الشورى

Ash-Shura

Consultation · Surah 42 · Ayahs: 53 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. Ha Mim.

  2. عٓسٓقٓ

    Open ayah 42:2

    Ain Sin Ƙaf.

  3. كَذَٰلِكَ يُوحِيٓ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ ٱللَّهُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 42:3

    Kamar haka ne Allah Mabuwayi, Mai hikima Yake yi maka wahayi da kuma waɗanda suka gabace ka.

  4. لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ

    Open ayah 42:4

    Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa nasa ne; kuma Shi Maɗaukaki ne, Mai girma.

  5. تَكَادُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ يَتَفَطَّرۡنَ مِن فَوۡقِهِنَّۚ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يُسَبِّحُونَ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَيَسۡتَغۡفِرُونَ لِمَن فِي ٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

    Open ayah 42:5

    Sammai suna neman su tsattsage ta samansu (don girmansa). Mala’iku kuma suna yin tasbihi da yabon Ubangijinsu, suna kuma neman gafara ga waɗanda suke cikin ƙasa. Ku saurara, Lalle Allah Shi ne Mai gafara, Mai rahama.

  6. وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ ٱللَّهُ حَفِيظٌ عَلَيۡهِمۡ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٖ

    Open ayah 42:6

    Waɗanda kuwa suka riƙi wasu majiɓinta ba shi ba, Allah Mai kiyaye da su ne, kai kuma ba wakili ne ba a kansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori gabaninta da irin waɗannan haruffan. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara domin ƙarin bayani]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, wahayin da ya yi masa irinsa ne ya yi wa annabawan da suka gabace shi. Allah ne mabuwayi wanda ya fi ƙarfin kowa, babu mai iya ja da shi, kuma mai hikima cikin dukkan al’amuransa na halitta da na shari’a. Allah kuma ya bayyana cewa, duk abin da yake cikin sammai da ƙasa nasa ne, halittarsa ce, mulkinsa ne kuma bayinsa ne. Shi ne kuma Maɗaukaki da Zatinsa da siffofinsa da Ƙudurarsa da rinjayensa, mai girma ne, wanda saboda girmansa sammai suna neman su tsattsage daga saman ƙassai, suna kuma cike da mala’iku waɗanda suke tasbihi suna tsarkake Ubangijinsu tare da yabon sa da gode masa, don nuna girmamawarsu a gare shi. Suna kuma neman gafara daga Allah ga muminai da suke bayan ƙasa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa shi mai gafara ne ga bayinsa da suka tuba daga zunubansu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi masu bautar wasu ba shi ba, da cewa yana sane da duk abin da suke ciki, kuma yana ƙididdige ayyukansu, kuma shi zai yi musu sakayya a kansu, bai ɗora wa Manzonsa nauyin kula da ayyukansu ba, don haka ba wanda zai yi masa tambaya a kan ayyukansu sai dai a tambaye shi game da isar musu da saƙon Allah.

  7. وَكَذَٰلِكَ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا لِّتُنذِرَ أُمَّ ٱلۡقُرَىٰ وَمَنۡ حَوۡلَهَا وَتُنذِرَ يَوۡمَ ٱلۡجَمۡعِ لَا رَيۡبَ فِيهِۚ فَرِيقٞ فِي ٱلۡجَنَّةِ وَفَرِيقٞ فِي ٱلسَّعِيرِ

    Open ayah 42:7

    Kuma kamar haka Muka yiwo maka wahayin Alƙur’ani Balarabe, don ka gargaɗi mutanen Makka da waɗanda suke kewaye da ita (watau duniya baki ɗaya), ka kuma yi gargaɗin ranar taruwa da babu kokwanto a game da ita. Wata ƙungiya tana cikin Aljanna, wata ƙungiya kuma tana cikin wutar Sa’ira.

  8. وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَهُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن يُدۡخِلُ مَن يَشَآءُ فِي رَحۡمَتِهِۦۚ وَٱلظَّٰلِمُونَ مَا لَهُم مِّن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ

    Open ayah 42:8

    Da kuma Allah Ya ga dama da Ya sanya su al’umma ɗaya (watau a kan addini ɗaya), sai dai kuma Yana shigar da wanda Ya ga dama cikin rahamarsa. Azzalumai kuma ba su da wani majiɓinci ko wani mataimaki. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya yi wa Manzon Allah (ﷺ) wahayi kamar sauran annabawan da suka gabace shi, ya saukar masa da Alƙur’ani cikin harshen Larabci don al’ummarsa su fahimce shi, ya kuma yi musu gargaɗi da shi, su da sauran garuruwan Larabawa da suke kewaye da Makka da sauran mutanen duniya baki ɗaya. Ya gargaɗe su game da ranar alƙiyama, ranar da Allah zai tattara halittun farko da na ƙarshe a farfajiya guda ɗaya domin yi musu hisabi da sakamako. Wannan ranar babu makawa sai ta zo, kuma mutane za su kasu gida biyu a cikinta, wasu su tafi Aljanna su ne muminai; wasu kuma su tafi wuta su ne kafirai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya fito gare mu yana ɗauke da wasu littattafai biyu a hannunsa sai ya ce: “Shin ko kun san waɗanne littattafai ne waɗannan?” Sai muka ce: “A’a, sai in ka faɗa mana ya Manzon Allah.” Sai ya ce dangane da wanda yake a hannunsa na dama: “Wannan littafi ne daga Ubangijin halittu yana ɗauke da sunayen ‘yan Aljanna da sunayen iyayensu da ƙabilunsu, an tattara su duka har na ƙarshensu, ba za a ƙara su ba, ba kuma za a rage su ba har abada.” Sannan dangane da na hannun hagunsa sai ya ce: “Wannan littafin ‘yan wuta ne da sunayensu da sunayen iyayensu da ƙabilunsu, an tattara su duka har zuwa na ƙarshensu, ba za a ƙara su ba, ba kuma za a rage su ba har abada.” Sai sahabbai suka ce: “To tunda abin haka yake don mene ne muke yin aiki idan har an riga an gama yanke komai?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce musu: “Ku daidaita ayyukanku kuma ku kwatanta bakin gwargwado, domin ɗan Aljanna zai cika ne da aikin \'yan Aljanna, ko ma wane aiki ya aikata (a baya), shi ma kuma ɗan wuta zai cika ne da aikin ‘yan wuta, ko ma wane irin aiki ya aikata (a baya).” Sannan sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi damƙa da hannunsa ya ce: “Allah mai girma da buwaya ya gama komai game da bayinsa.” Sannan sai ya watsa damƙar hannunsa na dama ya ce: “Wata ƙungiyar tana cikin Aljanna.” Ya kuma watsa na hagu ya ce: “Wata ƙungiya kuma tana cikin wuta.” [Ahmad #6563 da Tirmizi #2141]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa dukkan al’amuran bayi suna hannunsa; da ya ga dama da ya mayar da mutane dukansu sun zama al’umma guda a kan addini ɗaya, watau Musulunci, don ya shigar da su gaba ɗayansu gidan Aljanna. Sai dai hikimarsa ta riga ta hukunta cewa zai shigar da wanda ya ga dama cikin Musulunci don ya shigar da shi gidan Aljanna, su kuma waɗanda suka zalunci kawunansu da kafirci da saɓon Allah, su haɗu da azabarsa, don kuwa ba su da wani majiɓinci da zai jiɓinci al’amuransu ko ya kuɓutar da su daga azabar Allah.

  9. أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَۖ فَٱللَّهُ هُوَ ٱلۡوَلِيُّ وَهُوَ يُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 42:9

    Ko dai sun riƙi wasu majiɓinta ne ba Shi ba. To Allah Shi ne Majiɓinci, Shi ne kuma Yake raya matattu, Shi kuma Mai iko ne a kan komai.

  10. وَمَا ٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِيهِ مِن شَيۡءٖ فَحُكۡمُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبِّي عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ أُنِيبُ 

    Open ayah 42:10

    Kuma duk wani abu da kuka yi saɓani a kansa, to sai ku mai da hukuncinsa ga Allah. Wannan Shi ne Allah Ubangijina, gare Shi kawai na dogara, kuma wurinsa kawai nake mayar da al’amarina.

  11. فَاطِرُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ جَعَلَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَمِنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ أَزۡوَٰجٗا يَذۡرَؤُكُمۡ فِيهِۚ لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

    Open ayah 42:11

    (Shi ne) Mahaliccin sammai da ƙasa. Ya halitta muku mataye daga jinsinku, daga dabbobi ma (Ya halicce su) maza da mata; Yana yaɗa ku ta hanyarsa (haɗin jinsin biyu). Babu wani abu da ya yi kama da Shi; kuma Shi Mai ji ne, Mai gani.

  12. لَهُۥ مَقَالِيدُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

    Open ayah 42:12

    Mabuɗan taskokin sammai da ƙasa nasa ne; Yana shimfiɗa arziki ga wanda Ya ga dama, yana kuma ƙuntatawa. Lalle shi Masanin komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa mushirikai sun rungumi wasu gumaka suna bautar su ba Allah ba, alhali kuwa Allah shi ne abin bauta na gaskiya; duk wani abin bauta na daban to ba zai amfanar ko ya cutar ba. Allah ne kuma mai raya matattu domin yi musu hisabi da sakamako, shi ne kuma mai iko a kan komai, don haka shi kaɗai ya cancanci a bautawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya umarci muminai da cewa duk wani abu da za su yi saɓani a kansa wanda ya danganci shika-shikan addini ko rassansa, to su mayar da hukuncinsa ga Allah, watau su koma zuwa ga littafinsa Alƙur’ani da sunnar Manzonsa (ﷺ). Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya tabbatar musu cewa, wanda ya siffantu da waɗannan siffofi shi ne kaɗai Ubangijinsa, kuma a gare shi ya dogara cikin dukkan al’amuransa, kuma wurinsa yake komawa ya tuba, domin ya yafe masa laifukansa. Ya kuma tabbatar musu da cewa, Allah shi ne mahaliccin sammai da ƙasa ba tare da ya kwaikwaya a wurin wani ba, kuma shi ne ya halitta wa mutane matayensu daga jinsinsu, su ma dabbobin ni’ima, raƙuma da shanu da tumakai da awakai, ya halitta musu matansu daga jinsinsu. Yana kuma halittar mutane ta hanyar auratayyar da ya ƙaddara a tsakanin maza da mata. Kuma ya arzuta su da naman ci da nonon sha daga dabbobin na ni’ima. Babu wani abu da ya yi kama da shi daga cikin halittunsa; shi kuma yana jin duk maganganunsu, yana ganin duk ayyukansu, babu abin da yake ɓuya a gare shi, zai kuma yi wa kowa sakayya a kan ayyukansa kyawawa ko munana. Sannan ya bayyana cewa mabuɗan taskokin sama da na ƙasa duka nasa ne shi kaɗai, yana yalwata arzikinsa ga wanda ya ga dama cikin bayinsa, don ya jarraba shi ya tabbatar cewa zai gode masa ko zai yi butulci. Yana kuma ƙuntata wa wanda ya ga dama, don shi ma ya jarraba shi ya ga shin zai yi haƙuri ko kuma zai yi fushi da Ƙaddarar Allah. Lalle shi Allah masanin komai ne, shi ya fi kowa sanin maslahar halittarsa.

  13. ۞شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِۦ نُوحٗا وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَمَا وَصَّيۡنَا بِهِۦٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰٓۖ أَنۡ أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِۚ كَبُرَ عَلَى ٱلۡمُشۡرِكِينَ مَا تَدۡعُوهُمۡ إِلَيۡهِۚ ٱللَّهُ يَجۡتَبِيٓ إِلَيۡهِ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَن يُنِيبُ

    Open ayah 42:13

    Ya shar’anta muku (irin) abin da Ya yi wa Nuhu wahayi da shi na addini, da kuma wanda Muka yiwo maka wahayinsa, da kuma abin da Muka yi wa Ibrahimu da Musa da Isa wasiyya da shi cewa: “Ku tsayar da addini, kuma kada ku rarraba a cikinsa.” Abin da kake kiran kafirai zuwa gare shi ya yi musu nauyi. Allah Yana zaɓar wanda Ya ga dama zuwa gare shi (addini) Yana kuma shiryar da wanda Ya mayar da al’amarinsa zuwa gare Shi.

  14. وَمَا تَفَرَّقُوٓاْ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى لَّقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ أُورِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

    Open ayah 42:14

    Ba su kuma rarrabu ba sai bayan ilimi ya zo musu don zalunci da ke tsakaninsu. Ba don kalmar da ta riga ta gabata daga Ubangijinka ba (ta jinkirta musu) zuwa ga wani lokaci ƙayyadajje, da lalle an yi hukunci tsakaninsu. Kuma lalle waɗanda aka gadar wa da littafi a bayansu lallai suna cikin shakka mai sa kokwanto game da shi (Annabi Muhammadu). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, addinin Musulunci da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi irin addinin da annabawan Allah suka zo da shi ne, domin ya shar’anta wa wannan al’umma irin abin da ya umarci Annabi Nuhu da shi da abin da ya yi wa Manzonsa Muhammadu (ﷺ) wahayinsa da abin da ya umarci Annabi Ibrahimu da Annabi Musa da Annabi Isa su isar da shi su kuma yi aiki da shi. Abin da umarnin ya ƙunsa a dunƙule kuwa shi ne su tsayar da addini su kiyaye koyarwarsa, tushensa da ressansa, kada kuma su rarraba a kansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa abin da yake kiran mushirikai zuwa gare shi na Tauhidi da aiki na ƙwarai da ƙaurace wa bautar wanin Allah ya yi musu girma da wahala sosai, domin suna ganin ba za su iya barin bautar gumakansu su bauta wa Allah Ɗaya ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa shiriya da ɓata duka suna hannunsa, shi ne yake zaɓar wanda ya ga dama daga bayinsa ya shiryar da shi zuwa ga bautarsa da ɗa’arsa, ya kuma shiryar da duk wanda yake komawa gare shi da tuba daga zunubansa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin da ya jawo rarrabuwar mutane bayan ya umarce su da haɗa kansu, da cewa kafirai da mushirikai ba su rarrabu ba sai bayan da hujja ta tabbata a kansu da aiko Annabi (ﷺ) zuwa gare su, kuma sun rarrabu ne saboda zalunci da rashin jituwa a tsakaninsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ba don ya riga ya zartar a cikin iliminsa cewa ba zai yi musu azaba yanzu ba, zai jinkirta musu har zuwa wani ƙayyadajjen lokaci, shi ne ranar alƙiyama, to da tuni ya yi hukunci a tsakaninsu, ya gaggauto musu da azaba saboda kafircinsu da ƙaryatawarsu ga manzanninsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa Yahudawa da aka ba su Attaura da Nasara da aka ba su Linjila tun bayan wucewar kakanninsu suna nan a kan tababa da shakka game da Alƙur’ani da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi, saboda haka suka ƙaryata shi suka kafirce masa.

  15. فَلِذَٰلِكَ فَٱدۡعُۖ وَٱسۡتَقِمۡ كَمَآ أُمِرۡتَۖ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡۖ وَقُلۡ ءَامَنتُ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِن كِتَٰبٖۖ وَأُمِرۡتُ لِأَعۡدِلَ بَيۡنَكُمُۖ ٱللَّهُ رَبُّنَا وَرَبُّكُمۡۖ لَنَآ أَعۡمَٰلُنَا وَلَكُمۡ أَعۡمَٰلُكُمۡۖ لَا حُجَّةَ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمُۖ ٱللَّهُ يَجۡمَعُ بَيۡنَنَاۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 42:15

    Saboda wannan sai ka yi kira (zuwa ga addinin Allah), kuma ka tsaya kyam kamar yadda aka umarce ka, kada ka bi son ransu; ka kuma ce: “Na yi imani da abin da Allah Ya saukar na littattafai; an kuma umarce ni da yin adalci a tsakaninku; Allah ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku; (sakamakon) ayyukanmu namu ne, ku ma (sakamakon) ayyukanku naku ne; babu wata jayayya a tsakaninmu da ku; Allah zai tara mu; kuma zuwa gare Shi ne kaɗai makoma. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya yi kira zuwa ga bin miƙaƙƙen addini, ya kuma tsaya kyam a kansa kamar yadda Allah ya umarce shi, kada ya bi soye-soyen zukatan kafirai. Idan kuma suna jayayya da shi ne to ya faɗa musu cewa, shi ya yi imani da Allah ya kuma yi imani da littattafan da ya saukar wa manzanninsa, kuma Allah ya umarce shi da ya yi musu hukunci da adalci. Ya kuma tabbatar musu cewa wanda yake bauta wa shi ne Ubangijinsu baki ɗaya, kuma su sani cewa, kowa yana tare da sakamakon ayyukansa kyawawa ko munana, babu wata sauran jayayya a tsakaninsu bayan hujja ta riga ta bayyana a fili, hanyar gaskiya kuma ta fito sarari. Allah ne kuma zai haɗa su baki ɗaya a ranar alƙiyama, domin zuwa gare shi makomar kowa take, inda zai yi wa kowa sakayya gwargwadon irin aikinsa na alheri ko na sharri, a gane mai gaskiya da maƙaryaci.

  16. وَٱلَّذِينَ يُحَآجُّونَ فِي ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا ٱسۡتُجِيبَ لَهُۥ حُجَّتُهُمۡ دَاحِضَةٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَعَلَيۡهِمۡ غَضَبٞ وَلَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٌ

    Open ayah 42:16

    Waɗanda kuma suke jayayya game da Allah bayan an amsa masa (kiransa), to hujjarsu ɓatacciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma fushi ya hau kansu, kuma suna da azaba mai tsanani.

  17. ٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ وَٱلۡمِيزَانَۗ وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّ ٱلسَّاعَةَ قَرِيبٞ

    Open ayah 42:17

    Allah ne Ya saukar da Littafi da gaskiya da kuma adalci. Me yake sanar da kai cewa ko alƙiyama kusa take.

  18. يَسۡتَعۡجِلُ بِهَا ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِهَاۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مُشۡفِقُونَ مِنۡهَا وَيَعۡلَمُونَ أَنَّهَا ٱلۡحَقُّۗ أَلَآ إِنَّ ٱلَّذِينَ يُمَارُونَ فِي ٱلسَّاعَةِ لَفِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٍ

    Open ayah 42:18

    Waɗanda ba sa yin imani da ita suna gaggauto da ita; waɗanda kuwa suka yi imani a tsorace suke da ita, kuma suna sane da cewa ita gaskiya ce. Ku saurara, lalle waɗanda suke jayayya game da tashin alƙiyama tabbas suna cikin ɓata mai nisa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suke dogaro da ɓatacciyar hujja suna jayayya game da addinin Allah, watau Musulunci, bayan kuwa mutane sun amsa kiransa sun shiga addinin Allah ƙungiya-ƙungiya, to masu wannan jayayyar hujjarsu ta banza ce a wurin Allah da sauran muminai; ba ta da wani tasiri na a zo a gani, sannan fushin Allah ya tabbata a kansu saboda kafircinsu da ƙin gaskiyarsu, kuma wata azaba mai tsanani tana nan tana jiran su a ranar alƙiyama. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ingantacciyar hujja da Musulmi yake riƙe da ita, watau Alƙur’ani, da cewa Allah ne wanda ya saukar da Alƙur’ani, babu wata tantama game da shi, ya kuma saukar da adalci domin yi wa mutane hukunci da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa ranar alƙiyama da kafirai suke ƙaryata zuwanta kusa take, domin duk wani abu mai zuwa to kusa yake. To amma duk da haka sai waɗanda ba su yi imani da ita ba su riƙa gaggauto ta, domin ba su ma yarda akwai ta ba balle a yi hisabi da sakamako a cikinta. Amma waɗanda suka yi imani da Allah suna cike da tsoron ta domin idan ta zo suna tsoron makomarsu, amma sun tabbata ba sa kokwanto cewa ita gaskiya ce. Sannan Allah ya tabbatar da cewa, masu jayayya game da ranar alƙiyama suna ƙaryata zuwanta, ba shakka sun tabbata cikin ɓata mai nisa.

  19. ٱللَّهُ لَطِيفُۢ بِعِبَادِهِۦ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُۖ وَهُوَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡعَزِيزُ

    Open ayah 42:19

    Allah Mai tausasa wa bayinsa ne, Yana arzuta wanda ya ga dama; kuma Shi Ƙaƙƙarfa ne, Mabuwayi.

  20. مَن كَانَ يُرِيدُ حَرۡثَ ٱلۡأٓخِرَةِ نَزِدۡ لَهُۥ فِي حَرۡثِهِۦۖ وَمَن كَانَ يُرِيدُ حَرۡثَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِن نَّصِيبٍ 

    Open ayah 42:20

    Wanda ya kasance yana nufin ladan lahira to za Mu ƙara masa a kan ladansa; wanda kuwa ya kasance yana nufin ladan duniya to za Mu ba shi (wani abu) daga gare ta, kuma ba shi da wani rabo a lahira.

  21. أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَٰٓؤُاْ شَرَعُواْ لَهُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا لَمۡ يَأۡذَنۢ بِهِ ٱللَّهُۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةُ ٱلۡفَصۡلِ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 42:21

    Ko dai suna da wasu abokan tarayya ne da suka shar’anta musu wani abu na addini wanda Allah bai yi izinin yin sa ba? Ba don kalmar yin hukunci (a lahira) ta tabbata ba, da lalle an yi hukunci a tsakaninsu (tun a duniya). Lalle kuma azzalumai suna da azaba mai raɗaɗi.

  22. تَرَى ٱلظَّٰلِمِينَ مُشۡفِقِينَ مِمَّا كَسَبُواْ وَهُوَ وَاقِعُۢ بِهِمۡۗ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فِي رَوۡضَاتِ ٱلۡجَنَّاتِۖ لَهُم مَّا يَشَآءُونَ عِندَ رَبِّهِمۡۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَضۡلُ ٱلۡكَبِيرُ

    Open ayah 42:22

    Za ka ga azzalumai suna tsoron sakamakon abin da suka aikata, alhali kuwa ga shi zai faɗa musu. Waɗanda kuwa suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to suna cikin dausayoyin gidajen Aljanna; suna samun duk abin da suka ga dama a wurin Ubangijinsu. Wannan ita ce falala mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tausasawarsa ga bayinsa gaba ɗayansu, muminansu da kafiransu, yana yalwata arzikinsa ga wanda ya ga dama, ya ƙuntata wa wanda ya ga dama, duk dai cikin rahamarsa, ko da kuwa wasu a zahiri suna ganin ba haka ba ne, domin shi ne ƙaƙƙarfa wanda babu mai rinjayar sa, mabuwayi mai azabtar da maƙiyansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk wanda ya kasance yana nufin samun ladan lahira da ayyukansa nagari, to zai ninninka masa ladansa, domin duk kyakkyawan aiki ɗaya yana ninninka ladansa har sau goma har zuwa sau ɗari bakwai, har zuwa ninkin-ba-ninkin. Duk kuma wanda ya kasance duniya kaɗai yake nufi da ayyukansa, to shi ma zai ba shi gwargwadon rabonsa a nan duniya, amma kuma a lahira ba shi da sauran wani rabo, domin ya fifita duniya a kan lahira. An karɓo daga Ubayyu ɗan Ka’ab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ka yi wa wannan al’umma albishir na haske da ɗaukaka da nasara da kafuwa a bayan ƙasa. Duk wanda daga cikinsu ya yi aikin lahira domin duniya, to ba ya da wani rabo a lahira.” [Ahmad #21222 da Ibn Hibban #405]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya karanta faɗar Allah: “Wanda ya kasance yana nufin ladan lahira, to za mu ƙara masa a kan ladansa, wanda kuwa ya kasance yana nufin ladan duniya, to za mu ba shi daga gare ta, kuma ba shi da wani rabo a lahira.” Sannan Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah mai girma da buwaya yana cewa: “Ya kai ɗan’adam, ka ba da cikakken lokacinka domin bautata, zan cika maka ƙirjinka da wadata, zan kuma toshe maka talaucinka, idan ba haka ba kuwa zan cika ƙirjinka da shagaltuwa, ba kuma zan toshe talaucinka ba.” [Al-Hakim #3657]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi mushirikai da suke ƙaryata Manzonsa suna yin shirka da Allah cewa, shin suna da wasu alloli ne masu tarayya da Allah waɗanda suka shar’anta musu bin wani addini daban wanda Allah bai yi musu izinin bin sa ba, don haka suke yi masa shirka suke kuma haramta abin da ya halatta ko su halatta abin da ya haramta? Watau haƙiƙa ba abin da suke bi na shari’ar Allah in ban da soye-soyen zukatan shaiɗanunsu na aljanu da mutane masu haramta musu abin da Allah ya halatta, su kuma halatta musu abin da Allah ya haramta, su riƙa ingiza su cikin saɓon Allah da bijire wa bautarsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa ba don ya riga ya sanya wani ƙayyadajjen lokaci na yin hukunci tsakaninsu ba, watau ranar alƙiyama, to da tuni ya zartar musu da hukuncinsa tun a nan duniya. To amma su sani cewa lalle azzalumai waɗanda suka cuci kawunansu da aikata shirka da saɓon Allah suna da azaba mai raɗaɗi da take jiran su ranar alƙiyama. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda azzalumai masu shirka da saɓon Allah da kauce wa dokokinsa za su sami kansu a ranar alƙiyama, ranar da za a gan su cike da tsoron uƙubar da za ta same su saboda laifukansu, kuma ba makawa sai uƙubar ta auka musu, domin tsoronsu ba zai amfane su da komai ba a ranar. To amma waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa suka yi kyawawan ayyuka, to su kam suna cikin lambunan gidajen Aljanna suna morewarsu, duk abin da suka buƙata a wajen Ubangijinsu na dangogin ni’ima za su same shi, ba kuma mai yankewa ba. Wannan ita ce falala mai girma wadda babu irinta.

  23. ذَٰلِكَ ٱلَّذِي يُبَشِّرُ ٱللَّهُ عِبَادَهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِۗ قُل لَّآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًا إِلَّا ٱلۡمَوَدَّةَ فِي ٱلۡقُرۡبَىٰۗ وَمَن يَقۡتَرِفۡ حَسَنَةٗ نَّزِدۡ لَهُۥ فِيهَا حُسۡنًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ شَكُورٌ

    Open ayah 42:23

    Wannan fa shi ne abin da Allah Yake yin albishir da shi ga bayinsa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari. Ka ce: “Ba na tambayar ku wani lada a kansa (isar da saƙon), sai dai kawai soyayya ta zumunta”. Duk wanda ya aikata wani aiki kyakkyawa za Mu ƙara masa kyakkyawan sakamako a kansa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai godiya.

  24. أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗاۖ فَإِن يَشَإِ ٱللَّهُ يَخۡتِمۡ عَلَىٰ قَلۡبِكَۗ وَيَمۡحُ ٱللَّهُ ٱلۡبَٰطِلَ وَيُحِقُّ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

    Open ayah 42:24

    A’a, suna dai cewa ya ƙaga wa Allah ƙarya ne; to da Allah Ya ga dama da sai Ya rufe zuciyarka. Allah kuma Yana shafe ƙarya Yana kuma tabbatar da gaskiya da kalmominsa. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin zukata ne.

  25. وَهُوَ ٱلَّذِي يَقۡبَلُ ٱلتَّوۡبَةَ عَنۡ عِبَادِهِۦ وَيَعۡفُواْ عَنِ ٱلسَّيِّـَٔاتِ وَيَعۡلَمُ مَا تَفۡعَلُونَ

    Open ayah 42:25

    Shi ne kuma wanda Yake karɓar tuba daga bayinsa, Yake kuma yin afuwa game da munanan (ayyuka), Yana kuma sane da abin da kuke aikatawa.

  26. وَيَسۡتَجِيبُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضۡلِهِۦۚ وَٱلۡكَٰفِرُونَ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞ

    Open ayah 42:26

    Kuma Yana amsa wa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, Yana kuma ƙara musu daga falalarsa. Kafirai kuwa suna da azaba mai tsanani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk abubuwan da ya ambata a baya na ni’imomin Aljanna wani babban albishir ne yake yi wa bayinsa waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa, suka kuma yi aiki nagari. Haka kuma ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya shaida wa mushirikan Ƙuraishawa cewa shi fa ba ya neman wani lada a kan isar musu da saƙo na gaskiya, in ban da abu ɗaya wanda kuma su zai amfana, watau su ƙaunace shi saboda kusancin zumunta da ke tsakaninsa da su. An tambayi Abdullahi ɗan Abbas dangane da wannan, sai Sa’idu ɗan Jubair ya ce: “Ana nufin makusanta na iyalan Muhammadu (ﷺ).” Sai Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce masa: “Ka yi garaje, yadda abin yake, shi Annabi (ﷺ) babu wani gida daga gidajen Ƙuraishawa face yana da dangantaka ta zumunci da shi, shi ne ya ce: “Sai dai ku sadar da zumuncin da ke tsakanina da ku.” [Bukhari #4818]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk wanda ya yi kyakkyawan aiki to zai ninninka masa ladansa, duk kyakkyawan aiki ɗaya kuma zai ninka masa shi goma har fiye da haka. Allah kuma tabbas mai yawan gafarta zunuban bayinsa ne masu tuba, kuma mai yawan godiya ne a kan kyawawan ayyukan da suka yi dominsa. Yana daga cikin ƙarairayin kafirai da suke cewa Annabi Muhammadu (ﷺ) shi ne ya ƙirƙiri Alƙur’ani ba wahayinsa Allah ya yi masa ba. To Allah ya ƙaryata su ya kuma mayar musu da martani a kan haka da cewa, da a ce zuciyarsa za ta riya masa cewa ya ƙirƙiri Alƙur’ani da kansa ya jingina wa Allah, to lalle da Allah ya toshe masa zuciyarsa yadda ba zai iya ƙara fahimtar komai ba, kuma duk wani alheri ya ƙi shiga cikinta; da kuma ya shafe wannan ƙaryar da zai ƙirƙira ya wanzar da gaskiya. To tunda hakan bai faru ba, wannan ya nuna Annabi (ﷺ) gaskiya yake faɗa cewa Allah ne yake yi masa wahayin Alƙur’ani. Lalle shi Allah masanin abin da yake cikin zukata ne, babu abin da yake ɓuya a gare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana baiwar da yake yi wa bayinsa idan sun yi laifi sun tuba, da cewa, shi ne yake karɓar tubarsu ya yafe musu munanan laifukansu, yana kuma sane da duk abin da suke aikatawa, zai kuma yi musu sakayya a kai. Haka kuma yana amsa addu’ar waɗanda suka yi imani da shi da kuma manzanninsa, yana ma ba su har abin da ba su roƙe shi ba daga falalarsa. Su kuma waɗanda suka kafirce wa Allah da manzanninsa suna da wata azaba mai tsanani da take jiran su a ranar alƙiyama.

  27. ۞وَلَوۡ بَسَطَ ٱللَّهُ ٱلرِّزۡقَ لِعِبَادِهِۦ لَبَغَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِن يُنَزِّلُ بِقَدَرٖ مَّا يَشَآءُۚ إِنَّهُۥ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرُۢ بَصِيرٞ

    Open ayah 42:27

    Da kuma Allah Ya shimfiɗa wa bayinsa arziki to da sun yi tsaurin kai a bayan ƙasa, sai dai kuma Yana saukarwa ne daidai gwargwado yadda Ya ga dama. Lalle Shi Masani ne game da bayinsa, Mai ganin (ayyukansu).

  28. وَهُوَ ٱلَّذِي يُنَزِّلُ ٱلۡغَيۡثَ مِنۢ بَعۡدِ مَا قَنَطُواْ وَيَنشُرُ رَحۡمَتَهُۥۚ وَهُوَ ٱلۡوَلِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

    Open ayah 42:28

    Shi ne kuma Yake saukar da ruwan sama bayan sun ɗebe ƙauna, Ya kuma yaɗa rahamarsa. Kuma Shi ne Majiɓincin al’amura, Sha-yabo. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hikimarsa ne wajen raba arzikinsa ga bayinsa yadda zai amfane su, da cewa da zai yalwata wa kowa arziki, ya ba wa kowa fiye da buƙatarsa, to da yin haka ya haifar da ɓarna a bayan ƙasa, domin mutane za su riƙa yi wa junansu ɗagawa da ji-ji-da-kai, babu mai sauraron wani. Sai dai Allah yana saukar da arzikinsa ne daidai gwargwadon yadda zai amfani mutane ba za su lalace ba gaba ɗayansu, ya wadata wanda ya ga dama, ya talauta wanda ya ga talaucin ne ya fi dacewa da shi, domin shi ne mai cikakken sanin halayen bayinsa, mai ganin duk abin da suke ciki, don haka yake gudanar da komai cikin hikima. Sai kuma ya bayyana arzikin ruwan sama da yake saukar wa bayinsa bayan sun ɗebe ƙauna, sai ya wadata shi ko’ina, ƙasa ta fitar da shuke-shukenta, daga nan rahamar Allah ta wanzu ko’ina. Allah yana yin haka ne domin shi ne majiɓincin al’amuran bayinsa, sha-yabo a cikin kowane yanayi.

  29. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَثَّ فِيهِمَا مِن دَآبَّةٖۚ وَهُوَ عَلَىٰ جَمۡعِهِمۡ إِذَا يَشَآءُ قَدِيرٞ

    Open ayah 42:29

    Yana kuma daga cikin ayoyinsa halittar sammai da ƙasa da kuma dabbobin da Ya yaɗa a cikinsu. Kuma shi Mai iko ne a kan Ya tara su idan Ya ga dama.

  30. وَمَآ أَصَٰبَكُم مِّن مُّصِيبَةٖ فَبِمَا كَسَبَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَيَعۡفُواْ عَن كَثِيرٖ 

    Open ayah 42:30

    Abin da kuma ya same ku na wata masifa, to saboda abin da hannayenku ne suka tsuwurwurta, Yana kuma yin afuwa ga wasu (laifuka) masu yawa.

  31. وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ

    Open ayah 42:31

    Kuma ku ba za ku gagara ba a bayan ƙasa; kuma ba ku da wani majiɓinci ko mataimaki in ba Allah ba.

  32. وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلۡجَوَارِ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ

    Open ayah 42:32

    Daga cikin ayoyinsa kuma akwai jiragen ruwa masu gudu a cikin kogi kamar duwatsu.

  33. إِن يَشَأۡ يُسۡكِنِ ٱلرِّيحَ فَيَظۡلَلۡنَ رَوَاكِدَ عَلَىٰ ظَهۡرِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٍ

    Open ayah 42:33

    Idan da Ya ga dama da sai Ya kwantar da iska sai (jiragen) su zama a tsaye cak a kan (kogin). Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga duk wani mai yawan haƙuri, mai yawan godiya.

  34. أَوۡ يُوبِقۡهُنَّ بِمَا كَسَبُواْ وَيَعۡفُ عَن كَثِيرٖ

    Open ayah 42:34

    Ko kuma Ya nutsar da su saboda (munanan ayyukan) da suka aikata. Ko kuma ya yi afuwa ga wasu (laifuka) masu yawa.

  35. وَيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٖ

    Open ayah 42:35

    Kuma waɗanda suke jayayya game da ayoyinmu sun san da cewa ba su da wata matsera. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu hujjoji masu tabbatar da cikar Ƙudurarsa da yalwar ikonsa. Daga cikinsu akwai halittar sammai da ƙasa da dangogin halittu masu ban mamaki da ya sanya a cikinsu, sannan kuma duk sanda ya ga damar ya tara su don yi musu hisabi da sakamako shi mai iko ne a kan haka, babu abin da zai gagare shi, kamar yadda a karon farko halittarsu ba ta gagare shi ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutane illar saɓon sa inda ya shaida musu cewa, babu wata musifa da za ta same su a kawunansu ko a dukiyoyinsu, sai don sakamakon abin da suka aikata ne na saɓon Allah da rashin bin dokokinsa, kuma ma yana yafe musu wasu laifuka da dama, ba ya kama su da su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutane cewa ba za su gagare shi su tsere masa ba idan ya yi nufin azabtar da su, kuma ba su da wani mai jiɓintar lamarinsu ko mai taimakon su ya kautar musu da azabar Allah in ba shi ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wata babbar aya mai nuna cikar Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa da gaskiyar alƙawarinsa, su ne samar da jiragen ruwa manya-manya masu kamar duwatsu, suna gudu a cikin kogi maƙare da mutane da kayayyakinsu, daga wani yanki na duniya zuwa wani. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan ya ga dama sai ya kwantar da iskar da take tafiyar da su, sai su tsaya cak a cikin kogi ba sa motsi. Lalle game da wannan abu da aka ambata akwai ayoyi masu nuna girman Ƙudurar Allah ga duk wani mai yawan haƙuri mai yawan godiya a kan ni’imomin Allah. Ko kuma idan Allah ya ga damar hallakar da su sai ya aiko musu guguwa mai ƙarfi ta hallakar da mutanen cikinsu saboda laifukan da suka aikata, ko kuma idan ya ga dama sai yafe musu wasu laifukan masu yawa ba tare da ya kama su da su ba. Kuma yana yin haka ne don waɗanda suke jayayya game da ayoyinsa su sani cewa ba su da wata matsera da za su guje wa hallaka idan ya so hallaka su, don haka su tuba su bar bautar wani abu ba Allah ba.

  36. فَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَيۡءٖ فَمَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

    Open ayah 42:36

    Sannan duk wani abu da aka ba ku to jin daɗin rayuwar duniya ne; kuma abin da yake wurin Allah shi ya fi alheri ya kuma fi wanzuwa ga waɗanda suka yi imani suke kuma dogara ga Ubangijinsu.

  37. وَٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ وَإِذَا مَا غَضِبُواْ هُمۡ يَغۡفِرُونَ

    Open ayah 42:37

    Waɗanda kuma suke nesantar manyan zunubai da munanansu, idan kuma sun yi fushi sukan yafe.

  38. وَٱلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِرَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَمۡرُهُمۡ شُورَىٰ بَيۡنَهُمۡ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

    Open ayah 42:38

    (Su ne) kuma waɗanda suka amsa kiran Ubangijinsu suka kuma tsai da salla, al’amarinsu kuwa (suna) shawara ne a tsakaninsu, suna kuma ciyarwa daga abin da Muka arzuta su.

  39. وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَابَهُمُ ٱلۡبَغۡيُ هُمۡ يَنتَصِرُونَ

    Open ayah 42:39

    (Su ne) kuma waɗanda idan wani zalunci ya shafe su sukan rama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa bayinsa cewa, duniya ba a bakin komai take ba; duk wata dukiya da aka ba su ko mulki ko ‘ya’ya ko matsayi, to ɗan jin daɗin rayuwar duniya ne kawai mai gushewa ne babu makawa, jin daɗi na har abada shi ne ni’imar Aljanna wadda Allah ya tanadar wa bayinsa waɗanda suka siffantu da siffofi kamar haka: <b>Na ɗaya </b>: Waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa. <b>Na biyu </b>: Waɗanda suke dogara ga Ubangijinsu shi kaɗai cikin dukkan al’amuransu. <b>Na uku </b>: Su ne waɗanda suke nesantar manyan zunubai, kamar shirka da kisa da sata da cin dukiyar riba da shan giya. <b>Na huɗu </b>: Suke nesantar munanan ayyuka na alfasha, kamar zina da luwaɗi da maɗigo. <b>Na biyar </b>: Su ne waɗanda idan an fusata su da wata magana ko da wani aiki, to suna yafe wa wanda ya munana musu ba sa ramuwa. <b>Na shida </b>: Su ne waɗanda suka amsa kiran Ubangijinsu, suka aikata umarninsa, suka guje wa haninsa. <b>Na bakwai </b>: Su ne waɗanda suka tsayar da salla yadda ya kamata tare da lura da lokatanta da farillanta da sunnoninta. <b>Na takwas </b>: Su ne masu yin shawara a tsakaninsu wajen gudanar da al’amuransu, musamman waɗanda suka shafi al’umma, kamar batun yaƙi da na zaman lafiya da tattalin arziki. <b>Na tara </b>: Su ne masu ciyar da abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya arzuta su da shi don neman yardarsa. <b>Na goma </b>: Su ne waɗanda idan aka zalunce su suna ɗaukar fansa domin kare mutuncinsu da darajarsu, yayin da azzalumin ya kasance ba wanda ya cancanci a yi masa afuwa ba ne, kuma babu maslaha a cikin yi masa afuwar.

  40. وَجَزَٰٓؤُاْ سَيِّئَةٖ سَيِّئَةٞ مِّثۡلُهَاۖ فَمَنۡ عَفَا وَأَصۡلَحَ فَأَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّٰلِمِينَ 

    Open ayah 42:40

    Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai.

  41. وَلَمَنِ ٱنتَصَرَ بَعۡدَ ظُلۡمِهِۦ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَا عَلَيۡهِم مِّن سَبِيلٍ

    Open ayah 42:41

    Tabbas kuma duk wanda ya rama bayan an zalunce shi, to waɗannan ba wani laifi a kansu.

  42. إِنَّمَا ٱلسَّبِيلُ عَلَى ٱلَّذِينَ يَظۡلِمُونَ ٱلنَّاسَ وَيَبۡغُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

    Open ayah 42:42

    Laifi kam yana kan waɗanda suke zaluntar mutane ne suke kuma yin ta’adda a bayan ƙasa ba da wata hujja ba. Waɗannan suna da azaba mai raɗaɗi.

  43. وَلَمَن صَبَرَ وَغَفَرَ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

    Open ayah 42:43

    Tabbas kuma wanda ya yi haƙuri ya yafe, to tabbas wannan yana daga muhimman al’amura. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa ya halatta ga duk wanda aka cuta ya nemi haƙƙinsa, amma gwargwadon yadda aka yi masa ba tare da ƙari ko wuce iyaka ba. Sai dai ya sani cewa duk wanda ya yafe cutar da aka yi masa ya kuma kyautata alaƙa tsakaninsa da wanda ya cuce shi, to ladansa yana wurin Allah, shi ne zai biya shi daga taskarsa. Idan kuwa har ya yi zalunci wajen ramuwa, to ya sani lalle Allah ba ya son azzalumai. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da cewa waɗanda suka rama zaluncin da aka yi musu ba tare da sun ƙetare iyaka ba, to waɗannan babu wani laifi a kansu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Masu zagin junansu, laifin abin da suka furta (na zagi) yana kan wanda ya fara, matuƙar wanda aka zalunta bai wuce iyaka ba.” [Muslim #2587]. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa laifi da uƙuba sun tabbata ne a kan waɗanda suke zaluntar mutane, suke kuma aikata laifukan saɓon Allah a bayan ƙasa, to waɗannan suna da azaba mai raɗaɗi a ranar alƙiyama. Amma kuma ya bayyana cewa wanda ya yi haƙuri a kan cutarwar da wani ya yi masa ya yafe masa, to wannan haƙurin nasa zai zame masa alheri har ma da al’ummarsa gaba ɗaya, domin abu ne mai kyau da ba kowa ke iya yin sa ba sai mai babban rabo.

  44. وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن وَلِيّٖ مِّنۢ بَعۡدِهِۦۗ وَتَرَى ٱلظَّٰلِمِينَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَ يَقُولُونَ هَلۡ إِلَىٰ مَرَدّٖ مِّن سَبِيلٖ

    Open ayah 42:44

    Wanda kuma Allah Ya ɓatar, to ba shi da wani majiɓinci bayanSa. Kuma za ka ga azzalumai lokacin da suka ga azabar suna cewa: “Ina ma da akwai wata damar komawa (duniya)?”

  45. وَتَرَىٰهُمۡ يُعۡرَضُونَ عَلَيۡهَا خَٰشِعِينَ مِنَ ٱلذُّلِّ يَنظُرُونَ مِن طَرۡفٍ خَفِيّٖۗ وَقَالَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ ٱلۡخَٰسِرِينَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَأَهۡلِيهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَآ إِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ فِي عَذَابٖ مُّقِيمٖ

    Open ayah 42:45

    Kuma za ka gan su ana bijiro su a kanta (wutar) suna masu ƙanƙan da kai na wulaƙanci, suna kallo a sace. Waɗanda kuma suka yi imani suka ce: “Lalle asararru su ne waɗanda suka yi asarar rayuwarsu da ta iyalinsu a ranar alƙiyama.” Ku saurara, lalle azzalumai suna cikin azaba dawwamammiya.

  46. وَمَا كَانَ لَهُم مِّنۡ أَوۡلِيَآءَ يَنصُرُونَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن سَبِيلٍ

    Open ayah 42:46

    Kuma ba su da wasu majiɓinta da za su taimake su in ban da Allah. Duk wanda Allah Ya ɓatar, to ba shi da wata hanya daban (ta shiriya). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wanda ya nufe shi da ɓata ya hana shi bin gaskiya saboda mugun halinsa, to ba zai taɓa samun wanda zai jiɓinci al’amarinsa ya shiryar da shi in ba Allah ba. Sai kuma Allah ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, a ranar alƙiyama zai ga azzalumai waɗanda suka cuci kawunansu da kafirci da saɓon Allah yayin da za su ga azabar wuta da idanunsu, za su riƙa burin ina ma suna da wata damar komawa duniya domin su tuba su gyara halayensu. To amma ina, bakin alƙalami ya riga ya bushe. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya shaida masa cewa, a ranar zai ga waɗannan azzalumai lokacin da ake gindaya su a kan wuta, suna wulaƙantattu ƙasƙantattu, suna kallon mutane a sace saboda tsananin tsoro da ya cika musu zuciya, kuma dai abin da suke tsoro ɗin sai ya auka musu ba makawa. A ranar muminai waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa za su ce: Lalle asararru na haƙiƙa su ne waɗanda suka yi asarar kawunansu da iyalansu a ranar alƙiyama saboda azabar da suka haɗu da ita. Lalle azzalumai suna cikin azaba madawwamiya wadda ba za ta yanke ba har abada. Kuma ba su da waɗanda za su taimaka musu su kuɓutar da su daga azabar Allah a wannan ranar. Duk kuma wanda Allah ya ɓatar da shi saboda mugun halinsa, to ba shi da wata hanya da za ta kai shi zuwa shiriya.

  47. ٱسۡتَجِيبُواْ لِرَبِّكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۚ مَا لَكُم مِّن مَّلۡجَإٖ يَوۡمَئِذٖ وَمَا لَكُم مِّن نَّكِيرٖ

    Open ayah 42:47

    Ku amsa kiran Ubangijinku tun kafin ranar da ba ta da wata makauta ta zo daga Allah. Ba ku da wata mafaka a wannan ranar, kuma ba ku da damar yin musu.

  48. فَإِنۡ أَعۡرَضُواْ فَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظًاۖ إِنۡ عَلَيۡكَ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُۗ وَإِنَّآ إِذَآ أَذَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِنَّا رَحۡمَةٗ فَرِحَ بِهَاۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ فَإِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ كَفُورٞ

    Open ayah 42:48

    To idan sun bijire, to ba Mu aika ka don ka zama mai gadin su ba; ba abin da yake kanka sai isar da saƙo. Lalle kuma Mu idan Muka ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu sai ya riƙa tutiya da ita. Idan kuma wani mummunan abu ya same su saboda abin da hannayensu suka aikata, to lalle shi mutum butulu ne.

  49. لِّلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ يَهَبُ لِمَن يَشَآءُ إِنَٰثٗا وَيَهَبُ لِمَن يَشَآءُ ٱلذُّكُورَ

    Open ayah 42:49

    Mulkin sammai da ƙasa na Allah ne. Yana halittar abin da Ya ga dama. Yana ba da `ya`ya mata ga wanda Ya ga dama, Yana kuma ba da `ya`ya maza ga wanda Ya ga dama.

  50. أَوۡ يُزَوِّجُهُمۡ ذُكۡرَانٗا وَإِنَٰثٗاۖ وَيَجۡعَلُ مَن يَشَآءُ عَقِيمًاۚ إِنَّهُۥ عَلِيمٞ قَدِيرٞ 

    Open ayah 42:50

    Ko kuma ya haɗa musu maza da mata; Yakan kuma mayar da wanda ya ga dama bakarare. Lalle Shi Masani ne, Mai iko. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana kiran bayinsa ne da su gaggauta amsa kiransa, su yi aiki da umarninsa su guji haninsa, su daina ɓata wa kansu lokaci, tun kafin zuwan ranar alƙiyama wadda babu wanda ya isa ya hana zuwanta. Kuma ya shaida musu cewa a ranar ba su da wata mafakar da za ta ɓoye su daga Allah, kuma ba su da damar musanta zunuban da suka aikata a duniya. Domin idan ma sun yi musu gaɓoɓinsu ne za su ba da shaida a kansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa, idan kafirai suka bijire masa suka ƙi amsa kiransa na yin imani da Allah da Manzonsa, to yana tabbatar masa da cewa bai aiko shi don ya zama mai gadin su ba yana kula da ayyukansu; abin da kawai yake kansa shi ne isar da saƙon Allah zuwa gare su, amma hisabinsu yana wurin Allah. Sai kuma Allah ya bayyana wani mummunan hali na ɗan’adam, watau duk sanda Allah ya ɗanɗana masa wata rahamarsa ta wadata ko lafiya da makamantansu sai ya riƙa fariya da ita yana girman kai; idan kuma ya saukar masa wani bala’i saboda laifin da ya aikata, to sai ya zamanto mai butulce wa ni’imomin Allah mai rashin godiya, ko mai fushi da ƙaddarar Allah da rashin dangana. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakken mulkinsa da kamalar Ƙudurarsa, da cewa mulkin sammai da ƙasa duk nasa ne babu mai tarayya da shi a cikinsu; yana halittar abin da ya ga dama a sanda ya ga dama, namiji ko mace ko waninsu; idan ya ga dama ya ba wa wani ‘ya’ya mata zalla ya hana shi maza, wani kuma ya ba shi maza zalla ya hana shi mata, ko kuma ya haɗa wa wanda ya ga dama ‘ya’ya maza da mata, sannan ya mayar da wani bakarare ba ya haihuwa, domin shi masani ne na duk abin da ya wakana da wanda ma zai wakana nan gaba, mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi.

  51. ۞وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُكَلِّمَهُ ٱللَّهُ إِلَّا وَحۡيًا أَوۡ مِن وَرَآيِٕ حِجَابٍ أَوۡ يُرۡسِلَ رَسُولٗا فَيُوحِيَ بِإِذۡنِهِۦ مَا يَشَآءُۚ إِنَّهُۥ عَلِيٌّ حَكِيمٞ

    Open ayah 42:51

    Kuma zai yiwu ga wani mutum a ce Allah Ya yi magana da shi ba (baki da baki), sai dai wahayi ko kuma ta bayan wani shamaki, ko kuwa Ya aiko wani manzo (mala’ika) sai ya yi masa wahayin abin da ya ga dama da yardarsa. Lalle Shi Maɗaukaki ne, Mai hikima.

  52. وَكَذَٰلِكَ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ رُوحٗا مِّنۡ أَمۡرِنَاۚ مَا كُنتَ تَدۡرِي مَا ٱلۡكِتَٰبُ وَلَا ٱلۡإِيمَٰنُ وَلَٰكِن جَعَلۡنَٰهُ نُورٗا نَّهۡدِي بِهِۦ مَن نَّشَآءُ مِنۡ عِبَادِنَاۚ وَإِنَّكَ لَتَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

    Open ayah 42:52

    Kuma kamar haka ne Muka yiwo maka wahayin Ruhi (watau Alƙur\'ani) daga umarninmu. Ba ka zamanto ka san mene ne littafi ko kuma imani ba, sai dai kuma Mun sanya shi (Alƙur’ani) haske ne da Muke shiryar da wanda Muka ga dama daga bayinmu da shi. Lalle kuma kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.

  53. صِرَٰطِ ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِلَى ٱللَّهِ تَصِيرُ ٱلۡأُمُورُ

    Open ayah 42:53

    (Watau) tafarkin Allah wanda Yake da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake ƙasa. Ku saurara, zuwa ga Allah ne kawai al’amura suke komawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana hanyoyin da yake magana da manzanninsa da annabawansa, da cewa ba zai yiwu Allah ya yi magana da wani mutum ba sai ta ɗaya daga cikin hanyoyi uku: <b>Na farko </b>: Ta hanyar wahayin ilhama ko waninsa, watau Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kimsa masa maganarsa a zuciyarsa ba tare da ya yi magana da shi ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Ruhi mai amana (watau Jibrilu) ya yi mini busa a zuciyata cewa, babu wani rai da zai mutu har sai ya cinye arzikinsa…” [Ibn Abi Shaiba, Almusannaf #34332]. <b>Na biyu </b>: Ya yi magana da shi ta bayan wani shamaki inda zai riƙa jin maganarsa amma ba ya ganin sa, kamar yadda ya yi magana da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). <b>Na uku </b>: Ya yi masa magana ta hanyar mala’ika, kamar Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), sai ya sanar da shi abin da Allah ya yi masa izinin ya sanar da shi. Lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) Maɗaukaki ne a Zatinsa da siffofinsa da ayyukansa; mai hikima ne cikin halittunsa da tsare-tsarensa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda ya yi wa annabawan da suka gabata wahayi, to hakanan ya yi wa Annabi (ﷺ) wahayi wanda gabaninsa bai san wasu littattafai da aka saukar wa manzanni ba, bai kuma san mene ne imani ba, sai dai Allah ya saukar masa Alƙur’ani don ya zama haske da shiriya da yake shiryar da waɗanda ya ga dama daga bayinsa zuwa miƙaƙƙen tafarki, watau Musulunci. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Musulunci shi ne hanyar Allah mamallakin abin da yake cikin sammai da abin da yake ƙasa, halittarsa ne, bayinsa ne, kuma shi ne mai gudanar da su. Kuma ya tabbatar da cewa, makomar al’amura duka zuwa gare shi ne, domin ya yi sakayya a kan kowane aiki mai kyau ko mummuna.