الجاثية
Al-Jaathiya
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
حمٓ
Open ayah 45:1Ha Mim.
تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ
Open ayah 45:2Saukar da Alƙur’ani daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima.
إِنَّ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 45:3Lalle a cikin sammai da ƙasa tabbas akwai ayoyi ga muminai.
وَفِي خَلۡقِكُمۡ وَمَا يَبُثُّ مِن دَآبَّةٍ ءَايَٰتٞ لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ
Open ayah 45:4A cikin halittarku ma da abin da Yake bazawa na dabbobi, akwai ayoyi ga mutane masu sakankancewa.
وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن رِّزۡقٖ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَا وَتَصۡرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ ءَايَٰتٞ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Open ayah 45:5Da kuma sassaɓawar dare da yini da abin da Ya saukar daga sama na arziki, sai Ya raya ƙasa da shi bayan mutuwarta, da kuma jujjuyawar iska, akwai ayoyi ga mutanen da suke hakalta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe da haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori da irin waɗannan haruffa. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara don ƙarin bayani]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman darajar Alƙur’ani da matsayinsa babba inda ya nuna cewa, shi saukakke ne daga Allah Mabuwayi wanda babu mai iya ja da shi, mai hikima cikin halittarsa da hukuncinsa. Sai kuma Allah ya bayyana wasu manyan dalilai na cikar Ƙudurarsa da ikonsa wanda duk masu imani daga bayinsa sukan iya ganin su cikin halittar sammai da ƙasa da abin da suka ƙunsa na manya-manyan halittu, kamar rana da wata da taurari a sama da duwatsu da tsirrai da koguna a ƙasa waɗanda suke nuna girman ikon Allah da cikar Ƙudurarsa da kyan tsarinsa. Sai kuma ya bayyana cewa, har ila yau, akwai wasu ayoyinsa a cikin halittar su kansu mutane waɗanda ya samar da asalinsu daga taɓo sannan daga ɗigon maniyyi har suka zama cikakkun mutane. Da kuma abin da ya halitta na dabbobi masu yawo a bayan ƙasa, ya yaɗa su a ko’ina. Dukkansu ayoyi ne ga mutane masu sakankancewa da cewa Allah ne mahaliccin komai. Hakanan game da sassaɓawar dare da yini, wannan ya zo wannan ya tafi babu ƙaƙƙautawa. Da kuma ruwa da ya saukar daga sama wanda da shi ne ya raya ƙasa bayan mutuwarta, ya fitar da tsirran cikinta da shuke-shukenta bayan a da ta bushe ƙayau babu komai a kanta. Hakanan game da jujjuyawar iska da take kaɗawa daga nahiyoyi daban-daban, wani lokaci ta kaɗa daga arewa wani lokaci kuma daga kudu, wani lokaci ta zo da zafi wani lokaci kuma da sanyi, duka dai domin amfanin mutane da dabbobinsu da shuke-shukensu. A cikin waɗannan al’amura duka akwai ƙwararan dalilai masu nuna Kaɗaitakar Allah da cikar Ƙudurarsa ga mutanen da suke hankaltar ayoyin Allah, suke gane dalilan da suke ɗauke da su.
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۖ فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَ ٱللَّهِ وَءَايَٰتِهِۦ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 45:6Waɗannan su ne ayoyin Allah da Muke karanta maka su da gaskiya; to da wane zance ne za su yi imani bayan (zancen) Allah da ayoyinsa?
وَيۡلٞ لِّكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ
Open ayah 45:7Tsananin azaba ya tabbata ga duk wani maƙaryaci mai yawan saɓo.
يَسۡمَعُ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ثُمَّ يُصِرُّ مُسۡتَكۡبِرٗا كَأَن لَّمۡ يَسۡمَعۡهَاۖ فَبَشِّرۡهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٖ
Open ayah 45:8Yana jin ana karanta masa ayoyin Allah, sai ya doge yana mai girman kai kamar bai ji su ba; to ka yi masa albishir da azaba mai raɗaɗi.
وَإِذَا عَلِمَ مِنۡ ءَايَٰتِنَا شَيۡـًٔا ٱتَّخَذَهَا هُزُوًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ
Open ayah 45:9Idan kuma ya san wani abu daga ayoyinmu sai ya ɗauke su abin yi wa izgili. Waɗannan suna da wata azaba mai wulaƙantarwa.
مِّن وَرَآئِهِمۡ جَهَنَّمُۖ وَلَا يُغۡنِي عَنۡهُم مَّا كَسَبُواْ شَيۡـٔٗا وَلَا مَا ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡلِيَآءَۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Open ayah 45:10A gabansu akwai (wutar) Jahannama, kuma abin da suka tsuwurwurta (na dukiya da waninta), da abubuwan da suka riƙa majiɓinta ba Allah ba, (duk) ba za su amfana musu komai ba; suna kuma da (sakamakon) azaba mai girma.
هَٰذَا هُدٗىۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ لَهُمۡ عَذَابٞ مِّن رِّجۡزٍ أَلِيمٌ
Open ayah 45:11Wannan (Alƙur’ani) shiriya ne; waɗanda kuwa suka kafirce da ayoyin Ubangijinsu, suna da (sakamakon) wata mummunar azaba mai raɗaɗi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) cewa shi ne yake karanta masu ayoyinsa da ya saukar a cikin mafi girman littattafansa, watau Alƙur’ani, da gaskiya tare da hujjoji masu gamsarwa da za su sanya mutane su gaskata shi. To amma har idan dalilan da ke ƙunshe cikin Alƙur’ani ba su sanya mushirikai sun yi imani da shi ba, to da wane zance ne kuma za su yi imani bayan zancen Allah da ayoyinsa? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir ga duk wani babban maƙaryaci mai yawan saɓon Allah, ya kuma yi masa alƙawarin azaba mai tsanani. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana shi da cewa, shi ne wanda yakan ji ana karanta masa ayoyin Allah daga cikin Alƙur’ani amma sai ya doge a kan kafircinsa da saɓon Allah yana mai girman kai da guje wa gaskiya, kamar ba ya jin abin da ake karanta masa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya umarci Manzonsa (ﷺ) cewa ya yi masa albishir da azaba mai raɗaɗi da take jiran sa a ranar alƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara bayyana wannan taɓaɓɓen bawa nasa da cewa duk sanda wani ilimi na Alƙur’ani ya zo masa sai kawai ya shiga yi masa izgili da ba’a. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa da cewa ire-irensa masu yi wa addini da ayoyin Allah izgili a ranar alƙiyama suna da azaba ta wulaƙanci da ba su taɓa ganin irinta ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa a gabansu, watau lahira, akwai wutar Jahannama tana nan tana jiran su, kuma su daina taƙama da yawan dukiya ko wasu gumakansu da suke bauta wa a nan duniya, domin a lahira dukiyarsu da suka tara ba za ta amfane su da komai ba, hakanan allolinsu da suka riƙa bauta musu ba za su kare musu komai daga azabar Allah ba, suna da sakamakon azaba mai girma da babu wanda ya san iyakarta sai Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, wannan Alƙur’ani da ya saukar masa shiriya ne zuwa ga gaskiya, duk mai neman ya shiryu shi zai riƙe ya bi karantarwarsa sau da ƙafa. To amma waɗanda suka kafirce wa ayoyin Ubangijinsu da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) suna da mummunar azaba mai raɗaɗi a ranar alƙiyama.
۞ٱللَّهُ ٱلَّذِي سَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡبَحۡرَ لِتَجۡرِيَ ٱلۡفُلۡكُ فِيهِ بِأَمۡرِهِۦ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Open ayah 45:12Allah ne wanda Ya hore muku kogi don jiragen ruwa su riƙa gudu a cikinsa da umarninsa, don kuma ku nema daga falalarsa don kuma ku gode.
وَسَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا مِّنۡهُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Open ayah 45:13Ya kuma hore muku abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa gaba ɗayansu daga gare Shi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani.
قُل لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَغۡفِرُواْ لِلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ أَيَّامَ ٱللَّهِ لِيَجۡزِيَ قَوۡمَۢا بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Open ayah 45:14Ka ce da waɗanda suka yi imani su yi gafara ga waɗanda ba su damu da ni\'imomi ko musibu na Allah ba, don Ya saka wa mutane game da irin abin da suka kasance suna aikatawa.
مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَسَآءَ فَعَلَيۡهَاۖ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ تُرۡجَعُونَ
Open ayah 45:15Duk wanda ya yi aiki nagari to kansa ya yi wa; wanda kuma duk ya munana to a kansa; sannan wurin Ubangijinku ne kawai za a mayar da ku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalarsa ga bayinsa da wasu ni’imomi da ya yi musu, domin su yi masa godiya a kansu, su bauta masa shi kaɗai ba tare da yi masa shirka ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya hore wa ‘yan’adam kogi don jiragen ruwa su riƙa gudu a cikinsa da umarninsa, suna ɗauke da mutane da kayayyakinsu masu nauyi da kayansu na kasuwanci, domin su yi tafiye-tafiye na fatauci daga ƙasa zuwa wata ƙasa, don kuma su gode wa Allah wannan ni’ima da ya yi musu. Hakanan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hore musu duk abin da ke cikin sammai, kamar rana da wata da taurari da abin da yake ƙasa, kamar ƙoramu da bishiyoyi da duwatsu, don su zamo rahama da falala gare su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa a cikin wannan aiki nasa akwai manyan dalilai masu tabbatar da girman Ƙudurarsa da Kaɗaitakarsa ga mutanen da suke tunani game da ayoyinsa, suke kuma ɗaukar izina daga gare su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya umarci muminai da su rungumi kyawawan halaye da haƙuri da yafiya ga kafirai waɗanda za su cutar da su, waɗanda kuma ba su damu da ni’imomi ko musibu na Allah ba, domin Allah ne zai saka wa bayinsa muminai masu haƙuri, zai kuma yi sakayyarsa a kan kafirai masu ta’addanci da cutar da muminai, saboda abin da suka kasance suna aikatawa a duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana wa kowa cewa duk wanda ya yi kyakkyawan aiki, to ya yi ne don amfanin kansa ba don Allah yana da buƙatarsa ba; wanda kuma ya yi mummunan aiki, to kansa ya cuta, ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma dukkan halittu gaba ɗaya zuwa ga Allah ne za a mayar da su don yi musu hisabi da sakamako a kan ayyukansu.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 45:16Haƙiƙa kuma Mun bai wa Banu Isra’ila littafin (Attaura) da hukunci da annabta,. Muka kuma arzuta su da tsarkakan (abubuwa), kuma Muka fifita su a kan talikai.
وَءَاتَيۡنَٰهُم بَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِۖ فَمَا ٱخۡتَلَفُوٓاْ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Open ayah 45:17Muka kuma kawo musu (hujjoji) mabayyana na addini; to ba su sassaɓa ba, sai bayan da ilimi ya zo musu don hassada a tsakaninsu. Lalle Ubangijinka zai yi hukunci a tsakaninsu a ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna yin saɓani cikinsa.
ثُمَّ جَعَلۡنَٰكَ عَلَىٰ شَرِيعَةٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ فَٱتَّبِعۡهَا وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 45:18Sannan Muka sanya ka a kan wata shari\'a ta addini, to sai ka bi ta, kada kuma ka bi soye-soyen zukatan waɗanda ba sa sanin (gaskiya).
إِنَّهُمۡ لَن يُغۡنُواْ عَنكَ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗاۚ وَإِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۖ وَٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 45:19Lalle su ba za su maganta maka komai ba daga Allah. Kuma lalle azzalumai sashinsu masoya sashi ne; Allah kuwa Shi ne Majiɓincin al’amarin masu taƙawa.
هَٰذَا بَصَٰٓئِرُ لِلنَّاسِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ
Open ayah 45:20Wannan (Alƙur’ani) izina ne ga mutane da shiriya da rahama ga mutanen da suke sakankancewa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ni’imomi masu yawa da ya yi wa Banu Isra’ila, wasu ta fuskar addini wasu kuma ta fuskar rayuwarsu ta duniya. Waɗannan ni’imomi sun haɗa da: (a) Littafin Attaura da ya saukar wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda ya ƙunshi shiriya da hukunce-hukuncen shari’a ga Banu Isra’ila. (b) Yin hukunci a tsakanin mutane yayin wata husuma saboda mulki yana hannunsu. (c) Aiko annabawa masu yawa a cikinsu. Babu wata al’umma mai yawan annabawa kamar al’ummar Banu Isra’ila. (d) Arzuta su da daɗaɗan abubuwa, don haka suka rayu cikin ni’ima da wadata. (e) Fifita su a kan sauran mutane gaba ɗaya na zamaninsu, domin babu wata al’umma da ta haɗa mulki da annabta kamar Banu Isra’ila. (f) Ya ba su hujjoji bayyanannu na addini waɗanda suka haɗa da mu’ujizojin da ya ba wa Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kuma bayanai na wa’azi da tunatarwa da ke cikin littafin Attaura. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa ba su tashi yin saɓani a tsakaninsu ba sai bayan hujjoji sun gama tabbata a kansu ta hanyar aiko da Manzon Allah Muhammadu (ﷺ), don hassada da zalunci a tsakaninsu saboda neman shugabanci da ɗaukaka. Allah ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alƙiyama game da abin da suka kasance suna yin saɓani a kansa a nan duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa shi ya ɗora shi a kan wani tafarki da sunna na umarninsa irin wanda ya yi wa manzannin da suka gabace shi umarni da shi na imani da aiki nagari, ya kuma umarce shi ya bi wannan shari’ar da ya ɗora shi a kai, kada ya sake ya bi soye-soyen zukatan waɗanda ba sa sanin gaskiya ballantana su bi ta, domin bin son zuciyarsu kauce wa gaskiya ne. Allah kuma ya nuna masa rashin amfanin bin soye-soyen zukatan masu kauce wa gaskiya da cewa, su waɗannan mutane ba za su maganta masa komai ba daga Allah, domin ba za su kare shi daga shiga wuta ba in har ya bi su kan ɓatansu, kuma su azzalumai daga kowane addini suke masoya junansu ne masu taimaka wa junansu ne wajen faɗa da muminai, to amma shi Allah (Mai tsarki da daukaka) shi ne majiɓincin al’amarin masu taƙawa da aikata umarninsa da guje wa haninsa, mai taimakon su ne koyaushe a kan abokan gabarsu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan Alƙur’ani da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) hujjoji ne bayyanannu ga mutane, masu nuna musu gaskiya da ƙarya, kuma shiriya ne zuwa ga gaskiya, kuma rahama ne ga mutanen da suke sakankancewa da hujjojinsa, domin su ne masu gane tafarki madaidaici su kuma bi shi, don neman yardar Ubangijinsu da samun gidan Aljanna da kuɓuta daga wuta.
أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ ٱجۡتَرَحُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن نَّجۡعَلَهُمۡ كَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ سَوَآءٗ مَّحۡيَاهُمۡ وَمَمَاتُهُمۡۚ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ
Open ayah 45:21Yanzu waɗanda suka aikata munanan (ayyuka) suna tsammanin za Mu sanya su ne kamar waɗanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, ya zamana rayuwarsu ta duniya da mutuwarsu sun zama daidai? Abin da suke hukuntawa ya munana.
وَخَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّ وَلِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 45:22Allah kuma Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya, don kuma a saka wa kowane rai irin abin da ya aikata, alhali kuma su ba za a zalunce su ba.
أَفَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمٖ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَٰوَةٗ فَمَن يَهۡدِيهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 45:23Shin kuwa ka ga wanda ya ɗauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, Allah kuwa Ya ɓatar da shi a kan yana sane, Ya kuma rufe jinsa da zuciyarsa, kuma Ya sanya yana a kan ganinsa, to wane ne zai shiryar da shi in ba Allah ba? Me ya sa ba kwa wa’azantuwa? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da adalcinsa da sanya bambanci tsakanin muminai masu ayyuka nagari da kuma waɗanda suka aikata munanan ayyuka, da cewa ba zai taɓa daidaita su ba a nan rayuwarsu ta duniya ko kuma a rayuwar lahira, saɓanin yadda kafirai suke tsammani cewa, su da muminai duk ɗaya ne a wurin Allah. Allah ya bayyana musu cewa, wannan wani mummunan hukunci ne suke yi, hukuncin da ba wanda zai taɓa amincewa da shi. Sai ya bayyana musu babban dalili da ke tabbatar da adalcinsa da cewa, shi ne wanda ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya, watau domin tabbatar da gaskiya da adalci don a bauta masa shi kaɗai ba tare da an haɗa shi da komai ba, ya kuma zartar da hukuncin cewa zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna babu wanda za a zalunta, to don haka ba zai yiwu ba ya ɗauki mutanen banza su zama ɗaya da mutanen kirki. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Annabi (ﷺ) yadda kafirai suka cuci kansu suka yi sanadiyyar da har Allah ya ɓatar da su. Ya ja hankalinsa a kan cewa ya dubi mutumin da ya mayar da bin son zuciyarsa a matsayin abin bautarsa wanda ba zai iya saɓa wa umarninsa ba, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ɓatar da shi bayan ilimi ya zo masa saboda Allah ya san cewa ya cancanci ɓata, ya kuma toshe masa jinsa da zuciyarsa ta yadda, ba ya sauraron abin da zai amfane shi, ya kuma sanya rufi a kan ganinsa, ba ya ganin gaskiya ya bi ta. To irin wannan mutum wane ne zai iya dawo da shi kan hanyar gaskiya bayan Allah ya ɓatar da shi? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa mutane cewa wannan misalin ya isa ya sa su wa’azantu su gane illar bin son zuciya. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abubuwa uku masu hallakarwa ne: Biye wa rowa; da biye wa son zuciya; da jiji da kai.” [Al-Bazzar, #7293. Dubi, Al-Albani, As-Silsilatus Sahiha #1802].
وَقَالُواْ مَا هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا نَمُوتُ وَنَحۡيَا وَمَا يُهۡلِكُنَآ إِلَّا ٱلدَّهۡرُۚ وَمَا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِنۡ هُمۡ إِلَّا يَظُنُّونَ
Open ayah 45:24Suka kuma ce: “Ai ba wata (rayuwa) sai rayuwarmu ta duniya, da za mu mutu, kuma mu rayu (watau \'ya\'yansu), ba kuwa wani abu da yake hallaka mu sai juyin zamani”. Alhali kuwa ba su da wani sani game da wannan; ba abin da suke yi sai zato.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ مَّا كَانَ حُجَّتَهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ ٱئۡتُواْ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 45:25Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu mabayyana, ba su da wata hujja sai kawai su ce: “Ku zo da iyayenmu idan kun kasance masu gaskiya.”
قُلِ ٱللَّهُ يُحۡيِيكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يَجۡمَعُكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Open ayah 45:26Ka ce: “Allah ne zai raya ku sannan ya kashe ku sannan ya tara ku a ranar alƙiyama wadda babu kokwanto game da ita, sai dai kuma yawancin mutane ba sa sanin (haka).” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wani nau’i ne na kafircin mushirikai da tsananin wautarsu yayin da suke musunta tashi bayan mutuwa domin hisabi, suna cewa, wai babu wata rayuwa in ban da wannan rayuwar tasu ta duniya da suke a cikinta, sannan su mutu, sannan ‘ya’yansu su ci gaba da rayuwa a bayansu, don haka ba su yarda akwai ranar alƙiyama ba. Kuma suna ganin ma ba komai ne yake kashe su ba sai yau da gobe, watau juyawar zamani, don haka duk wata musiba idan ta same su sai su danganta ta da zamani ba tare da suna da wata hujja ta ilimi a kan da’awarsu ba sai tsantsar zato wanda ba ya amfanar da komai dangane da gaskiya. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Allah mai girma da buwaya ya ce: “Ɗan’adam yana cutar da ni, yana zagin zamani, ni kuma ni ne zamani, al’amari duka a hannuna yake, ni ne mai jujjuya dare da rana.” [Bukhari #4826 da Muslim #2246]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ɗayanku ya zagi zamani, domin Allah shi ne zamani…” [Muslim #2247]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk sanda aka karanta wa mushirikai ayoyinsa bayyanannu aka kuma ambaci tashi bayan mutuwa a cikinsu, ba su da wani abu da suke kafa hujja da shi wajen musunta tashi bayan mutuwa sai dai su riƙa cewa, wai in da gaske ne akwai ranar alƙiyama, to a dawo musu da iyayensu da suka riga suka mutu; idan Annabi (ﷺ) da sahabbansa sun yi musu wannan, to za su yi imani da tashi bayan mutuwa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya mayar musu da martani da cewa Allah ne yake raya su shi ne kuma ya halicce su daga babu, sannan kuma shi ne zai kashe su idan ajalinsu ya zo, sannan ya sake tashin su bayan mutuwarsu ya tattara su a ranar alƙiyama wadda babu kokwanto game da zuwanta, domin yi musu hisabi da sakamako, to amma yawancinsu ba sa sanin haka. Watau ya dace a ce sun yi la’akari da halittarsu ta farko daga babu, su kafa hujja da ita a kan yiwuwar sake dawo da su bayan mutuwarsu, domin Allah da ya yi halitta da farko ba zai gagare shi ya sake dawo da abin da ya halitta ba bayan mutuwa, to amma yawancin kafirai ba sa sanin wannan don haka suke musunta ranar alƙiyama.
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوۡمَئِذٖ يَخۡسَرُ ٱلۡمُبۡطِلُونَ
Open ayah 45:27Mulkin sammai da ƙasa kuma na Allah ne. Kuma ranar da alƙiyama za ta tashi, a wannan ranar maɓarnata za su yi asara.
وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٖ جَاثِيَةٗۚ كُلُّ أُمَّةٖ تُدۡعَىٰٓ إِلَىٰ كِتَٰبِهَا ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 45:28Za kuma ka ga kowace al’umma a durƙushe, kowace al’umma ana kiran ta zuwa ga littafinta, a wannan rana ne za a saka muku abin da kuka kasance kuna aikatawa.
هَٰذَا كِتَٰبُنَا يَنطِقُ عَلَيۡكُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّا كُنَّا نَسۡتَنسِخُ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 45:29(Za a ce da su): “Wannan Littafinmu ne da yake yi muku furuci da gaskiya. Lalle Mu mun kasance Muna rubuta abin da kuka kasance kuna aikatawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mulkin sammai da ƙasa nasa ne shi kaɗai, shi ne mai sarrafa su yadda ya ga dama, don haka shi kaɗai ya cancanta a bauta masa, yana da kuma isasshen iko na ya tashi matattu a ranar alƙiyama don yi wa kowa hisabi da sakamako a kan aikinsa, to a ranar ne maɓarnata waɗanda suka bauta wa wasu ba Allah ba suka ƙaryata ranar alƙiyama za su yi babbar asara. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, a wannan ranar zai ga kowace al’umma a durƙushe a kan gwiwoyinsu suna sauraron yadda za a yi da su, kowace al’umma za a kira ta zuwa ga littafin ayyukanta wanda mala’iku suka rubuta a nan duniya, kowa a yi masa sakamako gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna. Sannan za a tabbatar musu cewa, ba a zalunce su ba game da hukuncin da aka yanke musu, domin littafin da mala’iku suka rubuta na ayyukansu yana ba da shaida ne a kansu da tsantsar gaskiya, domin Allah ne da kansa ya umarci waɗannan mala’ikun su riƙa rubuta ayyukan mutane a duniya don yanke musu hanzari a lahira.
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَيُدۡخِلُهُمۡ رَبُّهُمۡ فِي رَحۡمَتِهِۦۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡمُبِينُ
Open ayah 45:30To amma waɗanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari, to Ubangijinsu zai shigar da su cikin rahamarsa. Wannan shi ne rabo mabayyani.
وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَفَلَمۡ تَكُنۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡ وَكُنتُمۡ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ
Open ayah 45:31Amma kuma waɗanda suka kafirce (za a ce da su): “Yanzu ashe ayoyina ba su kasance ana karanta muku su ba, sai kuka yi girman kai, kuka kasance mutane masu manyan laifuka?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda mutane za su kasu gida biyu a lahira bayan yi musu hisabi. Kaso na farko, su ne waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninsa suka kuma yi kyawawan ayyuka, to waɗannan Allah zai shigar da su gidan Aljanna da rahamarsa, wannan sakamako kuma da ya ba su shi ne rabo mabayyani da babu kamarsa. Kaso na biyu kuwa, su ne waɗanda suka kafirce wa Allah da manzanninsa, to su waɗannan za a tambaye su cikin zargi da tuhuma cewa, shin manzanni ba su zo suna karanta musu ayoyin Allah ba? To amma maimakon su miƙa wuya su yi imani sai suka ɗaura rawanin girman kai suka bijire wa imani da ayoyin Allah, don haka suka zama mutane masu manyan laifuka da suka haɗa da kafirci da shirka da saɓon Allah iri-iri?
وَإِذَا قِيلَ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَٱلسَّاعَةُ لَا رَيۡبَ فِيهَا قُلۡتُم مَّا نَدۡرِي مَا ٱلسَّاعَةُ إِن نَّظُنُّ إِلَّا ظَنّٗا وَمَا نَحۡنُ بِمُسۡتَيۡقِنِينَ
Open ayah 45:32Idan kuma aka ce, lalle alƙawarin Allah gaskiya ne, alƙiyama kuma babu kokwanto a game da ita kukan ce: “Mu ba mu da sanin mece ce ma alƙiyama, mu ba abin da muke tsammani (game da ita) sai zato, mu kuma ba mu da tabbas.”
وَبَدَا لَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 45:33Kuma irin munanan ayyukan da suka aikata suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu.
وَقِيلَ ٱلۡيَوۡمَ نَنسَىٰكُمۡ كَمَا نَسِيتُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَا وَمَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّٰصِرِينَ
Open ayah 45:34Aka kuma ce: “A yau za Mu manta da ku kamar yadda kuka manta haɗuwarku da wannan rana taku, makomarku kuma wuta ce, kuma ba ku da wasu mataimako.
ذَٰلِكُم بِأَنَّكُمُ ٱتَّخَذۡتُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ هُزُوٗا وَغَرَّتۡكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ فَٱلۡيَوۡمَ لَا يُخۡرَجُونَ مِنۡهَا وَلَا هُمۡ يُسۡتَعۡتَبُونَ
Open ayah 45:35“Wannan kuwa saboda lalle kun ɗauki ayoyin Allah abin yi wa izgili, rayuwar duniya kuma ta ruɗe ku.” To a yau ba za a fitar da su daga cikinta ba, kuma su ba za a nemi su kawo hanzarinsu ba.
فَلِلَّهِ ٱلۡحَمۡدُ رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَرَبِّ ٱلۡأَرۡضِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 45:36To yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin ƙasa, Ubangijin talikai.
وَلَهُ ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Open ayah 45:37Girma nasa ne a cikin sammai da ƙasa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda kafirai suka riƙa ƙaryata ranar alƙiyama duk kuwa da hujjojin da ake karanta musu, masu nuna gaskiyar Manzon Allah (ﷺ) da gaskiyar abin da ya zo musu da shi. Idan aka faɗa musu cewa, lalle alƙawarin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu na tayar da su don yi musu hisabi gaskiya ne, kuma ranar alƙiyama gaskiya ce babu kokwanto a game da ita, sai su kada baki su ce, su ba su san da wata ranar alƙiyama ba; ba abin da suke ji game da ita in ban da zato mai rauni wai ana cewa za ta zo, amma su fa ba su da wani tabbas a kan haka. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, ranar alƙiyama za ta zo, a ranar munanan ayyukan kafirci da saɓon Allah da suka aikata a duniya zai bayyana a gare su, sannan kuma azabar da suke yi wa izgili idan ana tsoratar da su da ita ta auka musu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, a ranar zai bar su ne a cikin wuta ya yi watsi da su sakamakon manta wannan ranar da suka yi, don haka suka ƙi yi mata wani tanadi na imani da aiki nagari. Sai ya tabbatar musu da cewa, makomarsu ita ce wutar Jahannama, kuma ba su da wasu mataimaka da za su kuɓutar da su daga azabar Allah. Allah kuma ya tabbatar musu mummunan aikin da suka yi har ya kai su ga wannan mummunan hali na azaba da wulaƙanci, watau shi ne izgilin da suka riƙa yi da ayoyin Allah da kuma ruɗar su da rayuwar duniya ta yi da ƙyale-ƙyalenta da sha’awe-sha’awenta, don haka suka rungume ta suka manta da Allah. To a ranar za a tabbatar musu cewa ba za a fitar da su daga cikin wannan azabar ba; za su yi ta zama ne a cikinta har abada, sannan kuma ba za a mayar da su duniya ba domin su gyara ayyukansu, don kuwa Allah ba zai taɓa yarda da su ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kammala Surar da kalmomin yabo da godiya gare shi Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin dukkan halittu. Ya tabbatar wa da kansa girma da cikar iko a sammai da ƙasa, shi ne kuma Mabuwayi wanda babu mai iya ja da shi ko ya fi ƙarfinsa, mai hikima kuma a cikin halittarsa da shari’arsa da ayyukansu duka.