الذاريات
Adh-Dhaariyat
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلذَّٰرِيَٰتِ ذَرۡوٗا
Open ayah 51:1Na rantse da iskoki masu ta da ƙura.
فَٱلۡحَٰمِلَٰتِ وِقۡرٗا
Open ayah 51:2Sannan da (giragizai) waɗanda suke ɗauke da nauyin ruwa.
فَٱلۡجَٰرِيَٰتِ يُسۡرٗا
Open ayah 51:3Da jiragen ruwa masu gudu a sauƙaƙe.
فَٱلۡمُقَسِّمَٰتِ أَمۡرًا
Open ayah 51:4Da kuma mala’iku masu raba abubuwa.
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٞ
Open ayah 51:5Lalle abin da ake yi muku alƙawarinsa tabbas gaskiya ne.
وَإِنَّ ٱلدِّينَ لَوَٰقِعٞ
Open ayah 51:6Kuma lalle sakamako tabbas mai afkuwa ne.
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡحُبُكِ
Open ayah 51:7Na rantse da sama ma’abociyar hanyoyi.
إِنَّكُمۡ لَفِي قَوۡلٖ مُّخۡتَلِفٖ
Open ayah 51:8Lalle ku (mutanen Makka) tabbas kuna cikin magana mai sassaɓawa.
يُؤۡفَكُ عَنۡهُ مَنۡ أُفِكَ
Open ayah 51:9Ana karkatar da wanda aka karkatar daga gare shi (Annabi ko Alƙur’ani).
قُتِلَ ٱلۡخَرَّٰصُونَ
Open ayah 51:10An la’anci maƙaryata.
ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي غَمۡرَةٖ سَاهُونَ
Open ayah 51:11Waɗanda suke rafkanannu a cikin jahilci.
يَسۡـَٔلُونَ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Open ayah 51:12Suna tambayar yaushe ne ranar sakamako?
يَوۡمَ هُمۡ عَلَى ٱلنَّارِ يُفۡتَنُونَ
Open ayah 51:13A ranar da su za a azabtar da su kan wuta.
ذُوقُواْ فِتۡنَتَكُمۡ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تَسۡتَعۡجِلُونَ
Open ayah 51:14(A ce da su): “Ku ɗanɗani azabarku, wannan shi ne abin da kuka kasance kuna neman gaggautowarsa.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da jerin rantse-rantse da wasu daga cikin halittunsa masu muhimmanci da amfani a rayuwar bayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rantse da iskoki masu ta da ƙura da giragizai da jiragen ruwa masu gudu a sauƙaƙe a cikin kogi da mala’iku masu rarraba abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su su raba na al’amuran bayinsa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana dalilin waɗannan rantse-rantse nasa, wanda shi ne don tabbatar da cewa, lalle abin da yake yi wa mushirikai alƙawarin faruwarsa na hisabi da sakamako gaskiya ne babu kokwanto a kansa. Kuma lalle sakamakon bayi a ranar alƙiyama mai aukuwa ne ba makawa. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake rantsuwa da sama mai kyakkyawar halitta, ma’abociyar hanyoyi, domin ya tabbatar wa mutanen Makka cewa, suna cikin maganganu masu sassaɓawa da suke cike da tubka da warwara game da Annabi (ﷺ) da Alƙur’ani; wani lokaci su ce matsafi ne, Alƙur’ani kuma tsafi ne; wani lokaci kuma sai su ce masa mawaƙi Alƙur’ani kuma waƙa ce; a wani lokaci kuma sai su kira shi da boka ko mai taɓin hankali. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ana karkatar da wanda aka karkatar daga yin imani da Alƙur’ani da Annabi (ﷺ), domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya riga ya san cewa da ma can ba zai yi imani ba, ba kuma zai dace da shiriya ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamakon maƙaryata waɗanda suke ta sharara ƙarya game da Annabi (ﷺ) da Alƙur’ani, da cewa an la’ance su an nesanta su daga samun rahamar Allah, domin kuwa su mutane ne rafkanannu cikin jahilci kuma ba sa tuna lahira, ba su damu da ita ba, har ma suna ganin ƙarya ce ba gaskiya ba, suna tambayar Annabi (ﷺ) da muminai cewa, wai yaushe ne ma ranar sakamako za ta zo? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya mayar musu da martani cewa, a ranar ne za a azabtar da su a cikin wutar Jahannama, ana ce musu su ɗanɗani azabarsu, wannan ita ce ranar da koyaushe ake tsoratar da su ita, kuma suke gaggauto da zuwanta don nuna izgili da shaƙiyanci.
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّٰتٖ وَعُيُونٍ
Open ayah 51:15Lalle masu taƙawa suna cikin gidajen Aljanna da idanuwan (ruwa).
ءَاخِذِينَ مَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُحۡسِنِينَ
Open ayah 51:16Suna masu kwasar abin da Ubangijinsu Ya ba su. Lalle su sun zamanto kafin wannan (ranar) masu kyautata ayyuka ne.
كَانُواْ قَلِيلٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مَا يَهۡجَعُونَ
Open ayah 51:17Sun kasance kaɗan ne na dare suke bacci.
وَبِٱلۡأَسۡحَارِ هُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ
Open ayah 51:18A gefin asuba kuma su suna neman gafara.
وَفِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ
Open ayah 51:19A cikin dukiyoyinsu kuma akwai wani haƙƙi na mai bara da mai kamewa daga yin ta.
وَفِي ٱلۡأَرۡضِ ءَايَٰتٞ لِّلۡمُوقِنِينَ
Open ayah 51:20A cikin ƙasa kuma akwai ayoyi ga masu sakankancewa.
وَفِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ
Open ayah 51:21Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?
وَفِي ٱلسَّمَآءِ رِزۡقُكُمۡ وَمَا تُوعَدُونَ
Open ayah 51:22A cikin sammai kuma akwai arzikinku da kuma abin da aka yi muku alkawarinsa.
فَوَرَبِّ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ إِنَّهُۥ لَحَقّٞ مِّثۡلَ مَآ أَنَّكُمۡ تَنطِقُونَ
Open ayah 51:23To na rantse da Ubangijin sammai da ƙasa, lalle shi (abin da ake yi muku gargaɗinsa) tabbas gaskiya ne kamar dai yadda kuke yin magana. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci masu kiyaye dokokinsa da bin umarninsa da guje wa haninsa, ya bayyana gwaggwaɓan sakamakonsu a ranar alƙiyama inda zai saka musu da gidajen Aljanna waɗanda idanuwan ruwa suke gudana a cikinsu. Za su riƙa kwasar ni’imomin da ya ba su a Aljanna suna masu gamsuwa da su, domin sun kasance tun a duniya masu kyautata ibadarsu ne ga Allah, suna bauta masa kamar suna ganin sa, sun kuma tabbatar idan ba sa ganin sa to shi yana ganin su, suna kuma kyautata wa bayinsa da duk wani nau’i na kyautatawa. Daga cikin kyautata ibadarsu ga Allah kuwa sun kasance masu yawaita sallolin dare ne, ba sa yin bacci sai ɗan lokaci ƙanƙani, da zarar kuma sun fuskanci asuba ta kawo kai sai su shiga yin istigfari suna neman gafarar Allah game da laifukansu da kasawarsu. An karɓo daga Abdullahi ɗan Salam (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane, ku yaɗa sallama, kuma ku ciyar da abinci, ku kuma sa da zumunci, ku yi salla cikin dare yayin da mutane suke bacci, za ku shiga Aljanna da aminci.” [Tirmizi #2485 da Darimi #1501 da Ibn Majah #1334]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana yadda waɗannan bayi nasa masu taƙawa suke kyautata wa bayinsa, domin sun san cewa a cikin dukiyoyinsu akwai wani haƙƙi da suke fitarwa don su ba wa mabuƙata, mai bara daga cikinsu ko mai kamewa ba ya roƙon kowa duk kuwa da buƙatarsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana ayoyinsa na sama da na ƙasa masu tabbatar da cikar Ƙudurarsa da ikonsa. Waɗannan ayoyi kuwa su ne, waɗancan bayin nasa koyaushe suke la’akari da su suna ƙara musu yaƙini da sakankancewa da alƙawarin Allah. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a ƙasa da abubuwan da ta ƙunsa na duwatsu da koguna da ƙoramu da bishiyoyi da tsirrai da dabbobi da sauransu, dukkansu akwai ƙwararan ayoyi masu nuna girman Ƙudurar Allah da tabbatar da cewa, shi ne mahaliccin da ya ƙagi duk wata halitta. Wannan yana ƙara wa bayinsa nagari yaƙini. Hakanan ya bayyana cewa, a tare da halittar mutane su kansu akwai ayoyi masu ɗimbin yawa da suke tabbatar da Kaɗaitakarsa da Ƙudurarsa, don haka ya ja hankalin mutane da cewa, me ya sa ba sa lura ne su gani don su ɗau izina? Ya kuma bayyana cewa, a cikin sama akwai arzikin da ya tanadar wa halittunsa, arzuki na duniya da na addini, domin daga nan ne ake saukar da sinadarin samun kowane arziki na duniya, watau ruwan sama; daga nan ne kuma wahayi wanda shi ne arziki na addini yake saukowa ta hanyar mala’ika. Hakanan daga sama ne abin da ake yi musu alƙawarinsa na alheri ko na sharri yake saukowa. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa da Zatinsa; watau zamantowarsa Ubangijin sama da ƙasa don ya tabbatar da cewa, tashi bayan mutuwa gaskiya ne babu kokwanto a cikinsa, kamar yadda mutane ba sa kokwanton maganar da ke fitowa daga bakunansu.
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ
Open ayah 51:24Shin labarin baƙin Ibrahimu masu girma ya zo maka?
إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ
Open ayah 51:25Lokacin da suka shiga wurinsa sai suka ce: “Muna maka sallama;” ya ce: “Aminci ya tabbata gare ku, (ku) mutane ne da ba sanannu ba.”
فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجۡلٖ سَمِينٖ
Open ayah 51:26Sai ya saɗaɗa da sauri zuwa ga iyalinsa, sai ya zo da wani ɗan maraƙi mai mai.
فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيۡهِمۡ قَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ
Open ayah 51:27Sai ya kusanta shi gare su, ya ce: “Yanzu ba za ku ci ba?”
فَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ
Open ayah 51:28(Da suka ƙi ci) sai ya tsorata da su, suka ce: “Kada ka tsorata;” suka kuma yi masa albishir da samun yaro mai ilimi.
فَأَقۡبَلَتِ ٱمۡرَأَتُهُۥ فِي صَرَّةٖ فَصَكَّتۡ وَجۡهَهَا وَقَالَتۡ عَجُوزٌ عَقِيمٞ
Open ayah 51:29Sannan sai matarsa ta gabato su cikin wata ƙara, sai ta mari fuskarta ta ce: “Yanzu tsohuwa bakarara (ita ce za ta haihu?)”
قَالُواْ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡعَلِيمُ
Open ayah 51:30Suka ce, “Kamar haka Ubangijinki Ya ce, lalle Shi Mai hikima ne, Masani.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba wa Annabinsa Muhammadu (ﷺ) labarin wasu baƙin mala’iku waɗanda suka zo wa Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a siffar mutane, ya kuma karrama su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, lokacin da suka isa gidan Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun yi masa sallama bayan sun shiga, shi kuma ya mayar musu da mafi kyan sallama, to amma sai a ransa ya ce: Waɗannan mutane ne da ba mu san su ba. Sai ya saɗaɗa a ɓoye da sauri zuwa ga iyalansa ya zo musu da wani gasasshen ɗan maraƙi mai mai, yana zaton su mutane ne. Sai ya kusantar da gasasshen ɗan maraƙin gare su yana yi musu tayin su ci tare da tambayar su ko ba za su ci ba ne? Yayin da ya kula hannnayensu ba sa isa wurin wannan abincin sai ya tsorata da su, sai su kuma da suka kula da ya tsorata da su sai suka kwantar masa da hankali da cewa, kada ya ji tsoro; su mala’iku ne, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko su don su hallaka mutanen Annabi Luɗu waɗanda suka ƙi yin imani da shi. Sannan suka yi masa albishir da samun ɗa mai ilimi, watau Annabi Is’haƙa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Matarsa Saratu tana jin wannan albishir sai ta nufo su da sauri tana sowa, saboda farin ciki, har tana marin kanta, tana cewa, ita fa tsohuwa ce kuma bakarara ba ta haihuwa, to ta yaya za ta sami ɗa, ga shi shekarunta da na mijinta Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sun ja sosai? Sai mala’ikun nan suka tabbatar mata da cewa, kamar haka dai Ubangijinta Allah ya ƙaddara, don haka babu abin da zai hana faruwarsa, domin shi mai hikima ne cikin duk halittarsa, mai kuma cikakken ilimi ne, ya san duk wani abu da ya shafi halittunsa.
۞قَالَ فَمَا خَطۡبُكُمۡ أَيُّهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Open ayah 51:31(Ibrahimu) ya ce: “To me yake tafe da ku, ya ku waɗannan manzanni?”
قَالُوٓاْ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمٖ مُّجۡرِمِينَ
Open ayah 51:32Suka ce: “Lalle mu an aiko mu ne zuwa ga wasu mutane masu manyan laifuka.
لِنُرۡسِلَ عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن طِينٖ
Open ayah 51:33“Don mu zuba musu ƙonannun duwatsu na taɓon (wuta).
مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُسۡرِفِينَ
Open ayah 51:34“Waɗanda aka yi wa alama daga wurin Ubangijinka saboda maɓarnata.”
فَأَخۡرَجۡنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 51:35Sai Muka tserar da duk wanda ya kasance a cikinta (alƙaryar) daga muminai.
فَمَا وَجَدۡنَا فِيهَا غَيۡرَ بَيۡتٖ مِّنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Open ayah 51:36Sai ba mu sami wani (gida) a cikinta ba in ban da gida ɗaya na Musulmi.
وَتَرَكۡنَا فِيهَآ ءَايَةٗ لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ
Open ayah 51:37Muka kuma bar aya ta wa’azi a cikinta ga waɗanda suke tsoron azaba mai raɗaɗi. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fahimci cewa waɗannan fa ba mutane ne ba, mala’iku ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko su, sai ya tambaye su, me yake tafe da su? Sai suka amsa masa da cewa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko su ne zuwa ga wasu mutane masu miyagun laifuka, watau mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), domin su sakar musu daskararren taɓo na wuta, wanda aka yi wa alama daga Allah (Mai tsarki da daukaka) domin hallaka mutanen da suka wuce iyaka wajen aikata laifuka. To a nan ne Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya shiga jayayya da su don yana son a janye musu wannan azabar, amma aka faɗa masa cewa, ya fita daga wannan maganar, al’amarin Allah ya riga ya zo, babu abin da zai tsai da shi. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fitar da duk wani mumini daga cikin wannan gari na Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) don kada wannan azaba ta shafe su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fita shi da ilahirin iyalan gidansa cikin dare, matarsa ce kaɗai wadda ba za ta kai labari ba, domin ita tana cikin waɗanda za su hallaka saboda kafircinta. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, gida ɗaya ne kawai na Musulmi aka samu a wannan gari, shi ne gidan Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) sauran gidajen duk Allah ya hallaka su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya bar aya ta wa’azi na guraben azabar da ta sauko wa wannan garin, domin ya zama abin izina ga waɗanda suke jin tsoron azaba mai raɗaɗi, don su guji aikata irin waɗannan munanan ayyuka.
وَفِي مُوسَىٰٓ إِذۡ أَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ
Open ayah 51:38Game da Musa kuma (akwai aya), lokacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir’auna da hujjoji bayyanannu.
فَتَوَلَّىٰ بِرُكۡنِهِۦ وَقَالَ سَٰحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٞ
Open ayah 51:39Sai ya ba da baya shi da ƙarfin rundunarsa, ya kuma ce: “(Musa) mai sihiri ne ko mahaukaci.”
فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٞ
Open ayah 51:40Saboda haka Muka kama shi tare da rundunarsa, sai Muka watsa su a cikin kogi, alhali yana mai aikata abin Allah-wadai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya aika Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) zuwa ga Fir’auna da hujjoji bayyanannu waɗanda suke tabbatar da gaskiyar manzancinsa, kamar sandarsa da hannunsa mai haske, to amma sai Fir’auna ya bijire wa gaskiya ya ƙaryata Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya riƙa tinƙaho da ƙarfin mulkinsa da rundunarsa, ya ƙi ya ɗauki darasi daga al’ummun baya da Allah ya hallaka. Ya shiga tuhumar Annabi Musa da cewa shi matsafi ne kawai da yake ruɗar mutane da tsafinsa, ko kuma ma mai taɓin hankali ne bai san abin da yake faɗa ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya damƙi Fir’auna shi da rundunarsa gaba ɗaya ya nutsar da su a cikin ruwa duk suka hallaka alhalin Fir’auna ya zo da abin Allah-wadai, abin assha, watau da’awar allantaka da ƙaryata Annabi Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
وَفِي عَادٍ إِذۡ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلرِّيحَ ٱلۡعَقِيمَ
Open ayah 51:41Kuma game da Adawa (akwai aya), lokacin da Muka aiko musu da iska marar alhairi.
مَا تَذَرُ مِن شَيۡءٍ أَتَتۡ عَلَيۡهِ إِلَّا جَعَلَتۡهُ كَٱلرَّمِيمِ
Open ayah 51:42Ba ta barin wani abu idan ta biyo ta kansa sai ta mayar da shi kamar daddagagge ƙashi.
وَفِي ثَمُودَ إِذۡ قِيلَ لَهُمۡ تَمَتَّعُواْ حَتَّىٰ حِينٖ
Open ayah 51:43Kuma game da Samudawa (akwai aya), lokacin da aka ce da su: “Ku ji daɗi zuwa wani ɗan lokaci.”
فَعَتَوۡاْ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ وَهُمۡ يَنظُرُونَ
Open ayah 51:44Sai suka yi tsaurin kai game da umarnin Ubangijinsu, saboda haka tsawa ta faɗa musu alhali kuwa suna kallo.
فَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ مِن قِيَامٖ وَمَا كَانُواْ مُنتَصِرِينَ
Open ayah 51:45To ba su sami damar tsayuwa ba, kuma ba su zamanto masu taimaka wa (junansu) ba.
وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Open ayah 51:46Kuma (Mun hallakar da) mutanen Nuhu a gabaninsu; don kuwa lalle sun kasance mutane ne fasiƙai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da kawo ƙissoshin al’ummun da suka gabata waɗanda ya hallaka su yayin da suka ƙaryata annabawansu, don hakan ya zama aya ga masu jin tsoron azabarsa mai raɗaɗi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ambaci labarin Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda suka ƙaryata Manzonsu Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu wata bakararar iska wadda babu alheri a cikinta ko kaɗan wadda ba abin da za ta biyo ta kansa na mutum ko dabba ko dukiya sai ta yi rugurugu da shi ta mayar da shi kamar daddagaggen ƙashi. Sannan da Samudawa waɗanda suka ƙaryata Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka cutar da taguwarsa bayan an ja musu kunne, don haka su ma aka ba su wa’adin kwana uku su ji daɗin rayuwarsu a cikinsu aka hallaka su. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, sun yi tsaurin kai game da umarnin Ubangijinsu suka ƙi yin imani da yi wa Annabi Salihu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) biyayya, saboda haka azabar tsawa ta auka musu suna kallo amma ba yadda za su iya kauce mata har suka hallaka gaba ɗayansu. Sai kuma mutanen Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) waɗanda sun gabaci Adawa da Samudawa, su ma sun ƙaryata Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), don haka Allah ya dulmiyar da su a ruwa, domin sun tabbata mutane ne fasiƙai da suke bijire wa Allah da Manzonsa Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
وَٱلسَّمَآءَ بَنَيۡنَٰهَا بِأَيۡيْدٖ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ
Open ayah 51:47Sama kuma Mun gina ta da ƙarfi, lalle kuma Mu tabbas Masu yalwatawa ne.
وَٱلۡأَرۡضَ فَرَشۡنَٰهَا فَنِعۡمَ ٱلۡمَٰهِدُونَ
Open ayah 51:48Ƙasa kuma Muka shimfiɗa ta, to madalla da Masu shimfiɗar.
وَمِن كُلِّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَا زَوۡجَيۡنِ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Open ayah 51:49Daga kowane abu kuma Mun halicci nau’i biyu, don ku wa’azantu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wasu manyan ayoyi guda uku waɗanda suke tabbatar da samuwarsa da Kaɗaitakarsa. <b>Ta farko </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, shi ne ya gina sama ya kuma inganta gininta da ƙarfin ikonsa ta zama kamar rufi ga ƙasa da abin da yake kanta. Sannan ya tabbatar da cewa, shi ne mai yalwatawa; yana yalwata sassan sammai da duk halittun da suke cikinsu da arziki wanda yake wadatacce. <b>Ta biyu </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, shi ne ya shimfiɗa ƙasa domin halittunsa su ji daɗin rayuwa a kanta, ta zame musu kamar shimfiɗa. Sai ya yabi kansa da cewa ‘madalla da masu shimfiɗar’, watau yana nufin shi kansa. <b>Aya ta uku </b>, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ya halicci kowane abu nau’i bibbiyu, kamar namiji da mace da sama da ƙasa da tudun ƙasa da ruwa, ya yi haka ne kuma don mutane su wa’azantu, su faɗaku da ganin ni’imomin Allah daban-daban waɗanda suke nuna cikar Ƙudurarsa.
فَفِرُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 51:50To ku gudo zuwa ga Allah, lalle ni mai gargaɗi ne game da Shi, mai bayyana (gargaɗi).
وَلَا تَجۡعَلُواْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ
Open ayah 51:51Kada kuma ku sanya wani abin bauta tare da Allah; lalle ni mai gargaɗi ne game da Shi, mai bayyana (gargaɗi) A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci bayinsa da su gudu zuwa gare shi, watau su guje wa azabarsa zuwa ga kyakkyawan sakamakonsa ta hanyar komawa gare shi da yi masa biyayya da guje wa saɓa masa. Sannan ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya faɗa wa mutane cewa shi mai gargaɗi ne mai bayyana gargaɗinsa gare su don su guje wa uƙubar Allah (Mai tsarki da daukaka). Sai kuma ya bayyana musu babban abin da za su yi na komawa zuwa ga Allah (Mai tsarki da daukaka), shi ne su guji riƙon duk wani abin bauta ba Allah ba; ya sake tabbatar musu cewa, shi fa mai gargaɗi ne mai bayyana gargaɗinsa gare su.
كَذَٰلِكَ مَآ أَتَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُواْ سَاحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٌ
Open ayah 51:52Kamar haka abin yake, ba waɗanda wani manzo ya zo musu a gabaninsu (mutan Makka) sai sun ce mai sihiri ne ko mahaukaci.
أَتَوَاصَوۡاْ بِهِۦۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٞ طَاغُونَ
Open ayah 51:53Shin wasiyya suke yi wa junansu ne game da shi? A’a, su dai mutane ne masu ƙetare iyaka.
فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ فَمَآ أَنتَ بِمَلُومٖ
Open ayah 51:54Sai ka rabu da su, don kuwa kai ba abin zargi ba ne.
وَذَكِّرۡ فَإِنَّ ٱلذِّكۡرَىٰ تَنفَعُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Open ayah 51:55Kuma ka yi wa’azi, don ko lalle wa’azi yana amfanar muminai. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mushirkan Makka da suke ƙaryata Manzon Allah (ﷺ) ba su ne farau ba. Irin wannan ƙaryatawar waɗanda suka gabace su ma sun ƙaryata annabawansu, domin duk sa’adda wani manzo ya zo musu daga Allah sai su ce shi mai sihiri ne ko mahaukaci. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, shin wannan ƙazafi da suke yi wa manzannin Allah wai wata wasiyya ce suka yi wa junansu, watau na farko suka yi wa na baya? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, ba wata wasiyya a tsakaninsu, su dai kawai mutane ne masu ɗagawa da ƙetare iyaka. Watau dukkansu ɗagawarsu ta sanya su ƙaryata manzannin Allah da yi musu ƙazafi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da cewa ya rabu da su, ya kawar da kansa daga duk wani izgilinsu, shi dai ya isar musu da saƙon da aka aiko shi da shi, don haka shi ba wanda za a zarge shi ne da ɓoye saƙon da aka aiko shi da shi ba. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa cewa kawar musu da kai ba ya nufin ya daina yi musu wa’azi, a’a, ya ci gaba da yin wa’azinsa da tunatarwa domin lalle wa’azi yana amfanar muminai.
وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ
Open ayah 51:56Ban halicci mutum da aljan ba sai don su bauta min.
مَآ أُرِيدُ مِنۡهُم مِّن رِّزۡقٖ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطۡعِمُونِ
Open ayah 51:57Ba Na neman wani arziki a wurinsu, kuma ba Na neman su ciyar da Ni.
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ
Open ayah 51:58Lalle Allah Shi ne Mai arzutawa, Mai tsananin ƙarfi.
فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذَنُوبٗا مِّثۡلَ ذَنُوبِ أَصۡحَٰبِهِمۡ فَلَا يَسۡتَعۡجِلُونِ
Open ayah 51:59To lalle waɗanda suka zalunci (kansu) suna da wani kaso na azaba kamar kason abokansu, saboda haka kada su nemi gaggauto shi.
فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن يَوۡمِهِمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ
Open ayah 51:60To tsananin azaba ya tabbata ga waɗanda suka kafirta a ranar da ake alƙawarta musu. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana babbar manufar halittar mutane da aljannu, watau shi ne su bauta masa kada su haɗa komai da shi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ba ya neman wani arziki daga halittarsa, kuma ba ya neman su ciyar da shi, domin shi mawadaci ne ta kowace fuska; mutane da aljannu da duk sauran halittu su ne suke da buƙata a wurinsa, don haka shi ne mai arzuta bayinsa kuma mai tsananin ƙarfi wadda babu mai iya ja da shi, mutum da aljan duka dole su rusuna wa ƙarfinsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, waɗanda suka ƙaryata Manzonsa (ﷺ) sun zalunci kansu da kansu, kuma su sani tabbas za su ɗanɗani kuɗarsu, domin suna da kasonsu na azaba da aka tanadar musu irin yadda aka tanadar wa kafiran farko nasu kasonsu na azaba; to su daina neman a gaggauto musu da shi wai don suna zaton ƙarya ne, su sani yana da ƙayyadadden lokaci da Allah ya ajiye masa; idan lokacinsa ya zo babu mai iya kuɓutar da su, don haka tsananin azaba ya tabbata ga mutanen da suka kafirce wa Allah, kuma suka ƙaryata Manzonsa a ranar alƙiyama wadda ake yi musu alƙawarin zuwanta.