الفتح
Al-Fath
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِنَّا فَتَحۡنَا لَكَ فَتۡحٗا مُّبِينٗا
Open ayah 48:1Lalle Mu ne Muka yi maka buɗi, buɗi mabayyani.
لِّيَغۡفِرَ لَكَ ٱللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنۢبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَيَهۡدِيَكَ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
Open ayah 48:2Don Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubinka, da kuma wanda ya jinkirta, Ya kuma cika maka ni’imarsa, kuma Ya shiryar da kai hanya madaidaiciya.
وَيَنصُرَكَ ٱللَّهُ نَصۡرًا عَزِيزًا
Open ayah 48:3Allah kuma zai taimake ka da nasara mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa ya yi masa gagarumin buɗi, ya ba shi nasara a kan abokan gabarsa ta hanyar yin sulhun Hudaibiyya, watau yarjejeniyar da Musulmi suka ƙulla da mushirikan Makka a shekara ta shida wadda ta ƙunshi dakatar da yaƙi a tsakaninsu na tsawon shekara goma, kuma Annabi (ﷺ) da sahabbansa suka haƙura da yin umara a wannan shekara sai shekara mai zuwa. Yarjejeniyar ta haɗa da duk waɗanda suke son ƙulla ƙawance da Manzon Allah (ﷺ) suna iya ƙullawa, hakanan masu son su yi ƙawance da Ƙuraishawa su ma suna iya yi. Kuma duk wanda ya gudu daga Makka zuwa Madina Annabi (ﷺ) zai dawo musu da shi, su kuma ba za su dawo da duk mutumin da ya yi ridda ya gudo daga Madina zuwa Makka ba. Duk waɗannan sharuɗɗa kuma Annabi (ﷺ) ya karɓe su, ya ƙulla sulhu da mushirikan Ƙuraishawa a kansu, tare da cewa ba su yi wa da dama daga cikin Musulmi daɗi ba, amma suka haƙura suka yi wa Manzon (ﷺ) Allah biyayya. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi wa Manzonsa (ﷺ) wannan ne domin ya gafarta masa zunubinsa da ya gabaci wannan buɗin da wanda ya jinkirta bai faru ba sai daga baya. Sannan kuma ya cika masa ni’imarsa da taimakon addininsa, ya kuma shiryar da shi hanya madaidaiciya wadda babu karkata a cikinta, ita ce Musulunci. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Annabi (ﷺ) ya kasance yana tsayuwar dare har dugadugansa su riƙa tsattsagewa. Sai A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce masa: “Me ya sa kake yin haka ne ya Manzon Allah, alhali Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka da abin da ya jinkirta?” Sai ya ce: “Yanzu ba kya fatan in kasance bawa mai yawan godiya?” Yayin da ya yi ƙiba sai ya riƙa sallar a zaune, idan ya yi nufin yin ruku’u sai ya tashi ya ɗan yi karatu sai ya yi ruku’u.” [Bukhari #4837]. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya yi masa alƙawarin ba shi cikakkiyar nasara a kan abokan gabarsa, wanda hakan ya sa Musulunci ya yi ƙarfi sosai.
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لِيَزۡدَادُوٓاْ إِيمَٰنٗا مَّعَ إِيمَٰنِهِمۡۗ وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Open ayah 48:4Shi ne wanda Ya sanya nutsuwa a zukatan muminai don su ƙara imani a kan imaninsu. Rundunonin sammai da ƙasa kuma na Allah ne, kuma Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima.
لِّيُدۡخِلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَيُكَفِّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عِندَ ٱللَّهِ فَوۡزًا عَظِيمٗا
Open ayah 48:5(Ya yi haka ne) don Ya shigar da muminai maza da mata gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu, Ya kuma kankare musu laifukansu. Wannan kuwa ya kasance babban rabo ne a wurin Allah.
وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ ٱلظَّآنِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۖ وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَلَعَنَهُمۡ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرٗا
Open ayah 48:6Ya kuma azabtar da munafukai maza da mata, da mushirikai maza da mata, masu munana zato ga Allah. Mummunar azaba ta koma a kansu; kuma Allah Ya yi fushi da su, Ya kuma la’ance su, Ya kuma tanadar musu Jahannama; makoma kuwa ta munana.
وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا
Open ayah 48:7Kuma rundunonin sammai da ƙasa na Allah ne. Allah kuwa Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ni’imar da ya yi wa muminai bayan gudanar da sulhu tsakanin Manzonsa (ﷺ) da mushirikan Ƙuraishawa, sulhun da sharuɗɗansa ba su yi wa muminai daɗi ba, to amma Allah ya sanar da Manzonsa manyan hikimomin da suke ƙunshe cikinsa, su kuma muminai sai ya saukar musu da natsuwa a zukatansu, don hankalinsu ya kwanta, kuma imaninsu ya ƙaru a kan wanda suke da shi, kuma ya nuna musu cewa, ba su nasara da rinjaye a kan kafirai a wannan lokaci ba wani abu ne mai wuya a wurin Allah ba, domin rundunonin sammai da na ƙasa duk nasa ne, ƙarƙashin ikonsa suke, to amma yana zartar da komai ne cikin hikima da ilimi, domin ya tabbata shi masanin komai ne, mai hikima cikin dukkan ayyukansa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi wa muminai ni’imar natsuwa a zukatansu da ƙarin imani a kan imaninsu domin ya shigar da su, mazansu da matansu cikin gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, ya kuma kankare musu laifukansu ba zai kama su da su ba, wannan sakamako kuwa shi ne babban rabo da bawa zai samu daga Allah (Mai tsarki da daukaka). Su kuma munafukai mazansu da matansu da mushirikai mazansu da matansu masu yi wa Allah mummunan zato cewa, ba zai taimaki addininsa ba, kuma ba zai ɗaukaka kalmarsa ba, to duk waɗannan a kansu kaɗai mummunan bala’i zai dawo na mugun zaton da suke yi wa Allah, kuma Allah ya yi fushi da su saboda kafircinsu da mummunan zatonsu, ya kuma la’ance s; ba su ba samun rahamarsa, kuma a lahira ya yi musu tanadin wutar Jahannama wadda za su shige ta su dawwama a cikinta har abada, makoma kuwa ta munana idan har ta zamanto wutar Jahannama ce. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara tabbatar wa muminai cewa babu abin da zai gagare shi, domin rundunonin sammai da ƙasa duk nasa ne, a ƙarƙashin ikonsa suke, kuma shi ya tabbata mabuwayi ne babu abin da zai fi ƙarfinsa, mai hikima ne kuma cikin halittarsa da ƙaddararsa da tsarinsa.
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ شَٰهِدٗا وَمُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا
Open ayah 48:8Lalle Mu Muka aiko ka don ka zama sheda kuma mai albishir mai gargaɗi.
لِّتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُۚ وَتُسَبِّحُوهُ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلًا
Open ayah 48:9Don (ku mutane) ku yi imani da Allah da Manzonsa ku kuma taimake shi (wato Annabinsa), kuma ku girmama shi, ku kuma tsarkake Shi (wato Allah) safe da yamma.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُبَايِعُونَكَ إِنَّمَا يُبَايِعُونَ ٱللَّهَ يَدُ ٱللَّهِ فَوۡقَ أَيۡدِيهِمۡۚ فَمَن نَّكَثَ فَإِنَّمَا يَنكُثُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِمَا عَٰهَدَ عَلَيۡهُ ٱللَّهَ فَسَيُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Open ayah 48:10Lalle waɗanda suka yi maka mubaya’a Allah kawai suke yi wa mubaya\'a, Hannun Allah yana saman hannayensu. To duk wanda ya warware, to kansa kawai ya warware wa, wanda kuwa ya cika abin da ya yi wa Allah alƙawarinsa, to ba da daɗewa ba za Mu ba shi lada mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana martabar Manzonsa (ﷺ) da matsayinsa a cikin al’umma da cewa, ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (ﷺ) domin ya zama mai yi wa al’ummarsa shaida ranar alƙiyama cewa, ya isar musu da saƙon Allah, ya bayyana musu duk wani alheri don su aikata shi, ya kuma nuna musu duk wani sharri don su guje shi, ya kuma zama mai yi wa muminai albishir da abin da Allah ya tanadar musu a duniya na samun nasara da kafuwa, da kuma abin da ya tanadar musu a lahira na ni’imar gidan Aljanna, sannan mai gargaɗi ga kafirai game da ƙasƙanci da karaya a fagen yaƙi a hannun muminai da kuma abin da ya tanadar musu a lahira na azaba mai raɗaɗi da take jiran su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, ya yi musu haka ne don su yi imani da Allah da Manzonsa, su kuma girmama Manzonsa (ﷺ) tare da darajta shi, su kuma tsarkake Allah da tasbihi safe da yamma. Sannan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalar sahabban da suka yi wa Manzon Allah (ﷺ) mubaya’a a Hudaibiyya a shekara ta shida bayan hijira zuwa Madina, yayin da ya aika Usman ɗan Affan zuwa ga Ƙuraishawa don ya shaida musu cewa, Annabi bai zo da niyyar ya yaƙe su ba, ya zo ne da niyyar ya yi umara kaɗai, don haka su ƙyale shi ya shiga garin Makka don gudanar da abin da ya zo dominsa, watau umara. Sai aka zo wa Manzon Allah (ﷺ) da labarin cewa Ƙuraishawa sun kashe Usman (Allah ya kara masa yarda), sai Manzon Allah (ﷺ) ya tara sahabbansa da suke tare da shi, waɗanda adadinsu ya kai mutum dubu da ɗari huɗu, dukkansu suka yi masa mubaya’a a kan jajircewa wajen yaƙi da Ƙuraishawa, ko su mutu ko su yi rai, ba gudu ba ja da baya. Annabi (ﷺ) ya ɗora tafin hannunsa na dama a kan na hagu ya ce wannan na Usman ne. Waɗannan su ne waɗanda ake ce wa ma’abota mubaya’ar ƙarƙashin bishiya ko kuma ‘Bai’atur Ridhwan’ , watau mubaya’ar samun yardar Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa cewa duk waɗanda suka yi masa muba’aya, to Allah suka yi wa, domin shi ne ya ba su umarnin su yaƙi mushirikai, kuma shi ne mai yi musu sakayya a kan haka. Allah ya tabbatar musu da cewa, hannunsa yana saman hannayensu lokacin da suke yin wannan mubaya’ar, don haka ya san komai babu abin da zai ɓuya gare shi. An karɓo daga Al-Bara ɗan Azib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ku kuna ɗaukar buɗi shi ne buɗe Makka, babu shakka buɗe Makka buɗi ne, amma mu muna ɗaukar buɗi shi ne ‘Bai’atur Ridhwan’ a ranar Hudaibiyya.” [Bukhari #3919]. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya faɗa mana a ranar Hudaibiyya cewa: “Ku ne mafi alherin mutanen da ke bayan ƙasa.” [Bukhari #3923 da Muslim #1856]. An karɓo daga Yazid ɗan Abu Ubaid (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na tambayi Salamatu ɗan Akwa’u (Allah ya kara masa yarda) cewa, a kan mene ne kuka yi wa Manzon Allah mubaya’a a ranar Hudaibiyya? Sai ya ce: \"A kan mutuwa.\" [Bukhari #6780 da Muslim #1860]. An karɓo daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Ya ji Ummu Mubasshir, (Allah ya kara mata yarda), tana cewa, ta ji Annabi (ﷺ) a wajen Hafsatu (Allah ya kara mata yarda), yana cewa: “In sha Allah, babu mutum ɗaya daga cikin mutanen da suka yi masa mubaya’a a ƙarƙashin bishiya da zai shiga wuta.” [Muslim #2469]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, yana sane da komai, don haka duk wanda ya warware mubaya’arsa bai cika alƙawarin da ya yi wa Allah na taimaka wa addininsa ba, to ya sani cewa kansa ya cuta ba Allah ba; wanda kuwa ya cika alƙawarin da ya yi wa Allah na taimaka wa addininsa, to Allah zai ba shi lada mai girma shi ne gidan Aljanna.
سَيَقُولُ لَكَ ٱلۡمُخَلَّفُونَ مِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ شَغَلَتۡنَآ أَمۡوَٰلُنَا وَأَهۡلُونَا فَٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَاۚ يَقُولُونَ بِأَلۡسِنَتِهِم مَّا لَيۡسَ فِي قُلُوبِهِمۡۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ لَكُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ بِكُمۡ ضَرًّا أَوۡ أَرَادَ بِكُمۡ نَفۡعَۢاۚ بَلۡ كَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرَۢا
Open ayah 48:11Waɗanda suka ƙi fita da kai daga cikin mutanen ƙauye za su ce maka: “Dukiyoyinmu da iyalinmu ne suka shagaltar da mu, sai ka nema mana gafara.” Da harsunansu suna faɗar abin da ba ya cikin zukatansu. Ka ce: “To wa zai amfana muku wani abu ne a wajen Allah idan Ya yi nufin ku da cutuwa, ko kuma Ya yi nufin ku da alhairi?” A’a, Allah yana sane da abin da kuka kasance kuna aikatawa.
بَلۡ ظَنَنتُمۡ أَن لَّن يَنقَلِبَ ٱلرَّسُولُ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ إِلَىٰٓ أَهۡلِيهِمۡ أَبَدٗا وَزُيِّنَ ذَٰلِكَ فِي قُلُوبِكُمۡ وَظَنَنتُمۡ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِ وَكُنتُمۡ قَوۡمَۢا بُورٗا
Open ayah 48:12“A’a, ku dai kun zaci cewa Manzo da muminai ba za su komo wajen iyalinsu ba har abada, aka kuma ƙawata wannan a cikin zukatanku, kuka kuma yi mummunan zato, kuma kun kasance mutane halakakku.”
وَمَن لَّمۡ يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ فَإِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ سَعِيرٗا
Open ayah 48:13Duk kuwa wanda bai yi imani da Allah da Manzonsa ba, to lalle Mu Mun tanadi wutar Sa’ira ga kafirai.
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Open ayah 48:14Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, Yana kuma azabtar da wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama. A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya zargi wasu mutanen ƙauye da suka ƙi fita zuwa Makka tare da Manzonsa (ﷺ); yayin kuma da ya tuhume su a kan haka sai suka riƙa cewa, kula da dukiyoyinsu da ‘ya’yansu ne suka shagaltar da su har ba su sami damar fita tare da shi ba, don haka suna roƙon sa da ya nema musu gafarar zunubansu a wurin Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, ƙarya suke yi ba gafarar Allah suke nema ba; bakunansu ne kawai suke furta abin da babu shi a zukatansu, domin da a ce da gaske suke da sai su tuba daga laifukansu, su gyara halayensu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya faɗa musu cewa, babu mai iya amfana musu komai a wurin Allah idan har Allah ya yi nufin su da alheri ko ya yi nufin su da sharri, watau dai su saduda su mayar da komai wurin Allah, su faɗi gaskiyar al’amari yadda yake, domin kuwa shi Allah masanin komai ne babu wani aikinsu da za su iya ɓoye masa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana gaskiyar abin da ya hana su su bi Manzonsa zuwa Makka, watau shi ne sun yi zaton cewa Manzo da sahabbansa duk za su hallaka ne a wannan tafiyar ba za su ƙara komawa Madina zuwa ga iyalansu ba har abada, Shaiɗan kuma ya ƙawata musu wannan mummunan zaton a zukatansu, suka kuma yi wa Allah mummunan zato na cewa ba zai taimaki Annabinsa ba, suka kuwa tabbata mutane halakakku saboda munana zato da suka yi wa Allah da ƙin fita tare da Manzonsa (ﷺ) ba da wani ƙaƙƙarfan uzuri ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda bai yi imani da Allah da Manzonsa ba to kafiri ne, kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tanadar wa kafirai azaba mai raɗaɗi a ranar alƙiyama tana nan tana jiran su. Sai kuma Allah ya jaddada wa bayinsa cewa shi ne kaɗai mai mulkin sammai da ƙasa, yana sarrafa su da duk abin da ke cikinsu kamar yadda ya ga dama, yana gafarta wa wanda ya ga dama idan ya bi umarninsa ya shigar da shi Aljanna da falalarsa, yana kuma azabta wanda ya ga dama idan ya bijire wa umarninsa da adalcinsa. Allah kuma ya tabbata mai yawan gafarta zunuban bayinsa ne yayin da suka tuba, mai jin ƙansu ne.
سَيَقُولُ ٱلۡمُخَلَّفُونَ إِذَا ٱنطَلَقۡتُمۡ إِلَىٰ مَغَانِمَ لِتَأۡخُذُوهَا ذَرُونَا نَتَّبِعۡكُمۡۖ يُرِيدُونَ أَن يُبَدِّلُواْ كَلَٰمَ ٱللَّهِۚ قُل لَّن تَتَّبِعُونَا كَذَٰلِكُمۡ قَالَ ٱللَّهُ مِن قَبۡلُۖ فَسَيَقُولُونَ بَلۡ تَحۡسُدُونَنَاۚ بَلۡ كَانُواْ لَا يَفۡقَهُونَ إِلَّا قَلِيلٗا
Open ayah 48:15Waɗanda suka ƙi fita tare da kai za su ce, lokacin da kuka tafi zuwa wasu wuraren ganima don ku samo ta: “Ku bar mu mu bi ku”, suna nufin su musanya zancen Allah ne. Ka ce: “Ba za ku bi mu ba, da ma tuni haka Allah Ya faɗa.” To za su ce: “A’a, kuna yi mana hassada ne kawai.” Ba haka ba ne, sun kasance ba sa fahimta ne sai ‘yan kaɗan. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rashin gaskiyar waɗanda suka noƙe suka ƙi fita tare da Manzonsa zuwa Makka, har suka ba da hanzari da cewa za su tsaya don su kula da dukiyoyinsu da ‘ya’yansu. To amma kuma yayin da suka ji cewa Manzon Allah (ﷺ) da muminai za su tafi Khaibar kuma za su samo ganima a can, sai suka fara nuna kwaɗayinsu da haɗamarsu a fili, suka riƙa roƙon Annabi (ﷺ) da sahabbansa cewa, a bar su su fita tare da su don su ma su sami ganima a bulus, wai suna ganin za su iya canza maganar Allah da ya riga ya yi ta cewa, wannan ganimar ta Khaibara ta muminai ce waɗanda suka halarci sulhun Hudaibiyya, su ne kawai Allah ya yi wa alƙawarin wannan ganimar. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya faɗa musu cewa, ba za su bari su bi su ba, domin alƙawarin da ya yi wa mutanen Hudaibiyya na samun wannan ganimar. To amma sai suka riƙa cewa, ai hassada ce kawai ta sa aka hana su fita zuwa Khaibara wai ba umarni ne daga Allah ba. Sai Allah ya mayar musu da martani cewa, ba haka ba ne ba, su ne dai ba sa son bin umarnin Allah da haninsa, don haka ne suka auka cikin saɓonsa.
قُل لِّلۡمُخَلَّفِينَ مِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ سَتُدۡعَوۡنَ إِلَىٰ قَوۡمٍ أُوْلِي بَأۡسٖ شَدِيدٖ تُقَٰتِلُونَهُمۡ أَوۡ يُسۡلِمُونَۖ فَإِن تُطِيعُواْ يُؤۡتِكُمُ ٱللَّهُ أَجۡرًا حَسَنٗاۖ وَإِن تَتَوَلَّوۡاْ كَمَا تَوَلَّيۡتُم مِّن قَبۡلُ يُعَذِّبۡكُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا
Open ayah 48:16Ka ce da waɗanda suka ƙi fita tare da kai daga mutanen ƙauye: “Ba da daɗewa ba za a kirawo ku zuwa wurin wasu mutane masu tsananin yaƙi don ku yaƙe su ko su musulunta. To idan kuka bi (wannan umarni), Allah zai ba ku lada kyakkyawa, idan kuwa kuka ba da baya kamar yadda kuka ba da baya a da can, zai azabtar da ku azaba mai raɗaɗi.”
لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَمَن يَتَوَلَّ يُعَذِّبۡهُ عَذَابًا أَلِيمٗا
Open ayah 48:17Babu wani laifi a kan makaho, babu kuma wani laifi a kan gurgu, kuma babu wani laifi a kan marar lafiya (game da rashin fita yaƙi). Wanda kuwa ya bi Allah da Manzonsa to zai shigar da shi gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, wanda kuma ya ba da baya to zai azabtar da shi azaba mai raɗaɗi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya jarraba waɗannan Larabawan ƙauyuka da suka ƙi fita zuwa Makka tare da shi ya sanar da su cewa za a kirawo su don a tura su su yaƙi wasu mutane masu tsananin ƙarfi na yaƙi, su yaƙe su don Allah, ko kuma su shiga Musulunci ba tare da yaƙi ba. To idan sun bi umarnin Allah sun amsa kiransa na fita wannan yaƙin, to sun tabbata masu gaskiya, kuma zai ba su lada kyakkyawa, watau gidan Aljanna; amma idan suka bijire wa yi masa biyayya kamar yadda suka yi a can baya, suka ƙi fita zuwa Makka tare da shi, to zai azabtar da su azaba mai raɗaɗi. Daga nan sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mutanen da aka ba wa damar su zauna a gida ba sai sun fita yaƙi ba saboda suna da uzuri karɓaɓɓe. Waɗannan su ne makafi da guragu da marasa lafiya, su kam babu laifi a kansu idan ba su fita zuwa yaƙi ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, duk wanda ya bi Allah, ya kuma bi Manzonsa, to zai shigar da shi gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, wanda kuwa ya bijire wa Allah da Manzonsa, to zai azabtar da shi azaba mai raɗaɗi.
۞لَّقَدۡ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ يُبَايِعُونَكَ تَحۡتَ ٱلشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ عَلَيۡهِمۡ وَأَثَٰبَهُمۡ فَتۡحٗا قَرِيبٗا
Open ayah 48:18Haƙiƙa Allah Ya yarda da muminai yayin da suke yi maka mubaya’a a ƙarƙashin bishiyar nan, to Allah Ya san abin da yake cikin zukatansu, sai Ya saukar musu da nutsuwa Ya kuma saka musu da buɗi na kurkusa.
وَمَغَانِمَ كَثِيرَةٗ يَأۡخُذُونَهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا
Open ayah 48:19Da kuma ganimomi masu yawa da za su yi ta kwasar su. Allah kuwa Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalar da ya yi wa sahabban Manzonsa (ﷺ), watau ya yarda da su lokacin da suke yi wa Manzonsa (ﷺ) mubaya’a a Hudaibiyya a ƙarƙashin bishiya a kan za su jajirce wajen yaƙi tare da shi har su yi nasara ko kuma su yi mutuwar shahada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya san abin da yake cikin zukatansu na imani da ikhlasi da gaskiya, don haka sai ya saukar musu da nutsuwa a zukatansu, ya kuma yi musu sakayya da wani buɗi na kurkusa, watau buɗe Khaibara a madadin rashin samun shiga garin Makka su yi umara. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi musu tagomashin ganimomi masu yawa da za su samu daga Yahudawan Khaibara, domin Allah ya kasance mabuwayi ne babu mai iya rinjayar sa, mai hikima ne cikin halittarsa da ƙaddararsa da tsarinsa. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mun kasance mu dubu da ɗari huɗu a ranar Hudaibiyya, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce mana: “Ku ne mafi alherin mutane a bayan ƙasa.” [Bukhari #4154]. An karɓo daga Ma’aƙil ɗan Yasar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na gan ni a ranar Mubaya’ar ƙarƙashin bishiya, Annabi (ﷺ) yana karɓar mubaya’a daga mutane, ni kuma ina ɗage masa reshenta daga kansa, yawanmu kuwa mutum dubu da ɗari huɗu ne, ba mu yi masa mubaya’a a kan mutuwa ba, mun dai yi masa mubaya’a ne a kan ba za mu gudu ba.” [Muslim #1858]. An karɓo daga Salamatu ɗan Akwa’u (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na yi wa Manzon Allah (ﷺ) mubaya’a a ƙarƙashin bishiya.” Sai aka ce masa: “A kan mene ne kuka yi masa mubaya’a a wannan ranar?” Sai ya ce: “A kan mutuwa.” [Bukhari #4169].
وَعَدَكُمُ ٱللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَةٗ تَأۡخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمۡ هَٰذِهِۦ وَكَفَّ أَيۡدِيَ ٱلنَّاسِ عَنكُمۡ وَلِتَكُونَ ءَايَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَيَهۡدِيَكُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
Open ayah 48:20Allah kuma Ya yi muku alƙawarin wasu ganimomi masu yawa da za ku yi ta kwasar su, sai Ya gaggauto muku da wannan (ganimar Khaibara) Ya kuma kame muku hannayen mutanen (wato Yahudu), don kuwa (wannan) ya zama aya ga muminai, Ya kuma shiryar da su hanya madaidaiciya.
وَأُخۡرَىٰ لَمۡ تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهَا قَدۡ أَحَاطَ ٱللَّهُ بِهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٗا
Open ayah 48:21Ɗaya (ganimar) kuwa ba ku sami iko a kanta ba, haƙiƙa Allah Ya san da ita, Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai.
وَلَوۡ قَٰتَلَكُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوَلَّوُاْ ٱلۡأَدۡبَٰرَ ثُمَّ لَا يَجِدُونَ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا
Open ayah 48:22Da kuwa waɗanda suka kafirta za su yaƙe ku, tabbas da sun juya da baya, sannan ba za su sami wani majiɓinci ko mataimaki ba.
سُنَّةَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلُۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّةِ ٱللَّهِ تَبۡدِيلٗا
Open ayah 48:23(Wannan ita ce) sunnar Allah wadda ta riga ta gabata tun tuni; ba kuwa za ka taɓa samun canji ba game da sunnar Allah.
وَهُوَ ٱلَّذِي كَفَّ أَيۡدِيَهُمۡ عَنكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ عَنۡهُم بِبَطۡنِ مَكَّةَ مِنۢ بَعۡدِ أَنۡ أَظۡفَرَكُمۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرًا
Open ayah 48:24Shi ne kuma Wanda Ya kame muku hannayensu, kuma (Ya kame) musu hannayenku a cikin Makka bayan kuwa Ya riga ya ba ku nasara a kansu. Allah kuma Ya zamanto Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake yi wa muminai albishir na ba su ganimomi masu yawa waɗanda za su samu a yaƙe-yaƙensu na Musulunci waɗanda za su yi a nan gaba, ya kuma gaggauto musu da ganimar Khaibara, ya kuma kame musu hannayen Yahudawa yayin da suka yi niyyar su cutar da iyalansu a bayansu. Sannan kuma don wannan ganimar da aka gaggauto musu da ita ta zama alama ce a gare su da ke nuna taimakon Allah da ƙarfafawarsa a gare su, ya kuma shiryar da su tafarkinsa madaidaici wanda babu karkata a cikinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake yi musu wani alƙawarin na ba su wasu ganimomi a nan gaba waɗanda a yanzu ba su da ikon samun su, to amma Allah ya tsare musu su bai ba wa wasu iko a kansu ba, har zuwa lokacin da ya ba su iko suka cinye su da yaƙi, kamar Farisawa da Rumawa waɗanda Allah ya ba wa Musulmi ikon cin su da yaƙi bayan a da can ba za su iya tunkarar su da yaƙi ba saboda rauninsu da tsananin ƙarfin waɗannan ƙasashe. Allah kuwa mai iko ne a kan komai babu abin da zai gagare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara wa muminai ƙarfin gwiwa inda ya tabbatar musu da cewa, da kafirai za su yaƙe su, to ba za su iya samun nasara a kansu ba, sai dai su juya da baya su gudu, sannan ba za su sami wani wanda zai jiɓinci al’amarinsu ba, ba kuma za su sami wanda zai taimaka musu ba su yaƙi Musulmi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, wannan ita ce sunnarsa tabbatacciya a kowane zamani a kuma kowane wuri, kuma ita ce sunnarsa da ta riga ta gabata a cikin al’ummun da suka shuɗe kuma babu wani canji game da sunnar Allah. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tuna musu wata ni’imar da ya yi musu lokacin da ya kame musu hannayen mutanen Makka, yayin da mayaƙa mutum tamanin suka nufo su a Hudaibiyya da niyyar cutar da su, to amma Musulmi suka farga suka kuma sami nasarar cafke su gaba ɗayansu a hannu, to amma sai Allah ya kame hannayen muminai ba su kashe su ba, ba su kuma cutar da su ba, sai ma dai suka sake su gaba ɗayansu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kasance masanin abin da suke aikatawa ne, don haka yana yi wa bayinsa muminai kyakkyawan tsari a cikin dukan al’amuransu. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “A ranar Hudaibiyya wasu mazaje su tamanin daga cikin mutanen Makka masu ɗauke da makamai suka fito daga ɓangaren dutsen Tan’im suka auka wa Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa suna son su mamaye su, sai Manzon Allah (ﷺ) ya yi addu’a a kansu, sai aka cafke su, amma daga baya Annabi (ﷺ) ya yi musu afuwa, sai wannan ayar ta 24 ta sauka.” [Muslim #1808 da Ahmad #12227].
هُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَٱلۡهَدۡيَ مَعۡكُوفًا أَن يَبۡلُغَ مَحِلَّهُۥۚ وَلَوۡلَا رِجَالٞ مُّؤۡمِنُونَ وَنِسَآءٞ مُّؤۡمِنَٰتٞ لَّمۡ تَعۡلَمُوهُمۡ أَن تَطَـُٔوهُمۡ فَتُصِيبَكُم مِّنۡهُم مَّعَرَّةُۢ بِغَيۡرِ عِلۡمٖۖ لِّيُدۡخِلَ ٱللَّهُ فِي رَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۚ لَوۡ تَزَيَّلُواْ لَعَذَّبۡنَا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابًا أَلِيمًا
Open ayah 48:25Su ne waɗanda suka kafirta suka kuma hana ku isa ga Masallaci mai alfarma, suka kuma hana dabbobin hadaya isa wurin yankansu. Kuma ba don wasu mazaje muminai da wasu mataye muminai da ba ku san su ba, don kada ku kashe su, sannan wani laifi nasu ya same ku ba tare da sani ba, (da Ya ba ku damar yaƙar su. Wannan ya faru ne) don Allah Ya shigar da wanda Ya ga dama cikin rahamarsa. Da sun ware to lalle da Mun azabtar da waɗanda suka kafirta daga cikinsu azaba mai tsanani.
إِذۡ جَعَلَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡحَمِيَّةَ حَمِيَّةَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ فَأَنزَلَ ٱللَّهُ سَكِينَتَهُۥ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَعَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَأَلۡزَمَهُمۡ كَلِمَةَ ٱلتَّقۡوَىٰ وَكَانُوٓاْ أَحَقَّ بِهَا وَأَهۡلَهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا
Open ayah 48:26Yayin da waɗanda suka kafirta suka sanya kishi irin kishin jahiliyya a cikin zukatansu, sai Allah Ya saukar da nutsuwarsa ga Manzonsa da muminai, Ya kuma kimsa musu kalmar imani, da ma kuma su suka fi cancantarta, kuma (su ne) masu ita. Allah kuma Ya kasance Masanin komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu dalilai da suka ba wa muminai damar su yaƙi mushirikan Makka, watau saboda sun hana Manzon Allah da muminai su isa zuwa ga Ɗaki mai alfarma na Makka wanda suka baro Madina domin ziyartar sa da yin ibada a wajensa, suka kuma hana hadaya ta isa wurin yankanta, na haramin Makka. Waɗannan duka dalilai ne da suka ba wa Musulmi damar su auka musu da yaƙi. To abin da kawai ya hana faruwar haka shi ne wasu muminai maza da mata da suke a tsakiyar mushirikan Makka waɗanda ba a ware suke a wani keɓaɓɓen wuri ko unguwa ba, ga shi kuma su Musulmi ba sanin su suka yi ba, don haka idan suka auka wa kafiran Makka da yaƙi za su iya kashe waɗannan muminan ba tare da sun sani ba, wannan kuwa zai jawo musu faɗawa cikin laifin kisan mumini da kuma biyan diyyoyinsu. To ba don wannan dalili ba da Allah ya ba wa muminai izinin yaƙi don buɗe garin Makka, domin Allah ya shigar da wanda ya ga dama cikin rahamarsa. Saboda haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, da kafirai sun ware gefe ɗaya ba su gauraya da muminai ba, da tabbas ya saukar musu azaba mai tsanani. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a lokacin da aka zo yin Sulhul Hudaibiyya kafirai sun sanya kishi a zukatansu irin kishin jahiliyya wanda ba ya da wata alaƙa da tabbatar da gaskiya sai dai son zuciya kawai. Domin a lokacin da za a rubuta takardar yarjejeniya sai suka ƙi yarda a rubuta ‘Bismillahir Rahmanir Rahimi’ a farkonta, suka kuma kafe ba za a rubuta wa Manzon Allah siffarsa ta manzanci ba, sai dai kawai a rubuta sunansa zalla, suka kuma kafe a kan cewa Manzon Allah da Musulmi ba za su shiga Makka a wannan shekarar ba sai shekara mai zuwa, wai suna ganin in sun bari ya shiga za su yi abin kunya a wurin sauran ‘yan’uwansu Larabawa, domin wai za a riƙa cewa Musulmi sun fi ƙarfinsu ne, shi ya sa har suka sami shiga Makka suka yi umara. To duk da waɗannan abubuwa na ban haushi da renin wayo, Allah ya saukar da nutsuwarsa ga Manzonsa da muminai, bai bari fushi ya sanya sun aikata abin da zai haddasa tashin hankali da hatsaniya ba, har ya kai ga hana tabbatar wannan sulhu, don haka suka danne zukatansu, Allah kuma ya kimsa musu kalmar taƙawa, watau Kalmar Shahada, suka tsaya a kan kiyaye haƙƙoƙinta; da ma kuma su suka fi cancanta da ita, kuma su ne masu ita, domin Allah ya san alherin da ke cikin zukatansu, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbata masanin komai ne babu abin da zai ɓoyu gare shi.
لَّقَدۡ صَدَقَ ٱللَّهُ رَسُولَهُ ٱلرُّءۡيَا بِٱلۡحَقِّۖ لَتَدۡخُلُنَّ ٱلۡمَسۡجِدَ ٱلۡحَرَامَ إِن شَآءَ ٱللَّهُ ءَامِنِينَ مُحَلِّقِينَ رُءُوسَكُمۡ وَمُقَصِّرِينَ لَا تَخَافُونَۖ فَعَلِمَ مَا لَمۡ تَعۡلَمُواْ فَجَعَلَ مِن دُونِ ذَٰلِكَ فَتۡحٗا قَرِيبًا
Open ayah 48:27Haƙiƙa Allah Ya tabbatar wa Manzonsa gaskiyar mafarkin cewa, lalle za ku shiga Masallaci mai alfarma insha Allahu, kuna cikin aminci kuna masu aske kawunanku da masu yin saisaye, ba tare da kuna jin tsoron (komai) ba, to Ya san abin da ba ku sani ba, sai Ya sanya buɗi na kusa kafin wannan.
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدٗا
Open ayah 48:28Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya don Ya ɗora shi a kan kowane addini. Allah kuma Ya isa Mai shaida. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa da Manzonsa (ﷺ) gaskiyar mafarkin da ya yi a Madina, inda ya gan shi tare da sahabbansa sun shiga garin Makka lafiya lau ba tare da suna cikin tsoron kowa ba, har ma sun gama umararsu, wasu sun aske kawunansu gaba ɗaya, wasu kuma sun yi saisaye. Annabi (ﷺ) ya ba wa sahabbansa labarin wannan mafarki nasa suka kuma yi farin ciki sosai. To lokacin da kafirai suka hana su shiga Makka har daga ƙarshe aka yi sulhu a kan cewa, su koma Madina sai shekara mai zuwa su dawo, wannan ya ɓata wa sahabbai rai matuƙa, suka kuma riƙa tambaya game da mafarkin da Manzon Allah (ﷺ) ya yi; to sai kuma ga yadda al’amarin ya kasance. Annabi (ﷺ) ya bayyana musu cewa ai bai faɗa musu cewa a wannan shekarar ne abin zai tabbata ba, don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da gaskiyar mafarkin Manzonsa (ﷺ), musamman ya yi musu tagomashi da gaggauto musu wani buɗi, watau abin da ya gudana na sulhun Hudaibiyya da abin da ya biyo bayansa na buɗe Khaibara, ta hannun muminai waɗanda suka halarci sulhun Hudaibiyya. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jaddada musu matsayin addinin Musulunci, da cewa nasa ne, shi ne wanda ya aiko Manzonsa (ﷺ) da shiriya, watau ilimi mai amfani, da kuma addini na gaskiya, watau aiki nagari, domin ya ɗora shi a kan dukkan addinai gaba ɗaya, kuma Allah ya yi shaida a kan haka, Allah kuwa ya isa mai shaida.
مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَى ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِم مِّنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ وَمَثَلُهُمۡ فِي ٱلۡإِنجِيلِ كَزَرۡعٍ أَخۡرَجَ شَطۡـَٔهُۥ فَـَٔازَرَهُۥ فَٱسۡتَغۡلَظَ فَٱسۡتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِۦ يُعۡجِبُ ٱلزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ ٱلۡكُفَّارَۗ وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِنۡهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمَۢا
Open ayah 48:29Muhammadu Manzon Allah ne. Waɗanda kuma suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne; za ka gan su suna ruku’i suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa; alamominsu na gurbin sujjada suna bayyana a fuskokinsu. Wannan shi ne misalinsu a cikin Attaura. Misalinsu kuwa a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fitar da reshenta sai ya ƙarfafe ta, sannan ta yi kauri sai ta daidaita a kan tushiyarta ta riƙa ƙayatar da manoma, don Ya cusa wa kafirai haushi. Allah Ya yi wa waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari daga cikinsu alƙawarin gafara da lada mai girma. A wannan ayar ta ƙarshen Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da manzancin Annabi Muhammadu (ﷺ), babu mai jayayya a kan haka sai kafirai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana kyawawan siffofin sahabban Manzonsa (ﷺ), waɗanda suka yi hijira da mutanen Madina, ya ambace su kamar haka: <b>Na ɗaya </b>, su masu tsananta wa kafirai abokan gaba ne ba sa sassauta musu, amma a junansu masu tausaya wa juna ne. <b>Na biyu </b>, su mutane ne a koyaushe masu tsayar da salloli na farilla da na nafila tare da ikhlasi. <b>Na uku </b>, su masu neman falala ne daga Ubangijinsu da lada da kuma yardarsa. <b>Na huɗu </b>, a fuskokinsu suna da alamomi na hasken sujjada da yawan salla. Waɗannan siffofi nasu kuma haka aka bayyana su a cikin Attaura. <b>Na biyar </b>, wata siffa kuma da aka siffanta su da ita a littafin Linjila ita ce dangane da taimakon junansu da cewa sun yi kama da shuka wadda take fitar da reshenta sai ya ƙarfafe ta sai ta yi kauri ta kuma daidaita a kan tushiyarta, sai cikarta da ƙarfinta su riƙa ba wa manoma sha’awa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙarfafi sahabbai da irin wannan siffa suna taimaka wa junansu wajen ɗaukaka addinin Musulunci da yaɗa da’awarsa, domin ya daɗa cusa haushi a zukatan kafirai, don ganin ci gaban addinin Allah da yaɗuwarsa a ko’ina. Sai kuma a ƙarshe Allah ya yi wa sahabbai waɗanda suka yi imani da shi da Manzonsa suka yi kyawawan ayyuka alƙawarin samun gafarar zunubansu da kuma samun lada mai girma, watau gidan Aljanna.