الحجرات
Al-Hujuraat
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Open ayah 49:1Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku wuce gaban Allah da Manzonsa, kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَرۡفَعُوٓاْ أَصۡوَٰتَكُمۡ فَوۡقَ صَوۡتِ ٱلنَّبِيِّ وَلَا تَجۡهَرُواْ لَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ كَجَهۡرِ بَعۡضِكُمۡ لِبَعۡضٍ أَن تَحۡبَطَ أَعۡمَٰلُكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تَشۡعُرُونَ
Open ayah 49:2Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku ɗaga muryoyinku sama da muryar Annabi, kada kuma ku ɗaga masa murya wajen yin magana kamar yadda shashinku yake ɗaga wa shashi, don kada ayyukanku su lalace alhali kuwa ku ba ku sani ba.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصۡوَٰتَهُمۡ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱمۡتَحَنَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمۡ لِلتَّقۡوَىٰۚ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٌ عَظِيمٌ
Open ayah 49:3Lalle waɗanda suke yin ƙasa-ƙasa da muryoyinsu a wurin Manzon Allah, waɗannan su ne waɗanda Allah Ya jarrabi zukatansu da imani. Suna da (sakamakon) gafara da lada mai girma. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira muminai waɗanda suka yi imani da shi, suka yarda za su bi dokokin shari’arsa, ya hana su wucewa gaban Allah da Manzonsa (ﷺ) wajen aikata wani aiki ko faɗar wata magana kafin su saurari abin da Allah da Manzonsa za su faɗa. Duk da cewa wannan ayar ta sauka ne game da jayayyar da ta faru tsakanin Abubakar (Allah ya kara masa yarda) da Umar a gaban Manzon Allah (ﷺ) a kan wanda ya cancanta a naɗa shugaba ga ƙabilar Tamim, kafin su ji abin da Manzo (ﷺ) zai faɗa, to amma ayar ta ƙunshi umarni ne ga muminai gaba ɗaya, watau duk wata magana ko wani aiki kada mumini ya sha gaban Allah da Manzonsa da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su kiyaye dokokinsa ta hanyar bin umarninsa da guje wa haninsa, ya tabbatar musu cewa, shi mai jin dukkan maganganunsu ne, kuma masanin dukkan ayyukansu, don haka zai yi wa kowa sakayya gwargwadon aikinsa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake yin kira ga muminai da kada su ɗaga muryoyinsu a kan muryan Annabi (ﷺ) yayin da suke masa magana, kada kuma su riƙa kiran sa da sunansa zalla, kamar yadda suke kiran junansu; su kira shi da siffar manzanci ko annabci da kuma tausasa murya, domin saɓa wa wannan umarni zai iya jawo musu rushewar ladan ayyukansu ba tare da sun ankara ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Zubair (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Umar (Allah ya kara masa yarda) ya kasance, bayan saukar wannan ayar, ba ya iya jiyar da Manzon Allah (ﷺ) sautinsa har sai Manzon Allah ya nemi ƙarin bayani daga gare shi.” [Bukhari #4845]. An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yayin da wannan ayar ta sauka: “Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku wuce gaban Allah da Manzonsa....” har zuwa ƙarshen aya ta 2, to akwai Sabitu ɗan Ƙaisu ɗan Shammas wani mutum mai babbar murya, sai ya ce: “Ni ne wanda na kasance ina ɗaga muryata ga Manzon Allah (ﷺ), don haka aikina ya rushe, ni ɗan wuta ne.” Sai ya zauna a gidansa cikin iyalansa cike da baƙin ciki. Da Manzon Allah bai gan shi ba kwana biyu, sai ya tambayi labarinsa, daga nan wasu suka je suka same shi suka faɗa masa cewa Manzon Allah (ﷺ) yana tambayar labarinsa, me ya same shi? Sai ya ce: “Ni ne wanda nake ɗaga muryata a kan muryar Annabi (ﷺ), don haka aikina ya lalace, kuma ni yanzu ɗan wuta ne.” Sai suka dawo suka faɗa wa Manzon Allah (ﷺ) labarinsa da abin da ya faɗa musu, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A’a, shi ɗan Aljanna ne.” Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Sai muka riƙa ganin sa yana yawo a cikinmu alhalin mun san shi ɗan Aljanna ne. Lokacin yaƙin Al-Yamama (watau yaƙi da masu ridda) sai rundunarmu ta ɗan ja da baya, sai ga Sabi’tu ɗan Ƙaisu ya zo sanye da likkafaninsa a jikinsa ya sanya turare yana cewa: “Tir da irin abin da kuke saba wa ‘yan’uwanku.” Sai ya yi ta yaƙi har aka kashe shi.” [Ahmad #12399 da Muslim #119]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi waɗanda suke yin ƙasa-ƙasa da muryoyinsu a gaban Manzon Allah (ﷺ) da cewa su ne waɗanda ya jarrabi zukatansu saboda taƙawa gare shi, ya zaɓe su ya ba su ita, ya kuma tabbatar musu da gafarar zunubansu da kuma lada mai girma a ranar alƙiyama, watau ya shigar da su gidan Aljanna.
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِن وَرَآءِ ٱلۡحُجُرَٰتِ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ
Open ayah 49:4Lalle waɗanda suke kiran ka ta bayan ɗakuna yawancinsu ba su da hankali.
وَلَوۡ أَنَّهُمۡ صَبَرُواْ حَتَّىٰ تَخۡرُجَ إِلَيۡهِمۡ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 49:5Da za su yi haƙuri har sai ka fito wurinsu da ya fiye musu alheri. Allah kuma Mai gafara ne, Mai jin ƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya soki wasu mutanen ƙauye da suke zuwa Madina wurin Manzon Allah (ﷺ) don wata buƙatarsu, sai su samu yana gidansa cikin ɗaya daga ɗakunan matansa, sai su kasa haƙura har sai ya fito, sai su riƙa ƙwala masa kira ta bayan ɗakunan matansa, suna kuma kiran sunansa zalla babu wani ladabi ko girmamawa, sai Allah ya siffanta yawancinsu da cewa ba su da hankali. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, da a ce sun yi haƙuri sun jira har sai ya fito wajensu da ya fi musu alheri, saboda yin haka shi ne girmamawa da nuna ladabi gare shi. Don haka ya ja hankalinsu zuwa ga tuba da neman gafara a kan laifukansu, domin shi mai gafara ne da jin ƙai ga bayinsa masu tuba.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن جَآءَكُمۡ فَاسِقُۢ بِنَبَإٖ فَتَبَيَّنُوٓاْ أَن تُصِيبُواْ قَوۡمَۢا بِجَهَٰلَةٖ فَتُصۡبِحُواْ عَلَىٰ مَا فَعَلۡتُمۡ نَٰدِمِينَ
Open ayah 49:6Ya ku waɗanda suka yi imani, idan wani fasiƙi ya zo muku da wani labari, to ku yi bincike, don kada ku cuci mutane cikin rashin sani, sannan ku wayi gari kuna masu nadama game da abin da kuka aikata.
وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ فِيكُمۡ رَسُولَ ٱللَّهِۚ لَوۡ يُطِيعُكُمۡ فِي كَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ لَعَنِتُّمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِي قُلُوبِكُمۡ وَكَرَّهَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكُفۡرَ وَٱلۡفُسُوقَ وَٱلۡعِصۡيَانَۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّٰشِدُونَ
Open ayah 49:7Kuma ku sani cewa Manzon Allah yana cikinku. Da zai biye muku game da al’amura masu yawa, tabbas da kun wahala, sai dai kuma Allah Ya sa muku son imani Ya kuma ƙawata shi a cikin zukatanku, Ya kuma sa muku ƙin kafirci da fasiƙanci da saɓo. Waɗannan su ne shiryayyu.
فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَنِعۡمَةٗۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Open ayah 49:8(Wannan) falala ce daga Allah da kuma ni’ima, Allah kuwa Masani ne, Mai hikima. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya koyar da bayinsa muminai wata kyakkyawar hanya ta karɓar labarin da aka zo musu da shi da cewa, duk sanda wani fasiƙi ya zo musu da wani labari game da wasu mutane, to su tsaya su yi kyakkyawan bincike game da ingancin labarin ko rashin ingancinsa, kada su yi gaggawar gaskata shi don kada su auka wa wasu mutane a bisa rashin sani, su kuma dawo daga baya suna da-na-sani game da abin da suka aikata na cutar da waɗanda ba su ji ba ba su gani ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gargaɗi sahabban Manzon Allah (ﷺ) inda ya nuna musu cewa, su sani fa Manzon Allah (ﷺ) yana nan cikinsu kuma ana saukar masa da wahayi a kan abubuwan da suke faruwa, don haka su guji yi masa ƙarya, domin duk wanda ya faɗa masa ƙarya, to wahayi zai zo masa ya fallasa shi. Ya kuma tabbatar musu da cewa Manzon Allah (ﷺ) ya fi su sanin abin da zai zame musu maslaha a rayuwarsu da addininsu; da zai biye musu a kan al’amura da dama waɗanda suke nema daga gare shi, to da sun faɗa cikin wahala wadda shi ba zai so ta same su ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana falalar da ya yi musu yayin da ya sanya musu son imani ya ƙawata shi a zukatansu don haka suka yi imani, ya kuma sa musu ƙin kafirci da fasiƙanci da saɓon Allah, don haka suka riƙa guje musu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, masu waɗannan siffofi su ne shiryayyu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa siffantuwarsu da son alheri a zukatansu da ƙin sharri wata falala ce da ni’ima Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu, kuma ya san bayinsa masu gode masa, don haka zai ƙara musu, kuma mai hikima ne domin yana ajiye komai a muhallinsa da ya dace.
وَإِن طَآئِفَتَانِ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱقۡتَتَلُواْ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَهُمَاۖ فَإِنۢ بَغَتۡ إِحۡدَىٰهُمَا عَلَى ٱلۡأُخۡرَىٰ فَقَٰتِلُواْ ٱلَّتِي تَبۡغِي حَتَّىٰ تَفِيٓءَ إِلَىٰٓ أَمۡرِ ٱللَّهِۚ فَإِن فَآءَتۡ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَهُمَا بِٱلۡعَدۡلِ وَأَقۡسِطُوٓاْۖ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُقۡسِطِينَ
Open ayah 49:9Idan kuma wasu ƙungiyoyi biyu na muminai suka yaƙi junansu sai ku yi sulhu a tsakaninsu; to idan ɗayarsu ta yi ta’adda a kan ɗayar, to sai ku yaƙi wadda ta yi ta’addar har sai ta komo zuwa bin umarnin Allah. Idan ta komo sai ku yi sulhu a tsakaninsu bisa adalci, ku kuma yi adalci; lalle Allah Yana son masu adalci.
إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ إِخۡوَةٞ فَأَصۡلِحُواْ بَيۡنَ أَخَوَيۡكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Open ayah 49:10Lalle muminai ‘yan’uwan juna ne, sai ku yi sulhu a tsakanin ‘yan’uwanku. Kuma ku kiyaye dokokin Allah don a ji ƙan ku. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nusantar da muminai yadda za su yi sulhu tsakanin jama’a biyu masu faɗa da juna daga cikinsu, ya umarce su da su yi musu sulhu ta hanyar hukunci da shari’ar Allah a kan abin da suke faɗa game da shi. To amma idan ɗaya jama’ar ta ƙi yarda a yi musu sulhu, ta yi ta’addanci a kan ɗayar, to Allah ya ba wa muminai dama su yaƙi masu ta’addancin har sai sun saduda sun yarda da hukuncin Allah, to idan sun dawo sun yarda a yi musu hukuncin Allah, to muminai sai su yi musu sulhu, ya kuma umarce su da su tabbata sun yi musu adalci, domin lalle Allah yana son masu adalci a cikin hukuncinsu. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ka taimaki ɗan’uwanka yana azzalumi ko wanda aka zalunta.” Anas ya ce: “Ya Manzon Allah, wannan zan iya taimakonsa yayin da aka zalunce shi, to yaya zan taimake shi yana azzalumi?” Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ka hana shi yin zalunci, wannan shi ne taimakonka a gare shi.” [Bukhari #6952]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An ba wa Annabi (ﷺ) shawarar ya je ya haɗu da Abdullahi ɗan Ubayyu (shugaban munafukan Madina) sai Annabi (ﷺ) ya hau jakinsa ya tafi tare da wasu Musulmi, suka wuce ta wata hanya mai taɓo. Lokacin da Manzon Allah (ﷺ) ya iso wajensa sai ya ce masa: “Tafi ka ba ni wuri, Wallahi warin jakinka ya dame ni.” Sai wani mutumin Madina ya ce masa: “Wallahi tabbas jakin Manzon Allah (ﷺ) ya fi ka ƙamshi.” Sai wani mutum ɗan ƙabilar Abdullahi ɗan Ubayyu ya fusata, sai suka shiga zage-zage da wannan mutum, sai ƙabilar kowane daga cikin mutanen nan biyu suka taso a fusace don taimakon ɗan’uwansu, har suka fara doke-doke a tsakaninsu da itatuwan dabino da hannaye da takalma. Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Sai muka samu labari cewa an saukar da wannan ayar ta 9.” [Bukhari #2691]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa muminai cewa su ‘yan’uwan juna ne waɗanda ‘yan’uwantaka ta imani da Musulunci ta haɗa su, don haka ya wajaba su yi sulhu a tsakanin ‘yan’uwansu masu rigima da juna, su kuma kiyaye dokokin Allah don su rabauta da rahamarsa. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne, kada ya zalunce shi kada kuma ya sallama shi. Wanda duk ya taimaka ya biya wa ɗan’uwansa buƙatarsa, to shi ma Allah zai biya masa buƙatarsa, duk kuma wanda ya yaye wa Musulmi wata damuwa, to shi ma Allah zai yaye masa damuwarsa ta ranar alƙiyama. Wanda ya rufa wa Musulmi asiri, shi ma Allah zai rufa masa asiri a ranar alƙiyama.” [Bukhari #2442 da Muslim #2580].
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمٞ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءٞ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Open ayah 49:11Ya ku waɗanda suka yi imani, kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgili, mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri, kuma kada wasu mata (su yi wa) wasu mata (izgili), mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri; kada kuma ku riƙa aibata junanku, kuma kada ku riƙa jifan juna da munanan laƙuba (da kuke ƙi). Tir da sunan fasiƙanci bayan imani. Wanda duk bai tuba ba, to waɗannan su ne azzalumai. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin muminai a kan yadda ya wajaba su yi mu\'amala da junansu, inda ya gargaɗe su a kan cewa kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgili ko ba’a, domin yana yiwuwa waɗanda suke yi wa izgilin su fi su a wurin Allah; hakanan kada wasu mata su riƙa yi wa wasu mata izgili, domin mai yiwuwa ne matan da suke yi wa izgilin su fi su a wurin Allah, saboda babu wanda ya san fifikon da yake tsakanin wani da wani sai shi Allah kaɗai. Sannan ya hana su su riƙa aibata juna, su kuma daina jifan junansu da munanan laƙuba, kamar yadda wasu mutanen Madina suke yi kafin zuwan Manzon Allah (ﷺ). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, duk wanda ya aikata irin wannan to ya zama fasiƙi, kuma tir da siffar fasiƙanci bayan imani. Don haka su gaggauta tuba zuwa ga Allah, wanda kuwa bai tuba ba ya yi watsi da waɗannan ayyuka na saɓon Allah, to yana cikin azzalumai waɗanda suka jefa kansu cikin hallaka.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱجۡتَنِبُواْ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلظَّنِّ إِنَّ بَعۡضَ ٱلظَّنِّ إِثۡمٞۖ وَلَا تَجَسَّسُواْ وَلَا يَغۡتَب بَّعۡضُكُم بَعۡضًاۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمۡ أَن يَأۡكُلَ لَحۡمَ أَخِيهِ مَيۡتٗا فَكَرِهۡتُمُوهُۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٞ رَّحِيمٞ
Open ayah 49:12Ya ku waɗanda suka yi imani, ku nisanci yawancin zace-zace, lalle shashin zace-zace laifi ne; kada kuma ku riƙa binciken laifukan wasu, kuma kada shashinku ya riƙa gibar shashi. Yanzu ɗayanku zai so ya ci naman ɗan’uwansa matacce? To sai kuka ƙi shi. To ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai karɓar tuba ne, Mai jin ƙai. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake kiran muminai da siffarsu ta imani ya hana su aikata wasu miyagun ɗabi’u guda uku: <b>Na ɗaya, </b> su nisanci yawancin zace-zace marasa tushe ko wani ƙwaƙƙwaran dalili, domin wani zaton laifi ne, kamar munana zato ga wanda a zahirinsa mutumin kirki ne. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ina gargaɗin ku da ku bar zato, domin zato ya fi kowane zance zama ƙarya.” [Bukhari #5143, 5144 da Muslim #2563, 2564]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya dubi Ka’aba ya ce: “Maraba da ke Ɗakin Allah, me ya kai girmanki, me ya kai girman alfarmarki, amma lalle mumini ya fi ki alfarma a wurin Allah. Abu ɗaya Allah ya haramta tare da ke, amma abubuwa uku ya haramta tare da mumini: Jininsa da dukiyarsa da yi masa mummunan zato.” [Al-Baihaƙi, Shu’abul Iman #6280 da Al-AlBani As-Sahiha #3420]. <b>Na biyu, </b> su nisance bibiyar laifukan wasu da binciken gano aibinsu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku guji zato, domin zato shi ne zance mafi zama ƙarya, kada ku yi satar sauraro, kada ku binciki laifukan wasu, kada ku yi wa juna hassada, kada kuma ku ƙi juna, kada ku ba wa juna baya, ku zama bayin Allah ‘yan’uwan juna.” [Bukhari #6064 da Muslim #6563]. An karɓo daga Mu’awiya (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle kai idan ka riƙa binciken laifukan mutane to ka lalata su, ko ka yi kusa ka lalata su.” [Abu Dawud #4888 da Ibn Hibban #5760]. <b>Na uku, </b> su guji yi wa junansu giba, watau ɓata mutum a bayan idonsa, har ma saboda muninsa Allah ya siffanta shi da cewa ya yi daidai da mutum ya ci naman ɗan’uwansa bayan ya mutu, wanda kuwa hakan abin ƙyama ne a wurinsa, don haka su ƙyamaci yi da mutane a bayan idonsu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa, mene ne giba? Sai ya ce: “Ka ambaci ɗan’uwanka da abin da yake ƙi?” Sai aka ce masa: “To idan abin da na faɗa game da ɗan’uwana yana da shi fa?” Sai ya ce: “Idan yana da abin da ka faɗa a kansa, to ka yi masa giba, idan kuma ba ya da shi, to ka yi masa ƙage.” [Muslim #2589 da Abu Dawud #4874]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lokacin da aka yi tafiya da ni zuwa sama na wuce ta gaban wasu mutane masu zaƙo-zaƙon farata na tagulla suna kartar fuskokinsu da ƙirazansu, sai na ce: “Su wane ne waɗannan ya Jibrilu?” Sai ya ce: “Waɗannan su ne waɗanda suke cin naman mutane (watau suke gulmar su bayan idonsu) suke auka wa mutuncinsu.” [Ahmad #13340 da Abu Dawud #4878]. Sannan Allah ya umarci muminai da su kiyaye dokokinsa, su aikata abin da ya umarce su, su guji abin da ya hana su, ya kuma tabbatar musu da cewa shi mai karɓar tuban bayinsa ne, mai rahama gare su.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن ذَكَرٖ وَأُنثَىٰ وَجَعَلۡنَٰكُمۡ شُعُوبٗا وَقَبَآئِلَ لِتَعَارَفُوٓاْۚ إِنَّ أَكۡرَمَكُمۡ عِندَ ٱللَّهِ أَتۡقَىٰكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٞ
Open ayah 49:13Ya ku mutane, lalle Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, Muka kuma sanya ku al’ummu da ƙabilu don ku san juna. Lalle mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku taƙawa. Lalle Allah Masanin sarari ne, Masanin ɓoye. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira mutane gaba ɗayansu ya kuma bayyana musu matsayinsu a wurinsa da kuma dangantakarsu da junansu, inda ya tabbatar musu da cewa shi ne ya halicce su daga namiji ɗaya da mace ɗaya, watau Adamu da Hauwa’u, don haka dukkansu asalinsu guda ne, saboda haka babu dalilin da zai sa wani ya yi wa wani alfahari da asali. Sannan kuma ya nufe su da zama al’ummu daban-daban da ƙabilu masu yawa a wurare daban-daban, don su san junansu, ba don su yi wa juna alfahari ba, domin fifiko ba ya samuwa sai da taƙawa, don haka ya tabbatar musu da cewa mafi girmansu a wurinsa shi ne wanda ya fi taƙawa, watau kiyaye dokokinsa. Sannan ya bayyana cewa, lalle shi masanin halin kowa ne, ya san wanda yake kammalalle da wanda ba kammalalle ba daga cikinku. An karɓo daga Uƙbatu ɗan Amir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lalle asalin kowane daga cikinku ba abin aibatawa ba ne, dukkanku ‘ya’yan Adamu ne, tsarekun juna ne, babu wanda ya fi wani falala sai da addini da taƙawa. Allah ba zai tambaye ku game da asalinku ko nasabarku a ranar alƙiyama ba, wanda ya fi ku girma a wurin Allah shi ne wanda ya fi taƙawa.” [Ahmad #17446]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Annabi (ﷺ) wane ne ya fi girma a cikin mutane? Sai ya ce: “Wanda ya fi su girma a wurin Allah shi ne wanda ya fi su taƙawa....” [Bukhari #3353 da Muslim #2378].
۞قَالَتِ ٱلۡأَعۡرَابُ ءَامَنَّاۖ قُل لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ وَلَٰكِن قُولُوٓاْ أَسۡلَمۡنَا وَلَمَّا يَدۡخُلِ ٱلۡإِيمَٰنُ فِي قُلُوبِكُمۡۖ وَإِن تُطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَا يَلِتۡكُم مِّنۡ أَعۡمَٰلِكُمۡ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Open ayah 49:14(Larabawa) ƙauyawa suka ce: “Mun yi imani.” Ka ce: “Ba ku yi imani ba, sai dai ku ce ‘mun musulunta’, don kuwa imani bai riga ya shiga zukatanku ba; idan kuwa kuka bi Allah da Manzonsa, to ba zai tauye muku wani abu daga (ladan) ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama.”
إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ لَمۡ يَرۡتَابُواْ وَجَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّٰدِقُونَ
Open ayah 49:15Muminai kawai su ne waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, sannan ba su yi kokwanto ba, suka kuma yi yaƙi da dukiyoyinsu da rayukansu a hanyar Allah, Waɗannan su ne masu gaskiya.
قُلۡ أَتُعَلِّمُونَ ٱللَّهَ بِدِينِكُمۡ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ
Open ayah 49:16Ka ce: “Yanzu kwa riƙa sanar da Allah addininku, alhali kuwa Allah Yana sane da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa? Allah kuwa Masanin komai ne.”
يَمُنُّونَ عَلَيۡكَ أَنۡ أَسۡلَمُواْۖ قُل لَّا تَمُنُّواْ عَلَيَّ إِسۡلَٰمَكُمۖ بَلِ ٱللَّهُ يَمُنُّ عَلَيۡكُمۡ أَنۡ هَدَىٰكُمۡ لِلۡإِيمَٰنِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Open ayah 49:17Suna yi maka gorin sun musulunta; ka ce: “Kada ku yi min gorin musuluntarku; a’a, Allah ne ma zai yi muku gori don Ya shiryar da ku zuwa ga imani, idan kun kasance masu gaskiya.”
إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ غَيۡبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Open ayah 49:18Lalle Allah Yana sane da abin da yake ɓoye a sammai da ƙasa, Allah kuma Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. A waɗannan ayoyi na ƙarshen Sura Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayani ne a kan wasu Larabawan ƙauye waɗanda suka shiga addinin Musulunci ba tare da cikakkiyar fahimtarsa ba, ba su kuma tsaya sun yi aiki da abin da imani yakan hukunta ba, to amma duk da wannan sai suka riƙa cika baki suna tinƙaho cewa ai su sun yi imani da Allah da Manzonsa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya faɗa musu cewa ba su yi imani cikakke ba, don haka su daina kai kansu matsayin da ba su kai ba, su kuma daina cika baki; su dai kawai su ce sun musulunta, watau sun miƙa wuya, su tsaya iya nan, domin kuwa imani bai riga ya ratsa zukatansu ba, amma duk da haka ana sa ran nan gaba imani ya ratsa zukatan nasu, su zama cikakkun muminai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu abin da za su yi imani ya ratsa su, watau su bi Allah da Manzonsa wajen kyautata imaninsu da ayyukansu da nisantar abubuwan da aka haramta musu. Idan har sun aikata haka, to Allah ba zai rage musu komai daga ladan ayyukansu ba, zai ba su sakamakonsu cikakke. Allah kuma mai gafara ne ga duk wanda ya tuba ya gyara aikinsa, kuma mai rahama ne ga bayinsa. An karɓo daga Sa’adu ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wasu jama’a sun zo wurin Annabi (ﷺ), sai ya ba su kyauta ya bar mutum ɗaya bai ba shi ba, sai Sa’ad ya ce: “Ya Manzon Allah, ka ba su kyauta dukkansu ka bar wane ba ka ba shi ba, Wallahi ina ganin sa mumini ne.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ko dai Musulmi.” Ya faɗi haka sau uku. [Bukhari #1478 da Musulmi #150]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana waɗanda suke muminai na gaskiya, waɗanda za su iya buɗa baki su ce su muminai ne, da cewa su ne waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa sannan ba su yi wani kokwanto game da imaninsu ba, suka kuma yi jihadi da dukiyoyinsu da kawunansu don Allah, lalle masu irin waɗannan siffofi su ne masu gaskiya game da imaninsu. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake umartar Manzonsa (ﷺ) da ya ja kunnen waɗannan Larabawa na ƙauye ya nuna musu cewa, ta yaya har za su riƙa cewa su ne za su sanar da Allah addininsu, alhalin Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya buƙatar haka daga gare su, domin masanin duk abin da yake cikin sammai da abin da yake ƙasa ne, ya san halin da kowa yake ciki ba sai sun faɗa masa ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa su waɗannan ƙauyawa, saboda rashin fahimtar addini ne ya sa har suna goranta masa cewa sun musulunta ba tare da ya sha wahalar yaƙar su ba. To sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya mayar musu da martani cewa, kada su yi masa gorin musuluntarsu, domin su ne za su ci moriyar Musuluncin, kuma gaskiyar lamari ma ita ce, Allah ne zai goranta musu yayin da ya ba su damar su musulunta, idan har da gaske suke da’awar cewa sun karɓi Musulunci. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu faffaɗan iliminsa, da cewa shi ne yake sane da ɗaukacin abin da yake ɓoye a sammai da abin da yake ɓoye a ƙasa, babu abin da zai ɓuya gare shi, kuma Allah yana ganin abin da suke aikatawa, zai kuma yi musu sakayya a kai.