محمد
Muhammad
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ أَضَلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Open ayah 47:1Waɗanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, to (Allah) Ya lalata ayyukansu.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَءَامَنُواْ بِمَا نُزِّلَ عَلَىٰ مُحَمَّدٖ وَهُوَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡ كَفَّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَأَصۡلَحَ بَالَهُمۡ
Open ayah 47:2Waɗanda kuwa suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, kuma suka gaskata abin da aka saukar wa Muhammadu alhali kuwa shi ne gaskiya daga Ubangijinsu, sai (Allah) Ya kankare musu munanan ayyukansu, Ya kuma gyara musu halayensu.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱتَّبَعُواْ ٱلۡبَٰطِلَ وَأَنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّبَعُواْ ٱلۡحَقَّ مِن رَّبِّهِمۡۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ أَمۡثَٰلَهُمۡ
Open ayah 47:3Wannan (sakamako) kuwa saboda waɗanda suka kafirta sun bi ɓarna, waɗanda kuwa suka yi imani sun bi shiriya daga Ubangijinsu. Kamar haka ne Allah Yake buga wa mutane misalansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayanin babban laifin kafirai na kafirce masa da hana mutane bin addininsa da Annabinsa yake kiran su zuwa gare shi, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, ya lalata ayyukansu, watau ba za su sami wani lada ba a kan ayyukan ƙwarai da suka yi, kamar ciyar da mabuƙata da sada zumunci da ayyukan jin ƙai. Hakanan ayyukan da suka yi tuƙuru don ganin bayan Musulunci da Musulmi su ma sun tafi a banza, haƙansu bai cim ma ruwa ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kyakkyawan sakamakon waɗanda suka yi imani da Allah suka kuma yi kyawawan ayyuka, suka kuma yi imani da abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Manzonsa Muhammadu (ﷺ), watau Alƙur’ani kuma shi ne gaskiya daga Ubangijinsu; to su Allah ya kankare musu laifukansu, ba zai kama su da su ba, kuma ya gayara musu al’amuransu na duniya da na lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, dalilin wannan sakamako ga waɗannan ƙungiyoyi biyu, watau kafirai da muminai, shi ne saboda waɗanda suka kafirce wa Allah sun bi ɓarna, su kuma waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa sun bi gaskiyar da ta zo musu daga Ubangijinsu, don haka sakamakonsu ya bambanta. To kamar yadda Allah ya yi bayanin hukuncinsa game da waɗannan ƙungiyoyi biyu, hakanan yake ba wa mutane misalai domin a haɗa kowane abu da ɗan’uwansa.
فَإِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَضَرۡبَ ٱلرِّقَابِ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَثۡخَنتُمُوهُمۡ فَشُدُّواْ ٱلۡوَثَاقَ فَإِمَّا مَنَّۢا بَعۡدُ وَإِمَّا فِدَآءً حَتَّىٰ تَضَعَ ٱلۡحَرۡبُ أَوۡزَارَهَاۚ ذَٰلِكَۖ وَلَوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَٱنتَصَرَ مِنۡهُمۡ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَاْ بَعۡضَكُم بِبَعۡضٖۗ وَٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَن يُضِلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Open ayah 47:4To idan kuka haɗu da waɗanda suka kafirta sai ku sare wuyoyinsu har lokacin da kuka yi musu jina-jina, sai ku tsananta ɗauri; to bayan nan ko dai yafewa su tafi bayan (kun ribace su), ko kuma karɓar fansa har sai yaƙi ya lafa. Wannan abu haka yake, da kuma Allah Ya ga dama da Ya yi nasara a kansu (ko da ba yaƙi), sai dai kuma (Ya yi haka ne) don Ya jarrabi shashinku da shashi. Waɗanda kuwa aka kashe su a hanyar Allah, to ba zai taɓa lalata ayyukansa ba.
سَيَهۡدِيهِمۡ وَيُصۡلِحُ بَالَهُمۡ
Open ayah 47:5Zai shirye su Ya kuma kyautata halinsu.
وَيُدۡخِلُهُمُ ٱلۡجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمۡ
Open ayah 47:6Ya kuma shigar da su Aljannar da Ya sanar da ita gare su. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da su tashi su yaƙi maƙiyansu kafirai waɗanda suka nuna tsangwama da ƙiyayya a gare su, har ta kai sun kore su daga garuruwansu da gidajensu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa idan sun haɗu da irin waɗannan kafiran a fagen yaƙi, to su tsaya tsayin daka su yi yaƙi da gaske ba ja da baya, su yi ta saran wuyansu suna kashe su har sai sun yi musu jina-jina sun karya lagonsu, to su kama su su ɗaure su tamau, daga nan suna da zaɓi: a. Ko dai su sake su ba tare da sun karɓi fansa a hannunsu ba. b. Ko kuma su karɓi fansa ta dukiya ko wani abu mai daraja sannan su sake su. Watau za su zaɓi abin da ya fi dacewa da masalaha a lokacin. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su ci gaba da yaƙar kafirai, suna kama su har sai yaƙi ya zo ƙarshe sun ajiye makamansu an yi sulhu da su, ko kuma ma sun musulunta. Ya bayyana cewa, wannan abu da ya jarrabi muminai da shi na yaƙi da kafirai da ba da nasara a kansu ko kuma su kafirai su yi nasara a kan muminai, hukunci ne nasa, haka ya ga dama; da kuma ya so yin nasara a kan kafirai ko da babu yaƙi, to da ya yi, sai dai ya shar’anta jihadi ne don ya jarrabi mutane a junansu, ya tantance a cikin muminai wane ne zai yi yaƙin wane ne ba zai yi ba, ya kuma jarrabi kafiri da mumini. Idan mumini aka kashe ya shiga Aljanna, idan kuma shi muminin ya kashe kafiri ya shiga wuta. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗanda aka kashe su wajen yaƙi don Allah, to ba zai lalata ayyukansu ba; zai karɓe su ya yi musu kyakkyawan sakamako a duniya da lahira, ya kuma datar da su ga bin hanyar gaskiya a rayuwarsu ta duniya, ya gyara musu al’amuransu, sannan a ranar alƙiyama ya shigar da su gidan Aljanna wadda tun a nan duniya ya riga ya bayyana musu siffofinta sun gane ta sosai, a lahira kuma ya shigar da su gidajensu da aka tanadar musu a Aljanna. An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Muminai za su kuɓuta daga faɗawa wuta (yayin ƙetare Siraɗi) sai kuma a tsayar da su a kan wata gada tsakanin Aljanna da wuta, sai a yi musu hukunci a junansu na zaluncin da ya kasance a tsakaninsu a duniya, har sai an tsaftace su an kuma tsarkake su, sai a ba su izinin shiga Aljanna. Na rantse da wanda ran Muhammadu yake hannunsa ɗayansu sai ya fi gane hanyar zuwa gidansa na Aljanna fiye da yadda ya kasance yana gane hanyar zuwa gidansa a duniya.” [Bukhari #6535].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تَنصُرُواْ ٱللَّهَ يَنصُرۡكُمۡ وَيُثَبِّتۡ أَقۡدَامَكُمۡ
Open ayah 47:7Ya ku waɗanda suka yi imani idan kuka taimaki Allah, to zai taimake ku, Ya kuma tabbatar da dugaduganku.
وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَتَعۡسٗا لَّهُمۡ وَأَضَلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Open ayah 47:8Waɗanda kuwa suka kafirce to kaiconsu, (Allah) kuma Ya lalata ayyukansu.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَرِهُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأَحۡبَطَ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Open ayah 47:9Wannan kuwa saboda cewa sun ƙi abin da Allah Ya saukar, sai Ya lalata ayyukansu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga waɗanda suka yi imani da shi da Manzonsa (ﷺ) suka rungumi aiki da karantarwarsa da su tashi su taimaki addininsa, su yi kira zuwa gare shi, su kuma yi jihadi don ɗaukaka kalmarsa, ya yi musu alƙawarin zai taimake su ya ba su nasara da rinjaye a kan abokan gabarsu, ya kuma tabbatar da dugadugansu, watau ya ba su juriya da haƙuri da jajircewa, ya hore musu duk hanyoyin cin nasara ta rayuwa. Su kuma waɗanda suka kafirce wa Allah da Manzonsa (ﷺ), to hallaka da hasara sun tabbata a kansu, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rushe duk ladan kyawawan ayyukansu da suka aikata, ba za su amfane su da komai ba a lahira. Hakanan duk wani aiki na makirci da suke ƙulla wa muminai a duniya don su ga bayansu, Allah ya lalata musu shi, ba za su taɓa samun nasarar karya Musulunci da Musulmi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, dalilin da ya jawo musu wannan mummunan sakamako shi ne, saboda suna ƙyamar Alƙur’ani da ya saukar wa Manzonsa (ﷺ) sun bijire wa duk abin da ya ƙunsa na Tauhidi, watau kaɗaita Allah da bauta, sai Allah ya rushe duk ayyukansu, suka yi hasara duniya da lahira.
۞أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ دَمَّرَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۖ وَلِلۡكَٰفِرِينَ أَمۡثَٰلُهَا
Open ayah 47:10Yanzu ba za su yi tafiya a bayan ƙasa ba sai su duba yaya ƙarshen waɗanda suka gabace su ya kasance? Allah Ya hallaka su; kafirai kuma suna da (sakamako) kwatankwacinsa.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ مَوۡلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَأَنَّ ٱلۡكَٰفِرِينَ لَا مَوۡلَىٰ لَهُمۡ
Open ayah 47:11Wannan kuwa saboda lalle Allah ne Majiɓincin al’amuran waɗanda suka yi imani, lalle kuma su kafirai ba su da wani majiɓinci.
إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَتَمَتَّعُونَ وَيَأۡكُلُونَ كَمَا تَأۡكُلُ ٱلۡأَنۡعَٰمُ وَٱلنَّارُ مَثۡوٗى لَّهُمۡ
Open ayah 47:12Lalle Allah Yana shigar da waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; waɗanda kuwa suka kafirta suna jin daɗi (a duniya), suna kuma ta ciye-ciye kamar yadda dabbobi suke yi, wuta ce kuma makomarsu.
وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ هِيَ أَشَدُّ قُوَّةٗ مِّن قَرۡيَتِكَ ٱلَّتِيٓ أَخۡرَجَتۡكَ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡ فَلَا نَاصِرَ لَهُمۡ
Open ayah 47:13Alƙaryu nawa ne waɗanda suka fi alƙaryarka wadda ta fitar da kai ƙarfi, Mun hallakar da su, don haka ba su da wani mai taimakon su.
أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّهِۦ كَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُم
Open ayah 47:14Yanzu waɗanda suka kasance a kan hujja daga Ubangijinsu, sa yi daidai da waɗanda aka ƙawata musu mummuna aikinsu, suka kuma bi son zuciyarsu? A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa mushirikai tayin cewa, ashe bai kamata su zagaya bayan ƙasa ba su gane wa idanunsu mummunan ƙarshen da mutanen da suka gabace su ya kasance yayin da suka ƙaryata manzanninsu suka kafirce wa Allah? Lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su, ya yi rugu-rugu da gidajensu da dukiyoyinsu. Kuma kafirai na kowane lokaci da kowane wuri suna da mummunan ƙarshe irin wannan. Su kuma muminai Allah (Mai tsarki da daukaka) zai kuɓutar da su daga azabarsa, ya ba su lada mai yawa saboda shi ne mai taimakon su a koyaushe, amma kafirai da suka bijire wa Allah suka ƙi shari’arsa ba su da wani mai taimakon su ko jiɓintar al’amarinsu. A lokacin da yaƙin Uhudu ya zo ƙarshe jagoran rundunar mushirkai a wannan lokaci, watau Abu Sufyan ya hau ƙololuwar dutse ya ƙwala wa Musulmai kira yana cewa: “Akwai Muhammadu a cikinku?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya hana su amsa masa. Sai ya sake ƙwalla ihu ya ce: “A cikinku akwai ɗan Abu Ƙuhafa?” yana nufin Abubakar (Allah ya kara masa yarda), sai ba wanda ya amsa masa. Sai ya sake cewa: “A cikinku akwai Umar ɗan Khaɗɗab?” Sai ba su amsa masa ba. Sai ya ce: “Amma waɗannan dai duk kun gama da su.” Yana faɗin haka sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya kasa haƙuri ya ce: “Ya kai maƙiyin Allah, duk waɗannan da ka ambata suna nan da ransu. Lalle Allah ya wanzar da abin da zai ci gaba da baƙanta maka rai.” Sannan Abu Sufyan ya ce: “Ɗaukaka ga gunki Hubal.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce wa sahabbai: “Ba za ku ba shi amsa ba?” Sai suka ce: “Me za mu faɗa masa?” Sai ya ce: “Ku ce: \'Allah ne mafi ɗaukaka, mafi girma\'.” Sannan Abu Sufyanu ya sake ɗaga muryarsa ya ce: “Muna da Uzza, ku kuma ba ku da Uzza.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ba za ku ba shi amsa ba?” Sai suka ce: “Me za mu faɗa masa?” Sai ya ce: “Ku ce masa: \'Allah ne majiɓincinmu, ku kuma ba ku da mai jiɓintar ku\'.” [Bukhari #4043]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babban sakamako da zai yi wa muminai a lahira, na shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashin manya-manyan gine-ginensu da lambunansu, don girmamawa a gare su saboda imaninsu da kyawawan ayyukansu. Su kuma waɗanda suka kafirce wa Allah da Manzonsa ba abin da suka sa a gaba sai sharholiya a duniya da ciye-ciye da biye wa sha’awarsu kamar yadda dabbobi suke yi. To waɗannan a ranar alƙiyama wuta ce makomarsu inda za su tabbata a cikin azaba babu mai fitar da su daga cikinta. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya kasance yana cin abinci mai yawa sai ya musulunta, sai ya dawo yana cin ɗan abinci kaɗan, da aka faɗa wa Manzon Allah (ﷺ) abin da ya faru sai ya ce: “Lalle mumini yana cin abinci ne ta hanji ɗaya, kafiri kuwa yana ci ne ta ‘yan hanji bakwai.” [Bukhari #5397]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tsoratar da mushirikan Makka, a lokaci ɗaya kuma ya lallashi zuciyar Manzonsa (ﷺ) ya kwantar masa da hankalinsa da cewa, kada kafiran da suka fitar da shi daga mahaifarsa, Makka, su zaci sun gagari Allah ne; to su sani cewa a baya can an yi al’ummu masu yawa waɗanda sun dama su sun shanye a wajen ƙarfin jiki da na dukiya da yawan ‘ya’ya, amma da suka ƙaryata manzanninsu sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hallaka su, ba su kuma samu wani mai taimakon su ya kuɓutar da su daga hannunsa ba. Don haka su ma mutanen Makka su shiga taitayinsu, don idan Allah ya ga dama zai iya yi musu azaba irin wannan idan ba su yi imani ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna bambancin da ke tsakanin ɓangarorin biyu, watau muminai da kafirai, da cewa, wanda ya yi imani da Allah a kan hujja bayyananna da ta zo masa daga Ubangijinsa game da addininsa, ya rungumi bautar Allah, ba zai taɓa zama daidai da mutumin da Shaiɗan ya ƙawata masa mummunan aikinsa, ya bi son zuciyarsa, ya yi watsi da shiriyar Allah ba.
مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ فِيهَآ أَنۡهَٰرٞ مِّن مَّآءٍ غَيۡرِ ءَاسِنٖ وَأَنۡهَٰرٞ مِّن لَّبَنٖ لَّمۡ يَتَغَيَّرۡ طَعۡمُهُۥ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ خَمۡرٖ لَّذَّةٖ لِّلشَّٰرِبِينَ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ عَسَلٖ مُّصَفّٗىۖ وَلَهُمۡ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَمَغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡۖ كَمَنۡ هُوَ خَٰلِدٞ فِي ٱلنَّارِ وَسُقُواْ مَآءً حَمِيمٗا فَقَطَّعَ أَمۡعَآءَهُمۡ
Open ayah 47:15Kwatankwacin Aljannar da aka yi wa masu taƙawa alƙawari da ita shi ne, a cikinta akwai ƙoramu na ruwa ba gurɓatacce ba, da kuma ƙoramu na nono da ɗanɗanonsa bai canja ba, da ƙoramu na giya masu daɗi ga mashaya, da ƙoramu na tatacciyar zuma, kuma suna da kowane irin nau’i na ‘ya’yan itace da kuma gafara daga Ubangijinsu. Yanzu (masu waɗannan sa yi) daidai da waɗanda za su dawwama a cikin wuta a kuma shayar da su ruwa tafasasshe, sai ya yayyanke kayan cikinsu? A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kaɗan daga ɗimbin ni’imomin gidan Aljanna da ya tanadar wa masu bin dokokinsa, da cewa a cikinta akwai ƙoramu na ruwan daɗi wanda ba ya wari ko zartsi, da kuma ƙoramu na nono da ɗanɗanonsa bai canja ba da kuma wasu ƙoramu na giya mai daɗin kwankwaɗa ga masu shan ta, ba ta kuma sa maye ko ciwon kai. Sannan kuma akwai wasu ƙoramu na tatacciyar zuma da babu wani sofanen haki ko gurɓata a cikinta. An karɓo daga Mu’awiya ɗan Haida (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A cikin Aljanna akwai kogi na nono da kogi na ruwa da kogi na zuma da kogi na giya, sannan daga baya a keto da ƙoramu daga gare su.” [Ahmad #20052]. Haka kuma duk abin da muminai suke so na ‘ya’yan itatuwa za a kawo musu, ga kuma uwa-uba wata gafara ta musamman da za su samu daga Ubangijinsu. Shin masu irin wannan kyakkyawan sakamako za su yi daidai da wanda sakamakonsa shi ne dawwama a cikin wuta har abada, a kuma shayar da su tafasasshen ruwa wanda zai yayyanke musu kayan cikinsu?
وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُ إِلَيۡكَ حَتَّىٰٓ إِذَا خَرَجُواْ مِنۡ عِندِكَ قَالُواْ لِلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مَاذَا قَالَ ءَانِفًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡ
Open ayah 47:16Daga cikinsu kuma akwai waɗanda suke sauraron ka, har lokacin da suka fita daga wurinka sai su ce da waɗanda aka bai wa ilimi: “Shin me ma ya ce ɗazu?” Waɗannan su ne waɗanda Allah Ya toshe zukatansu suka kuma bi son ransu.
وَٱلَّذِينَ ٱهۡتَدَوۡاْ زَادَهُمۡ هُدٗى وَءَاتَىٰهُمۡ تَقۡوَىٰهُمۡ
Open ayah 47:17Waɗanda kuwa suka shiryu Ya ƙara musu shiriya, Ya kuma kimsa musu taƙawarsu.
فَهَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗۖ فَقَدۡ جَآءَ أَشۡرَاطُهَاۚ فَأَنَّىٰ لَهُمۡ إِذَا جَآءَتۡهُمۡ ذِكۡرَىٰهُمۡ
Open ayah 47:18Ai ba wani abu da suke sauraro sai alƙiyama ta zo musu farat ɗaya; to haƙiƙa alamominta sun zo. To ƙaƙa tunawar tasu za ta zame musu idan abin (alƙiyamar) ta zo musu ne?
فَٱعۡلَمۡ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مُتَقَلَّبَكُمۡ وَمَثۡوَىٰكُمۡ
Open ayah 47:19To ka sani cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma ka nemi gafarar zunubanka da na muminai maza da mata, Allah kuma Yana sane da kai-kawonku (na rana) da kuma wurin kwanciyarku (da daddare). A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fallasa munafukai yayin da suke halartar majalisin Manzon Allah (ﷺ) sanda yake wani bayani, sai su nuna suna sauraron sa amma kuma ba sa ba da hankalinsu a kan abin da yake faɗa don haka ba sa fahimtar komai, sai sun fita daga wajensa sai su riƙa tambayar waɗanda Allah ya ba wa ilimi, wai su faɗa musu mene ne Manzon Allah (ﷺ) yake cewa ne ɗazu? Don su nuna cewa su maganarsa ba ta dame su ba, don ba su ɗauke ta da wani muhimmanci ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗannan mutane ya riga ya toshe zukatansu, babu wani alheri da zai shige su, domin sun zaɓi su bi son zuciyarsu, don haka idanuwansu suka makance ba sa ganin kowace gaskiya da ake nuna musu. To amma waɗanda suka yi imani suka zaɓi su bi hanyar gaskiya, su bi abin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da shi, to waɗannan Ubangijinsu zai ƙara musu shiriya da taƙawa, sai su yi aikin da zai kuɓutar da su daga fushin Allah da azabarsa. Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar da cewa, su kafirai ba abin da suke sauraro sai alƙiyama ta zo musu kwatsam ba zato ba tsammani, sun manta da cewa alamomin alƙiyama sun riga sun bayyana, daga cikinsu akwai aiko da Manzo (ﷺ) akwai kuma tsagewar wata da ya faru a gaban idonsu. To duk waɗannan ba su ishe su wa’azi ba; to ta yaya kuma za su wa’azantu idan har alƙiyamar ta zo musu, rayuwarsu ta duniya ta zo ƙarshe? A lokacin babu sauran wani hanzari da za su bayar sai dai su ga sakamakon ayyukansu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kwaɗaitar da Manzonsa (ﷺ) da ya sami ilimi na Tauhidi, watau sakankancewa a kan babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, sannan ya nemi gafarar zunubansa daga Allah ya kuma nema wa muminai maza da mata gafarar zunubansu daga Allah. Ya tabbatar masa cewa yana sane da kai-kawon kowa da rana da wuraren komawarsu da daddare, babu abin da yake ɓuya a gare shi. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance yana cewa: “Ya Allah, ka gafarta mini kuskurena da rashin sanina da wuce iyaka cikin al’amarina da abin da kai ne ka fi ni saninsa. Ya Allah, ka gafarta mini laifin da na yi da wasa ko da gaske da kuskurena da gangancina. Duk waɗannan suna tare da ni.” [Bukhari #6398 da Muslim #2719]. An karɓo daga Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance a ƙarshen sallarsa yakan ce: “Ya Allah, ka gafarta min abin da na gabatar da abin da na jinkirtar da abin da na ɓoye da abin da na bayyana da abin da na wuce iyaka a cikinsa da abin da kai ne ka fi ni saninsa, kai ne abin bautana, babu abin bauta da gaskiya sai kai.” [Muslim #771]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na rantse da Allah, lalle ni a kullum ina neman gafarar Allah ina tuba zuwa gare shi sau saba’in.” [Bukhari #6307].
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَوۡلَا نُزِّلَتۡ سُورَةٞۖ فَإِذَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٞ مُّحۡكَمَةٞ وَذُكِرَ فِيهَا ٱلۡقِتَالُ رَأَيۡتَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ يَنظُرُونَ إِلَيۡكَ نَظَرَ ٱلۡمَغۡشِيِّ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡمَوۡتِۖ فَأَوۡلَىٰ لَهُمۡ
Open ayah 47:20Waɗanda kuma suka yi imani suna cewa: “Me ya hana a saukar da wata sura (wadda za ta ba mu damar yin yaƙi)?” Sannan lokacin da aka saukar da wata sura mai ɗauke da hukunci aka kuma ambaci yaƙi a cikinta, sai ka ga waɗanda suke da raunin imani a zukatansu (watau munafukai), suna kallon ka kamar kallon wanda yake cikin magagin mutuwa. To abin da ya fiye musu.
طَاعَةٞ وَقَوۡلٞ مَّعۡرُوفٞۚ فَإِذَا عَزَمَ ٱلۡأَمۡرُ فَلَوۡ صَدَقُواْ ٱللَّهَ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡ
Open ayah 47:21(Shi ne) yin biyayya da magana mai kyau. To idan al’amarin yaƙi ya tabbata, to da za su nuna wa Allah gaskiyarsu, da ya fi musu alhairi.
فَهَلۡ عَسَيۡتُمۡ إِن تَوَلَّيۡتُمۡ أَن تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَتُقَطِّعُوٓاْ أَرۡحَامَكُمۡ
Open ayah 47:22Shin ba kwa ganin idan kuka ba da baya (daga bin Allah) sai ku yi ɓarna a bayan ƙasa, ku kuma yanke zumuntarku?
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فَأَصَمَّهُمۡ وَأَعۡمَىٰٓ أَبۡصَٰرَهُمۡ
Open ayah 47:23Waɗannan su ne waɗanda Allah Ya la’ance su, sai Ya kurumtar da su, Ya kuma makantar da ganinsu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin muminai na gaskiya da kuma halin munafukai waɗanda suke yin ƙaryar sun yi imani, da cewa su muminai koyaushe suna sauraron Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sauko musu da ayoyi da suka ƙunshi umarni da yin wasu ayyuka komai wahalarsu, don su yi aiki da su, ko da kuwa umarni ne na yaƙi da kafirai. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da zai saukar da wata sura mai ƙunshe da wani hukunci a cikinta a yi maganar yaƙi, to da sai an ga munafukai waɗanda zukatansu suka cika da kokwanto sun riƙa kallon Manzon Allah a firgice irin kallon mutumin da yake cikin magagin mutuwa, saboda ba abin da suka tsana irin a yi musu maganar fita wajen jihadi. Sai Allah ya yi musu alƙawarin narko na azaba wanda yake dab da ya auka musu saboda munafuncinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, su bi umarninsa su kuma faɗi maganar da ta dace, wannan shi ya fi musu alheri. Idan kuma aka wajabta musu yaƙi, kuma al’amarin ya tabbata da gaske babu ja da baya, to da za su nuna wa Allah gaskiyar imaninsu da shi, su kuma yi masa biyayya da wannan ya fi musu a kan su riƙa yin munafurci suna saɓa wa umarninsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, da mutane za su bijire wa imani da yi masa biyayya, to babu abin da zai riƙa faruwa daga wajensu sai dai su yi ta yaɗa ɓarna a bayan ƙasa ta hanyar kafirci da saɓon Allah, su kuma riƙa yanke zumuntarsu kamar yadda suka riƙa yi a lokacin jahiliyya kafin zuwan Musulunci. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, waɗanda suka siffantu da waɗannan miyagun siffofi ya la’ance su ya nisanta su daga rahamarsa, don haka sai ya kurumtar da su suka daina jin gaskiya ji na fahimta da miƙa wuya, ya kuma makantar da idanuwansu suka daina ganin gaskiya ballantana su bi ta.
أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلۡقُرۡءَانَ أَمۡ عَلَىٰ قُلُوبٍ أَقۡفَالُهَآ
Open ayah 47:24Yanzu ba za su yi tunani na basira ba (game da) Alƙur’ani ba, ko kuwa akwai wani rufi ne a kan zukatansu?
إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱرۡتَدُّواْ عَلَىٰٓ أَدۡبَٰرِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلۡهُدَى ٱلشَّيۡطَٰنُ سَوَّلَ لَهُمۡ وَأَمۡلَىٰ لَهُمۡ
Open ayah 47:25Lalle waɗanda suka yi ridda suka koma baya, bayan kuwa shiriya ta bayyana a gare su, to Shaiɗan ne ya ƙawata musu ya kuma yi musu shifta.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لِلَّذِينَ كَرِهُواْ مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ سَنُطِيعُكُمۡ فِي بَعۡضِ ٱلۡأَمۡرِۖ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِسۡرَارَهُمۡ
Open ayah 47:26Wannan kuwa saboda lalle su, sun ce wa waɗanda suka ƙi bin abin da Allah Ya saukar: “Za mu bi ku a wasu al’amura.” Allah kuwa Yana sane da asiransu.
فَكَيۡفَ إِذَا تَوَفَّتۡهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ
Open ayah 47:27To yaya za su zama lokacin da mala’iku za su karɓi rayukansu suna dukan fuskokinsu da bayansu?
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱتَّبَعُواْ مَآ أَسۡخَطَ ٱللَّهَ وَكَرِهُواْ رِضۡوَٰنَهُۥ فَأَحۡبَطَ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Open ayah 47:28Wannan kuwa saboda lalle su, sun bi abin da yake fusata Allah suka kuma ƙi bin yardarsa, sai ya rusa ayyukansa.
أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَن لَّن يُخۡرِجَ ٱللَّهُ أَضۡغَٰنَهُمۡ
Open ayah 47:29Ko kuwa waɗanda suke da cuta a cikin zukatansu suna tsammanin cewa Allah ba zai fito da ƙulle-ƙullen zukatansu ba ne?
وَلَوۡ نَشَآءُ لَأَرَيۡنَٰكَهُمۡ فَلَعَرَفۡتَهُم بِسِيمَٰهُمۡۚ وَلَتَعۡرِفَنَّهُمۡ فِي لَحۡنِ ٱلۡقَوۡلِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ أَعۡمَٰلَكُمۡ
Open ayah 47:30Kuma da Mun ga dama da tabbas Mun nuna maka su (watau munafukai), to tabbas da ka gane su da alamominsu. Kuma tabbas za ka iya gane su ta hanyar salon maganarsu. Allah kuma Yana sane da ayyukanku.
وَلَنَبۡلُوَنَّكُمۡ حَتَّىٰ نَعۡلَمَ ٱلۡمُجَٰهِدِينَ مِنكُمۡ وَٱلصَّٰبِرِينَ وَنَبۡلُوَاْ أَخۡبَارَكُمۡ
Open ayah 47:31Kuma tabbas za Mu jarraba ku har sai Mun bayyana masu jihadi daga cikinku, da masu haƙuri, kuma za Mu bayyana halayenku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jawo hankalin masu bijire wa sauraron karatun Alƙur’ani da fahimtarsa da cewa, me zai hana su nutsu su yi tunani mai zurfi game da Alƙur’ani, domin yin haka zai taimaka musu wajen fahimtar sa, ya kuma sanya su dace da duk wani alheri, su tsira daga duk wani sharri? Ko kuwa zukatansu ne a rufe ruf babu ta inda alheri ko wa’azi ko tunatarwa za su shige su? Watau dai al’amarinsu ba zai wuce ɗayan abubuwan nan biyu ba: Ko dai ba sa tsayawa su yi karatun ta-nutsu su fahimci abin da Alƙur’ani yake faɗa musu. Ko kuma gaba ɗaya sun rasa hankulansu ne ba sa iya gane komai. Kowanne ɗaya daga cikin biyun nan sharri ne ba alheri ba a gare su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana halin mutanen da suka yi ridda suka koma baya zuwa kafirci ko munafurci, bayan shiriya ta bayyana a gare su, hujjar Allah ta tabbata a kansu, sun gane gaskiyar Manzon Allah (ﷺ) sarai, to waɗannan mutane Shaiɗan ne ya ƙawata musu kafirci da munafurci, ya jefa musu dogon buri a zukatansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗannan mutane sun faɗa cikin wannan ɓatan ne, saboda sun haɗa kai da waɗanda suka ƙi Allah da Manzonsa (ﷺ) da wahayin da ya saukar masa, har ma suka faɗa wa mushirikai a ɓoye cewa, za su yi musu biyayya game da wasu al’amura idan sun taso, kamar daƙile mutane da hana su fita wajen yaƙi tare da Annabi (ﷺ) . Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, yana sane da duk abin da suke ɓoyewa da wanda suke bayyanawa, don haka zai tona asirinsu a wajen Manzonsa (ﷺ) duk sanda ya so. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da su da nuna musu cewa, idan suna zaton dabararsu a nan duniya za ta fisshe su, to yaya za su yi da kansu lokacin da mala’iku za su zo karɓar rayukansu suna dukan fuskokinsu da bayansu da gudumomin wuta duka mai tsanani? Wannan irin azaba kuwa da take jiran su lokacin mutuwarsu za ta same su ne saboda sun yarda su bi duk wani abu na kafirci da munafurci da yake fusata Allah, suka kuma ƙi bin duk abin da zai kusantar da su zuwa ga Ubangijinsu har su sami yardarsa, kamar imani da shi da biyayya ga Manzonsa (ﷺ), don haka Allah ya lalata ayyukansu kyawawa, kamar sadaka da taimakon gajiyayyu da sada zumunci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi munafukai waɗanda zukatansu suke cike da shakka, shin suna tsammanin cewa Allah ba zai fallasa su ba ya fito da ƙulle-ƙullen da ke zukatansu a sarari? Lalle wannan zato nasu na banza ne domin ya saɓa wa hikimarsa ta bambance mai gaskiya da maƙaryaci, har a gane mumini na gaskiya da ɗan jabu, watau munafuki. Saboda haka sai Allah ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, da ya ga dama da ya nuna masa munafukai ɗaya bayan ɗaya duk ya gane su da alamominsu, amma kuma bai yi haka ba don rufa wa bayinsa asiri da kuma gudun kada yin hakan ya jawo wa danginsu muminai wasu matsaloli. Amma duk da haka ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa zai iya gane su ta salon maganarsu wadda take cike da dungu da harshen damo. To amma Allah yana sane da ayyukan bayinsa duka, zai kuma yi musu sakayya a kai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babbar jarrabar da zai yi wa muminai, watau ya umarce su da yaƙar maƙiyansa, domin ya bayyana wa bayinsa su wane ne masu jihadi saboda shi masu kuma haƙuri a kan haka, ya kuma fito da mai gaskiya da maƙaryaci a fili.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَشَآقُّواْ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلۡهُدَىٰ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗا وَسَيُحۡبِطُ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Open ayah 47:32Lalle waɗanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, kuma suka saɓa wa Manzo bayan shiriya ta bayyana a gare su, to ba za su taɓa cutar Allah da komai ba, kuma zai lalata ayyukansu.
۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَلَا تُبۡطِلُوٓاْ أَعۡمَٰلَكُمۡ
Open ayah 47:33Ya ku waɗanda suka yi imani, ku bi Allah, kuma ku bi Manzonsa, kada kuma ku ɓata ayyukanku.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ مَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٞ فَلَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡ
Open ayah 47:34Lalle waɗanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, sannan suka mutu a halin suna kafirai, to Allah ba zai taɓa gafarta musu ba.
فَلَا تَهِنُواْ وَتَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱلسَّلۡمِ وَأَنتُمُ ٱلۡأَعۡلَوۡنَ وَٱللَّهُ مَعَكُمۡ وَلَن يَتِرَكُمۡ أَعۡمَٰلَكُمۡ
Open ayah 47:35To kada ku raunana, kuma kada ku kirawo su zuwa sulhu, alhali ku ne a sama, Allah kuwa Yana tare da ku, kuma ba zai tauye muku ayyukanku ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa kafirai na Yahudawa masu hana mutane bin hanyar Allah suna kuma nuna tsananin ƙiyayyarsu ga Manzon Allah (ﷺ) bayan sun gano siffofinsa a cikin Attaura, kuma sun ga mu’ujizoji a hannunsa masu tabbatar da cewa shi Annabin Allah ne. To su sani cewa ba za su cuci Allah komai da kafircinsu ba, sai dai su cuci kawunansu, kuma duk wasu kyawawan ayyuka da suke taƙamar sun aikata Allah zai rusa su ba za su sami ladansu ba. Hakanan duk makirce-makircen da suke ƙullawa don ruguza addinin Allah ba za su yi nasara ba, Allah zai lalata su. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kira ga muminai waɗanda suka yi imani da Allah suka yi aiki da shari’arsa da lalle su yi masa biyayya su kuma yi wa Manzonsa (ﷺ) biyayya, su yi aiki da umarninsa su kuma guji haninsa, ya kuma gargaɗe su da kada su kuskura su lalata ayyukansu ta hanyar aikata kafirci ko munafunci ko yin riya. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mu jama’ar sahabban Manzon Allah (ﷺ) mun kasance muna gani ko muna da’awar cewa, babu wani aiki mai kyau da za mu yi face an karɓa, har sai da wannan ayar ta sauka: “Ku bi Allah, ku bi Manzo, kada ku ɓata ayyukanku.” Yayin da ta sauka sai kuma muke tambayar cewa: “Mene ne wannan abu da zai ɓata mana ayyukanmu?” Sai muka ce: “Su ne manyan zunubai da munanan ayyuka. Sai kuma muka kasance duk sanda muka ga wani ya aikata wani mummunan aiki na laifi sai mu ce: “Lalle ya hallaka.” Har sai da faɗin Allah ya sauka inda yake cewa: “Lalle Allah ba ya gafarta a yi shirka da shi, yana kuma gafarta abin da bai kai wannan ba ga wanda ya ga dama.” Da wannan ayar ta sauka sai muka daina faɗar waccan maganar, sai muka zamanto idan mun ga ɗaya daga cikinmu ya yi wani babban laifi sai mu riƙa jiye masa tsoro, idan kuma bai aikata babban zunubi ba sai mu riƙa yi masa kyakkyawan fata.” [Al-Marwazi Ta’azimu Ƙadaris Salat , Juzu’i na 2, shafi na 646]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara jan kunnen kafirai da cewa idan har suka dage a kan kafircinsu, suka ci gaba da hana mutane bin hanyar Allah har suka mutu suna kafirci ba su tuba ba, to su sani Allah ba zai gafarta musu ba, sai ya kama su da miyagun laifukansu ya jefa su cikin azabarsa ta har abada. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafi gwiwar muminai ya umarce su da kada su karaya ko su yi rauni wajen fuskantar abokan gabarsu, ko su neme su da yin sulhu kafin su kafiran su nuna suna so a yi sulhu, alhalin kuma ya bayyana cewa, su ne a saman kafiran, Allah ya ba su rinjaye a kansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa yana tare da su da taimakonsa da dafawarsa, ba kuma zai taɓa tauye musu wani abu daga sakamakon kyawawan ayyukansu ba, sai ma dai ya ƙara musu daga falalarsa da karamcinsa.
إِنَّمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا لَعِبٞ وَلَهۡوٞۚ وَإِن تُؤۡمِنُواْ وَتَتَّقُواْ يُؤۡتِكُمۡ أُجُورَكُمۡ وَلَا يَسۡـَٔلۡكُمۡ أَمۡوَٰلَكُمۡ
Open ayah 47:36Rayuwar duniya wasa ce da sharholiya kawai. Idan kuwa kuka yi imani kuka kiyaye dokokin Allah, to zai ba ku ladanku, ba kuma zai tambaye ku ku ba da dukiyoyinku (duka) ba.
إِن يَسۡـَٔلۡكُمُوهَا فَيُحۡفِكُمۡ تَبۡخَلُواْ وَيُخۡرِجۡ أَضۡغَٰنَكُمۡ
Open ayah 47:37Don ko idan da zai tambaye ku ita (dukiyar gaba ɗaya) Ya kuma nace muku, to da sai ku yi rowa, Ya kuma fito da ƙulle-ƙullen zukatanku.
هَٰٓأَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ تُدۡعَوۡنَ لِتُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَمِنكُم مَّن يَبۡخَلُۖ وَمَن يَبۡخَلۡ فَإِنَّمَا يَبۡخَلُ عَن نَّفۡسِهِۦۚ وَٱللَّهُ ٱلۡغَنِيُّ وَأَنتُمُ ٱلۡفُقَرَآءُۚ وَإِن تَتَوَلَّوۡاْ يَسۡتَبۡدِلۡ قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ ثُمَّ لَا يَكُونُوٓاْ أَمۡثَٰلَكُم
Open ayah 47:38To ga ku fa ku ɗin nan ana kiran ku don ku ciyar a hanyar Allah, to daga cikinku akwai masu yin rowa; wanda kuwa duk ya yi rowa, lalle ya yi wa kansa rowa ne. Allah kuma Mawadaci ne, ku ne mabuƙata. Idan kuwa kuka ba da baya to zai canja wasu mutanen ba ku ba, sannan ba za su zama kamar ku ba. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, duniya ba a bakin komai take a wajensa ba, domin kuwa ita wasa ce da sharholiya kawai, don haka kada muminai su yarda ta shagaltar da su har su manta da jihadi domin Allah ko neman lahira, sannan su sani cewa, idan sun yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ) suka kuma kiyaye dokokin Allah ta hanyar aiki da umarninsa da guje wa haninsa, to zai ba su ladansu cikakke ba da tawaya ba. Sannan ya sanar da su cewa, ba ya nufin ya matsa musu a kan abin da ya fi ƙarfinsu, don haka ne bai taɓa neman su da su bayar da dukiyarsu gaba ɗayanta ba, sai dai ya neme su da su fitar da ɗan wani kaso ƙanƙani daga cikinta na zakka da ta wajaba a kansu. Saboda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya san halin ɗan’adam da tsananin sonsa ga dukiya da rowa wajen fitar da ita, da zai neme su da su bayar da dukiyarsu gaba ɗaya ya kuma matsa musu a kan haka, to da sai su yi rowa, sai Allah ya fito da abin da yake cikin zukatansu na kwaɗayi da rowa da tsananin son dukiya, wannan ya sa ya tausaya musu bai nemi su ba da duka dukiyarsu ba. A ayar ƙarshe kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗakar da muminai cewa, ga su suna ganin abin da yake faruwa a gabansu, inda akan kira su a nemi su ba da wani ɓangare na dukiyoyinsu don Allah, don kuma taimakon addininsa, to amma duk da haka sai a samu wasu rowa ta hana su su ba da wani abu, su manta da cewa duk wanda ya yi rowar ba da wani ɗan kaso kaɗan daga ckin dukiyarsa don Allah, to ba zai cuci kowa ba sai kansa, domin ya haramta wa kansa samun lada daga Allah, Allah kuwa shi cikakken mawadaci ne, ba ya da buƙatar komai a wurin kowa, kowa ne yake da buƙata a wurinsa a kowane lokaci a cikin dukkan al’amura. Don haka ya gargaɗi muminai da cewa idan suka bijire suka bar Musuluncin to yana iya hallaka su, ya kawo wasu mutane daban waɗanda ba su ba, sannan ba za su zama kamar su ba, sai dai su zama masu ɗa’a ga Allah da bin dokokinsa.