ص

Saad

The letter Saad · Surah 38 · Ayahs: 88 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. صٓۚ وَٱلۡقُرۡءَانِ ذِي ٱلذِّكۡرِ

    Open ayah 38:1

    SAD. “Na rantse da Alƙur’ani ma’abocin ɗaukaka.

  2. بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي عِزَّةٖ وَشِقَاقٖ

    Open ayah 38:2

    Sai dai <b> waɗanda suka kafirta suna cikin girman kai ne da jayayya.

  3. كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّن قَرۡنٖ فَنَادَواْ وَّلَاتَ حِينَ مَنَاصٖ

    Open ayah 38:3

    Al\'ummu nawa Muka hallaka gabaninsu, sai suka yi ta kururuwar neman agaji, alhali kuwa lokacin ba na neman tsira ba ne.

  4. وَعَجِبُوٓاْ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٞ مِّنۡهُمۡۖ وَقَالَ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا سَٰحِرٞ كَذَّابٌ

    Open ayah 38:4

    Suka kuma yi mamaki don mai gargaɗi ya zo musu daga cikinsu; kuma kafirai suka ce: “Wannan mai sihiri ne babba </b>n maƙaryaci.

  5. أَجَعَلَ ٱلۡأٓلِهَةَ إِلَٰهٗا وَٰحِدًاۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٌ عُجَابٞ

    Open ayah 38:5

    “Yanzu yaya zai mayar da alloli Allah guda ɗaya? Lalle wannan abu ne mai ban mamaki.”

  6. وَٱنطَلَقَ ٱلۡمَلَأُ مِنۡهُمۡ أَنِ ٱمۡشُواْ وَٱصۡبِرُواْ عَلَىٰٓ ءَالِهَتِكُمۡۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٞ يُرَادُ

    Open ayah 38:6

    Manyansu kuma suka tafi (suna cewa): “Ku yi tafiyarku, kuma ku yi haƙuri a kan (bautar) allolinku; lalle wannan wani shiryayyen abu ne ake nufi.

  7. مَا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِي ٱلۡمِلَّةِ ٱلۡأٓخِرَةِ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا ٱخۡتِلَٰقٌ

    Open ayah 38:7

    “Ba mu taɓa jin irin wannan ba a addinin da ya wuce, wannan ba komai ba ne sai ƙage.

  8. أَءُنزِلَ عَلَيۡهِ ٱلذِّكۡرُ مِنۢ بَيۡنِنَاۚ بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ مِّن ذِكۡرِيۚ بَل لَّمَّا يَذُوقُواْ عَذَابِ

    Open ayah 38:8

    “Yanzu a saukar masa da Alƙur\'ani a tsakaninmu?” Ba haka ba ne, su dai suna kokwanto ne game da tunatarwata; bar su, ai har yanzu ba su ɗanɗani azabata ba ne.

  9. أَمۡ عِندَهُمۡ خَزَآئِنُ رَحۡمَةِ رَبِّكَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡوَهَّابِ

    Open ayah 38:9

    Ko kuwa a wurinsu ne taskokin rahamar Ubangijinka Mabuwayi Mai baiwa suke?

  10. أَمۡ لَهُم مُّلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۖ فَلۡيَرۡتَقُواْ فِي ٱلۡأَسۡبَٰبِ 

    Open ayah 38:10

    Ko kuma mulkin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu nasu ne? To sai su kama hanyoyin zuwa sama (domin su aikata abin da suke so).

  11. جُندٞ مَّا هُنَالِكَ مَهۡزُومٞ مِّنَ ٱلۡأَحۡزَابِ

    Open ayah 38:11

    (Waɗannan) wata runduna ce da za a murƙushe ta, kamar sauran al’ummun da suka gabata (waɗanda suka ƙaryata manzanninsu). An buɗe wannan sura da hafarin ‘Sad’, kamar yadda aka buɗe wasu surori da haruffa irinsa. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara domin ƙarin bayani a kan waɗannan haruffan]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da Alƙur’ani ma’abocin ɗaukaka wanda kuma ya ƙunshi tunatar da mutane da abin da zai amfane su a duniya da lahira. Ya kuma bayyana cewa kafirai maimakon su yi imani da Alƙur’ani sai suka yi girman kai game da Tauhidi, suka kuma dinga saɓani da Annabi (ﷺ) da nuna masa ƙiyayya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da su da cewa ya hallaka al’ummu da dama a gabaninsu yayin da suka ƙaryata manzanninsa. Kuma lokacin da azabar Allah ta zo musu sun yi ta kururuwar neman taimako domin a tserar da su, to amma sun makaro, domin lokacin tsira ya riga ya wuce, don haka suka yi ta ihu a banza. Saboda haka su ma kafiran wannan al’umma lallai su shiga taitayinsu kafin irin haka ya faru gare su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai sun riƙa mamakin wai ta yaya wani manzo zai zo daga cikinsu yana yi musu gargaɗi game da azabar Allah idan ba su bar abin da suke yi na kafirci ba. Maimakon su saurare shi su gaskata shi sai suka shiga tuhumar sa da cewa, shi mai sihiri ne da yake sihirce mutane suna bin shi, kuma maƙaryaci ne yana da’awar manzanci ne kawai ba bisa gaskiya ba. Suka kuma ƙaryata duk wasu hujjoji da ya nuna musu na manzancinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa babban abin da ya ba wa kafirai mamaki game da Annabi (ﷺ) shi ne wai ta yaya zai mayar da ababen bauta su zama ɗaya, watau shi ne Allah? Suna ganin wannan abu ya isa abin mamaki a gare su. Daga nan sai manyansu suka tafi suna faɗa wa mabiyansu cewa su ci gaba da tabbata a kan abin da suke kai na bautar gumakansu, kada su sake su, kada wanda ya kuskura ya shiga addinin Muhammadu (ﷺ), su ƙanƙame wa addinin iyaye da kakanni. Suka kuma nuna wa mabiyansu cewa wai abin da Annabi (ﷺ) yake kiran su zuwa gare shi na bautar Allah shi kaɗai wani shiryayyen abu ne da ya ƙulla don ya mallake su su zama mabiyansa. Kuma wannan addini da ya zo musu da shi sabo ne a wurinsu, wai su ba su taɓa jin labarin bautar Allah shi kaɗai ba daga wurin iyayensu, ko ma a cikin addinin Annabi Isa, ba su taɓa jin an ce a kaɗaita abin bauta ba; su wannan abu da ake faɗa musu ba komai ba ne sai tantagaryar ƙarya. Kuma wani babban abin takaici da ban haushi a wurinsu shi ne wai a rasa wanda za a ba wa manzanci a saukar masa da wahayi a tsakaninsu sai Annabi Muhammadu (ﷺ), alhali su ne manyan mutane da suka fi cancanta, amma ba a saukar musu da komai ba? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa ba haka ne ba, su dai kawai suna kokwanto ne game da wahayin da ya yi wa Manzonsa, kuma har yanzu ba su ɗanɗani azabarsa ba ne; sun kuma ruɗu da saurara musu da ya yi. Da a ce sun ɗanɗani azabar Allah da ba su riƙa zaƙewa cikin kafirci da kokwanton wahayi ba. Game da jayayyar da suke yi kuma a kan an bai wa Annabi Muhammadu (ﷺ) manzanci ba a ba wa wani daga cikin manyansu ba, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, shin ko taskokin rahamarsa mallakarsu ne, don haka su ne za su zaɓi wanda zai yi wa baiwa da manzanci da wanda zai hana? Babu shakka taskokin komai a hannun Allah suke, shi ne yake zaɓar wanda ya ga dama ya ba shi annabta. Sannan ya sake tambayar su cewa, shin ko su ne suke da mulkin sammai da ƙasa da abin da yake cikinsu, don haka suka zamanto su ne masu haƙƙin bayarwa ko hanawa? Idan har sun ce haka ne to ai sai su kama hanyar da za ta kai su zuwa saman don su riƙa zartar da hukuncin bayarwar da hanawar daga can. Su ma kuwa sun san ba haka abin yake ba. Mulkin sammai da ƙasa da duk abin da suka ƙunsa a hannun Allah suke shi kaɗai, yana kuma aikata abin da ya ga dama babu mai ikon hana shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, su waɗannan kafiran masu ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) wata `yar ƙaramar runduna ce da za a murƙushe ta cikin sauƙi kamar yadda aka murƙushe rundunonin da suka gabace ta yayin da suka ƙaryata manzannin da Allah ya aiko musu. Don haka duk yadda suka haɗa ƙarfi don su karya tsarin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi ba za su yi nasara ba.

  12. كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَعَادٞ وَفِرۡعَوۡنُ ذُو ٱلۡأَوۡتَادِ

    Open ayah 38:12

    Mutanen Nuhu sun ƙaryata kafin su (mutan Makka) da Adawa da Fir’auna mai turaku.

  13. وَثَمُودُ وَقَوۡمُ لُوطٖ وَأَصۡحَٰبُ لۡـَٔيۡكَةِۚ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلۡأَحۡزَابُ

    Open ayah 38:13

    Da kuma Samudawa da mutanen Luɗu da mutanen Sarƙaƙiya. Waɗannan su ne al’ummun.

  14. إِن كُلٌّ إِلَّا كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ عِقَابِ

    Open ayah 38:14

    Babu ɗaya daga cikinsu wanda bai ƙaryata manzanni ba, sai uƙubata ta wajaba (a kansu).

  15. وَمَا يَنظُرُ هَٰٓؤُلَآءِ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ مَّا لَهَا مِن فَوَاقٖ

    Open ayah 38:15

    Kuma ba abin da waɗannan suke sauraro sai busa guda ɗaya wadda ba ta da makawa.

  16. وَقَالُواْ رَبَّنَا عَجِّل لَّنَا قِطَّنَا قَبۡلَ يَوۡمِ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 38:16

    Suka kuma ce: “Ya Ubangijinmu, Ka gaggauto mana rabonmu (na azaba) tun kafin ranar hisabi!” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci al’ummu shida da suka gabata waɗanda suka ƙaryata manzannin da ya aika musu ya kuma hallaka su baki ɗaya don wannan ya zamanto darasi da izina ga mushirikai masu faɗa da gaskiyar da Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da ita. <b>Na farko </b>, su ne al’ummar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka ƙaryata shi, Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ya hallaka su da ruwan Ɗufana. <b>Na biyu </b>, su ne Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), su ma sun ƙaryata Annabinsu Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ya hallaka su da iska mai ƙaraji da ƙarfi. <b>Na uku </b>, su ne Fir’auna da mutanensa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta Fir\'auna da mai turaku waɗanda a jikinsu ne yake ɗaure Banu Isra’ila yana gana musu azaba. Da shi da rundunarsa duka Allah ya nutsar da su a cikin ruwa. <b>Na huɗu </b>, Samudawa mutanen Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sun ƙaryata shi, su ma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su da tsawa. <b>Na biyar </b>, su ne mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sun ƙaryata Annabinsu Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kifar da garinsu, ya kuma bi su da ruwan duwatsu na wuta. <b>Na shida </b>, su ne mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda su ma sun ƙaryata Manzonsu Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai Allah ya hallaka su gaba ɗayansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗannan al’ummu su ne rundunonin da suka haɗu a kan ƙaryata manzannin Allah da kafirce wa saƙon da suka zo da shi na gaskiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikin waɗannan al’ummu da bai ƙaryata manzanninsa ba, don haka uƙubarsa ta cancanta gare su, ya saukar musu da azabarsa yayin da lokacin zuwanta ya yi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kafiran da suke ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) babu abin da suke sauraro sai zuwan lokacin da za a yi busar ƙaho ta biyu wadda babu tababa game da faruwarta, dole sai ta auku. Idan ta zo to a lokacin azabar Allah za ta tabbata a kansu matuƙar sun mutu ba su tuba ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin izgili da gatsali da kafirai suke yi wa Allah game da tsoratar da su azabarsa da yake yi, suna kira suna roƙon sa cewa ya gaggauto musu da kasonsu na azaba tun a nan duniya ba sai an jira alƙiyama ta tsaya ba ranar da za a yi musu hisabi. Watau suna nuna cewa Manzon Allah (ﷺ) yana faɗa musu ƙarya ne game da batun azabar lahira, idan kuwa gaskiya ne to su fara gani tun daga nan duniya ba sai an je lahira ba.

  17. ٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَا دَاوُۥدَ ذَا ٱلۡأَيۡدِۖ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ

    Open ayah 38:17

    (Sai Allah Ya ce): “Ka yi haƙuri a kan abin da suke faɗa, ka kuma tuna bawanmu Dawuda ma’abocin ƙarfi; lalle shi ya kasance mai yawan komawa ne (ga Allah).

  18. إِنَّا سَخَّرۡنَا ٱلۡجِبَالَ مَعَهُۥ يُسَبِّحۡنَ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِشۡرَاقِ

    Open ayah 38:18

    Lalle Mu Mun hore masa duwatsu suna yin tasbihi tare da shi a yamma da hantsi.

  19. وَٱلطَّيۡرَ مَحۡشُورَةٗۖ كُلّٞ لَّهُۥٓ أَوَّابٞ

    Open ayah 38:19

    Da kuma tsuntsaye a tattare; dukkaninsu suna biyayya a gare shi.

  20. وَشَدَدۡنَا مُلۡكَهُۥ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡحِكۡمَةَ وَفَصۡلَ ٱلۡخِطَابِ 

    Open ayah 38:20

    Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, Muka kuma ba shi hikima da bayyana hukunce-hukunce (tsakanin masu husuma). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi haƙuri game da maganganu marasa daɗi da kafirai suke faɗa masa da izgilin da suke yi wa maganar Allah (Mai tsarki da daukaka), ya umarce shi da ya tuna bayin Allah manzannin da suka gabace shi da haƙurin da suka yi wajen bautar Allah (Mai tsarki da daukaka). Bayin nasa kuwa su ne, Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Allah ya ba shi ƙarfin karo da maƙiyansa da ƙarfin juriya wajen bautar Allah. Allah ya yabe shi da cewa shi mutum ne mai yawan tuba yana komawa zuwa ga Allah yana aikin da zai jawo masa yardarsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Sallar da Allah ya fi so ita ce sallar (Annabi) Dawud; azumin da Allah ya fi so shi ne azumin (Annabi) Dawud; ya kasance yana barci rabin dare, ya yi tsayuwar salla gwargwadon sulusinsa (watau ɗaya bisa ukun dare); ya yi kuma barci na sudusinsa (watau kaso ɗaya bisa shida na dare); yana kuma azumi rana ɗaya ya sha rana ɗaya (watau yana tsallaken kwana ɗaya-ɗaya).” [Bukhari #1131 da Muslim #1159]. A wata ruwaya Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kuma ba ya ja da baya a lokacin karo da abokan gaba.” [Bukhari #1977 da Muslim #1159]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu manya-manyan ni’imomi da ya yi wa Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi): <b>Ta ɗaya </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya hore masa duwatsu suna tasbihi tare da shi da yamma da kuma hantsi. An karɓo daga Ummu Hani ‘yar Abu Ɗalib Allah ya yarda da ita, ta ce: “Annabi (ﷺ) ya shigo wurina a ranar Fathu Makka ƙura ta lulluɓe shi, sai ya nemi a kawo masa kwatanniya, sai na ga alamar ɓirɓishin tuƙaƙƙen gari a cikinta, sai na zuba masa ruwa a cikinta sai ya yi umarni a sanya labule tsakanina da shi. Sai ya shiga ya yi wanka da wannan ruwan, sannan sai ya tashi ya yi sallar walaha raka’a takwas.” Mujahid ya ce: “Na faɗa wa Abdullahi ɗan Abbas wannan hadisin sai ya ce: ‘Wannan ita ce sallar safiya.’” [Ɗabarani, Al-Mu’ujamul Kabir #1070]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Babu mai kiyaye sallar walaha sai mai yawan komawa ga Allah.” Ya ce: “Ita ce sallar masu yawan komawa ga Allah.” [Ibn Khuzaima #1224]. <b>Ta biyu </b>, ya bayyana cewa, ya hore masa tsuntsaye suna taruwa a gabansa, dukkansu kuma suna biyayya a gare shi, suna yin tasbihi tare da shi. <b>Ta uku </b>, Allah ya ƙarfafa masa mulkinsa ya kuma ba shi kwarjini sannan kuma ga ƙarfin jiki, da kuma nasarar da ya ba shi a kan maƙiyansa. <b>Ta huɗu </b>, ya ba shi annabta, wadda ta ƙunshi cikakken ilimi da kyakkyawan aiki. <b>Ta biyar </b>, ya ba shi zalaƙa ya kuma hore masa iya bayani dalla-dalla da sasanta masu husuma.

  21. ۞وَهَلۡ أَتَىٰكَ نَبَؤُاْ ٱلۡخَصۡمِ إِذۡ تَسَوَّرُواْ ٱلۡمِحۡرَابَ

    Open ayah 38:21

    Shin labarin abokan husuma ya zo maka, yayin da suka haura wurin ibada?

  22. إِذۡ دَخَلُواْ عَلَىٰ دَاوُۥدَ فَفَزِعَ مِنۡهُمۡۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ خَصۡمَانِ بَغَىٰ بَعۡضُنَا عَلَىٰ بَعۡضٖ فَٱحۡكُم بَيۡنَنَا بِٱلۡحَقِّ وَلَا تُشۡطِطۡ وَٱهۡدِنَآ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلصِّرَٰطِ

    Open ayah 38:22

    Yayin da suka shiga wurin Dawuda sai ya tsorata da su, suka ce: “Kada ka tsorata, (mu biyun nan) masu husuma ne, ɗayanmu ya zalunci ɗaya, sai ka yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya, kada kuma ka yi zalunci, kuma ka shiryar da mu hanya madaidaiciya.

  23. إِنَّ هَٰذَآ أَخِي لَهُۥ تِسۡعٞ وَتِسۡعُونَ نَعۡجَةٗ وَلِيَ نَعۡجَةٞ وَٰحِدَةٞ فَقَالَ أَكۡفِلۡنِيهَا وَعَزَّنِي فِي ٱلۡخِطَابِ

    Open ayah 38:23

    “Lalle wannan ɗan’uwana ne yana da awaki guda casa’in da tara, ni kuma ina da akuya guda ɗaya, sai ya ce: ‘Ka ba ni ita;’ ya kuma rinjaye ni game da maganar.”

  24. قَالَ لَقَدۡ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعۡجَتِكَ إِلَىٰ نِعَاجِهِۦۖ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡخُلَطَآءِ لَيَبۡغِي بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍ إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَقَلِيلٞ مَّا هُمۡۗ وَظَنَّ دَاوُۥدُ أَنَّمَا فَتَنَّٰهُ فَٱسۡتَغۡفَرَ رَبَّهُۥ وَخَرَّۤ رَاكِعٗاۤ وَأَنَابَ۩

    Open ayah 38:24

    (Dawuda) Ya ce: “Haƙiƙa ya zalunce ka saboda neman haɗe akuyarka cikin awakinsa; kuma lalle yawancin masu haɗa dukiyarsu tabbas wasunsu suna zaluntar wasu, sai fa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, su kuwa kaɗan ne ƙwarai. Sai kuma Dawuda ya tabbata cewa Mun jarraba shi ne, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma faɗi yana sujjada kuma ya koma (ga Allah).

  25. فَغَفَرۡنَا لَهُۥ ذَٰلِكَۖ وَإِنَّ لَهُۥ عِندَنَا لَزُلۡفَىٰ وَحُسۡنَ مَـَٔابٖ

    Open ayah 38:25

    Sai Muka gafarta masa wannan; lalle kuma yana da kusanci da Mu da kuma kyakkyawar makoma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Manzonsa (ﷺ) wani labari mai ban al’ajabi da ya faru da Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da wasu mutum biyu masu jayayya da juna suka hauro masa ta katanga a wurin ibadarsa. Lokacin da suka faɗo masa ba zato ba tsammani sai ya tsorata da su, don a zatonsa sun zo su cutar da shi ne, musamman ganin sun shigo masa ta wata hanya da bai saba ganin an shigo masa daga gare ta ba. Da suka fahimci ya tsorata sai suka kwantar masa da hankali suka ce, kada ya tsorata suka bayyana masa cewa su masu jayayya ne a tsakaninsu, ɗayansu ya zalunci ɗaya, don haka suna roƙon sa da ya yi hukunci na adalci a tsakaninsu, ya nuna musu mafita. Sai ɗayansu ya yi bayanin jayayyar da ta faru a tsakaninsu, da cewa shi da ɗan’uwansa ne wanda yake da awaki casa’in da tara, shi kuma yana da akuya guda ɗaya, to amma sai shi ɗan’uwan nasa ya nemi ya ba shi wannan akuyar tasa guda ɗaya don ya cike ɗari, ya kuma matsa masa da maganar har saura ƙiris ya rinjaye shi da hujja. Nan take sai Annabi Dawud ya yanke hukunci tsakaninsu, ya shaida wa mai ƙara cewa, lalle ɗan’uwansa ya zalunce shi da ya nemi ya haɗa akuyarsa ɗaya cikin awakinsa. Ya ƙara da cewa wannan da man ita ce al’adar waɗanda suke haɗa dukiyarsu wuri guda, yawancinsu sukan zalunci abokan tarayyarsu su ƙi yi musu adalci, sai dai mutanen da suka yi imani suka yi ayyuka na ƙwarai su ne suke yin adalci ba sa zaluntar abokan tarayyarsu cikin dukiya; amma kuma waɗannan ‘yan kaɗan ne ƙwarai a cikin mutane. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar da cewa wannan abu da ya faru da shi na haurowar waɗannan mutane da shigo masa ba zato ba tsammani da kuma ƙarar da suka kawo masa wata jarrabawa ce Allah ya shirya masa, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya faɗi ƙasa ya yi sujjada, domin neman kusanci da Allah, ya tuba ya mayar da al’amarinsa ga Allah. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (SAW) ya yi sujjada a Suratus Sad (watau daidai aya ta 24) sai ya ce: “Dawud ya yi sujjadar tuba zuwa ga Allah, mu kuma muna yin sujjadar godiya ga Allah.” [Nasa’i #957]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Annabi Dawud da cewa ya gafarta masa, kuma shi Annabi Dawud makusanci ne ga Allah sosai, yana da kuma kyakkyawar makoma a lahira.

  26. يَٰدَاوُۥدُ إِنَّا جَعَلۡنَٰكَ خَلِيفَةٗ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱحۡكُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَقِّ وَلَا تَتَّبِعِ ٱلۡهَوَىٰ فَيُضِلَّكَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَضِلُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدُۢ بِمَا نَسُواْ يَوۡمَ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 38:26

    Ya Dawuda, lalle Mun sanya ka halifa a bayan ƙasa, sai ka yi hukunci a tsakanin mutane da gaskiya, kada ka bi son zuciya sai ya ɓatar da kai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda suke ɓacewa daga hanyar Allah suna da (sakamakon) azaba mai tsanani saboda mantawar da suka yi da ranar hisabi. A wannan aya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya kira Annabi Dawud (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sanar da shi cewa ya sanya shi halifa a bayan ƙasa don ya riƙa hukunci tsakanin mutane, ya kuma umarce shi da yi musu hukunci na adalci. Ya kuma yi masa kashedi da cewa kar ya kuskura ya bi son zuciya, ya nuna goyon bayansa ga wani makusanci ko aboki yayin gudanar da shari’a, ko ya ƙi yi wa wani adalci saboda adawar da ke tsakaninsu. Domin bin son zuciya zai ɓatar da shi daga kan hanya madaidaiciya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk wanda ya kauce daga hanyar Allah madaidaiciya to zai haɗu da azaba mai raɗaɗi, saboda ya manta da ranar hisabi, domin tunawa da ita shi zai sa su kauce wa son zuciya.

  27. وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَآءَ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا بَٰطِلٗاۚ ذَٰلِكَ ظَنُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنَ ٱلنَّارِ

    Open ayah 38:27

    Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu a banza ba. Wannan zato ne na waɗanda suka kafirta. Saboda haka tsananin azabar wuta ya tabbata ga waɗanda suka kafirce.

  28. أَمۡ نَجۡعَلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ كَٱلۡمُفۡسِدِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ نَجۡعَلُ ٱلۡمُتَّقِينَ كَٱلۡفُجَّارِ

    Open ayah 38:28

    Shin za Mu mayar da waɗanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari kamar masu ɓarna a bayan ƙasa, ko kuma za Mu mayar da masu taƙawa kamar lalatattu?

  29. كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ مُبَٰرَكٞ لِّيَدَّبَّرُوٓاْ ءَايَٰتِهِۦ وَلِيَتَذَكَّرَ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

    Open ayah 38:29

    Littafi ne mai albarka da Muka saukar maka da shi domin su yi tuntuntuni game da ayoyinsa, don kuma masu hankula su wa’azantu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimarsa ta halittar sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu, da cewa bai halicce su a banza ba, ya tabbatar da cewa wannan zato ne na kafirai wanda bai dace su yi wa Allah shi ba; azabar wutar Jahannama a ranar alƙiyama kuma ta tabbata ga waɗannan kafirai masu irin wannan zato, matuƙar suka mutu ba su tuba ba. Sai kuma Allah ya bayyana cewa, adalcinsa da hikimarsa sun zartar da cewa ba zai taɓa daidaita mutanen kirki da na banza ba; ba zai kuma daidaita waɗanda suka aikata alheri da waɗanda suka aikata sharri ba, kamar yadda kafirai suke tsammanin babu wani bambanci na sakamako a tsakaninsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su da cewa, yanzu suna ganin zai mayar da waɗanda suka yi imani da shi suka bi Manzonsa suka kuma yi ayyuka nagari su zama daidai da maɓarnata a bayan ƙasa suna yaɗa kafirci da saɓon Allah? Ko kuma zai daidaita masu kiyaye dokokin Allah suna guje wa haninsa da kafirai ko munafukai waɗanda suka yi dumu-dumu cikin saɓon Allah? Lalle duk mai hankali ya san cewa daidaita tsakanin waɗannan kashe-kashen mutane tsantsar zalunci ne wanda bai dace a jingina wa Allah shi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawarin zai saka wa muminai masu tsoron sa da gidan Aljanna, ya kuma saka wa kafirai da gidan wutar Jahannama, domin ba ɗaya suke a wurinsa ba, don haka sakamakonsu ma ba zai zama ɗaya ba. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan Alƙur’ani littafi ne mai albarka da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) wanda yake cike da alheri da amfani mai yawa, domin mutane su riƙa tuntuntuni game da ayoyinsa su kuma fahimci ma’anoninsa; masu lafiyayyun hankula kuma su wa’azantu da shi.

  30. وَوَهَبۡنَا لِدَاوُۥدَ سُلَيۡمَٰنَۚ نِعۡمَ ٱلۡعَبۡدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ 

    Open ayah 38:30

    Muka kuma yi wa Dawuda baiwar (ɗa) Sulaimanu. Madalla da wannan bawan; lalle shi mai yawan komawa ne (ga Allah).

  31. إِذۡ عُرِضَ عَلَيۡهِ بِٱلۡعَشِيِّ ٱلصَّٰفِنَٰتُ ٱلۡجِيَادُ

    Open ayah 38:31

    (Ka tuna) lokacin da aka jera masa ingarmun dawakai masu tsayawa da ƙafa uku da yamma.

  32. فَقَالَ إِنِّيٓ أَحۡبَبۡتُ حُبَّ ٱلۡخَيۡرِ عَن ذِكۡرِ رَبِّي حَتَّىٰ تَوَارَتۡ بِٱلۡحِجَابِ

    Open ayah 38:32

    Sai ya ce: “Lalle ni na fifita son dukiya (watau dawakai) a kan ambaton Ubangijina (watau sallar La\'asar) har sai da (rana) ta faɗi.”

  33. رُدُّوهَا عَلَيَّۖ فَطَفِقَ مَسۡحَۢا بِٱلسُّوقِ وَٱلۡأَعۡنَاقِ

    Open ayah 38:33

    (Ya ce): “Ku dawo min da su;” sai ya riƙa saran su ta ƙafafu da wuyoyi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya yi wa Annabi Dawuda (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) baiwa da ɗa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) domin ya faranta masa rai ya kuma gaji annabta da ilimi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da yawan komawa ga Allah da tuba a gare shi. Sai kuma ya tunatar da Manzonsa (ﷺ) da wata baiwa ta tsoron Allah da son bautarsa da ya yi wa bawansa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), lokacin da aka jera masa ingarmun dawakai `yan asali, masu kuma tsayuwa da ƙafa uku su ɗage ta huɗu, a daidai lokacin sallar La’asar, ya riƙa zagaya su suna ba shi sha’awa ainun, bai ankara ba har rana ta faɗi. Da Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya lura da sakacin da ya yi har rana ta faɗi bai yi sallar La’asar ba, sai nadama ta lulluɓe shi ya gane lalle ya fifita son dawakan nan har sun ɗauke masa hankali ya bar zikirin Ubangijinsa, har rana ta faɗi bai ba da faralin La’asar ba, sai ya yi umarni a dawo masa da dawakan gaba ɗayansu. Da aka dawo da su sai ya riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya yana sassare ƙafafunsu da wuyoyinsu.

  34. وَلَقَدۡ فَتَنَّا سُلَيۡمَٰنَ وَأَلۡقَيۡنَا عَلَىٰ كُرۡسِيِّهِۦ جَسَدٗا ثُمَّ أَنَابَ

    Open ayah 38:34

    Kuma haƙiƙa Mun jarrabi Sulaimanu Muka ɗora wani jiki a kan gadonsa na mulki, sannan ya koma (kan mulkinsa).

  35. قَالَ رَبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَهَبۡ لِي مُلۡكٗا لَّا يَنۢبَغِي لِأَحَدٖ مِّنۢ بَعۡدِيٓۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡوَهَّابُ

    Open ayah 38:35

    Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka gafarta min, Ka kuma ba ni wani mulki wanda bai kamaci wani ba a bayana ya sami irinsa; lalle Kai Kai ne Mai yawan kyauta.”

  36. فَسَخَّرۡنَا لَهُ ٱلرِّيحَ تَجۡرِي بِأَمۡرِهِۦ رُخَآءً حَيۡثُ أَصَابَ

    Open ayah 38:36

    Sai Muka hore masa iska tana tafiya da umarninsa a natse duk inda ya fuskanta.

  37. وَٱلشَّيَٰطِينَ كُلَّ بَنَّآءٖ وَغَوَّاصٖ

    Open ayah 38:37

    Da kuma shaiɗanu masu yin kowane irin gini da kuma masu yin nutso (a ruwa).

  38. وَءَاخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ

    Open ayah 38:38

    Wasu kuma an ɗaɗɗaure su cikin maruruwa.

  39. هَٰذَا عَطَآؤُنَا فَٱمۡنُنۡ أَوۡ أَمۡسِكۡ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

    Open ayah 38:39

    Wannan kyautarmu ce, to ka yi kyauta ko ka hana ba da wani bincike ba.

  40. وَإِنَّ لَهُۥ عِندَنَا لَزُلۡفَىٰ وَحُسۡنَ مَـَٔابٖ 

    Open ayah 38:40

    Lalle kuma shi tabbas yana da kusanci a wurinmu, da kuma kyakkyawar makoma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata jarrabawa da ya yi wa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) game da mulkinsa, lokacin da ya ɗora wani jiki a kan kujerarsa ta mulki. An ruwaito maganganu da dama game da wannan jiki da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɗora a kan kujerar mulkin Annabi Sulaimanu. Yawancinsu maganganu ne marasa inganci. Mafi ingancin waɗanda aka ambata a nan guda biyu ne: <b>Na farko </b>, wani shaiɗani ne Allah ya ba shi damar hawa kan kujerar mulkin Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a matsayin shi ne Annabi Sulaimanu, ya yi ta gudanar da mulki na tsawon wasu ‘yan kwanaki, sannan daga baya mulkin ya dawo hannun Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Allah kuma ya hore masa iko da sarrafa shaiɗanu. Wannan shi ne ra’ayin da yawancin malaman tafsiri suka fi amincewa da shi. <b>Na biyu </b>, ya yi rantsuwa ne a kan zai kewaya ɗakunan matansa su ɗari a dare ɗaya, kuma kowacce za ta ɗauki ciki ta haifi jarumin mayaƙi da zai yi jihadi don ɗaukaka kalmar Allah, sai ya manta bai ce ‘in sha’ Allahu ’ ba, sai ya zamanto mace ɗaya ce a cikinsu ta sami ciki, ita ma kuma sai ta haifa masa rabin mutum. [Dubi, Bukhari #3424 da Muslim #1654]. To wannan shi ne jikin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambata, kamar yadda wasu malamai suke gani. Amma dai magana ta farko ta fi ƙarfi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka)ya bayyana cewa Annabi Sulaimanu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi nadama a kan ƙudurin da ya yi, sai ya koma ga Ubangijinsa ya miƙa masa dukkan al’amuransa, ya kuma roƙi gafararsa ya kuma nemi ya ba shi wani mulki na musamman da zai keɓance shi da shi, wanda bai kamaci wani mutum a bayansa ya sami irinsa ba, domin Allah shi ne mai yawan baiwa mai yawan kyauta. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle daren jiya wani ifritu daga cikin aljannu ya yiwo kaina domin ya yanke mini salla, sai Allah ya ba ni dama a kansa har na so in ɗaure shi a jikin ɗaya daga dirkokin masallaci domin ku wayi gari ku duka ku gan shi, sai na tuna addu’ar ɗan’uwana Sulaiman inda ya ce: “Ya Ubangijina, ka gafarta mini kuma ka ba ni mulki wanda bai kamaci wani mutum bayana ya sami irinsa ba....” [Bukhari #4308 da Muslim #541]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Yayin da Sulaimanu ɗan Dawud ya gama ginin Baitil Maƙdis sai ya roƙi Allah abubuwa uku: Ya roƙi Allah ya ba shi hukunci wanda zai dace da hukuncinsa, sai aka ba shi; ya kuma roƙe shi ya ba shi mulki wanda bai kamaci wani mutum ya sami irinsa a bayansa ba, aka ba shi; ya roƙe shi bayan ya gama gina masallaci cewa dukkan mutumin da ya zo gare shi ba don komai ba sai don ya yi salla a cikinsa, to kar ya fita daga cikinsa har sai ya wanke masa laifukansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” [Nasa’i #693 da Ahmad #6644 da Ibn Majah #1408]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa masa, ya kuma yi masa wasu manya-manyan ni’imomi waɗanda suka haɗa da: <b>Na ɗaya </b>, ya hore masa iska mai tafiya da umarninsa a cikin nutsuwa duk kuwa da ƙarfin kaɗawarta da kuma saurinta, takan ɗauke shi ta kai shi duk inda yake so. <b>Na biyu </b>, ya hore masa shaiɗanu masu bin umarninsa, daga cikinsu akwai magina da suke yi masa kowane irin gini yake so; akwai kuma masu nutso a cikin kogi suna fito masa da lu’u-lu’u da murjani da sauran duwatsun cikin ruwa masu daraja. <b>Na uku </b>, wasu kuma shaiɗanu ne masu taurin kai, su kuma an ba shi iko a kansu, don haka ya sa aka ɗaure su a cikin maruruwa ba sa iya motsawa nan da can. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa ya danƙa masa wannan gawurtaccen mulki da wannan baiwa mai girma, ya kuma ba shi izinin ya sarrafa ta yadda ya ga dama; ya ɗauki abin da ya ga dama daga arzukin da Allah ya yi masa a masarautarsa ya ba wa wanda ya ga damar ba wa, ya kuma hana wanda ya ga damar hana wa, babu wanda zai bincike shi a kan haka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabe shi da cewa lalle shi yana daga cikin makusanta a wurinsa yana da kuma kyakkyawar makoma watau Aljanna. Don haka kamar yadda ya yalwata masa a nan duniya to hakanan ma a lahira zai yi masa kyakkyawan sakamako.

  41. وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَآ أَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِنُصۡبٖ وَعَذَابٍ

    Open ayah 38:41

    Ka kuma tuna bawanmu Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa (yana cewa): “Lalle ni Shaiɗan ya shafe ni da wata wahala da azaba.”|

  42. ٱرۡكُضۡ بِرِجۡلِكَۖ هَٰذَا مُغۡتَسَلُۢ بَارِدٞ وَشَرَابٞ

    Open ayah 38:42

    (Aka ce da shi): “Ka hauri ƙasa da ƙafarka; (sai ruwa ya ɓuɓɓugo, aka ce da shi): “Wannan ruwan wanka ne mai sanyi da na sha.”

  43. وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ أَهۡلَهُۥ وَمِثۡلَهُم مَّعَهُمۡ رَحۡمَةٗ مِّنَّا وَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

    Open ayah 38:43

    Muka kuma yi masa baiwar iyalinsa da kuma (ƙarin) wasu kamarsu (na `ya`ya da jikoki) don jin ƙai daga gare Mu da kuma wa’azi ga masu hankula.

  44. وَخُذۡ بِيَدِكَ ضِغۡثٗا فَٱضۡرِب بِّهِۦ وَلَا تَحۡنَثۡۗ إِنَّا وَجَدۡنَٰهُ صَابِرٗاۚ نِّعۡمَ ٱلۡعَبۡدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٞ

    Open ayah 38:44

    Ka ɗauki danƙi na ciyawa da hannunka ka bugi (matarka da shi), kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mun same shi mai haƙuri. Madalla da wannan bawan; lalle shi mai yawan komawa ne (ga Allah). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) tana tunatar da Annabi (ﷺ) labarin bawansa Annabi Ayyub (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya kamu da wata matsananciyar rashin lafiya, amma ya yi haƙuri ya jure bai koka wa wani abin da yake ciki ba sai Allah, yayin da ya yi addu’a ya roƙe shi cewa, Shaiɗan ya shafe shi da wata cuta mai wahalarwa da azabtarwa. Ya kuma rasa iyalansa da dukiyarsa bayan ya kasance mutum mai yawan dukiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa masa roƙonsa ya umarce shi da ya hauri ƙasa da ƙafarsa. Da ya aikata hakan sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga cikinta wanda ya riƙa sha yana wanka da shi har cutar da ke tare da shi ta gushe. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya amsa addu’ar Annabi Ayyuba ya kuma yaye masa duk cutar da take damun sa, ya kuma dawo masa da madadin iyalansa waɗanda ya rasa, har ya ƙara masa yawan ‘ya’ya da jikoki don yalwata jin ƙan Allah gare shi. Wannan kuma sakamakon haƙurin da ya yi ne, kuma saboda mutane masu hankali su wa’azantu su gane cewa mahaƙurci mawadaci ne. Duk da halin da Annabi Ayyuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yake ciki sai da matarsa ta fusata shi har ya rantse da Allah cewa sai ya yi mata bulala ɗari. A kan haka sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya ɗauki danƙi na ciyawa da hannunsa ya bugi matarsa da shi don ya warware rantsuwarsa ba tare da ya karya ta ba. Sai ya aikata kamar yadda aka umarce shi, don haka bai yi kaffara ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabe shi da cewa ya same shi mutum mai haƙuri a kan bala’in da ya auka masa, kuma madalla da bawan Allah Ayyuba (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), lalle tabbas shi mutum ne mai yawan komawa ga Allah mai yawan tuba.

  45. وَٱذۡكُرۡ عِبَٰدَنَآ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ أُوْلِي ٱلۡأَيۡدِي وَٱلۡأَبۡصَٰرِ

    Open ayah 38:45

    Ka kuma tuna bayinmu Ibrahimu da Is’haƙa da Yaƙubu ma’abota ƙarfi da basira.

  46. إِنَّآ أَخۡلَصۡنَٰهُم بِخَالِصَةٖ ذِكۡرَى ٱلدَّارِ

    Open ayah 38:46

    Lalle Mun keɓance su da wata keɓantacciyar ɗabi\'a, (ita ce) tuna lahira.

  47. وَإِنَّهُمۡ عِندَنَا لَمِنَ ٱلۡمُصۡطَفَيۡنَ ٱلۡأَخۡيَارِ

    Open ayah 38:47

    Kuma lalle su a wurinmu tabbas suna daga cikin zaɓaɓɓu nagari.

  48. وَٱذۡكُرۡ إِسۡمَٰعِيلَ وَٱلۡيَسَعَ وَذَا ٱلۡكِفۡلِۖ وَكُلّٞ مِّنَ ٱلۡأَخۡيَارِ

    Open ayah 38:48

    Ka kuma tuna Isma’ila da Alyasa’u da Zulkifli; dukkaninsu kuma suna cikin zaɓaɓɓu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ƙara tunatar wa Annabi (ﷺ) labarin bayinsa kuma manzanninsa zaɓaɓɓu da ya aika su cikin al\'ummunsu, watau su ne Ibrahim da Is’haƙa da Ya’aƙubu, dukkansu sun zamanto ma’abota ƙarfi ne wajen bautar Allah da neman yardarsa kuma masu basira ne game da addinin Allah da fahimtar gaskiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu wata baiwa ta musamman da ya keɓance su da ita, watau ya raya musu zukatansu da tunanin lahira da yi mata tanadin aiki nagari da kiran mutane zuwa ga kyakkyawan aiki domin zuwan wannan rana. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, su waɗannan annabawa suna daga cikin bayinsa da ya zaɓo domin su bauta masa su yi masa biyayya, ya kuma zaɓe su ya ba su manzanci zuwa ga mutane domin su isar musu da saƙonsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tunantar da Annabi (ﷺ) labarin Annabi Isma’ila ɗan Annabi Ibrahim da labarin Annabi Alyasa’u da na Annabi Zulkifli; ya yi musu kyakkyawan yabo domin dukkansu suna cikin bayinsa zaɓaɓɓu.

  49. هَٰذَا ذِكۡرٞۚ وَإِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ لَحُسۡنَ مَـَٔابٖ

    Open ayah 38:49

    Wannan kyakkyawan ambato ne (a gare su). Kuma lalle masu taƙawa tabbas suna da kyakkyawar makoma.

  50. جَنَّٰتِ عَدۡنٖ مُّفَتَّحَةٗ لَّهُمُ ٱلۡأَبۡوَٰبُ 

    Open ayah 38:50

    (Wato) gidajen Aljannar dawwama, alhali ƙofofi suna buɗe saboda su.

  51. مُتَّكِـِٔينَ فِيهَا يَدۡعُونَ فِيهَا بِفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ وَشَرَابٖ

    Open ayah 38:51

    Suna kishingiɗe a cikinsu, suna kiran a kawo musu ababen marmari masu yawa da abin sha a cikinsu.

  52. ۞وَعِندَهُمۡ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ أَتۡرَابٌ

    Open ayah 38:52

    Kuma a wurinsu akwai tsaraikun mata masu taƙaita kallo (ga mazansu kawai).

  53. هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِيَوۡمِ ٱلۡحِسَابِ

    Open ayah 38:53

    Wannan shi ne ake yi muku alƙawari da shi a ranar hisabi.

  54. إِنَّ هَٰذَا لَرِزۡقُنَا مَا لَهُۥ مِن نَّفَادٍ

    Open ayah 38:54

    Lalle wannan tabbas arzikinmu ne ba mai ƙarewa ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa waɗancan annabawa da suka gabata, sun samu kyakkyawan ambato ne a cikin littafinsa mai girma, watau Alƙur’ani, wanda yake wata ɗaukaka ce a gare su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk bayinsa waɗanda suka kiyaye dokokinsa; suka yi aiki da umarninsa suka kuma guji haninsa, to suna da kyakkyawar makoma a lahira, watau gidajen Aljanna na zama dindindin a ranar alƙiyama; za su iske ƙofofinsu a buɗe don yi musu kyakkyawar tarba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin ni’imar da ya tanadar musu a Aljanna, da cewa za su zamanto masu kishingiɗa a kan gadajen da aka yi wa kwalliya ta alfarma, suna kiran masu yi musu hidima don su kawo musu duk abin da suke sha’awa na kayan marmari iri-iri na ci da na sha, kamar giyar Aljanna da madara da zuma da sauransu. An kuma shirya mata tsareku a shekaru masu taƙaita kallonsu ga mazajensu, ba sa kallon wasu mazajen daban. Allah kuma ya tabbatar da cewa wannan sakamako da aka ambata da ma can an tanade shi ne a ranar alƙiyama saboda masu taƙawa da kiyaye dokokin Allah, don kyawawan ayyukan da suka yi a duniya. Kuma arziki ne mai ɗorewa ba zai yanke ba har abada.

  55. هَٰذَاۚ وَإِنَّ لِلطَّٰغِينَ لَشَرَّ مَـَٔابٖ

    Open ayah 38:55

    Wannan (shi ne sakamakon masu taƙawa). Kuma lalle masu ɗagawa tabbas suna da mummunar makoma.

  56. جَهَنَّمَ يَصۡلَوۡنَهَا فَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

    Open ayah 38:56

    (Wato) Jahannama wadda za su shige ta, to wannan shimfiɗar zama ta munana.

  57. هَٰذَا فَلۡيَذُوقُوهُ حَمِيمٞ وَغَسَّاقٞ

    Open ayah 38:57

    Wannan (sakamako ne), sai su ɗanɗane shi na tafasasshen ruwa da mugunya.

  58. وَءَاخَرُ مِن شَكۡلِهِۦٓ أَزۡوَٰجٌ

    Open ayah 38:58

    Da kuma wani mai kama da shi iri daban-daban.

  59. هَٰذَا فَوۡجٞ مُّقۡتَحِمٞ مَّعَكُمۡ لَا مَرۡحَبَۢا بِهِمۡۚ إِنَّهُمۡ صَالُواْ ٱلنَّارِ

    Open ayah 38:59

    (Za a ce da su): “Wannan ma wani gungun ne (na mabiya) mai afkawa tare da ku;” (sai shugabannin su ce): “Ba ma yin maraba da su.” Lalle (su duka) wuta za su shiga.

  60. قَالُواْ بَلۡ أَنتُمۡ لَا مَرۡحَبَۢا بِكُمۡۖ أَنتُمۡ قَدَّمۡتُمُوهُ لَنَاۖ فَبِئۡسَ ٱلۡقَرَارُ 

    Open ayah 38:60

    (Mabiyan kuma sai) su ce: “A’a, ku dai ne ba ma maraba da ku; ku ne kuka kawo mana shi (wannan mummunan sakamako);” to wannan matabbata ta munana.

  61. قَالُواْ رَبَّنَا مَن قَدَّمَ لَنَا هَٰذَا فَزِدۡهُ عَذَابٗا ضِعۡفٗا فِي ٱلنَّارِ

    Open ayah 38:61

    Sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, duk wanda ya kawo mana wannan (sakamakon) to Ka ƙara masa ninkin azaba a cikin wuta.”

  62. وَقَالُواْ مَا لَنَا لَا نَرَىٰ رِجَالٗا كُنَّا نَعُدُّهُم مِّنَ ٱلۡأَشۡرَارِ

    Open ayah 38:62

    Suka kuma ce: “Me ya sa ne ba ma ganin wasu mazaje da muka kasance muna lissafa su cikin ashararai?

  63. أَتَّخَذۡنَٰهُمۡ سِخۡرِيًّا أَمۡ زَاغَتۡ عَنۡهُمُ ٱلۡأَبۡصَٰرُ

    Open ayah 38:63

    “Shin mun ɗauke su ne ababen yi wa ba’a (a duniya), ko kuwa idanuwanmu ne suka bauɗe ba sa hango su?”

  64. إِنَّ ذَٰلِكَ لَحَقّٞ تَخَاصُمُ أَهۡلِ ٱلنَّارِ

    Open ayah 38:64

    Lalle wannan jayayyar ta ‘yan wuta gaskiya ce. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa abubuwan da suka gabata an tanade su ne don masu taƙawa. To amma masu ƙetare iyakokin Allah (Mai tsarki da daukaka) ta hanyar rungumar kafirci da saɓon Allah, su kuma suna da mummunar makoma a ranar alƙiyama. Sakamakonsu ita ce wutar Jahannama da za su shige ta ta kewaye su ta ko’ina su ɗanɗani zafinta, ta zame musu tamkar shimfiɗa. Tir da wannan shimfiɗa tasu, watau Jahannama. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana dangogin azabar da za su ɗanɗana a wutar, bayan tsananin zafinta, abin shansu shi ne tafasasshen ruwa da kuma ruwan mugunyar da yake zuba daga jikin ‘yan wuta. Ba su da wani abin sha sai wannan mummunan ruwan wanda ba ya kashe ƙishi. Akwai kuma wasu dangogi na azaba iri-iri da za a yi ta yi musu wanda ba sa yankewa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan ‘yan wuta suka shiga wuta sai rigima ta kaure tsakaninsu, su shiga nesanta kansu da juna, ta hanyar la’antar junansu; wasu su ce wa wasu, waɗannan ma wata ƙungiya ce ta ‘yan wuta da za su shiga wuta tare da su, sai su kuma su amsa musu da cewa ba sa maraba da su, domin su ma za su ɗanɗani irin azabar da waɗancan suke ɗanɗana. Sai gungun mabiyan su mayar wa shugabanninsu martani da cewa su ma ba sa maraba da su, domin su ne sanadiyyar samun kansu a cikin wannan mummunar azaba, saboda su ne suka ɓatar da su, don haka sai su yi tir da wannan matabbata, watau wutar Jahannama, wadda za su yi tarayya ta zama a cikinta har abada. Sai mabiyan su kuma su ci gaba da roƙon Allah da cewa, duk wanda ya yi sanadiyyar ɓatansu a duniya har suka kauce wa hanyar shiriya, to su ma Allah ya ninninka musu azabar wuta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda maƙiya Allah za su shiga tattaunawa a cikin wutar Jahannama game da muminai waɗanda suka riƙa yi wa izgili a duniya, suna yi musu kallon wasu ɓatattu, sai kuma ga shi ba su gan su a cikin wuta ba, sai su riƙa tambayar junansu cewa, me ya sa ne ba sa ganin wasu mutane da tun a duniya suna lissafa su a cikin ashararai waɗanda suka cancanci azabtarwa? Sai su yi mamakin rashin ganin su a wuta, suna tambayar junansu cewa, ashe wai da man izgili da ba’ar da suke yi musu bisa kuskure ne, ko kuma daidai ne, idanuwansu ne kawai suka bauɗe ba sa iya hango su a cikin wutar? Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa, wannan labari da ya ba shi na rigimar ‘yan wuta a junansu bayan sun shige ta, tabbas gaskiya ne babu wani kokwanto a cikinsa.

  65. قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ مُنذِرٞۖ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّا ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ

    Open ayah 38:65

    Ka ce: “Ni dai mai gargaɗi ne kawai; kuma babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Allah Ɗaya, Mai rinjaye.

  66. رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفَّٰرُ

    Open ayah 38:66

    “Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu, Mabuwayi, Mai gafara.”

  67. قُلۡ هُوَ نَبَؤٌاْ عَظِيمٌ

    Open ayah 38:67

    Ka ce: “Shi (wannan Alƙur’ani) labari ne mai girma.

  68. أَنتُمۡ عَنۡهُ مُعۡرِضُونَ

    Open ayah 38:68

    “Da kuke bijire masa.

  69. مَا كَانَ لِيَ مِنۡ عِلۡمِۭ بِٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰٓ إِذۡ يَخۡتَصِمُونَ

    Open ayah 38:69

    “Ban zama na san wani abu ba dangane da mala’iku masu daraja lokacin da suke yin muhawara (game da halittar Adamu).

  70. إِن يُوحَىٰٓ إِلَيَّ إِلَّآ أَنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٞ مُّبِينٌ 

    Open ayah 38:70

    “Ba wani wahayi da aka yiwo min sai kawai cewa ni mai gargaɗi ne mai bayyanawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa wa mutanensa kafirai cewa, shi fa kawai ya zo ne don ya yi musu gargaɗi game da azabar Allah kada ta auka musu saboda kafircinsu da ƙaryata Manzonsa da suke yi, kuma ya tabbatar musu da cewa babu wani wanda ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kaɗai; shi ne makaɗaici a girmansa da sunayensa da siffofinsa da ayyukansa; mai rinjaye da galaba a kan komai. Shi ne kuma Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu; shi ne mahaliccinsu mai gudanar da lamuransu yadda ya ga dama; dukkansu bayinsa ne, shi ne kuma mabuwayi cikin mulkinsa, babu mai iya ja da shi; shi ne kuma mai gafarta wa bayinsa zunubansu idan sun tuba sun nemi gafararsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Manzonsa (ﷺ) ya tabbatar wa kafirai cewa, Alƙur’ani labari ne mai girman sha’ani, amma kuma sai ga su suna bijire masa. Sai kuma Allah ya sake umartar Manzonsa da ya shaida wa kafirai cewa, ba shi da wata masaniya game da muhawarar da ta kasance tsakanin mala’iku lokacin da suke tattaunawa game da halittar Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da sauko da shi bayan ƙasa. Ba don Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da shi ba da ba zai san komai a kai ba. Don haka ya shaida musu cewa shi fa kawai ana yi masa wahayi ne a kan ya yi wa mutanensa gargaɗi game da azabar Allah kada ta auka musu, ya kuma bayyana gargaɗinsa a fili. Wannan kuwa dalili ne mai tabbatar da annabcinsa.

  71. إِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِنِّي خَٰلِقُۢ بَشَرٗا مِّن طِينٖ

    Open ayah 38:71

    (Ka tuna) lokacin da Ubangijinka Ya ce da mala’iku: “Lalle Ni zan halicci wani mutum daga taɓo.

  72. فَإِذَا سَوَّيۡتُهُۥ وَنَفَخۡتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُواْ لَهُۥ سَٰجِدِينَ

    Open ayah 38:72

    “To idan Na daidaita shi Na kuma busa masa ruhina, sai ku faɗi kuna masu yi masa sujjada.”

  73. فَسَجَدَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ كُلُّهُمۡ أَجۡمَعُونَ

    Open ayah 38:73

    Sai mala’iku dukkaninsu gaba ɗaya suka yi sujjada.

  74. إِلَّآ إِبۡلِيسَ ٱسۡتَكۡبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

    Open ayah 38:74

    Sai Iblisa da ya yi girman kai ya kuma zama cikin kafirai.

  75. قَالَ يَٰٓإِبۡلِيسُ مَا مَنَعَكَ أَن تَسۡجُدَ لِمَا خَلَقۡتُ بِيَدَيَّۖ أَسۡتَكۡبَرۡتَ أَمۡ كُنتَ مِنَ ٱلۡعَالِينَ

    Open ayah 38:75

    (Allah) Ya ce: “Ya kai Iblisa, me ya hana ka yin sujjada ga abin da Na halitta da hannayena biyu? Ka yi girman kai ne, ko kuwa da man can ka kasance daga masu nuna isa?”

  76. قَالَ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡهُ خَلَقۡتَنِي مِن نَّارٖ وَخَلَقۡتَهُۥ مِن طِينٖ

    Open ayah 38:76

    Sai ya ce: “Ni ai na fi shi; (domin) Ka halicce ni ne daga wuta, (shi) kuma Ka halicce shi daga taɓo.”

  77. قَالَ فَٱخۡرُجۡ مِنۡهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٞ

    Open ayah 38:77

    (Sai Allah) Ya ce (da shi): “To ka fice daga cikinta (wato Aljanna) saboda kai lalle korarre ne (daga rahama).

  78. وَإِنَّ عَلَيۡكَ لَعۡنَتِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

    Open ayah 38:78

    “Kuma lalle la’antata tabbas ta hau kanka har zuwa ranar alƙiyama.”

  79. قَالَ رَبِّ فَأَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ

    Open ayah 38:79

    (Sai Iblisa) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka saurara min har zuwa ranar da za a tashe su.”

  80. قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ 

    Open ayah 38:80

    (Sai Allah) Ya ce: “To lalle kana cikin waɗanda za a saurara wa.

  81. إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡوَقۡتِ ٱلۡمَعۡلُومِ

    Open ayah 38:81

    “Har zuwa ranar lokaci sananne.”

  82. قَالَ فَبِعِزَّتِكَ لَأُغۡوِيَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 38:82

    Sai ya ce: “To na rantse da girmanka tabbas zan ɓatar da su baki ɗaya.

  83. إِلَّا عِبَادَكَ مِنۡهُمُ ٱلۡمُخۡلَصِينَ

    Open ayah 38:83

    “Sai dai bayinka waɗanda aka tsarkake daga cikinsu.”

  84. قَالَ فَٱلۡحَقُّ وَٱلۡحَقَّ أَقُولُ

    Open ayah 38:84

    (Allah) Ya ce: “Gaskiya (daga gare Ni take), kuma gaskiyar kawai Nake faɗa!

  85. لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكَ وَمِمَّن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ أَجۡمَعِينَ

    Open ayah 38:85

    “Tabbas zan cika Jahannama da kai da kuma waɗanda suka bi ka baki ɗaya.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Annabi (ﷺ) lokacin da ya faɗa wa mala’iku cewa zai halici mutum da taɓo, watau Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya kuma umarce su da cewa idan ya gama daidaita halittarsa, ya kuma busa masa ruhinsa, to dukkansu su faɗi su yi masa sujjada. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa, mala’iku sun bi wannan umarni nasa, sun faɗi sun yi wa Annabi Adamu sujjada ta girmamawa, ba kuma wanda bai yi sujjadar ba sai Iblis kaɗai, shi ne girman kai ya hana shi bin wannan umarni na Allah sai ya tabbata daga cikin kafirai. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Iblis cewa, me ya hana shi yin sujjada ga Annabi Adamu wanda shi ne ya halicce shi da hannayensa biyu? Shin girman kansa ne da yake nuna wa Annabi Adamu ko kuwa da man can yana nuna isa da jin kai ne ga Allah (Mai tsarki da daukaka)? Sai Iblis ya amsa wa Allah da cewa, shi ai fa ya fi Annabi Adamu, domin an halicce shi ne da wuta, Annabi Adamu kuwa da taɓo aka halicce shi, don haka yana ganin wuta ta fi taɓo daraja, saboda haka shi ya fi Annabi Adamu daraja, shi ya sa ya ƙi yi masa sujjada. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Iblis da ya fice daga gidan Aljanna a matsayin korarre. Kuma la’anar Allah ta tabbata a kansa har zuwa ranar alƙiyama, don haka ba shi ba gidan Aljanna har abada. To sai Iblis ya nemi wata alfarma a wajen Allah da ya saurara masa kada ya kashe shi har zuwa lokacin da zai tashi bayinsa domin hisabi. Sai ko Allah ya bayyana masa cewa ya ba shi abin da ya nema, ya saurara masa har zuwa wani iyakantaccen lokaci sananne wanda a cikinsa zai karɓi ransa. Daga nan sai Iblis ya yi rantsuwa da ikon Allah da Izzarsa cewa lalle sai ya ɓatar da zurriyar Annabi Adamu kakaf, in ban da bayin Allah da ya tsarkake su ya tsare su daga faɗawa cikin tarkonsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa daga gare shi gaskiya take, kuma tsantsar gaskiya kawai yake faɗa, cewa kada Iblis ya ji da wai, tabbas sai ya cika Jahannama da shi da duk waɗanda suka bi shi a kan kafirci daga cikin zurriyar Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).

  86. قُلۡ مَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٖ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُتَكَلِّفِينَ

    Open ayah 38:86

    Ka faɗa (musu): “Babu wani lada da nake tambayar ku game da shi, (wato isar da aike), kuma ni ba na cikin masu matsa wa kai (don in ƙago wani sabon saƙo).

  87. إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 38:87

    “Shi ba wani abu ba ne in ban da tunatarwa ga talikai.

  88. وَلَتَعۡلَمُنَّ نَبَأَهُۥ بَعۡدَ حِينِۭ

    Open ayah 38:88

    “Kuma tabbas za ku san gaskiyar labarinsa (watau Alƙur\'ani) bayan wani ɗan lokaci.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya shaida wa mushirikai cewa, ba ya neman su biya shi wani lada a kan saƙon Allah da yake isar musu da nasihar da yake yi musu, kuma har ila yau shi ba ya matsa wa kansa sai ya kawo wani ƙarin umarni a kan wanda aka yi masa, yana tsaye ne kyam a kan abin da aka yi masa wahayi da shi ba daɗi ba ragi. Kuma su sani cewa, shi Alƙur’ani tunatarwa ce ga talikai mutane da aljannu, kuma lalle tabbas za su san gaskiyar labarin wannan Alƙur’ani su gane cewa daga Allah ne da zarar sun mutu sun koma ga mahaliccinsu Allah.