فصلت

Fussilat

Explained in detail · Surah 41 · Ayahs: 54 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. HA MIM.

  2. تَنزِيلٞ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

    Open ayah 41:2

    (Alƙur’ani) saukakke ne daga (Allah) Mai rahama, Mai jin ƙai.

  3. كِتَٰبٞ فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

    Open ayah 41:3

    (Shi) Littafi ne Alƙur’ani Balarabe da aka rarrabe ayoyinsa ga mutanen da suke sanin (ma’anarsa).

  4. بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا فَأَعۡرَضَ أَكۡثَرُهُمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ

    Open ayah 41:4

    Mai albishir ne kuma mai gargaɗi, sai yawancinsu suka bijire, don haka su ba sa jin (kira).

  5. وَقَالُواْ قُلُوبُنَا فِيٓ أَكِنَّةٖ مِّمَّا تَدۡعُونَآ إِلَيۡهِ وَفِيٓ ءَاذَانِنَا وَقۡرٞ وَمِنۢ بَيۡنِنَا وَبَيۡنِكَ حِجَابٞ فَٱعۡمَلۡ إِنَّنَا عَٰمِلُونَ

    Open ayah 41:5

    Suka kuma ce: “Zukatanmu suna cikin rufi game da abin da kuke kiran mu zuwa gare shi; a cikin kunnuwanmu kuma akwai nauyi, kuma tsakaninmu da kai akwai shamaki, sai ka yi aiki da (addininka), lalle mu ma masu yin aiki ne (da namu).” An buɗe wannan Sura da wasu haruffa, kamar yadda aka buɗe wasu surori a baya. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara domin ƙarin bayani]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana matsayin Alƙur’ani da cewa shi saukakken littafi ne daga Allah wanda rahamarsa ta yalwaci kowa da komai a nan duniya, mai kuma keɓantacciyar rahama ga muminai a lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana siffar Alƙur’ani da cewa shi littafi ne da aka yi bayanin ayoyinsa daki-daki ta yadda kowa zai iya fahimta bakin gwargwado, sannan ya sanya shi Balaraben littafi ga mutanen da suke sanin ma’anoninsa suke amfana da shi da abin da ya ƙunsa na shiriya. Sannan Allah ya nuna cewa Alƙur\'ani mai yi wa muminai albishir ne da gwaggwaɓan sakamako da Allah ya tanadar musu, kuma mai gargaɗi ne ga kafirai game da azaba mai raɗaɗi idan ba su tuba zuwa ga Allah ba. To amma sai mafi yawancinsu suka bijire wa sauraron shiriyar da yake kiran su zuwa gare ta, suka daina sauraron sa sauraro na karɓa da miƙa wuya. Har ma kafiran suna cewa zukatansu a rufe suke ruf, ba za su taɓa fahimtar wa’azin da ake yi musu ba, kuma akwai kurumta tare da kunnuwansu, don haka ba sa jin duk wani kira da ake yi musu. Hasali ma tsakaninsu da Manzon Allah (ﷺ) da yake kiran su akwai shamaki da yake hana muryarsa isa zuwa inda suke, saboda haka suna sanar da shi cewa ya je ya yi aiki da fahimtarsa a kan hanyar da ya zaɓa, su ma za su yi aiki ne da fahimtarsu a kan hanyar da suka zaɓa wa kawunansu, su kam ba za su bi shi ba. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata rana Ƙuraishawa sun yi taro, sai suka ba wa junansu shawara a kan su duba a cikinsu su zaɓi wanda ya fi kowa sanin sihiri da waƙa da bokanci don ya je ya sami Annabi (ﷺ) wanda suke zargin sa da ya zo ne don ya rarraba kawunansu, ya tarwatsa musu al’amuransu ya kuma kushe musu addininsu. Ya tattauna da shi ya ga wace amsa zai ba shi. Sai suka zaɓi Utbatu ɗan Rabi’atu domin suna ganin babu wanda ya fi shi dacewa da wannan aiki. Sai ya tafi ya haɗu da Manzon Allah (ﷺ) ya tambaye shi cewa: “Kai Muhammadu, da kai da Abdullahi wane ne ya fi?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi masa shiru bai ce masa komai ba. Sai ya sake tambayar sa cewa: “To kai da Abdulmuɗɗalibi wane ne ya fi?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi masa shiru. Sai Utbatu ya ce: “Idan har ka yarda cewa waɗannan mutanen biyu sun fi ka, to su, sun bauta wa allolin da kake kushewa. Idan kuma kana ganin kai ka fi su, to sai ka faɗa mu ji. Mu dai Wallahi ba mu taɓa ganin ɗan da ya zame wa mutanensa alaƙaƙai ba kamarka. Ka rarraba kawunanmu, ka tarwatsa mana al’amarinmu, ka kushe addininmu, ka kuma kunyata mu a cikin ‘yan’uwanmu Larabawa; har labari ya bazu a cikinsu cewa an sami matsafi a cikin Ƙuraishawa, an kuma sami boka a cikinsu. Wallahi babu abin da ya rage mana sai dai kawai mu ji ihu irin na mace mai ciki, daga nan kuma kowa ya zare takobinsa mu yi ta sarar junanmu har sai mun ƙarar da kanmu. Kai wannan mutum, ka faɗa mana, idan buƙatar dukiya ce kake yi sai mu tara maka dukiya har sai ka fi kowa kuɗi cikin Ƙuraishawa. Idan kuma aure kake buƙata, to ka zaɓi matan Ƙuraishawan da suka yi maka, mu za mu aura maka guda goma.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Ka gama maganarka?” Sai ya ce: “Na’am.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi Bismilla ya fara karanto farkon wannan Sura har sai da ya kai aya ta 13, sai Utbatu ya ce: “Ya isa hakanan, ya isa hakanan. Ban da wannan ba ka da wata maganar?” Annabi ya ce masa: “Babu.” Sai ya koma wajen Ƙuraishawa, suka tambaye shi: “Mene ne labari?” Sai ya ce: “Babu abin da na bari wanda nake ganin za ku faɗa masa shi har sai da na faɗa masa.” Sai suka ce: “To ya ba ka amsa?” Sai ya ce: “A’a, na rantse da wanda ya kafa ginin Ka’aba, ban fahimci komai daga maganarsa ba sai dai kawai na ji yana muku gargaɗi da tsawa irin tsawar Adawa da Samudawa.” Sai suka ce: “Kaiconka, mutum yana yi maka magana da harshen Larabci amma ka ce ba ka fahimci komai daga maganarsa ba?” Ya ce: “E, Wallahi ba abin da na fahimta sai maganar tsawar nan kaɗai.” [Abdu bin Humaid #1119 da Ibn Abi Shaiba, Al-Musannaf #36560 da Abu Ya’ala #1818 da Al-Hakim #3002].

  6. قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَٱسۡتَقِيمُوٓاْ إِلَيۡهِ وَٱسۡتَغۡفِرُوهُۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡمُشۡرِكِينَ

    Open ayah 41:6

    Ka ce: “Ni ba wani ba ne sai mutum kamarku, ana yiwo min wahayin cewa, abin bautarku abin bauta ne Guda Ɗaya, sai ku miƙe kyam zuwa gare Shi, kuma ku nemi gafararsa. Tsananin azaba kuma ya tabbata ga mushirikai.

  7. ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ

    Open ayah 41:7

    “Waɗanda ba sa ba da zakka, kuma su masu kafircewa ne da (ranar) lahira.”

  8. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ

    Open ayah 41:8

    Lalle waɗanda suka yi imani kuma suka yi aiki nagari suna da lada marar yankewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa wa mushirikai masu jayayya da shi a kan manzancinsa da Alƙur’ani cewa shi fa kawai mutum ne kamarsu mai ƙirar jiki da kamanni irin nasu, watau shi ba mala’ika ba ne ba kuma aljani ne ba, bambancinsu shi ne, shi ana yi masa wahayi da cewa abin bautarsu na gaskiya Ɗaya ne shi ne Allah, don haka su kama hanyar da za ta sada su da shi, su nemi gafarar zunubansu daga gare shi. Kuma su sani cewa azaba da hallaka sun tabbata ga mushirikai masu bauta wa wasu tare da Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta mushirikai da cewa su ne waɗanda ba sa bayar da zakkar dukiyoyinsu kuma suna kafirce wa ranar lahira da abin da ta ƙunsa na ni’imominta da azabarta. Sai kuma ya ambaci sakamakon waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa suka yi kuma ayyuka nagari da cewa suna da sakamakon da ba ya yankewa, watau Aljanna.

  9. ۞قُلۡ أَئِنَّكُمۡ لَتَكۡفُرُونَ بِٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَرۡضَ فِي يَوۡمَيۡنِ وَتَجۡعَلُونَ لَهُۥٓ أَندَادٗاۚ ذَٰلِكَ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

    Open ayah 41:9

    Ka ce: “Yanzu kwa riƙa kafircewa da wanda Ya halicci ƙasa a cikin (gwargwadon) kwana biyu, kuna kuma sanya masa kishiyoyi? Wannan fa Shi ne Ubangijin talikai!

  10. وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِيَ مِن فَوۡقِهَا وَبَٰرَكَ فِيهَا وَقَدَّرَ فِيهَآ أَقۡوَٰتَهَا فِيٓ أَرۡبَعَةِ أَيَّامٖ سَوَآءٗ لِّلسَّآئِلِينَ 

    Open ayah 41:10

    “Ya kuma sanya kafaffun duwatsu a cikinta daga samanta, Ya kuma yi albarka a cikinta, Ya kuma ƙaddara dangogin abincinta a cikin kwana huɗu (tare da kwanaki biyu na halittar ƙasa) daidai da daidai ga masu tambaya.

  11. ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰٓ إِلَى ٱلسَّمَآءِ وَهِيَ دُخَانٞ فَقَالَ لَهَا وَلِلۡأَرۡضِ ٱئۡتِيَا طَوۡعًا أَوۡ كَرۡهٗا قَالَتَآ أَتَيۡنَا طَآئِعِينَ

    Open ayah 41:11

    “Sannan Ya nufi zuwa sama, (a sannan) ita kuma hayaƙi ce, sai Ya ce da ita da kuma ƙasa: “Ku zo cikin biyayya ko kuma bisa tilas.” Suka ce: ‘Mun zo muna masu biyayya’.

  12. فَقَضَىٰهُنَّ سَبۡعَ سَمَٰوَاتٖ فِي يَوۡمَيۡنِ وَأَوۡحَىٰ فِي كُلِّ سَمَآءٍ أَمۡرَهَاۚ وَزَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِمَصَٰبِيحَ وَحِفۡظٗاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ

    Open ayah 41:12

    “Sai Ya mayar da su sammai bakwai a cikin kwana biyu, Ya kuma yi wa kowacce sama wahayin umarninta. Muka kuma ƙawata saman duniya da taurari da kuma tsaro. Wannan tsari ne na Allah Mabuwayi, Masani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikar Ƙudurarsa da hikimarsa wadda ke tabbatar da cancantar a bauta masa shi kaɗai ba tare da haɗa shi da abokin tarayya ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ƙalubalanci mushirikai da cewa, me ya sa suke kafirce wa Allah (Mai tsarki da daukaka) wanda ya halicci ƙasa a cikin kwana biyu, watau ranar Lahadi da ranar Litinin, suke kuma sanya masa kishiyoyi suna bauta musu tare da shi? Wannan fa shi ne Ubangijin talikai gaba ɗayansu. Kuma shi ne wanda ya kakkafa duwatsu a cikin ƙasa domin su riƙe ta su hana ta yin tangal-tangal. Sannan ya ƙaddara samuwar abincin mutane da na dabbobi iri-iri a cikinta cikin kwana huɗu, watau haɗe da kwanakin halittar ƙasa guda biyu, su ne ranar Talata da Laraba, kwanaki huɗu cikakku don masu yin tambayar son sanin yadda al’amarin ya faru. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nufi halittar sama, ita kuma a lokacin hayaƙi ce, sai ya umarce ta ita da ƙasa cewa su zo suna masu miƙa wuya a bisa zaɓinsu ko kuma ala tilas, sai suka amsa masa da cewa za su zo a bisa zaɓin kansu, domin ba su da wani zaɓi bayan nasa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya cika halittar sammai bakwai a cikin kwana biyu, watau Alhamis da Juma’a, cikon kwana shida kenan na halittar sammai da ƙasa. Daga nan sai Allah ya yi wa kowace sama wahayin abin da ya ƙaddara samuwarsa a cikinta, da abin da ya yi umarni da shi na ɗa’a da bautarsa. Sai ya bayyana cewa ya sanya taurari a sama ta duniya domin su zama ado da kuma tsaro a gare ta daga shaiɗanu masu zuwa satar sauraro. Duk waɗannan abubuwa da aka ambata wani tsari ne na Allah mabuwayi wanda babu mai iya ja da shi, masanin komai da ke cikin halittunsa na sama da na ƙasa.

  13. فَإِنۡ أَعۡرَضُواْ فَقُلۡ أَنذَرۡتُكُمۡ صَٰعِقَةٗ مِّثۡلَ صَٰعِقَةِ عَادٖ وَثَمُودَ

    Open ayah 41:13

    To idan suka bijire sai ka ce: “Na tsoratar da ku da tsawa irin tsawar Adawa da Samudawa.

  14. إِذۡ جَآءَتۡهُمُ ٱلرُّسُلُ مِنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَۖ قَالُواْ لَوۡ شَآءَ رَبُّنَا لَأَنزَلَ مَلَٰٓئِكَةٗ فَإِنَّا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ

    Open ayah 41:14

    “Lokacin da manzanninsu suka zo musu ta gabansu da ta bayansu cewa: ‘Kada ku bauta wa komai sai Allah.’” Suka ce: “Da Ubangijinmu Ya ga dama, da Ya saukar da mala’iku, saboda haka mu lalle masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne.’”

  15. فَأَمَّا عَادٞ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَقَالُواْ مَنۡ أَشَدُّ مِنَّا قُوَّةًۖ أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَهُمۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ

    Open ayah 41:15

    Amma Adawa sai suka yi girman kai a bayan ƙasa ba a kan gaskiya ba, suka kuma ce: “Wane ne ya fi mu tsananin ƙarfi?” Yanzu ba su ga cewa lalle Allah wanda Ya halicce su Ya fi su tsananin ƙarfi ba? Sun kuma kasance suna musanta ayoyinmu.

  16. فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِيٓ أَيَّامٖ نَّحِسَاتٖ لِّنُذِيقَهُمۡ عَذَابَ ٱلۡخِزۡيِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَخۡزَىٰۖ وَهُمۡ لَا يُنصَرُونَ

    Open ayah 41:16

    Sai Muka aiko musu da wata iska mai ƙara a wasu kwanaki masu cike da shu’umci don Mu ɗanɗana musu azabar kunyata a rayuwar duniya; azabar lahira kuma ta fi kunyatarwa; alhalin su ba za a taimake su ba.

  17. وَأَمَّا ثَمُودُ فَهَدَيۡنَٰهُمۡ فَٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡعَمَىٰ عَلَى ٱلۡهُدَىٰ فَأَخَذَتۡهُمۡ صَٰعِقَةُ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡهُونِ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

    Open ayah 41:17

    <b> Amma Samudawa kuma sai Muka nuna musu hanyar shiriya, sai suka zaɓi ɓata a kan shiriya, sai tsawar azabar wulaƙanci ta kama su saboda abin da suka kasance suna tsuwurwuta.

  18. وَنَجَّيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

    Open ayah 41:18

    Muka kuma tserar da waɗanda suka yi imani suka kuma kasance masu kiyaye dokokin Allah. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar Annabi (ﷺ) da ya gargaɗi mutanensa mushirikai cewa idan suka bijire suka ƙi yin imani da Kaɗaitakar Allah da manzancin Annabi (ﷺ), to yana tsoratar da su da wata azaba da za ta saukar musu, irin azabar da ta sauka a kan Adawa da Samudawa yayin da suka ƙaryata manzanninsu. Lokacin da manzanni suka dinga zuwa musu ɗaya bayan ɗaya suna umartar su da abu guda ɗaya, shi ne su bauta wa Allah shi kaɗai kada su haɗa komai da shi, to amma maimakon su yi imani sai suka riƙa cewa, ai bai kamata a ce mutane irinsu ne Allah zai aiko a matsayin manzanni ba; da ya ga damar aiko da manzanni to ai sai ya saukar da mala’iku daga sama su riƙa yi musu wa’azi. Don haka suka tabbatar musu cewa su sun kafirce wa duk abin da aka aiko su da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin kafircin Adawa da na Samudawa da irin azabar da ya saukar musu, da cewa su Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) baya ga kafircinsu, su mutane ne da suka nuna girman kai a bayan ƙasa ba a kan gaskiya ba, suka zalunci waɗanda suke tare da su, suna kuma alfahari da ƙarfin da aka ba su, har suna cewa wane ne ya fi su tsananin ƙarfi? Watau suna ganin cewa babu wanda ya fi ƙarfinsu; wannan ne ya ruɗe su har suka riƙa aikata abin da suka ga dama a bayan ƙasa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa, shin ba su san cewa Allah wanda ya halicce su ya ba su wannan ƙarfin da suke taƙama da shi ya fi su tsananin ƙarfi ba? Ba don ya halicce su ba da babu su, da a ce sun yi tunani a kan haka, da ba za su yi ɗagawar da suka yi ba, amma sai suka musunta ayoyin Allah waɗanda Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo musu da su suka ƙaryata shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa sakamakon kafircinsu ya sa ya aiko musu da wata iska mai tsananin ƙara a cikin wasu shu’uman kwanaki mara sa alheri saboda tsananin azabar da ke cikinsu, don ya ɗanɗana musu azabar wulaƙanci da ƙasƙanci a rayuwar duniya, kuma azabar lahira wadda take jiran su ta fi tsananin ƙasƙanci da wulaƙanci, ga shi kuma a lahira babu wanda zai taimaka musu ya kuɓutar da su daga wannan azabar. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, su kuma Samudawa mutanen Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya bayyana musu hanyar shiriya amma sai suka fifita ɓata a kan shiriya, sai azabar tsawa mai wulaƙantarwa ta faɗa musu, saboda kafirci da saɓon Allah da suka riƙa aikatawa. Allah kuma (Mai tsarki da daukaka) ya tserar da muminai waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa suka kuma yi taƙawa, watau bin umarnin Allah da guje wa haninsa, ya kuɓutar da su daga azaba mai raɗaɗi.

  19. وَيَوۡمَ يُحۡشَرُ أَعۡدَآءُ ٱللَّهِ إِلَى ٱلنَّارِ فَهُمۡ يُوزَعُونَ

    Open ayah 41:19

    (Ka tuna) kuma ranar da za a tara maƙiya Allah zuwa wuta ana kuma kora su.

  20. حَتَّىٰٓ إِذَا مَا جَآءُوهَا شَهِدَ عَلَيۡهِمۡ سَمۡعُهُمۡ وَأَبۡصَٰرُهُمۡ وَجُلُودُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ 

    Open ayah 41:20

    Har sai lokacin da suka zo mata, jinsu da ganinsu da fatunsu za su ba da shaida a kan abin da suka kasance suna aikatawa.

  21. وَقَالُواْ لِجُلُودِهِمۡ لِمَ شَهِدتُّمۡ عَلَيۡنَاۖ قَالُوٓاْ أَنطَقَنَا ٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَنطَقَ كُلَّ شَيۡءٖۚ وَهُوَ خَلَقَكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

    Open ayah 41:21

    Sai Suka ce da fatunsu: “Don me kuka ba da shaida a kanmu?” Suka ce: “Allah da Ya bai wa kowane abu ikon yin furuci mu ma Shi Ya ba mu ikon furuci, Shi ne kuma Ya halicce ku tun farko, gare Shi kuma kaɗai za a mayar da ku.”

  22. وَمَا كُنتُمۡ تَسۡتَتِرُونَ أَن يَشۡهَدَ عَلَيۡكُمۡ سَمۡعُكُمۡ وَلَآ أَبۡصَٰرُكُمۡ وَلَا جُلُودُكُمۡ وَلَٰكِن ظَنَنتُمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَا يَعۡلَمُ كَثِيرٗا مِّمَّا تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 41:22

    Kuma ba ku kasance kuna ɓoye (ayyukanku) ba, don gudun kada jinku da ganinku da fatunku su ba da shaida a kanku ba, sai dai kuna tsammanin cewa Allah ba Ya sane da yawancin abin da kuke aikatawa.

  23. وَذَٰلِكُمۡ ظَنُّكُمُ ٱلَّذِي ظَنَنتُم بِرَبِّكُمۡ أَرۡدَىٰكُمۡ فَأَصۡبَحۡتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

    Open ayah 41:23

    Wannan kuma shi ne zatonku da kuka yi ga Ubangijinku da ya hallakar da ku, sai kuka wayi gari cikin hasararru.

  24. فَإِن يَصۡبِرُواْ فَٱلنَّارُ مَثۡوٗى لَّهُمۡۖ وَإِن يَسۡتَعۡتِبُواْ فَمَا هُم مِّنَ ٱلۡمُعۡتَبِينَ

    Open ayah 41:24

    To idan ma sun yi haƙuri wuta ce dai makomarsu; idan kuma suka nemi kawo wani hanzari, to su ba sa cikin waɗanda za a karɓi hanzarinsu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda zai azabtar da maƙiyansa a ranar alƙiyama, lokacin da za a tattara su a haɗa na farko da na ƙarshensu a gargaɗa su da ƙarfi zuwa wutar Jahannama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yayin da za su iso wannan wutar sai su dinga musunta laifukan da suka yi a duniya, daga nan sai jinsu da ganinsu da fatunsu su ba da shaida game da abin da suka kasance suna aikatawa na kafirci da saɓon Allah, watau kowace gaɓa za ta furta irin saɓon Allah da ta aikata da lokaci da kuma wurin da ta aikata shi. To daga nan fa kafirai ba su da ikon ci gaba da musu, sai su fara zargin gaɓoɓinsu a kan irin wannan shaida da suka bayar a kansu, har ma su ce da fatun nasu, me ya sa za su ba da irin wannan mummunar shaida a kansu? Sai fatun su amsa musu da martanin cewa, Allah wanda ya ba wa kowane abu ikon yin furuci su ma shi ne ya ba su wannan ikon, suka kuma nuna musu cewa kada su manta fa shi ne ya halicce su tun a karon farko, don haka babu abin da zai gagare shi, kuma zuwa gare shi shi kaɗai za a mayar da su domin ya yi musu hisabi a kan ayyukansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa za a shaida musu cewa, ai da man tun a duniya ba sa ɓoye wani aiki na kafirci da saɓon Allah da suke yi don gudun kada jinsu da ganinsu da fatunsu su ba da shaida a kansu; suna fitowa ne gaba-gaɗi su aikata ayyukan da suka ga dama a sarari, domin ba su yi imani da ranar hisabi ko uƙuba ko sakamako na bayan mutuwa ba, kuma suna tsammanin Allah ba ya sanin yawancin abin da suke aikatawa. Wannan mummunan zato nasu shi ne ya ruɗe su har suka ci gaba da aika-aikarsu ba tare da sun tuba ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa wannan mummunan zaton da suka yi wa Ubangijinsu shi ne ya hallaka su har suka wayi gari suna cikin hasararru waɗanda suka yi hasarar duniya da lahira. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa azabarsa ta riga ta tabbata a kansu, don haka ko su yi haƙuri da shaidar da gaɓoɓinsu suka bayar a kansu ko ba su yi haƙuri ba duka ɗaya ne, domin wuta ce makomarsu, idan kuma suka nemi Allah ya ɗauke musu azaba ya yafe musu laifukansu, to su sani cewa sun makara, ba za su taɓa samun afuwarsa ba ballantana har ya yafe musu su sami shiga Aljanna.

  25. ۞وَقَيَّضۡنَا لَهُمۡ قُرَنَآءَ فَزَيَّنُواْ لَهُم مَّا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَحَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ خَٰسِرِينَ

    Open ayah 41:25

    Muka kuma haɗa su da abokai (shaiɗanu), sai suka ƙawata musu abin da yake gabansu (na duniya) da abin da yake bayansu (na musun alƙiyama), sai kalmar (azaba) ta tabbata a kansu (na zamantowa) cikin al’ummun da suka gabace su na aljannu da mutane; lalle su, sun kasance hasararru.

  26. وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَسۡمَعُواْ لِهَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ وَٱلۡغَوۡاْ فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَغۡلِبُونَ

    Open ayah 41:26

    Waɗanda kuma suka kafirta suka ce: “Kada ku saurari wannan Alƙur’ani, ku riƙa yin hayaniya a cikinsa don ku yi rinjaye.”

  27. فَلَنُذِيقَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَذَابٗا شَدِيدٗا وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَسۡوَأَ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

    Open ayah 41:27

    To tabbas za Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta azaba mai tsanani, kuma tabbas za mu saka musu da mafi munin abin da suka kasance suna aikatawa.

  28. ذَٰلِكَ جَزَآءُ أَعۡدَآءِ ٱللَّهِ ٱلنَّارُۖ لَهُمۡ فِيهَا دَارُ ٱلۡخُلۡدِ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ

    Open ayah 41:28

    Wannan fa shi ne sakamakon maƙiya Allah (watau) wuta; suna da gidan dawwama a cikinta; sakamako ne saboda abin da suka kasance suna musuntawa na ayoyinmu.

  29. وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ رَبَّنَآ أَرِنَا ٱلَّذَيۡنِ أَضَلَّانَا مِنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ نَجۡعَلۡهُمَا تَحۡتَ أَقۡدَامِنَا لِيَكُونَا مِنَ ٱلۡأَسۡفَلِينَ

    Open ayah 41:29

    Waɗanda kuma suka kafirta suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka nuna mana waɗanda suka ɓatar da mu daga aljannu da mutane, mu sanya su a ƙarƙashin dugaduganmu don su zamanto cikin na can ƙasan ƙasa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya haɗa kafirai da wasu abokai shaiɗanu da koyaushe suke tare da su suna ƙawata musu kafirci da saɓon Allah a duniya, suna mantar da su ranar lahira suna kuma hana su yi mata kyakkyawan tanadi ko ma su sanya su ƙaryata ta, har lokacin da kalmar azaba ta tabbata a kansu su zamanto cikin sauran al’ummun da suka shuɗe gabaninsu na aljannu da mutane. Lalle dukkansu sun kasance hasararru, domin za su yi hasarar kawunansu da iyalansu a ranar alƙiyama, saboda wuta ce makomarsu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafiran Ƙuraishawa suka riƙa yaƙar Alƙur’ani suna hana mutane sauraron karatunsa suna faɗa musu cewa, kada su saurare shi kuma duk sanda suka ji ana karanta shi to su yi ta hayaniya da hargowa a wurin don kada mutane su sami damar jin abin da ake karantawa, domin suna zaton ta haka ne za su yi galaba su kawo ƙarshen da’awa zuwa ga Allah, su huta da jin karatun Alƙur’ani. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, lalle sai ya ɗanɗana matsananciyar azabarsa a ranar alƙiyama ga waɗanda suka kafirce masa suka ƙaryata manzanninsa, kuma tabbas sai ya saka musu da mafi munin abin da suka kasance suna aikatawa na kafirci da saɓonsa. Wannan azabar kuma da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambata ita ce sakamakon maƙiya Allah masu ƙaryata manzannin Allah; wuta ce wadda za ta zame musu gidan dawwama da ba za ta yanke ba har abada, sakamako ne a gare su saboda sun yi ta musunta ayoyin Allah suka ƙi yin imani da su duk kuwa da bayyanar ƙarfin hujjar da ke cikinsu. Allah kuma (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa bayan an jefa kafirai wuta a ranar alƙiyama manyansu da ƙanana, sai ƙananan su riƙa roƙon Allah da ya nuna musu waɗanda suka ɓatar da su daga cikin aljannu da mutane, watau kamar Iblis wanda shi ne jagoransu wanda ya sunnanta kafirci da saɓon Allah a bayan ƙasa shi da sauran shaiɗanu mabiyansa daga jinsin mutane da aljannu, domin su saka su a ƙarƙashin dugadugansu a wuta don su zamanto a can ƙasan ƙasa a wulaƙance cikin azaba mai tsanani.

  30. إِنَّ ٱلَّذِينَ قَالُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُ ثُمَّ ٱسۡتَقَٰمُواْ تَتَنَزَّلُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ أَلَّا تَخَافُواْ وَلَا تَحۡزَنُواْ وَأَبۡشِرُواْ بِٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ 

    Open ayah 41:30

    Lalle waɗanda suka ce: “Allah ne Ubangijinmu”, sannan suka tsaya kyam, to mala’iku za su sauko musu (lokacin mutuwa suna cewa): “Kada ku tsorata, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi farin ciki da Aljanna wadda kuka kasance ana yi muku alƙawarinta.

  31. نَحۡنُ أَوۡلِيَآؤُكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَشۡتَهِيٓ أَنفُسُكُمۡ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَدَّعُونَ

    Open ayah 41:31

    “Mu masoyanku ne a rayuwar duniya da kuma ta lahira; kuma a cikinta (Aljanna) za ku sami duk abin da rayukanku suke marmari, za kuma ku sami duk abin da kuke nema a cikinta.

  32. نُزُلٗا مِّنۡ غَفُورٖ رَّحِيمٖ

    Open ayah 41:32

    “Liyafa ce daga (Allah) Mai gafara, Mai jin ƙai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon bayinsa ne muminai waɗanda suka ce Allah ne kaɗai Ubangijinsu, ba su da wani abin bauta ba shi ba, suka kuma tsaya kyam a kan tafarkinsa miƙaƙƙe, suna aiki da umarninsa suna guje wa haninsa. To waɗannan idan lokacin mutuwarsu ya zo mala’iku ne za su sauko musu suna lallashin su suna kwantar musu da hankali da cewa, kada su ji tsoron mutuwa ko abin da zai biyo bayanta, kada kuma su yi baƙin cikin abin da za su bari a duniya, sai su yi musu albishir da gidan Aljanna wanda aka yi musu alƙawari da shi a duniya saboda imaninsu da kyawawan ayyukansu. Mala’ikun za su ƙara tabbatar musu cewa, su masoyansu ne a duniya, su ne suka riƙa kwaɗaitar da su a kan aikata ayyukan alheri da bin gaskiya, su ne kuma suka riƙa ba su kariya; hakanan kuma a lahira su ne masoyansu suna tare da su ba za su bar su ba. Sai su kwaɗaitar da su ni’imar Aljanna da cewa za su sami duk abin da rayukansu za su yi sha’awa na kayan marmari a gidan Aljanna da abubuwan morewarta, duk kuma wani abu da za su yi sha’awa su nema za a kawo musu shi nan take. Wannan kuwa duka masaukin baƙi ne daga Allah mai gafarta zunuban bayinsa da suka tuba, kuma mai rahama gare su. An karɓo daga Sufyan ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ce: “Ya Manzon Allah, ka faɗa mini wata magana a Musulunci wadda bayanka ba zan sake tambayar wani a kanta ba?” Sai ya ce: “Ka ce: Na yi imani da Allah, sannan sai ka tsaya kyam (a kanta).” [Muslim #62]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mala’iku suna halarto wa mamaci, idan ya kasance mutum ne nagari sai su ce: “Ka fito ya kai wannan rai mai tsarki da ke cikin jiki mai tsarki, ka fito kana abin yabo, ka yi farin cikin haɗuwa da hutu da ƙamshi da Ubangiji da ba mai fushi da kai ba. Haka za su yi ta faɗa har wannan ran ya fita, sannan a yi sama da shi…” [Ahmad #8768].

  33. وَمَنۡ أَحۡسَنُ قَوۡلٗا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا وَقَالَ إِنَّنِي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

    Open ayah 41:33

    Wane ne ya fi kyakkyawar magana fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah ya kuma yi aiki nagari, kuma ya ce: “Lalle ni ina daga cikin Musulmi?”

  34. وَلَا تَسۡتَوِي ٱلۡحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّيِّئَةُۚ ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِي بَيۡنَكَ وَبَيۡنَهُۥ عَدَٰوَةٞ كَأَنَّهُۥ وَلِيٌّ حَمِيمٞ

    Open ayah 41:34

    Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama ɗaya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, to sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce, ya zamanto kamar wani masoyi ne na ƙut da ƙut.

  35. وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ذُو حَظٍّ عَظِيمٖ

    Open ayah 41:35

    Ba kowa ake bai wa wannan kyakkyawar ɗabi’ar ba sai waɗanda suka yi haƙuri, ba kowa ake bai wa ita ba sai mai babban rabo.

  36. وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ نَزۡغٞ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

    Open ayah 41:36

    Idan kuma wani tunzuri daga Shaiɗan ya tunzura ka, to sai ka nemi tsari daga Allah; lalle Shi Mai ji ne, Masani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafa gwiwar masu kira zuwa gare shi, da nuna girman matsayinsu a wurinsa da bayanin wasu kyawawan siffofi nasu, da cewa babu mutumin da ya fi kyakkyawar magana kamar wanda ya haɗa waɗannan siffofi uku: <b>Ta ɗaya </b>, ya yi kira zuwa ga Allah, watau kaɗaita shi da yin biyayya gare shi. <b>Ta biyu </b>, ya yi aiki nagari ya kuma nisanci munanan ayyuka. <b>Ta uku </b>, ya yi alfahari da kasancewarsa Musulmi, yana mai aiki irin na Musulunci. To duk wanda ya yi haka ya fi kowa kyakkyawar magana. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda ya kamata Musulmi ya kyautata alaƙarsa da sauran mutane, da cewa kyakkyawan aiki da Allah yake so ya kuma yarda da shi ba zai zama ɗaya da mummunan aiki wanda Allah ba ya so ba. Sai Allah ya yi umarni ga duk mutumin da aka yi masa mummunan abu, to shi ya saka da sakamako mafi kyau; idan har ya aikata haka to zai ga wanda yake maƙiyinsa ne a can baya ya dawo ya zama masoyinsa, kamar ɗan’uwa na kusa ƙut da ƙut. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman falalar wannan kyakkyawar ɗabi’a da cewa, babu wanda yake dacewa da ita sai masu haƙurin gaske a kan cutarwa da musgunawar da ake yi musu, sai kuma mutum mai babban rabo, saboda ɗimbin alheri da ke cikin wannan kyakkyawan hali. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci hanyar magance sharrin Shaiɗan idan ya yi ƙoƙarin kautar da mutum daga wannan koyarwa mai matuƙar amfani, ya fara yi masa waswasi da miyagun saƙe-saƙe, to sai ya nemi tsarin Allah da kariyarsa daga sharrin Shaiɗan, domin Allah yana jin duk abin da yake faɗi, yana kuma sane da halin da yake ciki, saboda shi mai ji ne masani.

  37. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

    Open ayah 41:37

    Kuma dare da wuni da rana da wata suna daga ayoyinsa. Kada ku yi sujjada ga rana ko ga wata, ku yi sujjada ga Allah Wanda Ya halicce su idan har kun kasance Shi kaɗai kuke bauta wa.

  38. فَإِنِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فَٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ يُسَبِّحُونَ لَهُۥ بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَهُمۡ لَا يَسۡـَٔمُونَ۩

    Open ayah 41:38

    Idan kuwa sun yi girman kai, to waɗanda suke wurin Ubangijinka (mala’iku) suna yi masa tasbihi dare da rana, kuma su ba sa ƙosawa.

  39. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنَّكَ تَرَى ٱلۡأَرۡضَ خَٰشِعَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡۚ إِنَّ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاهَا لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

    Open ayah 41:39

    Yana kuma daga ayoyinsa cewa lalle za ka ga ƙasa a ƙeƙashe, to idan Mun saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura (ta fitar da tsirrai). Lalle wanda Ya raya ta Shi ne Mai raya matattu. Lalle Shi Mai iko ne a kan komai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin ƙarfafan hujjoji a kan cikar Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa, da cewa daga cikin manyan ayoyinsa masu nuna girmansa da Kaɗaitakarsa akwai jujjuyawar dare da yini, wannan ya zo wannan ya tafi, da rana da wata waɗanda rayuwar ɗan’adam a bayan ƙasa ba za ta yiwu ba sai da su. Duk waɗannan ayoyi ne masu nuna Allah ne kaɗai abin bauta, don haka ya kira mutane da cewa kada su yi wa rana da wata sujjada, sai dai su yi sujjada ga Allah shi kaɗai wanda ya halicce su in dai shi kaɗai suke bauta wa da gaske. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan mushirikai suka yi girman kai suka bijire wa bautar Allah shi kaɗai, suka ƙi yarda su yi masa sujjada a matsayinsa na mahaliccin komai, to su sani babu abin da za su cutar da Allah da shi, domin mala’iku da suke wurinsa suna yi masa tasbihi tare da gode masa ba dare ba rana, kuma ba sa ƙosawa daidai da ƙiftawar ido. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasu hujjoji na cikar Ƙudurarsa da ke bayan ƙasa, da cewa daga cikin manyan ayoyinsa masu nuna cikar Kaɗaitakarsa da kuma yiwuwar tashin alƙiyama, mutum zai ga ƙasa a ƙeƙashe babu tsiro a kanta, to amma da zarar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar mata da ruwan sama, sai a ga ta kumbura ta motsa ƙwayoyin da ke cikinta sun tsiro har sun ɗago sama. Lalle wanda ya iya raya wannan matacciyar ƙasa har ta fito da tsironta, to zai iya raya matattu don yi musu hisabi ranar alƙiyama, domin shi Allah mai iko ne a kan komai babu abin da yake gagarar sa a ƙasa ko a sama.

  40. إِنَّ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا لَا يَخۡفَوۡنَ عَلَيۡنَآۗ أَفَمَن يُلۡقَىٰ فِي ٱلنَّارِ خَيۡرٌ أَم مَّن يَأۡتِيٓ ءَامِنٗا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ ٱعۡمَلُواْ مَا شِئۡتُمۡ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ 

    Open ayah 41:40

    Lalle waɗanda suke fanɗara game da ayoyinmu, ba za su ɓoyu gare Mu ba. Yanzu wanda za a jefa shi a cikin wuta, shi ya fi ko kuma wanda zai zo yana amintacce a ranar alƙiyama? Ku aikata abin da kuka ga dama, lalle Shi Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.

  41. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلذِّكۡرِ لَمَّا جَآءَهُمۡۖ وَإِنَّهُۥ لَكِتَٰبٌ عَزِيزٞ

    Open ayah 41:41

    Lalle waɗanda suka kafirce wa Alƙur’ani lokacin da ya zo musu (tabbas Allah zai saka musu). Lalle kuma shi littafi ne mabuwayi.

  42. لَّا يَأۡتِيهِ ٱلۡبَٰطِلُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَلَا مِنۡ خَلۡفِهِۦۖ تَنزِيلٞ مِّنۡ حَكِيمٍ حَمِيدٖ

    Open ayah 41:42

    Ɓ</STRONG>arna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa; saukakke ne daga Mai hikima, Sha-yabo.

  43. مَّا يُقَالُ لَكَ إِلَّا مَا قَدۡ قِيلَ لِلرُّسُلِ مِن قَبۡلِكَۚ إِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغۡفِرَةٖ وَذُو عِقَابٍ أَلِيمٖ

    Open ayah 41:43

    Ba abin da ake faɗa maka sai irin abin da aka faɗa wa manzanni a gabaninka. Lalle Ubangijinka Mai gafara ne, kuma Mai uƙuba mai raɗaɗi ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi kafirai waɗanda suke fanɗare wa ayoyinsa, suna ƙaryata su, suna musunta su da jirkita ma’anoninsu ko canja lafuzansu, da cewa ba za su iya ɓoye masa ba, yana sane da duk abin da suke aikatawa kuma za su ga sakamakonsu, watau wutar Jahannama. Kuma su sani cewa ba za a gwada wanda za a jefa shi cikin wuta ranar alƙiyama da wanda zai zo yana amintacce ba. Sai kuma ya sake tsoratar da su da cewa su je su aikata duk abin da suka ga dama mai kyau ko mummuna, ya rage nasu, shi kuwa Allah mai ganin duk abin da suke aikatawa ne, kuma zai musu sakayya a kai. Waɗannan fanɗararru kuma masu kafirce wa Alƙur’ani lokacin da ya zo musu daga Allah, lalle azaba mai tsanani ta tabbata a kansu ranar alƙiyama. Sai kuma Allah ya ambaci wasu siffofi na Alƙur’ani guda uku: <b>Siffa ta ɗaya </b>, shi littafi ne mabuwayi, babu wanda zai iya jirkita shi ko canja shi. <b>Ta biyu </b>, ɓarna ba ta zuwa masa ta gabansa ko ma ta bayansa, watau babu wanda ya isa ya ƙara wani abu a cikinsa ko ya rage, dukkansa gaskiya ce tsantsa. <b>Ta uku </b>, saukakke ne daga Allah mai hikima Sha-yabo, watau duk abin da ya ƙunsa cike yake da hikima da maslaha ga halittun Allah, don haka babu makusa tare da shi, duk wani mai hankali zai yi sambarka da abin da ya zo cikinsa na shari’a da koyarwa.

  44. وَلَوۡ جَعَلۡنَٰهُ قُرۡءَانًا أَعۡجَمِيّٗا لَّقَالُواْ لَوۡلَا فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥٓۖ ءَا۬عۡجَمِيّٞ وَعَرَبِيّٞۗ قُلۡ هُوَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ هُدٗى وَشِفَآءٞۚ وَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ فِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٞ وَهُوَ عَلَيۡهِمۡ عَمًىۚ أُوْلَٰٓئِكَ يُنَادَوۡنَ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

    Open ayah 41:44

    Da Mun sanya shi Alƙur’ani Ba’ajame da tabbas za su ce: “Me ya hana a bayyana ayoyinsa? Yanzu (a ce Alƙur’ani) Ba’ajame (Annabi kuma) Balarabe?” Ka ce: “Shi ga waɗanda suka yi imani shiriya ne da waraka. Waɗanda kuwa ba sa yin imani akwai nauyi cikin kunnuwansu, shi kuma makanta ne a gare su.” Waɗannan (sun yi kama da waɗanda) ake kira daga wuri mai nisa.

  45. وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَٱخۡتُلِفَ فِيهِۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

    Open ayah 41:45

    Haƙiƙa Mun bai wa Musa Littafin (Attaura), sai aka yi saɓani a cikinsa, kuma ba don Kalma ta gabata daga Ubangijinka ba, tabbas da an yi hukunci a tsakaninsu. Lalle kuma su, tabbas suna cikin shakka mai sa kokwanto a game da shi.

  46. مَّنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَسَآءَ فَعَلَيۡهَاۗ وَمَا رَبُّكَ بِظَلَّٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ

    Open ayah 41:46

    Wanda ya yi aiki nagari, to kansa ya yi wa, wanda kuma ya munana, to a kan kansa ya yi wa. Ubangijnka ba Mai zaluntar bayi ba ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzo (ﷺ) game da ƙaryatawar da mutanensa suke yi masa da cewa, ba shi ne farau ba, domin duk abin da za a faɗa masa na ƙaryatawa ko izgili to an faɗi irinsa ga manzannin da suka gabace shi, don haka ya ci gaba da haƙuri, domin Ubangijinsa mai gafara ne ga bayinsa da suka tuba suka bar laifin da suke aikatawa, kuma mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya doge a kan aikata laifi ya ƙi tuba ga Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da amsa game da wani ruɗani da kafirai suke kawowa game da Alƙur’ani da cewa, wai me ya sa ba a saukar da shi da harshen Ajamanci ba, watau ba da Larabaci ba? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa da ya saukar da Alƙur’ani da wani harshe ba na Larabci ba, to da lalle kafirai za su ce: Me ya hana a bayyana ayoyinsa yadda za su fahimta? Za kuma su yi ta kwakwazon cewa yaya za a ce Manzo Balarabe littafin da aka saukar masa kuma Ba’ajame, watau wani harshe wanda ba Larabci ba? Don haka sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya toshe musu baki, ba abin da za su iya faɗa na suka ga Alƙur’ani ba tare da an gane ƙaryarsu ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, shi Alƙur’ani ai shiriya ne daga ɓata ga waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa, kuma waraka ne ga jahilcin da ke cikin zukata. Amma su waɗanda ba su yi imani da Allah ba akwai kurumta a kunnuwansu, don haka ba sa iya jin gaskiya su bi ta, kuma shi Alƙur’ani makanta ne a gare su ba za su fahimce shi ba, ba kuma za su ga shiriyarsa ba. Allah ya tabbatar da cewa su waɗannan mutane sun yi kama da waɗanda ake kiran su daga wani wuri mai nisa da ba za su iya jin sautin mai kiran su ba ballantana su amsa masa, watau sun zama waɗanda suka yi nisa ne ba sa jin kira, kamar yadda Bahaushe yake cewa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa su waɗannan masu ƙaryata Alƙur’ani ai ba su ne farau ba wajen bijire wa saƙon Allah; gabaninsu Allah ya bai wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) littafin Attaura, to amma sai mutanensa suka yi ta saɓani game da shi, wasu suka yi imani suka gaskata cewa daga Allah yake, wasu kuma suka kafirce masa suka ƙaryata shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ba don ya riga ya yi alƙawarin cewa a ranar lahira zai yi hukunci tsakanin bayinsa ba, da tuni ya bayyana mai gaskiya da maƙaryaci a tsakaninsu tun a nan duniya, ya karrama mai gaskiya ya kuma wulaƙantar da maƙaryaci ya gaggauto masa uƙuba. To amma kafirai a kowane lokaci suna cikin shakka mai jefa su cikin tantama da rashin sanin alƙibla. Sannan sai Allah ya bayyana sakamakon kowa gwargwadon aikinsa; wanda ya yi aiki nagari to kansa ya yi wa domin shi ne zai amfana da aikinsa, wanda kuma ya yi mummunan aiki to kansa ya cutar, domin shi Allah ba zai amfana da aikin wani ko ya cutu don aikin wani ba; zai saka wa kowa daidai da aikinsa, kuma ba zai zalunci bayinsa ba, ya rage wa wani ladan aikinsa nagari ko ya ƙara wa wani laifin da bai aikata ba.

  47. ۞إِلَيۡهِ يُرَدُّ عِلۡمُ ٱلسَّاعَةِۚ وَمَا تَخۡرُجُ مِن ثَمَرَٰتٖ مِّنۡ أَكۡمَامِهَا وَمَا تَحۡمِلُ مِنۡ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلۡمِهِۦۚ وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ أَيۡنَ شُرَكَآءِي قَالُوٓاْ ءَاذَنَّٰكَ مَا مِنَّا مِن شَهِيدٖ

    Open ayah 41:47

    Gare shi ne ake mayar da sanin lokacin alƙiyama. Kuma babu wasu ‘ya’yan itatuwa da suke fitowa daga kwansonsu, babu kuma wata mace da take ɗaukan ciki ko take haifewa sai da saninsa. Kuma a ranar da zai yi kiran su cewa: “Ina abokan tarayyar tawa?” Za su ce: “Mun sanar da Kai (a yau) babu wani mai yin shaida daga cikinmu.”

  48. وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَدۡعُونَ مِن قَبۡلُۖ وَظَنُّواْ مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٖ

    Open ayah 41:48

    Kuma abin da suka kasance suna bauta wa a da ya ɓace musu, suka kuma tabbatar ba su da wata matsera. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ranar da zai yi wa kowa sakayya a cikinta rana ce da babu wanda ya san lokacin zuwanta sai shi kaɗai, domin shi ne yake da faffaɗan ilimin sanin komai da komai na abin da ya wuce da abin da zai zo nan gaba, faffaɗan iliminsa ne ma ya sanya babu wasu ‘ya’yan itatuwa da za su fito daga kwansonsu, babu kuma wata mace da za ta ɗauki ciki ko ta haihu sai da saninsa. To amma abin mamaki, me ya sa mushirikai suke haɗa shi da wasu abokan tarayya waɗanda ba su san komai ba? Lalle za su gane kurensu ranar da zai yi kiran su ya tambaye su ina abokan tarayyar nasa da suke daidaita shi da su. A lokacin ne za su yi iƙirari da cewa a cikinsu babu wani da zai ba da shaidar cewa Allah yana da abokin tarayya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a ranar duk wani abu da kafirai suke bautarsa ya ɓace musu ɓat; ba su ma gan shi ba ballantana har ya cece su kamar yadda suke zato. Daga nan za su tabbatar da cewa ba su da wata matsera daga azabar Allah.

  49. لَّا يَسۡـَٔمُ ٱلۡإِنسَٰنُ مِن دُعَآءِ ٱلۡخَيۡرِ وَإِن مَّسَّهُ ٱلشَّرُّ فَيَـُٔوسٞ قَنُوطٞ

    Open ayah 41:49

    Mutum ba ya ƙosawa wajen roƙon alheri, idan kuwa wani sharri ya same shi, to sai ya zama mai tsananin ɗebe ƙauna.

  50. وَلَئِنۡ أَذَقۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنَّا مِنۢ بَعۡدِ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُ لَيَقُولَنَّ هَٰذَا لِي وَمَآ أَظُنُّ ٱلسَّاعَةَ قَآئِمَةٗ وَلَئِن رُّجِعۡتُ إِلَىٰ رَبِّيٓ إِنَّ لِي عِندَهُۥ لَلۡحُسۡنَىٰۚ فَلَنُنَبِّئَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِمَا عَمِلُواْ وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنۡ عَذَابٍ غَلِيظٖ 

    Open ayah 41:50

    Tabbas kuma idan Muka ɗanɗana masa wata rahama tamu bayan wata cuta da ta same shi, tabbas zai riƙa cewa: “Wannan nawa ne, kuma ba na tsammanin alƙiyama za ta tashi, kuma tabbas idan ma da za a mayar da ni zuwa ga Ubangijina, lalle zan zama mai samun mafi kyan sakamako a wurinsa.” To tabbas za Mu saka wa waɗanda suka kafirta da abin da suka aikata, kuma tabbas za Mu ɗanɗana musu azaba mai gwaɓi.

  51. وَإِذَآ أَنۡعَمۡنَا عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ أَعۡرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ فَذُو دُعَآءٍ عَرِيضٖ

    Open ayah 41:51

    Idan kuma Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya ja jikinsa nesa (daga tuna Allah), kuma idan sharri ya same shi, sai ya zama mai faffaɗar addu’a. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani mummunan hali na ɗan’adam na raki da butulci, da cewa shi ɗan’adam ba ya ƙosawa wajen roƙon alheri, kamar lafiya da dukiya da ‘ya’ya da sauran ni’imomi, to amma da zarar mummunan abu ya same shi, kamar talauci ko rashin lafiya, to sai ya zama mai yawan ɗebe ƙauna daga rahamar Allah, ya zaci wannan abu da ya same shi zai zama shi ne hallakarsa. Haka kuma idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɗanɗana masa wata rahama daga gare shi, kamar lafiya ko wadata, bayan wata cutar da ta same shi da farko, to zai riƙa cika baki yana cewa, wannan abu da aka ba shi da man can nasa ne, ya kuma cancanci a ba shi, sai ya butulce wa Allah ya shiga musunta tashin ƙiyama yana da’awar cewa ba za ta zo ba, kuma wai idan da gaske ne za ta zo, to sai ya tabbatar da cewa, a can ma sai ya sami ni’imar da ta fi ta duniya, domin a ganinsa ya cancanci haka, shi ya sa aka ba shi irinta a nan duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar masa da martani cewa tabbas zai ba wa kafirai labarin duk abin da suka aikata a nan duniya na kafirci da saɓonsa, kuma tabbas sai ya ɗanɗana musu azaba mai tsanani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana butulcin ɗan’adam bayan ni’ima da Allah ya yi masa, watau sai ya bijire wa ambaton Allah da godiya a gare shi, ya ja jikinsa nesa ya daina tuna Allah wanda shi ne ya ba shi wannan ni\'imar, don nuna girman kai da taƙadaranci. To amma kuma da zarar ya shiga wani mummunan hali na rashin lafiya ko talauci, to sai ya duƙufa ga addu’a yana roƙon Allah ya yaye masa bayan a da ya ƙi gode wa Allah ni’imomin da ya yi masa sannan kuma yanzu ya kasa haƙuri a kan jarrabar da Allah ya yi masa.

  52. قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كَانَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ ثُمَّ كَفَرۡتُم بِهِۦ مَنۡ أَضَلُّ مِمَّنۡ هُوَ فِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ

    Open ayah 41:52

    Ka ce: “Ku ba ni labari, idan (Alƙur’ani) ya kasance daga wajen Allah, sannan kuka kafirce masa, to wane ne ya fi ɓata fiye da wanda yake cikin saɓani mai nisa?”

  53. سَنُرِيهِمۡ ءَايَٰتِنَا فِي ٱلۡأٓفَاقِ وَفِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَهُمۡ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّۗ أَوَلَمۡ يَكۡفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

    Open ayah 41:53

    Ba da daɗewa ba za Mu nuna musu ayoyinmu a cikin nahiyoyi da kuma a kan kawunansu har sai sun gane cewa lalle shi (Alƙur’ani) gaskiya ne. Yanzu bai ishe ka ba game da Ubangijinka cewa Shi lalle Mai shaida ne a kan komai?

  54. أَلَآ إِنَّهُمۡ فِي مِرۡيَةٖ مِّن لِّقَآءِ رَبِّهِمۡۗ أَلَآ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَيۡءٖ مُّحِيطُۢ

    Open ayah 41:54

    Ku saurara, lalle su suna cikin kokwanto ne game da haɗuwa da Ubangijnsu. Ku saurara, lalle Shi Mai kewaye komai ne da saninsa. A ayoyi na ƙarshen wannan Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya tambayi kafirai masu ƙaryata Alƙur’ani cewa, idan Alƙur’ani ya zama tabbas daga Allah yake sannan su kuma suka kafirce masa, suka ƙaryata shi, to yaya suke tsammanin lamarinsu zai kasance? Sai Allah ya bayyana cewa babu wanda ya fi ɓata fiye da wanda yake jayayya da taurin kai game da gaskiya duk da cewa hujja ta bayyana a gare shi a fili. Sai kuma Allah ya tabbatar wa kafirai cewa zai nuna musu ayoyinsa a cikin nahiyoyin ƙasa daga garuruwan da zai ba wa Musulmi nasara su kama su. A kan kawunansu ma zai nuna musu ayoyinsa yayin da zai ba wa Musulmi nasarar cinye Makka da yaƙi, har su gane cewa Alƙur’ani gaskiya ne babu wani kokwanto a cikinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tambayar cewa, shin yanzu bai ishi mushirikai ba su gane cewa Alƙur’ani gaskiya ne saboda ganin cewa Allah ne (Mai tsarki da daukaka) da kansa ya ba da shaida a kan cewa shi gaskiya ne? To akwai shaidar da ta kai ta Allah ne? Ai tabbas da a ce su masu son gaskiya ne da shaidar Allah ta ishe su. Sai kuma Allah ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa, lalle mushirikai suna cikin kokwanto ne na gamuwa da Ubangijinsu ranar alƙiyama saboda ba su yarda da zuwanta ba, shi ya sa ma ba sa yi mata wani kyakkyawan tanadi, lalle kuma Allah ya kewaye komai da saninsa da ikonsa.