الزمر
Az-Zumar
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ
Open ayah 39:1Saukar Littafi daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima.
إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ
Open ayah 39:2Lalle Mu Muka saukar maka Littafi da gaskiya, to ka bauta wa Allah kana mai tsantsanta addini a gare Shi.
أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلۡخَالِصُۚ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ
Open ayah 39:3Ku saurara! Tsantsan addini na Allah ne. Waɗanda kuwa suka riƙi wasu majiɓinta al’amari ba Shi ba (suna cewa): “Ba ma bauta musu sai kawai don su kusanta mu ga Allah.” Lalle Allah zai yi hukunci a tsakaninsu game da abin da suke sassaɓawa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake maƙaryaci, mai yawan kafirci.
لَّوۡ أَرَادَ ٱللَّهُ أَن يَتَّخِذَ وَلَدٗا لَّٱصۡطَفَىٰ مِمَّا يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ سُبۡحَٰنَهُۥۖ هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ
Open ayah 39:4Da Allah Ya yi nufin Ya riƙi ɗa, da sai Ya zaɓi wanda Ya ga dama daga abubuwan da Yake halitta. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shi ne Ɗaya, Mai rinjaye. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da bayanin cewa, shi ne Allah Mabuwayi wanda babu mai iya ja da shi, mai hikima cikin ayyukansa, shi ne ya saukar da Alƙur’ani wanda gaskiya ce da babu wani kokwanto a cikinta. Sannan ya ƙara jaddada cewa lalle shi ne ya saukar wa da Manzonsa Annabi Muhammadu (ﷺ) wannan Alƙur’ani wanda yake cike da gaskiya ta fuskar labaransa, hukunce-hukuncensa kuma duk adalci ne. Sai kuma ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya kaɗaita shi wajen bauta tare da tsantsanta addini gare shi shi kaɗai. Ya tabbatar da cewa tsantsar addini wanda babu shirka a cikinsa nasa ne. Amma waɗanda suka riƙi wasu ababen, bauta gumaka ne ko wasunsu, suna bauta musu suna kuma fakewa da cewa, su fa ba komai ya sa suke bauta musu ba sai don kawai su kusantar da su wurin Allah, watau su isar da buƙatunsu wurinsa, su cece su a gabansa. Allah ya bayyana cewa zai yi hukunci tsakanin muminai masu kaɗaita shi da bauta da waɗannan da suke haɗa bautarsa da wasu abubuwan daban a ranar ƙiyama a kan saɓabin da suke yi game da sha’anin Tauhidi. Allah kuma ya bayyana cewa, duk mai yi masa ƙaryar yana da abokin tarayya mai butulce wa ni’imominsa, to ba zai shiryar da shi zuwa ga tafarkin gaskiya ba, domin zai doɗe zuciyarsa, hasken shiriya ya ƙi shiga cikinta sakamakon bijire wa ayoyin Allah da ya yi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da ya yi nufin samar wa kansa ɗa, to da sai ya zaɓi abin da ya ga dama daga cikin halittarsa ya mayar da shi ɗansa. To amma Allah ya tsarkaka daga duk abin da waɗannan mushirikan suke jingina masa na shirka, domin shi Ɗaya ne a zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, mai rinjaye ne a kan dukkan halittunsa.
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۖ يُكَوِّرُ ٱلَّيۡلَ عَلَى ٱلنَّهَارِ وَيُكَوِّرُ ٱلنَّهَارَ عَلَى ٱلَّيۡلِۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمًّىۗ أَلَا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفَّٰرُ
Open ayah 39:5Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya; Yana naɗa dare a kan yini, Ya kuma naɗa yini a kan dare; kuma Ya hore rana da wata; kowane yana tafiya zuwa wani lokaci ƙayyadajje. Ku saurara! Shi ne Mabuwayi, Mai yawan gafara.
خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ ثُمَّ جَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ ثَمَٰنِيَةَ أَزۡوَٰجٖۚ يَخۡلُقُكُمۡ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡ خَلۡقٗا مِّنۢ بَعۡدِ خَلۡقٖ فِي ظُلُمَٰتٖ ثَلَٰثٖۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُصۡرَفُونَ
Open ayah 39:6Ya halicce ku daga rai guda (shi ne Adamu), sannan Ya halicci matarsa daga gare shi, Ya kuma halitta muku dangogi guda takwas na dabbobin ni’ima. Yana (shirya) halittarku a cikin cikkunan iyayenku mata, matakin halitta bayan wani matakin, cikin duffai guda uku. Wannan kuwa Shi ne Allah Ubangijinku; Wanda mulki nasa ne; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. To ta ina ne ake juyar da ku? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya halicci sammai da ƙasa ba don wasa ba, sai don wata babbar hikima da gaskiya, kuma shi ne yake sarrafa su yadda ya ga dama, yana naɗa dare a kan yini, yana kuma naɗa yini a kan dare, watau yakan sanya dare ya lulluɓe yini da duhunsa, ko ya sanya yini ya lulluɓe dare da haskensa; duk sanda ɗaya ya zo sai ɗayan ya gushe. Ya kuma hore rana da wata, kowannensu yana gudu gwargwadon lokacin da aka ƙayyade masa, watau zuwa ƙarshen rayuwar duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa shi ne Mabuwayi wanda zai iya saukar da uƙubarsa ga masu saɓa masa, babu mai iya hana shi, kuma mai yawan gafarar zunuban bayinsa ne waɗanda suka tuba suka nemi gafararsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jawo hankulan mutane zuwa ga hikimar halittarsu da ta dabbobinsu, da cewa ya halicce su ne daga rai ɗaya shi ne Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), daga gare shi kuma ya halicci matarsa Hauwa’u. Sannan kuma ya halitta musu dabbobin ni’ima, watau raƙuma da shanu da tumakai da awakai, nau’uka guda takwas, watau kowane nau’i jinsin namiji da mace. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, mutane da dabbobi duka ya halicce su ne a cikin cikkunan iyayensu mata, ya shirya halittarsu mataki bayan mataki a cikin duffai guda uku, duhun ciki da duhun mahaifa da kuma duhun mabiyiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, mai yin wannan halittar shi ne Allah Ubangijinsu, kuma shi ne kaɗai mai cikakken mulki, babu wanda ya cancanta a bauta wa sai shi kaɗai, to amma abin mamaki ta yaya ake karkatar da su daga bautar mai kowa da komai zuwa bautar wanda bai halicci komai ba?
إِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنكُمۡۖ وَلَا يَرۡضَىٰ لِعِبَادِهِ ٱلۡكُفۡرَۖ وَإِن تَشۡكُرُواْ يَرۡضَهُ لَكُمۡۗ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Open ayah 39:7Idan kun kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin ku, ba Ya kuma yarda da kafirci daga bayinsa. Idan kuwa kuka gode Zai yarda da godiyar taku. Kuma wani rai ba ya ɗaukar laifin wani. Sannan zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sannan Ya ba ku labarin irin abubuwan da kuka kasance kuna aikatawa. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin ƙiraza ne.
۞وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَا رَبَّهُۥ مُنِيبًا إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَا خَوَّلَهُۥ نِعۡمَةٗ مِّنۡهُ نَسِيَ مَا كَانَ يَدۡعُوٓاْ إِلَيۡهِ مِن قَبۡلُ وَجَعَلَ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلَّ عَن سَبِيلِهِۦۚ قُلۡ تَمَتَّعۡ بِكُفۡرِكَ قَلِيلًا إِنَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ
Open ayah 39:8Idan kuma wata cuta ta sami mutum sai ya roƙi Ubangijinsa yana mai komawa gare Shi, sannan idan Ya ba shi wata ni’ima daga gare Shi, sai ya manta abin da ya kasance yana roƙon Sa a da, ya kuma sanya abokan tarayya ga Allah don ya ɓatar (da mutane) daga hanyarsa (Allah). Ka ce: “Ka ji daɗi ɗan kaɗan da kafircinka; lalle kai kam kana daga cikin ‘yan wuta.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakkiyar wadatarsa ga ɗan’adam da cewa, ba shi ne mai amfana da ɗa’ar da ake yi masa ba, domin kuwa da mutane duk za su kafirce masa, to lalle shi mawadaci ne ba ya da buƙatar imaninsu, kafircinsu kuma ba zai cutar da shi da komai ba, sai dai su ne za su cutu da wannan kafircin. An karɓo daga Abu Zarri (Allah ya kara masa yarda) daga Annabi (ﷺ) ya ce: “Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: ‘Ya ku bayina, ku ba ku isa ku cuce ni ba ballantana har ku cutar da ni, kuma ba ku isa ku amfane ni ba ballantana har ku amfanar da ni. Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljannunku za su kasance a bisa zuciyar wanda ya fi kowa taƙawa daga cikinku, wannan ba zai ƙara komai a cikin mulkina ba. Ya ku bayina, da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljannunku za su kasance a bisa zuciyar wanda ya fi kowa fajirci daga cikinku, wannan ba zai rage komai daga mulkina ba’”. [Muslim #2577]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa ba zai taɓa yarda da kafirci daga bayinsa ba, domin bai umarce su da shi ba, saboda Allah ba ya umarni da aikata mummunan aiki. Amma idan suka gode wa ni’imominsa suka yi imani da shi, to zai yarda da godiyar tasu har ma ya yi musu kyakkyawar sakayya a kai. Watau wannan wata rahama ce daga wajensa, ba don yana da buƙatar ɗa’arsu ba kuma ba don zai cutu da kafircinsu ba, sai dai don amfanin kansu kawai. Ya kuma tabbatar musu da cewa kowa zai ga sakamakon aikinsa ne kyakkyawa ko mummuna, domin kuwa babu wani rai da zai ɗauki laifin wani, sannan makomarsu gaba ɗayansu zuwa gare shi ne a ranar alƙiyama, zai kuma ba wa kowa labarin abin da ya aikata a duniya ya yi masa sakayya a kansa. Lalle kuma shi masanin abin da yake cikin zukatan bayinsa ne babu abin da yake ɓuya gare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata mummunar ɗabi’a ta kafiri ta butulci ga ni’imar Ubangijinsa da cewa, idan wata cuta ta sami kafiri ta rashin lafiya ko asarar dukiya ko shiga cikin halin tsoron nutsewa a ruwa da makamantansu, sai ya dage ya yi ta roƙon Allah domin ya yaye masa damuwarsa, ya koma gaba ɗaya wajen Allah shi kaɗai ba zai kira wani gunkinsa ba, to amma da zarar wata ni’ima daga Allah ta same shi, ya yaye masa cutar da ta same shi da damuwarsa, nan da nan sai ya manta da wanda ya kasance yana roƙon sa a da, watau Allah, ya ci gaba da sanya wa Allah abokan tarayya yana bauta musu don ya ɓatar da mutane daga hanyar Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya faɗa wa duk mai irin wannan mummunan hali, ya ji ɗan daɗi kaɗan da kafircinsa a cikin gwargwadon abin da ya rage masa na rayuwarsa ta duniya, to amma ya sani cewa lalle shi a ranar alƙiyama yana daga cikin ‘yan wuta masu dawwama a cikinta har abada, don haka daɗin da ya ji a nan duniya bai amfana masa komai ba a wannan ranar.
أَمَّنۡ هُوَ قَٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ سَاجِدٗا وَقَآئِمٗا يَحۡذَرُ ٱلۡأٓخِرَةَ وَيَرۡجُواْ رَحۡمَةَ رَبِّهِۦۗ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Open ayah 39:9Shin yanzu wanda yake shi mai ibada ne a cikin sa’o’in dare, yana sujjada yana kuma tsayawa, yana tsoron ranar lahira yana kuma ƙaunar rahamar Ubangijinsa (zai yi daidai da wanda ba haka yake ba?) Ka ce: “Yanzu waɗanda suke da sani za su yi daidai da waɗanda ba su da sani? Ma’abota hankula ne kawai suke wa\'azantuwa. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo wani gwaji ne tsakanin kyawawan halaye na muminai, da kuma butulcin kafirai, inda yake cewa, shin mumini mai biyayya ga Allah, mai raya lokutan darensa yana sujjada a gare shi yana tsayuwa domin bautar sa, yana kuma jin tsoron azabar lahira yana kuma fatan samun rahamar Allah, wannan ne ya fi ko kuma kafiri wanda zai bauta wa Allah idan ya shiga damuwa, amma ya kafirce masa yayin da yake cikin yalwa ya riƙa sanya masa kishiyoyi? An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya shiga wurin wani saurayi yana cikin gargarar mutuwa sai ya ce masa: “Yaya kake jin ka?” Sai ya ce: “Ya Manzon Allah, wallahi tabbas ina kyautata fata ga Allah, ina kuma tsoron zunubina.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Waɗannan abubuwa biyu ba su taɓa haɗuwa a zuciyar wani bawa a irin wannan wuri ba, face sai Allah ya ba shi abin da yake fata, ya amintar da shi daga abin da yake tsoro.” [Tirmizi #983]. An karɓo daga Tanimud Dari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya karanta aya ɗari a cikin dare to za a rubuta masa ladan ibadar dare.” [Ahmad #16958]. Sai kuma Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa wa bayinsa cewa, shin waɗanda suke da ilimin sanin Allah da haƙƙoƙinsa da shari’arsa za su zama daidai da waɗanda ba su san komai a kan haka ba? Ya tabbatar da cewa waɗanda kawai suke gane bambanci tsakanin waɗannan ɓangarori biyu su ne mutane masu lafiyayyen hankali.
قُلۡ يَٰعِبَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ لِلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٞۗ وَأَرۡضُ ٱللَّهِ وَٰسِعَةٌۗ إِنَّمَا يُوَفَّى ٱلصَّٰبِرُونَ أَجۡرَهُم بِغَيۡرِ حِسَابٖ
Open ayah 39:10Ka ce: “Ya ku bayina waɗanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Ubangijinku. Waɗanda suka kyautata a wannan duniyar suna da kyakkyawan (sakamako). Ƙasar Allah kuma yalwatacciya ce. Lalle masu haƙuri ne kawai ake cika wa ladansu ba da lissafi ba.”
قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ
Open ayah 39:11Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in bauta wa Allah ina mai tsantsanta addini gare Shi.
وَأُمِرۡتُ لِأَنۡ أَكُونَ أَوَّلَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 39:12“An kuma umarce ni da in kasance farkon Musulmi.”
قُلۡ إِنِّيٓ أَخَافُ إِنۡ عَصَيۡتُ رَبِّي عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 39:13Ka ce: “Lalle ni ina jin tsoron azabar wani yini mai girma idan na saɓi Ubangijina”
قُلِ ٱللَّهَ أَعۡبُدُ مُخۡلِصٗا لَّهُۥ دِينِي
Open ayah 39:14Ka ce: “Allah kawai nake bauta wa, ina mai tsantsanta addinina gare Shi.
فَٱعۡبُدُواْ مَا شِئۡتُم مِّن دُونِهِۦۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡخَٰسِرِينَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَأَهۡلِيهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَا ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡخُسۡرَانُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 39:15“Sai ku bauta wa abin da kuka ga dama ba Shi ba.” Ka ce: “Lalle asararru (su ne) waɗanda suka yi asarar rayuwarsu da ta iyalinsu ranar alƙiyama. Ku saurara! Wannan ita ce asara bayyananniya.
لَهُم مِّن فَوۡقِهِمۡ ظُلَلٞ مِّنَ ٱلنَّارِ وَمِن تَحۡتِهِمۡ ظُلَلٞۚ ذَٰلِكَ يُخَوِّفُ ٱللَّهُ بِهِۦ عِبَادَهُۥۚ يَٰعِبَادِ فَٱتَّقُونِ
Open ayah 39:16Suna da inuwoyi na wuta a samansu, a ƙarƙashinsu kuma akwai wasu inuwoyin. Wannan ne fa Allah Yake tsoratar da bayinsa da shi. Ya ku bayina, sai ku kiyaye dokokina. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi wa bayinsa muminai umarni kan su ji tsoron Ubangijinsu su kiyaye dokokinsa, ya kuma sanar da su cewa duk wanda ya kyautata aikinsa to yana da kyakkyawan sakamako a nan duniya, na samun taimako da ƙoshin lafiya da wadatar arziki, a lahira kuma yana da sakamakon gidan Aljanna. Sai kuma ya kwaɗaitar da su da yin hijira daga inda aka hana su bautar Allah zuwa inda za su sami sararin bauta masa, su kuma yi haƙuri da zafin raɗaɗin barin gidajensu; lalle ƙasar Allah tana da yalwa, don haka kada su takura wa kawunansu. Ya tabbatar musu da cewa masu haƙuri a kan bin Allah da guje wa saɓonsa da jure wa ƙaddararsa marar daɗi su ne kawai za a cika musu ladansu ranar alƙiyama ba tare da lissafi ba saboda yawansa. Sannan ya umarci Annabi (ﷺ) da cewa ya sanar da mushirikai cewa shi fa an umarce shi ne ya bauta wa Allah shi kaɗai ya kuma tsantsanta addininsa gare shi, don haka kada su yi tsammanin zai yarda ya bauta wa wani abu da suke bauta wa, kuma an umarce shi ya zamanto farkon wanda ya miƙa wuya ga Allah a cikin wannan al’umma. Kuma ya shaida musu cewa shi kansa yana jin tsoron idan har ya saɓa wa Ubangijinsa bai yi masa biyayya yadda ya kamata ba, to yana tsoron azabar wani yini mai girma, watau ranar alƙiyama. Allah kuma ya sake umartar sa da ya tabbatar musu da cewa shi fa Allah kaɗai yake bauta wa, yana tsarkake addininsa gare shi shi kaɗai, don haka su su je su bauta wa duk abin da suka ga dama, su ne za su gamu da mummunan ƙarshe, kuma za su tafka mummunar asara a ranar alƙiyama idan ba su tuba ba, lalle kuwa asararru na gaske su ne waɗanda suka yi asarar kawunansu da iyalansu a ranar alƙiyama, kuma wannan ita ce asara mabayyaniya. Watau ko dai iyalansu sun bi Allah a nan duniya sun shiga Aljanna a lahira, su kuma sun ɓata a duniya an jefa su wuta a lahira, don haka sun yi rabuwa ta har abada; ko kuma dukkansu sun mutu a kan kafirci, sun shiga wuta, kowa yana ta kansa babu wanda ya damu da wani. To lalle wannan ita ce babbar asara ta gaske. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin da za su tsinci kansu a cikin wuta a ranar alƙiyama da cewa, suna da wasu inuwowi na hayaƙi da harshen wuta da tsananin zafi a samansu da ƙarƙashinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shaida musu cewa, da irin wannan azabar ce yake tsoratar da bayinsa, don haka ya umarce su da lallai su kiyaye dokokinsa su aikata abin da ya umarce su kuma su guje wa abin da ya hana su.
وَٱلَّذِينَ ٱجۡتَنَبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ أَن يَعۡبُدُوهَا وَأَنَابُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ لَهُمُ ٱلۡبُشۡرَىٰۚ فَبَشِّرۡ عِبَادِ
Open ayah 39:17Waɗanda kuwa suka nisanci bautar ɗagutu, suka kuma koma ga Allah, suna da albishir (na Aljanna). To ka yi wa bayina aibishir.
ٱلَّذِينَ يَسۡتَمِعُونَ ٱلۡقَوۡلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحۡسَنَهُۥٓۚ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ هَدَىٰهُمُ ٱللَّهُۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Open ayah 39:18Waɗanda suke sauraron magana sai su bi mafi kyawunta, waɗannan su ne waɗanda Allah Ya shiriya, kuma waɗannan su ne ma’abota hankula.
أَفَمَنۡ حَقَّ عَلَيۡهِ كَلِمَةُ ٱلۡعَذَابِ أَفَأَنتَ تُنقِذُ مَن فِي ٱلنَّارِ
Open ayah 39:19Yanzu wanda kalmar azaba ta tabbata a kansa (kai ne za ka iya shiyar da shi)? Yanzu kai za ka iya kuɓutar da wanda yake cikin wuta?
لَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ لَهُمۡ غُرَفٞ مِّن فَوۡقِهَا غُرَفٞ مَّبۡنِيَّةٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ لَا يُخۡلِفُ ٱللَّهُ ٱلۡمِيعَادَ
Open ayah 39:20Sai dai waɗanda suka kiyaye dokokin Ubangijinsu suna da ɗakunan benaye, a sama da su kuma akwai wasu ɗakunan benaye ginannu, ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu; (wannan) alƙawarin Allah ne; Allah ko ba Ya saɓa alƙawari. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu siffofin bayinsa nagari da kyakkyawan sakamako da ya yi musu alƙawari, da cewa su ne waɗanda suka nisanci bautar gumaka da duk wani abin bauta ba Allah ba, suka kuma tuba zuwa ga Allah; to waɗannan suna da albishir na Aljanna a lokacin mutuwarsu da lokacin da suke cikin ƙaburburansu da kuma ranar alƙiyama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya yi wa bayinsa nagari albishir da ni’imomin gidan Aljanna. Ya kuma siffanta su da cewa su ne waɗanda suke sauraron magana sai su tantance tsakanin mai kyau da mummuna, sai su bi mafi kyan magana mafi amfani. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa masu siffofi irin waɗannan, su ne waɗanda ya yi wa dacen shiriya, kuma masu lafiyayyen hankali waɗanda suka san abin da ya dace da su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya shaida wa Manzonsa cewa duk wanda azabarsa ta tabbata a kansa saboda dogewarsa a kan kafirci da ɓata, to Manzo (ﷺ) ya sani ba ya da wata dabara ta shiryar da shi har ya karɓi gaskiya, don haka ba zai iya ceto shi daga shiga wuta ba bayan ya siffantu da siffar kafirci ya mutu a kanta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka siffantu da siffar taƙawa; suka yi aiki da umarnin Allah suka guji haninsa, da cewa suna da manyan gidajen bene wasu kan wasu waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Wannan kuma alƙawari ne Allah ya yi musu, shi kuma ba ya saɓa alƙawari idan ya yi. An karɓo daga Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle a gidan Aljanna akwai wasu benaye waɗanda ake ganin bayansu daga cikinsu, ake kuma ganin cikinsu daga bayansu.” Sai wani mutumin ƙauye ya tashi ya ce: “Na wane ne su ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Na wanda ya kyautata maganarsa ne, ya kuma ciyar da abinci, ya dimanci yin azumi, ya kuma yi salla da daddare yayin da mutane suke barci.” [Tirmizi #1984 da Ahmad #1338]. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle ‘yan Aljanna suna hango mutanen benaye a samansu kamar yadda kuke hango tauraro mai haske mai tafiya a sasannin sama daga gabas ko daga yamma, saboda fifikon da yake tsakaninsu.” Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, waɗannan ai gidaje ne na annabawa; babu mai samun su sai su kaɗai.” Sai ya ce: “E, haka ne. Na rantse da wanda raina yake hannunsa, akwai kuma wasu mazaje waɗanda suka yi imani da Allah suka kuma gaskata manzanni.” – watau su ma za su sami waɗannan gidajen – [Bukhari #3257 da Muslim #2831].
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَسَلَكَهُۥ يَنَٰبِيعَ فِي ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ يُخۡرِجُ بِهِۦ زَرۡعٗا مُّخۡتَلِفًا أَلۡوَٰنُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصۡفَرّٗا ثُمَّ يَجۡعَلُهُۥ حُطَٰمًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Open ayah 39:21Yanzu ba ka gani cewa Allah ne Ya saukar da ruwa daga sama, sannan Ya shigar da shi cikin idanuwan ruwa a ƙasa, sannan Yana fitar da shukoki masu launi iri-iri da shi, sannan ya bushe sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan Ya mayar da shi dudduga? Lalle a game da wannan tabbas akwai wa’azi ga ma’abota hankula. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin Manzonsa (ﷺ) game da saurin gushewar duniya da abin da yake cikinta na jin daɗi da cewa, ya duba ya ga yadda ya saukar da ruwa daga sama, sannan ya shigar da shi cikin idanuwan ruwa da magudanansa a ƙasa, sannan da wannan ruwa ya fitar da shukoki masu launi iri-iri. Sai daga baya wannan shukar ta bushe ta yi fatsi-fatsi bayan a da tana koriya shar; sannan bayan ta bushe sai Allah ya mayar da ita dudduga. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa lalle a cikin wannan aiki nasa akwai wa’azantarwa ga masu hankula lafiyayyu.
أَفَمَن شَرَحَ ٱللَّهُ صَدۡرَهُۥ لِلۡإِسۡلَٰمِ فَهُوَ عَلَىٰ نُورٖ مِّن رَّبِّهِۦۚ فَوَيۡلٞ لِّلۡقَٰسِيَةِ قُلُوبُهُم مِّن ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ أُوْلَٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ
Open ayah 39:22Yanzu wanda Allah Ya buɗa masa ƙirjinsa da Musulunci don haka ya zama cikin haske daga Ubangijinsa (zai yi kamar wanda zuciyarsa ta ƙeƙashe?) To tsananin azaba ya tabbata ga masu ƙeƙasassun zukata da ba sa ambaton Allah. Waɗannan suna cikin ɓata mabayyani.
ٱللَّهُ نَزَّلَ أَحۡسَنَ ٱلۡحَدِيثِ كِتَٰبٗا مُّتَشَٰبِهٗا مَّثَانِيَ تَقۡشَعِرُّ مِنۡهُ جُلُودُ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ ثُمَّ تَلِينُ جُلُودُهُمۡ وَقُلُوبُهُمۡ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُدَى ٱللَّهِ يَهۡدِي بِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٍ
Open ayah 39:23Allah Ya saukar da mafi kyan zance: Alƙur’ani mai kama da juna, mai biyunta (saƙo), tsikar fatun waɗanda suke tsoron Ubangijinsu suna tashi, sannan fatunsu su yi taushi, zukatansu kuwa su koma zuwa ambaton Allah. Wannan ita ce shiriyar Allah, Yana shiyar da wanda Ya ga dama da ita. Wanda kuma Allah Ya ɓatar to ba shi da mai shiryar da shi.
أَفَمَن يَتَّقِي بِوَجۡهِهِۦ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَقِيلَ لِلظَّٰلِمِينَ ذُوقُواْ مَا كُنتُمۡ تَكۡسِبُونَ
Open ayah 39:24Yanzu wanda yake kare mummunar azaba da fuskarsa a ranar alƙiyama (zai yi kama da wanda ba ya yi?) Aka kuma ce da azzalumai: “Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kuna aikatawa.”
كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَأَتَىٰهُمُ ٱلۡعَذَابُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 39:25Waɗanda suke gabaninsu sun ƙaryata, sai azaba ta zo musu daga inda ba sa tsammani.
فَأَذَاقَهُمُ ٱللَّهُ ٱلۡخِزۡيَ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 39:26Sannan Allah Ya ɗanɗana musu azabar wulaƙanci a rayuwar duniya, kuma lalle azabar lahira ta fi girma. Da sun kasance sun san (hakan).
وَلَقَدۡ ضَرَبۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖ لَّعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 39:27Kuma haƙiƙa Mun ba wa mutane kowane nau\'i na misali a cikin wannan Alƙur’ani don su wa’azantu.
قُرۡءَانًا عَرَبِيًّا غَيۡرَ ذِي عِوَجٖ لَّعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Open ayah 39:28Alƙur’ani Balarabe marar karkata don su sami taƙawa. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi cikakken bayani na wajabcin komawa ga bautarsa da guje wa ruɗin duniya, sai kuma bayyana cewa babu mai amfana da wannan bayani nasa sai wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yalwata masa ƙirjinsa ya buɗe masa zuciyarsa ya haskaka masa ita da hasken imani. Allah kuma ya yi tambaya cewa, shin yanzu mutumin da Allah ya yi masa irin wannan buɗin ya shiriya ya kama addinin Musulunci yana gudanar da rayuwarsa a kan basira da haske daga Ubangijinsa, zai zama ɗaya da wanda zuciyarsa ta riga ta ƙeƙashe babu ambaton Allah tare da shi? Lalle amsa ita ce ba za su zama ɗaya ba har abada, domin shiryayye shi ne zai samu kuɓuta a wurin Allah, wanda kuwa zuciyarsa ta ƙeƙashe shi ya yi hasara ta har abada. Kuma masu ƙeƙasassun zukata suna cikin ɓata bayyananne. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwarzanta littafinsa Alƙur’ani da cewa shi ne littafi mafi kyan zance da ya saukar wa Annabi Muhammadu (ﷺ) wanda kuma yake da kamanceceniya da juna a wajen gaskiya da kyan tsari da azancin Magana; sashinsa kuma ba ya warware wani sashi. Yana kuma biyunta batutuwansa da saƙwanninsa; ya ƙunshi ƙissoshi mabambanta da hukunce-hukunce iri-iri, da gargaɗi da albishir, da bayanin siffofin masu gaskiya da siffofin maƙaryata da sauran batutuwa daban-daban. Idan masu tsoron Ubangijinsu suka saurari abin da yake cikinsa na gargaɗi da tsoratarwa sai duk tsakar jikinsu ta riƙa tashi, sannan idan suka saurari abin da ya ƙunsa na albishir da kyakkyawan fata sai fatarsu ta yi laushi hankalinsu ya kwanta, su koma zuwa ga ambaton Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma ya bayyana cewa wannan tasirin na Alƙur’ani da aka ambata shiriya ce daga Allah da yake shiryar da wanda ya ga dama da ita, amma kuma duk wanda ya ɓatar ya hana masa shiriya to babu wanda ya isa ya shiryar da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo bambanci tsakanin shiryayyen mutum da taɓaɓɓe, da cewa ba za su taɓa zama ɗaya ba. Watau ba za a daidaita wanda Allah ya shiryar da shi, ya ba shi ikon yin aikin shiga Aljanna ya kuma shigar da shi cikinta a lahira, da mutumin da ya kafirce wa Allah ya mutu a kan kafirci, aka jefa shi cikin wuta yana a ƙuƙumce ba. Lalle wannan ya tabbata cikin azzalumai waɗanda a ranar za a ce da su su ɗanɗani mummunan sakamakon abin da suka riƙa aikatawa a duniya na kafirci da saɓon Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa al’ummun da suka gabaci waɗannan mushirikai su ma sun ƙaryata manzannin da ya aika musu, sai azaba ta zo musu kwatsam ta inda ba sa tsammani ballantana su yi shirin tuba zuwa ga Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɗanɗana musu azabar wulaƙanci da tozarta tun a nan duniya, kuma lalle azabar lahira da take jiran su ta fi wannan girma da tsanani, da a ce sun san haka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa a duk labaran da yake ba su a cikin littafinsa Alƙur’ani na mutanen kirki da na banza da bayanin gaskiya da ƙarya, to yana yin haka ne domin mutane su wa’azantu su saki ƙarya su kama gaskiya. Ya kuma tabbatar musu da cewa ya saukar da Alƙur’ani da harshen Larabci babu kuma wata karkata a cikinsa ko wani abu mai wahalar fahimta, don su karanta shi su kiyaye dokokin Allah da yake yi musu bayani a cikinsa.
ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا رَّجُلٗا فِيهِ شُرَكَآءُ مُتَشَٰكِسُونَ وَرَجُلٗا سَلَمٗا لِّرَجُلٍ هَلۡ يَسۡتَوِيَانِ مَثَلًاۚ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 39:29Allah Ya ba da misali na wani namiji (bawa) wanda yake da iyayen giji masu tarayya a kansa masu jayayya (a kan ba shi umarni) da kuma wani namiiji (bawa) da ya keɓanta ga wani namiji guda, shin misalinsu za su yi daidai? Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. A’a, yawancinsu dai ba su sani ba ne.
إِنَّكَ مَيِّتٞ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ
Open ayah 39:30Lalle kai mai mutuwa ne, su ma kuma lalle masu mutuwa ne.
ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عِندَ رَبِّكُمۡ تَخۡتَصِمُونَ
Open ayah 39:31Sannan kuma lalle ku ɗin nan a ranar alƙiyama a wurin Ubangijinku za ku yi husuma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayar da misalin mutumin da yake shirka da mutumin da yake kaɗaita Allah, ya haɗa misalinsu da wani bawa da iyayen giji suka yi tarayayya a kansa, sannan suna ba shi umarni daban-daban, idan ya daɗaɗa wa wani daga cikinsu sai ya fusata wani, don haka yana cikin ɗimuwa da rashin sanin abin yi don ya gamsar da kowa daga cikin iyayen gijinsa. Sai kuma ga wani bawa wanda ya keɓanta ga mutum guda shi ne ubangijinsa, ya san me yake so mene ne ba ya so, don haka yana gudanar da ayyukansa tare da shi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. To shin waɗannan mutane biyu za su zama ɗaya wajen kwanciyar hankali da nutsuwa? Lalle ba za su zama daidai ba. Sai Allah ya yabi kansa ya kuma tabbatar da cewa yawancin masu shirka da shi ba su san haka ba, shi ya sa suke haɗa shi da wasu wajen bautarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, babu makawa kowa sai ya mutu ya koma gare shi, babu mai dawwama a bayan ƙasa, har da shi kansa Manzo (ﷺ) shi ma mai barin duniya ne, don haka dukkansu za su haɗu a gaban Allah ranar alƙiyama inda za a raba musu gardamar abin da suke husuma a kansa, a bayyana mai gaskiya da maƙaryaci. An karɓo daga Zubairu ɗan Awwam (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yayin da wannan ayar ta sauka sai na ce: Ya Manzon Allah, yanzu sai an sake dawo mana abin da ya kasance a tsakaninmu (na husuma) tare da laifukan da muka yi a keɓe? Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “E, sai an dawo muku da su, har sai an mayar wa da kowa haƙƙinsa.” Sai Zubairu ya ce: “Lalle al’amarin mai tsanani ne.” [Tirmizi #3356 da Ahmad #1434].
۞فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَذَبَ عَلَى ٱللَّهِ وَكَذَّبَ بِٱلصِّدۡقِ إِذۡ جَآءَهُۥٓۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 39:32Wane ne ya fi zalunci fiye da wanda ya yi wa Allah ƙarya, ya kuma ƙaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu a cikin wutar Jahannama babu wurin zaman kafirai?
وَٱلَّذِي جَآءَ بِٱلصِّدۡقِ وَصَدَّقَ بِهِۦٓ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ
Open ayah 39:33Wanda kuwa ya zo da gaskiya ya kuma gaskata ta, waɗannan su ne masu taƙawa.
لَهُم مَّا يَشَآءُونَ عِندَ رَبِّهِمۡۚ ذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 39:34Suna da (sakamakon) abin da suke so daga wurin Ubangijinsu. Wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa.
لِيُكَفِّرَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ أَسۡوَأَ ٱلَّذِي عَمِلُواْ وَيَجۡزِيَهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 39:35Don Allah Ya kankare musu mafi munin abin da suka aikata, Ya kuma saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, babu azzalumin da ya fi wanda ya dangana wa Allah abokin tarayya, ko ya ce yana da ɗa ko mata don kawai ya ƙira wa Allah ƙaryar abin da bai dace ba. Hakanan babu azzalumin da ya fi wanda ya ƙaryata wahayin da aka yi wa Manzon Allah na Alƙur’ani. Idan mutum ya haɗa yi wa Allah ƙarya da kuma ƙaryata manzannin Allah to babu shakka wannan girman zaluncinsa ya wuce iyaka. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa a cikin Jahannama akwai mazauni ga duk wani kafiri azzalumi da ya butulce wa Ubangijinsa. To bayan Allah ya ambaci mai ƙarya kuma mai ƙaryata gaskiya, sai kuma ya ambaci sakamakon wanda ya zo da gaskiya cikin maganganunsa da ayyukansa kamar annabawa da mabiyansu, ya kuma gaskata wannan gaskiyar ya yi imani da ita ya yi aiki da ita. Allah ya tabbatar da cewa waɗannan su ne masu taƙawa na gaskiya, domin su ne suke aiki da umarninsa suke guje wa haninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa suna da sakamakon duk abin da suka ga dama suka so a wurin Ubangijinsu na ni’imomi na har abada. Allah ya bayyana cewa wannan shi ne sakamakon masu kyautata ayyukansu tsakaninsu da Ubangijinsu da kuma bayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi musu wannan sakamako ne, domin ya kankare musu mafi munin laifukan da suka aikata a duniya suka tuba zuwa ga Allah, ya kuma saka musu da sakamako mafi kyau daga ayyukan da suka aikata.
أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِكَافٍ عَبۡدَهُۥۖ وَيُخَوِّفُونَكَ بِٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ
Open ayah 39:36Yanzu Allah bai ishi bawansa ba? Suna kuma tsorata ka da waɗanda suke ba Shi ba. Wanda kuwa Allah Ya ɓatar to babu wani mai shiryar da shi.
وَمَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن مُّضِلٍّۗ أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِعَزِيزٖ ذِي ٱنتِقَامٖ
Open ayah 39:37Wanda kuma Allah Ya shiryar da shi to babu wani mai ɓatar da shi. Yanzu Allah ba Mabuwayi ba ne, Mai ramuwar gayya?
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلۡ أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ إِنۡ أَرَادَنِيَ ٱللَّهُ بِضُرٍّ هَلۡ هُنَّ كَٰشِفَٰتُ ضُرِّهِۦٓ أَوۡ أَرَادَنِي بِرَحۡمَةٍ هَلۡ هُنَّ مُمۡسِكَٰتُ رَحۡمَتِهِۦۚ قُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُۖ عَلَيۡهِ يَتَوَكَّلُ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ
Open ayah 39:38Tabbas da za ka tambaye su wanda ya halicci sammai da ƙasa, lalle za su ce: “Allah ne.” Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin waɗanda kuke bauta wa ba Allah ba, idan Allah Ya nufe ni da wata cuta, yanzu za su iya yaye cutar tasa, ko kuwa idan Ya nufe ni da rahama yanzu za su iya riƙe rahamarsa?” Ka ce: “Allah Ya ishe ni; a gare Shi ne kawai masu dogaro suke dogaro.”
قُلۡ يَٰقَوۡمِ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنِّي عَٰمِلٞۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 39:39Ka ce: “Ya ku mutanena, ku yi aiki a kan irin hanyarku, ni ma kuma zan yi aiki ne (a kan irin tawa), sannu ba da daɗewa ba za ku sani.
مَن يَأۡتِيهِ عَذَابٞ يُخۡزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيۡهِ عَذَابٞ مُّقِيمٌ
Open ayah 39:40“Wanda azabar da za ta kunyata shi za ta zo masa, kuma azaba madawwamiya za ta sauka a kansa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, zai kula da bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ) wanda ya tsaya kyam a kan bautarsa da cika umarninsa, zai biya masa buƙatunsa na duniya da na lahira, don haka ya ishe shi komai a rayuwarsa don babu wanda zai iya cutar da shi. Su kuma mushirikai saboda toshewar basirarsu da ɓatan da suke ciki wai har suna tsoratar da shi gumakansu da suke bauta wa suna cewa za su iya cutar da shi. Ba shakka wannan ɓatansu ne da toshewar basira; duk kuwa wanda Allah ya riga ya ɓatar to babu mai iya shiryar da shi, wanda kuma ya shiryar to babu mai ɓatar da shi. Sai kuma Allah ya nuna musu cewa, shi Mabuwayin Sarki ne da babu mai iya rinjayar sa, kuma mai yin uƙuba ga duk wanda ya kafirce masa kuma ya mutu bai tuba ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa, mushirikai sun san Allah shi ne mahaliccin komai, Rububiyya tasa ce shi kaɗai. Kuma da zai tambaye su cewa wane ne ya halicci sammai da ƙasa, da za su tabbatar masa da cewa Allah ne ya halicce su. Don haka ya umarce shi da ya nuna musu kasawar gumakansu da suke bauta wa ba Allah ba, kuma ya tambaye su cewa idan har Allah ya nufe shi da wata cuta, shin gumakan za su iya yaye masa wannan cutar? Ko kuma idan ya yi nufin sa da wata rahama gumakansu za su iya hana wannan rahamar ta same shi? Don haka ya tabbatar musu da cewa Allah kaɗai ne abin bauta, kuma shi kaɗai ne ma’ishinsa, kuma a gare shi shi kaɗai ya dogara, kuma lallai duk masu dogara su dogara gare shi, shi kaɗai ne zai iya biya musu buƙatunsu, ya share musu hawayensu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya yi wa mushirikai kashedi game da abin da suke dagewa a kansa na shirka, da cewa su ci gaba da aikata shirkarsu ta bautar gumaka, shi ma zai ci gaba da aikin da Allah ya umarce shi da shi na kira zuwa ga Tauhidi da tsantsanta bauta ga Allah shi kaɗai, ba da jimawa ba za su san wane ne zai samu kyakkyawan ƙarshe; za kuma su gane wanda azaba za ta riƙe shi tun a nan duniya ta wulaƙanta shi, sannan kuma a lahira ya gamu da wata mummunar azaba madawwamiya.
إِنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ لِلنَّاسِ بِٱلۡحَقِّۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٍ
Open ayah 39:41Lalle Mu Mun saukar maka da Littafi da gaskiya ga mutane; saboda haka duk wanda ya shiriya to ya yi wa kansa alheri, wanda kuwa ya ɓata, to lalle ya ɓata ne don kansa; kuma kai ba wakili ba ne a kansu.
ٱللَّهُ يَتَوَفَّى ٱلۡأَنفُسَ حِينَ مَوۡتِهَا وَٱلَّتِي لَمۡ تَمُتۡ فِي مَنَامِهَاۖ فَيُمۡسِكُ ٱلَّتِي قَضَىٰ عَلَيۡهَا ٱلۡمَوۡتَ وَيُرۡسِلُ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّىۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 39:42Allah Yana karɓar rayuka lokacin mutuwarsu, da waɗanda kuma ba su mutu ba a lokacin baccinsu; sai Ya riƙe waɗanda Ya ƙaddara wa mutuwa, Ya kuma saki sauran har zuwa wani lokaci ƙayyadadde. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani.
أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُفَعَآءَۚ قُلۡ أَوَلَوۡ كَانُواْ لَا يَمۡلِكُونَ شَيۡـٔٗا وَلَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 39:43Tabbas sun dai riƙi wasu masu ceto ne ba Allah ba. Ka ce: “Yanzu (kwa yi haka) ko da kuwa sun kasance ba sa mallakin komai, kuma ba sa hankalta?”
قُل لِّلَّهِ ٱلشَّفَٰعَةُ جَمِيعٗاۖ لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 39:44Ka ce: “Ceto gaba ɗaya na Allah ne; mulkin sammai da ƙasa nasa ne Shi kaɗai; sannan kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku.”
وَإِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَحۡدَهُ ٱشۡمَأَزَّتۡ قُلُوبُ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِۖ وَإِذَا ذُكِرَ ٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦٓ إِذَا هُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ
Open ayah 39:45Idan kuma aka ambaci Allah Shi kaɗai sai zukatan waɗanda ba sa ba da gaskiya da ranar lahira su takura; idan kuwa aka ambaci waɗanda suke ba Shi ba sai ka gan su suna ta walwala. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi zuciyar Manzonsa (ﷺ) ya kwantar masa da hankali game da abin da yake fuskanta na tirjiyar mutanensa da kafewarsu a kan kafirci da cewa, ya saukar masa da Alƙur’ani ne da gaskiya don ya gargaɗi mutane da shi ya tsayar musu da hujjar Allah a kansu, don haka duk wanda ya shiriya to ya shiriya ne don kansa domin shi ne zai amfana da shiriyarsa ba Allah ba; duk kuma wanda ya ɓata to babu shakka kansa kawai zai cutar; ɓatansa ba zai cutar da Allah da komai ba. Ya kuma nuna wa Manzonsa cewa shi fa ba an aiko shi ne don ya tursasa wani kan ya yi imani ba; shi kawai aikin da aka ɗora masa shi ne isar da saƙon Allah gare su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wani nau’i na Ƙudurarsa da ikonsa na gudanar da rayuwar ɗan’adam, da cewa, shi ne yake karɓar rayuka lokacin mutuwarsu yayin da ajalinsu ya cika, yake kuma karɓar rayukan waɗanda lokacin mutuwarsu bai zo ba yayin barcinsu. Sai ya riƙe ruhin wanda ya ƙaddara wa mutuwa a wurinsa, ya kuma saki wanda bai ƙaddara mutuwarsa a lokacin ba har zuwa wani ƙayyadajjen lokaci da ya bar wa kansa saninsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa a cikin waɗannan ayyuka nasa akwai ayoyi ga mutane masu tunani su gane cewa lalle wanda duk yake iya wannan aiki to zai iya tayar da mutane bayan mutuwa domin yi musu hisabi. An karɓo daga Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ɗayanku ya je wajen kwanciyarsa to ya kakkaɓe shi da cikin mayafinsa, domin bai san abin da ya maye gurbinsa ba a bayansa, sannan ya ce: “Da sunanka ya Ubangijina na kwantar da ɓarin jikina, da kuma taimakonka ne zan ɗaga shi; idan ka riƙe raina to ka gafarta masa, idan kuma ka sako shi to ka tsare shi da abin da kake tsare bayinka salihai da shi.” [Bukhari #6320 da Muslim #2714]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai sun ɗauki gumaka suna bauta musu domin tsammanin wai za su cece su a wurin Allah (Mai tsarki da daukaka) za kuma su amfane su a rayuwarsu ta duniya. Sai ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya tambaye su cewa shin za su riƙa bautar gumaka ne ko da kuwa ba za su mallaka wa kansu wani amfani ba ballantana har su mallaka musu wani abu? Kuma ko da ba sa hankaltar komai, sun kasance daskararrun abubuwa waɗanda ba sa ji ba sa gani ba sa kuma iya magana, sannan ba sa cutarwa ko amfanarwa? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya faɗa musu cewa lalle ceto gaba ɗaya na Allah ne, kuma babu mai ceto sai da izininsa, babu kuma wanda za a ceta sai wanda Allah ya yarda a cece shi. Kuma su sani cewa mulkin sammai da ƙasa duk nasa ne shi kaɗai, kuma zuwa gare shi kaɗai za a mayar da su ranar alƙiyama domin yi musu hisabi a kan ayyukansu. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani mummunan hali na mushirikai wanda yake nuna cewa sam ba su san girman Allah ba, watau duk sanda aka ambaci Allah shi kaɗai sai zukatan mushirikai waɗanda ba su yi imani da ranar lahira ba su yi matuƙar takura, su ji ba sa son jin wannan maganar. Amma idan aka ambaci gumakan da suke bauta wa ba Allah ba sai ka gan su suna ta farin ciki da walwala.
قُلِ ٱللَّهُمَّ فَاطِرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ عَٰلِمَ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ أَنتَ تَحۡكُمُ بَيۡنَ عِبَادِكَ فِي مَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 39:46Ka ce: “Ya Allah Mahaliccin sammai da ƙasa, Masanin ɓoye da sarari, Kai ne za Ka yi hukunci tsakanin bayinka game da abin da suka kasance suna yin saɓani a kansa.”
وَلَوۡ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦ مِن سُوٓءِ ٱلۡعَذَابِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَبَدَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مَا لَمۡ يَكُونُواْ يَحۡتَسِبُونَ
Open ayah 39:47Da a ce waɗanda suka yi zalunci za su mallaki abin da yake bayan ƙasa baki ɗaya har da wani kamarsa a tare da shi, to da sun fanshi kansu da shi saboda munin azabar ranar lahira. Abin da kuma ba su kasance suna tsammani daga Allah ba ya bayyana a gare su.
وَبَدَا لَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 39:48Kuma munanan abubuwan da suka aikata suka bayyana a gare su, abin kuma da suka kasance suna yi wa izgili ya auka musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya roƙi Ubangijinsa shiriya, ya mayar da duk al’amuransa gare shi, ya roƙe shi da sunansa Allah mahaliccin sammai da ƙasa ba tare da ya kwaikwaya a wurin wani ba, masanin abin da yake ɓoye da wanda yake sarari, ya kuma tabbatar da cewa shi ne kaɗai zai yi hukunci a tsakanin bayinsa ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna saɓani a kansa a duniya, ya bayyana mai gaskiya da marar gaskiya a tsakaninsu. An karɓo daga Abu Salama ya ce: Na tambayi A’isha, (Allah ya kara mata yarda) na ce: “Da me Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana buɗe sallarsa idan ya tashi cikin dare?” Sai ta ce: “Ya kasance idan ya tashi cikin dare yakan buɗe sallarsa da cewa: “Ya Allah Ubangijin Jibrila da Mika’ila da Israfila, wanda ya ƙagi halittar sammai da ƙasa, masanin abin da yake ɓoye da na sarari, kai ne kake yin hukunci a tsakanin bayinka game da abin da suka kasance suna saɓani a cikinsu, ka nuna mini gaskiya a cikin abin da suke saɓani a kansa da izininka, lalle kai ne kake shiryar da wanda ka ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.” [Muslim #770]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamako na waɗanda suka zalunci kawunansu a duniya ta hanyar shirka da saɓon Allah, da cewa da za su mallaki duk wata dukiya da duk wani abu mai tsada a bayan ƙasa, to da sun fanshi kawunansu da shi daga matsananciyar azabar da za su fuskanta a ranar alƙiyama. Kuma abin da ba su taɓa tsammanin ganin sa na azabar Allah ba ya bayyana a gare su; sai kuma ga shi mummunan sakamakon abin da suka aikata na shirka da saɓon Allah ya bayyana a gare su, sannan kuma azabar da suke yi wa izgili a duniya sai ga shi ta baibaye su ta ko’ina.
فَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلۡنَٰهُ نِعۡمَةٗ مِّنَّا قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمِۭۚ بَلۡ هِيَ فِتۡنَةٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 39:49To idan wata cuta ta samu mutum sai ya roƙe Mu, sannan idan Mun ba shi wata ni\'ima daga gare Mu sai ya ce: <b>“ </b>Ai an ba ni ita ne kawai don sanin (cancantata) <b>” </b>. Ba haka ba ne, ita wata jarrabawa ce kawai, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka).
قَدۡ قَالَهَا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 39:50Haƙiƙa waɗanda suke gabaninsu sun faɗe ita (wannan maganar), to abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar da su (komai) ba.
فَأَصَابَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْۚ وَٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡ هَٰٓؤُلَآءِ سَيُصِيبُهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْ وَمَا هُم بِمُعۡجِزِينَ
Open ayah 39:51Saboda haka sai (sakamakon) mummunan abin da suka aikata ya same su. Waɗanda ma suka yi zalunci daga waɗannan, (sakamakon) munanan abubuwan da suka aikata zai same su, kuma ba za su gagara ba.
أَوَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 39:52Yanzu ba su sani ba ne cewa, Allah Yana shimfiɗa arziki ga wanda Ya ga dama, Yana kuma ƙuntata wa (ga wanda ya ga dama)? Lalle a game da waɗannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata mummunar ɗabi’a ta kafirai wadda take nuna tsananin butulcinsu da rashin godiyarsu gare shi da cewa, idan wata damuwa ta samu wani kafiri ta rashin lafiya ko talauci da makamantansu, to sai ya roƙi Allah don ya yaye masa ita. To amma idan Allah ya biya masa buƙatarsa, ya ba shi lafiya ko dukiya sai ya riƙa cewa, ai Allah ya ba shi wannan ne don ya cancanci ya ba shi, bai san cewa Allah yana yi masa talala ne yana jarrabar sa da wannan ba. To amma yawancin kafirai ba su san haka ba, shi ya sa suke ruɗuwa da ni’imar da aka ba su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa irin wannan mummunar maganar da take fita daga bakin wannan kafiri, kafiran baya ma sun sha faɗar irinta, sun kuma yi ta ruɗuwa da yawan dukiyoyinsu da matsayin da suke a kai, to amma abin da suka riƙa aikatawa bai tsinana musu komai ba. Allah ya tabbatar da cewa mummunan sakamakon abin da suka aikata na shirka da saɓon Allah ya same su. Su ma kuma waɗanda suka zalunci kansu da aikata shirka da saɓon Allah cikin al’ummar Annabi Muhammadu (ﷺ), irin sakamakon da zai same su kenan, kuma ba za su gagari Allah ba ko su kuɓuce masa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi masu irin waccan ɗanyar magana cewa shin ba su san Allah shi ne yake yalwata wa wanda ya ga dama arziki ba don ya jarraba shi ya ga ko zai gode masa ko kuma zai butulce? Shi ne kuma yake ƙuntata arziki ga wanda ya ga dama don shi ma ya jarraba shi ya ga ko zai yi haƙuri ko zai nuna fushinsa ga ƙaddarar Allah? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa a cikin irin wannan aiki nasa akwai ayoyi masu nuna yadda Allah yake tsara al’amuransa ya gudanar da su a kan wannan tsarin ga mutane masu imani, domin su ne suke amfana da irin waɗannan ayoyi, amma kafirai suna ganin ba sa amfana da komai daga cikinsu.
۞قُلۡ يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ أَسۡرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُواْ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 39:53Ka ce: “Ya ku bayina waɗanda suka ɓata kawunansu sosai (da kafirci da saɓon Allah), kada ku ɗebe ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Yana gafarta zunubai baki ɗaya. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai rahama.
وَأَنِيبُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَأَسۡلِمُواْ لَهُۥ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ
Open ayah 39:54“Ku kuma koma zuwa ga Ubangijinku, ku kuma miƙa wuya gare Shi tun gabanin azaba ta zo muku sannan ba za a taimake ku ba.
وَٱتَّبِعُوٓاْ أَحۡسَنَ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ بَغۡتَةٗ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ
Open ayah 39:55“Kuma ku bi mafi kyan abin da aka saukar muku daga Ubangijinku tun gabanin azaba ta zo muku ba zato ba tsammani, alhali ku ba ku sani ba.
أَن تَقُولَ نَفۡسٞ يَٰحَسۡرَتَىٰ عَلَىٰ مَا فَرَّطتُ فِي جَنۢبِ ٱللَّهِ وَإِن كُنتُ لَمِنَ ٱلسَّٰخِرِينَ
Open ayah 39:56“Don kada wani rai ya ce: ‘Kaicona game da abin da na yi sakaci na haƙƙin Allah, ni tabbas na kasance daga masu yin izgili.’
أَوۡ تَقُولَ لَوۡ أَنَّ ٱللَّهَ هَدَىٰنِي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 39:57“Ko kuma ya ce: ‘Da Allah Ya shirye ni da tabbas na kasance daga masu taƙawa.’
أَوۡ تَقُولَ حِينَ تَرَى ٱلۡعَذَابَ لَوۡ أَنَّ لِي كَرَّةٗ فَأَكُونَ مِنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 39:58“Ko kuma ya ce lokacin da ya ga azaba: ‘Ina ma da ina da damar komawa duniya, don in kasance daga masu kyautatawa?’”
بَلَىٰ قَدۡ جَآءَتۡكَ ءَايَٰتِي فَكَذَّبۡتَ بِهَا وَٱسۡتَكۡبَرۡتَ وَكُنتَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 39:59(Sai a ce da shi): “A’a, haƙiƙa ayoyina sun zo maka sai ka ƙaryata su ka kuma yi girman kai ka kasance daga kafirai.” A waɗannan ayoyi, bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi kafirai sai kuma ya zo da bayanin rahamarsa da falalarsa ga muminai, ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya kirawo bayinsa waɗanda suka zaƙe da yawa wajen saɓon Allah har ma da shirka da cewa, kada su ɗebe ƙaunar samun rahamar Allah da gafarar zunubansu, domin Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya ga duk wanda ya tuba, domin shi mai rahama ne ga bayinsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Waɗannan ayoyin sun sauka ne game da al’amarin Ayyash ɗan Abu Rabi’ah da Al-Walid ɗan Walid da wasu Musulmi. Sun musulunta, amma sai aka fitine su aka dinga azabtar da su har suka sake komawa ga shirka. Sai muka riƙa cewa: ‘Har abada Allah ba zai karɓi nafilarsu da farillarsu ba; mutane su musulunta sannan don an azabtar da su sai su bar addininsu?’ Sai waɗannan ayoyin suka sauka. Umar ɗan Khaɗɗab ya kasance marubuci ne sai ya rubuta su da hannunsa ya aika su zuwa ga Ayyash da Walid da waɗannan jama’ar da suka musulunta, sai suka musulunta suka kuma yiwo hijira.” [Ibn Jarir, Jami’ul Bayan , Juzu’i na 20, shafi na 227-228]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu mutane masu shirka sun kashe mutane da yawa, sun yi zinace-zinace da dama, sai suka zo wurin Annabi (ﷺ) suka ce: “Lalle abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gare shi abu ne mai kyau, to ina ma za ka tabbatar mana cewa akwai kaffara ga abubuwan da muka aikata.” Sai faɗar Allah (Mai tsarki da daukaka) ta sauka: “Su ne waɗanda ba sa bauta wa wani abin bauta tare da Allah, ba sa kuma kashe ran da Allah ya haramta ba da haƙƙi ba, ba sa zina....” [Al-Furƙan, aya ta 67]; wannan aya ita ma ta sauka. [Bukhari #4810 da Muslim #122]. An karɓo daga Amru ɗan Abasa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani tsoho ya zo wurin Annabi (ﷺ) yana dogarawa da sandarsa ya ce: “Ya Manzon Allah, na karya alƙawura, na yi rashin mutunci da yawa, shin za a gafarta mini kuwa?” Sai Manzon Allah ya ce: “Shin ba kana shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah ba?” Ya ce: “Ƙwarai na yi, ina kuma shaidawa lalle kai Manzon Allah ne.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Haƙiƙa an gafarta maka karya alƙawuran da ka yi da rashin mutunci da ka yi.” [Ahmad #19432]. Sai Allah ya umarci bayinsa da su koma zuwa gare shi ta hanyar tuba da kyawawan ayyuka, kuma su miƙa wuya gare shi, tun kafin azaba ta zo musu a ranar alƙiyama, sannan ba za su sami wasu masu taimakon su ba daga gumakansu ko iyalansu su kuɓutar da su daga wannan azabar. Sannan kuma ya umarce su da su bi Alƙur’ani wanda shi ne mafi kyan abin da Ubangijinsu ya saukar wa Manzonsa (ﷺ), su bi umarninsa su kuma guji haninsa kafin azaba ta zo musu ba zato ba tsammani, ba kuma tare da sun san da zuwanta ba ballantana su yi mata kyakkyawan tanadi su tuba zuwa ga Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa ya yi musu wannan umarni ne don kada wani mai rai ya zo yana nadama ranar alƙiyama, yana cizon ɗan yatsa a kan babban sakaci da ya yi game da sha’anin Allah, ya rayu a kan kafirci da saɓon Allah da yi wa muminai izgili saboda sun yi imani sun bi Allah. Ko kuma wani mai rai ya zo ranar alƙiyama yana kafa hujja da ƙaddara, yana cewa da Allah ya shirye shi da ya kasance daga cikin masu taƙawa, masu bin umarninsa da guje wa haninsa. Ko kuma bayan ya ga azaba ƙarara ya riƙa burin ina ma za a mayar da shi duniya ya tuba ya zama cikin masu kyautata ayyukansu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wani ɗan wuta zai ga mazauninsa a Aljanna sai ya ce: ‘Ina ma a ce Allah ya shirye ni.’ Sai ya zame masa nadama. Duk wani ɗan Aljanna zai ga mazauninsa a wuta sai ya ce: ‘Yanzu ba don Allah ya shirye ni ba.’ watau da ya hallaka. Sai ya zamo masa godiya ga Allah. [Ahmad #10652]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa masa cewa, abin ba kamar yadda yake iƙirari ba ne, domin kuwa lalle ayoyin Allah sun zo masa amma sai ya ƙaryata su ya yi girman kai, ya kasance daga cikin masu kafirce wa Allah da ayoyinsa da manzanninsa.
وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تَرَى ٱلَّذِينَ كَذَبُواْ عَلَى ٱللَّهِ وُجُوهُهُم مُّسۡوَدَّةٌۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡمُتَكَبِّرِينَ
Open ayah 39:60A ranar alƙiyama kuwa za ka ga waɗanda suka yi wa Allah ƙarya fuskokinsu baƙi ƙirin. Yanzu a cikin wutar Jahannama ashe babu mazaunar masu girman kai?
وَيُنَجِّي ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ بِمَفَازَتِهِمۡ لَا يَمَسُّهُمُ ٱلسُّوٓءُ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 39:61Allah kuma zai tserar da waɗanda suka yi taƙawa da ayyukansu, wani mummunan abu ba zai shafe su ba, kuma ba za su yi baƙin ciki ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, a ranar alƙiyama zai ga waɗanda suke yi wa Allah ƙarya a nan duniya, suka danganta masa abokin tarayya ko suka ce yana da ɗa, fuskokinsu sun yi baƙi ƙirin na alamar suna cikin matsananciyar wahala da taɓewa, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya yi wa waɗannan mutane masu girman kai tanadin mazauni a cikin Jahannama saboda girman kansu da ya hana su yin imani da Allah da manzanninsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci sakamakon muminai masu taƙawa, da cewa zai tserar da su daga azaba, ya shigar da su wurin samun babban rabo shi ne Aljanna, babu kuma wata azaba da za ta shafe su, ba kuma za su yi baƙin cikin abin da suka baro a duniya ba.
ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ
Open ayah 39:62Allah ne Mahaliccin komai; kuma Shi ne Wakili a kan komai.
لَّهُۥ مَقَالِيدُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Open ayah 39:63Mabuɗan sammai da ƙasa nasa ne. Waɗanda kuwa suka kafirce wa ayoyin Allah, waɗannan su ne asararru.
قُلۡ أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ تَأۡمُرُوٓنِّيٓ أَعۡبُدُ أَيُّهَا ٱلۡجَٰهِلُونَ
Open ayah 39:64Ka ce: “Yanzu wanin Allah kuke umarta ta da in bauta wa, ya ku waɗannan wawaye?”
وَلَقَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ لَئِنۡ أَشۡرَكۡتَ لَيَحۡبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Open ayah 39:65Haƙiƙa kuma an yi maka wahayi kai da waɗanda suka gabace ka cewa: “Tabbas idan ka yi shirka lallai aikinka zai ɓaci, kuma tabbas za ka kasance daga asararru.”
بَلِ ٱللَّهَ فَٱعۡبُدۡ وَكُن مِّنَ ٱلشَّٰكِرِينَ
Open ayah 39:66A’a, Allah kaɗai za ka bauta wa, ka kuma kasance daga masu godiya.
وَمَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦ وَٱلۡأَرۡضُ جَمِيعٗا قَبۡضَتُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُ مَطۡوِيَّٰتُۢ بِيَمِينِهِۦۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Open ayah 39:67Ba su kuma girmama Allah ba kamar yadda Ya cancanta a girmama Shi, alhali ƙasa ga baki ɗayanta tana cikin Damƙarsa ranar alƙiyama, sammai kuma suna nannaɗe a Hannunsa na dama. Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma ɗaukaka game da abin da suke yin shirka (da shi). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi ne mahaliccin komai shi kaɗai, kuma shi ne wakili mai kula da kowa da komai, shi ne yake gudanar da kowane abu yadda ya so. Kuma mabuɗan taskokin alheri da ke cikin sammai da na ƙasa duka nasa ne shi kaɗai; yana yin kyauta ga wanda ya ga dama, ya kuma hana wanda ya ga dama. Ya kuma tabbatar wa kafirai cewa su ne suka yi hasara saboda sun kafirce wa ayoyinsa sun ƙi yin imani a rayuwarsu ta duniya, don haka a lahira duka wuta za su shiga kuma su dawwama a cikinta har abada. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya sanar da mushirikai waɗanda suke ta kiran sa a kan ya dawo ya bauta wa gumakansu, ya watsar da addinin kaɗaita Allah da bauta cewa, yanzu su jahilai marasa tunani da hankali su ne za su riƙa kiran sa ya zo ya bauta wa gumakansu, duk da cewa ya san babu wanda ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kaɗai? To su sani cewa wannan abu ba zai taɓa yiwuwa ba har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa Manzonsa (ﷺ) kashedi, (amma yana nufin al’ummarsa) cewa lalle ya yi masa wahayi, ya kuma yi wa manzannin da suka gabace shi wahayi cewa tabbas idan ya kuskura ya yi shirka, watau ya bauta wa wani tare da Allah, to babu shakka ladan aikinsa na ƙwarai gaba ɗaya zai ɓaci, kuma tabbas zai kasance daga cikin hasararru waɗanda suka yi hasarar duniya da lahira. Allah ya nuna masa cewa, ba shi da wani zaɓi face ya bauta wa Allah shi kaɗai, kada ya kuskura ya haɗa shi da wani, ya kuma zamanto cikin masu godiya a gare shi bisa ni’imomin da ya yi masa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mushirikai ba su girmama Allah yadda ya cancanta su girmama shi ba, yayin da suka yi tarayya da shi, suka haɗa shi da wasu gajiyayyu daga cikin halittarsa, suka manta da girman Ƙudurarsa wadda daga cikinta ƙasa da abubuwan da suke bayanta na duwatsu da bishiyoyi da koguna da ƙoramu a ranar alƙiyama dukansu suna cikin damƙarsa ne, sammai bakwai kuwa gaba ɗayansu suna nannaɗe ne a hannun damansa. Ya kuma ɗaukaka daga duk abin da mushirikai suke tara shi da su. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani malamin Yahudawa ya zo wurin Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya Muhammadu, mu mun samu (a littattafanmu) cewa Allah zai sanya sammai a kan ɗan yatsansa, ya sanya ƙassai a kan ɗan yatsa, ya sanya bishiyoyi a kan ɗan yatsa, ya sanya ruwa da turɓaya a kan ɗan yatsa, ya sanya sauran halittu a kan ɗan yatsa, sai ya ce: ‘Ni ne mai mulki.’ Sai Manzon Allah (ﷺ) ya fashe da dariya har sai da fiƙoƙinsa suka fito don gaskata maganar Bayahuden malamin nan, sannan ya karanta wannan ayar.” [Bukhari #4811 da Muslim #2786]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Allah zai damƙi ƙasa, ya naɗe sama da hannunsa na dama, sannan ya ce: ‘Ni ne Sarki, ina sarakunan duniya suke?’” [Bukhari #4812].
وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَصَعِقَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُۖ ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ أُخۡرَىٰ فَإِذَا هُمۡ قِيَامٞ يَنظُرُونَ
Open ayah 39:68Aka kuma busa ƙaho, sai duk abin da yake cikin sammai da ƙasa ya halaka sai wanda Allah Ya ga dama; sannan aka sake yin wata busar, sai ga su a tsaye suna jiran tsammani.
وَأَشۡرَقَتِ ٱلۡأَرۡضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ وَجِاْيٓءَ بِٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 39:69Ƙasa kuma ta yi haske da hasken Ubangijinta, aka kuma ajiye takardu (na ayyuka), kuma aka zo da annabawa da masu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakaninsu da gaskiya, ba kuma za a zalunce su ba.
وَوُفِّيَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَا يَفۡعَلُونَ
Open ayah 39:70Aka kuma yi wa kowane rai cikakken sakamakon abin da ya aikata, Shi ko (Allah) Yana sane da abin da suke aikatawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ranar da mala’ika mai riƙe da ƙaho zai busa ƙaho, a lokacin duk halittun da suke cikin sammai da na ƙasa za su mutu, sannan ya sake yin wata busar ta biyu sai ga su tsaitsaye suna sauraron yadda Allah zai yi da su. Sannan idan Ubangiji (Mai tsarki da daukaka) ya zo domin yi wa bayi hisabi, sai ƙasa ta yi haske da haskensa, sai kuma a baje takardun ayyukan mutane, sai a zo da annabawa, a kuma zo da al’ummar Annabi Muhammadu (ﷺ) don su ba da shaida game da cewa annabawa duka sun isar wa al’ummunsu saƙon Allah. Sai Allah ya yi musu hukunci na adalci gaba ɗayansu, babu wanda za a zalunta a ranar, ba za a ƙara masa laifin da bai aikata ba, ba kuma za a rage masa ladansa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kowane rai za a ba shi sakamakon aikinsa cikakke, na alheri ne ko na sharri, domin kuma Allah shi ne masanin abin da suke aikatawa mai kyau ko mummuna.
وَسِيقَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ زُمَرًاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوهَا فُتِحَتۡ أَبۡوَٰبُهَا وَقَالَ لَهُمۡ خَزَنَتُهَآ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَتۡلُونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِ رَبِّكُمۡ وَيُنذِرُونَكُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَاۚ قَالُواْ بَلَىٰ وَلَٰكِنۡ حَقَّتۡ كَلِمَةُ ٱلۡعَذَابِ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 39:71Aka kuma ingiza ƙeyar waɗanda suka kafirta zuwa (wutar) Jahannama ƙungiya-ƙungiya; har yayin da suka zo wurinta sai aka buɗe ƙofofinta, masu tsaronta suka ce (da su): “Yanzu manzanni daga cikinku ba su zo muku ba ne suna karanta muku ayoyin Ubangijinku, suna kuma gargaɗin ku game haɗuwa da wannan ranar taku?” Sai suka ce: “Haka ne, (sun zo mana),” sai dai kuma kalmar azaba ta tabbata a kan kafirai.”
قِيلَ ٱدۡخُلُوٓاْ أَبۡوَٰبَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ فَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلۡمُتَكَبِّرِينَ
Open ayah 39:72Aka ce: “Ku shiga ƙofofin Jahannama, kuna masu dawwama a cikinta;” to makomar masu girman kai ta munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon kafirai bayan an gama yi musu hisabi, inda mala’iku za su gargaɗa su zuwa Jahannama a wulaƙance ƙungiya-ƙungiya, har sai sun iso ƙofar Jahannama sai mala’iku masu tsaron ta su buɗe musu ƙofofinta, su ingiza su suna daka musu tsawa tare da tambayar su cewa, wai shin manzanni daga cikinsu ba su je musu ba ne suna karanta musu ayoyin Ubangijinsu, suna kuma tsoratar da su zuwan wannan ranar ta alƙiyama da abin da yake cikinta na azaba mai tsanani? Sai kafirai su yi iƙirari su tabbatar musu da cewa, duk waɗannan abubuwa sun faru, sai dai kuma kalmar azaba ta tabbata a kan kafirai, don haka su ma sun yarda da cewa sun kasance kafirai. Sai a ƙara yi musu wani wulaƙanci a kan wanda suke ciki inda za a ɗebe musu tsammanin samun rahamar Allah, ko fita daga wuta, a ce da su su shiga ƙofofin Jahannama suna masu dawwama a cikinta har abada, to makomar masu girman kai kuwa ta munana.
وَسِيقَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ إِلَى ٱلۡجَنَّةِ زُمَرًاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوهَا وَفُتِحَتۡ أَبۡوَٰبُهَا وَقَالَ لَهُمۡ خَزَنَتُهَا سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡ طِبۡتُمۡ فَٱدۡخُلُوهَا خَٰلِدِينَ
Open ayah 39:73Aka kuma raka waɗanda suka kiyaye dokokin Ubangijinsu zuwa Aljanna ƙungiya-ƙungiya; har yayin da suka zo wurinta, alhali an bubbuɗe ƙofofinta, kuma masu tsaronta suka ce (da su): “Aminci ya tabbata a gare ku, kun kyautata (ayyukanku), sai ku shige ta kuna masu dawwama.”
وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي صَدَقَنَا وَعۡدَهُۥ وَأَوۡرَثَنَا ٱلۡأَرۡضَ نَتَبَوَّأُ مِنَ ٱلۡجَنَّةِ حَيۡثُ نَشَآءُۖ فَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ
Open ayah 39:74Suka ce: “Mun gode wa Allah Wanda Ya tabbatar mana da alƙawarinsa, Ya kuma gadar mana da ƙasa muna sauka a Aljanna a duk inda muka ga dama; to madalla da sakamakon masu aiki!”
وَتَرَى ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ حَآفِّينَ مِنۡ حَوۡلِ ٱلۡعَرۡشِ يُسَبِّحُونَ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡۚ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡحَقِّۚ وَقِيلَ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 39:75Kuma za ka ga mala’iku suna kewaye da Al’arshi, suna tasbihi da yabon Ubangijnsu; aka kuma yi hukunci a tsakaninsu (halittu) da gaskiya, aka kuma ce: “Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai.” A ayoyin ƙarshe na wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon waɗanda suka yi imani suka kiyaye dokokinsa, da cewa, mala’iku za su raka su cikin nutsuwa da girmamawa zuwa gidan Aljanna ƙungiya-ƙungiya. Kafin ma su iso wurinta sun samu mala\'iku masu tsaron ta sun riga sun bubbuɗe ƙofofinta, sai su tarye su suna yi musu sallama, suna roƙa musu amincin Allah ya tabbata a gare su, suna kuma yaba musu da cewa zukatansu da ayyukansu sun yi kyau da nagarta, don haka su shiga gidan Aljanna suna masu dawwama a cikinta har abada. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan muminai sun gama shiga gidajensu na Aljanna sai su yi wa Allah godiya su yi masa kirari da cewa, ya cika musu alƙawarin da ya yi musu ta hanyar manzanninsa na cewa zai shigar da su Aljanna; to ga shi yanzu ya gadar musu da ita, duk inda suka ga damar sauka a cikinta to za su sauka babu mai hana su, don haka suna yi wa junansu sam-barka da sakamakon da Allah ya yi wa masu aiki irin nasu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a wannan rana mala’iku za su zagaye Al’arshi suna tsarkake Allah tare da gode masa da yi masa kirari. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi hukunci na adalci tsakanin halittunsa, ya karrama waɗanda suka cancanci karramawa, ya kuma azabtar da waɗanda suka cancanci azabarsa. A lokacin ne za a ce: Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai game da hukuncinsa na adalci ga kafirai da kuma falalarsa ga muminai.