الأحقاف
Al-Ahqaf
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
حمٓ
Open ayah 46:1Ha Mim.
تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ
Open ayah 46:2Saukar da Alƙur’ani daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima.
مَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَمَّآ أُنذِرُواْ مُعۡرِضُونَ
Open ayah 46:3Ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu ba sai don gaskiya da kuma (zuwa) wani lokaci ƙayyadajje. Waɗanda kuwa suka kafirta masu bijire wa abin da aka yi musu gargaɗi da shi ne.
قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِۖ ٱئۡتُونِي بِكِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ هَٰذَآ أَوۡ أَثَٰرَةٖ مِّنۡ عِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 46:4Ka ce: “Shin kun ga abin da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta na ƙasa, ko kuwa suna da tarayya ne a (halittar) sammai; ku kawo mini wani littafi da yake gabanin wannan (Alƙur’anin), ko kuma wani ɓirɓishi na ilimi idan kun kasance masu gaskiya.”
وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ
Open ayah 46:5Wane ne ya fi ɓata fiye da wanda yake bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amsa masa ba har zuwa ranar alƙiyama, kuma su (ababen bautar) rafkanannu ne game da bautar da suke yi musu?
وَإِذَا حُشِرَ ٱلنَّاسُ كَانُواْ لَهُمۡ أَعۡدَآءٗ وَكَانُواْ بِعِبَادَتِهِمۡ كَٰفِرِينَ
Open ayah 46:6Idan kuma aka tashi mutane (ababen bautar) za su kasance abokan gabarsu, kuma su zamo masu musanta bautar tasu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da wasu haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori da suka gabace ta da irin waɗannan haruffa. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara domin ƙarin bayani]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi wannan Alƙur’ani da cewa, saukakke ne daga wajen Allah Mabuwayi wanda babu mai iya rinjayar sa, mai hikima a cikin halittarsa da shari’arsa da tsarinsa. Sai kuma ya bayyana cewa, bai halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu don wasa ba, ya halicce su ne don gaskiya da wata babbar hikima wadda ta ƙunshi nuna wa bayinsa girman Ƙudurarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai ba tare da yi masa shirka ba, sannan kuma mutane su rayu a bayan ƙasa da kyakkyawar zamantakewa da khilafa har zuwa wani ƙayyadajjen lokaci da Allah ne kaɗai ya san shi. To amma duk da wannan kafirai ba su daina bijire wa abin da ake musu gargaɗi da shi ba a cikin littafin Allah suna watsi da shi suna bin son zuciyarsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambayi mushirkai masu bauta wa gumaka ba Allah ba su faɗa masa, wane abu ne suka halitta a bayan ƙasa, shin sun halicci wani dutse ne ko kuma sun halicci wata ƙorama? Ko kuma sun yi tarayya da Allah ne wajen halittar sammai don haka suna da wani kaso a ciki? Ya neme su da su zo masa da wani littafi da Allah ya saukar musu kafin Alƙur’ani ko wani ɓurɓushin ilimi na mutanen farko da ke nuna cewa gumakan da suke bauta wa sun cancanci a bauta musu. Babu shakka ba za su sami wannan ba, saboda haka suna jayayya ne kawai ba da wata hujja ba ta ilimi ko ta hankali. Sannan Allah ya bayyana wautarsu a fili yayin da suke bauta wa gunki wanda ba zai taɓa amsa addu’ar ɗayansu ba har alƙiyama ta tashi, hasali ma su waɗannan gumakan da suke bauta wa ba su ma san suna yi ba ballantana har su amsa musu addu’o’insu, ko su amfanar da su ko su kare musu wata cuta. Don haka babu ɓatacce kamar mai bautar wani ba Allah ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rashin amfanin bautar wani ba Allah ba a ranar alƙiyama, lokacin da za a tattara su gaba ɗayansu domin yi musu hisabi, to a lokacin ababen bautarsu ba Allah ba za su zame musu abokan gaba, su riƙa nesanta kansu da su, har su nuna musu cewa, su ba su san da bautar da suka yi musu ba a duniya.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٌ
Open ayah 46:7Idan kuma an karanta musu ayoyinmu bayyanannu sai waɗanda suka kafirce wa gaskiya lokacin da ta zo musu su ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.”
أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ إِنِ ٱفۡتَرَيۡتُهُۥ فَلَا تَمۡلِكُونَ لِي مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَا تُفِيضُونَ فِيهِۚ كَفَىٰ بِهِۦ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۖ وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Open ayah 46:8A’a, cewa dai suka yi: “Ƙagar sa ya yi.” Ka ce: “Idan har na ƙage shi ne to ba za ku amfana min komai ba game da Allah; Shi ne Ya fi sanin abin da kuke kutsawa cikinsa; Shi Ya isa Mai shaida tsakanina da ku; kuma Shi ne Mai gafara, Mai rahama.”
قُلۡ مَا كُنتُ بِدۡعٗا مِّنَ ٱلرُّسُلِ وَمَآ أَدۡرِي مَا يُفۡعَلُ بِي وَلَا بِكُمۡۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ وَمَآ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 46:9Ka ce: “Ba ni ne farau ba daga manzanni, kuma ba ni da sanin abin da za a yi min da abin da za a yi muku; ni ba abin da nake bi sai abin da ake yiwo min wahayinsa, kuma ni ba wani ba ne face mai gargaɗi mai bayyanawa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayanin taurin kan kafirai a yayin da ake karanta musu ayoyin Allah bayyanannu masu tabbatar da Kaɗaitakarsa sai su ƙaryata su, har su zargi Manzon Allah (() da cewa, sihiri ne ƙarara ya zo musu da shi, ba wahayi ne daga Allah ba. Haka kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kafirai wani lokaci suna zargin Annabi (ﷺ) cewa shi ne ya ƙagi Alƙur’ani ya danganta shi da Allah, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi ya faɗa musu cewa, idan har shi ne ya ƙagi Alƙur’ani ya danganta wa Allah, to ai su ba wata kariya da za su iya ba shi idan Allah ya yi nufin yi masa azaba, don haka me zai sa ya jefa kansa cikin haɗari yana sane? Sannan ya tabbatar musu da cewa Allah ne mafi sanin irin kutsen da suke yi wajen sukan littafinsa Alƙur’ani da sukan Manzonsa (ﷺ) kuma ya isa ya zama shaida tsakaninsa da su ya kuma bayyana wane ne mai gaskiya shi ko su. To amma idan sun gane sun tuba sun yi imani, to Allah mai gafarta zunuban bayinsa ne mai rahama ne gare su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya sake tabbatar wa mushirikai masu ƙaryata shi suna zarginsa da yi wa Allah ƙarya, cewa ba fa shi ne farau ba da Allah ya aiko da manzanci ballantana har su riƙa mamakin zamantowarsa manzon Allah; manzanin Allah masu yawa sun gabace shi, to don me suke musun manzancinsa. Sannan ya shaida musu cewa shi ba masanin gaibu ba ne don bai san abin da Allah zai yi masa ba ko ya yi musu a nan duniya, shi kawai abin da aka yi masa wahayi yake bi, don haka yana magana yana kuma aiki ne da wahayin da aka yi masa, shi ba wani ne ba sai mai gargaɗi mai bayyana gargaɗinsa ga kowa. An karɓo daga Ummul Ala, (Allah ya kara mata yarda), ta ce: Lokacin da Usmanu ɗan Maz’un (Allah ya kara masa yarda) ya rasu sai na ce: “Rahamar Allah ta tabbata a gare ka ya Baban Sa’ib, shaidata a gare ka ita ce, lalle Allah ya karrama ka.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce mata: “Mene ne ya sanar da ke cewa Allah ya karrama shi?” Sai ta ce: “Ban sani ba, mahaifina da mahaifiyata fansa ne gare ka ya Ma’aikin Allah.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Amma Usmanu lalle wallahi mutuwa ta zo masa, kuma lalle ni ina yi masa fatan alheri. Wallahi ban sani ba, alhali ni Manzo ne na Allah, me za a yi masa.” Sai ta ce: “To na rantse da Allah ba zan sake tsarkake wani ba bayansa har abada, kuma hakan ya baƙanta mini.” Sai ta ce: Sai na yi barci sai aka nuna mini wani idon ruwa mai gudana na Usman, sai na zo wurin Manzon Allah na ba shi labari sai ya ce: “Wannan aikinsa ne.” [Bukhari #2687].
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كَانَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ وَكَفَرۡتُم بِهِۦ وَشَهِدَ شَاهِدٞ مِّنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ عَلَىٰ مِثۡلِهِۦ فَـَٔامَنَ وَٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Open ayah 46:10Ka ce: “Ku ba ni labari, idan (Alƙur’ani) ya kasance daga wurin Allah yake, kuka kuma kafirce masa, kuma wani mai shaida daga Banu Isra’ila ya ba da shaida a kan irinsa, sai ya yi imani (da shi) ku kuma kuka yi girman kai; to lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.”
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَوۡ كَانَ خَيۡرٗا مَّا سَبَقُونَآ إِلَيۡهِۚ وَإِذۡ لَمۡ يَهۡتَدُواْ بِهِۦ فَسَيَقُولُونَ هَٰذَآ إِفۡكٞ قَدِيمٞ
Open ayah 46:11Waɗanda kuma suka kafirce suka ce wa waɗanda suka yi imani: “Da (addinin) ya kasance alheri ne, da su ba su riga mu zuwa gare shi ba.” To tunda kuwa ba su shiriya da shi ba, to za su riƙa cewa: “Wannan ƙarya ce daɗaɗɗiya.”
وَمِن قَبۡلِهِۦ كِتَٰبُ مُوسَىٰٓ إِمَامٗا وَرَحۡمَةٗۚ وَهَٰذَا كِتَٰبٞ مُّصَدِّقٞ لِّسَانًا عَرَبِيّٗا لِّيُنذِرَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 46:12A gabaninsa kuwa akwai littafin Musa wanda yake jagora ne da rahama. Wannan littafin kuma mai gaskata (na gabaninsa) ne a harshen Larabci, don ya gargaɗi waɗanda suka kafirta da kuma yin albishir ga masu kyautatawa.
إِنَّ ٱلَّذِينَ قَالُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُ ثُمَّ ٱسۡتَقَٰمُواْ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Open ayah 46:13Lalle waɗanda suka ce: “Allah ne Ubangijinmu”, sannan suka tsaya kyam, to babu wani tsoro a gare su, kuma su ba za su yi baƙin ciki ba.
أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ خَٰلِدِينَ فِيهَا جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Open ayah 46:14Waɗannan su ne ‘yan Aljanna madawwama a cikinta don sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da bayyana wa mushirikai gaskiyar Alƙur’ani wanda suke ƙaryatawa, ya umarci Manzonsa (ﷺ) cewa ya tambaye su, me za su ce idan Alƙur’ani ya tabbata daga Allah yake, kuma aka samu wani mai shaida daga Banu Isra’ila ya ba da shaida a kan ingancinsa, duba da abin da ya zo na bayaninsa a cikin littafin Attaura, sannan ya yi imani da shi, su kuma mushirkai suka kafirce masa, girman kai ya hana su su yi imani bayan gaskiya ta bayyana a fili. Yanzu in suka yi haka ba su tabbata azzalumai ba? To lalle su sani Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai masu ƙin gaskiya saboda girman kai da son zuciya. An karɓo daga Sa\'ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: \"Ban ji Manzon Allah (ﷺ) yana faɗa wa wani mai tafiya a bayan ƙasa cewa shi ɗan aljanna ne ba, sai ga Abdullahi ɗan Salam. A kansa ne wannan ayar ta sauka, watau: ( <b>… </b>kuma wani mai shaida daga Banu Isra’ila ya ba da shaida a kan irinsa)\". [Bukhari#3812 da Muslim#2483]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata wautar ta mushirikai da rashin hankalinsu lokacin da suka riƙa yi wa muminai izgili suna faɗa musu cewa, wai da a ce abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi gaskiya ne akwai kuma alheri a cikinsa, to da waɗannan bayin talakawan ba za su riga su karɓar sa ba, domin suna ganin waɗanda suka yi imani da Manzon Allah (ﷺ) ba manyan mutane ba ne, wasu faƙirai ne, wasu bayi, wasu raunanan mutane, su kuwa ba su cancanci samun wata ɗaukaka ko girma ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu martani da cewa, tun da taurin kansu ya fito fili ba su karɓi shiriyarsu ba, to za su riƙa sukan abin da Manzo ya zo musu da shi cewa wata daɗaɗɗiyar ƙarya ce su kuma ba za su riƙe ƙarya ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da ingancin Alƙur’ani da gaskiyarsa ya nuna musu cewa, kafin a saukar da Alƙur’ani a can baya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Musa Attaura wadda ba sa tababa a kanta, wadda ya sanya ta jagora a kan gaskiya kuma rahama ga wanda ya yi imani da ita ya bi karantarwarta. Shi kuma wannan Alƙur’anin da aka saukar wa Manzon Allah (ﷺ) littafi ne wanda yake gaskata littattafan da suka gabace shi, kuma Allah ya saukar da shi da harshen Larabci don ya gargaɗi mutanen da suka zalunci kawunansu da aikata shirka da saɓon Allah, kuma har ila yau bushara ne ga masu kyautata alaƙarsu da mahaliccinsu da alaƙarsu da sauran halittunsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana bayinsa nagari da kyakkyawan sakamakonsu, da cewa lalle sun yi imani cewa Allah ne Ubangijinsu, ba su da wani ubangiji ba shi ba, sannan suka daidaita a kan imani da aiki na ƙwarai, to waɗannan babu wani tsoro tare da su game da abin da za su fuskanta a lahira, kuma ba za su yi baƙin ciki a kan abin da suka bari ba a duniya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗannan su ne ‘yan Aljanna masu shigar ta su dawwama a cikinta har abada, sakamakon kyawawan ayyukan da suka yi a duniya.
وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ إِحۡسَٰنًاۖ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ كُرۡهٗا وَوَضَعَتۡهُ كُرۡهٗاۖ وَحَمۡلُهُۥ وَفِصَٰلُهُۥ ثَلَٰثُونَ شَهۡرًاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَبَلَغَ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗ قَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَصۡلِحۡ لِي فِي ذُرِّيَّتِيٓۖ إِنِّي تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَإِنِّي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 46:15Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa mahaifansa; mahaifiyarsa ta ɗauki cikinsa a wahalce, ta kuma haife shi a wahalce; ɗaukan cikinsa da yaye shi kuma wata talatin ne, har lokacin da ya cika ƙarfinsa ya kai shekara arba’in ya ce: “Ya Ubangijina, Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imarka, wadda Ka ni’imta ni da ita da kuma mahaifana, kuma (Ka ba ni iko) in yi aiki nagari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka kyautata min zurriyata; lalle ni na tuba a gare Ka, kuma lalle ni ina daga cikin Musulmi.”
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ نَتَقَبَّلُ عَنۡهُمۡ أَحۡسَنَ مَا عَمِلُواْ وَنَتَجَاوَزُ عَن سَيِّـَٔاتِهِمۡ فِيٓ أَصۡحَٰبِ ٱلۡجَنَّةِۖ وَعۡدَ ٱلصِّدۡقِ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ
Open ayah 46:16Waɗannan su ne waɗanda Muke karɓar mafi kyan abin da suka aikata, kuma Muke yafe musu munanan ayyukansu, suna cikin ‘yan Aljanna; (wannan) alƙawari ne na gaskiya wanda suka kasance ana yi musu alƙawarinsa (a duniya). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa mutum wasiyya da ya kyautata wa iyayensa a lokacin rayuwarsu da bayan mutuwarsu, ta hanyar da ba ta saɓa wa shari’a ba, musamman ma mahaifiyarsa wadda ta yi wahalhalun ɗaukan cikinsa da haihuwarsa. Ta yi ɗawainiyar ɗaukan cikinsa da yaye shi cikin wata talatin. Har lokacin da ya kai cikar ƙarfinsa, hankalinsa ya cika bayan ya kai shekara arba’in, to a lokacin zai riƙa addu’a yana roƙon Allah ya kimsa masa godiya a kan ni’imar da ya yi masa, ya kuma yi wa iyayensa, ya kuma hore masa yin aiki na ƙwarai da ya yarda da shi, ya kuma karɓi aikin nasa. Sannan ya roƙi Allah ya gyara masa ‘ya’yansa da ya ba shi, su zama na ƙwarai masu biyayya. Sannan ya tuba zuwa ga Allah a kan zunubbansa da ya aikata, ya tabbatar da cewa, shi yana cikin Musulmi masu miƙa wuya ga umarnin Allah masu bin sa sau da ƙafa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman sakamakon mutane masu irin wannan hali, da cewa yana karɓar mafi kyan ƙwararan ayyukansu yana kuma yafe musu laifukansu domin suna cikin ‘yan Aljanna. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, wannan alƙawari ne na gaskiya da ya yi musu sai ya tabbata babu makawa domin shi ba ya saɓa alƙawarinsa.
وَٱلَّذِي قَالَ لِوَٰلِدَيۡهِ أُفّٖ لَّكُمَآ أَتَعِدَانِنِيٓ أَنۡ أُخۡرَجَ وَقَدۡ خَلَتِ ٱلۡقُرُونُ مِن قَبۡلِي وَهُمَا يَسۡتَغِيثَانِ ٱللَّهَ وَيۡلَكَ ءَامِنۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ فَيَقُولُ مَا هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 46:17Wanda kuma ya ce da mahaifansa: “Tir da ku, yanzu kwa riƙa yi min alƙawarin za a fito da ni (daga ƙabarina), alhali kuwa tuni wasu al’ummu sun shuɗe gabanina?” Su kuma suna ta roƙon Allah da cewa: “Kaiconka, ka yi imani mana, lalle alƙawarin Allah tabbatacce ne,” sannan ya ce: “Wannan ba wani abu ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko!”
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ خَٰسِرِينَ
Open ayah 46:18Waɗannan su ne waɗanda kalmar azaba ta tabbata a kansu cikin al’ummun da suka gabace su na aljannu da mutane; lalle su sun kasance asararru.
وَلِكُلّٖ دَرَجَٰتٞ مِّمَّا عَمِلُواْۖ وَلِيُوَفِّيَهُمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Open ayah 46:19Kuma kowane yana da darajoji (na sakamakon) abin da suka aikata; don kuma tabbas zai cika musu sakamakon ayyukansu, ba kuma za a zalunce su ba.
وَيَوۡمَ يُعۡرَضُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَلَى ٱلنَّارِ أَذۡهَبۡتُمۡ طَيِّبَٰتِكُمۡ فِي حَيَاتِكُمُ ٱلدُّنۡيَا وَٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِهَا فَٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَسۡتَكۡبِرُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَبِمَا كُنتُمۡ تَفۡسُقُونَ
Open ayah 46:20(Ka tuna) kuma ranar da za a bijiro da waɗanda suka kafirta a gaban wuta, (a ce da su): “Kun tafiyar da jin daɗinku a rayuwarku ta duniya, kuma kun more ta, to a yau za a saka muku da azabar wulaƙanci saboda kun kasance kuna girman kai a bayan ƙasa ba da wata hujja ba, saboda kuma kun kasance kuna yin fasiƙanci.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana misalin wanda yake kangare wa iyayensa, yake ƙuntata musu, har ta kai ya dubi fuskarsu ya yi tir da su wai don suna yi masa wa’azi; suna kiran sa ya yi imani da Allah da ranar lahira, shi kuma yana ƙaryata su saboda sun faɗa masa cewa, za a tashe shi daga ƙabarinsa da ransa don yi masa hisabi a kan miyagun ayyukansa. Shi kuma yana nuna musu cewa, wannan maganar ba gaskiya ba ce, saboda ai wai a baya can mutane da yawa sun mutu ba a taɓa tashin ɗaya daga cikinsu da ransa ba. Su kuma iyayensa suna ta roƙon Allah ya shiryi ɗansu ya yi imani, suna gargaɗin sa cewa, lalle ya yi imani idan kuwa ba haka ba, to hallaka za ta tabbata a kansa, domin alƙawarin Allah na tashi bayan mutuwa gaskiya ne babu kokwanto a cikinsa. Shi kuma yana ƙara fanɗarewa yana gaya musu cewa, wannan magana da suke faɗa masa ba komai ba ce face tatsuniyoyin mutanen farko ba gaskiya ne ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, irin waɗannan mutane su ne waɗanda azabar Allah ta riga ta tabbata a kansu cikin jerin al’ummun da suka gabata na aljannu da mutane cewa dukkansu hasararru ne ‘yan wuta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin cewa, duka ɓangarorin nan biyu na ‘yan Aljanna da ‘yan wuta kowanne yana da matakai daban-daban na sakamakon abin da suka aikata, ‘yan Aljanna suna da matakai na can ƙoli, ‘yan wuta kuwa suna da matakai na can ƙasan ƙasa, Allah kuma zai cika musu sakamakon ayyukansu ba tare da an zalunce su ba a ranar alƙiyama, ta hanyar rage wa wani kyakkyawan aikinsa, ko ƙara wa wani mummunan aikin da bai aikata ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa kafirai halin tashin hankali da za su fuskanta a ranar alƙiyama lokacin da za a bijirar da su a gaban wuta don yi musu azaba a cikin izgili da cusa musu baƙin ciki, za a riƙa faɗa musu cewa, ai sun gama more jin daɗinsu a rayuwarsu ta duniya sun sha sharholiyarsu yadda suke so, to amma fa a yau za su ɗanɗani azabar da za ta ƙasƙantar da su ta wulaƙantar da su saboda girman kai da suka nuna a bayan ƙasa suka ƙi karɓar gaskiya da kuma ficewa daga yi wa Allah biyayya ta hanyar aikata kafirci da saɓon Allah. An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na shiga wurin Manzon Allah (ﷺ) a lokacin da ya ƙaurace wa matansa sai na gan shi kwance a kan tabarma babu wata shimfiɗa a kanta har kabar tabarmar ta yi burɗun-burɗun a gefen jikinsa, yana kishingiɗe a kan wani matashin kai na fatar da aka cika ta da zaren itaciyar dabino, sai na yi masa sallama… Umar ya ci gaba da cewa: Sai na ɗaga kaina na dubi ko’ina a cikin gidan Manzon Allah (ﷺ) ban ga wani abu da zai ja hankalina ba sai wasu buzaye guda uku da ke saƙale. Sai na ce: “Ka roƙi Allah ya yalwata wa al’ummarka, domin an yalwata wa Farisawa da Rumawa, an ba su duniya ga shi kuma su ba ma sa bauta wa Allah.” Annabi (ﷺ) yana kishingiɗe, da jin wannan magana sai ya tashi zaune ya ce: “Yanzu kana cikin kokwanto ne ya ɗan Khaɗɗab? Waɗancan fa mutane ne da aka gaggauto musu da jin daɗinsu a rayuwarsu ta nan duniya.” [Bukhari #2468 da Muslim #479].
۞وَٱذۡكُرۡ أَخَا عَادٍ إِذۡ أَنذَرَ قَوۡمَهُۥ بِٱلۡأَحۡقَافِ وَقَدۡ خَلَتِ ٱلنُّذُرُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦٓ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ
Open ayah 46:21Ka kuma tuna ɗan’uwan Adawa (watau Hudu) lokacin da ya gargaɗi mutanensa a al-Ahƙafu , alhali haƙiƙa masu gargaɗi sun shuɗe a gabaninsa da kuma a bayansa (suna cewa:) “Kada ku bauta wa (kowa) sai Allah, lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.”
قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَأۡفِكَنَا عَنۡ ءَالِهَتِنَا فَأۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Open ayah 46:22Sai suka ce: “Yanzu ka zo ne don ka kawar da mu daga ababen bautarmu? To ka zo mana da abin da kake yi mana alƙawarin narko (da shi) idan ka kasance cikin masu gaskiya.”
قَالَ إِنَّمَا ٱلۡعِلۡمُ عِندَ ٱللَّهِ وَأُبَلِّغُكُم مَّآ أُرۡسِلۡتُ بِهِۦ وَلَٰكِنِّيٓ أَرَىٰكُمۡ قَوۡمٗا تَجۡهَلُونَ
Open ayah 46:23Sai ya ce: “Lalle sani yana wurin Allah kawai, ni kuma ina isar muku abin da aka aiko ni da shi ne, sai dai kuma ni ina ganin ku mutane ne masu wauta.”
فَلَمَّا رَأَوۡهُ عَارِضٗا مُّسۡتَقۡبِلَ أَوۡدِيَتِهِمۡ قَالُواْ هَٰذَا عَارِضٞ مُّمۡطِرُنَاۚ بَلۡ هُوَ مَا ٱسۡتَعۡجَلۡتُم بِهِۦۖ رِيحٞ فِيهَا عَذَابٌ أَلِيمٞ
Open ayah 46:24To lokacin da suka gan ta (azabar) wani hadari ne mai gindayawa, ya doso wa kwarurukansu sai suka ce: “Wannan hadari ne mai ba mu ruwa!” A’a, (ba ku sani ba) shi ne abin da kuke neman gaggautowarsa, watau iska da take cike da azaba mai raɗaɗi.
تُدَمِّرُ كُلَّ شَيۡءِۭ بِأَمۡرِ رَبِّهَا فَأَصۡبَحُواْ لَا يُرَىٰٓ إِلَّا مَسَٰكِنُهُمۡۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 46:25Tana ruguza kowane irin abu da umarnin Ubangijinta, sai suka wayi gari ba abin da ake gani sai (kufaifan) gidajensu. Kamar haka Muke saka wa mutane masu manyan laifuka.
وَلَقَدۡ مَكَّنَّٰهُمۡ فِيمَآ إِن مَّكَّنَّٰكُمۡ فِيهِ وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ سَمۡعٗا وَأَبۡصَٰرٗا وَأَفۡـِٔدَةٗ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُمۡ سَمۡعُهُمۡ وَلَآ أَبۡصَٰرُهُمۡ وَلَآ أَفۡـِٔدَتُهُم مِّن شَيۡءٍ إِذۡ كَانُواْ يَجۡحَدُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Open ayah 46:26Haƙiƙa Mun kafa su (a bayan ƙasa) kafawar da ba Mu yi muku irinta ba, Muka kuma sanya musu ji da gani da tunani, sai jin nasu da ganinsu da tunaninsu ba su amfana musu komai ba, tunda sun kasance suna musanta ayoyin Allah, abin da kuma suka kasance suna yi wa izgili ya auka musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da labarin Annabinsa Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda yake da dangantaka ta jini da ƙabilar Adawa mazauna wani yanki da ake ce wa al-Ahƙaf a can kudancin tsibirin Larabawa a ƙasar Yaman, lokacin da ya gargaɗe su da su ji tsoron aukuwar azabar Allah a kansu, kuma ba shi ne farau ba wajen irin wannan gargaɗin, gabaninsa annabawan Allah sun shuɗe, wasu kuma sun zo a bayansa, dukkansu kuma sun riƙa sanar da mutanensu cewa, kada su bauta wa kowa sai Allah kaɗai. Don haka Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nuna wa mutanensa cewa yana jiye musu tsoron azabar wannan yini mai girma, watau ranar alƙiyama. To amma bayan sun ji wannan nasiha ta Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sai suka mayar masa da martani da zargin sa cewa ya zo ne kawai don ya raba su da bautar allolinsu, su kuma ba za su taɓa yarda da haka ba, don haka suna kiran sa da ya kawo musu azabar da yake tsorata su da ita idan har ya kasance mai gaskiya ne cikin abin da yake da’awa. Sai Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya nuna musu cewa, abin ba a hannunsa yake ba, bai kuma san takamaiman lokacin da azabar za ta auka musu ba, Allah ne kaɗai ya san wannan, shi kawai manzo ne da yake isar musu da saƙon da aka aiko shi da shi, to amma kuma ya lura cewa su mutane ne masu cike da wauta, ba su san abin da zai amfane su ba ballantana su karɓe shi ko abin da zai cutar da su don su guje shi. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da azabarsa, watau wata iska mai tsananin ƙarfi, yayin da suka hango hadari ya lulluɓe samaniya ya doshi kwaruruwansu, sai suka fara murna suna cewa, lalle ga hadari nan zai yi musu ruwa, sai Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya bayyana musu cewa ba hadari ne ba; wannan wata iska ce mai ɗauke da azaba mai raɗaɗi, kuma tana ruguza kowane abu da ta biyo ta kansa daga cikin abubuwan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce ta ta ruguza. Sai suka wayi gari ta ruguza komai ba abin da ta bari, ta hallaka dabbobinsu da dukiyoyinsu da su ma kansu, ba abin da ake gani sai kufan gidajensu da suke zaune a cikinsu don su zama shaidar cewa a da an taɓa yin wasu mutane a wurin. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, kamar yadda ya yi musu irin wannan mummunan sakamako saboda kafircinsu da ƙaryata Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), to hakanan zai saka wa duk wasu mutane masu manyan laifuka irin nasu, matuƙar ba su tuba sun koma ga Allah ba. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Annabi (ﷺ) ya kasance idan ya ga hadari ko iska ta taso sai a ga alamar tashin hankali a fuskarsa, sai ta ce: Ya Manzon Allah, mutane idan sun ga hadari sukan nuna farin cikinsu don suna tsammanin za su sami ruwan sama, amma kai kuwa idan ka ga hadari ya taso sai a ga fuskarka ta canza? Sai yace: “Ya A’isha, mene ne zai amintar da ni cewa, ba wata azaba ce a cikinsa ba, alhali an taɓa yi wa wasu mutane azaba da iska, wasu kuma da suka ga azabar sai suka riƙa cewa: \'Wannan hadari ne mai mana ruwa\'.” [Bukhari #4829] An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Annabi (ﷺ) ya kasance idan iska ta taso yana cewa: “Ya Allah ina roƙon ka alherinta da alherin da yake cikinta da alherin da aka aiko ta da shi. Ina kuma neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abin da yake cikinta da sharrin da aka aiko ta da shi.” Idan kuma hadari ya haɗo sai kamanninsa su canja, ya kasa zaune ya kasa tsaye, amma da zarar ruwa ya sauka sai hankalinsa ya kwanta. Sai na tambaye shi game da haka, sai ya ce: “Ban sani ba ko abin ya zama kamar yadda Adawa ne suka riƙa cewa: ‘Wannan hadari ne mai ba mu ruwa.’” [Muslim #899] Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana irin ƙarfin da ya ba wa Adawa don ya zama izina ga mutanen Makka, inda ya nuna musu cewa, lalle ya kafa Adawa a bayan ƙasa, ya kuma ƙarfafe su da abin da bai ƙarfafi mutanen Makka da shi ba, na ni’imomin duniya da ƙarfin halitta da dukiya mai tarin yawa, amma duk suka butulce wa wannan ni’imar da ya yi musu, sai azabarsa ta saukar musu ya hallaka su baki ɗaya, domin kuma ya ba su ji da gani da tunani, to amma duk sun yi watsi da su, ba su tsaya sun yi sauraro na fahimta ba, ba su kalli ayoyin Allah sun wa’azantu da su ba, ba su kuma yi tunani da hankulan da ya ba su ba, sai ba su tsinana musu komai ba lokacin da azabar Allah ta sauko musu saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah suna yi wa Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) izgili idan ya tsoratar da su azabar Allah, sai ga shi abin da suka kasance suna yi wa izgili ya sauka a kansu.
وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَا مَا حَوۡلَكُم مِّنَ ٱلۡقُرَىٰ وَصَرَّفۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Open ayah 46:27Haƙiƙa mun hallakar da abin da yake kewaye da ku na (mutanen) alƙaryu, Mun kuma jujjuya musu ayoyi (ta fuskoki daban-daban) don su dawo (kan hanya).
فَلَوۡلَا نَصَرَهُمُ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ قُرۡبَانًا ءَالِهَةَۢۖ بَلۡ ضَلُّواْ عَنۡهُمۡۚ وَذَٰلِكَ إِفۡكُهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Open ayah 46:28To me ya hana allolin da suka riƙe suna bautar su ba Allah ba, su taimake su? A’a, sun dai ɓace musu ne. Wannan kuma da man ƙaryarsu ce da kuma abin da suka kasance suna ƙagawa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tunatar da mutanen Makka azabar da ya yi wa wasu al’ummu masu maƙotaka da su waɗanda suka kafirce wa ayoyinsa, kamar Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mutanen Madyana. Duk waɗannan al’ummu Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu ayoyi daban-daban domin su wa’azantu su dawo kan tafarki madaidaici, amma suka bijire, sai ya hallaka su gaba ɗaya. Sannan kuma su mushirikan Ƙuraishawa sun san dai cewa, waɗancan al’ummu sun yi ƙaurin suna wajen bautar gumaka da mayar da su alloli ba Allah ba, to shin me ya hana su taimaka musu su kare su daga azabar Allah lokacin da ta zo musu? Sam ba su kawo musu wani ɗauki ba, a maimakon haka sai ma suka neme su suka rasa su, to da man ai ƙarya ce kawai suka riƙe wadda su ne suka ƙaga wa kawunansu ita don haka ba su yi musu wani amfani ba, ashe wannan ya ishi mushirikai wa’azi da izina.
وَإِذۡ صَرَفۡنَآ إِلَيۡكَ نَفَرٗا مِّنَ ٱلۡجِنِّ يَسۡتَمِعُونَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَلَمَّا حَضَرُوهُ قَالُوٓاْ أَنصِتُواْۖ فَلَمَّا قُضِيَ وَلَّوۡاْ إِلَىٰ قَوۡمِهِم مُّنذِرِينَ
Open ayah 46:29(Ka tuna) kuma lokacin da Muka juyo maka da wata jama’a ta aljannu don su saurari Alƙur’ani. To lokacin da suka halarto shi, sai suka ce: “Ku yi shiru;” sannan lokacin da aka gama (karatunsa) sai suka juya zuwa mutanensu suna yi musu gargaɗi.
قَالُواْ يَٰقَوۡمَنَآ إِنَّا سَمِعۡنَا كِتَٰبًا أُنزِلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّ وَإِلَىٰ طَرِيقٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Open ayah 46:30Suka ce: “Ya ku mutanenmu, haƙiƙa mu mun jiwo wani littafi da aka saukar bayan Musa, mai gaskata abin da yake gabaninsa, yana shiryarwa zuwa gaskiya da kuma zuwa tafarki madaidaici.
يَٰقَوۡمَنَآ أَجِيبُواْ دَاعِيَ ٱللَّهِ وَءَامِنُواْ بِهِۦ يَغۡفِرۡ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمۡ وَيُجِرۡكُم مِّنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ
Open ayah 46:31“Ya ku mutanenmu, ku amsa wa mai kira (zuwa ga) Allah, kuma ku yi imani da shi, (Allah) zai gafarta muku zunubanku ya kuma tsare ku daga azaba mai raɗaɗi.
وَمَن لَّا يُجِبۡ دَاعِيَ ٱللَّهِ فَلَيۡسَ بِمُعۡجِزٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَيۡسَ لَهُۥ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءُۚ أُوْلَٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ
Open ayah 46:32“Duk wanda kuwa bai amsa wa mai kira (zuwa ga) Allah ba, to ba zai gagara ba a bayan ƙasa, kuma ba shi da wasu mataimaka in ba shi ba. Waɗannan suna cikin ɓata mabayyani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kamar yadda a cikin mutane akwai waɗanda suka yi imani akwai kuma waɗanda suka kafirce, to hakanan su ma aljannu a cikinsu akwai waɗanda suka ba da gaskiya da Annabi (ﷺ), akwai kuma waɗanda ba su ba da gaskiya ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tunatar da Manzonsa (ﷺ) lokacin da ya juyo masa wata jama’a ta aljannu suka halarci majalisinsa inda yake karanta Alƙur’ani, suka saurari karatunsa cikin natsuwa, har wasu daga cikinsu suna umartar wasu da su yi shiru don su sami jin abin da yake karantawa sosai. Lokacin da suka gama sauraro, sai suka yi imani da shi, suka kuma juya suka koma cikin jama’arsu ta aljannu suna yi musu gargaɗi da wa’azi a kan su yi imani da Allah da Manzonsa da Alƙur’anin da aka saukar masa. An karɓo daga Alƙamatu almajirin Abdullahi ɗan Mas’ud ya ce: Na tambayi ɗan Mas’ud cewa, shin Annabi (ﷺ) ya tafi da ɗaya daga cikinsu a daren da ya haɗu da aljannu? Sai ya ce: “Bai tafi da kowa daga cikinmu ba, sai dai wata rana mun neme shi mun rasa shi, sai muka riƙa cewa, an yi masa kisan gilla ko kuma an ɗauke shi, ba mu san me yake ciki ba. Muka kwana cikin matuƙar baƙin ciki da tashin hankali. Asuba tana kawo kai sai muka gan shi yana dawowa ta nahiyar dutsen Hira, sai muka ba shi labarin halin da muka shiga, sai ya ce mana: “Mai kira ne daga cikin aljannu ya zo ya kirawo ni, sai na je musu na karanta musu Alƙur’ani.” Sai ya tafi da mu ya nuna mana guraben zamansu da ɓirɓishin wutacensu.” [Muslim #450] An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na kwana ina karanta wa aljannu Alƙur’ani waɗanda suka taru a wani wuri mai suna Al-Hajun .” [Ahmad #3954 da Ibn Hibban #6319] Al-Hajun sunan wuri ne a farkon Mina. Wasu sun ce maƙabartar mutanen Makka ce, tana kallon gidan Abu Musa Al-Ash’ari. [Dubi, Al-Bakri, Mu’ujamu Mas-tu’ujim , juzu’i na 2, shafi na 428] Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da jama’ar aljannun nan suka koma wajen jama’arsu sai suka gaya musu cewa, lalle sun saurari karatun wani littafi da Allah ya saukar da shi bayan Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), wanda yake gaskata abin da littattafan Allah na baya suka zo da shi, yana kuma shiryarwa zuwa ga gaskiya da tafarki madaidaici, watau Musulunci. Sai kuma suka kira jama’arsu cewa lalle su amsa kiran Annabi (ﷺ) da yake yi musu zuwa ga gaskiya, su yi imani da cewa, shi Manzon Allah ne wanda ya aiko zuwa gare su, idan sun yi imani Allah zai gafarta musu zunubansu, kuma ya tserar da su daga azaba mai raɗaɗi wadda take jiran duk wani wanda ya ƙi yin imani. Sannan suka ja musu kunne suka yi musu kashedi da cewa, duk wanda bai bi Annabi Muhammadu a kan gaskiyarsa da yake kira zuwa gare ta ba, to ba zai gagari Allah a bayan ƙasa ba ballantana ya tsere masa, kuma ba shi da wasu masoya ba Allah ba waɗanda za su kuɓutar da shi daga azabar Allah idan ya damƙe shi. Waɗanda za su zaɓi saɓa wa Manzo (ﷺ) to waɗannan suna cikin ɓata mabayyani.
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَلَمۡ يَعۡيَ بِخَلۡقِهِنَّ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Open ayah 46:33Ba sa ganin cewa Allah wanda Ya halicci sammai da ƙasa, Bai kuma gajiya ba wajen halittar su, Mai iko ne kan Ya raya matattu? Haka ne, lalle Shi Mai iko ne a kan komai.
وَيَوۡمَ يُعۡرَضُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَلَى ٱلنَّارِ أَلَيۡسَ هَٰذَا بِٱلۡحَقِّۖ قَالُواْ بَلَىٰ وَرَبِّنَاۚ قَالَ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ
Open ayah 46:34Kuma a ranar da za a bijiro da waɗanda suka kafirta a gaban wuta (a ce da su): “Yanzu wannan ba gaskiya ba ne?” Suka ce: “Haka ne (gaskiya ne) Mun rantse da Ubangijinmu.” Sai Ya ce: “To ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci.”
فَٱصۡبِرۡ كَمَا صَبَرَ أُوْلُواْ ٱلۡعَزۡمِ مِنَ ٱلرُّسُلِ وَلَا تَسۡتَعۡجِل لَّهُمۡۚ كَأَنَّهُمۡ يَوۡمَ يَرَوۡنَ مَا يُوعَدُونَ لَمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا سَاعَةٗ مِّن نَّهَارِۭۚ بَلَٰغٞۚ فَهَلۡ يُهۡلَكُ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ
Open ayah 46:35To ka yi haƙuri kamar yadda masu azama daga manzanni suka yi haƙuri, kada kuma ka nemi gaggauto musu (azaba). Kai ka ce ranar da za su ga abin da ake yi musu alƙawarinsa kamar ba su zauna (a duniya) ba sai wani ɗan lokaci na wuni. (Wannan) isar da saƙo ne. To akwai waɗanda za a halakar in ba mutane fasiƙai ba? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa kafirai masu ƙaryata tashin alƙiyama cewa, su tsaya su yi tunani su ga cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) wanda ya halicci sammai da ƙasa bai kuma gajiya ba wajen halittar su duk kuwa da girmansu da faɗinsu, babu shakka zai iya raya halittu bayan mutuwarsu, ya tashe su domin yi musu hisabi da sakamako domin shi mai iko ne a kan komai babu abin da yake gagarar sa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tsoratar da kafirai azabar ranar alƙiyama da suke ƙaryatawa da cewa ranar da za a bijiro su a kan wuta, a cikin zargi da wulaƙanci a riƙa tambayar su cewa, yanzu wannan azabar da suke gani a sarari har yanzu ba gaskiya ba ce, kamar yadda suke faɗa a duniya? A nan kuma dole su amsa su tabbatar da cewa, lalle gaskiya ne, sai mala’iku cikin izgili su ce musu, to su ɗanɗani azaba saboda kafircinsu da suka riƙa yi a duniya, watau wannan ne sakamakonsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya lallashi zuciyar Manzonsa (ﷺ) game da abin da yake gani na wulaƙanci da tsangwama daga kafirai, ya umarce shi ya yi haƙuri ya jure kamar yadda manyan manzannin Allah masu azama suka yi, watau Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Ibrahim (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Ya kuma neme shi da kada ya gaggauto musu da azabar da suke ta neman sa da ya kawo musu ita saboda jahilcinsu da tsananin wautarsu. Ba su san da cewa duk wani abu mai zuwa to a kusa yake? Don haka duk ranar da abin da ake yi musu alƙawari na azaba ya zo musu za su ga kamar dai ba su zauna a duniya ba sai ɗan wani lokaci na wuni, saboda tsawon azabar da za su tsinci kansu a cikinta. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, wannan Alƙur’ani da ya saukar masa saƙo ne wanda ya ishi mutane har da aljannu, domin yana ƙunshe da duk bayanin da suke buƙatar sa na rayuwarsu ta duniya da ta lahira. Sannan ya bayyana masa cewa ba wanda za a hallaka da azaba sai fasiƙan mutane waɗanda suka rungumi kafirci da saɓon Allah.