanin yadda zai raba mutanensa da gumakansu da suke bauta wa ba Allah ba, sai ya shirya dabarar da zai kakkarya su bayan mutanensa sun tafi wajen bukukuwansu, shi kuma ya ƙi bin su, ya nuna musu cewa ba shi da lafiya ne don haka ba zai iya fita tare da su ba. Sai suka bar shi suka juya suka tafi. Ganin wannan dama da ta samu sai Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya saɗaɗa da sauri wajen allolinsu domin ya farfasa su. Sai ya samu an ajiye musu dangogin abinci iri-iri wai don su sa musu albarka; sai ya yi musu magana cikin izgili cewa, me ya sa ba za su ci abincin da masu bautar su suka kawo musu ba? Kuma me ya sa ba sa amsa wa mai tambayar su magana? Yana nufin ta yaya za a ce waɗannan su ne ababan bauta? Daga nan sai ya yi kansu yana dukan su da hannunsa na dama domin ya kakkarya su. Ya kuwa yi rugurugu da su gaba ɗayansu sai babbansu kawai ya bari don mutanensa idan sun komo ya yi musu wa’azi da shi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ibrahimu bai taɓa yin ƙarya ba sai sau uku, biyu daga cikinsu ya yi su ne don Allah (Mai tsarki da daukaka) a faɗarsa: “Lalle ni ba ni da lafiya;” da faɗarsa: “A’a, wannan babban nasu shi ya aikata shi.” Annabi (ﷺ) ya ce: “Wata rana shi da matarsa Saratu suka je ga wani azzalumin sarki, sai aka faɗa masa cewa akwai wani mutum yana nan tare da matarsa mai matuƙar kyau. Sai ya aika aka zo da Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tambaye shi: “Wace ce wannan?” Sai ya ce: ‘Yar’uwata ce.’ Sai kuma ya sami matarsa Saratu ya faɗa mata cewa: ‘Ya Saratu, a duk bayan ƙasa babu wani mumini daga ni sai ke, to Sarki ya tambaye ni ke wace ce, na ce masa ke ‘yar’uwata ce, don haka kada ki ƙaryata ni.’ Sai Sarki ya aika aka zo masa da Saratu, ya miƙa hannunsa zai taɓa ta sai hannunsa ya ƙage. Sai ya ce mata: ‘Ki roƙa mini Allah, ba zan cutar da ke ba.’ Sai ta roƙa masa Allah sai hannunsa ya saki, sannan ya sake miƙa hannunsa zai kama ta sai ya sake ƙagewa fiye da karon farko, sai ya nemi ta yi masa addu’a kuma ba zai cutar da ita ba, sai ta yi masa addu’a hannunsa ya saki. Daga nan sai ya kira wani dogarinsa ya ce masa: ‘Lalle fa ku ba mutum kuka kawo mini ba, kawai kun kawo mini shaiɗani ne.’ Sai ya ba ta kyautar Hajara don ta riƙa yi mata hidima…” [Bukhari #3358 da Muslim #2371].
فَأَقۡبَلُوٓاْ إِلَيۡهِ يَزِفُّونَ
Open ayah 37:94Sai (mutanensa) suka fuskanto shi suna gaggawa.
قَالَ أَتَعۡبُدُونَ مَا تَنۡحِتُونَ
Open ayah 37:95Ya ce: “Yanzu kwa riƙa bauta wa abin da kuke sassaƙawa?
وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 37:96“Alhali kuwa Allah ne Ya halicce ku, da ma abin da kuke aikatawa?”
قَالُواْ ٱبۡنُواْ لَهُۥ بُنۡيَٰنٗا فَأَلۡقُوهُ فِي ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:97Suka ce: “Ku gina masa wani gini (ku haɗa wuta a ciki), sannan ku jefa shi cikin wutar.”
فَأَرَادُواْ بِهِۦ كَيۡدٗا فَجَعَلۡنَٰهُمُ ٱلۡأَسۡفَلِينَ
Open ayah 37:98Sai suka yi nufin sa da mugun shiri, sai Muka mayar da su mafiya ƙasƙanci.
وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهۡدِينِ
Open ayah 37:99Ya kuma ce: “Lalle ni zan yi ƙaura zuwa ga Ubangijina, zai ko shiryar da ni.
رَبِّ هَبۡ لِي مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 37:100“Ya Ubangijina, Ka yi min baiwa da (ɗa) ya zama daga (mutane) nagari.”
فَبَشَّرۡنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٖ
Open ayah 37:101Sai Muka yi masa albishir da yaro mai haƙuri. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mutanen Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun dawo zuwa wurin gumakansu da gaggawa inda suka sami Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi guntu-guntu da gumakansu, sai suka fara zargin sa da aikata wani babban laifi, sai shi kuma ya fuskance su yana kushe wa mummunar aƙidarsu ta bautar gumaka, yana nuna musu wautarsu da har suke bauta wa abubuwan da su ne suka sassaƙa su da hannayensu su bar bautar Allah wanda shi ne ya halicce su har da duk aikin da suke yi, daga ciki har da sassaƙa gumakansu duk halittar Allah ne shi kaɗai, don haka shi ya cancanta su bauta wa kada su haɗa komai da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa lokacin da mutanensa suka kasa fuskantar sa da wata ƙwaƙƙwarar hujja ta bautar wasu ba Allah ba, sai suka ga gara su ɗauki mataki na amfani da ƙarfi, sai suka yi shawara game da matakin da ya kamata su ɗauka a kan Annabi Ibrahim. A ƙarshe suka yanke shawarar su yi wani gini wanda za su hura wuta a cikinsa sai su jefa shi ciki ya ƙone ƙurmus kowa ya huta. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kunyata su inda ya ce, mutanen Annabi Ibrahim sun shirya masa mummunan makirci don su hallaka shi su huta da shi, to amma sai Allah ya mayar da su su ne taɓaɓɓu waɗanda suka yi hasara duniya da lahira, domin kuwa da suka jefa shi cikin wutar sai ta zama sanyi da aminci a gare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yanke shawarar cewa shi zai yi hijira zuwa ga Ubangijinsa, ya bar garinsa da mutanensa domin ya sami damar bautar Allah cikin kwanciyar hankali, ya kuma sakankance cewa Ubangijinsa zai nuna masa alherin duniya da lahira. Sai kuma ya roƙi Allah (Mai tsarki da daukaka) da ya arzuta shi da samun ɗa nagari wanda zai zama mai taimakon sa kuma ya zamanto madadin mutanensa da ya bari ya tafi baƙunta wani gari. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya karɓi addu’arsa ya kuma yi masa albishir da samun ɗa wanda za a haifa masa shi kuma ya girma ya zama mai haƙuri da juriya. Wannan ɗa kuwa shi ne Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعۡيَ قَالَ يَٰبُنَيَّ إِنِّيٓ أَرَىٰ فِي ٱلۡمَنَامِ أَنِّيٓ أَذۡبَحُكَ فَٱنظُرۡ مَاذَا تَرَىٰۚ قَالَ يَٰٓأَبَتِ ٱفۡعَلۡ مَا تُؤۡمَرُۖ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰبِرِينَ
Open ayah 37:102To lokacin da ya kai matsayin yin aiki tare da shi, sai ya ce: “Ya kai ɗana, lalle na ga ina yanka ka a cikin mafarki, sai ka yi tunani me ka gani?” Sai ya ce: “Ya babana, ka aikata duk abin da aka umarce ka, za ka same ni insha Allahu daga cikin masu haƙuri.”
فَلَمَّآ أَسۡلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلۡجَبِينِ
Open ayah 37:103To lokacin da suka sallama wa (Allah), ya kuma kwantar da shi ta ɗaya gefe na goshinsa (da nufin ya yanka shi).
وَنَٰدَيۡنَٰهُ أَن يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُ
Open ayah 37:104Sai Muka kira shi da cewa: “Ya Ibrahimu.
قَدۡ صَدَّقۡتَ ٱلرُّءۡيَآۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:105“Haƙiƙa ka gaskata mafarkin.” Lalle Mu kamar haka ne Muke saka wa masu kyautatawa.
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡبَلَٰٓؤُاْ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 37:106Lalle wannan tabbas shi ne bala’i ƙarara.
وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٖ
Open ayah 37:107Muka kuma fanshe shi da abin yankawa mai girma.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:108Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga \'yan baya.
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ
Open ayah 37:109Aminci ya tabbata ga Ibrahimu.
كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:110Kamar haka ne Muke saka wa masu kyautatawa.
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:111Lalle shi yana daga cikin bayinmu muminai.
وَبَشَّرۡنَٰهُ بِإِسۡحَٰقَ نَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Open ayah 37:112Muka kuma yi masa albishir da Is’haƙa a matsayin Annabi daga salihai.
وَبَٰرَكۡنَا عَلَيۡهِ وَعَلَىٰٓ إِسۡحَٰقَۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحۡسِنٞ وَظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ مُبِينٞ
Open ayah 37:113Muka kuma yi masa albarka, da kuma Is’haƙa. Daga zuriyarsu kuma akwai mai kyautatawa akwai kuma mai zaluntar kansa a fili (wato kafiri). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lokacin da Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya girma ya fara fita aiki tare da mahaifinsa Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai mahaifin nasa ya yi wani mafarki cewa ya ga yana yanka ɗansa. Mafarkin annabawa kuwa gaskiya ne. Da ya gaya wa ɗansa wannan mafarki, ya kuma nemi ɗansa ya duba ya yi tunani game da wannan mafarki. Sai Isma’ila (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya amsa wa mahaifinsa cewa ya aikata duk abin da Allah ya umarce shi da shi, kuma zai same shi cikin masu haƙuri da yarda da hukuncin Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da Annabi Ibrahim da ɗansa suka miƙa wuya ga hukuncin Allah suka sallama masa, sai Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kwantar da ɗansa Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a gefen goshinsa don ya cika umarnin Allah ya yanka shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira shi da sunansa Ibrahim, ya tabbatar masa cewa, lalle shi ya gaskata mafarkin da ya yi tunda ga shi yana ƙoƙarin yanka ɗansa, Allah ya yaba masa da karɓar jarrabawar da ya yi masa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle wannan jarrabawar wani bala’i ne a fili, kuma Annabi Ibrahim ya yi nasarar cinye wannan jarrabawar. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fanshi Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da wani rago babba wanda Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yanka a madadinsa. Allah kuma ya wanzar da kyakkyawan yabo ga Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a cikin al’ummun da suka zo bayansa, ya kuma tabbatar masa da aminci da kuɓuta daga duk wani sharri ko abin ƙi, ya nuna cewa kamar yadda ya yi wa Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) irin wannan sakamako to hakanan yake saka wa duk wasu masu kyautatawa, domin Annabi Ibrahim lalle ya kasance daga bayin Allah muminai masu cika bautarsu ga Allah da yi masa biyayya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Annabi Ibrahim albishir da samun wani ɗan, shi ne Is’haƙ wanda shi ma zai zama Annabi kuma bawa nagari, sakamakon biyayyar da ya yi wa Allah game da yarda ya yanka ɗansa ɗaya a lokacin, watau Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya yi wa Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ɗansa Is’haƙa albarka daga gare shi, ya yawaita musu ni’imominsa, daga cikinsu akwai yawan ‘ya’ya da ya ba su waɗanda a cikinsu akwai masu kyautatawa masu bin Allah, akwai kuma masu zaluntar kansu da kafirci da saɓon Allah da kuma bayyana zaluncinsu a fili.
وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Open ayah 37:114Haƙiƙa kuma Mun yi ni’ima ga Musa da Haruna.
وَنَجَّيۡنَٰهُمَا وَقَوۡمَهُمَا مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 37:115Muka kuma tserar da su da mutanensu daga babban baƙin ciki.
وَنَصَرۡنَٰهُمۡ فَكَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ
Open ayah 37:116Muka kuma taimake su, sai suka kasance su ne masu rinjaye.
وَءَاتَيۡنَٰهُمَا ٱلۡكِتَٰبَ ٱلۡمُسۡتَبِينَ
Open ayah 37:117Muka kuma ba su Littafi mabayyani (Attaura).
وَهَدَيۡنَٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ
Open ayah 37:118Muka kuma shiryar da su hanya madaidaiciya.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِمَا فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:119Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare su ga \'yan baya.
سَلَٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Open ayah 37:120Aminci ya tabbata ga Musa da Haruna.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:121Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa.
إِنَّهُمَا مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:122Lalle suna daga cikin bayinmu muminai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babbar baiwar da ya yi wa Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna ((). domin ya ba su annabta, ya kuma tserar da su da mutanensu Banu Isra’ila daga ƙangin bauta a hannun Fir’auna da jama’arsa. Ya kuma kuɓutar da su daga nutsewa a cikin ruwa, a ƙarshe ya ba su nasara a kan maƙiyansu Fir’auna da rundunarsa. Ya kuma ba wa Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna (() littafin Attaura bayyananne da babu rikitarwa a cikinsa, Allah kuma ya shiryar da su tafarki madaidaici wanda babu karkata a tare da shi, shi ne addinin Musulunci mai kai wa zuwa ga samun yardar Allah (Mai tsarki da daukaka), ya kuma wanzar musu da kyakkyawan yabo a cikin al’ummun da suka zo a bayansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa aminci ya tabbata ga Annabi Musa da ɗan’uwansa Haruna ((). Kuma kamar yadda Allah ya kyautata sakamako gare su saboda su ma sun kyautata, to hakanan yake saka wa bayinsa nagari masu biyayya ga Allah da kyautata wa bayinsa. Sannan ya tabbatar da cewa Annabi Musa da Haruna suna cikin bayinsa muminai masu aiki da shari’arsa.
وَإِنَّ إِلۡيَاسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:123Kuma lalle Ilyasu tabbas yana daga cikin manzanni.
إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ
Open ayah 37:124Lokacin da ya ce da mutanensa: “Yanzu ba za ku kiyaye dokokin (Allah) ba?
أَتَدۡعُونَ بَعۡلٗا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ
Open ayah 37:125“Yanzu kwa riƙa bauta wa (gunkin) Ba’alu ku riƙa barin Mafi iya kyautata halitta?
ٱللَّهَ رَبَّكُمۡ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 37:126“(Wato) Allah Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko?”
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ
Open ayah 37:127Sai suka ƙaryata shi, to don haka, lalle za a halarto da su (wuta).
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:128Sai dai bayin Allah waɗanda aka tsarkake.
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 37:129Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga \'yan baya.
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِلۡ يَاسِينَ
Open ayah 37:130Aminci ya tabbata ga Ilyasu.
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 37:131Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa.
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 37:132Lalle shi yana daga bayinmu muminai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin cewa Annabi Iliyasu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana daga cikin manzanninsa da ya ni’imta da annabta da kuma manzanci, lokacin da ya aika shi zuwa ga mutanensa Banu Isra’ila, don ya gargaɗe su a kan su kiyaye dokokin Allah su bi umarninsa su guji haninsa, su kuma rungumi Tauhidi su guje wa shirka. Ya zarge su da cewa yanzu sa riƙa bauta wa gunkin Ba’alu , su yi watsi da bautar mahaliccinsu wanda ya fi kowa kyautata halitta, watau Allah wanda shi ne Ubangijin da ya halicce su ya halicci iyayensu, shi ne kuma kaɗai wanda ya cancanci a bauta masa ba gumakan da ba sa amfanarwa ba sa kuma cutarwa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mutanensa ba su yi wata-wata ba sai suka ƙaryata shi, a dalilin haka suka zamanto waɗanda za a tattara su a wuta don yi musu azaba. Amma sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya togace bayinsa daga cikinsu waɗanda aka tsarkake su daga bautar wani ba Allah ba. Ya kuma wanzar wa da Annabi Iliyasu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kyakkyawan yabo a cikin al’ummun da suka zo bayansa. Amincin Allah da yabonsa kuma su tabbata ga Annabinsa Iliyasu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kamar yadda ya saka wa Annabi Iliyasu to hakanan zai yi kyakkyawan sakamakonsa ga bayinsa muminai masu kyautatawa. Ya kuma shaide shi da cewa lalle yana cikin bayinsa muminai na gaskiya masu tsoron Allah.
وَإِنَّ لُوطٗا لَّمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:133Lalle kuma Luɗu tabbas yana daga cikin manzanni.
إِذۡ نَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 37:134(Ka tuna) sanda Muka tserar da shi tare da iyalinsa baki ɗaya.
إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ
Open ayah 37:135Sai dai wata tsohuwa (wato matarsa) da take cikin halakakku.
ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Open ayah 37:136Sannan Muka hallakar da sauran.
وَإِنَّكُمۡ لَتَمُرُّونَ عَلَيۡهِم مُّصۡبِحِينَ
Open ayah 37:137Kuma lalle ku tabbas kuna wucewa ta wajan (gidajensu) da asussuba.
وَبِٱلَّيۡلِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Open ayah 37:138Da kuma cikin dare. Yanzu ba kwa hankalta ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ɗaya ne daga cikin manzannin da ya aika ga mutanensa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aika shi zuwa ga mutanen Sadum waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen neman maza da aikata miyagun ayyuka tare da yin shirka da Allah. Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya gargaɗe su ya yi musu wa’azi amma ba su ɗauka ba, sai Allah ya aiko musu da azabarsa ta hallaka su, ya kuma tserar da Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da iyalansa in ban da wata tsohuwa, watau matarsa wadda azabar Allah ta ritsa da ita tare da mutanensa, saboda kafircinta da bijire wa gargaɗin mijinta Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jawo hankalin mutanen Makka waɗanda suke wucewa ta gaban gidajen waɗannan mutane da ya hallaka safe da yamma lokacin tafiye-tafiyensu zuwa Sham, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gaya musu cewa, me ya sa ba za su hankalta ba, su ɗauki izina daga mummunan makomar masu ƙaryata Allah da manzanninsa da dogewa a kan kafirci da saɓon Allah?
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:139Kuma lalle Yunusa tabbas yana daga cikin manzanni.
إِذۡ أَبَقَ إِلَى ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
Open ayah 37:140(Ka tuna) lokacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwan da yake maƙare.
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُدۡحَضِينَ
Open ayah 37:141Sannan ya shiga ƙuri’a, sai ya zama cikin waɗanda aka yi galaba a kansu.
فَٱلۡتَقَمَهُ ٱلۡحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٞ
Open ayah 37:142Sai kifi ya haɗiye shi, alhali yana abin zargi.
فَلَوۡلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُسَبِّحِينَ
Open ayah 37:143Ba don dai shi ya zama daga masu tsarkake Allah (da yawan tasbihi) ba.
لَلَبِثَ فِي بَطۡنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
Open ayah 37:144Tabbas da ya zauna a cikin cikinsa har zuwa ranar da za a tashe su.
۞فَنَبَذۡنَٰهُ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٞ
Open ayah 37:145Sai Muka jefa shi a tudu, a halin yana cikin rashin lafiya.
وَأَنۢبَتۡنَا عَلَيۡهِ شَجَرَةٗ مِّن يَقۡطِينٖ
Open ayah 37:146Muka kuma tsirar masa wata bishiya ta kabewa.
وَأَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ مِاْئَةِ أَلۡفٍ أَوۡ يَزِيدُونَ
Open ayah 37:147Muka kuma aika shi zuwa ga mutum dubu ɗari, ko kuma sama da haka.
فَـَٔامَنُواْ فَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ
Open ayah 37:148Sai suka yi imani, sai Muka jiyar da su daɗi har zuwa wani lokaci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar da cewa shi ma ɗaya ne daga cikin manzanninsa. Amma kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci irin uƙubar da ya yi masa sannan ya kuɓutar da shi daga gare ta saboda imaninsa da kyawawan ayyukansa. Laifinsa shi ne ya gudu ya bar mutanensa waɗanda suka yi imani da shi bayan ya yi musu wa’azi. Ya je ya shiga cikin wani jirgin ruwan da yake maƙare da mutane da kayayyaki. Sai jirgin ruwan nan ya tasam ma nutsewa a ruwa saboda ya yi cikar da ta fi ƙarfinsa, sai mutanen cikinsa suka yi ƙuri’a, domin su jefa ɗaya daga cikinsu cikin ruwa su rage wa jirgin nauyi, don kauce wa nutsewar jirgin su hallaka gaba ɗaya a ruwa, sai ko ƙuri’ar ta faɗa a kan Annabi Yunusa sai suka jefa shi cikin ruwa. Jefa shi ruwa ke da wuya sai kifi ya haɗiye shi, domin ya aikata abin da za a zarge shi da shi, watau gudowa ya bar mutanensa ba tare da izinin Allah Ubangijinsa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba don Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana cikin mutane masu yawan tasbihi da tsarkake Ubangiji kafin faruwar haka ba, da kuma lokacin zamansa a cikin cikin kifi, to da ya yi ta zama cikin cikin kifin har zuwa ranar alƙiyama, domin zai zama shi ne ƙabarinsa; to amma saboda tasbihinsa da bautarsa ga Allah sai Allah ya tserar da shi daga wannan uƙuba ta duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya jefo shi daga cikin kifi zuwa tsandaurin ƙasa wanda babu tsirrai a kansa, alhali yana cikin rashin lafiya saboda zamansa a cikin wannan kifin. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsirar masa da bishiyar kabewa domin ya rufe tsiraicinsa da ganyenta, ya kuma ci ‘ya’yanta, ya kuma sha inuwarta. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani maɗinki ya yi abinci ya gayyaci Manzon Allah (ﷺ) sai na bi shi. Sai ya kawo wa Manzon Allah (ﷺ) gurasa da romo da ke da kabewa a cikinsa, sai na ga Manzon Allah (ﷺ) yana bibiyar gefe-gefen akushin abincin yana tsintar kabewar da ke ciki, tun daga wannan ranar na ji ina son kabewa.” [Bukhari #2092 da Muslim #2041]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya sake aika Annabi Yunusa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa mutanensa su dubu ɗari ko ma sun fi haka, sai suka yi imani suka ba da gaskiya da abin da ya zo musu da shi, sai Allah ya ƙyale su suka ci gaba da jin daɗin rayuwarsu har zuwa lokacin ajalinsu da ya iyakance musu.
فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَلِرَبِّكَ ٱلۡبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلۡبَنُونَ
Open ayah 37:149Ka tambaye su: Yanzu Ubangijinka ne Yake da ‘ya’ya mata, su kuma suna da ‘ya’ya maza?
أَمۡ خَلَقۡنَا ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ إِنَٰثٗا وَهُمۡ شَٰهِدُونَ
Open ayah 37:150Ko kuma Mun halicci mala’iku ne ‘ya’ya mata a gaban idonsu suna gani?
أَلَآ إِنَّهُم مِّنۡ إِفۡكِهِمۡ لَيَقُولُونَ
Open ayah 37:151Ku saurara! Lalle su saboda ƙaryarsu har suna cewa:
وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Open ayah 37:152“Allah Ya haihu!” Lalle kuwa su tabbas maƙaryata ne.
أَصۡطَفَى ٱلۡبَنَاتِ عَلَى ٱلۡبَنِينَ
Open ayah 37:153Yanzu Ya zaɓi ‘ya’ya mata a kan ‘ya’ya maza?
مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ
Open ayah 37:154Me ya same ku, ƙaƙa kuke yin irin wannan hukunci?
أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 37:155Me ya sa ne ba kwa wa’azantuwa?
أَمۡ لَكُمۡ سُلۡطَٰنٞ مُّبِينٞ
Open ayah 37:156Ko kuwa kuna da wata hujja ne bayyananniya?
فَأۡتُواْ بِكِتَٰبِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 37:157To ku kawo rubutaccen littafinku idan kun kasance masu gaskiya.
وَجَعَلُواْ بَيۡنَهُۥ وَبَيۡنَ ٱلۡجِنَّةِ نَسَبٗاۚ وَلَقَدۡ عَلِمَتِ ٱلۡجِنَّةُ إِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ
Open ayah 37:158Suka kuma sanya dangantakar nasaba tsakaninsa da mala’iku. Lalle kuwa su mala’iku sun san cewa tabbas su (masu wannan da’awar) za a kawo su (cikin wuta).
سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Open ayah 37:159Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffanta (Shi da shi).
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:160Sai dai bayin Allah waɗanda aka tsarkake. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambayi mushirikai masu cewa mala’iku mata ne kuma ‘ya’yan Allah ne cewa, yanzu sa zaɓa wa Allah (Mai tsarki da daukaka) ‘ya’ya mata su kuma su zaɓa wa kansu ‘ya’ya maza tare da cewa suna fifita ‘ya’ya maza a kan ‘ya’ya mata? Wane irin rabo ne na zalunci suke yi haka? Kuma da suke cewa mala’iku mata ne, to shin suna nan ne lokacin da Allah ya halicci mala’ikun har suka tabbatar da cewa mata ne? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa wannan shaci-faɗi ne kawai da ƙarya suke yi. Kuma jingina wa Allah ɗa ba komai ba ne sai ƙagensu da ƙaryar da suke yi masa. Ba shakka sun tabbata manyan maƙaryata. Kuma wane irin hukunci ne a ce shi Allah ya zaɓa wa kansa ‘ya’ya mata waɗanda su suke ganin nakasa ne a gare su, ya bar ‘ya’ya maza waɗanda su suke ganin su kamala ne a gare su? Allah ya tambaye su cewa me ya sa suke irin wannan ɗanyen hukunci wanda sun tabbatar a riyawarsu cewa babu adalci a cikinsa? Ya kuma nuna musu cewa, da tun farko sun tsaya sun yi tunani da sun gane ɓarnar da suke a kai da muguwar aƙidar da suka runguma. To me ya hana su yin tunani ne? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa soki-burutsu ne kawai suke yi, don ba su da wata rubutacciyar hujja daga Allah a kan abin da suke da’awa. Idan kuwa har suna ganin akwai ta to sai su kawo littafin da ya nuna hakan idan sun kasance suna da gaskiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, mushirikai sun sanya wata dangantaka ta nasaba tsakanin Allah (Mai tsarki da daukaka) da mala’iku waɗanda suke ɓoye ba a ganin su, suka ce wai ‘ya’yan Allah ne mata, alhali su mala’ikun sun san cewa sai Allah ya titse masu wannan da’awar ya yi musu hisabi a kanta. Wasu malaman tafsiri sun fassara wannan ayar da cewa, mushirikai sun sanya wata dangantaka tsakanin Allah da aljannu, yayin da suka yi da’awar cewa ya yi aure daga cikin aljannu, ta nan kuma ne wai ya samu ‘ya’ya mata, watau su ne mala’iku. Sai Allah ya tabbatar musu da cewa, su waɗannan aljannu da ake ƙaryar danganta alaƙar aure da su sun san cewa waɗannan maƙaryatan tabbas sai an halarto da su zuwa ga azabar Allah, saboda girman laifinsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkake kansa daga duk wani abu na shirka da mushirikai suke danganta shi da shi, kamar ‘ya’ya da abokan tarayya. Ya kuma yabi bayinsa waɗanda aka tsarkake su daga aikata duk wata shirka, sun kuma kasance bayi nagari masu tsarkake Allah.
فَإِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ
Open ayah 37:161Lalle ku da abin da kuke bauta wa.
مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ بِفَٰتِنِينَ
Open ayah 37:162Ba za ku iya ɓatar da kowa da shi ba.
إِلَّا مَنۡ هُوَ صَالِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 37:163Sai dai wanda zai shiga wutar Jahima.
وَمَا مِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٞ مَّعۡلُومٞ
Open ayah 37:164(Jibrilu ya ce da Mala’iku): “Ba ɗai daga cikinmu face yana da wani matsayi sananne.
وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلصَّآفُّونَ
Open ayah 37:165“Lalle kuma mu masu yin sahu ne.
وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡمُسَبِّحُونَ
Open ayah 37:166“Kuma lalle mu masu yin tasbihi ne.”
وَإِن كَانُواْ لَيَقُولُونَ
Open ayah 37:167Kuma lalle su (kafirai) sun kasance suna cewa:
لَوۡ أَنَّ عِندَنَا ذِكۡرٗا مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 37:168“Da muna da wani littafi irin na mutanen farko.
لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Open ayah 37:169“Tabbas da mun kasance bayin Allah waɗanda aka tsarkake.”
فَكَفَرُواْ بِهِۦۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 37:170(Yayin da Alƙur’ani ya zo musu) sai suka kafirce da shi; to ba da daɗewa ba za su sani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mushirikai cewa, lalle su da abin da suke bauta wa ba Allah ba, ba su da ikon ɓatar da wani daga kan hanyar gaskiya sai wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zartar masa da hukuncin cewa shi ɗan wuta ne. To wannan shi ne wanda hukuncin Allah zai tabbata a kansa, sai ko ya kafirta ya mutu ya shiga wutar Jahannama. Don haka kada mushirikai su zaci cewa suna da wani iko su da allolinsu na ƙarya a kan ɓatar da muminai daga hanyar Allah su koma ga kafirci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mala’iku sun tabbatar da matsayinsu na kasancewarsu bayin Allah masu yi masa cikakkiyar biyayya, ba sa saɓa masa daidai da ƙiftawar ido, domin kowanne a cikinsu yana da wani matsayi sananne na bautar Allah da yi masa ɗa’a, kuma dukkansu masu tsayuwa ne sahu-sahu suna bautar sa, hakanan suna tasbihi da tsarkake shi daga duk wata siffa wadda ba ta kamace shi ba, don haka su sun nesanta kansu daga duk ƙarairayin da mushirikai suke yi game da su da kiran su ‘ya’yan Allah mata. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin cika-baki da mushirikan Makka suka riƙa yi kafin a aiko musu da Manzon Allah (ﷺ) inda suke riya cewa, da a ce suna da wani littafi irin na mutanen farko, watau kamar Attaura da Allah ya saukar wa Banu Isra’ila, to da su ma sun kasance bayin Allah masu tsarkake ibada gare shi don su zama zaɓaɓɓu a wurinsa, alhalin kuwa ƙarya suke yi, domin ga shi nan Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da Alƙur’ani amma sun ƙaryata shi sun kafirce wa abin da ya zo musu da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya razana su da cewa ba da daɗewa ba za su gamu da abin da yake jiran su na azaba.
وَلَقَدۡ سَبَقَتۡ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:171Haƙiƙa kuma kalmarmu (ta ba da nasara) ta rigaya ga bayinmu manzanni.
إِنَّهُمۡ لَهُمُ ٱلۡمَنصُورُونَ
Open ayah 37:172Lalle su tabbas su ne ababen taimako.
وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ
Open ayah 37:173Kuma lalle rudunarmu tabbas su ne masu yin galaba.
فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ
Open ayah 37:174Sai ka rabu da su har zuwa wani lokaci.
وَأَبۡصِرۡهُمۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ
Open ayah 37:175Kuma ka ganar da su (sakamakon kafirci), sannan ba da daɗewa ba za su gani.
أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ
Open ayah 37:176Yanzu azabarmu suke neman gaggautowa?
فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمۡ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Open ayah 37:177To lokacin da (azabar) ta sauka a sararin gidajensu, ai asubar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta munana.
وَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ
Open ayah 37:178Kuma ka rabu da su har zuwa wani lokaci.
وَأَبۡصِرۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ
Open ayah 37:179Ka kuma ganar (da su sakamakon kafirci), ba da daɗewa ba za su gani.
سُبۡحَٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلۡعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ
Open ayah 37:180Ubangijinka wanda yake Ubangiji ne Mabuwayi Ya tsarkaka daga abin da suke sifanta (Shi da shi).
وَسَلَٰمٌ عَلَى ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Open ayah 37:181Aminci kuma ya tabbata bisa ga manzanni.
وَٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 37:182Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai. A ayoyin ƙarshe na wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa ya riga ya yi alƙawari tun farko ga manzanninsa da cewa, su ne za su yi nasara a kan abokan gabarsu bisa ga hujja da Allah ya hore musu, ya kuma tabbatar musu da cewa lalle rundunarsa waɗanda suke yaƙi domin ɗaukaka addininsa su ne za su yi galaba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya kawar da kansa daga mushirikai masu nuna masa tsangwama da ƙiyayya, har zuwa wani lokaci sananne a wurin Allah, yayin da azabarsa za ta afka musu, don haka ya saurara musu ya ga abin da zai same su na azabar Allah, su ma ba da daɗewa ba za su gane lokacin da ganewar ba za ta amfane su ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da su game da gaggauto da azabarsa da suke yi da cewa, lokacin da azabarsa za ta sauka gare su, to asubahinsu ta wannan ranar ta muninta ya tsananta. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya yi wa Yahudawan Khaibara sammako a lokacin da su kuma sun fita zuwa gonakinsu da fartanyoyinsu. Lokacin da suka yi kiciɓis da Manzon Allah (ﷺ) sai suka juya a guje suna cewa ga Muhammadu nan da rundunarsa. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allahu Akbar, Khaibara ta rushe! Lalle mu duk mutanen da muka dira a farfajiyar gidajensu, to asubar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta munana.” [Bukhari #371 da Muslim #1365]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya kawar da kansa daga waɗannan mushirikai ya ƙyale su har zuwa lokacin da Allah zai yanke hukuncinsa a kansu, ya saurara ya jira lokacin zuwan azabarsa a gare su, su ma za su gani. A ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe Surar da tsarkake kansa daga dukkan tawaya da aibu da mushirikai suke danganta shi da su. Ya tabbatar da aminci da yabo ga manzanninsa, kuma dukkan yabo da kirari da godiya sun tabbata gare shi; shi ne Ubangijin halittu baki ɗaya.