ق

Qaaf

The letter Qaaf · Surah 50 · Ayahs: 45 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. قٓۚ وَٱلۡقُرۡءَانِ ٱلۡمَجِيدِ

    Open ayah 50:1

    Ƙaf. Na rantse da Alƙur’ani mai girma.

  2. بَلۡ عَجِبُوٓاْ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٞ مِّنۡهُمۡ فَقَالَ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا شَيۡءٌ عَجِيبٌ

    Open ayah 50:2

    A’a, sun dai yi mamakin cewa, wani mai gargaɗi daga cikinsu ya zo musu, sai kafirai suka ce: “Wannan abu ne mai ban mamaki!

  3. أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗاۖ ذَٰلِكَ رَجۡعُۢ بَعِيدٞ

    Open ayah 50:3

    “Yanzu idan muka mutu muka zama ƙasa, (a ce za a komo da mu)? Wannan komowa ce mai nisa!”

  4. قَدۡ عَلِمۡنَا مَا تَنقُصُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۡهُمۡۖ وَعِندَنَا كِتَٰبٌ حَفِيظُۢ

    Open ayah 50:4

    Haƙiƙa Mun san abin da ƙasa take cinyewa daga gare su; a wurinmu kuma akwai wani littafi mai kiyayewa.

  5. بَلۡ كَذَّبُواْ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ فَهُمۡ فِيٓ أَمۡرٖ مَّرِيجٍ

    Open ayah 50:5

    A’a, sun dai ƙaryata gaskiya ne lokacin da ta zo musu, don haka suna cikin al’amari rikitacce. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da harafin ‘Ƙaf’ kamar yadda ya buɗe wasu surori da haruffa irin waɗannan. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara don ƙarin bayani]. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da Alƙur’ani mai girma saboda ɗimbin ma’anonin da ya ƙunsa da yawan alheri da albarka da ke tattare da shi, domin ya tabbatar da cewa, lalle za a tashi halittu bayan sun mutu a ranar alƙiyama don yi musu hisabi da sakamako wanda kafirai suke ƙaryata faruwarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin da ya sanya mushirikai suke ƙaryata Manzonsa (ﷺ) da cewa, ba wani abu ya haifar musu da haka ba sai don kawai suna mamakin wai ta yaya wani manzo irin jinsinsu na mutane zai zo yana yi musu wa’azi, watau me ya hana a aiko musu da mala’ika? Suna ganin lalle wannan abu ya cika abin mamaki ainun. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilinsu na ƙaryata tashi bayan mutuwa, watau suna mamakin wai yanzu idan sun mutu sun zama ƙasa, a ce za a sake dawo musu da ransu? Suna ganin lalle wannan abu ya yi nisa ƙwarai da tunaninsu, don haka ba za su yi imani da shi ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani da cewa, lalle shi ya san abin da ƙasa take cinyewa daga jikinsu bayan sun mutu an binne su a ƙaburburansu, kuma ba wani abin da bai sani ba game da su, domin a wajensa akwai littafin Lauhul Mahfuz wanda yake kiyaye duk wani abu da ya ƙaddara musu a rayuwarsu da bayan mutuwarsu. Watau wanda yake da wannan cikakken ilimi mai kewaye da sanin komai ta yaya za a yi mamakin cewa zai iya tayar da matacce bayan ya rududduge ya zama ƙasa? Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, su waɗannan mushirikan sun ƙaryata Alƙur’ani mai girma wanda Manzon Allah (ﷺ) ya zo musu da shi, don haka suka faɗa cikin wani al’amari mai rikitarwa, domin sun kasa tsayar da magana ɗaya game da Manzon Allah (ﷺ), wani lokaci su ce matsafi ne, wani lokaci kuma su ce boka ne, wani lokaci kuma su ce mawaƙi, da maganganu marasa kan gado irin waɗannan.

  6. أَفَلَمۡ يَنظُرُوٓاْ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَوۡقَهُمۡ كَيۡفَ بَنَيۡنَٰهَا وَزَيَّنَّٰهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٖ

    Open ayah 50:6

    Yanzu ba sa duban sama da take sama da su (su ga) yadda Muka gina ta, Muka kuma ƙawata ta, ba ta kuma da wasu tsage-tsage?

  7. وَٱلۡأَرۡضَ مَدَدۡنَٰهَا وَأَلۡقَيۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ

    Open ayah 50:7

    Ƙasa kuma Muka shimfiɗa ta, Muka kuma sanya turaku a cikinta, Muka kuma tsirar da kowane irin nau’in (tsiro) mai ƙayatarwa a cikinta.

  8. تَبۡصِرَةٗ وَذِكۡرَىٰ لِكُلِّ عَبۡدٖ مُّنِيبٖ

    Open ayah 50:8

    Don jan hankali da wa’azantarwa ga duk wani bawa mai mayar da al\'amarinsa ga Allah.

  9. وَنَزَّلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ مُّبَٰرَكٗا فَأَنۢبَتۡنَا بِهِۦ جَنَّٰتٖ وَحَبَّ ٱلۡحَصِيدِ

    Open ayah 50:9

    Muka kuma saukar da ruwa mai albarka daga sama sai Muka tsiro da lambuna da shi da kuma ƙwayoyin da ake girba.

  10. وَٱلنَّخۡلَ بَاسِقَٰتٖ لَّهَا طَلۡعٞ نَّضِيدٞ 

    Open ayah 50:10

    Da kuma itatuwan dabinai dogwaye da suke da ‘ya’ya dodo-dodo.

  11. رِّزۡقٗا لِّلۡعِبَادِۖ وَأَحۡيَيۡنَا بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗاۚ كَذَٰلِكَ ٱلۡخُرُوجُ

    Open ayah 50:11

    Don arzuta bayi, Muka kuma raya busasshen gari da shi. Kamar haka ne fitowa (daga ƙabari) take. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin mushirikai masu ƙaryata tashi bayan mutuwa da cewa, me ya hana su dubi wasu ƙwararan hujjoji a sama da ƙasa waɗanda suke tabbatar da cikar Ƙudurar Allah a kan raya matattu? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci guda biyar daga cikin waɗannan hujjojin: <b>Na ɗaya </b>, su ɗaga kai su dubi yadda ya gina sama ya kuma ƙawata ta da taurari masu haske, sannan ya haɗe ta tamau ba tare da wata tsaga da mutum zai iya gani a tare da ita ba. Duk wanda zai yi irin wannan babban aiki to lalle zai iya tayar da matattu. <b>Na biyu </b>, su kuma dubi ƙasa su ga yadda ya shimfiɗa ta har ta dace da rayuwar mutane da dabbobi a kanta cikin walwala da natsuwa. <b>Na uku </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kakkafa manyan duwatsu a cikin ƙasa don su hana ta yin tangal-tangal da abin da yake bayanta. <b>Na huɗu </b>, sannan su dubi yadda Allah ya fitar da tsirrai da bishiyoyi masu kyan gani daga cikin ƙasa, domin ‘yan’adam da dabbobinsu su sami abinci. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya yi waɗannan halittu duka domin su zamanto wa’azi da tunatarwa ga duk wani bawa mai komawa zuwa ga Allah da yi masa bauta da ɗa’a. <b>Na biyar </b>, Ubangiji ya saukar da ruwa daga sama mai cike da amfani da alheri, wanda da shi ya fitar da lambuna masu ban sha’awa da kuma ƙwayoyi da ake girbe su kamar alkama da masara da makamantansu. Har ila yau da wannan ruwan sama ne ya fitar da dogayen bishiyoyin dabino masu ‘ya’ya dodo-dodo wasu kan wasu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ya yi duk waɗannan abubuwa ne don su zama arziki ga bayinsa, su ci su kuma ciyar da dabbobinsu. Kuma da wannan ruwan yake raya ƙasa wadda fari ya kashe ta, sai ta sake komawa koriya shar cike da kayan amfanin gona da tsirrai iri-iri. To kamar haka ne Allah yake raya matattu su fito daga ƙaburburansu kamar yadda ya fara halittar su da farko.

  12. كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَأَصۡحَٰبُ ٱلرَّسِّ وَثَمُودُ

    Open ayah 50:12

    Mutanen Nuhu da ma’abota rijiyar Rassu da Samudawa (duka) sun ƙaryata (annabawa) a gabaninsu (watau mutanen Makka).

  13. وَعَادٞ وَفِرۡعَوۡنُ وَإِخۡوَٰنُ لُوطٖ

    Open ayah 50:13

    Da kuma Adawa da Fir’auna da ‘yan’uwan Luɗu (su ma sun ƙaryata).

  14. وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡأَيۡكَةِ وَقَوۡمُ تُبَّعٖۚ كُلّٞ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ

    Open ayah 50:14

    Da kuma ma’abota surƙuƙi da mutanen Tubba’u. Kowannensu ya ƙaryata manzanni, sai azabata ta tabbata (a kansu).

  15. أَفَعَيِينَا بِٱلۡخَلۡقِ ٱلۡأَوَّلِۚ بَلۡ هُمۡ فِي لَبۡسٖ مِّنۡ خَلۡقٖ جَدِيدٖ

    Open ayah 50:15

    Shin Mun gaza ne da halittar farko? A’a, su dai suna cikin shakka ne game da sake halitta. </b>A waɗannan ayoyin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa (ﷺ) cewa, a baya can kafin mushirikan Larabawa an samu al’ummu da dama waɗanda suka ƙaryata annabawan da ya aika musu, kamar yadda mushirikan suka ƙaryata shi, don haka ya hallaka su. Wannan jan kunne ne ga mushirkan Larabawa da su guji faɗawa cikin irin abin da waɗancan al’ummu suka faɗa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci cewa mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙaryata shi. Hakanan ma’abota rijiyar ‘Rassu’ su ma sun ƙaryata annabinsu. Samudawa mutanen Annabi Salihu su ma sun ƙaryata shi. Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ƙaryata shi. Fir’auna da mutanensa waɗanda su kuma suka ƙaryata annabawan Allah watau Musa da Haruna, kamar yadda mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka ƙaryata shi. Ban da waɗannan kuma akwai ma’abota surƙuƙi, watau mutanen Annabi Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) su ma sun ƙaryata Manzon Allah Shu’aibu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sannan da mutanen Tubba’u Sarkin Yaman, su ma sun ƙaryata annabin da Allah ya aika musu. Daga nan dukkansu uƙubar da Allah ya yi musu alƙawarin za ta same su idan sun ƙi yin imani ta tabbata a kansu, Allah ya hallaka su bai bar ko mutum ɗaya ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kafa musu hujja a kan abin da suke ƙaryatawa na tashi bayan mutuwa da cewa, shi ne fa wanda ya halicce su da farko ba tare da ya gaza ba, to ta yaya kuma za a ce ba zai iya sake dawo da halittarsu ba a karo na biyu? Su sun san haka kamar yadda suka san cewa yin halittar farko ta fi sake maimaita ta zama abin mamaki, sai dai kawai su mutane ne da shakku ya riga ya mamaye musu zukata ya hana su karɓar gaskiya da aiki da hankali.

  16. وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ وَنَعۡلَمُ مَا تُوَسۡوِسُ بِهِۦ نَفۡسُهُۥۖ وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنۡ حَبۡلِ ٱلۡوَرِيدِ

    Open ayah 50:16

    Haƙiƙa kuma Mun halicci mutum, kuma Mun san abin da ransa yake saƙa masa; kuma Mu Muka fi kusa da shi fiye da jijiyar wuyansa.

  17. إِذۡ يَتَلَقَّى ٱلۡمُتَلَقِّيَانِ عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ قَعِيدٞ

    Open ayah 50:17

    Yayin da (mala’iku biyu) masu haɗuwa suka haɗu ta dama da ta hagu suna zaune.

  18. مَّا يَلۡفِظُ مِن قَوۡلٍ إِلَّا لَدَيۡهِ رَقِيبٌ عَتِيدٞ

    Open ayah 50:18

    Ba wata magana da zai furta face a tare da shi akwai (mala\'ika) mai kula kuma halartacce.

  19. وَجَآءَتۡ سَكۡرَةُ ٱلۡمَوۡتِ بِٱلۡحَقِّۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنۡهُ تَحِيدُ

    Open ayah 50:19

    Kuma magagin mutuwa ya zo da gaskiya; wannan ne abin da ka kasance kana kakkauce wa.

  20. وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِۚ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡوَعِيدِ 

    Open ayah 50:20

    Aka kuma yi busa a ƙaho. Wannan ita ce ranar narko.

  21. وَجَآءَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّعَهَا سَآئِقٞ وَشَهِيدٞ

    Open ayah 50:21

    Kuma kowane rai ya zo a tare da shi akwai mai kora da mai shaida.

  22. لَّقَدۡ كُنتَ فِي غَفۡلَةٖ مِّنۡ هَٰذَا فَكَشَفۡنَا عَنكَ غِطَآءَكَ فَبَصَرُكَ ٱلۡيَوۡمَ حَدِيدٞ

    Open ayah 50:22

    Haƙiƙa ka kasance a cikin gafala game da wannan, sai Muka yaye maka yanarka, to ganinka a yau tangaran yake. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cikakken iliminsa game da ɗan’adam, domin shi ne Mahaliccinsa wanda ya halicci jinsinsa namiji da mace, don haka ya san komai nasa; ya san duk abubuwan da yake ƙullawa a ransa, domin shi Allah ya fi kusa da ɗan’adam fiye da jijiyar wuyansa wadda take haɗe da zuciyarsa, yayin da mala’iku biyu suke karɓar ayyukan da yake aikatawa suna rubutawa; ɗayansu a dama yana rubuta kyawawan ayyukansa; ɗayansu kuma a hagu yana rubuta munanan ayyukansa; kowannensu yana tsaye a kan aikinsa ba ya sakaci ko kaɗan; domin babu wata magana da mutum zai furta face a tare da shi akwai mala’ika yana kula da abin da yake faɗa yana kuma rubutawa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana lokacin da wa’adin ɗan’adam zai cika, mutuwa ta zo masa da tsananin magaginta da gaskiyar da babu mai iya guje mata, a nan ne za a tabbatar masa cewa wannan shi ne abin da ya kasance tsawon rayuwarsa yana kakkauce masa. To daga nan fa ƙaramar alƙiyamar mutum ta tsaya. Sai kuma lokacin da wa’adin tashin alƙiyama zai zo, to a lokacin Mala’ika Israfilu ne zai yi busa a ƙaho busa ta biyu, to wannan ita ce ranar alƙiyama, ranar narko ga kafirai da masu saɓon Allah. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wannan ranar kowane mahaluƙi zai zo tare da mala’ika yana kore da shi da kuma wani mala’ika mai bayar da shaida a kan dukkan ayyukansa masu kyau da munana. To a nan ne za a gaya wa duk wanda yake ƙaryata tashin alƙiyama cewa, tun a duniya yana cikin gafala game da wannan ranar, son zuciya da sha’awa da ruɗun Shaiɗan sun rufe masa ido, to yau ga shi an yaye masa dukkan gafalarsa, idonsa ya buɗe yana gani tangararan; yana ganin azabar Allah a fili, baƙin ciki ya rufe masa zuciya.

  23. وَقَالَ قَرِينُهُۥ هَٰذَا مَا لَدَيَّ عَتِيدٌ

    Open ayah 50:23

    Mala’ikan da yake tare da shi kuma ya ce: “Wannan shi ne abin da yake hallare a tare da ni.”

  24. أَلۡقِيَا فِي جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٖ

    Open ayah 50:24

    (Aka ce da mala’ikun): “Ku jefa duk wani kafiri mai taurin kai cikin Jahannama.

  25. مَّنَّاعٖ لِّلۡخَيۡرِ مُعۡتَدٖ مُّرِيبٍ

    Open ayah 50:25

    “Mai yawan hana alheri, mai ta’addanci, mai shakka.

  26. ٱلَّذِي جَعَلَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَأَلۡقِيَاهُ فِي ٱلۡعَذَابِ ٱلشَّدِيدِ

    Open ayah 50:26

    “Wanda ya sanya wani abin bauta daban tare da Allah, saboda haka ku jefa shi cikin azaba mai tsanani.”

  27. ۞قَالَ قَرِينُهُۥ رَبَّنَا مَآ أَطۡغَيۡتُهُۥ وَلَٰكِن كَانَ فِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٖ

    Open ayah 50:27

    Shaiɗaninsa ya ce: “Ya Ubangijina, ni ban ɓatar da shi ba, sai dai kawai ya kasance cikin ɓata mai nisa.”

  28. قَالَ لَا تَخۡتَصِمُواْ لَدَيَّ وَقَدۡ قَدَّمۡتُ إِلَيۡكُم بِٱلۡوَعِيدِ

    Open ayah 50:28

    (Allah) ya ce: “Kada ku yi husuma a gabana, haƙiƙa tuni Na gabatar muku da gargaɗin azaba.

  29. مَا يُبَدَّلُ ٱلۡقَوۡلُ لَدَيَّ وَمَآ أَنَا۠ بِظَلَّٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ

    Open ayah 50:29

    “Ba a sauya magana a gabana, kuma Ni ba mai zaluntar bayi ba ne.”

  30. يَوۡمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمۡتَلَأۡتِ وَتَقُولُ هَلۡ مِن مَّزِيدٖ 

    Open ayah 50:30

    A ranar da za Mu ce da Jahannama: “Shin kin cika?” (Ita) kuma ta ce: “Shin akwai wani ƙari?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a ranar alƙiyama mala’ika da ke tare da kafiri wanda aka wakilta shi ya kula da ayyukan wannan kafirin ya rubuta komai nasa, zai zo da duk abin da ya tattara na ayyukansa ya shaida wa Ubangiji cewa, ga abin da yake tare da shi a rubuce na dukkan ayyukansu. A nan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) zai umarci mala’ikun nan guda biyu, watau wanda ya kora kafiri da wanda ya bayar da shaida a kansa da cewa, su jefa duk wani kafiri mai taurin kai cikin wutar Jahannama, saboda kafircinsa da yawan saɓon Allah da yake yi, ga shi kuma mai hana duk wani alheri da ƙetare iyakokin Mahaliccinsa da rungumar wani abin bauta yana bauta masa tare da Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a nan ne shi kafirin zai nemi ya kawo wani hanzari na kauce wa hanyar Allah da cewa, shaiɗaninsa ne ya hallaka shi ya ɓatar da shi. Sai shi kuma shaiɗanin nasa ya musunta hakan, ya tabbatar wa da Ubangiji cewa, ba shi ne ya ɓatar da shi ba; da ma can ya kasance cikin ɓata mai nisa, watau yayin da ya haɗu da shaiɗaninsa za-mu ce ta tadda mu-je-mu. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, bayan husuma ta kaure tsakanin kafiri da shaiɗaninsa, sai ya daka musu tsawa cewa, su daina wata husuma da jayayya a gabansa, wadda ba ta da wani amfani, domin kuwa tun a duniya ya aika musu da manzanninsa da narkon azaba ga duk wanda ya kafirce masa ya bijire wa umarninsa. Ya kuma tabbatar musu da cewa, shi ba a sauya magana a wurinsa, kuma ba ya saɓa alƙawarinsa, ba kuma ya zaluntar bayinsa ko ya tauye musu kyawawan ayyukansu ko ya ƙara musu laifukan da ba nasu ba; yana dai yi wa kowa sakayya ne da irin aikinsa mai kyau da mummuna. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da bayinsa azabar wutar Jahannama wadda za a yi ta jibga kafirai da masu saɓon Allah cikinta dodo-dodo har a tambaye ta cewa ko ta cika? Ita kuma sai ta nuna cewa akwai sauran wuri a cikinta, idan akwai ƙari to a ƙaro mata. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Jahannama ba za ta gushe ba ana ta jefa ‘yan wuta a cikinta ita kuma tana cewa, shin akwai ƙari ne? Har sai Ubangiji Mai buwaya ya sanya duddugensa a cikinta sai sashenta ya tattaru ya haɗe da sashi tana cewa: “Ya isa haka, ya isa haka, na rantse da Buwayarka da girmanka. Ita kuma Aljanna ba za ta gushe da rarar wuri a cikinta ba, har sai Allah ya ƙagi wasu halittu daban waɗanda zai shigar da su rarar Aljanna.” [Muslim #2848].

  31. وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ غَيۡرَ بَعِيدٍ

    Open ayah 50:31

    Aka kuma kusantar da Aljanna ga masu tsoron Allah, ba tare da nisa ba.

  32. هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٖ

    Open ayah 50:32

    (Sai a ce da su): “Wannan ne abin da ake yi muku alƙawarinsa, (ga shi nan a tanade) ga duk wani mai yawan komawa ga Allah, mai kiyaye (dokokinsa).

  33. مَّنۡ خَشِيَ ٱلرَّحۡمَٰنَ بِٱلۡغَيۡبِ وَجَآءَ بِقَلۡبٖ مُّنِيبٍ

    Open ayah 50:33

    “Wanda ya ji tsoron Allah a ɓoye, ya zo kuma da zuciya mai komawa ga Allah.”

  34. ٱدۡخُلُوهَا بِسَلَٰمٖۖ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡخُلُودِ

    Open ayah 50:34

    (Za a ce da su): Ku shige ta da aminci; wannan ita ce ranar dawwama.

  35. لَهُم مَّا يَشَآءُونَ فِيهَا وَلَدَيۡنَا مَزِيدٞ

    Open ayah 50:35

    Suna da duk abin da suka dama a cikinta, kuma wurinmu akwai wani ƙari. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa bayinsa albishir ne da sakamakon gidan Aljanna ranar alƙiyama yayin da za a kusanto ta gare su saboda taƙawarsu da kiyayewarsu ga dokokin Allah, inda za su ga ɗimbin ni’imomin da ke cikinta waɗanda idanuwansu ba su taɓa gani ba, kunnuwansu ba su taɓa jin labarinsu ba, kuma ba su taɓa tunanin irinsu ba. A nan ne za a tarye su ana yi musu maraba da zuwa, ana kuma sanar da su cewa wannan tagomashi da suke gani shi ne gidan Aljanna da aka yi alƙawarinsa ga duk wani bawa mai yawan komawa ga Allah mai biyayya da tuba gare shi, mai kiyaye dokokinsa. Wanda ya ji tsoron Allah a ɓoye inda babu mai ganin sa sai Allah, ya kuma sadu da Allah yana mai lafiyayyar zuciya, mai komawa gare shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, za a ce wa ‘yan Aljanna su shige ta cikin aminci ba tare da sun haɗu da wani abu mai sosa zuciya ba, a kuma tabbatar musu da cewa wannan rana ita ce ranar dawwama, babu mutuwa a cikinta har abada. Sannan a nuna musu cewa, duk ni’imomin gidan Aljanna nasu ne su yi yadda suke so kuma duk abin da ransu yake so na ni’ima za a ba su har ma da ƙarin wasu ni’imomin waɗanda ba su san da su ba; daga cikinsu akwai ganin Fuskar Ubangijinsu da samun yardarsa ta har abada.

  36. وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّن قَرۡنٍ هُمۡ أَشَدُّ مِنۡهُم بَطۡشٗا فَنَقَّبُواْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ هَلۡ مِن مَّحِيصٍ

    Open ayah 50:36

    Al’ummu nawa Muka hallaka a gabaninsu waɗanda suka fi su tsananin ƙarfi, sai suka riƙa bincike cikin garuruwa ko akwai wata matsera.

  37. إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَذِكۡرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُۥ قَلۡبٌ أَوۡ أَلۡقَى ٱلسَّمۡعَ وَهُوَ شَهِيدٞ

    Open ayah 50:37

    Lalle game da wannan tabbas akwai wa’azi ga wanda ya kasance yana da hankali ko kuma ya karkaɗe kunne (don sauraron wa’azi), alhali zuciyarsa tana tare da shi.

  38. وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٖ

    Open ayah 50:38

    Haƙiƙa kuma Mun halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida, kuma wata gajiya ba ta shafe mu ba.

  39. فَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ قَبۡلَ طُلُوعِ ٱلشَّمۡسِ وَقَبۡلَ ٱلۡغُرُوبِ

    Open ayah 50:39

    To ka yi haƙuri a kan abin da suke faɗa, ka kuma yi tasbihi da yabon Ubangijinka kafin fudowar rana da kuma kafin faɗuwarta.

  40. وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡهُ وَأَدۡبَٰرَ ٱلسُّجُودِ 

    Open ayah 50:40

    Da daddare kuma sai ka tsarkake shi, da kuma bayan salloli. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da mushirikai azabarsa, ya tabbatar musu cewa, ya hallaka al’ummu da dama waɗanda sun fi su tsananin ƙarfi nesa ba kusa ba, amma yayin da azabar Allah ta zo musu sun yi ta ƙoƙarin neman garuruwan da za su gudu su tsere mata amma hakan bai samu ba har sai da azabar Allah ta cim musu ta kuma hallaka su gaba ɗaya, don haka su ma ba za su iya tsere wa azabarsa ba yayin da ta zo musu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalinsu da cewa, lalle idan sun yi la’akari da abin da ya faru ga kafiran da suka gabace su za su ga akwai wa’azi da izina mai tarin yawa, sai dai ba kowa ne zai gane haka ba sai wanda yake yana da hankali ko kuma ya karkaɗe kunnensa ya yi sauraro na nutsuwa yayin da zuciyarsa tana tare da shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu girman Ƙudurarsa da cikar ikonsa, domin shi ne wanda ya halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu a cikin kwana shida, watau ya fara ranar Lahadi ya gama ranar Juma’a, duk kuwa da cewa yana iya halittar su a cikin ƙasa da ƙiftawar ido da ya so yin hakan. Kuma ya yi duk wannan aikin ne ba tare da wata gajiya ta same shi ba, kamar yadda Yahudawa suke riyawa don ƙarya da kafirci. Sai kuma ya lallashi Manzonsa (ﷺ) wanda yake ta damuwa game da munanan maganganu da mushirikai suke faɗa masa da bijirewar da suke yi masa. Ya umarce shi da ya yi haƙuri, ya mayar da hankalinsa wajen bautar Allah ya riƙa yi masa tasbihi tare da gode masa a sallarsa ta asuba kafin hudowar rana da kuma sallarsa ta la’asar kafin faɗuwar rana. Hakanan ya tsarkake shi da tasbihi a sallarsa ta dare, watau magariba da isha’i, ya kuma yi ta yi masa tasbihi bayan salloli. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya yi tasbihi talatin da uku bayan kowace salla, ya yi kabbara talatin da uku, ya kuma yi hamdala talatin da uku dukansu gaba ɗaya tis’in da tara ke nan, sannan cikon na ɗari ya ce: ‘La Ilaha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu Lahul Mulku Wa lahul Hamdu Wa Huwa Ala Kulli Shai’in Ƙadir’ , to za a gafarta masa laifukansa ko da sun kai misalin kumfar kogi.” [Muslim #597].

  41. وَٱسۡتَمِعۡ يَوۡمَ يُنَادِ ٱلۡمُنَادِ مِن مَّكَانٖ قَرِيبٖ

    Open ayah 50:41

    Ka kuma saurara ranar da mai kira zai yi kira daga wani wuri makusanci.

  42. يَوۡمَ يَسۡمَعُونَ ٱلصَّيۡحَةَ بِٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلۡخُرُوجِ

    Open ayah 50:42

    A ranar da (talikai) za su ji tsawa ta gaskiya. Wannan ita ce ranar fitowa (daga ƙabari).

  43. إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيۡنَا ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 50:43

    Lalle Mu ne Muke rayawa, Muke kuma kashewa, kuma makoma zuwa gare Mu ne.

  44. يَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلۡأَرۡضُ عَنۡهُمۡ سِرَاعٗاۚ ذَٰلِكَ حَشۡرٌ عَلَيۡنَا يَسِيرٞ

    Open ayah 50:44

    A ranar da ƙasa za ta tsattsage musu (su fito) da gaggawa. Wannan tattarawa ce mai sauƙi a gare Mu.

  45. نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَقُولُونَۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِجَبَّارٖۖ فَذَكِّرۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ

    Open ayah 50:45

    Mu ne Muka fi sanin abin da (kafiran Makka) suke faɗa; kuma kai ba mai tilasta musu ba ne; saboda haka sai ka yi wa’azi da Alƙur’ani ga wanda yake tsoron azabata. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya saurara ya ji labarin abubuwan ban tsoro da firgici da za su faru ranar da mai kira, watau mala’ikan da aka wakilta domin busa ƙaho, zai yi kira daga wani wuri makusanci, zai kuma yi busa ta biyu wadda duk halittu za su ji tsawarta da gaskiyar da babu kokwanto a cikinta; to wannan ranar ita ce ranar fitowar matattu daga ƙaburburansu domin yi musu hisabi da sakamako. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, shi ne kaɗai mai rayawa mai kashewa, babu mai iya waɗannan ayyuka sai shi, don haka gare shi ne kaɗai makomar bayi take, watau ranar alƙiyama domin hisabi da sakamako. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, a ranar ne ƙasa za ta tsattsage wa ɗaukacin halittun da ke kwance cikinta, sai su fito daga ƙaburburansu cikin gaggawa, Allah ya tattara su gaba ɗayansu wuri guda domin yi musu hisabi. Allah kuma ya tabbatar musu da cewa wannan tattarawar a wurinsa abu ne mai sauƙi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙara lallashin Manzonsa game da baƙaƙen maganganu da yake ji daga bakunan mushirikai da cewa, kada wannan ya tayar masa da hankali, Allah yana sane da duk irin maganganun da suke faɗa masa na ɓatanci, don haka ba za su kuɓuce masa ba, shi dai Manzon Allah (ﷺ) kawai ya ci gaba da yi musu wa’azi cikin ruwan sanyi, kuma ba a ɗora masa alhakin ya tilasta musu yin imani ba, shi dai ya ci gaba da yin wa’azi da Alƙur’ani ga duk mai tsoron azabar Allah (Mai tsarki da daukaka) domin mai jin tsoron Allah ne kawai yake wa’azantuwa da abin da ake karanta masa na Alƙur’ani.