الزخرف
Az-Zukhruf
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
حمٓ
Open ayah 43:1HA MIM.
وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ
Open ayah 43:2Na rantse da Littafi mabayyani (Alƙur’ani).
إِنَّا جَعَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Open ayah 43:3Lalle Mu Mun sanya shi ya zamo abin karantawa cikin harshen Larabci domin ku hankalta.
وَإِنَّهُۥ فِيٓ أُمِّ ٱلۡكِتَٰبِ لَدَيۡنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌ
Open ayah 43:4Lalle kuma shi (Alƙur’ani) a cikin Littafi Lauhul-Mahafuzu a wurinmu tabbas maɗaukaki ne, mai hikima.
أَفَنَضۡرِبُ عَنكُمُ ٱلذِّكۡرَ صَفۡحًا أَن كُنتُمۡ قَوۡمٗا مُّسۡرِفِينَ
Open ayah 43:5Yanzu Ma fasa saukar muku da Alƙur\'ani Mu watsar da ku, don kun kasance mutane masu yawan ɓarna?
وَكَمۡ أَرۡسَلۡنَا مِن نَّبِيّٖ فِي ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 43:6Annabi nawa Muka aika wa mutanen farko?
وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 43:7Ba kuma wani annabi da yakan zo musu sai sun kasance suna yi masa izgili.
فَأَهۡلَكۡنَآ أَشَدَّ مِنۡهُم بَطۡشٗا وَمَضَىٰ مَثَلُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 43:8Sai Muka hallakar da waɗanda suka fi su tsananin ƙarfi, kuma bayanin yadda aka hallakar da mutanen farko ya riga ya shuɗe. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa biyu, kamar yadda ya buɗe surori da dama da irin waɗannan haruffan. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara don ƙarin bayani]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da littafinsa Alƙur’ani mai bayyana hanyar gaskiya da hukunce-hukuncen shari’a. Ya kuma saukar da shi ne da harshen Larabci domin Larabawa su fahimci ma’anoninsa da abubuwan da ya ƙunsa na shiriya, su isar da su zuwa ga sauran al’ummu waɗanda ba sa magana da harshen Larabci. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, shi Alƙur’ani ya riga ya tabbata a cikin Lauhul Mahfuzu cewa shi mai maɗaukakiyar daraja ne wanda yake cike da hikima. Watau duk abin da ya ƙunsa gaskiya ne, babu kokwanto a cikinsa, kuma maganar Allah ne, ya san da shi tun fil azal. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ba zai yiwu ya bar mutane hakanan kara zube ba, ba tare da ya aiko musu wani manzo, ko ya saukar musu da wani littafi ba, don kawai sun zama mutane maɓarnata. Don haka kada su yi tsammanin cewa, Allah ba zai saukar da Alƙur’ani ba; tabbas zai saukar musu da shi, ya yi musu bayanin komai filla-filla, wanda ya yi imani don kansa, wanda kuma ya kafirce shi ma don kansa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa aiko da manzanni sunnarsa ce daɗaɗɗiya, domin ya aika annabawa da yawa a cikin al’ummun farko, duk kuwa da kasancewar babu wani annabi da zai zo musu sai sun riƙa yi masa izgili, don nuna bijire wa abin da ya zo musu da shi na gaskiya. Amma duk da haka sai da Allah ya hallakar da waɗanda suka fi tsananin ƙarfi daga cikin al’ummun nan, don haka hallakar da raunana daga cikinsu ba wani aiki ne da zai gagare shi ba. Kuma bayanin yadda aka hallakar da su ya riga ya shuɗe, watau an yi bayaninsa a sarari a cikin Alƙur’ani, kamar yadda aka hallakar da Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanen Madyana na Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 43:9Lalle kuma idan ka tambaye su wane ne ya halicci sammai da ƙasa, to tabbas za su ce: “(Allah) ne Mabuwayi, Masani Ya halicce su.”
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَجَعَلَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا لَّعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Open ayah 43:10Wanda Ya sanya muku ƙasa ta zama shimfiɗa, Ya kuma sanya muku hanyoyi a cikinta don ku gane (inda za ku dosa).
وَٱلَّذِي نَزَّلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَنشَرۡنَا بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗاۚ كَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ
Open ayah 43:11Wanda kuma Ya saukar da ruwa daidai gwargwado daga sama sannan Muka raya mataccen gari da shi. Kamar haka ne za a fito da ku (daga ƙabarurruka).
وَٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَزۡوَٰجَ كُلَّهَا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡفُلۡكِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ مَا تَرۡكَبُونَ
Open ayah 43:12Kuma wanda Ya halicci dukkan dangogin abubuwa bibbiyu, Ya kuma sanya muku daga jiragen ruwa da kuma dabbobin ni’ima, abubuwan da kuke hawa.
لِتَسۡتَوُۥاْ عَلَىٰ ظُهُورِهِۦ ثُمَّ تَذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ رَبِّكُمۡ إِذَا ٱسۡتَوَيۡتُمۡ عَلَيۡهِ وَتَقُولُواْ سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَٰذَا وَمَا كُنَّا لَهُۥ مُقۡرِنِينَ
Open ayah 43:13Don ku daidaita a kan bayansu, sannan ku tuna ni’imar Ubangijinku lokacin da kuka daidaita a kansu kuma ku ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda Ya hore mana wannan, ba mu zamanto masu ikon sarrafa shi ba.
وَإِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ
Open ayah 43:14“Kuma lalle zuwa ga Ubangijinmu tabbas za mu koma.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Manzonsa (ﷺ) labarin wani abin mamaki da takaici na mushirikan Larabawa, da cewa da zai tambaye su wane ne ya halicci sammai da ƙasa, to tabbas za su ce wanda ya halicce su shi ne Allah Mabuwayi kuma masanin komai. To amma abin mamakin shi ne yadda suke yi wa Allah shirka suna bautar wasu gumaka ba shi ba tare da cewa sun san shi ne mahaliccin komai da kowa, sun kuma san gumakan nasu ba za su iya halittar ko da ƙuda ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci wasu ƙwararan dalilai masu tabbatar da girman Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa, da cewa shi ne ya shimfiɗa ƙasa don ta zama matsuguni ga mutane, domin su gudanar da rayuwarsu a kanta, ya kuma shata musu hanyoyi a cikin duwarwatsu da kwazazzabai domin zirga-zirgarsu, don kuma su riƙa gane inda suke dosa yayin tafiye-tafiyensu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya tabbatar da cewa shi ne wanda ya saukar da ruwa daga sama daidai gwargwadon yadda zai ishi buƙatar mutane da dabbobinsu da shuke-shukensu. Da wannan ruwan ne kuma ya raya mataccen gari wanda ba ya fitar da tsironsa. To kamar yadda ya raya wannan matacciyar ƙasar, haka zai raya matattu domin hisabi da sakamako a ranar alƙiyama. Allah kuma ya ƙara bayyana girman Ƙudurarsa da cewa shi ne wanda ya halicci kowane abu jinsi bibbiyu, kamar mace da namiji da dare da rana da sanyi da zafi da jinsin tsirrai da dabbobi da sauransu. Kuma har ila yau ya samar wa mutane abubuwan hawa kamar jiragen ruwa da dabbobi, waɗanda suke amfani da su wajen tafiye-tafiyensu a cikin ruwa ko a kan doron ƙasa. Allah ya yi wa mutane haka ne domin duk sa’adda suka hau abubuwan hawansu na ruwa ko na tudu ko na sama, suka daidaita a kansu, to sai su tuna ni’imar da ya yi musu da ya hore musu su, su tsarkake shi da bakunansu su yi tasbihi gare shi saboda ya ba su damar sarrafa waɗannan abubuwan hawan yadda suke buƙata. Ba don ya yi musu wannan tagomashi ba to da ba za su iya sarrafa waɗannan abubuwan hawan ba. Kuma su tabbatar da cewa makomarsu gaba ɗaya zuwa ga Ubangijinsu ne. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan ya hau abin hawansa yakan yi kabarbari sau uku, sannan sai ya ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda ya hore mana wannan, ba mu zamanto masu ikon sarrafa shi ba. Kuma haƙiƙa lalle zuwa ga Ubangijinmu za mu koma.” Sannan sai ya ce: “Ya Allah, ina roƙon ka duk wani alheri da taƙawa a wannan tafiyar tawa, da aikin da za ka yarda da shi. Ya Allah, ka sassauta mana wannan tafiyar tamu, ka naɗe mana nisanta. Ya Allah, kai ne abokin tafiya kuma halifa a cikin iyali. Ya Allah, ina neman tsarinka daga wahalhalun tafiya da rashin kyan gani da mummunar makoma game da dukiya da iyali.” Idan kuma yana dawowa sai ya sake faɗar wannan ya ƙara da cewa: “Muna masu mayar da al’amari ga Allah, muna masu tuba, masu bauta, masu godiya ga Ubangijinmu.” [Muslim #1342].
وَجَعَلُواْ لَهُۥ مِنۡ عِبَادِهِۦ جُزۡءًاۚ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَكَفُورٞ مُّبِينٌ
Open ayah 43:15Kuma suka mai da wasu daga cikin bayinsa wani ɓangare nasa (wato `ya`yansa). Lalle mutum mai yawan butulci ne mai bayyana (butulcinsa).
أَمِ ٱتَّخَذَ مِمَّا يَخۡلُقُ بَنَاتٖ وَأَصۡفَىٰكُم بِٱلۡبَنِينَ
Open ayah 43:16Yanzu Ya ɗauki `ya`ya mata daga abubuwan da Yake halitta, ku kuma Ya zaɓa muku `ya`ya maza?
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحۡمَٰنِ مَثَلٗا ظَلَّ وَجۡهُهُۥ مُسۡوَدّٗا وَهُوَ كَظِيمٌ
Open ayah 43:17Idan kuma aka yi wa ɗayansu albishir da abin da ya buga misali cewa na (Allah) Arrahmanu ne, sai fuskarsa ta yini a murtuke yana cike da baƙin ciki.
أَوَمَن يُنَشَّؤُاْ فِي ٱلۡحِلۡيَةِ وَهُوَ فِي ٱلۡخِصَامِ غَيۡرُ مُبِينٖ
Open ayah 43:18Yanzu (sa danganta wa Allah) wanda da ake renon sa cikin kwalliya, alhali kuma idan an zo wajen husuma ba zai iya bayyana kansa (wajan ba da hujja) ba?
وَجَعَلُواْ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ ٱلَّذِينَ هُمۡ عِبَٰدُ ٱلرَّحۡمَٰنِ إِنَٰثًاۚ أَشَهِدُواْ خَلۡقَهُمۡۚ سَتُكۡتَبُ شَهَٰدَتُهُمۡ وَيُسۡـَٔلُونَ
Open ayah 43:19Suka kuma mai da mala’iku waɗanda suke bayin (Allah) Arrahmanu ne `ya`ya mata. Shin sun halarci sanda aka halicce su ne? To za a rubuta shaidarsu, za kuma a tambaye su (a lahira). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana butulcin ɗan’adam kafiri da rashin adalcinsa ga mahaliccinsa da cewa, mushirikai sun yi wa Allah ƙarya yayin da suka riya cewa wasu daga cikin halittunsa ‘ya’yansa ne. Suna ɗaukar mala’iku wai ‘ya’yan Allah ne mata. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuwa ya yi tir da wannan mummunan hali nasu, ya tabbatar da cewa lalle shi ɗan’adam mai yawan butulci ne da nuna kafircinsa a fili. Kuma Allah ya nuna irin rashin adalcin mushirikai a gare shi, domin su mata a wurinsu ƙasƙantattu ne, suna fifita maza a kansu, to amma kuma sai suka danganta masa mata da cewa su ne ‘ya’yansa. Allah ya tambaye su game da wannan ɗanyen hukunci nasu da cewa, yanzu ya dace shi ya zaɓi ‘ya’ya mata daga cikin abin da ya halitta su kuma ya zaɓar musu maza? Hasali ma duk wanda aka kawo masa albishir daga cikinsu cewa an haifa masa ‘ya mace, watau jinsin abin da yake ƙyama suke kuma jingina wa Allah, sai fuskarsa ta yini a murtuke yana cike da baƙin ciki, saboda tsananin takaici. To amma kuma ga shi yana jingina wa Allah mahalicci abin da shi yake tsananin ƙyama. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara nuna musu rashin dacewar abin da suka jingina masa na cewa mala’iku ‘ya’yansa ne mata da cewa, ita fa ‘ya mace a ɗabi’arta ta taso ne cikin son kwalliya da ado domin ta burge wasu, tana neman cike giɓin halittarta da wannan, shi ya sa ma tun tana jaririya ake huda kunnenta don yi mata ado da ɗan kunne, yayin da ɗa namiji ba ya buƙatar haka. Haka kuma idan an zo wajen husuma da jayayya mace ba za ta iya kawo wata hujjar da za ta kare kanta da ita ba, kamar yadda ɗa namiji zai yi. Ko kuma idan yaƙi ya ɓarke ba za ta iya taɓuka wani abu na ba da kariya ba. Watau dai abin nufi a nan shi ne bayyana rashin tunanin mushirikai da rashin hankalinsu yayin da suka jingina wa Allah ɗa, suka kuma jingina masa `ya`ya mata raunana waɗanda su kansu suke ƙyamar su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kawo wata ƙwaƙƙwarar hujja da take ƙara tabbatar da ƙaryar masu jingina wa Allah ‘ya’ya kamar mala’iku, da cewa mala’iku fa dukkansu bayin Allah ne kuma halittarsa ne kamar yadda sauran halittunsa suke bayinsa. To amma sai su suka mayar da su mata kuma ‘ya’yansa. To sai Allah ya tambaye su cewa, shin sun halarci lokacin halittarsu ne suka lura cewa su mata ne ba maza ba? To su sani cewa mala’iku za su rubuta wannan shaidar tasu, kuma za a tambaye su game da ita a ranar alƙiyama, kuma za su ɗanɗani kuɗarsu a kanta.
وَقَالُواْ لَوۡ شَآءَ ٱلرَّحۡمَٰنُ مَا عَبَدۡنَٰهُمۗ مَّا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِنۡ هُمۡ إِلَّا يَخۡرُصُونَ
Open ayah 43:20Suka kuma ce: “Da (Allah) Arrahmanu Ya ga dama, da ba mu bauta musu ba (wato mala’ikun).” Ba su da wani takamaiman ilimi a kan hakan; ba abin da suke yi sai shaci-faɗi.
أَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ كِتَٰبٗا مِّن قَبۡلِهِۦ فَهُم بِهِۦ مُسۡتَمۡسِكُونَ
Open ayah 43:21Ko kuma Mun ba su wani littafi ne gabaninsa (Alƙur’ani), saboda haka suke riƙe da shi ƙam-ƙam?
بَلۡ قَالُوٓاْ إِنَّا وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٖ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم مُّهۡتَدُونَ
Open ayah 43:22A’a, cewa dai suka yi: “Lalle mu mun sami iyayenmu a kan wani addini ne, mu kuma lalle sawunsu muke bi.”
وَكَذَٰلِكَ مَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتۡرَفُوهَآ إِنَّا وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٖ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم مُّقۡتَدُونَ
Open ayah 43:23Kuma kamar haka ne, ba Mu taɓa aiko wani mai gargaɗi ba a wata alƙarya a gabaninka sai \'yan ta-moren cikinsu sun ce: “Lalle mu mun sami iyayenmu a kan wani addini, kuma lalle mu hanyarsu muke kwaikwayo.”
۞قَٰلَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكُم بِأَهۡدَىٰ مِمَّا وَجَدتُّمۡ عَلَيۡهِ ءَابَآءَكُمۡۖ قَالُوٓاْ إِنَّا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ
Open ayah 43:24Ya ce (da su: “Yanzu za ku yi koyi da su) ko da na zo muku da abin da ya fi zama shiriya a kan abin da kuka sami iyayenku a kansa?” Suka ce: “Lalle mu masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne.”
فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 43:25Sai Muka saka musu da azaba; to duba ka ga yadda ƙarshen masu ƙaryatawa ya kasance. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani salo na izgilanci da kafirai suke yi yayin da ake yi musu wa’azi ana kiran su cewa, su daina bautar wasu ba Allah ba, sai kawai suka ka da baki suka ce, ai da Allah ya ga dama da ba zai ƙyale su suna bauta wa mala’ikun ba; tunda har aka ga ya ƙyale su suna bauta musu, to wannan ya nuna ya yarda da abin da suke yi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙaryata su ya tabbatar da cewa ba su da wata hujja ta ilimi a kan wannan maganar tasu, suna dai ƙagen ƙarairayi ne kawai suna danganta masa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, shin ya ba su wani littafi ne kafin Alƙur’ani wanda a cikinsa ya halatta musu su bauta wa wasu ba Allah ba, don hake ne suke ƙanƙame masa? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa sam ba su da wani littafi daga gare shi da ya ba su wannan damar; suna dai bin hanyoyin iyayensu ne kawai ido rufe ba tare da wata hujja ba, domin duk sanda aka faɗa musu gaskiya sai su bijire mata, su ce su sun sami iyayensu ne a kan wannan addinin da suke a kai na bautar gumaka, kuma su ba za su daina bin hanyoyinsu ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) da cewa, ba mutanensa ne kaɗai suka kafirce wa Allah da manzanninsa suka riƙa kafa hujja da iyayensu ba; babu wani manzo da ya aiko zuwa ga wata alƙarya gabaninsa sai manyan cikin wannan alƙarya sun fito suna ƙalubalantar sa suna tabbatar masa cewa su addinin da suke bi shi ne wanda suka gada iyaye da kakanni, kuma iyayen nasu za su ci gaba da bi sau da ƙafa ba ja da baya. Sai manzon nasu ya tambaye su cikin mamaki cewa, yanzu za su bi hanyar iyayensu ko da kuwa abin da ya zo musu da shi ya fi zama shiriya a kan abin da suka samu iyayensu a kai? Sai kafiran suka tabbatar masa da cewa su fa sun kafirta da duk abin da aka saukar wa manzannin Allah ba ma shi kaɗai ba, watau ya daina ɓata wa kansa lokaci ba za su yi imani da shi ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ya saukar da azabarsa a kan al’ummun da suka ƙaryata manzanninsa, ya kuma umarci Manzonsa (ﷺ) ya duba ya ga yadda ƙarshen al’amarin masu ƙaryatawa ya kasance. Babu shakka ƙarshensu ya yi matuƙar muni. Don haka mutanensa ma ba su fi ƙarfin irin wannan azabar ta same su ba idan ba su yi imani ba.
وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦٓ إِنَّنِي بَرَآءٞ مِّمَّا تَعۡبُدُونَ
Open ayah 43:26Kuma ka tuna lokacin da Ibrahimu ya ce da Babansa da mutanensa: “Lalle ni ba ruwana da abin da kuke bautawa.
إِلَّا ٱلَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُۥ سَيَهۡدِينِ
Open ayah 43:27“Sai dai wanda Ya halicce ni, to lalle Shi ne Zai shirye ni.”
وَجَعَلَهَا كَلِمَةَۢ بَاقِيَةٗ فِي عَقِبِهِۦ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Open ayah 43:28Ya kuma sanya ta (kalmar Tauhidi ta zama) kalma ce mai wanzuwa a cikin zuri’arsa don (mutanen Makka) su komo (kan hanya).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa mushirikan Larabawa labarin kakansu mai daraja Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda suke tutiyar cewa su suna bin addininsa ne, domin ya tabbatar musu cewa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai taɓa bautar wani ba Allah ba; hasali ma fitowa ya yi fili ya shaida wa babansa da mutanensa cewa, shi fa ba ruwansa da gumakan da suke bauta wa ba Allah ba. Shi abin bautarsa Ɗaya ne, shi ne Allah wanda ya ƙagi halittarsa, shi ne kuma zai nuna masa hanya miƙaƙƙiya ta bautarsa, watau yarda da cewa babu abin bauta wa da gaskiya sai shi kaɗai. Sai Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya mayar da wannan kalma ta Tauhidi ta zama kalma mai wanzuwa a cikin zurriyarsa a bayansa, don haka sai aka yi ta samun masu kaɗaita Allah da bauta a cikinsu, ba sa haɗa shi da komai. Tabbas sanin wannan ga mushirikan Ƙuraishawa zai iya taimaka wa wasunsu su komo kan hanyar kakansu Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) su yi watsi da bautar gumaka su rungumi kalmar Tauhidi su bauta wa Allah shi kaɗai.
بَلۡ مَتَّعۡتُ هَٰٓؤُلَآءِ وَءَابَآءَهُمۡ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ وَرَسُولٞ مُّبِينٞ
Open ayah 43:29A’a, Na jiyar da waɗannan daɗi tare da iyayensu ne har gaskiya ta zo musu da wani manzo mai bayyanawa.
وَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ وَإِنَّا بِهِۦ كَٰفِرُونَ
Open ayah 43:30Yayin da gaskiyar ta zo musu sai suka ce: “Wannan sihiri ne, kuma lalle mu masu kafirce masa ne.”
وَقَالُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ عَلَىٰ رَجُلٖ مِّنَ ٱلۡقَرۡيَتَيۡنِ عَظِيمٍ
Open ayah 43:31Suka kuma ce: “Me ya hana a saukar da wannan Alƙur’ani ga wani babban mutum, daga alƙaryun nan guda biyu?”
أَهُمۡ يَقۡسِمُونَ رَحۡمَتَ رَبِّكَۚ نَحۡنُ قَسَمۡنَا بَيۡنَهُم مَّعِيشَتَهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَرَفَعۡنَا بَعۡضَهُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَتَّخِذَ بَعۡضُهُم بَعۡضٗا سُخۡرِيّٗاۗ وَرَحۡمَتُ رَبِّكَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ
Open ayah 43:32Yanzu su ne suke raba rahamar Ubangijinka (ta annabci)? Mu ne Muka raba musu arzikinsu a rayuwar duniya. Muka kuma ɗaukaka darajojin sashinsu a kan sashi, don wani sashin ya riƙi wani sashi mai yi masa hidima. Rahamar Ubangijinka kuma ita ta fi abin da suke tarawa (na duniya).
وَلَوۡلَآ أَن يَكُونَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ لَّجَعَلۡنَا لِمَن يَكۡفُرُ بِٱلرَّحۡمَٰنِ لِبُيُوتِهِمۡ سُقُفٗا مِّن فِضَّةٖ وَمَعَارِجَ عَلَيۡهَا يَظۡهَرُونَ
Open ayah 43:33Ba don kuma kada mutane su zama iri ɗaya ba, da sai Mu sanya wa waɗanda suke kafirce wa (Allah) Mai rahma rufi na azurfa a gidajensu, da kuma matattakala (irinta), da za su riƙa hawa ta kansu.
وَلِبُيُوتِهِمۡ أَبۡوَٰبٗا وَسُرُرًا عَلَيۡهَا يَتَّكِـُٔونَ
Open ayah 43:34Kuma (Mu sanya wa) gidajen nasu ƙofofi da gadaje da za su riƙa kishingiɗa a kansu.
وَزُخۡرُفٗاۚ وَإِن كُلُّ ذَٰلِكَ لَمَّا مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَٱلۡأٓخِرَةُ عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 43:35Kuma (Mu sanya musu) zinariya. Duk waɗannan ba komai ba ne sai ɗan jin daɗin rayuwar duniya. Lahira kuma a wurin Ubangijinka ta masu taƙawa ce. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa bai gaggauto wa mushirikai azaba ba; ya ƙyale su ne, ya kuma jiyar da su daɗi, sun yi tsawon rai, sun sami ni’ima ta duniya; su ma iyayensu ya jiyar da su daɗi suka yi ta bin sha’awe-sha’awensu har lokacin da Alƙur’ani ya zo musu da Manzo mai bayyana gaskiya, watau Annabi Muhammadu (ﷺ). To lokacin da Alƙur’ani ya zo musu sai suka ƙaryata shi suka ce sihiri ne, kuma suka yi iƙirari da cewa su sun kafirce masa ba za su yi imani da shi ba. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani shisshigi na mushirikai da rashin ladabinsu gare shi, yayin da suka fito fili suka ce wai me ya sa lokacin da Allah ya tashi saukar da Alƙur’ani bai saukar da shi ga wani babban mutum daga alƙaryun nan guda biyu ba? Watau suna nufin me ya sa bai saukar da shi ga Al-Walid ɗan Mughira a Makka ko kuma Urwatu ɗan Mas’ud a Ɗa’ifa ba, maimakon haka sai ya saukar wa Muhammadu ɗan Abdullahi wanda yake shi talaka ne ba shi da komai? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, shin wai su ne suke raba rahamar Ubangiji, su ba wa wanda suka ga dama, su hana wanda suka ga dama, ko kuma Allah ne yake rabawa? Don haka shi ya ga dama ya zaɓi Annabi Muhammadu (ﷺ) ya ba shi annabta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi ne mai raba komai, domin shi ne ya raba musu arzikinsu a duniya, ya yi wani mawadaci wani kuma matalauci, ya ɗaukaka wani a kan wani wajen samu da matsayi na duniya, don wasu su zama masu yin hidima ga wasu. Kuma lalle su sani cewa, rahamar Allah ga bayinsa a lahira ta fi abin da suke tarawa na tarkacen duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu ƙasƙancin duniya da wulaƙantarta a wurinsa, inda ya bayyana cewa, ba don kada mutane gaba ɗayansu su zama kafirai ba, da sai ya sanya wa gidajen waɗanda suka kafirce masa rufi na azurfa, ya sanya musu matattakala ita ma ta azurfa, wadda za su riƙa takawa suna hawa ta kanta. Ya kuma sanya wa gidajensu ƙofofi da gadaje na alfarma da za su riƙa kishingiɗa a kansu, ya kuma ba su kayan ado na zinare, don hakan ya zama talala a gare su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa duk wannan ƙyale-ƙyale da kayan more rayuwa ba komai ba ne a wurinsa sai wani ɗan jin daɗin rayuwar duniya wanda bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta shi da na lahira wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanade shi musamman saboda bayinsa masu taƙawa, watau masu aiki da umarnisa da guje wa haninsa. An karɓo daga Sahlu ɗan Sa’ad (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Da a ce duniya ta kai darajar fiffiken sauro a wurin Allah, to da bai shayar da kafiri maƙwarwa ɗaya ta ruwa daga gare ta ba.” [Tirmizi #2320, dubi Al-Albani, As-Sahiha #686]. Daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda), daga Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lokacin da na shiga wurin Manzon Allah (ﷺ) sai na same shi kishingiɗe a kan tabarma babu wata shimfiɗa a kanta, har kabar tabarmar ta yi masa alama a ɓarin jikinsa, yana kishingiɗe a kan wani matashin kai na jemammiyar fata wanda aka cika shi da zaren itaciyar dabino. Na kuma ɗaga kaina na dubi ko’ina a cikin wannan gidan nasa, na rantse da Allah ban ga wani abu mai jan hankali ba sai wasu buzaye guda uku. Sai na ce: ‘Ka roƙi Allah ya yalwata arzikin al’ummarka, domin ya yalwata wa mutanen Farisa da Rum, ya ba su duniya ga shi ba sa ma bautar Allah’. Annabi (ﷺ) yana kishingiɗe, da jin haka sai ya tashi zaune ya ce: “Shin kana cikin kokwanto ne ya kai Ɗan Khaɗɗab? Waɗancan da kake magana, mutane ne da Allah ya gaggauto musu da jin daɗinsu a nan duniya.” Sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ya Manzon Allah, ka nema mini gafarar Allah.” [Bukhari #2468 da Muslim #1479].
وَمَن يَعۡشُ عَن ذِكۡرِ ٱلرَّحۡمَٰنِ نُقَيِّضۡ لَهُۥ شَيۡطَٰنٗا فَهُوَ لَهُۥ قَرِينٞ
Open ayah 43:36Wanda kuwa ya zama mai dundumi game da ambaton (Allah) Mai rahma, to za Mu haɗa shi da Shaiɗan ya zama shi ne abokinsa.
وَإِنَّهُمۡ لَيَصُدُّونَهُمۡ عَنِ ٱلسَّبِيلِ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُم مُّهۡتَدُونَ
Open ayah 43:37Lalle kuma su (shaiɗanun) tabbas suna kange su daga tafarki nagari, su kuma suna zato cewa lalle su shiryayyu ne.
حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَنَا قَالَ يَٰلَيۡتَ بَيۡنِي وَبَيۡنَكَ بُعۡدَ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ فَبِئۡسَ ٱلۡقَرِينُ
Open ayah 43:38Har zuwa lokacin da suka zo mana (wato mutumin da shaiɗaninsa) sai ya ce: “Ina ma a ce tsakanina da kai akwai nisan gabas da yamma; to tir da aboki irinka.”
وَلَن يَنفَعَكُمُ ٱلۡيَوۡمَ إِذ ظَّلَمۡتُمۡ أَنَّكُمۡ فِي ٱلۡعَذَابِ مُشۡتَرِكُونَ
Open ayah 43:39(Allah Ya ce da su): “A yau tun da kun riga kun yi zalunci zamantowarku tare a cikin azaba ba zai amfane ku ba A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin uƙubarsa ga wanda ya makance da gangan ya bijire wa Alƙur’ani wanda shi ne mafi girman rahamar Allah ga bayinsa, da cewa duk wanda ya aikata haka to kansa ya cuta, domin kuwa ya jawo Allah (Mai tsarki da daukaka) ya haɗa shi da wani shaiɗani da zai ƙulla abota da shi ba dare ba rana, ya yi ta ƙara ingiza shi cikin ɓata da hallaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗannan shaiɗanun abokan masu bijire wa Alƙur’ani za su yi ta hana su bin tafarkin Allah, sai su ƙi bin umarninsa su ƙi guje wa haninsa, duk da haka kuma su riƙa zaton su shiryayyu ne suna kan gaskiya, don haka ba su da ranar tuba su koma ga Allah. Har sai lokacin da ɗayansu ya gamu da Allah ranar alƙiyama, a lokacin ne zai cika da nadama marar amfani, ya riƙa burin ina ma a ce tsakaninsa da abokinsa shaiɗani akwai tazara mai nisan gabas da yamma a tsakaninsu. Sai ya yi tir da wannan aboki nasa, ya nesanta kansa da shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa mushirikai waɗanda suka zalunci kansu da kafirci cewa, haɗuwarsu tare a cikin azabar wutar Jahannama ba za ta amfane su da komai ba a wannan ranar, domin babu wani daga cikinsu da zai iya rage wa wani tsananin azabar da yake ciki. Kuma kasancewarsu duk sun haɗu a cikin wuta wannan ba zai sa su ji sanyi-sanyi a zukatansu ba.
أَفَأَنتَ تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ أَوۡ تَهۡدِي ٱلۡعُمۡيَ وَمَن كَانَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Open ayah 43:40Yanzu kai ka iya jiyar da kurme, ko kuma ka iya shiryar da makafi da wanda ya kasance cikin ɓata mabayyani?
فَإِمَّا نَذۡهَبَنَّ بِكَ فَإِنَّا مِنۡهُم مُّنتَقِمُونَ
Open ayah 43:41To idan Muka karɓi ranka, to lalle Mu Masu yi musu uƙuba ne.
أَوۡ نُرِيَنَّكَ ٱلَّذِي وَعَدۡنَٰهُمۡ فَإِنَّا عَلَيۡهِم مُّقۡتَدِرُونَ
Open ayah 43:42Ko kuma Muka nuna maka irin abin da muka yi musu alƙawarin narko da shi, to lalle Mu Masu iko ne a kansu.
فَٱسۡتَمۡسِكۡ بِٱلَّذِيٓ أُوحِيَ إِلَيۡكَۖ إِنَّكَ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 43:43To ka riƙe abin da aka yi maka wahayinsa; lalle kai kana kan hanya madaidaiciya.
وَإِنَّهُۥ لَذِكۡرٞ لَّكَ وَلِقَوۡمِكَۖ وَسَوۡفَ تُسۡـَٔلُونَ
Open ayah 43:44Kuma lalle shi (Alƙur’ani) ɗaukaka ce a gare ka da mutanenka; ba da daɗewa ba kuma za a tambaye ku (game da haƙƙinsa).
وَسۡـَٔلۡ مَنۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رُّسُلِنَآ أَجَعَلۡنَا مِن دُونِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ءَالِهَةٗ يُعۡبَدُونَ
Open ayah 43:45Ka tambayi waɗanda Muka aiko gabaninka daga manzanninmu, shin Mun sanya wasu ababen bauta da ake bauta musu ba (Allah) Mai rahma ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rarrashi Manzonsa (ﷺ) ne game da damuwar da yake ciki dangane da kafircin mutanensa da yadda suke ta ƙara taurin kai da bijire wa kiransa da cewa, ya sani fa ba zai iya jiyar da kurame ba, ko kuma ya shiryar da makafi ko ya shiryar da wanda ya yi nisa cikin ɓata mabayyani ba. Watau kamar dai yadda kurma ba zai taɓa jin wata murya ba, makaho kuma ba zai iya ganin komai ba, ko kuma wanda ya ɓace ɓat ba zai taɓa gane hanya ba, to hakanan su ma waɗannan mutanen nasa zukatansu sun riga sun lalace, hankulansu sun gurɓata saboda sun bijire wa sauraron Alƙur’ani da wa’azi, don haka sun sanya katangar ƙarfe tsakaninsu da shiriyar Allah. Waɗannan mutane ba abin da ya rage musu sai azabar Allah ta zo musu, ko dai tun a nan duniya ko kuma in sun je lahira. To saboda haka Allah ya kwantar wa da Manzonsa (ﷺ) hankali da cewa, ko da ya karɓi ransa kafin yi musu azaba, to lalle zai azabtar da su a duniya da lahira. Idan kuma Allah ya ga dama sai ya nuna masa wani yanki na azabar da yake yi musu alƙawarinta, domin Allah mai iko ne a kan komai babu abin da ya fi ƙarfinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ƙanƙame abin da ya yi masa wahayinsa ya yi aiki da shi, ya tabbatar masa cewa lalle shi yana bisa hanya madaidaiciya wadda babu ruɗani a cikinta. Ya kuma tabbatar masa, har ila yau, cewa Alƙur’ani ɗaukaka ce a gare shi, shi da mutanensa, domin ɗimbin alherin da ya ƙunsa, don haka su sani cewa sai an tambaye su a lahira game da wannan Alƙur’ani; shin sun yi imani da shi sun bi karantarwarsa sun kira mutane zuwa gare shi ko kuwa a’a? Sai kuma ya umarci Annabi (ﷺ) ya tambayi manzannin da ya aiko gabaninsa ya ji cewa, shin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya wasu alloli ana bauta musu ba shi ba? Watau da Manzo (ﷺ) zai bibiyi labaransu ya yi tambaya a kansu, ba zai sami manzo ɗaya ba da ya yi kira a bauta wa wani tare da Allah. Wannan ya tabbatar da cewa mushirikai ba su da wata hujja ta wahayi ko ta hankali a kan abin da suke yi na bautar wanin Allah.
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَقَالَ إِنِّي رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 43:46Haƙiƙa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, sai ya ce: “Lalle ni Manzo ne na Ubangijin talikai.”
فَلَمَّا جَآءَهُم بِـَٔايَٰتِنَآ إِذَا هُم مِّنۡهَا يَضۡحَكُونَ
Open ayah 43:47To lokacin da ya zo musu da ayoyinmu sai ga su suna yi musu dariya.
وَمَا نُرِيهِم مِّنۡ ءَايَةٍ إِلَّا هِيَ أَكۡبَرُ مِنۡ أُخۡتِهَاۖ وَأَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡعَذَابِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Open ayah 43:48Ba Mu kuma nuna musu wata aya ba sai wadda take ta fi `yar’uwarta girma; Muka kuma kama su da azaba don su dawo (kan hanya).
وَقَالُواْ يَٰٓأَيُّهَ ٱلسَّاحِرُ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ إِنَّنَا لَمُهۡتَدُونَ
Open ayah 43:49Suka kuma ce: “Ya kai wannan mai sihiri, ka roƙa mana Ubangijinka da abin da Ya yi maka wahayinsa (Ya yaye mana azaba), lalle mu tabbas za mu shiriya.”
فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابَ إِذَا هُمۡ يَنكُثُونَ
Open ayah 43:50To lokacin da Muka yaye musu azabar sai ga su suna warware alƙawari.
وَنَادَىٰ فِرۡعَوۡنُ فِي قَوۡمِهِۦ قَالَ يَٰقَوۡمِ أَلَيۡسَ لِي مُلۡكُ مِصۡرَ وَهَٰذِهِ ٱلۡأَنۡهَٰرُ تَجۡرِي مِن تَحۡتِيٓۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ
Open ayah 43:51Fir’auna kuma ya yi shela a cikin mutanensa ya ce: “Ya ku mutanena, yanzu mulkin Misra ba nawa ba ne, kuma ga ƙoramu suna ta kwarara ta ƙarƙashina, ko ba kwa gani ne?
أَمۡ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي هُوَ مَهِينٞ وَلَا يَكَادُ يُبِينُ
Open ayah 43:52“A\'a, ni na fi wannan wulaƙantaccen wanda da ƙyar yake iya bayani.
فَلَوۡلَآ أُلۡقِيَ عَلَيۡهِ أَسۡوِرَةٞ مِّن ذَهَبٍ أَوۡ جَآءَ مَعَهُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ مُقۡتَرِنِينَ
Open ayah 43:53“To me ya hana a saukar masa da warawarai na zinare, ko kuma wasu mala’iku su zo tare da shi suna masu dafa masa baya?”
فَٱسۡتَخَفَّ قَوۡمَهُۥ فَأَطَاعُوهُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Open ayah 43:54Sai ya yi wasa da hankalin mutanensa sai suka bi shi. Lalle su sun kasance mutane ne fasiƙai.
فَلَمَّآ ءَاسَفُونَا ٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 43:55To lokacin da suka fusata Mu sai Muka saukar musu da uƙuba, Muka nutsar da su ga baki ɗaya.
فَجَعَلۡنَٰهُمۡ سَلَفٗا وَمَثَلٗا لِّلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 43:56Sai Muka sanya su ja-gaba (wajen hallakarwa), kuma wa’azi ga na baya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana ba da labarin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne yayin da ya aike shi zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, ya ba shi mu’ujizoji masu tabbatar da gaskiyarsa, kamar sandarsa mai rikiɗewa ta zama macijiya da hannunsa mai haske kamar fitila. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yayin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya je musu ya shaida musu cewa lalle shi Manzo ne daga Allah Ubangijin dukkan halittu, to amma maimakon Fir’auna da fadawansa su yi imani da shi sai kawai suka ɓige da yi masa dariya suna yi masa izgili. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da nuna wa Fir’auna da mutanensa hujjoji masu tabbatar da manzancin Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Duk sanda ya tashi nuna musu wata hujja to yakan nuna musu hujjar da ta fi wadda ta gabace ta girma, domin Fir’auna da mutanensa su gamsu, to amma sai suka ci gaba da bijirewa da kafircewa, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kama su da azabar duniya don su dawo kan hanya, kamar azabar fari da kwaɗi da jini da sauransu, to amma kuma wannan bai amfana musu komai ba. A duk lokacin da wata azaba ta auka musu sai su roƙi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya roƙa musu Ubangijinsa saboda wahayin da ya yi masa na cewa idan sun yi imani zai yaye musu azaba. Sai su tabbatar masa da cewa za su yi imani idan har ya yaye musu ita, za su shiriya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da zarar ya yaye musu azabar sai su warware alƙawarin da suka yi masa, su ci gaba da kafircinsu. Shi kuma Fir’auna, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da mu cewa, ya ci gaba da yi wa mutanensa burga yana tinƙaho da ƙarfin mulkinsa, yana nuna musu cewa shi ne mai sarauta a Misra gaba ɗayanta, sannan ga shi ya gina tafka-tafkan gidaje na alfarma waɗanda ya ja ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu. Don haka su duba su ga irin wannan matsayi nasa da ƙarfin mulki da arziki da yake da shi. Saboda haka ya nuna musu cewa yanzu shi ya kamata su bi, ko kuma za su bi Musa wanda yake wulaƙantacce talaka marar gata wanda ko magana bai iya ba? Sannan Fir’auna ya nuna wa mutanensa cewa idan Musa da gaske Allah ne ya aiko shi me ya hana ya haɗo shi da kayan ado na warawarai na zinare ko wasu mala’iku su zo tare da shi suna gaskata shi? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Fir’auna ya raina hankalin mutanensa har ya ruɗe su da maganganunsa na shirme, su kuma suka bi shi a kan ɓatansa, domin su mutane ne fasiƙai, shi ya sa Fir’auna ya sami lagonsu har ya ƙara dulmiyar da su cikin ɓata da hallaka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da Fir’auna da mutanensa suka fusata shi suka dage a kan kafircinsu da ƙaryata Annabi Musa, sai ya saukar musu da azabarsa, ya nutsar da su cikin kogi dukkansu suka hallaka, ya kuma tserar da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da waɗanda suka yi imani da shi daga Banu Isra’ila. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya Fir’auna da manyan fadawansa suka zamanto ja-gaba wajen hallakarwa, kafiran Makka kuma suna tafe a bayansu. Ya mayar da su wa’azi ga wanda zai wa’azantu ya guji irin aikinsu don kada irin abin da ya same su shi ma ya same shi.
۞وَلَمَّا ضُرِبَ ٱبۡنُ مَرۡيَمَ مَثَلًا إِذَا قَوۡمُكَ مِنۡهُ يَصِدُّونَ
Open ayah 43:57Lokacin da kuwa aka buga misali da (Isa) ɗan Maryamu, sai ga mutanenka suna ta annashawa game da shi.
وَقَالُوٓاْ ءَأَٰلِهَتُنَا خَيۡرٌ أَمۡ هُوَۚ مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلَۢاۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٌ خَصِمُونَ
Open ayah 43:58Suka kuma ce: “Yanzu ababen bautar mu ne suka fi ko kuwa shi (Isa)?” Ba su buga maka misali da shi ba sai don son jayayya. Ba shakka su dai mutane ne masu tsananin jayayya.
إِنۡ هُوَ إِلَّا عَبۡدٌ أَنۡعَمۡنَا عَلَيۡهِ وَجَعَلۡنَٰهُ مَثَلٗا لِّبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ
Open ayah 43:59Shi (Isa) ba wani ba ne face bawa ne da Muka yi masa ni’ima, Muka kuma sanya shi abin buga misali ga Bani-Isra’ila.
وَلَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَا مِنكُم مَّلَٰٓئِكَةٗ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَخۡلُفُونَ
Open ayah 43:60Da kuma za Mu ga dama tabbas da Mun sanya mala’iku ne za su maye gurbinku a bayan ƙasa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafiran Makka suka riƙa jayayya da Manzon Allah (ﷺ) don tabbatar da bautar gumakansu, lakacin da suka ji Manzon Allah (ﷺ) yana hana su bautar wani ba Allah ba, yana nuna musu cewa, su da duk abubuwan da suke bauta wa ba Allah ba gaba ɗayansu wuta za su. Ibn Is’haƙ ya ruwaito a cikin littafinsa na Sira cewa, wata rana Manzon Allah (ﷺ) yana zaune a Masallacin Makka tare da wasu manyan Ƙuraishawa irin su Al-Walid ɗan Mugira da Nadhru ɗan Haris, sai suka shiga jayayya da shi a kan bautarsu ta gumaka, sai Manzon Allah (ﷺ) ya karanta musu faɗar Allah: “Lalle ku da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, (duka) makamashin Jahannama ne, kuma ku masu shigar ta ne.” [Al-Anbiya aya ta 98]. Sai Abdullahi ɗan Az-Ziba’ara ya shigo ya zauna, da aka gaya masa abin da Annabi (ﷺ) yake karantawa sai ya ce: “Wallahi sai na ƙure shi da hujja, ku tambayi Muhammadu, shin duk abin da aka bauta wa ba Allah ba za a sa shi wutar Jahannama tare da wanda ya bauta masa kenan? To mu muna bautar mala’iku, Yahudawa kuma suna bauta wa Uzairu, Nasara kuma suna bauta wa Isa ɗan Maryam, watau duk za su tafi wuta kenan?” Da jin haka sai mushirikai suka yi ta murna suna shewa wai an ƙure Manzon Allah (ﷺ) da hujja. Yayin da Manzon Allah (ﷺ) ya ji abin da Ɗan Az-Ziba’ara ya faɗa sai ya ce: “Lalle duk wanda ya so a bauta masa ba Allah ba, to yana tare da wanda ya bauta masa, kuma lalle su shaiɗanu suke bauta wa da wanda suka umarta a bauta masa.” Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da faɗarsa: “Lalle waɗanda kalmarmu mafi kyau (ta cewa, su ‘yan Aljanna ne) ta riga ta tabbata a gare su, waɗannan waɗanda ake nesantawa ne daga gare ta (wutar). Ba za su ji hargowarta ba, kuma su masu dawwama ne a cikin abin da ransu yake so.” [Al-Anbiya, aya ta 100-101]. Watau mala’iku da Uzairu da Annabi Isa da sauran mutane nagari da aka bauta wa ba da yardarsu ba, ba za a sa su a wuta ba. [Dubi, Ibn Hisham, As-Sira , Juzu’i na 1, shafi na 359-360]. A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana cewa lokacin da Ibnu Az-Ziba’ara ya ba da misali da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don ya ƙure Manzon Allah (ﷺ) mushirikan Makka sun yi ta sowa suna murna, suna cewa “Mun yarda allolinmu su zama kamar Isa, watau idan har za a sa Isa tare da masu bautarsa wuta, to mu ma za a sa mu tare da gumakanmu, domin ababen bautarmu ne suka fi ko Isa?” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, wannan misalin da suka ba shi na Annabi Isa ba niyyarsu fahimtar gaskiya ba ne, manufarsu kawai ita ce jayayya don tabbatar da ƙarya, domin su da man mutane ne masu tsananin jayayya da husuma. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa shi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ba wani ne ba face bawa daga cikin bayin Allah da ya ni’imta shi da annabta da manzanci, ya kuma sa shi misali ga Banu Isra’ila don su gane cikar Ƙudurar Allah yayin da ya halicce shi ba uba kamar yadda ya halicci Annabi Adamu ba uwa ba uba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tsoratar da su da cewa da ya ga dama da sai ya hallaka su, ya kawo mala’iku a maimakonsu su maye gurbin ‘yan’adam a bayan ƙasa, su yi ta bautar Allah ba tare da suna haɗa shi da komai ba.
وَإِنَّهُۥ لَعِلۡمٞ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمۡتَرُنَّ بِهَا وَٱتَّبِعُونِۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
Open ayah 43:61Lalle kuma shi (Isa) alama ce ta zuwan alƙiyama, kada ku yi shakka game da ita, kuma ku bi Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.
وَلَا يَصُدَّنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُۖ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Open ayah 43:62Kada kuma Shaiɗan ya kange ku; lalle shi maƙiyi ne mai bayyana (ƙiyyaya) a gare ku.
وَلَمَّا جَآءَ عِيسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالَ قَدۡ جِئۡتُكُم بِٱلۡحِكۡمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعۡضَ ٱلَّذِي تَخۡتَلِفُونَ فِيهِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Open ayah 43:63Lokacin da kuma Isa ya zo da hujjoji bayyanannu ya ce: “Haƙiƙa na zo muku da hikima, don kuma in bayyana muku sashin da kuke sassaɓawa cikinsa; to ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku bi ni.
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ
Open ayah 43:64“Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.”
فَٱخۡتَلَفَ ٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَيۡنِهِمۡۖ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡ عَذَابِ يَوۡمٍ أَلِيمٍ
Open ayah 43:65Sai ƙungiyoyi suka sassaɓa a tsakaninsu; don haka tsananin azabar yini mai raɗaɗi ya tabbata ga waɗanda suka yi zalunci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin matsayin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) inda ya nuna cewa shi alama ce daga cikin alamomin tashin alƙiyama, lokacin da zai sauko daga sama ta biyu a ƙarshen zamani. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hana mutane su riƙa shakka game da zuwan ranar alƙiyama domin sai ta tabbata babu makawa. Ya kuma umarce su da su bi shi game da duk abin da yake labarta musu su gaskata shi, domin wannan shi ne hanya madaidaiciya. Sai kuma Allah ya tsawatar musu da cewa, kada su bari Shaiɗan ya hana su bin hanyar Allah miƙaƙƙiya da ruɗinsa da yaudararsa, domin shi maƙiyinsu ne mai bayyana ƙiyayya a gare su. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yayin da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya je wa mutanensa da dalilai bayyanannu a kan cewa shi lalle Manzon Allah ne, ya shaida musu cewa ya zo musu da wata hikima daga Allah, watau annabci da wahayi, kuma don ya yi musu bayanin wani ɓangare na addininsu da suke saɓani a kansa. Ya ja hankalinsu a kan su kiyaye dokokin Allah su bi umarninsa su guje wa haninsa, shi ma su yi masa biyayya cikin umarninsa da haninsa. Ya tabbatar musu cewa Allah ne Ubangijinsa su ma shi ne Ubangijinsu, ba su da wani abin bauta ba shi ba, don haka su tsarkake shi da bauta shi kaɗai. Wannan Tauhidin shi ne miƙaƙƙiyar hanya da babu karkata tare da ita. To amma duk da wannan bayani da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi musu sai ga shi wasu ƙungiyoyi a tsakaninsu sun sassaɓa dangane da sha’aninsa; wasu suka ce shi Allah ne, wasu kuma suka ce ɗan Allah ne, wasu kuma suka ce shi da mahaifiyarsa duka alloli ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa duk waɗanda suka yi zalunci wajen allantar da Annabi Isa da mahaifiyarsa ko da’awar cewa ɗan Allah ne, to tsananin azaba ya tabbata a gare su a ranar alƙiyama wadda tana nan tana jiran su.
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ
Open ayah 43:66Ba abin da suke jira sai alƙiyama kawai ta zo musu kwatsam, alhali ba tare da sun sani ba.
ٱلۡأَخِلَّآءُ يَوۡمَئِذِۭ بَعۡضُهُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوٌّ إِلَّا ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 43:67Masoya a wannan ranar maƙiyan juna ne sai masu taƙawa kaɗai.
يَٰعِبَادِ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡكُمُ ٱلۡيَوۡمَ وَلَآ أَنتُمۡ تَحۡزَنُونَ
Open ayah 43:68Ya ku bayina, babu wani tsoro gare ku a yau, kuma ba za ku yi baƙin ciki ba.
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ مُسۡلِمِينَ
Open ayah 43:69(Su ne) waɗanda suka yi imani da ayoyinmu, suka kuma kasance Musulmi.
ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ أَنتُمۡ وَأَزۡوَٰجُكُمۡ تُحۡبَرُونَ
Open ayah 43:70(Za a ce da su): “Ku shiga Aljanna ku da matanku, za a faranta muku rai.”
يُطَافُ عَلَيۡهِم بِصِحَافٖ مِّن ذَهَبٖ وَأَكۡوَابٖۖ وَفِيهَا مَا تَشۡتَهِيهِ ٱلۡأَنفُسُ وَتَلَذُّ ٱلۡأَعۡيُنُۖ وَأَنتُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Open ayah 43:71Ana zagayawa tsakaninsu da akusa na zinari da kofuna; a cikinta kuma akwai (duk) abin da rayuka suke sha’awa, idanuwa kuma suke jin daɗin (ganinsu); ku kuma a cikinta madawwama ne.
وَتِلۡكَ ٱلۡجَنَّةُ ٱلَّتِيٓ أُورِثۡتُمُوهَا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 43:72Waccan kuma ita ce Aljannar da aka gadar muku ita saboda abin da kuka kasance kuma aikatawa.
لَكُمۡ فِيهَا فَٰكِهَةٞ كَثِيرَةٞ مِّنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 43:73A cikinta kuna da `ya`yan itatuwa na marmari masu yawa, daga gare su kuma za ku riƙa ci. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa duk masu ƙaryata manzannin Allah da haɗa shi da wasu ababen bauta, ba komai suke jira ba sai alƙiyama ta zo musu kwatsam ba zato ba tsammani. To idan har ta riske su suna cikin wannan kafircin nasu to makomarsu ita ce azabar Allah mai tsanani. Sai kuma ya bayyana cewa duk wata abokantaka da soyayya za su rikiɗe a ranar alƙiyama su zama ƙiyayya, in ban da soyayyar da aka ƙulla ta don Allah, watau soyayyar masu taƙawa, wannan kam mai ɗorewa ce har abada. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abubuwa uku wanda suka kasance tare da shi to ya samu ɗanɗanon imani; ya fi son Allah da Manzonsa fiye da komai; ya kuma so bawa ba don komai ba sai don Allah; ya kuma yi ƙyamar komawa cikin kafirci bayan Allah ya tserar da shi daga gare shi, kamar yadda yake ƙin a jefa shi cikin wuta.” [Bukhari #21 da Muslim #43]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle Allah a ranar alƙiyama zai ce: ‘Ina masu soyayya domin girmana? A yau zan saka su cikin inuwata ranar da babu wata inuwa sai inuwata.’” [Muslim #2566]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa zai kirawo bayinsa a wannan ranar da siffar bayinsa masu daraja da cewa, babu wani tsoro da za su fuskanta a wannan ranar, kuma ba za su yi baƙin cikin abin da suka baro ba a duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta waɗannan bayi nasa da cewa, su ne waɗanda suka yi imani da ayoyinsa, watau Alƙur’ani mai girma, suka kuma kasance masu miƙa wuya a gare shi, suna aiki da karantarwarsa, suna bin umarninsa suna kuma guje wa haninsa. A ranar za a umarci waɗannan bayi da su shiga Aljanna su da waɗanda suke ire-irensu masu ayyuka na ƙwarai irin nasu, kamar matayensu da ‘ya’yansu da sauran makusantansu, inda za su sami farin ciki marar yankewa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani sashe na ni’imar da za a faranta musu rai da ita a gidan Aljanna, yayin da hadimansu za su riƙa zagayawa a tsakaninsu da akusa na zinare da kofunan zinare cike da abubuwan shaye-shaye. Kuma Allah ya tanadar musu duk abin da ransu yake sha’awa, idanuwansu kuma suke jin daɗin ganin sa a gidan Aljanna, ga shi kuma za su yi ta zama ne a cikinta har abada babu mai fitar da su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa wannan gida na Aljanna da yake cike da ni’imomi iri-iri shi ne wanda ya gadar musu da shi saboda kyawawan ayyukan da suka kasance suna aikatawa a duniya. Ya kuma sanar da su cewa, a cikin Aljanna suna da ‘ya’yan itatuwa na marmari masu yawa waɗanda ba sa yankewa, waɗanda za su riƙa ci. Watau bayan an ambaci abubuwan ci da na sha sai kuma aka ambaci kayan marmari domin a cika musu ni’ima da farin ciki.
إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي عَذَابِ جَهَنَّمَ خَٰلِدُونَ
Open ayah 43:74Lalle masu manyan laifuka suna cikin azabar (wutar) Jahannama suna masu dawwama.
لَا يُفَتَّرُ عَنۡهُمۡ وَهُمۡ فِيهِ مُبۡلِسُونَ
Open ayah 43:75Ba a yanke musu ita (azabar), su kuwa masu yanke ƙaunar (fita) ne daga cikinta.
وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن كَانُواْ هُمُ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 43:76Ba Mu kuwa zalunce su ba, sai dai su ne suka kasance azzalumai.
وَنَادَوۡاْ يَٰمَٰلِكُ لِيَقۡضِ عَلَيۡنَا رَبُّكَۖ قَالَ إِنَّكُم مَّٰكِثُونَ
Open ayah 43:77Suka kuma yi kiran: “Ya (kai mai tsaron wuta) Maliku, Ubangijinka Ya kashe mu mana!” Ya ce: “Lalle ku masu dawwama ne.”
لَقَدۡ جِئۡنَٰكُم بِٱلۡحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَكُمۡ لِلۡحَقِّ كَٰرِهُونَ
Open ayah 43:78Haƙiƙa Mun zo muku da gaskiya sai dai kuma mafiya yawanku masu ƙin gaskiya ne.
أَمۡ أَبۡرَمُوٓاْ أَمۡرٗا فَإِنَّا مُبۡرِمُونَ
Open ayah 43:79A’a, sun dai shirya wani makirci ne, Mu ma lalle Masu yin namu shirin ne.
أَمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّا لَا نَسۡمَعُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيۡهِمۡ يَكۡتُبُونَ
Open ayah 43:80Ko kuma suna tsammanin cewa Mu ba Ma jin asirinsu da ganawarsu ne? Ba haka ba ne, manzanninmu suna tare da su suna rubutawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon kafirai masu ƙaryata ayoyinsa, da cewa a ranar alƙiyama za su tsunduma cikin wutar Jahannama, za su kuma dawwama a cikinta har abada. Kuma ba za a sassauta musu azaba ba ko da ta yini ɗaya, sannan za su yanke ƙaunar samun wata rahamar Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa wannan azaba da ta same su ba Allah ne ya zalunce su ba, su ne suka zalunci kawunansu da aikata kafirci da saɓon Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa idan wuya ta yi wuya ga ‘yan wuta za su riƙa kururuwa suna kiran Mala’ika Maliku mai tsaron wuta suna kamun ƙafa da shi a kan ya roƙa musu Allah ya karɓi ransu don su huta da tsananin azabar da suke ciki. Sai Maliku ya amsa musu da cewa haka za su yi ta zama cikin matsananciyar azaba har abada babu ƙaƙƙautawa. Daga nan sai ya daka musu tsawa yana mai tuna musu taurin kansu a duniya shi ne ya jawo musu wannan wahalar, domin mala’iku sun yi ta zuwa musu da gaskiya, watau wahayin da Mala’ika Jibrilu ya riƙa sauka da shi zuwa ga annabawa, to amma mafiya yawansu masu ƙin gaskiya ne. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin makircin da mushirikai suka yi ta ƙulla wa Manzonsa (ﷺ) yadda za su murƙushe gaskiya su kashe ta murus, to amma ba su san cewa shi ma Allah yana shirya nasa al’amarin ba ne wanda zai murƙushe makircinsu da mummunan shirinsu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi kafirai da cewa, shin suna zaton cewa ba ya jin abin da suke ɓoyewa a zukatansu na mugun nufi ko wanda suke ƙullawa yayin ganawarsu ta sirri? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, yana jin komai da suke ƙullawa, kuma mala’ikunsa suna tare da su suna rubuta duk wani motsinsu.
قُلۡ إِن كَانَ لِلرَّحۡمَٰنِ وَلَدٞ فَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡعَٰبِدِينَ
Open ayah 43:81Ka ce: “Idan da (Allah) Mai rahma zai zamanto Yana da ɗa, to ni ne farkon masu bauta.”
سُبۡحَٰنَ رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ رَبِّ ٱلۡعَرۡشِ عَمَّا يَصِفُونَ
Open ayah 43:82Tsarki ya tabbata ga Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangiijn Al’arshi game da abin da suke siffantawa.
فَذَرۡهُمۡ يَخُوضُواْ وَيَلۡعَبُواْ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ
Open ayah 43:83Sai ka bar su su yi ta kutse suna wasanni, har su haɗu da ranar da ake alƙawarta musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya faɗa wa mushirikai masu cewa, Allah yana da ‘ya’ya mata watau mala’iku, cewa idan har za a ƙaddara cewa Allah mai rahama yana da ɗa, to ya tabbatar musu cewa shi ne farkon masu bauta wa wannan ɗan, domin kuwa zai zama wani sashi ne nasa. Shi kuma Manzon (ﷺ) Allah shi ne wanda ya fi kowa cancantar ya miƙa wuya ga abin da Allah yake so, to amma abin ba haka yake ba, Allah ba shi da ɗa, don haka Manzonsa (ﷺ) shi ne farkon masu musunta haka da kore wa Allah ɗa. Wannan shi ya tabbatar da ɓacin wannan aƙidar. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkake kansa daga duk wata tawaya ko aibu dangane da abin da mushirikai suke jingina masa na mata da ‘ya’ya, domin kuwa shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al’arshi mafi girman halittunsa. Sai kuma Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi watsi da mushirikai da duk wani irin kutsen da suke yi cikin kafirci da saɓon Allah da wasanninsu na duniya har sai sun haɗu da ranar da ake yi musu alƙawarin zuwanta, watau ranar alƙiyama inda za su ga sakamakon munanan ayyukansu.
وَهُوَ ٱلَّذِي فِي ٱلسَّمَآءِ إِلَٰهٞ وَفِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَٰهٞۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 43:84Shi ne kuma Wanda Yake Abin bauta a cikin sama kuma Abin bauta a ƙasa. Kuma Shi Mai hikima ne, Masani.
وَتَبَارَكَ ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَعِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلسَّاعَةِ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 43:85Kuma wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu alhairansa sun yi yawa, kuma a wurinsa sanin (ranar) alƙiyama yake, wurinsa kuma za a komar da ku.
وَلَا يَمۡلِكُ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِ ٱلشَّفَٰعَةَ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 43:86Waɗanda kuwa suke bauta wa wani abu ba Shi ba, ba sa mallakar ceto, sai dai waɗanda suka yi Kalmar Shahada ta gaskiya, alhalin suna sane (da ma’anarta).|
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَهُمۡ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۖ فَأَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ
Open ayah 43:87Tabbas kuma da za ka tambaye su, wane ne ya halicce su? Lalle za su ce: “Allah ne;” to ta yaya ake kautar da su?
وَقِيلِهِۦ يَٰرَبِّ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ قَوۡمٞ لَّا يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 43:88Kuma (sanin) faɗarsa (wato Ma’aiki) cewa: “Ya Ubangiji lalle waɗannan mutane ne da ba sa yin imani,” (yana a wurinsa).
فَٱصۡفَحۡ عَنۡهُمۡ وَقُلۡ سَلَٰمٞۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ
Open ayah 43:89To ka kawar musu kai, kuma ka ce: “Na kuɓuta (daga haƙƙinku). Don haka ba da daɗewa ba za ku sani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa shi ne kaɗai abin bauta na gaskiya a sama da kuma a ƙasa, kuma shi ne mai hikima a cikin halittarsa da Ƙaddararsa da tsarinsa; masanin halayen bayinsa da ayyukansu ne. Kuma albarkatunsa sun yawaita, shi ne kaɗai mamallakin sammai da ƙasa da duk abin da yake tsakaninsu, kuma shi kaɗai ne ya san lokacin zuwan ranar alƙiyama, ranar da kowa da komai za a mayar da su zuwa gare shi, domin yin hisabi da sakamako. Haka kuma ya tabbatar wa mushirikai cewa abubuwan da suke bauta wa ba Allah ba suna zaton za su cece su a wurinsa a ranar alƙiyama ba za su mallaki ceton kowa ba. Babu wanda zai yi ceto a ranar sai wanda ya shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah, yana kuma sane da ma’anar Kalmar Shahadar da ya yi, kamar Annabi Isa da Uzairu da mala’iku, waɗannan suna cikin masu ceto ga waɗanda suka mutu a kan Tauhidi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake bayyana wa Manzonsa (ﷺ) wata tufka da warwara ta kafirai masu barin bautar Allah mahalicci, su kama bautar waninsa, da cewa, da zai tambaye su, wane ne ya halicce su? Ba su da wata amsa da ta wuce su ce, Allah ne ya halicce su. To abin mamaki ta yaya ake kautar da su daga bautar Allah bayan sun yarda shi ne mahaliccinsu? Daga nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yana sane da koken da Manzonsa (ﷺ) yake kai masa na cewa, mutanensa sun ƙaryata shi, sun ƙi yin imani da abin da ya aiko shi zuwa gare su da shi. A ayar ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa da ya kawar da kansa daga gare su, ya faɗa musu abin da zai kare kansa daga sharrinsu, domin ba da daɗewa ba za su san uƙubar da za ta faru gare su.