غافر
Al-Ghaafir
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
حمٓ
Open ayah 40:1HA MIM.
تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ
Open ayah 40:2Saukarwar Littafi daga Allah ne Mabuwayi, Masani.
غَافِرِ ٱلذَّنۢبِ وَقَابِلِ ٱلتَّوۡبِ شَدِيدِ ٱلۡعِقَابِ ذِي ٱلطَّوۡلِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ إِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ
Open ayah 40:3Mai gafarta zunubi, Mai kuma karɓar tuba, Mai tsananin uƙuba, Mai ni’imatarwa; babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi; makoma zuwa gare Shi ne. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa, kamar yadda ya buɗe wasu surori da irinsu. [Dubi farkon tafsirinmu na \'Suratul Baƙara\' don ƙarin bayani a kansu]. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa shi Alƙur’ani saukakke ne daga Allah Mabuwayi wanda ya fi ƙarfin kowa da komai kuma masanin maslahohin bayinsa da abin da ya fi dacewa da su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta kansa da cewa shi ne mai gafarta zunuban bayinsa waɗanda suka tuba suka nemi afuwarsa, kuma mai tsananin uƙuba ga duk wanda ya ƙi tuba daga cikinsu; shi ne mai ni’imtawa kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai shi kaɗai. Makomar bayi gaba ɗayansu zuwa gare shi ne a ranar alƙiyama inda zai saka wa kowa da irin abin da ya aikata mai kyau ko mummuna.
مَا يُجَٰدِلُ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَا يَغۡرُرۡكَ تَقَلُّبُهُمۡ فِي ٱلۡبِلَٰدِ
Open ayah 40:4Babu mai yin jayayya game da ayoyin Allah sai waɗanda suka kafirta, saboda haka kada yawan zirga-zirgarsu a garuruwa ya ruɗe ka.
كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۖ وَهَمَّتۡ كُلُّ أُمَّةِۭ بِرَسُولِهِمۡ لِيَأۡخُذُوهُۖ وَجَٰدَلُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ لِيُدۡحِضُواْ بِهِ ٱلۡحَقَّ فَأَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ عِقَابِ
Open ayah 40:5Mutanen Nuhu sun ƙaryata kafin su, da kuma ƙungiyoyi (na kafirai) bayansu; kowace al’umma kuma sun yi mummunan nufi da manzonsu don su kama shi (su cutar da shi); suka kuma yi jayayya da (hujja ta) ƙarya don su rusa gaskiya da ita, sai Na kama su; to yaya uƙubata ta kasance?
وَكَذَٰلِكَ حَقَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ
Open ayah 40:6Kamar haka ne kuma kalmar Ubangijinka (ta azaba) ta tabbata a kan waɗanda suka kafirta cewa, lalle su ‘yan wuta ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa masu jayayya da ayoyinsa masu nuna Kaɗaitakarsa da gaskiyar manzancin annabawansa su ne waɗanda suka kafirce masa, saboda gurɓacewar hankulansu, don haka kada Manzon Allah ya nuna damuwarsa a kansu, kada kuma zirga-zirgarsu ta kasuwanci gari da gari da arzikin da Allah ya ba su ya ruɗe shi, ko ya ɗaga masa hankali; wannan ba komai ba ne, talala ce kawai Allah yake yi musu, amma ƙarshensu ba zai yi kyau ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) game da ƙaryata shi da kafirai suke yi, da cewa ba shi ne farau ba game da haka, domin mutanen Annabi Nuhu gabaninsu sun ƙaryata Manzonsu Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kuma ƙungiyoyin kafirai da suka zo bayansa su ma sun ƙaryata annabawansu, kamar Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanen Madyana da Fir’auna da jama’arsa, duk sun ƙaryata manzanninsu. Kowace al’umma daga cikinsu kuma sun yi yunƙurin su kama manzonsu su kashe shi, amma Allah bai ba su sa’a ba. Kuma sun yi jayayya da hujja ta ƙarya don su rushe gaskiya da ita; to amma daga ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya damƙi waɗannan al’ummu gaba ɗayansu ya kuma hallaka su. Sai Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya duba ya ga yadda uƙubarsa gare su ta kasance. Babu shakka azaba ce mai tsananin gaske. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Manzonsa (ﷺ) cewa, to kamar yadda ya hukunta waɗannan al’ummu da suka ƙaryata gaskiya suka ja da manzanninsa, haka kalmarsa ta azaba ta tabbata ga kafirai cewa, su ‘yan wuta ne ba makawa.
ٱلَّذِينَ يَحۡمِلُونَ ٱلۡعَرۡشَ وَمَنۡ حَوۡلَهُۥ يُسَبِّحُونَ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَيُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَيَسۡتَغۡفِرُونَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْۖ رَبَّنَا وَسِعۡتَ كُلَّ شَيۡءٖ رَّحۡمَةٗ وَعِلۡمٗا فَٱغۡفِرۡ لِلَّذِينَ تَابُواْ وَٱتَّبَعُواْ سَبِيلَكَ وَقِهِمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 40:7Waɗanda suke ɗauke da Al’arshi da waɗanda suke kewaye da shi suna yin tasbihi da yabon Ubangijinsu, suna kuma yin imani da Shi, kuma suna nema wa waɗanda suka yi imani gafara, (suna cewa): “Ya Ubangiijnmu, ka yalwaci kowane abu da rahama da ilimi, to Ka gafarta wa waɗanda suka tuba suka kuma bi hanyarka, Ka kuma kiyaye su daga azabar (wutar) Jahimu.
رَبَّنَا وَأَدۡخِلۡهُمۡ جَنَّٰتِ عَدۡنٍ ٱلَّتِي وَعَدتَّهُمۡ وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّٰتِهِمۡۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 40:8“ <b>Ya Ubangijinmu, Ka kuma shigar da su gidajen Aljannar zama waɗanda ka alƙawarta musu, tare da waɗanda suke salihai daga iyayensu da matayensu da kuma zuriyarsu. Lalle Kai Mabuwayi ne, Mai hikima.
وَقِهِمُ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ وَمَن تَقِ ٱلسَّيِّـَٔاتِ يَوۡمَئِذٖ فَقَدۡ رَحِمۡتَهُۥۚ وَذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 40:9“Ka kuma kiyaye su munanan (ayyuka). Duk kuwa wanda Ka kiyaye shi daga munanan (sakamako) a wannan rana, haƙiƙa Ka yi masa rahama. Wannan kuwa shi ne babban rabo.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna yadda mala’aikunsa suke ƙaunar muminai suke yi musu addu’o\'i na ƙwarai a ko da yaushe da cewa mala’ikun da suke ɗauke da Al’arshinsa da waɗanda suke kewaye da shi suna tsarkake shi daga duk wani abu da bai dace da shi ba tare da yabon sa, suna kuma yin imani da shi, suna kuma roƙa wa waɗanda suka yi imani da Allah gafara, suna tawassuli da yabon Allah (Mai tsarki da daukaka) wanda rahamarsa da iliminsa sun yalwaci komai, domin ya gafarta wa muminai da suka tuba suka bi hanyarsa ta gaskiya, a kan ya tsare su daga azabar wuta. Suna kuma roƙon sa da ya shigar da muminai gidajen Aljanna na zama har abada waɗanda ya yi musu alƙawari zai shigar da su, ya shigar da su tare da dukkan iyayensu da matansu da ‘ya’yansu waɗanda ayyukansu suka yi kyau. Saboda shi ne Mabuwayi wanda babu mai rinjayar sa, mai hikima cikin duk abin da ya halitta ko ya ƙaddara ya tsara. Mala’iku suka ci gaba da roƙa wa muminai Allah kan ya tsare su daga aikata munanan ayyuka da zai azabta su da su, domin duk wanda ya kuɓutar a ranar alƙiyama daga uƙubar munanan ayyukansa, to lalle ya yi masa rahama, wannan kuwa shi ne babban rabo.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُنَادَوۡنَ لَمَقۡتُ ٱللَّهِ أَكۡبَرُ مِن مَّقۡتِكُمۡ أَنفُسَكُمۡ إِذۡ تُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلۡإِيمَٰنِ فَتَكۡفُرُونَ
Open ayah 40:10Lalle waɗanda suka kafirta ana kiran su cewa: “Tabbas fushin Allah da ku ya fi girman fushinku ga kawunanku, lokacin da ake kiran ku zuwa imani (a duniya) sai kuke kafircewa.”
قَالُواْ رَبَّنَآ أَمَتَّنَا ٱثۡنَتَيۡنِ وَأَحۡيَيۡتَنَا ٱثۡنَتَيۡنِ فَٱعۡتَرَفۡنَا بِذُنُوبِنَا فَهَلۡ إِلَىٰ خُرُوجٖ مِّن سَبِيلٖ
Open ayah 40:11Suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka kashe mu sau biyu Ka kuma raya mu sau biyu, to mun amsa laifukanmu, shin ko akwai wata hanya ta fita (daga wuta)?”
ذَٰلِكُم بِأَنَّهُۥٓ إِذَا دُعِيَ ٱللَّهُ وَحۡدَهُۥ كَفَرۡتُمۡ وَإِن يُشۡرَكۡ بِهِۦ تُؤۡمِنُواْۚ فَٱلۡحُكۡمُ لِلَّهِ ٱلۡعَلِيِّ ٱلۡكَبِيرِ
Open ayah 40:12Wannan (sakamakon) saboda cewa, idan aka kira Allah Shi kaɗai sai ku kafirce, idan kuwa aka yi shirka da Shi, sai ku yi imani. To hukuncin na Allah ne Maɗaukaki, Mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa kafirai cewa a ranar alƙiyama za a kira su domin a shigar da su wutar Jahannama suna faman zargin kawunansu da jin haushin kansu; a lokacin za a faɗa musu cewa, tsananin fushin da Allah yake yi da su ya fi wanda suke yi wa kansu, yayin da a duniya ake kiran su su yi imani da Allah sai suka kafirce masa suka riƙa bauta wa wasu gumaka ba shi ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa furucin da zai riƙa fita daga bakunansu a lokacin shi ne za su riƙa cewa, ya kashe su sau biyu, watau a da babu su sai ya samar da su, sannan ya kashe su lokacin cikar ajalinsu. Ya kuma raya su sau biyu, watau lokacin da ya samar da su bayan a da babu su, sannan bayan mutuwarsu ya sake tashin su domin yi musu hisabi, suka kuma fito fili suka amsa laifukan da suka aikata a rayuwarsu ta duniya. To amma yanzu suna tambaya ne wai ko akwai wata hanya ta komawa duniya don su gyara ayyukansu su nemi yardar Allah? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa abin da ya jawo musu shiga wannan hali na takaici da mummunar azaba shi ne, tun a duniya idan an kira Allah shi kaɗai ba a haɗa shi da komai ba sai su kafirce masa su sanya masa kishiyoyi, amma idan an bauta wa wani tare da Allah sai su yi imani. Allah ya tabbatar musu da cewa hukunci nasa ne shi kaɗai, domin shi ne Maɗaukaki da Zatinsa da siffarsa da ikonsa, kuma mai girma wanda kowa da komai a ƙarƙashin ikonsa yake.
هُوَ ٱلَّذِي يُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُنَزِّلُ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ رِزۡقٗاۚ وَمَا يَتَذَكَّرُ إِلَّا مَن يُنِيبُ
Open ayah 40:13Shi ne wanda Yake nuna muku ayoyinsa, Yake kuma saukar muku da arziki daga sama (watau ruwan sama). Ba kuma kowa ne yake wa’azantuwa ba sai mai komawa (ga Allah).
فَٱدۡعُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 40:14Sai ku bauta wa Allah kuna masu tsantsanta addini gare Shi, ko da kuwa kafirai ba sa so.
رَفِيعُ ٱلدَّرَجَٰتِ ذُو ٱلۡعَرۡشِ يُلۡقِي ٱلرُّوحَ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ لِيُنذِرَ يَوۡمَ ٱلتَّلَاقِ
Open ayah 40:15(Shi ne) Mai maɗaukakan darajoji, Ma’abocin Al’arshi, Yana sauko da wahayi daga umarninsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa don Ya yi gargaɗin ranar haɗuwa.
يَوۡمَ هُم بَٰرِزُونَۖ لَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنۡهُمۡ شَيۡءٞۚ لِّمَنِ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡيَوۡمَۖ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ
Open ayah 40:16Ranar da za su bayyana; babu wani abu nasu da zai ɓuya ga Allah. (Zai ce): “Mulki na wane ne a yau?” (Sai Ya ce): “Na Allah Makaɗaici, Mai rinjaye ne.”
ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۚ لَا ظُلۡمَ ٱلۡيَوۡمَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
Open ayah 40:17A wannan ranar za a saka wa kowane rai da irin abin da ya aikata. Babu zalunci a wannan ranar. Lalle Allah Mai gaggawar yin hisabi ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, shi ne yake nuna wa mutane dalilan Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa a cikin sasannin sama da kuma a kawunansu, dalilai masu nuna cancantar a bauta masa shi kaɗai kada a yi shirka da shi. Shi ne kuma wanda yake saukar musu da ruwa daga sama wanda a sanadiyyarsa suke samun arziki na tsirrai da shuke-shuke; to amma babu mai wa’azantuwa da irin waɗannan ayoyi nasa sai wanda yake komawa ga Allah, ya tuba ya tsantsanta bautarsa gare shi shi kaɗai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci muminai da su roƙe shi suna masu tsantsanta addu’arsu da ibadarsu gare shi shi kaɗai, kada su haɗa wani da shi ko da kuwa kafirai ba sa son haka. Abdullahi ɗan Zubairu (Allah ya kara masa yarda) ya kasance bayan kowace salla idan ya yi sallama yana cewa: “Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, yabo ma nasa ne, shi kuma mai iko ne a kan komai. Babu wata dabara babu wani ƙarfi sai tare da Allah. Babu abin bauta da gaskiya sai shi, ba za mu bauta wa kowa ba sai shi kaɗai. Ni’ima da falala nasa ne, kuma yana da kyakkyawan yabo. Babu abin bauta da gaskiya sai shi, muna masu tsantsanta addini gare shi ko da kafirai ba sa so.” Ya ce: “Annabi (ﷺ) ya kasance yana ɗaga muryarsa da faɗar waɗannan kalmomi bayan kowace salla.” [Muslim #594]. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta kansa da wasu siffofi guda uku: <b>Siffa ta ɗaya </b>, shi ne mai maɗaukakan darajoji, watau yana sama da kowa, kowa da komai ƙasa suke da shi. <b>Ta biyu </b>, ma’abocin Al’arshi, mai girma wanda yake a ƙololuwar sama. <b>Ta uku </b>, yana saukar da wahayinsa ga wanda ya ga dama daga bayinsa, domin su rayu, kuma su raya wasunsu da shi, su kuma tsoratar da mutane da zuwan ranar alƙiyama wadda a cikinta ne za a haɗa halittun farko da na ƙarshe wuri guda domin yi musu hisabi da sakamako. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta wannan rana da cewa, ita ce ranar da duk halittu za su bayyana su tattaru a farfajiyar ƙasa ɗaya, babu wani abu da zai ɓoye wa Allah, su kansu ko ayyukansu. Zai yi tambaya a wannan ranar da cewa mulki na wane ne? A lokacin amsa ɗaya ce tak, mulki na Allah ne, Makaɗaici a Zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, mai rinjaye wanda ya fi ƙarfin kowa, kuma kowa da komai sun rusuna masa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta kansa da cikakken adalci, da cewa, a ranar za a cika wa kowane rai sakamakon aikinsa mai kyau ko mummuna, don kuwa a ranar ba za a zaluntar kowa, domin mai hukunci a ranar shi ne Allah mai cikakken adalci. Allah kuma tabbas mai gaggawar yi wa bayinsa hisabi ne domin saninsa ya kewaye komai. An karɓo daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ce: ‘Ya ku bayina, lalle ni na haramta wa kaina zalunci, na kuma sanya shi haramun a tsakaninku, don haka kada ku zalunci junanku…’ har zuwa inda Allah ya ce: ‘Ya ku bayina, ayyukanku ne kawai nake ƙididdige muku su, sannan in cika muku sakamakonsu. To wanda ya sami alheri sai ya gode wa Allah, wanda kuwa ya sami saɓanin haka, to kada ya zargi kowa sai kansa.’” [Muslim #2577]
وَأَنذِرۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡأٓزِفَةِ إِذِ ٱلۡقُلُوبُ لَدَى ٱلۡحَنَاجِرِ كَٰظِمِينَۚ مَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ حَمِيمٖ وَلَا شَفِيعٖ يُطَاعُ
Open ayah 40:18Ka kuma tsoratar da su ranar (alƙiyama) mai kusantowa, a yayin da zukata suke maƙare a wuyoyinsu (saboda tsananin tsoro). Azzalumai ba su da wani masoyi ko kuma wani mai ceto da za a yi wa biyya.
يَعۡلَمُ خَآئِنَةَ ٱلۡأَعۡيُنِ وَمَا تُخۡفِي ٱلصُّدُورُ
Open ayah 40:19(Allah) Yana sane da ha’incin idanuwa da kuma abin da zukata suke ɓoyewa.
وَٱللَّهُ يَقۡضِي بِٱلۡحَقِّۖ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَقۡضُونَ بِشَيۡءٍۗ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ
Open ayah 40:20Allah Yana hukunci da gaskiya; waɗanda kuwa suke bauta wa wanda ba Shi ba, ba sa hukunta komai. Haƙiƙa Allah Shi ne Mai ji, Mai gani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya gargaɗi kafirai ya tsoratar da su zuwan ranar alƙiyama wadda take tafe ba da daɗewa ba. Ya sanar da su cewa ita rana ce da take cike da abubuwan ban tsoro da firgici; domin saboda tsananin firgicin da ke cikinta zukata za su yunƙuro su yiwo sama har zuwa ga maƙoshi, watau kamar za su fito don tsananin razana, duk mutane kuma za su yi tsit babu wani mai iya cewa uffan sai wanda Allah ya yi masa izini. Azzalumai kuma waɗanda suka mutu suna shirka da saɓon Allah ba su da wani aboki ko makusanci ko wani mai ceto da za a yarda da shi a amince da cetonsa gare su. Allah kuma yana sane da duk wani ha’inci na idanu masu satar kallon abin da ya haramta su kalla, yana kuma sane da duk abin da zukata suke ɓoyewa, babu wani abu da zai ɓuya gare shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shi ne yake hukunci na gaskiya da adalci, babu wanda zai zalunta ya rage masa ladan kyawawan ayyukansa, ko ya kama shi da laifin da bai aikata ba. To amma abubuwan da mushirikai suke bauta wa ba Allah ba, ba sa iya hukunta komai, domin ba su mallaki komai ba, kuma ba za su iya taɓuka komai ba, shi kuwa Allah mai jin maganganun bayinsa ne, kuma mai ganin duk ayyukansu da niyyoyinsu ne, zai kuma yi musu sakayya a kai.
۞أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُواْ هُمۡ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡ وَمَا كَانَ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ
Open ayah 40:21Shin ba sa tafiya a bayan ƙasa sannan su ga yaya ƙarshen waɗanda suka kasance gabaninsu ya zama? Su sun kasance sun fi su tsananin ƙarfi da barin gurabe na tarihi a bayan ƙasa, sai Allah Ya kama su da laifukansu, ba su kuma da wani mai kare su daga Allah.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانَت تَّأۡتِيهِمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَكَفَرُواْ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ قَوِيّٞ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Open ayah 40:22Wannan (ya same su ne) saboda manzanninsu sun kasance suna zuwa musu da hujjoji bayyanannu, sai suka kafirce, sai Allah Ya kama su. Lalle Shi Mai (tsananin) ƙarfi ne, Mai tsananin azaba. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da kafirai azabar lahira, sai kuma ya tsoratar da su azabar duniya da cewa, shin ba su yawata a bayan ƙasa ba ne domin su gane wa idanuwansu irin yadda ƙarshen al\'ummun da suka gabace su waɗanda suka ƙaryata annabawansu ya kasance? Domin kuwa sun yi mummunan ƙarshe duk da cewa sun zarce waɗannan mushirikan da tsananin ƙarfi, sun kuma bar alamu na gine-gine da gonaki a bayan ƙasa fiye da yadda waɗannan mushirikai suka yi, to amma duk da haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su saboda zunubansu, kuma ba su da wani wanda zai kare su daga azabar Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa azabarsa ta saukar wa al’ummun da suka gabata ne, saboda manzanninsa sun yi ta zuwa musu da ƙarfafan hujjoji bayyanannu, amma sai suka kafirce, suka ƙaryata manzanninsu, sai Allah ya damƙe su ya hallaka su duk kuwa da irin ƙarfin da suke taƙama suna da shi, domin Allah mai tsananin ƙarfi ne Buwayi, kuma mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya kafirce masa ya kuma ƙaryata manzanninsa.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ
Open ayah 40:23Haƙiƙa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu da kuma hujja mabayyaniya.
إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَقَٰرُونَ فَقَالُواْ سَٰحِرٞ كَذَّابٞ
Open ayah 40:24Zuwa ga Fir’auna da Hamana da Ƙaruna, sai suka ce shi mai sihiri ne, babban maƙaryaci.
فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡحَقِّ مِنۡ عِندِنَا قَالُواْ ٱقۡتُلُوٓاْ أَبۡنَآءَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ وَٱسۡتَحۡيُواْ نِسَآءَهُمۡۚ وَمَا كَيۡدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ
Open ayah 40:25To lokacin da ya zo musu da gaskiya daga wajenmu sai suka ce: “Ku kashe `ya`yan waɗanda suka yi imani tare da shi, ku kuma ƙyale matansu da rai.” Makircin kafirai bai zama ba sai a lalace.
وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ذَرُونِيٓ أَقۡتُلۡ مُوسَىٰ وَلۡيَدۡعُ رَبَّهُۥٓۖ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُبَدِّلَ دِينَكُمۡ أَوۡ أَن يُظۡهِرَ فِي ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡفَسَادَ
Open ayah 40:26Fir’auna kuma ya ce: “Ku bar ni in kashe Musa, kuma (ya je) ya kirawo Ubangijin nasa; lalle ni ina jin tsoron kada ya sauya addininku ko kuma ya bayyanar da ɓarna a bayan ƙasa.”
وَقَالَ مُوسَىٰٓ إِنِّي عُذۡتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُم مِّن كُلِّ مُتَكَبِّرٖ لَّا يُؤۡمِنُ بِيَوۡمِ ٱلۡحِسَابِ
Open ayah 40:27Musa ya ce: “Lalle ni ina neman tsari da Ubangijina, da kuma Ubangijinku daga duk wani mai girman kai da ba ya yin imani da ranar hisabi.” A nan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Manzonsa labarin wasu al’ummun da suka ƙaryata annabawansu ne ya kuma saukar musu da azabarsa, don ya zama gargaɗi ga mutanensa da cewa, ya aiko da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ayoyinsa bayyanannu da ƙarfafan hujjoji masu tabbatar da ingancin manzancinsa, ya kuma aike shi ne zuwa ga Fir’auna da Wazirinsa Hamana da kuma Ƙaruna. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana musu ƙwararan dalilai da suke tabbatar da manzancinsa da gaskiyar abin da ya zo musu da shi. Yayin da Fir’auna da jama’arsa suka kasa kawo wata hujja don su kare kansu sai kawai suka ce, ai Annabi Musa mai sihiri ne, kuma babban maƙaryaci, ba manzo ne daga Allah ba. Daga nan ne fa Fir’auna ya ba wa zabaniyawansa umarni cewa, su kashe dukkan ‘ya’ya maza na ƙabilar Banu Isra’ila waɗanda suka yi imani da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), su ƙyale ‘ya’yansu mata, domin su ci gaba da tozarta su da bautar da su a gidajensu ta hanyar saka su aikatau na wulaƙanci. Duk kuma suna yin haka ne domin su hana mutane karɓar gaskiya da kuma rage yawan Banu Isra’ila ƙabilar Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), amma ba su san cewa makircin da Fir’auna yake ƙullawa duk a banza zai ƙare ba, babu wani tasiri da zai yi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Fir’auna bai tsaya a kan kashe ‘ya’yan Banu Isra’ila kaɗai ba, har ma sai da ya shiga yi wa Annabi Musa barazanar zai kashe shi, yana nuna kamar wasu ne suke dakatar da shi, shi kuma yana barazanar cewa su ƙyale shi ya gama da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), wai kuma in ya isa to ya roƙi Ubangijinsa da ya ce shi ne ya aiko shi, ya zo ya kare shi ya hana wani abu ya same shi. Fir’auna ya bayyana wa mutanensa dalilin da ya sa yake son kashe Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa, wai shi yana jin tsoron kada ya sauya musu addininsu wanda ya same su suna a kai na bautar wanin Allah, ya shigar da su addininsa na bautar Allah ɗaya, ko kuma ya bayyanar da wata ɓarna a bayan ƙasa, watau ya kawo rikici da saɓani tsakanin mutane wanda zai haifar musu da yamutsi da kashe-kashe. To lokacin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sami labarin barazanar da Fir’auna yake yi masa, sai ya roƙi Allah Ubangijinsa kuma Ubangijin Fir’auna da jama’arsa da ya tsare shi daga makircin duk wani mai girman kai mai ƙin gaskiya wanda ya ƙi yin imani da ranar lahira irin Fir’auna da jama’arsa.
وَقَالَ رَجُلٞ مُّؤۡمِنٞ مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَكۡتُمُ إِيمَٰنَهُۥٓ أَتَقۡتُلُونَ رَجُلًا أَن يَقُولَ رَبِّيَ ٱللَّهُ وَقَدۡ جَآءَكُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ مِن رَّبِّكُمۡۖ وَإِن يَكُ كَٰذِبٗا فَعَلَيۡهِ كَذِبُهُۥۖ وَإِن يَكُ صَادِقٗا يُصِبۡكُم بَعۡضُ ٱلَّذِي يَعِدُكُمۡۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ مُسۡرِفٞ كَذَّابٞ
Open ayah 40:28Kuma wani mutum mumini daga dangin Fir’auna wanda yake ɓoye imaninsa ya ce: “Yanzu kwa kashe mutum don ya ce ‘Allah ne Ubangijina’, kuma alhalin ya zo muku da hujjoji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan ya zama maƙaryaci ne to laifin ƙaryarsa yana kansa; idan kuwa ya zama mai gaskiya, to wani abu daga abin da yake yi muku gargaɗinsa zai same ku. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake shi mai yawan ɓarna ne, maƙaryaci.
يَٰقَوۡمِ لَكُمُ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡيَوۡمَ ظَٰهِرِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَمَن يَنصُرُنَا مِنۢ بَأۡسِ ٱللَّهِ إِن جَآءَنَاۚ قَالَ فِرۡعَوۡنُ مَآ أُرِيكُمۡ إِلَّا مَآ أَرَىٰ وَمَآ أَهۡدِيكُمۡ إِلَّا سَبِيلَ ٱلرَّشَادِ
Open ayah 40:29“Ya ku mutanena, a yau ku ne masu mulki masu ƙarfi a bayan ƙasa, to wane ne zai kare mu daga azabar Allah idan ta zo mana?” Fir’auna ya ce: “Ba abin da nake nuna muku sai abin da na gani (shi ne daidai), kuma hanyar shiriya kaɗai nake nuna muku.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin luɗufin da ya yi wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bayan ya roƙe shi ya kuɓutar da shi daga sharrin Fir’auna, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hore masa hanyoyin samun kuɓuta, daga cikinsu ya kimsa imani cikin zuciyar ɗaya daga cikin dangin Fir’auna wanda ya riƙa ɓoye imaninsa da Allah da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don tsoron kada Fir’auna ya hallaka shi, sai ya tashi ya nuna wa mutanensa rashin dacewar a kashe Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa, yanzu yaya za a kashe mutumin da bai yi wani laifi ba sai don kawai ya ce Allah ne Ubangijinsa, kuma ya zo musu da hujjoji da ƙarfafan dalilai waɗanda suke tabbatar da gaskiyar cewa shi Manzon Allah ne? Watau ya nuna musu cewa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai furta wata magana ba da har zai cancanci uƙubar ƙisa. Wannan mutum mumini kuma ya kawo musu wata hujja ta hankali wadda duk mai hankali zai gamsu da ita da cewa, da za a ce Annabi Musa maƙaryaci ne, to ai a kansa ƙaryar za ta ƙare, watau kansa kaɗai zai cutar ba zai cutar da kowa ba. Kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, to tabbas sai wata azaba da yake musu alƙawarin zuwanta ta auka musu ba da daɗewa ba idan ba su yi imani ba. Sannan ya tabbatar musu da cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya shiryar da mutumin da yake mai yawan ƙetare iyakokinsa, mai yi masa ƙarya ya yi wa manzanninsa. Mutumin nan ya sake kiran mutanensa Ƙibɗawa ya gargaɗe su da cewa, a yau su ne masu mulki da ƙarfi a ƙasar Masar, to amma su yi tunani su gane cewa wane ne zai taimake su ya kare su daga azabar Allah idan ta zo musu yayin da suka kashe Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi)? Watau yana nuna musu cewa shi ma ɗaya ne daga cikinsu, duk abin da ya same su to shi ma zai same shi. To bayan Fir’auna ya saurari nasihohin wannan mutum mumini, sai ya yi biris da duk abin da ya ji, ya kuma nuna wa mutanensa cewa shi mai matuƙar son su da alheri ne, kuma ba zai taɓa ɗora su a kan hanyar da ba daidai ba, don haka su yarda da cewa mafita kawai ita ce a bar shi ya kashe Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kowa ya huta, domin maganarsa ita kaɗai ce kan hanya wadda ya wajaba dukkansu su amince da ita.
وَقَالَ ٱلَّذِيٓ ءَامَنَ يَٰقَوۡمِ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُم مِّثۡلَ يَوۡمِ ٱلۡأَحۡزَابِ
Open ayah 40:30Sai kuma wannan da ya yi imani ya ce: “Ya ku mutanena, lalle ni ina jiye muku tsoron irin ranar gangamin ƙungiyoyin (kafirai).
مِثۡلَ دَأۡبِ قَوۡمِ نُوحٖ وَعَادٖ وَثَمُودَ وَٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۚ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلۡمٗا لِّلۡعِبَادِ
Open ayah 40:31“Kamar misalin al’adar mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa da kuma waɗanda suka zo bayansu. Allah kuwa ba Ya nufin zalunci ga bayi.
وَيَٰقَوۡمِ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ يَوۡمَ ٱلتَّنَادِ
Open ayah 40:32“Kuma ya ku mutanena, lalle ni ina jiye muku tsoron ranar kiraye-kirayen juna (ranar alƙiyama).
يَوۡمَ تُوَلُّونَ مُدۡبِرِينَ مَا لَكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنۡ عَاصِمٖۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ
Open ayah 40:33“ <b>Ranar da za ku juya kuna masu ba da baya, ba ku da wani mai kare ku daga Allah. Duk kuma wanda Allah Ya ɓatar to ba shi da wani mai shiryarwa.”
وَلَقَدۡ جَآءَكُمۡ يُوسُفُ مِن قَبۡلُ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا زِلۡتُمۡ فِي شَكّٖ مِّمَّا جَآءَكُم بِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَا هَلَكَ قُلۡتُمۡ لَن يَبۡعَثَ ٱللَّهُ مِنۢ بَعۡدِهِۦ رَسُولٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَنۡ هُوَ مُسۡرِفٞ مُّرۡتَابٌ
Open ayah 40:34Haƙiƙa kuma Yusufu ya zo muku da (hujjoji) bayyanannu tun kafin (zuwan Musa), to ba ku gushe kuna kokwanton abin da ya zo muku da shi ba, har yayin da ya mutu sai kuka ce: “Allah ba zai sake aiko da wani manzo bayansa ba.” Kamar haka ne Allah Yake ɓatar da duk wanda shi mai ɓarna ne, mai shakka.
ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ سُلۡطَٰنٍ أَتَىٰهُمۡۖ كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ وَعِندَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ قَلۡبِ مُتَكَبِّرٖ جَبَّارٖ
Open ayah 40:35Waɗanda suke yin jayayya game da ayoyin Allah ba tare da wata hujja da ta zo musu ba; ƙyamar (wannan) a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi imani ta girmama. Kamar haka ne Allah Yake toshe zuciyar duk wani mai girman kai, mai tsaurin rai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana nasihar muminin gidan Fir’auna ga mutanensa bayan ya ji ra’ayin Fir’auna da kafewarsa a kan mummunan ra’ayinsa, duk kuwa da irin hujjoji na hankali da ya kawo masa. Wannan bawan Allah ya ci gaba da yi musu nasiha yana nuna musu cewa idan suka kuskura suka kashe Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) to yana jiye musu tsoron irin azabar da ta auka wa al’ummun da suka ƙaryata manzanninsu a baya su ma ta same su, Allah ya hallaka su kamar yadda ya hallaka waɗancan, kamar yadda ya yi wa mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Samudawa mutanen Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka zo bayansu, duk sun kafirce wa Allah sun kuma ƙaryata manzanninsa sai Allah ya hallaka su baki ɗayansu domin kuwa sun cancanci haka. Allah kuma ba ya nufin zaluntar wani daga cikin bayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan bawan Allah ya sake kiran mutanensa ya ja hankalinsu game da ranar alƙiyama wadda yake jiye musu tsoronta, da cewa ita rana ce da mutane za su yi ta kiran junansu saboda dangantaka ta jini, ko saboda neman wata alfarma, suna tsammanin yin haka zai amfane su ya fitar da su daga tashin hankalin wannan ranar, amma ina sun makara. Ya kuma tabbatar musu cewa a ranar duk za su juya a guje domin tsere wa wutar Jahannama, amma babu wani wanda zai kare su daga azabar Allah. Ya kuma nuna musu cewa shiriya ta Allah ce, duk kuwa wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya taɓar da shi to ba shi da wanda zai iya shiryar da shi. Sannan ya tuna musu labarin Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Allah ya aiko shi zuwa kakanninsu da irin taurin kan da suka nuna masa, da cewa Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo musu da hujjoji bayyanannu masu nuna Kaɗaitakar Allah, to amma sun dage suna a kan shakkar gaskiyar abin da ya zo musu da shi, har ma sai bayan ya rasu shakkarsu game da gaskiyarsa ta daɗa ƙaruwa, suka ma fito fili suka ce wai bayansa Allah ba zai sake aiko wani manzo ba. Sai ya tabbatar musu cewa, da irin wannan ɓata nasu ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake ɓatar da duk wani mai ƙetare iyakokinsa mai shakka game da Kaɗaitakarsa. Sannan ya bayyana siffar masu irin wancan hali da cewa su ne waɗanda suke jayayya da ayoyin Allah don su rushe su ba tare da wata hujja ko wani dalili da ya zo musu ba. Ƙiyayyar jayayyarsu ta girmama a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi imani da shi da manzanninsa. Ya tabbatar musu cewa wannan ita ce sunnar Allah a kansu da ire-irensu, watau ya toshe zukatansu alheri ya kasa shiga cikinsu, kamar yadda yake toshe zuciyar duk wani mai girman kai mai fariya wanda ya ƙi gaskiya bayan ta bayyana gare shi da ƙarfafan hujjoji.
وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَٰهَٰمَٰنُ ٱبۡنِ لِي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَبۡلُغُ ٱلۡأَسۡبَٰبَ
Open ayah 40:36Fir’auna kuma ya ce: “Ya Hamana, ka gina min dogon gini ko na kai ga hanyoyi.
أَسۡبَٰبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ فَأَطَّلِعَ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ كَٰذِبٗاۚ وَكَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِفِرۡعَوۡنَ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَصُدَّ عَنِ ٱلسَّبِيلِۚ وَمَا كَيۡدُ فِرۡعَوۡنَ إِلَّا فِي تَبَابٖ
Open ayah 40:37“ <b>(Watau) hanyoyin (da ke kaiwa zuwa) sammai sai in gano Ubangijin Musa, lalle kuma ni ina tsammaninsa maƙaryaci ne.” Kamar haka kuma aka ƙawata wa Fir’auna mummunan aikinsa aka kuma kange shi daga hanyar (gaskiya). Makircin Fir’auna kuwa ba a komai yake ba sai cikin halaka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda taurin kan Fir’auna ya tsananta bayan ya ji wa’azin da muminin nan ya yi masa, har ta kai shi ga kiran Wazirinsa Hamana ya umarce shi da ya gina masa wani dogon gini wanda zai hau kansa ko zai sami hanyoyin da za su ɓulle da shi cikin sammai, wai don ya gano abin bautar Annabi Musa wanda ya faɗa masa cewa shi ne abin bauta na gaskiya. Sai kuma ya dawo yana cewa shi fa yana zaton Annabi Musa ƙarya yake faɗa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar haka ne aka ƙawata wa Fir’auna mummunan aikinsa, aka kuma kautar da shi daga bin hanyar gaskiya ya kama bin hanyar ɓata wanda hakan ya sanya shi irin wancan mugun tunani da mummunan tanadi don ya rusa gaskiya ya tabbatar da ƙarya, bai san cewa makircinsa ba a bakin komai yake ba sai asara da taɓewa, domin ƙarshensa shi ne taɓarɓarewa da lalacewa da tsiya ta har abada.
وَقَالَ ٱلَّذِيٓ ءَامَنَ يَٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُونِ أَهۡدِكُمۡ سَبِيلَ ٱلرَّشَادِ
Open ayah 40:38Sai (mutumin nan) wanda ya yi imani ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi ni in nuna muku hanyar shiriya.
يَٰقَوۡمِ إِنَّمَا هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا مَتَٰعٞ وَإِنَّ ٱلۡأٓخِرَةَ هِيَ دَارُ ٱلۡقَرَارِ
Open ayah 40:39“Ya ku mutanena, lalle wannan rayuwar ta duniya ɗan jin daɗi ne, kuma lalle lahira ita ce gidan tabbata.
مَنۡ عَمِلَ سَيِّئَةٗ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَاۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ يُرۡزَقُونَ فِيهَا بِغَيۡرِ حِسَابٖ
Open ayah 40:40“Wanda ya aikata wani mummunan aiki, to ba za a saka masa ba sai da kwatankwacinsa, wanda kuwa ya aikata wani kyakkyawan aiki, namiji ne ko mace alhali shi yana mumini, to waɗannan za su shiga Aljanna, a riƙa arzuta su a cikinta ba tare da lissafi ba.
۞وَيَٰقَوۡمِ مَا لِيٓ أَدۡعُوكُمۡ إِلَى ٱلنَّجَوٰةِ وَتَدۡعُونَنِيٓ إِلَى ٱلنَّارِ
Open ayah 40:41“Kuma ya ku mutanena, me ya sa ne nake kiranku zuwa ga tsira, ku kuma kuke kira na zuwa wuta?
تَدۡعُونَنِي لِأَكۡفُرَ بِٱللَّهِ وَأُشۡرِكَ بِهِۦ مَا لَيۡسَ لِي بِهِۦ عِلۡمٞ وَأَنَا۠ أَدۡعُوكُمۡ إِلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡغَفَّٰرِ
Open ayah 40:42“Kuna kira na da in kafirce wa Allah, in kuma tara Shi da abin da ba ni da wani sani a kansa, ni kuma ina kiran ku zuwa Mabuwayi, Mai yawan gafara?
لَا جَرَمَ أَنَّمَا تَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِ لَيۡسَ لَهُۥ دَعۡوَةٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَلَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَآ إِلَى ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ
Open ayah 40:43“Ba shakka abin da kuke kira na zuwa gare shi ba shi da wani kira karɓaɓɓe a duniya ko a lahira, kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah ne, maɓarnata kuma tabbas su ne ‘yan wuta.
فَسَتَذۡكُرُونَ مَآ أَقُولُ لَكُمۡۚ وَأُفَوِّضُ أَمۡرِيٓ إِلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ
Open ayah 40:44“To ba da daɗewa ba za ku tuna abin da nake gaya muku. Ina kuma miƙa al’amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai ganin bayi ne.”
فَوَقَىٰهُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِ مَا مَكَرُواْۖ وَحَاقَ بِـَٔالِ فِرۡعَوۡنَ سُوٓءُ ٱلۡعَذَابِ
Open ayah 40:45Sai Allah Ya kiyaye shi (sakamakon) mummunan abin da suka shirya; kuma mummunar azaba ta saukar wa mutanen Fir’auna.
ٱلنَّارُ يُعۡرَضُونَ عَلَيۡهَا غُدُوّٗا وَعَشِيّٗاۚ وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ أَدۡخِلُوٓاْ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ أَشَدَّ ٱلۡعَذَابِ
Open ayah 40:46(Ita ce) wuta da za a riƙa bijirar da su a gare ta safe da yamma; Ranar tashin alƙiyama kuma za a ce: “Ku shigar da mutanen Fir’auna mafi tsananin azaba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da faɗa mana wa’azin muminin gidan Fir’auna yayin da ya ga taurin kan Fir’auna da jama’arsa yana ta ƙaruwa, sai ya sake kiran mutanensa cewa su yarda su bi shi, zai nuna musu hanyar shiriya, watau yana nufin su yi watsi da ƙaryar da Fir’auna yake faɗa musu cewa, ba ya nuna musu komai sai hanyar shiriya. Ya ja hankalinsu game da biye wa ƙyale-ƙyalen rayuwar duniya, da cewa ita rayuwa ce ta jin daɗi kaɗan mai yankewa, don haka kada su kuskura su bari ta ruɗe su; su gane cewa lalle gidan lahira da ni’imomin da ke cikinta su ne tabbas waɗanda ba za su gushe ba har abada. Don haka su tashi tsaye su yi aiki domin samun rayuwar lahira mai ɗorewa su guji ruɗin duniya. Sai ya faɗakar da su game da adalcin Allah da girman rahamarsa da kuma falalarsa ga mutane da cewa, duk wanda ya yi mummunan aiki, to sakamakonsa daidai da gwargwadon laifinsa ne, amma wanda ya yi kyakkyawan aiki don Allah, namiji ne shi ko mace, alhali kuma ya yi imani da Allah da manzanninsa, to masu irin waɗannan siffofi su ne za su shiga Aljanna ranar alƙiyama inda za a riƙa arzuta su da abubuwan da ke cikinta na kayan marmari su yi ta more rayuwa ta jin daɗi marar yankewa ba tare da lissafi ba. Sannan ya fito fili ya bayyana wa mutanensa imaninsa da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya ci gaba da kiran su tare da nuna mamakinsa game da yadda shi yake ta kiran su zuwa ga hanyar tsira daga asarar duniya da ta lahira ta hanyar yin imani da Allah da aiki nagari, amma su kuma suna kiran sa zuwa ga shiga wuta ta ƙoƙarin tunkuɗa shi cikin kafirci da shirka da Allah da saɓon sa. Ya ci gaba da jaddada maganar da yake faɗa musu da cewa, tabbas abin da suke kiran sa da ya yi imani da shi ba shi da wani burbushin gaskiya a duniya ko a lahira, kuma shi ba zai taɓa amsa kiran duk wanda ya kira shi ba, sannan makomarsu gaba ɗaya zuwa ga Allah take shi kaɗai; maɓarnata a ranar kuma su ne ‘yan wuta waɗanda za su dawwama a cikinta har abada. Sannan ya rufe nasiharsa da tsoratar da su mummunan ƙarshensu idan har sun bijire wa abin da yake faɗa musu da cewa, akwai ranar da za ta zo su tuna irin nasihar da yake yi musu, su yi nadamar rashin karɓar nasiharsa a lokacin da nadamar ba za ta yi musu amfani ba. Ya bayyana musu cewa shi dai ya mayar da dukkan al’amuransa ga Allah shi kaɗai, domin Allah yana ganin komai na ayyukan bayinsa, ya kuma san halin da yake ciki na rauni da rashin mataimaki mai kare shi idan sun yi niyyar cutar da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya tsare wannan mumini daga mummunan makircin da suka shirya na kashe shi; shi kuma Fir’auna da mutanensa mummunar azaba ta auka musu yayin da aka nutsar da su cikin ruwa suka hallaka baki ɗayansu. Sannan kuma bayan wannan azabar a ranar alƙiyama za a ci gaba da bijirar da su a kan wuta safe da yamma, kuma a ba da umarnin shigar da su matsananciyar azaba saboda kafircinsu da saɓon Allah da suka dinga yi a nan duniya. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Idan ɗayanku ya mutu za a riƙa nuna masa mazauninsa safe da yamma, idan shi ɗan Aljanna ne, to daga mazauninsa na ‘yan Aljanna, idan kuma shi ɗan wuta ne, to daga masaukinsa na ‘yan wuta, sai a ce masa: ‘Wannan shi ne masaukinka har Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tashe ka zuwa gare shi ranar alƙiyama.’ [Bukhari #1379 da Muslim #2866].
وَإِذۡ يَتَحَآجُّونَ فِي ٱلنَّارِ فَيَقُولُ ٱلضُّعَفَٰٓؤُاْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُنَّا لَكُمۡ تَبَعٗا فَهَلۡ أَنتُم مُّغۡنُونَ عَنَّا نَصِيبٗا مِّنَ ٱلنَّارِ
Open ayah 40:47(Ka tuna) kuma lokacin da suke ta yin jayayya a cikin wuta, sai raunanan su riƙa ce wa waɗanda suka yi girman kai: “Lalle mun kasance mabiyanku (a duniya), to shin za ku iya ɗauke mana wani kaso na (azabar) wuta?”
قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُلّٞ فِيهَآ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ حَكَمَ بَيۡنَ ٱلۡعِبَادِ
Open ayah 40:48Waɗanda suka yi girman kai sai su ce: “Lalle mu duka a cikinta muke, lalle Allah Ya riga Ya yi hukunci tsakanin bayi.”
وَقَالَ ٱلَّذِينَ فِي ٱلنَّارِ لِخَزَنَةِ جَهَنَّمَ ٱدۡعُواْ رَبَّكُمۡ يُخَفِّفۡ عَنَّا يَوۡمٗا مِّنَ ٱلۡعَذَابِ
Open ayah 40:49Kuma waɗanda suke cikin wuta suka ce da masu tsaron Jahannama: “Ku roƙa mana Ubangijinku mana Ya sauƙaƙe mana azaba ta wuni (ɗaya).”
قَالُوٓاْ أَوَلَمۡ تَكُ تَأۡتِيكُمۡ رُسُلُكُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ قَالُواْ بَلَىٰۚ قَالُواْ فَٱدۡعُواْۗ وَمَا دُعَٰٓؤُاْ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٍ
Open ayah 40:50Suka ce: “Yanzu manzanninku ba su kasance suna zo muku da (ayoyi) bayyanannu ba?” Suka ce: “Haka ne (sun zo)”. Sai su ce: “To sai ku yi ta roƙon. Roƙon kafirai kuwa bai zamo ba sai a taɓe.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzo (ﷺ) da ya tuna lokacin da ‘yan wuta za su kaure da jayayya tsakanin shugabanni da mabiyansu, inda raunanan mabiyan za su riƙa yi wa manyansu ƙorafi cewa su fa mabiyansu ne a duniya, domin su ne suka ingiza su cikin ɓata, to shin yanzu za su iya ɗauke musu wani kaso na azabar Allah da suke ciki? Sai su kuma manyan masu girman kani su amsa musu da cewa, ai a wannan rana babu wani shugaba ko wani mabiyi, dukkansu suna cikin wutar ne, don haka zancen wani ya ɗauke wa wani azaba bai taso ba, domin kuwa Allah ne kaɗai mai yin hukunci a ranar, to ya riga ya yi hukunci tsakanin bayinsa, ya ba wa kowa kasonsa na azaba da ya cancance shi. Bayan su duka sun gane babu mai iya taimakon wani daga cikinsu, sai suka koma suna roƙon mala’iku masu tsaron wutar Jahannama don su roƙa musu Allah da ya sassauta musu tsananin azabar da suke ciki ko da na yini guda ne kacal ko za su samu su sarara. Nan take sai mala’iku su mayar musu da martani cewa, ashe manzanninsu ba su zo musu da hujjoji da dalilai bayyanannu ba? Sai kafirai su amsa da cewa, lalle kam an yi haka, watau dai son zuciya ne da taurin kai kawai ya hana su yin imani. Sai mala’ikun su amsa musu cikin gatsali da tsokana cewa, ai sai su dage su yi ta addu’a suna roƙon Allah ko sa sami biyan buƙata, amma ai addu’ar kafirai bayan sun shiga wuta a banza take ba ta da wani amfani gare su, don sun riga sun zo lahira suna shirka ba su tuba ba.
إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡأَشۡهَٰدُ
Open ayah 40:51Lalle Mu tabbas Muna taimakon manzanninmu da kuma waɗanda suka yi imani a rayuwar duniya da kuma ranar da shedu za su tsaya.
يَوۡمَ لَا يَنفَعُ ٱلظَّٰلِمِينَ مَعۡذِرَتُهُمۡۖ وَلَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ
Open ayah 40:52Ranar da hanzarin azzulamai ba zai amfane su ba; la’ana kuma ta tabbata a kansu, suna kuma da mummunan gida.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡهُدَىٰ وَأَوۡرَثۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ
Open ayah 40:53Kuma haƙiƙa Mun bai wa Musa shiriya, Muka kuwa gadar wa Banu-Isra’ila littafin (Attaura).
هُدٗى وَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Open ayah 40:54Don shiriya da wa’azantuwa ga masu hankali.
فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِبۡكَٰرِ
Open ayah 40:55Sai ka yi haƙuri, lalle alƙawarin Allah gaskiya ne, ka kuma nemi gafarar zunubinka, kuma ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka a maraice da safiya. Bayan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gama ba da labarin Fir’auna da mabiyansa da makomarsu a duniya da lahira, sai ya bayyana irin nasara da yake ba wa manzanninsa da mabiyansu a nan duniya da kuma lahira, ya tabbatar da cewa zai taimaka musu ta hanyar bayyana hujjarsu a fili ga kowa, zai kuma ba su nasara a kan abokan gabarsu, sannan a lahira zai yi musu rahama ya shigar da su Aljanna; maƙiyansu kuma ya ɗanɗana musu uƙuba a wutar Jahannama, bayan annabawa da mala’iku da muminai sun ba da shaidar cewa, saƙon Allah ya isa gare su amma suka kafirce suka ƙi yin imani da manzanninsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan ranar ita ce ranar da hanzarin waɗanda suka zalunci kawunansu da shirka da kafirci da saɓon Allah ba zai amfane su da komai ba, domin la’anar Allah ta tabbata a kansu, ba su babu samun rahamar Allah, kuma suna da mummunan gida na azaba mai raɗaɗi, watau Jahannama. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani ɓangare na taimakonsa ga manzanninsa da muminai a nan duniya, da cewa, ya bai wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) shiriya, watau ilimin da Banu Isra’ila za su samu shiriya da shi, ya kuma sanya Attaura littafi ne da za su ci gaba da gadar sa ‘ya’ya da jikoki. Littafi ne na shiriya da wa’azantuwa ga mutane masu hankali, domin ya ƙunshi hukunce-hukuncen shari’a, yana kuma kwaɗaitarwa game da aikin alheri da tsawatarwa a kan aikin sharri. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ƙara haƙuri game da ƙaryatawar da mutanensa suke yi masa da tsangwamar da suke nuna masa shi da sahabbansa, ya tabbatar masa da cewa, alƙawarin da ya yi masa na ba shi nasara shi da mabiyansa muminai gaskiya ne babu kokwanto a cikinsa, sai dai kawai ya ci gaba da ƙara ƙarfafa dangantakarsa da Ubangijinsa, ya nemi gafarar zunubansa, ya kuma yi ta tasbihi tare da gode wa Ubangijinsa safe da yamma.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ سُلۡطَٰنٍ أَتَىٰهُمۡ إِن فِي صُدُورِهِمۡ إِلَّا كِبۡرٞ مَّا هُم بِبَٰلِغِيهِۚ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ
Open ayah 40:56Lalle waɗanda suke yin jayayya game da ayoyin Allah ba tare da wata hujja da ta zo musu ba, ba komai a cikin zukatansu sai neman ɗaukaka wadda ba za su same ta ba. Sai ka nemi tsari daga Allah; lalle Shi Mai ji ne, Mai gani.
لَخَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَكۡبَرُ مِنۡ خَلۡقِ ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 40:57Tabbas halittar sammai da ƙasa ta fi girma a kan halittar mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa sanin (haka).
وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَلَا ٱلۡمُسِيٓءُۚ قَلِيلٗا مَّا تَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 40:58Kuma makaho da mai gani ba za su yi daidai ba, kuma waɗanda suka yi imani suka yi aiki nagari ba za su yi (daidai) da mai mummunan aiki ba. Kaɗan ne ƙwarai kuke wa’azantuwa.
إِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞ لَّا رَيۡبَ فِيهَا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 40:59Lalle alƙiyama tabbas za ta zo babu kokwanto a cikinta, sai dai kuma yawancin mutane ba sa yin imani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk masu jayayya da ayoyinsa don ganin sun rusa, su sun tabbatar da ƙarya ba tare da wata hujja ko wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, to babu abin da yake sanya su irin wannan mummunan aiki sai girman kai da neman ɗaukaka da ya mamaye zukatansu. Kuma ba za su sami hakan ba sai dai su gamu da ƙasƙanci da wulaƙanci. Don haka sai ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya nemi tsarin Allah daga duk wani sharri na mutum ko aljani, domin shi Allah mai jin maganganun bayinsa ne mai ganin ayyukansu, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan abin da ya aikata mai kyau ko mummuna. Daga cikin irin jayayyar da mushirikai suka riƙa yi wa Manzon Allah (ﷺ), akwai batun tashi bayan mutuwa, suna ganin abu ne da ba zai yiwu ba, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kafa musu hujjar yiwuwar hakan da dalilin da duk wani mai hankali ba ya da ja a kansa, watau halittar sammai da ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa tabbas halittar sammai da ƙasa ta fi girma a kan halittar mutane. Don haka wanda ya halicce su da wannan girman nasu da yalwarsu ta yaya za a ce ba zai iya dawo da halittar mutane ba bayan mutuwarsu? Tabbas duk mai hankali zai gamsu da cewa yin haka ga Allah abu ne mai matuƙar sauƙi, to amma kuma yawancin mutane ba sa gane hakan ballantana ya zamo musu hujja a kan tashin matattu bayan mutuwa, duk kuwa da cewa abu ne a fili. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana bambancin mumini da kafiri wajen fahimtar ayoyin Allah da gane hujjojin cikar Ƙudurarsa da cewa, makaho da mai gani ba za su yi daidai ba, hakanan waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa suka kyautata ayyukansu ba za su taɓa zama daidai da wanda ya munana aikinsa da aƙidarsa ba, to amma kuma ‘yan kaɗan ne a cikin mutane suke gane haka har su wa’azantu su yi ƙoƙarin shiga cikin shiryayyu waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa suka kyautata ayyukansu. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa lalle ranar alƙiyama tabbas tana nan tafe babu makawa, a lokacin ne zai tashi matattu domin yin hisabi da sakamako, amma duk da haka yawancin mutane ba su yi imani da zuwan wannan rana ba, don haka suka ƙi yi mata kowane irin tanadi.
وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدۡعُونِيٓ أَسۡتَجِبۡ لَكُمۡۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِي سَيَدۡخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ
Open ayah 40:60Ubangijinku kuma Ya ce: “Ku roƙe Ni zan amsa muku. Lalle waɗanda suke yin girman kai game da bauta min, ba da daɗewa ba za su shiga Jahannama a wulaƙance.”
ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ
Open ayah 40:61Allah ne wanda Ya halitta muku dare don ku natsu a cikinsa, rana kuma don ku ga yadda za ku yi harka. Lalle Allah Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa.
ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ
Open ayah 40:62Wannan Shi ne Allah Ubangijinku, Mahaliccin komai, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi; to ina ne ake kautar da ku?
كَذَٰلِكَ يُؤۡفَكُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ
Open ayah 40:63Kamar haka ne ake karkatar da waɗanda suka zamanto suna musanta ayoyin Allah.
ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ قَرَارٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡۖ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 40:64Allah ne wanda Ya sanya muku ƙasa ta zama wurin zama, sama kuma ta zama rufi, Ya kuma suranta ku, sai Ya kyautata surorinku, Ya kuma arzuta ku da daɗaɗan abubuwa. Wannan fa Shi ne Allah Ubangijinku. To Allah Ubangijin talikai albarkatunsa sun yawaita.
هُوَ ٱلۡحَيُّ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۗ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 40:65Shi Rayayye ne, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, sai ku roƙe Shi kuna masu tsantsanta addini a gare Shi. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kiran bayinsa da su roƙe shi kuma su bauta masa shi kaɗai. Ya yi musu alƙawarin zai amsa musu addu’arsu ya kuma biya su ladan bautarsu. Ya kuma gargaɗi masu girman kai game da roƙon sa da bauta masa, da cewa lalle a ranar alƙiyama za a jefa su Jahannama a wulaƙance, sakamakon girman kai da suka nuna. An karɓo daga Nu’umanu ɗan Bashir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle addu’a ita ce ibada.” Sannan ya karanta wannan ayar har ƙarshenta. [Ahmad #18386 da Tirmizi #3247]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ba ya roƙon Allah, to zai yi fushi da shi.” [Ahmad #9719 da Tirmizi #3373 da Ibn Maja #3827]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasu ni’imominsa da manyan dalilai masu tabbatar da cancantar a bauta masa shi kaɗai, da cewa shi ne ya sanya dare ya zama duhu don mutane su nutsu su huta a cikinsa, ya sanya yini ya zama mai haske don su fita harkokinsu na rayuwa a cikinsa; ba don ya yi musu wannan ni’ima ba da tabbas sun wahala kuma da rayuwarsu ta lalace, lalle Allah mai babbar falala ne ga mutane wadda ya kewaye su da ita ta ko’ina, ciki da waje, sai dai kuma yawancin mutane ba sa gode wa wannan ni’ima da ya yi musu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa mutane cewa wanda ya yi wannan aiki fa shi ne Allah abin bautarsu mahaliccin komai, babu wani abin bauta da gaskiya sai shi kaɗai; to me ya sa mutane suke bijire wa bauta masa suna komawa ga bautar abubuwan da ba za su amfane su da komai ba? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa kamar yadda aka kautar da waɗannan mushirikan daga bautar Allah shi kaɗai, to kamar haka ne ake karkatar da duk waɗanda suka zamanto suna jayayya da ayoyin Allah, ba za su taɓa gane hanyar Tauhidi ba ballantana su kaɗaita Allah da bautarsu a kowane zamani a kowane wuri kuwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana dalilan Kaɗaitakarsa waɗanda kowa yake iya gani da idonsa, inda ya bayyana cewa shi ne ya halitta wa mutane ƙasa ta zama wurin zamansu, ya kuma gina sama ta zama amintaccen rufi marar faɗowa. Shi ne kuma ya suranta mutane a cikin mahaifar iyayensu mata, ya kuma kyautata surarsu ta fi ta kowace irin halitta da ya yi, sannan ya arzuta su da kayan abinci na halal masu daɗi waɗanda za su riƙa ci suna rayuwa. Allah ya tabbatar musu da cewa, to wanda ya tanadar musu waɗannan ni’imomi manya-manya daban-daban shi ne Allah Ubangijinsu, to albarkatunsa sun yawaita, shi ne Ubangijin halittu duka babu wani abin bauta sai shi kaɗai. Ya kuma tabbatar musu da cewa, shi rayayye ne wanda ba zai mutu ba har abada, babu wani abin bauta da gaskiya sai shi, don haka ya umarce su da su bauta masa su kuma roƙe shi shi kaɗai suna masu tsantsanta addininsu a gare shi, kada su yarda su haɗa shi da komai daga cikin halittunsa, domin shi kaɗai ne wanda yabo da godiya suka tabbata gare shi, shi ne kuma Ubangijin halittu duka.
۞قُلۡ إِنِّي نُهِيتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَمَّا جَآءَنِيَ ٱلۡبَيِّنَٰتُ مِن رَّبِّي وَأُمِرۡتُ أَنۡ أُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 40:66Ka ce: “Lalle ni an hana ni in bauta wa waɗanda kuke bauta wa ba Allah ba a yayin da (ayoyi) bayyanannu suka zo min daga Ubangijina, an kuma umarce ni da in miƙa wuya ga Ubangijin talikai.
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ يُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡ ثُمَّ لِتَكُونُواْ شُيُوخٗاۚ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ مِن قَبۡلُۖ وَلِتَبۡلُغُوٓاْ أَجَلٗا مُّسَمّٗى وَلَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 40:67“Shi ne wanda Ya halicce ku daga ƙasa, sannan daga ɗigon maniyyi, sannan daga gudan jini, daga nan Ya fito da ku kuna jarirai, sannan don ku kai ƙarfinku, sannan kuma ku zama tsofaffi. Daga cikinku kuma akwai wanda ake karɓar ransa kafin wannan; don kuma ku isa zuwa wani lokaci ƙayyadajje, don kuma ku hankalta.
هُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَإِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Open ayah 40:68“Shi ne wanda Yake rayawa Yake kuma kashewa; to idan zai hukunta wani al’amari sai kawai Ya ce da shi: ‘Kasance’, sai ya kasance.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya bayyana wa mushirikai hanin da ya yi masa na bautar abin da suke bauta wa ba Allah ba, saboda hujjoji bayyanannu sun zo masa masu nuna ɓacin bautar wani ba Allah ba. Ya kuma shaida musu cewa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya miƙa wuya gare shi ya bauta masa shi kaɗai, domin shi ne Ubangijin halittu baki ɗaya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hujjojin Kaɗaitakarsa da girman Ƙudurarsa, inda ya tabbatar da cewa shi ne ya halicci uban mutane gaba ɗayansu, watau Annabi Adamu, daga ƙasa, sannan ya halicci sauran ‘ya’yansa daga ɗigon maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan bayan haka ya fito da su daga cikkunan iyayensu mata suna jarirai, sannan su yi ta girma har su kai cikar ƙarfinsu, watau ƙarfin jiki da cikar hankali, sannan su manyanta su zama tsofaffi. Daga cikinsu akwai wanda zai rasu kafin haka. Kuma Allah ya yi haka ne don ya ba su damar kaiwa zuwa wani lokaci da ya ƙayyade musu, wanda ba za su rage ba ba kuma za su ƙara ba; don kuma su hankalta su gane waɗannan hujjoji da dalilai da yake nuna musu na cikar Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa. Hakanan ya bayyana musu cewa shi kaɗai ne mai rayawa kuma mai kashewa, duk kuma sanda ya nufi zartar da wani abu to kawai sai ya ce da shi: ‘ya kasance’ sai ko abin nan ya kasance.
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ أَنَّىٰ يُصۡرَفُونَ
Open ayah 40:69Ba ka ganin waɗanda suke jayayya game da ayoyin Allah, to ta yaya ake kautar da su?
ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِٱلۡكِتَٰبِ وَبِمَآ أَرۡسَلۡنَا بِهِۦ رُسُلَنَاۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 40:70(Su ne) waɗanda suka ƙaryata Alƙur’ani da kuma abin da Muka aiko manzanninmu da shi; to ba da daɗewa ba za su sani.
إِذِ ٱلۡأَغۡلَٰلُ فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ وَٱلسَّلَٰسِلُ يُسۡحَبُونَ
Open ayah 40:71A yayin da ƙuƙumai suke a wuyoyinsu, da kuma sarƙoƙi ana jan su.
فِي ٱلۡحَمِيمِ ثُمَّ فِي ٱلنَّارِ يُسۡجَرُونَ
Open ayah 40:72A cikin tafasasshen ruwan, sannan kuma ana ƙona su a cikin wuta.
ثُمَّ قِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تُشۡرِكُونَ
Open ayah 40:73Sannan kuma a ce da su: “Ina abin da kuka kasance kuna shirka da shi?
مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا بَل لَّمۡ نَكُن نَّدۡعُواْ مِن قَبۡلُ شَيۡـٔٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 40:74“Wanda ba Allah ba?” Suka ce: “Sun ɓace mana; ai ba mu kasance muna bauta wa wani abu ba a da”. Kamar haka ne Allah Yake ɓatar da kafirai.
ذَٰلِكُم بِمَا كُنتُمۡ تَفۡرَحُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَبِمَا كُنتُمۡ تَمۡرَحُونَ
Open ayah 40:75Wannan fa (ya same ku ne) saboda abin da kuka kasance kuna yin girman kai da shi a bayan ƙasa ba da wata hujja ba, da kuma abin da kuka kasance kuna yin walwala da shi.
ٱدۡخُلُوٓاْ أَبۡوَٰبَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ فَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلۡمُتَكَبِّرِينَ
Open ayah 40:76(Za a ce da su): “Ku shiga ƙofofin Jahannama kuna masu dawwama a cikinta”; to makomar masu girman kai ta munana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake nanata wa Manzonsa (ﷺ) cewa, ya dubi yadda mushirikai suke jayayya game da ayoyin Allah, har ma suna ƙaryata su duk kuwa da bayyanar gaskiya a fili. Ya yi mamakin irin wannan tsaurin kai nasu, da bijire wa gaskiya duk da cewa ta fito sarari ga kowa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffofinsu da cewa, su ne waɗanda suke ƙaryata Alƙur’ani da gaskiyar da ya aiko manzanninsa da ita. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗe su da cewa, ba da daɗewa ba za su san mummunan sakamakon ƙaryatawarsu, za su kuma ga mummunar azaba a lokacin da za a sanya musu ƙuƙumi a wuyansu a ɗaure ƙafafunsu da sarƙoƙi, mala’iku zabaniyawa suna jan su cikin tafasasshen ruwa, sannan a jefa su wuta su zama makamashinta. A cikin irin wannan masifar azabar kuma za a riƙa yi musu tambaya ta izgili da cewa, ina ababen bautarsu da suke yi wa Allah shirka da su a duniya suka bar Allah; me ya sa ba za su zo su cece su ba? Sai kafirai su amsa da cewa, su ma ba su san inda suke ba, domin sun neme su sun rasa. Hasali ma za su dawo su ce, ai su ba su kasance suna bautar komai ba a duniya, watau su ƙaryata cewa sun bauta wa gumaka. Ko kuma suna nufin yanzu sun gane cewa abubuwan da suke bauta wa a duniya ba su cancanci bauta ba, domin ga shi sun kasa kare su daga azabar Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa kamar yadda waɗannan kafiran suka ɓace, to hakanan yake ɓatar da kafirai waɗanda suka ƙi gaskiya a kowane zamani a kuma kowane wuri. A nan ne kuma za a faɗa musu cewa, dalilin da ya sa suka tsinci kawunansu a cikin wannan mawuyacin hali shi ne, saboda farin ciki da suka riƙa nunawa a duniya da shirkar da suke yi wa Allah da kuma holewa da suka riƙa yi a kan haka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa za a umarce su da su shiga ta ƙofofin Jahannama suna masu dawwama a cikinta har abada; to makomar masu girman kai kuwa ta yi muni.
فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۚ فَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ
Open ayah 40:77Sai ka yi haƙuri, lalle alƙawarin Allah gaskiya ne. To idan Mun nuna maka sashin abin da Muke yi musu alkawari da shi na narko; ko kuma Mun karɓi ranka, to zuwa gare Mu dai za a dawo da su.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ مِنۡهُم مَّن قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّن لَّمۡ نَقۡصُصۡ عَلَيۡكَۗ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُ ٱللَّهِ قُضِيَ بِٱلۡحَقِّ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ
Open ayah 40:78Haƙiƙa Mun aiko manzanni a gabaninka, daga cikinsu akwai waɗanda Muka labarta maka akwai kuma daga cikinsu waɗanda ba Mu labarta maka ba. Ba zai yiwu ba ga wani manzo ya zo da wata aya sai da izinin Allah. Sannan idan al’amarin Allah ya zo, to sai a yi hukunci da gaskiya, kuma a nan ne maɓarnata za su yi asara. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da yin haƙuri game da cutarwar mutanensa da ƙaryata shi da suke yi, ya tabbatar masa cewa alƙawarin da ya yi masa na samun nasara a kansu gaskiya ne, babu kokwanto a cikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) zai nuna wa maƙiyansa azabarsa a duniya da lahira. Don haka Manzo (ﷺ) ya sanya ido ya gani, idan ya ga dama sai ya nuna masa tun a rayuwarsa wani ɓangare na azabar da ya yi musu alƙawari da ita, kamar yadda ya faru gare su a yaƙin Badar, inda aka karkashe manyansu, ko kuma idan ya karɓi ransa kafin hakan ta faru gare su, to duka dai zuwa ga Allah ne makomarsu take a ranar alƙiyama, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan abin da ya aikata a nan duniya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Annabi (ﷺ) da cewa, ba shi ne farau ba game da wannan al’amari, domin kuwa ya aika manzanninsa masu yawa gabaninsa zuwa ga al’ummunsu, to amma sun ƙaryata su, sun kuma cutar da su, sai suka yi haƙuri a kan abin da ya same su har Allah ya kawo musu nasararsa. Daga cikin waɗannan manzanni akwai waɗanda ya ba shi labaransu; akwai kuma waɗanda bai ba shi labaransu ba. Dangane da nacewar da kafirai suke yi wa Manzon Allah (ﷺ) a kan sai ya zo musu da wasu mu’ujizoji da suke nema, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani inda ya nuna musu cewa, zuwa da wata aya ba a hannun wani manzo yake ba; yana ga hannun Allah ne, amma shi Manzo ba (ﷺ) zai yiwu ya zo da wata aya ba sai da izinin Allah, don haka wannan dagewa tasu zalunci ne kawai. Abin da ya kamata kafirai su sani shi ne, idan wani buɗi ko hukunci ya zo tsakanin annabawa da mutanensu, to a nan Allah yana yin hukunci ne na gaskiya da adalci, sai ya hallaka kafirai, ya tserar da muminai da manzanninsu, su kuma maɓarnata hasara ce za ta tabbata gare su saboda kafircinsu.
ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَنۡعَٰمَ لِتَرۡكَبُواْ مِنۡهَا وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 40:79Allah ne wanda Ya halitta muku dabbobin ni’ima don ku hau wasu daga cikinsu, kuma daga cikinsu kuke ci.
وَلَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ وَلِتَبۡلُغُواْ عَلَيۡهَا حَاجَةٗ فِي صُدُورِكُمۡ وَعَلَيۡهَا وَعَلَى ٱلۡفُلۡكِ تُحۡمَلُونَ
Open ayah 40:80Kuna kuma da wasu abubuwan amfani game da su, don kuma ku isa (wurin) da kuke da buƙatar isa a cikin zukatanku a kansu, kuma a kansu ne da kuma a kan jiragen ruwa ake ɗaukar ku.
وَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ فَأَيَّ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ تُنكِرُونَ
Open ayah 40:81Yana kuma nuna muku ayoyinsa, to wacce (aya) ce (daga) ayoyin Allah kuke musawa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana hujjoji na Kaɗaitakarsa da girman Ƙudurarsa da cikar ikonsa, da cewa, shi ne wanda ya halitta wa mutane dabbobin ni’ima, watau raƙuma da shanu da tumakai da awakai, domin su hau wasu daga cikinsu kamar raƙuma, su kuma ci namansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa mutane ni’ima da abubuwan amfani daban-daban tare da waɗannan dabbobi a kowane zamani a kuma kowane wuri; ta hanyarsu ne mutane za su kai ga biyan buƙatunsu da ke cikin zukatansu, musamman tafiye-tafiye masu nisa daga gari zuwa wani gari, su kuma ɗora musu kaya masu nauyi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yana nuna wa mutane ayoyinsa masu nuna cikar Ƙudurarsa da kamalar ikonsa da Kaɗaitakarsa; to wace aya ce daga cikin ayoyin Allah kafirai suke musuntawa, cewa ba daga Allah suke ba? Watau idan har sun yarda da cewa, duk waɗannan ni’imomin daga Allah suke, to babu wani dalili kuma na musu da jayayya. Wajibi ne su miƙa wuya ga Allah su yarda da bautarsa shi kaɗai.
أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِنۡهُمۡ وَأَشَدَّ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 40:82Shin ba za su yi tafiya ba a bayan ƙasa sannan su duba yadda ƙarshen waɗanda suke gabaninsu ya zama? Sun zamanto sun fi su yawa, sun kuma fi su tsananin ƙarfi da barin gurabe a bayan ƙasa; to abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar musu da komai ba.
فَلَمَّا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَرِحُواْ بِمَا عِندَهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 40:83Sannan lokacin da manzanninsu suka zo musu da (ayoyi) bayyanannu, sai suka nuna farin ciki da ilimin da ke gare su, abin kuma da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu.
فَلَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَا قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَحۡدَهُۥ وَكَفَرۡنَا بِمَا كُنَّا بِهِۦ مُشۡرِكِينَ
Open ayah 40:84To lokacin da suka ga azabarmu sai suka ce: “Mun yi imani da Allah Shi kaɗai, mun kuma kafirce wa abin da muka kasance muna yin shirka da shi.”
فَلَمۡ يَكُ يَنفَعُهُمۡ إِيمَٰنُهُمۡ لَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَاۖ سُنَّتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي قَدۡ خَلَتۡ فِي عِبَادِهِۦۖ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Open ayah 40:85To imaninsu bai zamanto zai amfane su ba yayin da suka ga azabarmu; wannan sunna ce ta Allah wadda ta shuɗe a kan bayinsa. Kafirai kuma sun yi asara a nan. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana daɗa jan kunnen masu ƙaryata ayoyinsa ne don neman wani abin duniya, kamar dukiya ko matsayi ko kuma don nuna girman kai da tsaurin ido, da cewa su yi yawo a bayan ƙasa mana don su gane wa idanunsu yadda ƙarshen al’ummun da suka gabace su ya kasance bayan sun ƙaryata manzanninsu; su ga yadda Allah ya yi da su, don su ɗauki izina da wa’azi daga gare su. Waɗannan al’ummu sun fi su yawa da tarin dukiya, sun fi su ƙarfi, sun kuma fi su motsa ƙasa domin gine-gine da noma, to amma abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar da su da komai ba yayin da azabar Allah ta zo musu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babban laifinsu wanda ya jawo musu azabarsa, watau lokacin da manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu sai suka bijire suka ƙaryata su, suka ƙi amincewa da su, suka ci gaba da ƙanƙame ilimin da suke tinƙaho da shi wanda ya saɓa wa na manzanninsu, sai azabar Allah wadda suke yi wa izgili ta saukar musu ta hallaka su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da suka ga azabarsa ta tunkaro su gadan-gadan sai suka yi fargar-jaji suka gane kuskurensu, suka furta cewa, sun yi imani da Allah shi kaɗai, sun kafirce wa duk abubuwan da suke bauta wa ba Allah ba. A ayar ƙarshe ta wannan Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa imanin kafirai a wannan lokaci bayan sun ga azabar Allah ba zai yi musu wani amfani ba. Wannan kuwa sunnar Allah ce wadda ta riga ta shuɗe yake zartar da ita cikin bayinsa na cewa, imani ba zai yi amfani ba bayan azaba ta riga ta sauka. Kafirai kuwa sun yi mummunar asara da suka bari har azabar Allah ta zo musu ba su tuba sun koma gare shi ba.