الدخان
Ad-Dukhaan
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
حمٓ
Open ayah 44:1Ha Mim.
وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ
Open ayah 44:2Na rantse da Littafi mai bayyanawa (shi ne Alƙur’ani).
إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ فِي لَيۡلَةٖ مُّبَٰرَكَةٍۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ
Open ayah 44:3Lalle Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka. Lalle Mu Mun kasance Masu gargaɗi.
فِيهَا يُفۡرَقُ كُلُّ أَمۡرٍ حَكِيمٍ
Open ayah 44:4A cikinsa ne (daren) ake fasalta kowane tabbataccen al’amari (na wannan shekara).
أَمۡرٗا مِّنۡ عِندِنَآۚ إِنَّا كُنَّا مُرۡسِلِينَ
Open ayah 44:5Al\'amari ne (da Muke fasaltawa) daga wurinmu. Lalle Mun kasance Mu ne Masu aikowa (da manzanni).
رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 44:6Don rahama daga Ubangijinka. Lalle shi Mai ji ne, Masani.
رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Open ayah 44:7Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu; idan kun kasance masu sakankancewa.
لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 44:8Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, Shi ne Yake rayarwa Yake kuma kashewa; (Shi ne) Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko.
بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ يَلۡعَبُونَ
Open ayah 44:9A’a, su dai suna cikin shakka ne, suna wasanni. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da wasu haruffa kamar yadda a baya ya buɗe wasu surori da irinsu. [Dubi bayaninsu a farkon tafsirinmu na Suratul Baƙara ]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da Alƙur’ani wanda yake ɗauke da bayanin hanyar shiriya mai kaiwa zuwa gaskiya. Ya kuma tabbatar da cewa shi ne ya saukar da wannan Alƙur’anin a cikin wani dare mai albarka, shi ne daren Lailatul Ƙadari, wanda yake dare ne mai cike da alherai. Sai kuma ya bayyana hikimar saukar da shi da cewa, Allah shi ne mai gargaɗin mutane, ta hanyar nuna musu abin da zai amfane su da sanar da su abin da zai cutar da su, domin hujjarsa ta kafu a kan kowa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sirrin da ke cikin wannan daren na Lailatul Ƙadari da ya zaɓa don saukar da Alƙur’ani a cikinsa, inda ya ambaci cewa a cikinsa ne ake tantance dukkan tabbatattun al’amura waɗanda suka shafi rabon arziƙi da tsawon rai da sauran abubuwa da Allah ya hukunta za su faru a wannan shekarar. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa wannan wani al’amari ne daga wajensa, babu wanda ya isa ya canja shi ko ya kawar da shi, sannan mutane su sani cewa shi ne mai aiko da manzanni zuwa gare su don su karanta musu ayoyinsa. Ya kuma yi haka ne don rahama daga gare shi ga bayinsa domin su rarrabe tsakanin shiriya da ɓata, saboda shi mai jin maganganun bayinsa ne, masanin ayyukansu, don haka shi ya fi sanin abin da ya dace da su a rayuwarsu ta duniya da ta lahira. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kaɗaitakarsa a kan halittar sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu da iko da su, don haka idan mutane sun sakankance da haka, to lallai su yi imani da shi su bi Manzonsa (ﷺ) da ya aiko. Allah kuma ya tabbatar musu cewa shi ne kaɗai abin bauta na gaskiya, domin shi kaɗai ne mai rayawa mai kashewa, shi ne kuma Ubangijinsu kuma Ubangijin iyayensu na farko. To amma kuma su waɗannan mushirikai ba su sakankance da hakan ba, don haka suna cikin shakka, wasannin banza sun ɗauke musu hankali sun gafala daga tunanin manufar da ta sa aka halicce su, watau don bautar Allah shi kaɗai.
فَٱرۡتَقِبۡ يَوۡمَ تَأۡتِي ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٖ مُّبِينٖ
Open ayah 44:10Sai ka saurari ranar da sama za ta zo da hayaƙi bayyananne.
يَغۡشَى ٱلنَّاسَۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 44:11Zai lulluɓe (idanuwan) mutane; wannan azaba ce mai raɗaɗi.
رَّبَّنَا ٱكۡشِفۡ عَنَّا ٱلۡعَذَابَ إِنَّا مُؤۡمِنُونَ
Open ayah 44:12(Za su ce): “Ya Ubangijinmu, Ka yaye mana wannan azaba, lalle mu masu yin imani ne.”
أَنَّىٰ لَهُمُ ٱلذِّكۡرَىٰ وَقَدۡ جَآءَهُمۡ رَسُولٞ مُّبِينٞ
Open ayah 44:13Ta ina wa’azi zai amfane su, alhali kuwa haƙiƙa Manzo mai bayani ya zo musu?
ثُمَّ تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَقَالُواْ مُعَلَّمٞ مَّجۡنُونٌ
Open ayah 44:14Sannan suka juya masa baya suka ce: “Ai wani ne ya koya masa, (kuma shi) taɓaɓɓe ne.
إِنَّا كَاشِفُواْ ٱلۡعَذَابِ قَلِيلًاۚ إِنَّكُمۡ عَآئِدُونَ
Open ayah 44:15Lalle Mu Masu yaye muku azabar ne ɗan lokaci kaɗan. Lalle (kuma) ku masu komawa ne.
يَوۡمَ نَبۡطِشُ ٱلۡبَطۡشَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ إِنَّا مُنتَقِمُونَ
Open ayah 44:16(Ka tuna) ranar da za Mu damƙe su babbar damƙa, lalle Mu Masu sakawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi Manzonsa (ﷺ) tare da kakkausan jan kunne ga mushirikai masu ƙaryata shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya jira zuwan wata azaba ta kurkusa ga mutanensa, ranar da sama za ta zo da wani hayaƙi wanda idanuwansu za su riƙa nuna musu shi saboda tsananin yunwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, wannan azaba za ta lulluɓe mutanensa, a lokacin za a riƙa faɗa musu cewa wannan azaba ce mai raɗaɗi. Sai su kuma suna masu ƙasƙantar da kai ga Allah suna roƙon sa ya yaye musu azabar da suke ciki sun yi masa alƙawarin za su yi imani da shi da Manzonsa. To amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya san alƙawarinsu na banza ne ba cikawa za su yi ba, domin kuwa ta yaya za su wa’azantu su koma ga Allah alhali ga Manzo ya zo musu yana bayyana musu saƙon Allah a fili, sun kuma san gaskiyarsa da amanarsa amma suka ƙi yin imani da shi, suka ma juya masa baya suna zargin sa da cewa Alƙur’ani da yake karanta musu wani ne ya koya masa ba wahayi ne daga Allah ba, kuma shi mai taɓin hankali ne. Sai yanzu ne za su yi alƙawarin cewa za su yi imani da shi? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa lalle shi zai yaye musu azabar zuwa wani ɗan lokaci, to amma ya san ba za su cika alƙawarinsu ba; za su sake komawa ga laifukansu ne. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da su cewa idan wannan gargaɗin da azabar ba ta yi musu amfani ba, to su jira ranar da Allah zai damƙe su kyakkyawar damƙa, ita ce ranar yaƙin Badar, lalle a ranar Allah sai ya yi musu azabar ramuwa saboda kafircinsu ga Allah da Manzonsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da Ƙuraishawa suka tirje suka ƙi karɓar Musulunci daga hannun Annabi (ﷺ), sai ya roƙi Allah ya jarrabe su da fari da yunwa irin ta zamanin Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sai kuma Allah ya karɓi addu’arsa, aka jarrabe su da ƙunci da yunwa har ta kai suna cin ƙasusuwa da mushen dabba. Idan sun ɗaga kansu sama ba abin da suke gani sai hayaƙi saboda tsananin yunwa. Sai Abu Sufyana ya je ya sami Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Ya Muhammadu, kai ne kake umarni da a yi wa Allah biyayya da sada zumunci, to amma kana gani ga mutanenka nan suna ta mutuwa, ka roƙa musu Allah mana ya yaye musu halin da suke ciki?” [Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar da waɗannan ayoyin daga farkon aya ta 10 zuwa ta 16]. [Bukhari #1007 da Muslim #2798]. A wata ruwayar: Annabi (ﷺ) ya yi musu addu’a sai aka samu ruwan sama mai yawa har tsawon mako guda ba ƙaƙƙautawa har sai da mutane suka fara kokawa da yawan ruwan, sannan Manzon Allah (ﷺ) ya yi addu’ar a janye musu shi daga cikin gari zuwa bayan gari. [Bukhari #1020]. Daga baya kuma suka ci gaba da kafircinsu da muzguna wa Manzon Allah (ﷺ) sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu mummunar damƙa a yaƙin Badar inda aka kashe manya-manyansu. [Dubi, Bukhari #4822].
۞وَلَقَدۡ فَتَنَّا قَبۡلَهُمۡ قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَ وَجَآءَهُمۡ رَسُولٞ كَرِيمٌ
Open ayah 44:17Haƙiƙa kuma Mun jarrabi mutanen Fir’auna tun kafin su, kuma Manzo mai karamci ya zo musu.
أَنۡ أَدُّوٓاْ إِلَيَّ عِبَادَ ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
Open ayah 44:18(Da cewa): “Ku ba ni bayin Allah (watau Banu Isra’ila); lalle ni Manzo ne amintacce a gare ku.
وَأَن لَّا تَعۡلُواْ عَلَى ٱللَّهِۖ إِنِّيٓ ءَاتِيكُم بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ
Open ayah 44:19“Kuma kada ku yi wa Allah girman kai; lalle ni zan kawo muku hujjoji mabayyana.
وَإِنِّي عُذۡتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمۡ أَن تَرۡجُمُونِ
Open ayah 44:20“Kuma lalle ni ina neman tsari na Ubangijina kuma Ubangijinku, don kada ku jefe ni.
وَإِن لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ لِي فَٱعۡتَزِلُونِ
Open ayah 44:21“Idan kuma ba ku yi imani da ni ba sai ku ƙyale ni.”
فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنَّ هَٰٓؤُلَآءِ قَوۡمٞ مُّجۡرِمُونَ
Open ayah 44:22Sai ya roƙi Ubangijinsa cewa: “Lalle waɗannan mutane ne masu manyan laifuka.”
فَأَسۡرِ بِعِبَادِي لَيۡلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Open ayah 44:23Sai (aka ce masa): “Ka tafi da bayina da daddare, lalle ku za a biyo bayanku.
وَٱتۡرُكِ ٱلۡبَحۡرَ رَهۡوًاۖ إِنَّهُمۡ جُندٞ مُّغۡرَقُونَ
Open ayah 44:24“Kuma ka bar kogi a tsaye cak (bayan tsallakewa); lalle su runduna ne da za a nutsar.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Manzonsa (ﷺ) cewa ba shi ne farkon Annabin da mutanensa suka ƙaryata ba, akwai waɗanda suka gabace shi da yawa waɗanda mutanensu suka ƙaryata su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana masa cewa, a can baya ya jarrabi mutanen Fir’auna ya aika musu Manzonsa mai karamci, watau Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Yayin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya je wa Fir’auna da mutanensa sai ya neme su da su sakar masa bayin Allah waɗanda suke tsare da su suna gana musu azaba ba don sun yi musu wani laifi ba sai don zalunci, su ne Banu Isra’ila da ke ɗaure a wurin Fir’auna. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar musu da cewa shi Manzon Allah ne amintacce zuwa gare su, ba zai ɓoye musu komai daga saƙon Allah ba, ba kuma zai ƙara ko ya rage ba. Ya gargaɗe su cewa, kada su kuskura su ce za su yi wa Allah girman kai su ci gaba da kafirce masa da zaluntar bayinsa, ya tabbatar musu da cewa, zai zo musu da hujja bayyananna mai tabbatar da gaskiyarsa. To amma sai Fir’auna da mutanensa suka ƙaryata Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), suka fara tunanin kashe shi, sai ya koma ga Allah ya nemi tsarinsa daga sharrinsu don kada su jefe shi har lahira. Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nemi ɗayan abubuwa biyu daga gare su: Na farko, su yi imani da shi, na biyu, idan ba za su yi imani da shi ba, to su ƙyale shi su fita harkarsa kada su yi tunanin cutar da shi. To amma sai ya rasa ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa biyu, sai ma suka fara yunƙurin hallaka shi har da mutanensa da suka yi imani da shi. A nan ne Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roƙi Ubangijinsa cewa Fir’auna da jama’arsa mutane ne masu manyan laifuka, sun cancanci a gaggauto musu da uƙuba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa roƙonsa ya umarce shi da ya fita shi da mutanensa su gudu cikin dare, lalle Fir’auna da rundunarsa za su biyo bayansu. Haka kuwa ya faru, yayin da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fita da Banu Isra’ila kamar yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi, sai Fir’auna da rundunarsa suka bi bayansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bugi kogi da sandarsa, nan take kuwa kogin ya dare ya yi hanyoyi har goma sha biyu, Annabi Musa da jama’arsa suka tsallaka suka wuce. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya bar kogin yadda yake don Fir’auna da mutanensa su ma su shiga cikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa Fir’auna da rundunarsa duk za su nutse cikin ruwan. Haka kuwa ya faru, Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da jama’arsa suna gama fita shi kuma Fir’auna da rundunarsa sun gama shiga cikinsa sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci kogin ya haɗe da su, nan take duk suka nutse suka hallaka, ba ko mutum ɗaya daga cikinsu da ya tsira.
كَمۡ تَرَكُواْ مِن جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ
Open ayah 44:25Sun bar gonaki da kuma idanuwan ruwa masu yawa.
وَزُرُوعٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ
Open ayah 44:26Da kuma shuke-shuke da wurin zama mai daraja.
وَنَعۡمَةٖ كَانُواْ فِيهَا فَٰكِهِينَ
Open ayah 44:27Da kuma kayan jin daɗi da suka kasance masu ni’imtuwa da su.
كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا قَوۡمًا ءَاخَرِينَ
Open ayah 44:28Kamar haka ne; sai Muka kuma gadar da su ga wasu mutane daban (su ne Banu Isra’ila).
فَمَا بَكَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَا كَانُواْ مُنظَرِينَ
Open ayah 44:29Sannan (halittun) sama da na ƙasa ba su yi alhininsu ba, ba su kuma kasance ababen saurara wa ba.
وَلَقَدۡ نَجَّيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ مِنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ
Open ayah 44:30Haƙiƙa kuma Mun tserar da Banu Isra’ila daga azabar wulaƙanci.
مِن فِرۡعَوۡنَۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيٗا مِّنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Open ayah 44:31Daga Fir’auna. Lalle shi ya kasance mai girman kai daga maɓarnata.
وَلَقَدِ ٱخۡتَرۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ عِلۡمٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 44:32Kuma haƙiƙa Mun fifita su (Banu Isra’ila) bisa saninmu a kan (sauran) talikai.
وَءَاتَيۡنَٰهُم مِّنَ ٱلۡأٓيَٰتِ مَا فِيهِ بَلَٰٓؤٞاْ مُّبِينٌ
Open ayah 44:33Muka kuma ba su wasu ayoyinmu waɗanda a cikinsa akwai jarrabawa mabayyaniya. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin irin dangogin ni’ima da jin daɗin rayuwar duniya da Fir’auna da mutanensa suka bari bayan an dulmiyar da su cikin ruwa, da cewa sun bar gonaki da idanuwan ruwa masu yawa da shuke-shuke da majalisi na alfarma da kuma wata rayuwa ta jin daɗi da suke ciki. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa haka al’amarin ya faru da su kamar yadda aka yi bayani, kuma ya gadar wa Banu Isra’ila duk abubuwan can da aka bari na more rayuwa da gonaki da idanuwan ruwa. Bayan Allah ya hallaka su gaba ɗayansu babu wani mahaluƙi da ya nuna baƙin ciki ko alhini a kansu, har sama da ƙasa ba su nuna damuwarsu a kan abin da ya same su ba, domin kuwa sun cancanci uƙubar da aka yi musu, don haka ma ko saurara musu ba a yi ba ballantana su tuba a karɓi tubansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Banu Isra’ila irin ni’imar da ya yi musu yayin da ya tserar da su daga azabar wulaƙanci wadda Fir’auna da mutanensa suke ɗanɗana musu, lokacin da suka riƙa kashe musu ‘ya’ya maza suna barin mata, Allah ya hallaka musu Fir’auna da jama’arsa, domin shi mai girman kai ne kuma yana daga cikin maɓarnata masu ƙetare iyakokin Allah da addininsa. Allah kuma ya tabbatar wa Banu Isra’ila cewa, ya zaɓe su bisa sani da cancanta ya kuma fifita su a kan sauran al’ummun zamaninsu, saboda yawan annabawansu. Hakanan daga dalilai da ayoyi da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabi Musa don ƙarfafar sa akwai ni’ima ta sarari ga Banu Isra’ila, kamar al-mannu da tsuntsayen salwa da makamantansu.
إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَيَقُولُونَ
Open ayah 44:34Lalle waɗannan (kafiran Makka) tabbas suna cewa:
إِنۡ هِيَ إِلَّا مَوۡتَتُنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُنشَرِينَ
Open ayah 44:35“Babu wata mutuwa da za mu yi sai mutuwarmu ta farko, kuma mu ba za a tashe mu ba.
فَأۡتُواْ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 44:36“To ku zo mana da iyayenmu idan kun kasance masu gaskiya.”
أَهُمۡ خَيۡرٌ أَمۡ قَوۡمُ تُبَّعٖ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ مُجۡرِمِينَ
Open ayah 44:37Yanzu su ne suka fi ko kuwa mutanen Tubba’u da waɗanda suke a gabaninsu? Duk Mun hallakar da su. Lalle sun kasance masu manyan laifuka. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunar aƙidar nan ta kafirai ta rashin yarda da ranar alƙiyama, da cewa suna musunta tashi bayan mutuwa don suna ganin bayan rayuwarsu ta duniya babu sauran wata rayuwa daban, don haka idan sun mutu shi kenan babu tashi ko wani hisabi. Har ma suna ƙalubalantar Manzon Allah (ﷺ) da muminai da cewa, idan da gaske ne ana dawowa bayan mutuwa, to su dawo musu da iyayensu da suka riga suka mutu, tunda sun yarda Allah yana tashin matattu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu su ba su isa komai ba idan ya yi niyyar hallaka su ba za su gagare shi ba, domin kuwa ba su kai mutanen Tubba’u ba da wasu kafirai da suka gabace su, kamar Adawa da Samudawa; dukkansu Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su yayin da suka ƙaryata manzanninsa, don haka su ma waɗannan mushirikan Allah yana iya hallaka su don kuwa lalle sun tabbata mutane ne masu manyan laifuka kamar waɗancan kafiran.
وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا لَٰعِبِينَ
Open ayah 44:38Ba Mu kuma halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu don wasa ba.
مَا خَلَقۡنَٰهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 44:39Ba Mu halicce su ba sai don gaskiya, sai dai kuma yawancinsu ba su san haka ba.
إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ مِيقَٰتُهُمۡ أَجۡمَعِينَ
Open ayah 44:40Lalle ranar alƙiyama ne lokacin da aka ƙayyade musu gaba ɗaya.
يَوۡمَ لَا يُغۡنِي مَوۡلًى عَن مَّوۡلٗى شَيۡـٔٗا وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Open ayah 44:41Ranar da wani masoyi ba zai amfana wa masoyinsa komai ba, su kuma ba za a taimaka musu ba.
إِلَّا مَن رَّحِمَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 44:42Sai fa wanda Allah Ya ji ƙan sa. Lalle Shi ne Mabuwayi, Mai rahama. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikar Ƙudurarsa da girman ikonsa da kamalar hikimarsa, da cewa bai halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu domin wasa ba, ko hakanan kara-zube ba don wata manufa ba. Ya tabbatar da cewa ya halicce su ne don gaskiya, watau a bauta masa shi kaɗai ba tare da an haɗa shi da komai ba, kuma ya umarci mutane ya hana su don yi musu sakayya a kan ayyukansu, to amma yawancinsu ba su san haka ba, don haka ne ba sa tunani dangane da halittar sammai da ƙasa da ma kawunansu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa ranar alƙiyama wadda a cikinta ne zai rarrabe tsakanin halittunsa rana ce da aka sanya musu lokacin zuwanta da Allah zai tara su a cikinta baki ɗaya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta ta da cewa, rana ce da wani makusanci ba zai amfana wa makusancinsa komai ba, kuma babu wasu da za su kare musu azabar Allah a ranar, domin mulki gaba ɗaya a ranar na Allah ne babu mai iya yin wani abu sai da izininsa. Sai dai wanda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ji ƙansa daga cikin mutane, to wannan shi ne zai amfana da kyawawan ayyukansa da ya gabatar a duniya, domin Allah mabuwayi ne wanda babu mai iya rinjayar sa, mai hikima ne cikin halittarsa da tsarinsa da shari’arsa.
إِنَّ شَجَرَتَ ٱلزَّقُّومِ
Open ayah 44:43Lalle itaciyar Zaƙƙumu.
طَعَامُ ٱلۡأَثِيمِ
Open ayah 44:44Abincin mai babban zunubi ce.
كَٱلۡمُهۡلِ يَغۡلِي فِي ٱلۡبُطُونِ
Open ayah 44:45(Kuma) kamar narkakkiyar darma, tana tafarfasa a cikin ciki.
كَغَلۡيِ ٱلۡحَمِيمِ
Open ayah 44:46Kamar tafasar ruwan zafi.
خُذُوهُ فَٱعۡتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 44:47(Za a ce da mala’iku): “Ku kama shi sannan ku ja shi tsakiyar wutar Jahima.
ثُمَّ صُبُّواْ فَوۡقَ رَأۡسِهِۦ مِنۡ عَذَابِ ٱلۡحَمِيمِ
Open ayah 44:48“Sannan ku kwarara azabar ruwan zafi a tsakiyar kansa,.”
ذُقۡ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡكَرِيمُ
Open ayah 44:49(Sai a ce da shi): “Ɗanɗana, lalle kai ɗin nan kai babban mutum ne mai daraja.
إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِۦ تَمۡتَرُونَ
Open ayah 44:50(Za a ce da kafirai): “Lalle wannan ne abin da kuka kasance kuna shakkar sa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana munanan sakamakon ‘yan wuta a ranar alƙiyama, da cewa, bishiyar Zaƙƙum wadda take tsirowa a tsakiyar wutar Jahannama, ita ce abincin duk wani kafiri mai babban laifi; za a ciyar da shi munanan ‘ya’yanta waɗanda za su riƙa tafarfasa a cikin cikin ‘yan wuta, kamar tafasar narkakken baƙin mai ko tafasar ruwan da ya kai matuƙa wajen zafi. Sai kuma a umarci mala’iku zabaniyawan wuta da cewa, su kama wannan kafiri su ja shi da ƙarfi da tsanani zuwa tsakiyar Jahannama, sannan su kwarara masa azabar tafasasshen ruwan zafi a kansa, ya yi ta ɗanɗanar azaba babu ƙaƙƙautawa. Sannan cikin izgili da ba’a a riƙa faɗa masa cewa, ya ɗanɗani kuɗarsa, ai lalle shi babban mutum ne mai daraja a cikin mutanensa, kamar yadda ya kasance yana ɗaukar kansa a duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa kafirai cewa, wannan azabar ita ce abin da suka kasance suna shakkar aukuwarta domin ba su yi imani da ranar alƙiyama ba, to yau ga shi sun gani da idanuwansu babu kuma sauran shakka.
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٖ
Open ayah 44:51Lalle masu taƙawa suna cikin wani amintaccen wuri.
فِي جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ
Open ayah 44:52Cikin lambuna da idanuwan ruwa.
يَلۡبَسُونَ مِن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَقَٰبِلِينَ
Open ayah 44:53Suna saye da tufafi na alharini <b>mai shara-shara da mai kauri </b> suna fuskantar juna.
كَذَٰلِكَ وَزَوَّجۡنَٰهُم بِحُورٍ عِينٖ
Open ayah 44:54Kamar haka ne, Muka kuma aura musu (‘yan matan) Hurul-Ini.
يَدۡعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَٰكِهَةٍ ءَامِنِينَ
Open ayah 44:55A cikinta (Aljannar) suna kiran a kawo musu duk wani kayan marmari, suna cikin aminci.
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلۡمَوۡتَ إِلَّا ٱلۡمَوۡتَةَ ٱلۡأُولَىٰۖ وَوَقَىٰهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ
Open ayah 44:56Ba za su ɗanɗani wata mutuwa a cikinta ba sai dai mutuwar farko; Ya kuma tserar da su daga azabar wutar Jahima.
فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكَۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Open ayah 44:57(Wannan) falala ce daga Ubangijinka. Wannan shi ne babban rabo
فَإِنَّمَا يَسَّرۡنَٰهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
Open ayah 44:58To kawai Mun sauƙaƙe shi ne (wato Alƙur’ani) da harshenka, don su wa’azantu.
فَٱرۡتَقِبۡ إِنَّهُم مُّرۡتَقِبُونَ
Open ayah 44:59To ka saurara, lalle su ma masu sauraro ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon masu taƙawa waɗanda suke kiyaye dokokinsa ta hanyar aikata abin da aka umarce su da barin abin da aka hana su, da cewa a ranar alƙiyama suna da wani wurin zama amintacce inda babu wani abin ƙi da zai same su. Wannan wuri kuwa shi ne gidajen Aljanna masu idanuwan ruwa da ke gudana a cikinsu. Tufafin da za su riƙa sawa kuma na alhariri ne mai shara-shara da mai kauri, suna zaune a kan kujeru suna fuskantar juna. Bugu da ƙari kuma zai aura musu ‘yan matan Hurul-Ini masu tsananin kyau da manyan idanuwa masu tsananin fari da baƙi. A cikin Aljannar za su riƙa kiran masu yi musu hidima don su kawo musu kayan marmari iri-iri da suke da buƙata, hankalinsu kwance ba sa fargabar cewa wannan jin daɗin nasu zai yanke, ko wata cuta za ta same su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa za su zauna a cikin wannan ni’imar har abada ba za su sake ɗanɗanar wata mutuwa ba sai wadda suka riga suka ɗanɗana ta farko a rayuwarsu ta duniya, sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsare su daga faɗawa cikin azabar Jahannama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu wannan tagomashi ne don falala da kyautatawa daga gare shi. Allah ya tabbatar da cewa wannan shi ne babban rabo wanda babu kamarsa. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wanda aikinsa ne zai shigar da shi Aljanna.” Sai sahabbai suka ce: “Har kai ma ya Manzon Allah?” Ya ce: “Har ni ma, sai dai idan Allah ya lulluɓe ni da falalarsa da rahamarsa….” [Bukhari #5673 da Muslim #2816]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe Surar da tunatar da su ni’imar saukar da Alƙur’ani da harshen Larabci da kuma tsoratar da su mummunan ƙarshen masu ƙaryata gaskiya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, ya sauƙaƙe masa Alƙur’ani ta hanyar saukar masa da shi cikin harshensa na Larabci, domin mutanensa su fahimci saƙonsa su wa’azantu. Sannan Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya ƙara haƙuri, ya saurari lokacin zuwan nasarar da ya yi masa alƙawarin zuwanta; su ma masu laifi lallai suna sauraron lokacin hallakarsu ne.